*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[27➖28]_*
..............Babu dad'ewa Aunty Ruk'ayya ta iso asibitin, bisa kwatancen da Aliyu yay Mata ta iso d'akin.
Har yanzu yana zaune kusada Maimuna dake barci, hannunsu Na sark'e dana juna har yanzun, shigowar aunty Ruk'ayya da sallama ya sakashi zame hannunsa a hankaki dukdama tarigada ta gansu.
Hannu ya mik'a ya kamo hannun yaronta Najib fuskarsa d'auke da murmushi. “Najibullah kaine ka k'ara girma haka?”.
Najib dako magana bai gama iyawaba ya lafe a jikinsa, yayinda Aunty Ruk'ayya ta zauna saman kujera tana dariyar maganarsa.
Yaranta Sadiya da Naja'atu suka shigo da sallama hannunsu d'auke da ledoji.
“A'a Aunty kice harda y'ammatana kike tafe?”.
Sadiya da Naja'atu suka durkusa suna gaishesshi da tambayar ya Mai jiki?, fuskarsu washe da murmushi, shima cikin sakin fuska ya amsa yana tambayarsu makaranta.
Suka had'a baki wajen fad'in Alhmdllh Kawu.
“Naga gida gaba d'aya amma banga Ameer ba?”.
“Kawu ai yana tare da Abba sunje anguwa”. ‘Naja'atu tai maganar cikeda ladabi irin Na y'ay'an da suka samu tarbiyya’.
Aliyu yace, “ALLAH Sarki, to ALLAH ya dawo dasu lafiya”.
Da amin suka amsa, kafin ya maida hankalinsa ga aunty Ruk'ayya suka gaisa tana tambayarsa Mai jiki.
“Aliyu maimuna dukta rame fa, sai haske data k'ara, kodai munsamu k'aruwane?”.
Murmushi kawai yayi, kafin yabata amsa doctor yashigo da sallama, bayan yabama Aliyu hannu sunyi musabaha ya mik'a masa takardar result d'in yana masa murnar cikin dake jikin Maimuna Na watanni biyu da wasu kwanaki.
Tuni murna ta kacame tsakanin Aliyu da aunty Ruk'ayya dasu Sadiya, wasu kwallan farin ciki suka taruma Aliyu a gefen ido Na dad'i, Aunty Ruk'ayya kam ai saida suka zubo a kumatunta, koba komai samun lafiyar Aliyu ta tabbata, dama tana tunanin kar aita tsogumi akan wannan auren nasa dazai k'ara, Dama taji anfara k'ananun magana a gidansu akan Maimuna, amma yanzukam hankalinta kwance.
★★★★
Lokacin Salla na gabatowa Aliyu yatafi gida yabar auty Ruk'ayya da aunty Siyama datazo daga baya.
Bai koma asibitinba sai kusan tara Na dare, danma yau bai xauna karatuba, yanema uziri akan Mai d'akinsa batada lafiya.
Mutane sunta mata addu'a da fatan samun lafiya.
Lokacin daya dawo ya iske harda malam da matan gidansu suma sunzo duba Maimunatu data farka tuni, baiyi zaton ganin su malam ba, dukda dai shine yakira ya sanar masa batada lafiya, amma bai fad'i maganar cikinba saida sukazo sukeji a bakin su Aunty Siyama.
Maimuna nata duk'ar dakai tak'i yarda su had'a ido da kowa, koda Aliyu ya dawoma kasa kallonsa tayi, saicin abincin da aunty siyama takawo take a hankali. Duk yanda yaso su had'a ido tak'i bashi damar hakan, murmushi yayi yana k'arajin k'aunarta harcikin ransa. Yanason Maimunatu saboda k'yawawan halayenta Wanda Ada kafin aurensu baiyi zaton tana dasuba. Shiyyasa babu k'yau yakema mutum hukunci akan abinda baka tabbatarba, kakuma k'yautata zato ga kowa shine nagarta da cikar kimar d'an Adam.
Basu bar asibitinba sai kusan sha d'aya Na dare. Kowa gidansa ya nufa, shima ya d'auki matarsa sukai gida bayan yad'an Mata sayayya a hanya.
Yanata janta da hira amma takasa amsashi da k'yau saboda barcin dake cike da idonta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tunda Abba yabar kasuwa babu abinda ke caccakar zuciyarsa sai maganarsa da Alhaji Garba, sai k'ullawa yake da kwancewa, yana hangen k'urar da zata iya tasowa tsakaninsa da Umma da Uncle yahya, gefe kuma yana kallon d'unbin kud'in da Alhaji garba hace ya barmasa inhar Jiddah ta dawo garesa, yasan ko k'asa da sama zata had'e bashida kud'in biyan Alhaji garba, koda kuwa za'a saida gidansane da kayan kasuwarsa da komai daya malakka, dan kud'in daya ranta a banki a shekarun baya dasune ya ida ginin gidansa, ya kuma k'ara jari sosai a kasuwa, suka kuma hau kan sauran kud'in shida Hajia Hindu da y'ay'ansa sunaci hankalinsu kwance, da kud'in kasuwa yad'an fara bama banki miliyan goma, daga baya kuma saiya daina biya, lokacin da suka ajiye shida banki na cika suka nemi kud'insu, amma sai suka iske babu wani abun arzik'i a k'asa sai kayan kasuwarsa, kwanaki goma suka bashi ya maido kud'in kokuma komaima yafaru shi ya sani, wannan ne ya tashi hankalinsa sosai har hajia Hindu ta fahimta, tashin farko tabashi shawarar Neman bashi wajen Alhaji garba. Baiwani dogon tunaninaba ya amince saboda mafita yake nema a lokacin, da taimakon Hindu hajia deluwa ta lalla6a musu Alhaji garba yabada kud'in, sai dai a lokacin shi Alhaji garba saiya 6oyema Hajia deluwa adadin kud'in da Abba ya nema saboda wani dalilinsa, cemata yayi kawai miliyan gomane. Shikuma Abba maimakon dayazo kar6ar bashi ya kar6i miliyan arba'in tunda yabama banki miliyan goma tuni, saiya kar6i hamsin d'in, ya biya banki arba'i ya ajiye goma a hannunsa da zummar ya k'ara jari danya samu ya gama biyan Alhaji garba da wuri. Bayan faruwar haka babu jimawa Alhaji garba yaga Jiddah, d'uwawunsa Na rawa yace yabarma Abba rabin kud'in inhar yabashi auren Jiddah, yakuma lamunce masa ahankali ya biyasa sauran rabin. To dagabaya da auren Jiddah da Alhaji ya rabu sai Alhaji garba ya aikoma Abba cewa ya janye k'yautar dayaymasa ta Rabin kud'i, a yanzukam yanemi miliyan hamsin d'insa ya basa cif. To yanzu kuma Alhaji garba yadawo ruwa saboda ganin Jiddah daya k'arayi ya rud'e, a wannan karonma gaba d'aya ya barma Abba kud'in inhar an maido masa Jiddah, idan ank'i kuma abashi kud'insa da wuri. kunga kuwa dolene Abba yashiga cakwakiyar tunanin son wargaza auren Jiddah da malam Aliyu yakuma k'ullawa da Alhaji garba a Karo Na biyu.
Tofa masu karatu, Yaya wannan cakwakiya zata kasance? Minene makomar Abba zakari idan baisamu cikar burinsaba?.
Nidai bilyn Ku nace yasaka yan MASARAUTAR BILYN ABDULL DA MUTUM DA DUNIYARSA GROUPS a kasuwa yabiya bashinsa hankali kwance😝😂😂😂⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Baki hajia deluwa ta ta6e saboda sauraren zancen Alhaji garba da takeyi akan Jiddah. “Wai kana nufin da gaske itace kenan Alhaji?”.
“Minene ribata idan namiki k'arya Yahanasu, to yanzuma haka maganar da nake miki mun k'ark'are magana da mahaifinta zai dawomin da ita”.
A zabure hajia deluwa tace, “Ban gane zai dawo maka da itaba, dama ba Saki uku kai mataba?”.
“A'a k'arya haramun, wlhy Saki biyune, da bama tagama iddah ba datun yau zance na maidata a gabansa, to amma babu komai, nanma da sati d'aya za'a sake d'aura mana aure”.
Wata makirar dariya Mai had'e da shewa hajia deluwa tayi, kafin ta callara bud'a akan Alhaji garba tana fad'in ALLAH ya nuna mana ango”.
Da wani kallo tuhuma ya bita harta bar falon amma baice komaiba.
Hajia Deluwa na shiga d'aki wayarta ta d'auka ta dokama malam Na marwa Kira, yana d'agawa ko gaisuwa bata tsaya sunyiba tafara magana, “Malam Alhaji zai kuma maido shegiyar yarinyarnan, wannan Karon sonake ka haukata min ita kawai tabi duniya”.
Numfashi Malam Na marwa ya sauke, kafin yace, “Hajia hakan bazata yuwuba gaskiya, dan a yanzu haka zancen da nake miki wandama yake kanta zai iya zame miki babban Matsala, dan aljanin dana had'ata dashi yana shan wahala a hajenta, Sam yarinyar bata sakaci da ibadar ALLAH, danma aljanin yanada nacine, amma wlhy yafara nunamin gazawarsa, kibi tawata hanyar kawai kidai dakatar da auren inaga zaifi”.
Tsaki taja tana yanke wayar, “Dak'ik'i kawai, ashema bakomai zaka iyayiminba”. (Hummm)
Maida akalar kiranta tayi ga hajia Hindu bayan sun gaisa tace, “Hindu wani aikin zakimin akan Y'ar mijinki, amma kafin sannan idan kinada wani malami kimin rakiya gunsa koki bani lambarsa”.
“To Hajia kinsanfa ni indai harkar malamai ce ba'a yinta Dani, akullum bakina shike kwatata a hannun miji da kishiya, dan shine malamina shine bokana, amma bazan bama k'aton banza kud'ina yaci ya had'omin k'aryaba”.
“Kinga ya isa haka, idan bak'ya wannan ai saikimin aiki da bakin naki, sonake kiyi duk yanda zakiyi kar auren Y'ar mijinki yakuma k'ulluwa da mijina, idan har kikayi haka Zan baki miliyan d'aya”.
A rikice hajia Hindu tace, “Miliyan d'aya fa? Akan hana aure kawai? To kibani nanda kwana uku kacal zakisha mamaki”.
“Nabaki, amma karya wuce haka”.
Gaba d'aya Hajia Hindu ta rikice, batayi sanyaba wajen nufar d'akin Abba, tashin hankalin data iskeshi a ciki naneman mafitar k'ulla auren Jiddah da alhaji garba ne ya sakata samun damar bugar cikinsa, nanko yashiga Mata bayani dalla-dalla akan k'udirinsa Na sake aurama Jiddah Alhaji garba.
Tana gamajin komai tai saving d'in recording d'in datayi.
Abba dai baisan anayiba🤣.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe Gari Abba Na fita kasuwa hajia Hindu tai shiri tatafi gidan uncle yahya, abinda batayi a rayuwarta, dan inba Maman Sadiq ce ta haihuba bazaka ta6a ganinta a gidanba, shima barka take zuwa, minti talatin kuma yayi yawa zata baro gidan.
Maman Sadiq ma tayi mamakin zuwan Nata, tadai kawo Mata ruwa sannan suka gaisa. Suna cikin gaisawa Uncle yahya dayay shirin kasuwa ya fito, shikansa yayi mamakin ganin Hajia Hindu, amma saiya zauna suka gaisa danyaji dami tazo. Batawani ja musu ajiba tabashi recording d'in yaji. Sosai mamakin Abba da d'unbin wautarsa ta Kama Uncle yahya amma sai baice komaiba ya mik'ama hajia Hindu wayar yana fad'in “ALLAH ya k'yauta” kawai. Dan itama bata isa ya tattauna komai da itaba akan lamarin. Sallama ma yaymusu ya fita abinsa.
Uncle yahya bai zame ko inaba sai gidan Umma, ya iske ita kad'aicema a gidan, tana falo zaune tana sauraren redio.
Zama yay suka gaisa kafin yaymata bayanin komai kamar yanda yaji.
Umma zata birkice masa yace, “Kinga kwantar da hankalinki Maman Nafisa, ni nasan matakin dazan d'auka akan Yaya wannan karon, bayace kafin sati biyun da mukasa zai d'aura Mata aure ba, toni kafin sati d'ayan dayasa nima Zan d'aura mata”.
“Oni Yagana, wai Alhaji kuwa yasan miyakeyi? A ina yata6a ganin nema akan nema? Balle wannan da harma an biya sadaki? Anya kuwa lokaci baiyiba dazan raba jaha dashi?”.
“A'a dan ALLAH kibar fad'ar haka Maman Nafisa, ki duba yarannan dake suke kallo suji sanyi a ransu harsu Nafisa dabake kika haifesuba, mucigaba da masa Addu'a, dan son zuciyane kawai ke d'awainiya dashi, ita kanta hindun nasan akwai dalilinta nayin hakan, amma mu insha ALLAHU a garemu alkairi zai zama”.
“To ALLAH ya rufa mana asiri, wlhy ni sam Uncle d'insu bana ganin laifin Hindu, dan tunkan zuwanta gidannan yake fama da mugun halinsa, ita idan kagama ta aikata d'orata akayi a layi”.
“Wannan gaskiyane Maman Nafisa, ALLAH dai ya rufa mana asiri, ni bara naje wajen malam d'in mu tattauna, daga nan zan wuce kasuwa”.
“To ALLAH ya tsare, ya raya mana su Sadiq yabiyaka da mafificin alkairi kaima”.
Da amin ya amsa yana ficewa.
★★★★★★★
Kai tsaye gidan Malam Uncle yahya yanufa, dukda ya iskeshi da bak'i haka yasaka aka kai Uncle yahya falonsa ya taso ya saurareshi.
Bayanin dazai gamsu shima yay masa, shikansa malam ya girgiza da lamarin Abba, amma saiya bishi da addu'ar fatan shiriya kawai.
Sun k'ark'are magana akan zasu d'aura auren ranar juma'a bayan sakkowa masallaci, nanda kwana 4 kenan, kuma Abba zakari bazai saniba sai a wajen d'aurin auren.
Daga baya idan an kimtsa Jiddar saita tare.
★★★★★★★
Koda Aliyu ma yazo da yamma haka malam ya sanar dashi sun dawo da d'aurin aure Juma'a.
Kansa a k'asa ya amsa da “ALLAH ya kaimu baba, ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, duk yanda kuka yanke yayi”.
Malam ya jinjina kai yana saka masa albarka.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau dai kam malam Aliyu yasan dolene ya danne zuciyarsa yayma Maimunatu bayani yanda zata fahimta, dan yanason saiya gama da matsalarta kafin yaje ga waccan sarkin kukan (Jiddah😂).
Yau jikinta dad'an sauk'i, saidai abinda ba'a rasaba irin Na Mai laulayi.
Kamar yanda ya saba ya bud'e Mata hannayensa ta shige sunamai begen juna.
Bayan ya watsa ruwa sun dawo fallo takawo masa kayan marmarinsa, gefe takoma ta zauna, dan yanzu bata iya sha ita, ganin yayi shiru yakasa sha yanata kallon fruits d'in saita taso tadawo kusa dashi.
'Dago fararen idanunsa yayi yana kallonta amma baiyi maganaba.
Tad'an langa6e kanta gefe cikin salon kwantar da hankali tace, “Wai mike damunkane Annur? Kwana biyunnan nalura Abu Na damunka amma kana 6oyewa”.
Ajiyar zuciya ya sauke yana juyowa sosai gareta, “Maimoon ba 6oyewa nakeba, kawai dai ina tunanin ta yadda Zan fidda maganar ne gareki, dan bansan Yaya zaki d'auketa ba, kinsan Ku Mata duk dad'in zamanku da miji akazo wannan ga6ar idonku rufewa yakeyi”.
Cikin d'an nazartar maganarsa tace, “Indai nice bazaka fuskanci hakan daga gareniba insha ALLAH Yaya Aliyu, akoda taushe Zan kasance Mai biyayya a gareka da girmama buk'atarka, kodan nasamu rabauta a wajen ubangijina da gamawa da wannan rayuwar Mai tak'aitaccen kwanaki lafiya”.
Jawota yay jikinsa ya rungume sabodajin dad'in kalamanta, “Nagode gimbiyata, ALLAH yaymiki albarka, ina sonki da k'aunarki fiye da tunanin Mai hankaki”.
Maimuna dai Na saurarensa, yayinda a gefe d'aya zuciyarta ke tunanin mike faruwa? Kodai rabuwa zaiyi da itane?.......
Tunaninta ya katse lokacin da Aliyu ya d'agota daga jikinsa.
