_*Jinjina Agareki Faty Afreen Everything would be better if more people were like you!*_
_*Bazan Manta Kuba Smart Triplet & Narjis Da Duk Sauran Members Gaisuwa A Gareku Baki Daya.*_
Alhaji yace yanzo nan kai dan baka da kunya sai ka je kace ka kawo ta tayi kwana biyu?
faruk shiru yayi ya dukar da kai.
alhaji ya sake cewa kabar ta tayi sati biyu , duk tabi yan uwan ta ta gaida su, ai sun mana kara tunda aka kawota babu wadda yazo, kuma nasan alhaji ne zai hana .
faruk yace sati buyu fa yayi yawa fah ,abba sai dai ta bari indan an kwana biyu sai na kaita tayi sati daya.
alhaji ya kalli faruk ya girgiza kai ,yace to yanzun me zai hana ka kaita yau din tayi sati dayan.
faruk ya dade zaune ya dukar da kai yayi shiro .
sai cen yace bari naje na shirya.
alhaji yace to ka sai mata tsara ba ne.
yace eh muyi waya da nura zai suyo ya kawo, bari ma na kira shi naji.
mikewa yayi yana cewa abba bari naje na shirya.
alhaji yace ai sai dai nace muku Allah ya kiyaye hanya danni fita zanyi.
faruk dakin su ya nufa ya zauna a folo.
itako humaira daki momy taje.
momy tace a,ah har kun shirya .
humaira tace yaya ne har yanzun yaki shir yawa.
tace rabo da shi yau duk tsiyar shi dai yau sai kinje gida.
suna cikin magana da momy kiran faruk ya shigo wayar ta.
da sauri ta daga yace zo mana.
mikewa tayi tace da momy bari na dawo yaya na kira na.
humaira na shiga ta same shi a falo , sai wani daure fuska yake ta tsaya nesa da shi tace gani.
cikin fada yace anan zaki tsaya saboda kinga dodo ko?
tace to ba kai bane kake ta daure min fuska cikin shagwaba tayi maganar dan haka ta takara tafiya da imanin shi.
cikin lallashi yace zo nan ki zauna na bari.
humaira ta mike taje kusa dashi ta zauna.
ya tattaro hankalin shi gaba daya yadawa dashi kanta, yace humaira duk wannan kwalliyar ta tafiyar ce.
tace yaya batayi bane, ai ba ma wani kwalliya nayi ba.
Kin tashi da wuri kin hau shiri, ko tunani na bakiyi, wai ke baki da imani ne.
to yaya ba kai bane kake fushi da ni bayan kaikace min kana da budurwa a gidan inna.
faruk ya kwashe da dariya yace cemin zakiyi kinje ganin zee baby, humaira dariya tayi ta kai mai duka a kirji.
yace to shikenan zomuje dakina na danji dumin baby na sai mutafi.
humaira ta marairaice tace yaya nariga fa na shirya, dan Allah kazo mutafi.
yace ke wai kina hauka ne haka zaki tafi kibar ni har sati daya ke ko tausayi na bakiji , kinga indai kinaso mutafi da wuri ki biyu ni daki, mikewa yayi ya shiga dakin shi.
humaira ba yadda ta iya dolle ta bishi dakin sa, faruk yaba humaira wahala sosai ya dade be barta ba dan dama sun juma basu hadu ba cike da kwadayi yake .
sai da yaga ta gala bai ta sosai sannan ya barta yana mai tunanin inama su sake kasan cewa haka an juma
Itako humaira fadi tayi azuciyar ta wannan fitinanne ne wlh inba gani yayi mutun ya kasa mutsiba hankalin shi baya kwanciya.
faruk kuwa yana tashi yaje yayi wanka yafito yana goge jikin shi, yace tashi kije kiyi wanka ko nayi miki ne, zama ki iya tafiyar kuwa ko mu Bari sai gobe.
ai humaira najin ya fadi haka da sauri ta sakko ta shiga bayin .
itako momy shiru taji yayi yawa tace to ko dai wannan rike tatcen ya fasa tafiyar ne, dan haka ta mike tana fadin ai ba zai yiyoba.
bangaren su ta nufa ta shiga tayi taita sallama taji shiru, sai can faruk yaji kamar momy na magana, da sauri ya fito da riga ahannu sa yana kokarin sawa , lokacin har momy ta juya zata fita.
