Waziri ne zaune tare da Sarkin Fada, Waziri ya kalli
Sarkin fada yace, kasan nifa nafara gajiya da masarautar
nan, bamu samun komai se wahala, shi wancan Yana
zaune, jaririma yafishi dadin sha,ani, shikuma Sarki
Qaseem bawani aiki yake ba, kullum da anyi magana
yace Yayanshi, kawai idan bazasu iya ba, yakamata
sumika ma nawajenka.
Amma kuma zamusha shiririta, dan nasan Yarima kwata
kwata sarauta bata dameshi ba, shiyasa kozaman fada
bayaso. Wata irin dariya Sarkin fada yayi, da alama
antabo mashi inda yake mashi kai kai, baki ya karkace
yafara zuba, ashede kaima kana layina, yoni idan tanine
ai dayanzu an dade dashafe babin wadannan sarakunan
2.
Aduniya babu abinda natsana kamar inga wadannan
mutane 2 suna farin ciki, shiyasa bakaramin dadi najiba
alokacin da akace Sarki ya samu matsalar shanyewar
barin jiki. Naso ace Sarki Qaseem be anshi sarautar ba,
nasan kila da kai za abama.
Amma kana maganar wani Yarima ai har abada bazeyi
sarauta ba, sede idan ubanshi ya mutu, ai akwai dalilin
dayasa bayason sarauta, anfada maka son danake mashi
nabanza ne? Nifa banason wani daga zuri'arsu yaci gaba
da mulkin nan. Waziri yace amma nasan duk ranar da
akace angano inda Fulani take nasan daga ranar Sarki
zewarke.
Dasauri Sarkin fada yace ina, ai har abada kuwa baze
warke ba, dan bana tunanin Fulani tana raye, saurin
kallonshi Waziri yayi yace kamar ya kenan? Rufe baki
yayi yafara in ina, yace a,a kagane bawai ina nufin
tamutu ba, gani nayi yau shekaru nawa da batan ta, inda
tana raye ai da anganta. Wani murmushi Waziri yayi
yace dama musami labarin mutuwarta ai dayafi, Sarkin
fada dasauri yace wlh kuwa da kowa ya huta. Tashi yayi
yace bari inje gurin mutuniyata, waziri yace wakenan?.
Jakadiya Karima mana ai kasan duk gidan nan banida
aminiya kamarta, wato matar nan tasan takan duniya,
sallama yayi mashi yayi gaba. Wata irin zufa ce tafara
fitoma Waziri, ahankali yace Jakadiya Karima? Tasan
takan duniya? Aminiyarshi?. Murmushi yayi yace
nasamu daya, saura na biyu. Waya yaciro yakira malam,
sun dade suna magana kafin yakashe yanufi fada.
Areef ne kwance akafar Momynshi Jakadiya Safeeya tana
gefe suna fira, ahankali Gimbiya tashafi kanshi tace
Yarima haryanzu naji shiru tunda mukayi maganar aure
baka kara cewa komai ba, kasanfa kabar Abbanka cikin
damuwa. Wani murmushi yasaki tare da lumshe ido, ita
yakara gani aidonshi alokacin dayake bata abinci,
ahankali yace beauty.
Momy tace wacece kuma Beauty? Saurin bude ido yayi
yace kawai Momy inason mace me kyau, shiyasa kikaji
nace beauty, murmushi tayi tace to kasamu kenan? Kai
ya girgiza mata yace nade kusa samu kitayani addu,a.
Momy tace Allah yasa irin zabin muce? Bata fuska yayi
yamike tsaye yace Momy wai haryanzu baku cire
wannan ra,ayin daga ranku ba? Nifa agskiya bazan auri
yarinyar data taso gidan sarauta ba, duk wata al,ada tata
da dabi'unta duk na sarauta, nidan sarauta itama yar
sarauta towazeyi mulkin kenan?. Shiru Momy tayi tana
kallonshi, tashi Jakadiya Safeeya tayi takama hannunshi
tace haba dan autan Gimbiya, tomeye na bata ran?
Zomuje gida kafadamun abinda kakeso, amma nima
zanfada maka wanda nakeso, kayarda ? Kai yadaga mata
taja hannunshi suka fita, da murmushi Gimbiya tabisu,
aranta tana fatan Allah yasa ya amince.
Gimbiya Zakiyyah ce take tafaman masifa akan jakadiya
Karima, wai ke wace irin mata ce, harni zakizo kirika fada
ma, wai Sarkin fada yana gaishe ni. Toshi wanene
dazemun wannan aiken, ko anfada maki ni baiwace
dazakizomun da wannan maganar. Amma balaifinku
bane, dan kunsami sakin fuska daga gurina ne, shiyasa
kuke fadamun abinda kukaga dama, inda narike mulkina
wlh ko kusa dani akace kizauna baza kizoba.
