*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[47➖48]_*
..............Muryarta na rawa kanta a k'asa tashiga amsa masa,
“Sharuddan alwala guda goma ne 1.Musulunci, 2. Hankali, 3.Wayo, 4.Niyya, tare da kyautata hukuncinta tare da niyyar ba zai yanke ta ba har sai ya kammala alwalar, 5.Daukewar abunda ke hana alwala (Jinin al’ada da jinin biki), 6. Istinja’u ko istijmaru, 7.Ruwan ya kasance mai tsarki, Ruwan ya kasance na halasta, 9.Gusar da abunda zai hana shigar ruwan fata, 10.Shigar lokaci ga wanda ke da hadasi a kowani lokaci.
Abubuwanda ke wajabta alwala. Abunda ke wajabta shi ne samuwar hadasi.
Farillan arwala, Farillan alwala shida ne.1. Wanke fuska da baki da hanci wad'anda ke furkar. 2. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu. 3. Shafar kai tare da kunne 4. Wanke kafafuwa. ALLAH madaukaki yace:
“Ya ku wad'anda sukayi Imani! Idan kun tashi za ku yi sallah, to sai ku wanke fuskokinku da hannaye zuwa gwiwar hannu, kuma ku shafi kawunanku da kafafuwa zuwa idon sawu” (Ma’idah: aya ta 5).
5. Jerantawa, domin ALLAH maigirma da d'aukaka ya sanya jerantawar hakan sai ya sanya shafa tsakanin wankewa. 6. Jerantawa kamar yadda ANNABI (S.A.W) ya aikata.
SUNNONIN ALWALA. Daga cikin sunnonin alwala akwai; 1. Asuwaki
2. Wanke tafin hannu sau uku. 3. Kurkurar baki da shaka ruwa.
4. Tsefe gemu mai yawa da yatsun hannu da kafafuwa. 5. Damantarwa. (fara gabatar da dama). Wanki na biyu da na uku. (idan na farko ya game).
7. Debo ruwa domin wanke kunne. 8. Addu’ah bayan alwala. 9. Sallar nafila raka’a biyu bayan ta.
Daga cikin makaruhan alwala. 1. Yin alwala a wurin da ba shi da tsarki, domin tsoron abinda ke iya taba jikinsa na najasa. 2. Kari akan wanki uku, domin abinda aka ruwaito lalle ANNABI ya yi alwala sau uku-uku ne, sai ya ce duk wanda ya yi kari hakika ya munana, kuma ya yi zalunci. (Nasa’i ne ya ruwaito).
3. Barna da ruwa wajan alwala, ka tuna lokacin da ANNABI (S.A.W) ya yi alwala da mudin Nabiyy, shi ne kuma kanfatar hannu. Barna abace da aka hana a komai. Barin sunnah daya ko fiye da haka, daga cikin sunnonin alwala, lalle kuma barinta rashin lada ne, kuma bai kamata baya bari lada ya wuce shi.
Abubuwanda ke warware alwala. Abubuwa masu warware alwala bakwai ne;
1. Abubuwan dake fitowa daga mafita biyu (ta gaba ko ta dubura).
2. Abinda ke fitowa daga sauran jiki.
3. Gushewar hankali ta hauka ko farfadiya ko maye. 4. Shafar azzakarin mutum ko shafar gaban mace ba tare da shamaki ba. 5.Namiji ya shafi mace domin jin sha’awah ko mace ta yi hakan. 6. Cin naman rakumi.
7. Duk abunda ke wajabta wanka yana wajabta alwala, kamar shiga musulunci da
fitowar maniyyi da makamancin haka, saidai mutuwa lalle shi yana wajabta wanka ne banda alwala.
WANKA: Ma’anar wanka; A yare da kuma wurin mallaman fikhu, Alghuslu ) ( da wasalin dumma ruwan da ake wanka da shi ne, amma da wasalin fataha ) ( aiki ne (wato yin wankan) da wasalin kasra ) ( kuma shi ne darasin mu, watau tsarkakewa. Ma’anar shi a shari’ah: shi ne zuba ruwa a dukkan jiki, daga tsakiyar kai har zuwa kasan diddige da ruwa mai tsarki akan sifa kebantacciya. Mace da namiji wajan siffar wankan su dayane, saidai ga mace a lokacin da take wankan daukewar jinin al’ada ko na biki, to yana kamata a gare ta da ta wanke alamar jinin domin tsarkaketa da kuma kauda warin jinin.
Abubuwan dake wajabta wanka. Abubuwan dake wajabta wanka guda shida ne:-
1. Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji.
2. 6oyewar kan azzkari a cikin farji. 3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, sai dai in shahidi ne. 4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda.
5. Jinin al’ada.
6. Jinin biki (wato jinin haihuwa).
Daga cikin wankan da suke anso ayisu a musulunci.
1. Wankan jumu’ah.
2. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah). 3. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka.
4. Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah) 5. Idan mutum ya farfad'o daga hauka ko farfad'iya 6. Wankan shiga Makkah.7. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rok'on ruwa. 8. Wanka na mai istiha a kowacce sallah.9. Ga kowanne jima’i an so a yi wanka.
SALLAH:- Hukunce-hukunce da suka rataya da sallah. Sallar jam’i, Sallar Kasru, (Sallar matafiya), Hada salloli biyu, Sujjadar rafkannuwa (Kabaliyya da Ba’adiyya), Sallar nafila, Sallar juma’a, Sallar Idi biyu, Sallar rok'an ruwa, Sallar kisfewar rana ko wata, Jana’iza da hukunce hukuncenta.
RUKUNI NA BIYU DAGA CIKIN RUKUNAN
MUSULUNCI: SHI NE SALLAH.
Ma’anarta a yaren Larabci da kuma Shari’ah, Sallah a yare:- ita ce addu’ah, Allah ta’ala ya
ce:
“Kuma ka yi musu addu’ah, lalle addu’ar ka natsuwa ce a gare su” {Taubah: aya ta 103}.
Sallah a Shari’ah:- ita ce ‘zancene da ayukka ke6antattu, wacce ake bud'e ta da kabbara, kuma a rufeta da sallama tare da sharud'd'an ta ke6a66u, Tarihin Wajabta sallah. An farlanta sallah ne daren Isra’i kafin hijra, kuma da ya ce daga cikin rukunnan addinin musulunci, bayan imani da ALLAH da MANZONSA ita ce farko, domin ta kunshe su,
wacce MANZON ALLAH ya shardanta ta bayan Tauhidi, mai tsira da aminci ya ce:
“Kan dukkan al’amari shi ne musulunci, gimshikinsa kuma ita ce sallah, kuma kololon gimshi kuma shi ne jihadi domin daga Kalmar ALLAH.
{Tirmizi ya ruwaito}.
Hikimar Shar’anta ta. Sallah godiya ce ga ni’imomi masu girma, wace ALLAH ya ni’imata ga bayinsa, kamar
yadda take daga cikin ababan dake bayyana kad'aituwar ALLAH, ta yadda take bayyanar da fuskanta ga ALLAH mad'aukakin sarki da kusanci, k'ank'anta da kai a gaban shi, da kuma ganawa da shi mad'aukakin sarki, ta hanyar karatu, da zikiri, da addu’ah. Kamar yadda ta kasance hanyar da take hada bawa da Ubangijinsa, kamar yadda take daukaka shi akan wasu abubuwa na k'yalek'yali zuwa inda zai samu natsuwa a ransa da kwanciyar hankali, saboda haka duk wanda ya nitse wajen tunanin rayuwa mai d'aurewa to sallarsa ta kasance tabbatacciya ta hak'ik'a daga barin gafala daga ita. Hak'ik'a abindake nuni da akwai abun dake da girma fiye da wannan, ita rayuwa kuma bai kamata a tafiyar da ita akan wannan tsari ba, kuma tana juya mutum don yayi ruyuwa akan ta, amma yana shiga cikin wata rayuwa zuwa wata rayuwar.
Hukuncin sallah da adadinta. Sallah nau’i biyu ce; ta farilla da ta nafila. Amma farilla ta rabu kashi biyu: farali wanda ke kan kowa da farali wanda wasu na dauke wa wasu. Farali wanda ke kan kowa; shine wajibi akan kowanne musulmi mukallafi na miji ko mace. Sune kuma salloli biyar, ALLAH ta’ala ya ce:
“Lalle sallah ta kasance wajibi abun yiwa lokaci ga muminnai” (Nisa’i: aya ta 103).
Kuma
ya kara cewa; “Kuma ba a numurce su da komai sai don su bauta wa ALLAH, suna masu tsarkake addini gareshi, kuma suna masu karkata zuwa ga addinin gaskiya su tsaida sallah kuma su bada zakkah, wannan shine addini tsayayye” {Bayyana: aya ta 5 }.
MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: “An gina musulunci akan abubuwa biyar ne: Shaidawa babu abin bauta wa da cancanta sai ALLAH, kuma ANNABI MUHAMMADU bawansa ne kuma MANZONSA ne, da tsaida sallah da bada zakka”. {Bukhari da Muslim, suka ruwaito}.
Nafi’u dan Azrak ya ce Dan Abbas shin ana
samu sallah biyar a Akur’ani kuwa sai ya ce: “Eh”, sa’annan sai ya karanta fadin ALLAH madaukakin sarki:
“Tsarki ya tabbata ga ALLAH da maraice da kuma safiya, godiya ta tabbata a gareshi a cikin sammai da kassai lokacin dare da rana” {Rum: aya ta 15-16}.
Haka hadisin wani balaraben kauye, wanda ya zo wurin MANZON ALLAH ya ce masa: Menene ALLAH ya wajabta mini na sallah?. Sai yace: Salloli biyar”. Sai ya ce; Ko akai wasu a kaina bayansu?, sai Ma’aikin ALLAH ya ce: A’a, saidai idan nafila ka yi”. {Bukhari da Muslim}.
Yaushe ake umurtar yara da sallah?.
Ana umurtasu da sallah idan suka kai shekara bakwai, ana kuma bugun su game da kin yin sallah idan sun kai shekara goma, amma duka mara karfi, saboda Hadisi mai cewa:
“Ku umurci yaran ku da yin sallah idan sun kai shekara bakwai, kuma ku buge su akanta idan sun kai shekara goma, ku raba musu wurin kwanciya”. [Abu Dauwd da Tirmizi suka ruwaito}.
Hukuncin wanda ya musunta wajabcin sallah:- Duk wanda ya musunta wajibcin sallah to kafiri ne, idan ya kasance cikin wadanda ba sa jahiltar sallar kuma kuma ko da ya yi sallar, domin ya zama wanda ya karyata ALLAH da MANZONSA da kuma ijma’in al’umma. Haka kuma wanda ya barta kawaida don
wulakantar da ita ko kawai saboda kasala, ko da ya tabbatar da wajibcin ta, domin fadin ALLAH ta’ala:
“To ku yaki mushirikai a duk inda kuka samesu”. Har zuwa inda ALLAH ya ce: “To idan suka tuba, kuma suka tsaida sallah suka bada zakka to ku sakar musu hanya”.
{Tauba: aya ta 5}.
Kuma an ruwaito daga Jabir ya ce: MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce:
“(Abinda ke) Tsakanin mutam da shirka da kuma kafirci (to shi ne) barin sallah” {Muslim ne ya ruwaito shi}.
Rukunan sallah:- Rukunan sallah goma sha biyar ne, ba’a barin su dagangan ko da mantuwa ko da jahilci.
1. Tsayuwa cur a sallar farilla ga mai iko. 2. Kabbarar harama, ita ce kuma: “Allahu Akbar”. babu wani lafazin sai wannan.
3. Karatun fatiha.
4. Ruku’u.
5. Dagowa daga ruku’u da daidaituwa a tsaye 6.Sujjada.
7. Dagowa daga sujjada.
8. Zama tsakanin sujjada biyu. 9. Natsuwa, ita ce kuma kamewa.10. Tahiyar karshe.11. Zama domin tahiyar karshe. 2. Salati ga ANNABI (S.A.W)
13.Sallama.
Ita ce kuma mutum ya fada sau biyu,
“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”. Ta farko kar ya kara da “Wabarakatuhu”. Domin hadisin Abdullahi dan Mas’ud, lalle Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi ya kasance yana sallama daga damansa, “Asalamu alaikum Wa Ramatullah”. Daga hagu kuma: Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”. {Muslim ne ya ruwaito shi}.14. Jerantawa tsakanin rukunnai.
Cikin gamsuwa da dogon bayanin Jiddah Aliyu ya dakatar da ita ta hanyar rik'e hannunta a nasa yana fad'in Masha ALLAH, ALLAHU Akbar, ALLAH yayi miki albarka, ya k'ara ilimi mai amfani”.
”Amin” Jiddah ta amsa a saman la66anta.
Hannunta ya saki ya mik'e tareda mik'ar da ita, batareda yayi magana ba yafita, hakanne yasaka Jiddah saurin hayewa gadon ta kwanta batareda ta cire hijjabinba, mintuna kusan goma saigashi ya dawo hannunsa rik'e da Kofi. Idonsa akanta ya zauna bakin gadon, “Nasan dai bakiyi barciba, Taso ki gani”.
Tamkar Jiddah zata fasa ihu haka ta mik'e zaune, sai dai takasa kallonsa, matsawa yay sosai yahau gadon, yanda ta zauna k'afarta a tankwashe shima sai yayi haka yana mik'a Mata kofin.
“ALLAH banajin yunwa fa”.
Cikin kuma sanyaya muryarsa yace, “Wannan badan yunwa ake shansaba, ana shane domin koyi da sunnar MANZON ALLAH (S.A.W), tun a daren jiya yadace nashigo dashi, amma kasancewar ban samu kainaba shiyyasa ban kawoba, ina fatan za'amin afuwa”.
Dole Jiddah ta amsa ta kafa Kai tasha kad'an ta mik'a masa, kansa ya girgiza Mata damata nunin ta k'ara. Babu yanda ta iya tak'ara sha sannan ta bashi. Yanzunkam amsa yayi shikuma ya shanye sauran sannan ya ajiye kofin.
“Mu kwanta mu huta dare yayi fa” Cikin mintuna kad'an duhu ya mamaye d'akin saboda kashe fitilar da yayi, itadai Jiddah ta kwanta, jira take taji yace mata sai da safe, amma taji tsit.......
Kwanciyarsa kusa da itace yasaka tunaninta katsewa, tad'an muskuta zata matsa ya ruk'ota jikinsa, wani irin tsuma taji jikinta Na Mata ga tsoron dake k'ara girma a ranta.........
A cikin kunnenta yake fad'in “waya fad'a miki Matar aure na kwanciya da hijjab?”.
Muryar Jiddah na rawa tace, “Sanyi nakeji ai”.
“Karki damu ga bargonki yazo”.
Abubuwan da suka cigaba da biyo baya sun kasance babban al'amari ga Jiddah, tun tana 6oye kukanta harya fahimci tanayi, sai dai ko kad'an babu gaddama ko jayayya daga gareta. Lokacin da ya sheikh yanufi k'ofar da yake tunanin samu abud'e saiya isketa 6am da kwad'o, dukda yadad'e yana zargin hakan baigaza shiga al'ajabiba, hakanne ya sakashi dakatawa daga yunk'urinsa, har Jiddah tafara murnar yabartane saitaji ya sake sabon salo, dan fahimtar sabuwace ya sakashi Binta a salon da bazata cutuba, zuwa wani lokaci kuma UBANGIJI yay ikonsa wajen bama ya sheikh dama wajen mallakarta a matsayin matarsa halalinsa.....
★★★★★
Shine ya Fara farkawa sabodajin kiran sallah, ya lalubo wayarsa a durowar gefen gadon, mamaki ya kamashi ganin sun makara, dan sallar shigama ake Kira, “Ya Salaam” yafad'a yana dafe kansa, yasan dolene su makara, dan basu kwanta da wuriba, fitilar wayar ya haska yana janye Jiddah a a jikinsa ya tashi zaune, itama d'in ta farka tunda ya motsa, amma saita kasa yunk'urin tashi tayi luf. Fuskarta yad'an haska tai saurin jan bargo ta rufe. Murmushi yayi yana fad'in “Rowa za'amin amarya?”.
Itadai k'in bud'ewa tayi, saida taji yashiga bayi sannan. Bata saukaba harya fito yakuma dawowa gaban gadon, laimar hannunsa yad'an shafa mata, “Idan zaki iya tashi kiyi alwala, naje masallaci kinga Na makara”.
Kanta kawai ta iya d'aga masa.
Fita yay, a gaggauce ya lek'a Maimuna ya iske itama ta tashi, baiyi maganaba ya juya ya fita da hanzari.
Tashi Jiddah ta daure tayi dukda yanda takejin jikinta, danma ya taimaka Mata sosai tunda daddare ya gasata da ruwa mai d'umi sosai tareda bata dukkan taimakon dazataji sassauci. Kallo d'aya zakai Mata ka fahimci tafiyarta ba dai-dai takeba, hakadai ta daure ta d'ingisa tasake d'anyin tsarki da ruwan zafin daya rage a cikin filas d'in, sosai takumajin dad'i, alwala ta d'auro ta fito.
