(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Bismillahir Rahmanirrahim, inafarawa da sunan Allah
megirma da daukaka. Yanda zanfara rubutun nan lafiya
Allah yabani ikon kammalashi lfy.
GARGADI..... Banyarda wani ko wata su juyamun littafi
naba, ko kuma su canzamun labarina. Allah yabada ikon
kiyayewa.
GODIYA.....Ina mika godiya ta ga dukkanin masoyana
wadanda nasani dama wadan da bansani ba, nagode da
irin kaunar da kuke mani, duk da bazan samu damar
binku inyi maku godiya ba, amma nayi amfani da
wannan dama ga duk wanda yakaranta yazama
amatsayin sakon gaisuwa zuwa gareshi. Allah yakara
dankon zumunci.
Season 1⚜5
Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo
wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba, acikin
keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da
mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito
dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake
masa duk bayan kwana 3.
Sarki Qaseem ne yashigo dakin wanda yakasance
kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya
yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da
tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana,
Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine
hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi.
Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin.
Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da
damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace
zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka
wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a
akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma
kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi
tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake
so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya
Uba daya suke.
Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi
yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi
afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa
farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi.
Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan
mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh
Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska
acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni
acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da
Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika
sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar
maki Ticket nabarin duniyar baki daya.
Dariya Medaki tayi tace haba Gimbiyar Babbar Gida, aini
kinganni nan, tunda nataso haka Allah yayi ni, bandamu
dasena zama babba ba, inde zanzama 'yar kore kuma
inkarbu toni banida damuwa, zan iya yinkoma menene.
Dan haka kada kidamu, koda yanzu bamune matan sarki
Qaseem ba, aide kanin mijin mune. Kuma aide haryanzu
muna cikin masarautar.
Gimbiyar Babbar Gida tadauki apple tasa abakinta, ta
maida kallonta gurin Jakadiya, wadda take mata tausa
tace, Jakadiya bamu labarin cikin gida. Jakadiya ta gyara
zama tace Allah yatemakeki Babbar Gimbiya, wadda
babu kamarta, ba,ayi ba, kuma baza,a tabayin kamarki
acikin gidan nan ba. Allah yakara tsawon kwana. Babu
wani labarin daze firgitaki acikin gida, kinriga dakinsan
Gimbiya Shuwa haryanzu bata yarda dani ba. Narasa
dalilinta nayin haka, ace mace duk wani hali irin na
mijinta Sarki Qaseem tadaukeshi. Kodan ita tata sarautar
gado ce, shiyasa bata yarda da kowa? Medaki tace haba
Jakadiya atunanina babu wani abu daze baki tsoro acikin
masarautar nan, kinsan ketamu ce, muma haka. Dariya
tayi tace hakane, Gimbiya, karku damu asannu zakusha
labari.
Zaune take cikin wasu kodaddun kaya, acikin wata bukka
ta kara, wadda take daga gefen wata tsohuwar
MAKABARTA. Wani tsohon kwanone ahannunta,abinci
ne, aciki wanda gaba dayanshi bewuce rabin kwanonba.
Kyakkyawar matashiyace wadda bazata wuce shekaru 18
aduniya ba. Akusa da ita wata dattijuwa ce, wadda itama
bazata wuce shekaru 38 aduniya ba, da kaganta zakasan
tana cikin yanayi na hauka, gaba daya kamanninta sun
bata. Jawota diyarta tayi tana mata magana irin ta
kurame, tana mata nuni da kwano alamun taci abinci.
Dariya Uwar tayi cikin halin hauka tace a,a Babyta yau
bazanci abinci ba, kece zaki faraci, dariya yarinyar tayi
mata, dan taji abinda tafada, sede kawai maidawa ne
bata iyayi (KOMEYE DALILI🤔 OHO路♀ MUJE ZUWA).
Matsawa Wadda naji ankira da Baby tayi kusa da
Mamanta tasa hannu tafara bata abincin, itama hannu
tasa tana bata abinci. Kwalla ne, suka zubo ma baby tayi
saurin gogewa.
Wani Kyakkyawan Matashi ne, me kama da Larabawan
Shuwa, baze wuce shekaru 25 aduniya ba, da Sallama
yashiga dakin kyakkyawar matar, wacce take kishingide
abisa kafet din dakin. Murmushi tayi tace, Yarima Arif
sannu dazuwa. Kwanciya yayi kusa da ita yace yauwa
Momy na, sannu da hutawa. Kallon bayin cikin dakin
tayi, lokaci guda suka fita, Madarar shanu tamiko mashi,
ya amsa yana murmushi, yace Momy naje gurin Abba
ance yana dakin ganawa da baki, kuma inason magana
dashi. Kanshi tashafa tace to ai sekayi hkr kajira yagama
ko, wace irin magana kakeson yidashi? Momy dama
akan rashin lafiyar Baffa ne,tunda nadawo naga
yakamata ace anfitar dashi waje ko za,a dace. Murmushi
tayi tace Arif bakasan komai akan ciwon Yaya ba,
Abbanka yana kokari sosai amma koma menene idan
yafito zamu gana dashi. Kwallan idonta tagoge.
Kubiyoni domin jin labarin masarautar.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ...🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 5⚜10
Zaune suke adakin memartaba sarki Qaseem, Areef
yadora kanshi asaman kafar Abbanshi, Gimbiya Shuwa
Momyn Areef tana kusa da Sarki tana gyara mashi Inibi
tana mika mashi. Sarki yashafi kan Areef yace Yarima
inajinka wace magana kakeson kafadamun?
Tashi zaune Areef yayi yadauki inibi yasa abakinshi yace
Abba dama akan maganar Baffa ne, naga yanda nabarshi
haka nadawo nasameshi, shine nace meze hana afitar
dashi waje koza,a dace. Murmushi Sarki yayi yace wlh
Yarima nafika son inga Yaya yawarke, kozamu samu
damar yin bincike akan babbar matsalar datayi
sanadiyar shigarshi wannan halin. To amma Abba baka
ganin fitar dashi ze iya temakawa gurin samuwar lfyrshi
tunda acan sunfimu kayan aiki?
Hakane Yarima, amma babu yanda banyi da Yaya akan
yabari afitar dashi ba, yakiya gashi ba magana yakeyi ba,
sede yana jin duk abinda muke fada, yana ganin kamar
gara abarshi yayi tazama haka, wanda kuma hakan
bashine mafita ba, dole se mutum yana da lfy yake iya
komai arayuwarshi, ni babban damuwata wadancan
munafukan matan nashi, danni wlh haryanzu banyarda
dasu ba. Gimbiya tace hakane Me martaba, sede kasan
bamuda wata hujjar dazata nuna mana sune sanadiyar
faruwar komai agidan nan, kamarde yanda kace acigaba
da addu,a hakan zamuyi, fatanmu de Allah yasa Fulani
da abinda ke cikinta koma menene, yasa suna raye,
kuma cikin koshin lafiya.
Sarki yace amin. Kallon Areef yayi yace Yarima yanzu
angama karatu gashi zaka fara aiki kaga dole ace kaima
kashigo sahun manya ko? Kwantar da kanshi yayi saman
cinyar Gimbiya ya lumshe idonshi, shiru yayi bece komai
ba. Gimbiya tace Yarima yanaji kayi shiru kode boye
mana surikar tamu kakeyi? Murmushi yayi sosai wanda
har seda dimple dinshi ya lotsa duka 2, yace Momy
kubar maganar nan, niharyanzu banga macen danakeso
ba. Sarki yace aiko Yarima yakamata ace kafara
nemanta, dan kasan bazamu barka kazauna haka ba,
atsarin masarautar nan kasan baza,a barka kazauna haka
ba, damma de Yaya beda lafiya, ai da tunkafin kadawo
anduba maka acikin 'ya'yan sauran masarautun ansama
maka mata.
Dariya Areef yayi yace haba Abba niko aure zanyi ai
banason yar gidan sarauta, nafison insamu mace wadda
bata tashi acikin sarauta ba, kuma nibanason mace
wadda zatazo tarika rainamun iyaye, kawaide akaramun
lokaci ahankali zansamo wata wadda ra,ayina yayi dede
da ita.
Harararshi Gimbiya da Sarki sukayi atare, Sarki yace
uhm Yarima idanma mafarki kakeyi to kadena, acikin
masarautar nan babu yanda za,ayi kashigo mana da
bare, dole se yar sarauta, kana ganin yanda Momynka
dani kaina muka fito daga gidan sarauta, jininmu gaba
da baya cike yake da sarauta, kai kuma yanzu sekafara
zuwa mana da wani batu. Ka godema Allah Yaya beda lfy,
da kila seyafini daukar zafi akan wannan magana taka.
