*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[6......]_*
..............Da k'yar ya iya tashi da asubar farko, dan kansa ciwo yake masa, bayi yashiga ya d'aura alwala kafin ya fito ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya ruwan madara, yad'an fesa turare sannan ya fice.
Tunda ya dawo shike kiran sallar farko a masallacin, yauma kamar kullum zazzak'ar muryarsa mai cikeda sanyi ta karad'e anguwar. Koda ya kammala kiran salla ba zama yayiba, saida ya gabatar da nafila raka'a biyu kafin yay zaman karanta littafi mai tsarki. Ahankali mutane d'ai-d'ai suka fara fitowa, ciki harda malam.
Bayan an idar da sallar Asubahi Aliyu bai fitaba, zaman yin azkar na safe yay, saida ya kammala sannan yafito a massalacin. Shiga yay suka gaisa da Malam.
Kallo d'aya malam yayi masa ya karanci damuwa mai tsanani a fuskar d'an nasa, har zai mik'e ya tsaidashi ta hanyar kiran sunansa,
“Aliyu!”.
“Na'am baba” ya amsa yana waiwayowa ga malam.
“Dawo ka zauna”.
Bai musaba ya dawo ya sake zama kansa a k'asa.
“Mike faruwane? ko bakada lafiya?”. Malam ya tambayeshi cikeda kulawa.
Ajiyar zuciya M. Aliyu ya sauke, cikin sark'ewar murya yace, “Lafiyata k'yalau baba, kawai dai wani abune da ban ya girgiza dukkan kuzarina”. Shiru yad'anyi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya, yayinda malam ya kafeshi da Ido amma baice komaiba. M. Aliyu yaci gaba da fad'in “Wani sak'one ya birkita dukkan hankalina wlhy baba...............” tiryan-tiryan ya shiga karantoma baba sak'on yarinyar jiya. Shi kansa baba maganar ta girgizashi, har gumi yad'an tsatstsafo masa a goshi, yanayinsa dukya sauya. Wata ajiyar zuciya ya sauke k'arfi yafara fad'in “Dolene ka girgiza Aliyu, duniyarnan cike take da curkud'ad'd'un abubuwa masu hargitsa tunani, babu abinda ke kusanto duniya sai alamomin tashinta, inaga kamata yay kanemi gidansu ita yarinyar, dan mahaifinta yakamata mu fara gani”.
“To shikenan baba insha ALLAHU zanyi k'ok'arin hakan”.
“ALLAH ya bada nasara, ya maganarmu ka yanke shawaran”.
“Baba kawai nabar maka za6i”.
“To Alhmdllh ALLAH yasa mu dace”.
“Amin” m. Aliyu ya fad'a hannunsa dafe da kansa.
A k'ofar fita daga Falon malam yaci Karo da yayansa Abubakar, hannu ya bashi sukai musabaha cikin girmama juna, Aliyu ya tambayi iyalansa da aiki kafin suyi sallama, Abubakar ya shige shikuma Aliyu ya fice.
Cikin gida ya koma ya sake kwanciya, dan kansa ya matsa masa da ciwo ainun.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Umma ta dad'e zaune zuciyarta Na suya, ta tsurama tea d'in data had'ama Abba ido, wai ko kunya baijiba a gabanta yake fad'in zaije yakai yaransa makaranta saboda motar da ake kaisu babu mai, bayan a gaban idonsa su Walida suka fita amma ko ALLAH ya kiyaye baice musuba? Sai yaushene Alhaji zai fahimci kuskuren da yake tafkawa a rayuwarsa? Kosai guri ya k'ure masane?. Wani lokaci takanji kamar bazata iya jure wannan zamanba, musamman idan ta kalli halin k'unci da yaranta suke a ciki. Sai dai kuma wani 6angaren tana duba wani Abu, yaranta sunkai girman da gidan mahaifinsu shine adonsu, dan burin kowacce y'a a nema aurenta tana gidan mahaifinta gaban iyayenta biyu. Wasu hawayen takaicine suka ziraro mata, tayi murmushin da iyakarsa hak'oranta tareda mik'ewa tahau tattare kayan shayin da Wanda ta had'ama Abban.
Sallamar Dauda ta jiyo a tsakar gida, ta amsa masa tana fad'in, “Ina zuwa Dauda”.
Daga tsakar gida ya amsa da “to”.
Tea d'in data had'ama Abba ta d'auka ta fito, Dauda ya rissina yana gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa masa kamar yanda ta Saba. “Yau naga ka makara, ko Baku tashi a makaranta da wuri bane?”.
Dauda yace, “A'a muntashi, Na tsaya yin rubutune a allona”.
“To ALLAH ya taimaka, bara Na kawo maka abincinka ka karya saikai maza ka kaimin 6arzan masarannan dan ALLAH, yau sonake nayi dambu, kowa yagaji da shinkafarnan”.
“To hajia” dauda ya fad'a cikin girmamawa.
Kunu da fanke Umma ta kawo masa, ta had'o da shayin data had'ama Abba duk tabama Dauda.
Wasu y'an aikace-aikacen tafara ragewa kafin Dauda daya fita soro cin abinci yagama yakai mata 6arjin masaran.
Babu dad'ewa ko saigashi, dama ta had'a masa a wani k'aramin boket, dan haka kud'in 6arjin ta bashi dana abinda zai sayo Mata Na cefane. Sannan ta nuna masa masaran.
Bayan tafiyarsa bata zauna ba, ta kunna redio tana saurare da rage wasu ayyukan gudun zama tunani ya addabeta.
★★★★★★★★★★★★
Koda Jiddah ta fita bata zame ko inaba sai gidan Uncle yahaya, ta iske su Sadiq sun tafi makaranta, sai mamansu kawai da Uncle yahaya daya dawo jiya. Sosai ta nuna farincikinta da ganinsa, shima cike da tsokana da k'aunar yaran d'an uwan nasa yake fad'in “Sayyadata mafarkin dawowata kikayine?”.
Dariya Jiddah da Maman Sadiq sukayi, Jiddah tace, “kamar kasani kuwa Uncle, dukda dai banyi mafarkinba amma tunda asuba dana tashi zuciyata keta kwad'aitamin Abbana ya dawo, ashe da gaskene”.
Uncle yahaya yace, “ALLAH ya albarkaci wannan zuciya da tarin alkairi yarinyata”.
“Amin Uncle, kadawo lafiya? Wlhy munyi matuk'ar missing naka, kusanfa watanka biyu kenan?”.
“Nima ina cike da kewarku, dan banda yanda zanyine, inasu Zarah da Maman Nafisa?”..
“Duk kowa lafiya”.
“To Alhmdllh, nima yanzu nake shirin karyawa naje Na gaida Maman Nafisan ai”.
“To shikenan Uncle, Abba ma yana gidan, inba dai kafin kaje ya fitaba”.
“Yau kuma ya tuna da anguwar tamu kenan?”. Uncle yahaya ya fad'a cikin takaici.
Jiddah ma saida yanayinta ya canja. Maman Sadiq ce tai saurin canja yanayin nasu da fad'in “To Y'ar Uncle tashi ki had'a tea ga doya nan a kula”.
“Wai, wlhy mama cikina a cike yake, makaranta Zan tafima lokaci yayi”.
“Haba dai jiddodo ai d'anyar fata bata fashewa, ki k'ara lodawa kawai”.
Dariya Jiddah tayi tana mik'ewa da fad'in “Lallai Uncle ka tanaji kud'in kaini a d'inke nawa, dan nasan dai zai iya fashewa inhar na k'ara masa wani abu”.
Nanma dariya Uncle da Maman Sadiq sukayi. Jiddah ta nufi hanyar tafiya tana musu sallama.
Kiranta uncle yayi yabata d'ari biyu.
“A'a Uncle basai kabani ko nairaba, naci Na k'oshi mizanyi da kud'i?”.
“Hawa Napep mana, ko har yanzu dai bakiji fad'ana Na hanaki wannan tafiyar k'asanba?”.
Shiru kawai tayi tana murmushin yak'e, dan tasan tafiyar k'asa zuwa makaranta yazame mata tamkar dolene, tunda ba kullum Umma ke tashi da kud'iba, bazai yuwu ace kullum kuma zatazo wajensa ta amsaba, inama laifin wahalar da yakeyi dasu akan karatun da buk'atun yau da kullum alhalin mahaifinsu nada ransa bai mutuba................
Uncle ya katse mata tunani da fad'in “Ina kuma kika tafi Hauwa'u!?”.
Ajiyar zuciya ta sauke ta risina ta kar6a tana masa godiya, sannan tayi musu sallama ta fita.
Uncle yahaya ya jinjina Kai kawai yanamai jin takaicin halin d'an uwansa, wai ALLAH yay maka k'yau ka butulce masa saboda shaid'ancin zuciya, ga wasu can suna nema da miliyoyin kud'i basu samuba. Yaja guntun tsaki yana faracin abincin da Maman sadiq ta ajiye masa.
Batace masa komaiba, dan tasan inda tsakin nasa ya dosa.
Yau da wuri Jiddah ta Isa makaranta kasancewar ta hau napep da kud'in da Uncle yahaya ya bata.
Makarantace babba mai d'auke da d'alibai Mata zallah, amma yara da k'anana harma da matan aure.
Wata musabak'a dasu Jiddah sukaje tazo Na d'aya shine ta burge wani bawan ALLAH, a take a wajen yaymata albishir d'in d'aukar nauyinta zuwa wannan makaranta harta gama, dan da iyakarta islamiyyar anguwarsu, a yanzu haka kuma sune ke a aji shida fanin y'an Mata. Tunda Jiddah ta shigo makarantar take samun nasarori, kwakwalwarta takuma bud'ewa, dan ayanzu haka babu wani Kalmar larabci dazata layance mata, a littatafai kuwa Na fannin Addini tuni tayi babbar zarrah, 6an garan Qur'an tadad'e dayin sauka tana akan hadda. Kai bama itaba dukkan Wanda kagani a ajin su Jiddah to kwarone a makarantar, makarantace daduk Wanda yake cikinta lallai ya kwankwad'i ilimi ya k'oshi, dan ana tatosune daga wasu k'ananun makarantu Ana kawosu nan, babu ruwan wannan makaranta dakai d'an wanene?, duk Wanda kagani kaifin kwakwalwace ta kawoshi.
Kamar yanda dokar makarantar take duk Wanda ka iske a aji dolene kayi sallama, Na ciki su amsa maka, sannan kabisu d'ai-d'ai kabasu hannu kuyi musabaha🤝🏻.
Yanzuma hakace ta kasance ga Jiddah, bayan tayi sallama duk suka amsa, ta yaye nik'ab d'inta tanabinsu d'ai-d'ai suna gaisawa cikin musabaha da murmushi shinfid'e akan fuskarta, saida takai har k'arshe sannan tadawo mazauninta Na gaba ta zauna kusa da Madeena Isma'il da kusan itace k'awarta da suke mutunci sosai a makarantar.
Murmushi sukaima juna bayan sun kuma kama hannun juna suna gaisawa.
“Ukti yau naga kin iso da wuri?”.
Jiddah tace, “ki Bari kawai ukti, yau dai naji fad'anki banyo tafiyar k'asaba”.