Yaukam tana idar da sallah takoma saman gado ta kwanta, azkar ma azuciyarta tayi Wanda ta rik'e harma barci yakuma kwasheta.
Koda Aliyu ya dawo sashen Maimunatu yakona, dukda zazza6in ya sauka hakan bai hanashi tarairayarta ba da nuna Mata kulawa, yace ta shirya suje asibiti, amma saitace a'a yabarshi tunda zazza6in ya sauka, dole ya barta amma ya hanata shiga kicin yace ta kwanta ta huta.
Murmushi kawai taimasa, yana fita tatashi tashiga kicin, dan aganinta bai dace su zauna da yunwaba ai, itakuma Alhmdllh tanajin jikin nata da sauk'i.
Zama yay a bakin gadon kawai ya tsurama Jiddah idanu, bacci take, yakai hannu ya shafa fuskarta zuwa saman idanunta da suka kuma kumburowa saboda kukan datasha.
Hakanne ya saka Jiddah farkawa ta bud'e idanunta tamasa kallo d'aya ta maida idonta ta lumshe, fuskarsa d'auke da murmushi ya furta, “Dama ba barci kikeba”.
Tamkar zata nutse dan kunya, dukda Idonta a rufe suke ba kallonsa takeba, da k'yar tace, “Barci nakeyi” tayi maganar Idonta na cika da kwalla, dan duk a takure take da zamansa wajen.
Bai ankaraba yaga hawaye Na gangarowa a fuskarta.
Yace, “Ya salaam khairunnisaa! Kukannan dai bazai k'areba, ayi hak'uri Aliy yayi laifi yau mai girma ko?”. ‘Yay maganar yana kwantowa jikinta da d'ora goshinsa akan nata, cikin kuma k'asa da murya sosai yake fad'in,
*1 ربنا يحفظك نوري.2الله ينور عليك قلبي .3ربنا يحميك وسائر النساء دنيا كل*
_“ALLAH yakareki hasketa 2.allah ya haskaka zuciyarki .3allah yakiyayeki da Sauran matan duniya gaba daya”_.
“Wannan shine mafi alkairin kowacce mace, shine mutuncinta da kimarta a wajen miji, duk wadda taje gidan aure babushi tagama asarar daraja da kimarta, sai dai wadda ta kasance a k'addarar zalincin fyad'e, ALLAH yabaku ikon bama y'ay'ana tarbiyyar da suma zasu kasance kamilallu kamar yanda kuka kasance Mata kamilallllu salihai”.
Haka yayta fad'i Mata dad'ad'an kalamai da suka sanyaya ranta har barci yakuma kwasheta, ya d'an sauke ajiyar zuciya yana sumbatar la66anta da saman idonta zuwa goshi, shikam babu abinda zai cema Ubangiji sai godiya, shine buwaya gagara misali daya azurtashi da wad'annan mataye nagartatttu, samun Maimunatu matsayin cikakkiyar budurwane yasaka ginuwar k'aunarta a ransa, wadda har gobe take k'ara yad'o, a daren jiya kuma yakuma gamo da abin mamakin dabaiyi zatoba, shida ya auri bazawara saiyaci Karo da budurwa fil a Kwali, juyawa yay yasake kallon Jiddah dake barci yay murmushi.............✍🏻
*_kwace anya kuwa wannan matar zata cika mana alk'awari😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[49➖50]_*
..........Kasancewar yau mafi yawan bak'in suka wuce sai Umma tasamu damar zaman k'irga y'an kud'ad'en data samu a wajen dangi na gudunmawa ita dasu Aunty Hannatu, bayan sun kammala sukayi d'an lissafin abinda Jiddah bata dashi za'a Kai Mata, walida dake rubutawa ta kalli su Aunty Nafisa cikin kwantar da murya tace, “Auntys dan ALLAH baza'a sayama Yaya Jiddah freight ba wai?”.
Duka Umma takai mata tana fad'in, “Walida ki kiyayeni wlhy, Ubanki yabani kud'in? Yanzu kina gani dai a gabanki aka lissafa kud'in duka nawane ya rage a ciki”.
“Kiyi hak'uri Umma badan ranki ya 6aci na fad'aba, ni dama dan nagafa kishiyarta nadashine, sainaga itama da da hali sai a saya mata ko k'aramine”.
“Humm Walida kenan, bakisan mutuwar mageba sai kinga tana shure-shure, dan kawai abokiyar zamanta nadashi sai akace itama dole sai an saya mata? Tomu bagasa zamuyi da waniba, abinda ALLAH ya hore mana dashi zamuyi amfani”.
Dariya duk sukayi, Aunty Saudah tace, “ALLAH Umma maganar Walida abar dubawace, badan gasa za'a saya mataba, kinga kodai Sana'a tayi da kayanta ai, amu talakawa ajiye firij ai badan gayu muke ajiyewa ba, ina ganin mizai hana acire a sadakin Jiddah sai a saya ko Wanda bai wuce dubu arba'in baneba zuwa hamsin haka”.
A take kowa ya aminta da maganarta, Yaruwaiya tace, “Kumafa gaskiyane wlhy, inaga hakanma shi kawai za'ayi, amma afara sanarma kawunku yahya sanan, saimuji shi mizaice, mace babu sana'a ai akwai matsala, randa miji yatashi baidashi sai kowa yay zuru-zuru, irin wannan ke kawo yawan husuma kuma wlhy, shi yana wuya saboda talauci kaima kana mak'ogwaro, abu kad'an zai hasala kowa ya fusata saikiga anyi sama”.
Umma ce ta d'auki waya ta Kira Uncle yahya, cayay mata gashinan a hanyar gidan ma. Tana ajiye wayar babu jimawa saigashi yazo. Bayan an gaggaisa Yaruwaiya tamasa bayani, 100% ya yarda da shawarar, danshima aljihun nasane yayi k'asa, amma harga ALLAH yayi niyyar siyama Jiddah duk abinda yadace mace ta bud'e ido tagani a d'akinta, musamman abinda za's iya Mora har a sana'a.
Bayan sun gama tattaunawane yasamo musu motar dazata kwashi sauran kayan Jiddah da akwatinanta da kayan gara dadai sauran tarkace.
Umma kawai aka bari a gidan sai wasu tsoffi uku danginsu Jiddah 6angaren su Abba, su Balu, aunty Zulai, aunty hannatu, Walida, suka wuce gidan Jiddah. Maman Sadiq, Yaruwaiya, aunty Saudah, Aunty Nafisa, sai Zarah suka wuce kasuwa k'arasa sayo abinda ya rage Na Jiddah.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ikon ALLAH ne kawai yakawo Abba kano, ammafa wujiga-wujiga ya Iso saboda 6acin ran da yake a ciki.
Su Hajia Hindu na zaune a Dani itada yara suna dinner ya shigo ko sallama babu, Maneer yatashi da gudu yaje yana masa oyoyo. Rik'e hanunsa yayi kawai amma yakasa magana, saima wata uwar harara daya zubama su hajia Hindu itada yaran, “yanacan yana wahala su sunanan hankalinsu kwance”, dan duk sunwani zubo masa idanune amma babu Wanda yace masa koda sannu.
Tsaki yaja yana sakin hannun Muneer yashige abinsa. Hajia Hindu ta ta6e baki tana d'auke kanta. Shima Hussain bakin yad'an ta6e kafin yace, “Wai Mom mi akaima Dady ne daga dawowarsa?”.
“Ina Zan sani Hussain, ai tare muke daku anan ya shigo”.
Dariya Kalifa yayi yana fad'in, “ku nifa kwana biyunan gani nake kamar Dady a rikice yake, kokuma rud'un tsufane oho”.
Dariya suka sanya gaba d'aya, Hajia Hindu ta mik'e tana, “Kai yaranan ALLAH ya shiryeku, kodai tsohonne ma ai ubankune dai, bara naje naji mike faruwa”.
Kwance ta iske Abba hannunsa dafe da kansa, zama tayi gefen gadon kusa dashi, “Abban kalifa lafiya kuwa?”.
Banza yay mata tamkar baimajiba, saida ta maimaita sau uku kafin ya janye hannunsa ya kalleta da idanunsa dake jajur, sai dai yagaza cemata uffan.
Hakanne yad'an tada hankalinta, takuma maimaita masa tambayar.
Mik'ewa yay zaune yanajan guntun tsaki, “Yanzu nan Hindu na d'auki tsawon kwana shiddah bana gidannan, amma nadawo kuna kallona tamkar wani kashi, wane iron rainine wannan?”.
cikin kwantar da murya ta kallesa, dan zatonta koya samo kud'inne, shiyyasa ta aro sabon ladabi, “Ohni Hindu, yanzunan Abban kalifa wace irin maganace wannan dan ALLAH? To kayi hak'uri, wlhy mamakin yanda kashigone yasanyamu yin hakan, yaya Abuja? Ina fatan dai andace da samun kud'ad'en?”.
Jin yanda ta kwantar da murya sai Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta “Bansan yanda zanyiba Hindu, ina cikin tsaka mai wuya, kud'in danaje nema ban samoba, dolene a darenan naje na turke Y'ar iskar yarinyarcan yaronan ya saketa, nasan inhar Alhaji garba yaga zata dawo gareshi zai hak'ura ya barni”.
“Hummm Alhaji kenan, to ai daga baya kenan wannan, komafa miye ya faru laifinkane, Kaine ka 6ata komai a randa Alhaji garba ya kiraka, sannan nabaka shawarar musanya masa da Zarah, amma sai kak'i saurarena, to ai yanzu bakada hurumin rabama Jiddah aure kuwa balle bashi ita, dan ta tare tunma shekaran jiy.....”
A zabure ya mik'e, “k ban fahimcekiba? Ni da raina za'akai y'ata gidan miji ban saniba?”.
Baki hajia Hindu ta ta6e tana masa wani kallon rainin wayo, balle taji babu kud'in, “Oh kajimin Abban kalifa fa, yo yaune karan farko da aka Fara Kai y'ay'an naka gidan aure bada saninka ba? Naga ko hannatu sai dama tayi wajen wata biyu da aure ka sani, Zulai kuwama saida takusan haihuwa”.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya bangajeta ya wuce zuwa bayi. Bayansa ta raka da harara tana k'ya6e baki, saima ta fice abinta kawai tabar masa d'akin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kamar da wasa k'aramar magana saita zama babba, dan tsawon kwana uku Alhaji garba ya gagari hajia deluwa sakawa a ido, tunda ya shige sashen amarya a randa aka kawota bai sake ko lek'o wajeba, sallama agida yakeyi, abinci kuwa bashida Matsala, dan amarya ke musu daddad'en girki, cikin k'awayenta takira tabada umarnin ayo musu cefane mai yawa, wannan yasa suka kuma yima hajia deluwa nisa, sai dai tajiyo sautin kid'a Na tashi, knocking kuwa tayi har hannunta ya gajiya, tayi wujiga-wijiga da ita, nutsuwa ta gagareta, takira malam Na marwa yafi sau dubu amma wayar yak'i shiga, komai saiya kuma harmutse Mata. Su Kansu su Ashir sunma kasa gane kanta kwata-kwata, gefe kuma su hajia Hindu k'awayenta na kuma tunzurata a waya.
Aiki ya samu mata🤣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai wajen sha d'aya Jiddah ta farka, ta tashi kuma bata samu Sheikh Aliy a d'akinba, hakanne ya sata d'anjin dad'i, yunk'urawa tayi zaune da k'yar, dan jikinta duk ciwo yake Mata, ji kawai tayi hawaye suna zirara Mata, yanzu nan wannan abunne har kesa mace yin zina?, miye abin dad'i anan banda bak'ar wahala? Wai a hakanma shi bawani gama shigarta yay gaba d'aya ba kamar yanda yafad'a, tayi kusan zaman minti talatin tana hawayenta, Wanda dalilinsu yafi k'arfi a kewarsu Ummanta, sakkowa tayi a gadon zuwa bayi, tasamu takumayin tsarki da ruwan zafi tayi wanka, lokacin walha ya wuce, hakan Yakuma sakata takaici.
Saida ta shirya sannan ta gyara d'akin tasaka turaren wuta, takardar data gani saman mirror ta d'auka ta karanta.
_Ina fatan tashinki cikin aminci da farinciki Aglan Nisaa (Mafi tsadar mace) amin afuwa na fita saboda wani uziri, ga abinci nan a falo auntynki ta kawo miki, Ku yini cikin aminci da kariyar ubangiji matana._
Guntun murmushi tayi tana had'iye hawayen da suka cika idonta, ta linke takardar ta ajiye sannan tafito. A falo ta iske abincin karin kumallonta daya ce, bata cutama kantaba ta zauna taci dai-dai iyawa tasha maganin daya ajiye Mata. Tanason zuwa ta duba Maimuna amma tanajin kunyar tafiyarta, haka ta zauna shiru harma takai da kwanciya cikin kujera ta fad'a duniyar tunani.
A wannan yanayin su Walida suka iso suka sameta, wani farin ciki Na musamman ya kamata, ta tashi cikin hanzari domin tararsu, sai dai taku biyu tayi tatsaya cak saboda kallon dataga sun tsaya sunama k'afafunta.
Aunty Hannatu dayake tanada hankali saita basar dasu ta hanyar zuwa ta rungume Jiddah.
Jiddah tad'an sauke ajiyar zuciya dan a ganinta k'ila basu fahimci abinda take zarginba.
Kayan hannunsu suka ajiye suma sauran sukazo suka rungumeta, kafin su saketa su kuma fita kwaso sauran kayan.
Maimuna dataji hayaniya ta fito, dan dama tun d'azun take d'an zagayo Jiddah taga kota tashi, Aliyu yace Mata kanta ke ciwo, dukda zuciyarta ta sosu da tunanin wani Abu daban hakan bai hanata lek'owa taga kota tashiba.
Da fara'arta takemusu sannu dazuwa. Suma suna amsawa fuskarsu d'auke da Fara'a, koda tace zata tayasu d'aukar kayan sai Balu ta hanata, dukda haka saida ta amshi agogon dake wajen Aunty Zulai suka k'arasa falon Jiddah.
Jiddah Na ganinta tai k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta, dan ita gani take kamar Maimunatun tasan abinda sukayi a daren jiya.
“Ashe kin tashi K'anwata, tun d'azun nake zagayenki amma saina iske kina barci”.
Batare da Jiddah ta kalletaba tace, “eh wlhy aunty, maganin murar Dana Shane yasani barci”.
“Dama yace kanki ke ciwo, yanzu dai ya daina ko?”.
“Eh ya daina Alhmdllh”.
“To ALLAH ya k'ara afuwa, sannu”.
“Yauwa aunty, kema yanaki jikin?”.
“Alhmdllh”.
Su Balu ma duk sukaima Maimuna ya jiki bayan ta zauna sun kuma gaisawa cikin mutunta juna, mik'ewa tayi ta fita itada Walida data kira.
Suna fita aunty Hannatu tace, “Wlhy Jiddah kin more da abokiyar zama ba irin namuba da kullum fitina bata k'arewa, dan ALLAH kema ki kwantar da hankalinki Ku zauna lafiya, nasan kishi abune mai zafi, amma inka had'a da hak'uri sai ALLAH ya sauk'ak'a maka, ita kanta nasan tanajin zafi, amma take dannewa saboda tasan mutuncin kanta”.
Kan Jiddah a k'asa tace, “Insha ALLAHU aunty zan kiyaye, kumani wlhy bana wanijin haushinta, dan tanada kirki”.
Dariya sukayi, Aunty Zulai tace, “Zakijine Jiddah, har yanzu akwai saurankine, bakigama tantance abinda akema kishinbane ba, babu macen da zatace bata kishin mijinta ai”.
Balu zatayi magana su Maimuna sukayi sallama, hakanne ya sakasu barin maganar, ruwane ta kawo musu sai zo6o data dafa d'azun da safe da Aliyu yace yanaso, saita had'a musu shi yanzu takawo musu, akan shid'in saita data masa wani kafin ya dawo.
Sallamar su Yaruwaiya ce ta karad'e gidan, Maimuna talek'a tana amsawa, suma cikin fara'a take musu sannu da zuwa, suma suna amsawa cikin mutuntawa da sakin fuska.
Sun shigo da tarkacen da aka k'arasa sayama Jiddah dakuma freight d'inta madaidaici ruwan toka.
Sannu sukayiyyi musu sannan sukai gaisuwa da Maimuna tafita domin nema musu d'an abinci mai sauk'i.
Zarah da bakinta baya iya shiru ta kalli Jiddah tana fad'in “yaya Jiddah mi akayi miki? Dan dagani kuka kikayi amma? Idonki duksun kumbura fa”.
Rasa amsar da Jiddah zata bata tayi, kafin kuma wani ya bata amsa cikin manyan takuma d'auki kwalin maganin da Jiddah tasha na rage rad'ad'i da ciwon jiki tana dubawa, tad'ago zata kuma jeho wata tambayar Aunty Saudah ta dakatar da ita, “K akku ya isa haka da ALLAH, batajin dad'ine ko dole saikinji mike damun Nata?”.
