Bayan ya gama cin abinci saiya yi masu sallama kana ya tafi gidan Mama inda Abba yake. A varenda ya iske Abba yana sauraron BBC hausa.
Sallama yayi mashi sannan sukayi gaisuwan mutunci. Shima zama yayi gefe suka cigaba daji tare. Bayan minti akalla ashirin ya wuce basuce komai ba.
Naufal shi addu’a yakeyi saboda yanaso Abba ya amsa batunsa babu gargada. Gyara murya yayi sai yayi adjusting zamansa, idonsa na kallon k’asa ya soma magana cikin ɗa’a.
“Dama nazo muyi magana ne” Ya faɗa. Shikuma Abba rage karar radio sa yayi ya mayar da hankalinsa wajen Naufal, baiyi magana ba illa kallonsa yana jiransa.
“Dama batun Yasmeenah ne nakeso aje gidansu domin ayi magana”da kyar ya karasa maganar muryanshi sai rawa yakeyi saboda yanda Abba ke kallonsa kur.
“Bangane ba?”
“Ina Nufin maganar auren mu” ya amsa. Ashe Mama tana jinsu sai tayi karab ta chapke.
“Ban gane ba?Kamar ya kana so ka kara aure? Yaushe yaushe kayi aure ne? Ni duk daukana shiririta ne naku na yaran zamani ashe abin yakai haka. Ko mace ɗaya ka kasa rikewa balle biyu” ta faɗa, kara fitowa tayi varenda ta jingina da bango saita soma magana.
“tuntuni ake fama dakai akan kayi aure amma kakiyi shine kake so a cikin shekara biyu kayi mata biyu koh? Bazai yiwu ba asha fate ranar sallah” ta cigaba da sababi. Abba ne ya tsinke ta tareda faɗin, “Inbaa aure shine za’a aure ki?”
“Ai tunda shi yake son abinsa gwara a kyaleshi, tunda yanada halin da zai rike su. Kawai addu’a za’a bisu dashi Allah ya kauda tsautsayi da fitina”
“Amin summa Amin” Mama tace daganan sai tayi shiru. Naufal yaji daɗi sosai saboda zai shiga sahun manyan mutane watau masu mata biyu.
Abba ya umurce shi akan a gayama iyayen Yasmeenah gobe zasu kai gaisuwan iyaye kuma da sadaki duk za’a haɗa.
Godiya yayi saiya bar gidan ya tafi hanyar gidansu Meenah, murna sosai tayi harda rungumarsa. Daga nan ta soma zuba mashi sabon shagwaba. Bai bar kofar gidansu sai wajen sha daya saura kadan.
Washe gari anyi komai an bada sadakinta a dubu dari biyu, sai kudin gaisuwa dubu hamsin. An sanya biki da tarewa nanda sati shida watau ana kyautata zaton idan Deela ta haihu da sati biyu.
Da Anty Saudah taji maganar ta rasa ta inda zata fara gayama Deela, zaunar da ita tayi ta fara mata nasiha akan hakuri. Ita dai Deela batasan meke faruwa ba amma tasha jinin jikinta.
Da Anty Saudah ta gaya mata an saka auren Naufal ne, wani bakin ciki taji sosai wanda idan tana tsaye ne zata iya faduwa don takaici.
Saisaita kanta tayi saita sunkuyar da kanta kasa saboda hawaye sun fara mamalo mata, “Anty Allah ya sanya alheri” abinda ta iya furtawa kenan.
A hankali ta tashi da niyyar zuwa kitchen saboda danwake take so taci amma yanzu ya fita daga ranta, kawai su Anty zatayi mawa.
Tafe take tana tunanin rashin alkawari irin na ɗa namiji. Sai dai in zama da kishiya ne baya damunta saboda kowa halinsa zai kwaceshi.
Haka taje tayi abinci duk ranta a jagule, tana gamawa ta wuce daki tareda rufe kanta ta soma kuka. Lallai duniya budurwar wawa ne, idan ka saka shi a ranka zai kaika ya baro.
Duk jindadin da kake ciki within seconds idan Allah yaso saiya mayar maka da tashin hankali.
Ita dai tasan cewa kowa da nasa jarabawar kuma tana rok’on Allah ya bata Ikon cin nata. Fatan ta baifi Allah yasa ta sauka lafia ba babu wani complications.
Yasa duk wani abu da Dr tace ta kiyaye daidai gwargwado tanayi. Dadin ta ɗaya shine tayi scanning taga gender ɗin abinda zata haifa. Yadda take da san gayu haka take son ta haifi mace domin ta rinka mata.
Cikin ikon Allah abinda ke cikin cikinta kenan, yanzu duk siyayyar da zatayi ko Naufal ɗin kalar pink ake siyowa kokuma white.
Sun siya su cradle, drawer, kaya daban daban komai dai na tanajin haihuwa. Mama ta saka an sak’a mata showel masu kyan gaske da kuma rigar sanyi na yara.
Ita kuma Anty super ta dinka mata na fitar suna, su kuma su Bilqees, Abla da Amatullah da Miemie anko sukayi wani material purple mai ratsan lemon green.
Shikuma Naufal yayi ma Deela kala uku na fitar suna, sai kuma seti biyu na akwati da kit na faɗar kishiya. Sannan yayi ma kannasa kala ɗaya tareda iyayen sa duka.
Ita kuma Yasmeenah ce masa tayi ya bata kudi ta siya lefenta da kanta tunda ita zata saka abinta, dama zataje Dubai siyan ma kanta kayan dakine. Tana chan tana Siyayya saita rinka kiransa akan kuɗi ya kare ya gaggauta aiko mata.
Idan yayi mata korafi saita soma sababi tana cewa, ‘To keep a classy woman like her is not easy’ idan ta fada irin wannan abu yana mamakin ta sosai kamar ba ita ke rok’on sa ya aureta ba.
Kuma zancen classy da take magana, da zata ga matarshi da batace komai ba. Tun kafin aje Ko’ina har ya fara gajiya da yawan korafin ta.
Ita kuma murna fal ranta ta samu mai kuɗi gashi kyakyawa zata aura. Siyayya takeyi son ranta saboda tanaso bikinta ya jijiga Instagram.
Events kala shida zatayi, za’a buɗe da Fulani day, Korean Day saboda tana bala’in san film dinsu, sannan Kamu, Mother’s Day, Bridal shower da kuma Dinner.
Duk dinkinta a chan tayi, wedding gown dinta fari wanda zata saka ranar dinner Donatella Versace ta ɗinka mata.
Burinta ya cika saboda komai yana zuwa mata yadda take so. Yanzu matsalar ta ɗaya shine yadda zata fitar da matarshi daga cikin gidan.
Wani abin takaici shine ankai mata kaya jere cikin gida sai akace ɗakinta yana downstairs saboda duk na upstairs an cika shi. Abin yayi mata ciwo sosai amma ta kwantar da hankalinta saboda Hostile take over zatayi wa matarsa.
Dole ayi juyin mulki, duk wani abu datake controlling zata daina ne, Karyan iskanci takeyi!
Shikuma Mama ta gargade shi akan kada ya kuskura ya tada Deela daga cikin ɗakunan ta. Dama dakuna uku ke sama, kuma Deela na cikin 2 sai Naufal ɗaya.
A kasa kuma akwai ɗakuna biyu anan Yasmeenah zata zauna, kawai dai dakunan manya ne ba laifi kuma sunada bayinsu.
Batun kitchen kuwa lundary room aka kira carpenter yayi mata su shelves sannan aka kira plumber yayi sink da sauran su.
Dayake d’akin karami ne bazata ji dadin kitchen ɗinba, Komai a marmaste zatayi. Bazata wata ya kamar yadda Deela zata baza tabarma a kasa ba taji dadi.
Dama komai idan ba’a yi dakai ba bazaka ji daɗin abin ba. Dama shi Naufal ya tsara rayuwarsa da mace ɗaya ne yasa zuwan Meenah kamar takura masa ne.
Yasmeenah ta dawo daga Dubai shake da kaya zata kaima dangin mijinta, fitted gown material ta saka Ja da rastin silver wanda ya dame ta. sai tayi wrapping kanta da karamin gyale irin na Arabs.
Hannayenta kuwa wasu kwabɗa kwabɗan zabbai ne da warwazo.
Takalmin nan dai mai tsawo tareda igiyoyi ke kafarta zata gaida In-laws. Su sun saba a turai, soyayya kawai yaro yakeyi da yarinya zai kaita gidansu ta gaishe da iyayen shi amma sam Naufal yaki.
Ita kawai bataso tayi bakin jini wajen su yasa ta siyo masu turare zata kai masu. Bata sha wani wuya wajen gane gidan ba saboda kowa yasan architect.
Ta fara zuwa wajen Mama kafin taje taga Miemie saboda yadda yake maganar ta. Koda akayi mata iso wajen Mama akan tayi bakuwa, mamaki ya kamata da taga yarinya zaune tana jiran ta.
Gaisuwan yan bariki tayi ma Mama Irin,”Sannu Mama, ya kike?” mamaki ya bayyana a fuskar Mama karara wanda ya hanata amsawa.
“Yarinya daga ina?”
Murmushi Meenah tayi kana ta fara magana cikin salo, “Baki ganeni ba koh?”
“Ina zan ganeki baiwar Allah bayan ban sanki ba”
Sosa gemu tayi tana dariya harda makela kafada, ita kuma Mama haushi ya kamata saboda bata Santa ba gashi tazo falon ta tana mata salo.
“Mama nice fah Yasmeenah” ta faɗa tana dariya.
Kallon hadarin kaji Mama tayi mata sai tace, “lafiya kika zo min gida” jikin Meenah yayi sanyi amma ta dake ta soma magana, “Dama nace bari nazo na gaishe Kine, dama nayi tafiya ne shine nace bari na kawo maki wannan”
“toh fah!”Mama tace tana mata wani kallo, irin kallon you’re not welcome. Gyara zama tayi da kyau tana fuskantar saita soma magana idanunta babu wasa a cikin su.
“Mu fah a al’ada tun kaka da kakanni bamu saba budurwa taje gidan saurayi ba gaisuwa. Asali sai an kaita gidanta dangin miji zasu san fuskarta.”
