*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[37➖38]_*
..............Da sauri Umma ta sha gaban Abba dake nufar Jiddah tamkar wani bajimi, ture Ummar yayi yasaka k'afa ya tad'e Jiddah dake Neman guduwa.
Fad'uwa tayi k'asa akan hannunta, dan haka ta fashe dakuka saboda zafin daya ratsata.
Waya ya jefa Mata, “'Dauki wayar nan kikira Wanda aka d'aura miki aure dashi yanzunan kice ya sakeki”.
Kuka Jiddah takuma fashewa dashi, ta d'auki wayar ta rik'e, da sauri Umma ta kwace tana fad'in “Bazata kirashinba, Kai mizai hanaka kiranshi kace ya saketan?”.
“Yagana! Yagana!! Kina shigarmin hanci da yawafa”.
“To mizai hana ka fyatoni ka huta, wlhy wannan karon duk abinda zakayi sai dai kayi amma bazan d'auki wannan masifar ba.......”
A fusace ya d'aga hannu zai Mari Umma
“Wlhy karka sake ka ta6ata!!”. ‘Yaruwaiya dasuka shigo yanzu babu dad'ewa tafad'a a matuk'ar tsawace, dan sunji mafi yawan abinda ke faruwa’.
Cak Abba ya dakata, bai marentanba baikuma sauke hannunsa ba.
Zarah da Balu sukazo suka d'aga Jiddah dake kuka zaune, hannunta harya fara kumbura alamar taji ciwo. Itama Yaruwaiya zuwa tai ta janye hannun Umma suka bar Abba a wajen, yakasa motsi balle dogon tari.
Hayawaye kawai Umma taji sun gangaro Mata, duk k'ok'arinta Na 6oye mugayen halayyar Abba ga danginta yau sai da ya tonama kansa asiri, shekaru ashirin suna tare bata ta6a Kai k'ararsa wajen iyayentaba idan yamata Abu, aganinta hakuri shine maganin komai, sannan yawan Kai k'arar miji gidanku ko gidansu tamkar zubarwa da kanku darajane, dan iyayenka zasu rage ganin darajarsa, idan kuma iyayensane suma zasu rage ganin darajarka.
Zarah da Jiddah ma hawaye suketayi, ga hannunta dake Mata azabar zogi, shiru babu Wanda ya iya cewa uffan a cikinsu, kowa da abinda zuciyarsa take sak'awa.
A tsakar gida kam kwafa Abba yayi yafita yanamai jin haushin Yaruwaiya, amma ko giyar wake yasha bai isa cigaba da abinda yay niyyaba, dan Yaruwaiya ba kanwar lasa baceba, kad'an daga aikints ta ketashi gaban y'ay'ansa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tuni zufa ta jik'e hajia Hindu saboda azabar da k'afarta kemata, k'arar data kwallane yasaka kalifa zuwa d'akin.
“Momy miya sameki?”.
“Kalifa Abbanku ne ya karyamin k'afa”. Tafad'a cikin jin azaba. Gabanta yazo ya zube yana Kama k'afar dahar tafara kumbura, “Momy mikikai masa yay miki haka?”.
“Babu abinda nai masa kalifa, dan kawai Na fad'a masa gaskiyane”.
“Kiyi hak'uri Umma ALLAH ya saka miki, bara Na Kira direba mukaiki asibiti.
Da k'yar Kalifa ya iya taimakama Hindu tafito suka shiga mota, Wanda aka aiko daga makarantar su kalifa danyaje da Abba ganin yanda jama'ar gidan suke kamar a tashin hankali saiya sulale ya koma makaranta Kai rahoto.
A asibiti kam anduba hajia Hindu data samu targad'e a k'afa, nanda akaimata gyaran datasha azaba. Magunguna aka bata suka dawo gida.
Saidaifa a k'asan zuciyarta tanajin bazata bar abinda Abba yay mata yatafi a banzaba, dolene saita rama wlhy. Tana zaune afalo tana cika da batsewa Abba ya shigo, harara tashiga watsa masa, amma ko kallon inda take baiyiba yay shigewarsa d'akinsa zuciyarsa nacigaba da tafasa, shi yanzu a ina zai samo wad'annan kud'ad'en yabama Alhaji garba? Kodai shawarar Hajia Hindu zaibi yabashi Zarah? To amma kuma shi Alhaji garban zai amince ne?, kansa yadafe cikin matsananciyar damuwa, gaba d'aya yama rasa miya dace yayine?. Yana cikin wannan halin wayarsa tashiga ruri, sharewa yayi tamkar bazai d'aukaba, saikuma yaja tsaki yana fisgo wayar saikace itace tai masa laifin.
Daga makarantar su kalifa ne, a fusace ya d'aga, ko sauraren sallamar da akai masa baiyiba yace, “Minene?”.
“Babu komai Alhaji, akan maganar yaronkane da muka turo da d'an rakiya, yadawo mana babu Kai babu yaron kuma”.
“Kaga da ALLAH karku dameni, harma nawa kalifa yake dazai zauna fad'a dawani akan mace, nifa banason sharri, suje can sunema Wanda ya fasama d'ansu kai, Mtsoww aikin banza kawai”. K'itt ya yanke wayar.
Yin haka dakamar mintuna talatin saiga mai gadi yashigo wai ga y'an sanda sunason ganin Alhaji.
Da mamaki Hajia Hindu dake tule a zaune tace, “Y'an sanda kuma? To miya faru to?”.
“Wlhy hajia bansaniba”.
Kalifa ta kwalama Kira, yafito yana kumbura baki da k'unk'unin antasoshi yana hutawa, “Kaje kakira Abbanku yayi bak'i kazonan kana cunomin baki”.
Tafiya yay d'akin Abba yana mangara Kai dacigaba da k'unk'uninsa. Babu jimasa suka fito tare, yanzuma Abba baiko kalli hajia Hindu ba yafice kalifa Na biye dashi.
Koda suka fito kalifa yaga y'an sanda da Baban yaron dasukayi fad'a saiya juya zai gudu cikin gida, amma d'an sanda d'aya yay ram dashi.
Haukace musu Abba yayi da masifa, ko kad'an basu saurareshiba suka tafi da Kalifa dake kuka. Hajia Hindu ma data rarrafo danjin masifar Abba da kukan kalifa kukan ta sanya tana rok'onsu su dawo Mata da yaronta, amma kobi takantama basuyiba.
Abifa yayma Abba yawa🙆🏻😝.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau Aliyu a masallacin k'ofar gidansu yay sallar magriba saboda akwai majalisi da sukan shirya Na k'arshen kowane wata da akan gabatar bisa tsarin malam.
Masallacin yacika taf da magidanta, samari, harma da tsofaffi, Ana idar da sallar isha'i Sheikh Aliyu yafara gudanar da wa'azi mai taken *DAMI MUKA SHIRYA TAFIYA LAHIRA?* , masallacin yayi tsait, daga muryar malam mustafa dake jan bak'i saikuma Sheikh Aliyu dake fassara cikin tsantsar ilimi da kuma fad'ad'a kowace aya domin a fahimta, lokaci-lokaci mutane kanyi kabbara, jikinsu dukyayi sanyi saboda tsoro, har zuwa k'arfe goma da rabi aka fara karanto tambayoyi.
Kafin yabada amsar tambayar farko yacire gilas d'in idonsa yana gogewa da handky d'in hannunsa, cikin sanyin nan nasa yace, “Amin afuwa Zan amsa tambaya uku ne kacal acikin wad'annan tambayoyin, dan akwai tambayar danake da burin amsata anan wadda wani bawan ALLAH ya turomin, to Alhmdllh yace shi ma'abocin zuwa wannan masallacinne, sannan kuma wannan zaman baya wucesa aduk wata, to tambayarsa tanada muhimmancin data shafemu muduka, shiyyasa naza6i amsata anan domin mu farka daga sakacinmu, sauran tambayoyi kuma insha ALLAH zamu tsara yanda za a amsasu koda daga bayane”.
Take kowa ya aminta da batunsa, dan haka malam mustafa ya karanto tambayoyi uku kacal Aliyu yabada amsarsu daganan Yakoma kan Sak'on da Maimunatu ta sanarmasa d'azun da safe.
Saida ya maida siririn farin gilas d'insa sannan yace, “Mai sak'on yana magana ne akan matsala dayake fuskanta gameda rayuwar aure tsakaninsa da iyalansa irinta rauni wajen biyamusu buk'ata a shimfid'a, amma dukda yasan da hakan yaje Yakuma k'ara aure batareda yatashi yafara Neman maganiba. Lallai wannan sakacine mai girma, sannan akwai cutarwa ga iyalanka, tayaya baka iya gamsar da mace d'ayaba sannan kakuma tarkato ta biyu? Sannan babu wani mataki Daka d'auka akan hakan kafin ka k'aro d'in?, tayaya muke tunanin Matsaloli bazasu k'aruba?, ayanzu dukanku nan dazance wanene *Jarumin Namiji?* saikucemin Wanda ya iya rik'e gidansa daci da sha dadai buk'atu nayau da kullum ko?”.
Atake suka bashi amsa da eh.
Aliyu yay murmushi yana gyara zamansa, batareda ya kallesuba yace, “To lallai wannan bazamu kirashi cikakken jarumi ba gaba d'aya, sai dai dolene mu yaba masa wajen sauke nauyin dake kansa na wani 6angaren hak'k'ok'in aure. Jarumin namiji shine mai k'ok'arin tsare dukkan wani hak'i na iyalansa, ci, sha, sutura, wajen zama, ya kula da addinin iyalinsa, yakula da zamantakewarta da makwafta da zumincinta ta 6angaren danginta da danginsa, ya nuna mata soyayyar dazata saka zuciyarta kwanciya waje d'aya batareda y'an wasan kwaikwayo da jaruman littafi na birgetaba, a wajen shimfid'a yazama Oga kwata-kwata yanda za'a ringa kiransa maigida cikeda tsantsar girmamawa, ba yana magana ana kauda Kai da murgud'a bakiba”.
Dariya suka Sanya, yayinda shima Aliyu yake darawa da kare fuskarsa da hannu.
“ALLAH kuwa karkiji wasa, duk k'ok'arin mace wajen iya girki, tsafta da kwalliya daduk wata kisisina inhar batada nagartar kar6ar mijinta a shinfid'a zakaga Mijin baya kallonta da daraja, kuma duk yawan son da yake mata saiya gudu kaga babu komai, saigaka tarasa kansa, takuma rasa ina matsalar takene?. To haka shima namiji duk k'ok'arinsa na karema mace hak'k'ok'inta inhar bashida jarumtar biya mata buk'ata to wlhy zata daina ganin darajarsa da shakkar fad'a masa duk maganar datazo bakinta, da yawan rainin da matayenmu ke mana tushensa shine ragwantakarmu a shinfid'a, kabari basir da sanyi sun gama cinyeka amma kullum idonka nakan y'ay'an mutane, da yarinya tawuce kashiga lasar la66a da had'iye yawu kana mata kallon da addini ya haramta maka, amma matarka dake gidama baka iya biya mata 6uk'ata yanda ya kamata. Akulum matayenmu sunada k'ok'arin gyaran Kansu a kanmu, dan a hasashe babu wanda yakai matanmu k'ok'arin shaye-shayen magungunan nan na k'arin Ni'ima, dukda suma matan ina k'alubalantarsu dan basabin matakan daya dace wajen shan maganin. A mashayinka namai gida daga lokacin da kukai shekaru biyu da aure da matarka yadace kafara neman gyara kanka, danfa kafara komawa cus malam. Kai kanka kazauna ka k'iyasta da watannin farko na amarcinku irin nanuk'ema amarya da kakeyimana, kai abindama yakamata namiji yayi daga shekarar dayasan zaiyi aure yadace yafara dagewa da amfani da maganin sanyi dana basir, dan sune manyan abinda kemana lahani, bakuma komai ke kawosuba sai abincin da mukeci, mutum a yini saiyaci maka abinci Kala kusan goma sha dukshi kad'ai, kuma zaka samesu duk maik'one, tayaya basir bazaiyi ram damuba?, kafara gyara kanka malam tunkan amarya tashigo daga ciki, yanda idan tashigo tajika zam, kanayin magana zatace hakane Alhaji koda bakada ko sisi kuwa”.
Nanma dariya mutane keyi, samari damasu kunya nata sunkuy dakai, shima kansa malam Aliyun kansa a k'asa yake baya kallon kowa, dama malam bayanan yamayi tafiya.