“To Alhamdllh da farajin maganata”.
Y'ar dariya sukayi a tare, wadda shigowar malam Mustafa ta katsesu. Duk suka mik'e suna gaisheshi kafin yabasu izinin zama.
Jawabin daya kawoshi ya fara musu, danshi ba koyar dasu yakeba, shine Vice principal na makaranta.
”Umm Assalamu alikum, nasan zakuyi mamakin ganina a wannan lokacin, wani uzirine ya tasomana Na gaggawa, an gayyaci wannan makarantar cikin jerin taron k'arama juna sani Na k'asashe goma da aka shiryama d'alibai, taron kuma zai gudana ne a sati mai zuwa, insha ALLAH zamu za6i d'alibai biyarne kacal, wannan ajin shine Na manya idan aka cire ajin matan aure, dan haka mun yanke shawarar d'aukar d'alibai biyu a cikinku, insha ALLAH malam Usman zaizo anjima ya za6i wad'anda zasu jagoranci tafiyar amma ta hanyar rubuta jarabawa, daganan zuwa awa d'aya kunada damar yin nazari, zamu dakatar da malamai yau gaba d'aya daga kowanne darasi”.
Atare ajin ya d'auki kabbarar *ALLAHU AKBAR!!!*.
Malam mustafa yay musu sallama ya fita.
Nanfa kowacce tashiga duba littatafanta da fatan dacewa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Abba kam yana isa katafaren gidansa ya iske su kalifa tsaitsaye a harabar gidan suna jiransa. Babu Wanda ya gaidashi, saima tunzura masa baki da suka shigayi wai sunyi fushi.
Fuskarsa cike da fara'a ya hau fad'in “O shalelen Abba amin afuwa kunji, maza kushiga mota Na kaiku karku makara, Abba yayi laifi ayi hak'uri”.
Cikin tura baki Hassan yace, “Amma Abba tunfa d'azu muke jiranka, kabarmu dukmun bushe a tsaye”.
”Ai nace ayi hak'uri ko Hassan, Muneer taho kaji”. Yak'are maganar yana Kama hannun autansu Muneer.
Kalifa kuwa da Hussain uffan basuceba, shi kalifa ma iyafis ya saka a kunne, Hussain kam yayi cid'in-cid'in da fuska yana wani shan k'amshi.
Ko'a mota Muneer ne kawai ke fira da Abba, amma Hussain da kalifa da Hassan tamkarma babusu a motar.
Ya diresu a makarantarsu mai tsananin k'yau ta y'ay'an manya y'an gata, ya zaro dubu d'aya yabama Kalifa, babu ko godiya yay wucewarsa aji, Hussain da Hassan kuma d'ari biyar², suma dai babu godiyar, amma sun d'aga masa hannu alamar bye.
Munner ne aka bama d'ari biyu dukda an shiryo masa abinci a lunch box nashi kuwa.
Kalifa ajinsa uku 6angaren sakandire, Hussain da Hassan su kuma aji biyu, Munner kuwa yana firamare 5 ne.
Saida Abba ya raka Munner har sashen y'an firamare sannan yashiga motarsa ya fito daga makarantar................✍🏻
Kuyi manage please😄👌🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[7.....]_*
..............Kamar yanda malam Mustafa ya fad'a bayan awa d'aya malamin da zaima su jiddah jarabawa ya shigo, sallama yay suka amsa masa tare da gaisheshi.
Ajin yayi shiru kowa yana kallon malam Sulaiman, yad'an tura hularsa baya yana shafa gaban goshinsa da nazarinsu, saikuma yay murmushi ganin duk sunyi tsuru-tsuru sun zuba masa idanu. Zama yay inda aka tanada domin zaman malamai kafin ya kuma maida hankalinsa Kansu.
“Inaga nama canja shawara kawai, zanyi jarabawar da baki”.
Kallon kallo aka komayi tsakanin su Jiddah, kowanne a sanyaye ya amsa da,
“Na'am ya mu'allim”.
Fita malam Sulaiman yayi, babu jimawa ya dawo shida Malam Shu'aibu da malam mika'il. Nanma su Jiddah gaidasu sukayi. Malam Sulaiman yabasu izinin fita waje su duka, zuwa wajen wata bishiyar dake gaban aji. Ahaka zasu ringa zuwa d'aya bayan d'aya.
Da yawansu sun rikice, dan kowa baisan miza'a tambayeshiba, ga malam Sulaiman gwanine wajen iya zak'ulo tambaya.
Amirar ajin mai suna Shamsiyya jamilu yasaka ta rubuto sunayen kaf y'an ajin tazo saman baranda tana kiransu d'aya bayan d'aya. Hakan kuwa tafaru, bayan tagama rubuta sunan kowa aka Fara, gaba d'ayansu dama su 38 ne a ajin, dan haka aka fara komai a tsanake. Kowa ya fito saikaga yana mazurai, nanfa cikin Jiddah Yakuma d'urar ruwa, (dama ita kwai tsoro) saima Madina ce ked'an k'arfafa Mata gwiwa. Tunda aka kira Bilkisu Ahmad Jiddah takuma tsurewa, dan daga bilkisun sai madina sai ita. Bayan fitowar bilkisu aka kira Madina daga nan sai Jiddah, tamkar wadda k'wai ya fashewa a ciki haka ta shiga ajin, inda kowa ke zama idan ya shigo ta zauna itama.
Malam Sulaiman dake kallonta ya karanto mata tambaya,
*“Malama Jiddah ko zaki iya fad'a mana Kalmar shahada da Manarta?”*.
Dak'yar Jiddah ta iya had'iye yawu, k'asan zuciyarta tana addu'ar Neman nasarar yin bayani cikin nutsuwa, zamanta tad'an gyara cikin sanyinta tace,
*_“SHAIDAWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH , KUMA MUHAMMADU MANZON ALLAH NE”_*
_Wad'an nan kalmomin shahada guda biyu, sune kofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka k'unsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
*_MA'ANAR KALMAR SHAHADA_*
_Ma’anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma’anarta, da kuma yin aiki da abin da tak'unsa, zahiri da bad'ini, malamai sun had'u akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma’anarta ko yin aiki da abin da ta k'unsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma’anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi kad'ai matsarkaki mad'aukaki._
Rukunan wannan kalmar (shahada) sune (korewa da tabbatarwa), wato kore hak'k'in bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi kad'ai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta
K'unshi kafircewa d'agutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Mad'aukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha’awa), da nuna masa k'iyayya da yin kubuta daga gare shi.Wanda ya fad'i wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta
musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai fad'eta
ba.
ALLAH Mad'aukaki sarki ya ce:
“Kuma abin bautarku abin bauta ne guda d'aya. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi. Mai
rahama Mai jink'ai”.(Bak'ara: 163).
Kuma ALLAH Mad'aukaki ya ce:
“Babu tilastawa game da (shiga) addinin
(musulunci), hak'ik'a shiriya ta bayyana daga 6ata, saboda haka wanda ya kafirce wa d'agutu kuma ya yi
imani da ALLAH, to hak'ik'a ya rik'i igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masani
ne”. (Bak'ara: 256).
Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya kudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko Wanda yake da ikon kirkira, kuma ya kudurci cewa yin imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kad'aita
ALLAH da ibada ba, to hak'ik'a fad'in kalmar (La Ilaha illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shiba daga azaba madawwamiya.
ALLAH Mad'aukaki ya ce:
“Ka ce (da su): “Wane ne yake arzutaku daga
sama da k'asa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al’amura?” To za su ce: “ALLAH ne”. To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?” (Yunus: 31).
ALLAH Mad'aukaki ya ce:
“Ko wane ne ya halicci sammai da k'assai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki masu k'ayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare
da ALLAH, A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya)”.(Naml: 60).
Kuma ALLAH Mad'aukaki ya ce:
“Kuma lallai idan ka tambayesu, “Wane ne ya halicce su?, Lallai za su ce: “ALLAH ne” To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?” (Zukhruf: 87)”. Jiddah ta k'are jawabinta cikin sauke numfashi da ajiyar zuciya.
“ALLAHU Akbar”. malam uku suka had'a baki wajen ambata. yayinda jiddah keta addu'ar dacewa da tsoron yin kuskure.
Malam mika'il yace, “zaki iya tafiya”.
Kamar an bige mata gwiwoyi haka ta mik'e ta fito, a bakin barandar ta zauna kamar yanda su madina sukayi. Murya k'asa-k'asa madina tace, “Ukti mi aka tambayeki?”.
Jiddah tai murmushi cikin sanyinta tace, “Ma'anar Kalmar shahada. Kefa?”,
“Ni sharud'd'an Kalmar tauhidi guda biyar. Amma wlhy duk saina rud'e ukti”.
“Bake kad'aiba ALLAH, har yanzu ni kaina gabana baibar fad'uwaba”. Cewar Jiddah tana kar6ar ruwan da madina ta mik'a mata. Sosai tasha ruwan harta d'an samu nutsuwa. Suna zaune a wajen suna d'an ta6a hira har aka gamawa kowa suka koma aji. Bayan fitar malaman kowa ya shiga k'us-k'us da makwafcinsa a kan tambayar da akai masa. Da wannan suka cinye lokacin tashin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai kusan 9:30am Malam Aliyu yasamu tashi, kansa yad'an rage ciwon amma yanayi k'asa-k'asa har yanzu.
Tashi yay bakinsa d'auke da addu'a, yayi mamakin barcin da yayi, a gaggauce ya mik'e yayo alwala domin gudanar da sallar walha kamar yanda ya Saba, yau barci yasashi zai makara. Koda ya idar d'akin ya kimtsa, ya d'auki filas d'insa Na tea ya fita zuwa cikin gidan dan Neman ruwan zafi. Ta k'ofar cikin gidansu yabi inda Kai tsaye zata kaishi sashen iyalan malam. Shiru gidan babu wata hayaniya, Kai tsaye kicin ya nufa, nanma babu kowa dama baiyu tunanin samun kowanba, yana tsaye zuciyarsa Na tunani d'aura ruwan zafin sai yaji motsi a bayansa.
Waigawa yay da mamakin wanene?.
Maimuna dake bayansa tsaye ta saki murmushin basarwa tana fad'in “Yaya Aliyu ina kwana? mikake buk'ata ne?”.
Batare da yayi magana ba ya nuna mata filas d'in daya ajiye.
K'arasowa tayi ciki kicin d'in “Kaje Yaya bara Na dafa maka, asaka kayan k'amshi”.
“Eh ki saka, amma miya hanaki zuwa makaranta?”.
“Uhm... Uhm wlhy Yaya ciwon.......”
Saikuma tayi shiru ta kasa k'arawa.
Kad'an ya kalleta ya d'auke kansa, can k'asan mak'oshi yace, “Ba dole kuyi ciwon maraba kullum kunacin zak'i, yakamata kafin sati d'aya da zuwan jini ku ringa d'agama duk wani Abu mai zak'i k'afa, Ku kuma yawaita amfani da ruwan zafi yayin da yazo....”