Kara gyara zama tayi ta kalle Meenah da kyau kana ta cigaba da magana fuska a murtuke “koh matar Naufal watau Fadeela bamu sakata a ido ba, bata bi gida gida tana neman fada. Amma kince tsaraba kika kawo min koh? Toh ajiye kan table”
Daga nan sai Mama ta mayar da hankalinta kan SunnaTV dake aiki. Gwiwa babu kwari ta aikata abinda akace saita ce ma Mama “sai anjima”
“Yauwa mu jima da yawa” ta amsa ko kallon gefenta batayi ba. Tunda Yasmeenah take ba’a taba mata wani abu daya taɓa taba kamar yau. Ranta a jagule ta shiga motarta tayi hanyar gidansu kafin taje wajen Anty Saudah ayi mata wanda yafi wannan.
Ita kuma Mama ganin Ikon Allah ta tsaya yi wai budurwar da zai auro kenan, duk fake lashes da fake hair. Gashi sai yauki takeyi kamar danyen kuɓewa.
Naufal ta kira tayi mashi tas, shidai bata hakuri ya rinka yi kuma yayi mata alkawarin Yasmeenah zata canza yanayin shigar ta.
*********
Kwance tashi an kai satin haihuwar Deela, kullum cikin tambayarta akeyi ko tana jin wani ciwo amma sai tace masu ah ah.
Ita kuma sam bata jin komai saidai kafarta daya daɗe da kumbura, sau ɗaya bayanta yayi mata ciwo kuma cikin darene kafin safe ya daina yasa bata faɗi ba.
Dayake kitchen ɗin Anty akwai kananan kwari da kyankyasai, sai Deela ta saka maganin kashe su daga nan ta fita da duk wani kayan kitchen da Anty ta mallaka zata wanke.
Babu yanda Mai aikin Anty da ita kanta Anty ɗin basu hanata ba amma ta kafe, acewarta ai akan kujera zata zauna kuma hannunta suna aiki sosai.
Da taimakon Miemie sukayi tas tareda mopping kitchen komai yayi charasras. Bayan nan sai Deela ta haɗa masu dambun tsaki wanda yasha alayyahu, yakuwa, gyada, kashi, nama da sauran su.
Kowa yaji daɗin abin saboda a babban paranti aka zuba masu, Abba da Naufal aka zuba masu tare tun dayake ya zo kawo masu katin daurin aurene saiya taras an gama, shine yace bari yaci mai dadi kafin ya tafi.
Su kuma su Anty da Deela tareda Miemie a round tray Babba suka saka nasu, sannan ga kakiɗi a gefe suna aunawa ciki.
Bayan kowa yayi nat ya nare, Naufal ya tafi itama Deela ta kwanta. Wajen sha ɗayan dare sai bayanta ya rike yana mata wani irin zafi.
Zufa ya rinka yankomata ta ko’ina, dolenta ta sauko daga kan gado tana addu’a tareda safa da marwa cikin tsakar ɗaki tareda bankare baya.
Zafi sai karuwa yakeyi wata sa’in kamar ana tsikarinta. Saidai kawai ta tafa hannunta tareda rankamo salati tanayi tana sukurkurta gashin kanta.
Hawaye takeyi tana kokarin matse bakinta saboda bataso ta tashi kowa, wajen ɗaya da rabi sai ruwa ya fara fitowa ta kasanta.
Aikuwa duk wani dauriya datake yi ta daina, kwala ma Anty Saudah kira tayi. Dayake ɗakin Miemie yafi kusa so ita ta riga zuwa.
Abinka da tiles koina santsi yake gashi ɗakin sharkap. Nan take Anty ta haɗo mata kayan haihuwa kamar su zannuwa, auduga, detol, glucose, kayan jariri, pampers, feeding bottle etc.
Ita kuma Miemie tana daga gefenta ta riketa tana kuka, Abba yanada bakin kofa ya haɗe hannu a kirji yana tausayinta. Sai ya tuna da Naufal, zuwa yayi ya dauko wayarsa domin ya kirasa amma yaji switch off.
Ranshi yayi matukar baci amma babu yanda zaiyi, shikuma Naufal daya kaima Yasmeenah katin aure sai Aminu ya kirashi, karban wayar tayi ta kashe.
Acewarta idan suna tare dole yayi respecting ɗinta ya kashe wayarsa, toh tun daga lokacin bai tuna ya kunna ba.
Abba ya tuka motar da aka kai Deela wanda a locacin kuka kawai takeyi, Anty Saudah na yin mata sannu ita kuma Miemie na tayata da kuka tareda fiffita.
Nurses sun karbeta an wuce da ita maternity ward, saidai ba yanzu zata haihu ba zata iya kai 7 ko 8 na safe. Abba bai kira kowa ba yana jiran asuba tayi tukun.
Anty Saudah alwala ta dauro tayi sallah tareda neman mata easy delivery, ita kuma Miemie addu’o’i kawai take to fah mata.
Cikin awa kadan ta canza kaminta sai fizge fizge takeyi tana jefa hannu gashi kuma bayanta kamar zai balle.
4:53am.....
Har locacin bata haihu ba illa bakin azabar data kesha, ta kama bakin gado da jikin Miemie harta gaji. Gabaki daya babu wanda ya runsta a cikinsu. Kowa tausayinta yakeyi ga uwa uba mijinta baya wajen.
Bayan sunyi sallah sai Abba ya kira su Grand Kadi ya sanar dasu halin da ake ciki. Cikin minti talatin suka garzayo tunda safe ne babu hold-up.
Mommy na ganin halinda Deela take ciki ta fashe da kuka, Daddy ne ya kwaɓeta akan Fadeela tafi bukatar adduarta akan kukanta. Nan ta shiga mata sannu tana hadawa addu’a.
Har wajen bakwai saura wayar Naufal baya shiga, Abba ne da kansa ya tafi gidansa yaji ko lafia. Kwance ya riske Naufal a falo yana sharara barci.
Daga alamu tun daya dawo daga masallaci yakeyi. Zungurinsa yayi saiya soma masa magana , “Kai haka zaka bar gidan kayi ta barci sai an shigo anyi maku sata”
Naufal a firgice ya tashi dayaji muryan Abbanshi da safe haka cikin gidansa. Waige-waige ya somayi yana kokarin tantance ko mafarki yakeyi.
Murje idonsa yayi saiya ga Abbanshi da gaske ke kallonsa, “Dama matarka muka kai asibiti wajen ɗayan dare, amma dayake ka kashi wayarka bazaka sani ba” Abba yana faɗi ya nufa hanyar kofa.
A fusace ya figi mukullin motarsa wanda ke kan centre table yabi sahun Abba. Three quater baki ke jikinsa da riga mai guntun hannu amma bai dameshi ba.
Haka ya soma tuki yana tunanin irin pain ɗin datake ciki. Yana isa gaban asibiti yaga su Anty Saudah da Miemie anyi charko charko ana kuka.
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
#YarinyaMaiDimples
[15/2 22:30] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 32 ✨✨✨
It was narrated from Hakim bin Muawiyah, from his father, that a man asked the Prophet(): "What are the right of the woman over her husband?" He said: "That he should feed her as he feeds himself and clothe her as he clothes himself; he should not strike her on the face nor disfigure her, and he should not abandon her except in the house (as a form of discipline)." (Hassan)
************
Karasawa yayi da gudu tareda damkar Miemie yana tambayarta koh lafia. Cikin kuka ta faɗa mashi cewa Fadeela tana cikin labour gadan gadan yanzu.
Anan fa hankalin sa yadan kwanta saboda duk zatonsa mutuwa tayi. Sakin Miemie yayi saiya karasa cikin asibiti, kukan Deela yaji tun kafin ya karasa wajen.
Nurse Anisa take karban haihuwar, middle age woman mai akalla shekaru 35 a duniya. Shekarun ta wajen goma da aure amma bata taɓa koda ɓatan wata ba.
Yasa idan aka kawo mai naguda take jagora tayi, cikin ikon Allah idan tana wajen akan samu Successful delivery.
Da karfin tsiya ya tura kofan har saida ya buɗe, nurses ne suka zo da sauri akan ya fita amma ya kafe babu inda zashi.
An kawo mashi sanitizer dasu hand gloves sai aka barshi a wajen, zuwa yayi da sauri kan gadon datake ya soma mata sannu.
Tausayinta ya kamashi sosai saboda bazai iya kwatanta irin ciwon dake ciba, rike mata hannu yayi yana mata addu’a.
Suna cikin haka tareda taimakon Doctor saita haifa baby girl ɗinta wajen 7:45am. Da sauri ya karba babyn ya runguma tun kafin a gogeta. Karin sallah ya soma yi mata tareda addu’a.
Ita kuma Deela tana daga kwance tana numfashi kadan kadan, an karba babyn akayi mata abinda ya dace sai aka bashi ya fita domin ya nuna masu.
Babyn kyakyawa fara sol kamar Deela saidai fuskarta sak irin na Naufal harda kalan idanun. Yana tafe inda su Mama suke fuskarshi zallan annuri yana walwala.
Mai aikin Mommy watau Anty Husna ta soma guda tana faɗin anyi mata kishiya. Kowa yaso ɗiyar kuma ɗaya bayan daya suketa dauka ana mata addu’a.
Koda aka bama Miemie tace su gama dauka saboda itace karshe, duk sun dauka daga ABBA da Grand Kadi kuma tasha addu’a daidai gwargwado.
Daga nan sai Miemie ta dauka ta fara kallon ta, har ranta take jin san yarinyar komai about her is so innocent and fresh.
Shima Naufal yanada ga gefe yana wasa da ita, baiji kunyar surikansa ko irin kunyar ɗiyar fari. Mama ce tace a kawo ta za’a bata glucose tasha.
Daga shi har Miemie basu so ba amma babu yanda za ayi. Ana cikin haka saiga Deela an fito da ita tana taka kafa da kyar, ji yake kamar yaje ya dauketa amma kawai ya barshi.
Kowa sannu yake mata har aka kaita ɗakin da zata huta kafin a sallame su. Anje an kwantar da ita tareda kara mata ruwa, su Doctor saida suka jinjina kokarin ta.
Tana kwance kowa yana cikin dakin, Anty Saudah ta haɗa mata ruwan shayi cikin Katon kofi wanda yasha madara.
Kamar madaci taji amma dole tasha, ita har locacin bata kalli meta haifa ba saboda kunyar iyaye. Tadai san kawai mace ne ɗiyarta, gashi babyn sai barci takeyi balle tayi kuka ta sake jin muryanta.
Tana kwance a haka barci mai dadi ya dauketa, bata farka ba sai wajen sha ɗaya lokacin ruwan da ake kara mata ya kare. A hankali ta buɗe idonta taga yan barka birjik cikin ɗakin saboda baima isa mutane ba.