“Ina muku wannan maganarnefa akan gaskiya y'an uwana, domin wlhy sakacin gyara kayinmu yana bada gudunmawa wajen saka matayenmu a masifu Na mad'igo da zinace-zinace ko amfani dakansu wajen samun biyan buk'ata, wata badan kud'i take aikata wad'annan fasik'ancinba, saboda kawai mijinta baya iya gamsar da itane, mace tadage tasayi kayan gyaran kanta tasha babu ko sisisnka Alhaji, kuma dan kawai ta burgeka, buk'atar mijinta ta taso Mata amma dayazo bazai iya gamsar da ita yanda ya kamataba saiyaja gefe, tayaya muke tunanin bazata nemawa kanta mafitaba?, ga masifu da kafafen social network d'innan sukazo mana dasu iri-iri, matarka taje tashiga taganoma kanta masifar dazata dameta kai baka kusa da ita, koma kana kusa bazaka iya biya Mata buk'atartaba Yaya kake ganin za'a k'are? Wlhy inda zaka zama jarumi wajen bata kulawa da kare mata duk wani hak'k'inta a shimfid'a ko soyayyar da suke gani a finafinan banzarnan bazaiyi tasiri agaresuba, dan mace kota gani saitaga ai shirmece, wadda mijinta ke Mata tawuce wannan, tayaya ta film da hikayoyin marubuta zata birgeta balle har tadinga kokwanton anya akwai irin wannan soyayyar kuwa a duniya?. To tasaba Nata Mijin daga mazurai sai matsalar Neman kud'i yasani, wanima saiyakai k'arfe sha biyu a majalissar da ba'a komai saisurutan banza da wofi da nad'oma kai zunubi, lokacin dazai shigo gidan tajima dayin barci, saidai cikin barci taji yana Neman tausheta. Mufa mazan hausawa ko d'an soyayyarnan kafin biyan buk'atama ba iyawa mukaiba, kana zaune mace bazata ra6u da jikinkaba saikunzo kwanciya, data zauna kusa dakai kace batada kunya, wanima ko a wajen kwanciyar dayasamu biyan buk'atarsa to matar tana gabashin gado shikuma yana yammaci, burinka kawai ka kashe gobarar gabanka kakoma gefe. Haba tayaya mace zata yarda akwai soyayya a duniya inba ta film da littafiba? Addininmu babu abinda bai koya manaba, babu Wanda yakai MANZON ALLAH iya soyayya ga iyalansa, miyasa bazamuyi koyi dashiba domin samun farin ciki a gidajenmu, mudaina d'aukar matanmu bayinmu komasu kula mana da gida da yara kawai, ba haihuwa da raino da bautar cikin gida bane kawai aikin mace, baka bata ci dasha da sutura kawai bane yadace dakai, ka nuna Mata soyayya da kulawar dazata ringajin itad'in macece wadda ta isa hamshak'iya, babu birgewa a garemu ace da zarar mun aure mace tayi hauhuwa d'aya shikenan saimuce soyayya ta k'are, waya gaya maka soyayya takare malam? To komin tsufanku soyayya bata tsufa, soyayyar gaskiyama ana girmane tana Kara girma, tomu matsalarmu yawancinmu shawa'a ke kaimu ga aure ba soyayyaba, shiyyasa kwanaki naja matsalolin gidajen aurenmu Na k'ara girma da bunk'asa, amma kullum idanunmu nakan matan waje, kakasa gyara wadda ka ajiye tayaya wadda take a waje bazata birgekaba?. Dan ALLAH yakamata mu gyara, akwai abubuwa da yawa dasuke gyara namiji shima, ba Mata bane kawai keda wad'annan magungunan, akwai wad'anda idan kasha kaikanka zasu motsama jarumtarka ta yadda zaka gamsar da iyalinka, amma maganar gaskiya mu maida hankalinmu wajen Neman maganin basir dana sanyi a farko, insha ALLAHU namuku alk'awarin Baku wasu sirrika a zama nagaba dazai taimakeka wajen gamsar da iyalinka, abinda muka fad'a dai-dai ALLAH kabamu lada, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka hafe mana baki d'aya...................✍🏻
*_Dadai nace bazanyi posting ba, amma ganin nagama typing da wuri nace bara nayi muku kawai_*.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[39➖40]_*
..............Zuwa yamma lik'is Zazza6i mai zafi yarufe Jiddah saboda ciwon da taji, hannun harya kumbura, Ummace talura danhaka taje inda Jiddah ke a kwance takamo hannun.
Y'ar k'ara Jiddah tayi tana rik'e hannun Umma da fad'in “Wayyo Umma akwai zafi”.
“Yanzu nan ciwo kikaji a hannun Jiddah amma kikayi shiru da bakinki? Yanzu daban kulaba haka zakiyita zama dashi? Ga jikinkinan har zazza6i ya sauka”.
Hawaye kawai Jiddah keyi takasa magana, tsaki Umma tayi tana mik'ewa, yayinda can k'asan ranta ke k'ara zafafa da lamarin Abba, yau gaba d'aya a cikin 6acin ransa ta yini, kai dukama gidan harsu Balu.
Waya Umma ta d'auka takira Uncle yahya, yace yaje Jigawa amma gashinan a hanyar dawowa.
Sai bayan Sallar magriba Uncle yahya yazo damai gyara, sosai Jiddah ta jigata da kukan azaba, ga lalurarta, danma yanzu ALLAH ya sauk'ak'a abun sosai bakamar daba.
Ana gamawa aka bata maganin zazza6i Tasha ta kwanta sai barcin wahala.
Umma suka zauna da Uncle yahya bayan mai gyara ya tafi, bayani taimasa akan abinda Abba yazo yayi yau, sosai ran Uncle yahya ya6aci, ananma yake shaida Mata shima yaje nemansa a kasuwa akace yaje jigawa shine yayo nan gidan ya zubar musu da tujarar su.
Umma tarik'e ha6a tana fad'in “Anya kuwa Alhaji yanada isashshiyar lafiya Uncle d'insu?”.
“Wlhy lafiyarsa lau Maman Nafisa, abinda ya shukane kawai yafara girba, dan hak'in yarannan kawai ya ishesa ishara, yanzu haka d'azun Saudah takirani take shaidamin wai yakira mijinta yabashi bashin miliyan ashirin, dan ALLAH Maman Nafisa kijifa zubarwa kai mutunci”.
Ran Umma a matuk'ar 6ace tace, “Takirani nima wlhy, rasama mizance Mata nayi, dan ni lamarin mahaifinsu yafara fitamin a kai gaba d'aya, jira nake kawai naga yarananan sunsami matsugunni wlhy nak'ara gaba”.
“Kiyi hak'uri Maman Nafisa, dan ALLAH kibar wannan tunani, ke kamar uwace agaremu, idan babuke wazamu kalla muji sanyi, dagani sai d'an uwana iyayenmu suka Haifa suka Bari, amma kece kika mayemin gurbinsa, idan kin goce ni dawa kuma Zan zauna?”.
“Uncle d'insu abunne da ciwo, yaufa soyay yamareni gaban Jiddah, badan ALLAH yakawo su Yaruwaiya ba yakake tunanin za'a k'are? Dan wlhy nak'udiri aniyar ramawa daya mareni”.
Kasama magana Uncle yahya yayi, in banda tafasa babu abinda zuciyarsa kemasa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A police station dai rufe kalifa akayi yanata kuka, kusan a tare suka Isa da Abba, yayi-yayi iya iyawa abashi belin kalifa a sasanta magana amma uban d'an ya rantse sai kalifa yayi kwanan kanta, wasa-wasa har dare Abba yanacan yana fama, sai kusan sha d'aya yabaro station d'in yadawo gida, hankali tashe Hajia Hindu ta tareshi da zancen kalifa, bayani yaymata yay shigewarsa d'aki yabarta tana kuka harda kururuwa.
Suma sauran yaran duk sunyi jigum-jigum.
Washe gari dai dole Abba yaje makarantar su kalifa, amma Sam principal d'in saiyak'i saurarensa, acewarsa yanzu magana tana hannun hukuma, miyasa lokacin da suka buk'aci ganinsa yak'i zuwa?.
Duk yanda Abba yaso nuna musu kud'i abin ya gagara, ga hajia Hindu Nata musu kuka, dan kasa hak'uri tayi saida ta biyosu.
Kwasa sukayi zuwa station d'inma, canma Sam ba'a sauraresuba, saida Abba yakashe kud'i sosai kafin aka sasanta magana akan Abba zai biya kud'in asibitin yaron daduk wasu abinda zai buk'ata harya warke, aka kuma yiwa kalifa tsakani da yaron.
Sunje asibitin suka duba yaron, Ashe sosai kalifa yaji masa ciwo kuwa, sun masa sannu suka taho abinsu.
Aiko wujiga-wujiga suka dawo gida, hajia Hindu ta rungume kalifa tana kuka, hakama su Hassan duk sun rungumeshi da murnar dawowarsa.
Kan Abba yai zafi sosai, sannan dagashi har hajia Hindu babu Wanda yayma kalifa fad'a akan lamarin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A washe gari Uncle yahya yaje wajen malam Abdul-ra'uff suka tattauna maganar tariyar Jiddah, sosai malam yay farin ciki da matso da maganar, dan sun yanke nanda kwanaki uku kacal.
Ananma Sheikh Aliyu yazo ya samesu, shima sosai yagamsu dahakan, amma kunya ta hanashi Nuna farincikinsa a gabansu malam. Sai dai shi malam dayasan yanayin d'ansa tuni ya hango farin ciki tattare dashi.
★★★★★
A ranar da yamma kayan gadon Jiddah suka iso, kayane masu k'yau da tsari dakuma tsada gwargwadon k'arfin Uncle yahya, kowa yagani saiya yaba, saidai idan mak'iyi kuwa.
Ganinfa abin da gaskene sai jikin Jiddah yakuma sanyi, ga Yaruwaiya tadage sosai take kuma gyarata da tsumata a k'amshi.
Sheikh Aliyu yana kiran Jiddah su gaisa, yakuma bata hak'uri akan bazai samu sake shigowaba, dan yayi busy da yawa, ga shirin tarewarta ga walimar musabik'ar dataje Saudia wadda malam yace za'a had'a data aurensu.
Ita hakanma sai yay Mata dad'i, dan dama batason yazo yaga taji ciwonan Na hannunta, sannanma dai tafison su zauna nesa-nesan, shiyyasa jitake inama su Umma zasu yarda a kuma d'aga tariyar. Daka ganta kasan tana tare da damuwa, datasamu ke6ewa ita kad'ai sai kuka, ita kanta Umma dauriya kawai takeyi, su Zarah kam duk sunyi wani sukuku dasu suma, kewar Y'ar uwarsu Na matsuk'ar damunsu.
Washe gari aunty zulai dasu Aunty Saudah, hannatu suka iso, dan haka aka rankaya gidan Aliyu yoma Jiddah Jere.
Tarba ta mutunci suka samu dagasu aunty Ruk'ayya da Maimunatu, dan bazama kata6a cewa itace kishiryar Jiddanba, yanda taketa hidima dasu abun gwanin birgewa.
Dukda gidan Alhaji garba yafi Na Aliyu komai hakan bai hana gidan Aliyu k'ayatar dasuba, dan ba arzik'in bane abin birgewa kawai, zaman kafiya da kwanciyar hankali shine abun buk'ata ga kowacce d'iya mace.
Tsarin gidan babu ruwan kowa da kowa, dan kowacce kamar 6angarenta daban zamuce, sai dai bawani k'atun k'atunbafa, dan bawani katafaren gida baneba, yanada dai girmansa gwargwadon hali, kuma tsarin yayi, iri d'ayane da sashen Maimuna, babu wani banbanci saina kayan d'aki, komai Na Jiddah pink and White ne, iya gwargwadon iko dolene a yabama Uncle yahya, kayan gadonta d'aki biyun duk aka zuba, kicinma kam Alhamdllh, saidai mak'iyi. Dayake sunada yawa dandanan suka gama, dan zuwa magriba sun dawo gida, sunata zuzuta tsarin gidan, sun nunama Umma video recording d'in da sukayo, itama sosai ta yaba, dad'i kuma ya kamata, dan yanzune hankalinta ya kwanta da auren d'iyarta.
Koda suka nunama Jiddah k'in kalla tayi, saima ta fashe musu da kuka.
Aiko dariya suka sanya Mata, ganin da gaske takeyi duk sai jikinsu kuma yay saniyi suka shiga rarrashinta.
Washe garifa dangi suka Fara sauka, zuwa yamma gida yayi taf, dangin Umma danasu Abba, kamar taron farko wannan karonma sai rabuwa sukayi saboda gidan Umma yamusu kad'an.
A ranar da yamma kuma aka kawo lefen Juddatulkhair daga angonta Sheikh Aliyu maina, suma ammusu tarba ta girma da mutuntawa, kuma kowa ya yaba da lefen Masha ALLAH, dan saidai mak'iyi kam, abin tamkar bana bazawara ba.
Jiddah dai ko tarinta bakaji a gidan, koda su aunty siyama suka buk'aci ganinta k'in yarda tayi, dole suka hak'ura suna fad'in ai dai gobe iyanzu takusa shiga gidansu.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A yayinda ake shagalin tarewar Jiddah kuma shima Alhaji garba yanacan yana shagalin tarewa da sabuwar amaryarsa da aka d'aura aure yau hajia deluwa bata saniba, sai wajen tashin hantsi taga anzo ana kwashe kayan 6angaren Jiddah, dariya tayi sosai tana fad'in “Badole ka kwasheba, da kabarsu su shekara dan itadai tatafi kenan har Abadan”.
A wajen kwasar kaya masu kwasar sukaci Karo da abinda Hajia deluwa ta sakama Jiddah. Basuyi k'asa a gwiwa ba suka Kira Alhaji garba suka shaida masa..