“Yi hak'uri aunty Saudah, nifa kawai dana ganta wani irine, sainake ganin ko wani abu wani yamata, kinsan mai kishiya, gakuma hardasu maganin ciwon jiki, yaya Jiddahr ce tacika sanyi, naga kuma kishiyar nan tata akwai shegen way...”
Kulli Yaruwaiya tayimata a baya, “Zarah ki iya bakinki, banason maganar banza fa, irinkune dangin dake had'a fitina a gidajan y'an uwanku idan sunada abokiyar zama, wlhy koda wasa karna sakejin wannan banzar maganar akan abokiyar zamanta”.
Kai Zarah ta d'aga tana tura baki da shafa inda Yaruwaiya ta doketa, su aunty Saudah ma duk fad'a sukai Mata akan hakan da nuna Mata rashin k'yautawa.
Walida tace, “Wlhy matarnan tanama da kirki, wace macece za'aima kishiya a wannan zamanin ta iya dannewa ta kwar6i kishiyar da danginta kamar haka?”.
“Wlhy gaskiyarki Walida, aike kinfi Zarah hankali”.
“To maganar ta isa hakanan, a canja da wata kuma”.
Daga nan suka saki maganar suka koma wata daban, sunayi suna bud'e kayan, wasu na gyagygyarasu inda ya dace. Hakanne yasaka Jiddah d'an sakin jikinta, amma tak'i yarda ta tashi ko nan da can.
Kusan awa d'aya saiga Maimuna da kular abinci babba da zata iya d'aukar abincin dazai wadatar dasu, duk sukai Mata sannu da godiya.
Murmushi kawai tayi, dan hankalinta yakwanta dasu, yanda suke girmamata, dukda yawanci duk san girmeta, Zarah ce kawai takula kamar bata sakin jiki da ita sosai, amma hakan bai dametaba dan k'aramar yarinya take kallonta, kuma baizama dole dama kowa ace kamasaba.
Bayan fitarta sukayi haramar sallah, yayinda akabar wasu a kicin suna k'arasa gyarawa.
Aunty Saudah ta kalli Jiddah tana fad'in “Wane d'aki kuke kwana Jiddah?”..
Da hannu ta nuna mata kamar zata nutse dan kunya.
“A to bara muyi amfani da wannan mu kenan, wancan yazama Na k'aninmu ai”. ‘cewar Aunty Nafisa’.
Dariya sukayi irinta shak'iyanci suka shige. Jiddah k'in tashi tayi saida taga sun shige, su Zarah kuma hankalinsu na a kicin sannan ta lalla6a d'ayan d'akin domin yin salla.
Bayan an idar da sallah Aliyu ya shigo gidan, saida yafara shiga sashen Maimunatu sannan, itace take sanar masa zuwan y'an uwan jiddahr.
Hakanne yasashi zuwa dansu gaisa, amma saiya iske falon shiru, sai maganganunsu da yake jiyowa a kicin da d'ayan d'akin, kamar zai koma da baya saikuma ya nufi d'ayan d'akin da Jiddah take, a nufinsa saiya kirata a waya dan zatonsa tana kicin ko d'ayan d'akin da yakejin firarsu.
Jiddah dake canja kaya duk zatonta Zarah ce ko walida, batareda ta juyoba tace, “Zarah zoki jamin zip d'inan sama”.
Murmushi Aliyu dake tsaye yana kallonta yayi, yatako a hankali zuwa gareta................✍🏻
_Naga kuna Neman shiga rud'ani akan buk d'in da kuka gani jiya, wancan sunansa *WUTSIYAR RAK'UMI...* Na kud'ine da zamuyi Na k'ungiya, so dukmai buk'ata zai sayane, guda biyarne muka fitar, pages na jiya kuma d'and'anone😋, ciwon Kai ya hanani yimuku typing jiya🤦🏻♀_.
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[51➖52]_*
............Duk yanda yaso daurewa karta fahimci shine yakasa, maimakon ya zuge mata zip ɗin tamkar yanda ta buƙata saiya ɓige da tura hannayensa cikin rigar ya zagayo dasu saman cikinta.
Baƙaramar firgita Jiddah tayiba, tanemi juyowa a razane yay azamar ɗora kansa saman kafaɗarta yana faɗin, “Afuwa hajjaju nine ba Zarah ba”.
Kasa motsin kirki Jiddah tayi, sai jikintane ke mazarin tsumar tsoro, muryarta na rawa tace, “Sannu da dawowa”.
“Yauwa amarsun Aliy, yaya jikin dai?”.
Shiru tai ta kasa amsawa, gaba ɗaya tagama takura, gefen zuciyarta kam addu'a take ALLAH yasa kar cikinsu Walida wani ya shigo, ita abindama bata fayimtaba inasu Aunty Nafisa suke? Harya shigo nan....... Firgita tayi tana Saurin dafe hannunsa dake neman canja salon yawo a rigarta, cikin sarƙewar murya da matuƙar in ina tace,
“Su..su..s..u aunty Sau..dah sun.. zo fa”.
Dariyar dake nemen kufce masa ya danne da ƙyar, dama yayi mata hakane dan tayi magana. Fuskarsa ɗauke da shinfiɗaɗɗen murmushi ya cire hannunsa yana juyo da ita. Kasa kallonsa tayi, hannunsa yasaka ya ɗago haɓarta yana faɗin, “Tun randa na fara ganin wannan fuskar na fahimci matsoraciya ce ke kam”.
Murmushin da bata shirya yibane ya kufce mata, tasaka hannayenta ta rufe fuskarta. Yanzun kam saida ya dara, ya jawota jikinsa yasaka mata zip ɗin.
Komawa yay ya zauna a bakin gadon yana kallonta tana ta wani sinne kai, aransa kam dariyar yanda taketa kare ƙirjinta yakeyi da faɗin mata kenan, hakafa Maimunatu taita masa, amma kwanaki naja tana kuma sakin jikinta dashi, yasan itama Jiddahn zata koma dai-dai ne, duk macen kirki dolene asameta da wannan kunyar, danshi baiga birgewaba ga ƴammatan yanzun da idanunsu ke a soye, watama ɗan kukannan idan za'a kaita gidan miji batayi, ƙagarama take atafi, suna ɗaukar hakan wayewane basusan zubar da kimarsu suke ta ɗiya maceba, koshi mijin sai dai yaƙi faɗa maki amma saiyaji baki birgeshiba kwata-kwata, duk son wayayyar mace da wasu mazan keyi sunason koyaya taɗan ringa kunyarnan a gabansu, domin kunya ita kanta jan ajine ga ɗiya mata, kuma alamune na kin kwankwaɗi tarbiyyane a gidanku, danshi abinda yake kallon mace mara kunya *BALLAGAZACE* kawai mara isashshiyar tarbiyya. Numfashi yaɗan sauke yana kallon jiddah dake tattare kayan data cire, amma koda wasa taƙi duban sashen da yake. “Juddatulkhair muje na gaida su auntyn namu naje naɗan kwanta na huta kafin lokacin sallah ko”.
Kanta ta jinjina masa tana ajiye kayan hannunta, cikin sanyinta tace, “To”.
Harta kama hanyar fita yace, “Zonan na tambayekima”.
Dawowa tayi da baya, zata durƙusa ƙasa ya kamo hannunta yana faɗin, “Zauna anan”. Ya nuna mata bakin gado kusa dashi.
Bata musaba ta zauna, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
“Kinsan mizan tambayeki?”.
“A'a”.
Murmushi yayi mai sauti yana kuma maida hankalinsa gareta, “Wai kinsan sunanama kuwa?”.
A mugun bazata tambayar tasa tazo mata, dan haka ta ɗago kai tana kallonsa cikin waro idanu.
Babu shiri shima dariya ta kufce masa, miƙewa yay tsaye yana cewa, “Dama sonake naga idonki kuma nagani, tashi muje ki rakani”.
Jitai tamkar zata nutse dan kunya, wlhy rayuwar bawan ALLAHn nan tana matuƙar burgeta, tarigada ta taso Abbansu banda jaraba babu abinda ya iyayima Umma, idan sunga fira tsakanin mata da miji cikin aminci to sai dai idan gidan Uncle yahya sukaje, amma a gidansu dai a'a, itafa zatama iya lissafa dariyar Abba data gani a rayuwarta, wannan yasaka duk abinda Aliyu yay mata sai take ganinshi tamkar wani mijin novels ko film😝.
Fita tafarayi falon ta barsa a ɗakin, su aunty Hannatu na zaune sunacin abinci, yayinda su Balu ke ɗaki suna salla sukuma.
Yanda taketa wani nuƙu-nuƙu da sissinkuyar dakai ne yasakasu zuba mata idanu.
“Lafiya kuwa Jiddodo?” ‘Aunty Zulai tai maganar’.
Kuma ƙasa tayi da kanta kafin tace, “Aunty wai dama shine zaku gaisa”.
Harsun fara dariya saikuma kowacce ta rufe bakinta da hannu saboda harar da Aunty Saudah ta zuba musu dukda itama danne tata dariyar take, yanda Jiddah tayi maganarne dole tabaka dariya.
“Wlhy Jiddah yanda kikasan ƴar da haka kike, bakisan sunansa baneba?”.
Murmushi tayi kanta a ƙasa, “toni aunty bansan yanda zance muku ku ganeba”.
Cikin tsokana Aunty Nafisa tace, “Sai kice auntys Hubbiy zaizo ku gaisa”.
Ido jiddah ta zaro saikuma ta narke fuska, “kai Aunty Nafi wlhy nidai babu ruwana”.
Yanzukam kasa daurewa sukayi, saida sukaɗan dara kaɗan.
Yaruwaiya tace, “To ɗan nawa yana ina?”.
Da hannu jiddah ta nuna ɗakin data fito.
“K jiddah wai kina nufin yana ciki?”.
Kai ta ɗagama aunty hannatu mai maganar.
Hannu sukasa suna dafe bakuna, Aunty Sauda tace, “Wai kina nufin dama tun ɗazun yana nan?”.
Cikin son tsokanarsu Jiddah tace, “eh mana”.
Babu wanda bai rikiceba dukansu, Maman Sadiq ta zubama Jiddah daƙƙuwa tana faɗin, “Jiddah kinci gidanku, shine dan iya shege kika barmu muketa zuba da sakin magana”.
Dariya jiddah keyi, saikuma tarufe bakinta da hannu tace, “Wasafa nakeyi, wlhy yanzu yashigo kuna ɗaki kuna sallah, su Zarah kuma suna kicin”.
Babu wanda bai sauke ajiyar zuciyaba a cikinsu, yayinda aunty Nafisa ke faɗin, “ALLAH kafin nabar gidanan saikinci gidanku jiddah”.
Nanma dariyar Jiddah tayi tanama aunty Nafisa gwalo.
Shiekh Aliyu dake ɗaki duk yana jiyosu, murmushi yay yana mamakin dama tana magana haka, da sai yaga kamar tafishi shiru-shiru, amma yaukam dayaji bakinta saiya kuma tabbatar da kunyace kawai da rashin sabo dasu.
Ɗakin ta shigo da sallama, ya ɗago idanu yana kallonta da amsa mata.
“Na faɗa musu zakaje ku gaisa”.
”Wakikace musu zaizo?”.
“Kai mana”.
“Niwa?”.
Shiru tayi dan an ƙureta kuma.
“Shiyyasa nace bakisan sunanaba ai madam, muje kirakani to”.
Kafinma yakai ƙarshen maganar harta kai ƙofa, dan batason yazo yacim mata.
Tunkan su fito dama sun kimtsa, Aliyu ya zauna saman kujerar farko idan kafito daga bedroom ɗinsu, fuskarsa shimfiɗe da murmushi yana musu sannu da zuwa.
Duk suka amsa masa cikeda girmamawa, yau gasu ga babban malamin da sukeji a redio da tv a gabansu, matsayin mijin ƴar uwarsu.
Sun gaisa cikin mutunta juna, sunata kuma mamakin sauƙin kai irinna Aliyu, har yana tsokanar yaron Aunty Hannatu wanda dashi kaɗai akazo dan ƙaramine sosai.
Suma su Zarah sun fito suka gaisa dashi, yace, “Walida kece ƴar zaman ɗaki ko?”.
Dariya tayi tana faɗin “A'a malam, ai Umma bazata yardaba”.
“Aini sainaje na roƙeta tabamu ke auta. Idan kuma auta batason nesa da Umma sai a bamu Zarah”.
Dariys sukayi, Zarah na faɗin, “Ai sai arasa gane matar gidan da ƴar zaman ɗakin”.
Miƙewa yay yana murmushin maganar Zarahn, yaɗan saci kallon jiddah dake gefe kanta a ƙasa ya fita abinsa.
Sosai suka shiga yaba masa dajin ƙarin ƙaunarsa a ransu, tareda kuma taya ƴar uwarsu murna.
Sai la'asar lis suka bar gidan, bayan sun kammala kimtsa komai, kayan gara kuwa sashen Maimunatu suka kaisu tareda kayan cin-cin daduk suka ɗiba mata, itama Jiddah aka ajiye mata nata.
Har gate suka rakosu Jiddah na hawaye, duk sai tausayinta yakama Maimunatu, dan da gaske duk amarya saitaji wannan damuwar a farkon aurenta, kaitajin tamkar ka koma gidanku.
Itace taita lallashinta bayan tafiyarsu, harma jiddahn taɗan saki jikinta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Abba baibi takan hajia hindu ba yagama shirinsa ya fice, yau koma yaran bai sauraraba, danshifa haushinma kowa yakeji, shikaɗai yasan tanajin kalar rashin mutuncin daya shirya zuwa ya saukema Uncle yahya da Umma.
Koda ya fito gidan Alhaji garba ya nufa. Da ƙyar Amarya tabarsa ya fito, shima danya mata bayanin cewar kuɗi ƙila Abba ya kawo masa, har tsakar gida tamasa rakkiya, saima tasamu wajen zama tana jiran su gama taja abinta su koma. Hajia deluwa batasan hidimar da akeba, tanacan zaune jigum a falonta abin duniya yagama addabarta.
Fitowa abba yayi daga cikin mota yabama Alhaji garba hannu suka gaisa, kokaɗan fuskar Alhaji garba babu fara'a, sai wani ciccijewa yakeyi, shidai Abba ya danne tashi zuciyar dan masalaha yake nema yau.
“Alhaji idan ban takurakaba dan ALLAH magana nakeson muyi dakai”.
“Magana kuma Alhaji Zakari, to aini babu sauran wata magana a tsakaninmu yanzu saita kuɗina”.
“dukda haka dai ka daure ka saurareni, nasan zakayi farin ciki da hakan”.
Umarni Alhaji Garba yabama direba yakawo musu kujeru, hakan da hajia amarya taganine yasata komawa sashenta takawo musu lemo, Abba dai sai kallonta yake da mamaki, dan yasha ganinta tazo shagon Alhaji garba, har mutane kansha dangantata da karuwarsa ce, to yanzu kuma mitakeyi a gidansa?. Bashida mai bashi amsa dan haka ya maida hankalinsa kan Alhaji garban.
Sabuwar gaisuwa suka sake kafin Abba ya ɗora dayima Alhaji garba bayanin abinda ya faru akan auren Jiddah, Alhaji garba dai baice uffanba. Ganin haka sai Abba yakuma gyara zamansa yana faɗin, “To ni yanzun nayanke wata shawarar danasan zatai maka daɗi insha ALLAHU, tunda dai hakan ta kasance mizai hana nabaka ƙanwar ita Jiddah ɗin Zarah, itama yarinyace mai hankali, kuma tana kama da Jiddahn ma sosai wlhy”.
Wani banzan kallo Alhaji garba ya zubama Abba, “Alhaji Zakari nakula dai kama maidani wani sha katafi kawai, to bara namaka gwari-gwari dai kawai, bana buƙatar auren kowace yarinya ma ni yanzun, dan na auro wadda take tsaremin komai dake sakani aure-aure, yanzu hakama dai zancen danake maka gobenan zakaga sammaci, dan nariga na shigar dakai kotu akan kuɗina. Naji tausayin haɗaka da Ashir ne kawai wlhy, dan kaɗan daga aikinsa yasaka fitsari a tsaye, nabarka lafiya, saimun haɗu a kotu”.
Gaba ɗaya abba yagama ruɗewa, duk maganar da yakema Alhaji garba yaƙi saurarensa, saima yunƙurin shigewa sashen amaryarsa da yakeyi. Akuma dai-dai wanann lokacinne hajia deluwa ta fito saboda jin ƴar hayaniyar maganar da abba kema Alhaji garba.
Ai tanayin ido huɗu da Alhaji garba itama saitayi kansa da gudu. Saurin shan gabanta Amarya tayi.
“K ballagazar mace nutsu mana, minene kikeyi haka tamkar sabon kamu?”.
Takaicine ya cika Hajia deluwa, ta ɗaga hannu da nufin marin Hajia Bariki sai caraf aka riƙe hannun nata, Alhaji garbane yariƙe, yayinda ɗayan hannunsa ya toshe hancinsa dan wani irin mugun warin dayafi na jiddah yaji tana masa”.
