Washe gari. Basu suka tashi ba, se 8:00, dasauri Sarki
yatashi ganin ko sallah basuyi ba, gaba daya kunyar fita
yakeyi dan yasan kowa nagidan yasan baya fashin sallah
amasallaci, babban abin kunya ma abokananshi sunce
zasu biyo sugaisa da Amarya kafin su wuce, gashi nan
yamakara.
Kallon Rayhana yayi wadda take kwance fuskarta tayi
haske ga sahun kwallan datayi jiya nan kwance
afuskarta. Murmushi yayi yashafi gashinta wanda ya
hargitse, ahankali yace kece farin cikina GIMBIYA
FULANI. Kiss yayi ma goshinta yatashi yaje yayi wanka
yana fitowa yatada sallah, bayan yagama ya dauko Waya
yakira Qaseem, yana dauka yace ai Yaya dayanzu
zankiraka ince bakifa suna Falo harsun kusa gama
karyawa. Sosa kanshi yayi yakara kallon Fulani yayi
murmushi yace Uhm ka aika Safeeya taje takiramun
Jakadiya tazo gurin Fulani nizan fita gurin baki.
Shiru yayi sannan yace amma Yaya meze hana
kamaidata dakinta se inturo Safeeya tazo ta kula da ita,
kasan bazata yarda Jakadiya ta kula da ita ba, tunda basu
saba ba. Murmushi Sarki yayi yace shikenan to bari in
maidata dama dan naga Jakadiya ita kadai keshiga
dakina shiyasa nace haka amma yanzu zan maidata
dakinta. Kashe wayar yayi kunya duk takamashi yanzu
yazecema mutane.
Bayan yamaida Fulani dakinta wanda kofa ce kawai
tarabasu da falon Sarki, duk abinda yakeyi tana jinshi
kunya ce tahanata bude ido. Zama yayi yana kallonta,
can kuma yatashi yafita yanufi gurin baki, akofa yahadu
da Safeeya, cike da girmamawa ta durkusa tagaisheshi,
amsawa yayi yana me mata fara'a. Yace yauwa Safeeya
idan tashirya kaya suna nan su zata saka zasu gaisa da
baki. Da to ta amsa mashi yayi waje, yana fita fadawa
suka mara mashi baya suna kwasar gaisuwa.
Duk wanda yaganshi aranar yasan yana cikin farin ciki,
dan duk yanda yaso yaboye fara'arshi kasawa yayi. Yana
shiga falon baki suka fara yimashi tsiya, sosai yake dariya
dayake yashigo cikin abokanshi. Wani Sarki yace gskya
Hasheem bantaba ganin wannan farin cikin atare da kai
ba, kada muna skul baka wannan fara'ar. Lallai baseka
fada ba, kowa yasan yanzu ne kayi auren soyayya. Wani
yace aidole yayi farin ciki wlh auren so daban yake,
shiyasa banyi aure ba seda nasamu wadda nakeso. Haka
sukayita barkwanci suna dariya, wani yace kaga kada
muyi rana gara afiddo mana Amaryar data hanaka sallah
amasallaci muganta muga wane irin zabe ne kayi haka.
Dariya yayi yace a gaskiya sede muje Falona babu wanda
ze fitomun da mata tana amarcinta tafito waje. Dariya
suka saka yafita.
Abakin kofarshi yahadu da Jakadiya, saurin dukawa tayi
tana mashi kirari, murmushi yayi yace Jakadiya kina
lafiya? Tace lfy lau Rankai dade, dama tundazu naso inzo
induba yakuka kwana sekuma naji ance badakai akayi
sallah ba, shine nace to kobaku tashi dawuri ba?.
Murmushi yayi yace hakane, ai har Safeeya tazo tana
gurin Fulani. Fulani? Jakadiya takara maimaita sunan
aranta. Murmushi tayi tace to ai shikenan, bara inje
ingyara dakin yace to. Dakin Fulani yawuce, tunkafin ya
isa wani da daddai kamshi ya dakar mashi hanci wanda
yayi sanadiyar saukar kasala ajikinshi. Lumshe ido yayi
aranshi yanakara jin son Fulani.
Kwankwasa kofar yayi, da sauri Safeeya taje tabude.
Dukawa tayi tana fadin ai har angama, murmushi yayi
yace nagode, Jakadiya zata kawo maki tukuicinki. Godiya
takara yimashi tafita. Yana shiga yayi mutuwar tsaye,
ganin irin kyan da fulani tayi kamar ba mutum ba.
Tasbihi yafarayi aranshi yana kara yabon irin kyan
Fulani.
Zaune take tunda taji shigowarshi ta dukar da kanta,
hannunshi taji ya zagaye mata kafadu dasu, saurin rufe
ido tayi, mikar da ita yayi suna fuskantar juna,
murmushi yayi ya matso da fuskarshi dede ta ta
harsunajin numfashin juna, ahankali yace Fulanita babu
gaisuwa? Saurin kwantar da kanta tayi bisa kirjinshi tana
murmushi, kara rungumeta yayi sosai kamar ze maidata
ciki, kamshin turaren da Gimbiya Suhailat tabama
Safeeya tasa mata duk yafara rikitashi.
Sassanyar muryarta ta doki kunnanshi dafadin Ina
kwana. Seda ya hadiyi miyau sannan ya amsa tare da
lalubo lips dinta yahade danashi. Sun dade ahaka har
yana neman wuce gona da iri yaji karar kofa. Dagata yayi
yace kinga kinmantar dani mutane suna jiranmu,
gaskiya senayi da gaske kada kirika sani jin kunya afada.
Kamata yayi suka fito.
Akofar falon ya tsaya yakara gyara mata mayafinta, yace
gskiya dande kada suce namasu rowa dabazaki fita kowa
yakallemun ke ba. Ahaka suka shiga falon tana jikinshi,
kallo ne yadawo kansu, kowa seda ya yaba da zaben
Sarki, anan suka rika yimashi tsiya, itade sede murmushi,
ko fuskarta kasa dagawa tayi, ahaka suka gama gaisawa,
kyaututtuka da dama suka bata, daga masu kudi se zinari
wasu hada kyautar mota. Tasamu zinarai dayawa da
kudi, wasu kayan ma an nadesu bansan ko menene ba.
Sallama sukayi mata, Sarki yace bari inmaidata daki kada
tayi tuntube. Gabada sukasa dariya.
Qaseem da Waziri tare da Sarki dasauran fadawa suka
taka masu hargurin motocinsu, kowa yaji dadin
haduwar dasukayi haka suka tafi suna cike da farin ciki,
dan sundade basuyi irin wannan haduwar ba. Bayan
sungaisa dasu Waziri yawuce part dinshi dominsu karya.
Da Jakadiya yahadu tagama gyara mashi daki ankawo
abinci tashirya masu, yace sannu da kokari Jakadiya,
tace sannu da dawowa, Yace yauwa kije falon baki akwai
kayayyakin Fulani kyautace da abokanai na sukayi mata,
akwasosu ki kawomun su dakina, hannu yasa a aljihu
yaciro kudi masu yawa zasu kai 100k, yabata yace yauwa
gashi kibama Safeeya tukuicinta ne ayi mani godiya da
irin gyaran datayi ma Fulani dazu. Amsawa tayi ta tashi
tawuce.
Wani irin kululun bakin ciki ne, yarufe Jakadiya, ganin
irin kudin da Sarki yabama Safeeya, aranta tace wato
mutanan nan so sukeyi sucireni daga jikin Sarki,
ayanzunne yakamata insamu dukiya daga gareshi ta
dalilin Amaryarshi nasan akanta ze iya yima mutum
kyautar mamaki, amma dan bukulu suka turo wata tazo
tayi aikin da nice nakeyinshi aduk sanda Sarki yayi aure.
Tabbas sena tashi tsaye akan Safeeya naga alama nan
gaba Sarki ita zemaida yar gaban goshi.
Ninasan mezanyi, anfada maki sona da yakeyi haka
nabarshi. Tsaki tayi tawuce falon domin kwaso kayan,
mamaki da tsoro ne, suka cikata lokacin datayi arba da
irin kayan da tagani afalo. Gaba daya tarikice ganin irin
wannan dukiya. Aranta tace badan Sarki yaga kayan nan
ba, wlh dasenayi nawa. Wata babbar jaka tajawo tasaka
kayan duka aciki tadauka tanufi dakin sarki dasu. Bata
samesu afalo ba, da alama abincin ma adakinta suke ci.
Tsaki taja tace shikenan kuma za,a maida mana Sarki
bita zai zai, yo aduk matanshi akwai wadda yataba shiga
dakinta ma? Lallai Gimbiya zankai maki labarin daze
tarwatsa zuciyarki, wanda zesa ki karya akidarki ta rashin
zuwa gurin boka, ai wlh tunda nabace dole insamu
abokan tafiya. Murmushi tayi lokacin data tuna yanda
Sarkin fada yafara samun shiga gurin Medaki. Kwafa tayi
tajuya tafita.
Wasu zafafan kwalla ne, suke fitowa daga idon Gimbiya
Zakiyya, duk irin jiji da kanta, yau gashi agaban Jakadiya
tana kuka, damma Jakadiya takori sauran Bayin.
Lallashinta Jakadiya tacigaba dayi tana kara kwantar
mata da hankali.
Gimbiya hakuri zakiyi, amma dole sekintashi tsaye, wlh
bakiga irin makudan kudin da aka bama Fulani ba, dan
sunan danaji Sarki yakirata dashi kenan. Babbar
damuwata yanda taki barinshi yafito fada, abinci ma
adakinta sukaci. Infada maki...... Marin da taji ya sauka
akuncinta ne, yasata saurin hadiye sauran gulmar data
kwaso. Cike da tsoro takara dukar da kai tana neman
gafara.
Ke wace irin dabba ce? Wlh bansan ke dakikiya bace se
yau, anfada maki gidan sarauta gidan bayine? Inbanda
rashin sanin darajar sarauta taya zakizo kina fadamun
irin wadan nan sakarkarun maganganun irin na jahilai
irinku. Ina cikin damuwa zakizo kina fadamun abinda
bantambayeki ba. Bance kifadamun abinda sukayi ba,
kawai na tambayeki ina Me martaba shine zaki wage
sakaran bakinki wanda yasaba dashan bakar kuka da
daddawa kizo kina fadamun maganarsu.