Kuma inaso kifadamun akan wane dalili Sarkin fada yace
kigaisheni? Kasa tayi da kai tace Allah yahuci zuciyarki,
wlh bada wata manufa yace nagaisheki ba, dama ganina
yayi zanshigo nan shine yace ingaisheki, amma ai be isa
yayi maki irin gaisuwar dakike tunani ba, agafarceni
Gimbiya. Zama tayi tana huci tace, wannan shine karo
nakarshe dazaki kara batamun rai, idan bahaka ba, wlh
sekin fuskanci hukunci na. Godiya nake ranki yadade
uwargida agurin Sarki, mace daya tamkar da dubu, fitila
me haske zuciyar Sarki, Allah yakaramaki lafiya da
daukaka aduniya, Allah yasa kifi haka. Murmushi tasaki
sannan tadaga mata hannu tace muje kirakani gurin
Medaki inaso indubata. Zaro ido Jakadiya tayi tace Eye,
na'am , mekikace? Wata harara tasakar mata tace kina
nufin bakiji menace ba? Nima yau inaso inje bangarenta.
Wani miyau medaci Jakadiya tahadiya, dan ta tuna sanda
zatazo nan sunhadu da Sarkin fada kuma zeje gurin
Medaki. Tashi tayi jiki asanyaye suka nufi bangaren
Medaki, bayi suna take mata baya.
Koda suka shiga azaune suka sami yar baba tana kallon
casset din da Jakadiya ta kunna mata, tana ganin Areef
tashiga sakin murmushi, shima murmushin yasaki, tare
da sakin ajiyar zuciya, kusa da ita yazauna yana fadin
beauty jiki yayi sauki ko? Matsowa tayi kusa dashi tadora
kanta saman kafadarshi tare da daga mashi kai. Girgiza
kai jakadiya tayi aranta tace dole in nuna ma Yar Baba
matsayin kowane namiji agurinta, wato ita atunaninta
yanda take hawan Baba kowama zata mashi haka? Dole
musake sabon karatu. Tanaso tace mata ta tashi kuma
bataso Areef yadauka dawata manufa, zama tayi akasa
tace zonan yar Baba inji jikinki.
Tashi tayi taje tazauna kasa tare da dora kanta saman
cinyarta, hannu tasa ajikinta tace ai zazzabin ma yatafi
ko? Kai ta daga mata tana maida kallonta gurin Areef.
Itama Jakadiya shi ta kalla, aranta tace tabbas kuna kama
daga idonku har gurin bakinku, saukowa yayi shima
yazauna akasa,ya kalli Jakadiya yace.
Aunty kina ganin idan nafitoma Momy da Abba wadda
naji zuciyata tanaso, kuma bata kasance yar sarauta ba,
kina ganin zasu ansheta? Murmushi Jakadiya tayi tace
kwarai ma kuwa, amma dole sekayi abinda zanfada
maka idan bahaka ba to sede ka auri mata 2, nikam
banaso ka hada macen da kake so da wata, kana ganin
yanda Sarki yakasance alokacin daya samu wadda
yakeso, jiyayi dama beyi aure ba, da babu abinda zesa
yakara aure bayan ya aurin zabinshi. Kuma kasan yanda
sharrin matan sarauta yake, idan har sukaga mijinsu
yana nuna fifiko atsakinsu yanzu zakaga anfara shigo da
hassada.
Kuma nibanason kayi wani abu daze zo yaraba zumincin
dake tsakanin iyayenka, duk da bangama gano wacce
kake so ba, amma inaso yanzu kafada mun. Shiru yayi
yana kara kallon beauty, itama shi take kallo, yace Aunty
zanfada maki amma banaso beauty taji. Ai tanajin
abinda yafada tafara dirza kafa akasa, tana turo baki tare
dayin bayaninta da hannu na kurame. Dariya suka saka,
yace metace wai?.
Jakadiya tace a,a ni baruwana kaine dakayi magana take
wannan borin. Kallonta yayi yace beauty ai wannan
maganar manya ce shiyasa nace banaso kiji, tashi tayi
tadauki pillown kujera takwada mashi tashige daki tana
dira kafa, dariya yayi hada rike ciki. Wayarshi ce tayi
kara, yana dauka yace kasameni gidan Aunty.
Jakadiya tace hala Haisam ne ? Yace ai kinsan seshi,
shikadai ne abokina aduniya nayarda dashi kamar yanda
ya yarda dani, shiyasa bana tsoron yasan komai daga
gareni. Sallama sukaji, Areef yace kashigo mana katsaya
kamar kazo gidan surukai.
