Haka rayuwar Khattab da Miemie ya kasance, kusan kullum sai yazo yaga Miemie amma a falon su. Idan ta shiga motarsa to Naufal ne da kansa ya kira shi akan ya taimaka masa wajen daukanta daga School bcs bazai samu time ba.
A duniya Khattab yana san irin wannan locacin bcs yana samun daman zance sosai, ya kan biya da ita wajen su Vanilla joints haka da sauran su, ya siyo mata su shawarma da sauran kayan lashe lashe. Shake da Leda take komawa gida idan yazo.
Tsalla soyayya sukeyi mai tsafta, saidai shi kullum zulumin ya zaiyi da maganar auren shi da Lili yakeyi. Bcs an riga an kai baikonsu tun kafin ya gudu.
Yanzu abinta sai girma yakeyi bcs yanzu kayan aure take siya, bata da aiki sai Online shopping gashi kuma ta shiga whatsapp groups na business ɗin kayan aure bila adadin.
Haka take saving hoto ta ajiye mashi idan ya dawo saita rinka nuna masa. “Yaya wannan colour ɗin yayi? Wanne yafi tsakanin wa’annan” haka take damunsa da tambayoyi.
“kiyi abinda kike so” abinda yake amsa mata dashi kenan kuma bazai kara ce mata kala ba. Wata rana tayi zuciya ta tafi wata rana kuma ta zauna tayita tambaryasa a haka dukda baya amsawa.
Shikuma abinda yasa baya amsawa bcs bashi zai zauna da ita ba saidai ya sake guduwa, kuma koda ta aureshi saidai gangar jikinsa amma ba ruhinsa ba yasa gudun ba’a cigaba ba gwara ba’a soma ba.
On the other hand Lili kallonsa kawai takeyi, ana nan ana mata haɗin mata gangariya yar Maiduguri. Duk abinda Khattab ke mata tana ankare dashi, auren nan dole ayishi koda yana suma ne, jira kawai takeyi ya santa a matsayin ‘ya mace sannan maganin ta yana aiki.
Idan yayi mata wani abu dariya takeyi a ranta saita ce, “zaka shigo hannu ne, bakasan halina bane” Ni kuma Dimples nace hali na Wanne kuma?
*******
Fadeela tana shan maganinta daidai yanda akayi mata prescribing, gashi idan ta fara shagwaɓan ta na fama tana kuka, Naufal yana gefenta yana petting ɗinta.
At all Baya San yaga hawayenta, duk randa taje school taga yaran samɗa saita mashi jidali, gashi Hadiza matar sadeeq haihuwa yau ko gobe.
Shiyana tunanin hanata zuwa makaranta bcs zuwanta baya kara masa komai sai tashin hankali. Sannu a hankali harta kai 2 months tana shan magani.
Kawai saita tsira shan fanta mai kankara, Itafa ba ma’abociyar shan abin bane, tafi san Coke but kawai saita fara marmarin shan Fanta kuma shima fanta ɗin saiya fara kankara ko alamar haka.
Wata rana idan zata dawo daga School take siyo abinta, wata rana kuma Other half ɗinta zai siyan mata. Haka tayi stuffing ɗinsu a cikin fridge abinta, daganan sai kwaɗayin ya girma.
Daga fanta ta kara da agwaluma da gasharshen masara, Naufal tun baya complain har ya soma yi bcs shike siyowa saboda ta daina zuwa makaranta bcs sunyi exams, rana daya ko biyu take zuwa wajen supervisor dinta.
Abin ya fara damunsa sosai, bata da lalaci bcs tana duk wani aiki daya kamata mata but saidai ta sauya masu yanayin girkinsu. Kwata kwata bata san warin stew so batayi.
Saidai kullum sai sunci tuwo miyan kuka bcs shine yanzu best food ɗinta. Gashi tayi dundumemiya abaya kawai ke shigan ta sai kuma kimono tunda duk kayanta fitted ne. Ita dai kawai ta lura tayi ɓatan wata ne amma bata gaya ma kowa ba har Naufal.
Wata rana taje school suna zaune a garden chairs dasu samɗa da Mansura, kallonta sukeyi cikin tuhuma. Bata ko kallesu ba bcs kananan tsegumi ne bata so. Saiga mai masara dafaffe tazo wucewa.
“mai masara! Kawo mana, ina tsammani akwai canji cikin jakana”
Fadeela ta faɗa tana duba jakarta. Samɗa ne ta jungure Mansura tana mata kyas da ido alaman su kalle Deela.
“Gulma ajali !” Fadeela ta faɗa bata kallesu ba. Mansura ta gyara zama saita dafata sannan tace, “Baki lura kin fiye kiba bane halan? Gashi sai cin tsiya. Idan bakiyi hankali ba sai Naufal ya sake aure”
Dariya Fadeela tayi sosai kafin ta ce, “ wai wani Naufal ɗin? Badai nawa ba bcs baki lura yanda muke soyayya bane”
“Mun lura mana gashi ya bayyana a jikin ki” Samɗa ta chapke. Sekeke Fadeela ta kallesu sannan ta juya kai. Da sauri Mansura ta zaga ta duka gabanta, “Bakya jin wani motsi a cikin ki?”
“Banaji Rabu dani”
“Amma kina amai da ganin jiri?”
“ka nace maki babu abinda ke damuna, ah ahn kyaleni mana”
“Mansura tace lafianta lau ki kyaleta mana” Samɗa ta faɗa.
“Malama babu ruwanki, kana ganin Fadeela kasan akwai wani abu cikin jikinta, ga shegen kwaɗayi yanzu bata wuce tayi kwata kwata”
Shiru Fadeela tayi for some minutes Sai ta soma magana kasa kasa “Nima abin ya fara isana, gashi rabon danaga period dina tun kafin na fara shan magani”
“Oya bani kudina” Mansura ta faɗa ma Samɗa tareda mika mata hannu. Sai kawai Samɗa ta zuge cikin jakarta ta fito da 500 naira guda 4 ta bama Mansura.
Itadai Deela bata gane me sukeyi ba, sai bayan sun natsa Mansura ta soma magana, “Dama nace ma Samɗa ciki gareki shine tace wai baki gaman shan maganin kiba. Kawai wai kiba ne bcs kinajin daɗin aure”
“Shine nace idan cikine zata bani dubu biyu idan kuma ba shi bane zan bata dubu biyar”
Dariya suka kwashe dashi su duka suna shewa harda shan hannu, “Kunada kudin banza shine bazaku bani na kara na cin masara ba da fanta” Deela tace.
“Karki damu muje na siyo maki da kuɗin nan” Mansura tace.
“Amma fah kina wuta ” Samɗa ta faɗa tareda zungurinta.
“Toh dafa! Nina wasa ne” Deela ta faɗa tana ɗaga kafaɗa.
Haka suka gama hirar suka tashi kowa ya kama hanyar gidansu, yau Deela tayi alkawarin fada ma Other half ɗinta good news.
Gyara gidanta tayi tas ta bishi da turaren wuta dasu room freshener. Rissotto ta kirka wanda yasha Ugwu da albasa mai lawashi. Sai tayi ginger drink mai garlic a ciki.
Tayi setting table gwanin ban sha’awa bcs wasu sabbin coolers peach ta dauko yau. Upstairs ta wuce domin tayi wanka saboda tasan zashi gidansu kafin ya dawo.
Ta lura tunda Miemie tayi saurayi bashida katabus kullum saiya je shi a dole yaya babba.
Leggings ta saka baki sai crop top wanda bayan duk an yanka, jiran sa takeyi à falo dukta kagu ta faɗa masa sun kusan zama parents.
8:15pm.....
Locacin na ya dawo daga gidansu, sallama yayi sai ya ganta kwance akan couch tana jiransa. Ga kuma kamshin abinci da turare ta Ko’ina.
Murmushi suke sakar ma juna harya isa wajenta. Shafa mata kai yayi yana kashe mata ido. A hankali yace “How is my baby dis evening?”
“we are fine”
Kallonta yayi bai gane ba, “Me kike nufi da ‘We’?”
Dariya tayi saita daura hannunsa akan cikinta tana murmushi, nan take ya ɗago abinda take nufi. Da sauri ya rungume ta don murna. Ita kuma sai dariya takeyi. A hankali ya soma magana, “koba komai na huta da kukan dare”
Dukan wasa takai masa sai ta ce, “Dawa kake yi?”
“Nifa bance dake nakeyi ba Malama”
“Gwara dai” saita kara makale shi. Daga nan kuma ta raka shi yayi wanka tareda shiryawa kana sukaje wajen cin abinci. Yaji daɗi sosai daba tuwo miyan kuka bane bcs ya tsane abincin amma bazai iya magana ba.
Yanzu yasan ba laifin ta bane, cikin ne yake mata haka.
Saidai fatanshi Allah ya rabasu lafia kawai kowa ma ya huta.
3 days later...
Wajen karfe goma na safe ya shirya zashi office, panke tayi mashi wanda yasha ayaba. Saita yi masu oats suka haɗa dashi saida bata saka madara a nata ba.
Sun gamaci saita rike mashi brief case ɗinshi sannan hular sa duk yana hannunta. As usual kofa ta tsaya saboda kayan jikinta. A hankali ta daura masa hulan a kanshi saita kara gyara masa button ɗin dabai gama makala wa ba.
Ta juyo zata koma saiya jawota ya kaima bakinta kiss, da sauri tayi kokarin tureshi amma yafi karfinta, don kanshi ya kyaleta yana ɗaga mata gira. “Idan Kinsan bazaki min proper bankwana ba ki daina raka ni”
Dariya tayi kafin tace, “NI banason mai gadi ya ganni Wallahi” juyawa yayi ya kalle inda maigadi yake amma baya wajen, “Kwantar da hankalinki duba baima wajen”
“Okay” tace saita kara jawoshi sannan ta manna mashi wani, ya shagala kenan ta sake shi sannan ta rufe kofa karab. Dariyar ta kawai yakeji bcs tasan ta nema tsokana.
“Ai zan dawo nayi maganin rashin kunyar ki”
“Eh din ai bana tsoro” ta faɗa ta window.
“Zakiyi bayani ne yarinya”
Saiya tafi motarsa, yana tafe yana tunanin yanda san matarsa yayi tasiri cikin jikinsa, ashe dama haka aure keda dadi idan kanada right spouse.
Yanke shawara yayi gwara yaje ya fara siyan kayan yara kafin ya wuce Office, Mumtaza Stores ya tsaya bcs akwai girma sosai, ya shiga ya siyo kayan yara kala kala daga na maza da mata duk ya haɗa, saida ya siya san ranshi kafin ya biya kudi ya tafi.
Ya gama sakawa a boot yana zaune cikin motarsa, tunanin Fadeela yakeyi da sabon rayuwar da zasu gina. Dayake baiyi winning glass ɗin motarsa ba, yana jin hayaniyan jama’a.
Wata ya gani tana tafiya da sauri sauri ta fito daga store ɗin kuma wani namiji yana mata magana amma bata kulashi ba.
Sanye take da riga pink iya cinya da wando jens wanda aka yayyanka sai tayi daurin turban. Jakarta na bouquin Blue yana gefen hagunta. Tazo inda Naufal yake zata shiga motarta.
“Haba Yasmeenah, ji ina maki magana kin wani Share ni” a fusace ta juyo ta yi magana cikin harshen Hausa wanda kafin nan bazaka zata ta iya ba saboda ma yanayin shigarta da siffanta.
“sai me dan kasan sunana?”
“Haba Yasmeenah Nifa dan uwanki ne amma kike wulakanta ni for no reason” Guy ɗin ya faɗa. Harara ta watsa mashi sannan ta zura hannu cikin jakarta ta fito da mukullin mota.
Shi Naufal yana daga cikin mota yana jin su bai fito ba. Ita kuma Yasmeenah ta buɗe motarta zata shiga ciki sai guy ɗin ya jawota waje, “Haba Meenah” bai karasa ba ta sharara mashi kyakkyawan mari.
“are you stupid Yaya Huzaifah? How dare you ka saka kazamin hannunka a jikina? Rainin harya kai haka eyee?
Tana masifa jikinta yana ɓari.
Shikuma Huzaifah idonsa yayi ja sosai saboda bacin rai, “Dan ubanki ni kika mara koh? Don kin samu ina kallon ki har zaki raina ni haka?”
“An mareka Yaya Huzaifah ko bari nace Huzaifah..... Kayi abinda zakayi. Kuma ka sake saka filthy hands ɗinka a jikina saina kara maka” Ta fada tana zare masa ido tareda taunar chewing gum.
Gadan gadan Huzaifah ya nufota saita saka hannu kerere akan kugun ta tana jiransa babu tsoro a tareda ita.
Da sauri Naufal ya fito bcs yaki suke shirin yi. “ya isa mana” ya faɗa tareda janye Huzaifah.
“ Karyan iskanci yakeyi, aida ka kyaleshi na koya mashi hankali tunda yana jin kanshi kamar jaki” ta faɗa tana jijiga.
“Ba Kinga an shiga tsakanin muba ai dole kiyi kumfan baki. Banza asarrariya” Huzaifah yace sai ya nufa hanyar motarsa.