Daga yau kika kuskura kika kara fadamun abinda banice
na tambayeki ba, wlh, kinji narantse maki sekinbar
masarautar nan. Kara dukawa Jakadiya tayi, tana bata
hakuri, tashi tayi ta tureta tashige daki, tana fadin karna
kara ganin kafarki anan sena nemeki. Wasu hawayene
suka zuboma Jakadiya, diyar cikinta saboda kudi da
mulki yau itace take zaginta da cin mutunci har haka.
Tashi tayi tana fadin yo idan har nabarki kikaci ribar
zaman gidan sarauta ai ba macece ta haifeni ba.
Qaseem ya kalli Gimbiya Suhailat yace ni kaina yau ina
cikin farin ciki bansan abinda yasa ba, Yayana yana cikin
farin ciki dole in kasance acikin farin ciki, inama ace
Rayhana itace matar Yaya ta farko, nasan har abada baze
kara marmarin kara aure ba. Kamar yanda nasamu farin
cikin raina banajin zan iya kara aure, shiyasa akace
auren soyayya yafi komai dadi.
Murmushi tayi ta kara shigewa jikinshi tace nikaina ina
farin ciki da auren yaya, inajin Rayhana kamar kanwata,
insha Allahu ajikinta zamu sami babban rabo.
Rungumeta yayi yace inafatan haka, inaso inga jinin Yaya
agidan nan shine babban farin cikina. Fatana Allah
yadoramu akan duk wasu makiyanmu, dannasan
munadasu dayawa acikin gidannan, sede Allah ne kawai
yasansu. Gimbiya tace babu abinda zasuyi mana domin
munrigasu munce Allah. Jawota yayi yace yakamata fa
kiyima Areef kanwa dan kinsan ina son mace. Murmushi
tayi tace nima haka ina addu,ar Allah yabani mace, yace
to tashi muje daki ai ba,a samun mace abaki. Dariya tayi
yadagata suka nufi daki.
Afalon Medaki Jakadiya tasamu Sarkin Fada suna zaune
yanashan kayan marmari, medaki tana kusa dashi har
jikinsu yana gogar na juna, kofar da aka turoce tasasu
saurin matasawa, dan Medaki takori duk bayin.
Murmushin jin dadi jakadiya tayi ganinsu ahaka, aranta
tace kema kinshigo hannu.
Medaki duk kunya takamata, Jakadiya tace rankiyadade
ashe mutumin yana nan? Shiru tayi, Jakadiya tace uhm
kisaki jikinki kinganni nan nimafa haryanzu ina dan taba
duniyancin nan ai mace fitila ce bata aiki dole seda batir.
Dariya Sarkin Fada yayi yace da gaskiyarki Jakadiya,
ainafada mata nidake da ita munzama aminan juna,
akwai amana atsakaninmu, dan haka bakinmu adinke
yake muci tare mu tashi tare babu wanda zeji kanmu.
Medaki tace amma gaskiya nagode, tunda nasan yanzu
munzama saniyar ware aidole musami abokin fira. Anan
Jakadiya tafada masu rashin mutuncin da Gimbiya
Zakiyya tayi mata. Sarkin fada yace kirabu da ita, wlh
kotana so ko bata so seta aikata babban laifin daze
jamata kisa ko dauri acikin gidan nan, ita da anyi
magana seta nuna mana sarauta da mulki, zamu gwada
mata bakomai sarauta take bama mutum ba. Kibarta
mucigaba da binta wata rana zata dawo garemu, kuma
kada ki kara zuwa gurinta, da kanta zata nemeki. Ai ba ita
takawoki gidanba, karewa ma kinfita matsayi agurin
Sarki, kawai agurin shinfida zata gwada maki. Dariya
suka sa gaba daya.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, babu ruwan wani da
wani, Jakadiya tadena zuwa gurin gimbiya Zakiyya, ko
aikenta sarki yayi dataje zata fadama Babbar Baiwarta
tajuyowarta. Sunhade kai da Medaki, Sarkin fada tuni
yasamu shiga agurinta, wata rana har kwana yakeyi
agurinta, kasancewarshi babban mutum me karfi hakan
yasa Medaki takejin dadin mu,amala dashi. Baruwanta
da daga hankalinta, sede idan ranar girkinta yayi taje tayi
kwana 2 tadawo.
Sarki yana kokarin yin adalci atsakaninsu, sede Fulani
daban take agurinshi, duk ranar girkinta kowa seyasan
ita keda girki dan ko fada baya son zama sosai. Gimbiya
Zakiyya kuwa kissar datake mashi ce take dan kara
sanyata aranshi. Medaki kuwa hakanan yake zama da ita
dan bewani gamsuwa da ita, shiyasa wani lokacin idan
kwananta ne ba kullum yake kusantar taba.
Bayan shekara daya, aka saka Areef makaranta dan
alokacin yana da shekara 3, har lokacin Fulani bata samu
ciki ba, duk da Sarki yafara damuwa amma sbd son
dayake mata, ko maganar betaba yimata ba, akullum
yana addu,ar idan har haihuwa alkhairi ce agareshi to
Allah yabashi me amfani, idan kuma babu alkhairi Allah
yasa mashi dangana.
Jakadiya tazo shiga part din Gimbiya suhailata taji suna
maganar cikinta har yakai wata 5. Bakaramin tashin
hankali tashiga ba, cikin sauri tajuya tanufi gurin Medaki
da Sarkin fada. Suma hankalinsu yatashi dajin labarin,
anan Sarkin Fada yace yakike ganin za,ayi? Jakadiya tana
huci, tace na rantse da Allah baza ahaifi cikin nan agidan
nan ba, ai nafada babu wanda zekara haihuwa agidan
nan, dan haka gobe zanyi tafiya, kafin indawo ina me
tabbatar maku cikin zezube. Dariya sukayi Medaki tace
kinyi dede Jakadiya, Allah yabada sa,a. Bari indauko maki
tawa gudunmuwar.
Safeeya ce tafito da gudu tana neman dauki, karo sukaci
da Waziri zeje fada. Lafiya Safeeya naganki haka? Wlh
Gimbiyace bata lafiya se zubar da jini takeyi, naga
alamar ma kamar barine tayi, cikin sauri yadaga waya
yakira Qaseem, sannan ya aika wani bafade yakira
driver.
Likitane, yafito daga wani daki yace su sameshi office.
Bayan sunzauna yakalli Sarki da sauran mutanen, sannan
yace Rankaidade agaskiya sede kuyi hakuri domin
abinda ke cikinta yafita. Sede munyi bincike bamu gano
dalilin fitar saba, sede muce daga Allah ne. Qaseem yace
likita yajikin nata? Yace dasauki babu wata damuwa
anjima kadan za,a sallameta. Sarki yace innalillahi wa
inna illaihirraji,un. Waziri yace se hakuri, Allah yamaida
mafi alkhairi.
Bayan kwana 2 jikin Gimbiya yayi sauki sosai, sede
haryanzu tanajin zafin barin datayi, kallon Safeeya tayi
tace wlh ina mamakin abinda nagani acikin baccina,
wanda shine yayi sanadiyar yin bari na. Kinsan jiya nace
maki nagaji bacci kawai nakeji, harkikacemun inje inyi
alwala kafin inkwanta nace maki nide nagaji zanyi addu,a
kawai, to wlh ina kwanciya bacci yadaukeni, banyi
addu,ar ba, kawai cikin bacci naga wasu irin mugayen
halittu marassa kyan gani masu ban tsoro sunbiyoni ina
gudu kawai nafadi, suka zagayeni, daya gada cikinsu
yataka cikina, shine kikaji wannan karar daniyi kawai
senatashi naga jini yana zuba.
Safeeya tace tabbas Gimbiya rashin addu,ar dabakiyi
bane yasa wannan al,amari yafaru dake, kinsan addu,a
tana da matukar mahimmanci arayuwa, kuma alwala
kafin mutum yakwanta bacci tana da matukar tasiri
ajikinshi. Kodazu munyi magana da waziri shima seda
yayi mamakin al,amarin. Kuma yafadama malam, yace
ajirashi nan da kwna 2. Gimbiya tace koma menene
Allah yamana tsari dashi.
Bayan kwana 2 Fulani da Sarki sukaje asibiti Waziri da
Qaseem ne suka rakashi, babu wnda yasan inda zasuje
sesu Gimbiya Suhailat. Bayan likita yasa anyi mata test
aka kawo result, cike da farin ciki yasanar dasu abinda.
Yakejikin takardar. Kasa Sarki yasauka yayi sujada yana
me godema Allah da kyautar da yayi mashi, kowa dakin
seda yaji tausayin sarki ganin kwalla tana fita daga
idonshi, duk sunyi farin ciki da wannan labari, itako
Fulani kasa dago kanta tayi.
Qaseem yace likita wata nawa ne? Wata 3 ne, Hamadala
Sarki yayi yakara yima Allah godiya. Waziri yace lallai
likita anjima zakaga sakon tukuicin wannan albishir me
tsada. Sede munaso kada kabari kowa yaji wannan
maganar. Likita yace insha Allahu.
Suna fita Qaseem yakira malam yayi mashi albishir,
shima yayi farin ciki, kuma yace kada subari kowa yasan
da cikin, dan abinda yagani akan barin da Gimbiya
Sauhailat tayi yabashi tsoro, dan haka akillaceta kada
tarika fita har wani yaga cikin, yace ze rika aiko da
rubutun dazata rika sha harta haihu insha Allahu, Allah
zekare cikinta. Godiya sosai yayi mashi sukayi sallama.
Bayan sunkoma gida yafada masu abinda Malam yace,
Waziri yace wannan haka yake, nima nayi tunanin haka,
kunsan babu wanda yasan zuciyar mutane, abar
maganar anan, kuma mucigaba da addu,a Allah
yasauketa lafiya.
Nikam nace amin Waziri.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 55⚜60
Haka Suka cigaba da renon cikin Fulani, babu wanda
yasan da cikin agidan, duk wata hidima Safeeya ce take
zuwa tana mata, Waziri da kanshi yahana kowace baiwa
shiga dakin Fulani, sede komenene akwai wani
amintaccen bawan da waziri ya yarda dashi, shi suke
bama sakon yashiga yafada mata, matakin tsaro sosai
Waziri da Qaseem suka dauka akan cikin Fulani, Sarki
har mamakin kulawar dasuke bama Fulani yakeyi, hakan
yasa yakara basu babban matsayi aranshi, yanajin Waziri
tamkar yayansu.