Yana gama fad'a ya wuce abinsa tamkar bashi yayi maganarba. Ita kanta Maimuna da kallo ta bishi baki bud'e, sum-sum dashi sai zaro magana, komai girmanta babu ruwansa shi, to ita yaushema tace masa ciwon mara takeyi? “Kai Yaya Aliyun nan ni wlhy harma yaban kunya, a inama yasan Mata na ciwon Mara dalilin period🙈?”. Ta k'are maganar da rufe ido.
Shikam gogan naku ko'a jikinsa, hankalinsa kwance ya koma 6angarensu yashiga wanka.
Koda Maimuna tagama dafa ruwan batai gigin d'auka takai masaba, a kicin d'in ta barsa, dan basa Shiga sashen samarin gidan kwata-kwata.
Koda ya fito saiya koma cikin gida ya d'akko filas d'insa, yana shirin fita Maimuna ta shigo kicin d'in hannunta d'auke da kula madaidaiciya.
Kanta a k'asa tace, “yaya gashi inji iya”..
Baice komaiba, yadai mik'a hannu ya amsa yay ficewarsa, saida yafita sosai sannan yace, “kice Mata nagode”.
Maimuna ta girgiza kai tana fad'in “ALLAH ya k'yauta, shidai kullum baki 6am, idan kaji yana dogon bayani sai a tafseer ko k'arin karatu kokuma shida Malam”.
bakuma dan baya maganarba, danshi ba miskili baneba, kawai dai fahimtace bataiba, dan itad'ince baya sakewa da ita, dadukma macenda ba muharramarsa ba, muharamman nasama taka tsantsan yake dasu, sannan shi ba'a surutun banza dashi Mara ma'ana.
Baimasan tanaiba, dan shi tuni yaje d'akinsa. Tea ya had'a babu madara, sai wasu abubuwa daya zuba wad'anda suka saka turirin shayin fita da wani k'amshi mai dad'i da saka kwad'ayin shan shayin. Saida ya bud'e kular da Maimuna ta bashi yaga fankasune sai miya a robar kular tanata tashin k'amshi, maidawa yayi ya rufe, saida ya shanye shayinsa daya had'a sannan yafara cin fankasun a tsanake.
Bayan kammala cin abincinsa daduk wani uzirinsa yay shiri cikin shadda ruwan makuba mai duhu, d'as taimasa k'yau daka gansa kaga cikakken d'an Arewa, yad'au hularsa Zanna bukar kalar shaddar ya saka. Kafin kace me d'akin ya gauraye da wani mayatacen k'amshi mai sanyaya zuciya da sakata nishad'i.
Tunda ya fito aketa gaishesa a k'ofar gidan, yayinda shikuma yake gaida dattijan da suka girmesa, tuni wani saurayi yazo ya kar6i littatafan hannunsa, agogonsa ya kalla, dan yanason shiga wajen malam kafin ya wuce inda zaije, ganin sha d'aya saura saiya nufi cikin soron, dan yasan malam ya fito yanzu, a zauren farko ya iskeshi shida wasu mutane guda biyu a rukunin kujerun da'aka shirya tamkar falo acan gefen soron kasancewar babba, annan malam ke karatu da d'alibansa dakuma ganawa da b'aki.
Sallamar Aliyu ya sakasu amsawa a tare suka juyo suna kallansa, ya cire takalminsa a gefen kafet d'in kafin yak'arasa shiga rukunin kujerun, hannu ya mik'ama bak'in malam sukayi musabaha, sannan yaje gaban malam ya risina yana gaisheshi cikin mik'a masa hannu sukai musabaha (malam bai amince d'ansa yak'i samun ladan musabaha da shiba, shiyyasa kozai gaisa da yaransa suma yakanyi musabaha dasu tamkar kowa, hakama matansa).
“Ya ciwon kan Ali?”.
“Alhmdllh baba”. Aliyu yafad'a yana d'an murmushi kafin ya kuma fad'in “Babu wani Abu da za'ai maka? Zanje wajen Mustafa ne”.
“Eh to kaje abinka harma ka dawo, dan akwai bak'in da zasuzo inason ka gana dasu”.
“To bara kawai nabari saisunzo d'in, daga baya naje wajen Mustafan”.
“A'a kaje abinka kawai, dan sai k'arfe hud'u mukai dasu, nikuma akwai inda nakeson zuwa a wannan lokacin, shiyyasa nace musu zasu gana da kai”. Malam ya k'are maganar da mik'ama Aliyu key d'in motarsa.
Hannu biyu Aliyu yasa ya kar6a yana godiya kafin ya mik'e yay musu sallama. Yana k'aunar mahaifinsa sosai, akoda yaushe cikin kulawa dasu yake, haka yake masa inhar zaifita inda yazama saiya hau abin hawa, saiya d'auki makullin motarsa ya basa, saboda shi yama kasa sayen motar, dukda Alhamdllh gwargwadon hali yanada y'an kud'insa dazai iya sayen koda k'aramace dai-dai k'arfinsa, to amma akwai abinda ya dakatar dashi daga sayen tukunna.
Da wannan tunanin ya k'arasa inda motar malam take ya bud'e, yayinda Wanda ya kar6a littatafansa sanda ya fito yamatso jikin motar shima ya saka masa a gefen mai zaman banza.
Cikin murmushi Malam Aliyu yace, “Jazakhallahu khairan kamaludden”.
“Amin malam”. Kamal ya fad'a yana washe baki da rufema malam Aliyu k'ofar.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tunda Jiddah ta iso k'ofar gidansu bayan mai napep ya ajiyeta taga babu motar Abbansu sai farin ciki ya kamata, ta sauke ajiyar zuciya tana nufar shiga, da sauri ta dawo baya danta manta batayi addu'ar shiga gidabama (Kai jiddo😂).
A yanda ta shigo cikin farin ciki saiya saka Umma dake kwashe dambu a kula murmushi, “Kuluwa ko anyo mana samune yau?”.
Dariya Jiddah tayi tana fad'in “Umma mikika gani?”,
“Naganki cikin farin cikine ai, nasani ko suruki aka samowa yahaya”.
Da hanzari Jiddah ta shige d'akinsu tana dariya. Umma ma dariyar takeyi tanajin dad'in ganin d'iyar tata cikin farinciki akasin sanda suka fita. Kira ta k'walama Jiddah.
Jiddah ta ida cire hijjabinta sannan ta fito.
“Haba yarinya, kinga ina dambu koma kimin sannu”. ‘Umma ta k'are maganar dad'an harar Jiddah.
Hannu Jiddah tasa a baki tana dariya kafin tace, “O Umman mu kad'ai, ALLAH kece kika bani kunya, amma nasoyin magana, gaskiya yau zamuci dad'inmu, ALLAH ya tsumbula Ummanmu a aljanna”.
Umma tace, “Amin Jiddah, tare daku gaba d'aya”.
“Amma Umma wlhy kinmayi saurin aikin”.
“Kinsan Dauda idan ya saka kansa babu wasa, dandanan saigashi yayomin 6arjin, sandama yahay yazo gidannan harna had'a wuta”.
“Eh dama yacemin zaizo, dan can naje saida lokacin makaranta yayi na wuce, Humm Umma kinsan yau miya faru a makaranta?”.
“Inafa Zan sani, sai zubomin zance, amma tsaya Na dawo”.
Cikin Dariya Jiddah tace, “O Umma bafa wani Abu bane, naga kin d'aukeshi da girma”.
“Eh naji d'in ba komai”. Umma dake k'ok'arin shiga bayi ta fad'a.
A hankali Jiddah ta furta “Ina sonki Umma har cikin kowanne numfashina”. (jiddo Abba fa?🤭😝).
Bayan fitowar Umma itama fitsari taje tayo sannan tazo tabama Umma labarin abinda yafaru a makaranta.
Umma tace, “to ALLAH ya bama mai rabo sa'a”.
Cikin shagwa6a Jiddah tace, “Kai Umma, kice ALLAH yabama Jiddanki sa'a saikice mai rabo”.
Ha6a Umma ta rik'e tana kallonta, “Yo inbanda abinki Jiddah suma sauran ai y'ay'anane, miyasa Zan wareki namiki addu'a ban had'a da suba, kamar yanda idan kinci zanyi farinciki haka suma iyayensu, duk wanda kuma yay nasara a cikinku nasarar musulincice da mu ko”.
“E gaskiyane Umma, shiyyasa kullum nake k'ara sonki, dan bakida sonkai balle Hassada ko kad'an”.
Dariya Umma tayi. Tace,
“Kinga Zubaida tashi ki soya mana mai, yanzu zakiga su auta sun dawo faran-faran da yunwa”.
“Wlhy kuwa Umma, ballema yau Zarah bawani abin kirki taciba saboda anyi mak'iyinta fanke”.
“kinga kuwa ni nama manta batason fanke, ai danace tazo ta d'ebi biredin wajen Nafisa”.
”Aiko dai wlhy Umma”.
Jiddah na gama suyar mai sagasu Zarah, duk a d'arare suka shigo, amma ganin Jiddah da Umma Na dariya sai sukaji sanyi, sunsan dai Abba baya gidan kenan.
Jiddah tai saurin Fad'in “Albishirinku kwailolin Umma”.
“Goro suka fad'a a tare”.
“Humm kunsan mi Umma ta dafa mana yau?”.
Kai suka shiga girgiza Mata.
A hankali Jiddah tace, “Dambu”.
Wani ihun murna sukasa suna kwaso rawar shoki. Mi Umma da Jiddah zasuyi inba dariyaba, Zarah da Walida sukaje sukaima Umma kiss a hannu.
Dak'k'uwa taimusu tana fad'in “k'aniyarku wannan shaid'ancin fa?”.
Dariya suka hau yima Umma.
Bayan sun kimtsa aka zauna cin dambu kowa cikin zumud'insa, yayinda Dauda yazo ya kar6a Na Uncle yahaya da Umma ta zuba masa tace yaje yakaimasa gida yazo ya kar6a nasa shima.
Su Walida anacin dambu Ana santi amma bana surutuba.
Daka gansu zaka fahimci farincikinsu yadawo sa6anin jiya daya 6ace 6at................✍🏻
🚶🏻♀🧳kowa ya shirya gobe zamuje gidan Abba zakari hutun k'arshen mako🤣⛹♀😝
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_________________________
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
Duk mai buk'atar jin raina Kama a audio zai iya bin wannan link Na Abban dausayi YouTube channel😄🥰🤝🏻.
_________________________
*_[8......]_*
..............Zancen yarinyarnan data turoma malam Aliyu sak'o yata damunsa a rai da zuciya, dan haka ya buk'aci tabashi address Na inda suke.
Batayi musuba ta turo masa suna cikin Kaduna ne.
Washe Gari ya sanarma malam yanda sukayi. Kai tsaye malam yabashi Umarnin shiryawa suje shida Mahmud (kaninsa) da mustafa.
A washe garin wannan ranar suka shirya domin cika umarnin malam.
Bayan sun Isa kaduna masauki suka fara samu gidan babban malaminnan Sheirk Haruna bala, sanin zuwansu da yayi yaymusu tarba mai k'yau da mutuntawa, dan malam Abdul-ra'uff amininsane sosai. A ranar kam basu bar malam Aliyu ba, dukda gajiyar daya kwaso da daddare bayan isha'i saida ya gudanar musu da lecture Mai taken *_ILIMI DA RAYUWA ABOKAN TAFIYA_*.