“eh ɗin, soko kawai” ta mayar masa. Ikon Allah Naufal ya tsaya gani bcs gaba ɗayansu basuda tarbiya.
Karar wayarsa yaji saiya bar wajen yaje motarsa, ita kuma nan ta bisa da kallo tana yaba kyansa da kuma kamalan sa. “woow dis Guy is so marriage material ta faɗa a ranta”
Shikuma kamar yadda ya saba idan ya dauki business phone ɗinsa saiya faɗi sunar sa, “Hello ! Naufal Hussain Beli speaking, how may I help you”
Anan Yasmeenah taji sunar shi, murmushi ta somayi saita gyara tsayuwanta tana yauki. Bayan Naufal ya gama wayanshi baima koma inda take ba saiya ce “Sai anjima Allah ya kiyaye na gaba”
Nan take ya shiga motarsa ya fice, cizon yatsa Meenah ta soma yi bcs taso ta karba number ɗinsa amma ya tafi. But ta dauki Alwashin saita binciko shi duk inda yaje tunda tayi mai Wuyan tasan sunar shi.
Wayanta ya soma ringing, kawarta Laila ke kiranta a waya. Da fara’arta ta dauka sai tace, “Sorry my dear gani nan zuwa, I just met Mr right. Nanda 3 months Idan banyi aure ba zan baki dubu hamsin”
“Yayi daidai aminiya ta, faran mace hasken tsakar gida. Kura mai kallabin kitse, karya gwafa shahon karfe, Mace daya tamkar dubu, dukan matan duniya a bayanki suke.....” laila tace
Dariya Yasmeenah tayi bcs idan ta kyale Laila zasu kwana ana kirari.
“okay naji tawan, thanks but Ina so daga yau ki rinka kirana Mrs Naufal Hussain saboda tunda na ganshi to fah saina mallake shi”
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 25 ✨✨✨
Ibn 'Abbas said, "If any Muslim obeys Allah regarding his parents, Allah will open two gates of the Garden for him. If there is only one parent, then one gate will be . If one of them is angry, then Allah will not be pleased with him until that parent is pleased with him." He was asked, "Even if they wrong him?" "Even if they wrong him" he replied.
**********
Haka Yasmeenah ta tada motarta tana tafe tana kewar Naufal, tunaninsa ya saukar mata cikin rai. Komai akanshi ya burgeta daga siffansa har shigan sa.
Gashi yanda yake magana cikin kamala lafuza yariyari. Murmushi takeyi kawai tama rasa ta inda zata fara, abinda kawai ta sani koma waye shi saita aureshi.
Haka tayita tunani harta kai gidansu Lubna inda zasu haɗu harda Laila. Daga nan suka soma hirarakin su na yau da kullum.
Shikuma Naufal yana isa office ya rufe kofa ya hau kiran Fadeela, ita harta soya kifi Catfish ta barbaɗa mashi yaji ta hauci. Daga ita sai vest da Under wear tayi daidai ta zauna a kasa tana ci.
Kallo takeyi wani American film 'live by Night' a laptop ɗinta wanda Ben Aflek da kuma Zoey Salderna. Ta shafa'a tana kallo sai wayanta yayi kara. Da fara'arta ta kara a kunne sai ta soma magana tana kashe murya.
"My other half inata kewar ka"
"Nima kewarki nakeyi yasa nace bari na duba ki, yanzu dai ya kuke?"
Dariya tayi saita shafa cikinta sannan tace, "Lafian mu kalau, har mun soya kifi muna girba"
Murmushi yayi ta ɓangaren sa yana cizon laɓe kamar mai shirin barci kana ya lumshe idanu. A haka suka cigaba da hira hankali kwance suna watsa ma juna kalamai masu rikitarwa har wajen minti arba'in da rabi kafin sukayi sallama.
Yanzu tunda yayi magana da babyn sa hankalinsa ya dawo jikinsa, bakin aiki ya koma gadan gadan dama yanada zanen da zaiyi na wani plaza haka.
Ita kuma tana gama cin kifi saita sha kankaran fanta sannan taji daidai. Tashi tayi tsam ta soma aikin gida, kafin awa biyu da rabi harta gama duk wani aikace aikace ɗinta tanayi tana hutawa.
Su kuma su Abba tunda sukaji Fadeela na dauke da juna biyu suka rinka jindadi, wani idan yaga yanda suke murna zaka zata ba'a taɓa jika cikin gidan ba.
Mama da kanta tasa aka tsinko kuka sannan aka busar tareda dakawa Fadeela, kuma ta haɗa dasu kayan yaji da kuma na kamshi. Harda su Na'a Na'a duk ta haɗa mata.
Itama Anty Saudah kullum tana cikin mata aiken abinda ba'a rasa kuma Miemie ke zuwa wata rana da driver wata rana kuma da Khattab.
Idan taje bata bari Anty Yar gayu tayi aikin komai, wala tayi ita kadai kokuma Deela ta rinka nuna mata. Wata sa'in har mamakin yanda suke mata takeyi, kuma gashi dai dangin mijinta. Kawai tana rayawa wannan shi ne fa'idar hakuri.
Daga wajen yan uwanta kuwa kullum Mommy nasiha take mata akan tsabta, saboda wasu matan suna daukar ciki zasu tara shargi har sai sun haihu. Kuma idan akaci abu sai dai idan miji ya gaji da wari ya kawar.
Kullum tana cikin mata nasiha akan hakkin aure, kamarsu girki, tsabta, kwanciyar da sauran su. Daidai gwargwado kuma ta dauki abinda ake faɗa mata.
Bayan mako ɗaya.........
Yasmeenah tana kwance ɗaki tayi daidai kaman ɗakin mijinta. Sanye take da wani gajeren riga iya cinya kuma bata haɗa shi da komai ba.
Kafa a harɗe tana amfani da IPad ɗinta sannan tana shan wakar Falz the Bad Guy Mai taken Bad Baddo Baddest.
Tana bin wakar tana rausaya kanta cikin rangaji, tunanin Naufal ya faɗo mata. Duk wani hanya da zata bi ta neme shi tayi amma bata samu ba.
Abin yana daure mata kai sosai saboda farad ɗaya babu shi babu dalilinsa. Kawai wani tunani ya faɗo mata ta nemeshi ta Facebook.
Nantake tayi downloading abun dalilin bata taɓa yiba saboda baya burgeta, saidai taji su Laila suna magana akan abun wai kusan kowa nayi.
Naufal Hussain ta soma rubutawa sai gashi masu irin sunar sunfi ɗari, shiru tayi tana tunaninta inda zata fara. Dabara ya faɗo mata akan ta kara Beli a cikin sunar, kaddara ta riga fata saiga shi ya fito shi kaɗai.
Da sauri ta gyara zama saboda ruɗewa, hotansa ne akai yana murmushi ga idanun nan kore dasu gwanin ban sha'awa.
Bincike ta farayi ciki harta gano inda yake aiki, tasan wajen saboda sun shahara wajen zana gidaje.
Kallon agogon bango tayi saita ga karfe sha ɗaya da rabi. Da sauri ta tashi tayi wanka, wani jumpsuit mai kalar hoda ɗin Ellie Saab ta saka saita ɗaura blazer mai kalar karfe.
Purple jan baki ta damp'ara saita zane girarta kamar fuka fukai zasu tashi, tamke gashinta tayi baya sai wani yayi jela ta gaba.
Ita yau tafa dauki alwashin saita gyarota da Naufal, zungureriyan takalmi inchi shida ta kwama mai rufewa. Tana tafe tana kwas kwas da kafa sai layi takeyi kamar zata faɗi.
"Mommy saina dawo" ta faɗa ma Hajia Hindu mahaifiyar Huzaifah.
"okay baby Sai kin dawo" ta amsa mata. Su dama haka suke rayuwarsu cikin gidan, kwata kwata babu tarbiya kuma duk me kayi ba'a tsawata maka.
Tana cikin tafiya wajen motarta saiga Hilal mai binma Huzaifa ya fito daga motarsa.
Dama yafi kowa rashin ji cikin gidan, sune ake cema sheɗanun mutane. Kallon Yasmeenah yayi yana lashe baki saboda wankarta yakai mashi karo.
"kanwata sai ina da wannan wankar?" ya faɗa yana lashe baki tareda shafa gemu duk alamun yan iska. Zuwa yayi ya tsaya dab da ita saiya soma magana kasa kasa. Yanayi yana numfashi a jikinta, duk ta tsorata amma saita dake.
"kinsan halina amma kike wannan shigar? Kar kiga tun kina yawo da pant kike gidan nan, wallahi zan mance ne nayi maki abinda naga dama" ya faɗi saiya shafa kumatun ta ya wuce.
Batace komai ba saboda ba Huzaifah bane mai saukin kai da sunyi cha chan baki. Wannan kanshi na motsawa, yanzu yanzu zai iya rabata da mutuncinta na 'ya mace a cikin parking lot dinnan.
Ya daɗe da shiga cikin gida kafin ta dawo daidai, ɗabiun yaran gidan yana cikin dalilin data keso tayi aure ta bar musu gidansu tun kafin su far mata, dama sun saba amma basa samun nasara.
Gashi maza har biyar ita kadai ce mace sai Mommy, gwara tun wuri tasan nayi saboda Mommy bata tsawata ma yaro at all.
Shiga tayi ta soma tuki, dabara take nema na yanda zata ma Naufal magana. Kawai saita yanke shawara taje kai tsaye wajen daga nan tayi yauki da sauran dabarun mata harta cimma burinta.
Shikuma Hilal ya shiga cikin ɗaki zai kunna sigarinsa amma baiga abun kyastawa ba, yana kyautata zaton ya barshi cikin motarsa yanzu. Kiwiyan komawa yaji saiya ce bari ya shiga ɗakin Haisam kaninsa wanda yake kusa da nasa ɗakin.
Yana tura kofa ya shiga ciki sai Haisam da Huzaifah suka fara kokarin ɓoye Wiwi da suke busa. Dariya Hilal yayi sai yace "Matsorata kawai"
"Tsoron me? Kana ganin Mommy ta fara biye ma zigin kawayenta wai bamu jin magana, shine waccan satin Ina bakin varenda ina busa sigari sai kwastam wai karna kara sha a cikin gidanta" Huzaifah ya faɗa duk ranshi a bace, daga nan saiya zuka Wiwi ya hura ta hanci da baki cikin kwarewa.
"Dama nazo na ara lighter ne amma tunda kuma sana'a kukeyi bari na zauna muyi tare" Hilal ya faɗa yana kanne ido.
Haisam ne ya tashi ya saka sakata a kofa, yana juyawa suka kwashe da dariya su uku. Sai Hilal ya fito da hodar iblis.
Tsaki Huzaifah yayi sai yace, "Dalla Meye haka? Sai ka rinka bata kudinka akan wannan abu"
"Mallam ina ruwanka? Kudinka ko nawa? Baka san daɗin abinnan bane saboda idan ka fara baka iya denawa. Ko gidan ka zaka iya sayarwa akan ka siye shi" ya amsa mashi.
"Nidai bazan iya cire kudina in siya wannan yar hodar ba, gwara nayi ta amfani da Wiwi cikin sauki" Haisam yace.
"Shine ai Danuwa" Huzaifah ya amsa yana dariya saiya mika ma Haisam hannu suka sha.
"Ku kuka sani, ni dai yanzu na fara" Hilal ya faɗa tareda buɗe hodar sa. A kasa ya barbaɗa kan tiles ya soma sinsina yanayi yana jan numfashi da karfin tsiya ga idansa jazur.
Saida yayi wajen sau uku sannan ya kishingida yana hutawa kamar wanda yayi aikin karfi. Sai ya soma jero magana mara kan gado.
"Yanzu naga Babe ɗinnan, sa'a taci yau juma'a kuma bana iskanci ranar danayi maganinta"
"wace yarinya?" Haisam yace
"Wanda ta mare Huzaifah mana" saiya faɗa yana babbaka dariya, ihu ya kwarara kafin ya cigaba da magana, "Ba'a haife macen da zata mareni ba, idan na fara dukanta kamar Allah ya aikeni in kasheta"
Daga nan saiya sake ɗukawa ya sinsina hodarsa sau ɗaya kana ya dago kuma akwai wani a hancinsa amma bai goge ba.
"Wallahi gaskiya ake faɗi kafi hankali cikin mu, saboda yanda bakayi mata komai ba" Hilal ya faɗa.
"Ai da nine ta mara wallahi ɗakinta zanje nayi yanda nakeso a jikinta, gobe bazata sake" Haisam ya faɗa.
"Allah yayi maka albarka, nima abinda na faɗa kenan... Amma wancan ya tsaya kamar wani soko" Hilal ya chapke.
Saidai Huzaifah baice komai ba yanata busar Wiwi, Saida ya gama kana ya dauko Shisha ya fara dashi, ahankali ya soma magana, "Gwara ku daina tunanin ta saboda Daddy yace zan aureta"
Ciza yatsa Hilal yayi saboda baiso daya ji labarin ba, dama cikin yan kwanakin nan yakeso ya far mata tareda gwangwaje wa a jikinta saboda indai haduwa ne to tayi.