Zama yayi bayan sungaisa da Jakadiya yamika ma Areef
hannu suka gaisa yana fadin ai garani bagidan surukan
nazo nazauna ba. Dariya suka saka, Areef yace yauwa
Aunty inajinki menene abinda kikeso inyi? Zama ta gyara
ta kalli Haisam tasake fadin abinda tafada da farko,
sannan takara dacewa abinda nakeso da kai yanzu
kafadamun wace yarinya kakeso kuma a ina take, daga
nan ni kuma zanfada maka mezakayi.
Sarki Qaseem ne zaune afalon gimbiya suna fira tana
mika mashi kankana, kallonshi tayi tace Hubby, kayi
hakuri nayi wani hukunci kuma bansanar da kai ba.
Jawota yayi yasata ajikinshi sannan yace bakida damuwa
kome kika yanke nasan zeyi dede da ra,ayi na, kinsan
muna tafiya akan tsari daya. Murmushi tayi tace haka ne,
dama bawani abu bane, munyi waya da Yaya nace mata
tashiryo Ayman tadorota jirgi gobe ta taho.
Naga alamar Yarima yakasa samun wadda yakeso, nayi
tunanin baya shiga cikin yan mata ne, shiyasa besamu
wadda yakeso ba, amma idan Ayman tazo zansata tarika
yimashi duk wata hidima, kuma surika fita tare nasan yin
hakan zesa su shaku har soyayya tashiga tsakaninsu.
Murmushi Sarki yayi yace, shiyasa nake sonki dayawa,
kinyarda ra,ayinmu yana tafiya dede? Kai tadaga tana
wasa da hannunshi. Yace amma ina fatan baki fadama
Ummin Aymana dalilinki nasan tazo ba ko? Tace kamar
kasani, banaso mushiga tsakaninsu harsesun shirya
kansu sannan.
Yace da kyau, nafison kamar yanda naganki naji inasonki
kema haka banaso mushiga hakkin Areef, duk da idan ya
gwada bazebi zabinmu ba, bazanyarda ba, amma ko ita
kada kifada mata dalilin sawa tazo, kawai kibarta, nasan
zasu saba. Rungumeshi tayi tana fadin nagode hubby na.
Kiss yayi mata akumatu, yana fadin bari inje gurin yaya
yau likitan daze fara yimashi gashi zezo daga,
U.S, Tace Allah yasa adace, amma anan zezauna ko? Yace
e zeyi kamar wata guda, kuma insha Allahu munasa ran
nasara. Tace Allah yasa.
Da sallama suka shiga falon Medaki, sede bata nan, cike
da fargaba Jakadiya karima tace rankiyadade kizauna
bari inje indubota, zata shiga kenan tafito tana fadin
ashe yau manyan baki garemu, Gimbiya Yaya da kanki
aida kin aiko nazo. Ya mutsa fuska tayi tace kawai nima
sha,awar fitowar nakeyi.
Zama tayi Jakadiya sebinta da idanu takeyi jikinta yana
tsima, wata baiwa ce tashigo hannunta rike da katon
faranti medauke da kayan marmari, jakadayi tace barka
da fitowa Gimbiya, tace yauwa sannunki. Jakadiya tace
ina fatan wannan kayan marmarin nadazu da aka kawo
marasa kyau anfitar dasu ko? Medaki ta kalli Jakadiya,
tayi murmushi tace ai basu dade bama. Gimbiya
Zakiyyah tace shiyasa nakeso arika duba kayan daza,a
kawo base ankawo ba ace basuda kyau.
Jakadiya tace kwarai ma kuwa, ai tunda basu cikin gidan
nan hankalina ai yakwanta. Gimbiya Zakiyyah tace se
akara kula. Medaki datake dariya aciki takara kallon
Jakadiya wadda jikinta yayi sanyi, aranta tace lallai
Jakadiya yar duniya ce, aifa sekayan marmarin, Sarkin
Fada ai yamafisu komai. Gimbiya Zakiyyah tace yanzu fa
idan Sarki yafadi ya mutu shikenan munzama yan kallo
agidan sarauta ko?
Medaki tace nima nayi wannan tunanin anya babu saka
hannun kaninshi arashin warke warshi kuwa? Ace ciwo
shekara 18 harda watanni amma be warke ba. Kiduba fa
kiga yanda yaki yarda afitar dashi waje, kullum seyarika
fadin wai yace baya so, to mutumin da baya magana
taya zece bayaso?
Jakadiya tace nizan fada maku haka, nida ake komai
agabana, aduk lokacin da za,ayima Sarki gashi ko za,a
bashi magani, daga Sarki Qaseem se Waziri kadai suke
shiga dakin, nima nasan akwai abinda suke kullawa, kalli
yanda Waziri da Sarki suka hade kansu, kullum yana
manne dashi, Sarkin fada beda wani anfani agurinsu.
Gimbiya Zakiyyah tace, to gaskiya bazan yarda ba, daga
yanzu inaso kirika saka idanu akan duk wani abu
dasukeyi, tunda kowa yasan kece makusanciyar Sarki,
dole subarki kizauna tare dashi. Jakadiya tace angama
Gimbiya, tashi tayi tace nizan koma. Medaki tace nagode,
kigaida gida sena shigo.
