Kwance tashi ba wuya wajen Allah, shakuwa ne mara misaltuwa ya kullu tsakanin Khattab da Miemie. Tun yana fushi idan ta kirashi da ‘YaNaufal’ Har ya hakura.
An raba routine dinta, Naufal ke kaita makaranta sai Khattab ya dauko ta. Shi dai Naufal bai sake jiki da Khattab ba. Baiga dalilin da wani katon banza zai rinka sintiri gidansu ba. Thou a ranshi deep down yana jin dadi atleast someone yana appreciating sister dinshi without discrimination.
A chan gidansu Khattab kuwa an lura ya fiye fita kuma he is distracted, but ba’a San me yakeyi ba. Kawai ana tunanin zaman kadaici ne baya so. Shi kuma koda wasa bai taɓa tunanin ya faɗa masu ba saboda yasan za ayi tashin hankali.
Haka rayuwar shida miemie ya kasance, kullum shakuwa sukeyi. Kwata kwata baya son damuwarta, abinda taga dama takeyi, sangarta ta yakeyi sosai har saida Naufal ya taka mashi birki kafin ya ɓata mata tarbiyya. Shi Khattab komai na Miemie burgeshi yakeyi, deep down a ranshi Idan ta soma hauka kadan kadan baya yarda, kawai k’uruciya yake daukan abin saboda tun haɗuwan su batayi tuburan ba saboda tana shan magani akai akai.
Naufal yana nan yana aiki tareda su Mr Sutter, yaro mai hazaka suna jin daɗin aiki dashi. Basu ɓoye mamakin suba saida suka cemasa basu taɓa ganin bakin fata mai rik’on amana kamar shiba. Sunyi alkawari suma zasu saka mashi nan bada daɗewa ba.
Ta ɓangaren aurenshi da Fadeela kuwa, babu abinda ya canza both families anata hada hada aga an kece tsara. Sau ɗaya Naufal ya tada maganar wajen Abba amma bai samu fuskar karasawa ba saboda wanki babban bargo yayi mashi, kuma da yaje wajen Mama itama bata sake mashi fuska ba saboda tun ranar da Abba ya tarasu da daddare yayi masu tas ta hankalta dashi.
Zancen sadaki kuwa an biya dubu ɗari cash da kuma Ningi(shanu) guda biyar. Alhaji Musa ne watau Big Daddy ya jagoranci komai saboda a gidansa akayi komai tunda shine zai bada aurenta. Shi kuwa Alhaji Sulaiman ya bada kudin sadaki saboda shine zai karba auren Fadeela.
Anyi komai cikin mutunci tareda tanɗe tanɗe, zumunci sosai ya kullu tsakanin iyayen kai zaka zaci sun san juna da daɗewa kuma ba surikai bane. Ko Mommy takan kira Anty Saudah domin taji lafiyan Miemie, jefi jefi tana kiran Mama itama.
Saidai su kaɗai ke abinsu, Daga Naufal har Fadeela kowa harkan gabansa yakeyi kamar ba zancen aure nan kusa. Kuma rabon dasu haɗu tunbayan yaje bada hakuri gidansu. Zuwan bazata yakeyi kuma cikin ikon Allah bai taɓa riske taba. Mommy yake gani sai sau ɗaya yaga Grand Kadi.
Kullum Mommy adduar daidaituwan tsakanin Su takeyi saboda bata san Fadeela tasha wahala zaman aure. Aure dace ne kuma idan kayi sa’a kaji daɗi.
Siyayya babu kama hannu yaro Mommy kema Fadeela, kullum tana ziryan zuwa Kanti kwari dake Kano. Ita bataga bambanci tsakanin kayan dake Nigeria da kuma Kasar waje ba, acewarta yan Nijeriya ke zuwa Kasar waje siyowa saboda haka sun hutarshe ta.
Kana ganin abinda aka siyan mata kasan cewa ‘yar so akema wannan siyayya.
********
Ita kuma Amatullah ba’a san ranta tayi siyayyan lefe ba. Data siyo na farkon saida ran Mama ya baci. Karanci k’arara ta nuna kamar lefen matsiyata. Nan take Mama ta sakata ta mayar dakomai. Dukda itama ba wai tana wani san auren bane amma za'a zageta a mak’ota saboda ace wai duk kuɗin Naufal tsiyan da ya iyayi kenan.
A karo na biyu tareda Anty Uwani k’anwar mama akaje. Wannan Karon komai yayi sai san barka, akwatuna set 2 akayi mai gudu hudu making eight boxes altogether. Komai yaji duk yanda Amatullah taso tayi k’arancin Anty Uwani bata fuska ba, dole ta hakura da duk wani mugunta data soyi babu hali. Dama akwaita da san Duniya taso ta siya fake abubuwa saita ci sauran kudin.
Itama Anty Saudah akwati set guda tayi purple Calvin Klein mai guda shida. Saboda ita ta dauki Naufal a matsayin yaronta bana kishiya ba. Gabaki daya set din akwatuna uku akayi wanda za’a kaima Fadeela.
********
Kwance yake akan three seater yana kallon JSC sport, favorite sports ɗinshi ake nunawa watau Badminton but baya ganewa. Tunani yakeyi kala kala ranshi duk ya jagule.
Mommyn shine ta shigo ta soma magana, “Kaiko Khattab tun dazu Lili ke ɗakin ka tana jiranka amma kazo falon Daddyn ka. Halan ka daina san Lili din ne?” sai kuma ta fashe da dariya tareda faɗin, “Khattab na Lili babu mai raba ku. Nasan kaima baka ji dadi da akace saita gama school kafin ayi bikin ku, but karka damu yau da gobe duk ɗaya ne wajen Allah.”
Yak’e kawai yake mata saboda yanzu kwata kwata baya son zancen Lili, dama bawai Santa yakeyi kawai yanuwan taka ne sai aka kai baikonsa dana Lili. Toh dayake ta haɗu iya haɗuwa yasa baiyi gardama ba. Amma yanzu komai zai faru saidai ya faru saboda shi k’anwar Naufal yakeso.
Dukda yasan cewa yarinya ce kuma gata da taɓun hankali amma shifa yaga matar aure saboda ko Naufal bai isa ya hana shiba.
“Yaya Khattab nan dama kake shine ka barni Inata kewarka” Lili ta Faɗa tana shagwaba tareda yauki kamar kuɓewa.
“Eh” ya amsa mata dashi saiya mayar da hankalin shi kan Plasma dake bango.
“Yanaga kayi shiru? Ko yunwa kake ji?”
“Eh”
“Na dafa maka Indomie ne?”
“Eh” shifa abinda yasa yake amsa mata da eh kawai bai wuce baiso ya bata fuska takama mashi surutu ba. Domin idan ta fara tana jin kanta kamar ta haɗiye radio. Amma ya lura Sam bata ganewa, ko ka bata fuska ko baka bata ba saita yi.
Harta kai kofa ya dakatarda ita, “A haka zan aureki kina dafa min Indomie?” murmushi tayi tareda dawowa kujera ta zauna daf dashi tareda rik’o hannunsa, “Yaya kada ka bari k’aramin abu kamar girki ya shiga tsakanin mu.”
“But kinsan farinciki na shine naga kwanan abinci koh?”
Shiru tayi na wasu seconds haka saita ce, “Akwai masu aiki ai, kokuma muje restaurant muyi ordering abinci irin mai yawa wanda ake stocking a fridge kaga da munji yunwa sai dai muyi micro waving”
“Lallai” ya iya faɗi kawai domin abar maganar.
25 mins later......
Lili ne ta dawo tareda tray ɗin abinci a hannun ta, Indomie ne wanda yasha kayan haɗi, daga su carrots, peas, sweet corn da baked beans duk ta kwaɓa. Amma yana sakawa a baki ya shak’e ya kasa haɗewa. Idanun shiya firfito duk yayi ruwa. Da sauri Lili ta tallafa mashi kafaɗan shi, “Yaya Lafia?”
“Na kware ne”
Roban chi exotic dake wajen ya kurɓa, bai barsha ba saida ya shanye.
Tunanin shi ɗaya bai wuce ina zaije da sauran abincin. Bcs yasan cewa mata basa so idan sunyi girki ak’i ci. Rashin dadin Indomie ɗin baya misaltuwa, closest da zai iya faɗi shine kamar an wanke kan tsohuwa ko mahaukaciya k’azama.
Haka ya sake tura wani loma tareda taimakon ruwa. “jeki dauko min wani exotic kinga bai isheni ba”
Da fara’arta ta mik’e tayi downstairs hanyar kitchen. Yana ganin tayi nisa ya tashi da gudu yayi hanyar bayi domin yayi flushing din abinci ciki. Ya dawo ya zauna kenan yana haki sanadiyar gudun dayayi saita dawo.
Kallo ɗaya tayima kwanon saita sakar mashi wani lallausar murmushi tareda fari da idanu. Shima murmushi yayi tareda sosa k’eya.
“Narrow escape” ya faɗa a ranshi. Ita kuma ta mik’a mashi exotic ya hau kyankyama. Yana gamawa saiya dauki mukullin motarsa yayi hanyar k’ofa, “Bari naje wajen Sambo” bai jira amsa dinta ba ya ficewarsa.
Abokinsa Kabir Sambo shine suke haɗa baki dashi idan zashi wajen Miemie incase an tambaya. Yana tafeyana tunanin irin artabu da za’a sha idan ya kuskura ya furta Soyayyar Miemie but he can’t help it.
Dama in life you don’t chose who you fall in love with. Yana isa gidan gonar Anty Saudah maigadi ya buɗe mashi saboda sun saba. Kai tsaye Babban falo ya wuce, Anty Saudah kawai ya riske a falo tana kallon Sunna TV.
Rinsinawa yayi ya gaishe ta saiya zauna akan One seater, ya shafa’a ya mance da komai yana danna waya saiya ji kamshin turare ya dake hancin sa. A hankali ya ɗaga ido yaga ko waye, Saida ya k’ara murje Idonshi da kyau kafin ya ganeta.
Sanye take cikin wani peach Da viva wanda yasha ɗinkin shoki. Dayake kwanan biyu Bilqees tana gidan ita tayi mata daurin gwargwaro saboda ta lura Khattab baa matsayin k’anwa ya dauketa ba fyace masoyiyarsa, shine tace bari tayi surprising ɗinsa.
Light makeup tayi mata na nude lips sai light smoky eyes. Saida ta kwaɓeta akan tayi tafiya a hankali kuma karta faɗa jikinsa. Dayake kanta yana ɗan daidai kwanaki biyu haka tayi duk abinda akace tayi.
Sallama tayi a hankali cikin siririn murya saita kame a one seater. Shi kuma bai samu daman amsawa saboda ya shagala yana tunani. Gabaki daya ta canza ba Miemie yar 14 yrs ba, ta zama cikarkiyan mace san kowa k’in wanda ya rasa.
Naufal ne ya shigo saiya lura da meke faruwa, snapping fingers dinshi a iska yayi tareda cewa “ me kake kallo haka?”
Dariya yayi tareda cewa, “Haskena”
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 12 ✨✨✨
It was narrated from Aws bin Aws that The Prophet (pbuh) said: "One of the best of your days is Friday. On this day, Adam was created and on this day he died, on this day the Trumpet will be blown, and on this day all creatures will swoon. So send a great deal of salah upon me on this day, for your salah will be presented to me." They said: "O Messenger of Allah (), how will our salah be presented to you when you have decomposed (after death)?" He said: "Allah (SWT), the Mighty and Sublime, has forbidden the earth to consume the bodies of the prophets, peace be upon them." (Da'if)
***********
Kallon up and down Naufal yayi mashi sai yayi kwafa ya zauna shima a falon. Abin baiyi ma Khattab daɗi ba amma babu yanda zaiyi tunda gidansu ne.