Gimbiya Zakiyya abun duniya yafara isarta, gashi tayi
fada da Jakadiya, tanaso takirata amma girman kanta
yahanata. Ganin itace meso yasa ta aiki wata baiwarta
takira mata ita, alokacin suna part din Medaki ita da
Sarkin Fada. Dariya Jakadiya tayi tace ai nafada maku
wlh babu wanda zekara samun da acikin gidan nan,
kuma banida haufin Boka ya iya aiki. Sarkin Fada yace ai
naga alama, tunda kikayi nasarar zubar da cikin Gimbiya,
gsky na jinjina maki.
Karar buga kofa sukaji, dasauri Sarkin fada yamike
yashige daki, Jakadiyace ta tashi tabude, gaishe da ita
baiwar tayi sannan tafada mata sakon Gimbiya Zakiyya.
Murmushi Jakadiya tayi tace kice inazuwa. Komawa tayi
tace seka fito matsoraci, dariya medaki tayi tace ai da
gaskiyarshi, duk munfiki tsoro kekam kinci dubu, tace
wlh kuwa.
Abinda baiwar tafada mata take fada masu, dariya Sarkin
fada yayi yace ai gara ki koma, Medaki tace nimade bana
shiga gurinta sosai, amma tunda zaki koma nima zan
koma, Jakadiya tace bara naje inji dame tadawo.
Zaune take afalo bayan sungama gaisawa Gimbiya takara
kallon Jakadiya tana yamutsa fuska, tace wai naji ance
Gimbiya suhailat tayi bari? Murmushi Jakadiya tayi tace
haka ne, ranki yadade. Gimbiya tace ammade nasan
akwai abinda yafaru ko? Dariya Jakadiya tayi batace
komai ba, dan bata manta da irin zagin data sha ba.
Gimbiya tace bani labari idan ko har naji dadinshi kinada
babbar kyauta.
Jakadiya nan tasaki baki tabata labarin abinda yafaru,
tace wlh kuwa Gimbiya ai nafada maki tunda de baki
haihu agidan nan ba, amatsayinki na babba acikin gidan
nan ke kadai yakamata ki sama mana da agidan nan.
Wani murmushin jin dadi Gimbiya tayi tace gsky kin
bani labari medadi, hannu tasa tadauko kudi masu yawa
tabata amatsayin tukuici.
Godiya sosai Jakadiya tayi, Gimbiya tace kina de saka ido
akan Rayhana ko? Tace e sosai ma, itama haryanzu babu
komai atare da ita, Gimbiya tace yayi kyau, aikinki yana
kyau.
Har cikin Fulani yashiga wata 8 da sati 2 babu wanda
yasan da cikin, alokacin yafito sosai. Rungume take ajikin
Sarki yana bata kankana abaki tana tayi mashi shagwaba,
kallonta yayi yace Fulanita idan kika haifi mace wane
suna zamu samata?
Murmushi tayi tashafo fuskarshi tace idan namiji ne fa?
Hancinta yaja yace harga Allah inason diya mace shiyasa
bantaba tunanin haihuwar namiji ba, nasan mutane
dayawa sunamun kallon wanda beda magaji, nikam
nikeda babban magaji, dan koda ace inada namiji ko
mutuwa tazo mani zan bada wasiyar abama Qaseem
sarautar.
Dan haka koda banida namiji bazan damu ba. Ko
kinason haihuwar namiji? Kai tagirgiza tace nima inason
mace sosai, Allah yabani mace, yace amin. Kura mata
ido yayi, hura mashi iska tayi tace wannan kallon fa
namenene? Jawota yayi ya rungumeta sosai harseda tayi
kara ya sassauta mata, kallonshi tayi idonshi yayi ja
sosai, tashi tayi niyaryi yakara riketa, ahankali tace akwai
abinda ke damunka ko?.
Kai ya girgiza yace kwana 2 ina wani mafarki wai muna
zaune kintashi kin ruga inata kiranki amma kinki kidawo,
kuma har kika bace bankara ganinki ba. Jikinta taji yayi
sanyi tace insha Allahu babu abinda zerabamu kai nawa
ne nima haka. Yace Allah yasa.
Karar buga kofa sukaji, Sarki yace shigo dan yasan inde
aka buga kofa to wannan bawan ne,shine kuwa yashigo
yaduka kasa yace rankai dade Jakadiya ce, Sarki yace to
kuma shine kabarta awaje, tashi yayi cikin sauri yafita.
Fulani tace bari inshiga ciki kafin ku gama, riketa yayi
yace haba kiyi zamanki mana kinsan yanda nake da
Jakadayi ai, tace amma kasan malam yace..... bata karasa
ba Jakadiya tayi sallama, cak ta tsaya ganin Fulani atsaye
da katon ciki, Sarki wanda be kula da halin data shiga ba
yace shigo mana Jakadiya.
Saurin seta kanta tayi ta shigo, tana zuwa tazube tana
kwasar gaisuwa, zama Fulani tayi bayan sun gama
gaisawa, kwata kwata Jakadiya bata gwada taga cikin
jikinta ba, kallon Sarki tayi tace dama shigowa nayi inj ko
akwai wani aiki da za ayi maka?.
Kai yagirgiza yace babu komai Jakadiya kije kawai, dariya
tayi tace toshikenan afito lafiya, kallon Fulani tayi tace
Gimbiya ahuta lafiya, fita tayi zufa tana fito mata. Sarki
yace ai nasan Jakadiya bata iya daga kai ta kalleni, bare
kuma ke, kinga batama kula da abinda ke jikinki ba,
nasan data gani zatafi kowa murna, dan tana daya daga
cikin wadan da suka shiga damuwa akan rashin
haihuwata. Shiyasa naso abari infada mata amma su
Qaseem da Waziri suka hana. Fulani tace idan na haihu
ai zataji, yace to Allah ya kaimu.
Hartuntube Jakadiya takeyi sbd sauri, jikinta har rawa
yakeyi sbd bacin rai. Ko sallama batayi ba tashiga falon
Gimbiya Zakiyya, suna zaune ita da Medaki, Gimbiya tace
lafiya Jakadiya zaki shigo mana guri babu sallama bare
neman izini? Zubewa kasa tayi tana haki tace Allah
yahuci zuciyarki, wlh wani bakin labari ne yake tafe dani,
sede inajin fargabar fadin shi, amma idan kinmani izini
zan iya fada. Gimbiya tace yi maganarki.
Abinda tahani ajikin Fulani tafada masu, cike da firgici
Gimbiya Zakiyya ta mike, wata irin zufa tafara keto mata,
Medaki tayi saurin tashi tariketa suka zauna. Gimbiya
tace wlh baze yuwuba, haba Jakadiya meyasa jakiyimun
haka? Amma mekika cemun kince babu komai ajikin
Rayhana? Jakadiya tace kigafarceni, wlh tun lokacin da
kika hanani zuwa gurinki alokacin naso infada maki bana
ganin Gimbiya Fulani kona shiga gidan bata zama falo,
shiyasa bana sanin halin datake ciki.
Medaki tace toyanzu mekike ganin za,ayi kinsan de
baza'a barta ta haihu ba. Gimbiya Zakiyya tace idan har
nabar Rayhana ta haihu agidan nan to wlh nikuma
aranar zanbar gidan nan, kai kuma ce niba 'yar halak
bace. Jakadiya meye shawara? Jakadiya tace Gimbiya
hanya daya ce, amma bazaki jita abakina ba, nasan
bakisonta, amma zanje insamu Sarkin Fada kinga shi
namiji ne, yafimu zurfin tunani, zanje inji yanda zamuyi.
Gimbiya Zakiyya tace banason kidau lokaci, kuma
kintabbatar Sarkin Fada ba munafuki bane, kina ganin
yanda yake shige ma Qaseem da matarshi, yaronsu ma
agurinshi yake zama. Jakadiya tace Sarkin fada
mutumina ne, banida wani abokin shawara aduk gidan
nan se shi, banida haufi akanshi, dan haka kibarni dashi
anjima zakiji abinda muka yanke dashi. Amma bazamu
bari tahaihu agidan nan ba. Gimbiya Zakiyya cike da
bacin rai tace kaini harzamanta agidan nan banaso, sede
kinsan banason maganar boka atsarina.
Sarkin fada kanshi seda yashiga tashin hankali dayaji
labarin cikin Fulani, mikewa tsaye yayi yace tashin
hankali, lokaci yayi dazamu fara aiwatar da aikinmu
agidan nan, babu wani yaro daza,a kara haifa
amasarautar nan, dan haka kicema Gimbiya idan har ta
amince anjima da dare zanzo semu tattauna idan zata
amince da shawarata, kuma kifada mata babu wani
batun boka ko malam aciki. Jakadiya tayi ajiyar zuciya
tace yanzu naji natsuwa, bari inje insameta infada mata
seka jini. Yace kigaishemun da Gimbiyata.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 60⚜65
Zaune suke afalon Gimbiyar Baban Gida, wani shu'umin
murmushi Gimbiya tayi, tashi zaune tayi daga
kishingiden datake, alokacin data gama jin bayanin da
Sarkin Fada yayi masu. Ahankali tace lallai dole nabaka
kyauta me tsoka saboda wannan shawara daka
kawo,lallai kayi tunani mekyau.
Gaka de kafito daga cikin matsiyata talakawa, kuma kazo
gidan nan amatsayin bawa, kafin daga baya kasamu
yanci, amma kana da tunani irin na yan sarauta.
Kodayake ance kunfi wasu mata zurfin tunani, naji dadin
wannan shawarar taka kuma ita za'abi, dan haka kaje
kayi shiri kamar yanda kace zaka samu abokan aiki, bana
son inkara jin labari mekama da Rayhana bare kuma
cikin jikinta.
Asalwantar da ita idan samune tabar duniyar gaba daya.
Badamuwata bace, inde nizan rayu to kowama yamutu
banida matsala, dama can bata fito daga jinin sarauta
ba, niko duk wanda baya daya daga cikin jininmu, wato
sarauta, dashi da kaskantattar dabba duk daya suke
agurina, koda kuwa na nuna mashi so, to bana gaskiya
bane, koyakikace Medaki?