“k shashasha, karki sake ƙazamin hannunki ya hau kan matata”. Ya ƙare maganar tareda hankaɗe hajia deluwa yakama amarya suka shige abinsu.
Tibiran Hajia deluwa tashiga hauka a cikin gidan, ta koma sashenta ta ɗakko taɓarya tazo taita dukan ƙofar, su balki mai aiki da mai gadi da Abba dabai tafiba sunyi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH. Daga ƙofa hajia deluwa saita koma winduna taita fasa gilasan.
Dolefa Alhaji Garba ya sake fitowa, ƙyaƙyƙyawan mari ya zubama Hajia deluwa.
hannunta dafe da hancinta. Cikin jin azabar shigar marin ta cakumi wuyan rigarsa, tunifa kokawa ta hargitse a tsakaninsu, ƙarfi ba ɗayaba yahau jibgarta ganin zata zubar masa da mutunci gaban ma'aikatan gidan. Saida yay mata lilis tana kuka da zaginsa da jan ALLAH ya isa ya turata cikin sashenta ya kulle.
Su Ashir duk basa gida, shiyyasa Alhaji garba yasamu wannan damar.
Mota Abba ya shiga yafita yana sheƙa dariyar mugunta, aganinsa wannan tashin hankalin kaɗai ya ishi Alhaji garba mantawa da maganar kuɗinsa, indai hakane kam zaisa hindu taita tunzura Hajia deluwa dan ta ɗauke hankalin Alhaji garba.
😆😆maga yanda za'a kwashe to⛹♀😝.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Umma na zazzaune a tsakar gida tanashan labarin gidansu jiddah da su aunty hannatu ke basu Abba ya shigo fagan-fagan tamkar an jehoshi.
Saikuma yayi turus ganin duk ƴaƴansa gasu Yaruwaiya kuma, gashi duksun watso masa idanu tamkar wani ojuju.
Ɗauke kai Umma tayi tamkarma bata gansaba, sai yaranne suka shiga gaidashi, cikin sarƙewar harshe ya amsa musu da tambayarsu ya yara. Abin yabasu matuƙar mamaki.
Umma data fahimci tsorata yayi da ganinsu sai abin yabata dariya, dan alamunsa duk sun sunana bada arziƙi yazoba, ita dama tasan arziƙin bazai kawoshi a irin wannan lokacinba, ballema Jiddah ta tare bai saniba.
Gani kawai sukai yajuya yafita batareda yashiga cikiba, hakanne yasasu tunanin anya lafiya kuwa?, Yaruwaiya tayi murmushi dan itama ta fahimci ba arziƙi ya kawoshiba, ganinsune yasakashi tsorata shine yafita..
Daga nan gidan Abba gidan Uncle yahya yaje ya aika a kira masashi, danya kira wayarsa a kashe.
Amma koda ɗan aiken ya fito saiyace ai Uncle yahya bayanan ma, ance yaje Adamawa.
“Adamawa kuma?” Abba yafaɗa a fili cikin mamaki da al'ajabin uwarmi akeyi a adamawar kuma?.
Bashida mai bashi amsa, danhaka yabar anguwar da ƙudirin ai gobema ranace ko, zai dawone.
🤣🤣Abba kana ruwa gaskiya😝.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*BAYAN KWANAKI UKU*
Abubuwa dayawa sun faru takowanne ɓangare, dan hajia deluwa tana cikin jin azabar jin jiki su Ashir suka dawo suka sameta, hankalinsu tashe sukahau tambayarta miya faru, cikeda magagin azaba tafaɗa musu abinda ya faru, takumace Alhaji Zakari ne da Amarya suka saka Alhaji garba dukanta.
Sosai Ashir da bala suka hasala, suka kuma kira babban wansu suka sanar masa abinda ya faru.
Ransa a matuƙar ɓace shima yazo gidan, sai dai kuma Alhaji garba yaƙi fitowa, wannan ne yasaka su sakawa amusu bincike akan Abba.
Ita kuma suka kaita asibiti, kwananta uku cif tana jinya acan, yau da safe aka sallamosu, suna direta a gida kuma suka nufi gidan Abba da akai musu kwatance.
🙆🏻😨⛹♀Abba maza bisa kanka.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gidan Sheikh Aliyu dai sai muce Alhmdllh, dan suna cikin aminci gwargwadon iko, bandama dai Maimuna dake fama da lalurar laulayi, wadda kuma Alhamdllh tana samun kulawa ga mijinta da Jiddah ma, dan ƙiri-ƙiri Jiddah ke ƙoƙarin hanata wasu ayyukan, dukda itama Maimuna na hana jiddah, acewarta amaryace saita gama amarci sannan.
Amma sam Sai Jiddah taƙi bari. Hakanne yasaka Aliyu kuma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, a gefe kuma yana addu'ar ALLAH yasa su ɗore hakan.
Shida Jiddah dai kam tun ranar bai kuma takurata ba, dan soyake takuma sakin jikinta tamkar yanda yaga ta fara, ƴan wasanni dai kam yakanyi da ita, dan har yanzu a sashenta yake kwana saboda kwanakin da Maimuna ta ƙara musu, da safe Jiddah taita ɓoye fuska batason su haɗa ido, shikam yata tsokanarta kenan yana dariya.
Yaukam tunda suka gama fira a sashen maimunatu ta dawo nata sashen, tana gama shirin barci saiga Aliyu ya shigo shima cikin nasa shirin.
Kallonsa taɗanyi tana amsa sallamar a saman laɓɓanta, mamaki yabata, takula tunda yasha kunun kwakwar ɗanzun yakoma wani shiru, firarma daina saka musu baki yayi, yabarta itada Maimuna kawai.
Cikin sauke numfashi tace, “Kobaka jin daɗine?”.
Murmushi yay mata danya kula batasan dawan garinba, amma harga ALLAH tausayintama yakeji shi, dan yasan yau kam bazai iya juriyar binta a hankaliba tunda yasha kunun kwakwarnan............😶✍🏻
*_Ya Sheikh masoyan jiddah fa sunce kabi a sannu dan ALLAH🙊😆⛹♀_*
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[55➖56]_*
..............Belin Abba dai ya gagara gasu Uncle yahya gaba ɗaya, dagashi har Umma kallo ɗaya zakai musu ka fahimci suna tare da damuwa, hakama su Zarah harda kukansu, sai Ummace taita lallashinsu.
Ɓangaren Hajia Hindu ma tashiga damuwa, hakama yaran data sanar musu duk sai suka shiga rashin walwala, itama saita kwantar da kai suka haɗu dasu Uncle yahya akai cuku-cukun lauya aranar.
*WASHE GARI*
Washe gari ƙarfe shabiyu aka shiga shari'ar su Abba, tun a bayanin ƙarar jikinsu Uncle yahya yay sanyi, anama Abba tambaya, amma sai yaƙi amsa laifinsa, saida aka kai ruwa rana shida Lauyan Alhaji Garba, saida shedun dake tsakani lokacin da aka amshi kuɗin suka bayyana kafin Abba ya nutsu. ya amsa karɓa kuɗin Alhaji garba da yayi, amma yay bayanin yanda sukayi dashi daya bashi auren Jiddah, daga baya kuma saiyace ya janye.
Sosai ran Alƙali ya ɓaci jin sunyi amfani da yarinya cikim harƙallarsu, take anan ya yanke hukunci dan ƙ
Shari'ar bata buƙatar zama na gaba kuma
“Bisa ga sauraren wannan shari'a da mukayi, dakuma amsa laifin da wanda ake ƙara yayi, tareda shaidu ƙwarara, wananan kotu ta yanke hukuncin dolene Alhaji Zakari yaro ya biya Alhaji garba kuɗinsa naira miliyan ashirin da biyar kamar yanda suka tsara lokacin auren ƴarsa, sanan miliyan Ashirin da biyar dayace ya barmasa dolene yacika alƙawari ya bar masa ɗin, tunda anyi auren, kuma yarinyar harma ta tare a gidansa, wani abune daban ya rabasu bayan auren, shikuma Alhaji zakari yaro bazaici miliyan ashirin da biyar ɗinnan shi kaɗai ba, zai ɗauke miliyan goma ne a ciki, sauran miliyan sha biyar kacokan zai ɗaukesu yabama ƴarsa da yay auren jari da ita. anmasa sassauci yafara biyan Alhaji garba ƙuɗinsa kafin ƴarsa, yanzunan za'aje da dillalai gidansa da inda yake sana'a a ƙiyasta da kuɗin da ake binsa, idan sunkai abashi canjinsa, idan basukaiba yanema ya cika nanda sati ɗaya kacal. Kotu”. Alƙali ya buga guduma an tashi kenan.
Sosai hankalin Abba yagama tashi, banda zufa babu abinda yakeyi, kotu kam tuni ta ɗauki ƙananun maganganu, kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan wannan lamari
Ita Umma ma tarasa abin cewa, jinwai Jiddah taci miliyan goma sha biyar. Shi kansa Uncle yahya abin yay masa wani gingiringin, su zarah kam sunrasa mizasuyi, baƙin cikin halin da abbansu yake ciki, ko farin cikin kuɗin da ƴar uwarsu ta samu. Hajia hindu kam ai tana cikin ruɗani, a ganinta wannan shari'ar batayiba, ita kuma ƴaƴanta shikenan su tashi a tutar babu, kai ina da sake alƙur'an.
Umma da yara gida suka nufa gwiwa a sake, Uncle yahya kuwa yabi jami'an tsaro dake tare da abba.
Kasuwa aka fara zuwa babban shagonsa dake danƙare da kayan kicin, nan take mahukunta suka fara ƙiyasta abinda ke cikin shagon da shagon kansa, dan tuni yazama mallakinsa dama.
Har magriba suna cikin kasuwa ana cakusawa, daga ƙarshe akaima shago da kayan ciki kuɗi naira milyan ashirin da biyu, sai cinikin ciki dubu ɗari tara da wasu canji a sama, amma basu cika miliyan ɗayaba, hakanne yasa akabarsu a miliyan 23 kawai.
Sallah kawai sukayi aka nufo gidansa, dama tuni su ashir sun kawo dillalalai ana zuwa maganar kuɗi kawai akayi, ansaya naira miliyan bakwai shima gidan, kuɗi sun kama miliyan talatin kenan, saura miliyan goma ake nema kenan harda na Jiddah.
Hindu dai kuka take rurus yaranta na tayata, wanan wace iriyar masiface, shikansa Abban kukan zuci yake, shikenan yau tashi tagama ƙarewa, ƴar kwanciyar hankalinsama ɗayace sune kuɗin da akace yabama jiddah, yasan insha ALLAHU hannunsa zasu dawo, dan karɓewa zaiyi koda karfin tuwone.
Komawa akai da abba station, Uncle yahya yawuce gida jikinsa a sanyaye.
Sunbar Hajia Hindu na neman yin ƙaramin hauka, dan taci alwashin sam bazata amince da wanan tsarinba. A daren ta kira ƙaninta tantirin ɗan isaka yana zaune a legas tace yataho kano gobe-gobe.
Baƙaƙen magana yafara sakar mata dan basa shiri sosai dama, ta dakatar dashi tanai masa bayani dalla-dalla, jin zancen kuɗine saiya kwantar da hankalinsa, atake yay mata alƙawarin baro legas shida yaransa da adaren ranar.
Wannan shine yaɗan saka mata kwanciyar hankali, dan tasan bazasu tashi a tutar babuba dai kenan suma.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah duk batasan hidimar da akeba, dan Umma ta hana kowa ya sanar mata, amma su Aunty Nafisa dasu Aunty Sauda duk an sanar musu da halin da ake ciki, dukda abinda yay musu kasancewarsa mahaifinsu hakan bai hanasu shiga tashin hankaliba da tsananin damuwa.
Washe gari aka ida tattare kuɗin dake bank accaunt ɗin Abba da wani gidansa dake karkasara ana haya, kuɗi sukakai miliyan talatin da shifa da ƙyar, baida wata sauran kaddara sai gidan dasu Umma suke ciki, shima sai akayi cinikinsa miliyan uku da rabi, yamayi darajane saboda a cikin tsohuwar anguwa yake wadda gidaje keda daraja komai lalacewarsu, dukda ma dai gidan fes yake, ballema anmasa fenti lokacin bikin Jiddah da alhaji garba.
Dabarar da Uncle yahya yayi itace roƙar alƙali a saka gidan dasu Umma suke ciki a lissafin kuɗin jiddah, hakanne yasa aka ɗeba kuɗin Alhaji garba miliyan ashirin da biyar aka danƙa hannun su ashir, sauran miliyan sha shida da takardun gidan dasu Umma ke a ciki aka damƙama Uncle hayha, saura dubu ɗari biyar Abba zai cikama jiddah, anbashi sati ɗaya yakawo cikon kuɗin Jiddah rabin miliyan.
A ranar aka sako Abba da yamma liƙis suka taho da Uncle yahya daya ɗakkoshi da nufin ajiyeshi gida, shikuma yakoma yakai ƙuɗin Jiddah banki, dan canne kawai zasu tsira sai ƙura ta lafa kuma asan abinyi da su.
Zuciyar Uncle yahya a tsarkake take, dan haka yayma abba rakiya har cikin gidansa da aka sayar wanda hajia hindu take ciki.
Abin mamaki saiga hajia hindu taimusu tarba mai nuna alamun damuwa da halin da Abba yake ciki, harda rungumeshi a gaban yara babu ko kunya. Da wanan damar Abba yasamu damar gwargwaɗa mata wata magana. Kanta ta jinjina masa sanan ta sakesa tana kallon Uncle yahya.
“Dama dawowarku muke jira yahya, dan harma munfara haɗa kayanmu, kwanaki biyu kawai suka bamu mubar gidanan, dan ALLAH kozaka taimaka mana da kimtsa kayan ɗakin Abban kalifan”.
Kallonta uncle yahya yayi, kamar zaice wani abu saikuma ya fasa yaɗan kalli agogonsa, yamma tayi lis, ga kuɗinnan da yakeson kaiwa banki “Hindu inaga mubar aikinan zuwa da safe, yanzukam dare yayi gaskiya”.
“To shikenan hakanma babu damuwa, amma taimakamin ka dakkomin wani akwati dake sama a cire takardun gidan Jiddah karsu shiga ruguntsumi”.
Uncle yahya bai kawo komai aransaba, ya maida kallinsa ga Abba dake zaune su Hussain sun zagayeshi, “Babu damuwa, wannene ɗakin?”.
Da hannu ta nuna masa, babu musu ya nufi ɗakin kansa tsaye, saɗaf-saɗaf hajia jindu tabi bayansa, yana shiga taja ƙofar ta rufe.
Da sauri Uncle yahya yajuyo yana ƙwala mata kira da roƙon ta buɗesa, amma ƙiri da muzu taƙi.
Dawowa tayi wajen Abba tana faɗin “Nagama aikin da kasani Abban kalifa”.
Da sauri Abba yaja hannunta sukabar gaban yaran, “Yauwa hindu, abinda yasa nace mu kullesa saboda mu samu mubar gidanan, dan ko sama da ƙasa zata haɗe bazan bama jiddah waɗannan maƙudan kuɗinba, maza duk abinda yadace ki haɗa mu kama hanyar kamaru, dagacan zamuyi sudan, munbar Nageria kenan har abada”.
“ɗari bisa ɗari na gamsu da jawabinka, amma muyi haƙurin asubanci, dan yanzu dare yafara, tafiya da waɗannan makudan kuɗin haɗarine Abban kalifa”.
Shiru Abba yay yana nazarin maganarta, zuwa can yace, “To babu damuwa, yanzu dai ki haɗa mana dukkan abinda yadace, a yanzu mu lodasu a mota, ko yara karki sanar musu komai”.
“Hakan yayi amma kuma matsala ɗaya, idan Yahya yakira mana ƴan sandafa?”.
“Kwantar da hankalinki, saida na tabbatar yabar wayarsa a mota sanan”.
Daɗi ya kama hajia hindu ta rungume abba cikeda ɗoki.
Duk bugun ƙofar da Uncle yahya keyi basu buɗeshiba, harma yagaji ya bari, hankalinsa yayi matuƙar tashi dajin bayanin da Abba yazo yamasa a bakin ƙofa.
Idanunsa na zirar da hawaye yace, “Yaya karka aikata haka, Jiddah fa ɗiyarkace data fito daga jinin jikinka, miyasa zaka aminta da cigaba da zalintarsu suda mahaifiyarsu, kana ganin adalcine gudun da zakayi ka barmu saboda dukiya? Baka tsoron ita wadda zaka gudun da ita taci amanarka?, wlhy nasan jiddah zata iya barmaka kuɗinnan, amma sh........”
Cikin daka tsawa Abba yace, “Ya isheka haka munafiki, babu abinda ya isa dakatar dani wlhy”.
“shikenan naji yaya, Amma makomar auren maman Nafisa fa?”.
”Aurenmu na nan munafiki babu mai rabashi, bazan taɓa yadda bakin inna ya biniba, tunda tace idan na saketa ALLAH ya isa ko bayan ranta to bazan saketanba balle kaje ka aureta, dan nasan burinka kenan a kulum, saidai ta mutu da aurena wlhy”.