Shi dama yaso a hankali da lallaɓi da wayau ya rinka cusa mata sanshi a zuciyarta but ga wanta yazo yayi masu k’erere.
Miemie ta riga ta faɗa mashi yayanta yana fushi da ita idan tayi mashi maganar sabuwar amaryarsa, so daga dukkan alamu baya san auren da za’a yi mashi. Shi dai abinda ya sani cewa soyayya gamon jini ne kuma dashi aka haife mu, kuma yana saka ran ya haihu dashi saboda haka idan Naufal bayayi toh shi yana yi.
Hankalin kowa yana kan TV a Nickelodeon channel inda ake nuna Sponge Bob Square Pants. Wannan shine favorite program ɗin Miemie Kuma idan kana Santa dole ka kalla.
Ni dai Khattab bana gane abinda ake nunawa, jefi jefi saina kalli inda Miemie take. Sau da dama idan nayi haka muna haɗa ido da Naufal sai ya haɗa girar sama dana k’asa.
Dama tun kafin shigowar Miemie Anty Saudah ta koma ɗaki, haka na gaji da zama na tashi zan tafi.
“Lil sis Haskena, goodbye and see you tmr” Sai na ɗaga mata gira. Shi kuma sai na bashi hannu muka gaisa. Ashe abin ya bala’in bashi haushi har na buɗe murfin mota zan shiga, “Khattab ji mana” ya faɗa.
“Lafia dai koh?” na tambaya.
“me kakeso wajen k’anwata? I mean Wats ur end game?”
“Ban gane question ɗin ba”
“Okay! Bari nayi maka dalla-dalla, kasan cewa kanwata batada lafiya kuma she is young. So Karka ce mun duk kuɗin ka da aji itace yarinyar da kake so which kasan bazan yarda ba. Nasan cewa kawai kanaso kayi taking advantage ɗinta kuma bazan iya bari haka ya furu ba.”
“So tun kafin ranka ya ɓaci gwara ka nisance duk wani plan ɗinka bcs Miemie tayi maka nisa kamar sararin samaniya.”
Shiru Khattab yayi na wasu ‘yan mintuna sai yayi ajiyar zuciya kafin yace, “Wallahi banida wani manufa daya wuce alheri tsakanina da ita. Thou nasan tayi k’arama kuma bai kamata na furta mata komai. But ni zan iya jiranta harta k’ara wayau. Please YaNaufal kar ka rabani da ita saboda bansan halin da zan shiga ba”
Yana kaiwa nan sai wayar shi tayi k’ara, Suna ɓaro ɓaro ya fito akan screen wanda aka rubuta ‘Bae’.
Harara Naufal ya watsa mashi saboda shima ya karanta, kai tsaye wajen mai gadi ya wuce, “Karka k’ara barin wancan ya shigo mana gida”
“An gama Oga daga yau ya gama” Mallam Bello mai gadi ya amsa.
Har ya soma tafiya ya hau benen dake varenda saiya juyo ya kalli Khattab tareda faɗin, “For thelast time baka babu ita” saiya garke kofa.
Shikuma Khattab ya rasa mai zaice bcs tabbas Naufal yaga daidai but locacin suna ɗasawa da Lili shine yayi saving ɗin sunanta as ‘Bae’ amma number ɗin Yafi six months da ɓacewa so bata amfani da shi gashi ya mance yayi deleting.
Jiki babu kwari ya shiga motarsa zai tafi saiga Miemie tazo da sauri, “Yaya Khattab tsaya kaji wani abu”
Mamaki k’arara a fuskarshi saboda tun dayake da ita Naufal take cemasa.
“Kaga ɗazu nayi shiru koh? Toh wlh Anty Bilqees tace wai na daina magana a gaban ka, duk mekace min kawai nayi murmushi ne. Sai kuma me ta ce min......” ta ɗaura yatsan ta akanta tana tunani.
Tun da yake da ita sai yau ya tabbatar da ciwon na gaske ne bcs anyi abu a sirri tazo tana faɗa mashi. Murmushi kawai ya rinkayi bcs Dis is the least of his problem.
“Sai kuma me tace?” ya tamabayeta
Shiru tayi kafin tayi ihu tareda daka tsalle, “Yauwa na tuna.... Wai na rinka kiranka da Yaya Khattab”
“Toh kice ma Bilqees nagode sosai, bye Haskena be a good gal kinji koh”
Gyada kai tayi alamar Okay, shikuma ya tafi.
A mota yana tuk’i yana tunanin wani matsala zai fara magancewa, Naufal ko Lili?
******
“Wa’anan Sune last set koh?” Mommy ke tambayan Fadeela.
“Eh Mommy, kinsan tun jiya na fara kaiwa”
Shiga mota sukayi suka bar haraban gidansu, tafe suke zasu Larema inda Fadeela zata yi exhibiting Art works ɗinta. Su paintings ne daya jiɓanci k’orama, sararin samaniya, ciyayi da gonaki, fituwan rana da saukar shi, hasken taurari, al’adun Mallam bahaushe da sauran k’abilu.
Akwai kuma laka data k’era abubuwa daban daban kai duk dai kayan Arts. An gyara hall an gayyaci manyan ɓaki kuma duk sun hallara.
Grand Kadi ne ya buɗe taron da addu’a sai aka bama Fadeela dama tayi bayani akan abinda ta zana. Yarinya mai hazaka tayi komai gashi turanci ya zauna mata a baki. Bayan ta gama sai mutane suka shiga siye, wakilin Commissioner of Culture and Tourism ya siya guda uku wanda za’a kai gallery ɗin ma’aikatan su.
Su Jawahir da Mijinta suma sun dauki ɗai-ɗai, an siye komai saura guda ɗaya kuma shi ne wanda Fadeela tafi so, wanine ya shigo da saurinsa ya ɗauka tareda biyan kudin.
Bayan komai ya daidaitu sai Fadeela da k’awayenta suka keɓe ana hira tareda tanɗe-tanɗe.
“Oh yanzu baza mu k’ara taruwa haka ba sai bikin Deela” Samɗa ta faɗa
“Aikuwa dai” Mansura ta chapke.
Ita dai Deela bata ce komai ba illa wasa da Ihsan yarinyar Samɗa. Kawai a ranta tana sha’awan dama ɗiyarta ce. Batada wani buri a duniya daya wuce ta haihu amma tasan cewa indai da Naufal ne to zata bushe!
“Saura kwana nawa yanzu?” Samɗa tayi tambaya tana kallon Deela, taɓe baki tayi tareda faɗin, “Ni ina na sani, kya tambaya kaza hanyar rafi ai agwagwa zaki tambaya Kisha labari. Sai kije ki tambaya wanda zasu min auren” ta faɗa tana matse kwalla.
“Babban magana!” Mansura ta faɗa sai sukayi shiru.
Mommy ne tazo wajen zamansu tareda Baby Fauziya yarinyar Jawahir, “Halan baki gayyaci Naufal bane naga bangan shiba?”
Tsuru tsuru Deela tayi saboda tabbas Mommy ta gargaɗeta akan lallai saita gayyaci shi toh amma bata san yanda zata fara cewa batada number ɗinsa ba kuma koda ta ɗauka a wayar Mommy bata san me zata ce masa ba.
Da Mommy taga Fadeela batada gaskiya sai tayi kwafa tareda Faɗin, “Kin kyauta tunda ke bakya jin magana” saita juya ta bar wajen.
“Wai meye haka kike yi ne?” Samɗa ta faɗa.
“Inace duk cikin mu kinfi hankali amma shi ne kike so ki nuna ba’a yaban ɗan kuturu saiya girma da yatsa”
“Wai tsakani da Allah meye aibun Naufal? Ga kuɗi ga kyau dream ɗin yanmata amma shine kike misbehaving”
“Please Karki basu mommy kunya kinga dai yanda suke ɗawainiya dake,”
Buɗen bakin Fadeela saita ce “Nifa ban masa komai ba ya tsane ni tun kafin a kaini gidansa kenan! Shikenan dan mutum baya magana sai a taka sa?”
“Toh ai kece mace saboda haka dole ke zaki rage girman kai kiyi masa biyayya. Wai shin wani irin zama kike so kuyi idan an kaiki? Doya da manya? Wallahi yarinya ko mak’iyina bana ma wannan fatan”
“Ya isa haka ni bari naje na samu ma Ihsan Bobo ta sha” Deela ta faɗa tareda barin wajen.
Dariya Samɗa kawai tayi tareda faɗin “Wasa kike yarinya, baki san aure ba wallahi! ”
Daga ɗayen ɓangaren bayan Khattab ya tafi, Naufal yazo wucewa wajen Larema saiya ga Flyers na Art exhibitions haka, a cikin hoton saiya hangi akwai paintings ɗin fitowa da saukar rana shine yaje siya. Yanda gurin ya cika sai kawai yayi parking ɗin motarsa a waje tareda bama Secretary ɗinsa kuɗi ya siyo mashi kuma cikin ikon Allah the last one that was remaining shine choice ɗin Naufal.
Shidama tun fil azal ya saba suje su kalle sunset da sunrise tareda Anastacia, yasa daya ga paintings ɗin ya kwallafa saiya siya. Thou yanada paintings shigan haka a ɗakin shi but their is smtin unique about dis one.
Ya gama duk wani harkar gabansa na ranar ya koma gida, ya kai painting ɗin dakinsa yanata neman inda zai ajiye. Duk ɓangaren daya saka sai yaga baiyi ba, a karshe awards ɗinshi dake manne a bango ya cire ya saka.
“Perfectly placed” ya furta a fili. Hannayenshi yana harɗe akan kirjinsa yana kallon painting ɗin yana murmushi sai idanshi ya hange wani rubutu a ciki ta gefe, “Deela” aka rubuta da style ɗin calligraphy.
Murmushi ya sakeyi tareda faɗin “koma waye Deela, you’re talented and unique” hayewa gadonsa yayi tareda dai-dai har barci ɓarawo yayi awon gaba da shi.
10:45pm.....
Locacin ne Khattab ya bar gidan Sambo ya koma gida. Yana isa cikin gidan sai ya risk’e wutan falo a kashe, jindadi mara misaltuwa ya kamashi saboda kwata kwata baya son ya haɗu da Lili.
Yana isa wajen stairs sai yayi karo da wani abu tim ya kusan faɗi. Karon rago yayi da Lili wanda ta kefa kanta akan gwiwoyinta tana sharban kuka.
Da hasken waya ya haska mata fuska saiya lura idanunta sunyi luhu luhu. “Daga ina kake?”
Kallon up and down yayi mata baice komai ba saiya ratsa ta ya haye sama abinsa.
“Da Kai nake Yaya Khattab, ina kaje ka daɗe haka? A haka zan aure ka kana kaiwa tsakar dare? Wallahi da sake wai anba mai kaza kai”
“Toh uwata jirani nazo nayi maki bayani” ya faɗa mata still bai waiga ba.
“Gaskiya Yaya I won’t tolerate it, saboda haka dole ka bani kwakwaran dalili idan bahaka ba......”
“..... Idan ba haka ba me zai faru?” ya juya a fusace yana kallon ta, ido cikin ido yana haki duk ranshi ya baci. Ita kuma jikinta ya soma rawa duk ta tsorata.
Hannunshi guda ya daura akan shoulder ɗinta sai ya soma magana cikin raɗa raɗa, “Daga yau sai yau, Karki k’ara min tambaya daya wuce gona da iri. Babu ruwanki da al’amura na,....” sai ya cize leɓansa tareda saketa.
Dakinsa ya wuce direct, ji kake Dam ya banko k’ofa. Ita kuma da sauri taje ta rinka bugawa. Sababi takeyi babu kama hannun yaro wai bazata bar wajen ba saiya buɗe.