Washe Gari kusan misalin goma na safe ya nema yarinyar da sukazo dominta, dan yanaso a gobe su juyo Gidane.
Da taimakonta suka iso gidan nasu, gidane babba badai can sosaiba, amma komai a tsare.
Afrah yarinyar data turama malam sak'oce ta fito tarbarsu, k'yak'yk'yawace a fuska kam sosai, sannan akwai Fari amma irin na kanti, sanye take da hijjab iya gwiwa dan haka su malam basuda damar tantance shigarta, dukdama kallo d'aya sukai Mata kowa ya d'auke kansa, ita kanta cike take da kunyar ganinsu, dan haka kanta a k'asa tabasu umarnin shiga falon Abbansu da k'ofar take a harabar gidan.
Bayan duk sun zauna ta fita, shidai malam Aliyu yana mamakin da tsarkake sunan ALLAH akan wannan hargitsatstsen al'amari.
Kusan mintunanta goma da fita saigata tadawo itada wata dattijuwa d'auke da tirirrika, sudai su malam basuce komaiba, fita ta kumayi kafin mintuna kad'an ta sake dawowa ita kad'ai d'auke da wani tiren, bayan ta ajiye ta gaidasu.
Duk amsawa sukayi.
Kanta a k'asa tace, “Malam kuyi hak'uri Dady bai dawo aiki baneba, amma yana hanya, dan yasan da zuwanku, dukda dai ban sanar masa ainahin abinda ya kawokuba”.
“Masha ALLAH”. malam Mustafa ya fad'a.
Malam Muhmud shima yace, “babu damuwa, ALLAH ya maidoshi lafiya”.
Malam Aliyu dai baiyi maganaba, dan k'ok'arin amsa kiran da akai masa a waya yakeyi.
Mik'ewa tayi tana rok'onsu dan ALLAH suci abincin.
Zaman kusan mintuna talatin saiga Dadynsu Afrah ya shigo falon da sallama, da alama ma yadawo tuni, saida ya kimtsa ma sannan ya fito.
Daka gansa kaga cikakken d'an boko kam, dan sanye yakema da wando tree quarter da T-shirt Mara nauyi, hannunsa rik'e da wayoyinsa, a hasashe zai iya kaiwa shekaru 60, Afrah Na matuk'ar Kama dashi, kawai dai shi bak'ine, itako tayi fari (amma na kanti😝 ). Tarba ta mutunci yayma su malam Aliyu tankar ya sansu, dan sunkula mutumne Mai yawan fara'a.
Fuskarsa d'auke da murmushi yake fad'in “Lallai nazama Mai sa'a da farin ciki, yau sheirk Aliyu bin Andul-ra'uff maina ne da kansa a gidan, dukda bansan mike tafe dakuba ina muku lale marhabun, amma tabbas nayi mamaki sosai da wannan zunwan, tun jiya da Afrah ta sanarmin abin yak'i barin raina, harma Na tsareta da tambayar ina ta San babban mutum irinka? Dahar zaizo gidannan?”.
Murmushi su Aliyu duk sukayi, kafin Aliyu yad'anyi gyaran murya, cikin sanyinsa da nutsuwa irinta masu ilimi yace, “Alhaji inafa manya, har gobe mu d'aliban ilimine, abinda ya kawomu kuwa gaskiya babban al'amarine Dani kaina yahana zuciyata da ayyukana sukuni, ina ganin har saina sauke kayan dake kainane Zan sami nutsuwa. Da farko dai tabbas nayi mamaki da kokwanto akan abindama ya kawonin, saboda ganin karanci da mutuncinka, saidai banida wani hurumi na k'in gaskatawar tunda nasamu zancen ne daga amintacciyarku”.
Kai Dady ya jinjina, sannan ya gyara zama yana kuma damk'e kofin lemon hannunsa, “malam maganganunka sun sakani a duhu matuk'a, amma Zan kwantar da hankalina domin k'ara fahimtarsu daga gareka”.
“Masha ALLAH, Alhamdllh Alhaji, mun gode da wannan karamci, da farkodai in babu damuwa ina son ganin dukkan iyalanka anan tare damu, wannan ne zai bamu damar fahimtar abinda ya taramun”.
“To shikenan babu damuwa, Nawwas ne dama kawai baya gida, amma nasan ya dawo insha ALLAH” duk kiran wayoyinsu yayi d'aya bayan d'aya, acikinsu Afrah ce kawai a tsorace, amma Nawwas da Namrah duk basusan ma'anar kiranba.
A yanda Nawwas da Namrah da mahaifiyarsu kawai suka shigo ya isa Fara gaskata zancen Afrah. Gaisuwa ma ta sifirin a kaima su malam🤣.
Dan Hajia Mansura ma tana taunar cigam ta shigo, dukda dai cin masu aji ake masa bana karuwaiba, Afrah ce kawai a k'asa zaune, amma Nawwas da Namrah duk a kujera suka zauna kusama da juna, hannun Nawwas akan Na Namrah wadda ke sanye da wando da Riga masu bin jiki, sai siririn mayafi data yano, shima saida mamansu Tamata magana, kanta yaci uban kitson gashin doki, daka gantadai kaga wayayyun wannan zamanin. Shiko Nawwas wandone irin Na babansa iya gwiwa, sai singlet ruwan d'orawa, askin kansa abun takaici da kuka ga al'ummar musulmai, dan an saisaye gefe da gefe da k'eya, anbar gashin iya tsakkiyar kai sannan akai masa k'itso kalba (Dada) daga kasan gashin bak'i, sama kuma k'arshen kitson Brown.
Duk a cikin mintuna kad'am su Malam Aliyu suka nazarcesu.
Dady yace, “Malam ga iyalin mawa, d'ayane babu a ciki autansu, yana jami'ar legas yana karatu, kwannan ma yatafi, wannan itace matata mahaifiyar yarana, sai babban Nawwas mai shekaru 27 a duniya, yagama p.h.d d'insa, watansa shidda kenan, yanzu haka yana aikinsa. Sai Afrah, tagama degree d'inta itama kwannan, muna mata shirin zuwa masters, sai Namrah tana jami'a tanan jos L200 yanzu”.
Masha ALLAH su malam Aliyu suka fad'a a tare, da d'orawa da addu'ar fatan alkairi.
Daga Nana malam Aliyu ya d'ora da fad'in “Dalilin zuwanmu nan gidan shine yarinyarka Afrah”. Atare suka kalli Afrah da kanta ke a k'asa. Malam Aliyu yacigaba da fad'in “Wani sak'o daya kasa barin zuciyata ta turamin, harma naji nakasa hak'uri saina dangane da wannan family, Afrah indai ban shiga huruminki ba inason ki kuma maimaita abinda kika turamin domin Na tabbatar”.
Hawayen dake d'iga a kumatunta ta share, kafin tace, “Dady da mah-mah Ku gafarceni, yau Zan bud'e sirrin daku baku saniba, saidai har a yanzu ina tambayar kaina Sakacinku ne kokuwa ak'idar boko ce? Da wautar barin tarbiyyar addinin islama?. Har yanzu zuciyata ta Gaza amsamin tambayar, amma ban saniba ko idan Na fad'a yanzu amsar zata fito”.
Ba k'aramin fad'uwa gaban Nawwas yayiba, dukda baisan mi Afrah zata fad'aba yaji ya tsargu. Mik'ewa yay niyyar yi amma dad ya tsaidashi da Ido, dole ya koma ya zauna yana wani kumbura baki.
Afrah takuma fashewa da kuka sannan tafara jawabi dalla-dalla kamar yanda taima malam Aliyu a sak'o, harma ta k'ara da abinda bata sanar masaba.
Gaba d'aya falon jikin kowa ya mutu murus, Dady da mah-mah ma jikinsu rawa yakeyi, hakama Namrah datayi wani tsalle zuwa k'asa saboda tsorata, bata ta6a zaton wani mahaluki yasan suna tarayya da Nawwas ba, sannan bata ta6a zargin yanayin abinda yakeyi da ita da Afrah ba.
Gani kawai sukayi Dady ya kifo k'asa, Mah-mah ma data mik'e domin zuwa garesa saita yanke jiki ta fad'i. Nawwas kam dukya rikice, yarasa ina zashi ya 6uya saboda kunya da tsantsar tashin hankali.
A tsorace su malam Aliyu duk sukayo kan Dady, yayinda Afrah tayi kan mah-mah d'insu.
*bayan awa biyu* su Dady suka dawo a hayyacinsu, saboda kiran likitansu da Namrah tayi, annan yake sanarda jininsu ne yahau sakamakon jin abinda ya tsoratasu.
Bayan tafiyar doctor da nitsawar komai, malam Aliyu yafara magana a matuk'ar sanyaye da k'unar zuciya. Ya Fara dajan ayoyin alkur'ani da hadisai, sannan ya d'ora da nasiha Mai girgiza zuciya.
“Wlhy iyaye Ku farka😭, karku d'auki wancan zancen matsayin labarin littafi kawai, wannan fitinace data shigo acikin wannan al'ummar, Uba kaga yana Neman y'ay'ansa, Uwa ta nemi d'anta ko abokin d'anta, ko abokin mijinta, ko makwafcinsu, Yaya da k'annensa suringa Neman junansu, Yaya da kanwa su ringa aikata mad'igo, ko Matar uba da y'ay'an miji😭, aboki yaringa zina da d'iyar abokinsa, k'anin uwa ya ringa zina da Y'ar k'anwarsa ko yayarsa, k'anin Uba yana zina da y'ay'an d'an uwansa, shin dan ALLAH wad'anne irin al'umma muke son zamane? Anya kuwa muna tsoron mutuwa da kwanciyar kabari da hisabi? Muna tuna duniya tak'aitaciyace? Innalillahi wa inna'ilairaji'un, wlhy kaiconmu da toshewar imani dana zuciya😭, k'iri-k'iri munason barin dokokin addininmu muna aro Na yahudanci da tsantsar tsagwaron kafirci a matsayin wayewa, *MUTUM DA DUNIYAR, y'an uwana YA DACE MU GYARA KANMMU* dai tunkan lokaci ya k'ure mana, wlhy tunkan muga kayinmu cikin WUTAR JAHANNAMA mu farka daga wannan barcin asarar, duk yanda muke kallon mutuwa a nesa damu saitazo garemu, domin a kullum k'ara kusantomu take a kowacce safiya, mimuka tanada mikuma zamu tarrar?”.
Malam ya k'are maganar hawaye Na cika idonsa, malam mustafa da malam Mahmud Kansu jikinsu Yakuma yin sanyi lis da maganar malam Aliyu.
Kafin kacemi kuka ya 6alle a tsakanin wannan ahali, kowannensu yana kaico da koyi da al'adar yahudanci da barin tafarkin addininsu bisaga rud'in duniya da wayewa Mara amfanii a duniya da lahira. Duk Wanda ya kallesu saisun bashi matuk'ar tausayi. Har kusan magrib su malam Aliyu Na gidan, saida sukaga komai ya natsa sannan suka wuce, sukabar wannan ahali cikin tsantsar rud'ani da nadama.