Gaba daya falon yayi shiru jin irin kazaman kalaman da
Gimbiya Zakiyya take fadi akan talakawa, kallonsu tayi
taga gaba daya fuskarsu tacanza, se alokacin ta tuna
baram baramar datayi, cikin sauri tace shiyasa nake
godema Allah daya hadani da mutanen kirki irinku,
daban kuke agurina, kunfi kowa matsayi azuciyata acikin
gidan nan.
Murmushin yake Jakadiya da Sarkin Fada sukayi, can
Sarkin Fada yace bakomai Gimbiya muma muna tare
dake, kuma dasannu zamu nuna maki muma muna cikin
masoyanki, kinsan bawa akwaishi da amana. Murmushi
tayi tace yayi kyau.
Shima murmushin mugunta yayi ya kalli Jakadiya da
Medaki yakanne masu ido. Medaki tace yanzu yazakayi
kasanfa dole aikin yakasance ranar da Sarki baya
dakinta. Gimbiya tace kabari seyadawo gurina dan nasan
Medaki bawani sanin yanda zata dauke mashi hankali
tayi ba, kasan jinin sarauta ako ina daban yake, dan haka
kabari nan da jibi. Yace angama ranki yadade.
Fita sukayi shida Jakadiya, acikin Lambun gidan suka
sami guri suka zauna, Jakadiya wadda acike take da
bacin rai ta kalli Sarkin Fada cike da bacin rai, tace yanzu
haka zamu cigaba da zama tare da Wannan matar, diyar
cikinmu tana mana cin kashi akullum? Wlh dole
mugwada mata talaka ma, yanada yanci, kuma zata gane
bakomai bane jinin sarauta suka sani, mune acikin gidan
nan, dan haka zamu gwada mata munfita sanin gidan
nan.
Dariya Sarkin fada yayi yace dadina dake saurin hawa,
kalli nan, aljihunshi yayi mata nuni dashi, sede banga
komenene aciki ba, lekawa tayi, tace meye amfanin
hakan? Dariya yayi yace kisa ido kawai malama, zakiga
yanda akeyin duniyanci, kinganni nan bana yarda da
jinin sarauta, duk yanda ka kai dayi masu hidima wata
rana dole sumaka butulci.
Shiyasa acikin aikina bana barin sahu, ko kuma baya da
kura, dan haka kizuba ido kigani wata rana dole Gimbiya
tanemi juya mana baya, alokacin zan nuna mata asalin
kalata. Dariya Jakadiya tayi tace amma naji dadi, ai
nadauka duk zagin datayi mana zetashi abanza? Yace
tama isa, haba Sarkin Fada fa nake, kinsan yanda akayi
nasamu wannan matsayin kuwa, nikaina ina tsoron
kaina, bari infada maki abinda babu wanda yasani
agidan nan seni kadai, sekuma marigayi ya matata, itama
dalilin sanin abinda na aikata yasa nakara mata iska,
wanda haryanzu babu wanda yasan da mutuwarta, kowa
yadauka yanda nace guduwa tayi sbd bata haihuwa
nikuma nace zanyi aure shine tagudu.
Har yanzu maganar ahaka take, alokacin Sarki dakanshi
yarika bani hakuri, Waziri da Qaseem kuwa cewa sukayi
kada insake inje bikonta, dama ba'a garin nan take ba,
nace masu ai tama tafi garinsu.
Murmushin jindadi Jakadiya tayi tace inajinka bani labari
insha, kara gyara zama yayi yace alakocin da za'a nada
sarautar Sarkin Fada, mu 3 aka tsaida, sede yanda
mutane suka zabi sauran biyun suka barni hakan yayi
mani ciwo, shiyasa nashiga damuwa saboda nasa rai
akan sarautar, bayan an kara kuri'a aka tsaida mutum
daya acikin su biyun.
Hmmm kinsan menayi? Tace seka fada, cikin dare
nashiga dakin Mati wanda shine za'a nada washe gari,
dama kuma tare suke kwana da abokin takararshi,
inazuwa na saka wuka nakashe Mati, Kallah yana
baccinshi besan abinda yake faruwa ba, haka na debi
jinin Mati duk nashafa ma Kallah ajiki harda fuska, kuma
nadauki wukar nasaka mashi ahannu, haka najuya
nafita.
Inazuwa gida nayi saurin dibar ruwa domin nima jikina
duk yabaci da jini, hanyar bandaki na nufa kawai senaji
maganar matata ta faramun salati, tana fadin inakaje da
wannan daren, dama muna kwance naga sanda kadauki
wuka ka boye awondonka kafita, kuma gashi yanzu
kadawo jikinka duk jini. Anya megida ba wani abun kaje
ka aikataba?.
Aje bokitin nayi najata zuwa daki, anan itama na shaketa,
nan take ta mutu, haka na hada duka kayanta na kullesu
adan kwali, naje cikin bayan lambun nan na haka rami
sannan naje nadaukota ita da kayanta narufesu aciki,
namaida kasa sosai, yanda babu wanda zesan anrufe
wani abu nazuba, dama kuma gurin ba'a shigarshi sosai
ai kingani.
Washe gari da safe naji ana kururuwa, ina fita naga
mutane sunzagaye Kallah yanata kuka jikinshi duk jini ga
wuka ahannunshi, yana fadin wallahi banine na kashe
shiba. Haka aka jashi zuwa fada, bayan anyi bincike aka
gane sahun hannunshi ajikin wukar, nan take shima aka
yanke mashi hukuncin kisa. Sede babban abin ban
haushi wannan shegen Wazirin wanda yakeda dogon
hangen nesa, da zurfin tunani, shine yaja Sarki daki,
bansan mesuka ceba, Sarki yazo yace hukuncin kisan
daurin rai da rai agidan yari za,ayi mashi, bahaka naso
ba, amma sanin kowa yaji hukuncin nasan baze taba fita
ba hakan yasa hankalina ya kwanta.
Bayan kwana 2 kawai naji ance niza,a bama sarautar.
Dadi sosai naji, sede ban gwada afuskata ba, Sarki yake
cemun meyake damuna haka, anan nafada masu karyar
kwanana 4 banga medakina ba, dama mundade muna
rigima, shine kawai natashi naga takwashe kayanta
tacemun garinsu zata tafi. Nace masu nayi neman
harnagaji banganta ba. Anan kowa yatausayamun
sukayita lallashina, dahaka washe gari akamun sarauta.
Kuma daga ranar babu wanda yakara tamabayar
medakina, asalima Waziri cewa yayi kawai inkara aure,
nikuma nace tunda bana haihuwa bazanyi aure ba,
shiyasa suka kyaleni.
Tokinji babban sirrina, kuma nafada makine, saboda
nasan bazakici amanata ba. Wani irin murmushi
Jakadiya tayi nikaina bangane kona menene ba, tace
haba aini taka ce, cikinmu daya. Sarkin Fada yace
kisamomin maganin saka mutum bacci, amma na
fesawa, tace angama.
Fulani ce zaune afalo ita da Babanta sunata fira, tundazu
yazo sundade suna fira, yakasa tashi yatafi, itama bataso
yatafi, kallonta yayi yace Rayhana inaso bayan kin haihu
idan abinda kika samu yayi kwari, zamuje gida domin
mugansu, kuma suga abinda kika haifa, kinga zasuji dadi.
Tace nima Baba inason zuwa gida, insha Allahu dana
haihu kamar da wata 7 semutafi ko? Yace hakan yayi,
amma kibari sekin haihu sekima mijin naki maganar.
Hannu yasa a ajjihunshi yaciro wani zobe mekyau,
yamika mata, sakashi tayi ahannunta, ta kalli Babanta
tace wannan fa? Kwallan idonshi yagoge sannan yace
zoben mariganyi yane, nima jiya ina duba kayanta,
kinsan tunda tarasu bandaga kayanta ba, to acikin wata
jakarta naganshi shine nace bari inkawo maki kisaka
ahannunki. Itama kwallan ta goge tace nagode Baba,
yace bakomai bari intafi yamma tayi, tace Baba kabari se
anjima mana, yace a,a ai na dade, gara intafi sena kara
dawowa. Har bakin kofa tarakashi idanunta sunkasa
dena zubar hawaye, shikanshi kwallace tacika mashi ido.
Sun jima abakin kofa yana lallashinta kafin yatafi.
Gimbiya Suhailat ce da Safeeya sukazo duba Fulani
takawo mata farfesun yan ciki, zaune suke tanaci sunata
fira, Gimbiya tace kinde kusa haihuwa kihuta, nasan
insha Allah nan da kwana 7 zaki cika wata 9 dede, nasan
kozaki kara kwanaki bazaki kara dayawa ba. Fulani tace
nima nagaji nakosa in haihu, sede bansan abinda yasa
ba, yan kwanakin nan se intaji yawan faduwar gaba.
Safeeya tace kada kidamu kirika fadin Innalillahi
Wainnailai Hirraji'un, insha Allah zaki samu sauki, kuma
koma wani abune zesameki zezo maki dasauki. Tace
shikenan nagode, Gimbiya suhailat tace bari mutafi
nasan yanzu Yaya zeshigo, Fulani tace ai banan yakeba. E
duk dahaka aidole yazo yaganki kafin ya kwanta. Fulani
tace Allah banaso kutafi, to kibar Aunty Safeeya ta kwana
anan tunda nikadai zan kwana. Dariya Gimbiya tayi tace
a,a kibari kawai mutafi.
Kamar zatayi kuka tace dan Allah Aunty. Safeeya tace to
bari inje idan yatafi seki kirani sena taho, murmushi tayi
tace yauwa nagode, haka suka yimata sallama suka tafi.
Suna fita tashiga daki ta kwanta, ba dadewa Sarki yashigo
dakin, kusa da ita yaje yakwanta ta bayanta
yarungumota yana me tusa kanshi cikin wuyanta,
murmushi tayi tace sannu da shigowa, yace yauwa,
inacen sunrikeni afada, nikuma duk nakosa inzo kada
kiyi bacci bamuyi sallama ba, tace kaima kasan bazan iya
bacci bankarbi sakon seda safe daga gareka ba.