Su Jawahir ana rike da babyn lokacin, “Malama saiki tashi ki bata Nono tun dazu sai wani barci kikeyi kamar wanda tayi aikin wahala” ta faɗa tana dariya.
Sinna kanta kasa tayi batace mata komai ba saboda tana bala’in kunyar su Mama da Anty Saudah, “Woow Maman Baby” Jawahir tayi exclaiming saita koma gadon inda Deela take domin su gana.
Su kuma su Naufal sunci Abinci sunyi nat saboda Bilqees da Abla sun kawo breakfast daya isa kowa. Doctor ta kira Naufal yayi signing takardun sallama.
Nurse Anisa tayi masu sallama kuma tace zata rinka zuwa duba su bcs little one tanada shiga rai sosai.
Ya basu kudi sosai fiye da bills ɗin haihuwa kuma an umarce Deela ta dawo nanda kwana biyu saboda aga lafiyan jikinta. Ita kuma Mai aikin Anty ta daura garwan ruwan zafi ana jiran Deela ta dawo tayi wanka.
Darbejiya masu kyau da kwari aka tsinko kuma saida ruwan ya tausa sau uku kafin aka juye a wani katon baho. Hajia Rabi matar Big Daddy tayi mata wankar da kanta.
Tun Deela na ihu don azaba harta hakura ta daina. Nishi sama sama kawai takeyi, ita kuma Mama tayima baby wanka sau bakwai tareda gyarata tsaf ta saka mata kaya.
Deela na fitowa daga wanka Jawahir ta taimaka mata ta shirya tsaf cikin wani atampha kore dinkin a shape na riga da zani. Tayi ras abinta sai kamshi takeyi sabuwar mai jego.
Ta kowane bangare nuna mata kulawa akeyi, ko su samɗa da Jumaymah sun zo. Ita kuma Mansura bata samu daman zuwa ba saboda tana Abuja.
An gama abincin rana inda akan dafa tuwan semovita da miyan karkashi wanda aka barbaɗa yaji da kuma man shanu. Ga nama jaɓa jaɓa saboda kowane loma saika hada dashi.
Ga kuma peppersoup din kayan ciki a gefe yana jiranta, sai kuma kunun kanwa mai zafin gaske wanda yasha kayan kamshi. Kafewa tayi wai yayi mata yawa saboda idan taci zatayi katon ciki.
Mommy ta zare mata ido dolenta taci tana tura baki, shima Naufal yana daga wajen garden yan cin nashi abinci. Jefi jefi yake aikawa akai masa ɗiyar sa.
Son duniya ya daura mata da Mamanta. Shi ya tabbata yanzu Deela itace soulmate dinshi, burinsa bai wuce Deela ta yarda ta koma suyi rainon babyn tare cikin kwanciyar hankali babu mai takura masu.
Kuma gashi har yanzu baiyi mata magana ido da ido ba, Waya ne ya kira kuma batayi wani cooperating ba. Bayan ya tambaye ta karfin jikinta saita amsa bata sake ce abinda yafi ‘uhm ko uhm uhm ba’
Shi dai yaketa watsa mata kalamai yana faɗin irin kewarta dayake yi. Da taga zancen sa bashida niyyar karewa sai tace yan barka sunzo zatayi attending masu, daga nan saita kashe wayar.
Ita kuma Yasmeenah ya kirata ya gaya mata sau ɗaya zasu rinka waya kuma da daddare ne saboda yanzu his family needs him. Abin yayi mata ciwo sosai amma saita danne.
Congratulations tayi mashi tace ya tura mata pictures,ko sau ɗaya baiyi crossing ranta akan taje barka ba. Laila kawarta ta kitsa mata akan taje kafin Deela ta kullaceta.
Tunda bikinsu bai wuce saura sati biyu ba so itama family ce, ita Laila abinda yasa tace haka bai fi yanda take mutuwar san yara ba.
Yasmeenah taje stores ta ciko leda wajen uku da kaya na yara da niyyar kaiwa ranar suna.
********
Nurse Anisa takan zo duk safe kafin ta wuce aiki domin ta duba lafiyan Deela dana baby. Ko ranar daya kamata ayi ma jaririya allura ita tazo ta dauketa sukaje tareda Miemie suka dawo.
Matar mutunci kowa na yaba yadda takeda halin kwarai, yanzu kawance ya kullu sosai tsakaninta da Deela.
Wajen taran dare jajibarin suna, gida ya cika da yan suna daga Ko’ina duk anzo tayasu murna. Ga raguna manya manya wanda suka amsa sunarsu guda biyu sai kuka sukeyi.
Abinci kuwa, Mommy ta dauki nauyin girka komai daga catering company ɗinta. Shi tuntuni ya saka ma yarinya suna saboda masu printing su Memo da paper bags. Saidai bai faɗi ba.
Ita kuma Deela ta goge sosai tayi fresh kamar ta rinka haihuwa koda yaushe. Tana wanka da ruwan zafi sau biyu yadda ya dace kuma an fara koya mata yanda zata rinka ma kanta.
A nesa yake ganinta kuma yana kallon ta yana hadiye miyau, ya lura hankalinta kwance bata ko missn ɗinshi, ba kamar yadda yake kwad’ayi su zauna tare ba.
Gashi tana shan kunun kanwa sosai yasa kirjinta ya cika da dukiyar fulani. yarinyar ta bata rasa abinci, ci takeyi sosai saita ture. Itama tayi murmur tayi yar kiba, very chubby ga kuma fara’a. Sannan dimples dinta waje biyu sun lotsa sosai, gata kuma da gashi tunda ta biyo babanta.
Tana zaune a bakin gado tana shayar da yarinyar ta, yanda yarinyar keshan Mama yana karasa ma Deela taji sonta cikin ranta. Murmushi kawai take yi saboda soyayyarta ya mamaye mata rai.
Ita yanzu batada wani farin ciki daya wuce ɗiyarta, duk wani san duniya ta daura mata. Tana ganin tafi Maman sharukhan a Kabbi Khushi Kabbi Gham san yaro. Dukda ita wancan daga gate tana jin alamar shigowarsa.
Tana cikin haka sai ga Naufal ya shigo, sallama yayi tareda saukar mata murmushi. Fuskanta babu yabo babu fallasa ta amsa mashi.
Jawo kujerar mirror yayi saiya zauna dab da ita ya watsa mata ido kur. Sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da ɗiyarta.
“Baby Yanzu kin dena kallona” ya faɗa. Ita kuma bata amsa ba saboda bama tada niyyar magana.
Mika mata hannu alamar ta mik’a masa yarsa. Babu musu ta bashi, ita jaririyar harta soma barci dama abinda takeyi kenan all the time.
“Yarinya mai kamada the gorgeous Fadeela” ya faɗa yana kallon ta. Murmushi tayi kadan saita kauda fuskarta.shima murmushi yayi wanda ya bayyana kwarjininsa da kyau.
Riko hannun Deela yayi sai tayi kokarin kwacewa amma ta kasa, “Baby kiyi hakuri da abinda nayi maki, nasan ban kyauta ba amma inaso ki yafe min. Rabon kwado baya wuce cikin ruwa, Allah ya kaddara min auren nan tun kafin nazo duniya, please inaso mu runguma kaddara mu mance da differences dinmu”
Gyara zama yayi sosai saiya tallabo ma Deela gemu kana ya cigaba da magana. “Haba uwargidan Naufal, uwar gida zuciyar miji, uwar gida sarautar mata,uwar gida lantarkin gida, uwar gida babu kamar ki”
“I know you are a strong woman, Koda yaushe kina kokarin ki ɓoye damuwar ki koda yana cin maki rai. Kuma nasan cewa deep down you don’t hate me, kawai you miss me ne.”
“Nima wallahi i miss you, gashi yanzu babyn mu tazo. Ko ba zakiyi don ni ba Please kiyi saboda Pha’eexah”
Daga ido tayi tareda murmushi saboda yanzu taji sunar yarinyar, Daga mata gira yayi yana dariya. “Eh na saka mata Pha’eexah, please ki dawo mu raineta tare cikin gidan mu, Baby i love you so much”
Matse mata hannu yayi cikin kulawa yana mata wani irin kallo mai rikitarwa, gashi idanunsa sun canza kamanni, kana gani kasan yana cikin tashin hankali ne, “Baby Karki Bari kishi ya raba mu, kinsan cewa kece kika fara nuna min asalin soyayya, kece farkon matana a duniya kuma in sha Allah harda aljanna”
“Gashi kuma kin haifar min wannan Beautiful Angel mai kamada ke, please i need my family back. Baki lura you are my first everything bane, Komai dazai faru dani second ne saboda kin riga kinyi min komai and I will forever cherish you for that. Baby bakiga Allah ya riga ya karrama kiba tareda baki girma, girma fah baiwa ce! Please i will do anything Dan Allah ki yarda kawai ki dawo wajena”
“Banaso kuyi min nisa keda Pha’eexah, kinason na canza maki motane ko kayan daki? Just name it baby please”
Ita kuma a dikilce tace, “I like my furnitures and my car, thanks” saita juya fuskanta.
Dukawa kasa yayi saiya daura kanshi akan cinyarta, “Baby please ki dawo wajena, ina shan wahalar rashin ki, please gobe ko jibi sai ki dawo koh?” saiya duba yaga yanayinta.
“Okay zan yi tunani” ta faɗa
Da sauri ya dago tareda rungumota, ingijeshi tayi saita ce, “Sakeni Mallam, baka lura jego nakeyi ba halan”
Suna cikin haka sai ga Miemie tazo rike da pillow tana hamma daga alamu barci takeso tayi. Dama tun haihuwar Pha’eexah take kwana tareda su.
Patting bayan Deela yayi saiya sumbace yarsa a goshi kana ya tafi, yana tafe yana annashuwa bcs he is hopeful nanda Kwana biyu zata dawo.
Ita kuma Deela tana tunani gwara ta koma, ko babu komai yanzu akwai rabo tsakanin Su. Bazata yarda wata yar bariki ba ta rainan mata yarinya.
Kuma bazata bari azo a kwace Naufal haka kurum ba, ta gama taming dinshi, ta nuna mashi yadda ake Soyayya shine za’a rabata dashi.
Zata koma ɗakinta kuma zata zauna, zata nuna mashi ta fita daban cikin sauran mata.