Gaba d'aya da zazza6i Malam Aliyu ya kwana a ranar, washe garima haka suka tafi kano baida lafiya, koda suka dawo har k'arin ruwa yasha, saboda azababben ciwon kai da damuwa sun kasa barin zuciyarsa, komai kallonsa yake tamkar ba gaske ba ma. Amma dole zuciyarsa ta tilasta masa gaskatawa tunda yaje yaga zahiri.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai da jarabawar su Jiddah takai kwanaki hud'u sannan sakamako ya fito. Cikin amincin Ubangiji Jiddah taci ita da Mariya Ibrahim wata y'ar ajin, sosai suka shiga farinciki da wannan nasara, nanfa y'an aji suka shiga tayasu, dukda zukatan wasu babu dad'i akan rashin nasarar.
Da tsantsar farin ciki Jiddah ta iso gida, ta kanand'e Umma dake shanya kayan da take wanki.
“An dace kenan?”.
Umma tafad'a tana dariya bayan ta juyo ta kalli Jiddah dake mak'ale da ita.
“Alhmadllh Umman mu naci wlhy, kai ina cikin farin ciki”.
“Alhmdllh Jiddon Uncle, ALLAH ya sanya albarka da nasara tagaba”.
“Amin Ummana”.
Su Zarah na shigowa gida Umma ta taresu da wannan farin ciki suma, tuni sun kaure da murna suna k'ara yima yayar tasu adduar nasara. Itama Aunty Nafisa suka takura saida Umma ta kurata ta gumtsa Mata. Sosai tayi farinciki itama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau gaba d'aya Malam Aliyu a busy yake, saboda tafiyar da tazo masa babu shiri, dukda dama yasan da tafiyar, amma bai tsammaceta cikin wannan watanba.
Muhimmancin abinda zashiyine ya sakashi shiryawa babu wata damuwa da zuwan tafiyar a yanayin rashin shiri. Ko d'alibansa bada kowa ya samu damar yin sallamaba, sai sak'on ban hak'uri daya barmusu, da d'ora malam Mustafa matsayin Wanda zai cigaba da yimusu karatu harya dawo tafiyarsa ta watanni uku zuwa hud'u insha ALLAH.
Cikin gida ya Shiga yayma matan Malam sallama, y'an uwansa kuma dukya kirasu ta waya musamman Ruk'ayya da Siyama daya dad'e yana waya dasu domin yin sallama, yaso su had'u kafin ya wuce, amma ina lokaci yariga da ya k'ure sosai.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
“Haba hindu, fushinnan ya isa haka mana, tunda kika dawo kink'i saurarena, minene amfanin dawo da abinda akayi ya wuce, kuma nabaki hak'uri”.
Shiru tayi tamkar bata jisaba, tacigaba dacin abincinta, shiko ya k'ura Mata ido yana juya nasa cokalin akan filet.
A haka su Hussain suka fito suka samesu, kowanne kujerar Dani d'in yaja ya zauna, ko sallama basuyima iyayen nasuba.
Kalifa daya zauna kusada Abba ya kallesa yana fad'in “Abba wai sai yaushe zaka cikamin alk'awarina?, ALLAH wayarnan bana sonta, Su Faisal duk an canja musu ni bandani, harma kunyar zuwa school nake da wayata”.
Murmushi Abba yayi ya shafa kan kalifa, “Haba babana ka kwantar min da hankalinka mana, aina fad'a maka Zan sake maka, yanzu wasu abubuwane suka d'an tushemin, amma kabani nanda k'arshen watannan insha ALLAH taka wayarma duksai tafi tasu, dan nayima Nabel magana ma ya za6o maka mai k'yau”.
Washe hak'wara kalifa yayi yana rungume Abba da fad'in “Kana birgrni Abbana......”
“Abbanmu dai”. Cewar Hassan cikin jin haushi.
Kallonsa Hajia hindatu da Abba sukayi, yayinda kalifa ke antaya masa harara kafin yaja tsaki da fad'in “Jealousy”.
Hassan ya ta6e baki shima yana hararar kalifan “Jealaus d'in Ubanmi za'a maka, gaskiya Abba muma ka siya mana phones, nidai nafasa sai munkai js3 d'inma, ai gashi Aisar nan suna dashi”.
Hajia Hindu dake dariya tace, “Y'an biyun Abba da gaske dai kishin kukeyi da babban Yaya”.
“ALLAH ya kiyaye wlhy Mom, kibarma hura masa wannan k'aton kan nasa”.
“Kai dan Uwarka waye mai k'aton kan?”. Kalifa ya fad'a a fusace yana mik'ewa zai kaima Hussain dayay maganar duka. Amma sai Abba yay nasarar tarewa.
“Haba yaran Abba minene abin fad'a anan, ya Isa haka to abar maganar, kowa za'a saya masa indai wayace. Kai Auta mikake buk'ata?”. ‘Abba ya k'are maganar da kallon Munner daketa kallonsu kawai’.
“Abba ni sonake ka siyamin motar da muka gani ni da mom ranar, nace ta sayamin saitace kud'inta bazai kaiba”.
Jinjina kai Abba yayi yana maida kallonsa ga Hajia Hindu. Da ido tai masa alamar anyi haka.
Murmushi yayi, “To Auta mom zata rakani na saya maka insha ALLAH”.
Sosai Munner yake murna shima.
Haka dai suka cigaba dacin abincin kaya-kaya tamkar wasu kaji. Bayan sun gama kowa ya kama gabansa.
Sayayyar da Abba yay alk'awarin yimasu Munner ce ta saka hajia Hindu sauka daga fishinta Na kwananda Abba yaje yayi a gidan Umma. Dan suna shiga d'aki ta rungumeshi.
Sosai yaji dad'in, shiyyasa ya kudiri aniyar kokartawa ya siya musu duk abinda ya alk'awarta musu..................✍🏻
(Humm🚶🏻♀😏).
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[9......]_*
...........Alhamdulillah komai ya kankama Na shirin tafiya taron su Jiddah, Wanda Abba baimasan anayiba, sai Ana gobe tafiyarne Uncle yahaya ya kirashi ya sanar masa.
Masifa yaytayi akan shifa bayason gantali, yagaji da yawon da Jiddah take zuwa Ana fakewa da addini, yarinya balaggiya ce zata tafi har wata uwa duniya Abuja, to bai aminceba.
Banza Uncle yahaya yamasa, daga k'arshema ya yanke wayar, koda yaje gidansu Jiddah da daddare cemusu yay kawai Abban ya amince.
Sosai Jiddah taji dad'i, dan dama gobene tafiyar tasu, duk abinda yadace Uba yayi Uncle yahaya ne yaje makarantarsu yay Mata, (dama idan irin haka ta taso shine ke musu, bama sabi takan Abba).
Tun a Daren ranar suka farajin kewar juna itada su Zarah, kad'an-kad'an saisuce gobe iyanzu kuna Abuja Yaya Jiddah, wlhy zamuyi kewarki”.
Umma da ita kanta takejin babu dad'i tai dariya, “to in banda abinki walida yaune tafara tafiya? Kuma wataranfa gidanma aure duk zaku tafi, baga Nafisa ba kamar bata zaunaba”.
Duk kasa magana sukai, sai hawaye dake zirara a kumatun kowaccensu, duk sanda Umma zatai musu zancen tafiya gidan aure duk saisu shiga damuwa, tunaninsu tayaya xasu rabu da juna? Tayaya zasu barta ita kad'ai?.
Umma ta ta6e baki tana fad'in “Tofa, ta6arar tazo? To kunga bara nayi nan ALLAH ya bamu alkairi”.
Umma ta shige d'aki abunta, tana shiga itama ta share hawayen da suka mak'ale mata cikin ido. (😫aure yak'in Mata).
Suma bayan sun gama shashshare hawayensu suka tashi daga tabarmar suna kaye-kayen tsakar gida kafin su shige d'akinsu. Acan d'inma babu mai magana, jikinsu duk a sanyaye sukai shirin barci, kowacce ta kwanta da tunanin. (🤣zakuyi bayani indai aurene).
Abubuwa da yawa ke saka su Jiddah kuka idan suka tuna zasuyi sure. Na farko rabuwa da juna da kuma Ummansu farin cikinsu. Na biyu wane irin miji zasuci karo dashi? Mai irin halin Abbansu ne kokuwa Wanda yafi nashi muni? Na uku tayaya Ummansu zataji dad'in rayuwa babusu a kusa? Tunda suka tashi sune take gani taji dad'i, k'aunar da take musuce tasakata hak'urin zama da mahaifinsu dukda munin halinsa da rashin k'aunar da yake nuna musu da ita kanta, to ta Yaya bazasu damuba a yayin da suka tuna zasu tafi su barta cikin kad'aici bayan ita ta zauna danta gusar da nasu kad'aicin a lokacin da suke matuk'ar buk'atarta.
Haka kowaccensu taita sak'awa da kwancewa har dare yay nisa, ganin sun kasa barci Jiddah tace su tashi suje suyi alwala suzo suyi salla.
Wannan shawarar sukabi, suka fito domin d'aura alwala, Umma dake sallar itama duk tana jiyo motsinsu. Godiya taima ALLAH daya bata y'ay'a irinsu Jiddah, dama akance Ubangiji baya had'ama bawa zafi biyu, idan ta k'untata wajen mahaifinsu saitaji sauk'i da farinciki a garesu, itako tayaya zata jahilci ni'imar Ubangiji buwayi gagara misali, shima dayake a cikin duhun kai ALLAH ya ganar dashi gaskiya.
★★★★
Washe gari duk sukuku suka tashi, gashi ranar lahadice babu makaranta, haka dai suka taimakawa jiddah ta shirya kayanta kala biyu sai Uniforms d'inta kala buyi suma (tafiyar ta kwana uku ce kacal, ko hud'u).
Bayan sun gama Karin kumallo Uncle yahaya ya iso, dan tare zasu tafi, k'a'idar makarantar su Jiddah ce inhar tafiya irin wannan ta Kama saida muharraminka, basu yarda tafiya iya malamai da d'alibaiba, kowacce zatazo da muharraminta ne aje dashi, sauk'insu ma koda tafiya ta Kama ta k'etare to lallai makwaftan Najeriyane irinsu Cameroon, Niger dadai sauransu, mafi yawanci kuma duk tafiyace ta mota balle ace babu kud'in biyan jirgi.
Har makaranta Zarah da Walida saukai mata rakkiya, sun iske malam mustafa da malam Bilal (kanin M. Aliyu) sai malam mika'il da sauran d'aliban da za'ayi tafiyar suma da y'an rakkiyarsu. Basu wani 6ata lokaciba suka shiga motar da za ayi tafiyar.
Har suka fice su Walida basubar d'agama Jiddah da Uncle yahaya hannuba, itama Jiddah Na d'aga musu, yayinda Uncle yahaya suke k'ara birgeshi da k'arajin k'aunar yaran, dan tarbiyyarsu da zumincinsu Na birgeshi, sosai yayarda da maganar man ta bahaushe dayake cewa mace itace ginshik'in zuminci, dan inhar babu ita saikaga kan y'ay'anka kowanne da inda yayi.
