K’ara kokarin daura kafar tayi a kasa amma ta kasa. Wani azabataccen zafi taji har cikin birnin kwakwalwarta.
Nan take zafafan hawaye suka fara malalo mata. Changala kafarta tayi har cikin bayi ta kunna mashi ruwan zafi but still babu wani improvement.
Haka ta koma cikin ɗaki ta hau kan gado tana tunanin duk yanda zata rinka ma ‘Other half’ ɗinta hidima. Bata gano answer ɗinba har barci ya fara fizgarta, gashi bata kashe wuta ba amma bazata iya tashi ba saboda azaba.
Shikuma Other Half ɗin Fadeela Kawai tunanin abinda ya faru tsakanin shida ita Few minutes ago yake.
‘Kardai ace yarinyar nan ta fara sona ne?’ wani zuciya ya raya masa.
‘No no no... Allah ya kiyaye, it’s not even possible. Haba duk wulakanci danake mata!’ wani zuciyar ta sake raya mashi.
‘Maybe kuma kuɗi takeso’
‘Yes I’m very sure, dama mata idan suna san kuɗinka sai su ta maka iyayi’
Yayi concluding Kudi takeso sai yayi tunanin ajiye mata check ɗin 50k kafin ta takura masa.
Haka ya gama kallonsa saiya kashe kayan kallon tareda lantarki sanda zai tafi.
3 days....
Ciwon Fadeela sai gaba yakeyi saboda ko Makaranta ta daina zuwa. Dakyar take komai gashi ko kauɗin girki kala kala ta daina, dayake tanada stew dayawa a fridge sai ta rinka dafa white rice or Macaroni ta ajiye mashi.
Drink kuma saita ajiye mashi Fanta ko Pepsi kawai, idan kuma breakfast ne Tea and bread Zata ajiye.
Kuma rabon daya ganta tun ranar data turguɗe.
‘Dingisa kafarta from upstairs to downstairs and vice versa Yana bata wahala saboda tana tafe tana kwalla gashi ya kumbura sintim kamar Doya.
Shikuma Other Half abin ya fara damunsa, ya lura check ɗin daya ajiye bata ɗauka ba kuma next day yayi withdrawing cash ya ajiye mata amma bata bi takai ba. Ya rasa menene matsalar ta gashi ko abinci anyhow takeyi.
Kuma rabon daya ganta tun sanda tayi wani hot kwalliya. Shi Bawai Santa yake ba but atleast.... Sai kawai ya kasa Karasa tunanin.
Zama yayi a falo daga safe har wajen azahar yaki zuwa aiki yana son yaga kozata wulkita amma Sam. Kwafa yayi saiya dauki key ɗin motarsa ya tafi gidansu, gwara yaje yaga Miemie yafi kafin Bad luck ɗinta ya jaza mai!
À wajen Miemie babu yabo babu fallasa tanata fara’a kuma sunsha hira. “ina Anty yar gayu?” ta tambaya. Dadi sosai ya kamashi saboda an taɓo mashi inda yake mai k’aik’ayi.
“Ban sani ba amma bari na ara wayar Momyn ki sai mu kirata. Zulumi a ranshi yana tunanin mai zai ce ma Anty Saudah bcs kwata kwata bayada number ɗinta.
Aiko wayar ya gani akan centre table kuma Anty Saudah tana kitchen, a guje ya sure wayar yana jin ɗadi. Bugu ɗaya, biyu sai ta dauka.
“Assalamu Alaikum, Anty ina wuni?” ta faɗa. Shi kuma yana jin muryanta sai ya kauda da sauri tareda kara ma Miemie a kunnenta.
“Anty yar gayu yaushe zaki zo?”
“Ah ah Miemie Kece ?”
“Eh please yaushe zaki zo?”
“Gaskiya ban sani ba saboda banida lafiya”
Kallon Naufal Miemie tayi tareda faɗin “Ya Naufal dama Anty batada lafiya shine baka faɗa min ba?”
Tsuru tsuru yayi saboda baiso Fadeela taji yana wajen ba, harara ya watsa ma Miemie tareda juyar da kansa.
“Anty kiyi hakuri kinsan halinsu koda nace zanzo dubaki bazasu barni ba” ta cigaba da wayarta. Hira sosai sukayi daga bisani aka kashe.
Burin Naufal ya cika yasan meke faruwa but still baisan meke damunta in particular ba. Anty Saudah tazo tana tambayar Naufal koyaga wayanta data ajiye a falo.
“Eh dama nine na dauka saboda Miemie tanaso tayi waya da Anty ɗinta”
“bakada wayane? Innalillahi kodai bakada number ɗinta ne?”
Kana ganin yanda yayi kasan cewa bashida gaskiya, kallonsa Anty Saudah tayi kafin tace, “Allah zai saka mata koma menene”
Anan ta barshi tsuru tsuru ta koma ɗaki saboda haushin takeji ainun, ita tasan basa jituwa amma batayi tunanin haka bane.
Baiji daɗin yanda ran Anty Saudah ya ɓaci ba, kawai saiya yanke shawara ya bita ya bata hakuri tunda a matsayin uwa ya ɗauketa ba step mom ba, Thou bazata haife shiba.
A bakin gado ya ganta tana matse kwalla, kakalo murmushi tayi data ganshi. Yasan sarai shi takema kuka.
A kasa ya zauna dab da ita saiya daura hannunsa akan cinyarta. Nadama karara saiya soma magana kasa kasa.
“Dan Allah Anty kiyi hakuri, Karki min haka, bana so kiyi kuka a kaina. Insha Allah I will do better.”
“Allah yasa” kawai ta iya faɗa bcs zata iya barkewa da kuka wiwi.
Sallama yayi mata kuma tashi mai da albarka saiya koma wajen Miemie sukayi sallama sannan ya tafi.
A hanya tunani kawai yakeyi bcs ya ɗebo ruwan dafa kansa tunda yayi ma Anty Saudah alkawari amma baya tunanin zai cika mata ba.
*****
Ita kuma tana jin tashin motarsa saita ɗingisa kafarta har kitchen, Feldin ɗinta ya kare saura Paracetamol gashi tana shan wuya.
Abinda yasa take gudun Naufal baifi sanin halinshi na mugunta data yiba, tabbas muddin yaga tana pain zai kara inflicting mata more bcs burinsa kenan yaganta ta su suce.
Nan take ta yanke shawara akan tayi Cous Cous saboda it’s very easy.
Ta gama saita je dauko Fanta a fridge amma to her surprise ya kare. Dama tasan ya kusa gashi bazata iya zuwa kasuwa ba. Ruwa na sachet ta ajiye mashi kawai saita koma ɗaki.
Zaman ɗirshan tayi a kasa tana numfashi sama sama, fisge ɗankwalin kanta tayi ta jefar. Ji tayi kamar ana tsikarinta a kafan gashi yayi nauyin. Ko numfashi ta lura yana kara mata zafi.
Dukta fita hayacinta ta rasa meke mata daɗi, kwalla kawai takeyi gashi bata iya cin abinci sai shayi. “Wayyo ni Fadeela na shiga uku!”
Shi kuma yana shiga falo ya lura har tayi abinci, kwafa yayi a ranshi tareda faɗin “ke kika sani”
Haka yaci abincin kamar maɗaci saboda ya kwaɓe. Daya gama saiya kora ruwa yayi ɗakinsa, daya kai kofar Fadeela saida yaɗan tsaya koh zaiji motsi amma shiru kawai.
8:30 pm...
Yaune nake ina tunani tareda kallon TV, ko ganewa banayi saboda tunanin yarinyar chan nakeyi, “karfa ta mutu” na faɗa da sauri tareda mikewa saboda nasan Abba zaiyi balangu dani muddin haka ya faru.
A hankali na haye sama saboda banso taji karar zuwana. Safa da Marwa na rinka yi wajen ɗakinta na kasa shiga. Ni dai ban iya amai ba na lashe, Sam idan na shiga zata iya raina ni.
Shiru nayi na rasa TUDUN DAFAWA(littafin my awesome UmmieeJafar) Kawai na yanke shawara na shiga tareda zare mata ido kamar mugu. Idea ɗin yayi min daɗi bcs haka nayi.
Banka kofa nayi da k’arfin gaske tareda shiga, ina jin ta yanda tayi salati a razane. Ta bani tausayi ainun amma no time for weakness yanzu.
“Ke dan raini zaki dafa min wani abinci babu kyan gani? Waye sa’anki?” sanda na faɗa ina jin ciwo a raina but a haka na cigaba.
Narai narai tayi da ido tana kuka batace komai ba, jan magina kawai takeyi. Tausayinta ya kamani sosai saboda nasan tana kokari but it’s not enough bcs Itace dai Bad luck.
Bance mata komai ba kawai na tsaya ina kollonta, data lura ita nake jira ta bani amsa saita fara share hawayenta, “Kayi hakuri Yaya wlh bada gangan nayi ba, banida lafia ne” ta faɗa cikin muryan kuka.
“But Bari naje na dafa maka wani” saita fara Kokarin tashi. Duk rashin imaninka saika sosu. A hankali nace, “Dont worry” saina fita daga ɗakin, nawa na koma saina zauna akan gado.
Hannaye biyu na daura akan kumatu na ina tunani, gaskiya ya kamata na taimaka mata koba dan halinta ba sai dan Allah. Ban koma cikin ɗakin ba but haka na rinka zirya wajen, idan naje sai na saka kunne na akan kofarta.
Kukanta nakeji a hankali yana tashi. Gabaki daya ranar dagani har ita bamuyi barci ba. Sau biyu ko uku a cikin awa daya ina bakin ɗakin, sai wajen asuba naji tayi shiru da alamun barci tayi.
Ban kwanta ba illa nafila danayi, na rok’on ma Miemie lafiya tareda ita bcs dey need it.
7:30am...
Ta fito tana ɗingisa kafa which sai a locacin na lura da mai ke damunta, dukta kumbura ta susuce. Ji nayi kamar naje na daukota tsam daga stairs bcs ta dade bata sauko ba balle dama akwaita da nawa.
Sannu a hankali harta isa inda nake, “Ina kwana yaya?” ta faɗa murya kasa kasa.