Inajinka Yarima fadamun kasande babu abinda bazan
iya yimaka ba, dan farin cikinka. Shiru yayi yana sosa kai,
Haisam yace Aunty wlh beauty yakeso, tunda nake da
Areef bantaba jin yayi maganar wata ba, amma aranar
dayafara haduwa da beauty beda magana se tata,
kumani tun alokacin nagane yafada soyayyarta, amma
sanin halin iyayenshi yasa yayi shiru.
Jakadiya Safeeya tace, na jima dasanin haka, sede akwai
abinda nakeso kasani, idan har kanason yar Baba dole
Kaboye ma Iyayenka harse zuwa wani lokacin daya
kamata, banaso azo ahada tashin hankali, wanda zeyi
sanadiyar rushewar zumunci. Areef yace Aunty akwai
wani zumunci atsakaninki dasu Abba ne? Saurin girgiza
kai tayi tace bahaka nake nufi ba, kaide kawai kayi yanda
nace, kawai kanuna masu kana nema nan da dan lokaci
komai zezo karshe.
Areef yace amma Aunty yanaga kamar beauty ba irin ta
yan nigeria bace, gsky kyanta yawuce misali. Rasa
mezata ce mashi tayi, tace kasan dangin mamarta ba yan
nan bane, buzaye ne. Areef yayi murmushi yace haba
shiyasa. Amma haka aka haifeta bataji, tomeyasa ba,a
kaita asibiti ba? Jakadiya tace gsky ba,a kaita asibiti ba,
kuma banaso kace zaka kaita ayanzu, idan lokaci yayi
seka kaita, nima inaji ajikina kamar zata warke. Haisam
yace mungode Aunty Allah yabiyaki, tace amin, tashi yayi
yace bara inje inbada hakuri.
Jakadiya tace, a,a nasan tayi bacci kabarta kawai anjima
sekadawo. Haisam yace malam muje akwai inda nakeso
muje, sallama sukayi mata suka fita. Ajiyar zuciya tayi
tace Allah katona asirin mutanen dasukayi wannan abu
kowa yahuta, nasan Gimbiya zakifi kowa farin cikin zabin
da Yarima yayi, sede ina tsoron zuwan Ayman kada
ahada rigima, nasan duk mun son da kikema Fulani
bekai na yar uwarki ba. Tashi tayi tashiga dakin Fulani.
Zama tayi takura mata ido tana kwance tana bacci, tace
tabbas wahala tana canzama mutum kamanni, nayi
mamakin yanda banganeki ba tun farko, amma ba abun
mamaki bane, sbd irin wuyar da kikasha ashekaru 18 ko
Sarki baze iya ganekiba. Fita tayi tanufi dakin beauty.
Jawota tayi tana fadin haba yar leleta, yihakuri, yace
zedawo anjima ai, kobakison yadawo? Kaita girgiza tana
turo baki, dariya Jakadiya tayi tace, shikenan, tashi muyi
wata magana me amfani, tashi tayi tazauna tare da dora
kanta bisa kafadar Jakadiya, murmushi tayi tace Sarkin
son jiki, to kinsan menakeso infada maki? Daga yau
banason inkara ganin Yarima yazo kinhau jikinshi, ko
hannunshi banaso kitaba, kinsan nafada maki babu kyau
kataba namijin da ba,a maku aure ba ko? Dan haka
yanzu yace yana sonki, kuma aurenki zeyi.
Tokinga duk macen da akace anaso bazata kara bari
saurayinta yataba taba harse an daura aure, kinji ko? Kai
tadaga tana rufe fuska, Jakadiya tace kobaki sonshi,
dasauri tayi mata alamun a,a dariya tayi tace kamar
gaske keda bakisan wani so ba. To inde kinasonshi idan
yazo kirika zama nesa dashi kinji? Ta daga kai. Jakadiya
tace yauwa tashi kidauko Fikhu mucigaba da karatunmu.
Shiru Sarkin fada yayi yana jin bayanin Jakadiya
karima, harta gama yayi dariya yace lallai, wato nine ma
kayan marmarin? Amma kinhadu, wlh kamar nasani
inazuwa nace mata sauri nakeyi. Ita kuma Gimbiya dan
tasamu ance ana gaisheta zata fadamun haka. To wlh
tunda miyau na yabiya da ita kota halin yaya senasha
romonta. Jakadiya tace wlh bakada dama, wato duk
matan Sarki seka more? Yace kede muje zuwa kawai.