Dariya Huzaifah yayi yana nuna Hilal kana ya soma magana, "Musamman kai nasan ka iya maita tun wuri nayi maka iyaka da matana"
Sosa k'eya yayi saiya manne tafin hannunsa biyu kana yace, "It's all good, ba matsala na kyaleta. Amma ba haka rai yaso ba, gaskiya anfi sanka à gidan nan"
Haisam ne yace, "toh amma babu tastin?" ya kalle su yana warware idanu. Pillow guda biyu Huzaifah ya wurga mashi suna dariya.
Yasmeenah ta isa wajen aikinsu Naufal ta rasa me zatayi, babban gini ne mai bene da yawa kuma akwai office daban daban. Ta fito daga motarta ta rufe harta soma tafiya ɗaya ɗaya cikin kasaita.
Naufal ta gani yazo wucewa shi baima lura da ita ba, da sauri ta tsayar dashi. "Hello! Baka gane ni bane?"
Saida ya ware ido da kyau kana ya tuna, baiyi murmushi ba kawai ya soma magana. "Ohh! Allah sarki! Sannu"
Murmushi tayi saita taka taje gabansa, "Ina wuni ina gajiya?"
"lafia" ya amsa.
"OMG! Locacin lunch yayi Muje na siyan maka mana saboda na biya taimakon daka min."
"Karki damu dan Allah nayi badan komai ba"
"Noo ni ban yarda ba, I insist please. Karka yi turning ɗina down mana. Just lunch ne Fah" ta faɗa tana kanne ido.
Haka kawai ya hakura yace suje.
Ita kuma Fadeela tayi tuwon shinkafa da miyan egusi wanda yasha ganda da busharshen kifi. Wani mai masu wanki ta kira kana ta bashi dari biyar akan ya kaima Naufal abinci office.
Yana zuwa baiga Naufal ba haka ya maida abincin gida, sai ta gwada wayarsa amma ringing sau uku bai ɗauka ba. Shiru tayi tana tunanin inda yaje, kiran wayar Miemie tayi kuma akace mata baya wajen.
Abinda yake daure mata kai shi ne yau yanada aiki da ko fita daga office bazai iya ba shine tace bari tayi surprising ɗinsa da abinci gashi kuma babu shi babu dalilin sa, wani zuciya ya raya mata kila ya fita da Aminu ne, tabbas taba kanta amsa.
Su Yasmeenah an samu abin so, rufe motarta tayi ta shiga motar Naufal wani Benz yar yayi GLK 350. Sai yauki take masa suna tafiya, shi haushin sa ɗaya abu yazo dauka motarsa gashi wayarsa yana office.
Sun isa Larema zasu ci abinci, shi shinkafa yace akawo mashi duk ya kagu ya bar wajen, ita kuma sai zuba turanci takeyi tana salo. Daga karshe saita ce akawo mata chips da kebab.
Har waiter ɗin ta tafi sai Yasmeenah ta kirawo ta " I like my chips the way I like my men, hot and brown" saita kanne mashi ido.
Wayancewa yayi ya kawar da fuska. Bayan an kawo masu abinci suka ci sukayi nat, Naufal ya tashi ya biya sai Yasmeenah ta fara kukan shagwaba wai ita zata biya gashi yayi mata wayo.
Hakuri ya soma bata amma ta kafe sai buga takalmi takeyi a kasa, ji kakeyi kwas kwas tana taramasa jama'a. Daga nan tace saidai wata rana su sake zuwa ta biya. Dole ya yarda, daga nan juya mashi bayanta ta tafi hanyar mota cikin salon rausaya.
Sun koma office ɗinsa saita ce "Yanzu yaushe zan kara ganinka"
"Yaushe kike so?"
"ko anjima bai dameni ba"
"No saidai within the week"
"Toh babu damuwa, Im Yasmeenah by the way"
Daga nan su kayi exchanging number kana kowa ya tafi, da sauri ya shiga domin yaga wayarsa. Missed call ɗin Fadeela ya gani dama yana kyautata zaton haka.
Da sauri ya bar office yayi hanyar gida, yana isa Fadeela ya gani kwance a kan 3 seater sanye da A shaped atampha ɗinkin gown.
A hankali ya tadata saboda barci ya soma dibanta. Murmushi tayi saita ja masa kumatu, "Baby harka dawo?"
"Eh nayi missing ɗinki yasa na dawo da wuri"
Murmushi tayi tana kokarin tashi, "Muje kaci abinci"
"Sorry baby Yanzu Aminu ya Kaimu muka ci shinkafa"
"Ni gaskiya zan kira Aminu na bashi warning ya daina kai mun miji yawon cin abinci, toh yanzu ya zanyi da wanda na dafa?"
"Baby sai muci anjima bazai baci ba"
Murguda baki tayi ranta baiso ba, suna makale da juna suna tafe zasu ɗaki sai tace "Other half akwai abinda ya faru yau ne?"
Gabansa faduwa yayi, miyan bakinsa ya bushe, da kyar ya saita kansa kafin yace , " Babu abinda ya faru, kinsan bazan ɓoye maki komai ba"
"Other half na sani mana, dama kawai jikina yana min wani iri ne"
"Karki damu Baby babu abinda ya faru kuma babu abinda zai faru. Jira yakeyi sukai daki domin yayi deleting number ɗin Yasmeenah da komai daya jibance ta.
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 26 ✨✨✨
Narrated Ibn 'Umar, The Messenger of Allah (pbuh) found 'Umar al-Khattab in a caravan while he was swearing by his father. So he said: Allah forbids you to swear by forefathers. If anyone swears, he must swear by Allah or keep silence.
**********
Same day wajen 9:45pm.......
Su Fadeela suna zaune a falo suna kallon 9 O clock news na NTA, shi ya zauna akan 3 seater ita kuma ta kwanta akan cinyarsa anayi ana hira.
Saiga wayarsa ya fara ruri alamun an kirashi, da sauri ya saka silent saboda ya gane wanda ya kirashi. Ita Fadeela bata ma lura da abinda yake ciki ba, duk hankalin ta yana wajen TV dake aikinsa.
Haka wayar ya cigaba da kara a karo na biyu shima ya kuma sakawa a silent, a hankali ya zame kan Fadeela dake jikinsa ya Mike tsaye.
“Baby bari inje bayi na dawo” Ya faɗa kana ya soma tafiya. Hanyan upstairs ya nufa zuciyarshi yana duka saboda bashida gaskiya.
“Ah ahn Other half baga bayi a kasa ba saika je wani upstairs” Ta mashi magana yayin dayake tafiya.
Cak ya tsaya tareda juyawa rai baiso ba, bakinsa yana rawa ya soma magana, “Kanin wanka fa zanyi”
“Ohhh kace babban Harka ne, gwara kaje chan kafin naji wari”
Murmushi yayi saiya juya ya tafi, yana tafe yana rarrabe ido alamun rashin gaskiya. Yana isa ɗaki saiga wayar Yasmeenah ya sake shigowa.
Da zumuɗi ya dauka tareda karawa a kunnen sa, “Hello!”
Ita kuma gyara kwanciya tayi saita makale murya chan kasa, “Hi Mine, ya kake?” shiru yayi dayaji tace mashi mine amma saiya basar ya cigaba da magana.
“Lafia lau, kefa?” “Ni gaskiya I’m not fine, Wai ace baka kira kaji yana kai gida ba koh? Bcs I’m not important to you”
“Ba haka bane, kinsan ina aiki da yawa but I’m sorry” sake mirginawa tayi daga kan gado sannan ta harde kafafu.
“Okay naji Mine, Kaci dinner kuwa? ko nazo na dauke ka mu fita mu ci?”
“Ai ni da wuri nake ci Wallahi”
“Ni gaskiya ban yarda ba, kawai rowa kayi min but It’s all good nima zan rama” ta faɗa muryanta à shagwaɓance.
Daga nan suka cigaba da hira kala kala har sunfi minti talatin suna zantawa. Ita kuma Fadeela tasan Other half ɗinta Baya daɗewa a bayi, saita bishi taji ko lafiya?
Yana kwance yana hira saiya ji zuwan Deela, da sauri ya tashi harda tuntuɓe zai shiga bayi, kafin ta buɗe kofan harya kunna famfo domin taji karar ruwa. Ajiyar zuciya ya rinka yi duk zufa yana keto masa.
Text yayi ma Yasmeenah akan he is busy zasuyi Waya gobe. Saiya dauraye fuskarshi da ruwa sannan ya fito.
Deela yagani zaune tana jiran shi, “Other half lafiya ka dad’e a bayi?”
“Mts gaskiya kamar cikina ba lafiya ne” saiya zauna yana ajiyar zuciya.
Dukda yanda jikinta ke mata ciwo bai hanata sauka downstairs ba wajen First Aid box domin ta dauko masa Lemotin.
Tana taka matakalan karshe saida ta huta, a hankali ta karasa ɗakinsa domin ta bashi. Inda ta barshi anan ta iske shi, bare masa tayi kana taje bedside fridge ta dauko masa ruwa.
“Ungo karbi ko zaka ji dama dama”
Amsa yayi saiya yi kamar ya saka a baki amma ɓoyewa yayi a tsakiyar hannunsa, ruwan kawai yasha sai yayi wayo ya saka a aljihun wandon sa.
Ita kuma shafa masa kai take tayi tana masa sannu, ranar kwana tayi tana jinyarsa, ta kwantar dashi saita rufe shi da duvet. Saida ta tabbata yayi barci kana ta koma downstairs dukda tana ganin jiri Idan ta fiye bin wajen.
Kayan kallo ta kashe tareda kulle kofa da kyau, komawa tayi wajen Other half ɗinta duk tausayinshi ya mamaye ta. Ji takeyi kamar ta dauki ciwon ta daura ma kanta, fatan ta daya shine gobe kada ya farka dashi. Nima dai DIMPLΣS nace Amin ya rabb.
Washe gari misalin biyar da rabi na asuba suka tashi, sannu tayi mashi sannan ta koma dakinta. Shi kuma bayan ta tafi saiya dauki wayarsa wanda ke cikin bedside drawer.
Text msg ɗin Yasmeenah ya gani tayi mashi reply kamar haka, “Okay Mine, can’t wait to see you. Goodnight and chocolate dreams” Murmushi yayi wanda baisan yanayi ba.
Nan take yayi saving sunarta as ‘Aminu Office’ saboda kada Deela ta zarge shi dukda bawani abu yakeyi ba.
Ita kuma Deela tana idar da sallah ta wuce kitchen kasancewa yau talata kuma zata awo asibiti. Strawberry pancake tayi masa mai honey saita haɗa da sap ɗin Acha.
Yau da ciwon kai ta tashi saboda a daddafe take aiki ko ganin gabarta batayi, shiru tayi bata faɗa ma Naufal ba kasancewar shima yanaji da jikinsa.
Wajen karfe takwas ya ajiyeta a haraban asibitin Al madina saiya koma office idan ta gama saiya je ya dauketa.
Tana cikin asibiti tabi layin ganin Doctor, Dr Hadiza Pate tana ganin Deela saita mata murmushi.
“Bagashi Allah ya nufa fah” ta faɗa yayin da Deela take kokarin zama.
Daga nan aka duba yadda take tareda kwanakin cikin a jikinta. Anan ne aka gano satinshi goma sha daya.
Duk wani protocol daya kamata masu ciki subi duk tayi, ba ita ta gama ba sai wajen 11 ɗaya da wasu kananan mintuna.
Ta bala’in gajiya saita kira Naufal amma taji call waiting alamun Yana waya. Kashewa tayi tana jiran ya gama saiya kirata.
Shikuma daga ɗayan ɓangaren waya yakeyi da Yasmeenah sai Deela ta kira. Dayake ear piece yake amfani yana kallo yake ringing amma baiyi gigin dauka ba harya tsinke.
Shi yana so ya gama da Yasmeenah ne kafin ya kira Deela saboda yana kyautata zaton ta gama daga asibiti ne.
Ita kuma Yasmeenah sai zuba takeyi wai bata karya kumallo ba tana so ya raka ta. Yanata nokewa amma taki yarda wai saiya rakata koda baci zaiyi ba.
Suna cikin gardama saiga Aminu yazo da wani drawing yana so Naufal ya duba masa.
Da hannu yayi masa alama ya kashe wayar, sallama yake ma Yasmeenah saiya ajiye. Anan ya soma dubawa shaf ya mance zai kira Deela. Suna cikin haka 30 mins later sai Yasmeenah ta kira wai tana Larema tana jiran sa.
Nan take yayi ma Aminu sallama saiya tafi, Aminu shikuma ya ɗaga masa k’afa ne saboda yaji yace, “okay gani nan zuwa” duk zatonsa Deela ce ke ɗayan ɓangaren.
Sanye take da Swiss Lace mint green Wanda akayi mashi ɗinkin peplum. Ya ɗameta dakyar take numfashi balle tafiya.
Gwawaro style ta daura kawai amma bata saka mayafi ba kasancewa ita ba ma’abociyar sa bane. Chewing gum ta saka a bakinta tana tauna kas kas tareda wulla idanu.