momy ta waigo tace wai ba zaku tafi bane rana fa nayi, ina humaira.
yace yanzun nan zamu wuce.
momy ta tura kofar humaira zatashi dan dama ta dauka ko faruk na ciki ne shiyasa bata shiga ba.
faruk yace momy bata ciki fah tana wanka ne.
momy ta wuce da sauri tana fadin ai tooh .
bayan sun gama shiryawa tsaf suka fito faruk ya riko akwatin humaira , faruk yace to momy zamu tafi. momy ta juyo ta kalli humaira taga tayi kyau matuka duk wanda ya kalli humaira ba na miji ba ko mace sai tayi marmarin sake kallon ta.
humaira na ta yake hakora.
faruk yace momy kalleta sai murna takeyi.
to ya kake son tayi
bayan sunyi sallama da kowa na gidan faruk yace to zo muje kiyiwa su aminu sallama.
tace yaya faruk gaskiya ba zanje ba, zan kira yaya aminu awaya na mai.
yace saifa kinje humaira, haka ko aka yi sai da ya kaita har dakin samira tayi mata sallama sannan suka shiga muta , su momy har bakin mota suka rakota, suna daga mata hunnu , sai dariya takeyi.
faruk ya kalli humaira yace kinata murna zaki rabu da makiyin ki.
da sauri ta kalle shi tace kai yaya ka daina irin wannan maganar.
kwatar da kanta tayi ta rufe ido dan ta fahimci faruk be san azauna lafiya.
da haka bacci ya dauke ta har suka isa humaira bata bude ido ba.
ta dade da tashi amman ta lura faruk beson surabu lfy dan haka tarufe idon ta
suna shiga harabar gidan Humaira ta bude idon ta dan bazata iya boyewa murnan ta ba, gani tayi gidan ya canza mata, kamar bata taba yin rayiwa acikin saba, da gudo ta bude murfin mutar ta fita aguje.
faruk futowa yayi shima aguje yana kiran humaira humaira baki da hankali ko , baza ki tsaya ba sai kinje kin fadi.
wannan ihun da yake ya jawo hankali mutane da ke cikin gidan, zainab da auwal suka mike atare domin kiran sunan humaira da suka ji anayi suyi waje aguce.
Itako ummi mahaifiyar humaira gabanta taji ya fadi da sauri ta tashi ta daga labilen window ta leka humaira ta tahongo rike tam ahannun faruk
_*💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞*_
*_81 to 83_*
_*FADEELA LAMIDO*_
_*MMN YAZEED........✍*_
*gaisuwa a gare ku*
*Ummasalma Ahmad*
&
*Aysha 💄big girl💋*
ummi tana hango humaira taji wani sanyi azuciyar ta humaira ce haka tayi kiba mulmul da ita.
su kuwa auwal da zainab tuni sun isa gun humaira, faruk ganin mutanen da yayi suna nufu su besa ya sake humaira ba.
zainab kallon humaira take da mamaki ikon Allah yanzun humaira ce harda ciki gata gwanin ban sha awa daga gani kasan naira ta zauna.
bakin ciki yarufe zainab.
har suka shiga gidan faruk be sake humaira ba yana ruke da hannunta, hajiya rabi na zaune a falo , nan da nan ta sake fara,a tace lale da zuwanku.
humaira ko zama ba tayi ba tace hajiya ina ummi na. tana ciki ta bata amsa.
humaira ciki cikin kwace hannun ta tashiga yi daga hannun faruk, hajiya rabi na kallon su.
ganin da faruk yayi basu kadai bane adakin yasa ya sake humaira ba wai dan tana da karfen da zata kwace ba, kamar yadda take gani.