Shikuma direct bayi ya wuce yayi wanka, yana dawowa ya saka green three quarter da farin singlet. Still yana jin mostin ta a kofa tana kuka. Wayanshi ya dauko ya shiga YouTube ya fara kallon video.
Bubbuga k’ofa ta k’ara yi wannan karon harda kafafuwanta, Mommy ce ta fito tayi mata magana amma tayi kunnen uwar shegu da ita.
“Badake nakeyi ba, nace ki bari ya isa haka”
Tsandara ihu tayi tareda faɗin, “Mommy ni bansan meyasa yake min wulakanci ba for no reason”
“Ki bari gobe zan ci masa but go and sleep yanzu” saita jawo Lili jikinta tana bubbuga mata baya har suka bar wajen.
Yana jin duk abinda sukeyi amma bai sa ma su baki ba, Sam bai ji daɗin yanda Lili take treating Mahaifiyarsa ba but duk laifin Mommy ne.
Itace tace ta dawo gidansu da zama, yanzu shekara ɗaya kenan. Kuma ita ce ta cusa ma Lili idea taso shi, gashi idan tayi magana anyhow bata kwaɓan ta.
Saidai bazai dauki iskanci ba, tana mashi yake mata ko sanda yake santa balle da yanzu komai salam.
Kawai yasan cewa akwai ranar k’in dillanci, wai randa babban rigan Maigari ya ɓace.
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 13 ✨✨✨
On the authority of Anas, who said: I heard the messenger of Allah say: Allah the Almighty has said: "O son of Adam, so long as you call upon Me and ask of Me, I shall forgive you for what you have done, and I shall not mind. O son of Adam, were your sins to reach the clouds of the sky and were you then to ask forgiveness of Me, I would forgive you. O son of Adam, were you to come to Me with sins nearly as great as the earth and were you then to face Me, ascribing no partner to Me, I would bring you forgiveness nearly as great as its." Related by Al-Tirmithi, who said that it was a good and sound Hadith.
******
Muddin an tsayar da lokacin abu toh inda rai da lafiya sai anyi. Yau Asabar kuma yazo daidai da ranar tarban lefen Fadeela.
Lefe yana daga cikin al’ada na Mallam Bahaushe idan zaayi aure, ya jiɓanci kawo kayan sawa dana amfani daga dangin miji zuwa ga amaryarsa. A al’adan daya gabata ana kaiwa a cikin kwalla ko makamancin haka, amma yanzu zamani yazo da su akwati seti seti.
Toh dayake Fadeela yar zamani ce itama akwati aka kai mata, akwatuna guda goma sha huɗu watau seti kala uku wasu ‘yan huɗu wani mai shida.
Kamar yanda al’ada ya nuna, ana taruwa a gidan Amarya tareda yanuwa, makwabta da abokan arziki. Ana tanajin su kayan motsa baki kamarsu Sambousah(Samosa), Meatpie, spring rolls, peppered chicken or meat etc Wanda za’a bama dangin miji as tukwici.
Mommy itama ta tsaya a tsaye saida taga an tanaji komai na bak’in. Anty Saudah itace a gaba wajen ganin komai ya kankama daga ɓangaren su, mota uku sukayi aka dunguma GRA inda gidansu Fadeela yake.
Kowa ya hallara a babban falon Grand Kadi ana zaune, Anty Uwani ta buɗe taro da addu’a sai aka fara. Gwaggo Mahaifiyar Grand Kadi aka mik’a ma trinket box.
Ran Anty Saudah fari sol saboda bataji kunya ba, itama Mommy ta yaba da kaya saboda komai yaji Tabarakta Masha Allah.
“Wai banga Amaryar bane?” Anty Saudah ta Faɗa
“Eh nima inaso na ganta” Miemie ta chapke.
“Kunsan ta da kunya, wallahi tun jiya ta dawo gidana kada ku riske ta” Hajia Rabi matar big Daddy ta amsa.
“Babu komai muda zata dawo cikin mu da zama” Anty Saudah ta faɗa tana dariya.
“Allah ya Kaimu lokacin, yasa ɗakinta ne ya kuma basu zuri’a ɗaiyiba” Maman Humairah makwabciyar su Fadeela ta faɗa.
“Amin summa Amin” kowa ya faɗa.
Daga nan sai aka basu tukwicin kuɗi tareda na abinci aka watse.
In ran Miemie yayi dubu to ya ɓaci, taso taga amaryar amma bata samu dama ba. Dayake da Abla akaje sai tayi mata raɗa ko suje gidan Hajia Rabi don suga Fadeela. Harara ta daka mata wanda ya natsar da ita.
Ita kuma Fadeela tun jiya take kuka data lura abin da gaske ne. Yanzu saura sati biyu cur a daura mata aure da wanda baya santa. Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin haka zai faru ba.
Ita irin Telemundo gal ce, batada wani buri daya wuce tayi zaman soyayya da mijinta thou bawai ta taɓa yin shi Soyayyar bane, but still!
Kuka tayi babu k’akkautawa tana k’okarin ta tattara tunaninta waje ɗaya ta gano dalilin da Naufal ya tsaneta amma ta kasa ganewa, ita dai ba wai ta sanshi bane daga wani waje balle ace wani abu. Kawai dai ta lura idan ya ganta har wani jijjiga yake saboda bala’i.
Tashi tayi tsam ta wuce bayi ta daura alwala, sallah raka’a biyu tayi tareda mayar ma Allah komai. Tasan cewa nata jarabawar kenan kuma tana fatan taci da flying colours.
Bayan la’asar sakaliya Hajia ta dawo daga wajen tarban lefe, washe baki kawai takeyi tana murna.
“Amma ‘yannan kinyi tagomashi. Lefe sai kace na yaran sarakuna kokuma masu gwamnati” Hajia Rabi ta faɗa
Murmushi kawai Fadeela tayi ta cigaba da kallon wani reality program a ‘E’ mai suna The Rich Kids of Beverly Hills. Hajia Babba sai kawo mata maganar lefen takeyi amma bata sakar mata fuska ba, dolenta ta hakura da hirar.
******
Kullum sai Khattab yaje k’ofar gidansu Naufal sau biyu ko uku amma baya samun damar yaga Miemie.
Sau biyu yana riske Naufal amma baya bashi dama ya shiga. Babu irin magiyan da rok’o da bai yiba amma ko kulashi baiyi ba. Ita kuma Miemie tafiya Naufal ya faɗa mata Khattab yayi, harda karyan cewa ai randa yazo sallama yayi mata saidai bata lura ba.
“Allah ya dawo dashi lafiya” abinda kawai ta iya faɗi kenan saboda tasani sarai k’arya yakeyi.
Sau da dama Khattab yana zuwa makaranta Miemie amma Naufal har cikin school yake shiga da motarsa ya dauko ta. Da abin ya isheshi saiya mayar da ita gidansu wajen Mama wai tayi mata hutu tunda yasan Khattab baisan wajen ba.
Shi kuma Khattab abubuwa sun cunkushe mashi, na farko an hanashi ganin Miemie. Na biyu kuma jarabar Lili, tariga ta raina shi kamar mijinta ko sa’anta. Kullum suna cikin bala’i kamar kaji kuma koda yaushe Mommy tana mara mata baya.
Fatan shi ɗaya next week Mommy Zata tafi Ummarah kuma gashi Daddy ba mai zama bane, Lili tana mashi yayi mata ɗan iskan duka da saita raina kanta. Ya ɗauki alwashin saiya saisaita mata duk wani rawar kan datake tak’ama dashi kuma gashi mai cecenta bata nan.
Sam Khattab bai iya tashin hankali ba sai sanda ya dawo gida bayan yayi graduating Masters ɗinshi a Almadina University dake Shah Alam Malaysia. Ya karanta Information Technology kuma yanzu haka yana serving a wani ICT center haka Thou ba kullum yake zuwa ba.
Khattab dai fari dogo ne, yanada cikar halitta kuma fuskar shi akwai saje wanda ya kara k’awata wajen.
Shi cikakken bakano ne a wani gari da ake kira Danbatta. Mahaifin shi IG Hamza Aminu Danbatta ya aure mahaifiyarsa Hajia Shatu kumaAllah ya albarka cesu da yaro ɗaya tilo watau Khattab.
Bayan wasu shekaru sai k’anin IG watau Alhaji Ibrahim ya aure k’anwar Hajia Shatu. Sun haifi yara uku, Usman, Halima wanda ake cema Lili sai auta Lubna.
Lili shekarunta 19 a duniya kuma tana School of Nursing and midwifery dake ATBU a garin Bauchi. Yanzu haka tana 3rd year ɗinta.
Kyakyawan yarinya san kowa k’in wanda ya rasa saboda Allah bai rageta da komai ba wajen fannin halitta, in hasken ne tana dashi, tsawon gashin shima kazo wajen, shape kamar an zana number ‘8’, zak’in murya ka samu.... In fact everything.
Saidai dama ɗan adam tara yake bai kai goma ba, kyau kawai gareta babu halin kirki. Yanda kasan empty vessel ko fanko to haka take. Kwata kwata batada daɗin sha’ani. Bata iya magana ba at all, duk abinda ya fito daga bakinta zata yaɓa maka kuma ko taji kunya saidai na gefenta su ji. Ga tsiwa ga rashin kunya ga kuma bala’i koda yaushe kamar dage.
Tun kafin Khattab ya dawo daga school Mommy ta dauko Lili ta dawo da ita gidan saboda yana dawowa yayi arba da ita su fara soyayya. Duk mugun halin Lili Mommy bata gani, ko tana mayar da abin yarinta ne ko kuma menene dalilinta Oho?
Sau da dama Lili na chaba ma Mommy magana amma sai Mommy ta kauda kanta. Sanda Khattab ya dawo yaga Lili yayi Na’am da batun Soyayyar su saboda yar gaban mota ne, but daga baya daya lura da halinta saiya fara ja da baya da ita but yanzu dai it’s too late saboda Har Iyaye maza sun shiga maganar.
Shi Khattab mutum ne mai san girma kamar gyambo ita kuma Lili akwai k’ask’anci, yasa idan suka fara gardama basa tsayawa. Tun yana kyaleta amma yanzu ya dauki alwashin tana mashi zai rama, when it comes to Lili to bayada hakuri kamar zawo.
Shidai ya gwammace ya zauna da wanda rashin hankalinta ciwo ne kuma idan sauki yazo mata tanada daɗin sha’ani da yazauna da Lili, Wannan kenan!
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 14 ✨✨✨
On the authority of Sahl bin Saad Al-Saedi, who said : A man came to the prophet and said: "O Messenger of Allah, direct me to an act which, if I do it, [will cause] Allah to love me and people to love me." He said: "Renounce the world and Allah will love you, and renounce what people possess and people will love you." A fine Hadith related by Ibn Majah and others with good chains of authorities
*********
Yanda yaga rana haka yaga dare, tsaye yake gaban agogon bango. Kallon kur yayi mashi yana kallon sauran awanni nawa a daura mashi aure da ‘Bad luck’ wanda shi bai taɓa kiranta da sunan taba.
Duk jijiyoyin fuskarshi ya mimik’e, idanunshi sunyi jazur daga bacin rai da kuma rashin barci.
“Wai tsakani da Allah a ina aka taɓa yima namiji auren dole?” ya faɗa da karfin gaske tareda naushin bango.
Hura iska ya rinka yi ta baki da hanci.
Rabon daya kwana a gidansu kwana huɗu kenan tun kafin zuwan ‘yan biki. Da akayi mashi magana saiya wayance wai bai so ya takura ma mutane ne.
Mama taji daɗin abin sosai saboda ya nuna yanada hangen nesa. Shi kuma abinda yasa ya bar gidan baifi rashin san yaga yanda ake shige da fice kuma daya ci karo da mutum zai iya sanya alheri a lamarin kuma abinda baya so kenan.