“Lafia lau, ya jikinki?” ashe na sosa mata inda yake mata k’aik’ayi. Nan take ta barke sosai da kuka babu kama hannun yaro. Tanayi tana Sheshek’ar, bata tafi illa tsayawa a wajen.
A hankali na karasa wajen datake, har zan saka hannuna nayi patting bayanta saina fasa kafin ya zama wani abu.
“Kinaso akaiki asibiti ne?”
Bata amsani ba kuma nima naji haushin tambayan bcs yanda take tana ɓukatar medical attention. Key ɗin mota ɗina na zura saidai kash.........
Bazan iya bari ta fita haka ba, wani armless chiffon gown ta saka kuma bazan yarda wani Katon banza ya ganta ba, thou bawai ina Santa bane, but still!
“Bakida wani kaya dazaki haɗa da wannan kinsan akwai maza a wajen?”
Kallon kanta tayi saita sinna kai kafin tace, “bari naje na dauko abaya ɗina”
Juyawa tayi ta fara tafiya, idan na biye mata zamu kwana a wajen.
“just wait! Yana Ina ne idan na biye maki zaki ɓata min lokaci”
Kallona tayi kafin tace, “Cikin drawer ɗina third shelf” Haka naje na dauko mata na bata abinta. Tana ɗingishi kamar raina zai fita saboda ni ko ban san mutum banaso naga ciwonsa .
Wani private mukaje nan kusa damu, cikin sa’a Doctor yana nan. Tambayoyi ya rinka watso min wanda na kasa amsawa, wani irin kallo yayi min wanda kaida matarka amma bakasan komai a kanta ba.
Kunyar duniya naji shi ranar saboda mutumin yana mutuntani sosai saboda unguwar mu ɗaya but daga alamu ya daina.
Fadeela ne ta rinka shigan min tana amsawa, gaskiya yarinyar is very smart Kuma nagode mata cikin raina.
Anzo za’a ja mata k’afa shi kuma Naufal zai fita kawai ta chapke masa hannu ”please stay with me Yaya, Karka tafi ka barni. Im very scared”
Ta faɗa da puppy face idonta yana kwalla.
#NiDaDiYata
*My Lil sis, Amigo, Mon Amie, Te amo, Habibtee, Noor, Pyar........ I’ve no words to appreciate ur Respect, loyalty, kindness, compassion, honesty and support. I love you to the moon and back(NoHomo), Allah ya albarkace rayuwar ki. Ur enemies will never find peace, may they suffer till they perish.... Amin. Calm down her name is UmmieeJafar aka Pha’eexah, the author of My marriage series, My Greatest Weakness,Tudun Dafawa etc*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 19✨✨✨
It was narrated from Aishah that the Messenger of Allah said: "Marriage is part of my sunnah, and whoever does not follow my sunnah has nothing to do with me. Get married, for I will boast of your great numbers before the nations. Whoever has the means, let him get married, and whoever does not, then he should fast for it will diminish his desire." (Hasan)
**********
Hannunta na mak’ale da nawa ta rike tsam, kawai wani iri nakeji. Juyawa nayi bance komai ba kuma ban kwace hannuna ba.
Tsaya nayi dab da ita, ita kuma ta rufe ido tana hawaye. Mamaki kawai take bani yanda bata gajiya da kuka.
Shikuma Doctor yazo ya fara matsa mata kafa, ihu ta tsala tareda mirganawa kamar zata faɗi, da sauri na tarbo ta tareda daka mata harara. "Ni raki ne da rashin juriya ne banso”na faɗa mata.
Narai narai tayi da ido tareda saka hannunta ta matse bakinta. Doctor Yanata complain akan sakacin damu kayi bamu zo da wuri ba.
“Afuwan doctor wlh bansan abin zai kai haka bane dana kawota da wuri” Naufal ya faɗa mashi
Shidai Doctor baice komai ba illa cigaba da aikinsa, yana kawai kallon Naufal as complete idiot ne bcs gaskiya kafan Fadeela ya lalace.
Ita kuma Fadeela sai matse baki takeyi tana share hawaye, wata sa’in ta faɗa jikina idan an murɗa mata kafan but da sauri take bari idan taji daidai.
Bawai zance bana jin daɗin abin bane idan ta taɓa ni, kawai I’m just neutral. Kafin a gama mata tasha kuka sosai duk ta galabaita.
Daga nan aka bata magunguna da allurai, dole aka kwantar da ita saboda akwai na barci da sauransu.
“Toh Alhaji saika je gida ka kawo mata abinci da sauran kayan amfani” Doctor ya faɗa mani.
Toh kawai nace mashi na tafi, motana na wuce kai tsaya, ina ciki nafi 20mins banyi komai ba. Bansan me zanyi ba.
Na farko dai ban iya girki ba, na biyu kuma bazai kyautu na siyo abinci daga restaurant ba tunda bazai taɓa Kamada na gida ba.
Balle yanda Doctor ke mun kallon mugu, yana lura da abincin zai gama concluding banida saura imani.
Kawai wani dabara ya faɗo min akan naje wajen Mommy bcs tana sona, ita kaɗai ne zata mara min baya.
Nan take na tada motar nayi hanyar gidansu, Grand Kadi na gani a parking lot da suit and tie daga gani zashi court case ne.
Har k’asa na ɗuka na gaishe shi kafin na zayyana mashi komai. Salati yayi cikin damuna tareda alkawarin zaije direct bayan ya fito daga kotu. Tun daga lokacin jikina yayi la’asar yanda naga ya razana, tabbas yanzu na fara sanin gatan Fadeela.
K’afa babu kwari na shiga cikin gida, Mommy na riske a falo tana kallon Manara TV. Itama har k’asa na gaisheta which dama ɗabi’a na ne. Tashi tayi wai tana zuwa, dawowanta keda wuya sai gata tareda mai aiki shak’e da kayan breakfast.
Nan take kunya ya fara ɗawainiya dani, wai ace tsakani na da mutanen nan banda mutunci da arziki babu abinda ke shiga tsakanin mu. Ni kuma banda tsiya bana masu komai.
“Ga abinci kaci, nasan bazaka rasa guntun yunwa ba” Mommy ta faɗa. Sinna kai nayi bcs kunyar ta nakeji, “Mommy bazan iya ba, dama Fadeela ce ke asibiti”
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun, meya sameta? Tun yaushe?”
Yanda naga ta ruɗe sai na fara jin nauyin faɗa mata yarinyar ta tafi kwana uku ba lafiya sai yau na kaita asibiti. Ina cikin tunani ashe har Mommy ta zura hijabi tana tsaye kaina.
“Mu tafi koh”
tace
“Dama abinci nazo karɓa saboda idan ta tashi saita ci”
Bata kulani ba kawai ta wuce kitchen, bayan 30 mins haka sai gata ta fito da Katon flask ɗin ruwan zafi dasu kofuna tareda kayan shayi.
“Sai mu siyan mata bread a hanya kuma na saka Husna (Mai aiki) ta dafa abinci, anjima zaka dawo ka karba”
“Nagode sosai Mommy, Allah ya saka da alheri”
Muna tafe a cikin mota zulumi fal raina, kawai yanda Fadeela ta susuce nake tunani. Da akwai yanda zanyi mata makeup karda a gane danayi. Dadin abin su Abba da Anty Saudah basu sani ba aiko cinye nama ɗina zasuyi bcs na lura dis days sunfi Santa akaina.
Mun isa cikin asibiti lokacin Fadeela ta farka, tana ganin Mommy ta barke da kuka. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” na rinka nanatawa kafin Fadeela ta tona min asiri.
Kawai Mommy patting bayanta takeyi ciki so da kulawa, “Yi hakuri My baby, Kowa da jarabtan shi. Karki damu an kankare maki zunnuban ki ne... Daddyn ki shima ya kusan zuwa” Haka Mommy ta rinka shafa mata baya tana bata baki.
“Ka kira Hajia Saudatu kuwa dasu Hajia Sarai?” Mommy ta tambaye ni, yak’e nayi kafin nace, “Yanzu zan kira su”
A gabansu na kira Anty Saudah da Mama harda Abba akan an kwantar da Fadeela, yanda hankalin su ya tashi yafi na iyayen Fadeela.Nidai bazan iya barin ɗakin ba bcs ina tsoron kada ta fayyace ma Mamanta komai.
1 hr 45 mins later.....
Motar Anty Saudah ya fara isowa cikin haraban asibitin. Tazo tareda cooler ɗin abinci dasu fruits da kayan shayi. Tana shiga tayi ido da Fadeela ba tace komai ba, kawai ajiye kayan tayi suka gaisa da Mommy har tana tambayar ta jikin Miemie shine take cewa gaskiya yanzu yayi sauki sosai.
Bayan nan ta matsa wajen Fadeela tana mata kallon tuhuma, “Sannu kinji! Tun yaushe kikaji ciwon?”
Ita Fadeela bata gane abinda akeyi ba saita faɗa ranar. “Shine dan mugunta yau kaga damar kawo ta asibiti” ta juya tanama Naufal sababi.
“Dan wulakanci an gaya maka jaka aka kai maka, salan ta mutu ko ta nak’asa?” Mommy ne ta chapke, “Yi hakuri Hajia Aiba laifin shi bane”
“Karki ce haka, nasan halinshi sarai kuma nasan abinda zai iya aikatawa”
Suna cikin haka ne saiga Mama da Abba da Bilqees. Mama kallona tayi ta juyar da kanta kuma koda na gaisheta bata amsa mani ba.
Shikuma Abba da nace mashi “Ina kwana” da kai ya amsa min. Chan gefe na koma na tsaya kamar bare saboda kowa fuskarshi yana ɗauke da irin kallon da kake ma mugu.
Abba ya soma magana k’asa k’asa, “Yanzu Naufal me muka yi a duniya da kake so ka hana mu sakat?” sai kuma ya kafa min ido. Kunyar duniya ya kamani kamar kasa ta buɗe na shiga. Bance komai ba nayi shiru.
“Gwara dai ka tambaye shi sai mu bashi hakuri?” Mama tace. Ita kuma Anty tace, “Ai kuwa dai, saboda wannan ɗebo ruwa dame yayi kama?”