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
~Yarinya Mai Dimples~©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 33 ✨✨✨
~LESSON~
Life comes with both happiness and sadness. Learn to be patient when sad and be grateful when happy. Allah will reward you and elevate your status.
It was narrated from Hafsah, the wife of the Prophet (pbuh) that The Prophet (pbuh) said: "Going to jumu'ah is obligatory for everyone who has reached the age of puberty.'" (Sahih)
**********
Ranar Suna...
Tun wajen karfe hudu na asuba as usual aka daura garwan ruwan wanka, wajen biyar da yankai ruwan yayi tausa uku aka sauke ma Deela.
Anty Saudah ta tada ta locacin data tashi sallar asuba, as usual Miemie ne mai rike Pha’eexah idan Deela ta shiga wanka har saita fito. Yau da kanta tayi wanka yasa saida ta dauki lokaci, abinda akeyi na minti talatin saida tayi wajen awa daya, tana fitowa little one tayi kuka ta gaji tanaso taci abinci.
Zama tayi gefen gado ta soma shayar da ita, tana tunanin sun kusa komawa inda ya dace watau asalin gidansu. Jawahir kawai take jira ta iso saita faɗa mata cewa gobe takeson komawa tunda Mommy bazata zo gidan suna ba irin yadda al’adan Mallam Bahaushe yake.
Shikuma yayi radin sunar Pha’eexah a masallaci tareda gayyata walima karfe biyun rana. Kowa yayi masa fatan alheri tareda addu’a, yaji daɗi sosai yanda aka nuna masa kulawa saboda limamin masjid ɗin yayi alkawarin zuwa.
Wasu tun daga nan suka soma kiransa da Abu_Pha’eexah kuma yaji daɗin abin sosai. Kiran Deela yayi after that ya faɗa mata, itama sanya alheri tayi kana suka cigaba da magana.
Yau tayi mashi magana daidai gwargwado, kuma shima abin ya burgeshi sosai domin har cemata yayi suyi breakfast tare.
Babu musu wajen 7am ta saka aka kai kayan abinci ɗakin Abba saita kirashi a waya yazo suci.
Kunun kanwa ta zuba masu da kosai, shi bawai yana san abin bane amma tunda Deela tanaci kuma bata mutu ba toh shima zai sha.
Bata wani sha sosai ba dama batasan cin abinci tun asalinta. Yayi mata magana saita ce masa ta koshi ne, wasa da hannun Pha’eexah takeyi while ita tana tsotso.
Wayar Anty Saudah suka gani akan ya saka Deela taci abinci kokuma Deelan ta fito haka an fasa breakfast ɗin tare. Mika ma Deela kokon yayi amma taki karba.
Asalima murguda masa baki tayi saita kawar da fuskanta gefe, rok’o yakeyi amma ta kafe akan bazata shaba. Haka ya hakura saiya sha harda nata kason saboda idan Anty ta riske abinci cikin kwano zata saɓa masu.
Shi bai damu idan anyi mashi faɗa ba, kawai ya daukin ma kansa alkawari ne akan Fadeela ta daina zubar da hawayen takaici saina farin ciki.
Yanaci yana zaro ido gashi ko rabi bai shanye ba, tun Deela tana matse dariya bata san sanda ta bushe tayi a bayyane ba. Kallon ta yakeyi yana jin dadin yadda take nishaɗi.
Murna fal ransa saboda koba komai shine yasata dariya, “this is beginning of a new era, Yanzu zaki rinka samun farin ciki sosai” shi duk zatonsa tunanin zuci yayi ashe ya faɗa a fili kuma taji.
Gimste dariyar tayi ta cigaba da kallon yadda yake shan kokon cikin wahala, sam batayi tunanin taimakonshi ba saboda dama tana so tayi watching weight ɗinta amma babu dama.
Ya gama kenan saiga Anty ta shigo kamar an aiko ta, tana ganin kwanon empty sai tayi murmushi kana ta tafi. Deela still murguda masa baki tayi tana masa gwalo.
“baby kin koya rashin kunya koh?” Ya faɗa tareda janyo ta jikinsa. Tureshi tayi saita matsa baya kana tace, “Sake ni mana, jego nakeyi”
“Shikenan bazan rike matana ba domin tana wani jego”
“Eh” saita wulla masa idanu.
“Oh really! Ni da matana.... Okay bari naga wanda zai hanani” saiya nufota gadan gadan. Jan baya takeyi shikuma yana mata smug face yana matsawa kusa da ita.
Dataga babu sarki sai Allah saita mintsili Pha’eexah dake kwance tana jin daɗin barcin ta. Tsandara ihu tayi sai yayi sanadiyar kaste mashi hanzari, kallon babyn dake kuka ido rufe sukeyi.
Daga na sai babyn ta buɗe ido tana kokarin ganin waya tada ta, bushewa da dariya sukayi saboda it was funny.
“Allah ya soki, yau danayi maganin rashin kunyarki. Ki gode ma Pha’eexah”
“Allah dai ya soka saboda nidai bani tsoron ka” tana maganar ta sunguma diyarta suka bar ɗakin a guje.
“Ai da kin tsaya mana” ya faɗa yana dariya.
12pm.......
Mutane sun fara hallara, Mommy ta aiko da duk wani abinci da za ayi amfani dashi. Daga su White rice, coconut rice, fried rice, tuwan shinkafa, sakwara, alale, samosa, spring rolls, doughnuts, salad da coslow etc.
Drinks Kuma akwai na gargajiya kamarsu xobo rodo, ginger, kunun aya dana zaki, sai kuma anyi Punch, milk shake Gasu katon katon ɗin Coke dasu fanta.
Su Miemie anci kwalliya kamar za’a fashe domin kyau, ankon da suka ɗinka suka saka yanzu kafin anjima kowa ta canza zuwa personal ɗinsa.
Fadeela cikin atamphan da Anty ta ɗinka mata take, ɗinkin yasha aiki da stones kowa yabawa yakeyi. Baby Pha’eexah kuma mai green eyes ta saka riga da skirt fari sol.
Daga ita har Mamanta sun saka gwalagwalai na yan kunne, sarka da abin hannu. Su Samɗa anzo ana tayata murna.
Sosai kawayen Deela sunyi mata kara, kusan kullum suna tafe cikin so su duba lafianta. Itama Anty Anisa ma haka saidai yau bata iso da wuri saboda tanada wani uzuri.
Samɗa baby clothes masu tsadar gaske ta kawo mata guda uku, sai sinkin sabulun wanka dakuma na wanki biyu biyu.
Itakuma jumaimah Dankunnen gold ta kawo ma baby,Mansura kuwa dayake ta iya ɗinka su duvet da throw pillows. Shi ta ɗinka ma baby Pha’eexah na yara.
Sauran kawayen Deela duk sunzo kuma sunyi mata kara, yau taga amfanin mutunci.
Wulla ma Mansura waya tayi saita ce, “Kashe mana hotuna masu kyau sosai NI Da Diyata”
“Wooooo! Masu yara, badai dani kikeyi ba” Samɗa ta faɗi tana dariya. Deela bata amsa ba illa mayar da hankalinta kan hoton da ake mata.
Ita kuma Yasmeenah saura sati ɗaya ta mallake Naufal, tasha gyaran amare harta koshi. So take idan Naufal yaji yadda take saiya manta da tsohuwar matansa.
Gashi fatanta yasha coiling saboda yayi farin gaske, dama Deela ta fita haske amma yanzu ina ai wutsiyar ragumi yayi nesa da kasa.
Wani pink lace ta dauko wanda akayi mashi ɗinkin gown fitted, saita haɗashi da blue fashion earrings da Kuma su abin hannu. Hajjoe Makeovers ta kira suyi mata saboda bata so ‘yan suna su rainata.
Komai nata is ready kawai tana jira la’asar yayine sai Lubna da Laila su rakata. Ta kira Naufal taji inda yake saiya ce mata yana gidansu saboda anan za ayi taron suna.
Toh anan taji inda Deela take dama tanata zulumi saboda bai taɓa faɗa mata location ba. Yanzu sai dai kawai yaji taje saboda bata faɗa mashi ba. Tana so ta nuna mashi ita mace ta gari ne tunda ta ajiye kishinta zata ganin yarsa.
Shiko Khattab yaci kwalliya kamar shine uban jaririya, program ɗin wajen biyu za’a fara amma shi tun ɗaya yazo saboda ya samu su zanta da Haskensa.
Yanzu yana jira a gama taro sai ya tambaya Naufal auren kanwarsa. Ya riga ya gaya ma Mommy ɗinsa komai akan Miemie kuma tayi naam da batun sa.
Ita yanzu komai na Lili ya isheta, fitsari sosai takeyi mata yasa itama ta mara ma Khattab baya ya auro wanda yake so.
Kuma cikin ruwan sanyi zata canza ma Daddyn Khattab ra’ayinsa. By the time idon Lili zai buɗe lokacin it will be too late.
2 pm...
Su yan uwan Fadeela sun iso, wasu daga chan kauyen su watau shira wasu kuma daga cikin Bauchi da sauran garuruwa.
Anata walwala da annashuwa saboda yafi daurin auren Deela armashi. Amarya ta canza zuwa shadda blue dayasha aiki gaba da baya kuma daga sama har kasa.
Gashi Mansura ta tsala mata kwalliya da kuma gwargwaro style, kowa burgeshi takeyi saboda kana ganinta kaga yar gata.
Mitsi Mitsi kadan Naufal zai kirata yaji lafiyarta, an kawo abinci taci. Wannan Karon babu Naufal da zai tayata, haka ta rinka tura sakwara da miyan agushi wanda yasha stock fish, dry fish da kuma ganda.
Idon Hajia Rabi kur a kanta tana jiran taki ci ta mazgeta. Taci rabi saita ɗaga ido taga ko Hajia ta daina kallonta saita ajiye. Lokacin kuwa Hajia tana waya, da sauri Deela ta cire hannu tana lashewa.
“Idan baki cigaba daci ba saina ballaki na balla banza” Hajia ta faɗa tana zare ido. Kashe wayar data keyi tayi saita cigaba da sababi.
“Wai ace kamar yarinya karama kullum sai anyi k’aramin badar dake akan cin abinci. Ke baki ciba mai kike so Pha’eexah taci?”
“Nifa bansan nayi katon ciki ne” ta faɗa tana matse kwalla.
“Lallai yaran zamani da shiririta, toh gwara kici abinci kiyi dundumemiya ba kamar yadda kike da a bushe ba” wata kakar su dake gefe ta amsa.