Hannayenta ya rik'e cikin NASA, idanunsa a k'asa dan kimarta tawuce ya kalli cikin idonta yafad'a Mata zai k'ara aure. “Maimoon Zan k'ara aurene”.
Wata zabura tayi tana cire hannunta daga cikin nasa, yayinda tuni wasu hawaye masu zafi sun Fara bin kumatunta, tana niyyar mik'ewa yakai hannu zai ruk'ota, amma saita kauce tashige d'akin baccinta da gudu.
Kansa ya dafe a hankali ya furta “Ya salam”.
Kasa tashi yay a wajen kusan minti talatin, saida ya tabbatar inma kukane take, tayi Wanda zai rage nauyin da zuciyarta tayi, kafin yamik'e ya bita.
Zaune ya isketa saman stool d'in mirror ta kifa kanta akan Mirror d'in tana shashshekar kuka..
Yad'an dad'e tsaye a bayanta yana kallonta, kafin yasaka hannu ya d'agota zaune sosai. Yanda fuskarta tai jajur sai tausayinta ya kamashi, kafad'unta ya Kama ya mik'ar da ita tsaye, yaja hannunta zuwa saman gado, koda suka zuna saiya sakata a jikinsa, ya saka hannayensa yana share Mata hawayen.
“Haba Maimunatu, mumini Na k'warai shike kar6ar dukkan abinda yazo a shari'ance garesa koda yana kallonsa k'untata a rayuwarsa, kefa Mai ilimice, iliminma Na addini, sannan ALLAH yayiki cikin Mata masu hankaki da Nisan tunani, nasan kishi abune Mai zafi, amma idan muka gaurayashi da hak'uri da k'yautata zaton Alkairi a junanmu saimu sameshi da sauk'i, kisaka a rankin mijinki Na matuk'ar sonki, kuma insha ALLAH zaiyi adalci agareku, itama wadda zata shigo matsayin k'anwa a gareki ki k'yautata Mata zaton samunta Mai k'yawun hali da fatan zamu zauna lafiya, dan ALLAH ki kwantar da hankalinki kodan babiena dake tare dake, badan bana sonki bane zanyi aurennan, bakuma dankin gazamin a komai baneba, kawai dai kisaka a ranki San k'ara aure ga kowanne namiji tamkar an haliccemu dashine, dan ALLAH kiyi koyi da halin matayen MANZON ALLAH (S.A.W), hakan shine zaikuma girmama k'aunarki a raina, dan abinda Mata basu ganeba, shirme da sukeyi yayinda mazajensu zasu k'ara aure shike janye k'aunarsu da tausayinsu a zukatan mazanma gaba d'aya, amma idan kika kwantar da hankalinki saikiga Mijin Nata k'ok'ari danya faranata miki Yakuma kare martabarki ga wadda zata shigo, dukda dai nasan akwai azzaluman maza da inhar zasu k'ara aure burunsu shine su wulak'anta matayensu Na gida, suyita tozartasu gaban yarinyar da zasu aura, wannan kuma ba daidai baneba zaluncine, kuma sai ALLAH ya sakama Matar, shiyyasa saikiga yarinya kanta shigo babban burinta shine data shigo ta kori Matar gidan, kinga tunkan tazo cikin gidansa ya gama wargaza farin cikin gidansa gaba d'aya. Nidai insha ALLAH bazan kasance irin wad'annanba Maimoon, dakinga kuma Zan kauce kiyi azamar maidoni, dan kinada kima da daraja Mai yawa a zuciyar Aliyunki wlhy”.
Tashi zaune maimuna tayi sosai tana k'ara share hawayenta, ”Kayi hak'uri Yaya Na fahimceka, ka yafemin tasowar danai Na barka d'azun, wlhy Yaya kishi Nada zafi, dama Ashe haka duk wadda za'aima kishiya takeji Yaya?, Yaya kamin Addu'a ALLAH yabani ikon jurewa, wlhy ina sonka sosai, amma hakan bazai sakani bijirema ubangiji naba, domin yayimin dukkan ni'imarsa.....”. Tak'are maganar da k'ara fashewa da kuka.
Jikinsa ya jawota ya rungumeta tsam, tsantsar tausayinta da k'aunarta na ratsashi, sun dad'e a haka kafin ya d'agota ya mik'e, ruwa ya d'ebo a Kofi ya dawo ya isketa zaune inda ya barta tana cigaba da zirarar da hawaye, alkur'ani ya d'akko ya bata sannan yakoma ya zauna yana Mata nuni data karanta, batayi musuba tabud'e tafara karantawa a zuciyarta tana cigaba da hawaye, yayinda shikuma yake tofa Mata addu'oi a ruwa yana kallonta.
Yadad'e yanayi, yana kammalawa ya kar6i alkur'anin yabata ruwan addu'ar, kar6a tayi ta shanye tana masa murmushi, dan tad'anji nauyin zuciyarta ya ragu.
Koda ta shanye ruwan addu'ar saiya jawo kayarsa jikinsa yashiga nuna Mata tsaftatacciyar soyayya. (daganan naji bulum😂⛹♀).
Saida yakuma bata nutsuwa da kuma jaddada Mata k'aunarta dake ransa sannan suka dawo falo yasha fruits d'in...............✍🏻
⛹♀⛹♀duk Wanda naji ya zagi Maimunatu yau dashi za'a biya bashin Abba zakari🥺👯🏻.
_Maman Salma sak'onki ya iso ga bilyn Abdull, ina godiya kwarai da gaske da addu'arki, alkairin ALLA YAKAI gareki aduk inda kike a fad'in duniya🥰🥰🥰🥰🥰🥰❤🤝🏻👍🏻_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[29➖30]_*
...........Shirye-Shiryen biki dai ya kankama, dukda aure kawai za'a d'aura biki sai satin sama, dangima mazane kawai zasuzo d'aurin aure, mata kuma sai ranar tariya.
A wannan Karon kam dolene ka fahinci ana biki gidansu Jiddah, dukkan tanadin da Umma keyi Na kayan d'akin y'ay'anta ta fiddo Na Jiddah fili, abinda babu kuma ta had'a y'an kud'ad'enta Aunty Nafisa da Maman Sadiq ɖa Balu suka shiga kasuwa.
Uncle yahya ma yanata shirinsa akan kayan gado, dan baimayi tunanin Neman Abba ba balle ya tunkareshi.
A 6angaren Jiddah kam tanajin k'aunar Sheikh Aliyu, amma kuma batajin son auren kwata-kwata, duk d'okin da y'an uwanta keyi kallonsu kawai take, babban ma abinda ke damun ranta da akace yanada Mata, tana tsoron komawa Y'ar gidan jiya gaskiya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Duk suna a tsakar gida, Umma da Balu suna kan tabarma, Balu na yima Umma kitso suna hirarsu ta zuminci, sai Jiddah dake yankan alayyahun da zasuyi miyar taushe, Zarah Nata aikin tuwo daga can k'ofar kicin.
Da sallama Walida ta shigo hannunta rik'e da madaidaiciyar bak'ar leda data sayo kifin miya, kallo d'aya zakai Mata ka fahimci tagaji.
Duk sannu sukai Mata bayan sun amsa Mata sallama, ta ajiye ledar a gaban Jiddah tana fige hijjabinta ta jefe saman igiya sannan taje kusa da su Umma ta zauna tana fad'in “Wash ALLAH k'afafuna”.
Balu tai Y'ar dariya “Sannu Walida, kona goyakine? Naga kin gaji”.
“kai Aunty A'a na hutashsheki, kawai gajiya nai da tafiya, ga wani shegen Mai naci daya nanuk'emin tundaga titi har k'ofar gidannan”.
“Tofa, auta kice dai Umma tayi suruki”.
“Kai Yaya Jiddah dan ALLAH, ni wlhy ban fad'aba”.
Dariya Zarah dake k'ok'arin tuk'a tuwo takeyi tace, “O su walidatu an kusa aure ashe”.
Umma ta zubama Zarah harara tana fad'in “Ya isheku hakanan malamai, yanzu zaku tasomin yarinya gaba ko huce gajiyar wahalar da kuka sata batayiba, tama dawo kod'an ruwa baku bataba”.
“To Umma naga ai da ita za'aci?”.
“Yo Yaya Jiddah tamafi kowa lauma ai”.
“Gaskiyarki kuwa Zarah”.
Dariya itadai Balu take musu, dan tsarin yayarta da y'ay'anta Na matuk'ar birgeta, idan sun Mata laifi zata tsawatar musu tamkar bata sansuba, amma hakan bazai hanata ta Saki jiki dasuba tamkar k'awarsu, hakanne yasa take saurin gano matsalarsu, suma kuma basa iya 6oye Mata komai nasu.
“Yaya Jiddah Ku tsaya, nifa dukma ba wannanba, Naga matar Alhaji garba a kasuwa yanzunan, sannan tare Na ganta dawata Y'ar budurwa, amma alamun yarinyar baimin Kama da y'artaba kamar mai aiki”.
Jiddah dake kallon Walida itadasu Umma tace, “A kwarai akwai mai aiki agidan Bilki”.
“Kai Yaya Jiddah, amma shine baki fad'aba, duk wannan kullawa da kwancewar da mukeyi kullum akan yanda za'a zak'ulo abinda ta binne a kanki”.
“Humm Zarah kenan, ni nama manta da Bilkin wlhy, sannan kuma ma munada tabbacin bilkisun zata taimakemu”.
Umma tace, “Wannan gaskiyane Jiddah, tunda dai kunga tare muka gansu, kamar dai yanda Uncle d'inku yace mubi komai a sannu to mubi d'in, insha ALLAH komai yanada iyaka, yanzuma mungode ALLAH tunda abubuwa sun dai-daita sosai”.
“Hakane Umma, ALLAH ya datar damu dai”.
Balu zatayi magana sukaji sallamar Uncle yahya, hijjab Umma tajawo ta saka sannan tace, “Uncle d'insu ka shigo”.
Uncle yahya ya shigo, zama yay inda Walida ta saka masa tabarma, bayan duksun gaidashi har Balu suka gaisa da Umma ma.
Kallonsa ya maida ga Jiddah dake bakin rijiya tana wankin Alayahu da kifi. “Jiddah ki shirya Sheikh Aliyu zaizo anjima kad'an, dan yacemin bayan la'asar idan ALLAH ya kaimu”.
Kai Jiddah ta duk'ar alamar jin kunya, sai Balu ce ta amsa da “ALLAH ya kaimu”. Amma Jiddah ta kasa.
Shima bai damu da rashin amsawar tataba, dan yasan duk y'a mai tarbiyya za'a sameta da kunya.
Mik'ewa yay yana kallon tuwon da Zarah ke gyarawa bayan ta tuk'a, “Fati a ajiyemin tuwonan Zan dawo naci”.
Zarah tace, “To Uncle, kamar kasan kuwa miyar taushece dama kanaso”.
“A'a lallai yau saina kasa tashi kenan ashe, Walida kidafa zo6o saboda bak'oma, kar6a wannan”. Yay maganar yana mik'a mata dubu d'aya.
Zuwa tai ta kar6a hannu biyu tai godiya, shima yaymusu sallama yafita suna masa addu'ar dawowa lafiya.
★★★★★★
Balu da kanta ta tsare Jiddah tayi wanka gab da la'asar, sai zum6ure-zum6ure takeyi su Walida namata dariya, da Zarah tace zata Mata kwalliya saita sanya musu kuka.
Umma ma dai har dariya tayi, “Wlhy Jiddah kinji haushi, ke komai abin kukane a wajenki? Humm gidan dai kishiya zakije, saikije da miji yamiki Abu ko abokiyar zamanki kihau kuka”.
“A'a wlhy bazatayiba, yanzuma su Zarah d'inne suncika takura, tunda tace bataso basai subartaba”.
“Yo Balu ayi mace babu kwalliyane a rayuwa?”.
“Ai zata ringayi insha ALLAH”.
★★
Anayin Sallar la'asar Uncle yakira Umma akan ta turo Jiddah gidansa.
Hijjabinta ta zabga har k'asa da nik'af, walida taimata rakiya hannunta d'auke da k'aramin basket da aka saka zo6o.
Gidan babu kowa sai Uncle yahya dan Maman Sadiq tafita gidan suna tunda safe, gaidashi sukayi, walida tafita kicin ta shirya zo6on akan tire ta had'a da ruwa.
Zamansu baifi Na minti 5 ba Sheikh Aliyu da malam mustafa suka Iso. Uncle yahya yafita yashiga dasu seatroom d'insa dayasha gyara yanata tashin k'amshi.
Gaban Jiddah babu abinda yakeyi sai fad'uwa, har Walida taje takai musu ruwa ta dawo tace taje suna jiranta.
Idonta cike da kwalla ta fita, dan Walida ta kwace Mata nik'af, gabanta na dukan tara-tara ta isa, saidai kuma takalmi d'aya tagani bak'i, abin yabata mamaki, dan walida tace Mata su biyune, kuma Uncle yahya ma yana can.
Ganin batada mai bata amsa saita danne zuciyarta tashiga da sallama.
Sheikh Aliy dake zaune cikin kujera sanye da wani lallausan farin yadi daya d'au guga ya kwanta luf, sai hularsa Zanna, k'amshin turarirrikansu dukya mamaye falon. Cikin sassanyar muryarsa ya amsa mata sallamar yana d'ago fararen idanunsa akanta.
Kanta a duk'e yake, dan haka baya ganin fuskarta sai kad'an. Daga can farkon k'ofar ta zauna a k'asan kafet, muryarta nad'an rawa tace, “Sannu da zuwa ina yini”.
Numfashi yad'an sauke yana gyara zamansa, “Lfy lau, kina lafiya?”.
“Alhmdllh”.
“To Masha ALLAH” ya fad'a idonsa a kanta, komi yake kallo oho. Shiru sukayi Na wani lokaci kafin yad'anyi gyaran murya.
Ba tareda jiddah ta shiryaba ta d'ago kanta ta kalleshi, caraf suka had'a Ido, saurin janyewa tayi ta maida kanta k'asa.
Murmushi yayi yana fad'in “Ahaka ake za6en miji dama?”.
Kuma k'asa tayi da kanta jikinta na wata tsuma. Tsaf ya lura da halin da take ciki, sai tausayinta ya k'ara kamashi, har tunani yake Yaya zasu kwashe idan ya tuno matsalarta......
Tunaninsa ya katse sabodajin tarinta, Wanda da alama yawune ya sark'eta. Ruwan da walida ta zuba masa yasha rabi ya d'auki sauran da hanzari yamatso kusada ita yana jera mata sannu.
Ansa tayi Tasha, idanunta harsunyi jajir sun cika da kwalla, sai kuma jera Mata sannu yake tana d'aga masa kai, saida tarin yalafa sannan yakoma wajen zamansa ganin jikinta na rawa.
“Ki daure kina k'arfafa zuciyarki dan ALLAH”.
Kanta tad'an d'aga tana share hawayen da suka cika Mata ido.
“Magana kuka, karatu kuka, Anya kuwa ked'in jarumace?”.
Batareda ta saniba tad'an turo bakinta, dan taji haushin maganarsa.
“Yi hak'uri Malam, maida bakin nagani, Bari sai nan da kwana uku amma ba yanzuba”.
Bata fahimci ina ya dosaba, amma hakan bai hanata jin kunyar maganarsaba.
Murmushi yasakeyi yana kallon agogonsa silver dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, “Bara nayi abinda ya kawoni, dan wannan hajiyar bata shan inuwa d'aya da jinsina. Malam Jiddah nasan zakiyi mamakin shigowar maganar aurenmu da wuri, gashi kuma maganar so bata had'ani dakeba, wannan hukuncine Na ALLAH dakuma cika burin mahaifina dayay tunkan aurenki na farko, cikin Amincin Ubangiji nima dana ganki sainaga kin cancanci zama matata, wannan yasaka iyayena suka shigo da zafi-zafi, dan hausawa kance da safe ake Kama Fara, anzo nema min izinin neman so a gareki saikuma akamace an bani, na jinjinama dattako da halin girma irin Na iyayenki, dan sun tabbatar mana sud'in iyayene nagari, yanzu dai fatan da zanyi shine ALLAH yasa Na kar6u, karna zama macen shige, Ku mata kunce bata kwarjini”.
K'asa Jiddah tai da kanta takasa magana.
“Ki daure kice wani Abu, dan ayanzu kinada ikon za6arma kanki miji a matsayinki na wadda ta ta6a aure”.
Nanma bata iya cemasa komaiba, amma yanayinta yabashi amsar tambayarsa.