Abba yayi ajiyar zuciya saiya kalle Fadeela sannan ya sake kallona, “Dube yarinyar nan fisabilillahi, halan kana tunanin jaka aka kai maka? Dafa gatan ta da komai ka k’askantar da ita.... Kalleta da kyau kamar an hak’ota a rami”
“Ai idan rami ne da sauki, ji yanda tayi kamar ita ce k’asan da aka hau sanda ake yin Badar” Mama tace.
Mommy ne tace,”Kuyi hakuri bafa laifin shi bane yasa ta faɗi, ai tsautsayi baya wuce ranar shi”
“Toh sai akace kada ya kawo ta asibiti??” Anty Saudah ta faɗa.
“Ina dasu Paracetamol a ɗaki yasa nace kada ya damu bari mu gani ko zanji sauki” Fadeela ta tare min.
Mama ce a hasalce tace, “Idan kika kara saka baki saina mauje ki. Watau ke mai miji koh? Kina tsoron kada ya rama abinda mukayi mashi akan ki koh?” Saita juyo tana fuskantana, “Kana ji na koh?”
Bance komai ba sai Abba yace “bada kai ake magana ba, you’re Very stupid” Ba shiri na amsa Mama saboda na lura da girmana sunaso su tara min gajiya.
“Ciwon kai naji labarin yarinyar chan tayi sai anjimu a gari, dama ɓata min suna kake so kayi na kasa shiga makwabta, ina tafe ana nunani ga Maman Mugu.” Sai kawai tayi kwafa ta juyar da fuskanta.
Dama Hausawa sunce abinda ka suka shi zaka girba, idan alheri ne to, idan kuma tsiya toh shima haka saboda babu wanda zai shuka shinkafa yaga rake. Tas bayin Allah ɗinnan suka min, wanki babban bargo suka min la’ada waje saboda su uku ba wanda ya raga min.
Mommy babu magiyan duniya da batayi su bari ba amma ina, sai mita sukeyi.Kamar kwallo suka mayar da abin, sai attacking ɗina sukeyi tareda passing ma junar su.
Harda cewa Abba yayi, “Toh Hajia Sarai Kinga abinda yaronki yayi”
Da sauri ta chapke, “Ba yarona bane, yaron Saudatu ne”
“Nima banaso gaskiya, Hajia kinaso?” sai Anty Saudah ta kalli Mommy tana dariya tareda tambayar ta.
“Sosai ma kuwa tunda kun haɗe mashi kai”
Dama tun zuwansu Bilqees ta fara ba Fadeela abinci bcs tun tea ɗin da Mommy ta bata babu komai a cikin ta. A baki ake bata ana lallashinta gwanin ban sha’awa.
Anty Saudah ta ɗauki kankana da abarba ta fara ferewa, kallo nayi tareda shiru bcs cikina ya fara kiran ciroma tunda banci abinci kwata kwata yauba.
Mommy daga baya ta zuba min abinci tareda bani Fanta, Motana na wuce naci nayi gyatsa tareda guntun gyangyaɗi bcs na galabaita daga sintiri danayi ɗakin Fadeela jiya.
Bayan kwana uku......
Babu wanda baizo gaishe da Fadeela ba including Miemie, saboda tana jin Anty yar gayu batada lafia sai kan ya fara motsawa. Dole aka kawo ta kuma cikin ikon Allah babu handcuffs kuma batayi anything funny ba.
Ita tayi ɗawainiya bata abinci da ruwa, ita abin dariya ya bata saboda ciwon K’afa takeyi ba na hannu ba, kuma ta fara taka kafan kaɗan kaɗan.
Kana ganin ta cikin kwanakin nan kasan cewa yar so ce kuma ba abin wulakanta wa bane. Hatta Big Daddy da iyalansa Ba’a barsu a baya ba, ko Alhaji Sulaiman baban Sadeeq yaje dashi kanshi Sadeeq da matarshi.
Abinci kuwa mai aikin Anty Saudah ke kawo three square meal tareda Mai aikin Mommy. Itama Jawahir duk sanda taje saita kai masu wani abu.
Kwata kwata Naufal baya jin daɗin asibitin idan Anty Saudah da Mama nanan, yafi son idan sun tafi gida ya zauna da Mommy Asha hira.
Bilqees ke kwana da Fadeela thru out. Ni Naufal wajen 6am na isa asibitin kafin su Mama su rigani zuwa asibitin su kama kirana ‘Mugu’ bcs na tsana sunan har cikin raina.
5pm....
An haɗa kayan Fadeela komai da komai ana jiran Doctor ya gama prescribing magani ya sallame su. Itama ta ɗan warware tayi ɗan armashi abinta ba kamar yadda aka kaita ba.
Mama ce tace saidai Fadeela ta wuce wajenta ta k’ara murmurewa saboda tasan halin Wa’e saita kalleshi ta gefen ido. Idan ana sabo da tozarci ya riga ya saba dashi dis past few days saboda sun mayar dashi laughing stuff, mocking ɗinsa anyhow kawai sukeyi.
Saidai ba fault ɗinsu bane, dama komai kayi akwai reckoning ko a duniya ko lahira baki ɗaya. Da bai zubar da girman da Allah ya bashi ba yayi abin tsiya da haka bai faru ba. But he promised to do better.
“Nifa ba inda za’a je min da mata” ya faɗa masu.
Mama ta dubeshi a kaikaice, irin duban hadarin kaji “Toh mara kunya hanamu” ta hayayyakoshi.
“Ai dama da bakice haka ba, wajena zata zauna kinsan sun saba da Miemie” Anty Saudah ta faɗa.
Haka suka rinka jani in jaka shi babu wanda zai tafi mashi da matarsa wani wajen.
Fadeela na daga kwance tana jinsu duk rai a jagule, tsakani da Allah tunda yace he will do better gwara a barta ta koma ɗakin ta. Sai wani zuciya yace mata “Karya yakeyi kawai bauta yake so ta koma tana yimashi”
Kauda tunanin tayi bcs aure ibada ne kuma ladanta yana sama wajen Allah. Indai da aure tsakanin su gwara tayi masa koma menene muddin bazai kare hakkin addini ba.
Kowa yasani Allah yana tareda masu hakuri Besides Hausawa sunce mai hakuri shike dafa dutse har yasha romonta.
Anty Saudah ta dafa mata kafaɗa “ ‘yata! Zaki bini muje gidan gona?” Bata ce mata komai ba illa Sinna kai kasa tana wasada hannunta.
“Sauraron ki nakeyi”
Daga ido tayi saita lura kowa kallonta yakeyi, musamman shi gwaskar ya kafa mata ido babu kiftawa. Sunkuyar da kai tayi tareda cewa, “Anty duk abinda kuka ce shi za’a yi”
Kwafa yayi ranshi ya bala’in ɓaci bcs tunda suna Santa idan tace zata zauna dashi babu mai hanata. “Ko kai bazaka zauna da kanka ba idan an barka” wani siririn murya ya raya mashi.
Ita kuma koda wasa bazata iya cewa tana son zama da mijinta ba bcs rashin kunyarta bai kai haka ba besides suna kwatan mata yancin tane.
Daidai lokacin su Grand Kadi da Mommy suka shigo, Naufal bai bari sun natsa ba ya fara masu k’orafi akan za’a rabashi da matarsa.
Murmushi Grand Kadi yayi, “ karka damu babu mai hanaka tafiya da matarka, kai ka shigo da ita kuma kai zaka fita da ita”
“Woooow!” ya faɗa tareda naushin iska. Ko kunyar kowa baiji ba ya nuna murnarsa a fili. Harda shaking hannun Grand Kadi yana godiya.
Dariya yake masu Anty Saudah domin yaci argument ɗin, ita kuma takaimai dukan wasa a kafaɗa sai shikuma ya kauce tareda saurin barin ɗakin.
Fadeela sinna kai tayi ba tace komai ba but murna fal ranta zata koma wajen Other Half ɗinta.
An tarasu su biyu an masu nasiha akan aure mai shiga jiki, idan kayi shi da kyau ka kuɓuta, if not Zai kaika ga hallaka. Aure ba abin wasa bane kuma yana cikon manyan sunnonin Manzan Allah SAW.
Zo mu zauna dama zo mu saɓa ne, kuma mistakes are what makes you human but Yanda Kayi handling ɗinshi makes u a better person.
Wajen 30 mins kowa na tofa albarkacin bakinsa kafin aka shi masu albarka suka wuce.
Dama da safe Bilqees, Abla harda Miemie sunje gidanta sun gyara mata tsap. Ita Miemie tun sanda ta fara fita wajen Anty yar gayu aka fara gane kanta, tana shan magani akai akai kuma bata gardama.
Thou ba’a barinta alone, sun shirya ma Fadeela komai hardasu laundry aka tayata.
Shikuma ya tsaya Vanilla joints ya siyan masu kayan lashe lashe sai kuma ya siyan masu kaji gasarshe na kan titi.
Shi Bawai Santa yakeyi ba but kawai after everything he put her through, tayi deserving something sweet. Ita tana mota tana mamakin yanda yakeyi kamar ba shiba.
#NiDaDiyata
*Big shout-out to all the fans of this book, Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Especially those dana keda direct contact dasu kamar su UmmieeJafar Novels, Xarah Novels, The Queen Bee, Deyart Novels, Hamagee Novels, Billy Galadanci Novels, Marubuci, Rash Kardam Novels, Xoubhie Novels etc*
#TeamNiDaDiyata
#TeamFadeela
#TeamNaufal
#TeamMiemie
#TeamKhattab
*Ni dai TEAM NAUFAL ce*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 20 ✨✨✨
*Lesson*
Patience is when you're able to conquer that angry voice in your head which wants to take revenge on others who hurt you or are mean to you!
Mufti Ismail Menk
Ibn Mas'ud (May Allah be pleased with him) said: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "He who says: 'Astaghfir ullah-alladhi la ilaha illa Huwal-Haiyul-Qayyumu, wa atubu ilaihi (I seek the forgiveness of Allah, there is no true god except Allah, the Ever-Living, the Self- Subsisting, and I turn to Him in repentance),' his sins will be forgiven even if he should have run away from the battlefield (while he was engaged in fighting for the Cause of Allah)."[Abu Dawud, At-Tirmidhi and Al-Hakim
**********
CYPRUS
A East ɗin Mediterranean akwai wani Island da ake kira Cyprus, chan daga wajen Arewan garin akwai wani k’aramin gidan gona wanda ya k’unsa ɗakuna biyu da bayi uku tareda da kitchen daya.