Baisan gaibu ba amma baya jin akwai alheri a tareda lamarin.
11:09am abinda ke rubuce akan agogo, “Saura awa uku a kaini makisa na”
Bayi ya shiga yayi wanka saboda ya mance rabon dasu haɗu da ruwa saboda tashin hankali, yana fitowa ya nema inda wayarsa na handset yake. “20 missed calls” ya gani.
Shiru yayi daya lura da wanda yayi Most Call ɗin. Abbanshi ne tareda Anty Saudah kuma indai abu daya jiɓance bukin ne toh basa raga mashi, yanzu yanzu sai suyi balangu da namanshi.
Shi abinda yafi bak’anta mashi rai bai wuce yanda Fadeela ta saka soyayya ɗinta a zukanta yan uwanshi. Wai tun ma kafin ta shiga kenan!
Mutum ɗaya ce ya lura bata san abin, watau Amatullah amma tana aure a Gombe balle su taru su musguna ma Fadeela.
Daga ɗayan ɓangaren Fadeela ta saka bala’i baza ayi mata kowane gyaran amare ba. Tun ana binta da lallami da ɗadin baki saida Mommy ta shiga jikinta da duka, farfasa mata jiki tayi sosai saboda hanger ta ciro a drawer ta rinka auna mata.
Hajia Rabi matar big Daddy ta shiga tsakaninSu, Mommy ta rinka sababi duk takaici ya isheta.
“Ke bahun ubanki, yar tselan uwa! ” mommy tayi ashar bata masan tayi ba.
Ita dai Fadeela kuka takeyi kamar ranta zai fita, wai akan Naufal aka taɓa lafiya jikinta. Abinka da farar mace duk ta kumbura tayi jazur, kana ganinta saita baka tausayi. Idanunta sunyi k’anana saboda kuka da rashin isharshen barci.
Ta hakura za ayi mata auren dole amma babu wanda zai mata wani gyaran jiki, ko kitso bata so kawai a kyale ta.
A daki Hajia Rabi ke mata nasiha akan rashin bin maganar iyaye amma abin baya shigan Fadeela, sai kawai tace mata, “Wannan rashin kunyan da fitsara da kikeyi halan wani yace ki kashe auren ki ne zai aure ki?”
Sai a locacin abin ya dake ta, Sam bata so tayi zawarta da wuri kuma ita batada wanda ke jiran ta. Nan take tayi ma kanta karatun ta natsu, bcs ga yanmata birjik a gari babu mazajen aure ita ta samu tana yanga.
Tun daga lokacin aka samu kanta, har kitso da kunshi ta yarda anyi mata. Da aka yi mata maganar tsimi da maganin mata sai kawai ta taɓe baki tareda kawar da fuska.
Nan aka kyaleta ba’a kuma takura mata ba. Ta ɗanyi fara’a sosai ba kamar jiya ba, Mommy itama taji daɗin yanda ta sauya tana harka cikin ‘yan uwanta.
Koda Mommy tayima Naufal magana ko yanada events ne dayake so Fadeela tayi attending, sai yace mata shi bazai yi komai ba. Amma kuma ya tambayeta idan akwai wani abu daga nasu ɓangaren, uku uku zuciyar shi ke bugawa saboda baiso wani abu ya haɗashi da ita.
Gaskiya bazai iya zama waje ɗaya da ita ba, ai saiya rasu!
Kaddara ta riga fata saboda Mommy tayi assuring dinshi suma ba zasuyi komai ba. Kuɗi sosai ya aika ma Fadeela wai kada tayi lacking saboda sha’anin biki.
Har cikin ran Mommy taji daɗin abin, ita kuma Fadeela da farko taso tak’i amfani da kuɗin amma sai ta tuna bahaushe yace ‘Raba mugu da makami ibada ne’ nan take ta soma fachaka tana spending anyhow.
2:30pm......
Hausawa sunce ranar wanka ba’a ɓoye cibi, an daura auren Naufal Hussain Beli tareda Amaryarsa Fadeela Abbas Bello akan sadaki naira na gugan naira har Dubu dari ɗaya.
Mutane daga kowane ɓangaren Bauchi har Nigeria baki ɗaya duk sun hallara. Kowa yazo ya tayasu murnar wannan haɗin tunda duk gidan mutunci ne aka haɗa.
Walima mai rai da lafiya akayi wajen ɗaurin auren, kowa ya goge wuyansa da abinci yanda ya dace.
Suma daga cikin gida kawai shige da fice na abinci akeyi, kowa fuskarshi a washe kamar gonar auduga anata raha. Mommy ranta fari sol ta aurad da yarta. Ita Fadeela fuskantar babu yabo babu fallasa take abinta. Kowa ya yaba da yanda ta sake jiki tana komai.
Su Samɗa, Sadiya da Mansura sune kan gaba a k’awayenta. Dayake Sadiya taje Makeup school ita ta tsala ma Fadeela kwalliya mai rikitarwa. Tayi kyau sosai babu kama hannun yaro, ko Fadeela tayi mamakin yanda kimanin ta ya sauya farad daya.
Ta tabbata idan Naufal ya ganta sai zuciyar shi ya sosu ya rage tsanarta, dama itama saboda ya tsaneta shine take mayar mashi da martani.
Basai ta faɗa ba amma kowa yasan zaman doya da manja zasuyi dashi, ita kawai adduar daidaituwan tsakanin Su zatayi saboda Sam bata saba da faɗa ba kokuma a zauna a gida ɗaya ba’a ma mutum magana ba.
Tarbiyan da akayi masu shine bayan ka faɗa ma mutum laifin shi toh komai ya wuce an rufe babin amma ba wai ayita jan magana ana haɗuwa ana banka ma juna harara ba.
Shikuma Naufal ya saka wani dakarkiyar farin shadda wanda akayi mashi dinkin zaren hannu kuma babban rigane tareda yar ciki da wando. Farin hula da agogo duk ya haɗa dashi. Thou yana san saka fararen kaya but still Abba ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura yazo wajen ɗaurin auren kamar rainbow.
Fara’ar dole ya rinka yi yana shan hannu dasu, ana sanya mashi alheri shikuma yana amsawa ciki ciki. Haka yayi tayi har taro ya watse.
8:30pm....
Kuka babu kama hannu yaro Fadeela keyi a yayin da ake mata nasiha. Duk ‘yanuwa an taru anyi mata nasiha mai tsuma rai. Mommy kasa cewa komai tayi tanata sharban kuka, fyace majina take da haɓan zaninta. Kowa tausaya masu yakeyi saboda an san yana yin shakuwan su. Duk inda akaga Fadeela zaaga Mommy, barci kawai ke rabasu kamar k’awaye.
Ajiyar zuciya Mommy tayi tareda gyaran murya “ Dan Allah idan ankai ki inaso ki nuna mashi cewa daga gidan mutunci kike. Yi nayi, bari na bari a koda yaushe”
“Ba yau aka fara karatun zaman aure ba, ke mai ilimi ce kuma kinsan right and wrong. Please show him how well trained you are, kada Kiyi abinda za’a ce waye mahaifiyar ki da batayi maki tarbiyya ba.”
“Kinsan cewa aure ibada ne kuma idan kikayi da kyau zai iya sanadin shigar ki aljanna, nima nan da kika ganni nawa ibadar nakeyi kuma bana fatan denawa sai ranar mutuwa na”
Haka Mommy tayi ta mata nasiha daga nan tace, “Duk abinda kikayi min wanda na sani da wanda bansani ba duk na yafe maki da fatan Allah Mahaliccin ya yafe mana baki daya.
A haka Fadeela ta faɗa jikin Mommy tana kuka wiwi kamar wanda za’a kai makisa. Dakyar aka rabasu, Anty Saudah da sauran yanuwan Naufal sunji tausayinta ainun saboda rabuwa da mahaifa bashida dadi.
Haka aka kaita gidanta wanda daga ita sai halinta da zai kwaceta. Anty Saudah ta sallami duk k’awayen amarya wai babu wanda zai kwana a gidan saboda dole ta fara neman aljannarta from the first day.
An sake fashe gidan dasu turaren wuta da room freshener komai sai san barka.
As expected, babu Naufal babu dalilinsa. Tun Fadeela na kallon wucewar agogo daga 11, 12pm, 1am. Hakura tayi taje tayi azkar ta rufe Ko’ina tareda kwantawa. Dan tsoro da kayanta na lace da alkyabba ta kwana bcs bata san stories that touch.
Shi kuma gogan jin kansa yayi kamar ɗan tasha, bayan su ABBA da Mama sunyi mashi nasiha mai shiga jiki, sumi sumi yayi kamar komai ya shige shi ashe banan gizo ke sak’a ba. Shi ya riga yayi planning ɗin zaman aurenshi.
Bayan isha’i sai yayi hanyar Club domin ya huce takaicin shi, ya ɗauki alwashin gwara ya kwana a club daya kwana gida ɗaya da Bad luck. Dayake baya shan Barasa ko wani kayan maye, VIP table ya kama aka kawo mashi fresh peppersoup na kifi ya fara bi takai.
Daga bisani aka kawo mashi zafafan tsire yana taci yana shan Smoove hankali kwance, shi dama idan yana matsakancin ɓacin rai to kawai yaci abinci komai zaizo mashi da sauki.
Bayan nan ya rinka kallon masu rawa kafin barci ɓarawo ya sace shi, “Abeg Oga wake up its 4:30 am and we want to close” Wata mai aiki a club ɗin da kayanta iya cinya take tadashi taga barci.
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun!” ya faɗa a tsorace tareda ja da baya saboda ta firgita shi da kamininta.
‘yan kunnaye wajen shida shak’e a kunnuwanta, ga kuma ta huda k’asan bakinta wajen gemunta kuma shima ta bishi da ɗan kunne round babba. Eye shadow ne blue ɗampare a idonta ga green jan baki ta mulka a baki, sai kuma gashin kanta ɗan guntu, shiba dreadlocks ba.... Wani k’azamin abu haka babu fasali.
Tsaki yayi, “Amma dai bariki bai yiba Wallahi!” ya wuce motarshi. Wani waje chan nesa da gidan shi yayi parking motarsa, baya ya koma ya hau barci, da kyar wajen 6:30am ya samu yayi sallah a wani masjid saiya koma barci.
7:45am....
Locacin ne aka kawo ma Fadeela abinci, Abla aka tura tareda Miemie. Ba k’aramin jin daɗin ganin Fadeela Miemie tayiba, kuma wai ance idan sun huta da buki zata koma wajen su da zama.
Itama Fadeela taso Miemie, nan take Sister’s ɗin Naufal suka burgeta. Bata barsu suka tafi ba saida ta basu kyautar underskirt, vest, eye shadow, body spray tareda lipstick.
Bayan tafiyar su tayi wanka tareda fesu kwalliyar kamar zata buki, duk wani kusurwa na gidan inda akwai switch sai ta saka burner ɗin turaren wuta, kafin 10mins gidan ya gane Amaryar ba kuchaka bace.
Abba ne ya shigo cikin falon yanata sallama tareda Alhaji Sulaiman, Shi kuma Naufal bai shiga da motarsa cikin gidan ba, yazo ne kawai a gurguje don ya canza kaya saiya ware. Baima lura da motarsu a parking lot ba hankalin shi yana abinda ya kawo shi.
Fadeela ta sauko daga upstairs kuma idonta ya kumbura saboda kukan data kwana tana yi, saiga Naufal ya shigo cikin falon tareda turesu Abba saboda labule ya ɓoye su.
Charko Charko Naufal yayi saboda ga babban rigar shi a hannu duk ta chukurkuɗe kamar ya fito daga bakin kada sannan yasan meAbba yace akan aurenshi da Fadeela.