Washe gari tunda safe aka shiga da Sarki Hasheem dakin
gashi, inda sabon likitan yafiddo kayan aiki masu nagarta
yafara yimashi gashi dasu, Sarki Qaseem da Waziri se
addu,a sukeyi Allah yasa adace. Jakadiya Karima ce tayi
sallama tashigo falon, bayan tamika gaisuwarta da
tambayar me jiki, tace dazu naga wani bature shine nace
ko bako mukayi ne?
Waziri yace abokin Sarki ne, tace aiyo, nace memartaba
ko wanka akemashi ne? Waziri yace dan Allah kifita
koma menene idan angama za,a kiraki, tashi tayi tana
cewa to to afito lafiya, da harara yarakata aranshi yana
fadin tabbas abinda zuciyata take fadamun akanki yafara
zama gaskiya, amma muje zuwa nasan lokacin yataho.
Sarki yace meyasa baka fada mata gaskiya ba, kasan
aduk gidan nan babu wadda Yaya yakeso kamarta, Yanda
muka dauketa kamar Uwa take agaremu dan mundade
da ita. Waziri cike da takaici yace nasani, kawai banason
yawan magana ne kasan addu,a mukeyi shiyasa nace
mata haka dan karta katsemu. Kallonshi Sarki yayi badan
ya yarda da abinda yafada ba.
Sarkin fada ne zaune adakinshi hannunshi rike da wani
abu yana kallo yana murmushi, yace Gidan sarauta babu
gsky, nasan wata rana dole asirinmu zetonu, akullum
idan bayi suka hada kai da yan sarauta karshe sune
masha wuya, nasan mu munfi bayi matsayi, amma
kuma kaskantattau Gimbiya take daukarmu agidan nan,
ranar tonan asiri aranar zakamun rana. Dariya yayi
yamaida abun cikin jakarshi yana fadin wai Sarkin Fada?
Kode Sarkin tsiya? Wata dariya yayi yace koni ina tsoron
kaina.
Seda Ayman takwana 1 dazuwa sannan suka hadu da
Areef, yafito da yamma cikin shirin fita afalo yagansu
zaune, Areef yace kai, Momy yaushe Ayman tazo bansani
ba? Murmushi tayi tace kana can gurin Haisam kuma
sanda kadawo tayi bacci, dasafe kuma kafita aiki bata
tashi ba, dama cewa nayi zaka ganta da idonka. Dariya
yayi yazauna yana fadin mutanen misrah tace Yaya Areef
inakwana, yace lfy lau, kinzo lafiya ya yan gidan? Tace
lafiya lau suna gaisheka, yace to ina tsarabata? Tace tana
nan, yace yauwa bari inje Haisam yana jirana idan
nadawo zan karba.
Momy tace inazakuje? Yace wlh kawai zamufita garine,
tace to ai dakuntafi tare itama taga garin, yace hakanefa
taso muje kiga birni, dariya tayi tace wane birnin kuma,
fita sukayi suna fadin semun dawo Momy. Da kallon
sha,awa tabisu tana murmushi, tare da fadin Allah kasa
su hada kansu amin.
Tare suka jero har bakin motar da Haisam yake tsaye
yana jiranshi. Idanu Haisam yaware yana kallon Ayman
wadda taketa dariya ita da Areef, gaba daya tagama
tafiya dashi, suna zuwa gaban motar Areef yace yi hakuri
kaga wadda ta tsaidani nan, se alokacin itama ta kula
dashi. Idanu itama tazuba mashi tana kallonshi cike da
burgewa, gaba daya yagama tafiya da ita. Areef ya tsaya
yana kallon Haisam wandda bemasan abinda yakeyi ba,
juyawa yayi yakalli Ayman, itama mamaki tabashi yanda
ta tsaya tana kallon Haisam, dariya Areef yayi ya harde
hannuwa akirji tare da jingina jikin mota yana fadin ikon
Allah.
Nima nace Ikon Allan gaske, Areef tayani gani.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 80 ⚜85
Season 80 ⚜85
Da karfi Areef yabugi kafadar Haisam yana dariya,
cikin sauri Haisam da Ayman suka dawo cikin
hankalinsu, kunya duk takamata ganin Areef yagane
kallon dasukeyi, cikin dakewa Haisam yace wlh kai dan
iska ne, ni nayima haka lokacin dakaga Beauty?.
Dariyar da yakeyi ya dena yana fadin ai gani nayi
kunmaida ni dan kallo, Haisam yajuya yakara kallon
Ayman wadda ta sadda kanta kasa tana wasa da
yatsunta, murmushi yayi yace yaushe kukayi bakuwa
bansani ba?.
Areef yace kaide kashiga mota muje, kuma kabani key
din, Haisam yace saboda? Areef yace kaima kasan bazan
shiga tukinka yanzu ba, idan ko zaka tuka to wlh sede
acire center mirrior. Dariya Haisam yayi ya cilla mashi
key din, yana fadin ai se inzauna baya kaga nahuta da
waige.