A cikin falon akwai dinning area, drinks cabinet da kuma chimney.
Wani matashi ne wanda bazai kai shekara 25 a duniya ba ya shiga cikin gidan, hannunsa shak’e yake da itatuwa kuma ya nufa hanyar fireplace ɗin falon, yana zuwa wajen saiya dire tareda ajiyar zuciya.
Kayan sanyin dake jikinsa ya fara k’okarin ragewa, safar hannu ya cire sai kuma maufler tareda head warmer.
Yanzu fuskarshi ya bayyana sosai wanda da baka ganin komai sai k’wayar idanu. Jacket ɗinsa ya cire tareda ajiye wa akan couch sai ya rige daga shi sai sweat pants tareda T-shirt.
Kai tsaye dinning area ya wuce ya haɗa ma kanshi shayi a wasu fararen Chinese wears. Yana sha yana lumshe ido,Saida ya zuba ma kansa kofi biyu na ruwan bunu kuma ya shanye tas.
Tsam ya mik’e tsaye ya wuce wajen wani calendar haka wanda yayi kacha kacha da rubutu. “Day 190” ya rubuta a bangon saiya wuce hanyar bedroom ɗinsa ya shiga bayi direct.
Kallon kansa ya tsaya yi a mirror ɗin bayin, duk ya canza kamanni ya susuce. Rabon daya aske gashin kansa kona gemunsa tun yana Nigeria. Yanzu Afro yayi tsawo kamar jirgi ya doso gari ga kuma fuskarshi jaɓa jaɓa da gashi.
Mutane biyu kawai yake tausaya mawa, na farko dai Mahaifiyarsa wanda yasan tana cikin matsananci tashin hankali akan rashinsa.
Na biyu kuma Haskensa Miemie, rashinta yayi sanadiyar gudunsa. Shifa bazai iya zama gari ɗaya babu ita yasa kawai ya tafi.
Wanta yayi making ɗinshi clear bazai taɓa bashi ita ba saboda wasu dalilai nashi. Shikuma idan ba Miemie bazai zauna da wata mace a inuwar aure ba.
Babu makawa idan yana gidansu za’a tursasa shi akan ya aure Lili which bazai iya buɗe idonsa ya ganta ba.
Wanka yayi sannan ya shirya cikin Long sleeve da jens wando, ɗayan ɗakin opposite nashi ya wuce tareda shiga. Maidaidacin ɗaki shake da kayan computer kala kala tareda sauran abubuwa daya jibanci haka.
Zama yayi akan wani kujera dayake gaban babban computer. Kunnawa yayi sai wani rubutu ya fito inda aka rubuta NTI TELECOMMUNICATIONS.
Nan ya saka password ya soma aiki gadan gadan, kana ganin yanda yake aiki cikin kwarewa kasan cewa ba sabon hannun bane.
NIGERIA
“Inspector mun samu leads akan shi” wani Sergent ya Shiga office ɗin IG tareda mashi salute.
Ajiye takarda yayi dake hannunsa sannan ya gyara zama tabaransa.
“A Ina ne wajen?”
“Sir Chan Cyprus ne, akwai wani ICT company dayake ma aiki. Toh wani ɗan department ɗinmu dayayi tracking hotonsa a cikin database ɗinsu”
“Innalillahi, tuntuni muna nemasa amma yana chan Cyprus. How true is this information?” IG ya tambaya.
“Anyi kowane bincike kuma an gane Khattab ne”
“Kuma kun tabbata anan yake aiki ba scam bane?”
“Affirmative Sir”
“Okay ku shirya mana Visa muje Cyprus muga gari”
2 days later....
Khattab ne ke cikin Garden ɗinsa yana gyarawa, dayake Miemie ta koya mashi yanda zaiyi shuka da sauran su so bashida matsala wajen yi yanzu.
Saboda yana Missing Miemie in the first place Yasa ya siya gida mai yanayin gidansu watau na gona. Yana cikin gyara sunflowers da kuma Hydrangeas sai kawai yaji an shigo mashi gida, bai yi kokarin dubawa ba saboda mutum ɗaya ya sani watau makwabcin sa Mr Kareem.
Tafiya yaji ta wajen ɓangaren dayake Kuma yasan Mr Kareem bazai zo wajen ba. A hankali ya ɗaga tareda juyawa, fuskar da bazai taɓa manta wa ya gani. IG ne yake tafiya wajen dayake.
Nan take gabansa yayi mumunar faduwa, da sauri ya mike tsaye tareda da sakin shovel ɗin hannunsa. Jikinsa rawa ya somayi baisan mai zaice ba.
Shikuma Daddy ɗin Khattab zuwa company ɗin Khattab yayi sai akace mashi Khattab a gida yake masu aiki wai baya san cuɗanya da mutane, toh dayake he is good babu Yanda zasuyi.
IG yana nuna masu clearance ɗinshi a matsayin jama’an tsoro kuma ana neman Khattab dead or alive a Nigeria. Nan take suka haɗashi da wani officer domin ya jagoranci shi zuwa gidan.
Yana isa saiya ji motsi ta wajen garden yasa yaje ya duba. Ido cikin ido yake kallon Khattab shi wanda ya maza ya sauke nasa saboda kwarjini.
“Ka kyauta kenan Khattab?” Mahaifinsa yace.
*********
Motar shiru babu abinda ke tashi sai tafsir ɗin Sheik Aminu Ibrahim Daurawa akan aure. Sannu a hankali har suka isa gidansu, horn sau ɗaya yayi Maigadi ya buɗe masu.
Suna cikin parking lot sun fito sai Maigadi Mallam Idi yazo wajen su.
“Ina wuni Hajia ya jiki?”
“Lafia lau ya aiki?
“Alhamdulillah” Daga nan saiya ɗaukan masu jakar su, har cikin falon ya ajiye masu sannan ya masu saida safe.
Fadeela a hankali ta ɗingisa kafarta har ɗakinta domin tayi sallah, shima Naufal ya wuce Masallaci.
Bayan ta idar saita sauka ta sake microwaving kazan saita haɗa mashi da snacks ɗin da suka siya.
Ta ɗeba nata tana kokarin wucewa saiya shigo falon, kallon ta yayi sau ɗaya saiya kawar da fuskarshi. Kan Dinning ya kalla sai yaga komai is set.
Murmushi yayi a ranshi yana tafe fuskarshi kuma babu yabo babu fallasa.
“Saida safe Yaya” ta faɗa sannan ta haye sama.
“Toh” ya amsa mata dashi.
Tana ɓacewa saiya tsaya cak, haushin kanshi ya fara ji sosai bcs yanda ya amsata bai dace ba. Besides shida yake neman sulhu.
Amma zai gyara abin, yayi assuring kansa.
Next Day....
Ya kasance Weekend so Naufal bazashi aiki ba, kuma koba haka ba babu inda zashi bcs ya barma Aminu komai a hannunsa tunda shi yana jinya.
Wajen asuba ta farka tana mitsike idanu, tana cikin bargo tana ajiyar zuciya a hankali. Karar kofan Naufal taji da alamu zashi Masjid ne.
Murmushi tayi mai bayyana hakora saboda Other half ɗinta akwai ibada.
“Allah ya daidaita tsakanin mu” ta faɗa tareda yin mik’a, salati tayi saita wuce bayi.
Shikuma Naufal yaso ya tsaya ɗakinta domin ya tasheta amma wani zuciya yace masa “Meye ruwanka da ita salan raini ya shiga tsakani, halan da kai kake tashin ta?”
Bayan an Idar da sallah saiya tsaya lazimi kafin gari ya k’ara haske, yanayi sai kuma Fadeela ta faɗo masa a rai. Da sauri yake kawar da tunanin but still ya kasa bari, haushin abin yakeyi matuka but babu yanda zaiyi.
Da gari yayi haske saiya wuce gida abinsa, a hanya ya haɗu da Doctor daga gani asibiti zashi. Sun tsaya sukayi gaisuwan mutunci but still Doctor ɗin Bai wani sake jiki dashi ba kamar da.
Ya tambaye shi lafiyan Fadeela kuma ya jaddada mashi amfanin magani da kuma tayi kokarin taka kafanta.
“Karka damu Doctor” Naufal yayi assuring ɗin sa.
“Toh” yace saboda yana bala’in jin haushin Naufal. So da dama ya saba ganin couples wanda basa shiri amma ba kamar yanda nasu yake ba. Ya lura matar batada matsala kawai mijinta ne mai zafin kai yasa ya dena sake mashi fuska.
Bayan ta idar da sallah saita mirgina gefe ta kama barci, ba ita ta farka ba sai wajen 7:30 am. Wanka ta somayi saita shafa ma kafarta wani magani haka mai suna ‘Power Heat’
Zama tayi akan mirror ta rasa wani irin kwalliya zatayi, sai kawai tayi smoking eyes da purple lips. Wardrobe ɗinta ta wuce ta ciro wani bakin dogon pencil gown saita dauki wani peach kimono ta haɗa dashi.
‘Daurin turban tayi wanda ya kara k’awata mata fuskarta. Su humra da turaren Chanel No 5 ta fashe kanta dashi. Tayi kyau ainun ita kanta ta yaba balle wani, takalmin soso baki ta saka mai dunlop.
Kitchen ta wuce kai tsaye ta auno wake ta fara wankewa saboda kosai zatayi masu da kunun gyaɗa. Dayake blender ɗinta na zamani ne saita markaɗa abinta.
Shikuma koda ya dawo bai ganta ba sai ya wuce kai tsaye ɗakinsa, baiyi 5mins ba barci mai kyau yayi awon gaba dashi. Wajen 9 am ya tashi kuma kamshin abinci ya cika mai hanci. Shima wankar yayi saiya saka 3 quater camouflage da sleeveless riga fari.