Sannan gashi ta fashe kanta da turaren Unbreakable Bond. Tana cikin motarta kirar kia picanto tana jiran isowar Naufal. Tunanin irin salon da zatayi mashi ne yau saboda ta lura yanada zafin kai.
Shikuma yana isa Larema ya fito daga cikin motarsa, harya kulle saiya tunada Fadeela. Nan take yaji babu daɗi tareda haushin kansa.
Wayarsa ya dauko domin ya kirata, itakuma ta kulu tayi fam kamar ta fashe, a parking lot zaune take duk rana ita kaɗai kamar mayya. Taso tayi zuciya ta tafi amma kawai ta hakura kila yana wani abune, saisaita kanta tayi tana faɗin Allah yana tareda mai hakuri.
Sunansa tagani baro baro ‘other half’ murmushi tayi saita dauka, shikuma bugu ɗaya, biyu, na uku yaji ta dauka tareda faɗin, “ My Other half”
Bai kai ga amsa mata ba sai Yasmeenah tayi karab ta kwace wayan tareda kashewa.
Kallonta yayi a fusace ya rasa me zaice, “Meye haka? Bani wayana mana” Ya faɗa a sanyaye.
Murguɗa masa baki tayi cikin wasa tana jijiga jikinta komai nata yana rawa, “Bazan bada ba, lunch zamuci so no phones allowed” saita fara rausaya ta tafi ciki.
“idan kana so kazo ka karba” ta nuna masa wayan sannan ta zura cikin jakarta. Ranshi a bace ya bita ciki duk fargaban yanda Fadeela zatayi yake.
Ita kuma ta rinka Hello! Hello!! Amma taji Shiru. Sake kira tayi sai kawai taji an kashe, “kambu” ta ce saboda bata san sanda tayi ashar ba.
Da karfin tsiya ta fige jakarta, dama gidansu Anty Saudah zata saboda rana ya bigeta gashi jiri yana fizgarta.
Napep ta tare tayi gidanta tunda bata tambaye shiba, tana isa locacin azahar yayi. Bayi ta shiga ta watsa ma kanta ruwan zafi sai tayi alwala.
Sallolinta tayi tareda addu’a, bata bar kan sallaya ɗinba mirginawa kawai tayi ta soma barci. Gashi yunwa ya soma addabarta amma bazata iya tashiba saita huta.
Yasmeenah ta zauna wannan Karon a wajen VIP tana jiran Naufal, sannu a hankali ya taka wajen datake zaune. Murmushi ta sakar masa Shikuma fuskarshi babu yabo babu fallasa.
Duk ya kagu daya bar wajen saboda ya lura da abin iya shege ne. Kawai ordering jollof yayi baima ciba tsakura yayi.
Ita kuma Shawarma aka kawo mata da Non alcoholic wine.
Tana Ci tana mashi salon turanci kamar zata karya harshe, bai biye mata ba illa uhm da kuma uhm uhm dayake amsawa. Jira yakeyi su gama ci ya karɓi wayarsa domin ya kira Fadeela saboda yasan tana jiransa.
Bayan nan saita ce wai suje Vanilla joints shan Ice cream, wani mugun kallo ya watsa mata kana yace, “Halan bakisan inada aikin yi bane?”
“Oh na mance, muje na rakaka office I promise bazan dame kaba” saita ɗaga hannunta sama alamar rantsuwa.
Baiko kalleta ba ya buɗe motarsa.
“Maybe some other time” Yace sannan ya shiga ciki.
“Okay ba matsala” tace saita ɗaga masa hannu.
Yana tafe yana Zura gudu saboda yasan bai kyauta ma Fadeela ba, duk tausayinta ya kamashi kuma yayi mata alkawarin bazai sake ba.
Yana isa asibiti babu alamar Fadeela babu dalilinta, masu gadi ya tambaya sai suka ce masa ta kusa awa daya da tafiya. Dafa kansa yayi yana salati saboda yasan yanzu hankalinta ya tashi.
Wayanta ya kira amma bata ɗauka ba, dama yana kyautata zaton zatayi haka. Ita kuma wayar ta barshi cikin jakarta kuma yana downstairs saboda bazata iya jigilarsa ba.
Yasmeenah gidansu Laila ta wuce kai tsaye domin ta bata labarin abinda tayi kwana biyu. Anan ne Laila ke fada mata indai Architect Naufal ne to fah yanada mata, Amatullah kawar cousin dinta itace kanwarsa.
Cizon yatsa tayi tana jin haushin labarin, sai kuma kawai tayi fuska. Ita zata aureshi koda mata ɗari gareshi ballantana kwara ɗaya karamin alhaki.
Zata zama amarya sa uwar gida hauka tareda maida uwar gida ta zama bora. Koma waye matarsa kawai tayi hakuri ta bar mata Naufal salin alin kafin ta samata bakin ciki ya kasheta.
Kowa yasan Yasmeenah bata iya kishi ba, ba’a cin nasara akanta. Kawai a ganta a kyaleta!
Yana isa gida yaga jakar Deela a falo amma bata wajen, hankalin sa ya ɗan kwanta saboda ya buɗe yaga Wayanta ciki.
Dakinta ya nufa saiya ganta kwance a kasa, yayi nadaman abinda yayi mata ainun. A hankali yaje inda take saiya tallabota.
Mistike ido tayi sai tayi murmushi kamar babu abinda ya faru, dama ita bata iya mita ba. Shine domin borin kunya ya fara jero mata zance.
“Babyna kiyi hakuri, dazu da kika kirani muna conference call dasu Mr Sutter, muna gamawa shine na kiraki saiga wani ogan mu yazo yasa na kashe wayar”
“please I’m really sorry my love, in sha Allah bazan kara ba” kakalo murmushi tayi saita sumbace kumatunsa, “Babu komai, ya wuce saboda nasan baza kayi da gangan ba”
Daga nan ta tashi zata wuce kitchen, rakata yayi domin suyi tare Thou kawai mika mata abu yakeyi. Jollof din Cous Cous ne sukayi sai suka wuce dinning domin yunwa yana damun Deela, shi kuma karfin hali kawai yakeyi saboda ya riga yayi nat tareda Yasmeenah.
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 27 ✨✨✨
On the authority of Al-Numan bin Basheer, who said : I heared the messenger of Allah say : "That which is lawful is plain and that which is unlawful is plain and between the two of them are doubtful matters about which not many people know. Thus he who avoids doubtful matters clears himself in regard to his religion and his honor, but he who falls into doubtful matters falls into that which is unlawful, like the shepherd who pastures around a sanctuary, all but grazing therein. Truly every king has a sanctuary, and truly Allah's sanctuary is His prohibitions. Truly in the body there is a morsel of flesh which, if it be whole, all the body is whole and which, if it be diseased, all of it is diseased. Truly it is the heart." Narrated by Bukhari and Muslim.
*********
Yasmeenah Yusuf(YY) kokuma Meenah yanda friends ɗinta suke ce mata. Ita bafillatana ce yar asalin garin Shandam dake jihar Jos.
Mahaifinta Marigayi Alhaji Yusuf ya rasu tareda matarsa Hajia Jidda à car accident tun tana shekara biyar. Daga nan saita koma zama wajen wan mahaifinta Alhaji Abdulrahman.
Shi yana zaune locacin a Las Vegas da matarshi Hajia Hindu tareda yaransa guda biyar. Babban yaronsu mai suna Huzaifah yanada shekaru 28, sai Hilal 27yrs, Haisam yanada 25yrs, Hashim 23yrs, sai dan auta 20 yrs. Ita kuma Yasmeenah tanada shekaru 22 a duniya.
Shekarar daya gabata suka dawo Nigeria sanadiyar Daddy yayi retire a aikinsa. Yara rainan turai Sam basuda tarbiyya kwata kwata, gaba d’ayansu karka cire kowa duk jakai ne.
Dama dama Hashim, shi duk rinsti yana sallah kuma bai kwana da mace, shisha ne dasu codine. Ko auta Habeeb yana shan Wiwi, balle ayi maganar gwaska Hilal.
Shi wannan tsakanin shi da sallah sai ranar Eid, shima saboda ana taruwa aje baki ɗaya. Ga Cha Chan bala’i, Bin mata kamar bunsuru, shaye shaye kamar salansa. Dab da zasu dawo Nigeria da zama ya koyi shan Hodar iblis.
Sannan yanada bala’in zafi, baya daukan rainin at all. Yanzu saiya tara maka gajiya. Dukkansu babu mai aikin yi daga Huzaifah sai Hashim kasancewar duk sun gama.
Tun suna yara Daddy ya siyan masu Shares mai yawan gaske, kowa da nashi har Yasmeenah yasa suke fachaka babu kama hannun yaro.
A cikin su tarbiyan Yasmeenah ne yafi dama dama, at all bata shaye shaye kuma bata bin maza suyi fasikanci. Kawai dai ka barta da shigan banza saboda takan fita ma babu kallabi.
Sannan takan saka gashin gira, kumba da kuma gashin kanti dukda nata yanada tsawo.
Itace ma taci Prom queen a makaranta saboda tana cikin kin yadda. Gashi tanada kokari babu laifi saboda bata faɗi jarabawa.
Tunda Yasmeenah takai shekara sha shida a duniya kyanta ya fara bayyana a mastayinta na ‘Ya mace. Tun daga nan suka fara far mata, tana tafiya yayyinta zasu shafa mata jiki. Tada bala’i tayi sosai saida Mommy ta shiga tsakanin su.
Tun daga nan ta raina su saboda girma ya faɗi, suna ce mata kule zata ce masu chas. Wata rana idan Mommy bata gidan haka zasu zauna suyita hirar yanda suka kwana da mace.
Komai suke faɗi kuma basa damuwa idan Yasmeenah tana wajen. Saidai taji kunya ta tashi, idan kuma ta bar wajen sai su bita da zagi, “Shegiya munafuka kamar bakiyi”
Tasan cewa tarbiyanta akwai gyara sosai amma ita Manzo ne a gaban su. A sanda taji kishin kishin wai za’a haɗata da ɗaya daga cikin yaran gidan, kuka ta kwana tanayi.
Ta ɗanji dama dama da taji Huzaifah ne saboda shi solobiyo ne, juyashi zata yi kamar waina. Amma dai dukda haka bata so, sam bazata iya haɗa zuri’a da yaran gidan ba.
Yasa tun dataga Naufal ta birkice akansa, duk wani aji data ke dashi a matsayinta na ‘ya mace ta ajiye gefe. Dama Hausawa sunce da zafi zafi akan daki karfe, ta dauki alwashin bazata hakura dashi ba harta sameshi.
Zatabi kowane hanya daya dace daga kissa, yauki, iyayi kai har Malaman zaure zata iya bi domin Naufal.
Abinda yake mata daɗi shine tun kafin aje Ko’ina ta fara samun lambar zuciyarshi dukda bawai sun wani sake bane yanda takeso amma tana kyautata zaton cewa ya kusan zama nata baki daya.
********
A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, yanzu a kalla cikin Fadeela ya kai wata biyar a duniya. Tayi katuwa sosai kuma kafanta ya soma kumbura, komai a wahalce takeyi amma bata fasa aikin gida ba.
Ko Defence na project tayi kawai yanzu zaman gida takeyi tana rainon cikinta. Saidai bata jin daɗin yanda aiki ya kacame ma Naufal, tun safe idan ya fita sai goman dare yake komawa gida.
Tun tana complain akan abin saboda yana damunta sosai gashi ko waya sau ɗaya sukeyi shima sai idan ta kirashi. Flimsy excuse yake bata koda yaushe akan yana conference call da su Mr Sutter, wata rana kuma yace yana construction site ne.
Hakuri takeyi koda yaushe tayi masa uzuri, koba ta faɗa ba tasan Allah yana tareda mai hakuri. Sam bata nuna masa ɓacin ranta saboda tasan cewa duk zafin neman dayake yi akan itane da abinda zasu haifa.
Shikuma yana zuwa aiki karfe 2 yake tashi daga nan zai tafi yawo da Yasmeenah. Basu Ice cream joints Ko wajen shawarma duk dai wurare marasa kan gado kuma baya komawa sai sunci dinner tukun.
Shakuwa mara misaltuwa ke tsakin su, soyayya mai karfi ya shiga tsakanin su. Tun yana ɗari ɗari da ita har yake sake sosai.
Weekends kawai Fadeela ke ganin sa sosai saboda shima bazai iya karyan aiki ba, amma wata rana idan Yasmeenah ta nace dole yace zashi dauko wasu takardu office.
Yanzu jin kansa yakeyi kamar tubabban sarki don karya, tun yana ɗari ɗari idan yanayi kuma yana jin wani iri ajikinsa har yazo ya saba.
Yin karya yakeyi kamar yana faɗin gaskiya. Akwai wani rana haka da asuban fari Abba ya kirashi akan yana san ganinsa.
Yana isa ya rufe shi da faɗa akan dalilin da bai siyan ma matarsa mota ba, nan take yi charap yace ai Birthday ɗinta ya kusa ya kuma order akawo mata.