Wannan shine zuwan Jiddah Abuja Na uku, dan haka bata wani damu da 6ata lokaci wajen kallon hanyaba, hasalima ramuwar barci tashigayi, sa6anin abokan tafiyar tata dake hira a hankali, su Uncle yahaya dasu malam mustafa ma hirarsu sukeyi wadda ta danganci rikicin rayuwa da ta'addancin dake faruwa a duniya kullum Ana cewa musulmaine.
Sun Isa Abuja k'arfe uku Na Rana, dan kokad'an basuyi guduba, tafiya sukai a tsanake babu wani cida zuci, sun tsaya a Kaduna masunyi salla, sunkuma dad'e kusan Awa d'aya da wani Abu.
Tuni Jiddah ta tashi, dukda ba hira takeba tana sauraren hirar ta 6angarori biyu, y'an uwanta d'alibai da malamsu da iyayensu.
Sun Isa Babbar makaranta ta Arabic da akeji da ita a ciki da wajen Nageriya, dan akwai d'alibai cikinta harda Na k'etare, sannan ta had'a k'abilu daban-daban. Makarantace da duniyar ilimin addinin Islam keji da ita matuk'a, dan duk Wanda yaje nan lallai yakai abin kallo da tutiya ga al'ummar musulmai, makarantace tundaga nursery har zuwa University, guda biyuce makarantar, ta mata ce a farkon shiga layin, sai ta maza acan k'arshe wanda nisansu yakai zaka iya hawa mashinma, babu yanda za'ayi namiji ya shigo sashen mata, hakama mata basuda hurumin shiga sashen maza, akwai tsaro sosai a makarantun mai ban sha'awa da tutiya ga al'ummar musulmi. wani taro dasu jiddah sukazo a makarantar suka sauka, amma lokacin anma d'alibai Hutu, sai y'an manyan kawai suka tarar y'an jami'a, amma wannan Karon d'alibai Na nan.
Bayan y'an wasu abubuwa da suka gudana aka kai su Jiddah masaukinsu a cikin hostel. Tarba suka samu ta mutunci ga d'alibai y'an uwansu, sai kaf-kaf akeyi dasu. Hakama sauran d'aliban da suka halarci taron daga k'asashe daban-daban.
Dukda wad'annan abubuwan hankalin Jiddah naga tunanin Ummanta da y'an uwanta, kad'an-kad'an saita ayyana “komi sukeyi yanzu?”. a zuciyarta.
Yawan murmushinta yasaka wata d'aliba Mai suna kemi tambayarta cikin harshen larabci, (dan yoroba ce, bakuma tajin Hausa, ita kuma jiddah bajin turanci takeba sai tsinta-tsinta da ake koya musu a makaranta dakuma Wanda y'an uwanta ke koya mata).
Murmushi Jiddah tai Mata, kafin tace, “babu komai”.
Badan kemi ta yardaba tabarta.
Ranar dai haka suka kwana cikin d'alibai, inda da daddare aka gudanar da lecture mai ta6a zuciya da ruhi, wadda aka sakama suna *_TARBIYYAR MUSULMAI A YAU!!_*.
sosai wannan lecture ta shigi su jiddah da sauran d'alibai, k'arfe sha d'aya aka tashi kowa ya nufi makwancinsa. Da k'yar jiddah tasamu tayi barci, dan kewar su Zarah ta addabi zuciyarta matuk'a.
Washe garima bayan Sallar Asuba ankuma yimusu lecture, ita kuma Mai taken *_YAYA YAKAMATA MU RAYU A MATSAYIN MUSULMAI?!!_*.
Itama dai tashigi su jiddah sosai, dan har kuka wasunsu sukasha saboda jin kura kurai da al'umar musulmai suke tafkawa a cikin zaman takewar rayuwa, wadda a yanzu mafi yawancinmu bama kare hak'k'ok'i da dokar da addininmu ya sharad'd'anta mana mu rayu, kowa gaban kansa yakeyi da abinda yay maisa a zuciya. (Ya rabbi ka gyaramu muda halayenmu😭🙏🏻).
Sosai ake shiryama zuwan manyan bak'i wannan taro, an gyara k'aton fili da akan gudanar da makamanta wannan taron, mazaunin d'alibai, mazaunin manyan bak'i, Na iyaye, da d'alibai irinsu Jiddah daga kasashe 10 na Africa.
K'arfe kusan 9am su Jiddah suka fito daga hostel, tuni har waje ya d'inke da jama'a, manyan bak'in da aka gayyata duk sun iso.
Malam Abdul-ra'uff Adam Maina yana d'aya daga cikin manya-manyan malamai da akeji dasu a wannan wajen, tun kusan k'arfe takwas na safe ya iso shida tawagarsa, dan haka komai dake gudana a wajen akan idonsune, tundaga fitowar d'alibai da isowar sauran jama'a bak'i.
K'arfe 10 waje ya nutsa, dan mafi yawan wad'anda ake jira sun iso, acikin d'aliban makarantar aka tada wata tafara karatun alkur'ani cikin nutsuwa, tsitt kakeji wajen yayi kowa Na sauraren zazzak'ar muryarta. Bayan itama wata takuma zuwa tayi, daganan wani malami ya kar6a yana jan doguwar addu'a da fatan alkairi ga kowa tareda mik'a gaisuwar barka da zuwa ga manyan bak'i irinsu malam Abdul-ra'uff Wanda shine farkonma ambata.
Komai yana gudanane da harshen larabci. (Da banaji Nima danaga idi, rahoton da bai d'aukuba. 😝😂)
Malam Andul-ra'uff shine Wanda ya fara gufanar da jawabi awajen taron, tareda yima kowa fatan alkairi Na musamman, daganan sauran manyan bak'in daya kamata su tofa nasu suma suka tofa.
Taro yafara gudana bisa jagorancin lectures daga malamai daban-daban da suka fito a sassan k'asashe, kowa da taken tasa lecture d'in mai shiga 6argon jiki.
Su Jiddah dai sunata saurare da d'aukar darussa, lallai wannan taro ya cancanci a kirashi Na *k'arama juna sani* .
Zuwa k'arfe d'aya aka tafi gudanar da sallah dakuma bama bak'i filin cin abinci da hutawa.
Su Jiddah duksun koma hostel domin gudanar da sallar zuhur suma.
Zuwa k'arfe 2 aka daddawo aka d'ora daga inda aka tsaya, akuma wannan lokacinne aka bama su Jiddah dama suma, an Fara kiransune makarantu-makarantu suna gudanar da karatun alkur'ni Mai girma, sannan kowacce abata damar yin bayani akan wani Abu cikin mintuna biyar.
Koda akazo makarantar su Jiddah sai malam mustafa yace Jiddah ta tashi.
Gaba d'aya jikinta rawa yakeyi, dukda ba yaune Karon farko data Fara halartar taro irin wannanba, saidai wannan ya banbanta saboda yawan jama'a, gashi kowa ya zubo mata ido, cikin takunta Na sanyi da nutsuwa ta isa inda ake buk'atar ganinta, kanta a k'asa bata iya kallon kowa saboda ta Saba ko yaushe fuskarta sanye da nikab. Koda ta tsaya agaban microphone d'inma kanta Na a k'asa, tad'anyi shiru Na wasu seconds kafin tayi gyaran murya, ahankali muryarta tafara ratsa lasifikan da ambaton bismillah tashiga karanto suratul Al-anfal.
Bawai dan Jiddah tafi kowacce d'aliba iya karatu bane zata burgeka, a'a nutsuwa wajen karatun da yanda zak'in sautin muryarta ke fita wajen fidda kowanne harafine yasaka zukatan bayin ALLAH nutsuwa, masana Na fassara kowacce aya daki-daki idan ta karanto a zukatansu.
UBANGIJI yaba jiddah matuk'ar murya mai sanyi wajen jan k'ira'ar alkur'ani Mai girma, idan tazo ayar dake gargad'i, saikaji muryarta Na rawa alamar tahowar kuka, har sai tasaka handkerchief d'in hannunta ta share idonta. Dad'in sautin muryar tama ya hana a dakatar da ita, saida takai aya ta 68 sannan malam yasamu damar dakatar da ita, yayinda hawaye masu d'umi suka wanke fudakarta, handkerchief tasa tana tsanewa kanta a k'asa, yayinda shashshekar kukanta ke fita a hankali daga cikin lasifikan.
Guri fa yayi tsit babu Mai kwakwkwaran motsi, dan kukan Jiddah ya raunana zukatan jama'a da yawa, ita kanta batasan miya k'arfafa kukan nataba ma, bayaninma da kowa keyi Na mintuna biyar ita sai hak'ura akai aka barta.
Malam Abdul-ra'uff Kama sai ajiyar zuciya yake saukewa yana k'arabin Jiddah da kallo, yayinda ransa ke hamdala da samun irin wad'annan y'ay'a acikin al'ummar musulmai.
Malamin dake kiran sunayensu yay gyaran murya yana fad'in,
ماشا ، الله ، المعلم ، جدة ، هي الطائفة المسلمة التي يحتاجها المسلمون ، لقد بارك الله حياتك.
أهنئ والديك على الحصول على الوضع الراهن ، وهذا بالنسبة لنا ، في كل مرة تقرأ فيها القرآن وتقرأه بدمك ومعناه وما يتحدث عنه ، بكل طرق الخوف من الله و قوة الإيمان ستكثر أيضا في قلوبنا. كان الأمر كما لو كنا قد سلمنا طفل جدة في رحم طفلها.
“Masha ALLAH malama Jiddah, irinku sune al'ummar musulmi da musulinci ke buk'ata, ALLAH ya albarkaci rayuwarki. ina taya iyayenki farin ciki da samunki matsayin d'iya, wannan wa'azine a garemu, yanada k'yau idan kana karanta alk'ur'ani karingajinsa har cikin jininka, ma'anarsa da abinda yake magana akai, ta wannan hanyarne tsoron ALLAH da k'arfin imani zai kuma yalwatuwa a zukatanmu. kamar dai yanda mukaga malama Jiddah zakari yaro ta tsinci kanta a ciki yanzu”.
“Kuma sauran d'alibanmu ALLAH ya albarkaci rayuwarku gaba d'aya”.
A take wajen ya d'auki kabbara ta d'alibai da ambaton Amin.
Dad'i ya kama Uncle yahaya sosai, sai nanata godiyar ALLAH yake a zuciyarsa, da takaicin d'an uwansa daya gaza fahimtar baiwa da ni'imar da ALLAH yay masa ta samun wad'anan yara.
Jiddah kam wajen zamanta takoma ta zauna tana cigaba da sauke ajiyar zuciya.
Abubuwa masu muhimmanci sun cigaba da gudana har zuwa k'arfe 3:40pm, lokacinne kuma taro ya tashi lafiya, cikeda addu'oi ga d'alibai da iyayensu.
*washe Gari*
Washe gari kam an gudanar da lecture ne, wadda gaba d'ayanta malam Abdul-ra'uff maina ne yayita, sosai tsohon ya birge Jiddah, jitake inama ita jininsace. Bayan kammala lecture d'in malam aka bada k'yauta gasu Jiddah, wadda cikin amincin Ubangiji tasamu babbar k'yauta da saka sunanata a jerin d'alibai uku da za'a tantance su wakilci Nageria musabak'a dazata gudana a k'asar saudia ta y'an shekaru 20 zuwa k'asa.