“Yaya karkayi haka dan ALLAH, wanan zaluncine wlhy, ka tausayama baiwar ALLAH nan koda a wanan gaɓarne”.
Tsaki Abba yay yabar masa bakin ƙofar.
Sosai hankalin Uncle Yahya yakuma tashi, haka yahaƙura ya zauna yana ƙulla abinda zai fisheshi, gashi wayarsa na a mota ya bari.
Cikin dare saiga ɓarayi sunyi dirar mikiya a gidan Abba, tun Uncle yahya najin hayaniya sama-sama harya fara jiyo magiyar da Abba kema ɓarayi da roƙonsu.
Zuwa can kuma yajiyo suna dukan Abba yana kukan ihu, sai ihun hajia himdu da yara dayake jiyowa suma, gabannin asubahi saiyaji tsitt alamun ƴan fashin sun tafi, sai koke-koken yaran da hajia hindu.
Hindun yashiga ƙwalama kira yana buga ƙofar, kalifa yaje ya buɗe Uncle yahya.
Uncle yahya na fitowa yaci karo da Abba a yashe tamkar gawa, kallo ɗaya zakai masa kasan amatuƙar jigace yake da duka.
Kansa kawai Uncle yahya yayi yana kuka, itama Hajia Hindu da alama an daketa a ƙafa, dan zaune kawai take gaban Abba tana hawaye.
Ganin Abba ko motsi bayayi yasaka Uncle yahya barinsa yatashi ya fita neman motar kaisu asibiti....
★★★★★★★
Taimakon gaggawa aka shiga bama Abba, da ita kanta hajia hindu da aka jima ciwo a ƙafar haggu.
Hankalin Uncle yahya bai kwantaba saida akace masa Abba ya farfaɗo, amma anmasa Allurar barci. Itama hajia Hindu barci takeyi.
A lokacinne yasamu nutsuwar ɗaukar su Hassan yakai gidan Umma.
Duk da Uncle yahya bai sanar musu tushen matsalarba, Hankalinta yatashi daga ita harsu Zarah dajin abinda ya faru, kuka sukeyi sosai abin tausayi.
Umma da Uncle yahya ne kawai suka koma asibitin, akabar su kalifa anan gida taredasu Walida.
Batun tashin hankalidai ba'a maganarsa ga wanan family yau, dolene kagansu su baka matuƙar tausayi, ƴan adamawa ma duk an sanar dasu, hakama Aunty Zulai dake huntuwa.
Aunty Nafisace ma hartazo asibitin, Jiddah ce kawai Uncle yahya yaƙi sanar mata.
A ranar a asibitin Uncle yahya da Umma suka kwana wajensu Abba.
Su Kalifa kuwa acan wajensu zarah, sukaita zubama su Zarah rashin kunya akan bazasuci garau-garau da Walida ta dafa ba, wai sai dai aimusu miya, su Mom bata basu abinci da mai da yaji.
Daga Walida har Zarah watsar dasu sukayi suka cigaba da hidimarsu, idan yunwar ta rarakesu ai saci.
Ilai kuwa zuwa dare da sukaga babu mafita sai suka ɗauka sukacin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari su aunty Hannatu dawasu a cikin dangi suka iso, Abba dai ya farko, sai dai ko magana baya iyayi saboda kumbura da fuskarsa tayi dam, tsakaninsa da mutane sai dai ido, ga karaya har biyu a ƙafarsa da ƙugunsa saboda duka sukai masa na fitar hankali.
Itama hajia hindu ta farko, kuma ita da sauƙi sosai, dan nata gocewar ƙashine.
Duk wanda yaga Umma da Uncle yahya a wanan lokacin saisun baka tausayi, dan dukkan lokacinsu yanakan Jinyar Abba da hajia hindu ne, hakama hidimar asibitinsu sai da kuɗinsa akeyi.
Zuwa dare su Aunty Sauda suka ƙarasa gida dansu huta. Dukda ba abin daɗi bane ya kawosu, kuma basu daɗe da tafiyaba daga bikin Jiddah hakan bai hanasu Zarah murnar zuwansuba.
Su kalifa kam sai suka hau kumbure-kumburen baki wai basason wanan gidan hayaniya tayi yawa da ƙauyawa.
Hakanne ya fusata Aunty Nafisa ta zubama kalifa mari har biyu ƙwarara, aiko ya zauna yana zaginta, Aunty Zulai tasa wayar caja ta zaneshi sosai, dama haushin yaran sukeji to🤣
Wanan duka da akaima kalifa yasaka su Hassan nutsuwa waje ɗaya suka haɗiye tasu rashin kunyar, shi dama Munner bashida matsala, kasancewarsa ƙarami baikai sauran wayoba.
Zarah ce ta sanar musu Jiddah fa bata san halin da ake cikiba, Uncle yahya ya hana a sanar mata.
Numfashi Aunty Sauda ta sauke tana faɗin, “Nidai a ganina yakamata ta sani, dan gaskiya Abba yanajin jiki, mubama Uncle shawarar ya sanarma koda mijintane koya kukace?”.
“Wanan shawarar taki tayi aunty Saudah wlhy”. Cewar aunty Nafisa dake bama yaron aunty hannatu akamu.
Sun yanke shawarar masa magana da safe idan sunje asibiti.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau Jiddah cikin ɗoki take Aliyu zai koma wajen Maimunatu. Dan kwanakinta goma sun cika harda kwana shidan da maimuna ta ƙara musu. Dukda ba takurata yakeba itadai sotake ya koma can.
Su kaɗaima sukai hirar dare yau, danshi tunda safe yay tafiya shida malam dawasu malaman yin wa'azi jihar katsina.
Har sukai sallama Jiddah tatafi sashenta bai shigoba.
Saida tagama shirin barci tana ƙoƙarin kwanciya taji bugun ƙofa da sassanyar muryarsa yana kiran sunanta.
Hijjab ta saka tazo ta buɗe masa ƙofar falon.
Taɗanyi mamakin ganinsa da jallabiya, kenanma harya dawo yay wanka, haka kawai saitaji wani iri a zuciyarta, ya dawo amma ba'a sanar mataba balle tafito masa sannu da zuw.......
Numfashi ta sauke saboda jinta a jikinsa, cikin kunnenta ya raɗa mata “Yadai Jiddatulkhair? Ko bakiyi kewata baneba?”.
“Humm nayi mana”.
“Shine kikaƙi zuwa tarbata?”.
Shiru tai bata bashi amsaba, hakan yasakashi ɗago kanta yana kallon fuskarta data canja alamar damuwa.
“Mike faruwa? Naga kamar ranki a ɓace”.
”Babu komai” tai maganar tanason janye jikinta daga nasa.
Rikota yayi daƙyau, yajata zuwa saman kujera, saida ya zauna sanan ya ɗorata a cinyarsa.
“Mike faruwa? Faɗamin kinji Habibty”.
“Nifa nace babu komai”.
“Uhm-uhm ban yardaba wlhy Jiddah, karkiga ban daɗe da saninkiba kiyi tunanin ban fara fahimtar halayyarkiba, wani abun akai miki”.
“Ba aimin komaibafa ni, Amma shine ka dawo bamsaniba har saida ka daɗe, bayan tun ɗazun muna dakon zaman jiran dawowarka tare da auntyn”.
Murmushine ya ƙwace masa babu shiri, wato duk yanda mace take baka rabata da kishi, wanan jinin jikinsune, rungumeta yay sosai yana faɗin “To amin Afuwa amarsu, nayi tunanin kar in takurakine, dan kina baro sashen auntynki babu daɗewa ina shigowa”.
Yinƙurawa tai zata tashi yay saurin maidota a cinyarsan, zatayi magana ya ɗora bakinsa kan nata.....🙊
Ajiyar zuciya taita saki bayan ya saketa, uffan bata iya cemasaba har ya kawota ɗaki ya kwantar, saida yay mata addu'a ya tofeta sanan yashiga mata tausa a hankali.
Luf tayi tamkar tayi barci, hakanne yasaka Aliyu barinta, ya kashe mata fitila sanan ya fita tareda ja mata ƙofar.
Yana fita hawayen da batasan dalilinsuba suka ziraro mata, itadai tasan tayi murna dazaije can ya kwana, dan itadai takura takeyi da kwanciyarsu a gado ɗaya, amma batasan dalilin dayasa wani sashen zuciyarta yakejin ɗaciba, komi hakan yake nufi oho?.
Ta daɗe batayi barciba tanata juye-juye, sai can tsakkiyar dare barci ɓarawo yay awon gaba da ita.
★★★★★★★
Da asuba lokacin daya leƙo tashinta salla harta tashi, tana zaune a bakin gado tana addu'ar tashi daga barci ya shigo. Kallo ɗaya taimasa tai ƙasa da idonta tana gyara wuyan rigarta take a buɗe sosai.
baice da ita komaiba ya juya ya fita, ta ɗanbi bayansa da kallo harya ɓacema ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tamiƙe zuwa bayi ɗauro alwala............✍🏻
_Masoyan Abba zakari Amin afuwa fa, babu ruwana Alƙaline🙊⛹♀⛹♀⛹♀🤣_.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[53➖54]_*
............A matuƙar kasalance ya zauna a bakin gadon idonsa akan ƙirjinta, hakan data fahimtane yasata yinƙasa da kai da ƙoƙarin gyara ƙaramin gyalen data ɗaura akanta ya rufe mata ƙirji sosai.
Sassanyan murmushi yayi yana lumshe ifanunsa da sauke ajiyar zuciya kafin yakuma buɗewa a kanta yana miƙewa tsaye, hanyar fita ya nufa, saida yaje ƙofar sanan yajuyo yana kallonta “Idan kingama abinda kike, Kisameni a ɗakina”.
Kamar zata fasa ihu tace, ”to”.
Bai kuma cewa komaiba ya fice abinsa.
Shiru jiddah tayi a tsaye, zuciyarta sai saƙawa da kwancewa take, tana mamakin miyasa yace taje can? Tunda tazo gidan bata taɓa shiga ɗakinsaba, kullum shike zuwa ya sameta, taja wasu mintuna kafin ta matsa gaban madubi ta ɗauki turare ta fesa da wasu sirrikan ƙamshi na humra, sannan ta saka hijjab har ƙasa ta fita.
Gidan tsitt babu wata hayaniya gashi babu nepa, rabonsu da wutarma tunda safe, saida aka tada gen ɗin masallaci, kuma suna kammala karatu aka kashe, koda Aliyu ma yashigo gidan har an kashe.
Taja wasu adadin mintuna a bakin ƙofar falon kafin ta tura ta shiga da sallama. Babu kowa a falon, hasalima dunɗum yake da duhu, fitilar wayarta ta haska falon dashi, komai yamata ƙyau gwargwadon iko, kujeru da labuloli duk kalar ruwan siminti, sai baƙi kaɗan, ƙofa ɗaya dake rak a falon ta nufa, ta ɗora hannunta saman handle ɗin, harzata murɗa saikuma ta fasa tayi tsaye tamkar mai fargabar shiga ɗakin jarabawa.
Saida taja kusan mintuna biyu kafin ta murɗa ƙofar ta buɗe, da sallama ta shigo a bakinta kanta a ƙasa.
Aliyu dake zaune a bakin gado laptop a gabansa yana dannawa ya ɗago ido yana kallonta da amsa mata, kafin ya ɗauki kofin shayinsa yakai baki.
“Kosai na taso nayi tarbane Amarya?”.
Kai Jiddah ta girgiza tana cigaba da takowa ciki da faɗin, “A'a nagode”.
Murmushi yayi yacigaba da abinda yakeyi, “Bismillah ki zauna to”.
Takowa tayi zuwa bakin gadon ɗan nesa dashi ta zauna.
Kofin shayin ya miƙa mata. ta girgiza masa kai alamar a'a.
Baice mata komaiba ya cigaba da akinsa, itama saita jawo littafin *KITABUT TAUHID* daya ajiye tana dubawa.
Kusan mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago yana kallonta, ”Afuwa gimbiya inaɗan rage saƙwannine, kozaki tayani?”.
Murmushi tayi tana riƙe baki, “Wai inani ina wannan saƙwannin? Aina manyane”.
Ɗan murmusawa yay kawai yana cigaba da aikinsa, “Hakadai kikace, amma ai kuma bana wasa baneba Jiddatulkhair. Shin Kin haddace littafin nan ne?”.
Ɗagowa tai taɗan kallesa ta janye idonta “A'a ba dukaba, mun fara babu daɗewa na daina zuwa makarantar”.
Sosai ya kalleta yace, “miyasa?”.
da ƙyar ta iya fisgo maganar tana inda-inda, tunda yataɓa cemata bayason ya tuna ta taɓa aure, ”lo lokacin wancan au..ren ne”.
“Humyim” kawai yace yamaida kansa.
Kasa daurewa tai saida taɗan kallesa saboda yanda ya bata amsar, ganin yacigaba da aikinsa itama saita cigaba da duba littafin.
Minti kusan ashirin yanata aikinsa, kafin ya janye laptop ɗin gefe yana faɗin “Alhamdulilahi, hajiyata basai kicemin na huta hakananba”.
Cikin rufe fuska Jiddah tace, “Haba saikace wani aiki?”.
“Aikine mana tunda nabar Matata ita kaɗai” yay maganar yana Matsowa jikinta.
Jitai duk kasala ta saukar mata, taɗan matse jikinta waje ɗaya tana sinne kanta.
Sumbatar hannunta yay dake riƙe a nasa, “kinyi alwalar barci?”.
“A'a” ta faɗa tana girgiza masa kai.
Batareda yace komaiba ya fara ƙoƙarin cire mata hijjabin, batayi jayayyaba ta barsa ya cire, kayan barcinta wando da riga kalar pink suka bayyana, sihirtaccen ƙamshin da take zubawa ya shaƙa yana lumshe idonsa, kansa ya ɗaura bisa kafaɗarta, gashin gemunsa dake taɓata ya saka tsigar jikinta tashi, hancinsa yakai jikin wuyanta yana shinshina, tuni jikinta yakuma yin sanyi ƙalau.
Ganin yana neman zurmawa tace, “Zanje nayi alwalan to”.
A kasalance ya sauke numfashi kafin ya matsa daga jikinta yana nuna mata hanya alamar taje tayi.
Sum-sum tamkar munafuka ta wuce bayi ɗauro alwalar barci. Bayinma yamata ƙyau, gashi a tsaftace babu wani ƙazanta, kodayake dama batai tunanin samunta daga gareshiba, dan ko farcen malam ka kalla kaɗai ya isa shaida maka shimai matuƙar tsaftane.
Taɗan jima sannan ta fito, yanda ta barshi haka tazo ta iskeshi yana duba littafin data ajiye. Ta gefen ido yake kallonta harta zo ta ɗayan gefen ta kwanta can ƙarshen gadon.
Ruwa takeson zuwa tasha, amma kallon ƙurullar da yake mata duk saita daburce. Shima lura da hakanne ya sakashi ɗauke idonsa daga kanta yana faɗin, “Ko kina buƙatar wani abune?”.
“Uhm zan sha ruwa ne”
jug ɗin Ruwan dake ajiye a dirowar gefen gadon ya tsiyayo ya miƙo mata. Zaune ta tashi ta karɓa tanasha, shikuma ya miƙe yanufi bayi.
Lokacin daya fito Jiddah hartayi addu'ar barci tai luf.
Baice mata komaiba ya shinfiɗa abin sallah domin yin shafa'i da wutiri kamar yanda ya saba. Duk abinda yake Jiddah na kallonsa, amma taƙiyin koda ƙwaƙwƙwaran motsi dazai tabbatar da hakan.
Yaɗan jima yana addu'a kafin ya miƙe yay shirin barci, tunda Jiddah taga zai cire jallabiyar jikinsa saita rumtse idonta, shi baimasan tanayiba, duk zatonsa kotayi barcine mashi.
Harya hawo gadon ya kwanta da kashe fitilar tana jinsa, hannu yasa ya lalubota yana jawota jikinsa, “Haba Kairunnisaa, waya ce miki haka mata da miji ke kwanciya?”.
Shiru tai takasa koda tari, saida taji yana hura mata iska a kunne ne tashiga sauke numfashi da ƙyar, hakanne yasakashi fahimtar idonta biyu dama, sai kawai ya canja zuwa wani salon daban..........🙊⛹♀
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Baƙi dai duk sunyi ƙaura, hatta dasu balu duk sun tafi, sai umma taji gidan duk babu daɗi, yayinda kewar jiddah ta dawo musu sabuwa fil a zuciya.
Koda Uncle yahya yazo ɗazunma da safe haka yaytajin babu daɗi da baiga jiddah ba. Yazone sun tattauna akan batun sauran kuɗin sadakin Jiddah daya rage a wajensa, shinema har yake sanar mata Abba yaje nemansa ranar, amma sai ya cema yaron yace yaje Adamawa, kuma yana gida babu inda yaje.
Murmushi Umma tayi tana faɗa masa suma dayazo nan bai zaunaba ya fice abinsa.