Duk da shima matar daya aura ta 2 data 3 basu fito daga
cikin gidan sarauta ba, amma kowa yayi mashi uzuri,
matarshi ta 2, agidan nan kowa yasan yanda akayi ya
aureta, haka ma ta 3 dole ce tasashi ya aureta, sekuma
babban rabon daya shiga tsakaninsu, bayan wannan
babu abinda zesa Yaya ya auri wata mata wadda ba,a
gidan sarauta ta taso ba.
Gimbiya tace Allah yahuci ranka Me martaba, banason
ranka yana baci akan wannan maganar, abinda bamu
taba yima Yarima agidannan ba, Fada shine yau da
bakinka kake mashi, kaima kasan Yarima mebin duk
wani umarninmu ne, ai base anbata mashi rai ba,
sekasashi shiga damuwa, wanda kuma betaso acikinta
ba, karka manta mungina rayuwarmu abisa soyayya dan
Allah kada kabari zafin zuciya yacanza maka zuciyarka.
Sarki yakamo Areef wanda idonshi har yayi ja dan bacin
rai.
Kwantar dashi yayi saman kafarshi yana shafa kanshi
yace ba ina nufin bata maka rai bane, kaji, kawai ina
maka tuni da ra,ayin masarautarmu ne, banaso kasa
wannan aranka haryadameka. Hawayene suka zubo daga
idon Areef, cike da damuwa Gimbiya tamatso kusa dashi
tace kagani ko, kalli abinda kajawo mashi, yaushe rabon
da Yarima yayi kuka agidan nan? Inajin tun yana yaro,
jawoshi tayi tamaidashi saman kafarta tace Ya isa haka
Yarima na, kasan Abbanka yana sonka baya son bacin
ranka yishiru hakanan.Sarki yace ya isa haka maganar
tawuce kaji, amma kaima kaje kayi tunani.
Lumshe ido Areef yayi, aranshi yana fadin akwai babban
aiki agabana, kuma gaskiya yanda ra,ayina yake bazan
taba canzashi ba, bana bukatar yar sarauta, duk da
haryanzu bansamu wadda nakeso ba, amma zantajira
seranan dana samu sannan, nasan suna sona, dole zasu
barni na auri ra,ayina. Amma dole nacirema su Momy
wannan ra,ayin nasu.
Anesa da masarautar Sarki Qaseem, wani dankaramin
gidane, me kyau, duk da karami ne, amma anyi mashi
gini mekyan fasali. wani tsoho ne, fari, yafito daga cikin
gidan, daka ganshi zaka gane ba asalin bahaushe bane,
yafi kama da irin larabawan dasuka baro garinsu sukazo
nigeria har zama yakamasu anan, zama yayi bisa wata
kujera dake kofar gidanshi ya kunna redio yana kokarin
kamo tasha.
Tundaga nesa yahango fadawan sarki suna zuwa,
murmushi yayi, cikin hausarshi wadda bata gogeba, yace
aikin kenan, kullum azo adameni da kira, kuma haryanzu
ankasa samo mani Diyata, da abinda ke cikinta. Kwallar
data zubo mashi ce yasa hannu yagoge. Da sallama suka
karaso gurinshi, ahankali ya amsa masu. Daya daga cikin
fadawan yace Barka da hutawa Baba, yace yauwa
sannunku, yauma wani kiran neko?
Murmushi Bafaden yayi yace a,a Baba, dama Sarki ne,
yace muzo mukawo maka kayan abinci. Murmushi yayi
yace to madalla, nagode, yajikin me martaba? Bafaden
yace to Baba dasauki zamuce, kasan sauki sede agurin
Allah, fatanmu de Allah yanuna mana inda Gimbiya take
ko zamu samu Hankalin kowa ya kwanta. Baba yace
addu,a kam kullum munayinta, sede haryanzu acikin
raina nakasa yarda cewa Rayhana itace tabar gidan Sarki
da kanta, kuma nakasa yarda cewa bata raye, inaji
ajikina wata rana zamu gana da ita, fatana de Allah yasa
kome tahaifa ace yana raye. Sukace amin Baba, bara
mushigar maka da abincin ciki, yace tonagode, dama
gashi bayin dasuke dafamun abincin sungama aikinsu
suntafi, kushigarmun dashi ciki.
Jakadiya ce take tafaman Sallama abangaren Gimbiyar
Babban Gida, daga ciki akace shigo mana Jakadiya, tace
Gafaranku de, ai nadauka ko bacci kikeyi, Allah
yatemakeki Babbar Gimbiyar Sarki, Allah yakaramaki
lafiya da tsawon kwana, Allah yabaki muma musamu
awajenki, ke kadaice Babbar mata agurin Sarki, duk
wanda yazo sede yabiyo bayanki. Daga gefe Gimbiya me
Daki tarika wurga mata harara jin irin kirarin datakeyi
ma Kishiyarta.
Murmushi Gimbiyar Babban Gida tayi tamata nuni data
zauna, guri tasamu tazauna sannan takalli Gimbiya
medaki tace Ina gaisuwa ranki yadade. Murmushi tayi
tace sannu Jakadiya, daga ganin bakinki akwai magana,
meke tafe dake?
Babban labari ne yake tafe dani kuwa Gimbiya. Dazu
nazo wucewa tagefen Dakin memartaba Sarki Qaseem,
senaji yana magana kamar yana fada, dajin haka nayi
saurin daukar tsintsiya nayi kamar ina shara, sede na
boye fuskata, gudun kada aganni tunda ansan ba,a
bangarensu nake aiki ba, asalima nice mebada umarnin
ayi aikin........ nan takwashe duk abinda taji sunfada ta
fada masu.
Tashi zaune Gimbiyar Babban Gida tayi, tace gaskiya naji
dadin wannan labari naki Jakadiya, dan haka kina da
kyauta me tsoka. Washe baki Jakadiya tayi tace godiya
nake Gimbiya, Allah yakara girma. Amma Me daki wace
irin shawara kike ganin yakamata mubi don mu samu
muyi amfani da wannan dama?.
Gyara zama tayi tace, inaganin tunda har Sarki ya furta
Bayason Yarima ya kawo mashi bare, meze hana kisamo
daya daga cikin matan gidan sarautarku kimaidota gidan
nan. Murmushi Gimbiya tayi tace Medaki kenan, kina
tunanin Gimbiya Shuwa zata bari Yarima yaso wata data
fito daga bangare na? Kinfi kowa sanin bama ga maciji
da ita, dan haka wannan shawara taki bata karbu ba.
Jakadiya kawo mana mafita.
Kara hade rai Medaki tayi jin ba,a karbi shawararta ba,
sede yata iya, tunda bata da karfi agidan, dole tabi
asannu kodan tasamu fada. Jakadiya tace Gimbiya
inaganin tabayan gida yakamata mubiyo masu, tunda
bazasu taba karbar abinda yafito daga gurinki ba,kamar
yanda mukayi da farko yanzuma hakan yakamata ayi.
Kayataccen murmushi Gimbiya tayi tace haka nake sonki
Jakadiya. Allah yakaimu.Yarima Areef ne kwance adakinshi, shida abokinshi
Haisam, suna fira, Haisam yace Yarima yanaga kamar
wani abu yana damunka? Yamutsa fuska Areef yayi yace
kawai kabari Man, wlh jiya Abba da Momy suka kusa
samun hawan jini. Dariya Haisam yayi yace uhmm nasan
wasa kakeyi, yanda Abba Da Momy suke sonka, harzasu
iya bata maka rai, kaifa agurinsu haryanzu yaro ne, dan
haryanzu baka girma da hawa cinya ba. Areef yace
banason sharri, idan wasu sukaji kace hawan cinya ai
sesu dauka rungumeni akeyi.
Dariya suka saka, Areef yace wlh Man ba maganar wasa
ba, aide kasan irin burina akan matar danakeso na aura
ko? Yace E, yauwa to jiya daga nafada masu kalar matar
danakeso shikenan, suka rufeni da fada, kasan ai ra,ayin
momy da Abba duk daya ne, kuma nasan wannan
magana dasuka fada harcikin ransu. Haisam yace kada
kadamu, kaida ko matar ma baka samuba, meye naka na
damuwa?.