Mamakine ya kamashi, babu jimawa yadawo gida bayan an d'aura aure, kai kawai yake iya jinjinawa saboda takaici, ko tantama bayayi wannan aikin deluwa ne, wato wannan shine yasaka Jiddah haukacewa idan tagansa, shine kuma yasatake masa wari?. Sakasu yayi suka k'ona, itakuma bai Mata maganaba dan yanzu bashida lokacinta, ta amaryarsa yakeyi wadda takasance gogaggiyar Y'ar bariki, dan hajia bariki ma ake kiranta, tafi hajia deluwa komai, idanma kud'ine itama ta Tara, tadad'e tana nunama Alhaji garba so amma yana shareta, hajia deluwa kuwa sosai ta tashi hankalinta lokacin dataji hajia Rahina bariki Na sonsa, dan shige-shigen malamai taitayi dan kar hajia rahina tashiga zuciyar Alhaji garba.
To a yanzu kuma gashi tashigo batareda ta saniba, ko wane irin zama za'ayi😹 kuma🙆🏻?.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah datasha kuka zazza6i ya rufeta ta kwanta, duk hayaniyar ganin lefe da y'an biki sukeyi sama-sama takejinsu saboda barci dake fusgarta, zuwa wani lokaci barcin yay awon gaba da ita gaba d'aya.
Cikin barci tafara mafarki mai ban tsoro, kafin daga bisani tasamu k'arfi akan Wanda suketa dambe a mafarkin, a fili kuwa tajik'e sharkaf da zufa, ga mazari da jikinta kemata.
Fannah data shigo domain gwargwad'a Mata lefe da kayan arzik'in da ya sheikh ya zuba ta isketa a wannan hali, jijjiga Jiddah tafarayi tana kiran sunanta, ihunta shine yajawo hankalin mutane sukayo d'akin.
Da k'yar aka samu Jiddah ta farka, amma saita Fara wani fisge-fisge da gurnani cikin wahaltuwa, numfashima dak'yar take fisgarsa, daga k'arshema saita sank'ame alamar ta suma.
Ummace ALLAH yabama k'arfin zuciyar d'akko magungunan Jiddah da sheikh Aliyu ke bata har yanzu ta zuba turare a rushi, yayinda Maman Sadiq keta shafama Jiddah ruwan addu'oin a fuska.
K'ara ta k'walla kafin tafara rawar jiki da zufar dake cigaba da kwararo Mata, bayan kamar mintuna uku saita koma tayi lakwas tamkar ba itaba, saikuma hawaye dake kwarara Mata a fuska. Daga baya kuma barci ya sake kwasheta.
Uncle yahya da aka Kira a waya ya k'araso, Koda sukai masa bayani sai sukaga ya d'aga hannu sama yana fad'in “Alhamdullahi, ALLAH mungode maka dakabama yarinyarnan lafiya, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan”.
Tambayarsa suka shigayi, nanfa yaymusu bayanin insha ALLAH Jiddah tasamu lafiya daga lalurarta.
Kowa murna yashigayi, saidai Umma Na mamakin ya akayi haka cikin sauk'i? Kodai Uncle yahya ya d'auki wani matakine basu saniba?. Ganin babu mai bata amsa yasa ta hak'ura, tasan idan komai ya lafa zai Mata bayani.
Da wannan aka cigaba da shagali.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dukda Busy da Aliyu yayi haka yasamu ya nemi Jiddah a waya saboda duk yau basu gaisaba, amma saima yaji wayar switch up, dole ya hak'ura dan yasan gobe iwar haka insha ALLAHU tana gefensa.
Baiwar ALLAH Maimunatu, duk yanda kaso gano halin datake a ciki baka isaba, dan ta danne zuciyarta sosai, yayinda kulawa da tattalin da mijinta ke bata ya danne kaso mai yawan gaske Na damuwarta.
Harkokinta taketayi, danma laulayi yana takura Mata sosai, batajin dad'in jikinta, dauriya kawai takeyi.
Yauma gaba d'aya da daddare bayan yadawo nasiha yayta Mata da lallashinta cikin kalamai masu sanyi da saka zuciya nutsuwa. Hakanne yasakata itama bashi dukkan farin ciki batareda ta d'auki fushi Na tunanin gobe iyanzu yana tare da amaryarsa ba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.
Washe gari Jiddah ta tashi garau da ita, wannan Yakuma tabbatarma dasu Umma lallai an dace kam. Yau tunda aka tashi da gyaran jikin Jiddah aka fara, dan sunayin sallar asubahi aka Fara zuba Mata kunshi da kitson Bare-bari d'an asalai (barbarawa😹🤭⛹♀), tayi k'yau harta gaji.
Sai dai daka ganta kasan batada sukuni, magana kad'an za'ai Mata ta6are baki tana kuka.
Y'an uwama saisuka koma tsokanarta, musamman abokan wasa, saisu Aunty Sauda ne ke kareta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Abba dai duk wannan hidimar da akeyi baya gari, dan tun Randa aka fiddo kalifa daga station suna dawowa yahad'a kaya zuwa Abuja wajen wani Alhaji Sammani Moddibo, abokinsane amma yanzu ya haye dan d'an majalisane a Adamawa, Da Abba yabuga tunaninsa yagama yaga babu wajen mafaka, danya Kira Mijin y'arsa Sauda danya ranta masa kud'i ALLAH ya tak'aita wahala Sauda ta d'aga sannan wayar na agunta, saida yagama fad'ar buk'atarsa sannan tace masa “To Abba ai nice, Ashe dama y'a mace nada amfani da Rana? Ai nazata bazakama ta6a tunamu a cikin y'ay'ankaba balle kabiyo mazajenmu da buk'ata”. Batajira cewarsaba ta yanke wayar taredayin blocking d'insama gaba d'aya, shinefa takira Uncle Yahya da Umma ta sanar musu.
Wannan Abu da Sauda taimasa ba k'aramin Sosa masa zuciya yayiba, dan haka yashiga tsinarta yana had'a kaya, aranar yawuce Abuja.
Harkuma yau da Jiddah zata tare bai dawoba, ya iske Alhaji Sammani bayanan, amma saiya zauna jiransa saiya dawo, dan ance tafiayar kwana biyar zaiyi, to aganinsa dayayi wahala biyu bai dawoba ai gara ya zauna ya jirasa kawai, yama huta da bala'oin daya baro a cikin kano.
Auren Jiddah kuwa yana komawa yabiya Alhaji garba kud'insa saiya tsinkashi, danyayi alk'awarin tunda Yaruwaiya taci zarafinsa gaban y'ay'ansa saiya huce akan Umma, sannan saiya shukama Uncle yahya rashin mutuncin da ko'a hanya bazai sake nunashi a matsayin d'an uwansaba.
🤦🏻♀Aɮɮa ʍɨҡaҡɛsօռ ʐaʍaռɛ աaɨsɦɨռ?.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_11:00pm_*
Harabar makarantar su Jiddah tagama cika taf, bakajin komai sai k'ira'ar alkur'ani mai girma, tarone daya tara manyan bak'i daga yankunan arewaci da kudanci.
Dan taron an shiryashine da manufa biyu, Na murnar nasara da Nageria tayi a gasar diniya, dakuma murnar taya hazik'in malami Sheikh Aliyu da Amaryarsa Jiddah tauraruwa a daular musulinci.
Jiddah na sanye cikin k'yak'yk'yawar sutura, ko ina Nata a rufe ruf, ko tafin hannunta da k'afa baka gani, fuskarta kam tamkar kullum tana lullu6e da nik'ab, sai sirrin k'amshi mai sanyi take fitarwa.
Madina ce a kusa da ita sai sauran d'aliban ajinsu.
Ahakanma hawaye taketayi, dukda ayau tanajinta wani sakayau tamkar an sauke Mata kaya, ko kad'an batajin komai game da maza.........
Sassanyar muryarsa data farajan k'ira'ar alkur'ani cikin suratul Bak'ara ce ta katse tunaninta, cikin fad'uwar gaba da bugawar zuciyarta sauri-sauri ta d'ago ta kalli saitin inda muryar ke fitowa.
Zaune yake a cikin kujera 1Seat, hannunsa rik'eda microphone, yana cikin shadda wagambari kalar sararin samaniya (skyblue) harda babbar riga, hularsa da takalmansa ma duk kalar shaddar saidai su masu duhune, babu abinda ke fita tattare dashi sai wani annuri Na kwanciyar hankali, yayi wani fresh dashi alamun komai yana tafiya masa dai-dai. Yau shine Rana tafarko data samu zarafin masa kallon tsaf, Masha ALLAH gwargwado Sheikh Aliyu maina yanada k'yansa, Abu mafi k'awata taswurar kamilalliyar fuskarta shine tambarin salla dan6arere dake a goshinsa, sai sajensa zuwa gemu daya kuma fidda sirrin nagartarsa da cikar kamala musamman dayasha gyaran fuska da aski a yau. Harya gama karatun yafara Addu'a Jiddah batasan anayiba, saida aka kirayi sunanta sannan Madina ta zungureta ganin batai ko motsiba.
Babu shiri tadawo hayyacinta kafin tamik'e bisa taimakon Madina. Itace taimata rakkiya har inda ake buk'atar ganinta.
Tunda aka Fara shelanta sunanta yake baza Ido yaga ta ina zata 6ullo ne? Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke daya ganta tamkar yanda yay fata, danshi mutumne shi mai kishi sosai, dan taronnan da farko k'ok'arin hanata zuwa wajen yayi, kasancewarsa komansa yakan nema shawarar malam kafin ya aiwatar saiyaje ya sanar masa. Malamne ya lallashesa akan yabarta taje yaudai d'aya, kodan manyan mutane dazasu halarci taron, dan kowa zaiso ganin wannan gwana data samo mana nasara. Da wannan malam yaci k'arfin sheikh Aliy.........
Bai ankaraba yajiyo zazzak'ar muryarta na jawo ayoyi cikin kwarewar larabci da takatsantsan. Lumshe idanunsa yayi bugun zuciyarsa Na k'aruwa. Wajen yayi tsitt bakajin komai sai ajiyar zuciyar jama'a.
Tuni muryar Jiddah ta karye alamun kuka takeyi, wad'anda sukasan hali su malam Abdul'ra'uff dama sunsan za'a rina, tuni ta karya zuciyar jama'ar wajen, wasu sai sharce yawaye sukeyi.
Saida takai har k'arshen suratul Al-Anbiyaa kafin a dakatar da ita. Wajen zamanta takoma itada madina, dad'i yasaka Umma share hawayen da suka wanke fuskarta, itakam kullu yaumin tana alfahari da haihuwar y'ay'a Mata, babu abinda zatacema Ubangiji saidai godiya.
An fara gudanar da abinda ya tara mutane, Wanda dukkan manya sun yabama Jiddah dajan Addu'ar fatan alkairi dazaman lafiya nahar abada itada gwarzon mijinta tauraron duniyar musulunci, duk kuma k'yautar data samu shike zuwa ya kar6a Mata. Mutane sai k'usk'us suke akan hakan, yayinda y'ammata irinsu Tawan (Miss Xoxo😝😂) suketa k'yasawa, jisuke inama sune sukeda wannan Hafizin masani a gidauniyar addinin islama.
Sak'on jawabi daya kamata Jiddah tayi Na godiya shine yakar6a microphone yayi a maimakonta. Dan yayi alk'awarin babu mai sake jimasa muryar mata gaskiya, karatunma datayi jiyay tamkar yaje ya hanata, da k'yar ya iya tausar zuciyarsa harta gama, shiyyasa yaturama malam mustafa massage akan karsu sake kiran Jiddar, duk abinda ake buk'atar tayi akirashi a maimaikonta.
Murmushi malam mustafa yayi, dan yasan wanene Aliyu akan kishi. Dan haka yabi dokarsa, komai za'a buk'aci ganin Jiddah saiya Kira Aliyun.
Bayan andawo salar zuhur malamai suka fara gudanar da lecture mai taken *_GIDAN AURENMU_*, wadda dai anyitane ta musamman domin ango da amarya.
Jiddah dai Tasha kuka acikin Nik'ab harma kanta namata ciwo.
Gab da la'asar aka tashi, bayan Jiddah tayi gaisuwa da mutane da hotuna tasamu ta sulale batareda sunko gaisa da Aliyu ba.
★★★★★★★
Koda suka dawo gidama ba zama sukayiba, dan shirye-shirye aka faraima Jiddah Na mik'ata gidan miji.
'Dakin Umma taje ta k'unshe a k'arshen gado saboda azabar ciwo da kanta kemata, duk hayaniyar y'an yinin biki ta addabeta.
Anayin Sallar magriba kuma Fandau ta tasota aka fara tsumata dawasu sirrikan k'amshi Na musamman.
*_08:00pm_*
Angamawa Jiddah dukkan abinda ya dace da ita, sai iyaye dasuka baibayeta ana Mata nasiha, Umma ma a wannan Karon kasa cewa komai tayi, saima hawaye dake bin kumatunta, dan haka takasa magana. Said da k'yar tace, “ALLAH ya bada sa'a, yabaku zaman lafiya, adaiyi hakuri, ayi hak'uri, ayi hakuri dakomaima za'aci karo dashi”. Daganan Umma tayi shiru bata sake maganaba.
Sosai su Zarah ma ke kuka, dan Walida ma hardasu amai, hakan saiya saka mutane dayawa kuka, dukmai d'iya mace yanacin Karo da Abu biyune a irin wannan ranar, farinciki dakuma d'acin rabuwa da y'arsa.
Haka aka fita da Jiddah gidan Uncle yahya, acanma fad'an Tasha sosai da nasiha, Uncle yahya ya kamo hannunta har wajen motar y'an d'aukar amarya, dagashi sai Jiddah suka shiga d'aya, sauran jama'a suka shiga.