“To ALLAH ya ƙyauta, insha ALLAH idan ya huce zanje nabashi haƙuri, dan nasan da gaske ba a ƙyauta masaba ɗin, amma bamuda wata mafitane sai wannan ɗin”.
Murmushi kawai Umma tayi, dan tasan ko maƙiyi bazaice yahya baiyiba, mutumin kirkine dayasan haƙƙin ɗan adam da darajar zuminci. a wannan zamanin irinsu ƙalilanne a cikin al'umma.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Ashir harsun kama hanyar gidan Abba sai yayansu ya dakatar dasu bayan zuciyarsa tamasa wani tunani.
Canja hanya yayi zuwa police station.
Bala yace, “Wai ina kuma zaka kaimune yaya?”.
“Station zamuje Bala, ɗaukar hukunci a hannunmu bai daceba, ai dama da jiƙaƙƙiyar kuɗi a tsakani, kunga daganan saimu wuce kotu”.
A fusace Ashir yace, “Amma yaya kabarmu muɗan sassafashi mana, kaga daga yanzu baya sake munafincin zuga waniba ai”.
“cooldown ƙanina, abinda zamuyi masa yanzu saiyafi duka zafi ai”.
Shiru duk sukayi badan sun soba, a station duk abinda ya dace sun yishi, atake akaje kamo Abba.
Abba yana kasuwa hankalinsa kwance, dan sosai yakejin daɗi ganin a kwana ukunan babu sammacin da Alhaji garba yace za'a kawo masa na kotu, shi kansa Alhaji garban ma baya zuwa kasuwa gaba ɗaya.......
Yana tsaka da wannan tunaninne ƴan sanda suka iso shagon bisa kwatancen dasu Ashir sukai musu.
Sosai gaban Abba ya faɗi, amma saiya fuske yana mazurai, ƴan sanda dai bayani sukai masa na buƙatar ganinsa a ofishinsu. Kamar Abba zai musa saikuma ya fasa ganin idanun mutane yadawo kansa gaba ɗaya.
Tunda aka baro kasuwa da Abba ƙananun magana ke tashi, kowane baki da abinda yake faɗa akan wannan tafiya da ƴan sanda sukayi dashi.
★★★★★★★★★.
Hajia hindu da yara tun suna tsumayen shigowar Abba har suka bari, gashi yau yamusu alƙawarin sayo musu kayan daɗi idan zai dawo kasuwa, hakanne ya saka yaran zumuɗin dawowarsa, amma har goma na dare tsit kakeji babu amo babu labari.
Ƙosawar dasu kalifa sukaice tasakasu fara tsaki, itako hajia hindu takaicinta da tunaninta yanakan cewa Abba yana gidan Ummane jarabarsa ta kaisa, hakanne yasakata ɗaukar masifaffen fushi, tacika tayi fam dan kumbura, sai kaɗa ƙafafu take na tsumuwar bala'i.
Wasa-wasa dai har shabiyun dare, tuni ta kora yaran ɗaki sunje sun kwanta, itakam tana zaune tana shiryama Abba shika-shikan bala'in da zata ɓarar masa idan yadawo gidan. Dataga lokaci ya jane taje ta kwanta itama.
Hummm😑😶
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Iya tantance tsakanin aya da tsakuwa jiddah tayi a daren jiya kam, shikansa ya Sheikh yasan yabuɗe ƙwanji da yawa, kuka dai hajjaju jiddah an shasa har an godema ALLAH, sai taji ranar ashe wasan yara akayima, yau ɗinne ta tabbatar da menene daren farkon.
Tana zaune bisa abin salla ya dawo masallaci, kanta a ƙasa ta amsa masa sallamar.
Muskarsa shinfiɗe da murmushi ya zauna a bakin gadon yana kallonta, cikin rawar murya tace, “Ina kwana”.
“Ba irin wannan gaisuwar akema mijiba ai kairunnisaa”.
Batareda ta shiryaba taɗan ɗago ta kallesa tai saurin janye idonta gefe.
“Ya kika fasa kallon nawa Hauwa-Jiddah?”.
Shiru tayi takasa bashi amsa, tasowa yayi da kansa ya kamata ya miƙar tsaye, dukda tagaza kallonsa bai damuba, ya cire mata hijjabin tareda sumbatar goshinta da laɓɓanta, cikin kuma sanyaya muryarsa yace, “ALLAH yay miki albarka kinji, yabama su Ummi ladan tarbiyar da suka baku”.
Hawayen da take maƙalewa suka silalo, a zuciyarta ta amsa da amin.
“Kukandai bazai ƙareba Jiddatulkhair?”. Yay maganar yana share mata hawayen.
Haɗiye sauran kukan tayi da ƙyar, cikin sinne kanta tace, “A'a na daina, bara naje kar aunty tace zatayi aiki da kanta, kaga jiya ta yini batajin daɗi ma”.
Murmushi yay idonsa akan laɓɓanta dake motsawa a hankali, ya ɗora goshinta saman nasa yana kallonta, “Ai kema bakida lafiyar, kiyi kwanciyarki zanje na tayata ni, dan yau a gida zan yini”.
Ba ya da ta iya dole tabi Umarninsa ta kwanta ɗin, shikuma ya fice sashen Maimuna.
A kicin ya sameta tana ƙoƙarin kwaɓa filawar da zatai fankasu, ya sumbaci gefen kuncinta yana faɗin, “Jazakillahu bil jannah Ummudduniyah”.
Murmushi tayi dukda kishinsa da takeji na taso mata, taɗan juyo itama ta sumbaci kuncinsa tana amsawa da, “Tare da kai Kalby”.
“Ya babyna?”. Yay maganar yana zagayo da hannunsa a cikinta daya fito sosai.
“Yana cikin ƙoshin lafiya Nurry, sai dai kewar Abbunsa da yakeyi sosai”.
Numfashi ya sauke a cikin kunnenta, cikin raɗa yace, “Shima Abbu yana kewarsa matuƙa, ko zamuje yanzu mu gaisa”.
Dariya Maimunatu ta sanya, “Yaya nikam rufamin asiri, ina ƙanwata?”.
Murmusawa yay yana sakinta kafin ya shafa kansa, cikeda jin kunyarta yace, “nabarota tana azkar, mizan tayaki dashine?”.
Maimuna tai murmushi kawai, dan tasan badai azkarba, da azkarne ai dabaizo tayata aikiba, a filikam sai tace, “A'a na hutashsheka”.
“Nikuma ban hutar da kainaba madam”.
Babu yanda ta iya dole ta barsa sukayi aikin tare, bayan sun kammala yakoma ɗakinsa.
Wayam ya tarar babu kowa jiddah ta gudu, amma an gyara ɗakin tsaf yanata ƙamshi.
Wanka yayi yashirya cikin ƙananun kaya, sosai yay ƙyau tamkar ba shiba.
Jiddah data gudo tuni koda tadawo sashen natama ba kwanciyar tayiba, gyara ɗakinta zuwa falo taɗan kumayi, ta ɗaura ruwa ta dafa takuma gasa jikinta sosai sannan tai wanka, tagama shirinta tsaf tana ƙoƙarin kunna wayarta Aliyu ya shigo.
Kallo ɗaya tamasa ta ɗauke kanta tana amsa masa sallamar, sai dai yamata ƙyau sosai, yaune ranar farko data taɓa ganinsa da ƙananun kaya, ashe dama yana sakawa....?
Har ya iso gabanta bata saniba, saida ya riƙo hannuntane tadawo hayyacinta. “Malama jiddah tunanin mi akeyine haka? Ko nawa?”.
Murmushi tamasa kawai.
Shima saiya murmusa yana faɗin “Kinyi ƙyau sosai tawan, irin wannan gayu haka mai hana ango fita?”.
Sosai ta dara yanzukam tana rufe baki, shima dariyar yakeyi zuciyarsa namasa daɗi da sakin jikinta da takeyi dashi sosai yanzun.
Saida ta saka gyale sanan suka nufi sashen Maimunatu, yauma dai kosau ɗaya Jiddah bata yarda sun haɗa ido da maimuna ba, sanan bata saka baki yau a hirarsu sosai kamar sauran ranakun, shi Aliyu yasan kunya da sauyin da jikinta ya matane ya kawo hakan, itakuma Maimuna sai takejin tsoro a ranta kar jiddah ta fara sauyawa saboda daɗin miji data fara ji.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da safe koda su Kalifa suka wuce makaranta sai hajia hindu tai shirin zuwa gidan Umma da nufin mata barka da tashin baƙi wai, amma kuma abinda ke a ranta shine son ganin idon Abba.
Ta iso Umma ce kaɗai a gidan, Walida da Zarah duk sun wuce makaranta, zarah wata islamiyya ta shiga anan anguwarsu ta matan aure, ana zuwa tara a taso sha ɗaya, gani tagama ssce exam ɗinta da zaman banza sai Umma tace tashiga islamiyyar kafin ALLAH ya kawo mafita, idan auren ne kokuma saɓanin hakan.
Umma na jan ruwa a rijiya Hajia hindu tayi sallama ta shigo.
Ɗagowa Umma tayi tana amsa mata sallamar da mata sannu da zuwa, sai dai ƙasan ranta tayi mamakin ganinta, dan ranar tariyar jiddah ma sai yamma liƙis tazo gidan, kuma bata daɗeba ta tafi.
Amma sai Umma ta tareta da ƙyaƙyƙyawar fuska, bayan tace mata tashiga falo itakuma ta ɗiba ruwa ta bita.
Kafin Umma ta shigo hajia Hindu tai saurin leƙa bedroom ɗinta wai ko Abba yana ciki, wayam ta gani, hakanne ya sakata saurin komawa ta zauna saboda jin motsin tahowar Umma.
Ruwan Umma ta ajiye mata sanan ta zauna suka gaisa suna tambayar juna yara. Kafin cikin kissa hajia hindu tace, “Ai zuwa nai dama Zarah ta rakani nagano gidan ƴata Jiddah”.
Umma tace, “ALLAH sarki, gashi kuma kunyi saɓani tanama islamiyya”.
“Kai amma banso hakanba wlhy, shiyyasa naita roƙon Abbansu ya jirani mufito tare tunda yace nan zaizo”.
Murmushi Umma tayi batace komaiba, hakanne yasakasu yin ɗan shiru na wasu mintuna......
Sallamar Uncle yahya ne yasaka Umma miƙewa tafito tana amsawa, yanda ta gansa kamar a rikicene ya sata tambayar “lafiya kuwa Uncle ɗinsu?”.
“Wlhu Maman Nafisa babu lafiyarnan, dan yaya aka kama tun jiya, sai da safenan naje kasuwa nakeji, naje station ɗin da aka kaisan kuma sunƙi bani belinsa, yanzu dai haka zancen danake mikima sunce kotu za'a shiga gobe idan ALLAH ya kaimu”.
Cikin dafe ƙirji Umma tace, “Akanmi ni Yagana?”.
Cikin tsantsar damuwa Uncle yahya yace, “maganar kuɗin Alhaji Garbane”.
Hajia hindu tafito itama a rikice tana sallallami, mamaki sosai Uncle yahya yayi da ganinta, amma dayake a ruɗe yake sai baibi takantaba suka shiga maganar mafita kawai.............✍🏻
*_Masoya ina miƙo ɗunbin gaisuwa a gareku tareda fatan alkairi, alkairin ALLAH ya kai a gareku aduk inda kuke, Comments naku na sakani nishaɗi ƙwarai da gaske, shikuma ke ƙaramin ƙwarin gwiwar muku typing koban niyyaba, ina godiya da addu'oinku gareni ga mahaifina😄🥰🥰🥰😘🤝🏻👍🏻❤_*
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[57➖58]_*
.............Ciwon dake ƙafarta ba shine matsalarta ba, hankalinta naga kuɗin hannun ƙaninta, gashi bataga alamun wayarta na tare da itabama........
Umma ta katse mata tunani da faɗin, “Maman Hussain ki daure kici abincin nan, ciwo bayason zama da yuwafa”.
Hajia hindu ta ɗan sauke numfashi, ta ƙasan ido ta harari Umma kafin ta yatsine fuska, “Zanci Maman Nafisa, abincinne gaba ɗaya bayamin daɗima ni wlhy”.
Umma taɗan murmusa, saboda tasan baƙa hajia hindu ta faɗa mata. Abba ma na jinsu, sai dai babu bakin magana, a zuciyarsa kam babu abinda yake jinjinawa sai ƙyaƙyƙyawar zuciyar Umma, wai ita wace irin mutumce mai maida sharri da alkairi?. Bashida mai bashi wannan amsar, sai hawayen da suka gangaro masa ta gefen ido wanda su Umma basu gsniba. Shi kansa baisan dalilin zubarsuba, zafin ciwone? tausayin kansane? Kokuwa nadamace?, shidai yasan har yanzu baiji a ransa ya aikata badaidaiba gasu Umma, yanzu da ace ƴaƴansane maza sukazo a manya da ƙasar waje za'a kaisama jiyyarnan.........
Shigowar Uncle yahya ce ta katse tunanin Abba, tare yake da mijin Aunty Nafisa, saisu Aunty Zulai dake a bayansa suduka harsu kalifa.
Da gudu su Hassan suka nufi uwarsu, Maneer ne kawai yaje wajen Abba yana faɗin “Abbanmu bakada lafiya? Miya sameka?”.
Ummace ta janye Muneer ganin zai fara kuka, Abba ya janye idonsa daga Muneer da Umma ya maida kansu Kalifa da ko sau ɗaya basu kalli inda yakeba, sun zagaye uwarsu suna faɗa mata ƙarya da gaskiya da akai musu a gidan Umma. Tuni ita kuwa launin fuskarta yagama canjawa...
Tsawa Uncle yahya ya dakamusu, kafin ya zubamusu daƙƙuwa da faɗin, ”Kunci gidanku, toku su wanene da idan kukai laifi baza'a hukuntakuba?, waɗannan ba yayyenku baneba?, ko Walida ce ta tsawatar muku ba dole kujiba balle Zulaiha da Nafisa, duk wanda na ƙarajin bakinsa saina zanesa a asibitinnan, gida kam ai dole kuzauna tunda bakuda kamarsa yanzu. Kekuma maman kalifa kin zauna saurarensu bazaki ko tsawatar musuba”.
Cikin Kumbura fusaka tace, “Yo yahya minene abin tsawatarwa anan?, daba a cuta musuba zasu faɗane”.
Tsit gurin yay duk suna kallonta, Abba ne kawai yaji daɗin abinda tayi a ransa, danshima yaji haushin an dokar masa ƴan lelensa, saidai babu bakin magana.
Daganan babu wanda yakuma tofa baki acikin lamarin su kalifa, anan suka yini a asibitin har yamma liƙis sanan Uncle yahya yace su koma gida.
Hajia hindu naji na gani Uncle yahya ya kora su kalifa daketa ƙunƙunai su bazasu komaba, wai tuwo da koko da shinkafa kawai akeci a gidan, sukuma basu iya ciba (hhhhh ƴaƴan turawa😹).
Ko kallonsu Uncle yahya baiyiba, danshi dariyama suke bashi wlhy.
Su Aunty Saudah suka tuntuɓi Uncle yahya akan batun faɗama Jiddah, murmushi yayi, “Karku damu zata sani, amma sonike sai zuwa kamar jibi haka, duka yaushe taje gidan mijin da za'a sakata fitowa?, sonake sai zuwa jibi ta cika sati biyu insha ALLAH, suma zuwa sanan sun fara samun sauƙi, kunsan Jiddah da ruɗiya, kuma zuwanta bashine zai basu lafiyaba ai”.
Sun amsa da to, tareda gamsuwa da maganarsa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_Bayan kwana biyu_*
Har zuwa yau Jiddah batasan mike faruwaba, kuma tana waya da Umma da Uncle yahya, hakama aunty Nafisa, babu kuma wanda ya faɗa mata.
Yauma dai haka ta yini ita kaɗai a sashenta, saboda zuwan da Amina da Hassana sukayi gidan, sanda sukazo tana sashen Maimuna suna kallon wani tafseer ɗin Sheikh Aliy, amma tundaga shigowarsu jikinta yay sanyi, dan wani kallon banza sukaita binta dashi, koda ta gaidasu babu wanda ya amsa saida Maimuna tace Auntys jiddah nafa gaisheku. Duk a yatsine sukace “oh ALLAH sarki, bamuji bane”.
Jiddah bata gazaba takuma maimaita musu gaisuwa, lokacin ita Maimunatu taje kicin kawo musu ruwa, tsaki sukayi mata basu amsaba, hakanne ya sakata miƙewa tabaro sashen ta dawo nata jikinta sanyi ƙalau da tunanin sukuma su wanene? Tagadai ɗaya na bala'in kama da Maimunatu (Hassana). Koda ta dawo sashenta sai abin yakuma ƙuntata zuciyarta, tana cikin tunani a falo saigasu sun shigo Maimuna ta rakosu wai zasuga ɗaki, dan ita maimuna batasan abinda suka kuma yima Jiddah ba.