Kuma alhali karya yakeyi, dayake baya zaman gidan ya mance Fadeela Keke Napep take hawa duk kuɗin mijinta. Shi yanzu duk girman mutum zai iya mashi karya yasa ko tunani baiyi ba yayi ma mahaifinsa.
Babu mamaki idan aka bashi ministan kula da lafiyar karya. Yanzu ne zaisa akaima Fadeela Mota. Koda yake ya ɗanji tausayinta, ga ciki ga kuma rashin abin hawa but he promised to do better.
Last week ya kashema Yasmeenah dubu dari da hamsin akan motarta, ita bawai ta tambayeshi bane saboda tanada kudinta. Shine don raayinsa ya bada wai ‘Meye amfanin zama tare’
Tun daga nan bata sake masa musu ba wajen kudi, haka yake siyan mata su designer bags dasu takalma. Sauda dama yakan mance daya kamata ya siyan ma Fadeela.
Sai daga baya ya tuna, daga nan saiya rinka siyan komai guda biyu. Leda ɗaya Yasmeenah ɗayan kuma Fadeela.
Idan yakai gida wajen Deela, ta rinka shi masa da albarka kenan tana jindadi. Shi karin kansa yana jindadin addu’o’inta unlike Yasmeenah dake cewa ‘Thanks’ sai a wuce wurin.
Gashi kuma wayarsa ya saka password, shima idan ka bude akwai wani a Whatsap, msg, phone book etc.
Kuma idan ya dawo goman dare zaita danna waya, idan Deela tayi masa complain zai ce tayi hakuri Email yake aika masu Mr Targeyen.
Wata rana tana jiransa wata rana kuma tana kwanciya ta kyalesa, kawai daɗin abin su Miemie da Bilqees sukanje sukai har Magrib sai Khattab yaje ya daukesu.
Wani alhamis haka bayan sun gama karin kumallo kafin ya fita, saita tambayeshi izinin tafiya kasuwan Muda lawal domin tayi masu cefane.
Ya bata izinin ta tafi tareda cika mata jakarta da kudi. As expected shi masa da albarka tayi sannan ta rakashi wajen motarsa saiya tafi...
11 am.......
Locacin ta gama aikace-aikace daya kamata tayi sai tayi wanka domin ta tafi kasuwa. Tana gaban mirror saita lura da gashin kanta yayi datti ya chukurkuɗe, anan ta yanke shawaran gwara taje saloon tunda duk hanyar ne.
Ita kuma Yasmeenah jindadi takeyi sosai saboda zata fita date da Mine ɗinta. Zumuɗi Kawai takeyi, wani bakin leather wando na Victoria Beckham ta saka saita haɗashi da riga na chiffon white and black Mai guntun hannu.
Takalmin Jimmy Choo silver ta saka saita dauki Bouquin din Marc Jacobs. Fuskanta shake da makeup kamar mannequin. Sai kuma wani munafikin gyale data dauka.
Tafe take cikin motarta zata salon ayi mata gyaran gashi dasu kafa kafin yamma yayi. Taje har an fara mata sai ta kira Laila kawarta akan tazo ta tafi da motarta saboda Naufal zata kira banyan nan.
Suna zaune a cikin dryer suna hira saiga Fadeela ta shiga itama, kafin a gama wanke ma Fadeela ayi mata setting har nasu yayi sai suka fito suna yauki kana suka zauna dab da ita.
Kana ganin Fadeela kasan babban mace ce, iPhone 7 ke hannunta ga kuma tasha qwala qwalai daga kunnenta har yatsun ta. Sannan atamphan Super wax ke jikinta kuma anyi mashi ɗinkin masu hannu da shuni.
Gashi dama jikinta ya murmure, dole ta birge ka. Su Yasmeenah saida suka kasa hakuri sukayi mata magana. “Halan ke amarya ce?” Yasmeenah ta tambaya Deela.
Murmushi Deela ta sakar mata saita amsa da eh.
“Wallahi kin burgeni ne kawai, ina so nayi kama dake idan nayi aure”
dariya Deela tayi bata cekomai ba.
“Ki tayani addu’a, inada wanda nakeso na aura da fatan Allah ya tabbatar da alheri”
“Aminsumma Amin” Deela ta amsa. Daga nan ta tashi zata shiga dryer, anan ne sukaga tanada ciki. Laila ce tace ‘Lahhhh ciki gareta! Wallahi ina son yara sosai kamar raina”
“Kai nayi maki murna, Allah ya saukeki lafiya” Yasmeenah ta ce.
“Amin summa Amin” ta amsa mata dashi.
Daga nan sukayi sallama saboda anzo daukar su. Ita Deela kawai tana amsasu ne amma sam basu burgeta ba. Duk sunyi shigar arna ga gashin Kanti da kuma gashin ido.
Da basuyi hausa ba bazata zata musulmai bane, kawai tana tunanin wanda zai auresu a haka. Wayanta ya soma ruri saita tashi taje ta dauka.
Ta window ta hange shigan motar Naufal yana barin parking lots, bayan tagani kuma yayi nesa da ita. Kauda tunanin tayi ta koma aka gyara mata gashin kanta.
Bayan ta gama sai tayi chatan Napep taje kasuwa tayi Siyayyanta. Data koma gida ta daura masu dinner saboda Naufal ya daina cin lunch a gida, ko office ta tura masa bata samunsa kila ya tafi construction site.
Tuwan alkama tayi da miyan karkashi, saita fasa kwakwa da pineapple ta markaɗa masu. As usual ta kanyi kwalliyar tarban miji, yau kawai daɗi takeji saita saka wani bakin guntun free gown.
Gashi kanta yasha gyara so bata daura kallabi ba, dama wajen goma yake dawowa amma wannan Karon har wajen minti arba’in da biyar.
Sam batayi fushi ba saboda hakuri shine zaman aure, koba komai saboda ita yake neman kuɗi. Yana shiga falo ta tashi da sauri ta karasa wajensa tayi hugging ɗinsa.
“My Other half, Finally ka dawo.... Yau na rasa dalilin dayasa nayi missn dinka sosai”
Manna mata kiss yayi sai yace, “Toh gani me kika ajiye min”
“Muje kayi wanka sai kazo kaci abinci, yau favorite dinka na girka”
Daga kanshi yayi sannan ya soma magana kasa kasa, “Afuwan babyna Wallahi Aminu ya isheni da yana jin yunwa shi ne na kaishi daga nan saina ci”
Shiru tayi batace komai saboda ta bala’in shaka, gashi har konewa tayi wajen wrapping tuwon. Idanta Saida ya canza kala saboda bacin rai, ba wannan karon bane take abinci yaki ci, yayi yafi a girga amma na yau ya ɓakanta mata rai.
“other half Ko drink ɗin bazaka shaba” ta faɗa cikin muryan kuka.
Shafa bayanta yayi saiya ce, “Ki ajiye min a fridge gobe sai na sha”
“Allah ya kaimu lafiya”
“Amin babyna”
Sun tafi ɗaki har yayi wanka tana goge jikinsa da hand towel, “Other half yau Kaje wannan sabon plaza ɗin ne wanda ke kusa da Apple clinic?”
Datana kallon fuskarshi dataga rashin gaskiya karara ya bayyana. Dakewa yayi saiya amsa mata da, ‘Ah ah, menene ?”
“Babu komai kawai naga kamar motarka ne a wajen”
“NI dama yanzu zan faɗa maki a Gombe na wuni, Zaayi renovating Government house shine mukaje meeting” tabbas akwai zance kamar haka amma meeting ɗin saura sati biyu.
“Oh Allah sarki other half dina nayi maka murna sosai, Allah ya sanya alheri”
“Amin, amma kema meya kaiki wajen? Inace kasuwa zaki amma shine kika biya wani wajen? A duniya karya yana cikin abinda na tsana Wallahi. Idan kika tambayeni ai bazan hanaki ba, amma dan nuna ban isa ba shi ne kikayi abinda kikaga dama koh?”
Nan take ta firgice yanda taga karamar magana ya zama babba, saukowa gabansa tayi ta rike masa hannu, “Other half Kayi hakuri dan Allah, ka mance na saba biyawa saloon idan zani kasuwa saboda banso nayi fita biyu”
“Toh donkin saba sai akace banajin haushi ko me? Ni dai Karki saki saboda bana san karya”
“In sha Allah Other half bazan kara ba” Daga nan ta hau gado tana shafa masa bayan shi tana watsa mashi kalamai masu dadi.
Dolenshi ya sauko ya biye mata suka fara soyayyar su, suna haka har barci ya kwashe su.
#NiDaDiyata
#TeamFadeela
#TeamNaufal
#TeamYasmeenah
I'm proudly Team Fadeela this time around.
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs[9/2 15:52] Dimples: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 28 ✨✨✨
*Lesson*
Beware the liar. He lies so much that he forgets the truth. He even finds it hard to accept the truth & ends up believing in his own lies.
MUFTI ISMAIL MENK
Abu Ayub narrated that the Messenger of Allah said: "Whoever fasts Ramadan, then follows it with six from Shawwal, then that is (equal in reward) to fasting everyday." (Sahih)
***********
Washe gari..........
Tun sanda Fadeela ta tashi daga barci bata koma ba, kitchen ta wuce ta fara wanke wake saboda tana sha’awan cin kosai da kunun tsamiya.
Ta gama wankewa saita markaɗa à blender, shima ruwan zafin yana cikin Kettle amma yaki tausa. Wucewa tayi upstairs domin ta kira Naufal ya taimaketa ya duba mata.
Tana isa taji karar wayarsa amma kafin ta karasa ya tsinke,, kuma waya da password balle ta duba. Shikuma yana cikin bayi yana wanka.
Tana zaune a bakin gado tana jiransa saiga wayan ya sake shigowa, da hanzari ta dauka kuma cikin ikon Allah wanda takeso tayi magana dashi ya kira, watau Aminu office.
Ta kara a kunnenta kafin tayi magana sai taji muryan mace tana magana cikin yauki, “Mine tun dazu nake kiranka amma baka dauka ba”
Mamaki karara ya kama Deela saita cire wayar daga kunnenta ta sake kallo da kyau kuma tabbas Aminu ne.
Mayarwa tayi kunnenta sai taji, “Mine baka jina ne? Hello Naufal!” nan take gaban Fadeela ya faɗi sai tayi maza ta kashe wayar.
Jikinta ya soma bari, tabbas ba wrong number bane tunda ance ‘Naufal’ amma yaushe Aminu Office ya koma mace. Gashi harda kiran mijinta Mine.
Shiru tayi tana jiran shi ya fito daga bayi, yana fitowa sai yaganta zaune. Murmushi ya sakar mata kana yace, “Babyna yadai?”
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta soma magana, “Other half Aminu ya kiraka kuma na dauka amma naji muryan mace saina kashe. Probably wrong number ne”
“Probably” ya amsa saiya soma shafan mai. Dayake yanzu ya kware a iya shararo karya yasa baya girgiza idan yana yi. Tabbas yasan Yasmeenah ne kuma yayi warning ɗinta data daina kiransa idan yana gida amma bataji.
Kallon rainin arziki tayi masa sannan tayi kwafa, dama ta saba dauko masa kaya amma wannan Karon tayi kememe. A duniya rainin wayo yana cikin abinda ta tsana.
Ji yanda yayi pretending bayan harga Allah tasan ba wrong number bane. Ita abinda bata sani ba shi ne ko amsar wayan Aminu tayi ta kira Naufal kokuma itace Aminu ɗin da ake magana kullum.
Suna cikin haka sai wayarshi ya sake kara, toh dama yana hannunta, kallo ɗaya tayi saita lura da Aminu Office ke kira. Cilla mashi wayar tayi kamar zai faɗi sannan tace, “Gashi ya sake kiranka”
Kallo ɗaya shima yayi saiya yastina fuska kana yace, “bazan dauka ba tunda yanzu zani office”
Ita tasan yanada aboki Aminu amma kawai yanzu komai ya chunkuse mata ne. Kawar da tunanin tayi yanzu kafin zuciyar ta ya buga. Ya lura tayi shiru saiya je gabanta ya ɗuka tareda kama mata hannu.
“Babyna meke damunki? Murmushi tayi wanda bai kai ciki ba sannan tace, “Kaina ke ciwo” shafa mata goshi yayi tareda kumatu “Allah sarki babyna, ko na zauna ne nayi jinya”
“Na hutarshe ka” saita mike tayi hanyar kofa harta kusan ficewa saita tsaya tace “Bari naje kitchen”
Saboda bacin rai bata fada mashi kettle ya baci ba, kawai zataje ta daura akan gas. Shikuma dama gaste yake mata saboda koda tace ya zauna awa daya zai kara yace mata ana nemashi maza maza a office.
Dama yau zai raka Yasmeenah Kano karban dinki wajen wani tailor ɗinta. Ita kuma Fadeela tana aiki a kitchen duk ranta yana mata zafi, bata ma lurada suyan data keyi dukta kona.