Wannan Abu bak'aramin farin ciki yasaka malam Abdul-ra'uff maina ba, ganin d'aya daga cikin d'aliban yankinsa kuma yarensa tasamu wannan dama.
Yayinda Jiddah ke gudanar da godiyarta ga ALLAH da jigogin wannan taro sai kuka ya sark'e.
Malam Abdul-ra'uff yay murmushi yana ambatar “sarkin kuka kenan” akan la66ansa, shi kansa malam mustafa murmushi yayi, yayinda uncle yahaya idonsa yacika da hawaye, dan shikam ya fahimci kukan Jiddah da biyune.
Yau kam antashi karfe 1pm, yayinda manyan bak'i sukayi haramar tafiya.
Sukuma su Jiddah sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da rai..............✍🏻
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
Zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel😄👌🏻.
*_Larabawa Idan kunga kuskure alarabcina please azo amin gyara, kar a sakamin Ido nacigaba da tafka kuskure, kai adukama littafin, dan maganar addini tawuce gaban wasa, bilyn taku ajizace tana kuskure, dan Allah Da anga Na sauka alayi ayi azamar tunatar dani🙏🏻😿._*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[10...]_*
..............Baje suke a falo su Kalil Na homework, yayinda Abba ke kallon labarai, hajia Hindu kam Ana zaune gefe ankashe kan d'auri Ana latsa waya da d'ora lemo.
“Lah Abba wannan tana Kama da Jiddahn gidan Umman gwammaja”. Hussain yafad'a idonsa a TV shima.
Ware ido sosai Abba ya kumayi, itama hajia hindu dasu kalifa duk suka kalli TV.
Wata Y'ar zabura Abba yayi dan mamaki, tabbas wannan Jiddah ce y'arsa, wato dayace kartaje saida taje kenan?. Baikai k'arshen tunaninsaba aka wuce rahoton taron dasu Jiddah sukayi.
Hajia Hindu cikin ta6e baki tace, “Itace kuwa Hussain, anje nunamana su masu addinine ko, ai tsoron ALLAH a zuci yake dai”.
Dariya Kalifa yay suna tafawa da Hassan tareda fad'in “Tab d'i, su ustaziya kenan”.
Dariya duk yaran sukayi har hajia Hindu, amma banda Abba da Munner dayay barci. Abba kam ransane a 6ace wai jiddah batabi Umarninsa ba, da ace dare baiyiba da yanzu sai yaje ya saukema Umma ta cikinsa kafin jiddah ta dawo yaci Ubanta.
Humm🚶🏻♀😏.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Umma dai basusan wainar da ake toyawa ba, dansu ba kayan kallon ke garesuba, sai yau da yamma saiga Sadiq da majeed sunzo gidan (yaran uncle yahaya).
Da fara'a Umma ta taresu, hakama su Jiddah, walida da Sadiq Kansu d'aya, dan shekarunsu kusan d'ayane, dan haka take kiransa Hussain, shikuma yace bai yardaba itace Hussaina shine hassan.
Yauma tanajin sallamarsu da gaida Umma tafito daga d'akinsu tana fad'in “Oyoyo Hussain d'ina”,
Hararta yayi cikin wasa shima yana fad'in “Hassan dai, Umma dan ALLAH ni da ita wanene babba?”.
Dariya Zarah dake wankin Uniforms d'insu ta saka musu, “Umma dan ALLAH yaudai kiraba gardamar gayunnan, kokuma abari sai Yaya Jiddah tadawo sannan”.
Da sauri majeed shima yace, “Eh abari sai Yaya Jiddah tadawo, dan karsu musama, kunga anyi gaban kowa kenan”.
Umma dake dariyarta har yanzu tace, “ALLAH ya shiryaku dai”.
A tare suka amsa da amin Ummanmu.
“Kunsan wane albishirma mukazo fad'a wannan k'anwar tawa ta katse mana hanzari?”.
Umma da Zarah sukace, a'a saika fad'a. Yayinda Walida ta antayama Sadiq harara shima ya rama yana Mata gwalo.
Da sauri Majeed yace, “Umma wlhy an nuna Yaya Jiddah a TV jiya”.
“Dan ALLAH da gaske?”. ‘Zarah tafad'a tana saurin ajiye kayan datake cud'awa a hannunta’.
Umma da walida ma a d'okance sukace da gaske majeed?.
“Wlhy kuwa Umma...........”
Zama sukayi suna basu labari, farin ciki duk ya cika su Umma, harda hawayen dad'i suka cika mata idanu.
Anan su Majeed sukakai har dare, basu tafi gidaba har saida sukaci abinci.
Daga Umma harsu Walida kwana sukai mik'a godiyarsu ga Ubangiji ga wannan nasara da Jiddah tasamu. Fatansu ALLAH ya dawo musu da ita lafiya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tunda malam suka baro Abuja sai yarinya Mai kuka keta masa Kai kawo a zuciya, haka kawai yakejin farinciki da kasantuwarta Y'ar yankinsa kuma yarensa, dad'in dad'awa kuma gashi a makarantarsa take karatu, yana mamakin yama akai bai Santantaba, lallai dolene yayi bincike akan yarinyarnan, dan yana ganin zata dace da tunaninsa.....
Yad'anyi murmushi saboda hangota tana kuka, kokad'an ya Lura kuka baya Mata wahala saikace Aliyunsa. Shima abu kad'an ke tada masa hankali Yakama kuka tamkar wani mace, mutumne shi Mai yawan tausayi.
Malam Yakuma murmushi saboda jin k'arin k'aunar Aliyun Wanda jama'a ke kira magajinsa.
Har suka iso gida da tunanin Jiddah a ransa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A yau k'arfe 12 su Jiddah suka baro cikin Abuja cikeda kewar k'awayensu d'alibai, dakuma murnar nasarar da suka dace da ita acan.
Gaba d'aya Jiddah cikin zumud'in son ganin y'an Uwanta take da Ummanta, saikace wadda ta shekara bata gida.
Sai kusan biyar Na yamma suka iso cikin kano, kaf d'aliban da iyayensu kowanne har gida aka kaishi, su Jiddah sune Na ukun saukewa a k'ofar gidansu.
Yau ko Addu'ar shiga gida bata tsaya yiba ta shiga gida da murna tana kwala kiran sunansu Zarah.
Ummace kawai a gidan, dan haka tafito daga d'aki itama cike da murna.
Jiddah ta ajiye kayan hannunta ta mak'alk'ale Ummansu tana sakin kukan farin ciki. Umma ma cikeda murna taimata kwakkwaran rik'o, a haka Uncle yahaya yashigo ya samesu yana waya. Murmushi kawai yayi yacigaba da amsa wayarsa.
Jiddah da suka saki juna da Umma tafara tambayar “Umma ina y'an uwana?”.
“Yanzu zasu dawo, gidan indo sukaje siyo awara. Yanzu zaki gansunan, d'akkoma babanku tabarma mana ambarsa a tsaye.
'Dakin Umma Jiddah ta shiga ta d'akko tabarma ta shimfid'ama Uncle yahaya da har yanzu yake waya.
Walida da Zarah ne suka shigo da sallama, ganin Jiddah yasakadu ajiye kayan hannunsu suka mak'alk'aleta suna ihun murna. Tuni sun haukata gidan da hayaniya. Umma da Uncle daya gama waya sai dariya suke musu da mamakin wannan soyayya. Saida suka gama murnarsu kafin Umma da Uncle yahya su sami damar gaisawa, suma sukazo suna gaisheshi da masa sannu da zuwa.
Yayinda su Jiddah ke murnarsu Uncle yasami damar yima Umma bayanin komai daya faru, farincikine sosai ya kamata, tama rasa yanda zata musalta, video d'in dayayma Jiddah da waya ya kunna Mata tana gani, tuni hawaye sun wanke fuskarta, suma su Zarah suka amsa suka gani, jisuke tamkar su lashe Y'ar uwar tasu dan dad'i.
Da k'yar Uncle ya tsaya aka bud'e k'yautar da Jiddah ta samo, litattafaine da kud'i naira dubu Hamsin. Atake duk suka zaro idanu dan mamaki, Umma ta ajiyema Uncle kud'in duka a gabansa tace ya d'auka ita Jiddah tunda ga littatafai.
Murmushi yayi yana mamakin kawaici irinna yagana, ya mik'e yana fad'in “Lallai Maman Nafisa, to wannan tsarin naki kam baiyiba, jiddodo ALLAH ya huta gajiya ni nayi nan”.
Duk magiyar da Umma kemasa bai sauraretaba ya fice abinsa.
Sabon shafin murna suka k'ara bud'ewa bayan fitar Uncle. Walida Na had'a wutar gawayin da zasu soya awara, Zarah kuma Na yankan su albasa da kabeji, Jiddah dake kusa da Umma zaune tanata basu labarin komai daya faru a wajen.
Haka suka kasance a wannan dare cikin firar yaushe gamo, yayinda sukaci awaransu sukayi nak.
😋😋😫nima zanci awara dan ALLAH.
Washe Gari tunda safe saiga Abba a gidan, Walida da Zarah na shirin tafiya makaranta, yayinda Jiddah ke gaban rijiya zaune zatayi wankin kayansu.
Duk tsit sukayi daga dariyar da sukeyi saboda shogowarsa, hakan yasaka Umma dake falo fad'in “Su auta suntafine naji gidan tsit?”.
“A'a Umma”. ‘Zarah tafad'a a hankali kamar munafuka’.
Fitowa Umma tayi, saitaci karo da Abba dake tsaye tamkar tsohon soja, sai harare-harare yakeyi. Tuni Umma ta had'e fuska itama sannan tace, “Zarah kuwuce ku tafi karku makara”.
Sum-sum suka fice daga gidan.
Cikin tsantsar masifa Abba yace, “Idanma sun zauna Uwarmi zasumin? K dan Ubanki bance karkije Abuja ba?”.
Ya kare maganar yana nuna Jiddah da kanta ke a kasa tana hawaye.
Jikinta Na rawa ta d'ago ta kalleshi, “Abba wlhy bansan ka hanaba da.......”
Katseta Umma tayi da sauri.
”Jiddah tashi kiwuce gidan Sa'adatu” (makwafciyarsu).
Ai tunkan Umma takai k'arshe Jiddah ta zari hijjab tafice da hanzari tamkar zata kifa dan har tuntu6e tayi da k'ofar zaure babban yatsanta ya fashe, amma bata kula da zafi da jinin da yakeba tafita abinta.
“To tafita, saiki nemo iccen dukana Yagana”.
Murmushin takaici Umma tayi, cikin fushin dabai ta6a sanin tanada shiba tace, “Ka kwantar da hankalinka Alhaji, yagana batada k'arfin dukanka, amma lallai akwai babbar kotu Mai hukuntaka, yanzu dan ALLAH bakaji kunyar d'akko k'afa kazo cin zarafin yarinya akan taje taron addini ba? Anya kuwa Alhaji kana tsoron rad'ad'in d'aukar rai da kwanciyar kabari kuwa? Wlhy kaji Na rantse a wannan Karon kace zakayima yarinyata wani Abu akan zuwa taro namasu k'yak'yk'yawar manufa ALLAH saimun gurfana kotun musulinci dakai. Idan kuma kaji k'arya bismillah gata ga kanan ai”.