Koda ya shiga falo bai ganta ba kuma babu abinci akan dinning kawai kamshi ne yacika Ko’ina. Zama yayi akan Couch ya fara kallo, Keeping Up with the Kardashian ya gani yana aiki kuma Yasan ita ta Saka bcs koda yaushe abinda yake riskewa kenan, dariya yayi saboda baiga amfanin kallon mutanen da basuda sana’a sai shopping.
JSC sport ya saka ana nuna Basketball kuma favorite player ɗinshi Kobe Byrant ke wasa, nan ya shagala Yanata kallo. Ita kuma ta fito zata ajiye cooler sai taga ya shafa’a yana kallo.
Bayan ta gama jere komai yayi tsaf saita taka sannu a hankali har wajen dayake, wannan Karon babu karap karap ɗin takalmi. Kamshin Chanel No 5 yaji but bai hasala ba kamar da yanda yakeyi, wannan Karon jindaɗin kamshin yayi.
A gefen sa ta tsaya ta rasa me zata ce bcs ya kura mata ido Which baisan ma yanayi ba. “yaya ina kwana?” ta faɗa tana wasa da yatsunta.
“lafia lau, ya jikinki?” ya faɗa fuskarshi babu yabo babu fallasa.
“I’m much better, thanks” sai sukayi Shiru basu ce komai ba, kana ganin su kasan akwai tension a tsakanin su. Da wani siririn murya tace masa, “Dama yaya nazo na faɗa maka na gama abinci ne”
“Okay sai muje kiyi serving ɗina”
Tana tafe yana binta da ido kawai kallon ta yakeyi, tanaji à jikinta ya kafa mata ido saboda duk ta birkice. Dadin abin kayanta bai nuna matsewa saboda Kimono data saka if not tasan Zata kara turguɗewa.
Kamar yadda ta saba ita ke jawo masa kujera saiya zauna, wannan karon yace mata, “Thanks”
Gyada kai kawai tayi saita soma zuba mashi, yanda yake abin har mamaki yake bata bcs he was very polite.
Ta gama zuba masa kunun saita saka masa madara a ciki yanda akeyi, ashe shi bai taɓa gani ba. “Toh fah!” ya faɗa a ranshi bcs da bfr ne saiya watsa mata a jiki koya haska mata mari bcs baya san shishigi.
Ita kuma ta shafa’a cikin tunani ta mance kofinshi ne saita saka madara, koda ta ankara salati kawai takeyi bcs tasan shi. Tayi mamaki sosai da baiyi magana ba.
Hanyar ɗaki ta nufa saita ji muryan shi, “Ke bazaki ci abinci bane?”
Cak ta tsaya saita juyo a hankali, bata yarda sun haɗa ido ba bcs idanunsa yana making ɗinta uncomfortable sosai.
“Banajin yunwa” ta faɗa tana murza ido tareda tura baki. Kawar da fuskarshi yayi saiya ce, “Maganin fah?”
Bata ce komai ba illa wasa da yan yatsun hannunta, tanayi tana kallon kasa.
“Please kici abinci saboda Kisha magani” ya faɗa kasa kasa. Babu yanda zata yi dole ta hakura ta koma, komai a hankali takeyi bcs duk ya takura mata da Idonshi.
Da a kaikaice yakeyi amma daga baya saiya fito ɓaro ɓaro yana kallon ta, ko sun haɗa ido saidai taji kunya ta cire nata amma bazai cire nashi ba.
Shi kawai yanda take yin komai yake mashi kyau, komai a hankali kamar batada jini. Gashi ta tsantsara kwalliya kamar yanmatan TV.
Haka suka gama cin abincin ta kwashe komai ta gyara tas. Ita tunda take zaman gidan bata taɓa takura ba kamar yau, duk inda taje kanshi yana kanta. Ya mayar da ita abin kallo dukta tsargu.
Tunanin yanda zai nemo sulhu tsakanin su yakeyi amma ya rasa. Gashi ko number ɗinta bashida shi balle ya aika mata text.
Kiran Bilqees yayi a waya akan ta tura mashi number ɗin Fadeela, within Minutes tayi mashi sending. Murna yayi sosai kuma yayi mata alkawarin waya dama tuntuni tana rok’on sa amma yaki sai yanzu.
Komawa ɗakinsa yayi bcs tuntuni Fadeela ta barshi shi kadai. Zama yayi akan bedside drawer ya daura kafa ɗaya kan ɗaya fuskarshi dauke da annuri. A hankali ya soma composing mata msg ya tura mata.
Yayi rubutu sosai saiya tsaya kafin ya cikata da surutu kuma still wani zuciya yana raya mashi zata raina shi amma wannan karon ko ajikin sa, indai zata amsa batunsa bai damu ba.
Ita kuma data koma ɗaki hawa kan gado tayi ta rungume pillow, kawai yanda Naufal yakeyi ke bata mamaki bcs farad ɗaya ya canza from the mean husband ɗinta to someone sweet and gentle.
Blushing Kawai takeyi bcs idan ya fara santa batasan irin daɗin da zataji ba. Tana kwance tana tunani tareda kallon ceiling, wani msg ya shigo mata, ta karanta yafi sau uku tana mitsike idanu amma still abu ɗaya tagani.
“Nasan cewa we didn’t start on the right foot, but fate ya kawo mu tare. I feel wrong but I’m human Kuma dan Adam ajizine, I Can’t help it but you reflect in my heart. You blossom in my heart and I’m going to cherish it till my last breath.
You are my sound of redemption, the faith that I’ve lost, the answer that I’m seeking no matter the cost. You taught me forgiveness by giving your love back to me even when I don’t deserve it.
I see truth somewhere in your eyes, I can’t ever change without you bcs you reflect Me and I love that about you.
No matter how I dodge trying to be careful, going round in circles still my feelings grew more for you.
What I’m trying to say is that, I just wish for us to be like other couples.”
Kallon msg ɗin take wai ita Fadeela ya tura ma wannan abu, gyara zamanta tayi saita kalle kanta ta madubi ta kalle waya bakinta a buɗe tana mamaki.
#NiDaDiyata
#TeamNiDaDiyata
*Awwwn I'm so sad, Wai yanzu ace TEAM FADEELA su suka lashe gasar. Ya akayi kuka zabeta bayan idon Naufal yana glimmering.*
*And before I forget this page belongs to you Zeenaseer author of AMAL and MARAICI Allah ya albarkace rayuwar ki, Amin*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 21 ✨✨✨
Abu Umamah Al-Harithi narrated that he heard the Messenger of Allah (pbuh) say "No man seizes the wealth of a Muslim unlawfully by means of his (false) oath, but Allah will deny Paradise to him and will doom him to Hell." A man among the people said: "O Messenger of Allah, even if it is something small?" He said: "Even if it is a twig of an Arak tree." (Sahih)
********
Dama bahaushe yace mai hakuri zai dafa duste kuma yasha romonta, a yau naga fa’idan hakurin danayi a gidan Naufal, duk wulakanci da yayi min na shanye shi.
Wannan shine wanka ya biya kuɗin sabulu. Dama kaso, kuma a soka shine ribar aure. Burin ma’aurata kenan su zauna da spouse masu kaunarsu kuma nima yanzu na shiga sahun su.
Haka na rinka bin gado ina mirginawa daga bangare ɗaya zuwa wani. Karanta msg din nakeyi saida na haddace, na shafa’a na mance da ya kamata na amsa mashi. A haka har barci ɓarawo yayi gaba dani.
Shikuma Naufal ya rasa meke masa dadi, jira yakeyi tayi masa reply tunda ta IMessage ne yaga ta karanta amma kuma batayi reply.
Nan take ya fara over reacting, safa da Marwa kawai yakeyi cikin ɗakin from bango ɗaya zuwa wani.
Kwakwalwarsa ta fara rage aiki saboda abubuwa sun cunkushe masa, “Shikenan na cuce kaina, nayi sanadiyar da ta tsane ni”
Haka yayita nanatawa tareda dafa kanshi. A yau yayi dana sanin duk abinda yayi mata, dama shi zuciya ba’a kwabarsa. Idan yace yana san abu to dole a bashi.
Yayi hanyar bayi kenan zai kama ruwa, wani kara yaji alamar msg ya shigan masa waya. Da gudu yaje domin ya buɗe kuma fuskarshi dauke da annuri.
Ashe MTN ne sukayi mashi msg ɗinsu na fama akan How to learn English. Ranshi yayi mumunan ɓaci saboda yaso ya kirasu yayi masu tas.
Bayi ya koma yayi abinda zaiyi ya fito, a hankali yaje wajen ɗakin ta tareda kafa kunne akan kofa amma baiji komai. Haka ya hakura ya koma ɗakinsa saboda ko zaman falo ya isheshi musamman yanzo data tsane shi.
1 pm.....
Locacin yana zaune akan mirror yayi tagumi, tunani kala kala kawai yakeyi. Jin an kira sallah yayi saiya wuce masallaci.
Koda aka idar baiga amfanin shiga ciki ba kawai saiya zauna tareda Maigadi.
Ni kuma koda na tashi sallah nayi kafin na makara, bayan na idar wayana na dauka sai na kira Yaya amma bai dauka ba.
Nan take na canza zama bcs shine kaga samu kaga rashi. Kara kiransa nayi amma bawan Allah nan bai dauka ba, a kalla nayi masa 5 missed calls but still babu response.
Nan na soma zufa, “Ko dai wasan April fool yayi min” saidai ba watan April muke ba, muna January ne.
Ni dama ban iya firgita ba, da sauri naje dakin Yaya saina kwankwasa amma shiru. Dole na tafi bcs tuntuni yayi min iyaka da ɗakinsa.
Hawa nayi kan mirror na kifa kaina, sana’a ta na kuka na somayi. Saida nayi ma’ishe naje bayi na fyace magina tareda dauraye fuskana.
Ko makeup banyi ba kawai kitchen na wuce domin na shafa ma cikina lafia saboda naji yana kuka. Jollof ɗin shinkafa da wake nayi tareda Fish Nugget, sai na haɗa da ginger drink wanda yasha kayan kamshi.
Still Koda na gama na jera komai banga yaya ba. Zama nayi ina kallo, daga 3 seater sai 1 seater sai kuma kasa na rinka bi.