Haka sukaci ita kokon kawai ta tsakura. Daya lura da yanayinta saida ya tambaye ta matsalarta saita ce masa kanne. Shi kwata kwata baiyi tsammanin ta ɗago sa bane saboda yasanta da nawa a al’amura ta, kafin ta ɗago locacin kila ta haihu kuma dama abinda yake jira kenan.
Harda cewa ta dauko mayafi ya ajiye ta a asibiti amma taki, ce masa tayi idan ta kwanta zataji daidai. Harya kai kofa bata tashi domin ta rakashi ba, juyowa yayi saiya fara magana, “Baby tunda bakida lafiya ba sai kinyi girki dani ba”
“Zaku fita Kuci da Aminu koh?” tayi charab ta tari numfashin sa. Murmushi yayi yana sosa k’eya saiya ce “Eh baby zamu koma Gombe kuma”
“Allah ya dawo daku lafiya” ta faɗa tana mashi kallon tuhuma. Dama ance kukan kurciya jawabi ne kuma sai mai hankali ke ganewa, amma sam bai saka a ranshi ta gane komai ba.
Inshut yau ya kara jindadin yanda yayi mata karya dazu kuma bai girgiza ba, kanne ido ɗaya yayi saiya furta a fili “Kai Naufal bakada dama”
yana tafe hanyar gidansu Yasmeenah yana Nishaɗi tareda sauraron wakar Young Alhaji na Nomis G.
Ita kuma Deela kifa kanta tayi a kan dinning tayi kuka san ranta, wai yaushe yaushe da shiryawa da shi harta gundureshi ya soma kallon wata.
Upstairs ta wuce dakinta domin ta dauki wayarta, kawarta da suka tashi tare Jumaimah ta kira a waya akan tazo gidanta yanzu yanzu. Within hour ɗaya ta iso. A falo ta riske Deela ido yayi sutu sutu ya kumbura.
Bata iya karasa sallama ba ta wulla jakarta kasa tareda rugawa wajen Deela. Rungumota tayi saita soma magana da sauri sauri “Deela meya faru? Dukanki yayi?”
Rushewa da kuka Deela tayi dama abin nema ya samo wai matar falke ta haifi jaki. Jijigata Jumy tayi saida taga ta rage kuka sannan ta kuma tambayarta “Deela my dear kin ruda ni, kiyi wa Allah ki faɗa min saboda hankalina ya huta”
Cikin muryan kuka ta soma magana gwanin ban tausayi, “Tunda nake ba’a taɓa min rainin hankalin da Yaya Naufal yake minba” Daga nan tana kuka ta fayyace mata komai da komai duk abinda Naufal yakeyi wanda duk bata lura ba sai yanzu.
“ni nama rasa me zance Wallahi” Jumy ta faɗa tana jinjina ma kokarin Fadeela. Daga nan saita ce, “Toh yanzu me zakiyi? Zaki tambayesa ne ko me?”
“In tambayesa? Wallahi karya zai shirgo min. Aini tun karyan dayayi min dazu na firgita dashi”
“Okay ki bani nanda awa biyu Deela, zan nemo maki waye asalin Aminu. Office ɗin su zani nayi masu hadarin kudi dole su faɗa min wake zuwa wajen mijinki”
Murmushi Deela tayi saboda taji daɗin shawarar. A kwance Jumaimah ta bar Deela kana ta wuce bank ta ciro dubu hamsin. Kai tsaye office ɗin Naufal ta wuce.
Masu gadi suka tareta suna mata magana akan inda zata da sauransu. Murmushi tayi saita yi parking motarta daga gefe saboda hanya ne.
Sannu a hankali ta fito daga cikin motarta taje inda suke, murmushi ta sakar masu kana ta gaishe su. “Da alheri nazo wajen nan bayin Allah” saita zuge jakarta ta kyallara masu kuɗi su gani.
Dama su biyar ne, hudu suka soma washe baki daya kuma fuskarshi babu yabo babu fallasa.
“Dama tambaya nakeyi”
“yarinya Allah ya sa mun sani”
“Kunsan Arc Naufal Hussain”
Noke noke suka farayi basaso suyi magana, data lura da yanayin su sai tayi murmushi kana ta kara matsawa kusa dasu, “Kar kuji tsorona, niba muguwa bace kawai wasu abu ke faruwa a office ɗinnan shine nake so na sani”
“eh mun sanshi, lafiya koh?”
“Bansani ba ko akwai wata wanda ke yawan zuwa wajen shi ?”
“kice mai shigar arna” Daya daga cikin su ya chapke. Daga nan suka soma magana akanta, kowa na faɗin magana marasa daɗin ji akanta.
Jumy taji dadi sosai koba komai Fadeela ta kace mata tsara tunda ita ba mutumiyar arziki bane.
“Toh kun san sunanta ko wani abu game da ita” ta tambaya. Wani daga cikin su yaje ya dauki wani takarda daya kunsa sunarta da address dinta.
Acewarsa tazo cikin motarta shine zasu fita a motar Oga sai aka bashi address ya mayar mata nata. Jumy taji dadi sosai saita dauki dubu talatin ta basu zasu raba akan dubu shida shida.
Dama aikin dubu ashirin ne a wata toh gashi sun sami kwantan shi, nan suka rinka godiya suna shi mata da albarka. Dadin zance suka faɗa mata yau Naufal baizo aiki ba jiya ma tun goma daya fita bai koma ba.
Tana zuwa ta fayyace ma Deela komai daya faru, kuma tace mata tanada wani uzuri a gabanta amma gobe bayan Naufal ya fita sai tazo suje suci kaniyar karuwarsa.
Deela taji dadi sosai kuma tayi Na’am da shawarar. Batayi girki ba saboda tasan bazai ciba, sauran kokon ta take ta sha sai wajen yamma tayi Indomie da sardine.
Wajen yamma su Naufal ana Kano Anje shoprite da Yasmeenah ana kallon wani sabon American film ‘XXX return of xender cage’ anayi ana shan ice cream da popcorn.
Dama tun safe suka karba ɗinkin kawai ana holewa ne. Siyayya ba kadan ba tayi saida kuɗi sukace Allah ya isa kudaina kasheni haka.
Waya akayi ma Naufal wai an kawo motar Deela daga Cotonou, dayake baya garin sai yace kawai a kaimata dukda birthday ɗin shigarta 21 saura kwana uku.
Shi a dole yayi abin arziki ya bata early birthday present, da farko har zata mayar masa da abinshi amma saita tuna raba mugu da makami ibada ne.
Shikuma sai kallon waya yakeyi yana jiran yaga ta kirashi ta fara kwarara mashi addu’a amma sai yaga wayam. Haka ya hakura da tunanin kira sai ya mayar kila batada kati ne, yanzu yana kyautata zaton ta saka English wear mai rikitarwa tareda saka turaren wuta tana jiran sa.
As expected wajen goman dare ya koma gida, Deela tana jin karar motarsa ta kashe wutan ɗakinta tareda kwanciya abinta. Yana shigowa bai ganta ba sai tausayinta ya kamashi sosai saboda yasan ciwon ne ya sakata a gaba.
Yana zuwa ɗakinta yaga harta kwanta, zuwa yayi yana shafa fuskantar amma ta rinka mashi magagin karya. Dole yaje ɗakinsa ya barta, basuyi wani Chatting sosai da Yasmeenah ba saboda ya gaji sosai gashi kuma ranshi baya mashi daɗi Deela babu lafiya.
Washe gari.....
Dankali da kwai ta soya mashi, dukda yana hanata akan batada lafiya amma taki ji. Ita kawai badan shi takeyi ba sai dan Allah.
Batayi mashi maganar motar ba shine ya gaji da shirun ya tambaya. “Eh dama naga an kawo mota amma bansan na menene ba?”
Kanne mata ido yayi yana dariya,”Babyna zatayi birthday dole na fito da ita”
“Ai ashe zaka tuna?”
“Meyasa bazan tuna ba?”
“Naga yanda kuke fita sosai aiki da Aminu ne yasa banyi tsamanin zaka tuna ba?”
Shiru yayi ya cigaba da shan Coffee ɗinsa saboda kamar magana ta gaya mashi. Har mota ta raka shi daganan ta sake kallon nata.
Venza ce 2016 model kuma kana gani kasan tasha kuɗi. Wajen 10am Jumy tazo tana zuwa sai taga mota a parking lot. Cikin mamaki ta tambaya Deela kona waye shine tace ai shiya turo jiya.
“Dauko mayafinki mu shiga ciki muje muci ubanta” dama Deela ta iya tuki saboda takan tuka motar Mommy.
A hanya suka dauke Mansura aka wuce da ita, suna isa kofar gidansu Yasmeenah sai suka tsaya a bakin gate wai ayi masu iso da ita. Daya tambayesu sunar su sai Jumy tace ace mata Naufal ne.
Yasmeenah tana zaune tana kallon wani tsohon Comedy The big bang Theory Sai akace Wai Naufal yana jiranta. Dayake bata expecting ɗinsa sai bayan la’asar saboda yanada aiki sosai.
Daga ita sai leggings da t-shirt kai babu kallabi ta ruga a waje saboda dama tana missing ɗinshi. Tana fita gate bata ganshi ba sai wasu mata uku. Tambayar maigadi tayi sai yace ai sune suke nemanta.
Tana karasawa tareda magana, “Bayin Allah daga ina haka..?” bata karasa ba Fadeela ta dauketa da mari, zatayi magana saita sake kai mata wani.
Hannunta biyu a kunci tana mamakin meya faru da ita, sai a locacin suka kalle juna kuma sun gane cewa sun haɗu a saloon.
“me na maki da zaki mareni?” Ta tambaya.
“ni bazan ce ki daina kula mijina ba, kawai nazo nayi maki bushara ne bcs kin kawo kanki gidan wahala. Saina nuna maki iskanci ba karuwai irinki kawai suka iya ba.”
Anan Yasmeenah ta hasala, “Dama akan Naufal kika mareni shine na tsaya kallonki, wallahi zaki san wa kika mara?” Saita nufa Deela. Jumy ce ta mauje mata baki da jakarta.
Nan take jini ya barke, kukan kura ta sakeyi saita koma kuma anan Mansura ta samu nata rabon tareda wanka mata mari. Da gudu maigadi ya shiga tsakani tareda korar su Deela.
Sun tafi murna fal Ransu koba komai sun girgizata, sun koma gidan Deela a inda Jumy da Mansura sukayi mata sallama suka tafi.
Ita kuma Yasmeenah kiran Naufal tayi a waya tana masa kuka akan matarsa tazo da gayya sun fasa mata baki. Yayi mamakin yanda ta sani amma wannan bashi ke gabansa ba.
Zuwa yayi gida ko shiga da motarsa baiyi ba kawai yayi parking a waje saiya shiga ciki, motsi yaji a kitchen da alamu tana ciki.
Zuwa yayi wajen baiyi wata wata ba saiya haska mata mari, “Wayece ki dake matar da zan aura?” yana huci kamar mayunwacin zaki.
Hannunta akan kumatu tana hawaye, cikin muryan kuka ta soma magana “Nika mara? Wallahi ka mari aurenka”
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[10/2 18:21] Dimples: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 29 ✨✨✨
*Lesson*
"FASBIR SABRAN JAMILAH". Patience is one of d most beautiful attributes one can ever have, It makes one listen, understand, forgive, forget, endure and move on in life. May Almighty Allah in His Infinite Mercy and wisdom uphold our faith in Him and may HE grant us d best of this world & d best of hereafter. Ameen
********
Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa, jikinsa yayi la’asar sosai. Dama yasan saurin hannunsa wata rana zai kaishi ya baro, daɗin abin Fadeela tanada hakuri kuma yasan zata yafe masa.
Magana ta cigaba cikin kuka, “Duk Meka min à duniya bazanga laifin ka ba! Don ka ganni cikin gidanka ne” saita kashe gas dama ta daura ruwan miya ne.
Zuwa tayi zata rastashi ta wuce, sai yayi kokarin kama hannunta. Da sauri ta kwace tareda nuna masa yatsa tana hawaye, “This is the last time da zaka mareni” sai tayi hanyar upstairs abinta.
Shikuma yasan ya tabo ta saboda bai taɓa ganin tayi haka, koda yaci zalinta bata nunawa, burinta bai wuce ta kyautata masa ba. Haushin kansa yayi saboda ya bar shedan yayi tasiri a rayuwarsa.
Barin gidan yayi saboda ya bata dama ta sauko, idan yaso anjima zai bata hakuri yadda zasu fahimce juna.
Wayarsa yayita kara kuma Yasmeenah take kiransa.
Kashe wayarsa yayi gabaki daya saboda yasanta da raki, yanzu hankalinsa baya jikinsa gwara yayi dealing da mace ɗaya tukun idan yaso gobe zaije wajenta.
Deela tana hawa upstairs ta dauko wani zungureriyan akwati tareda buɗe drawer ɗinta. Zuba kaya kawai takeyi tareda tunanin zuci. Saida ta gama saita fara tunanin inda zata.
Tasan cewa Mommy bazata barta ba sai kawai ta yanke shawaran zuwa gidan gona. Nan take ta ɗebo takalma da duk wani abinda zatayi amfani.