Numfashi ya sauke, “To koba'a amsamin a bakiba nasamu sak'on zuciya, ALLAH yay miki albarka, kunya adone na d'iya mace, hakama jan aji mayafine Na kimarku, kin kuma tabbatarmin kinada banbanci da zawarawa na yanzu, wad'anda suke ganin sunsan komai idonsu abud'e yake akan namiji, Abu nabiyu shine inada Mata, kuma maganar gaskiya inasonta sosai, saboda tanada halaye Na kwarai da tarbiyya, sannan bata gazamin a komaiba Na rayuwar zamantakewa da hak'k'ok'ina na aure, hasalima har yanzu amarci muke dan aurenmu bazai gaza watanni shida ba zuwa bakwai, to ban saniba ko malama Jiddah zataso tsoho mai mata”.
Kan jiddah a k'asa, ko kad'an kalamansa basu Sosa rantaba, dan duk jarumin namiji Na kwarai bazai tozarta uwargidansa agaban ta wajeba, hakannema yakuma saka Mata kwanciyar hankali akan aurensa, ko anan gaba bazataji shakkaba idan zai k'ara ta uku akan itama zai tozartata. Cikin sanyinta tace, “Duk namijin kwarai shike mutunta matarsa ga macen waje, halayen matarka sun birgeni, kuma ina addu'ar ALLAH yabani ikon yin koyi da ita, dakuma girmama ta amatsayin wadda take a gaba dani”.
“Masha ALLAH, Alhamdllh, ALLAH yay miki albarka, yanzukam hankalina yasake kwanciya, ina kuma miki albishir da samun soyayya tsaftatacciya agareni inhar kika girmama zaman lafiya tsakaninki da matata insha ALLAH, sannan Zan kasance mai adalci a tsakaninku da yardar ALLAH, fatana muyi koyi da rayuwar aure irinta gidan MANZON ALLAH (S.A.W)”.
“Insha ALLAHU”.
“ALLAH yay muku albarka, bara na barki haka kije ki huta, inaga sai bayan an d'aura aure kuma insha ALLAH zaki kuma ganina saboda sabgogina yawane dasu, mikike da buk'ata na shagalin biki?”.
“Bana buk'atar komai, dan babu abinda zanyi”.
“Haba dai malama Jiddah, kod'an rawan coge d'innan Na Mata bazakuyi a cikin gidaba”.
Dariya yabata wai coge, amma saita danne batayiba, sai murmushi datayi Wanda harya bayyana fararen hak'oranta a fili.
“Kin iya murmushi haka ashe amaryar Aliy? amma jan aji yasa ba'a ta6amin naganiba tunda muke had'uwa?”..
Da sauri Jiddah ta kudundune kanta a hijjab, shima ya mik'e yana fad'ad'a murmushinsa. “Tunda rowa akemin bara nayi gida matana tamin”.
Ita dai Jiddah takasa d'agowa, takula yanada yawan tsokana, amma a fuska saikaga tamkar baya magana ma.
Kujerar dake d'an kusa da ita kad'an ya sake zama, addu'a yaymusu kafin ya kuma mik'ewa yana fad'in “Na barki lafiya”.
Batare data d'agoba tace, “ALLAH ya tsare, ka gaidamin auntyna”.
Yaji dad'in maganarta, dan haka ya amsa da amin ngd, auntynki kuma zataji, kafin ranar juma'a kuma kid'an canja dan ranar babu y'ar nesa-nesa..”.
Ya k'are maganar ahankali bayan yad'an duk'o kusa da ita kad'an.
Sosai jikinta yake tsuma saboda jinsa kusa da ita, ga k'amshinsa yakuma mamaye hancinta, ta takure jikin kujera sosai har saida ya fita sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya”.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gidan Malam Aliyu kam da yamma saiga Aminatu k'anwarsa dasuke uba d'aya, d'iyar iya habi mai ruk'on Maimunatu, sai kuma yayar maimunatun Hassana.
Tarbar mutunci tai musu, bayan takawomusu ruwa ta zauna suka gaisa.
Aminatu ta kalli maimuna baki a ta6e tana fad'in “Miya samu idonki nagansa jajur kuma a kumbure?”.
Dariyar yak'e maimuna tayi, sannan tace, “Babu komai Aunty Amina, kawai dai kinsan bajin dad'in jikin nakeba”.
Kallon juna Amina da Hassana sukayi suka ta6e baki, Hassana ta maida kallonta kan maimuna, “To Uwar y'an zurfin ciki, auren na Mijin nakima 6oyewa zakiyi? To ai kin makaro, dan kowa yasani, yanzunan maimuna sabodake wawuyace zama kikai kina kwad'a kuka saboda za'ai miki kishiya?, kishiyarma bazawara, to wlhy idan zaki mik'e ki mik'e, kuka babu maganin ubanda zai miki, ni bammasan sanda zakiyi hankaliba kekam.....”
“Ke wlhy da hankalinta, son mijine kawai, kinsanfa ita batason laifin Yaya Aliyu saboda shine autan maza”. Amina takatse Hassana tana huci.
Maimuna ta share hawayen da suka zubo Mata, wad'anda dama suta yini yi, bayan fitar Aliyu dayace mata zaije wajen amaryane Yakuma tunzura kukanta, shinema suka iske tanayi, jin sallamarsu tai saurin zuwa ta wanke fuska ta shafo fauda, “Haba Aunty Amina yakikeson nayi, Zan hanashi yayi aurene?”.
“Bakuwa zaki hanashiba wawuya kawai, yoke banda kin rako Mata duniya wata shida da aurenku kacal kizauna a dank'aro miki kishiya? Wato ya Danna miki ciki amfaninki yak'are shine zai auro wata ko? To wlhy kibud'e kunne kiji bayani, idan zaki mik'e kitada masa hankali ki haukace masa, duk yanda ya taroki kice bakisan zancenba.....”
”Hummm, aunty Hassana kenan, da hauka Na hana namiji k'aro aure da mata da yawa sun tsira daga kishiya, da asiri Na Hana maza aure da wasu matan ba'ai musuba, yakamata muringama kammu adalci kafin ai mana, idan mun hana mazajenmu aure yazamuyi da y'ay'an da muka Haifa?, Kituna yanzu haka mamanmu yara hud'e kannenmu Mata agabanta, idan munce mazanmu bazasu auro mana wasuba, su wanene zai auresu?, dukma ba wannanba, shin munada tabbacin kaiwa darene dahar mukeda kwarin gwiwar Hana abinda ALLAH ya halatta?, kuyi hak'uri inason mijina, kuma ina matuk'ar kishinsa, amma hakan bazaisakani bijire masaba Na lalata alak'ata da Ubangijina akan son zuciya, kishi gaskiyane amma bata mummunar hanya yakamata mu Mata mu jagoranceshiba, kamata yayi Ku koyamin yanda Zan kuma damk'e zuciyarsa, Na zama tauraruwa a garesa ba yanda Zan tsinke igiyar aurenaba, iyayenmu babu wadda bataje ta tadda kishiyaba, miyasa su iyayensu basu k'i aurar dasuba saboda zasu iske wata? Saimu da za'azo a iskene zamuce bazai yuwuba?.......”.
“Kinga Amina taso mukama gabanmu kafin tace mana y'an wuta”, Hassana tafad'a tana mik'ewa.
”Wa'iyazubillahi aunty Hassana, mak'iyinama bazan dangantashi da wutaba balle ku”.
Basu tanka mataba suka fice, duk kiransu datake ta biyosu har gate basu sauraretaba.
Kuka tayi sosai akan hakan, a ganinta bai cancanci manya dasu su kawo mata rabuwar hankaliba.
Koda Aliyu ya dawo bata fad'a masaba, shima bai tambayeta ba dukda yakula ranta a 6ace yake, yanayinta kuma ya nuna masa tayi kuka. Kulawa yayta bata yanda hankalinta zai sake kwanciya da sake rarrashinta, dan tunda yaymata zancen aurennan duk sai ta susuce, dukda dai tana dannewa a gabansa.
Hakan saiya k'ara dasa masa k'aunarta da tausayinta, koba komai ya yarda da son da take masa mai nagartane, kamar yanda shima ayanzu yakejin sonta tun bayan aurensu, sokuma Na gaskiya mai gauraye da zallar k'auna.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A 6angaren Jiddah ma ranar kwana tai da tunanin Aliyu, hardasu mafarki.
Komai nasa yamata yanda take addu'a da fatan mijinta ya kasance, fatanta ALLAH yasa matarsa ba irin hajia Deluwa baceba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_RANA BATA K'ARYA_*
Yau take juma'atu babbar Rana, duk tarone Na maza kawai hakan bai hana su Maman Sadiq yin abinci ba dai-dai misali saboda y'an Adamawa maza su kusan goma da y'an barno biyar da sukazo d'aurin auren, a Mata kam gajiram da yaruwaiya ne kawai sukazo (Yayar Umma, da k'anwarsu wadda Balu ke bimawa).
Abba zakari dai baisan hidimar da akeba, amma har gida Uncle yahya yaje yacemasa yashiryo suje d'aurin auren wani yaron malam Abdul-ra'uff, da farko cayay akwai inda zaije, amma Hajia Hindu ta saka baki harya amince.
A babban masallacin juma'ar dake anguwar gwammaja sukaje sallah, mamaki ya Kama Abba ganin Kawunansa, Kawu Surajo da bashida 6oye-6oye yafito yasanarma Abba auren Jiddah za'a d'aura yau d'innan, kafin Abba yasamu zarafin magana tawagar malam Abdul-ra'uff data ango suka Iso.
Su Kawu Surajo basubi takansaba suka shiga hidimar tarbarsu, babu yanda ya iya dole yabi ayari dan karyaji kunya, dan manyan malaman sun cika masa idanu, amma daka gansa kasan a birkice yake gaba d'aya, kuma hankainsa baya jikinsa.
Ana idar da sallar juma'a wadda su malam sukayi anan suma aka d'aura Auren *Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina da Jiddah Zakari Yaro* akan sadaki dubu d'ari biyu ciff🤩🥳..............✍🏻
*_Munga idi, ya za'ayi da Abba zakari da Alhaji Garba kenan🙆🏻🤭?._*
*_⛹♀🧳kayana a shirye suke nayin hijira walla, kad'an daga aikin Abba ya lallasa gayu🤣🤣😝_*
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d'in na sama sisters, Abban dausayi YouTube channel tv😄🤝🏻_*
*_Ubangiji yabama d'an uwan momin khairi malam Adamu lafiya, bisaga had'arin mota da yayi, muna barar addu'arku. Dama dukkan y'an uwa musulmi dake kwance sanadin ciyo😿🙏🏻_*.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[31➖32]_*
............Can na hango muku ango Sheikh Aliy shar cikin d'anyar shadda gizna ruwan toka mai haske, sai zabga k'amshi yake yana gaisuwa da jama'a da suketa masa ALLAH ya sanya alkairi, yau d'imma dai baka isa shaida yanayinsa ba tamkar lokacin aurensa da maimuna.
Yazo ya gaida su Abba da gaba d'aya jinsa ya barsa, sama-sama yakejin hayaniyar mutane, koda Aliyu na gaisheshi saida Kalla ya zunguresa sannan ya amsa cikin alamun baya a hayyacinsa.
Shidai Aliyu ya gaidashi cikin mutuntawa tareda masa godiya ya mik'e
Aliyu Na barin wajen Abba ya fisgi hannun Uncle yahya sukai baya inda babu jama'a.
“Yaya wai miya farune kaketa jana? ina zaka kainine?”.
Banza Abba yay masa bai tankaba, kuma bai Saki hannunsaba. Sai da suka Isa can bayan k'aramin d'akin da Gen......take Na masallacin, Sannan ya sakeshi tare hankad'a Uncle yahya jikin bango ya shak'eshi. Da farko Uncle yahya ya tsayane yaga iya gudun ruwan Abba, amma ganinfa da gaske yake saiya shiga k'ok'arin rik'e hannunsa domin kare kansa, amma Sam Abba yak'i sakinsa, sai kuma k'ok'arin shak'arsama yakeyi, tuni kiciniya ta 6arke a tsakaninsu.
Kawu Surajo dayaga fisgar da Abba yayma Uncle yahya ne yaji zuciyarsa takasa nutsuwa, dan haka yabiyo bayansu...
“Subahanallahi, Zakariyya! Kanada hankali kuwa? 'Dan uwan naka zaka kashe? Miyaymaka?”. ‘Kawu Surajo yay maganar yana kiciniyar kwace Uncle yahya daga hannun Abba’.
Uncle yahya ya k'yale Abbane kawai amma badan yafi k'arfinsaba, Abba dai bai Saki Uncle yahya ba saida Kawu Surajo ya maresa, saurin sakin Uncle yahya yay yana kalon Kawu Surajo dake huci (dan shima akwai zuciya dam) hannunsa dafe da kuncinsa yace,
“Kawu shine zaka mareni?”.
“An mareka d'in kozaka Rama? Waishin Zakariyya mikakeson zama kaikam a rayuwarka? A ina ka gado wannan halinne? Wlhy mahaifinka bashida wannan bak'ar halayyar taka, hakama Mahaifiyarku, girma kake kullum amma halin yara da rashin sanin yakamata yakasa barinka, kanason gamawa da duniya lafiya kuwa?”.
Cikin harzuk'owa Abba yace, “Yaza'a dakeni sannan a hanani kuka? Yazaku zauna Ku k'ulla munafuncin aurarmin da yarinya sannan ace bazanyi maganaba?, Jiddah dai nina haifi abata bawani ya haifarminba, wlhy yahya kayi maza ka saka ya sakarmin yarinya, bashi nai niyar bawaba kuma bazan bashiba, inko ba hakaba wlhy saina maka rashin mutuncin dabaka ta6a tunaniba”.
Kawu Surajo zaiyi magana Uncle yahya ya dakatar dashi ta hanyar fad'in kaga “Kawu barshi, nima Zan bashi amsa dai-dai dashi, domin Yaya bai cancsnci kowacce irin girmamawa ba agareni yanzun. Yaya a wannan Karon bazan maka shiruba kamar yanda Na Saba, kaimin dukkan abinda zuciyarka ta fad'a maka dai-dai, sai dai kuma kasani Wannan auren yayi k'ulluwar da insha ALLAHU mutuwace kawai zata rabashi, duk kuma abinda kaga zakamin ga fili gamai doki nan, ko kunyar ALLAH bakaji ka saida yarinya akan kud'i kadawo kana hura hancin y'arkace, dan wannan wlhy saidawane, tunda batasan kaje kaci bashinkaba, k'ilama ko sisi bataci a cikiba.....”
Duka Abba yakaima Uncle yahya amma sai Kawu surajo ya janye Uncle yahyan yana fad'in ”Kaga yahya barsa muje kawai, wannanma kad'ai ta isheshi, yaje ya nemawa masu kud'i kud'insu”.
K'iri-k'iri Abba yashiga mulmulo ashariya yana nakama Uncle yahya da tabbatar masa saiyayi dana sani, kuma aurene saiya rabashi.
Badan wajen babu kowaba kam dasun tara y'an kallo bana wasaba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gida kam Jiddah duk sai tayi wani sukuku, duk tsokanar dasu Aunty Nafisa kemata bata kulaba, dayake ba taro za'ayiba batayi wani kwalliyaba, tadaiyi wanka ta saka sabon d'inkinta. Zaune take a d'akinsu ta zuba tagumi tana tunanin rayuwa, wai itace aka d'aurama Aure sau biyu cikin shekara d'aya, rayuwa kenan, mai tafiya da jarabawa.
Dukda ba taro za'ayiba gidan nasu yad'an cika da makwafta, koda y'an d'aurin aurema suka dawo sai akaita bud'e-bud'e, wad'andama basu shigoma suka shishshigo sunama Umma ALLAH ya sanya alkairi.
★★★★
Bayan su Uncle yahya sungama cin abinci suka shiga tattauna batun Abba da yanda zasu 6ullo masa.
Ana cikin wannan magana saiga y'an sanda sunzo tafiya da Uncle yahya Abba yakai k'ararsa akan ya aurar masa da yarinya batare da saninshiba.
Wannan lamari kam ya girgiza kawunnansu sosai, batareda an Bari su Umma dake cikin gida sun saniba Uncle yahya dasu Kawu Bilya sukabi y'an sanda station.
Acan ma suka iske Abba a Office d'in d.p.o .
Jin da d.p.o yayi zancene Na family saiyay nufin sulhuntasu a office d'insa, amma sai Abba yace Sam bai aminceba, shidai kawai akira sheikh Aliyu yanzunnan ya sakar masa y'arsa.
Su Kawu Surajo kuma sukace bai isaba yayi kad'an. Nanfa rikici ya hark'ume sosai, babu Wanda Abba yake hara sai Uncle yahya, yayinda kuma yake datsama Su Kawu dukkan maganar datazo a bakinsa, har dare suna station ana abu d'aya, su kamsu police d'in yau dukkan aikinsu ya tsaya rikicin su Abba ya d'auke hankalin kowa.