“Eh din, ai haka mijina ke sona” Deela ta amsa tana mata gwallo.
“Toh daman wannan mai idon Mayun ai baisan kyau ba. In ba haka ba wazai aure mata a bushe kamar kara”
“Ni wallahi ba a bushe nake ba” ta faɗa tana murguda ma tsohuwar baki. Ita Hajia na daga gefe tana jin daɗin drama ɗinsu.
“Ni dama da biyu nazo suna, samun Naufal zanyi anjima na faɗa mashi nayi masa mata chan kauye yar duma duma”
“Ai saiki aura mashi mu gani, wake tsoro. Kafan daya shigo da ita shi zai mayar da ita” sai tayi kwafa tana cin abinci. Haushin tsohuwar sosai taji yasa bata sake kulata ba.
“Jikalle,haba Uwar gidan Naufal. Kishin ya motsa ne”
Yake Deela tayi bata kuma cewa komai ba, suna cikin haka sai ga Miemie ta shigo zatayi sallah saita canza kaya saboda Sheik Kabiru Gombe yazo.
Dama abokin Grand Kadi ne so shine yazo yayi huduba akan Tarbiyar yara a Musulunci.
Mutane da dama sun hallara,kowa yazo ya kara ilimin sa. Mata an saka masu canopy cikin gida da fararen kujerun roba. Maza kuma suna daga waje an saka loudspeaker yanda kowa zaiji harda mutanen unguwa.
Ita dai Deela bata fita ba saboda iska, tana zaune a daka tana ji, sudai su samɗa an tafi gaba gaba, gidan ya washe tas banda Deela. Shikuma Naufal yaci babban riga yayi kyau abinsa.
Ya shiga ciki ya duba Fadeela, anan take faɗa masa gobe zata koma ɗakinta, yayi murna sosai saboda yayi mata alkawarin kujerar Makka as present ɗin haihuwa.
Taji daɗin abin sosai dukda ta taɓa zuwa, nan ta rinka jero masa addu’a tana godiya. Jawota jikinsa yayi yana patting bayanta. Yau yasan cewa Hausawa sunyi gaskiya da suka ce, “Siya na gari maida kuɗi gida” Mace na gari daban take cikin sauran mata.
Abinda bai taɓa haɗashi da ita Yasmeenah kenan, Addu’a bai taɓa shiga tsakanin suba. Shidai abinda yasani kawai sha’awarta yakeyi amma nothing else bayan wannan.
Bata kuɗi sosai yayi akan aje ayo Siyayya abinda zata koma dashi, daga nan zai faɗa ma Bilqees da Miemie suje gobe su wanke mata abinda ya dace a wanke. Tareda gyara gidan tsab.
Yau yaji daɗi sosai saboda mood ɗin Deela ya canza, murmushi kawai takeyi batada wani matsala. Daukar yarsa yayi ya tafi da ita wajen taron tareda kewar matarsa.
4 pm...
Lokacin an gama tafsir an kuma ci sosai an sha, daga nan aka raba so souvenir. Maza daga waje an basu jaka wanda akwai hankachief, key holder, memo da biro, mug da kuma husnul Muslim.
Mata sukuma nasu akwai Mascara da powder,sai memo da Husnul Muslim. Daga nan kowa yayi alwala aka fito da tabarma akayi sallah kafin kowa ya watse.
Naufal ya tafi gidanshi ya dauko sauran souvenir saboda ya kusan karewa na wajen. Su kuma cikin gida kowa hira akan wa’azi da akayi sukeyi .
Kowa yana gasganta abinda akace akan sakacin da iyaye keyi akan tarbiyan yaransu, iyaye sun dauki ɗabi’un turawa da wasu al’ada masu gurbanar da tarbiya.
Yara zasu girma basu san idan matsala yana damunsu suyi azkar ko sallah ba, ah ah zasu dauki waya da ear piece su saka wakar Lil Wayne ko Wizkid suna cashewa.
Idan suka dauki rawar shoki daga sama sai sun kai kasa zasu dire, da kuma rashin girmama na gaba dasu. Saboda baka haifa mutum ba bazaka faɗa mashi gaskiya ba if not zai zageka tas babu ruwanshi.
Deela addu’a takeyi Allah ya bata Ikon kare hakkin addini wajen tarbiyar da Yarta. Mai aikin Anty ta daura ruwan wankar dare, dariya Deela tayi saboda harta fara gajiya tun kafin a kai Ko’ina.
Anty Anisa tazo tana basu hakuri akan rashin zuwa da wuri da batayi ba. “Haba Anty babu komai tunda mun zama ɗaya”
“Gaskiya ne, amma kuma aiki zai kai mijina Port Harcourt kuma gobe da asuba zani tafi.”
Har cikin ran Deela bataji daɗin ba amma babu yadda zatayi, kawai fatan alheri tayi mata sai aka kawo mata abincin ta dasu souvenir.
Itama ta kawo mata atampha na Da viva da kuma kayan baby.
5:30pm.....
Taro ya kusan watsewa, mutane sun soma tafiya. An kawo gara daga gidanmu, akwatuna uku da kit akayi mani daga wajen dangina.
Kayan abinci shake kamar su shinkafa, semovita, taliya dasu mangyaɗa. Wani mota ne ya shigo cikin gidan.
Miemie locacin tana haɗa kujerun da akayi amfani dasu. Wani mota ne ya shigo sai taga yan mata su uku sun fito suna feleke. Sannu a hankali taje ta gaida su. A yatsine Meenah ta amsa, Laila ne da Lubna suka amsa da kyau.
Daga nan suka tambayeta inda mai jego take, “Ku biyoni” tace masu.
Sannu a hankali suka bita har inda nake, ni kuma na fito daga wankar dare har na saka Lace wanda akayi zani da riga simple dinki.
Fuskana babu komai sai natural beauty ɗina, su Mansura kuwa anata kwalliya zasu tafi saboda saurayinta zai zo daukar ta.
Su Laila suka shiga suka tsaya a bakin kofa, sallama sukayi tareda gaisuwa a tsartsaye. Ina ganin su na gane su, itama Mansura ma haka.
Nan take muka haɗa girar sama dana kasa. Mika ma Miemie katon sallaya nayi akan ta shimfiɗa masu.
“Miemie jeki kawo ma amaryan Yayanki abinci koh?” Mansura ta faɗa rai a haɗe.
“OMG keh ce Miemie? wallahi MINE yana bani labarin ki all the time” Yasmeenah ta faɗa tana washe hakora.
“Allah sarki” kawai tace tareda balla mata harara. Haushi ne ya kamata wai ace yanzu YaNaufal wannan yar iskan zai auro.
Laila ce cikin fara’a tace a mika mata jaririya su gani, daga nan ta tambaya sunar ɗiyar. Yarinyar tanata ma Laila murmushi har dimples ɗinta yana nunawa.
Nan take Yasmeenah taji sha’awar ta, har cikin ranta taji soyayyarta. Gata tana kama sosai da Mine ɗinta, fuskar da kuma idanun.
Itama mika hannu tayi a mika mata, tana karba ta fara mata wasa saita ta fashe da kuka maimakon dariya. Tanata jijigata a hankali amma taki shiru, Lubna ne ta karba domin ta gwada.
Itama batayi shiru ba, ina daga kwance akan gado na hakince ni a dole matar gida. Anty Saudah ce ta shigo sai suka mika mata Pha’eexah “Jikata,kunyarsu kikeyi?” Anty tace.
“She is not comfortable ne kawai around strangers” nace ina gimtse baki.
Yasmeenah tasan magana ta gaya mata amma babu komai, nanda Next week Zata zama matarshi.
An kawo abinci Meenah ko kallo batayi ba, kawai latsa wayar ta takeyi tana murmushi. Su Laila ne suke cin samosa da cake.
Miemie ce ta shigo da sauri tareda wayana a hannunta wai YaNaufal yana kirana. Saidai kafin na dauka ya tsinke, Daga nan saita soma wasa ni.
“ Anty yar gayu uwar gida sarautan mata, kece ta farko kuma kece ta karshe a zuciyar Yaya. You bring out the best in him” guɗa tayi kana ta cigaba da wasani.
“ ke kura ce kuma dole karnuka suji tsoron ki, walkiya mai haskaka gari, ɗawisu adon tafiya.....” Zata cigaba saina tsinke ta. Ina dariya nace, “Ya isa haka mana, It’s getting lame”
Itama Miemie dariya takeyi harda Mansura da Sadiya, “Anty ai gaskiya na faɗa”
Su Yasmeenah haushi sukaji sosai, mikewa tsaye tayi wai zasu tafi, Laila ce tace Uwar gida bazaki raka muba, harda bazan kula maganar ba sai Mansura ta tashi wai itama zata tafi.
Mika ma min kayan gaisuwan su sukayi kuma na gode masu sosai. An ajiye Pha’eexah cikin Craddle ɗinta saboda ta fara barci.
Miemie ce ta zauna da ita saboda ɗakin babu kowa. Nikuma ina rike da souvenir ɗinsu Meenah a hannuna har wajen motarsu kana na mik’a masu.
Basu tafi ba nan take wai suna jiran friend ɗinsu dake unguwar ta zo ta samesu, sallama nayi masu kana na karasa wajen Motana inda Mansura take.
Munata hira abinmu sai mukaji ihu daga cikin gida anayi ana salati. Da sauri muka karasa wajen shine akace wuta ne ya kama a dakin mai jego.
Da gudu muka ruga domin baby Pha’eexah tana ciki, muna karasawa mukaga wuta yana ci fal fal fal kuma kamar chinnawa akayi.
Kuka na barke dashi inayi ina kururuwa. Gashi kuma kofa a rufe gam babu daman shiga. Bubbugawa nakeyi ina kiran sunar yarinya na.
Mutane anyi charko charko ana kuka,gashi an kasa shiga ciki. Duk abinda akeyi babu Miemie babu dalilinta.
Wani cousin ɗin Naufal mai suna Hadi yazo ya rinka dukan kofar, daga bisani sai gashi ya buɗe. Da gudu naje zan shiga amma wuta ya korani baya.
Ruwa aka watsa mashi amma kamar ana karawa ne, ina kuka duk na fita hayacina gashi kuma saura kadan ya karasa Craddle din Pha’eexah.
Omo aka saka cikin bokatin ruwa sai aka watsa ma wutan sai ya fara lafawa, ina shiga na soma gudu kenan sai nayi tuntube da abu. Kallon da zanyi saina ga Miemie ce kwance a sume jini yana malalo mata daga fuska da alamun ta bige ne.