Kara rungumeta yayi, yace aide jibi kamar yanzu muna
tare, tace sosai ma, kallonta yayi yace kinyi kyau sosai
Ummin AMATULLAH. Dariya tayi takara shigewa jikinshi
tace wato harma kasan mace zan haifa, kuma kasa mata
suna? Yace sosai ma, tace ai nadauka sunan Ummanku
zakasa? Yace naso insaka sunanta, sede yanda na dade
ban haihu ba, kuma Allah yabani yanzu shiyasa naga
yadace insaka wannan sunan kinsan idan akace
Amatullah ana nufin amintattar Allah, idan kuma namiji
ne, tozansa AMINULLAH. Shima fassarar duk daya ce.
Murmushi tayi tace kayi gaskiya, idan Allah yakara bamu
wasu se asaka, yace hakane, zatayi magana yahade
bakinsu guri guda, sundauki lokaci me tsawo ahaka,
ganin yafara fita hayyacinshi yasata saurin sakinshi ta
matsa. Runtse ido yayi yana maida numfashi.
Ahankali cikin mutuwar jiki tace nasan Gimbiya Yaya
tana jiranka adakinka, yakamata katafi, bude idonshi
yayi sede idon yayi ja sosai, maidawa yayi yarufe, sega
kwalla sirara suna saukowa, dasuri tamatsa kusa dashi
tace meyafaru? Saurin rungumeta yayi yana fadin dan
Allah kada kibarni kinji, wlh kece farin cikina, duk ranar
da babuke akusa dani rayuwata bata da amfani.
Saurin rufe mashi baki tayi tana fadain wai meyafaru
kake wannan maganar? Murmushi yayi yace bakomai,
kawaide ina fada maki ne, tun safe yau nakejin faduwar
gaba, addu,ar danakeyi ce tasa nakejin sauki.
Tace babu abinda zefaru se alkairi, katashi katafi kada
tayi fushi, yace wlh da ace Medaki ce, nasan zata iya
saidamun kwananta, amma Zakiyya ko duniya zan bata
bazata yarda ba. Tace a,a nima banaso nafison kwanana
yazo da kanshi.
Murmushi yayi yace bazaki gane yanda nakeji bane
shiyasa, tashi yayi yace muje kirakani to, tace to kuma
idan katafi waze sani bacci? Yace kai namanta, jawota
yayi yakwantar da ita akusa dashi, tausa yafara yimata
ahankali yanayi yana mata fira medadi, tun tana bashi
amsa haryaji shiru.
Zama yayi yana kallonta yadauki kusan minti 30 yana
kallonta, daga karshe ya sumbaci goshinta, wuyanta da
bakinta sannan yatashi yafita jikinshi asanyaye.
Washe gari tunda asuba, Sarki yatashi dawani irin firgici,
sakamakon mafarkin dayayi, Gimbiya Zakiyya tace lafiya
naga kana zufa? Tashi yayi bece mata komai ba,yanufi
part din Fulani. Turus ya tsaya ganin bata cikin dakin,
kuma dakin duk ahargitse, karar ruwan dayaji ne,
abandaki yasa yaji hankalinshi yadan kwanta, juyawa
yayi yaje yayi wanka ya nufi masallaci.
Tare dasu Qaseem da waziri suka taho, Waziri yace lafiya
rankaidade naga tundazu kamar kana da damuwa?
Kallonshi yayi, yace wlh wani mummunan mafarki nayi
kuma da Fulani nayi mafarkin, shine nashiga dakinta da
asuba sede naga dakin ahargitse, kuma Fulani bata yima
daki haka, sede karar ruwan danaji abandaki yasa
hankalina ya kwanta, amma kuma haryanzu gabana
yana faduwa.
Waziri yace to kayi mata magana abandakin kaji ta
amsa? Yace a,a Qaseem yace Yaya mudeje ka kara
dubawa ko? Waziri yace haka yakamata.
Part din suka wuce, sede afalo suka tsaya shi kuma
yawuce dakin. Karar dasukaji ce tasasu saurin shiga
dakin, Sarki suka gani kwance kasa da alama faduwa
yayi, hawaye suna zuba a idonshi, dasauri Qaseem
yamatsa kusa dashi yana fadin yaya lafiya?
Da hannunshi yayi masu nuni dawani guri, jini suka gani
agurin, ga kofar bandaki abude ruwa na zuba a famfo,
babu alamun mutum aciki. Da kyar Sarki yake fadin
babu ita wlh bata nan, Waziri yafita waje dasauri, haka
yarika bin masu gadin gidan sede babu wanda yace yaga
wani abu yafaru cikin dare, abu kamar wasa har rana
tafito babu Fulani.
Gaba daya gidan antaru ankira hukuma ansanar da ita
sede haryanzu babu wanda yakira yace ansamu wani
labari akanta. Sarki kuwa tun faduwar dayayi haryanzu
akwance yake tun maganar dayayi da farko bekara cewa
komai ba. Gimbiya Suhailat da Safeeya se kuka sukeyi,
Baban Rayhana kuwa zaune kawai yake, idonshi harsun
kumbura sbd kuka, yakasa cewa komai.
Abu kamar wasa har dare yayi babu Fulani, yan sanda
harsungaji da nema, hankalin kowa atashe yake, banda
munafukai, sede Jakadaiya tana zaune kusa da Sarki,
idonta itama ya kumbura dan kuka, mutane se hakuri
suke bata. Waziri yakira malam yayi mashi bayanin halin
da,akeciki, shima ya jajanta masu. Yace sujirashi zuwa
washe gari.
Washe gari tunda asuba. Malam yakira waziri yace mashi
agaskiya Fulani tana cikin mawuyacin hali, sede besan
inda take ba, amma kuma tana raye, za,a cigaba da
addu,a. Anan yafada mashi halin da Sarki yake ciki, anan
malam yace bakomai nan da kwana 2 zezo se asan
abinda za,ayi.
Jikin sarki babu sauki, ko abinci bayaci se dakyar suke
matsa mashi yaci kadan, Ranar da Malam yazo ne, suka
shiga suka tattauna da mayan fada, kuma suka yanke
hukuncin nada Qaseem amatsayin Sarkin masarautar
Bubayero. Lokacin da Qaseem yaji kin amincewa yayi.
Da kyar suka shawo kanshi, washe gari aka nadashi Sarki.
Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba, se
fada take tana fadin wannan ai shine kai kai koma kan
mashekiya, wato munyi abu kuma yadawo kaina, kai
bazeyuwu ba yanzu shikenan natashi daga matar Sarki?
Wlh dasake. Jakadiya tace haba Gimbiya najifa ance
rikon kwarya ne aka bashi, da sarki yasamu lfy zemaida
mashi mulkinshi.
Haka sukayita bata baki, da kyar ta hakura, abu daya ne
yasata kara yarda mulki zedawo hannunsu dataji ance
Qaseem yace baze dawo gidan Sarki ba.
Bayan anyi nadi malam yakoma Darazo, haka akacigaba
da nema ma Sarki magani da adduo'i, ankaishi asibitoci
dayawa amma jikinshi babu sauki, matsalar shanyewar
barin jiki ne tasameshi, hakan yasa aka fara yimashi
gashin kashi, sede babu yanda basuyi ba akan afitar
dashi waje, amma sarki yaki yarda koda suka fadama
malam, seyace su kyaleshi, babban abinda zesa yadawo
dede to ganin Fulani ne, hakan yasa suka kyaleshi aka
cigaba da yimashi maganin gida.
Medaki kuwa cin duniyarsu sukeyi da tsinke, ita da
Sarkin fada. Duk wani munafunci yadawo daga Jakadiya
se Sarkin Fada. Gimbiya suhailat da Safeeya haryanzu
sunajin kadaicin rashin Fulani, Babanta kuwa tundaga
ranar yadena zuwa ko ina kullum yana kofar gida, sede
masu aiki suzo suyi mashi aiki sutafi.
Wannan shine asalin labarin Masarautar Bubayero.
Zamucigaba da cigaban labarin anext page. Nagode
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 65 ⚜70
Tafiya sukeyi amota, Jakadiya Safeeya, kallon Wannan
mahaukaciyar kawai takeyi, tana kara tuno maganganun
da malam yafada mata ana gobe zasu taho, waigawa tayi
takara kallon Yar Baba wadda tayi lamo ajikin Baba tana
ta bacci.
Aranta tace tabbas suna kama sosai ma, sede kawai
wahalar duniya zatasa baza,a iya gane kamar suba. Dole
nayi yanda malam yace idan har muna son musami
abinda muke so. Tunawa tayi da abinda malam yafada
mata akan Waziri, aranta tace tabbas da ace kowane
Sarki zesamu mutum me amana kamar Waziri dayaji
dadi, addu,a tayi akan Allah yate makesu akan mutanen
masarautarsu.
Alokacin dasuka isa Masarautar Bubayero Jakadiya
Safeeya tayima Waziri waya akan sun iso, alokacin gurin
karfe 12 , Waziri yace togani nan zuwa. Yana zuwa
yabada umarnin abude masu gate, direct gurin part din
Sarki Qaseem suka nufa, dayake ranar asabara ce, kuma
azahar batayi ba, babu kowa awaje se bayin dasuke kai
da kawowa.
Suna fitowa Jakadiya Safeeya takama matar, shi kuma
Baba yakama Yar Baba Waziri yayi masu jagora zuwa
bangaren Jakadiya Safeeya, dayake, dakuna ne, guda 2 se
falo da kitchen, kuma kowane daki akwai bandaki aciki,
idan kaga yanda Gimbiya Suhailat tasa aka gyara ma
Jakadiya Safeeya part dinta zaka dauka nawata
mekudice, babu abinda ba,a zuba ba na kyale kyale
afalon, dakunan ma haka, gidan yayi kyau sosai. Duk da
abangaren Gimbiya takecin abinci amma a kitchen dinta
ma akwai kayan girki da kayan abinci.
Bayan sun shiga Waziri yakalli Baba yace sannunku da
hanya, Baba yace yauwa munsameku lafiya? Yace lafiya
lau, Waziri yace Alhamdulillahi Baba gashi kazo
masarautar mu, kuma insha Allahu zakaji dadin zama
damu, sede akwai abubuwan danakeso ka kiyaye kuma
ka kula dasu, na farko de nasan malam yafada maka
yanayin yanda gidan sarauta yake, dan haka abu daya
zan fada maka shine akwai Wani mutum Sarkin Fada,
inaso duk yanda zeso yashiga jikinka kada kabari wata
magana wadda tashafeka tahadaku, zan kaika gurin Sarki
amatsayin wanda malam yaturo domin kazauna tare
damu, ka kula dashi sosai dasauran mutane, idan muka
fita zan kaika gurin Baban Gimbiya Fulani, mutum ne,
nagari kuma shima dattijo ne, nasan zakaji dadin zama
dashi, koba komai daka zauna kana fira da mutanen
gidan nan gara karika zuwa gurinshi kuna fira.