Areef yace kaide ai dole nadamu, kasan me kwarmin ido
dawuri yake fara kuka. Haisam yace abinda nakeso
dakai, addu,a zaka cigaba dayi domin itace mafita,
nikaina bana maka sha,awar auren macen gidan sarauta,
kasan mata da sarauta, basu iyata ba, nafison kaje waje
ka auri wata daban, hakan zebaka kwanciyar hankali
sosai. Areef yace nima ai jinsu nakeyi, dan bansamu
wadda nakeso bane, shiyasa nayi shiru, amma duk
lokacin dana samu, agskiya sede kowa yayi hkr, dan
bazan iya biyayya anan gurinba. Haisam yace muje
mugaida Baban Umma fulani kwana 2 bamuje ba, tashi
Areef yayi yana fadin wlh nima yana raina, dan
bakaramin tausayi yake bani ba, ace mutum yazo gari da
iyalinshi amma yanzu beda kowa, matar ta mutu diyar
kuma babu wanda yasan halin datake. Muje mudawo,
dan dazu waziri yake fadamun gobe zamuje darazo wai
Abba ze aikemu. Haisam yace kai gsky zanje, nima
inason zuwa Darazo, fita sukayi suna dariya.
Washe gari tunda safe suka dauki hanyar bauchi, daga
can suka wuce darazo, tare suke da Jakadiyar Gimbiya
Shuwa, dan itama garinsune shiyasa tabiyosu tanason
tayi kwana 2. gidan wani babban malami sukaje, kuma
dama shine malamin dayake masu addu,a akan batan
matar Sarki Fulani. Bayan sungama gaisawa, suka fadi
sakon Sarki, malam yace haryanzu muna nan muna
addu,a sede kuma babu abinda ya nuna mana bata raye,
akullum muna ganin tana raye, kuma akusa damu, danni
abinda nake gani tafi kusa dani akan inda kuke, to Allah
shine masanin gaibu, shikadai yafimu sanin gsky. Zamu
cigaba da addu,a har Allah yasa mudace.
Ruwan addu,a yabada akaima Tsohon Sarki, godiya
sukayi mashi, Waziri yasa fadawa suka shigo da kayan
dasukazo dasu. Waziri yace to muzamu koma. Malam
yace tonagode, kallon Jakadiya yayi yace ammade
Jakadiya ke anan za,a barki kidan mana kwana 2 ko?
Tace E Malam, dama cewa nayi inzo inganku. Yace to ai
yayi dede kishiga daga ciki. Tashi tayi tace to Yarima
Allah ya kiyaye. Yace amin sekin dawo.
Bayan suntafi wani tsoho yazo yace yanason ganin
malam, malam yace ashigo dashi, bayan sungaisa Malam
yace Baba meke tafe da kai? Tsohon yace wlh wata
magana ce take tafe dani, nadade inaso inzo insameka
amatsayinka na babban malami agarin nan, duk da ba,a
cikin gari nake ba, amma inada labarinka, nine megadin
MAKABARTAR datake wajen gari. Akwai wani abun
mamaki dayake damuna, wanda yadade yana faruwa,
sama da shekara 18, akan wata mata da diyarta. Malam
yace Baba inajinka bani labarin abinda kasani.
Kubiyoni zakuji yanda komai yake. Nagode da
kaunarku.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 10⚜15
Malam yace inajinka Baba, dama Allah gafarta
malam, tsawon shekaru 18 dasuka wuce nakasance ina
gadi a MAKABARTAR bayan, gari, akwai ranar danayi
rashin lafiya har kimanin tsawon sati guda banje gurin
gadi ba, arana ta 8 danaje, inadan zagaya
MAKABARATAR. Can daga nesa da ita naga wata rumfar
kara, wadda daga gani kasan bata dade dayi ba, kuma
gsky malam rumfar bawata rumfar arziki bace, dan
ansha yin ruwan sama tana yacewa, sede abun mamaki
da gari yawaye zan iske anmayar da ita.
Ganin wannan rumfa danayi bakaramin tsoro naji ba,
dan tunda nake gadi rumfata ce kadai agurin, matsawa
nayi abin mamaki malam senaji kukan jariri aciki. Bayan
nayi addu,a sena karasa gurin. Inazuwa daga ciki
nahango wata babbar mata me alamun tabin hankali
tana rike da yarinya ahannunta.
Da sallama nashiga gurin, saurin dagowa matar tayi tana
kallo na, guri nasamu nazauna, nace baiwar Allah
mekikeyi acikin MAKABARTA kuma hada yarinya
jaririya? Kawai senaga tanamun dariya, malam abinda
na lura wannan yarinyar diyarta ce, dan agabana naga
tafiddo nono tana bata.
Ganin wannan mata bazatayi mani magana ba, kawai
sena fita , cikin rumfata naje nadauko abincin danaje
dashi nakoma nakai mata. Inazuwa na iske yarinyar
hartayi bacci, matar namika ma abinci, segashi ta amsa
tana dariya, zama nayi harta gama namika mata ruwa
tasha, kallonta nayi nace baiwar Allah kozaki bini gidana
inkaiki keda jaririyarki? Saurin kallona tayi tana girgiza
kai, nace ba cutarki zanyi ba, amma akwai hadari
azamanki gurin nan.
Kuka naga tafara tana kara rike diyarta, haka nayita
lallashinta hartayi shiru, ganin idan nakara mata magana
zatayi kuka yasa nafita nabarta. Ganin har magriba tayi
duhu yakarayi se tausayinsu yakamani, komawa nayi
nasameta rike da diyarta, sun kwanta. Maganar dazu
nakara yimata. Amma abun mamaki seta samun kuka,
kamar daga sama naji wata murya tafara magana.
Yakai wannan bawan Allah me tausayi, kasani kamar
yanda kayi niyar temakon wannan mata da diyarta,
muma haka muke temakonta, kuma kaci sa,a dakazo da
niyar temako, dan munyi alkawarin duk wanda zezo da
niyar cutar dasu bazamu kyaleshi ba. Wannan mata haka
Allah ya kaddaro mata rayuwarta agurin nan, kuma
tunda ba,a sonta mu muna sonta, dan haka babu wanda
zamu bari yadauketa agurin nan. Kabarta, Allah yana
tare da ita, kuma muma muna tare da ita, amma tunda
kaima mazaunin gurin nan ne, zaka iya temaka mata.
Bakasan komai game da ita ba, mune muka sani, dan
haka munaso kabarta kamar yanda ka ganta, shiyasa
aduk lokacin daza,a kawo wata gawa babu wanda yake
cin sa,ar ganinta.
Malam tunda naji wannan magana na tabbatar ma kaina
lallai ba Bil,adama bane suke magana aljanune, hakan
yasa na kyale matar nan, dan sunce basu san na matsa
mata da tambaya, haka muka cigaba dazama a
MAKABARTA tare dasu, yanda suka umarceni kada
infadama kowa, haka nayi shiru ko medakina ban
fadamawa ba, sede yan kayan diyana mata harma dana
medakina idan naga sun tsufa nakan dauka ince mata
wasu zan kaimawa.
Tun ina tsoron zama dasu har muka saba sosai, kuma
ina kokarin bata abinci, sede duk sanda naje inasamu
kamar taci abinci, dayake akwai rafi agaba damu, haka
nasamu bokiti ina kawo masu ruwa ina aje mata, dan
naga ita kezuwa tana dibar ruwan dakanta, kuma acikin
wata karamar robace. Haka rayuwarsu taci gaba da
tafiya, har wannan yarinya tayi wayo, da kaina naje nace
tadena bata nono, nadauki yarinyar nafara bata abinci,
daga nan tafara cin abinci.
Aduk lokacin dana tafi daniyar fadama wani wlh malam
dana dawo zan iske bata gurin, setayi kwana 2 ko 3 bata
dawo ba, haka suka kara jamun kunne akan inyi hankali,
tunda har aka haifi yarinyar nan agurin to nanne gurin
zamansu, duk ranar dana kara kokarin fadama wani duk
abinda yafaru dani ni najama kaina. Haka na hakura
mukaci gaba dazama, amma harcikin raina na kudurta
sena temaka masu, dan abinda suke masu ba temako
bane, duk da agurinsu suna ganin kamar temakonsu
sukeyi, amma abinda nagani taya za,ayi dan adam
yazauna a MAKABARTA kuma ace anan ze rayu.
Ganin idan nacigaba da matsa masu zan iya rasasu kuma
bansan inda zasu kaisu ba, yasa naja bakina nayi shiru,
dannasan wata rana zantemakesu. Haka muka cigaba da
rayuwa, munyi sabo dau sosai, diyarta tayi girma sosai,
ganin yarinyar tayi girman daza,ace tafara sanin addinita
yasa nace bari infara koyamata daga cikin abinda nasani,
duk da nima bawani ilimi mezurfi gareni ba, amma
Alhamdulillahi inada dede gwargwado. Dayake tunbayan
daya kamata ace yaro yafara magana yayi, amma shiru
ita yarinyar wadda Innarta tarada mata Baby, amma
nikuma ina kiranta da yar Baba sbd munshaku da ita
sosai, tun lokacin dana gane bata iya magana, sena lura
da idan Innarta tayi mata magana tanaji, kuma nima
haka, tun alokacin nagane yarinyar tanada matsalar
rashin magana, wanda bansan dalilin hakan ba, dan duk
kurman dana sani inde ba harshenshi ne yadatse ba,
zaka sameshi bayaji, kuma baya magana, amma ita nata
seyazo dasabani.