Tunda suka fara tafiya Haisam yakasa zama dede, ita ko
duk kunya takamata, da kyar ta iya gaishe shi. Haisam
yace lfy lau kinzo lfy? Tace lafiya lau, Areef yace malam
yazaka barni ina tuki karika juyawa gurinta anbarni
sekace driver. Dariya Haisam yayi yace Allah yabaka
hakuri Yaya Babba.
Dariya Areef yayi, yace kaji munafunci, zakayi bayani ne.
Wani gurin shakatawa sukaje, bayan yayi parking suka
sami guri suka zauna, haryanzu Haisam yakasa dauke
idonshi akan Ayman. Jan Areef yayi gefe, anan yace dan
Allah abokina ina kasamo wannan me kyan? Dariya Areef
yayi yace diyar Yayar Momy ce fa, jiya tazo, nima seyau
naganta shine Momy tace mufito tare. Ajiyar zuciya yayi
yace Allah yasa wani beriga ni ba, kasan Allah? Alokacin
dana ganta jinayi numfashina yana neman tafiya.
Bantaba haduwa da macen data tafi dani alokaci guda
ba, se Ayman, kuma yanzu ba se anjima ba, zanshigar da
kaina. Areef yace ai bazaka sha wahala ba, dan naga
itama ta kyasa. Haisam yace muje munbarta ita kadai,
Areef yace kawaide kutashi mutafi gida nima wlh beauty
na nakeson gani. Haisam yace dan Allah kabani 5
minutes ya isa.
Cikin wani shopping complex Areef yashiga, haka yayi ta
daukarma Beauty kayan lashe lashe. Zama Haisam yayi
akan kujerar datake fuskantar Ayman, shiru yayi yana
kallonta har nawani lokaci, ahankali cikin murya mecike
da so yakira sunanta da Angel. Seda taji wani Yarrr
alokacin dataji sunan, kara dukar da kanta tayi tana
murmushi.
Kara kiran sunan yayi, ganin bazata dagoba yace haba
Angel, ko rowar fuskar ake mani? Wlh bazan boye maki
ba, tun lokacin danayi ido biyu dake, kika tafi da
zuciyata, Allah yasa babu kowa ataki zuciyar kamar
yanda tawa take empty? Wani dadi ne yaziyarci zuciyarta
jin abinda yafada.
Angel kode in hakura akwai wani dan uwanki kuma dan
kasarku wanda yarigani. Batasan lokacin datace a,a ba,
dariya yayi yace kina nufin nasamu karbuwa kenan? Kai
tadaga, wani sanyi yaji aranshi, hannu yamika mata yace
tobani wayarki insa maki number ta.
Yana cikin sawa Areef yadawo hannunshi dauke da
manyan ledoji guda 2, yace kai wlh nagaji zantafi kuma
sede kunemi mota. Haisam yace ai mungama harna
kashe boss. Dariya yayi yace ainasan dama bazaka sha
wahala ba. Ayman cikin hausarta wadda bata goge ba,
tace Yaya tsaraba kasiyomun?.
Dariya yayi yace haba Ayman ai yanzu kinfita daga
hannuna, nima iyalina nasiya mawa. Turo baki tayi tace
kai Yaya yaushe kayi aure? Yace keyanzu aure kikayi dana
ganki kina fira? Murmushi tayi tare da saddar da kanta.
Haisam yace Angel tashi muje kizabi abinda kike so,
Areef yace oho de, aide seda nayi sannan kuma kuyi
sauri.
Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai, dan yanzu yafara
motsa hannunshi da kafarshi dasuka dena amfani ada,
bakaramin dadi Waziri da Sarki Qaseem sukaji ba, sede
haryanzu befara magana ba, kuma akullum tare suke fita
dashi fada, sede idan yana bacci.
Acikin matanshi babu wadda take zuwa gurinshi da
sunan wani abu, tsakinsu dashi sede su shiga su duba
jikinshi, amma ko abinci Waziri ko Sarki Qaseem suke
bashi.
Gimbiya Suhailat ce, zaune tare da Sarki, kallonshi tayi
tace kasan hubby Ayman da Yarima sunfita yawo,
bakaga lokacin daya ganta ba, yanda yake fara,a, itama
haka, wlh bakaji yanda naji dadi ba. Sarki yace lallai
munkusa shan biki agidan nan, sede inaso abari har yaya
yakara samun sauki sannan. Tace hakan ma yayi, Allah
yakara mashi lafiya, yace amin.
Suna dawowa, suka nufi gidan jakadiya Safeeya, sede
Areef yace ma Haisam sujirashi yashiga yayi magana da
Aunty, kade gane menake nufi? Haisam yace hakane
gskiya jeka bari muzauna alambu.