Rufe gidan tayi saita bama Maigadi key idan Naufal ya dawo saiya bashi. Cikin sabon motarta ta shiga saboda bazata bar masa ba.
Tana isa gidan gona taga Miemie a garden chairs da Khattab, su da farko basu ganeta ba saida ta sauko tayi hanyar boot tukun.
Da hanzari suka tashi domin su taimake ta, “Anty kin dawo nan da zama ne?”
“Eh Miemie”
“Ke kuma babu gaisuwa babu komai kin rufeta da tambaya” inji Khattab.
Daga nan suka wuce cikin gida.
Sun isa cikin falon sai aka gaisa yadda ya dace, locacin Anty Saudah tana daki sai Miemie taje ta kirata.
Bayan tazo an gaisa, sai kuma Khattab ya tashi wai shi zai tafi kuma Miemie tazo ta rakashi. Daga nan Anty Saudah ta soma mata kallon tuhuma. Kallon kasa ta somayi kana tace, “Aiki yayi mashi yawa sai goman dare yake dawowa tun safe, kuma ganida ciki. Yasa nace bari na dawo nan har na haihu”
Shiru Anty Saudah tayi saboda tasan bashi bane kaɗai dalilin, sai dai kawai taji daɗin yanda bata koma gidansu ba ko wajen Mama da abin ya tabarbare.
Mai aikinta ta kira taje ta gyara mata wani daki tareda canza zanin gado. Fadeela taji daɗi sosai yadda Anty batayi mata binkice ba dukda tasan karyan takeyi.
Bayan an gama gyaran ɗakin saita wuce domin ta huta, daɗi taji sosai saboda yanzu bata da wani aiki sai bin gado ko hira. Sam bata kewar Naufal asalima haushin sa takeji.
Wayarta ta dauka ta kira Mommy da Jawahir sai ta faɗa masu Exactly abinda ta faɗa ma Anty. Mommy tayi faɗa sosai akan dalilin da bata dawo da rainon gidanta, ita dai bata hakuri tayi.
Tasan yadda Mommy ke san Naufal, yana zuwa sau ɗaya zata ce ta bishi.
8:30 pm....
Biyawa yayi Vanilla joints tareda Oasis ya siyo kaya shak’e da leda, yana isa gida yayita bugawa amma ba’a amsa ba.
Komawa yayi wajen mai gadi ya tambayesa koba mutum ne. Anan ne ya mika masa key wai an bashi dazu ya mance bai bashi ba.
Shiru yayi ya rasa me yayi zafi da ta tafi gida amma ya dauki alwashin Ko’ina taje saiya dawo da ita. Haka ya shiga cikin gidan gwiwa babu kwari.
Washe gari Fadeela bata tashiba sai wajen 9am saboda ta kara barci bayan tayi sallah. Tana fitowa su Anty na kan dinning suna karin kumallo saita zauna itama tareda dasu.
Ana cikin haka saiga Naufal ya shigo, kallo ɗaya tayi masa ta watsar saita bar dinning ɗin gaba ɗaya. Shikuma yazo ya dauki Anty Saudah aje bikon Fadeela sai yaga motar Fadeela a parking lot.
Yaji dadi sosai saboda da kanshi zaiyi bikon abinsa, ba fariya ba amma yasan ya kware a watsa kalamai. Abin ya daure mashi kai dayaga har yanzu bata sauko ba.
Shidai Fadeela daya sani batada riko amma yanda wannan ke kumbure kumbure. Zama yayi akayi gaisuwa da Anty Saudah, koda aka kai masa breakfast shayi kadan ya kurba.
Anty ta lura yana inda inda saita mashi magana, “Lafiya dai koh?”
“Dama bansan ko meta faɗa miki bane?”
“Ban gane me kake nufi ba?”
“Ina nufin ta faɗa maki dalilin zuwanta ne”
“Eh tace yanzu bakada wani sana’a sai gantali yasa ta dawo nan har Allah ya sauketa lafiya”
Shiru yayi, sai dai kuma yaji daɗi data rufa mashi asiri. Koba komai ta kara nuna masa ita mace ta gari ce.
Tashi yayi ya bar Anty wajen zaune saiya tafi ɗakin da Fadeela take. Ita kuma bayan ta bar falon laptop ɗinta ta kunna tana kallon wani horror film mai suna Rings.
Tanayi tana matse ido tareda rungumar pillow saiga Naufal yazo, ko sallamarsa a ciki ta amsa saita cigaba da kallonta.
Mamaki ya kamashi sosai saboda ko gaida shi bata yi ba, asalima haɗa girar sama dana kasa tayi tamau tareda tsuke bakinta. Yana tsaye a bakin kofa yaga batada niyyar mashi magana.
Shine ya soma magana kasa kasa cikin lallami da lumana, “Kinki kallona kuma ko gaishe ni bakiyi ba kin kyauta kenan, koma mene maki bai kamata ki dauki zafi dani........”
Bata bari ya karasa maganar ba tayi pausing film ɗin saita figi wayanta ta shige bayi tareda banko kofa ‘dam’
Abinda yasa ta wuce ta kyaleshi baifi yanda ranta ya ɓaci sosai ba, saboda tayi alkawarin randa zata bashi amsa sai yayi mamakinta but yanzu gasu Anty bata so suji.
Shikuma sororo ya tsaya shake da mamaki daya lura babu wasa a abinda takeyi, asalima kamar soyayyarsa ya fice mata a rai farad ɗaya. Haka ya rinka kallon hannun daya mareta dashi yana jin haushin kanshi saboda gashi yanzu ya kaishi ya baro.
Ranshi na mashi kuna saboda baisan yadda zai yi da ita ba, dayake bata taɓa daukar zafi dashi ba so baima san me zaiyi ya wanke kanshi ba.
Haka yayita tsayuwa gefen kofa ya jinjina da bango tareda daura hannu daya akan kwankwaso, ɗayan kuma ya dafe kai dashi. daya lura batada niyyar fitowa saiya fita, yana komawa falo saiya tarad da Yasmeenah tayi masa Missed calls kamar zata rusa mashi waya.
Haka ya tashi yaje with the aim Zai dawo anjima ya dauki Fadeela su tafi gida. Ita kuma saida ta tabbatar ya tafi kafin ta fito tareda komawa ta kammala kollonta. Murguɗa baki tayi tareda magana a fili, "Babu inda zani, zama daram dam"
Koda taji dawowarsa da daddare saita garke kofanta, yana turawa yaji karfi. Yafi minti uku tsaye yana tattara tunanin sa waje guda, “Abin yarinyar nan da gaske nefa!” ya faɗa cikin ransa.
Gwiwa babu kwari yayi hira kadan tareda cin abinci saiya wuce gida, yanzu babu mai kwabarsa yayi waya da Yasmeenah sosai. Ita kuma murna fal ranta duk tsammanin ta agaban Deela yake wayan.
Sai wani rangaji da kafa takeyi tanata mashi shagwaba, Sam Shikuma bai faɗa mata Deela ta gujeshi ba saboda yasan halinta na rashin hankali zata rinka ziyarar sa tayi making situation ɗinsa ya tabarbare. Kawai yace yayi handling komai bazata sake ba. Ita kuma harda samun waje wai sai Deela ta bata hakuri, wani irin kallo ya watsa mata kana ya soma magana a hasalce.
“Halan bakida hankali ne? Matana mother of my child kike so ta kiraki? Better watch ur tongue”
Kwafa tayi tana zumbure zumbure, dama kofar gidansu ne saita fita daga cikin mota tareda banging kofa. Tsaki yayi kana yace “Allah ya raka taki gona”
Da daddare ta kirashi tana neman sulhu saboda ta lura ya fita iya shege.
Kwana sunata tafiya babu alamar komawar Deela babu dalilin sa, kwance tashi yanzu satin ta biyu da barin gidan Naufal, tana jin zuwanshi zata bar duk inda take ta koma ɗaki ta rufe kofa.
Haka tana sallar isha’i take kwanciya, babu mai takura mata daga Abba har Anty kullum cikin mata hidima suke. Gashi ta murmure ta kara fresh abinta hankali kwance.
Yau Asabar tun takwas Miemie da Anty Saudah suka tafi islamiyya. Dama Abba a gidan Mama yake, Deela na zaune a falo sai gyangyaɗi ya ɗebeta.
Muryan Naufal taji a kanta, a hankali ta buɗe sannan ta sake rufewa. Murmushi yayi saiya cigaba da magana.
“Fadeela sarauniyar mata, babyna Matana na kaina, kece shugaba a cikin Matana a aljanna..... Haba babyna I’m sorry please”
“Nagane laifina please kizo mu tafi gidan mu, wallahi nayi missing dinki, your smile, jokes, care in fact everything about my sweet Other half”
Buɗe ido tayi domin ta kalleshi, green eyes dinnan Sai sheki sukayi. Kuma kana kallonsa kasan cewa yana cikin damuwa.
Idan baka sanshi ba zakaji tausayinsa amma banda ita, ita yanzu zuciyar indai akan shine toh a bushe yake kamar stock fish, aslima haushin sa takeyi. Dayake mata magana muryanshi kamar narkarkiyan dalma ne a cikin zuciyarta.
Zama tayi sosai ta gyara daga kishingiɗin, kallon up and down tayi ta watsar kana ta cigaba da kollonta. Shikuma yaje dab ta ita zai zauna tareda rike mata hannu.
Da sauri ta mik’e dukda cikin jikinta, yanda tayi kamar an soka mata mashi, a fusace ta soma magana muryanta yana rawa.
“Menene haka zaka taɓa ni? Baka burgeni ba! da sai kaje wajen matar da zaka aura saika taɓa ta”
“Haba babyna ki daina faɗin haka mana, nace am sorry fah”
“ Mai I’m sorry dinka zai kara min a jiki? Bazai kareni da komai ba kuma bazai rage niba. So I don’t need it”
“Nika mara akan wata karuwa da batasan darajar kanta ba balle na wani koh? ai duniyar nan babu wanda yayi min abinda kayi min”
“All the lies, deciet, betrayal for what? Haba Naufal! ban chanchanci haka ba a wajen ka. I thought I meant more than this to you”
Kuka kawai yaci karfinta, shikuma jikinsa yayi sanyi tareda la'asar, saiya matsa wajenta zai taɓa ta, da sauri daja baya harda tuntube. Cikin kuka ta soma magana a hasalce, “karka kuskura ka taɓani, you’re done touching me”
Cak ya tsaya bai iya motsi ba, yasan cewa yayi gaggawan ɗaukan hukunci but ya kamata subar komai a past tunda abin yafi two weeks da faruwa.
Rufe ido tayi tanata masa bala'i babu kakkautawa, yanda kasan ta haɗiye tabarya haka take jin kanta a tsartsaye.
“Wallahi ban taɓa tunanin haka zai faru dani ba so soon, kaci amanar soyayya Naufal. Idan haka ake soyayya to I don’t want to have anything to do with it”
“Baby please kiyi hakuri nasan na bata maki rai, but I promise to do better”
“Don’t you dare lie to me kana so kace kasan yanda nakeji, you have no idea how I went through all the Loneliness, Kawai ka baka damu ba. Duk abinda nake maka baka taba gani ba”
“Duk rashin mutuncin da kake min ban taɓa nuna bacin raina ba, kullum hakuri nakeyi. Ko ance maka banida zuciya soso ke wajen. Amma na shanye komai saboda hakuri shine zaman aure”
"Shine zaka mareni akan......"
Anan kuka yaci karfinta tayi shiru da magana saidai rasgar kukanta, muryanta ya soma dishewa gashi karfin jikinta yana raguwa. A hankali ya soma magana cikin nadamar halinsa, “please baby I’m sorry, kizo mukoma gidanmu, our home mu haife babyn mu”
Dagowa tayi cikin masifa, “ Home! Wat home? Gidan da bakasan komai a kaiba saboda baka zama kun tafi gantali da Aminu office”
Daga nan ta juya ta wuce tareda barin shi a wajen, da sauri ya sha gabanta.
“Wallahi ka matsa min If not duk me nayi maka kaika ja ma kanka” saita kalle wani golf stick dake gefe, shima yana kallo saiya matsa mata kafin ta illanta shi.
Kawai tunanin gwara yaje ya faɗa ma Mommy gaskiya, a dawo mashi da matarsa. Ita kuma rastashi tayi ta wuce hanyar ɗakinta.
Binta ya cigaba dayi amma tayi burus dashi, tana tafe tana hawaye sanadiyar tuna irin rainin dayayi mata.
Buɗe kofa tayi ta shiga daki, ta juya zata rufe kofa saita ganshi tsaye gaban wajen, fuskarta babu annuri ta harɗe gira kana ta fara magana confidently, “Ni da kai, we are done”
Karab ta rufe kofar ɗakinta tareda saka key.
#NiDaDiyata
*I’m Dedicating this page solely to all the fans of NI Da Diyata, I really appreciate your love and support. Your awesome comments keep me going all the time. Allah ya barmu tare har mugama lafiya Amin*
*Ya kamata Fadeela ta koma, kokuma ta zauna har saita haihu?*
*Waiting for your answers*
*All Rights Reserved*
💥∂ιмρℓεs💥
[13/2 07:02] Dimples: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 30 ✨✨✨
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace be upon him) said: When Allah decreed the Creation He pledged Himself by writing in His book which is laid down with Him: My mercy prevails over my wrath. It was related by Muslim (also by al-Bukhari, an-Nasa'i and Ibn Majah).