Haka muka rika maganar kurame da ita amma idan itace
zatamun magana, amma idan nine zanyi mata lafiya lau
zanyi tunda tanaji. Dun daga wannan lokacin muka fara
karatu tundaha sarki harzuwa sallah da karatun da akeyi,
sede nine kawai nake koya mata, idan bata gane ba,
tanamun alamu.
Mahaifiyarta wani lokaci se inga tazauna tana ta kuka
wanda idan tafara batayin shiru seta dauki lokaci, konaje
zan bata hkr yar Baba zatamun alamu da in kyaleta,
alokacin da girma yazo ma Yar Baba haka nazaunar da
ita nakoya mata yanda zata gyara jikinta, da abinda zata
bari na ibada, da kuma yanda zata tsarkake jikinta idan
lokaci yazo. Wlh malam hankalin yarinyar da natsuwarta
kadai ya isa yasa tashiga ranka.
Hatta da kitso wannan matar ita take yimata, sede ita
matar bata bari agyarata, shiyasa idan kaganta zakaga
gaba daya tafita hankalinta. Ko ciwo yasamesu nine nake
samo masu magani, amma wadannan aljanu basu barin
ko matar tabar cikin MAKABARTAR, iyakarta bakin rafi,
shima tunda nake dauko masu ruwa tadena fita.
Akwanakin baya nayi rashin lafiya wadda ta tadamun
hankali, banyi tsammanin zan tashi ba, kullum tunanina
yazanyi da wadannan bayin Allah. Inacikin ciwon
nasamu na tafi MAKABARTA gurinsu, haka naje nasamu
Yar Baba duk tarame, kuka kawai takeyi, tana ganina ta
taso da gudu tazo tana murna, alokacin nagane dalilin
kukanta, harta da ita Matar marar hankali seda tayi ta
murna. To malam bayan nawarke kuma nafara tunanin
yanda zanyi, shine nasamu labarinka, nikuma nayi
alkawarin zanzo gurinka, duk da ayanzu bansan wane
mataki aljanun zasu dauka akaina ba, kuma zamuje
musamesu, ko kuwa sun daukesu. Wannan shine babbar
damuwar dana taho ina tunani.
Salati malam yafarayi, da tasbihi jin wannan al,amari.
Gyaran murya yayi yace tabbas Baba kazo da magana
me ban al,ajabi, kuma kaima kayi kokari sosai, wanda
bakowane ze iya abinda kayi ba, lallai duniya babu gsky,
tsoron Allah yayi karanci aduniyarmu da zukatan
mutane, yanzu dan Allah ina wanda yakeda alhakin
haukatar da wannan mata zesa dumbin zunuban daya
dauka nata ita da yarta har na tsawon shekaru 18?.
Innalillahi Wainnailaihirraji'un. Yanzu Baba abinda
nakeso da kai, ka kwantar da hankalinka, insha Allahu
babu abinda ze sameka, kuma zamuje musamesu a inda
kabarsu, addu,a zata temakemu akan wadan nan aljanu,
kuma zanyi magana dasu, dan suma basuda niyar cutar
dasu, asalima suna temakonsu ne. Bara inkira sauran
dalibaina su shirya muje musamesu, amma ai bazamu
bar bayin Allah acikin daji ba, kuma a MAKABARTA.
Kodan lafiyar ita yarinyar.
Tashi yayi yakira yaranshi yafada masu su shirya zasuje
wani guri, koda yadawo, yasamu Baba yana jiranshi,
haka suka dauki mota yasa aka kira Jakadiya da matarshi
suka shiga, dan sutemaka masu gurin daukosu. Baba
addu,a kawai yakeyi Allah yasa su samesu, agurin.
Nima nace amin Baba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 15⚜20
Hankali tashe Baba yafito daga motar yanufi inda
rumfarsu take, amma abun mamaki babu ita babu
dalilinta, idan ba wanda yasan da ita ba, babu wanda
zece mutane sun taba zama agurin. Wasu irin zafafan
hawayene suka fara zarya afuskarshi yan fadin Innalillahi
wainna ilaihirraji,un. Zama yayi adede inda rumfar take
yana kuka.
Malam ne, yakaraso gurin yadafashi yace Baba ba kuka
yakamata kayi ba. Insha Allahu nizan dawo dasu duk
inda sukaje, dama munsaba da aljanu, masu taurin
kaima ina gogawa dasu, har kafiran cikinsu muna fama
dasu, bare kuma wadannan da alama musulmai ne.
Baba yace wlh malam, da,a ace sun dauke su Yar Baba
bansan inda suke ba, gara ace banfada maka ba, muyita
zama dasu anan har mutuwa tazo tasamemu. Tsautsayi
ne, da kuma tausayi yasani karya dokar dasuka saka
mun.
Shiru malam yayi, can ya kalli daya daga cikin yaranshi
yace daukomun shinfida acikin mota kataho mun da
gorar ruwa, bayan yakawo mashi ya amsa yafara alwala,
shikuma ya shinfida mashi abin sallah. Kallonshi yayi
yace kacemasu Jakadiya sukoma mota suzauna
harsenace sufito.
Sallah yafara yi, kowa yana kallonshi, seda yayi raka,a 4
sannan yazauna yafara karatu, da yayi seya tsaya yayi
adduo,i sannan yacigaba. Seda yadauki tsawon minti
talatin, sannan wata kura ta taso kafin wani lokaci sega
rumfar su Yar Baba ta bayyana agurin datake. Hamdala
malam da Baba sukayi, dasauri Yar Baba ta iso kusa
dashi tana dariya. Daya daga cikin yaran malam, wani
yace Tsarki ya tabbata ga mahaliccin dayake tsara
halittun bayinshi. Anya wannan yarinya mutum ce? Aini
tunda nake bantaba ganin yarinya me kyanta ba, damma
wai tana cikin rashin galihu, wannan da,a birni take
gidan masu kudi ai se anrika boyeta.
Dariya nakusa dashi yayi yace kaima kenan dakake iya
magana. Baba se shafa kan Yar Baba yakeyi yana
murmushi, ita ko tashige jikinshi don da alama tsoron
mutanen gurin take, dan atsawon rayuwarta bata taba
ganin kowa aduniya ba, daga Mamanta se Baba.
Mamanta kuwa kasa fitowa daga runfar tayi, se kuka
takeyi.
Malam yace Alhamdulillahi, Allah mungode maka, kallon
gefenshi yayi yace bayin Allah, meyasa bakuso atemaki
wadannan mutanen? Kowa yafara kallon inda malam
yake magana, sede babu alamun kowa agurin, maganar
mutum daya tafara tashi me cike da alamun ladabi.
Allah yagafarta malam, mundauki tsawon shekaru 18
muna tare da wadannan bayin Allah, mune muka temaki
wannan mata, alokacin da takusa halaka, wanda babu
wani dan adam daze iya temakonta, semu, kuma ga
dukkanin alamu munga kamar hadari ne, ya jefota gurin
datake, sede koda muka bincika bamuga alamun mota
tayi hadari ba, asalima mugunta akaso ayima wannan
mata. Shiyasa muka temaketa, sede haryanzu Allah
bebamu ikon gano dalilin daya kawota nan ba, kuma
babu wani asiri ajikinta, wannan lalurar datake tare da
ita da alama kode ajikinta take, ko kuma buguwar datayi
ne yakawo mata ita. Malam yace naji, amma me kuka
sani game da ita? Tsawon shekaru 18 dasuka wuce wata
rana da dare muna zaune afadarmu.
Se kawai mukaji fadowar wani abu akusa damu, sede
abun mamaki, muna dubawa semukaga mace ce da
tsohon ciki, kuma cikin ikon Allah babu abinda yasamu
cikin, anan muka kara dubawa semukaga tabbas bil
adamace, anan nasa yarana dasu dubamun ko hadari ne
akayi, dayake akasan wani rami muke, hakan yasa nayi
zaton ko hadari ne, dan wani lokacin idan akayi hadari
mutane suna fadowa nan. Bayan yadawo yace mun
babu wata mota datayi hadari, kafin mu ankara
semukaji wannan mata tana nishi da karfi, nan take
nagane haihuwa zatayi, anan nasa akayima me dakina
magana.
Allah gafarta malam, ita dasauran wasu jinsinmu suka
temaka mata harta haihu, sede koda ta haihu bata cikin
hayyacinta, haka suka gyarata ita da diyarta, aka samo
kaya aka samata, anan nace su kwantar da ita kusa da
mahaifiyrta. Dayake safiya takusa, haka muka tashi
mukabarta agurin ita da yarinyarta, anufina idan gari
yakara haske kila wasu suganta sutemaketa.