Baba yace nagode sosai, kuma insha Allah zaka sameni
merike alkawari, fatanmu de Allah yabama wannan
baiwa tashi lafiya, suka ce amin. Waziri yace muje
ingwada maka masaukinka kafin Sarki yafito, kallon
Jakadiya Safeeya yayi yace nasan akwai abubuwa da
dama dasuke bukata, anjima kamar da yamma zankawo
maki kudi, sekije kasuwa kisiyo masu kayan amfani,
game da sutura ma, duk kisiyo masu, idan yaso seki
hado da dogayen riguna surika sawa kafin tela ya gama
dinkawa. Kallon Yar Baba yayi yace daga cikin gidan nan
kada kifita ko ina kinji? Ta daga mashi kai, yace yauwa,
dakin fita akwai mutanen dazasu kamaki, saurin boyewa
tayi bayan Jakadiya safeeya jin abinda Waziri yafada.
Murmushi yayi yace tsoro kamar farar kura.
Tashi sukayi shida Baba, yace Sena dawo anjiman, tace
to mungode, nima abinci zan dafa masu kafin inshiga
gurin Gimbiya. Yar Baba tashi tayi ta matsa kusa da
mamanta wadda take zaune akasa tayi shiru tana ta wasa
da kafet din falon, kwanciya tayi bisa cinyarta, tana mata
murmushi, dankwalin kanta mamar tacire, tafara yimata
wasa da gashin kanta, ita kuma se lumshe ido takeyi.
Jakadiya Safeeya tana kallonsu tace ikon Allah, Uwa da
Diya se Allah, gaba daya sungama burgeta, murmushi
tayi tace Allah yasaka maki, akan duk wanda yayi maki
wannan abun. Tashi tayi tanufi kitchen.
Waziri ne, zaune afadar Sarki, bayan sungama gaisawa
yafada mashi Jakadiya Safeeya ta dawo, tare da wani
tsoho, malam yace sutaho tare, yazauna anan, amma
nabashi masauki abangarena, shine nace bari infada
maka. Murmushi Sarki Qaseem yayi yace, Waziri ai duk
abinda kayi dede ne, babu laifi, kazaba mashi duk aikin
daze iya mesauki kasan abinda zaka rika biyanshi ai?
Yace hakane, godiya muke.
Sarki Qaseem yace Waziri akwai maganar danakeso
muyi akan Yarima, kasan yagama karatunshi kuma
yacemun shi aikin gwamnati yakeson yayi, to munyi
magana da abokina harma an daukeshi , ranar litinin
zefara zuwa, anan gidan gamnati, sun bashi assistant
director. Kuma nasan saboda abokinshi ne yanace
yanason yayi aiki acan, dan shima acan yake aiki.
Kasan wani magana dayazo mani da ita? Munyi mashi
maganar aure, Momynshi tanaso tayi mashi maganar
diyar yayarta datake can kasarsu, amma seta fara
tambayarshi koyana da wadda yakeso, budar bakinshi se
cewa yayi yafison yasamu wadda bata fito daga gidan
sarauta ba. Haba Waziri yama zece haka, ko Yaya daya
auri mata 2 ba yan sarauta ba, ai matarshi tafarko daga
gidan sarauta tafito, shine mukace bamu yarda ba,
amma zaka iya kiranshi ka karaji daga bakinshi, kasan
banason bacin ranshi, inaso kanuna mashi nayarda
yafara auren yar sarauta daga baya se ya auri zabinshi.
Waziri yace wannan ba wata matsala bace daza'a bata
rai, kabarni dashi zanji tabakinshi tunda beriga yasamu
wadda yakeso ba, ai dasauki, kuma zanga abokinshi
Haisam nasan shima zeyimashi magana. Murmushin jin
dadi Sarki Qaseem yayi yace. Hakan yayi kyau, muje
muga jikin Yaya.
Jakadiya Safeeya ce zaune afalon Gimbiya Suhailat,
Gimbiya tace bakiji yanda naji ba, yan kwanakin nan
dabaki nan, idan Sarki yafita sede inta zama nikadai,
dariya Jakadiya Safeeya tayi tace nima duk banji dadi ba,
ya Sarki da jikin? Gimbiya tace jiki kam dasauki, da ranar
dasu Waziri suka kawo mashi magani, dakuma maganar
da malam yayi akan Fulani ranar har murmushi seda
yayi, kuma nantake yashanye maganin, inasha Allahu
zesamu lafiya. Jakadiya tace Allah yabashi lafiya, ina dana
Yarima?.
Hmmm Yarima rigima, kinsan abinda yazo mana dashi
kuwa? Tace a,a. Nan tafada mata yanda sukayi dashi,
tace kuma nibazan amince mashi ya auri kowa ba, se
jinin sarauta, Jakadiya tace kiyi hakuri, ita harka ta aure
ba,aso ana tsanantawa acikinta, addu,a yakamata kiyi
mashi amatsayinki na mahaifiyarshi se Allah yayi mashi
zabi nagari.
Gimbiya tace hakane, amma nafison yabi zabin dana
yimashi, diyar yayata nakeso ya aura,duk da ban fada
masuba, banaso infada masu Yarinyar tasa abun aranta,
nasan bayanzu zatayi aure ba,shiyasa nayi shiru harseya
amince, sannan nayi masu magana. Jakadiya tace
bakomai Allah yashige mana gaba, nima zanyi mashi
magana tunda de besamu wadda yakeso seya auri
zabinku, idan yaso daga baya seya auri zabinshi. Gimbiya
tayi murmushi jin dadi tace shiyasa nake sonki. Allah
yayi mana zabi nagari.
Da yamma kamar yanda Waziri yace, haka yasa driver
yadauki Jakadiya Safeeya yanufi kasuwa da ita, acan
tasiya masu kayan amfani dayawa, sede yawan siyayyar
duk ta Yar Baba tafi yawa, kananan kaya ma duk nata
sunfi yawa, dasauran kayan amfani na yan mata. Data
gama suka wuce gurin tela, anan tayi mashi bayanin
yanayinsu tabiya kudin dinki yabata ranar karba.
Jakadiya Karima ce zaune afalon Gimbiyar Babbar Gida
tare da Medaki, Gimbiya tace waini Jakadiya kina kula da
Suhailat kuwa? Kada fa ta shammacemu kamar yanda
Rayhana tayi mana. Jakadiya tace haba Ranki yadade ai
ita da haihuwa sede alahira, kada kidamu bazan baki
kunya ba. Murmushi tayi tace, haka nakesonji.
Medaki tace bari intashi inje nasan yanzu angama shirya
Sarki inje induba jikinshi, yamutsa fuska Gimbiya tayi ta
kauda kai, Jakadiya tace afito lafiya Gimbiya. Tana fita
Gimbiya taja tsaki tace aikin banza kamar wata tsiya zata
iya yimashi, ni wannan mata tsau tsayi ne kawai yasa
Sarki ya aureta, shide talaka duk yanda akayi dashi baya
iya sakewa. Shiru de Jakadiya tayi bata ce komai ba, tashi
tayi tace bari inje gurin Sarkin Fada.
Koda Jakadiya Safeeya takoma part dinta har lokacin
maman Yar Baba bata tashi daga baccin datakeyi ba,
saboda acikin maganin da likita yabata akwai mesa
bacci, dan yace idan tana yawan bacci kwakwalwarta
zatafi samun hutu, YarBaba kuwa tana zaune tana kallo.
Jakadiya tace Yar baba zokiga wani abu, tashi tayi
tamatsa kusa da ita tazauna tare da jingina da jikinta,
jakadiya Tayi murmushi tace, hmmm ke kam mage ma
nan taganki tabarki inde gurin sonjiki ne. Dariya Yar
Baba tayi takara kwantawa jikinta.
Kayan tafiddo tafara nuna mata, hada inner wears duk
tarika gwada mata yanda ake saka su, se murna Yar Baba
takeyi, Jakadiya tace zankoya maki yanda ake amfani
dasu duka, kuma kinsande nafada maki banason kazanta
ko? Kai ta daga mata, tace yauwa, yanzu tashi muje ciki
kiyi wanka semu fara.
Ranar litinin Areef yafara zuwa office, aranar duk macen
data ganshi se miyanta ya tsinke, sbd kyawun da yayi,
tare suke da Haisam, Areef yace nifa nafara tsarguwa,
naga se kallona akeyi. Dariya Haisam yayi yace kada
kadamu sunga dan saurayi me kyau ne. Duka ya
kaimashi yana fadin kai dan iska ne, yace emana kasani
ko anan kasamu zabinka tunda babu yar gidan sarauta
acikinsu.
Areef yace Allah ya kyauta, anfada maka ni matata zatayi
aiki ne, lallai ma, kai bakasan irin macen danake so na
aura ba. Kawaide katayani da addu,a. Haisam yace ato
idan kuma nizan rigaka aishikenan,Areef yace nima zanfi
son haka, da haka suka isa Office dinsu.
Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai sbd yanzu
yanashan magani tunda yaji maganar da Malam yayi,
kuma yana cin abinci sosai, hakan yasa Sarki Qaseem
yace afara fita dashi fada hakan zerika rage mashi zaman
kadaicin dayakeyi.
Haka suka cigaba da rayuwa agidan Sarki, babu wanda
yasan dazamansu, aduk lokacin da Baba yaso ganin Yar
Baba yakanje yaganta susha fira, har mamakin ganin
yanda tacanza cikin lokaci kadan yakeyi, gashi tsafta
agurinta kamar da ita aka halicceta, akullum setayi
wanka so 3 kuma ko sallah tayi setayi kwalliya, Jakadiya
safeeya kam har mamakin saurin fahimtar datake da ita
take, kome takoya mata ba wuya tadaukeshi.
Akullum da dare kafin su kwanta se sunyi karatun
littattafai, dan zaman datayi takara sanin abubuwa
dayawa agurin Jakadiya safeeya, harta da girki tafara
koya mata, sbd tace idan bata nan setarika dafa masu.