Itako hajiya rabi kallon faruk take tana fadi azuciyar ta wannan dan duniya ne, bashi da kunya.
itako ummi tana daki farin ciki ya cika ta har gwallah ke fitowa daga idonta saboda farin ciki, saijin humaira tayi tabugo kofar da karfi ta shigo, fadawa tayi jikin ummi tace ummi kinaji na kinki fitowa.
da sauri ummi tarike humaira tace yanzun nake shirin fitowa humaira, har inacewa kinji dadin zama kin manta da mu ashe kina tafe.
tace ummi yaya zan manta da Ku, kulum inama yaya magana yakawo ni sai yace bayan zunba, yanzun ma sai da su momy sukasa baki tukun ya bari.
ummi tace to yazun dai jiki ki kai mai abin mutsa baki, bayan humaira ta fita ummi ta fito, faruk naganin ta ya sauka daga kan kujera ya tsuguna yana gaida ta.
amsawa tayi cikin Fara,a tace ya mutanen gidan, ya amsa da lfy lau sunce agaishe ku kanshi a kasa.
humaira ta shigo ta ajewa faruk ruwa agaban shi, yasa hannu ya dauke karamin cofi ya tsiyaya ruwan yakai bakin sa.
ummi ta juya tama humaira kallon tuhuma sannan tace humaira haka kike ba mijinki ruwa ko a gida.
humaira shiru tayi dan bata da amsan da zata bada
faruk yace ummi ai idai humaira ce zaki ga abubuwa iri iri .
ummi tace to aiko bata ji dadi ba.
humaira ta hada rai dan taji haushin maganar faruk
ummi mikewa tayi ta shiga daki.
humaira tace yaya dan Allah ka daina gayawa ummi irin wannan maganar zakasa tai tamin fada , kuma inta gayawa abba har duka na zai iya yi.
yace kai naji dadi ai duk a binda kike min sai na fada, saboda baki kula dani yadda ya kamata, ni zanso ma azane ki, su momy ne suka bataki saboda duk abinda ya faru basa ganin lefinki, ko kinada gaskiya ko baki dashi sai agoyi bayanki shi yasa kika sangar ce
humaira tacika tayi fam da haushin faruk watou shi so yake ya hada ta da iyayenta.
faruk ya kalli humaira yayi murmu shi sannan yace, kuma wai humaira ba kince momy mamarki bace ?
da sauri tace eh.
yasake cewa kuma ke da bakin ki kikace kinbar min ummi
eh tasake cewa da shi.
faruk yace kinga idan kinmin abu haka momy mamarki take goyan bayanki , taita min fada har duka na ma tayi , haka zan hakura da abin ko inaso ko banaso, ummi ko tunda mahaifiya tace dole kema ta gaya miki kiji ko kina so ko baki so, inma takama azane ki Zan so haka.
ummice ta kwalawa Humaira kira.
humaira ta mike da sauri tabar wajen dan ayan zun ta kosa faruk ya wuce, dan ta fahimci faruk akwai abin da ya shirya .
tashiga ummi tace maganar abinci ne, shinkafa muka da fa, wata kila shi baya so, me aza,a dafa mashi.
humaira tace ummi zai ci shinka far ai kome su momy suka dafa shi yake ci.
tace kina nufi abincin gidan kuke ci baki mai girki.
Sai alokacin humaira ta tuno kuskurenta, tace ai baita cewa namai girki ba.
Lallai nagano irin zaman da kikeyi , tarbiyan da aka baki kenan, haka kikaga inawa baban ki, to bari baban ki yadawo zan fada mai halin da ake ciki.
humaira idon ta ya cika da hawaye tace ummi karki fada mai na Bari.
taje ta dauko abincin ta ajiye agefen shi tabude ta zuba mai, faruk ya kalla fuskar Humaira ya tabbatar fada aka mata, bayan yagama cin abinci ,ummi ta dawo ta zauna , tace ashe humaira bata maka girki, su kuma su hajiya aisha suka sa mata ido.
faruk ya sosa keya yace ummi ai yar lelan momy ce, ita ke shagwa bata.
tace lallai kuwa zama ki bari ne bari baban ki ya dawo.
faruk yace ummi inason na koma yau ne kuma gashi baba baya man.
to ka bari sai gobe mana saika wuce, yaka mata ku gaisa da shi, kuma sai anyi mangariba zai dawo , ai yan zon yamma tayi 5:48 in katafi dare zai maka a hanya.