Shi d.p.o jin Mijin da yarinyar ta aura yasakashi k'in goyama Abba baya, dan aganinsa babu wani mutumin kirki dazaice baya buk'atar had'a jini da Malam Abdul-ra'uff maina a k'asarnan, musamman ma ace d'ansa Sheikh Aliyu ne Mijin. Shiyyasama yak'i amincewa akira sheikh Aliyun, dan aganinsa zubar da kimane ga Abban.
Dadai d.p.o yaga kansa na Neman d'aukar zafi sai kawai yayma yaronsa inkiya da ya nemo masa maganin barci a lemo ko ruwa, babu dad'ewa kuwa yakawo lemo. Abba kawai akaba, ganin hakan yasaka Abba kuma yin fad'i irin shi an girmamasa, dandanan yafara zuk'ar lemo yana kumfar baki, ba a wani ja dogon lokaciba ya kife a tebirin ya hau barci.
A wajen babu Wanda bai sauke ajiyar zuciyaba, kafin su Uncle yahya sushiga yima d.p.o godiya.
“Ai babu godiya a tsakaninmu, domin wannan yima Kaine, Na fahimci Alhaji baya tare da hankalinsa yanzu, wane ubane mai mutunci ALLAH zai masa wannan ni'imar ya bijire?. Shekaranjiya muka gama makamancin irin Case d'innan naku, shima Uban bayason yara mata, ya watsar dasu uwarsu Nata wahala dasu, sai yanzu cikin y'ay'an wata ta auri mai arzik'i shine yadawo zaima uwar fin k'arfi, itako tace Sam bai isaba, rikici dai ya kawosu har nan. Wato shawarar dazan Baku shine kusami likitan dazaita dank'ara masa allurar barci daganan harta tare gidan mijinta, dan baima kamata kubari gidan malam suji wannan shirmen nasaba wlhy, kodan Ku nemama y'arku mutunci, lokacin dazai dawo hayyacinsa rikicinsa da wancan Alhajinma ya isa ya d'auke hankalinsa”.
'Dari bisa d'ari sun gamsu da shawarar d.p.o, dan haka sukaita zubamasa godiya da fatan gamawa da duniya lafiya, kafin y'an sanda suyi kama-kamar Abba sukaishi mota.
Har gida su Uncle yahya suka kai Abba, Hajia Hindu zatai musu hauka suka taka Mata birki akan baida lafiyane, likita zaizo ya ringa dubashi.🤣
★★★★..
Su Uncle yahya basu fad'ama kowa halin da ake cikiba har Umma, dan basason 6ata musu farimcikinsu.
Washe garima su Kawu Surajo suka juya bayan sunma Jiddah Nasiha mai ratsa jiki, akan ta Zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamanta, dan a wannan auren sunA k'yautata Mata zaton alkairi da samun kwanciyar hankali mai d'orewa har abadan insha ALLAH. Tadai sha kuka sosai.
Su Yaruwaiya dai nan aka barsu, dansufa da shirin gyaran y'arsu Jiddah sukazo, dan haka tun a washe garin d'aurin aure suka fara gyara Jiddodon Uncle lungu da sak'o, dansu duk zatonsu jiddar tarasa budircinta a aurenta Na farko, itakuma dayake ba yawan surutune da itaba takasa fad'ima kowa babu abinda yashiga tsakaninta da Alhaji Garba, sai dai a gefe kuma Umma datasan halayen yaranta kaf tuni ta fahimci Jiddarta har hanzu budurwace.
Umma na mamakin rashin zuwan Abba gidan, harma takasa hak'uri ta tambayi Uncle yahya, shine yace Mata bashida lafiya. Tsakanin Mata da miji sai ALLAH, duk sai ta damu kanta kuwa, harma ta matsa akan zata dubashi Amma Uncle yahya ya bata shawarar tayi zamanta, daga baya kuma saiyaga yadace suje d'in kodan kauda hankalin mutane..
Gaba d'ayansu gidan da iyalin Uncle yahya suka rankaya duba Abba, dukda ma sun iske yana barci, hajia Hindu sai cika take tana batsewa. Babu Wanda yabi takanta a cikinsu in banda Balu da taita yanka Mata habaici ita da Gajiram, sai da Umma ta tsawatar musu da harshen kanuri, duk dariyar dakecin Zarah da walida basuyiba, dan wannan ba tarbiyarsu bace saka Kansu a hurumin manya, tun suna k'anana Umma bata ta6a basu damar cin zarafin hajia Hindu ba ko Mata rashin kunya, koda kuskure kayi hakan kuwa ranar zakaci uwaka wajen Umma.
Tsakanin su Umma dasu kalifa kuwa babu ko gaisuwa, hasalima d'auke Kansu sukai suna cigaba da kallon ball d'insu da hayaniya da uhu kamar basu ga su Umma ba. (Sun manta Ubansu Na kwance🙆🏻😓).
Suma su Jiddah babu Wanda yashiga harkar yaran.
Garama Umma tamusu magana suka wani basar da ita, kuma sarai sunsan matsayinta a gunsu, Itama daganan saitayi shiru. Kuma hajia Hindu naji da kallonsu amma bata tsawatar musu ba.
Basu wani dad'eba suka taho, kuma ko a Hanya Umma Hana kowa maganarsu tayi balle asamu Na saka zuciya 6acin rai.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Maimunatu dai ta kuma kwantar da hankalinta a gaban jama'a da mijinta, amma inhar tana ita kad'ai takansha kukanta ta k'oshi, kullum kuma addu'arta shine ALLAH ya k'ara Mata dangana da juriya, yakuma basu zaman lafiya da amarya.
Ko'a ranar d'aurin auren da kanta ta shirya Aliyu, shikam yanata saka Mata albarka da kuma nuna Mata tsantsar k'aunar da yake mata. Amma yana fita saboda kiranda Malam mustafa kemasa a waya saita rushe da kuka, shikenan yau mijinta yazama nasu su biyu, komansa yanzu saita raba da wata.
A wannan halin Aunty Ruk'ayya da Aunty Siyama sukazo suka isketa, zama sukai suna lallashinta da Mata nasiha mai ratsa jiki, hakanne yasaka Mata jin sanyi a ranta, koba komai y'an uwan mijinta suna k'aunarta.
Su Hassana da sukazo sai sukai turus ganinsu Aunty Ruk'ayya a gidan, hakanne yasaka suka Kama Kansu.
Suna a gidan harsu Aliyu suka koma daga d'aurin aure, nanfa suka shiga masa addu'ar ALLAH ya sanya alkairi da fatan zaman lafiya.
Dukkan wani zumud'i ya danne a binsa a zuciya yanda ran matarsa bazai sosuba, daga k'arshema yaja abarsa suka shige d'akinsa ya hau lallashi, dan yakula tasha kuka, idonta kawai sun Isa shaida. Hakan dayay Mata saiya sake bata nutsuwa harta d'an Saki jikinta ma.
Har dare su aunty Siyama Na gidan, harma da sauran y'an uwansu da Matan yayyensu da sukaita zuwa daga baya. Wasa-wasa dai sai sukasha wani d'an k'aramin shagali a cikin gidan, Wanda kowa yake bama Maimunatu kulawa da nasiha tareda fatan zaman lafiya, bakuma su munana amarya ko k'intaba ko sau d'aya a gabanta, kowa dai Na fad'a Mata ta rik'e girmanta shine mutuncinta ga miji ga abokiyar zamanta harma dasu danginsa.
Aliyu kam tuni yabar musu gidan dayaga sunfara cika, bai dawoba sai dare.
Akuma lokacinne yakejin yakamata koda a wayane yaji muryar Jiddah, dan yanzu dai hak'k'inta yarigada ya rataya a wuyansa dukda bata tareba.
Amma kokad'an baibari wannan tunani yayi tasiri a ransaba dahar zai hanashi bama matarsa kulawa, koma a fuska bai nuna Mata yana tunanin Jiddah bane, saima ita dataketa yawan sakko sunan Jiddah a hirarta, harma ta tambayi number ta.
Kwanciyarsa ya gyara yana kallonta, “Maimoon k'anwar nan takifa banyi zaton tana rik'ema wayaba gaskiya”.
“Haba dai Yaya miyasa?”.
“Ban saniba nima, sai dai inaga daga gidansune suka hanata, kinsan wayoyinne yanzu sunada tasu illar suma, shiyyasa wasu iyayen kan Hana yaransu rik'ewa har sai sunyi aure”.
“Hakane kuma, nikam banga laifinsu ba, dukda hakan ba shine zai tsare maka yaroba, amma to yanzu dai yakamata a barta ta rik'e”.
“Insha ALLAHU zanyi k'ok'ari a saya Mata koda k'aramace kafin abubuwa su warware, dan a tsakaninan banida wani isashshen kud'i Maimoon, inaga aikinnan da aka bani nak'i Zan koma Na kar6a, dama ganinai nauyin zaimin yawa, kuma dai-dai gwargwado dai sana'ar magungunan nan tana rik'emu, ga wadda Adeel ke mana a saudia, to amma yanzu nauyi ya k'aru, inaga sai nahad'a da aikinnan kodan nasamu damar sauke nauyinku”.
“Yaya bazance maka a'a ba, amma Zan saka lamarin cikin addu'a ALLAH ya za6a mana abinda yafi alkairi”.
“To Amin matata”. Aliyu yay maganar yana jawota jikinsa ya rungume.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Alhaji garba baya gari, dan haka baisan wainar da ake toyawa ba akan auren Jiddah, matarsa kuwa koda wasa bata sanar masaba ko a waya, dukda ita kuwa tanajin komai a wajen hajia Hindu, harma rashin lafiyar Abba da hajia Hindu batasan sirrinba saida hajia deluwa taji.
**********
Washe gari da yamma lik'is Abba ya farka, sai dai jikinsa duk babu wani k'arfi.
Ganin ya farka hajia Hindu ta Kira Uncle yahya kamar yanda ya buk'ata.
Uncle yahya najin haka yakira doctor Abbas doguwa akan yaje Abban ya farka.
Doctor Abbas kwararren likita a asibiti. Aminu kano, Wanda d.p.o ya had'asu Uncle yahya dashi. Yanajin shirin da sukai akan Abba saiya canja musu shawara akan baza'a masa Alluraba barciba, dan zata iya cutar dashi, zai dai bi wata hanyar ya tsarashi.
Wannan daliline yasa koda Dr Abbas yaje duba Abba saiya sanar masa jininsa yakai k'arshen hawa, a zahiri kuma jinin Abban yahau k'ololuwa, Dr Abbas ya k'ara da fad'in “Alhaji inhar kayi wani hayaniya zuciyarka zata iya bugawa, kuma komai zai iya faruwa, mutuwa ko mummunan ciwon dayafi Wanda kake ciki yanzu, dan haka kahuta a gida tsawon kwana goma mugani, koda wanene yazo nemanka ace bakanan, idankuma ka amince inada inda Zan kaika ka huta”.
Da hanzari Abba yace, “Dr kakaini koma inane, hakanne kawai zaisa Na tsira daga Alhaji garba, danshi kad'ai ya Isa yasani bak'untar kabari yau-yau d'innan”.
“To shikenan Alhaji babu damuwa, ALLAH ya k'ara lafiya”.
Wannan dabara ta likita itace tasaka aka samu damar killace Abba waje guda domin asamu Jiddah ta tare gidan mijinta lafiya.🤩
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A washe garin d'aurin auren Aliyu bai samu shigowa wajen Jiddah ba, saboda zazza6i da amai da Maimuna taita fama dashi, saida aka maidata asibiti aka k'ara Mata ruwa sannan tad'an samu k'arfi-k'arfi.
Kwana biyu da d'aurin auren ya Kira Uncle yahya ya sanar masa zaizo.
Dan haka Uncle yahya shima yaje ya sanarma Jiddah dakeshan gyara itama.
A gida kuma ya saka Maman Sadiq ta shiryama malam Aliyu abin tarba dukda yace zuwan dare zaiyi.
★★★★★
Da taimakon Maimuna dake fama da kanta ya shirya, dan yanzu tarigada ta shagwa6ashi da komai sai an masa.
Yayi matuk'ar yin k'yau cikin boyal blue mai duhu sosai, hakama hularsa blue sai takalmi bak'i, sosai Maimunatu ta zazzage masa turarurruka har saida ya kwace yana fad'in “Malama ya isheki haka, sokike ki karyamin tattalin arzik'in turare ne?”.
Cikin dariya Maimuna tace, ”Haba dai Yaya, yada saurin karaya haka? Indai turarene zamu saka maka a lefe nida k'anwata Jiddah, kasanfa mu maza Na had'a lefe to mu mune zamu had'a maka wannan karon tsabar kaid'in d'an gatanmu ne”.
“A haba dai tawajena da gaske? To kinga k'ara zazzagamin kawai”. ‘Yay maganar yana mik'a Mata kwalaben turarurrukansa’.
Dariya sosai Maimuna ta sanya masa, “Oh ni Yaya, ashe dama malamai sun iya son bati suma?”.
Murmushi yayi har hak'oransa Na bayyana, ya damk'i hannunta yana matsawa yanda zataji zafi “Sake fad'e naji”.
“Wayyo Yaya ALLAH da zafi, idan ka tsinke hannun maga Wanda zaima girki a gidannan, dan k'anwatama bazata makaba”.
“Ahaf yarinya, basai naje Na auro Nana Hafsat (miss Xoxo) ba, dama kullum saitamin massage Na soyayya safe da yamma, dukda nace Mata matana biyu tace ko uku ne zatazo ata hud'u dan tsabar k'aunar da takemin”.
Cikin had'e fuska Maimuna tace bazazzage zaka zama kenan? To ALLAH kama fad'amata ta kiyayeka, kai d'in mijin mace biyune kacal insha ALLAH, dan naji su Yaburra har suna yad'awa a gidan Alhaji khaleel mai mota dakaje duba y'arsa Islam cewa zaka auri Hafsat d'in, damadai shiru namaka naga gaskene?”.
(Zazzagawa bayinmufa akwai son Mata da gaske uwargidan malam😝⛹♀)
Hannu yakai zaikuma damk'ota ta gudu bayi tana fad'in “Wlhy katafi k'anwata Na jiranka, inba hakaba nakirata nace karta baka ruwa mai sanyi”.
Dariyar dabai shiryaba yad'anyi, kafin ya juya ya fita yana d'aura agogonsa da fad'in “Habawa yarinya Zan kamakine, saikinmin bayani dalla-dalla idan Na dawo ai”. Zuciyarsa cike take da farin ciki dakumajin k'arin k'aunar Maimunatu a ransa, gefe d'aya Na zuciyarsa Na ayyano masa yanda zai iske amaryar tasa mai idon kuka.............✍🏻
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*_Sisters mai buk'atar Raina Kama a audio zai iya bin wannan link d'in Na sama, Abban Dausayi YouTube channel tv🤩🤝🏻_*
*_Saura naji wani yace Abba Zakari ya zare kuma😑😏🙄🤣😂🙆🏻🚶🏻♀🤺_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[30➖31]_*
..............dajin an daura aure da jidda abba ya yanke jiki yafadi 🏃🏿♀🤣🤪🤓 nima shinake jira
...........Shirye-Shiryen biki dai ya kankama, dukda aure kawai za'a d'aura biki sai satin sama, dangima mazane kawai zasuzo d'aurin aure, mata kuma sai ranar tariya.
A wannan Karon kam dolene ka fahinci ana biki gidansu Jiddah, dukkan tanadin da Umma keyi Na kayan d'akin y'ay'anta ta fiddo Na Jiddah fili, abinda babu kuma ta had'a y'an kud'ad'enta Aunty Nafisa da Maman Sadiq ɖa Balu suka shiga kasuwa.
Uncle yahya ma yanata shirinsa akan kayan gado, dan baimayi tunanin Neman Abba ba balle ya tunkareshi.
A 6angaren Jiddah kam tanajin k'aunar Sheikh Aliyu, amma kuma batajin son auren kwata-kwata, duk d'okin da y'an uwanta keyi kallonsu kawai take, babban ma abinda ke damun ranta da akace yanada Mata, tana tsoron komawa Y'ar gidan jiya gaskiya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Duk suna a tsakar gida, Umma da Balu suna kan tabarma, Balu na yima Umma kitso suna hirarsu ta zuminci, sai Jiddah dake yankan alayyahun da zasuyi miyar taushe, Zarah Nata aikin tuwo daga can k'ofar kicin.
Da sallama Walida ta shigo hannunta rik'e da madaidaiciyar bak'ar leda data sayo kifin miya, kallo d'aya zakai Mata ka fahimci tagaji.