Bayan dare yakarayi muka sake dawowa fadarmu,
abun mamaki kuma bamuga wannan mata ba, senayi
tunanin wasu sun daukesu, muna nan zaune sega daya
daga cikin yarana yazo yacemun ahanyarshi tazuwa nan
yaga anyi wata runfa agefen wata MAKABARTA sede yar
karama ce akayi, daya kara matsawa seyaga wata
jaririyace kwance acikin rumfar, saman hakukuwa
anshinfida mata zani tana bacci, daga waje kuma wata
mata ce kwance agaban rumfar, dan tayi masu kadan
bazasu iya shiga su 2 ba, asalima rumfar yara ce, abinda
yabashi tsoro yaga wata halitta daga cikin jinsinmu sede
basa cikin zuri,armu wato musulmai, yaganta tana
kokarin daukar yarinyar.
Shine yaje gurin dasauri, to dayake sunsan kowaye kuma
suna tsorona, yana ganinshi yayi saurin bacewa. Shine
yazo yana fadimun, koda nasa adauko munsu senaga
wannan matar ce tajiya, nan take tausayinta yakamani,
anan nayi alkawarin kareta ita da yarta kuma babban
dalilin dayasa nabarsu aMAKABARTA, sbd bazeyiwu
nakaisu cikin jinsina ba, haka kuma nagane bil adama
basuda tausayi harsuka iya barin wannan mata ita da
yarta acikin daji babu metemakonsu, shiyasa nasa
yarana suka yimata rumfa babba wadda zata isheta ita
da yarta, kuma nasaka yarana suzama masu gadinsu.
Kasancewar bata da hankali yasa abubuwa da dama
mune muke temakonta dasu, tundaga abinci dakuma
ruwa, na hana yarana subarta tafita daga MAKABARATAR,
sbd ina gudun kaidin bil adama, ko gawa aka kawo babu
wanda yake iya ganinsu, nina zaba masu suyi rayuwarsu
ahaka. Aranar da megadi yazo lokacin yarana suna
sallah, basuyi tunanin wani zezo ba, hakan yasa shima
yayi sa,ar ganinsu.
Danaga shima yanada zuciyar imani hakan yasa na
kyaleshi yacigaba dazama dasu, sede banyarda
yafadama kowa ba, dan nasan zuciyar kowa daban take,
kuma yayimun alkawarin baze fada ba, mune muke
daukesu aduk lokacin dayayi niyar fadama wani.
Koyanzu yaci sa,a kaine yafada mawa, amma daba kai
bane, yanda muka daukesu nayi niyar bazan ajesu anan
kasar ba gaba daya, gara nakaisu wata kasa inda babu
wanda yasansu, nasan zasu temakesu. To malam
wannan addu,ar dakayi ita kadai tadawo damu. Kuma
nayima Baba hakuri tunda naga alkhairi yakeson su
dashi, yanzu Malam kome kayanke zamubi umarninka,
amma kasani duk inda zaka kaisu kada karabasu dan
yarinyar nan bazata iya zama awani guriba batare dasu
ba. Kaima Baba kasan yanda kuka shaku.
Malam yace naji dukkan bayaninka, kuma naji dadi sosai
daya kasance kaine katsinci wadannan bayin Allah, nasan
irin halin temako dakake dashi bazaka taba barin wani
abun cutarwa yasamesu ba. Allah yabiyaka kaida
yaranka, hakika zakaran da Allah yanufa da cara, to ko
ana muzuru ana shaho seyayi. Tabbas wannan yarinya
Allah kadai yasan irin alkhairin data debo kuma shine
yaraya abunshi. Yanzu abinda nakeso infada maka,
gaskiya zaman yan adam agurin nan beyi ba, saboda
rayuwar gaba, kaga wannan yarinya tagirma, yakamata
ace tashiga cikin mutane, dan kada wata rana tafi haka
girma ace zata koma cikin mutane abun ya gagara, kalli
yanda take cike da firgici sbd ta ganmu wanda banga
laifinta ba, nasan bata taba ganin kowa ba, se mutum 2.
Dan haka nayi maka alkawarin zandaukesu zamuje mu
sama ma wannan mata magani, duk da kace ciwonta
babu asiri ajiki, zamukaita asibiti aduba lafiyarta, kuma
nizan rikesu tamkar jinina. Nagode sosai daka
fahimcemu. Godiya sosai Malam yayima wannan
shugaban aljanu sannan yabace.
Malam yace to Baba kajide yanda mukayi dashi, yanzu
yakake ganin za'ayi? Baba yace naji dadin abinda kayi,
kuma dama abinda nake fata kenan arayuwata inga
ranar dasu Yar Baba zasu bar gurin nan, shiru yayi yana
goge kwallan idonshi. Malam yace yanzu kutashi muje
gida semusan abinyi. Jakadiya da matarshi yasa sukamo
maman Yar Baba, tana ganin zasu dauketa tafara kuka
sosai, da kyar suka kamata, shima seda Baba yaje
yakamota yarike hannunta dana Yar Baba sannan ta
bisu, gurin shiga mota kuka Yar Baba tasa masu, tsayawa
tayi takishiga motar, duk tarike Baba, dakyar yasamu
tashiga, haka suka nufi cikin gari.
Zaune suke afadar Sarki Qaseem, Waziri yamika gaisuwa
tare dafadin Allah yatemakeka, munje kuma mun isar da
sakonka, malam yace afada maka sunanan suna addu,a
insha Allahu za,a dace, kuma yace afada maku Fulani
tana nan araye, sede haryanzu Allah be gwada mashi
inda take ba. Ga wannan ruwan addu,a ne yace akawo
na me martaba.
Areef ne ya amshi addu,ar ya ajeta agefen Sarki.
Gyaran murya Sarki yayi yace to Alhmdullh, inaganin
muma semucigaba da addu,a nasan wata rana Allah ze
bayyana mana Fulani da kuma abinda tahaifa, addu,ar
mu Allah yasa kome ta haifa ace shima yana raye. Waziri
yace maganar gashin jikin memartaba, meze hana a
maidashi yazamana duk bayan kwana 2 sbd inaganin
hakan zefi temaka mashi. Sarki yace hakan ma yana da
kyau, muje abashi maganin. Areef yatashi yadauki
maganin suka nufi gurinshi.
Gimbiyar Babbar Gida suka samu agurinshi tana bashi
kayan marmari, sallama Waziri yayi, daya daga cikin
fadawan yaje ya sanar da ita zuwan me martaba.
Komawa yayi yamasu iso sannan suka shiga, bayan
sungaisa yatambayeta mejiki tace dasauki, tashi tayi
tafita, jakadiya ta mara mata baya.
Duka sauran bayin suka fita, se Babban Hadiminshi ne,
kuma wanda sarki ya aminta dashi ne kadai yarage,
karbar robar Sarki yayi yazauna kusa da Yayanshi, yace
sannu yaya, Malam yace yana gaisheka, kuma yace
abinciken dayayi yagano Fulani tana raye bata mutu ba,
insha Allahu zecigaba da addu,a za,a ganta. Kokarin dago
kanshi yafarayi jin anyi maganar Fulaninshi, cike da farin
ciki Sarki da Waziri suka temaka mashi yajingina, wani
murmushin farin ciki ne, ya bayyana afuskarshi. Shima
Sarki dasauran mutanen dakin kowa farin ciki ne, yacika
fuskarshi.
Sarki yace hakane Yaya bata mutu ba, ga wannan
maganin yace abaka kasha, dan Allah kada kaki karba,
kaga yau shekara nawa ana kawo magani baka sha, ayau
naga farin cikin dana dade bangani afuskarka ba, inaso
kasha maganin nan, kaga kaima zaka samu karfin yimata
addu,a.
Babu bata lokaci yabude baki, Sarki dakanshi yabude
robar yayi bismillah yafara bashi maganin, tas yashanye,
aka dauko dayar robar Sarki yace wannan ajiki za,a shafa
maka, kallon Waziri yayi, babu bata lokaci yakama keken
yaturashi suka nufi daki. Cike da farin ciki Areef yafita
yanufi bangaren Momynshi. Dede zewuce alambu
yahadu da sarkin Fada, kara hade fuska yayi, sarkin fada
yamatso dasauri yana washe baki yace Allah yatemaki
mejiran gado. Hannu kawai Areef yadaga mashi yawuce,
da harara Sarkin Fada yabi bayanshi, kwafa yayi sannan
yayi gaba.