Itako hajiya rabi tunda suka shiga bara yin su basu fito ba, bakin ciki ke cin su da dana sani, inama ta bari zainab ta aure faruk.
hakalin su be kara tashi ba saida su kaga ana shigo da tsarabar humaira, atanfufine masu kyau da turaruka masu tsada
sai bayan sallah mangari ba alhaji ya dawo tundaga waje lbr ya zo mai cewa humaira tazo, dan haka yaji dadi azuciyar shi yasan yanzun hakilin mahaifiyar ta zai kwanta.
humaira najin ance alhaji ya dawo ta mike da sauri zata fita , ummi ta dakatar da ita tana fadin karki kuskura ki fita.
bayan alhaji ya shigo yaji dadin ganin faruk sun gaisa cikin farin ciki, ya tam baye shi muta ne gida , faruk ya tabbatar mai suna lfy.
alhaji yakalli humaira yace humaira angirma tayi dariya ta dukar da kai tace bayan kun manta dani.
alhaji yace aini na hana kowa yazo gara abarki ki natso.
Ummi dake gefe tace kuma sai gashi bata natsun ba, tunda a inda nalura humaira bata kula da mijinta kwata kwata, dai dai da ruwa dungura masa take.
alhaji yaji mamaki yace humaira haka kika koma kuma, kai kuma kasa mata ido kana kallon ta, baza ka bata kashi ba.
faruk ya dukar da kai yace ai su momy basa bari, shi yasa take yi.
alhji mikewa yayi cikin bacin rai, yace ina zuwa , zaki gane kuranki.
_*💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞*_
_*84 to 86*_
_*FADEELA LAMIDO*_
_*MMN YAZEED........✍*_
Humaira kuka ta fara dan ta tabbatar dukan ta zaiyi ,dan abba baya wasa, ummi dan Allah kibashi hakuri wlh na daina, bazan kuma ba.
faruk ko atunanin sa alhj firgita humaira zai yi, dan shi aganin shi humaira ta wuce duka, koma ko za abige ta, ai baza a bigeta da ciki ba, dan haka da yaga humaira ta firgita yaji dadi zociyar shi.
sai ganin alhj su kayi ya fito da wata sharbebeyar durina sai huce yake ya nufi humaira gadan gadan , ya zuba mata ta sake kara.
faruk ya zaro ido ya mike da sauri, humaira ma mikewa tayi da gudu tayi bayan faruk ta cukuikuye shi tanà kuka alhj be barta ba biyota yayi ya kuma daga bulalar zai gara mata, faruk yace baba dan Allah kiyi hakuri ka bar ta , ko sauraran shi beyi ba ya zuba mata ganin da faruk yayi da gaske alhj keyi.yasa shi rudewa , juyawa yayi ,yama humaira runfa, yana fade baba bafa ita kadai bace.
alhj bebar dukan humaira ba sai da yaga ba ita yake samu ba, faruk kawai yake samu sannan ya bari.
humaira sai kuka take yi dan ma Allah ya tai make ta befi bulala biyu bane yasame ta, amman sauran duk ajikin faruk ya sauka.
bayan faruk ya sake humaira taje gaban alhj ta tsuna tana rokon gafara, sài da yayi mata nasiha me ratsa jiki sannan yace taje taba mijinta hakuri.
zuwa tayi gaban faruk ta tsuguna duk da cewa shima akasa yake, tace yaya kayi hakuri na daina bazan kuma ba.
har ga Allah humaira tabawa faruk tausayi besan haka baban humaira yake da zafi ba da be fada ba.
dan haka yace ba komi humaira ya wuce.
mikewa tayi ta shiga dakin ummi, dama ummi tuni ta bar wajen, tabar faruk da alhj suna hira.
koda humaira da shiga dakin babu abinda ummi take mata bada nasiha, kuma tabas nasihar ta shegeta dan jikinta yayi sanyi sosai.
faruk ne ya kalli agogon hannun sa karfe goma saura dan haka yace baba bari na tafi naga dare yayi.
alhj yace kana tunanin ina garin nan zakaje wanne waje ka kwana.
faruk yace ba haka bane baba , akwai wani abokina da zanje wajensa da safe saina tafi.
alhj yace sam bazai yiyu ba, ba in da zaka.
daga murya yayi ya kira auwal yayan humaira, bayan auwal ya shigo alhj yace kaishi dakinka.
auwal yakai faruk dakin sa yadan zauna suka dan taba hira duk da cewa auwal karami ne, befi shekara biyu ba tsakanin sa da humaira dan ko aminu ya girmi auwal nesa, amman haka be hana faruk yayi hira dashi ba.