Jiddah ta saki fuska takuma tarbarsu da mutuntawa a nan ma, babu inda basu shigaba, amma sai wani yatsine fuska suke, komai suka gani sai Amina tace, “Aunty Hassana nikam ba wanan abun bane ranar muka taya a wajen ƴan gwangwan ɗincan dubu uku?”.
“Shinefa ƴar uwa, kinma manta dubu biyu suka barmana daga baya”.
“Hakanefa wlhy, nama manta”.
Gadajen Jiddah ma da kujerunta haka sukaita musu iskanci, wai Hassana taje kasuwa akace za'ai mata a dubu arba'in, amma tace basuyi mataba tawuce nan.
Ran Maimunatu ya ɓaci sosai, dan haka taja hannun aunty hassana suka fice, amma saita fisge tana mata masifa.
Acan kuma Amina nata gaggasama Jiddah magana ta rashin mutunci, itadai jiddah batace mata komaiba, saima kanta data duƙar a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, har Amina tayi tagama ta fice sanan ta ɗago tana kallon ƙofa hawaye na ziraro mata, ta daɗe a falon tana kuka kafin ta koma bedroom ta kwanta, ganin zata ƙuntata kanta da yawa ta kunna karatun Al-Qur'ani tana saurara, a haka barci ya kwasheta.
Sai da Maimuna tazo kawo mata ɗanwake da tamusu na ranane ta tadata dan har anyi salla ma.
Sannu tamata da godiya, Maimuna tafita saboda su Amina basu tafiba, da zama ta kawo mata abincinan da hanawa sukayi sunata mata masifa, sai da tace wlhy zata kira Malam ta sanar masa kafin shima Aliyu ya dawo ta faɗa masa, sannan ne suka bata hanya suna zaginta wai baiwar kishiya. Itadai batabi takansuba ta fito kawoma Jiddah abincin.
Har yamma lis su Hassana suna gidan, sai bayan la'asar ne suka tafi, jiddah najin tafiyarsu saboda dariyar da sukeyi suna sakin magana a kanta, amma sai taƙi fita, dan duk zuciya nason mai ƙyautata mata.
Maimuna sashenta ta koma, duk zuciyarta babu daɗi itama, dolene tasaka a takama su Aunty Amina birki akan zuwa gidan, dan itadai baza'azo a haɗa mata fitina a gidan aurenta ba, suna zaune lafiya a ɓata musu zama, badan Jiddar tanada hankaliba da biyema su Aunty Hassana zatayi sosai, dan ba kowa zai yarda da wannan cin kashinba, jitai Jiddah takuma birgeta, sai dai yanzu tsoronta karta faɗama Aliyu abinda ya faru ne.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Alhmdllh jikin Abba yaɗanyi sauƙi, dan kuwa kumburin fuskarsa ya sauka, sai daifa yanashan azamar ƙafa da ƙugu, wanima tashin hankali shine ɗorin karayar ƙugunsa bata ɗoruba, likitoci sukace sai an sake, ankumayi yau da safe yaci azaba iya iyawa amma ba'a daceba, shine Uncle yahya ya yanke shawarar kiran wani na gargajiya, dan haka yaroƙi likitan akan su sallami Abba za'a canja masa asibiti, sunyi hakanne dan sunsan idan sukace na gargajiya za'a likitocin bazasu yardaba, shikuma tsoro yake kar goma ta lalace biyar bata gyaruba.
Sosai hajia hindu tayi murna da wanan sallama, dan itafa ba damuwarta Abba ba, hankalinta nakan kuɗin data saka ƙaninta yazo yay musu fashi. Kamar yanda Umma da Uncle yahya suka yanke shawara haka akayi, kai tsaye gidansu Umma aka wuce dasu Abba, ɗakin dake soro Uncle yahya yasaka aka hudo ƙofa ta cikin gida tun jiya, ita kuma hajia hindu aka kwashe kayansu Zarah daga ɗakinsu aka gyara mata.
Su aunty sauda duk basuso hakaba, dan yanzu dai ba gidan Abba baneba na Jiddah ne, saida Umma taita tausarsu sannan suka bar zancen.
Sosai hankalin hajia hindu ya tashi, wai ana nufin wanan gidan data bari tsawon shekara sha shida dawasu watannine za'ace ta dawo da zama?, wanan ai ci bayane, dolene ta nemo ƙaninta a yau yakawo kuɗin nan tanemi ƙaramin gida tasai musu itada ƴaƴanta, shiko Abba yazauna nan yayi jiyya, idan ya warke ya nemesu.
Abba kam yana cikin azabar ciwo, bayama tantance a ina yake balle asan sirrin ransa
Gidan dai yamusu kaɗan sosai, amma haka sukai maleji, da daddare wasu sukaje gidan Uncle yahya suka kwana.
Su kalifa kam abufa ya damesu, sai kuka sukema hajia hindu basa son wanan gidan, sudai akoma gidansu. Hajia hindu saita sake rikicewa, dan ita kaɗai yaran suke addaba, basayi gaban su Uncle yahya.
Washe gari da safe mai gyara yazo, sabon ɗori ya sakema Abba a ƙugu, suma kam Abba yayita babu adadi, su Zarah kuka kawai sukeyi, hakama Umma takasa daurewa, sosai takejin tausayin Uban ƴaƴan nata dukda tsiyatakun daya shuka mata.
An gama gyaran Abba ya samu barci na wahala, a lokacinne hindu tasamu zarafin tambayar Uncle yahya wayarta wai zata sanarma danginta.
“Wayoyinku suna cikin wata jakarki na zuba, tana nan inaga an taho da ita, amma ina Zulaiha itace kamar nabama jakar dazamu taho?”.
aunty Zulai dake sharo ɗakin Umma tace, “Eh Uncle tana nan ɗakinta a jar jaka”.
“yauwa to kinji tana nan, sauran kayanku suna gidan malam Alfah na roƙi alfarma aka kai can, saboda mu gidajen namu babu inda za'a iya lode waɗan nan kayan, kayan gado dai dasu kujeru duk an saidasu harma katufun, guda ukunan dakika gani kaɗai muka bari, acikin kuɗinne ma akabama mai gyaranan kuɗinsa, dan wlhy nidai kuɗin dake wajena sun ƙare, a jiyama saida na taɓa kuɗin sadakin jiddah dubu ashirin aka ɗako sauran kayanku, amma an maida mata yanzu haka, wanan daliline yasa muka matsa aka sallamoku daga asibiti, tunda bamuda kuɗin cigaba da biyan kuɗin gado da sauransu, yarannan kuma su Hannatu iya ƙoƙari sunyi dagasu har mazajensu, koma nace suna cikinyi”.
A ɗage hajia hindu ta amsa da “Uhhum”. Dan taji haushin saida musu kayan gado kuwa, amma babu komai aiga kuɗinan.
Babu wanda yasakebi ta kanta, saboda amsar da tabama Uncle yahya ta Uhum kowa tabashi takaici.
Shidai Uncle yahya yay musu sallama yatafi gida danya ɗan huta kafin Abba ya farka.
***********
Da rana akayi faten doya da wake da alayahu, ƙiri-ƙiri su Hussain sukace bazasu ciba, babu wanda ya tanka musu sai Umma daketa musu nasiha da lallashinsu, amma ƙiri da muzu sukaƙi saurarenta, saima rashin kunya da suka nemi yimata, aiko Aunty Hannatu dukda haƙurinta tai azamar taka musu birki.
Hakan saiya harzuƙa hajia hindu tafara sakin magana, gashi tana ƙyaɓe waje ɗaya tana fama da kanta.
Aunty Zulai zatai magana Umma ta hana, takumace kar wanda ya sake tankawa, daga yanzuma komi su Halifa zasuyi a gidan babu ruwansu, abinci dai idan andafa a basu, suci ko karsuci wanan yarage nasu ai.
Hajia hindu dai tanata neman ƙananun magana babu wanda ya kulata, ga takaicin neman kaninta da take a waya amma taƙi shiga, tamasa kira yafi hamsin sai dai ace mata Busy, tun tana ɗaukar abin wasa har nutsuwa ta fara gagararta.
Hummm hajia Hindatu yaya dai⛹♀😹?.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah na zaune a falo bayan tayi sallar la'asar tana duba littafin *Ahdhari* Aliyu ya shigo da sallama, ɗago idonta da sukai alamun tayi kuka tayi ta kallesa tana amsawa, ya tsaya a ƙofa tareda buɗe mata hannayensa alamar tazo gareshi.
Murmushi tayi tamiƙe jiki a sanyaye, dan yariga ya shaida mata hakan dokane acikin tsarinsa, kuma koba komai tana buƙatar jin ɗuminsa a halin yanzun da zuciyarta ta wuni a ƙuntacennan.
Shigewa tayi ajikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
shima numfashi ya sauke, yace, “Nayi kewarki Jiddah na”.
Ahankali ta furta “Nayi kewarka sosai nima”.
Babu shiri yay azamar ɗago kanta, dan maganarta tabashi matuƙar mamaki, baiyi zaton hakan agareta ba nan kusa. Lumshe idanunta tayi tana murmushi, dan batason su haɗa ido.
“Jiddatulkhair da gaske koda wasa?”.
Fuska taɗan shagwaɓe tana tura masa baki, “Da gaske mana”. Ta kare maganar da maida kanta a kirjinsa.
“Masha ALLAH, Alhmdllh Adaratul ainy (Turaren zuciyata) ya kuma rungumeta yanajin sonta nakuma tasiri a ransa”.
Bayan sun zauna taje ta kawo masa ruwa. Yana sha idonsa a kanta, dan ya kula tana tare da damuwa kamar yanda maimuna ta sanar masa, saboda sashenta yafara zuwa, itama ya isketa cikin damuwa, ya tsareta da tambaya shine ta sanar masa abinda su Hassana sukazo sukayi, ransa ya ɓaci sosai. Amma sanin halin Maimuna bazata taɓa sakasu suma Jiddah hakanba sai itama ya lallasheta akan karta damu, shi yasan bazata sakasu suyiba hakanba ga jiddah, sunyine kawai dan raɗin kansu, amma zai taka musu birki insha ALLAH.
hakan sai ya saka zuciyar Maimuna ɗan samun nutsuwa, amma damuwarta kuma halin da jiddah take a ciki.
Aliyu ya ɗauki aniyar gwada Jiddah yagani kozata masa maganar abinda su Aminar sukazo sukayi.
“Ƴammatana mike faruwa? Na ganki wani sukuku, ga idonkifa kamar kinyi kuka”......
Murmushi jiddah tayi tana danne abinda ya tokare ranta, “Babu komai, kumani ba kuka nayiba, kawai kewar Ummana nakeyi”.
Idanu ya tsura mata zuciyarsa na tunanin ita takeson sanarma kenan? To amma dataso hakan ai da tayi tunda ga waya a hannunta, saurin kauda wanan tunanin yayima daga ransa, ya ajiye kofin da yasha ruwan yakamo hannunta cikin nasa idonsa akan fuskarta, “Haba tawan, anya kuwa kewar su Ummace kawai? Kodai Auntynki ce?”.
“lah A'a wlhy, ni aunty tsakanina da ita sai sambarka, kawai dai kewar su Ummance”.
“Shikenan, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zan kaiki, yanzuma tashi ki shirya danayi wanka zamuje mu gaida su malam, kinga baki taɓa zuwa gidanba tunda kikazo.
Daɗine sosai ya kama jiddah, harga ALLAH tana ƙaunar dattakon tsohon, tuni taji nauyin da zuciyarta yayi kaso mafi yawa ya ragu.
tace, “To abincifa?”
“Naci abinci a office din mustafa, shiyyasa na kira auntynki nace karkuyi dani”.
Murmushi tayi, dukda batasan anyi hakanba, kuma girkin Maimuna ne har rana, sai yanzu da yammarnan ita zata karbesa, batareda tace komaiba ta mike, harta nufi ƙofar fita Aliyu ya kirata, juyowa tayi ta kallesa, yace,
”Ina zakije kuma?”.
“Zan haɗa maka ruwan wankane”.
“Karki damu zoki haɗamin a bayinki kawai”.
Kanta ta jinjina masa ta dawo da baya zuwa bedroom nata. Binta yayi da kallo harta shige, ya ɗan sauke numfashi yana jingina kansa da kujera, a zuciyarsa yana tunanin miyasa taƙi faɗa masa abinda akai matan? Zai sake gwadata dai ya gani, harga ALLAH yana mamakin yanda wasu lokutan halayyar Jiddah da Maimuna suke kamanceceniya da juna, kodan dukansu sunada ilimin addinine da tarbiyya, kuma Alhmdllh suna aiki da sanin da ALLAH yay musu, sarai yasan salon kishin kowacce amma hakan bai hanasu ƙyautata zamantakewar dake tsakaninsuba..........
Jiddah ta katse masa tinani, idanunsa ya buɗe, ya kama hannunta yana faɗin “Zomuje ki tayani wankan to”.
Sosai ta zaro idanu da faɗin “Wankafa?”.
Tabashi dariya data zaro idon, ya ranƙwafo kanta yana jan hancinta, “Malama baƙyason koyi da sunnar MANZON ALLAH ne? ANNABI yana wanka da Matansa har hannayensu na gogayya a cikin ruwa, baƙyason samun wanan ƙatotuwar ladar tawajena”.
Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana ƙaramar dariya, shima yay dariyar yana jan hannunta sukai ciki....
✨✨✨✨✨✨✨
Gabda magriba suka fito da nufin barin gidan, dan Aliyu soyake yay sallah a masallacin ƙofar gidansu, Kasancewar Jiddah ce da girki maimuna tace ya shiga gaba, amma sai taƙi tace, “A'a wlhy Aunty ke zaki shiga, ba girki zaki dubaba, kimarki ta matsayin babba a gareni”.
Daga Maimunatu har Aliyu binta sukai da kallo harta shige baya, sanan suka kalli juna sukai murmushi, kowannensu yanajin ƙaunarta da kimarta a ransa, yayinda itama hakanne daga gareta.
Sun isa anata hada-hadar shiga sallar magriba, Jiddah da Maimuna suka shige cikin gidan, shikuma Aliyu yashiga masallaci..........✍🏻
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[59➖60]_*
............Duk da agidan Maimunatu ta girma, kuma akwai mariƙiyarta Iya Habi, hakan baisakata kaisu canba itada Jiddah, saita nufi ɗakin hajia bah-bah uwargidan Malam.
Sosai Hajia bah-bah taimusu tarbar mutunci, hakama Na'ima tafito fuskarta ajiƙe da alamar alwala tayo tana musu oyoyo.
Harara Maimuna ta zuba mata tana faɗin “Anƙi a amsa ɗin, aini yarinya mun ɓata”.
“Haba-haba Uwar ukunmu, yi haƙuri, nasan nayi laifi amma wlhy tafiya nayi tun bayan bikin yaya Ali, kuma tambaya bah-bah kiji. Aunty Amarya sannu dazuwa kinji”.
Murmushi Jiddah tayi tana amsawa.
Hajia bah-bah ta katse musu jancen da faɗin, “Da wannam surutun da kika tsaresu dashi da alwala kika kaisu sukayi ga Aliyu can zai tada salla”.
“To bah-bah. Kunga kumuje to”.
Ɗakin Na'ima suka koma, domin yin sallar acan.
Bayan an idar da sallah Aliyu na gaisuwa da mutane wayarsa tayi ring, cirota yay daga aljihu ya duba, ganin Uncle yahya saiya faɗaɗa murmushinsa, bai ɗagaba saida ta tsinke sannan shi ya kirashi da kansa.
Daga can shima Uncle yahya murmushin yayi ya ɗaga, cikin girmama juna suka gaisa, Uncle yahya yama Aliyu bayanin halin da Abba ke ciki kusan kwana uku.
Sosai hankalin Aliyu ya tashi, yace, “Uncle aida an sanar mana, babu wata damuwa, ko yau aka kaita washe gari hakan ta faru ai dolene tafito, kuma koni aida nazo dubashi. Insha ALLAH gamunan zuwa bayan isha'i”.
“ALLAH ya kawoku, nagode a gaida min malam”.
“Zaiji insha ALLAH”.
Sosai lamarin ya zauna a zuciyar Aliyu, duk zuciyarsa taimasa babu daɗi, tausayin Abba sosai ya ɗarsu a ransa. Matsawa yay kusada malam dake zaune yana duba alƙur'ani ya sanar masa da abinda ke faruwa.
“Ya Salam, ALLAH yabashi lafiya, yasa kaffarane a gareshi, insha ALLAH zanje na dubashi nima”.
“Amin baba, to ALLAH ya bada iko, suma tare muke dasu sunzo gaisheku, daga nan zamu wuce mu dubashi insha ALLAH”.
“To masha ALLAH, hakanma yayi”.
Bayan an idar da salla malam yasaka Abba a cikin doguwar addu'a, wadda ta saka Aliyu jin daɗi sosai.
A cikin gida kuwa su Jiddah suna idar da salla sukazo suka gaida hajia bah-bah, cikin fara'a ta amsa musu tareda sanya musu albarka. Sanan tace suje su gaida su Gwaggo.