Tana gama fad'a tayi shigewarta d'aki tabarsa tsaye zororo a waje. Takaici ya kumeshi yakasa koda motsi, sai huci da hura hanci yakeyi. Kusan mintuna biyar Umma taji fitarsa cikin buga murfin gidan da k'arfin tsiya.
Ta6e baki Umma tayi tana fad'in “Oho dai, wannan shashancin ya isheni, ka tsaya a rashinson nasu, amma bazan lamunci a zugoka kazo kana cimin zarafin yara akan hanyarsu ta aikata dai-dai da alfaharin kowad'anne iyayen kwaraiba wlhy”.
Jiddah kam saida taga lokaci yaja sannan tadawo gidan tacigaba da wankinta, bata tambayi Umma Abba ba, itama Umma batace Mata komai akan Saba, saima d'akko Mata hirar zuwa Barno datayi wajen bikin Y'ar kaninta autansu.
Nanfa Jiddah tashiga murna sosai, dan tanason zuwa danginsu saboda tarbar mutunci da koyaushe ake musu, ga dad'in zama da kakarsu dasukeji over. (Mahaifiyar Umma💃🏻).
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tsawon kwanaki goma kenan da dawowarsu daga taron Abuja, amma gaba d'aya tunanin yarinyar yakasa barin malam, dan haka yau ya buk'aci ganin malam mistafa.
Bayan la'asar lis malam Mustafa ya iso, lokacin malam yana waya da Aliyu.
Malam Mustafa na zaune har suka kammala sannan ya gaidashi cikin girmamawa. Malam ya amsa yana tambayarsa ya k'ok'ari da d'alibai?.
“Alhamdllh malam”.
“To Masha ALLAH mustafa. Niko wata tambaya biyu Zan maka”.
“To malam ALLAH yasa inada ilimin sani”.
Murmushi malam yayi yana gyara zamansa, “Abokinka bashida wata wadda yake so ne?”.
“Gaskiya malam babu, dan nidai tun Asma'u ban sakejin zancen wata mace a bakinsa ba, koda yadawo ma banji yanama maganarba, nakan tsokaneshi akan maganar Aure lokaci-lokaci amma amsata dashi shine (ba yanzuba), har Maimuna danaga kamar tana nuna alamar sonshi nabashi shawarar aurenta amma baima tankaminba a lokacin”.
Nanma murmushi malam yayi yana girgiza kansa kafin yace, “Maimunatu tanan gidana?”.
“Eh ita malam”.
“To Masha ALLAH. tambaya ta biyu akan yarinyar datai karatu awajen taron ranar ce, d'iyar wanene? Konace mizaka d'an fad'amin game da ita?”.
Gaban malam mustafa ne, Yay mugun fad'uwa a ransa yace wayyo ALLAH badai Jiddah taba? Yarinyar da kullum nake kaffa-kaffa da duk wani motsinta. Amma a fili saiya had'iye abinda ya toshe mak'oshinsa, cikin danne abinda ke ransa yace, “Malam itama d'alibarmuce, maikuma tsananin hazak'a da rik'o da addini, duk yanda kake zatonta ta zarce hakan, tarbiyya da duk k'yak'yk'yawan hali Na *MACE TA GARI* za'a iya samunshi gareta. Mahaifinta kam da wuya idan zaka sanshi, sunansa Alhaji Zakari yaro, ni kaina sau d'aya nata6a ganinsa, dan komai Nata k'anin mahaifinta kezuwa makaranta yay Mata a koyaushe aka buk'aci ganin iyaye”.
Kai malam ya jinjina cikin gamsuwa, “Mustafa kana ganin zata iya dacewa da tsarin abokinka kuwa?”.
Bak'aramin wuntsilawa cikin malam mustafa yayiba, harya d'ago yad'an kalli malam d'in, amma sai yay saurin maida kansa k'asa ya duk'ar, muryarsa nad'an shak'ewa yace, “Insha ALLAH malam zasu dace, dan dukkan abinda zai iya buk'ata Na tarbiyya daga gareta zai iya samu insha ALLAH”.
Malam dayaso fahimtar wani Abu yay d'an shiru yana kallon Mustafan, kafin yace, “To Alhmdllh, amma kana ganin babu maganar auren wani kanta? Kokuma Mai neman aurenta?”.
Da Sauri malam Mustafa ya dai-daita kansa, danya kula kamar malam yafara harbo jirginsane. Cikin sabuwar natsuwa yace, “Banajin hakan gaskiya malam, amma insha ALLAH zanyi binciken daduk yadace akanta”.
“Nagode sosai mustafa, ALLAH yayima rayuwa albarka, ya raya maka yaranka”.
“Amin malam”. ‘malam mustafa ya amsa cike da kunya.
(Malam mustafa shike auren Siyama k'anwar Aliyu dasuke Uwa d'aya Uba d'aya, to shifa da burinsa Jiddah nagama makarantarsu yayi ta biyu da ita, amma sai baita6a koda nuna mataba saboda wani dalilinsa, gashi malam yamasa shigar sauri😂).
★★★★
Dukda son da malam mustafa kema Jiddah haka ya danne da rok'on ALLAH ya cire masashi yahau bincike sosai akanta. Lallai yana taya abokinsa kuma d'an uwansa murna da samun Jiddah matsayin matar aure.
Jiddah kam dabatasan mi akeba tanata harkokinta, hutunsuma Na kwanaki hud'u Na k'arewa takoma zuwa makaranta abunta. Yayinda a gefe suke cikin k'yak'yk'yawar zaman takewa itada ahalinta.
Abba ne kawai kansa yay kudu, lokaci-lokaci idan yaga dama ya lek'osu, wani lokacinma da Rana yake zuwa idan bukatarsa ta tsunkuloshi sannan su jiddah basa gida, dayazo yasamu kuma yak'ara gaba. Hakan kuma bazai hana idan gobe ya dawo Umma tasake bashi kantaba.
A wannan yanayinne su Zarah suka sami hutun makaranta, yayinda gefe kuma Umma keta musu shirin tafiya Barno biki Wanda zasu tafi har aunty Nafisa da yaranta.
Yau lahadi takama babu makaranta gasu Zarah, Jiddah kuma take suka taso da wuri saboda suna jarabawa, Jiddah ta fita sayo abu a shago dan almajirinsu dauda bai zoba bashida lafiya tun shekaran jiya, Walida da Zarah kuma suna wanki.
Da sallama Jiddah ta shigo shagon, Mai shago sama'ila ya amsa yana tsokanarta da “Malama Jiddah mikike buk'ata?”.
Murmushi tayi tacikin nik'ab d'inta kafin tafara lissafo masa a nutse da sanyinta. Juyawa yay cikin shagon yana had'o mata, itakuma takoma gefe jikin k'ofar ta tsaya tana jiransa dan tabama masu zuwa sayyaya hanya.
Hirar samarin dake d'an gefen shagonce kad'an taja hankalinta, saboda maganarta kamar akeyi. Wani taji yana fad'in,
“Tab, wlhy ban kwarar kaina Na auri Matar dabata wayeba, kullumfa tana cikin hijjabi kamar Matar liman, yanzu haka inza'a kasheni bazan iya fad'ar kamanninta ba ma”.
“Aiba kaikad'aiba wlhy Labaran, nikaina inason wayayyar mace wadda zata fiddani kunya aduk inda muka saka k'afa, amma irin wad'ancan mizasu iya banda suyita jawo maka aya da hadisi a kowanne minti”.
Gaba d'aya suka kece da dariya. Wani yakuma fad'in,
“Nikam dukma ba wannan bace matsalata deeni, kaje aimaka ta ubansu aita Haifa maka y'ay'a mata su karya maka tattalin arzik'i, ka ciyar dasu suna gabanka suyi aure kakoma shari'ar matsalolinsu, babu ribar daka samu na wahala dasu sai k'arin wata wahalar”.
“Tab Ashe kagane Ishaq, wlhy koni bana ra'ayin a cikamin gida da y'ay'a Mata, guda d'aya ta isheni sauran su zama duk maza, rayuwar yarancan tama isheka ishara, nifa ban ta6a ganin wani saurayi a k'ofar gidansu Neman aurensuba, hakafa yayarsu Nafisa tayi bandaro a anguwarnan, to nama lura wannan ustaziyar saita fita tsufa a gida”.
Nanma dariyar suka shigayi, jiddah da takaici yasakata hawaye tayi wucewarta gida batareda ta kar6a abinda tazo sayenba.
Sai sama'ila ne yabama wani yaro yabita dashi.
A zaure ta tsaya ta share hawayenta sannan ta kar6a ledan kayan da Sama'ila yasa abiyota dasu.
Da sallama ta shigo gidan, ta ajiye kayan tashige d'aki batareda ta cire Nikab d'inba.
Umma Na bayi, su Walida kam sun duk'ufa wanki shiyyasa basu Lura da halin da jiddah ke cikiba.
Sosai tasha kukanta, saida taji Umma Na kwala Mata Kira sannan ta share hawayen tafito.
Kallo d'aya Umma tayi Mata tafahimci tana cikin damuwa.
”Omon dake hannunta da jiddah ta sayo yanxun dan suyi tsaraba ta ajiye tana fad'in “Lafiyarki kuwa?”.
Murmushin yak'e Jiddah tayi, “Umma babu komai, k'asace ta shigarmin Ido saboda iskar da akeyi, alamu zubar ruwa Nata kuma bayyana”.
Badan Umma ta yardaba tabarta, saima ta d'akko wani zancen.
“Walida ku gama wankinnan kije gidan zainabar bashari ki amsomin dakan kuka da ku6ewarnan da Sauda (babbar yar su jiddah) tace aimata, Gurasar Hannatu (yayarsu ta biyu, y'ay'an matarsa Na farko Amina) dai sai a bari gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma sai'a a amso gidan y'an gurasa dan karta bushe”.
“To Umma bara mugama sainaje d'in”.
Zarah ta mik'e tsaye tana rik'e kugu da sauke numfashin gajiyar wanki, “Umma waikuwa aunty Zulaiha (yayarsu, y'ar matar abba ta biyu) zataje d'in?”.
“Wlhy Zarah ban saniba, tadai cemin yau zata Kira da daddare akan yanda sukai da Mijin Nata, idan ya amince gobe zata baro huntuwa tazo nan kano ta kwana saimu wuce jibin”.
“To ALLAH dai yasa ya barta, wannan Mijin Na aunty Zulai bayason yaga tamatsa ko nan da can”. ‘Cewar Jiddah dake kulle omo a leda’.
Dariya su walida sukayi suna fad'in wayaga Yaya Adam cigam d'in aunty zulai.
“Kunci gidanku”. ‘cewar Umma tana musu dak'k'uwa’.
Dariya sukayi har Jiddah..............✍🏻
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
_Zaku iyabin wannan link d'in na sama domin sauraren littafin RAINA KAMA a audio, Abban dausayi YouTube channel😄🤝🏻_
*_Abba zakari Na gaisheku🤭, jiya gidansa Na yini tunda duk kunki zuwa gaisheshi ku😆😆😝⛹♀_*
*_ALLAH ka gafaiyayenmu😭🙏🏻_*
0 comments:
Post a Comment