Gashi wuta ya soma cin wajen cikinta. Kuka na sake fashewa da shi saboda ban taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Da sauri na tashi domin naje na dauko Pha’eexah tunda ya kusa karasawa inda take.
Nan naga babu yarinya, gashi kuma wutan bai fara cin wajen ba. Dama yafi karfi a bakin kofa. Waige waige na samoyi ina kuka. Wata sabuwa kuma inji yan cha cha!
Wayam kawai saboda babu alamar yarinyar nan a cikin ɗakin. Da gudu aka janye Miemie waje aka soma watsa mata ruwa amma hayaki yayi yawa a lungs ɗinta. Ko motsawa batayi ba kuma da kyar in akwai rai a tareda ita.
kuka nakeyi sosai saboda tashin hankali baya misaltuwa, babu Pha'eexah gashi kuma Miemie rai yana hannun Allah. Duk na sukurkuce na kasa saisaita tunanina a waje guda.
Wani tunani nayi saina ruga parking lot nayi ko zan ga Yasmeenah da ayarinta amma babu su a wajen.
Nan take na yanke jiki na faɗi sumammiya.
#NiDaDiyata
~Yarinya Mai Dimples~©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 34 ✨✨✨
It was narrated form Anas that the Messenger of Allah said "None of you should wish for death because of some harm that befalls him, rather he should say: 'Allahumma ahini ma kanatil-hayatu khairanli wa tawaffani idha kanatil-wafatu khairanli (O Allah, keep me alive so alive so long as life is good for me, and cause me to die when death is good for me.)"' (Sahih)
***********
Nan take mutane sukayo kan Fadeela tareda kwanon ruwa, watsa mata akayi ana mata fifita.Tana farfaɗowa taga mutane charko-charko akanta tasan cewa ba mafarki takeyi ba da gaske ne.
Nanta sake barkewa da kuka mai tsuma rai, ita kuma Anty Saudah tana chan tana ganin tashin hankali saboda Miemie bata motsi har locacin.
Hadi ne ya sungumeta ya tafi da ita cikin Mota saboda zasu asibiti. Haka Anty tabi sahun shi a ruɗe ko mayafi babu, a hanya ne wajen parking lot wata ta mik’a mata hijabi.
Deela na ganinsu ta mik’e wai zata bi su, anyi anyi a hanata tareda cewa ta zauna a gida kila Babyn an fita da ita unguwa ne.
Nan Deela ta fashe da kuka, zama tayi dirshan a parking lot sai rizgar kuka takeyi. Kana ganinta gwanin ban tausayi, Hajia Rabi tazo ta janyeta daga wajen saboda maraice ne kafin sanyi ya shigeta.
Bilqees ne ta kira Naufal ta faɗa mashi abinda ake ciki, dama locacin yana hanyar layinsu. Juyawa yayi ya nufa hanyar asibiti.
Abinda yasa bai fara zuwa wajen Deela ba yasan cewa she is a strong woman unlike Anty Saudah. Yana isa locacin an shigar da ita ER, Hadi ne yayimasa bayani a gurguje.
Ita lokacin Anty Saudah tana kan kujera tanata kuka a hankali. Tunani ɗaya yake mata yawo a kai, ya zata yi idan ta rasa yarta ɗaya tilo. Nan ta soma kuka a bayyane, Naufal duk zafin dayake ji a ranshi ya shanye yana bata hakuri.
Itakuma Fadeela tanata kuka kamar ranta zai fita, bata san Wanne yafi mata ciwo ba. K'onewan da Miemie tayi kokuma ɓacewan da Pha’eexah tayi?
Idanta yayi jazur kamar garwashi domin kuka kuma kanta sai sara yakeyi. Ji takeyi kamar Allah ya dauki ranta ta huta da wannan tashin hankali.
Suma su Mommy sunajin abinda ya faru tazo gidan gona, anan kuma Fadeela ta soma sabon kuka, Mommy bata hanata ba illa tayata.
Haka suka runguma juna sunayi gwanin ban tausayi, kowa a wajen tausaya masu yakeyi. Gashi Fadeela tayi trying wayar Naufal bai dauka ba.
Sabon kuka ta somayi saboda duk a zaton ta yana wajen Yasmeenah ne. Cema Mommy tayi bari taje asibiti wajen Miemie da Anty tunda anyi ransacking gidan ba’a ga Pha’eexah ba. Zamanta anan baxai fito da ita ba.
Mommy bata hanata ba saboda ita ta tuka ma motar da suka tafi.
Shikuma cikin ruɗewa ya bar wayar a cikin motarsa. Yasa bazai san wanda ke kiran sa ba. Su Grand Kadi da Abba sun tafi police station dasu gidan radio.
A wajen police station ɗinne sukaga IG watau babban Khattab yazo duba abu wajen DPO. Nan take ya saka kwararrun yan sanda akan case ɗin kuma yayi masu alkawarin basu huta ba sai anga duk wanda akwai saka hannunsa a cikin abun.
IG da kanshi ya kira Khattab ya faɗa mashi halinda ake ciki, anan fah Khattab ya ruɗe. Mukullin motarsa ya figa ya soma gudu babu ji ba gani.
Sau biyu yana kusan aukawa ma trailer amma yana kaucewa da wuri.
Haka yaketa yi harya kai asibitin.
Ko rufe motarsa baiyi da kyau ba ya soma gudu ciki, lokacin kuma yayi daidai da isarsu Fadeela.
Suna tsaye a bakin Emergency Room babu wanda ya fito daga ciki, likitoci ne keta aikinsu.
Anty Saudah tana ganin Fadeela saita sake barkewa da wani sabon kuka, nan suka rinka yi su biyu. Duk cikin family suna cikin wanda sukafi shakuwa da ita.
Shima Khattab yana ganin yadda suke kuka saiya kame chan kurya yana kuka. Hankalin Deela ya kwanta dataga Naufal a wajen.
Tsagaita kukanta tayi taje inda yake ya dafa kumatu yana tunani ta zauna, riko masa hannu tayi ta soma magana cikin kuka, “Pha’eexah ta.........” saita barke da kuka, kwantawa tayi akan kafadarsa tana kuka wiwi.
A hankali ta soma magana, “Shikenan an tafi da ita, na shiga uku na lalace” tana kuka sosai wannan karon kamar ranta zai fita daga jikinta.
Lokacin yayi daidai da fitowan wani doctor, da sauri suka tashi kowa yana so yaji me ake ciki. Shikuma Dr din baice komai ba zai ratsa su ya wuce.
Khattab ne finkico shi yana masa masifa “Meye haka Doctor kana ganin mu tsaye zaka wani ratsa mu ka wuce”
“Mallam sakeni mana” Doctor yace
“Basan sake ba ɗin, dan rainin wayo” ya amsa
Naufal ne ya shiga tsakanin su, shima yaji haushin abinda Dr din yayi kuma yaji daɗin yadda Khattab ya saisaita shi. Kawai baya jin daɗin jikinsa ne da sai yayi ma Doctor ɗin dukan tsiya.
Doctor ɗin ya soma tafiya abinsa tareda nuna Khattab da yatsa yana hararar shi, Mommy tayi magana daga zaune.
“Doctor Haba mana ya zaka wuce mu baka ce mana komai ba”
“Kiyi hakuri Mama, jini zani store in dauko” saiya tafi.
Yaje ya dauko zai shiga ciki sai Naufal ya tambayeshi “Doctor please ta farfardo kuwa?”
“Kuyi hakuri shi muke kokarin yi” nan take Khattab ya fashe da kuka, wai ace kusan awanta uku a ciki amma an kasa tada ta. Shima baya maso ya kawo wani mugun tunani waiko bazata farka ba.
Daddyn shine ya shigo tareda Grand Kadi da sauran jama’a. “Meye haka kake yi kamar mara tawakkali? Maimakon kayi mata addu’a” Daddyn shi ya faɗa.
Mikewa yayi ya tafi kurya inda yake kukanshi babu mai kwaɓansa.
9:30 pm......
Locacin wasu Doctors su huɗu suka fito duk suna zufa, ga kuma leberori suma suna fitowa da Miemie akan gadon da ake turawa.
Da sauri yan uwan Miemie sukayi wajen ta, kana ganinta saita baka tausayi matuka. Duk bandage a jikinta manya manya, daga fuskanta, cikinta haɗe da bayanta, kafar dama da kuma hannun damanta.
Ga wani an zagaye goshinta dashi, sannan an saka mata Oxygen domin shakar numfashi. Da sauri suka rinka bin gadon dakin da aka ware masu.
Daga nan wani Doctor mai suna Abdullahi ya soma magana, “Bincike ya nuna cewa ba bigewa tayi ba, an buga mata kanta da sledgehammer ne. Kafin wutan ya soma ci”
Salati kowa ya somayi, masu matse kwalla kuma kamar su Fadeela da Anty suka soma. Kowa Mamaki yakeyi wai da gangan akaso kashe Miemie. Dr ne ya cigaba magana.
“Munyi kokari munga munyi stabilizing ɗinta amma gaskiyar magana shine sai anyi addu’a saboda har yanzu jini yana fitowa daga cikin kanta kadan kadan”
“Kuma hayaki yayi yawa a cikin lungs ɗinta, yanzu dai idonta biyu kuma tana jinku. Amma bansan ko zata iya magana ba ko buɗe idonta”
Daga nan sai Naufal ya tambaya asalin meya faru, Fadeela ta labarta masu komai daga zuwan su Yasmeenah har batan Pha’eexah da kuma konewan Miemie.
Kuka takeyi sosai saboda tana tunanin yau zata rasa mutane biyu da sukeda mahimmanci a rayuwarta. Duk juriyar da Khattab yake kokarin Nunawa saida wani hawaye na takaici ya gangaro daga idanunsa.
Shiko Naufal abin duniya yayi masa chunkoso, ‘yarsa ta ɓace ga kuma k’anwarsa rai yana hannun Allah. Zuciyar shi sai zafi yakeyi yana tafasa, shiko kuka ya samu yayi ko zaiji sanyi amma ya kasa.
Idanunsa a kafe sai zallan ɓacin rai dake bayyana, tausayin kowa yake a wajen musamman wanda abin yafi shafa kamar Khattab, Anty da kuma Fadeela.
Doctor yace su Abba su biyoshi office zai masu magana, duk sun watse sai Khattab yaje inda Miemie ke kwance.