Tsuru tsuru yayi yana adduar daya dace da wanda bai dace ba. Abba ne ya kalle Fadeela saiya kalle Naufal kafin yace, “Daga ina kake?”
#NiDaDiyata
*Shout-out to my Tawan khadeejerh Abubakar, Allah ya bar so da kauna*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 15 ✨✨✨
On the authority of Abu Malik Al-Harith bin Asim Al-Ashari said that the messenger of Allah said: "Purity is half of faith. alhamdu-lillah [Praise be to Allah] fills the scales, and subhana-Allah [How far is Allah from every imperfection] and alhamdu-lillah [Praise be to Allah] fill that which is between heaven and earth. Prayer is light; charity is a proof; patience is illumination; and the Quran is an argument for or against you. Everyone starts his day and is a vendor of his soul, either freeing it or bringing about its ruin." Related by Muslim.
*******
Naufal ɓarin laɓe ya soma yi ya rasa mai zaice, kawai kallon Fadeela yayi, irin kallon Please help me. But ya tuna da yanda dake da nawa bata abu da jiki, yasan baza tayi saurin taimakon saba.
Ita kuma dayake yar gari ce saita kakalo murmushi tareda faɗin, “Laaaa Abba yaje ɗauko babbar rigarsa ne a hotel ɗin dayake kwana kafin yan room service su kwashe”
“Ai gwara daka je da wuri, nima sun taɓa yimin gaba da agogo na” Alhaji Sulaiman ya chapke.
Dukda Abba yasan karya ne, but irin matan dayake son yaronshi ya zauna da ita kenan, mai rufawa mijinta asiri a koda yaushe itace mace.
“Okay ba matsala dama nazo naga yanda kuka kwana ne, kuma ku sani zuwan bazata zan rinka maku, so ku kiyaye!”
Naufal har k’asa ya ɗuka ya gaishe dasu Abbansa, Fadeela ma haka. Babu yanda basuyi dasu akan su tsaya karin kumallo amma suka k’i.
Bayan tafiyar su Abba, Naufal ya tsaya yana kallon Fadeela. Ita har ta fara murmushi a ranta ta samu lambar sa, shi kuma sai yanzu ya kalleta da kyau a rayuwarshi ‘Za’a je da babe ɗin nan fah’ wani siririn murya ya a ranshi ya faɗa.
Kawar da tunanin yayi da sauri,taku daya daya ya soma cikin k’asaita rai a bace har yakai wajen matakalan bene inda Fadeela ke tsaye. Bai waiga ba kawai magana yayi a bayyane, “Iska na wahalar da mai kayan kara” sai yayi gaba abinsa.
Ita kuma abin dariya ya bata saboda bata taɓa irin rayuwar nan ba. Zuwa tayi ta fara touring cikin gidan, gaskiya iyayenta sunyi kokari babu abinda zata faɗa sai Allah ya saka masu da alheri.
Shi kuma kai tsaye ya wuce master bedroom a zatonsa nanne ɗakin sa, yanda yaga komai Orange daga jere, curtains and rug Kuma ba color dinsa bane. Haushi ya kamashi wai ace shida gidansa amma bashi ke cikin babban ɗaki ba.
Rufewa yayi ya koma wani ɗaki wanda ke biye da master room din, shikuma purple ne kayan ciki. A fusace ya fito yana masifa “Wai tsakani da Allah ina ne ɗakina?”
Yayi maganar lokacin Fadeela ta gama taka matakalan bene na karshe. Tsayawa tayi tana kallonshi cikin Tuhuma irin me akayi maka saboda taga yana wani zazzare idanu.
“Ke ina ne ɗakina? Infact dan kin rainani watau ke zaki zauna a master bedroom koh?”
Shiru tayi tana kallon ikon Allah, “Kayi hakuri dama ina son Katon daki ne dats y, but bari na koma wancan” sai tayi ciki zata kwashe kayanta.
“Wa zai zauna a cikin ɗakin chan mai kalar yan secret society, salan a cinye min kuruwa na. Yi zaman ki ni saina zauna a falo” taji muryanshi.
Fitowa tayi tana nazarin shi bcs ta rasa meke damunsa, “Ga wani daki chan fari, idan kuma baiyi maka ba saina saka Mommy su kawo color of ur taste” saita nuna wani daki mai girma madaidai ci.
Kwafa yayi sai ya tafi hanyar dakin, kamshin turaren wuta ya fara mashi welcome. Dakin fari sol daga bedsheets, curtains etc. Cire takalmi yayi saiya taka carpet, wani laushi yaji mai daɗin gaske. Lumshe ido yayi yana murmushi wanda bai masan hakan ya faru ba.
Ya mike tsaye zaiyi wanka sai kuma ya tsaya yana tunani, tsaki yayi tareda naushin iska “Wallahi banso haka ba” shi yaso suyi Jani in jaka da ita ne kuma yaso batada farin daki yayi sanadiyar mata dukan tsiya.
Sai yanzu ya lura batada hayaniya at all Kuma tashin hankali bai dameta ba, Ranshi yayi mummunar baci bcs bazata bashi reason to beat her ba, kuma haka kurum bazai kama dukanta babu gaira babu dalili tunda shiba mahaukaci bane.
Ita kuma sororo ta tsaya tana ganin ikon Allah, wai zaka ga abu muddin kana raye. Ita dama farin ɗakin ta shirya mashi kuma koda aka kawo kayensa nan aka ajiye. Cikin orange room ɗin ta shiga tayi ɗai-ɗai akan gado tareda ajiyar numfashi a hankali, sai kuma tayi zumbur ta tashi da sauri.
Dakin Naufal ta wuce, a hankali ta tura kofa tareda sallama, babu wanda ya amsa Still ta shiga. K’arar ruwa taji a bayi da alamun yana ciki. Shikuma ya fito daga shi sai boxers da hand towel a hannu sai kawai ya ganta tsaye tayi zurfi cikin tunani.
“ke meye haka? Meya kawoki ɗakina?”
Rasa me zatace tayi sai kawai ta kafa mashi ido.
“Badake nake ba? Wayace ki shigo”
“Dama abincin Kane nake so na tambaya inda zan jera maka”
Kallonta yayi baice komai ba ya wuce mirror ya fara shafa man Nivea, yana gamawa fashe spray din same Nivea for men sai ya haɗa da Hugo boss. Yana yi yana takama Still Fadeela tana wajen baice komai ba.
“Ina kayana yake?” ya tambaya amma ko kallonta baiyi ba.
“Yana cikin wardrobe”
Bai kalleta ba yaje ya buɗe, a yatsine ya kalle ciki saiya fito da wani milk jallabiya ya zura. Hawa gado yayi ya dauki wayar shi ya kunna wakar 2pac.
“Ki kawo min abincin nan” ya faɗa yana wasa da wayar shi.
Ita kuma fita tayi waje tareda rufo kofa, “ina da aiki a gabana” ta faɗa yayin datake sauka stairs tayi hanyar dinning area.
Abincine mai rai da lafiya Anty Saudah ta aiko masu dashi. A cikin cooler ɗin farko Appetizer ne na minced chicken wanda yasha kayan lambu kamar su carrots da green beans Sai kuma kayan kamshi da barkono.
A cooler na biyu aka soya dankali da plantain sai kuma wainar kwai. Sai kuma pancakes mai vanilla flavor. Daga nan sai Fruits salad wanda aka kwaba madara a ciki.
Daidai gwargwado ta zuba mashi akan tray saita kai mashi cikin ɗakin. Harta ajiye ta juya ta fara tafiya sai kawai yace, “OMG! I’ve change my mind. Biyo ni downstairs dashi”
Bai tsaya jin mai zata faɗa ba sai ya wuce abinshi. Wani kololon bakin ciki ya tokareta, tunda take bata taba ganin k’askanci irin wannan ba, wai dan wulakanci up and down Zai rinka mata, hakuri kawai tayi saboda zaman aure takeyi kuma ya jiɓanci haka.
Cikin yanayinta na sanya sanya ta karasa wajen dinning area ta ajiye abincin. Ta fara tafiya saiya kirata, “keh meye haka? Dalla zokiyi serving ɗina”
Cak ta tsaya na wasu seconds kafin ta juya taje tanayi, ranta duk ya jagule. Shi kuma haushi ya kamashi saboda yanda take abu kamar babu jini a jikinta, ji yake kamar ya kwace chukalin yayi da kanshi amma da yake mugunta na cin sa saiya barta da abinta.
Dayake Mommy chef ce, Fadeela tasan yanda ake decorating plate yayi kyan gani. Koshi abin yayi mashi kyau saidai bai nuna ba.
“Saura ccoffee” ya faɗa tareda kai spoon din abinci baki.
Ta haɗa mashi cappuccino a Nespresso machine dake kan coffee table ɗin wajen. Ta ɗaura akan saucer tareda teaspoon ta kai mashi.
Tas kake ji alamun cup ɗin ya faɗi ya fashe. Data mika mashi cup ɗin saiyaga cappuccino kuma shi Latte yake so yasa bai amsa ba komai ya zube a jikinta tareda faɗi kasa.
“Kefa bakida hankali! Wannan wani irin busy body ne? Waye ce maki ina shan Cappuccino? I only take latte”
“Yi maza ki haɗa min yanzu kafin na tara maki gajiya...... Mts”
Kananan hawaye suka soma malala a fuskarta sai tayi sauri ta goge, ta lura yanaso ya bakanta mata raine amma bazata bashi damar ba. She will always be happy.
Latte ta mashi a wani cup tunda na farkon ya fashe, little sugar ta saka daidai misali. Koshi sanda ya saka a baki saida yayi mamakin to his own taste ne.
Kitchen ta wuce ta dauko vacuum cleaner saboda wajen yayi kacha kacha, tsaf ta gyara wajen tunda ta iya aiki ba’a sangartar da ita ba.
Bayan nan daki ta wuce ta rufe kanta.
Kwanciya tayi rub da ciki tareda dauko babin kuka, wiwi takeyi mai tsuma rai kamar ranta zai fita, kana ganinta saita baka tausayi. A duniya rainin hankali tafi tsana amma gashi anayi mata kamar pure water.
Datayi kukanta ma ishi saita mirgina tareda rungumo pillow tayi barci abinta.
1:15pm.......
Locacin ne su Bilqees suka kawo lunch, hayaniya dinsu ya tada ta. Da fara’arta ta karramasu kamar kannenta na jini. Tana zuwa wajen dinning taga komai yayi normal saboda sunyi mata wanke wanke Thou tanada dish washer, but still!
Miemie ne taje ɗakin Naufal amma bata riske shiba daga alama ya tafi Masjid ne. Horn sukaji a waje driver yana masu alamar su fito.
“Anty yar gayu mun tafi, sai kuma mun Kawo dinner” Miemie tace tana dariya.
“Sai anjima Anty” Bilqees tace tana murmushi. Har kofa ta rakasu ana raha.
Ta koma daki tayi alwala tareda sallah itama. Bayan nan ta sake gyara make up ɗinta da kyau tareda daurin ture kaga tsiya. Tayi matukar kyau tunda her skin is fluffy Kuma she is fair.
Gashi dama fitted gown ta saka komai nata aziman. Tana tafe tana feleke kamar rashen bishiya, tako daidai yarinya yar kwalisa Amaryar Naufal.
A falo ta riske shi yana kallon CNN inda ake Inauguration ɗin Donald Trump sabon shugaban k’asan USA. Tsaki yayi tareda canza channel daga alamu abin bai kai mashi karo, BBC ya koma still suma abinda suke nunawa kenan. Kwafa yayi tareda rufe idanun sa.
Sai kawa yaji kamshin dake firgitar dashi, “Chanel No 5” ya faɗa saiya bude idonsa.