Sun fara zuwa sashen gwaggo amarya, itama ta tarbesu da fara'a, basu baro sashenba saida za'a kabbara sallar isha'i, sashen iya habi suka shiga, itama ta tarbesu da barkwancinta, tareda jin daɗin ganin Maimunatu ta bata cikin damuwa, saitaji Jiddah ta kwanta mata arai, nanma sunɗan jima dan saida sukai sallar isha'i, suka koma sashen Hajia bah-bah saboda kiransu da Na'ima tayi suzo suci tuwo.
Lokacin da Aliyu ya shigo gidan ya iskesu sunacin tuwo a falon hajia bah-bah. Bayan sun gaisa da bah-bah Na'ima ma ta gaisheshi, bisa kuskure Jiddah ta ɗago kai suka haɗa ido, gira yaɗan ɗaga mata yana nuna mata tuwon da ido.
Murmushi ta masa haɗe da ƙaramin gwalo, ya murmusa shima yana miƙewa domin zuwa gaida sauran matan gidan.
“Aliyu ka zauna a kawo maka tuwo”.
“A'a Bah-bah, Alhmdllh, kinsan ni ba cin abincin darenma nakeba kwata-kwata”.
Cikin hangame baki tace, “Wai wanan halin naka har yanzu baka barshiba Ali? Randa baka yini agidaba shikenan bazakaci abincin iyalinka ba?”.
“Bah-bah ai inacin na safe, rashin cin abinci dare abune mai ƙyau, yana ƙara lafiya inhar mutum zai iya jurewa”.
“A'a wlhy badaniba kam, yoni idan banci tuwo da darebama jinake tamkar banida lafiya a gidan nan”.
Dariya su Jiddah saukayi kaɗan, kujifa hajia bah-bah da wani batu, saikace wadda batayi salla ba.
Shidai Aliyu fita yay yana mata dariya. Bai daɗe sosai ba ya dawo yana faɗin, “Kumuje ku gaida malam akwai inda zamuje insha ALLAH”.
Maimuna da Jiddah suka miƙe, dan dama sungama cin abincin, harma sun wanko hannunsu da baki. Sallama sukaima Hajia bah-bah, suka koma ɗakunan su gwaggo suma sukai musu sallama, harda ƴar tsarabarsu ta kuka da ɗanyen kuɓewa da daddawa suka samo.
Saida sukai sallama a ƙofar falo aka basu izinin shiga sanan suka shiga, sun iske malam da Aliyu zaune suna magana, idan ka gansu dolene su baka sha'awa, harsun tsuguna daga farkon falon malam yace, “A'a ƴaƴana ku shigo mana ciki”.
Duk a kunyace suka koma gabansu sosai, kansu a ƙasa suka gaidashi, ya amsa musu cikin fara'a tareda tambayarsu gidan da rayuwar yau da kullum, sanan ya ɗora da nasiha a garesu su duka ukun mai ratsa jiki, yakuma sanya musu albarka tareda fatan alkairi a zamansu.
Suko kansu na ƙasa sunata amsawa da amin, yayinda ƙaunar tsohon da girmansa na ƙara yalwatuwa a ransu.
Baija zancen yayi tsawoba yace, “Aliy tashi kuje dare nayi, dan ALLAH ka gaidamin shi, ga wanan kabashi kafin nazo”.
Tashi Maimuna da Jiddah sukayi suka fita, dukda basu fahimci zancenba sunga yadace su basu waje ko akwai abinda zasu tattauna.
Bayan fitarsu Aliyu yace, “Zaiji insha ALLAH baba, amma kabar kuɗinka zan bashi injika insha ALLAH”.
“A'a karɓi wanan ai tsakanina dashine, kuma nima ina buƙatar ladan sarkin wayo” yaƙare maganar da tsokana.
Murmushi Aliyu yayi ya karɓi kuɗin, sanan sukai sallama da malam ya fito. Ya iske harsu Maimuna sun shiga mota, sai Na'ima dake tsaye ajikin motar suna magana.
Cikin samarin dake gefe ɗaya yazo ya buɗe masa motar da addu'ar sauka lafiya, dama sunzo suka gaida su Jiddah cikin mutuntawa.
Koda suka tafi a hanya bai musu bayanin inda zasujeba.
Ita kuma Jiddah gaba ɗaya hankalinta ma bakan hanya yakeba, game kawai take a waya tana sauraren hirarsu jefi-jefi suma, saida har suka shigo cikin anguwar sosai ne Jiddah ta ɗago kanta donson ganin inama suka dosane?.
Taɗan waro idanu da faɗin “Ai nan anguwarmune”.
Dariya Maimuna tayi ta juyo tana kallonta, “Wai da gaske dan ALLAH?”.
“Wlhy kuwa aunty”.
Aliyu na jinsu amma yaƙi tanka musu, a ƙofar gidansu Jiddah yay fakin sannan ya juyo yana kallon Jiddah.
“Ku shiga, zan shigo daga baya nima”.
Jikin Jiddah kuma sai yayi sanyi, cikin langaɓar da kai tace, “Basai gobe idan ALLAH ya kaimu kaceminba?”.
Ganin Maimuna ta fita saiya shafa kumatun Jiddah, shima cikin kwantar da murya yace, “Haka naje, insha ALLAHU zan kawoki gobenma kinji”.
Haɗiye ƙwallan daya cika idonta tayi, ta sauke ajiyar zuciya sanan ta fita. Har suka shiga gidan idonsa na kansu, saida suka ɓacema ganinsa ne ya sauke ajiyar zuciya da ɗaukar waya domin kiran Uncle yahya.
✨✨✨✨✨✨.
Su Umma duk suna tsakar gida zagaye da Abba da Uncle yahya ke bama Abinci.
Hakanne yasaka Jiddah yin turus tana binsu da kallo, dama ƴan uwanta basu tafiba? Idonta ta sauke akan Abba dake kwance ɗaɗɗaure da karan ɗori, sai Hajia Hindu dake gefe zaune ƴaƴanta zagaye da ita itama.
“Lah yaya Jiddah kece?” ‘Cewar walida data fito daga ɗakin Abba ɗauke da kwanon magani’.
Sauranma duk sai suka maido kallonsu ga ƙofar, Zarah tazo ta rungume Jiddah suka saki kuka tare, dan Jiddah ta fahimci gidansu babu lafiya.
Aunty Hanantu data hangi Maimuna ce ta miƙe tana faɗin “Ashe tare kuke? Shigo mana Maimunatu”.
Gwiwar Maimuna a sanyaye itama ta shiga ciki, dan alamu dai sun nuna babu lafiya kam.
Uncle yahya yayma Jiddah da Zarah magana sanan suka saki juna, Jiddah tazo gaban Abba ta durƙusa tana hawaye, “Abbanmu miya sameka?”.
Dukda haushinta da yakeji dan shi duk akanta yadora laifin, data zauna gidan Alhaji garba wanan bala'in da duk bai afka masaba, amma ya daure yace, “Wannan kukan ya isa haka ko?”.
Kasa tsayar da kukan Jiddah tayi, Maimunatu tazo gabansa itama ta durkusa ta gaidashi, da masa ya jiki?.
Amsawa yay cikin alamun yanajin jiki matuƙa, itama Jiddah ta gaidashi, ana cikin haka Uncle yahya daya fita suka shigo da Aliyu, dama su Umma duk sun kimtsa, gashi a kwai wutar nepa.
Tabarmar dake shinfiɗe a farkon shigowa wadda Jiddah taje ta zauna kusa da Abba Uncle yahya ya nunama Aliyu, kansa a ƙasa bai kalli kowaba ya zauna, Jiddah da gaba ɗaya hankalinta baya wajen saijinsa tayi kusa da ita, miƙewa tai tabar wajen, takoma inda Umma take tana sharar hawayenta.
Aliyu ya gaida Abba yana faɗin,
“لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .
La ba'asa tahoorun in sha'al-lah. (Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda).
أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)
Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7). (ina rokon ALLAH mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
*_(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya”)_*.
_Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya._
*_(ANNABI, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, yace; "Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar 'ya'yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari)_*.
Aliyu yaja doguwar addu'a ga Abba yana share kwallar da shima suka cika mada ido na tusayin Abban
Su Aunty Sauda na amsawa da amin.
Duk sun gaidashi da masa godiya, itama Umma ya gaidata tareda jajanta lamarin, Jiddah na jikinta tana hawaye, yayinda Umma keta shafa kan Jiddah alamar lallashi.
Aliyu ya janye idonsa daga jiddah ya maida akalar gaisuwar ga Hajia Hindu data cika tai fam da haushi, itama yay mata addu'ar samun afuwa.
Ta amsane kawai dan yayi mata mugun kwarjini, yanda takema mazajen su Aunty Nafisa yatsine-yatsine shi saita gaza masa, harshenta har sarƙewa yake wajen saurin amsa gaisuwarsa.
Basu baro gidanba sai goma da rabi, shima saida Uncle yahya yace yakamata su tafi dare yayi, ƴan dubiya daketa shigowa ma sinɗan rage saboda dare ya farayi.
Ƙiri-ƙiri Jiddah ta sanya kuka ita anan zata kwana, tun kowa na ɗaukar abin wasa har suka lura da gaske take, shikuma Aliyu baice uffanba yay musu sallama ya fice abinsa bayan ya ajiye kuɗin da malam yace aba Abba da wanda shima ya bashin, sai kayan marmari dasuka tsaya a hanya suka saya.
Uncle yahya ne yayma Jiddah jan ido sanan ta miƙe su Zarah suka rakota inda Maimuna da Aliyu ke jiranta.
Babu wanda ta kalla ta buɗe bayan motar tashiga tana cigaba da kukanta, Uncle yahya yabama Aliyu hannu sukayi musabaha da godiya shikuma Aliyu nama Abba addu'ar samun lafiya.
Saida suka bar ƙofar gidan su Zarah da Uncle yahya suka koma cikin gida.
A hanyama Jiddah kukanta takeyi, sai dai bamai sautiba, amma su Aliyu na jinta, Maimunatu ce kawai keta lallashinta da bata baki, amma sam Aliyu yaƙi tankawa, ita kuma shirunsa saiya kuma tunzurata takasa yin shiru kodan lallashin da Maimuna ke mata.
Suna isa gida itace farkon fita tabarsu a mota, da kallo kawai Aliyu ya bita, Maimuna zatabi bayanta Aliyu ya dakatar da ita, “Kinga Maimoon barta kinji”.
Cikin langaɓe kai tace, “Haba yaya yazakace a barta, kukafa takeyi?”.
Fitowa yay daga motar shima, “Tunda nace kibarta kawai ki barta, kukan nata harda na hanata kwanane, indai banda rashin son gaskiya taya za'a ƙara musu nauyi bayan wanda suke ciki, idan tayi haƙuri da safe zata koma insha ALLAH”.
Shiru kawai Maimuna tayi, amma ita harga ALLAH bataga laifin Jiddah ba, ko itace sai taso kwana ɗin, to amma ita kanta shaidace akan wannan halin nasa, zata iya rantsewa tunda akai aurensu bai taɓa barinta taje gida ta kwana ba, yini ma yata ɓata rai kenan. Dan haka sai bataja maganarba ta wuce sashenta.
Shima nasa ya nufa batare da yabi ko wannensu ba.
Tunda Jiddah ta shigo ko hijjab bata cireba ta kwanta a gado tana cigaba da kukanta, tausayin Abbansu da baƙincikin an hanata kwana cikin ƴan uwanta yake kuma tunzura kukan nata, ga haushin Aliyu, dan da ace yaso ta kwana ai zaice ta zauna, kuma babu wanda zai hana, rashin amincewar tasane ya saka Uncle yahya korota.
Tana nan kwance harya shigo, dukda taji ƙamshinsa ko motsi batayiba.
Kansa kawai ya ɗan girgiza, ya ajiye kofin shayinsa da Maimuna ta haɗo masa sannan ya zauna kusa da ita.
“Hauwa'u!”. ‘Ya kirayi cikakken sunanta abinda bai cika yiba, saboda sunan mahaifiyarsa kenan’.
Tsoro ya kama Jiddah, saboda jin yanda ya kirata a dake, tamkar ba shiba, hawayenta ta goge sanan ta amsa cikin rawar murya.
“Tashi zaune ki cire wanan hijjabin”.
Bata musa masaba ta tashin, takuma cire hijjabinta amma taƙi kallonsa.
Shima bai kalletan ba yace, “Tashi kiyi shirin barci”.
Tamkar munafuka haka ta tashi sum-sum zuwa bayi. Shikuma ya ɗau shayinsa yafara sha yanamai jin tausayinta da ahalinta, sosai lalurar Abba ta tsaya masa a zuciya, ita kuma tana neman ƙara masa zafi da ƙuruciyarta.
Yana shan shayin ta fito, kayan barcinta ta ɗiba ta dawo ta bayansa ta saka, nanma baice mata ƙala ba, amma da lafiya-lafiya ne cazai shi zai saka mata.
Tana gama shiryawa ta ɗaura zani tazo ta kabbara shafa'i da wutiri. Shidai Aliyu na zaune yana kallonta harta idar.
Sai kumbura fuska takeyi tana cigaba da share hawayen dake zubo mata, hannu ya miƙa mata alamar tazo, da tayi nufin noƙewa, amma sai taga rashin dacewar hakan, tadai turo baki sanan ta matsa kusa da gadon.
Hannunta ya kamo ya jawota zuwa jikinsa a hankali. Tana jinta kwance a ƙirjinsa saita kuma fashewa da sabon kuka.
“Oh ALLAH, ya isa haka mana Jiddah, ko sokike nima namiki kukan ne?”.
Kanta ta girgiza masa alamar A'a.
“To kiyi haƙuri kinji, insha ALLAH zai samu lafiya, Addu'a ya kamata muyi masa ai ko”.
“Amma shine kaƙi yin magana danace zan kwana?”.
Murmushi yayi yana shafa kanta, cikin kuma sanyaya murya yace, “To nayi laifi amin afuwa, amma kema kinsan hakan bai ƙyautuba, kwananki ai ƙarin wani nauyine, idan ALLAH ya kaimu saikije ki yini kinji”.
Da sauri ta kallesa, “Da gaske dan ALLAH?”.
Yanda tai maganar saita so bashi dariya, amma sai ya gimtse ya sumbaci goshinta yana faɗin “Insha ALLAH Qurratul ain, ALLAH dai ya basu lafiya, yakuma tsare gaba”.
“Amin ya rabbi, ammafa ni babu wanda ya faɗamin abinda ya faru”.
“Ni dai Uncle yace min ƴan fashine suka shiga, amma nasan za'a faɗa miki insha ALLAH, sai kinje gobe idan ALLAH ya kaimu”.
Shiru kawai Jiddah tayi, tausayin Abba nakuma ratsata.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari da wuri ta tashi ta haɗa breakfast, kunun gyaɗa sai soyayyan dankalin hausa data yankashi dogaye, saita soya miyar attarugu zalla da albasa, harta gama Aliyu bai shigoba daga massalaci dayaje. Tana gyaran bedroom ya leƙo.
Durkusawa tayi ta gaidashi, bai shigoba ya amsa daga inda yake tsaye a ƙofa, “Mizan tayaki dashine?”.
Kanta ta girgiza masa tana faɗin “A'a ka barshi, shara kawai zanyi”.
Kansa ya jinjina mata ya juya ya fita, ta bishi da kallo saida ya fice sannan ta miƙe taci gaba da aikinta. Ko morping yau ƙinyi tayi, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atanfa, kayan karin kumallon ta ɗiba zuwa sashensa. Shima har yayi wankan yana shiryawa ta shigo.
Idanu ta zaro tana ɗan dafe ƙirji, sanan ta marairaice fuska tana faɗin, “Dan ALLAH kayi haƙuri, banzo na haɗa maka ruwan wankaba”.
“Tab ai bazan haƙuraba yarinya”..
Durƙusawa tayi agabansa, “Dan ALLAH fa nace”.
“To saikin faɗi sunana”.
Babu shiri ta ɗago ta kallesa, yako yi kicin-kicin da fuska tamkar gaske, “Idan har baki faɗaba gwammajan ma bazaki jeba ko”.
Tuni ta fara hawaye, “ALLAH ni bazan iya faɗar sunanka ba”.
“To saikin faɗi abinda zaki ringa kirana dashi, danni nagaji da maidani surukinki da kikeyi”.
Wai shi dama haka wanan mutumin yake?
Jiddah ta ambata a zuciyarta dan takaici, harga ALLAH da burin zuwa gidansu ta kwana, hardasu mafarki, dan haka gara tafaɗa tasamu taje, kuma kasa tayi da kanta sanan tace, *_“Zauji ghaliy”_*.
Kafaɗunta ya kamo ya ɗagota zuwa jikinsa yana faɗin “Masha ALLAH Aglannissa, daga yau karna sakejin an ɓoyemin suna ana kwana-kwana”.
Kanta ta ɗaga amasa alamar amsawa.
Sakinta yayi ta taimaka masa ya ƙarasa shiryawa, sanan taje kiran Maimuna dansuyi kari..........✍🏻
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
0 comments:
Post a Comment