Har wajen uku da rabi bai dawo ba, haka na koma upstairs na cigaba da zama a wajen.
An kira sallah na tashi nayi tareda nafilfilo, as usual daidaituwan tsakanin mu na roke Allah. Nifa a duniya Ban iya zama ba’a min magana ba yasa duk kamanni na ya canza.
Kimono ɗin duk ya isheni sai nace bari na cire sai nayi maza naje na ɗebo ma kaina abinci. Wayana yana hannuna ina tafe ina sana’ata na shan waka. Wakar su Taylor Swift da Zayn Malik Mai suna ‘I don’t wanna live forever’ na saka akan repeat.
Shikuma Naufal bai bar dakalin gate ba saida aka kira sallah, masallaci yaje daga nan ya koma gida. Duk baya jin dadin jikinsa, a hankali yake tafiya sanya sanya kamar Fadeela.
Yana isa falo yayi sallama ciki ciki saikana kusa zaka ji, karar wakar yaji saiya mayar da hankalin sa wajen dinning area inda yaga Fadeela. Tana bin wakar ta a hankali tareda ɗiban abinci kana gani bata san yana wajen ba.
Kafa mata ido yayi sosai babu kiftawa, “Every disappointment is a blessing in disguise” a yau yasan ma’anar abinda babba ya hango yaro koya hau Kufena bazai gani ba.
Yau ya gode ma iyayensa da basu bari wawancin sa ya kai shi ga losing ɗinta. Kuma ya godema iyayen Fadeela dasuka kara bashi second chance ba’a wuce da ita ba.
Tana bin wakar dai dai wani baiti saita kara murya, “I'm sittin' eyes wide open and I got one thing
stuck in my mind.
Wondering if I dodged a bullet or just lost the love
of my life
Baby, baby, I feel crazy
Up all night, all night and every day
I gave you something, but you gave me nothing
What is happening to me?”
Haka ta rinka bin wakar shi kuma kawai kallon ta yakeyi bcs kara shigan masa rai takeyi by the minute. An kai wani baiti shima ta fara yi wannan Karon kamar performance takeyi bcs harda motsa hannunta. Gashi muryanta shigan masa rai yakeyi.
“I just wanna keep callin' your name
Until you come back home
I just wanna keep callin' your name
Until you come back home
I just wanna keep callin' your name
Until you come back home”
Wani zuciya yace masa waye take jira? ya dawo kamar wakar da gayya takeyi. Kawai ya yanke shawara yaje yayi mata magana koma mai zai faru shikenan.
Karar tafiyar shi taji, bazata ce bataji daɗin ganinsa ba but gaskiya bataso ya ganta cikin kayanta ba, kunyar sa takeyi tunda ta lura ya fiye kallo.
Da sauri ta bar diban abinci zata bar wurin, kasa magana tayi zata ratsa ta wuce sai kawai yasha gabanta. Bata ɗago ta kalleshi ba bcs bazata iya ba.
Kara kokarin ratsawa tayi ta wani ɓangaren shima ya tareta. A hankali ta soma magana kamar zatayi kuka bcs duk ta birkice, “Yaya please bari na kai abincin ɗaki saina dawo na saka maka naka”
Shiru yayi baice komai ba, kawai a ranshi yake ayyana shikenan ta gama tsanar sa saboda ko kallonsa ta kasa yi.
“Kin tsane ni koh?” ya faɗa cikin raɗa. Da sauri ta dago ta kalleshi ashe shima kallonta yakeyi, suna haɗa ido saita sauke nata.
“Bazaki amsani ba? Nace kin tsane ni koh?” Daga kai tayi masa alamar ta ‘ah ah’
“Toh idan baki tsane niba menene? Bakiga text ɗina bane?” Daga ido tayi suka kara hadawa saita sauke, gashi abinci yana hannunta yana kona ta.
“Yaya bari naje ɗaki na dawo?”
“Au yanzu ma bazaki iya cin abinci tareda niba sai a daki koh?”
“wlh ba haka bane, Hijab ɗina zan dauko”
Wani kallo ya watsa mata tareda janyo hannunta zuwa dinning, kamar yadda ta saba mashi ta janyo mashi kujera haka shima yayi mata.
Abincin dake hannunta ya amsa ya ajiye saiya dauko cokali. Mamaki kawai takeyi amma bata ce komai ba, kawai kallon gefe takeyi tana wasa da yatsan ta. Kana ganin yanayinta kasan she is intimidated by him.
Shi kuma daɗi yakeji yanda ta natsu ta kasa sakat, abinci ya deba zai bata a baki, “Na lura bakya shiri da abinci, fisabilillahi ji wanda kika diba!”
Kallonsa tayi yana kokarin bata a baki saita kauda fuskarta tana kokarin magana a shagwabance, “Yaya Please da zafi kalle yanda yake tiriri”
“Shhhhh, bana san surutu”
Haka dan dole tayi shiru ya rinka bata, ita kuma sai zuba mashi shagwaba takeyi wai yana cika cokali. Dariya take basa sosai saboda yanda take abinta, Komai cikin sanya sanya.
A yau yaga fa’idan sanya sanya ba garaje ba. Bayan ya gama bata dukda ba sosai taci ba shima ya ninke hannu saita bashi.
Kunya sosai ya kamata bcs Naufal ya sauya sosai kamar bashi ba. K’ememe yayi wai bazai iya ci da kanshi ba.
Dole ta rinka bashi yana ci kamar zai tauna harda hannunta, shagwaba sosai ya rinka zuba mata kamar yaro karami, ko abinci ya taɓa masa gefen fuska zai tabe baki wai sai an goge masa.
Dariya ya rinka bata ita kuma tayita yi, NI kuma DIMPLΣS bakina kamar gonar auduga saboda taya Fadeela murna akan ta samu other half ɗinta.
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨ ✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 22 ✨✨✨
Yahya related to me from Malik from Sumayy, the mawla of Abu Bakr ibn Abd ar-Rahman, from Abu Hurayra that the Messenger of Allah, may Allah bless him and grant him peace, said, "If people knew what was in the adhan and the first row of the prayer and could only draw lots for it, they would draw lots. And if they knew what was in doing dhuhr early, they would race each other to it. And if they knew what was in Isha and subh they will go to them even if they had to crawl”
**********
Cyprus
Tsuru tsuru yayi ya rasa meke masa dadi, baice komai illa kallon kasa cikin nadama. Tunanin shi bai wuce yanda suka san inda yake ba bcs yayi covering tracks ɗinshi daidai gwargwado.
“Da Kai nakeyi, abinda kayi ka kyauta kenan?” IG ya faɗa. Daga Idonshi yayi suka haɗa da mahaifinsa amma saiya mayar kasa bcs kunyar kansa yakeyi.
“Nifa bawai nazo nace maka ka bini bane, kawai nazo naga lafianka ne. Tunda dai bakasan ka zauna damu, saboda mahaifiyarka ta samu natsuwa akan ba saceka akayi ba kuma ba mutuwa kayi ba.” Yana kaiwa nan saiya juya ya tafi.
Da sauri Khattab yaje gaban Daddyn sa yana rok’on sa hannu biyu, IG ko kallonsa baiyi ba ya ture shi tareda cigaba da tafiya.
“Dan Allah Daddy kayi hakuri, wallahi k’uruciya ne. Please karka kyale ni.... Im really sorry”
Sekeke IG ya kalli Khattab tareda kwafa, “Kuruciya koh? Ka raina kanka bani ba. Wannan tozarci dame yayi kama? Wai ace dan ɓata suna shi ne kayi gaba abinka saboda ka tozarta ni akan ban isa ba”
“Kaga duk bincike ɗinnan danakeyi Bawai saboda kai nayi ba, kaji ni da kyau saboda Matata nakeyi bcs dukta birkice kullum kuka. Mutane suka zauna babu yara balle ni don kace ka gaji dani”
IG yake magana muryanshi zallan ɓacin rai ke tashi, shi kuma Khattab yana ɗuk’e a kasa yana kuka tareda rike masa k’afa. Haka yayita rok’on sa Shi kuma IG yayita sababi yana mita, don kansa yayi shiru saboda Khattab yayi alkawarin binsa gida.
IG a gidan Khattab suka yada zango shida Boys ɗinsa, shi ya kwana a ɗakin Khattab while boys ɗinsa su biyu tareda Khattab suka kwana a falo.
Next day around 10am.......
Khattab ne a airport tareda mahaifinsa tareda escorts suna jiran lokacin tashin su saboda shi IG baya san garin at all.
Saidai Khattab ya kasa sukuni,tun jiya bai rutsa ba, tunani ɗaya ya sark’e masa zuciya. Gashi kuma Daddy dinsa bai sake masa fuska ba balle ya tambaye shi anything about her.
Kawai shiru yayi zuciyar sa yana masa kuna, fatan shi ɗaya ace tana sanshi har yanzu kamar yadda yake son ta.
Amma cikas ɗinshi ɗaya yayanta amma zai nema yanda zaiyi maganinshi. Haka yaketa tunani harya shiga jirgi suka ɗaga zuwa gida.
Jirgin su ya sauka a Murtala Muhammad Airport dake Lagos. Daga nan wani jirgin suka shiga direct sai Bauchin Yakubu. Suna fitowa daga jirgi motoci na tarbasu yana jiransu kuma harda Lili.
Tana ganin shi ta ruga da gudu tareda shigewa cikin jikinsa, babu kunyar idanu balle tsoron Allah.
“Yaya Khattab I miss you so much, please don’t ever leave me again” ta faɗa tana wani k’ank’ameshi. A hankali ya zame jikinsa tareda shiga mota ya barta a wajen.
Bata ko damuba illa binsa cikin motar, dayaga ta shiga ɓangaren baya inda yake wani haushi ya kamashi yana dana sanin abinda yasa bai shiga gaba ba.
Kara hawa kan kafadarsa tayi ta kwanta, harda bazai kulata ba sai kuma wani zuciya ya raya masa gwara ya kwaɓeta.