Sun Isa gidan Aliyu inda aka had'a wani taron walima da d'alibansa suka shirya masa, sun samu k'yak'yk'yawar tarba daga dangin Sheikh Aliy gadanga k'usar yak'i, yayinda Uncle yahya yatsaya da Jiddah har k'ofar Maimunatu, saida tafito ta durk'usa har k'asa ta gaisheshi sannan ya dank'a Mata hannun Jiddah yana jaddada musu Kalmar hak'uri da tsoron ALLAH wajen kwatanta nagartaccen zama da ALLAH bazai k'onasu akansaba wajen cutar da juna takowace siga.
Maimunatu ta amsa da insha ALLAH Abba tana hawaye itama, dan ita duk zatonta Uncle Yahya mahaifin Jiddah ne.
Maimunatu itace taima Jiddah rakkiya har cikin d'aya daga d'akunan barcinta, saida ta zaunar da ita a bakin gado sannan tace, *_“Amincin ALLAH ya tabbata a gareki k'anwata kuma Y'ar uwata, ina miki marhaban da shigowa wannan gida, ina rok'on Ubangiji ya kad'e dukkan wata fitina dazata shiga tsakaninmu, ALLAH yabamu zaman lafiya ya dasa mana k'aunar juna mai tsafta a zukata, yabamu ikon yima mijinmu biyayya da k'yautata zaman takewa a tsakanimu har ranar da mai rabawa mutuwa zata raba”._*
Kasa magana Jiddah tayi, sai hannun Maimuna data kuma matsewa a Nata tana kuma sakin kuka, rungumeta Maimunatu tayi itama tana Nata hawayen.
Wannan lamari ya burge jama'a, wasuma sunaji inama sune da wad'annan k'yawawan zukatan masu sauk'i da d'aukar rayuwa ba komaiba.
Munafukai masu burin kunna wuta kam sai jikinsu yay sanyi k'alau, a fili kuma sukaita ta6e bakuna.
Dangin Jiddah sunyi farin ciki da sauyin alkairi da d'iyarsu ta samu, dan haka suka juya cikeda farin ciki. Dan Uncle yahya yace babu mai kwana.
Tunda kowa yafita sai Jiddah tazame a gadon ta kwanta, dan kanta wani irin ciwo yake mata, har wani jiri-niri take gani. Zuwa 12:30 gidan yay tsit alamar kowa yatafi, har lokacin Jiddah Na kwance takasa barci, saima hawaye datake zirarwa har yanzu...............✍🏻
*_Harda sauran Na jiya Na had'a muku🙄, kai gaskiya harma dana gobe, irin wannan dogon page haka😨🙆🏻😹_*⛹♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[41➖42]_*
..............Aliyu bai samu shigowa gidaba sai wajen sha biyu, gidan yayi tsit bakajin komai sai k'arar Gen... Da aka kunna, sashen Maimunatu ya nufa, nanma dai tsit yake, komai kuma a kashe, bedroom d'inta ya wuce.
Tana kwance tayi luf tamkar mai barci, amma idanunta biyu tana kuka Mara sauti, jin an bud'e kofar yasata saurin share hawayenta cikin dabara kafin ya kunna wutar d'akin.
Cikin sanyinsa yake takowa gaban gadon yana fad'in “Habibty kalb badai barciba?”.
Maimuna najinsa amma tayi shiru, ya zauna a bakin gadon yana lek'a fuskarta, kasa daurewa tayi tasaki murmushi saboda hannunsa daya tura a rigarta. Hannunsa ta janye tana tashi zaune cikin kumbura fuskar shagwa6a. “Haba dai Yaya barcifa nake amma ka tadani”.
“O ALLAH yaushe wannan malamar tafara koyan k'arya?”. ‘yak'are maganar dajan hancinta’.
Dariya tayi, tace, “Ya gajiyar taro?”.
“Uhm wannan Ku za'a tambaya ai Habibty, yanzu dai ya za'ayi dani?”.
Idanunta tad'an waro waje, “Yaya a wajenmi?”.
“Komaima madam”.
“To yanzu dai tashi kaje kayi wanka ka baza turare kaje wajen k'anwata tana jiranka, nikam sai jango wlhy barci sosai nakeji ga gajiya”.
Matsawa yay jikinta yana murmushi, “Haba hajiyata kod'an wankanma baza'a tausaya amunba yau?”.
Maimuna ta marairaice fuska tana fad'in “ALLAH yaya bakaji jikinaba, ko ina ciwo yakeyi, danma nasamu zazza6in ya saukane fa”.
Cikin tausayawa yakuma rungume ta yana k'ara jinjina mata da k'aunarta mai girma dake kuma k'arfi a ransa, tunda yashigo ya fahimci kuka take, amma kasancewar Matar kwarai saita had'iye ta taresa da farin ciki, shikam yama za'ayi ya wulak'anta wannan baiwar? Ai ta wuce hakan a garesa.
Yanda ya matseta sosai yasata sakin k'aramar k'ara, da sauri ya sassauta Mata rik'on tareda kallon fuskarta, yanda ta tura bakin gaba yabashi damar d'ora nasa akai. Tunma tana zame-zamen bataso harta nutsu tabashi had'inkai.🤭
Bai bartaba saida ya tabbatar jikinta yay sanyi da zuciyarta sannan ya kwantar da ita yana shafa matashin cikinta daya fara d'agowa.
Addu'ar barci yafara karanto Mata, itadai tanata kallonshi da k'arajin k'aunarsa musamman da kishinsa, tanaji tana gani yau zasu raba shinfid'a, tunda tazo gidan hakan bai ta6a faruwaba sai dai idan tafiya yayi, amma yazatayi? Idan har takasance mai tsannatawa saidai ta saka kanta a musabar damuwa da rashin kwanciyar hankali, dan bata isa yin jayayya da hukuncin ubangiji ba.
Bayan ya shafa Mata addu'ar ya kwanto jikinta, zatayi magana ya d'ora hannunsa saman bakinta alamar tayi shiru. Shirun kuwa tayi tana sauke ajiyar zuciya.
Iska yafara hura Mata a kunne, ahankali tafara lumshe idanunta, saida yaga barci yafara cin galaba akanta kafin Yakoma Mata tausa, dand'in hakan yasaka nannauyan barci kwasheta, dama gashi gajiya tamata ligif. Saida ya tabbatar barcinta yayi nauyi sannan ya kuma tofeta da addu'oi ya gyara Mata kwanciya ya kashe fitilar ya fice yana murmushin dashi kad'ai yasan ma'anar kayansa.
Nasa sashen yanufa, Wanda ya kasance a tsakkiyar nasu Jiddah, amma shifa falone kawai da bedroom, shima kuma yaune zai Fara amfani dashi, danda a d'ayan bedroom d'in sashen Maimunatu yake, bayan d'aura aurensa da Jiddah kuma ya gyara nasa, dukda bai ta6a kwanaba saikuma yau.
Komai an saka, bakajin komai sai k'amshin sabon kaya Dana turaren da Maimuna ta saka. Baiwani 6ata lokaciba yashiga wanka ya fito, jallabiya Fara k'al mai gajeren hannu ya saka, yad'an saka turare ya fito, Gen... Yaje ya kashe, saima yaga an maido wuta wadda yake k'yautata zaton yanzu suka kawota, canjawa yay sanan ya doshi sashen jiddah.
Garin yakumayin tsitt dan d'aya takusa, sosai ya yaba da k'ok'arin iyayenta, sai fad'ar “Masha ALLAH yakeyi, komai yagama dacewa da sashen.
Saida ya lek'a bedroom d'in farko yaga babu kowa, sai dai nanma komai tsaf yake, ga k'amshi mai dad'i yana tashi. 'Dayan ya nufa, inda ya hango Jiddah kwance a kan gadon, tawani takure waje d'aya.
Bata dad'e dayin barci ba, dan fuskartama jik'e take da d'anyun hawaye daya kuma tabbatar masa hakan, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana zama kusa da ita, yakai hannu ya d'auke gyalen dayad'an rufe mata fuska kad'an, babu wata kwalliya mai yawa a fuskarta, saima ruwan hawaye dake jik'e da fuskar, murmushi yayi aransa yana jinjina k'aunarta da kuka, akance yacika saurin kuka, amma yalura jiddah senior d'insace.
Yanda jijiyoyin kanta suka tashi saiya fahimci batada isashshiyar lafiya, yakai hannunsa saman goshinta, hakanne yasaka Jiddah farkawa ta bud'e Idonta, da sauri ta tashi zaune jikinta yana 6arin tsorata. Saurin rik'o hannunta yayi dan ya lura tsorata tayi.
“Relax Hajiyar tsoro”.
Dukda ta fahimci shine hakan baisakata nutsuwaba, dan bata Saba kusanci da wani namiji irin hakaba, balle ace sukad'aine a waje. Muryarta Na rawa amalar tahowar kuka tace, ”Inayini?”.
Murmushi yayi yana sakar Mata hannu, sai dai a k'asan ransa yana mamakinta, yanda take masa bai Kama da wadda tata6a aureba, a 6angaren ciwonta kuma Alhmdllh sun sami mafita ai, duk da bazasuce tadawo normal ba lokaci d'aya, ciwo shike shigar Bawa a lokaci d'aya, sauk'i kam sai a hankali.
Kallonsa Yakuma maidawa kanta, tana sanyane cikin lifaya orange da d'igo-d'igon blue, ga ainahin kitson bare-bari akanta, saita koma masa kanuri sosai, ”Kibar kukannan haka dan ALLAH, kingama kanki ciwo yakeyi harma da zazza6i, tashi ki canja kayanki nakawo miki magani kisha”.
Baijira amsartaba yatashi yafita, kukanta tacigaba da rairawa itako, babu abinda kecin zuciyarta sai kewar y'an uwanta da Ummanta, jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta koma garesu. Harya dawo bata motsaba balle ta canja kayan. Baice Mata komaiba ya ajiye kofin hannunsa daketa turiri da magani.
Akwatin da aka kawota dashi ya bud'e, kayantane na sakawa sai kayan barci kala uku a sama, ta farko dai tacika k'ank'anta, sai d'aya kuma wando da rigane, amma sunda kauri, suya fido ya maida akwatin ya rufe yadawo bakin gadon ya zauna kusa da ita sosai.
Jitai kawai ya d'agota ya sakata a jikinsa, duksai takuma daburcewa, baice da ita komaiba yafara warware lafayan jikinta, blue d'in rigar ciki mai dogon hannu databi jikinta ta bayya, saurin kare k'irjinta tayi, dan rigar sosai ta fidda surarta, Sheikh Aliy yay murmushi mai sauti dayin magana cikin rad'a, “Ah Qurratul ain bar wahalar 6oyewa, narigada nagani”.
Ba k'aramin kunya tajiba, dan haka tayi sarin k'udundune jikinta tana gyara lifayar.
“Yi hak'uri wasa nake banga komaiba, tashi ki canja kayan kisha magani ki kwanta ki huta, kinga har d'aya tayi, nanda minti uku kuma zan dawo nacanja miki da kaina idan bakiyiba”. ‘yana gama fad'a yatashi ya fita’.
Dak'yar ta iya sakkowa a gadon, tabud'e akwatin ta d'auki hijjab sannan ta d'au kayan barcin daya d'akko tashiga bayi.
Kusan mintuna goma ta fito hannunta rik'e da kayan data ciren, Aliyu dake zaune ya d'ago ido yana kallonta. Tsaye tayi akusan tsakkiyar d'akin takasa k'arasowa, taa duk'ar dakanta dan sai yanzu ta ganshi.
“Na tasone?”. ‘yafad'a yana k'ok'arin mik'ewa’.
Da sauri ta k'araso har tana had'awa da sassarfa, shi abunma dariya yabashi, amma saiya danne yay guntun murmushi kawai.
Kayan ta d'aura saman akwati kafin tazo ta zauna a k'asa saman kafet d'in dake jikin gadon.
Shima sakkowa yay ya zauna kusa da ita tareda bata tea d'in, kanta dake duk'e ta girgiza masa alamar ta k'oshi.
Hannu yasaka ya d'ago ha6arta, ta lumshe idanunta dan batason su had'a idanu, saukar la66ansa kawai taji a bakinta, dan haka tai masifar rikicewa, jikinta yahau rawa tana yunk'urin zamewa amma babu dama.
Cikin sauke numfashi ya janye bakinsa yana fad'in “To Yaya zakisha yanzu kokuwa nakuma wani abun.......”
Da sauri tace, “Zansha d'in”.
Dariya taso kufce masa yanada yaga tayi da fuska, ga hawaye Na tsiyaya kamar anbud'e fanfo, jikinta kuwa banda tsumar tsoro babu abinda yakeyi. Kofin yakuma d'akkowa yabata, babu musu ta amsa tafara sha, dayake babu zafi sosai dandanan tasha da yawa sannan ta ajiye, bai takura mataba yabata maganin da saida akasha fama sannan Tasha, dan Jiddah batason magani sai dai dole, daka bata magani gara kaimata allura a wuce wajen kawai.
“Tashi ki kwanta to”.
Batayi musuba ta mik'e tahau gadon ta kwanta a mauk'ar takure, addu'a yay Mata ya tofa a hannunta ta shafa, shima ya tofa mata yana fad'in “ALLAH ya tashemu lafiya Amarsu”.