Duk sannu sukai Mata bayan sun amsa Mata sallama, ta ajiye ledar a gaban Jiddah tana fige hijjabinta ta jefe saman igiya sannan taje kusa da su Umma ta zauna tana fad'in “Wash ALLAH k'afafuna”.
Balu tai Y'ar dariya “Sannu Walida, kona goyakine? Naga kin gaji”.
“kai Aunty A'a na hutashsheki, kawai gajiya nai da tafiya, ga wani shegen Mai naci daya nanuk'emin tundaga titi har k'ofar gidannan”.
“Tofa, auta kice dai Umma tayi suruki”.
“Kai Yaya Jiddah dan ALLAH, ni wlhy ban fad'aba”.
Dariya Zarah dake k'ok'arin tuk'a tuwo takeyi tace, “O su walidatu an kusa aure ashe”.
Umma ta zubama Zarah harara tana fad'in “Ya isheku hakanan malamai, yanzu zaku tasomin yarinya gaba ko huce gajiyar wahalar da kuka sata batayiba, tama dawo kod'an ruwa baku bataba”.
“To Umma naga ai da ita za'aci?”.
“Yo Yaya Jiddah tamafi kowa lauma ai”.
“Gaskiyarki kuwa Zarah”.
Dariya itadai Balu take musu, dan tsarin yayarta da y'ay'anta Na matuk'ar birgeta, idan sun Mata laifi zata tsawatar musu tamkar bata sansuba, amma hakan bazai hanata ta Saki jiki dasuba tamkar k'awarsu, hakanne yasa take saurin gano matsalarsu, suma kuma basa iya 6oye Mata komai nasu.
“Yaya Jiddah Ku tsaya, nifa dukma ba wannanba, Naga matar Alhaji garba a kasuwa yanzunan, sannan tare Na ganta dawata Y'ar budurwa, amma alamun yarinyar baimin Kama da y'artaba kamar mai aiki”.
Jiddah dake kallon Walida itadasu Umma tace, “A kwarai akwai mai aiki agidan Bilki”.
“Kai Yaya Jiddah, amma shine baki fad'aba, duk wannan kullawa da kwancewar da mukeyi kullum akan yanda za'a zak'ulo abinda ta binne a kanki”.
“Humm Zarah kenan, ni nama manta da Bilkin wlhy, sannan kuma ma munada tabbacin bilkisun zata taimakemu”.
Umma tace, “Wannan gaskiyane Jiddah, tunda dai kunga tare muka gansu, kamar dai yanda Uncle d'inku yace mubi komai a sannu to mubi d'in, insha ALLAH komai yanada iyaka, yanzuma mungode ALLAH tunda abubuwa sun dai-daita sosai”.
“Hakane Umma, ALLAH ya datar damu dai”.
Balu zatayi magana sukaji sallamar Uncle yahya, hijjab Umma tajawo ta saka sannan tace, “Uncle d'insu ka shigo”.
Uncle yahya ya shigo, zama yay inda Walida ta saka masa tabarma, bayan duksun gaidashi har Balu suka gaisa da Umma ma.
Kallonsa ya maida ga Jiddah dake bakin rijiya tana wankin Alayahu da kifi. “Jiddah ki shirya Sheikh Aliyu zaizo anjima kad'an, dan yacemin bayan la'asar idan ALLAH ya kaimu”.
Kai Jiddah ta duk'ar alamar jin kunya, sai Balu ce ta amsa da “ALLAH ya kaimu”. Amma Jiddah ta kasa.
Shima bai damu da rashin amsawar tataba, dan yasan duk y'a mai tarbiyya za'a sameta da kunya.
Mik'ewa yay yana kallon tuwon da Zarah ke gyarawa bayan ta tuk'a, “Fati a ajiyemin tuwonan Zan dawo naci”.
Zarah tace, “To Uncle, kamar kasan kuwa miyar taushece dama kanaso”.
“A'a lallai yau saina kasa tashi kenan ashe, Walida kidafa zo6o saboda bak'oma, kar6a wannan”. Yay maganar yana mik'a mata dubu d'aya.
Zuwa tai ta kar6a hannu biyu tai godiya, shima yaymusu sallama yafita suna masa addu'ar dawowa lafiya.
★★★★★★
Balu da kanta ta tsare Jiddah tayi wanka gab da la'asar, sai zum6ure-zum6ure takeyi su Walida namata dariya, da Zarah tace zata Mata kwalliya saita sanya musu kuka.
Umma ma dai har dariya tayi, “Wlhy Jiddah kinji haushi, ke komai abin kukane a wajenki? Humm gidan dai kishiya zakije, saikije da miji yamiki Abu ko abokiyar zamanki kihau kuka”.
“A'a wlhy bazatayiba, yanzuma su Zarah d'inne suncika takura, tunda tace bataso basai subartaba”.
“Yo Balu ayi mace babu kwalliyane a rayuwa?”.
“Ai zata ringayi insha ALLAH”.
★★
Anayin Sallar la'asar Uncle yakira Umma akan ta turo Jiddah gidansa.
Hijjabinta ta zabga har k'asa da nik'af, walida taimata rakiya hannunta d'auke da k'aramin basket da aka saka zo6o.
Gidan babu kowa sai Uncle yahya dan Maman Sadiq tafita gidan suna tunda safe, gaidashi sukayi, walida tafita kicin ta shirya zo6on akan tire ta had'a da ruwa.
Zamansu baifi Na minti 5 ba Sheikh Aliyu da malam mustafa suka Iso. Uncle yahya yafita yashiga dasu seatroom d'insa dayasha gyara yanata tashin k'amshi.
Gaban Jiddah babu abinda yakeyi sai fad'uwa, har Walida taje takai musu ruwa ta dawo tace taje suna jiranta.
Idonta cike da kwalla ta fita, dan Walida ta kwace Mata nik'af, gabanta na dukan tara-tara ta isa, saidai kuma takalmi d'aya tagani bak'i, abin yabata mamaki, dan walida tace Mata su biyune, kuma Uncle yahya ma yana can.
Ganin batada mai bata amsa saita danne zuciyarta tashiga da sallama.
Sheikh Aliy dake zaune cikin kujera sanye da wani lallausan farin yadi daya d'au guga ya kwanta luf, sai hularsa Zanna, k'amshin turarirrikansu dukya mamaye falon. Cikin sassanyar muryarsa ya amsa mata sallamar yana d'ago fararen idanunsa akanta.
Kanta a duk'e yake, dan haka baya ganin fuskarta sai kad'an. Daga can farkon k'ofar ta zauna a k'asan kafet, muryarta nad'an rawa tace, “Sannu da zuwa ina yini”.
Numfashi yad'an sauke yana gyara zamansa, “Lfy lau, kina lafiya?”.
“Alhmdllh”.
“To Masha ALLAH” ya fad'a idonsa a kanta, komi yake kallo oho. Shiru sukayi Na wani lokaci kafin yad'anyi gyaran murya.
Ba tareda jiddah ta shiryaba ta d'ago kanta ta kalleshi, caraf suka had'a Ido, saurin janyewa tayi ta maida kanta k'asa.
Murmushi yayi yana fad'in “Ahaka ake za6en miji dama?”.
Kuma k'asa tayi da kanta jikinta na wata tsuma. Tsaf ya lura da halin da take ciki, sai tausayinta ya k'ara kamashi, har tunani yake Yaya zasu kwashe idan ya tuno matsalarta......
Tunaninsa ya katse sabodajin tarinta, Wanda da alama yawune ya sark'eta. Ruwan da walida ta zuba masa yasha rabi ya d'auki sauran da hanzari yamatso kusada ita yana jera mata sannu.
Ansa tayi Tasha, idanunta harsunyi jajir sun cika da kwalla, sai kuma jera Mata sannu yake tana d'aga masa kai, saida tarin yalafa sannan yakoma wajen zamansa ganin jikinta na rawa.
“Ki daure kina k'arfafa zuciyarki dan ALLAH”.
Kanta tad'an d'aga tana share hawayen da suka cika Mata ido.
“Magana kuka, karatu kuka, Anya kuwa ked'in jarumace?”.
Batareda ta saniba tad'an turo bakinta, dan taji haushin maganarsa.
“Yi hak'uri Malam, maida bakin nagani, Bari sai nan da kwana uku amma ba yanzuba”.
Bata fahimci ina ya dosaba, amma hakan bai hanata jin kunyar maganarsaba.
Murmushi yasakeyi yana kallon agogonsa silver dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, “Bara nayi abinda ya kawoni, dan wannan hajiyar bata shan inuwa d'aya da jinsina. Malam Jiddah nasan zakiyi mamakin shigowar maganar aurenmu da wuri, gashi kuma maganar so bata had'ani dakeba, wannan hukuncine Na ALLAH dakuma cika burin mahaifina dayay tunkan aurenki na farko, cikin Amincin Ubangiji nima dana ganki sainaga kin cancanci zama matata, wannan yasaka iyayena suka shigo da zafi-zafi, dan hausawa kance da safe ake Kama Fara, anzo nema min izinin neman so a gareki saikuma akamace an bani, na jinjinama dattako da halin girma irin Na iyayenki, dan sun tabbatar mana sud'in iyayene nagari, yanzu dai fatan da zanyi shine ALLAH yasa Na kar6u, karna zama macen shige, Ku mata kunce bata kwarjini”.
K'asa Jiddah tai da kanta takasa magana.
“Ki daure kice wani Abu, dan ayanzu kinada ikon za6arma kanki miji a matsayinki na wadda ta ta6a aure”.
Nanma bata iya cemasa komaiba, amma yanayinta yabashi amsar tambayarsa.
Numfashi ya sauke, “To koba'a amsamin a bakiba nasamu sak'on zuciya, ALLAH yay miki albarka, kunya adone na d'iya mace, hakama jan aji mayafine Na kimarku, kin kuma tabbatarmin kinada banbanci da zawarawa na yanzu, wad'anda suke ganin sunsan komai idonsu abud'e yake akan namiji, Abu nabiyu shine inada Mata, kuma maganar gaskiya inasonta sosai, saboda tanada halaye Na kwarai da tarbiyya, sannan bata gazamin a komaiba Na rayuwar zamantakewa da hak'k'ok'ina na aure, hasalima har yanzu amarci muke dan aurenmu bazai gaza watanni shida ba zuwa bakwai, to ban saniba ko malama Jiddah zataso tsoho mai mata”.
Kan jiddah a k'asa, ko kad'an kalamansa basu Sosa rantaba, dan duk jarumin namiji Na kwarai bazai tozarta uwargidansa agaban ta wajeba, hakannema yakuma saka Mata kwanciyar hankali akan aurensa, ko anan gaba bazataji shakkaba idan zai k'ara ta uku akan itama zai tozartata. Cikin sanyinta tace, “Duk namijin kwarai shike mutunta matarsa ga macen waje, halayen matarka sun birgeni, kuma ina addu'ar ALLAH yabani ikon yin koyi da ita, dakuma girmama ta amatsayin wadda take a gaba dani”.
“Masha ALLAH, Alhamdllh, ALLAH yay miki albarka, yanzukam hankalina yasake kwanciya, ina kuma miki albishir da samun soyayya tsaftatacciya agareni inhar kika girmama zaman lafiya tsakaninki da matata insha ALLAH, sannan Zan kasance mai adalci a tsakaninku da yardar ALLAH, fatana muyi koyi da rayuwar aure irinta gidan MANZON ALLAH (S.A.W)”.
“Insha ALLAHU”.
“ALLAH yay muku albarka, bara na barki haka kije ki huta, inaga sai bayan an d'aura aure kuma insha ALLAH zaki kuma ganina saboda sabgogina yawane dasu, mikike da buk'ata na shagalin biki?”.
“Bana buk'atar komai, dan babu abinda zanyi”.
“Haba dai malama Jiddah, kod'an rawan coge d'innan Na Mata bazakuyi a cikin gidaba”.
Dariya yabata wai coge, amma saita danne batayiba, sai murmushi datayi Wanda harya bayyana fararen hak'oranta a fili.
“Kin iya murmushi haka ashe amaryar Aliy? amma jan aji yasa ba'a ta6amin naganiba tunda muke had'uwa?”..
Da sauri Jiddah ta kudundune kanta a hijjab, shima ya mik'e yana fad'ad'a murmushinsa. “Tunda rowa akemin bara nayi gida matana tamin”.
Ita dai Jiddah takasa d'agowa, takula yanada yawan tsokana, amma a fuska saikaga tamkar baya magana ma.
Kujerar dake d'an kusa da ita kad'an ya sake zama, addu'a yaymusu kafin ya kuma mik'ewa yana fad'in “Na barki lafiya”.
Batare data d'agoba tace, “ALLAH ya tsare, ka gaidamin auntyna”.
Yaji dad'in maganarta, dan haka ya amsa da amin ngd, auntynki kuma zataji, kafin ranar juma'a kuma kid'an canja dan ranar babu y'ar nesa-nesa..”.
Ya k'are maganar ahankali bayan yad'an duk'o kusa da ita kad'an.
Sosai jikinta yake tsuma saboda jinsa kusa da ita, ga k'amshinsa yakuma mamaye hancinta, ta takure jikin kujera sosai har saida ya fita sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya”.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gidan Malam Aliyu kam da yamma saiga Aminatu k'anwarsa dasuke uba d'aya, d'iyar iya habi mai ruk'on Maimunatu, sai kuma yayar maimunatun Hassana.
Tarbar mutunci tai musu, bayan takawomusu ruwa ta zauna suka gaisa.
Aminatu ta kalli maimuna baki a ta6e tana fad'in “Miya samu idonki nagansa jajur kuma a kumbure?”.
Dariyar yak'e maimuna tayi, sannan tace, “Babu komai Aunty Amina, kawai dai kinsan bajin dad'in jikin nakeba”.
Kallon juna Amina da Hassana sukayi suka ta6e baki, Hassana ta maida kallonta kan maimuna, “To Uwar y'an zurfin ciki, auren na Mijin nakima 6oyewa zakiyi? To ai kin makaro, dan kowa yasani, yanzunan maimuna sabodake wawuyace zama kikai kina kwad'a kuka saboda za'ai miki kishiya?, kishiyarma bazawara, to wlhy idan zaki mik'e ki mik'e, kuka babu maganin ubanda zai miki, ni bammasan sanda zakiyi hankaliba kekam.....”
“Ke wlhy da hankalinta, son mijine kawai, kinsanfa ita batason laifin Yaya Aliyu saboda shine autan maza”. Amina takatse Hassana tana huci.
Maimuna ta share hawayen da suka zubo Mata, wad'anda dama suta yini yi, bayan fitar Aliyu dayace mata zaije wajen amaryane Yakuma tunzura kukanta, shinema suka iske tanayi, jin sallamarsu tai saurin zuwa ta wanke fuska ta shafo fauda, “Haba Aunty Amina yakikeson nayi, Zan hanashi yayi aurene?”.
“Bakuwa zaki hanashiba wawuya kawai, yoke banda kin rako Mata duniya wata shida da aurenku kacal kizauna a dank'aro miki kishiya? Wato ya Danna miki ciki amfaninki yak'are shine zai auro wata ko? To wlhy kibud'e kunne kiji bayani, idan zaki mik'e kitada masa hankali ki haukace masa, duk yanda ya taroki kice bakisan zancenba.....”
”Hummm, aunty Hassana kenan, da hauka Na hana namiji k'aro aure da mata da yawa sun tsira daga kishiya, da asiri Na Hana maza aure da wasu matan ba'ai musuba, yakamata muringama kammu adalci kafin ai mana, idan mun hana mazajenmu aure yazamuyi da y'ay'an da muka Haifa?, Kituna yanzu haka mamanmu yara hud'e kannenmu Mata agabanta, idan munce mazanmu bazasu auro mana wasuba, su wanene zai auresu?, dukma ba wannanba, shin munada tabbacin kaiwa darene dahar mukeda kwarin gwiwar Hana abinda ALLAH ya halatta?, kuyi hak'uri inason mijina, kuma ina matuk'ar kishinsa, amma hakan bazaisakani bijire masaba Na lalata alak'ata da Ubangijina akan son zuciya, kishi gaskiyane amma bata mummunar hanya yakamata mu Mata mu jagoranceshiba, kamata yayi Ku koyamin yanda Zan kuma damk'e zuciyarsa, Na zama tauraruwa a garesa ba yanda Zan tsinke igiyar aurenaba, iyayenmu babu wadda bataje ta tadda kishiyaba, miyasa su iyayensu basu k'i aurar dasuba saboda zasu iske wata? Saimu da za'azo a iskene zamuce bazai yuwuba?.......”.
“Kinga Amina taso mukama gabanmu kafin tace mana y'an wuta”, Hassana tafad'a tana mik'ewa.