Bayan sunje gida dakyar Yar Baba tasaki Baba Jakadiya
takamata ita kuma Ladidi matar Malam takama Maman
yar Baba suka shiga ciki, haka yaran gidan suka rika sakin
baki suna kallon Yar Baba, itam seboyewa take ajikin
Jakadiya. Daki takaita tazaunar da ita, haka suka kama
Mamanta suka nufi bandaki da ita, da kyar sukayi mata
wanka, sun sabata yafi so 5, haka suka fito da ita se kuka
takeyi.
Dakin Ladidi suka kaita, sannan Jakadiya tariko Yar Baba
takaita bandaki, kintsayawa tayi, dan bata taba ganin irin
shiba, seda Jakadiya ta tsaya takoya mata yanda zata
wanke jikinta da soso haka tasata tayi wanka tawanke
mata kanta, sannan suka fito, kallo daya zakayima yar
Baba kagane tsanin kyan datake dashi, dan kamatake da
larabawa.
Bayan sungama shiryasu suka basu abinci anan maman
Yar Baba takwanta se bacci, yar Baba kuwa tanajikin
Jakadiya takwanta tayi shiru, ita kuma tana gyara mata
gashinta, wanda yaji mai se kyalli yakeyi, daga haka
itama tayi bacci. Malam ne yaleko yace idan sungama
sufito suji abinda ya yanke akan su Yar Baba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 20⚜25
Malam yayi gyaran murya ya kalli Baba yace nataraku
anan dan infada maku abinda nayi tunani akan
wadannan bayin Allah, da farko de dakai zanfara Baba,
kaga kamar yanda akayi mana bayanin akan 'Yar Baba,
bazata iya rabuwa da kai ba, shine nace meze hana idan
har kanajin zaka iya zama dasu, kayi hkr da waccan
sana'ar taka kadawo nan cikin gari kaida iyalanka
nikuma namaka alkawarin gurin zama harma da aikinyi
aduk inda kake so.
Amma Baba kaduba kagani mekace? Gyara zama yayi
yace agskiya Malam, nikaina banajin zan iya hkr da
rashin 'Yar Baba akusa dani, nayi sabo da ita sosai wanda
basauki bane ace za'a rabamu, kuma kamar yanda nayi
alkawari zankula dasu nayarda zanbar aikina da
muhallina indawo nan mucigaba dazama.
Malam yace gaskiya naji dadi, kuma insha Allahu zaka
samu aiki me kyau, duk da acan ma aikin lada kakeyi nan
ma wani aikin ladan ne, tunda temakon bayin Allah
zakayi. Zamucigaba dazama dasu anan kuma gobe
zamuje asibiti mukai ita wannan mata domin a aunata
asan wace irin kalar hauka gareta, idan maganin asibiti
ne, se adorata akan magani, idan kuma na hausa ne,
semudawo acigaba dayi mata addu'a.
Jakadiya tace Yaya, dayake kanwarsu ce itace auta, tunda
mijinta yamutu bata kara aure ba kuma bata taba
haihuwa ba, shine Malam yasama mata aiki agidan Sarki,
ta dalilinshi Gimbiya Shuwa tabata Jakadiya dan tace ta
aminta da ita. Kallonta yayi yace inajinki meyafaru?
Saddar da kanta kasa tayi tacigaba da magana.
Dama wata alfarma ce nakeso zannema agurina kaida
Baba, amma dan Allah kada kucemun a'a. Wlh tun da
muka dauko bayin Allan nan naji 'Yar Baba tashiga raina,
musamman dazu datake kwance akan cinyata senake
mata kallo kamar 'Ya ta dana haifa da cikina, duk da
Allah be bani haihuwa ba, amma ayau naji inada
sha'awar samun diya tabbas da za'a bani 'Yar Baba zanfi
kowa farin ciki da hakan, kuma zantafi da ita can gidan
Sarki mucigaba dazama da ita, amma Yaya mekace?.
Shiru yayi yana kallon kanwar tashi, yana ganin lokacin
datake goge kwalla afakayce dan tasan yahanata kuka
akan rashin haihuwa. Tausayinta yakamashi, kallon Baba
yayi yace Baba mekace game da maganarta? Baba yace
ai Malam kai muke saurare duk abinda kayanke dede ne,
nide fatana kada akawo wani abun dazeyi sanadiyar
nisantani da kuma mahaifiyar wannan yarinya daga 'Yar
Baba. Allah yasani nidanake cikin hankalina zanshiga
damuwa sosai, bare kuma ita wadda ta haifeta.
Malam yace shikenan gobe idan mundawo daga asibiti
mukaji bayanin likita nikuma zan fada maku abinda
nayanke, amma Baba dan Allah kada kacemun a'a aduk
abinda zan zartar, kuma kaima insha Allahu babu abinda
ze rabaku da Yar ka, duk inda taje kaima zakaje. Bayan
kowa yatashi Malam ya kwanta yana kara tuno yanda
wannan aljanin yafada mashi yanda suka tsinci wannan
mata, rufe idonshi yayi yakara tuno lokacin da Sarki yake
fada mashi halinda Fulani take ciki alokacin dasuka
nemeta suka rasa. Ajiyar zuciya yayi yatashi cike da
tunani aranshi yana addu'ar Allah yasa tunaninshi
yazamo gaskiya, amma koma menene yace zeyi istahara
da dare.
Wai lafiya Yarima naganka cikin farin ciki haka?
Murmushi yayi yace wlh momy yau Baffa yayi
murmushi, kuma yasha maganin damuka karbo mashi
agurin Malam na Darazo, Tashi zaune tayi cike da
annashuwa tace lallai ga dukkan alamu kunzo mashi
dawani bayani me dadi ko? Nan yafada mata abinda
Malam yace, hamdala tayi tace ai insha Allahu Allah
zebayyana Fulani da ita da abinda akema bakin ciki
agidan nan, kasanni tausayin Baba nakeyi, shiyasa
banason haduwa dashi sede nayi mashi aike.
Yarima yace Momy niduk lokacin damuka hadu da
Sarkin Fada kawai se inji raina yana baci, kawai nide
mutumin be kwantamun arai ba, ganinshi nake da siffar
munafukai. Momy tace Allah sarki, kaine kake ganinshi
haka, amma aduk cikin fadar Sarki ai inaji babu wanda
yake maka son da sarkin Fada yake maka tun kana yaro,
kama cire wannan abun daga ranka kawai shedanne
yake maka wasiwasi azuciyarka. Shiru Areef yayi amma
sam zuciyarshi bata yarda da abinda tafada ba.
Bayan sungama shafa mashi maganin ajikinshi bacci
yadaukeshi, kamashi sukayi suka kwantar dashi bisa
gadonshi suka rufo mashi kofar, Sarki yace insha Allahu
Allah yakusa kawo mana karshen wannan halin da muke
ciki. Waziri yace da alama wannan maganin zeyi aiki
ajikinshi dan tunda naga yasha naga wasu alamu. Sarki
yace Allah yasa, suna fita sukaci karo da Jakadiya, kara
gaishesu tayi, Sarki ya kalleta yadauke kai, Waziri yace
zaki iya tafiya dan me martaba baya bukatar wani abu,
kuma ma yasamu bacci, Jakadiya tace to ai shikenan
Allah yabashi lafiya, juyawa tayi ta tafi tana me hararar
Waziri tagefe.
Da Sallama tashiga falon Gimbiya ita kadai tasamu se
bayin dasuke mata hidima, zama tayi tana fadin Allah
yatemakeki, Allah yasa kifi haka, murmushi tayi tadaga
mata hannu, Jakadiya ta kalli sauran bayin dasuke falon,
lokaci guda sukayi hanyar waje.
Gimbiya tace da alama akwai magana abakinki? Tace
kwarai ma kuwa Gimbiya, waigawa tayi tace amma
rankishidade banga Gimbiya karama ba, ko lafiya?
Yamutse fuska tayi tace oho kinsanta da nawa yanzu
haka tana can tana shiryawa kinsan yau ita zata karbeni.
Gyara zama Jakadiya tayi tace ai me martaba ma yasamu
bacci, kuma da alama ya karbi maganin dasuka bashi,
dasauri Gimbiya ta tashi zaune, tace haba Jakadiya wane
irin labari ne marar dadinji kike fadamun haka?
Allah yahuci ranki Gimbiya 'Yar Babbar Gida, kaina bisa
wuya, banga amfanina aduniya ba idan har nazamo daya
daga cikin masu bata maki rai, agafarceni Gimbiyar Sarki
mace daya tamkar da dubu, kedayace me haske agurin
me martaba, duk sauran matanshi bayinki ne Gimbiya
me mulki gaba da baya. Wani kayataccen murmushi
Gimbiya tasaki, ahankali tace inajinki menene shawara?