Nan take suka haɗa ido saiya banka mata harara. Sinna kai kasa tayi saboda idonsa yana firgita ta musamman idan ya zare.
“Yaya ina wuni?”
Bai amsataba kuma bashida niyar amsawa.
“Dama nazo na tambaya ne ina zan kai maka abinci”
Nanma kamar bazai ce komai ba saiya ce, “Set the table, Yanzu zan ci”
“Please idan Kinga dama ki rinka yin busy body idan kina abu, mutum sai shegen nawa kamar kunkuru” Ya faɗa yana wani yatsine fuska.
Tana tafe tana gunguni tareda magana ciki ciki, “Bani bace kunkuru saidai......” kafin ta karasa maganar saiga shi agabanta yana huci kamar mayunwacin zaki.
“Saidai wa?.......” ya tambayeta.
#NiDaDiyata
*Corpers wee! Shout-out to all corpers I know the struggle is hard esp now that dey have not paid our allowee, we will still survive biko! Special shout-out to 2016 Batch B stream 1 most esp Ummunah Bende corpers. If you are reading this you are wrong! Is that clear!*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 16 ✨✨✨
Abdullah bin 'Amr bin Al-'as (May Allah be pleased with them) reported: A man asked the Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam): "Which act in Islam is the best?" He (Sallallahu 'alaihi wa sallam) replied, "To give food, and to greet everyone, whether you know or you do not."[Al-Bukhari and Muslim].
********
Rufe ido tayi ta kasa haɗawa dashi tareda karkarwa, ji kawai tayi an damk’eta. Ihu ta tsandara saboda rik’on dayayi mata babu sassauci kuma abinka da farar mace babu makawa hannunsa saiya nuna.
Still bata buɗe ido ba kawai hawaye suka soma fitowa kamar a bakin teku.
“Bada ke nake ba? Nace karasa maganar mana. Ashe ke karamar mara kunya ne. Tun ba yau ba nace ki hankaltu dani.”
“Idan nace zan rinka dukan kine kawai kasheki zanyi saboda bakida wani abun duka tunda bakifi loma ɗaya da rabi a haɗiye kiba. Kuchaka kawai!”
“Sai shegen iya rashin kunya ga kuma shegen tsoro kamar farin kura. Da an riskeki sai ki fara kukan munafunci kamar ana kashe ki..... Mts”
Saiya wurga ta k’asa ta faɗi wanwar. Baka jin komai sai Sheshek’ar kukanta kawai tana jan majina a hankali.
“Idan kinso gobe ki kara, Karkiga yanzu na kyale ki” ya cigabada sababi har ya koma wajen couch ya zauna. Kafa ɗaya kan ɗaya ya daura yana kallon TV dake aiki. Wannan karon ESPN ya saka.
Ita kuma a hankali ta tashi jiki babu kwari rai a jagule tayi hanyar dining, karap karap kake ji karar takalmi ta isheshi kuma da gangan takeyi.
Ko cooler da karfin gaske take buɗewa kamar zata karya murfin, haka take amfani da chokali karap karap ita kanta ta damu balle shi. She was just acting clumsy Sai ɓari takeyi ta ishe kowa.
Tsaki yakeyi saboda duk ta cika mashi kunne, a fusace ya juyo rai a bace yana nuna mata ɗan yatsa.
“Ke dalla meye haka ba zakiyi abu a natse ba kin cika min kunne”
Puppy eyes tayi mashi tareda cewa, “Kayi hakuri yaya bansan yana damunka ba”
“Okay yanzu kin sani gwara ki bari kafin na damk’eki”
Bata ce komai ba illa sinna kai tana dariya, tabbas taji daɗin abinda tayi tunda da gangan ne. Cikin ruwan sanyi zata rinka frustrating ɗinshi.
Ta jera mashi abinci wanda multi-colored rice ne da stew ɗin Cat fish. Sai kuma Coslow wanda yasha Macaroni da hanta. Drink kuma coconut ne aka markaɗa da shinkafa na tuwo tareda pineapple.
Karap karap ɗin slippers ya sanar dashi gatanan zuwa, dab dashi taje ta tsaya kamar zata auka mai.
“Yaya ga abincin na zuba maka”
Harda bazai amsata ba sai kuma ya canza ra’ayinsa.
“Sai kin fado jikina zan san kina min magana?” ya tambaya yana mata kallon raini.
“oh sorry!” saita matsa baya
Shiru sukayi for some seconds saitace, “Akwai abinda zanyi maka kuma?”
Bai tanka taba saiya mike tsaye, yanda dunkaro ta idan da batayi saurin matsawa ba daya banke banza.
Hawa yayi dinning ya zauna, yanda ta jera ya k’ara burgeshi. Ita kuma dama ta ɗiba nata yana kitchen. Karap karap takeyi harta wuce ta shiga kitchen, wannan Karon harda juya mai jiki.
Shiru yayi saboda ya shaka matuk’a, “indai jiki ne toh I’ve seen better” ya faɗa a ranshi. Sannu a hankali ya gama cin abinci saiya tashi ya wanke hannu, sink ɗin wajen yayi hooking yaki budewa so dole yaje wani wajen.
Nearest to the dinning area kitchen ne, ranshi baiso ba amma haka ya hakura ya tafi.
Ita kuma ta gama cin abinci har ta fara wanke wanke sai Naufal ya faɗo mata a rai. Dariya ta tuntsire dashi tareda magana a fili, “Wai ace mutum bashida sana’a sai faɗa, dage yafi shi hakuri.... Haba kullum faɗa kamar a Syria aka haife shi”
“Ina jinki” Ya faɗa.
A tsorace ta juyo tareda sakin plate ɗin hannunta, tas kakeji ya fashe. Neman wajen guduwa taso yi amma shike hanya. Tabbas yau kashinta ya bushe saboda saita daku.
Narai narai tayi da ido bakinta na rawa amma babu abinda ke fita. Zufa ya soma yanko mata duk ta fita hayacinta.
Takowa ya somayi tareda smug face, kana ganin shi kasan yana shirin mugunta. Sannu a hankali har ya kai wajen datake ya tsaya.
Da hannu yayi alamar ta matsa mashi, wucewa yayi ya wanke hannunsa saiya bar kitchen ɗin.
Shi abinda yasa baice komai ba saboda yanda ta tsorata, ihu yayi mata zata iya haɗiye ranta ta mutu ta jawo mashi bala’i babu gaira babu dalili.
Amma tabbas maganar datayi ya taɓa shi, wai yau shi ake ce ma dage da kuma yana faɗa kamar haihuwar Syria, lallai!
Ita kuma sororo ta tsaya tana tunanin abinda ya faru few seconds ago, gaskiya ya bata mamaki matuka saboda bata sanshi da hakuri ba, wani zuciya ya raya mata kila tayi Azkar da kyau ne.
“Gaskiya ba mamaki!” ta faɗa a fili saita ɗuka kasa ta fara gyara ɓarnar datayi. Dama wayanta yana gefe sai kawai ta dauka ta kunna wakar Nazeefi Asnanic mai taken Ga Amarya, Haka ta rinka rero wakar kamar ita ta rubuta mashi.
Dakinshi ya koma ya zauna akan gado yana tunani, faɗa Sam sam ba ɗabi’arsa bane kuma kowa ya shedeshi. But tun haɗuwarsu yake wasu shikashikan rashin mutunci babi babi.
“Ka manta Bad luck ɗin dake binta ne ya canza ka” wani zuciya ya raya masa.
“Hakane fah” ya faɗa a fili. Tashi tsaye yayi saiya canza kaya.
Farin Boyel ya saka wanda aka ɗinka jumper da wando. Sai ya haɗashi da coffee Brown hula da takalmi. Turaren Ralph Lauren ya fashe jikinsa dashi har ya fara choking saboda yawansa.
Yaci kwalliya kuma yayi kyau sosai a matsayin shi na kyakyawa, wannan green eyes ɗin yana glimmering. fine guy san kowa, ko makiyan sa basa kushewa. Ni kuma Dimples nace “ Na Fadeela bada kanka a sare!”
Yana tafe taku dai-dai zashi gidansu Fadeela yayi godiya akan karamcin da suka yi mashi. Abba ya gargaɗe shi akan dole saiya je ya gode masu, kuma shima yana so ya daki tsuntsu biyu da dutse daya.
Tunda ya lura Mommy tana sanshi gwara yayi mata shishigi saboda koda ta kai k’ara babu mai gasgata ta.
********
A chan gidan lambu kuwa, Miemie ce ke gyara flowers ɗin datayi planting da kanta. Sun flower ne kuma kullum saita duba su, ta dauki wani flower pot sai kuma ta sake shi k’asa ya faɗi ya fashe.
Bata ko damu ba saima takashi da tayi kurmus. Kana ganinta kasan ‘yan kanta sun motsa.
Tunda baya Naufal ya bar gida take jin kanta wayam, tunanin Khattab kawai takeyi. Ya diran mata kamar kibiya batada wani katabus sai shi.
“Ba Ya Naufal, ba Ya Khattab.... Toh wallahi bazai yiwu ba”
Komawa cikin gida tayi wanda ‘yan biki sun ragu yanzu. Abla ta gani a hanya saita ce mata, “Kinga Yaya Khattab kuwa?"
Harara ta watsa mata kafin tace, “Eh yana buje na” sai tayi wucewarta.
Miemie bata ce komai ba illa wucewa ɗakin Mamanta watau Anty Saudah, “mama ki kaini wajen Yaya Khattab dan Allah”
Shiru Anty Saudah tayi kafin ta fara magana a hankali, “Mamana yau Kinsha magani kuwa?”
“Ni wajen Yaya Khattab zaki kaini....”
“idan Kinsha magani sai muje koh”
“Wallahi ban yarda ba, nasan bazaki kaini ba” Sai kawai ta fashe da kuka. Anty Saudah da sauri ta ɗauko magani domin ta bata atleast su samu saukinta.
Fizgewa tayi daga hannun Mamanta ta zubar dashi ta rinka takawa da kafarta tana yi tana kuka tayi kacha kacha da wajen.
“Bazan shaba” ta faɗa tana rusa kuka a ɗuk’e. Nan take ran Anty Saudah tashi.
Number ɗin Naufal ta soma nema, bugu ɗaya, biyu, uku saiya ɗauka. A gurguje tayi mashi bayanin komai. Nan take ya yi hanyar gidan saboda yabar gidansu Mommy kenan zai koma nashi.
Yana tafe yana tunanin condition ɗin Miemie bcs sun ɗade batayi tuburan ba.
Bai rufe k’ofan motarshi ba da sauri yayi cikin gida, yana isa wajen yagasu Abla anyi charko charko a waje saboda Miemie tace bata san taga kowa.
Tana zaune ko Mommy ɗinta ta kasa zuwa wajenta kafin ta mauje ta, Kiran sunar Miemie yayi a hankali tareda tura kofa.
“karka matso kusa dani”
“Calm down Lil sis,nine fah”
“I hate you” ta faɗa tareda kuka sosai.
“Kace min Yaya Khattab yayi min sallama ne, saboda ka maida ni mahaukaciya koh?”
Shiru Naufal yayi ya rasa me zaice kafin ya faɗa wrong thing tayi losing mind ɗinta hauka yazo gadan gadan.
Ita kuma ta kifa kai akan gwiwa sai kuka takeyi mai tsuma rai. Kawai saita mike tsaye tace, “Muje ka kaini wajen Yaya Khattab”
Zuwa yayi dab da ita ya ce babu inda zata. Wani irin kukan ta somayi kawai saita ruga window ta fara buga kanta dashi, duk da glass ɗin wajen ya fashe sai karfe Still bata daina ba.
Yaya Khattab ta rinka maimaita wa.
Duk yanda Naufal yayi kokarin kwanceta yana so ya gaza mashi. Tausayinta yake matuka saboda yasan zafin so.