”Wa'iyazubillahi aunty Hassana, mak'iyinama bazan dangantashi da wutaba balle ku”.
Basu tanka mataba suka fice, duk kiransu datake ta biyosu har gate basu sauraretaba.
Kuka tayi sosai akan hakan, a ganinta bai cancanci manya dasu su kawo mata rabuwar hankaliba.
Koda Aliyu ya dawo bata fad'a masaba, shima bai tambayeta ba dukda yakula ranta a 6ace yake, yanayinta kuma ya nuna masa tayi kuka. Kulawa yayta bata yanda hankalinta zai sake kwanciya da sake rarrashinta, dan tunda yaymata zancen aurennan duk sai ta susuce, dukda dai tana dannewa a gabansa.
Hakan saiya k'ara dasa masa k'aunarta da tausayinta, koba komai ya yarda da son da take masa mai nagartane, kamar yanda shima ayanzu yakejin sonta tun bayan aurensu, sokuma Na gaskiya mai gauraye da zallar k'auna.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A 6angaren Jiddah ma ranar kwana tai da tunanin Aliyu, hardasu mafarki.
Komai nasa yamata yanda take addu'a da fatan mijinta ya kasance, fatanta ALLAH yasa matarsa ba irin hajia Deluwa baceba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_RANA BATA K'ARYA_*
Yau take juma'atu babbar Rana, duk tarone Na maza kawai hakan bai hana su Maman Sadiq yin abinci ba dai-dai misali saboda y'an Adamawa maza su kusan goma da y'an barno biyar da sukazo d'aurin auren, a Mata kam gajiram da yaruwaiya ne kawai sukazo (Yayar Umma, da k'anwarsu wadda Balu ke bimawa).
Abba zakari dai baisan hidimar da akeba, amma har gida Uncle yahya yaje yacemasa yashiryo suje d'aurin auren wani yaron malam Abdul-ra'uff, da farko cayay akwai inda zaije, amma Hajia Hindu ta saka baki harya amince.
A babban masallacin juma'ar dake anguwar gwammaja sukaje sallah, mamaki ya Kama Abba ganin Kawunansa, Kawu Surajo da bashida 6oye-6oye yafito yasanarma Abba auren Jiddah za'a d'aura yau d'innan, kafin Abba yasamu zarafin magana tawagar malam Abdul-ra'uff data ango suka Iso.
Su Kawu Surajo basubi takansaba suka shiga hidimar tarbarsu, babu yanda ya iya dole yabi ayari dan karyaji kunya, dan manyan malaman sun cika masa idanu, amma daka gansa kasan a birkice yake gaba d'aya, kuma hankainsa baya jikinsa.
Ana idar da sallar juma'a wadda su malam sukayi anan suma aka d'aura Auren *Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina da Jiddah Zakari Yaro* akan sadaki dubu d'ari biyu ciff🤩🥳..............✍🏻
*_Munga idi, ya za'ayi da Abba zakari da Alhaji Garba kenan🙆🏻🤭?._*
*_⛹♀🧳kayana a shirye suke nayin hijira walla, kad'an daga aikin Abba ya lallasa gayu🤣🤣😝_*
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d'in na sama sisters, Abban dausayi YouTube channel tv😄🤝🏻_*
*_Ubangiji yabama d'an uwan momin khairi malam Adamu lafiya, bisaga had'arin mota da yayi, muna barar addu'arku. Dama dukkan y'an uwa musulmi dake kwance sanadin ciyo😿🙏🏻_*.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[33➖34]_*
..............Cikin masifa Gajiram ta mangare Jiddah da akema kwalliya tana kauce-kauce, “K wlhy kishiga taitayinki, angaya miki mud'in sakarkarune irinki da zamu Bari kitafi harbutsai-harbutsai gunsa? Nakula saina miki sabon sabis akan zaman gidan aure Jiddah”.
Dariya Zarah da Walida suketa k'umshewa, dan sudai yau iyayen nasu dariya da kunya suketa basu, sai 6aro manyan magana suke irinta manya. Umma da Yaruwaiya ma nadaga d'aki suna jiyosu, girgiza Kai kawai sukeyi suna dariyarsu daga can.
Tsaf suka kimtsa Jiddah, tareda bajeta da wasu sirrikan k'amshi na ainahin jinin barbarawa, bawata kwalliyar hauka sukai mataba, faudace kawai sai kwalli da lips gloss mai dad'in k'amshi, harda abin saka k'amshin baki aka zazzagama Jiddah a baki, waiko ya sheikh zai rage zafi inji Balu.
Kuka kawai Jidddah ta sanya musu, saboda maganganinsu sunmata girma, gawani tsoro da suke sake cusa mata, Gajiram harda cewa k'ilama su samo babie yau🤭.
Su Zarah sukai Mata rakkiya gidan Uncle yahya, lokacin harma Aliyun ya iso, dan haka Maman Sadiq batabar Jiddah tama zaunaba tace tacire hijab ga gyale ta sanya. Idanu Jiddah ta gwalalo kamar zata fasa ihu, cikin sanyinta daya had'u da rawar muryar son Fara kuka tace, “Mama dan ALLAH ki barni naje a haka, ALLAH bazan iya........”.
Uncle yahya daya shigo ya katse Jiddah da tuni kwalla sun cika idonta, “Wai mikuke jirane kuma? Tun d'azu yana jiranta haka babu k'yau ai”.
“Yi hak'uri Abban Sadiq yanzu zata tafi”. ‘Maman Sadiq tayi maganar tana cirema Jiddag hijjab da kanta. Gyalen ta yafo Mata tana d'an harararta, murya k'asa-k'asa yanda Uncle yahya dasu Walida bazasujiba tace, “Saura kije kimasa dososo wlhy, ki Saki jikinki komi ya nuna yanaso kibarsa, dan wlhy wata yabaro a gida kema kin sani”.
Kai kawai Jiddah ta d'aga Mata tafita tana gyara gyalen zuwa saman kanta, abinda bai dametaba a rayuwarta kenan, wato saka gyale, zama ta iya rantsewa tunda ta mallaki hankalinta bata ta6a saka gyale tafita anguwaba.
Da wannan tunanin ta k'arasa k'ofar seat room d'in, saida taja gyalen sosai takuma rufe jikinta da fuskarta sannan tayi sallama a hankali.
Malam Aliyu dake tsaye akusan tsakkiyar falon ya amsa Mata cikin sanyinsa da zumud'in ganinta, gaba d'aya fitinannen turarenta ya dabaibaye hancinsa tunkan ta shigo, saida taja wasu seconds kafin ta d'aga labulen ta shigo kanta a k'asa, dama gashi gyalen ya rufe Mata fuska, amma tana ganinsa saboda gyalen babu kauri.
Shima yana hango fuskarta kad'an dukda tayi k'asa da ita, dan falon kwanyar yake da wutar Gen... Da Uncle yahya ya tayar.
Sassanyar ajiyar Zuciya Aliyu ya sauke, kafin ya bud'e dukkan hannayensa alamar tazo gareshi.
Ina Sam Jiddah bazata iyaba, dan haka takoma jikin bango ta mak'ure tana kumayin k'asa da kanta, yayinda bugun zuciyarta ke k'aruwa.
Murmushi yay mai sauti yana takowa a hankali gareta, duk wani takunsa kuma tsulmata a tsoro yake, dan ta gama lura da gaske kanta yayo.
Daf da ita yazo ya tsaya, k'amshinsu yagama gaurayewa waje d'aya yana fidda wani sirri na musamman saboda iskar fanka dake kad'awa tana kuma gaurayeshi.
Kallonta ya tsayayi daga sama har k'asa, dukda tana sanye da gyale hakan bai hanashi yaba halittar Ubangiji ba, shikam yadace da mata masu k'yak'k'yawar sura, dan Maimunatu ma masha ALLAH.
Sosai Jiddah takejin idanunsa na yawo a jikinta, dan haka takuma k'ank'ame jikinta waje d'aya. Murmushi yakuma saki yana d'an rankwafowa kanta yanda hartakejin fitar numfashinsa, cikin sassanyar muryarsa yace, “Lallai wannan amaryar mai tsadace, indai sayen fuskane nasiya da farashi mafi daraja Hauwa'u-Jiddah”. Ya k'are maganar yana saka hannayensa duk biyu ya d'age gyalen data yane fuskarta ya saukeshi kan kafad'arta.
Da hanzari ta d'ago idonta daya gama tara kwalla ta kallesa, tuni idonsu ya shige cikin na juna, Jiddah tayi azamar janyewa da k'ok'arin duk'ewa k'asa saboda mazarin da jikinta yakeyi sosai, dan tunda take bata ta6a samun irin wannan kusancin dawani d'a namijiba, ko alhaji garba da aka d'aura musu aure bai ta6a koda rik'e mata hannuba, dan haka a yau takejin lamarin da girman gaske......
Kafin takai k'asa itada tunaninta tuni Aliyu yayi azamar ruk'o kafad'unta ya maidata tsaye, kafin tasamu damar yin maganar da take k'ok'arin yi tuni ya sakata a jikinsa ya rungume.
Rikicewa sosai Jiddah tayi, ga jikinta Na wani irin tsuma da rawar mazari, abin ya had'e Mata uku, sabon al'amari, lalurarta, gargad'insu Maman Sadiq dasu Balu.
Sheikh Aliyu kam lumshe manyan idanunsa yayi yana karanto addu'ar godiya ga Ubangiji ayayinda kasamu wata ni'ima daga garesa,
الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
*_“Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat”._*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
*_“Alhamdu lillahi ala kulli halin”._*
_Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali._
Jin d'umin hawayen Jiddah a k'irjinsa ya sakashi d'agota da hanzari, raba idanu ya shigayi akan fuskarta wadda sai a yaune yasamu yimata kallon tsaf, masha ALLAH tanada k'yawunta dai-dai gwargwado, baiyi magaba sai hannunta kawai daya kama zuwaga kujera, yana k'ok'arin sakata ta zauna a kujerar tai saurin zamewa k'asan carpet ta zauna.
Fuskarsa d'auke da murmushi shima ya zauna a k'asan kusa da ita daf, k'afarsa d'aya a tankwashe d'aya kuma a zaune ya d'ora hannunsa Na haggu akai, yayinda yarik'o hannun Jiddah Na haggu Dana damarsa.
“Sannu da zuwa, ina yini”. ‘Tafad'a hawaye na sauka a kumatunta”. Jikinta kuma har yanzu rawa yakeyi.
“Ya salam *_Khairunnisaa_*, minene ya sakaki kuka haka? A zatona yau farincikinki bazai musaltuba kamar yanda nakasa kwatanta nawa nima, kisaka a ranki insha ALLAHU babu wani shaid'ani dazaiyi cigaba da tasiri a kanki a halin yanzun, indai kina k'arfafa ranki zakibarma jin wannan tsoron kwata-kwata kinji”. ‘Yay maganar yana d'ago da ha6arta da hannunsa na Haggu, Na damarma kuma yana rik'e da hannunta har yanzun yana murza yatsun a hankali.
Lumshe idanunta tayi, dan bazata iya had'a ido dashiba, sosai takejin kunyarsa irin wadda bata ta6ajinta gawaniba tunda take, dan abinda yake Mata babu wani mahaluki daya kwatanta yimata bayan alhaji garba da d'ansa, sukuma nasu ya banbanta da nashin. Kanta ta d'aga amasa alamar amsawa.
Shi Aliyu duk zatonsa lalurartace takawo hakan, danshi kallon bazawara yake mata, shiyyasa bai kawo a ransa wannan shine Karon farko data samu kusanci da wani d'a namiji irin haka ba, da bazai zo Mata kaitsayeba, zai bita mataki-matakin dazata fara sakin jiki dashine. Goshinta ya sumbata kafin yadawo ya sumbaci la66anta ma da tun d'azun hankalinsa ke wajen. Wani irin zirrr Jiddah taji a jikinta, Wanda harya sakata saurin ja da baya.
“O, ALLAH. A kulani mana, ai najawu sosai hakanan Amarya”.
Yanda yay maganar sai Jiddah duk taji babu dad'i a ranta, dan haka tace, “Kayimin afuwa dan ALLAH, ni....ni...wlhy...”.
Saikuma tayi shiru takasa k'arasawa.
Rank'wafowa yay saitin kunnenta cikin rad'a sosai yace, ”K...k...mi? madam! Ke a bari saikinje can gidan ko?”.
Batare data shiryaba ta d'ago idonta ta kalleshi jin ya canja mata magana. Ganin yanda ta waro ido saiya bashi dariya, amma baiyiba yasaki lallausan murmushi yana fad'in “Maida idon karki sakan Na kasa gane hanyar gidana hajiya”.
Gyalenta taja ta rufe fuskarta, Kafin tabashi amsa Walida da Zarah sukayi sallama a k'ofar d'akin.
Shine ya amsa yana mik'ewa ya koma saman kujera ya zauna, tareda nasu Izinin shigowa.
Kallo d'aya sukai musu kowacce tai k'asa da kanta, yayinda tuni kunyar duniya ta taru akan Jiddah da itama tai azamar matsawa baya tunda su Walida sukai sallama, amma Aliyu ya zauna jikin kujerar data matsa, harma k'afarsa Na gogar jikinta .
Kayan hannunsu suka ajiye, suka durk'usa suna gaisheshi. Cike da kulawa da fara'a ya amsa, yagane Walida, Zarah ce bai saniba, dan haka ya tambayi sunanta itama ta fad'a masa, daganan yacigaba da musu tambayoyi suduka akan karatu suna amsa masa. Sosai suma suka birgeshi, dan ya yaba da tarbiyyarsu d'ari bisa d'ari.
Sallama sukai musu suka fita.
Suna fita yay shirin dawowa k'asa kusa da ita, amma sai tayi azamar fad'in “Dan ALLAH kayi hak'uri karka zauna a k'asa kuma”.
Kansa yad'an langa6e gefe yana narke Mata murya “Sai dai idan kema zaki dawo nan”. Yay Mata nuni da cinyarsa.
K'irji Jiddah ta dafe irinna tsorata d'innan.
Sheikh Aliyu da dariyar abinda tayi ke cinsa yace, “Oh bazaki iyaba ko? Aiko saina fad'ima matata”.
“matarka?!” tayi maganar tana kuma waro idanu akansa sosai da bud'e baki tana fad'in, “Rufamin asiri”.
Kasa hak'uri yayi yanzunkam saida ya dara kad'an musamman dayaga idonta harya kawo ruwan hawaye. “To shikenan nafasa tunda kin karaya, ammafa ki d'auka 1-0, nine nayi winning kenan”.
Gefen gyalen tasaka ta share hawayen da suka cika idonta tana fad'in “naji ba komai”.
“Lallai wannan amaryar tawa shagwa6a66ace, Ashe aiki ya samemu nida Maimoon”.
Baki tad'an turo masa batareda ta saniba.
Lumshe idanunsa yayi yana sauke ajiyar zuciya, datasan turo bakinnan abinda ke sakashi data daina, amma zaiyi maganintane inhar bata bariba kafin yabar gidannan.
Itakam batasan yanayibama, tuni tamik'e takoma gaban tiren dasu Walida suka kawo tafara zuba masa kunun aya mai sanyi daketa tashin k'amshi.
“Bismillah”. Tafad'a cikin sanyinta.
Bud'e idonsa yayi yana d'ago kansa daya jingina jikin kujera, hannunta da kofin ya had'a ya rik'e yana kallon abinda ke ciki, “Madam minene wannan?”.
Batareda Jiddah ta kalleshiba tace, “Kunun ayane”.
“Toke hajjaju dakika bani kunun aya matata Na fama da kanta yakikeson Na k'are?”.
Jiddah bata fahimcesaba, dan haka tad'an kallesa tana fad'in “Baka sonshine?”.
Kallonta yay sosai, danta fara d'aure masa Kai, gaba d'aya yanda take masa sai yake ganin tamkar bata ta6a mu'amula dawani d'a namijiba da sunan miji, had'iye tunaninsa yayi saboda hannunta data motsa, saurin janye idanunta tayi dan satar kallonsa takeyi da.
Shima saiya kar6i kofin yana gyara zamansa, “Badan inada kishi mai tsananiba dana miki wata tambaya, amma bazanyiba, saboda ko'a tunani banason tuna kin ta6a auren wanina kafinni d'in. bara Zansha kawai, ALLAH ya fidda A'i daga rogo dai”.
Jiddah batace komaiba itadai, dukda maganarsa ta d'aure Mata kai, dan batasan miyay niyyar tambayartaba. Kulolin tafara bud'ewa, tuwon shinkafane miyar ganye sai tashin k'amshi take. Tana k'ok'arin zubawa Aliyu dake shan kunun aya yace, “Afuwan Juddatulkhair, danasan zakiyi abinci danace karkiyi, banacin abinci da daddare, wannan kununma ya wadatar dani, amma insha ALLAH zanzo darana kodan naci abincinki kafin kikoma kusa Dani gaba d'ayanki”.