Duk da ankawo dinkunansu amma bata son saka atamfa
ko less, tafison tasa kananan kaya, Mamanta kuwa tunda
takeshan magani, yanzu haukanta da sauki, batayin
komai, sede tazauna tayi shiru idan kuma kaga tana
dariya to ita da yarta ce, duk da baccinta yafi yawa akan
idonta biyu.
Zaune Areef da Haisam suke acikin lambu suna hutawa,
babu kowa agurin, danshi Areef becika son fadawa suna
binshi ba, yafison daga shi se Abokinshi Haisam wadda
yakasance da ga dupty gvernor na gombe, kuma tare
sukayi karatu dashi.
Yar Baba tana gama kwalliya tafito dasauri dan ta nuna
ma Jakadiya dan tasan bata fita ba, tana zuwa falo taga
bata nan, kitchen tashiga nan ma bata ganta ba, turo
baki tayi dantagane tafita, hanyar dataga tana bi tashigo
ko tafita tabi, tana zuwa ta tura kofar cikin sa,a tajita
abude, murmushi tayi tafita.
Cike da tsoro tafara takawa tana bin cikin lambun,
swimming pool tagani kallonshi tayi. Taci gaba da
tafiyarta, can taji dawisu yafara kuka, ai batasan lokacin
data juya dagudu zata koma inda tafito ba, cikin rashin
sa,a tayi tuntube da dutse kawai tafada cikin ruwan.
Su Areef dasuke zaune nesa da ruwan sukaji karar wani
abu acikin ruwa, koda Areef yakai kallonshi ga ruwan
kawai yaga mutum yana ta daga hannu da kafa acikin
ruwa. Cikin sauri yatabo Haisam yana nuna mashi, duk
da basu san kowaye ba, Dasauri suka nufi bakin ruwan.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 70 ⚜75
Babu bata lokaci Yarima Areef ya fada cikin ruwan, yana
zuwa kusa da ita yadaukota, alokacin tasha ruwa harta
suma, fitowa yayi daga ruwan tana rungume ajikinshi,
abisa kafet din dasuke zaune yakwantar da ita yadora
kanta saman cinyarshi, Haisam yana biye dashi duk sun
rude.
Kallon tsoro, mamaki suka farayi mata, addu.a duk
wadda tazo bakin Areef yinta yakeyi danshi gani yake
kamar ba mutum bace. Haisam yace Areef bakada
hankali kana ganin kamar ba mutum ba amma zaka
dorata akan cinyarka? Tunda de kacirota tashi mutafi,
fara jan hannun Areef yayi.
Areef da jikinshi yagama mutuwa sbd tsabar firgici bema
san yanayi ba. Da karfi yajashi sannan yadawo
hankalinshi, katashi mubar gurin nan, nidama can
nafara zargin gurin, gashi yanzu munfara gani. Areef
yafara girgiza kai, yamaida kallonshi kan kyakkyawar
fuskarta, sannan yace ba aljana bace, duk da bantaba
ganinta amasarautar nan ba, amma kalli kafarta babu
alamun tako ajiki. Haisam yace anfada maka aljanu basa
fitowa asiffar mutane? Hmmm kaga malam wannan
yarinya kyanta yayi yawa, wlh zantafi inkira mutane ko
katashi mutafi.
Idanun Areef suka cika da kwalla yakalli Haisam yace dan
Allah, katsaya ni nayarda mute maketa ta farfado, kaga
zamu fidda kanmu daga zargin da muke mata. Haisam
yace naji, idan ma Mutum ce daga ina tafito? Areef be
tsaya bashi amsa ba, kawai yaduka tare da saka bakinshi
cikin nata yafara hura mata iska, shiru yaji, yamike yana
kara kallonta.
Kamshin jikinta duk yagama cika mashi hanci, Haisam
yace kadanna cikinta, hannu yasa, jikinshi se rawa yakeyi
yafara danna cikinta, can sega ruwa yafara fitowa ta
bakinta, haka yayi tayi, harseda tagama fitar da ruwan
datasha.
Tari tafarayi hakan ya tabbatar masu data farfado, cike
da firgici ta tashi ta shige jikin Areef, duk ta kanan
nadeshi, tafara kuka. Areef kasa magana yayi, dan duk
tasakan mashi kasala ajiki, dukawa Haisam yayi yace ya
isa haka, tashi muji daga ina kike.
Kintashi tayi, sede tadena kukan datakeyi , tayi lamo
ajikin Areef kamar wata yar baby, Areef kuwa kallonta
kawai yakeyi, bemasan abinda Haisam yake fada ba,
ganin haka yasa Haisam ya bugi kafadar shi, dasauri
yamaida kallonshi gurinshi, gira yadaga mashi yana fadin
kallon fa nameye?.
Kabari mutambayi yarinya daga ina tashigo amma
kawani rungumeta kamar kana shirin bata mama.
Murmushi Areef yayi yana sosa kai. Dagota yayi, ahankali
ta tashi tana kallonshi, sede taki barin jikinshi, se rawar
sanyi takeyi.
Areef yace daga ina kike, meyakawoki nan har kika fada
ruwa? Hannu ta daga tana mashi nuni da hanyar part din
Jakadiya Safeeya. Haisam yace baki iya magana ne, kinaji
ana maki magana zaki tsaya kina mana maganar
kurame, kuma gashi alamu yanuna kinji me yace.
Komawa tayi jikin Areef zata kwanta, dan gaba daya wani
zazzabi takeji, sanyi sekara shigarta yakeyi.
Dasauri Haisam yajawota yana fadin yau ko sunanki
mage senaga karshen son jiki. Areef yace haba bros
kabita ahankali mana, kama hannun Areef tayi tarike
sosai tafara kuka. Tsaki Haisam yaja yace toni zantafi.
Areef kamar zeyi kuka yace plsss kabari muji daga
bakinta. Kallonta yayi, yace Beauty tashi kifadamun daga
ina kike kinji, kinga kada yatafi yabarni kuma nasan
mutane zekira kuma kamaki zasuyi, ai dasauri ta tashi
tarike hannunshi, shima tashi yayi yana murmushi.
Haisam yace daganinta batada gaskiya gashi daga yin
maganar kamawa tamike. Hannu tasa tana kara nuna
mashi hanyar data fito, Areef yace baki iya magana ne?
Kai tadaga mashi, tare da fara janshi zuwa hanyar.
Atunaninshi ko sanyi ne yahanata magana, hakan yasa
yafara binta. Da har Haisam ya kyaleshi se kuma yayi
tunanin kada ta cutar dashi seyabisu.
Sunkusa zuwa gurin sukaci karo da Jakadiya tafito daga
cikin gida hankalinta atashe. Cak ta tsaya tana masu
kallon mamaki, kara kallon Yar Baba tayi, nan hankalinta
yafara tashi ganin kayanta ajike, sede ganin wanda suke
tare, yasa taboye tashin hankalinta. Da gudu taruga ta
rungume Jakadiya Safeeya, janta tayi zuwa cikin gida,
suma suka bi bayansu.
Seda tashiga da ita daki tasata tacire kayan tace tasaka
wasu kafin tafito, juyawa tayi takoma falo. Bayan
sungama gaisawa, Areef yace Aunty ashe beauty agidanki
take? Kawai muna zaune nida Haisam agurin lambu
semukaji karar wani abu acikin ruwa, muna dubawa
ashe ita ce tafada, koda nacirota, ta suma, da kyar ta
farfado. Shine tabamu tsoro, dan bamutaba ganinta
agidan nan ba, gashi kuma kyanta ya kai akirata da
aljana.
Koda muka fara tambayarta bata bamu amsa ba, sede
kuma tanajin abinda muke fada, shine daga karshe
tajawo ni muka taho nan. Ajiyar zuciya Jakadiya tayi jin
bayanin da Areef yayi mata. Murmushi tayi tace Allah
sarki sannunku nagode sosai, inbadanku ba kila data
halaka, mantawa nayi ban kulle kofar ba, kuma nasan
nitafito nema dan banyi mata sallama ba dazantafi.
Shirun dakaji tayi ai bata iya magana, tunda aka haifeta
ahaka take, sede tanajin duk abinda aka fada. Tausayinta
ne yakamasu, jikinsu duk yayi sanyi bakamar Haisam.
Areef yadaga baki zeyi magana kenan tafito, baki yasaki
yana kallonta, gani yake kamar ba ita bace, tasaka riga
doguwa me siririn hannu tayi mata kyau sosai, kalarta Ja
ce, gashi bata daura dankwali ba, fuskarta tasha kwalliya
kamar meshirin zuwa gasar kyau, hannunta rike da
comb, tana zuwa tafada jikin jakadiya ta mika mata
comb din.
Murmushi tayi tace Uhm Yar Baba sarkin kwalliya yanzu
seda kika kara wata kwalliyar? Kwantawa tayi jikinta
takamo hannunta tadorashi akan wuyanta, jakadiya tace
kai naji jikinki dazafi, ko ruwan dakika shiga ne, ze sakar
maki Zazzabi?.
Kai tadaga mata, tana lumshe ido, Haisam yace Aunty ai
dama yakamata abata magani tasha, kada yarufeta. Jawo
hannunta takarayi tana mata nuni data sharce mata
gashinta, fara Sharce mata tayi tana fadin kuma gashi
babu magani agidan nan, sede inje gurin Gimbiya kozan
samu.
Haisam yace a,a bari kawai idan muka fita semu siyo
mata, kallon Areef yayi yace kai kuma mr. Watching seka
tashi mutafi musiyo magani, shiru yayi mashi yana
kallon yanda tarufe ido tana bacci, ga gashinta daya
gama tafiya dashi. Dan bakinta yasha red janbaki, tayi
mashi kyau sosai. Dukan dayaji akafadarshi ne yamaido
dashi tunanin dayakeyi.
Hararar Haisam yayi, gwalo yayi mashi yana murmushi.
Areef yace Aunty amma bansanki da diya ba ina kika
samota? Tace tare muka dawo da ita daga Darazo, acan
gidan Malam take, diyar Dan uwanmu ce. Zekara
magana Haisam yace katashi muje musamo mata
magani bata lafiya, idan mundawo seka idasa tambayar
taka. Tashi yayi yana sosa kai yana murmushi yace Aunty
semun dawo.