Fincikarta yayi ya watsar a Kasa, jini ke fito mata ta hanci ta baki gashi kuma daga kanta yana gangaro wa. Kuka takeyi sosai tana kiran Khattab da muryanta daya fara dishewa, idanunta sunyi jazur kamar garwashi saboda wahala, duk ta galabaita a hankali takeyi.
“Kashe kanki kike so ki yi?”
Ko kallon shi batayi ba kawai tana kuka ne, duk abinda akeyi su Anty Saudah da Abla ana gefe ana kuka. Gashi Abba ya tafi Kano.
Kawai Miemie ta ankara da inda take saita soma sabon aiki. Daukar kwalba tayi a k’asa ta soma chachaka ma hannun ta, tana kaiwa wajen jijiyanta saita kwala ihu tareda sakin komai. Nan take ta fita hayacinta tareda sumewa.
Anty Saudah ta rusa ihu tareda rugawa wajen ta, Abla ma haka. Shi kuma Naufal mutuwar tsaye yayi saboda duk laifin shi ne.
Saida wasu seconds suka wuce kafin ya dawo hayacinsa, kukan zuci yake wanda yafi na baiyane ciwo.
Daukarta yayi kamar ‘yar tsana yayi waje cikin ruɗewa, ko mota bai shiga ba kawai ya nufa titi yana gudu da ita. Dadin abin Anty Saudah ta iya mota Saita tuka na Naufal ta riske shi a hanya.
“Saika shigo muje tunda ba’a kafa za’a ba” yaji kunya sosai daya lura da abinda yayi amma babu time for that.
Suna kaiwa Asibiti ER aka wuce da ita direct saboda tayi losing jini babu adadi. Kacha Kacha sukayi da jini kuma asibiti ɗin saida yasan da zuwansu.
Anje za’a kara mata jini amma babu match ɗinta saboda haka sai anje blood bank.
Dauke Doctor ɗin da mari Naufal yayi tareda cin kwallarsa, “Dan ubanka meyasa tuntuni baku nema ba dan sakarci sai yanzu?”
Sai kawai ya sake shi ya koma gefe yana kuka, ya tabbata idan suka rasa Miemie shiya kasheta.
Suna zaune aka kawo jinin, nan take aka soma yi mata aiki gadan gadan cikin awa biyu an gama komai.
10:45pm......
Fadeela tana zaune akan Couch tana jiran other half ɗinta babu shi babu dalilinsa kuma su Miemie basu kawo dinner ba, kawai komai yana mata wani iri amma bataso ta kawo mugun zato a ranta.
Har wajen 11:30 bai dawo ba, idanunta ya cika da hawaye tun tana matsewa har saida ta barke da kuka wiwi. Akan 3 seater ta kwanta tayi ma’ishi har barci ya dauketa.
Ita kuma Miemie tana buɗe ido a hankali ta soma magana. Kamar kowane mara Lafiya ruwa yake nema amma banda Miemie, “Khattab” ta furta tana hawaye. Naufal yaji sarai sai ya kyaleta, kwakwal warsa baya aiki abin duniya yayi mashi chunkoso.
Kana ganinta saita baka tausayi, ga jikinta duk bandage ko fuskarta an rufe wajen rabi dashi. Gashi kuma an saka mata oxygen ta hanci saboda numfashi.
Shi baisan yanda zai fara faɗa mata Khattab ya bar Nigeria ba, tunda ya rasa Miemie saiya gudu yabar gidansu, yanzu haka baada tabbacin ga inda yake.
Wasu Doctors su uku suka shigo tareda Nurse guda ɗaya.
“gaskiya zakuyi hakuri bcs alamarinta sai addu’a, yanzu kawai for safety shine za’a rinka k’ulleta saboda idan hannayenta is free saita rinka kokarin nakasa kanta.”
Sai suka fito da handcuff guda biyu, sun gark’e mata hannu ta kowane ɓangaren tareda gado. Itadai kallon kowa takeyi bata masan sunayi ba, “Yaya Khattab” tayita nanatawa.
“Wannan wani irin sone?” Naufal ya tambaya kansa.
#NiDaDiyata
*Fatan alkairi zuwa ga yan group din DIMPLΣS, Allah ya bar zumunci*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 17 ✨✨✨
Jabir bin 'Abdullah, may Allah be pleased with them, narrated that Allah's Messenger said: "The key to Paradise is Salat, and the key to Salat is Wudu'." (Hasan)
It was narrated from Abu Hurairah that The Messenger of Allah said: "When it is very hot, then wait for it to cool down before you pray, for intense heat is from the flaring up of the Hell-fire." (Sahih)
**********
Six months later.....
Hakuri shine gishirin zaman duniya, kuma ainun Fadeela tayi exhibiting ɗin wannan abu. Babu abinda Naufal baiyi mata ba na cin zarafi kuma duk ta shanye.
Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin zata faɗa ma Mommy ba ko Jawahir, ita kawai tasan nata jarabtan kenan. Sau biyu taje gidansu kuma shima sallah babba da karama ne.
Saidai kuma bai takura mata akan karatu, ya kyaleta ta cigaba amma koda wasa bai taɓa rage mata hanya ba. Idan kuma tanada 8am class toh tun wajen 4am take tashi tayi breakfast and lunch duk ta saka a cooler.
Azumi kuwa na Monday and Thursday baya wuceta Muddin tana cikin lafiya, ma’ana idan tana sallah.
Daga ɗayan ɓangaren ana nan ana fafutukan neman ma Miemie magani, Shidai Khattab har yanzu babu zancensa babu dalilin sa.
Sau da dama idan ciwon Miemie ya tashi Naufal ya rasa tudun dafawa sai kawai yaje gidansu Khattab ko office ɗin babansa ya zauna yayita rusa kuka.
The last time dayaje Sai Abban Khattab ya rantse mashi da girman Alkuran akan baisan inda yaronshi yake ba, shima rabon dasu haɗu tun text msg daya aika mashi akan ya tafi kuma daga nan yayi disconnecting layin, koda akayi tracing ɗakin Khattab ne last location.
Anan fa hankalin Naufal ya tashi sosai saboda ciwon Miemie sai gaba yakeyi. Akwai wani rana haka, Anty Saudah takaita bayan gida domin ta zaga, unfortunately ta cire mata hand cuff sai kawai Miemie ta naushe window da hannunta. Nan take jini ya soma gangaro wa kuma sai ta dauki broken glass tayi slitting wrist ɗinta.
Tashin hankali Anty Saudah ta gani mara misaltuwa saboda nan take Miemie ta sume, sau dama Miemie tayi abubuwa da zai janyo mata asarar ranta.
Akwai wani lokaci tafi One week bata kira sunar Khattab ba, kowa hamdala yakeyi ta fara samun sauki sai Naufal ya cire mata hand cuff ɗinta. Aiko basu suka ganta ba sai bayan kwana biyu.
Shima wajen data fara haduwada Khattab ne, ta zauna a gefen da ake gasa masara tanata rusa kuka, babu wanda yabi ta kanta saboda kana ganinta kasan babu hankali, gashi batada takalmi ga kai a tsefe yayi sama duk kacha kacha.
Tunda daga lokacin sukayi taka tsantsan da ita, yanzu dai basu saka mata Handcuffs akwai wani igiya haka mai yanayin beat. Shi ake saka mata kuma tana wani ɗaki ne wanda babu komai ciki sai carpet.
Wata rana tayita ihu tana buga kanta a kasa amma saboda laushin carpet bata jin ciwo. Wata rana kuma tayita kiran sunan shi a hankali tana hawaye, haka rayuwa ya kasance mata!
Duk Safe da yamma sai Naufal yaje ya dubata, da farko bata san ganinsa. Dayazo ta window inda ake lak’enta saita rinka ihu tana rufe idonta. Kullum kalmar “Ka cuce ni take furtawa”
Ba karamin tashin hankali ya shiga ba, ya kan rufe kanshi sau da dama a ɗaki yayita rusa kuka, tabbas yasan shine sila but yanzu da zai iya maida hannun agogo baya daya yi.
Amma yanzu ta rage mishi haka, tana zuwa har wajen window ta tsaya, Thou bata cewa komai but tana murmushi jefi jefi. Idan kuma time ɗin abinci da magani yayi yana shiga yayi feeding ɗinta.
Ita kuma Fadeela bata wuce One week bataje ta duba taba, abin yana burgeshi sosai amma baya nunawa, kuma ko sau ɗaya bai taɓa tunanin yabar ɗiban albarkan dayake mata ba.
Shi dama yace aurenshi zai zame mata ɓakin canji a rayuwarta, kuma daidai gwargwado yana kokarin ya nuna haka. Dukta susuce tayi fari kamar fatalwa, yasa bataso taje gidansu kafin hankalin Mommy ya tashi.
Ko Jawahir baifi sau biyar taje nata gidan ba kuma shima a gurguje ne. Kullum tana cikin waya da Mommy, “babu abinda kike nema? Lafiyan ki kalau? Me za’a yi maki?” shine tambayar datake mata kuma ko sau ɗaya bata taɓa furta abinda zai jawo ma mijinta kaskanci ba ko bakin jini.
Idan ta gama aikace aikace ɗinta saita je wani empty room haka wanda kayan art work ɗinta suke tayita painting hankali kwance. Shi kaɗai ne abinda takeyi mai kawo mata solace, idan tana yi saita mance da bakin cikin gidan aure.
******
Yau Juma’a kuma kamar kowane sati inada 8am class. Tun wajen 4am alarm ɗina ya tashe ni but ban samu daman saukowa daga kan gado ba sai wajen 4:30am.
A daddafe na sauko inayi ina murje ido bcs barci bai isheni ba. Wajen karfe sha biyu da rabi na kwanta sanadiyar projet dana farayi kasancewar mune final year student.
Kitchen naje na fara kama aiki watau breakfast kuma shima Soyayyar dankali ne wanda tun jiya da daddare na fere na ajiye abina a fridge domin na samu sauki yau.
Daga nan sai nayi jollof Rice na saka ma Naufal abinsa na rana a cooler saboda bazan samu daman dawowa da wuri ba bcs ina Missing Miemie.
Kafin na gama aiki Asbah ta danno kai gadan gadan tunda sai karfe shida akeyi. Pausing girkin nayi na mayar da komai on low heat saina wuce ɗaki.
Alwala na dauro tareda nafilar raka’atanil fijr, ina cikin azkar sai aka kira sallar karshe which nima na tashi nayi. Adduar safe nayi wanda kowane ɗan Adam ya kamata yayi sai kuma na haɗa da neman ma kaina, mijina,iyayena da al’umma baki daya tsari daga sharrin masharranta watau mutum ko aljani.
Kai tsaye kitchen na koma na cigaba daga inda na tsaya, ina ciki naji Ya Naufal ya dawo daga masallaci, murmushi nayi k’arara saboda My other half yasan darajan sallah, at all Baya wasa dashi. Saboda haka ni bana cire ran wata rana zai soni.
Nasan cewa wata rana zai gane nice other half ɗinsa Kuma nasan zaiyi alfahari dani kamar yadda nakeyi dashi. Kwata kwata yanzu bana jin haushin cin kashin dayake mun, I’m not making excuses for his actions but nasan cewa yana cikin damuwa akan ciwon Miemie, fatana kullum Allah ya bata lafiya kila nima na samu lambar zuciyar sa.
12 pm.....
Locacin ne na gama lectures ɗina, kasancewar yau Friday kuma short working day so banyi tunanin zuwa wajen project supervisor ɗina ba.
Tafe nake da Samɗa,Jumaimah da kuma Mansura k’awayena. Muna tafe muna hira hankali kwance. Samɗa ce tayi hanyar parking lot inda motarta yake.