Nagode Gimbiya, amma aganina meze hana mubi
shawarar dana fara kawowa daga farko inaganin ita
kadaice hanyar dazata bulle mana, dan mutanen nan
suntashi tsaye akan wannan al'amari inajin tsoron
abinda zedawo. Maganar Gimbiya medaki sukaji tana
fadin wannan shawara taki Jakadiya tayi dede, amma ina
ganin kamar haryanzu Yaya batayi na'am da ita ba.
Zama tayi tare da daukar apple tafaraci. Jakadiya tace
Allah yatemakeke Gimbiya, barka da fitowa, hannu
tadaga mata tamaida kallonta gurin Gimbiya tace Yaya
dan Allah wannan karin kada kice zaki ki karbar
shawararmu, wlh ayanzu kissa da tuggu basuci kawai
mubama Jakadiya dama kamar yanda tanema daga
farko.
Wani kallo Gimbiya tabita dashi, sannan tace wai meyasa
kuka kasa fahimtata, koda yake ba laifinku bane daga ke
har ita babu wanda yakeda jinin sarauta ajikinshi. Tashi
tayi ranta abace tashige daki, da kallo Gimbiya medaki
tabita, Jakadiya ko cikin sauri tabi bayanta jiki na bari.
Karamin tsaki Gimbiya medaki taja ta tashi itama tabi
bayan Jakadiya tana Allah wadai da wannan kaskancin
datasa kanta ake mata.
Washe gari bayan sunje asibiti likitoci suka taru akanta,
anyi mata gwaje gwaje kala kala, bayan sungama likitan
yakira malam office, seda yayi rubutunshi sannan yakalli
malam yace, agsky munyi duk wani bincikenmu kuma
sakamako daya yake bamu, wannan mata lalurarta
acikin kanta take, kuma mtsalace mesauki, sede kafin
asamu abinda zedawo maka da hankalinka shine aiki,
abinciken damukayi mungano cewar buguwa tasamu
akanta, komade hadari ne, ko kuma akwai abinda
yabugar mata kai, wanda shiyayi sanadiyar
haukacewarta.
Amma abu mafi sauki shine duk ranar data kara samun
makamancin abinda yafaru da ita, kota bige ko kuma
ace arika nuna mata abubuwan datayi tarayya dasu kafin
tasamu matsalar to zata iya dawowa hankalinta. Dan
haka yanzu gida zaku koma da ita, akwai magungunan
dana rubuta sekuyi mata amfani dasu. Godiya malam
yayi mashi yakarbi takardar maganin yafita.
Koda sukaje gida ajikin Jakadiya Yar Baba takwanta
hartayi bacci, dan yanzu tafara sakin jikinta, sede daga
Jakadiya bata yarda da kowa agidan se ita. Adaren ranar
bayan sallar isha'i malam yakara tarasu, hada Baba dan
yaje yadauko iyalanshi yazo anan malam yabashi daya
daga cikin gidajenshi suka sauka aciki kuma yasa aka
zuba mashi kayan abinci dana amfani.
Malam yace to Baba kajide abinda likita yace agame da
ciwon wannan mata ko? Dan haka nayanke shawarar
za'a bama Jakadiya su ta tafi dasu can masarautar
datake, dan Sarki mutumina ne, dazu munyi waya da
waziri, kuma nafada mashi komai sede banfada mashi
tarihinsu ba, kuma Baba wannan tafiya hada kai za'ayita,
acan zaka samu aikin dazakayi idan yaso daga baya idan
komai yadedeta zaka iya zuwa kadauki iyalinka.
Sede Baba banaso kafadama kowa labarinsu, kasan
mutane akwai son zuciya nafiso kabarshi atsakaninmu
wata rana zasuji labarinsu, kuma abangaren Jakadiya
Waziri yace zasu zauna, kasan kuwa bangarenta yana
daga bayan lambun gidan, bakowane yake zuwa ba, sede
kai tunda sunsan kowaye kai zaka iya zuwa aduk lokacin
dakakeso. Allah yabaka ikon rike sirrinku, sekayi ahankali
da gidan sarauta, ba,a aboki agidan, kowa da halinshi
yake zaune, dan haka kazama cikin shiri gobe insha
Allahu zakutafi da safe. Allah yakareku daga dukkan
sharri.
Baba yace amin, kuma naji dadin abinda kamun, ga
iyalai na nan, nasan zaka kulamun dasu Allah yabaka
ikon zama dasu lafiya, amma taya zamurika magana da
kai? Murmushi malam yayi yace kada kasamu damuwa
akwai waya ahannun Jakadiya, kuma iyalanka zasu zauna
cikin kwanciyar hnkl, fatana Allah yabaku sa'a. Haka
kowa yatashi Jakadiya tanacike da murna, harta tashi
yace Jakadiya kisameni adaki, Bayan sun shiga naji
malam yafara magana, akwai abubuwa da dama da
zuciyata take sakamun akan wannan matar, shiyasa ma
nace zakutafi tare. Kara rage murya yayi yana mata
bayani,akan yanda yakeson abubuwan sutafi, sede duk
yanda naso inji abinda suke fada ya gagara, haka
nadawo inajiransu sufito, sundauki kusan awa daya suna
tattaunawa sannan tafito.
Washe gari dasafe Malam yabada mota akadaukesu suka
nufi babbar masarautar Gombe.
To jama,a bara muji menene asalin labarin wannan
masarauta.
Tuna baya,
Asalin Labarin.
MASARAUTAR BUBAYARO.
Muhadu a page nagaba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 30⚜35
Qaseem yayi saurin fadin haba Yaya kasan mekake
fada kuwa? Sarki yace koma menene Qaseem nasan
baze wuce tace in....... kara kamo rigarshi datayi ne
yasashi yin shiru yamai da hankalinshi gareta. Bawan
Allah ga 'Yata nan, ita kadai Allah yabani, mahaifinta
yarasu nikadai narage mata, kuma nima gashi Allah
zerabata dani. Daga cikin wancan kauyen muka fito,
mutanen garin suka koromu sbd kawai wani yayi ma
mahaifinta kazafi, sakamakon hakan ciwon zuciya yayi
ajalinshi.
Mu kuma suka koromu komai basu bari mundauka ba.
Inarokonka kobayan babu raina kada kabari Nafeesa
takoma garinmu, kamar yanda kamun alkawari inason
rayuwar Nafeesa tayi albarka dan Allah kadaure ka auri
Nafeesa.
Qaseem cike da bacin rai yace dalla malama kifadi abu
meyuwuwa kinko san dawanda kike magana? Idan baki
sani ba, to........ tarin daya taso matane yasashi yinshiru
suka maida hankalinsu kanta bakaramin shiga tashin
hankali Sarki yashiga ba, ganin tana wani irin aman jini,
Nafeesa ko se kuka takeyi, Sarki yatashi yace ma Waziri
adauketa ko akan doki ne, mutafi da ita asibitin cikin
gari.
Wani bafade Waziri yasa yadaukota, Haka Nafeesa ta
tashi tana kuka. Cak bafaden daya dauketa ya tsaya jin
jikinta yakara nauyi, Waziri yace muje mana katsaya
kana bata lokaci, Ranka yadade ade zo aduba wannan
baiwar Allah naji jikinta yasaki, dasauri Sarki yadawo
dabaya, suna zuwa Waziri yataba hannunta yaji yadawo,
yasa hannunshi gurin hancinta yaji ba numfashi, sam
yamanta da diyarta agurin yace Rankai dade inaji fa ta
mutu. Wani kara da Nafeesa tasaka nan take tafadi kasa
sumammiya. Sarki cike da damuwa yasa Fadawa suka
dauketa da mahaifiyarta aka dorasu akan doki aka nufi
gida dasu, Qaseem kanshi jikinshi yayi sanyi yatausaya
ma Nafeesa sosai.
Ko kafin sukai gida maman Nafeesa harta saki, dan akwai
dan tafiya, suna zuwa sarki yasa aka kira Jakadiya nan
Waziri yayi mata bayanin komai aka shiga da gawar cikin
gida. Ita kuma Nafeesa aka kira likitansu domin
yadubata.
Babu bata lokaci aka gama shiryata akayi mata sallah
tasamu jama'a sosai, haka aka kaita gidanta na gaskiya,
jikin Sarki yayi sanyi sosai dan yasan yariga da yadauki
alkawarin da dole yacikashi. Bayan sundawo yakira
Waziri dan suyi magana, bebi takan Qaseem ba, dan
yasan baze bada goyon baya ba.
Sosai Waziri yakara karfafa mashi guiwa kuma yakara
tunasar dashi muhimmanci alkawari, da kuma irin
jihadin dazeyi, Waziri yace kobaka aureta ba, kasama
mata miji acikin gidan nan ko awaje hankalinka baze
taba kwanciya ba sbd bakasan irin rikon dazeyi mata ba.