Itadai Jiddah kanta kad'ai ta iya d'aga masa ta lumshe idanu, shikuma yamik'e ya fita harda kashe Mata wuta tamkar gaske. Ganin haka yasata sauke nannauyar ajiyar zuciya da fad'in ”Alhamddllh” a fili..
Aliyu dake tsaye bai fitaba yana jinta saiya Saki murmushi. Baiyi motsiba yanda zata jisa, soyake saitayi barci. Cikin sa'a kuwa yaji numfashinta yafara sauka a hankali alamar tayi barci, dan tattare take da gajiya, ga rashin samun barcin da tai Na kwanakin bikinnan da damuwar mahaifinsu.
Wayarsa ya Ciro a aljihu ya danna, da hasken screen d'in yay amfani yataka zuwa gaban gadon a hankali.
Yaja kusan mintuna uku yana k'are Mata kallo dukda acikin hijjab take, kafin ya sauke numfashi tareda zare Mata hijjabin cikin dabara shima ya zagaya d'ayan gefen ya kwanta yanda bazataji motsinsaba balle ta farka..
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Hajiya deluwa Na hakimce a falo taringajin shigowar motoci ana rabga bud'a, mamakine ya kamata, tamik'e cikeda masifar mak'wafta sun takura musu, harda cewa “koma Ubanwaye ya haihu suka takurama kunnuwanmu?”. Jin hayaniyar tamkar a cikin gidantane yasata lek'awa Mamaki ya kamata matuk'a ganin a harabar gidansunefa, jikinta har 6ari yake ta fito, Cikin daka tsawa tafara tambayar y'an kawo amarya, “Kai lafiya kuka cikamin gida da ihu? Kodai 6atan Kai kukayine?”.
Wata hamshak'iya a cikinsu ta daddage ta callara gud'a kafin ta kalli Hajia deluwa shek'ek'e, “Madam Mijin naki bai sanar dake tauraruwarsa zata shigo baneba?”.
Kan hajiya deluwa saiya k'ara d'aurewa, yayinda can k'asan ranta kewani irin lugud'en tsoro, jikinta sai tsuma yakeyi.
Y'an kawo amarya kam basu kumabi takantaba suka nufi sashen Jiddah na da akabar Deluwa nan tsaye.
Jin tana Neman fad'uwa yasata saurin barin harabar gidan takoma sashenta, waya ta d'auka takira Alhaji garba, harta tsinke bai d'agaba, bata hak'uraba ta sake Kira. Yana d'agawa babuko sallama tahau masa tambayoyi. Tsaki yaja kafin yace, “inma kin kwantar da hankalinki ai gidan zan dawo Na kwana, dan babu angon dazai guji k'amshin a maryarsa a daren farko”.
Baijira cewartaba ya yanke wayar.
Cikin matuk'ar gigita hajia deluwa tayi wurgi da wayarta saman tayis tana huci tamkar wata bajima, wata ashar ta lailayo ta dire da cire d'an kwalinta ta d'aure k'ugu alamar yau akwai bala'i kenan.
⛹♀⛹♀saimun dawo jin yanda za'a k'are😂👌.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kiran sallar farko Na asubahi malam ya farka.
Hakama Jiddah motsinsane ya farkar da ita, ahankali take karanto addu'ar tashi barci, Sam tama manta a inda take, jinta a kamar ajikin mutum yasata bud'e ido sosai, gabantane ya fad'i jinta d'are-d'are a jikin Sheikh Aliy, tayi k'ok'arin jan jikinta amma saiya kuma rik'eta sosai, wayarsa yajawo a k'asan filo ya danna screen d'in ya kawo haske, ganin hakan yasa Jiddah cusa kanta a k'irjinsa saboda wata masifar kunya data baibayeta.
Idanunsa ya lumshe yana murmushi, baice komaiba ya kunna fitilar wayar sosai dan da'alama an d'auke wuta. Tashi yay zaune, Jiddah ma tasamu tamik'e tareda sauka ta d'ayan 6angaren tai saurin cacumo hijjabinta ta saka tana mamakin yama akai ta cire? Yaushe kuma ya sheikh ya dawo d'akin?.....
Motsin shigarsa bayi yasata waigawa ta kalli wajen, ganin harya shige saita koma ta kwanta tana shak'ar k'amshin turarensa daya barmata.
A haka yafito ya sameta, fuskarsa jik'e da ruwa alamar yayi alwala ya tako side d'in da take, “Kuluwa sarkin kuka a tashi ayi haramar alwala ko”.
Daga kwancen ta d'aga masa kanta, ganin bazata tashiba saboda yana d'akin saiya kamo hannunta ya sumbata sannan ya fice da cemata saiya dawo. Sosai Jiddah taji sumbar har a yatsun k'afarta, ta k'ank'ame jikinta tana matseshi waje d'aya, ga zuciyarta tana wani irin Kai kawo kamar zata fito, (duk abinda baka sababa arayuwa yanada wahalar d'auka) gaba d'aya Jiddah jitake al'amuran malam sunmata girma, tanada ilimi sanin zaman takewar aure, amma ko kad'an ba haka take tunaninsa ba.
Da k'yar ta iya tashi jin ya fice, itama alwalar tayo tazo ta canja kayan jikinta zuwa doguwar Riga.
Aliyu na fita sashen Maimuna ya nufa, zaune ya isketa a bakin gado ta tashi, shigowarsace ta sakata waigowa tana kallonsa, da sauri ta kauda kanta, dan wani Abu taji ya tokare mak'oshinta, atake tafara karanto sunayen ALLAH domin samun nutsuwa, kai kishi yanada zafi, amma tana rok'on Ubangiji yabata jarumtar koyi da matayen Manzon ALLAH wajenyin mai tsafta.......
Hannunta da ya sumbatane ya maidota hayyacinta, ta Saki murmushin k'arfin hali batareda ta kallesaba.
“Gimbiya gajiyarce har yanzun?”.
Kanta ta d'aga masa batareda ta kalleshi d'inba, kamata yay ya mik'ar tsaye.
A hankali tace, “Nagode yaya” ta ra6a ta gefensa tawuce bayi.
Binta yayi da kallo harta shige, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi da girgiza kansa kafin yajuya ya fita.
★★★★★
Aliyu bai dawo gidanba sai da gari yay haske sosai, lokacin har Jiddah ta kammala azkar d'inta ta gyara d'akin tsaf tasaka turare, a 6angaren iya gyara da girki batada Matsala, dan mahaifiyarsu tsaye take a kansu tun suna k'ananunsu, zuwa makaranta da suke bai hanata tsayawa wajen koya musu dukkan abinda zai amfanesuba idan sunbar gabanta, gakuma lecture ta musamman da Yaruwaiya taringama Jiddah gabannin aurenta.
Gawayin nan Na kunnawa ta kunna ta saka turare sannan tafito falo, Masha ALLAH tafad'a kwalla Na cika Idonta dajin k'arin k'aunar Uncle Yahya, basuda abinda zasu biya bawannan dashi saidai addu'a, da kowanne dangi zasu zama irin Uncle yahya da zuminci bai lalaceba a wannan zamanin. Saida ta zagaya har kicin da d'ayan d'akin kafin ta dawo tafara d'an kakka6e kurar daba'a rasaba, dan babu wani datti kam. Tana gamawa takoma d'akin da suka kwana tashiga wanka, alokacinne Sheikh ya dawo, jin motsinta a bayi yasashi komawa nasa sashen.
Maimuna ma dai haka ta dage tahau gyaran sashenta tana hawaye, harga ALLAH taji tananin kishin mijinta a yau fiye da ko yaushe, shikenan yazama nasu su biyu, a fili tace, “ALLAH ka bamu zaman lafiya, kasakamin danganar hak'uri nida y'ar uwata, ka kad'e dukkan wata fitina dazata saka mu fitini adalin mijinmu” da wannan tad'anji sanyi a ranta, tacigaba da gyaranta tana Kama dukkan addu'ar datazo bakinta. Tsaf ta kimtsa ko ina, ta shiga kicin tana tunanin miya kamata tayi musu Na Karin kumallo?.
Tsaf Jiddah ta shirya cikin atanfa ruwan hanta da zanen ganye manya ruwan toka, sai bak'i kad'an daya ratsa, kayan sunmata k'yau, dan d'inkin ya zauna d'as a jikinta, aunty Nafisa ce takaima telanta yayma Jiddah d'inkuna na garari, dan basujira lefeba suka had'a y'an kud'ad'ensu sukai Mata kusan kala ashirin danta samu Na kwalliyar amarci, tunda babu Wanda yasaka ran lefen, saikuma gashi an Kai ana gobe zata tare. Su hajiya Jiddah ba'a iya d'aurin y'an gayuba🤭😂. Zama tayi tanata juya d'an kwalin a hannu, “ALLAH Sarki Zarah, kullum saikin rok'eni na zauna ta koyamin amma nak'i, yau ga ranar hakan a gareni”.
Aliyu dake tsaye a bakin k'ofa yana saurarenta ya murmusa, kafin ya ida takowa ciki bakinsa d'auke da sallama.
Saurin Jan hijjab tayi zata saka amma sai yay azamar rik'e hannunta tareda rankwafowa ta bayanta suka kalli juna ta madubin. K'asa tayi da idonta kunya Na cinta tamkar zata nutse. Hijab d'in ya zare daga hannunta ya maida ya ajiye inda ta d'auka. “Daga yau inhar ba salla ba ko bak'i ko fita na haramta saka hijjab a gidannan madam”.
Kamar ta fasa ihu taji, dan wannan dokar tasa tamata tsauri da yawa, ta ina zata iya zama a gabansa ahaka? Ai da kunya......
Tunaninta ya katse saboda jin hannunsa saman kanta yana shafa kitsonta dayay masifar tafiya dashi, musamman ma Wanda ya zubo gaban goshinta da aka tufk'e ya kwanta luf a fuskarta, bakinsa yakai ya sumbaci kan yana fad'in “سُبْحَانَ اللهِ!
Subhanal-lah!. (Tsarki ya tabbata ga ALLAH.) Juddatulkhair gaskiya kitsonan ya kitsu, اللهُ أَكْبرُ!
ALLAHU akbar (ALLAH ne mafi girma)”.
Murmushi kawai tayi, aranta tana fad'in irin wannan santi haka? Kujimin mutum.
Shidai sai kuma shafa kitson yakeyi da mamakin yandama ta iya zama aka yisa k'ananu haka.
Ganin santin nashi yagaza k'arewa ta zamo ta durk'usa k'asa tana gaisheshi.
“Lafiya lau Amaryar Aliy, barkanki da shigowa gidan Aliyu. Jiya bansamu danar miki maraba ba saboda kina a yanayin da bai kamata a takurakiba”.
Murmushi tad'anyi kanta a k'asa tana kallon k'afarsa zuwa k'afar wandonsa na milk d'in shadda da bata sauka k'asaba sosai.
Kafad'unta ya kamo ya tadata tsaye, “Zauna ni Na d'aura miki d'an kwalin tunda kin kasa ke”..
Jiddah tarufe fuskarta da hannayenta tana fad'in “Na iyafa”.
“To zauna ki d'aura Na gani”.
“To saika fita”.
Y'ar dariya yayi yana zame hannunta data rufe fuskar, yace, “Na takura miki ko?”.
Kasa magana tayi, sai kanta data girgiza alamar a'a, shima bai samu bata amsaba ya zaunar da ita a stool d'in madubin yana k'ok'arin Ciro wayarsa a aljihu da ake Kira...........✍🏻
_A daina gulmar ya sheikh y'an Groups d'in mutum da duniyarsa😹, gashinan baiyi komaiba dai😂, duk kunbi kun saka masa ido, shiyyasa yayi kawaici😝🤣⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀_
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[43➖44]_*
.............Zaman amsa wayar yayi d'an kwallin Jiddah a hannunsa, yanda yake amsa wayar zaisa ka tabbatar shi da malam ne, kusan mintuna uku kafin suyi sallama ya ajiye wayar saman gado yamik'e yana fad'in “Baba na gaisheku ke da auntynki”.
“Muna amsawa, yana lafiya shima?”.
“Lafiya lau yake”. ‘Yay maganar yana warware d'an kwalin’.
Duk yanda yaga Maimunatu nayi haka ya lankwasa d'an kwalin kafin ya d'ora akan Jiddah, itadai saima ta hangame baki, dan da farko dukta d'auka wasa yakeyi. Kasa daurewa yayi.
tace, “Kawo Zan iya d'aurawa fa”.
“Yarinya kin makaro kuma ai, kedai tsaya kawai”.
Babu yanda ta iya dole ta tsaya tana kallon ikon ALLAH itakam. Aiko sai gashi ya d'aura mata, sai dai yanda yay d'aurin dolene kayi dariya, saikace irin tsofaffin yarabawannan Wanda suka k'ware a iya d'aura gwagwgwaro. Hakanne yasaka jiddah saka dariya batareda ta shirya ba, shima dai abin yabashi dariya dan haka ya d'an dara yana fad'in “Wannan bai yiba kawo a sake”.
“Nidai Na gode, bara kawai Na d'aura Wanda Na iya”.
“Haba hajiyata, d'aurin nan dai duk wanda ya gansa dolene yabani Aword akansa, kinga kuwa yanda kika wani had'u”.