Ihsan Baby ɗin Samɗa na dauka wanda ke tareda mai aikin ta, wasa nakeyi sosai tunda ina san yara, kallona samɗa tayi cikin tuhuma kuma kana ganinta kasan da magana a bakin ta.
“Faɗa karya kasheki” nace ita kuma dariya tayi kafin tace, “Kinsan cewa ke zaki rinka nuna masa salo da zai janyo maki hankalin shi? ”
“Wallahi kin bani dariya, meye banyi ma bawan Allah ɗinnan ba amma banza yake dauka na. Ke ni na gaji wlh”
“Ah ah Karki ce Haka, da lallami da kissa zaki sameshi. Dama Wayace maki shiga Aljanna cin tuwo ne, ai sai kin nuna juriya da hakuri tukun”
“Allah dai yasa mu dace” nace sai mukayi shiru.
A al’ada yanda ake gane matar aure a cikin makaranta mu shi ne ta hanyar mota, sau da dama idan mijinki yanada k’umban susa zai siyan miki mota amma dai banda nawa mijin. Idan na shiga motarshi to naje gaida Miemie kuma yamma yayi kuma shima ya gargaɗe ni da na daina kaiwa dare tunda shi ba driver ɗina bane.
Samɗa kawai kallon kawarta takeyi, yanda abin duniya bai dameta ba. At all bata jin kunyar hawa bus ko napep Thou kana ganinta kasan babban mace ce, idan ba wai kayi mata sanin da bane toh bazaka gane ta lalace ba.
Naufal yafi mijin Samɗa arziki nesa ba kusa ba, bazama ka haɗa ba esp yanzu dasu Mr Sutter suke ji dashi sosai.
Kudi mara misaltuwa suke sakin mashi sosai yasa indai batun maganin Miemie ne to baya damuwa, but dama sauki na Allah ne!
As usual wajen roundabout ɗin Yelwa Samɗa take ajiye Deela sai kowa ya kama gabansa.
Direct gidan gona na wuce tareda tsaraban masara a hannuna bcs of Miemie.
“Assalamu Alaikum” Na faɗa yayin dana shiga cikin falo, Anty Saudah Nagani da kuma Abba harda Mama duk ana zaune.
Nan take fara’arsu ta karo sosai which dama haka sukeyi idan sun ganni.
“Ina wuni? Ina gajiya?” na Faɗa tareda duk’awa kasa.
“Lafiya lau, ya kike?” Suka amsa
“Lafiya lau” nace.
“Bari na shiga daga cikin wajen Miemie”
Ba Abba ba har Mama akwai tuhuma a yanayin Fadeela, indai ba ciki gareta toh tabbas ana musguna mata ne, shi dai Abba saiya tsareta Thou yasan bazata ce komai ba but he wants to assure her yana side ɗinta.
Ita dama Anty Saudah tayi tambayar harta gaji but Deela batace komai ba. Tana ankare da yanda Naufal ke mata wani mugun kallo. Sau da dama tana tsare shi akan yaji tsoron Allah, “Inba dai ita tace ina mata wani abu ba, toh ni ba wani abu dake hadani da ita” abinda yake faɗa kenan.
“Hello Miemie!” Deela ta faɗa tareda shiga cikin ɗakin. Ita kadai Miemie takeso ta rinka shiga unless abinci zaka bata, toh kayi tsayuwar ka a waje.
Murmushi Miemie tayi batace komai ba, Fadeela ta karasa inda take zaune chan kurya saita zauna kusa da ita. Riko hannunta tayi tana mata murmushi tareda murzawa a hankali.
Magana tayi ciki ciki saika saka Mind ɗinka da kunnuwa kafin kaji.
“My Miemie please come back, Ya Naufal really needs you” ta faɗa tana kuka. Miemie na jinta batace komai ba sai daga bisani tace, “NI kin cika min kunne"
“Oh sorry!” ta faɗa tareda share hawayenta. Kakalo murmushi tayi saita mika ma Miemie masara, nan take ta karba ta soma cabza.
“Kema zaki biye masu ne bazaki kaini wajen Ya Khattab ba?”
“kina tunanin banida hankali ne koh?”
Fadeela batace komai ba illa kallonta, ita kuma ta cigaba da cin masara bata ɗaga idonta ba.
“Idan an kai ki wajen Khattab ɗin mai zakiyi masa?”
“Kawai ina son ganinsa ne bcs I have a bad feeling”
“Dan kina son ganinsa sai kin kashe kanki ?”
“Eh, har saina samu abin nakeso” ta faɗa kana ganin fuskantar babu wasa.
Shiru sukayi for some minutes Har Miemie ta cinye masara guda uku, Magana Miemie ta somayi.
“Ya Yaya Naufal yake? Nasan he is not alright but Kema haka. Yana miki wani abu ne?”
Ta tambaya tareda kama mata haɓan fuskanta. Hawaye kawai ya soma gangaro ma Fadeela saboda ko Miemie da bata da lafiya ta gane komai balle sauran mutane.
Da sauri ta goge tareda cewa, “Just try and be alright Naufal Shima zai zama daidai” ta faɗa cikin muryar kuka.
Tashi Fadeela tayi tsaye zata tafi sai kawai Miemie itama ta mik’e wai zata bita, “Please Anty Karki tafi ki barni, bakiga yanda suke treating ɗina ba. Please don’t leave me here”
“Miemie dont worry, zan dawo next week kinji koh!”
“Please ki tafi dani, Anty kada kiyi min haka. I promise to behave myself. Insha Allah Bazan k’ara jima kaina ciwo ba”
Hawaye ke malala a fuskar Fadeela, karasa wa tayi dab da ita tana shafa mata kumatu tareda da share mata nata hawayen.
“My sweet Miemie I’m sorry but ban yarda ba, jibe hannunki da bandage ga wani a cinyar ki. Tuntuni kike min alkawari kin daina amma last week kikayi wannan. Ko totuwan masara da zai illanta ki da kinyi dashi”
“Anty bazan kara ba Please”
Murmushi Fadeela tayi na takaici tareda sumbatar goshinta saita juya tana kuka ta tafi, muryan Miemie kawai take ji yana echoing.
“Dan Allah Anty Karki tafi ki barni, wallahi na tuba. Bazan kara ba, please kiyi min rai”
Haka ta rinka maimaitawa tana fizge fizge ta karfin tsiya, rusa kuka takeyi gwanin ban tausayi but babu yanda Fadeela zatayi.
Haka Miemie ta rinka fizgo hannunta tana kokarin kwance kanta saita kasa. Kawai zubewa tayi a kasa ta fara ihu, “Yaya Khattab kana ina ne” ta faɗa sai kuma ta fara buga kanta akan carpet tana kuka, Anty Saudah tana falo tareda Fadeela suna rusa kuka.
Itama Mama tana matse hawaye saboda Miemie abin ban tausayi ne, shiko Abba tuni ya tafi Masallaci kafin yayi missing huɗuba.
Sallah Fadeela tayi saita wuce gida, hankalin duk ya tashi. Tana isa gida saida tayi kuka ma’ishi saboda yanzu kuka shine latest hobby dinta bcs bata 3 days bata yiba.
6:30pm....
Wani dabara ya faɗo min akan nabi shawarar samɗa, bayi na shiga nayi wanka tareda ɗauro alwala. Akan dressing mirror na zauna na Fara shafa mai, Saida na lura ina kyali sosai tukun.
Body spray ɗin Victoria secrets na saka tareda turaren J’adore sai nayi light make up almost nude a fuskata. Jumpsuit ɗin Naeem Khan nasa sai na saka wani Gladiators na Giuseppe Zanotti.
Nayi kyau ainun kamar zani Red carpet, kitchen naje na haɗa ma other half ɗina White Macaroni da sauce ɗin kwai.
Na sake gyara falo tareda kunna turaren wuta da kuma spraying room freshner, tafiya nakeyi ina rangwaɗa duk practice yanda zanyi idan ya dawo.
Shikuma Naufal bayan ya tashi daga aiki as usual wajen Miemie yaje, kuka takeyi haryanzu amma bata burgima, a hankali takeyi saboda duk ta galabaita.
Sunar Khattab take faɗi kawai repeatedly, bai samu yayi mata mata ba bcs baya so yaje gabanta ya barke da kuka, ko yau a office bayan sun gama conference call dasu Mr Sutter Sai kuma sukaje wani site tareda Aminu.
Yana komawa office ɗinshi ya garke yana hawaye, duk ya gaji komai yayi masa yawa. Gashi duk abinda yakema Fadeela amma maiyar yarinya tak’i zuciya ta tafi gidansu. Ita a dole ta samu wajen zama, shi yaso ya wulakanta ta to the extend da zata tafi gidansu saiya koma wajen Miemie full time.
Saida yayi sallar isha ya koma gida, yana tafe yana tunanin salon cin fuskar da zaiyi mata yau kowama ya huta.
Shiga falo yayi tareda sallama a matsayinshi na musulmi, but to his surprise Sai yaga wutan falo a kashe amma TV yana aikinsa.
Haushi ya kamashi saiya fara sababi, “Meye aka kashe wuta salan na faɗi” saiya kunna. Zaune ya ganta akan 3 seater ta daura kafa ɗaya kan ɗaya tana mashi murmushi.
“I’m sorry! Bansan Yanzu zaka dawo ba yasa na kashe” yanda ta faɗa cikin siririn murya da kissa dole saika sosu. Da sauri ta tashi zataje ta karba briefcase ɗinsa kuma tana tafe tana rangwaɗa.
“Sannu da zuwa” ta faɗa data karasa dab dashi. Ja da baya yayi saiya ce a fusace, “keh meye haka” saiya ratsata ya wuce abinshi. Ko kaɗan bataji haushin abinda yayi ba, Infact tanaji yanzu ta fara.
Daki ya wuce domin ya kimtsa kafin yaci abinci, jallabiya ya zura bayan yayi wanka. A kan dinning table ya ganta zaune tana jiran shi fuskanta dauke da annuri.
Rai a bace ya haɗa girar sama dana kasa yana wani mazurai ya zauna akan kujera Which tun kafin ya iso ta jawo mashi, harara ya doka mata amma ta mayar masa da murmushi. Haushi yaji sosai saboda ya lura ta bala’in rainashi bata jin tsoron sa again.
Tanayi tanata baɗa mashi kamshin turarenta harta gama serving, maimakon ta tafi kamar yadda ta saba sai ta zuba ma kanta itama tana ci. A cikin yanayinta na sanya sanya ta rinka ci kamar bata so taci, shikuma jefi daya, biyu yakan kalle ɓangaren ta.
Haka har suka gama cin abinci ta kwashe ta kai kitchen shi kuma ya wuce kan couch domin ya kalle 9 o clock news na NTA.
Itama taje ta zauna akan One seater, baice komai shiru yayi mata kamar baisan tana wajen ba. Yana ankare da ita sai gyangyaɗi takeyi kanta yana rawa amma dan jaraba tana forcing kanta a wajen.
Dariya abin ya bashi kuma yau ne rana na farko da wani abu nata yasashi dariya. Data gaji dan kanta ta tashi tana tangal tangal kamar yar k’waya.
“Yaya saida safe” ta faɗa muryanta yayi kasa saboda barci.
“uhm” yace yana kallonta ta gefen ido.
Sannu a hankali ta rinka layi harta kai cikin ɗakinta, takalmi kawai ta cire ta shiga bayi domin ta kama ruwa, ta fito tana cikin tafiya sai raguwan ruwa tareda santsi na tiles ya ɗibe ta.
Tim ta faɗi a kasa, salati ta somayi kuma idonta yanzu yayi ras saboda barcin ya tafi. A hankali ta dafa gado tareda mikewa tsaye, amma sai me? Kafa yace tsaya mugani mana..... Ashe ta turguɗe ne.
0 comments:
Post a Comment