Kanta ta gyad'a a kunyace, kafin ta maida kulolin ta rufe, gefe takoma ta zauna sosai yanzuma kanta a k'asa, tace, “Yaya auntyna?”.
“tana gaisheki sosai itama, dan lafiya tamata k'aranci, shiyyasama kikaga tun ranar da aka d'aura aure ban zoba, alhalin hakan kuma ya cancanta, dan ALLAH amin afuwa”.
“ALLAH Sarki ALLAH yabata lafiya, yasa kaffarane, mike damunta haka?”.
“Babienkune”. Yafad'a a wani yanayi daya kuma dulmiya Jiddah a kunya, harma tayi dana sanin tambayartasa.
Murmushi kawai yayi ya canja firar. “Kinga sarkin kunya da kuka, k'aramin kununnan tunda kin zurmani gara nasha dama hujja, amma Zan fad'ama auntynki duk ranarda zaki tare tayi kununnan aya itama danta rama”.
“Ni Hauwa'u, yin kunun ayar yazama laifi malam?”.
“Niba malaminki baneba yarinya, amsarki kuma sai a nan gaba zaki samu, nidai k'aramin”.
Tashi Jiddah tai ta k'ara masa, ita dai yau gaba d'aya bata fahimtar maganganunsa, sannan yana k'ara bata mamaki, batai zaton yana magana hakaba itakam.
Haka yayta d'ora kunun aya yana Mata hirar da rabinta duk sakata kunya yakeyi, iyakarta murmushi ko e ko a'a.
Goma da rabi nayi ya mik'e, “To Juddatulkhair bara Na matsa ga Uwargida itama, zuwa talata insha ALLAH zankuma zagayowa gaisheki, a gaidamin Umminmu da k'yau”.
Itama Jiddah tashi tayi tsaye, “Zataji insha ALLAH, ka gaida aunty, ALLAH yabata lafiya”.
Harya d'an Fara tafiya yadawo da baya kusa da ita sosai yana fuskantarta, “Yanzu nan ba'amin oyoyoba, Na gaida gidanma bazan samuba kenan?”.
Yunk'urin ja tayi da baya yay azamar d'ora hannunsa a k'ugunta ya matsota jikinsa ya rungume, duk tsumar da jikinta yake da rawa bai saketaba, saima bakinsa daya d'ora saman goshinta ya sumbata kafin yace, “wannan lalurar taki batamin adalciba, dolene kafin ki tare da izinin ALLAH na nemo mafita”. Yana gama fad'a ya sumbaci la66anta sannan ya saketa.
Dukda halin datake ciki Na gushewar nutsuwar wucin gadi hakan bai hanata yomasa rakkiyaba kamar yanda Gajiram ta gargad'eta.
Tun a bakin k'ofa ya Danna key d'insa motarsa takawo haske day'ar tsuwwa, bud'ewa yay yashiga yana d'ebo ledojin gefensa ya mik'o Mata.
K'in kar6a tayi tana shirin juyawa. Da hanzari ya damk'o hannunta yana fad'in “Hajiyata tunadai miji nake ba saurayiba”.
Dariya maganarsa ta bata, ledojin ya zura mata a hannu yana sumbatar hannun, “Kiyi mafarkina daga farkon dare har k'arshe”.
Kanta a duk'e tace, “Nagode ALLAH ya k'ara bud'i na alkairi, yakaika gida lafiya”.
“Amin *Qurratul ain*, maza shiga gidan dan bak'aramin k'ok'ari naiba barinki fitowa nan da wannan gyalen, danma kawai Darene kuma mota ta kare”.
Murmushi tayi tana d'an risinawa da fad'in “saida safe”.
Harta shige idonsa k'yam akan bayanta, ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tareda jingina da kujera yana lumshe idanunsa, yakai hannu yana shafa gemunsa Na sunnah kafin ya maida hannun ga cikinsa, a hankali ya furta “Kunun aya yafara aiki kenan”.
Bud'e idonsa yayi yatada motar a kasalance yabar anguwar tamkar bayason tuk'in.
✨✨✨✨✨✨.
Duk a falo Jiddah ta iskesu har Uncle yahya dasu Sadiq da basuyi barciba, gaba d'aya suka zubo Mata idanu, hakanne yasakata yin kasa da kanta tana sakin ledojin hannunta a k'asa, gani take kamar duk sunsan miya faru tsakaninta da Sheikh Aliyu.
“A'a Jiddodo yada sakin ledoji haka?”.
Uncle yahya yafad'a fuskarsa a washe da murmushi.
“Babu komai Uncle”.
“To Alhamsullhi, ya tafi ne?”.
“Eh”.
“To ALLAH ya tsare, basaikin zaunaba kumuje Na rakaku gida dare yayi”.
Ledojin Jiddah ta d'iba takaima Maman Sadiq.
“A'a Walida d'aukar Mata, wannan nakine ai”.
“A'a mama bafa nawa baneba”.
Uncle yahya ya katse zancen da fad'in “Kinga walida d'auka Mata kumuje”.
Babu Wanda yay masa musu sukabi Umarninsa.
Jiddah ta d'auki hijjabinta ta saka suka fita sunama Maman Sadiq dasu Mageed saida safe.
Har k'ofar gida ya rakasu, saida yaga sun Shiga sannan ya juya batareda yashigaba shi.
Su Umma duk suna zaune basuyi barciba suna jiransu.
Balu ce ke fad'in “A lallai wannan d'an nawa ya iya zuwa, amarya mikika samo mana?”.
Fita Jiddah tayi takoma d'akinsu takasa bata amsa, nanfa suka shiga yimata dariya da tsokanarta, tana jinsu amma tak'iyin ko tari, sai abinda ya faru tsakaninta da Aliyu keta dawo Mata kamar wata almara ko shirin film.
A can kuwa Gajiram ta bud'e ledojin dasukazo dasu. Kayan marmarine sai ice-cream da kaji guda biyu, sai kuma kwalin waya harda Sim card.
Nanfa suka shiga godiya ga Aliyu da fatan alkairi dana zaman lafiya garesu.
Gajiram tace walida ta d'auka takaima Jiddah, amma sai Umma ta dakatar da ita. “Ba haka ya kamata ba, ki raba kowama ya samu, wannan shine dai-dai”.
Gajiram tasan halin Y'ar uwarsu da k'yak'yk'yawan tsari akan yaranta, dan haka tabi umarninta, kaza d'a aka ajiyema gidansu Uncle yahya, kayan marmarinma aka d'iba musu, ice-cream aka ajiye roba d'aya, ta raba komai nasu tabama su Jiddah rabi suma su uku suka d'auki rabi.
'Dauka su Zarah sukai da wayar Jiddah suka nufo d'akinsu zuciyarsu wasai dakumajin lallai yanzune Y'ar uwarsu tayi aure.
A tsanake sukaci komai sukai gidiya ga ubangiji, kafin su dasa fira da k'ok'arin had'a wayar Jiddah dukda babuma wuta.
Suma su Umma dai hirar tasu duk akan tariyar jiddahrne, sunayi sunacin abin arzik'in da ya sheikh Aliy ya kawo.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.
A haka ya lalla6a hanyar gida bayan ya tsaya yasayama Maimunatu abin motsa baki itama.
Dukda dare yafarayi hakan bai hana ya iske tsirarun mutane a bakin masallacin k'ofar gidansaba, dayake akwai wuta a anguwar tasu su, dukda yabaro anguwarsu Jiddah babu kuwa.
Wani saurayine dasuke a bakin masallacin ya tashi ya bud'e masa gate, bayan yashiga ya rufe, saida ya tsaya Aliyu yafito a mota ya gaidashi sannan yafito yana masa saida safe.
Aliyu kuma ya kulle gidan danya shigo kuma kenan, tsarabar Maimunatu ya d'iba yanufi cikin gidan duk a matuk'ar kasalance, Wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da bashida kuzari ko kad'an, dukda shi mutumne mai sanyi dama amma saiya kuma narkewa yanzu.
A yanda Maimunatu dake zaune a falo taji sallamarsa kawai saida ta d'ago da sauri ta kallesa da k'yau.............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[35➖36]_*
..............Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta tana murmushin k'arfin hali, jikinta duk sai ya kuma sanyi, itadai tasan Aliyu ba mutum bane mai yawan fitina, hasalima sunkan jera kwana hud'u batareda ya nemeta ba, sannan baya d'aukar dogon lokaci tare da ita, wannan dalilin yasakashi dagewa wajen gyara kansa, dan a ganinsa ba mace kawai yakamata taima miji gyaraba, suma mazan yadace suna gyarawa........
“Ko ba'ayi murna da dawowataba Na koma Gimbiya”. Maganarsa ta katsema Maimunatu tunaninta, mik'ewa tayi ta nufosa, sai da ta rungumesa da sumbatar kumatunsa kafin ta sakesa ta amshi kayan hannunsa tana danne kwallar data cika idonta, dan sosai taji k'amshin turaren daba nashiba a jikinsa, tasan kuma bai wuce Na amarya ba, a yandama yadawo mata kad'ai ya isheta amsa.
Bin bayanta yay ya zauna yana sauke numfashi, kallonsa tad'anyi batareda tace komaiba tawuce kicin, babu dad'ewa tadawo d'auke da tire.
Gabansa ta dire, ya d'ago kansa daya jingina a kujera yana kallonta, itama shi take kallo, cikin danne zuciyarta tasaki murmushi tana fad'in “Wai miya sakaka laushi haka Annur?”.
Zamansa ya gyara sosai tareda kamo hannunta ta zauna a gefensa. Muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, “Babu komaifa madam, naga kin damu”.
“To ba doleba Yaya, kafita muna farin ciki kadawomin a sanyaye, kaga sainaga ko wani abune yafaru da jiddan ko wani a gidansu ai?”.
“To kwantar da hankalinki, babu abinda yafaru tanama gaisheki. Bani ruwa nasha kedai”.
“ALLAH Sarki, ina amsawa nima, kuma Alhmdllh tunda babu wata damuwa”. Jug dake kan tire ta d'auka tafara tsiyaya abin ciki a k'aramin kofi.
“Minene wannan zaki bani?”.
Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli jug d'in, “Yaya had'in kwakwar dakace namakane d'azun ai, to wlhy nama manta, sai bayan fitarnan taka dasuka kawo wuta Na tuna shiyyasa nayi, kajiko harma yayi sanyi”.
Amsar jug d'in da kofin yayi ya ajiye k'asa, “Barshi dan ALLAH Maimoon inba kasheni zakuyiba”.
Cikin waro ido Maimuna tace, “Yaya kashewa kuma?”.
“Eh mana, ba dole nace kashewa ba, ita tabani kunun aya, kekuma zaki bani had'in kwakwa?”.
Babu shiri Maimuna ta kwashe da dariya, haba no wonder tagansa a sanyaye.
Harara ya zuba Mata yana wani shagwa6e fuska da fad'in “Abindama zakimin kenan ko? Maimakon kiji tausayina”.
Baki Maimuna ta toshe da hannu tana had'iye dariyarta da k'yar, “ALLAH Yaya kaid'inne kaban dariya, ni duk kasakani a tsorone da farko”.
“Humm bazaki ganeba wlhy, tsautsayi kawai ya sakani shan kunun ayarnan da yawafa, gashi kuma yasha had'i kamar yanda kikemin, Nidai Ahmad ai yagama dani daya bani wannan sirrin”.
“Haba dai Yaya godiya yakamata Kai masa ai”.
Hannu yasa ya jawota jikinsa, murya k'asa-k'asa yace, “Wayace ban gode masaba, badan iyakancewar Mahaliccina da taimakon Ahmad ba da yanzu ban mallaki koda mace d'aya ba balle Mata biyu ma ai Sarauniyata, amma wad'annan had'in ba k'aramar harmutsani sukeba”.
Hanu Maimuna tasaka ta rufe fuskarta tana Y'ar dariya. Shima saiyay murmushi yana kuma sakata a jikinsa.
Tarigada tasan muhimmmanci duk irin wad'annan abubuwan ga mijinta, hakanne yasakata kar6arsa d'ari bisa d'ari tun a falo aka fara canja hanya.
🙆🏻⛹♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah dai gaba d'aya tama rasa yanda zata fassara abinda sheikh Aliy yay Mata, wani iri duk takeji a jikinta, duk hirar dasu Zarah keyi hankalinta baya tare dasu, har aka maido wuta suka saka cajin wayar.
“Wai Yaya Jiddah mike matsalarkine? Tunda muka dawo kinyi sukuku”.
Kallon Zarah tayi mai maganar, kamar bazata tankaba saikuma ta sauke numfashi tana cewa, “Babu komai, kaina ked'anmin ciwo kawai”.
Sannu suka shiga jero Mata cikin tausayawa, Walida harda zuwa ta samo Mata magani. Bata musaba ta kar6a tasha sannan tayi shirin barci suka kwanta.
Barcinma k'in d'aukarta yayi, sai tunane-tunane takeyi, tunda take bata ta6a soyayyaba, hasalima baifi sau uku zuwa hud'uba ta ta6a tsayawa da saurayi, dan dawahala tana tafiya samari su tareta a hanya ko yimata magana (Muhimmancin nagartacciyar sutura ga d'iya mace, yakan saka mutanen banza shakkar zuwa gareka, abinda y'anmatan yanzu dama matan auren muka gaza fahimta kenan), wannan yasaka komai Na Aliyu take masa kallon *Sabon al'amari* a gareta, ganin barcin yama gagareta saita mik'e tafito domin d'aura alwala.
Nafilfili taita gabatarwa, kafin tayi zaman karatun littafi mai tsarki, a wannan time d'inne suma su Zarah suka farka, sai suma sukayo alwala.
Koda Jiddah tasamu ta kwanta sai barcinta yazama mafarkin Aliyu kusan gaba d'aya, da asuba abin ya tsaya mata a rai, tasara miyasa ya mannema zuciyarta har irin haka?.
Fans zasu baki amsa jiddodo🤩⛹♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Gaba d'aya Abba zakari a takure yake, yasaba harkokinsa Na kasuwanci a kullu yaumin, amma anzo nan an ajiyeshi wai dan ya huta, anyama kuwa wannan ba tsarin Yahya baneba? Zumbur yamik'e saboda amsar da zuciyarsa ta basa, lallai wannan haka yake, akwai munafinci a wannan lamarin, tunda dai ai shine ya kawo likitan, to waima miyasa yagaza tariyo yanda suka k'are a Station ne?, shiru yay nawani lokaci, kafin babu shiri ya lailayo wani ashar ya dire a k'asan tayis, a lallai yahya yagama ganin gadon barcinsa, yanzu kuwa zaije ayita tak'are wlhy.
Batareda jiran likitaba ya had'a inasa-inasa ya nufo gidansa da Hajia Hindu ke a ciki.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.
Hajia deluwa hakimce a falonta Na alfarma tana waya da hajia Hindu akan auren Jiddah, sai dariya take kwasa tasamun nasara, dan yanzu sakayau takejinta tamkar an sauke Mata kaya a Kai, Alhaji Garba datun farkon fara wayar yashigo yay tsaye tamkar gunki yana saurarenta, dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi, cikin zumud'i yanufo sashenta saboda shigar bazata yay mata batasan da dawowarsaba yau, amma saiyaci Karo da abinda ke Neman fasa masa zuciya.
Jiddah tayi aure bashiba, mahaifinta ya yaudaresa, matarsa itace ta ruguza masa dukkan shiri ta k'ark'ashin k'asa.
A fusace ya fisge wayar ya ratsata da k'asa akan tayis, nan take tayi kwatsa-kwatsa.
Hajia deluwa data mik'e a fusace tuni mamaki da tsoro ya baibaiyeta, dan batasan da shigowarba ko kad'an, amma dayake manyan matane sunsan takan duniya saita dake tana kallonsa hankali a kwance.
“Alhaji lafiya kuwa? Ya daga dawowa sai fushi haka? Mi wayata Tamaka?”.
“Ban saniba Yahanasu, yanzunan kece da kanki zaki aikata shed'anci Na ruguza auren sunna? Dama son aurena da Jiddah dakiketa nunawa da farko munafuncine Ashe? Lallai yau nakuma yarda makircin mace yafi Na shaid'an girma, anyama kuwa bakece kika kori Jiddah daga gidannanba?”.
“Yo Alhaji kaga laifinane? idanma ni d'ince”.
“No ya za'ayi inga laifinki, ban ganiba wlhy” yay wata dariya ta basawa, kafin ya nunata yana cigaba da fad'in “Kijira sakamakon aikinki Na ruguzamin auren Jiddah da kashe mana aure”.