Jiddah ta rufe fuskarta da hannu tana dariya, sosai rayuwarsa take birgeta, shi mutumne mai sauk'in kai, kuma haka yakamata kowanne miji ya kasance da iyalinsa kodan shima ya samu farin ciki, MANZON ALLAH har y'ar tsere yanayi da iyalinsa saboda susami farin ciki, amma banda mazanmu Na hausawa, wani zakiga yanata dariya da fara'a a waje, amma da zarar yashigo gida saiya hau kumbura fuska tamkar fulawar da aka kwa6a danyin burodi. Hakan kuma yana k'untata iyalansa sosai, kwata-kwata mazanmu basa koyi da ilimantarwar da addininmu yay mana akan rayuwar aure, kowa tasa yake tsarawa, alhalin kafin ya kawoki gidansa lalla6aki yake da soyayya tamkar kwai a cokali..........
“Tunanin mi kikeyine Jiddah?......”
Firgigit tadawo hankalinta saboda ta6atan da yay, ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in “Babu komai”.
“Okay, to tashi muje ki gaida auntynki ko”.
Kanta ta jinjina masa, sannan cikin marairaicewa tad'an kallesa ta janye idonta, “Dan ALLAH na saka hijjab? Wlhy bazan iya zuwa gabanta a hakaba”.
Murmushi yad'anyi, “Uhm saka, amma fa yau kad'ai”.
“Nagode”.
Tunda suka fito take kallon tsakar gidan, bawani k'ato baneba, gashi nan dai d'an cif dashi, rayuwa dai ta duniya ya wadatar dasu Alhmdllh, dan bazasu dai takuraba koda ansamu yara a nan gaba, tunda suka iso k'ofar d'akin Maimuna gabanta ke fad'uwa, haka kawai sai takejin tsoro-tsoro, dan bata mance had'uwarta da Hajia Deluwa ba.
Shine ya fara shiga bayan yayi sallama Maimuna dake zaune ta amsa masa, murmushi yamata kafin yay mata alamar tare yake da bak'uwa.
Maimuna data fahimci shida Jiddah ne saita mik'e ta nufo inda yake, hannu ya bud'e mata alamar tazo, kansa tayo gadan-gadan, saida tazo dab dashi saita waske tanufi k'ofa.
Baki bud'e yabita da kallo, tajiyo tamasa gwalo kafin ta bud'e labulen tana fad'in “Amarya shigo mana”.
Kan Jiddah a k'asa tad'anyi murmushi kafin tashigo da sallama, Maimuna ta amsa tana kama hannunta suka ida shiga cikin falon.
Aliyu dake zaune yad'ago yad'an kallesu, ganin kan Jiddah a k'asa yake saiya harari maimunatu. Yanzuma murmushi tad'an masa, kansa ya nuna wai shi?. Saita girgiza kanta alamar A'a.
Itadai Jiddah batasan mi sukeyiba, data zaunama saitacema Maimunatu “Aunty ina kwana?”.
Zama kusa da ita Maimunatu tayi tana amsawa fuskarta d'auke da murmushi, “Lafiya lau Amarya, ina fatan kin tashi lafiya? Ya kuma bak'unta?”.
“lafiya lau aunty”.
“To masha ALLAH Amarya, yanzu dai ga abinci, oga bismillah”.
Aliyu dake kallonsu yad'anyi murmushi, yayinda acan k'asan ransa yake ambata ”Matar kwarai rabin addini, duk Wanda yasamu yagama dacewa”.
A filait d'aya Maimun ta zuba musu soyayyar doya, sannan ta had'ama kowa tea.
Har Oga da Uwargida suka fara ci Jiddah takasa, sai juya cokali take a cikin shayin, Maimuna ce tayi magana ganin Jiddah bataci ko sau d'ayaba.
“Amarya kobak'ya sonshi a canja mikine?”.
Da sauri Jiddah tace, “A'a aunty”.
“To dan ALLAH kici, nanfa gidankine, mukuma y'an uwankine, babu batun bak'unta a tsakaninmu kinji”.
“kai Jiddah ta kuma gyad'a mata”.
Aliyu dai najinsu baice komaiba.
Da k'yar dai Jiddah tasamu tad'anci kad'an, shima dan Maimunatu tana magana ne idan taga tayi shiru, ahaka suka kammala, Maimuna tafara tattare kayan, hakanne ya saka Jiddah mik'ewa ta tayata, saida suka kimtsa wajen sannan suka dawo suka zauna.
Zama Aliyu ya gyara tareda dai-daita kansa yakoma fuskar babu wasa, hakanne yasakasu suma duk suka nutsu wajen maida hankali a garesa.
Yay maida idonsa a Kansu “Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu”.
Atare suka amsa masa.
“Alhamdulillahi, godiya ta tabbata ga ubangijin talikai daya taramu anan wajen matsayin Abu d'aya, wannan ikonsane kuma hakan rubutaccene agareshi tunkan musan zamuzo duniya, shine mai tsara yanda yaso, yakuma tabbata ga Wanda yaso. Da farko Jiddah muna miki barka da zuwa cikinmu, muna kuma miki fatan alkairin samunki kamar yanda muke k'yautata miki zato, kamar yanda na shaida miki tun farko ina zaune da matata lafiya, kuma tanamin dukkan abinda Na buk'ata, idan kinga sa6ani a tsakaninmu saina tsakanin harshe da hak'ori, k'yawawan halayenta yake k'ara girmama k'aunarta a raina kullu yaumin, insha ALLAH indai kika kwantar da hankalinki nasan zaman lafiya zai cigaba da girmama a gidanan. Maimunatu ga Jiddah nan, Y'ar uwarki kuma k'anwa a gareki, kamar yanda Na fad'a miki ina k'yautata zato a gareta, domin mutuniyar kirkice da kowa ke yabon k'yawawan halayyarta, kamar yanda nake k'aunarki a zuciyata itama inajin k'aunarta, yarinyace mai tarbiyya da sanin yakamata, insha ALLAH ina fatan bazaku samu matsalaba koda anan gaba. Nasihar dazan mana gaba d'aya amatsayinmu na iyali shine hak'uri, hak'uri jagorane, kuma katangane ga kowanne bawa, sannan kuma mutuncine ga cikar kamalar d'an Adam, duk inda akace maka wane yanada yawan hak'uri, to lallai zaka sameshi nagartaccen mutumne shi abin son koyi ga kowa, babu wata nasara dake tabbata saida hak'uri, idan babu hak'uri ko ibadar da mukema bazamu jureba, dukanku Na yarda da tarbiyyarku, ina kuma k'yautata zaton samun farin ciki a gareku, ayanzu banida wani makusancin daya kaiku, dan kafin kowa yasan matsalata kune zaku fara sani, hakama a tsakaninku, kunfi kowa kusanci da juna, dan kafin Abu ya sameku wani yataso daga danginku kunma kankushi, so babu kusancin da yakai wannan muhummanci kuwa a tsakaninmu, ina rok'inku amatsayinku Na masu ilimin addini, kunsan dokar ALLAH da abinda MANZONSA ya koyar damu, to ina fatan zamu gina rayuwarmu akan wanan tsarin, dan bai k'yautu ga d'iyan musulmai ba ace yana koyi da wani Abu Na yahudanci, dukkan mai kwaikwayon wani Abu daya fita daga tsarin koyarwar MANZON ALLAH da sahabbansa, to lallai za'a tasheshi da Wanda yake kwaikwayo aranar tashin alk'iyama, to duk abinda zamuyi yakamata mubishi a bisa tsarin addinin islama saimuga mun samu kammu cikin aminci da kwanciyar hankali. Lallai shi kishi gaskiyane, duk kuma macen dazaka ajiye bata kishinkama wannan ba Sanka takeba, to amma muringa tunawa ba kishin matan yanzu ne kishiba, dan wani kishin banda tsantsar jahilci babu komai a cikinsa, kishi mai cike da tsafta shine rige-rige wajen k'yautatama miji tamkar yanda matan msnzon ALLAH suka gunadar da nasu, tananne zakuga miji ya karkata ga son wata, dan ita zuciya Na son mai k'yautata Mata, sannan tanak'in mai munana Mata, harga ALLAH inajin sonku da k'aunarku a raina ku duka, wadda zatafi zama a zuciyata kuma yana a gareku, dan wadda ta kwantarmin da hankali da bani kulawa itace da wannan nasarar, abinda zaisa muji sassaucin kishin juna kuwa shine tsoron ALLAH da danne zukatanmu, mu d'auki rayuwar tak'aitacciya mai yankewa babu shawara, muringa tuna zafin d'aukar rai da kwanciyar kabari da tsayuwar hisabi, duk Wanda ya munanama d'aya acikinmu koda da hararane wlhy sai ALLAH ya tambayesa, dan haka saimu kiyaye, ba shakkan ganin idona zakuyiba, kuji tsoron Wanda ya haliccemu baki d'aya, sannan Ku tayani da addu'ar samun damar yin adalci a tsakinku, dan ina tsoron ranar da za'ace gani natashi cikin mutane masu shanyayyen jiki saboda rashin adalci a tsakanin iyalina. Daga k'arshe ina kuma rok'onmu dan ALLAH muji tsoron ubangiji adukkan abinda zamu aikata a wannan zaman, karmu zama cikin masu shiryama juna makirci ko jifan juna da sharri koda Na maganane, karmu biyema duk Wanda zai kawo 6atanci a zamantakewarmu, koda kuwa acikin makusantanmu ne, karmu biyema sharrin zuciya ta sak'a mana abinda zamu dawo muna Dana sani, muringa tinawa a kowanne motsinmu akwai mala'iku dake biye damu rik'e da alk'alaminsu, kuma Ubangijin al'arshi yana jinmu yana ganinmu, ALLAH yay muku albarka yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali Na har abadan”.
Kowacce ta amsa da amin, zukatansu duk sai suka kuma raunana dayin sanyi, aganinsu minene abin zafafawa akan wannan gajeruwar rayuwar da bakada tabbacin kaiwa safiya.......
Aliyu ya katse musu tunani da fad'in “Maimunatu mizakice?”.
'Dan murmushi tayi na k'arfin hali tana had'iye hawayenta da suka cika mata ido, “Duk abinda Zan fad'a Yaya ka fad'eshi, sai dai nace ALLAH yabamu zaman lafiya da hak'urin jure yau da gobe, dan itace mai wahalar, insha ALLAHU zaka samemu fiyema da yanda kake tunani, kamar yanda kafad'a hak'uri shine jigon komai Na rayuwa, ALLAH ya bamu mai amfani, yakuma baka k'arfin gwiwar adalci agaremu, dukda Alhmdllh kakai ayaba maka, dan nidai Zan iya bugar k'irji ako ina nace mijinmu adaline, ya banbanta da maza da yawa dakan wulak'anta matansu aduk lokacin da zasu k'ara aure, sannan kuma bakaimin romon bakaba nacewa k'addarace ta sakaka k'arawa badan kasoba, kafito kanka tsaye kasanarmin sonta kakeyi shiyyasa zaka aurota, kaga hakan dakayi ka k'ara Mata kima da daraja a idona, sannan baka tozartaniba yanda Zan kalli k'ara aurenka a matsayin gazawata ba, kabi dukkan sharud'a da matakan da kowanne musulmi adalin magidanci yakamata ace ya d'ora gidansa akai, dan maza da yawa suke gur6ata zaman lafiyar gidansu tunkan aure da bayan shugowar amarya, harga ALLAH ina k'aunar y'ar uwata a matsayinta Na musulma kuma Mace, abinda zai k'ara sakamin ita arai kuma shine zamantakewarmu cikin aminci babu cutar da juna ko k'untatawa, ALLAH yabamu zaman lafiya yakuma k'ara mana tsoronsa koda gujema azabar wuta”.
Amin, jiddah da malam suka fad'a. Sannan ya d'ora da fad'in “ALLAH yaymiki albarka, yakuma k'ara muku k'arfin gwiwa bisa k'yak'yk'yawar niyyarki”.
Nanma Jiddah ta amsa da amin.
Ya maida kallonsa ga Jiddah itama, “Jiddah fa mizakice?”.
Kai Jiddah ta girgiza, cikin sanyinta tace, “Duk abinda yadace kun fad'a, fatana ALLAH yabamu k'warin zukatan aikatawa da hak'uri, sannan nima harga ALLAH Aunty tashiga raina saboda k'yak'yk'yawan halinta da awannan zamanin yay k'aranci ga mata, akanyi dogon bincike kafin asamu mace irinta, wadda miji zai k'ara aure sannan ta kar6i matar da hannu biyu dakuma zuciyar musulinci, nagode sosai aunty, halayyarki na gari da ya sanarmin tunkan shigowata gidannan tabbas nagansu a yanzu a gareki, ALLAH yabani ikon koyi da nagartarki”.
Murmushi Aliyu yayi sannan ya amsa da amin. “To Alhamdullahi matana nagodema ALLAH Na gode muku, sai maganar kwana, Yaya kuke ganin za'ayi?”.
Itadai Jiddah k'asa tayi da kanta, dan a ganin wanan ba huruminta baneba yanzun.
Maimunatu tayi murmushi tareda d'an kallonsa ta kauda idonta. “Nidai a 6angarena banida matsala, akan kwana hud'un a marya Na k'ara muku shida, wannan shine gift d'ina agareku na aure, sannan aganina kwana bibbiyu Alhamdllh, amma k'anwata ya kika gani?”.