**********
Kwanaki sai wucewa sukeyi babu alamar komawanta, da kanshi ya tafi gidan Grand Kadi ya faɗa masu abinda ke faruwa.
Mommy ta kirata tayi mata faɗa sosai kuma tace she is disappointed in her, duk tarbiyan da sukayi mata saida ta watsa masu kasa a cikin idanu.
Grand Kadi ne yace ayi mata uzuri gwara ajita bakinta. Washe gari suka tafi gidan gona inda Fadeela take, Naufal yaci shadda dakarkiya fari ɗinkin babban riga.
Yana tafe yana raha tareda full confidence yau zai tafi da matarsa. Kowa ya taru a falo, Big Daddy, Grand Kadi, Abba, Mommy, Mama sai kuma Anty Saudah.
Sannan saisu Deela da Naufal. Grand Kadi ya buɗe taro da addu’a sannan ya fara faɗin fa’idojin aure.
Daga nan sai Big Daddy ya fara magana akan batun auren su, Fadeela aka tambaya menene ainihin abinda ya faru tsakanin su.
Bata ɓoye komai ta fayyace musu komai, kowa salati ya rinka jerowa bayan ta gama wanda ita a lokacin kuka takeyi. Mama ce ta soma magana “Amma baki kyauta minba, aida kin faɗa min da ban rinka bashi abinci ba idan yazo”
Big Daddy yace yanzu babu wani sauran magana kawai Fadeela zata koma ɗakinta ta haihu a chan.
Nan take Deela ta barke da kuka tana sheshek’a. Kuka takeyi babu kakkatawa kamar zata haɗiye ranta.
Abba ne yace bai kamata Abi sarai ba, ayi mata hakuri tunda yanzu baifi saura wata ɗaya ta haihu ba.
Dagowa Naufal yayi zaiyi magana sai Anty ta kasteshi akan ya rufe masu baki, dole yayi shiru tunda babu sa’anshi a wajen.
Mommy ranta yayi bala’in baci saboda kawai ana sangartar da Deela ne, sau da dama mazajen wasu suna dukansu amma suke zaune ras, kawai dan an mare Deela za’a ce bazata zauna ba.
Ita tana ganin ana bama Fadeela dama ta raina shi ne. Haka dai aka kyale Fadeela ta cigaba da zama gidan Anty har Allah ya rabata da cikin lafiya.
Naufal ya nuna bacin ranshi a fili saboda ba’a gama magana ba ya fita daga falon ya koma cikin motarsa ya kifa Kanshi.
Kuka ya soma rizga wiwi saboda ya gaji, gashi yanzu Yasmeenah ta sakashi a gaba wai saidai ya aureta kuma bazai soma zancen wani aureba tunda Deela bata gidan.
Ita kuma Deela murna fal ranta ta samu nasara, Mommy magana sama sama take mata bayan abin ya faru saboda takaici. Koda suka kebe a ɗakin Deela karfin jikinta kawai ta tambaya sai sukayi shiru.
Kuka Fadeela ta somayi kana ta soma magana, “Mommy ki yafe min. Nasan na bata maki rai kuma zakice na watsa maki kasa a ido, but I promise you tarbiyan da kika min shiyasa yake kwaɗayin zama dani, please kiyi hakuri harna haihu tukun kafin ku mayar dani”
Mommy kawai kallon Deela takeyi yadda ta kafe, ba k’aramin abu zai mayar da ita haka, duk cikin yaran family itace batada riko ko naci akan abu, tunda ta nace akan haka to gaskiya ita kadai tasan ukuban datake fuskanta.
Murmushi ta sakar ma Deela saita matsa inda take ta soma bubbuga mata baya, babu komai baby, Allah ya sauke ki lafia”
“Amin summa Amin”
Bayan kwana biyu......
Naufal yana kwance a office ɗinshi abin duniya yayi mashi chunkoso, saiga Secretary ɗinshi ya shigo ya bashi wasu takardu.
Nan take ya haushi da faɗa wai baza’a barshi ya huta ba, daga nan yayi tsaki ya dauki jakarsa zai koma gida.
Yana isa yayi horn sau ɗaya, biyu, uku kafin mai gadi ya buɗe masa. Aiko nan ya soma masa masifa yana mai barazanar kora idan bai dauki hankali ba.
Yanzu yana Missing Fadeela to the extend daya zama very aggressive, kana kallonsa zai iya gaya maka magana san rai, idan kai mai hayaniya ne sai faɗa ta kaure maku.
Dakin Deela ya wuce wanda ya mayar nasa tun kwanaki, kwanciya yayi akan gado yana tunaninta ga kamshin turarenta ta Ko’ina. Abin bai isheshi ba dauko Chanel No 5 yayi ya fesa akan pillow kana ya runguma kamar ita ke wajen.
Turaren da idan ta saka da yakeji kamar ya kasheta yanzu shine abin so wajen shi. Yana kwance sai cikinsa ya fara kiran ciroma alamun yunwa, babu kidan da bayayi daga yori yori sai bumper to bumper.
Murmushi yayi mai kuna a rai kana yace a fili “Allah ya jikan Fadeela badan bata mutu ba, da yanzu tazo tana rok’ona naje naci abinci”
Saida ya huta gajiyarsa yayi sallah tukun kana ya wuce kitchen yana kallon me zai dafa, Indomie ya yanke shawaran ya dafa tunda yafi sauki.
Ya daura Indomie akan gas saiya fara kokarin buɗe Geisha. Cikin Kaudi ya karya karamin handle din abun dole yayi amfani da wuka.
Ya dukufa yana wannan ashe ya mance bai saka seasoning ba, maganar albasa da kayan miya bai taso ba saboda baima yi niyyar sakawa ba.
Kaurin konewa yaji gashi ko Geisha bai gama fafewa ba, yana zuwa da sauri ya taba zai sauke dama wajen electric ne. Nan take wuta ta fizgeshi, da sauri ya bar wajen saboda har cikin zuciyarshi yaji kamar za’a cire mashirai.
Gashi bai cire ba, ga shocking ga kone hannu dayayi, saida yadan huta kafin ya koma gashi yana gani Indomie ɗin yayi kurmus yayi bakin kirin.
Ko’ina kauri kamar ana gobara, kashe socket yayi saiya bar cikin kitchen ɗin bcs shi karin kanshi abin ya dame shi.
Buɗe fridge yayi zai dauki koda lemu ne amma wayam saboda ya cinye komai tas kuma bai siya wani ba, koda yaushe Deela tana hanyar kasuwa idan ta lura abincin su yayi kasa.
Haka ya sake hawa sama yaje bayi ya saka hannusa a cikin ruwa saboda yana masa zugi, gashi masu restaurant ɗin layinsu sun fara mashi sheda har sun daina cewa ‘Welcome Oga’ sai ‘Customer welcome’
Yanda yake sintiri gidan abinci ba kimansa bane a matsayinshi na namijin aure, daidai gwargwado Deela ta kare masa wannan hakkin saidai idan shine bayaso yaci.
Shikuma yanzu baya son yana haduwa da Yasmeenah saboda tana stressing ɗinshi akan ya nuna soyayyarsa yace zai aureta. Shikuma ya bata uzuri akan tabari matarsa ta haihu tukun.
Shi a locacin yanada tabbacin dole Deela ta dawo saboda batada wani excuse, sai yayi aurensa hankali kwance.
Kuma abu na biyu dayasa yake gudun ta face karta gane cewa Fadeela bata gidan a irin cikin zance haka kafin ta raina shi akan ya kasa rike gidansa.
Haka ya hakura yaje ya siyo kayan shayi wanda dama ya kare da bread, yana shiga kitchen zai daura ruwan zafi saiya tuna haɗuwarsu da rana, girgiza kai yayi ya bar wajen.
Bayi ya wuce ya ɗebo ruwan zafi kana ya soma dakan bread ɗinsa. Yaci yafi rabin babban leda amma cikinsa kamar an shafa ne. Wani matsananci yunwa yakeji saboda rabon dasu haɗu da abinci tun jiya da suka fita lunch da Yasmeenah.
Coke yayita sha sai yanzu, mukullin mota ya dauka yace gwara yaje gidansu kafin yunwa ya kashe shi.
Yana isa parking lot yaga Miemie da Khattab suna cikin mota ana dariya.
Haushi ya kamashi ya nufesu gadan gadan, su basu ma sani ba kawai suka ganshi a gabansu yana haki.
Su kuma abinda suke ma dariya shine Khattab yana bata labarin Lili, yanzu baya ɓoye mata komai tun wani rana da Lili ta kira a gaban Miemie har yayi sanadiyar dena masa magana na kwana biyu.
Yanzu baya ɓoye mata komai, duk shirmen data ke masa yake faɗa mata sai suyita dariya. Ita Miemie murna take ta samu wanda ta fita hauka.
Muryan Naufal sukaji wanda shiya saka suka bar dariya tareda tsayawa cak.
“Bana hanaku zance cikin mota ba?”
Khattab ne ya fito yana kokarin mika ma Naufal hannu su gaisa amma yaki bashi, mayar dasu cikin aljihu yayi kafin ya cigaba da magana cikin faɗa.
“Wannan wani irin abune? Idan kanwarka akema haka zakaji dadi? Koda yake bakada kanwa you wouldn’t know”
Juyawa yayi ya kalle inda Miemie take tsaye tana tura baki, “wuce ciki, ta ɗin an fasa”
Tura baki tayi tareda makale kafada tana bubbuga kafa a kasa, “Haba Yaya yanzu yazo fah!”
“Ni kike gaya ma haka, Karyan iskanci! Ni sa’anki ne ?Wallahi na sameki a wajen saina karya ki”
Saiya cire takalminsa ya nufa inda take, Khattab yana ganin za’a nakasa mashi Haskensa saiya ce mata ta tafi kafin taci dukan banza. Anan ta ruga tana faɗin “saina gaya ma Anty abinda kamin” ta faɗa tana kuka.
Yaji haushin da za’a kai kararsa wajen Deela amma babu yanda zaiyi. Juyawa yayi ya kalle Khattab, da sauri ya shige motarsa kafin Naufal yayi masa magana tareda mashi saida safe.
Shikuma saiya tafi cikin gida, yana shiga tareda sallama ya tarar da kowa a falo, as expected Deela a ciki ta amsa mashi.
Murmushi yayi saboda komai zatayi bai zai koreshi daga rayuwarta ba. Miemie ta soma korafi akan masifan da yayi mata. Anty Saudah ce ta zungureta da kafa akan tayi masu shiru.
Deela na daga gefe tana fere kankana da abarba. Zama yayi akan kujera harda canza masu chanel daga ZeeTv zuwa CNN, “Ya haka Mallam?” Anty Saudah tace.
Itama Deela taji haushin abin amma ta danne, dariya ya soma kafin yace, “news ne fah”
“Maza ka canza mana, kaje gidanka chan amma nan gidana ne”
Baiso ba ya canza masu, yana lura da yadda Deela taki kallonsa, yama mance yaushe rabon dayaga idonta. Kullum tana cikin kallon kasa kafin tabar wajen baki ɗaya.
“Miemie jeki dauko min plate matana ta saka min kankana” ya faɗa yana kallon Deela yaga yanayinta.
Babu musu tayi yadda yace, itama Deela ta zuba masa sosai yasha ya nare. Daga nan ta soma kokarin tashi tsaye, yanda takeyi komai da kyar gata da nawa asalinta.
Gashi ciki komai a hankali zakayi, sannan kafarta sun kumbura sunyi narka narka kamar doyar Benue. Duk tausayinta ya kamashi.
A hankali ta soma tafiya tayi hanyar ɗakinta saboda idanunsa yana takura mata. Bayan ta tashi Anty ta tambaye shi ko a kawo masa abinci, baiyi musu yace mata eh.
“Daka rike matarka da kyau ai bazaka rinka bin gida je kwaɗayi ba” Anty Saudah ta faɗa sai tayi hanyar kitchen.
Wani tunani ya faɗo mashi a rai ko ya auri Yasmeenah kurum koba komai zai rinka samun abinci a sauki.
Wayarsa yayi kara kuma wanda yakeso yayi magana da ita ne.
Yana dauka yaji kukanta sosai daga ɗayan ɓangaren, “da kyar nasha wajen Yaya Huzaifah” taketa nanatawa tana kuka.
“calm down meya faru? Talk to me please”
Cikin kuka ta fayyace masa abinda Huzaifah yayi mata, hankalin Naufal yayi mumunan baci. Hankalinsa ya kasa daukar abinda ya faru, ya kasa saisaita tunanin sa waje ɗaya.
Wai ace wanda zai aura akeso a lalata, gwara yayi gaggawa ya aureta kafin suyi mata mai gaba ɗaya, besides jiran meya keyi!
#NiDaDiyata
0 comments:
Post a Comment