Rike mata hannu yayi yana rero kuka, ko ajikinsa baya jin kunyarsu Anty ko Deela. Baice komai ba haka ya kafa ma fuskanta da baka ganin komai daga bandage da Oxygen.
Saida yayi ma’ishi sai ya fara magana still hawaye yana malalo mashi daga idanu. Abinda yasa yaketa kuka baifi yadda yau da rana Miemie ke masa maganar mutuwa.
“Yaya Khattab idan na mutu ya zakayi?” “Miemie meye haka?” “Please just answer me” “Bazaki mutu ba sai munyi aure kin haifan min yara masu kalan ‘yan gidan ku” dariya tayi kafin tace “You never know......”
Kuka ya sakeyi sosai daya tuna abinda ya wakana tsakanin shida Miemie da azahar dazu. Cikin kuka yace, “Please Haskena ki tashi karki mutu. Nasan anso a kasheki ne amma ina so ki basu kunya by staying alive”
“Kuma i promise you duk wanda yayi ɗanyen aikin nan za’a kamashi duk inda yake.....” saiya cigaba da kuka.
Rike mata hannu yayi yana matsawa a hankali, itama ta rike masa hannu amma idanun ta a rufe. Suna cikin haka sai su Naufal da Abba suka dawo.
Yanda suka ga Khattab jaɓe jaɓe da hawaye gwanin ban tausayi, ita Anty tana tausayin shi saboda yama fita damuwa.
“Meye haka kake kuka? Wayace maka mutuwa zatayi?” Naufal ya faɗa a takaice. Mikewa Khattab yayi yana jan manjina saiya bar ɗakin gaba daya.
Motarsa ya koma kai tsaye, sai a lokacin ya lura baima kulle ba. Kifa kai yayi akan steering yana sheshek’ar kuka.
Itakuma Deela zuwa tayi tana shafa mata goshinta wanda akwai bandage akai, hawaye itama takeyi saita soma magana da dishenshen muryanta.
“Please Miemie ki tashi kinji, kinga an tafi da little one. Im sure zaki san wanda yayi wannan abun....” kuka ta barke dashi mai kara, su Mommy da Anty sunata matse kwalla saboda tausayin Deela.
Tabbas zata shiga wani yanayi idan ta rasa Miemie kuma bayan ta rasa ‘yarta. Ciwon Miemie yanzu ya hanata kukan rashin yarta.
Naufal ne ya janyo Kujera ya zauna dab da ita, bubbuga mata baya yayi ya kwantar da ita akan kafaɗarsa.
“Kiyi hakuri kinji, in sha Allah komai zai daidaita”
“Allah yasa” ta amsa.
Suna haka kowa yana addu’a a ranshi. Abba ne yace masu Fadeela su tafi da Anty. Akwai nurses da aka ware zasu rinka dubata kafin gari ya waye.
Kuka Deela ta barke dashi wai baza’a bar Miemie ta kwana ita kadai da bare ba. Hakuri aka rinka bata amma taki shiru. Naufal ne yace zaije ya dauko Abla ta kwana da ita.
Anan ta rage kukanta sai tace yaje ya dawo zata zauna da ita tukun kafin yazo ya mayar da ita gida idan an dauko Abla ɗin. Kowa ya tafi tareda mata addu’a.
Naufal ya tafi ya dauko Abla, yana parking lot dasu Anty da Abba za’a tafi sai suka ga Khattab cikin motarsa yana kuka. Tadashi aka yi ya tafi gida sai yace ba yanzu ba tukun.
Abba ne yace ya shiga ciki ya zauna kafin Naufal yaje ya dawo saiya tafi. Shiga yayi ciki jiki babu kwari duk ya gaji. Ga wani matsananci ciwon kai da kuka da haifar masa.
Zuwa yayi cikin ɗakin saiya tarar da Deela ta shingiɗa, zama daga chan bakin kofa amma ta ciki. Tagumi yayi saiya soma gyangyaɗi saboda gajiya.
Itama barci yana daukarta amma tana buɗe idonta ta. Suna cikin haka sai barci ya dauke su duka. Basu suka farka ba sai sanda Naufal ya dawo da Abla.
“Ya akayi wanchan abin ya daina motsi? Naufal ne ya tambaya sanda ya shigo kana ya nufa hanyar ECG da aka haɗa da jikin Miemie.
A firgice suka tashi, Deela tana mitsike ido Shikuma Khattab ya zura da gudu wajen gadon. Saka kunnen shi akan kirjinta yayi amma baya jin alamun bugun zuciya.
“Why is she not breathing?” Deela ta faɗa hankali a tashe.
Da sauri ya mayar da kunnen sa wajen hanncinta tareda cire Oxygen tube ko zaiji alamun shakar numfashi amma wayam.
Innalillahi wa inna ilayhi rajiun ra rinka maimaitawa yana yi yana jijigata amma bata motsa ba, asalima jikinta a kankame.
Fadeela ce ta tsandara ihu saita sulale kasa, da sauri Naufal ya tarbota. Bata hakuri ya somayi yace kila wani abune daban.
Ko ba’a faɗa mashi ba yasan Miemie ta koma gidanta na gaskiya. The worst part shine an kasheta ne bawai hakanan bane, tunanin sa ɗaya how can someone be this cruel?
Abla zuwa tayi ta rungume Deela sunata kuka tare, Fadeela ne ke magana cikin kuka a hankali, “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun, shikenan Miemie ta tafi barmu”
Shikuma Khattab gefe yake ya zauna a kasa zaman dirshan, kwakwalwarsa sai tafasa yakeyi. Shi tunda yaji labarin accident ɗin yasan za’a yi haka.
Yau gaba ɗaya sai maganar mutuwa takeyi da kuma rok’on sa gafara. Har haushi yaji yayi mata magana, ce masa tayi “you never know when you’ll die, gwara ka shirya kafin lokacin ka”
Duk kalamanta yanzu yawo yake masa a kai, saidai yanzu Idonshi ya kafe. Yama kasa kuka, salati kawai yake cikin ransa. Kirjinsa zafi yakeyi ga gudu da sauri kamar zai fashe.
Ji yayi kamar an daura mashi katon dutse cikin kirjinsa, ga kuma miyau na bakinsa ya kafe k'ab. Karkarwa kawai yakeyi kamar yana jin sanyi.
Shikuma Naufal komawa yayi bakin Varenda yayi tagumi, abin daure masa kai yayi wai dazu ya ganta yanzu kuma ta rasu. Daukar wayarsa yayi domin ya kira ABBA.
“Assalamu Alaikum, ya akayi ne Naufal” Abba yace ta ɗayan ɓangaren. Naufal bai iya amsa sallamar ba, kawai magana ya soma.
“Abba shikenan Miemie ta tafi ta barmu. Abba Miemie ta rasu, ta koma gidanta na gaskiya”
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” abinda Abba ya iya faɗi kenan.
Shikuma Naufal wasu zafafan hawaye suka soma gangarowa daga idanunsa, da farko kadan kadan sai kuma suka fara gudu.
#NiDaDiyata
~Yarinya Mai DIMPLΣS~©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💦 Ni Da Diyata 💦
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples
💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦
✨✨✨Page 35 ✨✨✨
'Imran bin Husain (May Allah be pleased with them) reported: Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "Shyness does not bring anything except good."[Al-Bukhari and Muslim].In a narration of Muslim: Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "All of shyness is good."
***********
Kullu Nafsin Za’katul maut. Valar Morghulis. Kowane mai rai mamaci ne, sai dai zamuyi fatan mu cika da kyau da imani.
Fadeela da Abla suna cikin ɗakin suna hawaye, jiki babu kwari Abla ta mik’e tsaye taje inda gadon yake ta rufe mata jiki da mayafi.
Mamakin mutuwar Miemie takeyi, abin yayi mata zuwan ba zata. Addu’a yanzu kawai zata ya Allah yakai haske kabarinta, ya kuma basu hakurin jure rashinta.
Gaba daya babu wanda yayi barcin kirki, Naufal yakan shigo akai akai ya duba su. Saidai kuma Fadeela tayi shiru bata ma cewa komai, kana ganinta kasan cewa kukan zuci takeyi wanda yafi na bayyane ciwo.
Hawaye neke gangaro mata ɗaya bayan ɗaya. Haka har gari ya waye, suka fara shirin komawa gida.
Khattab yanata tunanin dogon suma tayi, Naufal ma haka. Amma Doctors sun masu confirming lallai babu rai a tareda ita.
Anyi making preparations na tafiya da ita gida, shikuma Naufal ya tukasu zuwa gida saboda Deela tana jego kuma sanyi ya fara shigarta.
Cikin gida kuma anata koke koke, Anty Saudah ce tace duk wanda ke kaunar Miemie yayi mata addu’a instead. Daga nan aka rage hayaniya sai masu hawaye kawai.
Shiko Khattab dakyar ya iya tuka kansa zuwa gida. Yana shiga falo babu sallama ya tarar da Daddynshi da Mommy akan dinning suna kalaci.
Ko kallonsu baiyi ba ya haye sama inda ɗakinsa, yana shiga ya banko kofa Karab. Hayewa gadonsa yayi ya kwanta rub da ciki.
Anan ya soma sabon kuka, yanayi yana shesheka gashi muryanshi ya dishe. Mommy ce ta bishi domin ba ɗabi’arsa bane, kofa taji a garke saita firgita.
Komawa tayi wajen IG ta gaya mashi, nan take ya dauke wayarsa dake gefe ya kira Abba. Anan ne ake sanar dashi rasuwar kuma jana’iza karfe 9 na safe.
Yana soma salati Mommy ta gane cewa rasuwa Miemie tayi, nan take tansoma gumi. Kawai tunanin irin halin da Khattab zai shiga take, Allahu Musta’an ta faɗa a fili.
Su Fadeela tana komawa gida sukayi ido da Anty, hawaye ya soma malalo ma Deela amma batace komai ba. Dama ruwan zafi yana jiranta, Hajia Rabi ta chuɗa ta da kanta.
Tayi ɗan kan gado, an kuma kawo mata abinci amma ci takeyi kamar magani. Fuskanta a cunkushe babu annuri kwata kwata gashi ta daina magana.
Suma Forensic tun kafin isowar su Naufal gidan suka zo suka fara aiki gadan gadan. Kokari sukeyi suga wani trace da zaiyi leading ɗinsu wajen gane wanda yayi wannan ɗanyan aikin.