Shiru Jiddah tayi tana sunkuyar dakai.
“Kiyi magana k'anwata, dan kema kinada hak'in fad'ar ra'ayinki”.
“duk yanda kikace yayi”.
Maimuna zata sake magana Aliyu ya dakatar da ita, “Yanda kika fad'ad'in yayi, sannan kuma maganar kwana shida da kika k'ara mana mun amshi uku kawai, mun gode”.
“Kayi hak'uri babu jayayya a tsakaninmu, idan kukak'i amsa sainaga kamar kun rainane”.
Harara yad'an zabga Mata sannan yace, “To mungode”.
Itadai Jiddah Uffan batace dasuba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Abba tun yana zama Abuja da shauk'i harta fita aransa, gashi sai cinye y'an kud'insa yake wajen biyan hotel da abinci, kullum ya zagaya gidan Alhaji Sammani sai mai gadi yace ai bai dawoba.
Yauma dai yana tsaye a bakin gate sai hucin 6acin rai yake saboda abinda mai gadin yamasa Na wulak'anci da jifansa da Kalmar maula, da girmansa da mutuncinsa a kirasa d'an maula?, horn d'in mota ya sakashi saurin d'agowa, dad'i ya kamasa domin ganin Alhaji Sammani, ajiyar zuciya ya sauke tareda ambaton Alhamdullahi.
Har driver zai shige Alhaji Sammani ya dakatar dashi saboda ganin Abba dake jingine a jikin motarsa, ya sauke gilas lokacin da suka tsaya dai-dai saitin Abban.
“Wanake gani haka kamar Alhaji Zakari yaro?”.
Abba yay dariya mai cike da tsantsar farin ciki yana matsawa jikin motar Alhaji Sammani, “Wlhy nine kuwa abokina, inata zaryar ganinka amma hakan yaci tura”.
“Ashsha Alhaji zakari, wlhy banda wannan labarin, gashi kuma kullum ina gari, yanzu dai shigo muje ciki”.
Jikin Abba Na tsuma ya bud'e motar ya shiga kusada Alhaji Sammani, sai wani dad'i yakeji dajinsa a sama, jiyake yagama da matsalar Alhaji garba ma kawai.
😹😹🤫Abba😂
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Koda Alhaji garba yadawo gida baiko dubi sashen Hajia deluwa ba balle tasan da dawowarsa, itako tanacan tana cika da bunk'asa har yanzu, yayinda Bala da Ashir keta kuma tunzurata da tsinema amaryar Uban nasu, har suna fad'in tabasu dama su lakad'a mata duka yanda gobe zata tattara da k'afarta tabar musu gidansu.
Kumbura Hajia deluwa ta sakeyi, dan ita tafison Alhaji yadawo sufara cashewa kafin tabi takan waccan banzar, dan bak'aramin iskanci k'awayen Amaryar suka 6ararba yau a gidan, gud'a da habaici babu irin Wanda deluwa batajiba, gashi sun fita yawa, tanajin tsoron ta fita su lakad'a Mata duka. Hakanne yasata mak'alewa akan cewa da Alhaji zatayi badasuba.
Shikam baimasan tanayiba, yanacan yasamu tarba ta musamman ga amarya, tunima ya manta dawata banza hajia deluwa, Amaryarsa kawai yakeji da gani, yayinda ta gama kasheshi da dabaibayeshi da soyayya itakuma.
Har kusan 11 babu Alhaji babu labarinsa, hakanne yasaka su Ashir fitowa zasu sashensu, mamakine ya kamasu ganin motar Abbansu, Bala yakasa hak'uri yaje yana tambayar mai gadi ko Alhaji ya shigo. Mai gadi yace, “Ah tun kusan takwas da rabi ai Alhaji ya shigo gidan ai”.
Idanu bala ya zaro, sannan cikin sassarfa yanufi sashen Hajia deluwa ya shaida mata.
Wata uwar ashar ta lailayo ta dire, kafin ta fisgi waya tahau kiran Alhaji, amma harta k'araci ringing ta katse bai d'agaba, saida tayi Kira kusan goma sannan aka d'aga.
Cikin masifa tace, ”Sannu munafiki, to ALLAH ya tona asirinka kadaw......”
A wata irin muryar kwarkwasa Hajia bariki ta katseta, “O madam kekuma haka naki salon yake babu tarbiyya da girmama miji? Please kid'an jinkirta yana sunnah ne, zuwa safiya zaki iya ganinsa bye”.
Bata tsaya jin zagin da Hajia deluwa ta antayo mataba ta yanke wayar tana dariya.
Zubewa kawai a k'asa hajia dealuwa tayi ta daddage ta kwad'a ihu🤫😹🤣.............✍🏻
*_Gobe idan ALLAH ya kaimu bazanyi typing ba sisters, amma inada page daban k'arasaba Zan k'arasashi anjima kad'an insha ALLAH, Na turo muku anjiman kokuwa abari sai gobe?_*
_Wanda naga ra'ayinsu yafi yawa to shi za'abi😹🚶🏻♀_
_Barkanmu da Juma'a_☄🎇
**_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[45➖46]_*
..............Hira suka cigaba dayi a sashen Maimunatu har kusan sha biyun rana, itadai Jiddah bama saka baki takeba, sai idan sun sako sunantane take d'an murmushi, Sheikh Aliy ne yafara tashi ya fita saboda kiran da Malam Mustafa yaymasa akan gashi da bak'i a k'ofar gida.
Bayan fitarsane Maimunatu ma ta mik'e tana fad'in “Kinga Jiddah bara nashiga kicin rana tayi, ga hotuna ki kalla karki zauna shiru”.
“A'a aunty bar hotunan, daga baya saina kalla, muje kicin d'in”.
Cikin waro idanu waje Maimuna tace, “Wai inani ina saka amarya aiki, wlhy Na yafe miki zauna ki huta abinki”.
Duk yanda Maimuna taso Jiddah ta zauna k'i tayi, tabita kicin d'in suka fara aiki tare, sunayi Maimuna nad'an janta da hira, mafi yawan hirar itama duk akan abinda yashafi gasar da Jiddan taje Saudia ne, hakanne yasaka Jiddah d'an sakin jikinta da ita tana bata labari.
Har suka gama girkin da kimtsa kicin d'in Aliyu bai shigoba, time d'inma anata shirin shiga sallar zuhur, dan haka Jiddah tanufi sashenta cikeda jin Maimuna ta kwanta mata a rai, itadai koda ake cewa kishiya bata maka Abu dan ALLAH saidan kissa ta aminta da Maimuna da zuciya d'aya, kuma insha ALLAH zata bata had'inkai su zauna lafiya, dan tunda suke da Ummansu ba'a ta6a jinta tana hayaniya da kishiyaba, to ita mizaisa tayi da tata.
Da wannan tunanin takoma sashenta, tsaf ta iske komai yanda ta barsa, tashiga bayi ta d'aura alwala tafito domin gabatar da salla. Bayan ta idar kayan jikinta ta cire ta sauya da doguwar riga ta material rowan ganye mai haske, sunmata k'yau dan d'inkin yamata d'as, tad'an gyara fuskarta sannan ta saka turare. Batayi yunk'urin komawa sashen Maimuna ba, saima laluben wayarta data shigayi dan san kiran su Umma, ta gama zazzage handbag d'inta amma babu wayar, shiru tad'anyi tana tunani, saikuma zuwa can ta dafe kanta dan ta tuna wayar na a hannun walida, tasan itama mantawa tayi bata bataba, saikuma duk taji tadamu, ga kewarsu dake cin ranta, kwanciya tayi a gefen gadon, zuciyarta Na karyewa da tunanin rayuwa mai sauyawa a kowacce safiya.
Saida aka idar da salla Aliyu ya shigo gidan, kai tsaye sashen Maimuna ya nufa, babu kowa a falo dan haka yanufi d'akin barcinta.
Zaune ya isketa tana karatun Qur'ani, ya jawo stool d'in madubi ya zauna yana sauraren zazzak'ar muryarta. Dukda taga shigowarsa bata tsayaba saida takai inda ya kamata ta tsaya sannan ta rufe tana ajiyewa da kallonsa.
“Sannu da shigowa”.
“Yauwa Maimoon, bak'uwar takifa? Tad'an sake dake ko?”.
Murmushi Maimuna tayi tana mik'ewa tsaye da cire hijjabinta, “Ai tanada sauk'in kai Yaya, tarema mukayi girki, duk macen da za'ama kishiya takan Shiga matsananciyar damuwa saboda batasan wa za'a kawo mataba, dan y'ammatan yanzu burinsu dasun shigo su Kora ta ciki waje, watama tun a y'an kawota zasusaka jikin Uwargida kuma sanyi, saboda gugar zana da habaici, amma Alhamdllh ni sai Ubangiji yaymin k'yauta da samun baiwarsa kamila mai addini da tarbiyya, wlhy da ace amarya zata kasance irin Jiddah da babu wata Uwargida da zata Gaza kwantar da hankalinta a zauna lafiya, dukda har yanzu banida tabbaci akan Yaya zata kaya nan gaba amma ina kyautata Mata zato da fatan tabbatuwar nagartarta”.
Murmushi Aliyu yayi yana kamo hannun Maimuna cikin nasa, ya matso da ita gabansa idonsa akan fuskarta, “Maimuna bake kad'ai kika dace da samun Jiddah matsayin abokiyar zamaba, har itama tadace da samunki, sai nikuma Na dace da samunku baki d'aya, kinyi abinda Mata da yawa suka kasa a wannan zamanin, dan inhar akace miji zai k'ara aure to shikenan zaman lafiya ya k'auracema gidansa, tsakaninsa da matarsa sai Y'ar harara da ya6a magana, amma ke sai kika Nuna kin cika Y'ar halak mai aiki da ilimi da tarbiyya bisa addinin islama, duk wandda yazama mai k'yak'yk'yawar zuciya ALLAH bazai ta6ar dashiba Maimoon, inhar kayi k'yak'yk'yawa saikaga k'yak'yk'yawa, da sauran Mata zasuyi koyi dake da dayawa sunzama taurari a zukatan mazansu kamar yanda kika zama a tawa zuciyar, ALLAH yay miki albarka kinji, nasan kinajin kishin amma kike dannewa saboda k'yak'yk'yawar zuciyarki”. ‘ya k'are maganar da rungumeta a jikinsa’.
Itama rungumeshin tayi tanajin k'arin k'aunarsa.
Sun jima a haka sannan ya saketa,
“Hayaty bara na sauya kayanan nad'an kwanta Na huta”.
“Kwanciya kuma Nurry, abincinfa?”.
Cikinsa yad'an shafa yana yamutsa fuska, “Mikuka dafa mana a gidan?”.
Cikin tsokana tace, “Taliya da mai da yaji”.
“Taliya kuma?”. ’Yay maganar cikin had'e fuska’.
Maimuna ta sanya dariya tana shafa k'irjinsa, “maida wuk'ar Alhaji wasafa nakeyi, kus-kus ne da miyar kayan lambu”.
'Dan hararta yayi, “Zan kamakine ai, dama kinsan d'azun kinada laifi”.
“Ni munari, baka mantuwa Yaya?”.
“Aiba tsufa nayiba balle nafara mantuwar, zoki bani abinci naci naje nad'an huta”.
Koda tazo bashi abincin zata Kira Jiddah cayay “Kinga barta, kinga d'azun batawani ci abun kirkiba saboda bata saba damuba, mubata lokaci koda na kwana biyu haka, bani naci idan Zan wuce saina tafi Mata dashi”.
“Okay Yaya hakanma yayi gaskiya, dama inata tunani tun d'azun akan hakan wlhy”.
Tare ta zuba musu sukaci, bayan sun kammala sukai hamdala ga Ubangiji.
Kulolin tasaka a karamin basket duka tace ya tafima Jiddahn dasu, “Yazakice a kai duka, yamata yawa ai, k'ila kuma wani yazo”..
“A'a kakai Mata Yaya, dan yanzu hakama saikaga ita tayi bak'in ni banyiba ai”.
Baice komaiba ya amsa ya fita.
Kwance ya isketa tana barci, da alama daga tunaninta barcin ya saceta, abincin ya ajiye gefe ya gyara Mata kwanciya dan tana a bakin gadone sosai.
Shima fita yay zuwa sashensa danya d'an kwanta kafin la'asar.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A katafaren falon bak'i Na gidan sanata Sammani aka sauke Abba, dan danan aka cika gabansa da kayan motsa baki.
Bayan kamar awanni biyu da shigar Alhaji Sammani saigashi ya shigo falon da Abba yake, zama yay suka gaisa cikin fara'a da tambayar iyalai. Daganan suka d'ora da hira.
Sai da Abba yabari hirar tayi nisa sosai sannan ya sakkoma Alhaji Sammani buk'atarsa ta rancen kud'i miliyan hamsin.
Wani kallon K'asan ido Alhaji Sammani yakema Abba, tuni kuwa fara'ar fuskarsa ta gushe, ya gyara zamansa yana fad'in,
“Kaiko Alhaji Zakari duk mizakayi da wad'annan kud'in zunzurutu haka?”.
Cikin nisawa Abba yace, “Wlhy Alhaji Sammani wani business yazomin babu shiri, gashi kuma zamuyi had'akane da wani, nikuma kud'in hannuna narigada na zuba kaya dasu”.