“Ke! Wai Meye haka? Baki lura tafiya nayi ba kuma duk na gaji”ya faɗa a hasalce. A hankali ta ɗago tana shagwaba kamar zatayi kuka “Haba yaya nayi missn ɗinka ne, baka san irin kukan danayi sanadiyar rashin ka ba”
Sai kuma ta fara matse karamin kwalla ta cigabada magana “Yaya ni na gaji Wallahi, kawai gwara ayi mana aure haka kowa ma huta”
Wani haushine ya turnuke shi, gyara zama yayi tareda ingijeta. “Ashe bakida hankali! Na dawo ko hutawa banyi ba, ko gida bankai ba kin kawo min shirme” kwafa yayi ya soma kallon window
“Yaya Maganar auren mu ne shirme? Ka daina so na ne?” ta watso mashi tambaya.
Juyawa yayi ya kalleta saiya watsar, bashida locacinta balle na cha chan baki da ita.
Sun isa cikin gidansu mutane cike sunzo ganin shi kuma duk yan uwa da abokan arziki ne, duk inda ya ratsa abu ɗaya suke tseguntawa.
“Laaa ga Khattab, ya canza kamar bashi ba” Baiko kula suba ya wuce falon Mommy ɗinsa, zaune take kuma gefenta Maman Lili ne.
Har kasa ya duka ya gaishe su, Mommy muryanta duk kuka ta amsa, ita kuma Maman Lili kallon rainin arziki tayi ta watsar tareda amsawa à wulakance. Inda sabo yaci ace ya saba da halinta bcs halinta Lili tayi biyo na empty vessel kyau babu hali.
Rike hannun mahaifiyarsa yayi yana murzawa a hankali, magana ya somayi cikin natsuwa. “Mommy ki yafe min, nasan cewa na sakaki cikin zulumi da fargaba”
Bata amsa shiba illa kukanta a hankali, haka ya rinka mata magana sai daga baya ta ɗago tayi murmushi tareda cewa, “Allah ya yafe mana baki daya”
Zuwa yayi sai yayi patting bayanta sannan yace, “bari naje na kimtsa” ko kallon Maman Lili baiyi ba ya wuce abinsa dama basa shiri.
Yana shiga ɗaki sai yaga Lili kwance tana jiransa, a fusace yace, “Ke Meye haka? Oya oya zo ki fita kafin raina ya baci”
“Ni ban san me nayi maka ba duk ka tsaneni” saita fashe da kuka.
Indawani ya yi kukan zaiyi wani iri amma yanzu kamar tana busa sarewa a kunnen bebe ne. Zuwa yayi wajen data ke ya finciketa kamar yar tsana har waje sannan ya banko kofar ɗakinsa.
“Damn!” ya faɗa tareda daura hannu akan waist yana tunanin irin rashin kamun kai nata. Ita kuma as expected ta tsaya tana buga kofar tareda watsa kalamai na rashin kunya.
Mommy ne tazo ta taka mata birki tareda Faɗi, “Meye haka kikeyi kamar wanda zamu kai turu? Gwara ki natsu kisan me kikeyi, shifa namiji yana son space ɗinshi baya son takura. Idan yace ki tafi ai saiki tafi tunda ba’a ma mutum dole. Ace ko 12hrs da dawowa baiyi ba kin soma tada mashi hankali. Nifa kada kisa yarona ya kara gudu”
Tana kaiwa nan saita bar Lili à wajen à ruɗe, shi kuma yana daga ɗaki yana jin su.
“Woooow! Allah ya barmin ke Mommy” ya faɗa saiya shiga bayi.
*******
Bayan 3 days....
Haka rayuwa ya cigaba da kasance ma Naufal da Fadeela cikin tsantsar so da kulawa. Koda yaushe ana tare ana hira, girki ko cin abinci.
Sam Sam yaki zuwa aiki yabarma Aminu komai, abu ɗaya ke fitar dashi daga cikin gidan watau sallah. Sai kuma sau ɗaya dayaje stores domin ya siyo masu kayan abinci da ba’a rasa ba.
Tun jiya Aminu ke kiran Naufal akan ana bukatarsa cikin office bcs su Mr Sutter sunyi zuwan bazata. Ranshi yayi mumunan baci bcs baya son abinda zai nisance shida da ita.
Tun da daddare yaketa mita, “Haba banda bakin ciki karara wannan dame yayi kama? Shikenan ba’a bari mutum ya zauna da matarsa lafiya”
Fadeela na daga kwance tana murmushin k’eta, sai kawai ya ganta. Daga gira yayi kafin yace, “Au you will not sympathise with me shine kike min dariya koh”
“No Other half ba haka baneba, I want to be with you but kasan cewa nima zani school”
Saita mike daga kwance tana kokarin tashi, “Bari naje na haɗa mana breakfast kafin ka makara”
Harta kai wajen kofa saita ji muryanshi “A me zaki”
“A me na saba zuwa? Motar haya mana” ta amsa bata ko juya ba.
Shiru yayi yana jin haushin kanshi akan duk abubuwan dayayi mata, bcs ya kaskantar da ita ba kadan ba. Dadin abin bata dauki duniya da zafi ba.
Ita kuma taje kitchen ta fara fere masu doya zatayi yam balls, tagama ta daura akan gas kenan sai kawai taji ya riketa ta baya. Bata ce komai ba shima haka kawai shiru sukayi for some minutes.
Itace tayi masa magana cikin raɗa “Other half”
Bai amsata ba illa kara kamkameta kamar wani zai kwace mashi ita.
“Other half please kasan zamu fita yau koh?”
“Na sani mana” Daga nan saiya saketa.
“Okay wat can I help you wit?” ya tambayeta
Murmushi tayi tareda jan masa kumatu cikin wasa saita ce, “Dont worry dear, na hutarshe ka”
Lagwaɓe kai yayi waishi bai yarda ba, da sauri ta rike masa hannu sannan ta matsa dab dashi har suna shakar numfashin juna.
“Bana son ka wahala ne, but If you insist dauko min sardine a cikin shelf. Daga nan saika fasa min kwai”
Ita kuma ta dauko kayan miya tayi jajjage saboda yafi tunda babu ruwa ko kadan. Haka suka rinka abinsu gwanin ban sha’awa.
Koda doyan ya nuna tare sukayi mulmula. Dama tun yau yake mata salon shagwaba kala kala, indai wannan ne ta saba da halinshi dis past few days Kuma yana burgeta ainun.
Latte ta haɗa mashi ita kuma ta haɗa ma kanta cappuccino. Zaune take akan kujera dab dashi tana bashi. Yaci sosai a matsayinshi na ma’abocin doya.
Daga nan daki sukaje ya shiga wanka ita tana wajen drawer ɗinshi zata ciro masa kaya. Blue suit ta dauko mashi tareda grey tie da kuma farin riga.
Bayan ya gama shiri ita tayi mashi knotting tie, to his surprise ta kuma iya sosai. Ta lura yana mamaki saita ce, “nike ma Daddy knotting idan zai fita”
Daga gira yayi alaman ya gane, ita ta rike masa jakarsa sannan tana makale dashi har suka kai kofar falo, bata rakashi mota ba saboda kayan jikinta bai kyautu maigadi ya ganta.
Yatsunta biyu ta saka akan bakinta sannan ta daura akan nasa. Da sauri ta koma cikin gida tana dariya bcs tasan me tayi. Shikuma cikin dariya yace “Zanyi maganin ki ai”
Saiya juya ya tafi, yana cikin tafiya yaji maganar ta, “eh din” juyawa yayi sai ya ganta a window tana murguɗa masa baki. Dariya yayi yana nuna mata yatsa saiya tafi bcs idan ya biye mata babu inda za shi.
Ita kuma ɗakinsa taje zata gyara, rigan daya cire ta dauka ta rungume, ji takeyi kamar shine ke wajen. Kawai ta rufe idonta tana shakar kamshin.
Tunawa tayi zata fita saita tashi da sauri ta gama aikinta, har lunch saida tayi kafin ta bar gidan.
Ta rufe kofa tareda faɗin
“Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah.”
tafe tana nishaɗi bcs she is in her perfect neighborhood, with her perfect husband, tanayin rayuwar data ke sha’awa.... Wat could possibly go wrong?
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 23 ✨✨✨
Abu Hurariah said; 'The Messenger of Allah said 'When it is Ramadan, the gates of Paradise are opened, the gates of Hell are closed, and the devils are chained up."' It was narrated by Ibn Ishaq from Az-Zuhri. (Sahih)
*******
Bayan wata haɗu....
Rayuwar Naufal da Fadeela ya kasance rayuwa ne mai ban sha’awa, kowane ma’auraci idan ya gansu saiya ji sun burgeshi.
Yanzu Fadeela takanje gidansu kuma Mommy na yabawa da yanayinta, kosu Anty Saudah sunji daɗin yanda suka daidaita kansu.
Gashi tayi bala’in murmurewa kuma tayi armashi, ko fatar jikinta abin kallone, ta kile abinta kuma dukwanda ya ganta will wish he was her and guys zasuyi wishing matarsu ne.
Daga kowane ɓangaren shi masu da albarka akeyi tareda fatan masu akan su samu zuri’a ɗayyiba.
Dama Fadeela ma’abociyar san yara ne, duk inda ta haɗu da yaro saita murmusa masa. Ko yaran Jawahir ana kawo mata daga safe har yamma.
Yanzu burinta ɗaya ta samu nata na kanta, wata huɗu da shiryawa da Naufal amma har yanzu babu labarin ciki.
Tun suna wata ɗaya ta kwallafa ranta akan batada juna biyu,dariya Naufal yakeyi sosai wata sa in har yana shakewa idan yaga tana mita akan abin.
Kullum tana cikin zulumi da fargaba bcs sau da dama wasu suna aure suke daukar ciki kamar yana jiransu bcs ko Jawahir abinda ya faru da ita ne amma banda Deela.
Da Naufal ya gaji da mitan ta gashi kuma wata hadu, suna kwance wajen sha ɗayan dare saita soma magana a hankali, “Other half”
“Uhmm” ya amsa mata saboda barci ya soma daukar sa.
Jijigashi ta farayi tana magana cikin shagwaba, “nika tashi Wallahi magana zamuyi”
A hankali ya buɗe emerald eyes ɗinshi ya sauke akanta yana mata wani kallo cike da so da kauna. Cizan leɓansa yayi wanda ya soma bushewa. Thou yasan labarin Gizo bai wuce na Koki ba.