zawa wani lokaci auwal ya mike yayi wa faruk sallama ya fita.
humaira tayi shirin kwanciya ummi tace ta tafi gurin faruk, badan ranta yasoba tafita .
tana shiga ta same shi ya fara barci mutsin ta ya sashi ya tahi, zama tayi agefe batace masa komi ba.
gani yayi humaira bata da niyar tashi dan haka yace humaira tashi kije ki kwanta.
ummi ce tace nazo nan na kwana.
faruk yace humaira bazan iya ba ki koma dakin ummi ki kwata, yaya za ayi na kwana dake daki daya agidan nan, ban so ma nakwana ba wlh dan baba yaki yarda ne.
humaira tace yaya gaskiya bazan koma ba, innakoma ummi fada zata min.
to muje na raka ki, da sauri humaira ta mike dan dama baso take ba.
suna shiga bakin kofar yace mata saida safe, ta bude dakin ta shiga, yana jiwo fadan da ummi kewa humaira , au dawowa kika yi.
tace shine yace nadawo.
faruk dake bakin kofar yace ummi ni nace ta kwanta anan, ummi ta girgiza kai .
bayan faruk ya wuce ummi tace Allah ya baki miji me natsuwa ga kunya amman ke baki sani ba, idai bak gyare halinki ba sai asamo mashi wata, kinga lokacin saiki zama yar kallo.
humaira jitayi haushi ya kamata dan ta tatsana taji ance faruk zai kara aure duk da dai ba wani son shi take ba.
washe gari faruk da wuri ya gama shirya wa, yana kokari fitowa sai ga humaira da kayan kari niki niki.
yace nifa bazan tsaya cin abinciba tafiya Zanyi.
saboda me tace da shi, yau fa baranar aiki bace balle kace zaka aiki
eh amman inason nakoma gida da wuri.
to ai in baka ci abincin ba ummi bazata ji dadi ba.
faruk yace hakane kuma, zubamin to.
waina ce lafiyayya da kunun tsamiya, ta tura mai gaban shi, yaja ya fara ci, tas ya cinye shi sannan yace humaira idan akwai karamin ,gaskiya ummi ta iya girki.
humaira dake kokari juye wa faruk ragowar wainan tace to malam ba ummi bace tayi nice niyi.
faruk dake kokari kai waina baki yace kai humaira anya kuwa, ban son karya fah.
tace to katam baye ummi kaji.
saida fatuk yaci ya koshi sannan ya musu sallama ya fito humaira na biye dashi har gun mutar sa
ya bude ya shiga yace to natafi sai na zo kenan .
eh tace tana yake hakora, faruk yace kinata murna makiyin ki zai tafi.
tace yaya wlh ba haka bane.
tsayawa yayi ya kare mata kallo ya hada rai yace koma ciki nina tafi
faruk haka yakoma gida jikin shi babu kwari shifa ko humaira bazata mai wani abuba yana son yaganta kusa da shi.
su momy na zaune sukaga yashigo wani iri.
momy tace lfy kuwa ko wane abu ya sami humair ne?
yace lfy lau momy kaina ke ciwo.
tace Allah ya kawo sauki, ya ka baro su?
yace lfy lau.
mikewa yayi ya shige daki, cikin dare kasa bacci yayi sai juyi yake akan gado, dan haka washi gari yana mikewa yadau waya ya kira number humaira , harta katse ba adaga ba, faruk ya kara kulewa.
itako humaira lokacin da faruk ya kirata, bata daki sai da ta shigo taga kiran dan haka takira shi , har so shida amman be dauka ba.
dan haka humara tayi tunanin ko yayi fushi ne, nan tafara neman number momy dan ta gaya mata, momy tace a,a kila dai baya kisa da wayar ne
bayan momy ta kashe wayar saita kirashi bugu daya ya dauka, tace mai inka tashi kazo, lokacin 8:35 na safe.
yana shigowa momy tace me yasa humaira takira baka amsa ba.
momy kiran ta nayi taki dauka, kuma ni gaskiya bazan iya barin ta tayi kwana biyar ba nan gaba, gobe zanje na dauko ta.
07014197556✍
***RABUWAR BAZATA***
(10)
ASALIN LABARIN
Cikin kankanin lokaco Iman ta fita hayyacinta, domin wani irin zazzafan zazzabi ne ya rufeta.