Bayan sun gaisa yayi mata bayanin abinda yake tafe
dashi. Wani irin dadi ne, yashiga zuciyarta, sede bata
fada mashi dalilin zuwan Ayman ba,kallonshi tayi tace
gskiya naji dadin wannan maganar kuma Haisam
mutumin kirki ne, nasan ko kanwarka yanuna yana so
zaka bashi, dan kafi kowa sanin halinshi, amma akwai
wani abu guda danakeso infada maku daga kai har
Ayman.
Kada ku kuskura kubari Gimbiya ko Sarki wani yasan
tarayyarsu da Haisam, kasan dalilin dayasa nafada maka
haka? Saboda kasan ra,ayin iyayenka akan sarauta, kubar
abin aranku, nan da wani lokaci komai zeyi dede, kaima
alokacin zanyi masu maganar Yar Baba, kaga se ahada
datasu Ayman, kaje kakirawosu, bakomai nasan idan
nace ma Ayman kada tafadama kowa Yar Baba tana gida
bazata fada ba. Areef yace Aunty kamar akwai wani abu
dakike boyemun dan Allah kifadamun, kinsan halina
babu wanda zan fada mawa.
Kai tagirgiza tace babu abinda nake boye maka, kaide
inaso kayi biyayya da duk wata magana dazan fada
maka, nafika sanin masarautar nan, dan haka kabi
abinda nafada maka, kasan bazan taba cutar da kai ba.
Kirawosu inyimasu jawabin dana maka, inaso inshiga
cikin gida. Waya yadauka yakira Haisam yace su shigo.
Bayan sun gaisa Jakadiya Safeeya tayi masu irin bayanin
datayi ma Areef, kallon Ayman tayi tace inafatan kingane
abinda nake nufi? Idan har kunaso burinku yacika to
kubi abinda nafada, bance soyayyarku akwai matsala ba,
sede kuyi hakuri na wani lokaci zaku gane abinda nake
nufi. Ayman tace mungode Aunty kuma bazan fadama
kowa ba. Tace naji dadin haka, bari inshiga cikin gida.
Yar Baba tana shiryawa ne. Kasan mutuniyar ko bacci
zatayi setayi kwalliya.
Areef yace ai haka akeso Aunty, wai niko Aunty Beauty
bata iya rubutu ba, inaganin kamar tunda tanaji ai zamu
iya fira ta waya, muna rubutu ko kuma ta takarda. Shiru
tayi kafin tace , kasan tunda tagirma aka gane bataji,
shiyasa ba,a sata makaranta ba, amma karatun addini
tasan abubuwa da dama kuma Allah yabata wata baiwa
tasaurin fahimtar abu, kome aka koya mata cikin lokaci
kadan zata daukeshi, har mamakin kokarinta nakeyi, ni
kaina danayi boko da hada rubutu zan rika koya mata.
Haisam yace, abu me sauki kenan, ina ganin Areef kafara
koya mata rubutu, ahankali sekurika shiga cikin karatun
boko, kuma nan gaba za,a iya daukar mata me lesson.
Areef yace hakane, tunda tana saurin fahimta, insha
Allahu setayi karatu, Allah yayi mana jagora, Aunty
kirata, se mubar mata Ayman muje muyi sallar magrib.
Bayan tafito, tazauna kusa da Ayman, tana ta murmushi,
Ayman ma murmushi tayi tare da jawo hannunta, ai
kamar jira take tadora kanta saman kafadar Ayman,
dariya duka suka saka, jakadiya Safeeya tace naga ranar
da zaki dena son jiki kekam, daga ganin mutane, baki
santa ba amma kin hayeta. Daga ta tayi tana murmushi,
Ayman takara jawota tace Aunty kibarta, kinga dama
bani da kanwa yanzu nasamu, kwantawa tayi saman
cinyarta tana murmushi.
Haisam yace tashi muje masallaci kada Abba yace
beganmu ba, Jakadiya tafita tace sekun dawo, akwai
abinci akitchen idan kundawo, suka ce to. Areef yaduka
kusa da beauty yace wato yau kinga yar uwa shine ko ki
kalleni ko? Kai tagirgiza ta tashi ta kalleshi. Dariya Haisam
yayi yace beauty bakida matsala, kome akace kiyi sekiyi,
gaskiya nan gaba zankoya maki bakomai zaki rika yiba.
Duka Areef yakaimashi yana fadin todan bukulu, ai seka
hanata, Allah yakashe yabani idan munyi aure base
narika magiya ba shine zakace wani tadena. Haisam yace
sosai ma, har wannan son jikin duk sena hanata. Dariya
Areef yayi yanufi hanayar fita yace tunda kaine mijin ai
se ingani, aini naji dadin wannan abu, sonjiki. Ai shine
abinso, fita sukayi suna dariya.
Ayman tace sister da kikayi wanka kinyi alwala ko? Kai
tadaga mata, tace yauwa tashi muje kiyi sallah nima inyi
alwala inyi, hannunta takama suka nufin daki.