“Baka ganin ya kamata muje asibiti kila something is wrong”
Murmushi yayi wanda ya bayyana masa hakorarsa, gyara kwanciya yayi saiya jawota jikinsa sosai. “Talk to me Baby, what’s ur problem?”
Shiru tayi batace komai ba tana wasa da yatsunta, “Duk kin dame kanki akan rashin haihuwa Wen I’m not even complaining. Bakya Jin daɗin zama dani ne?”
Da sauri ta ɗago ta kalleshi tana girgiza kai kamar zata yi kuka, “Ba abinda nike nufi ba kenan, kawai ina jin akwai wani matsala ne a raina”
Kallonta yakeyi yana tunanin irin wannan san yara data keyi, amma dole yayi reasoning da ita bcs halitta ne saboda haka take.
Tallabo mata gemu yayi sai yace, “Okay Baby, menene? Wat do you want?”
“Asibiti zamu”
“Asibiti dai zaki bcs ni babu inda zani”
“Okay fine, Nagode sosai. You’re the best husband anyone can have”
Daga nan suka soma hira thou Deela keyi, sai surutu kawai takeyi kamar ta haɗiye radio. Tana bashi labarin project supervisor ɗinta da rashin mutuncin dayake ma wasu but baya mata probably bcs tanada aure.
Shi banda “uhm” sai “uhm uhm” yake amsawa kuma Idonshi a rufe bcs duk ya gaji saboda sunje wani construction site ne.
Daga baya ya daina amsawa kawai sai numfashi taji kaɗan kaɗan alamun yana barci. Dariya tayi saita gyara mashi pillow sannan saita rufeshi dakyau da Duvet, itama ta kishingiɗa da kyau ta kwanta.
The next day.....
Zaune suke a motar Naufal zasu asibiti thou shi rakata zaiyi amma bazai shiga ba. Babu magiyan da batayi masa ba amma yayi kememe,
“Sorry Baby, kinsan zan iya ciro zuciya na in baki but I can’t grant you this wish”
Dole ta hakura ta kyaleshi tunda yace baya so kafin yazama masu jidali.
Ta shiga ciki tabi duk wani protocol daya kamata saura ganin Doctor, an kaita wajen Dr Hadiza Pate akan ta dubata.
Tana zaune cikin wani katafaren office na Doctor ɗin saboda tana wajen wani patients daya bukace attention ɗinta. Sallama Doctor ɗin tayi tareda shiga ciki.
A hankali Deela ta juyo ta kalli Doctor ɗin, Mace kyakyawa mai kyan halitta. Bayan sunyi gaisuwan mutunci sai Deela ta bayyana ma Doctor komai.
Dariya Doctor tayi tareda gyara zaman tabaran ta. “kiyi hakuri mana wasa suna kai shekara da shekaru kafin suzo test”
Deela batace komai illa jiran doctor ta gama surutan ta sannan ta fara duba ta. Murmushi tayi saita tashi ta fara dubata cikin kwarewa kuma tana mata tambayoyi.
Anan ta gane cewa Fadeela nada matsalar daukan ciki bcs tanada excessive menstrual pains. Nan take Fadeela ta ruɗe, Haba tasan a rina wai an sace zanin mahaukaciya.
Nan take ta ruɗe tareda barkewa da kuka, wayanta ta dauka ta kira Naufal amma bai dauka ba. Wani tashin hankalin ta shiga. Doctor tayita bata hakuri sannan tayi mata prescribing drugs kuma aka sakata a 3 months observation.
Daga ɗayan ɓangaren kuwa, ko sau ɗaya Khattab bai nema Miemie ba. Mahaifinsa ya samo masa aikine a wani ICT company inda yake aiki babu kama hannu yaro.
Bawai ya mance da Miemie bane, kawai baya so yaje ya tada mata hankali ne bcs yaji irin ciwon datayi akan rashinsa kuma yanzu ta samu sauki sosai.
Sau dama yana zuwa ta wajen School dinta amma nesa sosai. Ya lura da yadda tayi kyau sosai gashi ta zama budurwa. Gashi yaga tana walwala sosai, kawai tsoron kada yanzu ta daina sansa bcs It’s really a long time.
Ita kuma Miemie tana al’amuranta kamar every normal teenage girl. Sauki yazo mata sosai har ana tunanin kaita makaranta masu lafia.
Gameda Soyayyar ta da Khattab kuwa, yananan dirshan babu inda yaje. Akwai wani rana haka dataga kamar shi a gefen School dinsu but dayake tasan baya gari bata saka Mind dinta ba.
Kawai ta mayar da abin maybe ciwonta yake so ya tashi. Ita dai kullum idan tayi sallah rok’on Allah takeyi ya bayyana mata shi duk inda yake, idan kuma akwai alheri tsakanin Su Allah ya tabbata idan kuma babu Allah ya cire mata shi daga ranta.
Ita kuma Lili banda jaraba babu abinda ta saka a gaba, yanda takeyi wani idan ya ganta zai zata mijinta ne. Kullum matsala daban take complain about.
Kuma it’s mostly about girkinta da baya ci, tun yana mata kara tareda bata flimsy excuse har saida takai shi bango ya sauke mata komai.
Still bata hakura ba, kullum saita girka masa kwamachala wai kuma saiya ci. Wata sa’in har office take kai masa don rashin hankali.
Itafa irin matan nanne da basuda kintsi at all. Zata iyama saurayi komai, acewarta tunda zata aureka gwara ta fara sabawa da maka ɗawainiya tun kafin ta shiga.
Kuma gashi bata iya komai sai rawar kai, daka bari tayi maka abu gwara kayi da kanka bcs it’s useles. Ko wanke wanke tayi saika sake, balle shara kamar ta karo kurane a wajen.
Kuma kamar ta saka ma dakin Khattab ido, kullum sai taje ta tada mashi kura ta fice. Idan tanayi ko kallonta bayayi saidai yayi dariya a ranshi tareda faɗin, “Iska na wahalar da me kayan kara”
Tashi yayi ya tsala wanka tareda fesa kwalliya kamar sabon ango. Yau ya dau ma kansa alwashin komai zai faru saidai ya faru.
Yana tafe yana addu’a saboda baisan me zai biyu baya ba, daidai Office ɗin Naufal ya faka. Ya fito yana zulumi wani zuciya yana cemasa ya koma bcs he is not ready amma ya dake ya cigaba da tafiya.
Sanda ya kai Naufal yana conference hall amma aka umurceshi daya jira shi. Haka ya zauna duk fargaba yanata addu’a.
Cikin ikon Allah ya jira for less than an hour saiga Naufal yazo. Kallon kallo sukayi ma juna kowa da abinda ke ransa. A hankali Naufal yayi magana, “Me kake yi anan?”
Da sauri Khattab ya tashi tsaye sai yaje wajen Naufal ya rike masa riga, “Please ka bari mu fahimci juna”
“Mallam Meye haka? Sake ni mana” Naufal ya faɗa a hasalce kuma fuskarshi babu wasa.
“Dan Allah kayi hakuri ni bazan taɓa cutar Miemie ba, idan na cuceta kamar kaina nayi mawa bcs ita ce rayuwata”
“Cuta na nawa kuma? Ka saka ma yarinya Soyayyar ka sai kuma ta tafi ka barta you were no where to be found dukda kasan condition ɗinta”
Kallon mamaki Khattab yayi ma Naufal,ji yanda ya juya abin kamar bashi ya kore shi ba, kawai yanzu ba locacin daura ma wani laifi bane.
“Eh naji na dauki laifi kawai amincewarka nake nema” Shiru Naufal yayi kafin ya kalle Khattab cikin ido irin man to man yana nuni da hannunsa.
“Okay na yarda, but idan kayi wani abu na cutarwa akanta babu mai rabani da kai sai Allah” tun kafin ya karasa ya rungume sa yana murna.
Da sauri Naufal ya turesa sannan ya haɗe girar sama dana kasa, “Nace maka bana san ana rike ni koh!”
Sannu a hankali Naufal da Khattab suka tafi gidan gona, dukansu zulumi sukeyi bcs basu san yanda zatayi reacting ba.
Sanda suka isa falon babu kowa a ciki, Naufal ya shiga dakinta amma bai ganta ba. Sai ya wuce ɗakin Anty Saudah, kwance ya ganta tayi daidai tana kallon ceiling.
“Ke saka Hijab ki biyoni falo”
Yanda ya umurceta tayi, tana shiga cikin ciki sai tayi ido da Khattab wanda shi bai ganta ba bcs ya rufa ido kuma yayi Zurfi cikin tunani.
Ihu kawai ta kwala tareda rike kanta. “Yaya Khattab ka cuce ni, meyasa ka tafi ka barni” abinda taketa nanatawa kenan.
Da sauri Khattab yaje wajenta, “Haskena I’m really sorry. Gani na dawo kuma in shaAllah bazan sake tafiya ba. Please control yourself”
Hawaye ta rinka yi hannunta yana dafe da kanta, “Please control urself” yayita nanatawa.
A hankali ta rage sautin kukanta saita sake kanta, hannu tasa tana Share hawayenta. “ Ina so kayi min alkawarin bazaka sake guduna ba”
Murmushi yayi tareda cizon leɓensa, “Ni Da Ke mutuwa zata rabamu in sha Allah”
Shiru sukayi babu wanda yace komai, shine yace “okay Haskena smile for me Ko zan samu sauki cikin raina”
Nan ta somayi saiga Naufal ya fito, “Oya zo ka tafi ya isa haka, remember yarinya ce so akwai abubuwa da dama da bazan lamunta ba. Misali zance ko taɗi.... Koma me ake kiran abun, banaso kuma baza ayi ba.”
“kawai zaka shigo har falo ne ku gaisa sannan ka kara gaba”
Murmushi Khattab yayi sannan yace shima nagode sosai Allah ya saka da alheri.
Daga nan sukayi sallama da Miemie duk suka bar gidan, Khattab na murnar samun Haskensa sannan Naufal na ɗokin zuwa wajen nasa Hasken tauraruwan mata.
#NiDaDiyata
0 comments:
Post a Comment