Yana gama fad'a yay ficewarsa, mamakine ya kama hajia Deluwa, tafara safa da marwa Na tunanin to mizai Mata? Miya shirya? Kodai sakinta zaiyi?. Gabantane yay wata mummunar fad'uwa, jikinta Na rawa tabi bayansa.
Amma saita tarar ya gark'ame k'ofarsa, duk Nokin d'in datai masa bai kulataba. Kuma yana jinta sarai, dan yanama zaune a falonsa yana k'ok'arin kiran Abba Zakari a wayane.
Abba datunda yabaro gidan doctor yadawo gidan hajia deluwa ta tareda da farin cikin samun lafiyarsa, dukda tagansa awani tsume alamun zuciyarsa a kusa take hakan bai hanata tarairayarsa yay wanka yaci abinci ba, harzai fita gun Uncle yahya ta dakatar dashi da maganar kalifa daya shigo gidan yanzu babu jimawa sannan Abba yana wanka.
“Kin dakatar Dani, bakice komaiba kin zubamin idanu”.
“A'a Abban kalifa, bafani nakar zomonba, dama kalifane aka koro daga makaranta sunyi fad'a dawani yaro akan budurwa ya fasa masa Kai, yanzuma haka abinda ake ciki iyayen yaron sunce bazasu yardaba, shiyyasa aka koro kalifa yazo yaje da mahaifinsa yana d'akinsu, Wanda aka turosu tare kuma yana a bakin gate yana jiranka”.
Zugudi yayi yana kallonta, bakinsama yamasa nauyin daya gaza furta komai, harma yaushe Kalifan yagama balaga dazai fasa kan wani akan mace?, ina wannan sharrine kawai za'aima yaronsa, dan haka babu inda zayi yanada matsalar data girmi wannan shirmen........
K'arar wayarsa daya kunna babu dad'ewa ta katse masa tunani. Wata mummunar fad'uwa gabansa yayi saboda ganin mai kiran, yanda ya gwalalo idanune yasaka hajia Hindu lek'a wayar, itama saida ta fiddo ido kafin tace, “Abban kalifa ka d'aga mana”.
Kallonta yayi awani yanayin data kasa fassarawa, wayar Na tsinkewa aka sake bugowa, amma Abba yakasa d'auka.
Hakanne Yakuma fusata Alhaji Garba daga can, a matuk'ar harzik'e yakuma dannoma Abba Kira.
“Alhaji ka d'auka mana” hajia Hindu tafad'a tana nuna masa wayar, ganin bashida niyyar amsawa ita saita amsa tana saka masa a kunne.
Yanda Alhaji garba yay magana dagacan a harzuk'ene yasaka Abba kwarewa da yawu yahau tari.
“A lallai Alhaji zakari, ni zakaima d'ibar albarka, k'in amsa wayata da kayi kawai ya isa bani shaidar kana kan sani ka aurar da y'arka, to ni bazan zauna 6ata lokacina akan hayaniya dakaiba, saidaifa ina mai tuna maka maganar kud'ina miliyan hamsin cif nanda wata d'aya kacal wlhy, dan wannan shinema adalcin dazan maka, sannan kuma namik'a komai a hannun d'ana Ashir dashi zakuyi nabarka lafiya”.
Wani haushine ya turnik'e Abba, Dama ga zuciyarsa a kusa take, jira yake a ta6osa ya fidda fushinsa, cikin tsantsar bala'i shima ya dakatar da Alhaji garba dake shirin katse kiran. “To naji d'in saime, ank'i a baka auren Nata, waishin kasheni zakuyi da haukankune?, shin da wanne zanji? Kama tambayeni yanda akayi mana amma saika hau kaina saboda wata banzar miliyan hamsin, Kai da mutuncinafa babu Wanda ya isa ya takani”.
Tsaki Alhaji garba yayi ya yanke wayarsa.
“Amma Abban kalifa da bakai masa hakaba ai, gara ka lalla6ashi ko Zarah saika bashi madadin Jiddar ko?”.
Wata uwar harara ya zuba Mata, kafin yasaka hannu ya hankad'ata baya, tareda tad'e k'afarta dake hanyar dazai wuce, a take k'ashin k'afar yay k'arar samun rauni.
dukda k'arar wahala data saki baibi takantaba ya tsallaketa yafuce a fusace.
Turk'ashi🙆🏻😨.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Gaba d'aya yau Sheikh Aliyu bai fita ko inaba tunda yadawo sallar asuba, dukda kuma yau litinin amma sai yay lafewarsa gida, ga Maimuna ma dai bawani isashen lafiyane da itaba, amma dayake tanada dauriya sai bata cika langa6ewa ba, da taimakonshi suka gyara gidan, kicinma shine ya tayata had'a musu Karin kumallo sannan suka gyara komai tsaf. Wanka yatafi yi yabarta tana shirya abincin a falo.
Yad'an jima a bayi kafin ya fito, wayarsa daketa haske ya kalla takawa yay inda take a saman durowan gefen gado ya d'auka, mamakine ya kamashi ganin sak'one aka turo da Number Jiddah daya saya mata jiya. Bud'e sak'on yayi zuciyarsa na mamakin kona minene?, saida ya zauna a baking gado kafin yafara karantawa.
*_“Amincin ALLAH ya tabba ga adalar zuciya ma'abociyar tsoron ALLAH da addini, ina fatan ka Isa gida lafiya? Kakuma iske Y'ar uwata lafiya itama?. Fatana karayu cikin aminci da tsaftataccen farin ciki a wannan yini na litinin ya kai jarumina tauraron Al-umma a k'ark'ashin duniyar musulunci, nagode kwarai da gaske da alkairinka a gareni, ALLAH yak'ara bud'e na alkairi mai albarka kuma🤝🏻”._*
_Taka Hauwa'u-Jiddah_.
Idanunsa ya lumshe yana sauke wani nannauyan numfashi, yayinda can k'asan ransa yake kuma gauraya dawani farin ciki na musamman, ko kad'an baiyi zaton hakan ga jiddahr ba, musamman idan yay dubi da yanda suka k'are a jiya.
Idanunsa ya bud'e akan wayar yana sake maimaita karanta sak'on, saida ya tisashi sau babu adadi kafin ya danna kiranta dan bazai iya hak'uri ba.
Jiddah suna zaune a falo gaba d'ayansu suna Karin kumallo Walida ce kawai babu taje makaranta, Zarah kuwa batajeba suna shirye-shiryen fara jarabawane ta SSCE. hankalinsu kwance sukecin Taliyar da Jiddah ta dafa musu (Y'ar Hausa) wayar Jiddah dake hannun Balu da Zarah tashiga tsuwa, kallon juna sukai sukai murmushi, Zarah taima Balu alamar Jinjina da fad'in “Aikinmu Na k'yau nida uwata”.
Hannu balu taba Zarah suka tafa kafin ta mik'ama Jiddah dake kallonsu wayar. Su Umma ma dai kallon Su Zarahn sukeyi, amma basuce komaiba, saima Yaruwaiya datacema Jiddah “Wai bazaki tashi kije ki amsaba saita tsinke”.
Tashi Jiddah tayi tafita jikinta a sanyaye, kafin ta Isa d'akinsu ta d'aga har kiran ya yanke an sake Kira. 'Dagawa tayi tana zama a bakin katifarsu.
Jin ta d'aga sai Aliyu ya d'an sauke ajiyar zuciya yana fad'in, “Assalamu alaiki warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu”.
Wani yarrr Jiddah taji tsigar jikinta ta tashi, cikin had'iye yawu da k'yar da janyo numfashi, ta amsa da “Wa'alaikassalam, ina kwana”.
Murmushi yayi daga can yana shafa gemunsa zuwa k'asumba, cikin kuma sanyaya murya yace, “Lafiya lau Amarsu, ina fatan kema kina lafiya?”.
“Lafiya lau, ya jikin Aunty”.
“To masha ALLAH, jikin auntynki kuma Alhamdulllahi”.
Shiru Jiddah tayi, dan batasan kuma mi zataceba (abinka da farin shiga😂), sai dai a k'asan ranta tarasa miyasa muryarsa ke sakata a wani yanayi?.....
Katse Mata tunani yay da fad'in “Naga sak'o Na gode sosai, sakallahu khairan Juddatulkhair”.
Mamaki ya kama Jiddah, tana shirin tambayarsa wane sak'o? Dan itadai tasan bata tura masa wani sak'oba saiya katse Mata hanzari da fad'in “Lallai Na yarda anyi mafarkina daga farkon dare zuwa k'arshe da gaske, wannan sak'o ya cancanci tukuyci mai nagarta, Na bayar anan? Kosai nazo kusa?”.
Cikin shagwa6ar da Jiddah batasan tayiba tace, “Nidai Na yafe”.
“A'a madam yada saurin karaya haka kuma? Nifa ba fad'ar tukuycin dazanyiba nayi aiko, yanzu dai kin amince nazo anjima na bada?”.
Da sauri Jiddah tace, “A'a nagode, abama aunty a maimakona”.
“Kin yarda Na bata?”.
“Eh wlhy Na yarda nikam”.
“To shikenan, Zan bata rabi nazo nabaki rabi”.
“A'a kabata duka nidai”.
Murmusawa yayi yana mik'ewa tsaye, ya k'arasa gaban mirror yana fad'in “To ai shikenan tana godiya sosai, yasu Zarah?”.
“Lafiyarsu lau suna gaidaku suma”.
“Muna amsawa, suna kusa dake kenan?”.
“A'a”.
Zaiyi magana Maimuna ta shigo da sallama, yanda yake murmushi yasata tsarguwa ko yana waya da matarsane? Dan haka tai niyyar juyawa. Saurin damk'o hannunta yayi yana k'arema kwalliyarta kallo, tayi k'yau sosai tana baza k'amshi.
Jin yayi shiru gakuma d'an motsi Jiddah Na jiyowa yasakata itama tsarguwar k'ila matarsace, saitai saurin fad'in “Sai anjima”.
Matse Maimuna yayi a jikinsa shima yace, “To sai anjima a gaishe dasu Ummi”.
“to” kawai Jiddah tace ta yanke wayar. Haka kawai taji ranta ya sosu, wato da shikad'aine shiyyasa yaketa wani narke Mata, amma yanzu matarsa tazo yama kasa magana, “humm halin maza saisu” tai maganar a fili tareda ta6e baki ta mik'e takoma wajensu Umma, sai dai k'asan ranta abun ya tsaya Mata sosai. (Madam Jiddah yayane🙆🏻😂?).
Data dawoma daina saka baki a firarsu Umman tayi, har Yaruwaiya da Balu da Zarah suka shirya suka fita kasuwa k'arasa sayayyar Jiddan data rage, aka barta itada Umma kawai.
Umma nakula da zum6ure-zum6uren da Jiddah keyi, amma sai bata kulata ba balle ta tambayeta ma.
Saima zama datayi tana tambayarta akan magungunan sanyi data bata Tasha tun kwanaki.
“Wai Jiddah magungunan Dana baki kuwa kina amfani dasune?”.
“Eh Umma inayi”.
“Idanma bak'yayi kekika sani dai, dan wannan shine gatan dazan miki, a zamaninnan da sanyi yayma Mata katutu, ba maganin mata kawai yakamata mu iyaye muyita Danna mukuba idan zakuyi aure, yakamata mufara bincikar lafiyarku ta 6angaren sanyi kafin wad'annan magungunan, dan duk macen dake tare da sanyi kozatasha tirelar maganin gyaran Kanta to wlhy tamkar a banzane, dan bazai Mata amfanin komaiba, dan haka idanma zaki maida hankalinki ki maida, yanzu hakama hajiya ladidi mai adashe tace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata kawo miki wani”.
Kan Jiddah a k'asa tace, “To Umma nagode”.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Aliyu kam ya ajiye wayar yay yana maida hankalinsa ga Maimuna, dan kimarta tawuce ya amsa wayar wata mace a gabanta, a ganinsa hakan tamkarma cin fuskane da had'a k'iyayya a tsakanin matan nasa.
“Hiya-huwa kinyi k'yau ainun Masha ALLAH”.
Wani dad'ine ya ratsata jin sunan daya kirata dashi, ta kama hannunsa ta sumbaci tsakkiya, cikin narke masa tace, “Hilmy yanzu kaima zakayi fiyema dani”.
“haba-haba, ai idan ana dara fidda uwa ake gimbiyata, samun k'yak'yk'yawa irinki acikin Mata sai an tona, kina kallon kaniki a madubi kuwa?”.
“Kai yayana kadaina fasamin Kai hakanan fa, kaidai zauna Na shiryaka muje ka karya, dan sak'onin daka sakani Na amsa wad'anda Zan iya jiya naci Karo dawani mai muhimmanci”.
Kallonta yayi sosai, “Mi sak'on yace?”.
”A'a kabari saika karya”.
“Karki damu fad'amin kinji”.
Mai tafara shafa masa, _“Cayay ka taimakeshi da shawara akan lafiyarsa, yanada Mata harda yara a tsakaninsu, iya gwargwadon iko suna gamsar da juna a shimfid'a, dukda dai ya fuskanci shi mutumne mai rauni dan baya iya jan lokaci wajen tarayya da ita amma sai bata ta6a nuna damuwartaba akan hakan, Sai kuma dukda wannan matsalar daya sani saiya k'ara aure, to a yanzu halin dayake ciki shine baya iya gamsar dasu su biyun, amaryar tashi kuma tafara nuna itafa bazata iyaba, itama Uwargidan haka, hakan kuma yafara kawo musu matsalar yawan hayaniya da matan nasa musamman Amaryar, shikuma yarasa yanda zaiyi, ya gwada magunguna da ake saidawa Na gargajiya sai dai tasirinsu kuma bawani mai tsayi baneba agaresa ake komawa Y'ar gidan jiya, shikuma duk yanason matansa yanason cigaba da rayuwa dasu.”_
Ajiyar Zuciya Aliyu ya sauke, ya taimakama Maimuna dake k'ok'arin saka masa kaya, saida suka kammala tasa masa turare sannan suka fito yana fad'in “Wannan matsalar abar dubawace, kuma insha ALLAH zanyi magana akanta yau a masallaci, dan munada majalisi, matsalace babba wannan Maimoon data dabaibaye Mazajenmu Na arewaci, ammafa tamafi illa a kudancinmu, kawai sudai sun fimu himmar gyara kansune, matsalarmu mu mazan arewa shine mun d'auka mace ita kad'ai yadace ta gyara mana kanta, mukuma abinda muka iya kawai munemo kud'i muyita aure Ana kiranmu jarumai a waje, a cikin gida kuwa bama iya hasalama iyalinmu komai, Mata da yawa suna cutuwa ta wannan sigar, saidai basa iya magana saboda kunya, soyayyar mutumin arewa a iya wajene kawai saikuma amarcin watanni uku, ita kuma mace kota tsufa tana buk'atar tattali da soyayya ga mijinta, koda bakada wadatar dukiya soyayyar dazaka nuna Mata kad'ai wlhy zakiga ta gamsar da ita da jagorantar zamanku har k'arshen rayuwa”.
“Wlhy Yaya maganarka gaskiyace kuma”. Maimuna dake zuba masa a bincin tafad'a cikin damuwa.
Ajiyar zuciya shima ya sauke, dan abi yana Sosa masa rai, amma insha ALLAH a wannan Karon zai amayar dashi ya huta, dan ba Neman ilimi da tafseer kawai al'umma suke buk'ataba, akwai wasu manyan abubuwa Na rayuwa da muhimmancinsu yakai adinga tunatar da mutane shi kodan samun sauk'in da duniyar aurarrakinmu ke fuskanta a halin yanzu.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah da Umma na a tsakar gida suna shirin girkin rana da hira wadda rabinta duk ilimin zaman aure Umma ke k'arama Jiddah haske akai cikin hikima.
Tamkar an jefo Abba ya banko k'ofa jikake garam!!!, duk zabura sukayi suna kallonsa, Kai tsaye kan Jiddah dake tsaye a bakin rijiya yayi tamkar wani bajimin zaki...........✍🏻
😨Abba zakari mi zakai mata kaikuwa?.🙆🏻
_Barbarawa ayimin afuwa (Au bare-bari🙆🏻🤭). wata tace ba sunansu hakaba, Barbarawa kamar bunsuru wai😂, bani Na fad'aba Y'ar uwarkuce tace, karku dafani yau su tawan (miss Xoxo)⛹♀⛹♀⛹♀._
*_Albishirinku fa, CIKI DA GASKIYA mafa ya sauka a gareku adai YouTube channel tv na Abban Dausayi, saiku garzaya kar ayi babuku gayis_*.⛹♀⛹♀⛹♀
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
0 comments:
Post a Comment