Kallonshi tayi tace dan Allah banason inji wannan
maganar agurin kowa, koda kuwa Gimbiya ce, ko Sarki,
kuje kudawo zakuji dalilina nafadar haka. Suka ce to, fita
sukayi Areef yanayi yana waige, bugewar dayayi da kofa
ce tasashi saurin dafe goshin shi. Dariya Haisam yasa
hada rike ciki, suna fita Areef yakai mashi duka yana kara
dafe goshin shi. Haisam ya tsagaita dariyarshi yana fadin
sannu abokina ai bansan kaji zafi ba. Areef yace kacigaba
lokacinka ne dariya ma yanzu kafara yimani inde akan
beauty ne. Haisam yazaro ido yace akwai wata a kasa
kenan? Areef yayi murmushi yace a,a sede asama dan
iska. Dariya suka saka kafin suka nufi hanyar parking
space.
Cak sarkin fada yatsaya ganin abinda beyi tsammani ba,
adede lokacin dayake fitowa daga part din Medaki, daka
ganshi kasan baya cikin nutsuwarshi. Wani irin kallo
Waziri yake binshi dashi, cikin tsarguwa Sarkin fada ya
matso yana washe baki yace rankaidade barka da fitowa,
nima yanzu nafito zani fada shine Jakadiya Karima take
shedamun Gimbiya Medaki tana nemana. Toyanzu
nashiga ko minti 3 ma banyi ba, tambayta tayi shine
kaga nafito. Muje fadar ai can kayi ko? .
Da ido Waziri ya kafeshi, bece mashi komai ba, kifce
kifce yafarayi yana fadin ai semu wuce ko? Murmushi
Waziri yayi ya girgiza kai yace muje, haka suka nufi fada
cikin Sarkin fada duk ya duru ruwa, se addu,a yake Allah
yasa Waziri be harbo jirginshi ba.
Baban Fulani ne zaune akofar gidanshi tare da Baba suna
ta fira, dan zaman dayayi bakaramin sabo sukayi ba,
Baba yace gaskiya ina tausaya maka halin daka shiga,
tabbas ka hadu da jarabawa, sede kuma hakurin dakayi
gashi nan Allah yabarka da lafiyarka, kuma dama anason
me hkr aduk lokacin da wata jarabawa tasameshi. Baban
Fulani yace hakane, nima ada nayi niyar komawa kasata,
sede ganin irin karamcin da mutanen nan sukayi mani
da kuma rashin sanin Rayhana tana raye ko mace,
wannan dalilin shine babban abinda yahanani tafiya,
amma insha Allahu nasan za,a ganta tunda de anfada
mana tana raye. Baba yace ai Allah baya bacci, koma a
ina take wata rana zata dawo.
Koda su Areef suka koma jikin Yar Baba yarikice, Zazzabi
ya saukar mata sosai, dan bata tabayin zazzabi
mezafinshi ba, se kuka takeyi dama kuma gata raguwa,
kwance take ajikin Jakadiya Safeeya suka shigo bakinsu
dauke da sallama, dasauri Areef yazauna kusa da
Jakadiya yana fadin Aunty bade jikin bane?.
Tace wlh kuwa, tunda kuka fita ta kwanta shikenan
zazzabi yarufeta, Haisam yace Aunty kawai kutashi
mutafi asibiti, zaro ido tayi tace A,a kawai ku kawo
maganin inbata nasan zata samu sauki, kaga abincinma
taki ci. Zata kara magana kenan taji motsi adakin Maman
Yar Baba, saurin tashi tayi ta kwantar da ita bisa kujera
tace inazuwa bari inshiga bandaki, Yarima kabata abinci
kila taci seku bata maganin nasan zata samu bacci, bari
infito.
Abakin kofa tasameta, dama tasan lokacin cin abincinta
yayi jira take Yar Baba ta kyaleta taje ta tadata tabata
abinci tasha maganinta, saurin kama hannunta tayi
tasama kofar key suka koma ciki, bandaki tajata seda ta
wanke mata baki tayi fitsari, sannan suka dawo tazauna
dan tabata abinci.
Abincin yadauka ya matsa kusa da ita, hannu yasa
yadagota, tana tashi ta lafe ajikinshi, zama yayi akan
kujerar, hakan yasa takara shigewa jikinshi. Dariya
Haisam yayi yazauna yana fadin wlh Beautyn Areef keda
mage bansan wanda yafi wani son jiki ba, Areef yace
kaga malam kabarta taci abinci tunda ba,a jikinka ta
kwanta ba. Haisam yace ato adebi ahankali dan wlh
kosannu bazan cemaka ba idan kacemun,,,,,,, gira
yadaga mashi yana murmushi yace ai kagane?.
Areef yace kaide kasani dan iska kawai, kamata yayi ya
rungumeta ahankali yace kinajina ko beauty? Kai tadaga
mashi tana turo baki, murmushi yayi yace yauwa idan
bakiso inkira mutane sukamaki to kici abinci inbaki
magani zaki warke, ai dajin haka tabude baki. Dariya
Haisam yayi yace anya beauty bata tsoron mutane
kuwa? Wannan shine karo na biyu danaga tana tsoro
idan ance mutane. Areef yace haka ne, nima nalura da
haka, kuma inaso Aunty tafito tadan bani labarinta, dan
ban gamsu da bayaninta nadazu ba, yarinyar nan tafi
kama da diyan larabawa.
Haisam yace shiyasa naga kuna dan kama , harararshi
yayi yace ta ina? Haisam yace wlh ba batun wasa ba,
dazu data kulle idonta na kalleta naga kundanyi kama,
musamman tagurin idanunku da bakinku. Areef yace
kaji dashi, nibanga wata kama ba, kyaleshi yayi yadauki
cokali yafara bata abinci.
Hankalinshi gaba daya yana gurin kallon yanda take cin
abincinta, shikanshi abun burgewa ne, tana jikinshi
ahaka tagama cin abincin, shiko Haisam kallonsu kawai
yakeyi, yafiddo waya yana daukarsu vedio, sun bala,in
burgeshi, gani yake kamar atare aka halicce su. Magani
ya ballo sede da kyar tasha, shima seda yayi mata wayo,
tana gamasha ta koma jikinshi ta kwanta, kallonta yayi
yace bacci zakiyi? Kai tadaga mashi, tare da lumshe ido,
ko minti 5 ba,ayi ba. Bacci yadauketa. Areef yace beauty
bakida matsala, yarinya cekace jaririya acikin minti 5
harkinyi bacci.
Bayan tagama bata abinci tabata magungunanta, sannan
tajata zuwa bandaki, wanka tayi mata, bayan sunfito
tagoge mata jiki, ta dauko wata doguwar riga tasa mata,
kwantar da ita tayi bisa gado. Idanu ta kura mata ganin
yanda dan kwanakin dasukayi tasake sosai, kara kallonta
tayi, gabanta taji yana bugawa dasauri, matsawa tayi
kusa da ita dan takara tabbatar da abinda tagani. Tabbas
wannan matar zargin malam yazama gaskiya, wasu
hawayen farin ciki ne, suka rika fito mata, zama tayi
takama hannunta tana fadin ita ce, wlh itace, dama
nasan malam baze taba fadin abu yazama ba haka ba,
aiko ayau Sarki zeji labari medadi.
Waya tadauko takira Malam, bayan sungaisa, yace
Safeeya yanajiki cikin farin ciki haka? Wlh malam
tunaninka yazama gsky, dama kace kana tunanin
wannan matar kamar Gimbiya Fulani, wlh, itace, nadade
dafara tunanin haka tun akan diyarta, kamarsu da ita
nake gani afuskarta, sede bakowane ze gane hakan ba,
amma nide wlh yanda nasan Fulani kamarta bazata iya
bacemun ba.
Hamdala Malam yayi yace nadade da tunnin haka, sede
kinsan irin wannan al,amarin ba,a saurin yanke mashi
hukunci, dole muyi ma Allah godiya, kuma zansa ayi
sadaka, sede akwai abu daya danakeso daga gareki,
wannan maganar daga ni seke se Waziri mukasanta,
shima yanzu zankirashi infada mashi zarginmu yazama
gaskiya, ammafa dole muyi shiru da bakinmu, kinsan
idan har baka iya kama barawo ba, toshi seya kamaka,
acikin gidan sarautar nan, akwai munafukai dayawa,
idan bamubi asannu ba, bazamu iya kamasu ba.
Dan haka nasan haryanzu babu wanda yasan dazamansu
agurinki, inaso kicigaba da rike sirrinmu, har ranar da
Allah zebama Gimbiya lfy, bincikenmu zefi tafiya dede.
Shiru tayi can kuma tace amma malam akwai mutum 2
dasuka san Yar Baba tana gurina, Yarima da abokinshi,
yanzu haka suna gidan nan,,,,,,,,, kwashe duk abinda
yafaru tayi tafada mashi, malam yace babu damuwa
inaso kibarshi ayanda kika fada masu, sede kada kibari
suga Gimbiya tunda dama kince bata fitowa falo,sallama
yayi mata yace zekira Waziri.
Falo tafita ta iske su zaune, murmushi tayi tace kuyi
hakuri nabarku dajira. Areef yace bakomai, hartayi bacci
ma, Jakadiya tace kwantar da ita muje nima fita zanyi
nasan gimbiya tana jirana, Areef yace a,a muje inkaita
daki ahaka ai seta fado. Daukarta yayi kamar baby ya
nufi dakin jakadiya, saman gado yadorata, juyi tayi
takara rungumoshi, harseda yafada mata. Wani yarrr
yaji ajikinshi, murmushi yayi yacire hannunta yajawo
pillow yasa mata, nan take tarungumeshi, tsayawa yayi
yana kallonta, dukawa yayi ya sumbaci goshinta, tare da
fadin Allah kasa Momy da Abba sukarbi zabina. Juyawa
yayi yafita.
Bayan malam yakira Waziri sundade suna magana,
bakaramin dadi Waziri yajiba dayaji bayanin malam,
haka suka dade suna tattaunawa, daga karshe Waziri
yace akwai wani sirri dana fara ganowa agidan nan
amma inaso inkara tabbatar dashi kafin infada maka.
Malam yace Allah yayi mana jagora, insha Allah komai
yakusa zuwa karshe, zan aiko da maganin me martaba.
Godiya Waziri yayi mashi sukayi sallama.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
0 comments:
Post a Comment