Abin da ya kara dagawa su Mina hankali shine, duk abinda taci ko tasha sai ya dawo, ga wani matsanai cin ciwon kai da jiri da yake damunta, wanda ko iya mikewa tsaye bata iya yi sai dai a riketa.
** ** **
Muhib ya kasa zaune ya kasa tsaye, labarin da yaji su Mahmud na bayarwa dazu ya tsaya masa a rai mutuka, dan wani irin tsorone da fargaba suke shigar shi, domin yasan duk abun da ya sameta shine sila.
Tausayin yarinyar da dana sani yake yi, domin shima tun daga ranar da abun ya faru yake cikin tashin hankali mara misaltuwa, saboda rashin dacewar abin da yayi, musanman ma ta fusakar addini, yasan ya sabawa Allah mutuka.
A kullum istigifari yake yi amma sai ya rinka jin laifin shi kamar dada karuwa yake. Yana ganin ya dauki fansar abinda tayi masa.
Sai kuma washe gari ya tashi da matsanaicin damuwa da bacin rai, saboda wannan shine laifi na farko da yataba aikatawa makamancin wannan a rayuwarshi.
Yana cikin wannan tuna nine su Munnir suka zungure shi.
''Lafiya over tun dazu muna ta magana baka jimu ba?''
Ya dan waske yace ''Sorry, ban ji bane shiyasa''.
Mahmud yace ''tuna nin mi kake hakane?''
Ya dan sosa keya yace, ''i am just thinking about some thing (kawai ina tuna nin wani abune)''
Muzaffar ya kalle shi yace, ''Nifa na fahimci wani abu''
Muhib ya ce '' me kake nufi kenan?''
Ya karasa saman sit din da suke ya zauna yace, ''Ina nufin tun da abun nan ya faru a social night kake cikin wani hali, kana dai boye mana kawai bayan kuma ka san bama haka a tsakanin mu, saboda duk damuwar dayan mu taruwa muke muyi maganinta gaba dayanmu''.
Munnir ya amshe da cewa, ''Ni ban ma ga abun damuea ba, tunda ka samu ka dauki fansar abinda tayi maka''.
Mahmud ya ce, ''Yanzu dai duk ba wannan ba, kayi mana bayanin abinda ke damun ka''.
Muhib yayi ajiyar zucia ya nisa yace, ''Na san za ku yi mamakin abinda zan fada, to amma har ga Allah ni iya gaskiyata kenan, domin abinda nayiwa yarinyar nan na mutukar damuna, musanmanma rashin lafiyar da takeyi a yanzu''.
Munnir ya ce, ''To ina ruwan mu, ba ita ta jawa kanta ba, kuma ma in ban da gulma mene ne abun rashin lafiya''.
Muzaffar yayi saurin dakatar dashi ya ce, ''Ba wannan maganar ya kamata mutsaya mu tattauna hanyar da zamu taimakawa Muhib kawai''.
Mahmud yace ''gaskiya ne, to yanzu mai yadace muyi?''
Munir ya ce, dazu a daining hall na ji wasu 'yan class dinsu na cewa, wai gida za a kai ta saboda magungunan da take bukata sunfi karfin hukumar makaranta''
Mahmud ya ce ''Ya ya za mu taimaka mata da magani, ai ina ganin sai dai mu nemi wata hanyar''.
Muzaffar yayi ajiyar zucia ya ce, ''Ni ina ganin bamu da wata hanya bayan wannan, ko ba haka bane Muhib? Anata magana kayi shuru.
Yadan sauke wata kasalalliyar ajiyar zucia ya ce ''To ni me kuke so in ce?''
Mahmud ya ce ''Kaima sa baki zakayi ayi shawarar da kai''.
Muhib ya nisa ya ce, ''Eh to , ni ina ganin shawarar da munir ya bada ta yi a matakin farko''.
''kana nufin bayan wannan taimakon nan gaba sai mun kara wani?'' in ji Muzaffar.
Muhib yayi wani dan murmushi mai ciwo yace ''idan ma ita ba zaku kara taimaka mata ba, ni kam ina da yakinin ni sai kun kara taimaka min a kanta''.
Via
¤Sman U.K
0 comments:
Post a Comment