Sarki yace bakomai ai itama mutum ce, kamar kowa
kuma yin hakan dazanyi baze ragemun wani abuba, sede
Allah yasani atsarina banida ra'ayin auren macen da bata
fito daga gidan sarauta ba, kuma wannan ra'ayi nane
shiyasa Qaseem yakeda irin ra'ayin, segashi nashi haryafi
nawa. Nasan zeji haushi na, amma dole incika alkawarin
dana dauka dazaran Nafeesa tasamu sauki za adaura
auren banason tashiga cikin damuwa. Allah yabani ladar
abinda nayi.
Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba da
Jakadiya takawo mata maganar auren Sarki ba, duk da
batason Jakadiya amma daga ranar tafara sakar mata
fuska dan tasan zatayi mata amfani. Koda tafada ma
mamanta shawara daya tabata, kada tasake tanuna
bacin ranta akan auren, kogurin Sarki banyarda ki nuna
bacin ranki ba. Da wannan shawarar Gimbiya tasamu
sauki aranta. Koda Jakadiya taga tafara samun sakin
fuska agurin Gimbiya seta kawo mata shawarar kozata
kaita gurin bokanta.
Dawani kallo Gimbiya tabita, cike da bacin rai tace waiku
meyasa bakuda tunani idan zakuyi magana. Ko anfada
maki gidan sarauta gidan hauka ne? To kada kikara
zomun da wannan maganar banzar. Jakadiya cike da
ladabi tace Allah yahuci zuciyarki, kiyi hkr insha Allahu
baza'a karaba, tace tashi kije idan kinsamo wata
shawarar wadda tayi dede da tsarina zaki iya dawowa.
Wacece NAFEESA?
Diyace ga malam Audu da Uwani sunkasance talakawa
ne, sosai mal. Audu beda wata sana'a data wuce Caca
haka Uwani muguwar masifaffiyar mata ce, dama cirani
yakawosu kauyensu alakocin Nafeesa tana da shekara
15, Uwani macece mesan kudi sosai hakan yasa take
dorama Nafeesa tallar gyada, duk sanda taje talla acikin
tasha dakin wani saurayinta take zuwa yasiya duka
yabiya bukatarshi da ita. Seda tayi ciki har so 3 suna
zubarwa, kuma Uwani bata cemata komai, shikuwa mal.
Audu dama babu ruwanshi dasu.
Gaba daya sun dami yan garin, ana haka wata rana mal.
Audu yayi Caca aka cinyeshi beda abinda ze bada hakan
yasa yaje gidan wani mutum yasato rago, yana fitowa
aka kamashi, anan mutane suka haushi da duka har
gidanshi, seda sukayi mashi raga raga sannan abokanan
Cacarshi sukace sutashi subar gidan dasuke ciki zasu
sayar sudau kudinsu.
Uwani da Nafeesa bakaramin shiga tashin hankali sukayi
ba, suna zaune suka farajin hargowar mutane, Mal. Audu
yana kwance ko tashi be iyayi yaji mutane sun shigo
sunfara yimasu wurgi da kaya, nan take zuciyarshi ta
buga ya mutu, koda mutanen suka zo gurinshi se suka
samu ya mutu, anan suka fadama Uwani sukayi
tafiyarsu, kuka suka saka Uwani tana fadin shikenan
katafi kabarmu da tashin hankali.
Da kyar suka samu wasu daga cikin abokananshi suka
yimashi wanka da sallah suka kaishi makabarta, duka
basufi mutum 10 ba wadanda suka kaishi. Bayan kwana
biyu da rasuwarshi Uwani tafara rashin lafiya, gashi
basuda abinci bare kudin magani, haka Nafeesa tayita
jinyarta, koda taje gurin saurayinta yabata kudi tasiyo
mata magani korarta yayi dan alokacin ma tare da wata
tagansu, haka tadawo tana ta kuka. Lokacin da akayi 7 da
mutuwar mal. Audu masu siyan gida sukazo, anan suka
koresu, duk inda sukaje neman temako babu me
temakonsu dan babu wanda besan halin Nafeesa da
uwani ba. Daga karshe suka baro garin har suka hadu da
Sarki.
××××××××××
Bayan kwana 7 da rasuwar Maman Nafeesa aka daura
aurenta da sarki, mutanen garin sunyi matukar
mamakin aurensu, sede wasu suna cewa auren tausayi
ne Sarki yayi. Duk wasu kayan aure Sarki ne yayi mata,
aka gyara mata bangarenta aka hadata da bayin dazasu
rika yimata hidima. Haka Sarki yasa Jakadiya takoya
mata duk wasu al'adu na masarautar.
Seda Nafeesa tayi wata 1 agidan sarki Jakadiya tana
gyarata sannan takaima Sarki ita, bakaramin kyau tayi
ba, dan gyara akayi mata bana wasa ba, fatar jikinta
kanta seda ta canza. Abubuwa da dama Jakadiya takoya
mata, wanda aciki harda biyayya ga gimbiya dan tafada
mata ko ita wacece kowa binta yakeyi. Haka kuma ta
bata Gimbiya Suhailat agurin Nafeesa.
Aranar da Sarki ya kwana da Gimbiya Nafeesa yasameta
bata da budurci ajikinta, yayi mamaki sosai, bayan sunyi
sallar asuba yadawo yasameta tana kuka, zama yayi
yafara tambayarta lafiya, cike da kissa tace kayi hakuri
rankai dade dama nasan tunda Mama tarasu bata ida
baka labarina ba, nasan dole zaka fahimci wani abu,
nasan kagane banzo da budurcina ba, hakan yasamo
asaline ta dalilin barayin dasuka shigo mana gida ana
gobe za'a koremu daga garinmu, sune suka yimani fyde
wanda shine dalilin ciwon Mamana dan Allah kayi
hakuri, naso ace tunkafin adaura auren mun samu dama
nayi maka bayani dako daya daga cikin bayinka kahadani
dashi.
Tausayinta yakara kama Sarki yace bakomai Nafeesa,
kada insake inji wannan maganar abakin kowa, kibarta
tsakaninmu nayafe maki kinji, tace tonagode.
Haka zamansu yacigaba da tafiya, Sarki da kyar yasamu
yashawo kan Qaseem dan tunda yayi aure yake fushi
dashi. Gimbiya Shuwa da Gimbiyar Baban Gida da
Gimbiya medaki kwata kwata basa shiri, shiyasa babu
me shiga harkar wani, Su biyu sunware Gimbiya shuwa,
basa sata acikin harkarsu, sede itama Gimbiya madaki
wato Nafeesa awulakance take agurin Gimbiya babba, se
abinda tace takeyi, ita kuma tana kaskantar da kanta ne,
kawai dan tasamu fada agurinta, dan Gimbiya Shuwa
bata kulata, sbd akidarta na tsanar wanda ba dan sarauta
ba.
Sarkin Fada ne, da jakadiya zaune alambu. Sarkin Fada
yace waini Jakadiya haryanzu acikin matan Sarki babu
me ciki ne? Yamutsa Fuska tayi tace inaji fa Sarki beda
rabon samun da aduniya, bare aje ga maganar magaji,
kaga ko mutuwa yayi ai sede abama Kaninshi. Sarkin
Fada yace kinko san banason Qaseem ya anshi mulki
kinsan yafi Sarki mugun hali, towai meze hana muyi
masu kullalla. Jakadiya tayi dariya tace lallai Sarkin fada
baka da dama, aini nafison ace sunbata shida kaninshi,
shiyasa lokacin dayayi fushi dashi dan zeyi aure naji
dadi, sede dayake akwai kauna atsakaninsu kaga basu
wani dade ba, suka shirya.
Sarkin fada yace amma Jakadiya babu wata hanya
dazakibi kishiga jikin Gimbiya Shuwa? Zaro ido tayi tace
ni? Rufamun asiri, kana ganin sbd tsabar jinkai irin nata
haryanzu bata yarda da kowa ba, sede mijinta. kai de
kawai ayi sha'ani amma ina nan ina shirya masu gadar
zare kaide kawai ka tsaya kayi kallo. Matso kaji wata
magana. Ko kasan cewa nice nan na hana Gimbiya
Zakiyya haihuwa agidannan? Sarkin Fada yace lallai
Jakadiya nasara maki. Tace uhm kawai ka kalleni kabarni
akwai sauran abubuwan bam mamaki atattare dani.
Kaide muje zuwa, da sannu sena tarwatsa farin cikin
masarautar nan, haka nake bani da kyau, banki kowa
yarasa ba, tunda har Allah yasa nazo a Jakadiya.
0 comments:
Post a Comment