Alhaji Sammani yay murmushin takaici yana kallon Abba sosai. “Lallai Alhaji zakari Kai lafiya lauma kake, yo dole nace nafiya lau kake mana, Kai kud'in Business kake nema yanzu, bayan kuma kanayin wani, niko yanzu maganar nan danake maka tunanin yaya zan shirya kamfen a shekara mai zuwa nake, maganar gaskiya bara namaka gwari-gwari, banida wad'annan ruwan kud'in da kake buk'ata, idan kace nabaka rance ina kaga kud'in biyanama? So karka kawo abinda zai ruguza mana zuminci please ”.
Tunda Alhaji Sammani ya fara magana Abba ke kallonsa baki hangame kawai, harshine zai buk'aci abu wajen Alhaji Sammani ya hanashi? Yamanta wahalar Campaign da sukai masa? Ya manta kud'ad'ensu da suka zuba danya samu mulki?....
Afili saiya kuma kwantar da murya ga Alhaji Sammani, “Haba abokina, nasandai wad'annan kud'in bazasu gagarekaba, yazan kawo maka matsalata ka kalleta a k'amar matsala, dan ALLAH ka duba mana”.
Mik'ewa Sanata Sammani yayi tsaye yana ta6e baki, ya Ciro dubu Hamsin a aljihunsa yana ajiyewa gaban Abba, “Alhaji Zakari ga wannan kasha mai, ka gaida iyalan naka da k'yau”.
Sakatata Abba yabi Alhaji Sammani da kallo harya bar falon, ya maida kallonsa ga kud'in daya ajiye masa zuciyarsa Na tafasa, waishi wannan mutumin zaima haka saboda sunriga sun tura motar ta tashi? A lallai lamarin y'an siyasa abin tsorone, wato lokacin da suke buk'atar mulkime muke mutane a wajensu? Cikin cizon yatsa Abba yamik'e yana harar kud'in.
Harya Kai k'ofar fita kuma yadawo yana kwafa ya kwashe kud'in ya zuba a aljihu yana fad'in “Garama Na d'auka narage asarar danayi”. (🤣🤣ho Abbanmu).
Nadai tak'aice muku bayani aranar Abba yabaro Abuja ya kamo hanyar kano, sai surutai yake a mota tamkar sabon kamu.😂
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai gabannin la'asar Aliyu ya tashi, wanka yayi danyaji k'arfin jikinsa, barcin dayayi yasaka jikinsa nauyi sosai.
Jiddah kam barcinta bai wuce Na awa d'aya ba ta farka, Tasha mamakin yanda akai takoma tsakkiyar gadon, tana sakkowa taci Karo da kayan abincin da Aliyu ya ajiye, tashitai taje ta duba ganin abincine saita rufe tafara shiga bayi, bayan wasu mintuna tafito, zama tayi taci abincin, dan dama yunwa takeji.
Bayan ta kammala d'akkowa tai tadawo falo, tana zama Ana maido wuta, taji dad'i sosai, saidai kuma matsalar ma ba'a had'a Mata kayan kallonta ba, koma fiddasu a Kwali su Yaruwaiya basuyiba, komawa tayi cikin kujera ta kwanta tafad'a duniyar tunani. Har aka Kira sallar la'asar tana falon, daga bisani takoma d'aki domin yin sallah.
Bayan an idarne Aliyu ya shigo, sanye yake da yadi mara nauyi kalar shanshanbale mai duhu, kansa da hula kamar ko yaushe.
Kan Jiddah a k'asa tace, “Sannu da dawowa”.
“Yauwa amarya, ya bak'unta?”.
Murmushi kawai Jiddah tayi amma batace komaiba.
Shima saiya zauna a bakin gadon yana fad'in, “Naga kin kirani d'azu a waya, nasakata a silent na kwanta barci, sai dana tashi nagani, mike faruwa?”.
Kallonsa tayi da mamaki, “Aini wayarma bata wajena, na mantata a gida”.
“Tofa, to kosu Zarah ne dai?”. ‘yay maganar yana Ciro wayar a aljihun gaban rigarsa’.
Jiddah tace, “K'ila sune to”.
Baice komaiba yashiga k'ok'arin kiran Number tata, amma kuma a kashe yanzu, kallonta yayi yace, “wayarkuma a kashe ai”.
“k'ila babu cajine, ni nazatama zasuzo yau amma babu Wanda yazo saikace basa sonama”. ‘Tak'are maganar Idonta na cika da k'walla’.
Fuskarsa d'auke da murmushi yace, “Malama waya fad'a miki dama ana zuwa gidan amarya irin wannan ranar?”.
Matso hawayen tayi sannan ta saka gefen hijjab ta share.
Shi dariyama tabashi, yacire hularsa yana ajiyewa gefen gadon, “Kincika shagwa6a da sonyin kuka, kuka yana miki matuk'ar sauk'i hajiyata, toyi hak'uri insha ALLAH nasan zasuzo kinji”.
Kanta ta jinjina masa, shikuma yay murmushi yana mik'ewa, “Bara naje gadon k'aya na gaida malam dasu hajia, inaga sai dare zan dawo insha ALLAH”.
“Adawo lafiya, ALLAH ya tsare hanya”.
“Amin ya rabbi Khairunnisaa”.
Harzai fita yadawo ya manna Mata Sumba a kumatu sannan ya fice.
Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke, harma tad'an fara sabawa da halayyarsa itakam.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ihuntane yasaka Bala da Ashir shigowa aguje suna fad'in “Mami lafiya? Mi akayi mikine?”.
“Ashir bazaku ganeba, zuciyata neman tarwatsewa takeyi, yanzunan har akwai ranarda dama kishiya zata fad'amin son ranta akan mijina? Ni ni Deluwa? Wlhy sai matarnan tabar gidannan koda zanyi yawo tsirarane kuwa, har abada dagani sai y'ay'ana zan rayu a gidannan”.
Cikin fusata Ashir yace, “Mami ki kwantar da hankalinki, wlhy idan kika bamu dama bazata cika satiba a gidannan zata Kama gabanta, narasa mike damun kan Dady, yarasa wadda zai kwaso mana sai wannan tsohuwar karuwar, ALLAH garama yarinyar nan Jiddah, dama ita kika hak'ura muka zauna da Dady bai kwaso mana wannan motar hayarba ai”.
Hararsa hajia deluwa tayi, “Kai dan Ubanka waya fad'a maka kishiya duk k'ank'antarta tanada sauk'i, dalla kuficemin anan kafin najuye muku takaicin dake kaina yanzunnan”.
Kallon juna sukayi shi da bala suna ta6e baki, suka fice suka barta tana cigaba da borinta da zagi kwando-kwando ga Alhaji garba da amaryarsa.🙃😹
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai 10:30pm Aliyu ya dawo gida, tunda magriba ya dawo anguwar amma bai shigoba yana massalaci, bayan sungama karatun dare yakuma barin anguwar, sai dai baiwani dad'eba yadawo, Kai tsaye gida ya shigo, tsitt kakeji tamkar babu mutane, leda d'aya ya d'auka yanufi sashen Maimuna, kwance ya isketa harma tayi barci, ganin magani a durowar gefen gado yabashi tabbacin batada lafiya, zama yay kusa da ita yajanye bargon datake ciki yana ta6a wuyanta zuwa goshi, jikinta ringim da zazza6i, tausayintane ya kamashi, bai tadata ba ya tofeta da addu'a ya maida mata bargon sannan yafito.
Kicin d'inta ya shiga yasaka Mata abin cikin ledar a firij sannan yadawo falo, tea d'insa da kayan fruits data gyara ya d'auka yafita yaja Mata k'ofar.
Saida Yakoma mota ya d'auki d'ayar ledar sannan yanufi sashen Jiddah itama.
Bai isketa a faloba, dan haka yawuce bedroom. Zaune take tana duba littafin Umdatul Ahkam, kanta ta d'ago tana amsa masa sallamar, ganinsa da kaya saita ajiye littafin tamik'e ta amshesa tana masa sannu.
“Yauwa Juddatulkhair, ya zaman shiru? Amin afuwa kinsan nid'in sai a hankaline”.
Fusakarta d'auke da murmushi amma batace komaiba.
Zama yay kan k'aramin kafet d'in gaban gadon ysna kallonta, itakam takasa kallon nashi, tana k'ok'arin aje kayan gefe tace, “Aunty fa batada lafiya, amma tasha magani tun d'azu ta kwanta, zan kiraka amma ta hana”.
“Eh naje wajenta kafin nashigo nan, Mata kuna k'ok'ari, tunda tasamu cikinan haka taketa fama, nikaina bansan adadin ledar ruwan data shaba ma”.
Cikin tausayawa Jiddah tace, ”ALLAH Sarki, ALLAH ya k'ara Mata lafiya, wlhy Na tausaya mata, dan d'azun daga cin abincin sai amai”.
Shima duk fuskarsa ta Nuna alamun damuwa yana tausayama Maimunatu matuk'a.
★★★★
Bayan sunsha fruits d'inda saida yasha fama da ita sannan yasa ta had'a masa Shayin, koda yace taci naman daya kawo catai ta k'oshi, bai takurataba ya kammala shan tea d'insa yamik'e yana fad'in tayi alwala kafin ya dawo”.
Bai jira amsartaba ya fice, kwashe kayan tayi cike da tsarguwa tafito, tabud'e abinda tasan zai iya lalacewa dan batada firij.
Umarninsa tabi, bayan tayi shirin barci ta d'auro alwala, duk yanda su Yaruwaiya suka koyar da ita wajen saka k'amshi da tsaftace bakinta saida tayi, kafin tasaka hijjab ta zauna zaman jiransa.
Bai wani jimaba can sosai ya dawo cikin jallabiya ruwan k'asa.
Kallonta yay damata alamar ta tashi, itadai duk jikinta yayi sanyi, addu'a kawai takeyi a k'asan ranta ALLAH yasa ba zargin datake baneba.
Sheikh Aliy ya jasu salla raka biyu kafin suyi zaman addu'ar, yaja addu'a mai tsayo tafatan zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al'umar musulmi kafin su shafa ya juyo gareta.
Cikin tsareta da idanu ya jeho Mata tambaya..............✍🏻
*_Zan d'anyi jan hankalo anan please, wasu suna ganin maganar da Maimunatu tafad'a akan mutumin da ya turo sak'o tamkar da Aliyu take, a'a badashi takeba, sak'one aka turo masa kamar yanda ta fad'a, mun ta6o wannan ga6arne kuma saboda girmanta da yawautarta acikin al'umma, sannan masu gani shi Aliyu kamar baya iya Mata komai ba haka baneba, itadai tace yakan had'ama kwanaki hud'u bai nemetaba, sannan baya dogon zango tare da ita, (abinda nakeso mu fahinma anan shine yanada k'yau muringa kwatanta rayuwarmu ta zahiri a cikin novels, babu wani namiji da azahiri zaikai tsawon awoyi hud'u ko sama da haka tare dake, inkuwa hakane to lallai munshiga uku🙆🏻😌, idan kuwa har za'a samu irin wannan to basuda yawa gaskiya, nata6ajin wani likita Na fad'in yawan jima'i kullum-kullum yana ragema ma'aurata sha'awa da jindad'i harma suji abun yana fita Kansu basa wani shauk'in yinsa, sai dai suyi domin sabo kawai, sannan yana ragema mace d'and'ano awajen miji, abinda kuma zamu kalla bakowane namiji baneba a zahirima zai kasance dake a kullum, dan wani yaje aiki ya gaji, wani kuma damuwa tamasa yawa da sauransu, kuma ke kankima wlhy saikinji lamarin da takura dukda dai halittarmu kala-kala ce, akwai masu yawan buk'ata a mazan da matan, a dalilin karatun novels Mata da yawa sunama mazajensu kallon ragwaye, a buk akan saka namiji yayi awa uku tare da matarsa, maybe ma bai ishesaba, sannan da safe zai k'ara, idan yadawo aikima haka, tayaya ke a zahiri da ba'aima haka bazakiga gazawar naki mijinba?, wannan yasa lokuta da dama ake kalubalantarmu mu marubuta, dan mungaza fahimtar tasirin da alkalumanmu kedashi ga al'umma, badan nishad'i kawai ake rubutu ba, yakamata y'an uwana marubuta muringa saka hakan a ranmu, dan yanda zaki rubuta Abu Mara k'yau ALLAH ya tambayeki haka idan kika rubuta k'yak'yk'yawa zai baki lada, balle idan wani ya amfanu dashi Yasamu amfani kuma, idan awannan littafi kin saka yawan bukatar ma'aurata to Ya kamata acan kisaka k'asa-k'asa, awanima kisaka rauni sosai domin wasu su sami mafita daga matsalarsu Na gidajen aure, hakanne yasakani a farkon buk d'inann Na nuna Aliyu yanama da Matsala gaba d'aya, wadda kuma a sanadinta harya rasa matarsa da yake matuk'ar so da k'auna. Ina fatan kun fahimceni, nayi wannan maganarne domin murunga tafiya akan abinda ya dace, dan idan mun kauce kuke Fara k'alubalantar mu, alhalin kuke tunzura marubuta da yawa rubuta abinda zai burgeku a buks nasu, kuma koda ya kasance Mara tsari ga al'umma)_*.
_ALLAH yasa mudace_.🙏🏻😊
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
0 comments:
Post a Comment