Dama mutane sunfi bada karfi idan Miemie ta tashi zata faɗa koma waye amma kuma ta rasu. Tabbas kuma Miemie taga wanda yayi mata haka saboda bincike ya nuna a jikinta tayi dambe da mutumin kafin aka buga mata karfe.
9am.....
Mutane sun hallara za’ayi ma Laurat Hussain Beli watau Miemie sallah. Shi Khattab kulle kanshi yayi cikin ɗaki yaki zuwa, yana cikin kwance saiga Lili tazo da shiririta wai tana so suyi magana.
Bai kulata ba haka ta gama tsayuwa ta tafi tareda watsa ashar. Ita kuma Yasmeenah tayi kiran duniya Naufal bai ɗauka ba, shi yana kyautata zaton da saka hannunta wajen wannan aika aikan.
Jira yakeyi agama jana’iza ya raka ‘yan sanda har gidansu suyi gaba da ita. Idan yaso bayan sun kulleta su saka ɗanmakullin cikin rafi.
Mommy ɗinta ne ke kallon NTA ita kuma tazo wucewa sai taga hoton Pha’eexah ɓaro ɓaro wai ta ɓata. Tashin hankali ta shiga sosai saboda ta ganta kafinta jiya.
Daga nana kuma sai taga sanarwa akan rasuwar Miemie, anan tayi mutuwan tsaye saboda abin yayi yawa. Sai alocacin ta gane abinda yasa Naufal baya daukar wayanta.
Shiryawa tayi tsab da niyyar zuwa tayi mashi ta’aziyya. Ita kuma Mommy Khattab ta shirya zata gidan gona ta’aziyya, lili ta tambayeta ina zata saita ce “Wanda Khattab yakeso dazu ta rasu”
Taɓe baki Lili tayi sai tayi Magana ciki ciki, “To ni ina ruwana” ashe Mommy taji.
“Babu ruwanki Halima, amma bari nayi maki albishir ko bayan raina ban yarda Khattab ya aureki ba. Na gwammace ya zauna babu aure”
“Babu ruwanki koh?” Mommy tayita nanatawa tana tafiya saboda taji haushi sosai. Ita kuma Lili kuka takeyi saboda bata san meyasa uwar mijinta ta tsaneta haka for no reason.
Gaskiya yanzu bataga lafin da wasu matan ke fada “Idan Uwar mijina nada kirki Allah ka barmin ita, if not Allah ka kasheta tun kafin in shiga”
******
Anyi sallah kuma an kai Miemie gidanta na gaskiya, mutane sunzo sosai saboda kyawawan ɗabiun ta dukda ma tanada taɓun hankali.
Kowa fatan hasken kabari yake mata, Naufal shi ya jagoranci sakata a rami kuma ya tabbatar babu wani guri daya buɗe.
Bayan nan police station ya wuce kai tsaye saboda yaji labarin bincike amma basu bashi wani labari mai daɗi ba. Shi yanzu hankalinsa ya rabu kashi uku.
Na farko mutuwar Miemie, sai kuma ɓatan yarsa ga kuma matarsa ta shiga wani yanayi. Haka suka zauna a gidan gona anata karban gaisuwa.
Baiyi mamakin rashin gainin Khattab ba saboda yasan zaifi kowa missing ɗinta. Sun gaisa da mahaifiyarsa da kuma Mahafinsa kuma shima anjima yayi alkawarin zuwa duba shi.
Ita kuma Deela ɗakin Miemie ta koma zama. Hawaye takeyi bata cewa komai gashi nonota sai ruwa yakeyi saboda rashin tsotso. Duk sai jika mata riga yayi, gashi tana jin alamun kukan Pha’eexah a ranta.
Ita tasan ɗiyar ta tanada rai amma kuma babu ita babu dalilinta. Haka ake zuwa mata gaisuwa, binsu da ido kawai takeyi bata cewa komai.
Koda Yan sanda suka zo karban statement wajenta kallonsu kawai taketa yi, Mansura ce ta faɗa abinda ya faru.
Wajen azahar saiga Yasmeenah tazo sanye cikin purple After dress tayi wrapping kanta irin na Arabs. Tana parking a waje saboda kowa nan ya ajiye nasa.
Naufal yana hangota daga nesa saiya tashi da sauri ya nufa inda take. Ita kuma tana tafiya sannu a hankali saita hange shi.
Wajen dayake ta nufa tana kokarin masa magana kenan, shikuma baiyi wata wata ba ya dauketa da mari. Kafin ta ankara ya kara mata guda ɗaya sannan ya hambareta da kafarsa a cikinta.
Rike ciki tayi ta faɗi kasa tana kuka, a hasalce ya fara mata masifa.
“ke dan Ubanki ina yarinya na?” kallonsa cikin rashin fahimta tayi tana kokarin gane meyasa yake mata irin tambayar.
Fincikarta yayi ya shake, “Ina yarinya na nace dan ubanki? Ki gaggauta fito da ita ko ki yabama aya zakinta.”
“Halan kishi hauka ne? Zaki zo ki daukan min yarinya kuma ki kashe min k’anwa.”
“Infact Uban wa yace kizo gidan suna, shishigi da shiga sharo ba shanu”
“Naufal meye haka? Sai kace bakada tawakkali?” Anty Saudah tace.
Sakin Yasmeenah yayi saita ɗurkusa tana kuka, ita yau abin al’ajabi take gani. Wai daga zuwa gidan rasuwa ance ita tayi kisan.
Jiki babu kwari ta shiga cikin gida, tana tafe kowa yana mata kallon muguwa. Haka har takai ɗakin da Deela take, Fadeela tana ganinta ta rufe ido bata sake buɗewa.
Hawaye kawai taketa yi, haka Yasmeenah ta gama zamanta ta tafi. A wajen fita sai tayi kicibis da Naufal, ja da baya tayi saboda ta tsorata dashi.
Zai buɗe baki yayi magana saiga Yan sanda sunzo mata tambayoyi as protocol. Ana mata tambaya tana kuma amsawa kuma kana ganinta Kasan akwai alamar gaskiya a tareda ita.
Shi karin kanshi Naufal ya karaya amma bai nuna ba. Abba ne yace tace ma iyayenta biki nanda kwana biyar ne babu ɗagawa.
Dama Daddyn ta ya kirashi a waya yayi mashi ta’aziyya kasancewa yana Lagos. Naufal ya fara korafi akan a ɗaga bikin amma Abba ya dakatar dashi.
“Bana son karanci da shiririta Mallam! Kai kace kana so kuma dole ayi babu fashi”
Yasmeenah taji daɗi sosai saboda har kasa ta ɗuka tayi godiya which dama godiya ba ɗabi’anta bane. Harga Allah idan ba’ayi bikin ba zata shiga tashin hankali saboda magunguna na mata daketa dirka.
Da yamma......
Naufal ne yaje da kanshi ya ba Fadeela abinci bayan ta fito daga wanka. Ita yanzu ta daina magana ko musu, yin komai takeyi sannu a hankali amma bata cewa uffan.
Haka ya ciyar da ita harta koshi, yana isarta saita kawar da fuskanta. Magana yayi mata na duniya amma taki amsa shi, daya takura mata saita soma hawaye, dole ya hakura rai baiso ba yabar ɗikin.
Hanyar gidansu Khattab ya nufa tunda dama ya taɓa zuwa sanda Miemie tayi ciwo akanshi. A falo ya tarar da Mommy da Lili.
Dukawa yayi suka sake gaisuwan mutunci da Mommy tunda dama sun haɗu dazu. Ita kuma Lili ‘sannu’ tace ta cigaba da ɓare gyada tana murzawa cikin bakinta.
“kaje upstairs, first room on your left shine ɗakinsa” Mommy tace
“Nagode sosai” ya amsa
Zuwa yayi yana buga kofa a hankali amma babu wanda ya amsa shi, lokacin Khattab shikuma ya soma barci sai yaji bugun kofa. Duk zatonsa Lili ne, tsaki yayi saiya ɗaura pillow a kanshi saboda ya rage noise.
“buɗe mana, nine fah!” murya yaji kamar na Naufal, kasa kunne yayi ko kizo ne amma ya sake jin muryan Naufal.
Da sauri ya tashi ya buɗe, yana ganin fuskar Naufal saiya fashe da kuka.”Dalla Mallam meye haka? Kashe kanka kake so kayi kamar baka yarda da kaddara ba”
“YaNaufal kasheta fah akayi, i can’t imagine the pain she went through” ya faɗa cikin Muryar kuka.
Patting bayansa Naufal yayi saboda shima yana dab da hawaye. “Kaci abinci kuwa?”
“Yanzu zan ci”
“Haba Khattab tun jiya fah” kallonsa Naufal yayi yana tunani saiya tashi ya fita. Downstairs yaje saiya gaya ma Mommy abinci yakeso na Khattab.
Alamun zata tashi saiya dakatar da ita, “tashi ki samu ma Khattab abinci” ya faɗa ma Lili. Watsa mashi harara tayi saita basar.
Mommy ce kunya ya soma ɗawainiyan da ita, “bari kawai naje” Mommy tace.
“Ita wancan meyasa bazata ba?” ya tambaya yana kallon Lili. Sai kuma ya soma masifa tunda dama yanzu ya koya gashi yana neman inda zaiyi pouring frustration ɗinshi.
“Bada ke nakeyi ba? Better hurry up Kije ki kawo min abinci kafin na saɓa maki. Niba ɗan nan gidan bane yanzu zan saɓa maki”
“Bakida hankali ne Mommy tana maki magana kin kyaleta, waye sa’anki? You have lost your goddamn mind, idiot kawai”
Mamaki ya kamata yanda yazo yana mata masifa, amma kuma ta mik’e saboda ta lura kanshi yana motsawa kafin ya jibgeta. Tana jan kafa tana tura baki har taje dinning ta dauko cooler.
“maza ki kai mashi sai ki dawo ki dauko mashi ruwa.” Haka tayi abinda yace, Mommy ce ta fara kuka.
“wai da yanzu wannan akeso a lika ma Khattab, munzo mun samu Miemie shine rai yayi halinsa”
“Yi hakuri Mommy, dangana kawai zamuyi”
Dakin Khattab ya koma, bai bar gidan ba saida ya tabbatar yaci ya koshi kuma yayi wanka tareda sallah.
Shi yanzu yana tausayinshi sosai, kawai yana tunanin yanda zai taimake shine!
0 comments:
Post a Comment