Sarkin fada ne tsaye abakin kofar Gimbiya Zakiyyah se
waige waige yakeyi kamar marar gaskiya, wani abu
yadauko aleda yasa a idonshi, kafin yashiga gidan,
alokacin tagama sallah tafito falo, da sallama yashiga,
cike da mamaki tace kai? Waya baka ikon shigowa part
dina? Ko kuma wani yace maka ina nemanka? Kai
yadago suka hada ido, wani irin abu taji ya tsikareta,
saurin rufe ido tayi, ganin halin data shiga yasa yayi
murmushi aranshi yace anzo gurin. Kallonta yayi yace
nadauka ai kinason ganina shiyasa nazo amma bari
inkoma.
Saurin bude ido tayi tasaki murmushi tace ni na isa nace
ka koma? Shigo sannu da zuwa, zama yayi abisa kujera,
tace a,a muje daga ciki kada wasu suganka. Murmushi
yayi yatashi yana lashe baki aranshi yana fadin wayyo ni.
Daki suka shiga tace meza,a kawo maka? Murmushi yayi
yace bakomai zoki zauna kawai fira nazo muyi, wani irin
yanayi taji tashiga, tahowa tayi kusa dashi tana wani
girgiza, kusa dashi tazauna tace togani, kallonta yayi
yakamo hannunta yace babu wanda zeshigo ko? Lumshe
idanu tayi alokacin taji wani bakon yanayi yashigeta, tace
ina zuwa bari inbada sako akulle mun gidan kuma kada
abar kowa yashigo, yace akulle gida nida ba nan zan
kwana ba, wani irin kallo tayi mashi tace, kama isa, ai
tunda kashigo sede da asuba kafita. Dariya yayi yace duk
abinda kika fada dede ne rankiyadade, murmushi tayi
tafita. Wani irin tsalle yayi na farin ciki, hannunshi yasa a
aljihu yaciro wani abu aranshi yana fadin saboda tsaro.
Bayan sundawo daga sallah part din Jakadiya Safeeya
suka wuce, anan suka samesu afalo beauty tana kwance
kan cinyar Ayman ita kuma tana ta wasa da gashinta
tana bata labari, da sallama suka shiga, Haisam yace to
wlh baze yuwu ba, wannan matar taka zata sama Angel
dina taurin cinya, Areef yace wlh kai dan iska ne, agaban
beauty kake wannan maganar sokake ka kangararmun
da ita, bacin kasan yarinya ce. Ai dasauri beauty ta tashi
jin abinda Areef yafada, kafafuwa tafara durzawa akasa
tana turo baki tana kunkunai.
Dariya Ayman da Haisam sukayi, Ayman tajawota tace yi
hakuri, shine yace maki yarinya ko? Kai tadaga tana kara
turo baki, kamar zatayi kuka, ai ganin haka yasa Areef ya
matso yaduka kasa kusa da ita yana fadin yihakuri
beauty na wasa nakeyi kinji? Kai ta daga tana murmushi,
Areef yace yauwa beauty na, tashi muci abinci in baki
tsara barki. Tashi tayi tanufi kitchen.
Haisam yace gsky kaci sa,ar mata wannan saurin sauka
haka, to wlh kaji tsoron Allah, Areef yace da tsoronka
nakeji? Sarkin sa ido kawai, kuma badakai zanci abinci
ba, nida beauty zanci. Haisam yace Allah nagode maka
nima daka hadani da abin sona ayau, nadana shiga 3
agurinka, Angel muma tare zamuci ko? Kai tadaga tana
murmushi, lokacin da beauty tafito tasan alokacin ake
bama mamanta abinci, harta nufi dakinta se kuma ta
tuna da maganar Jakadiya Safeeya,,,,,,,, kada kisake
kishiga dakin can idan akwai mutane agidan nan, idan ba
haka ba, kamata zasuyi bazaki kara ganinta ba. Maganar
Areef ce tadawo da ita, beauty mezakiyi awannan dakin
kuma?
Juyowa tayi tana murmushi ta girgiza kai, tanufo
gurinsu, ansar abincin yayi ta koma tadauko sauran,
atare yazuba masu yamika ma Haisam yace ganaku nan,
dariya yayi yajawo yazuba masu, Areef yace taho beauty
na muci, zama tayi kusa dashi, sede bega ta jingina dashi
ba, murmushi yayi aranshi yace su beauty anfara girma
kenan, abaki yafara bata tanaci, shima yace nima bani
zakiyi ko? Kai tadaga tana murmushi, haka sukarika cin
abincinsu sun manta dawasu Su Haisam.
Dariya Jakadiya Safeeya tayi jin abinda Gimbiya Suhailat
tafada, tace ai sundawo tundazu suna gidana, acan
nabarsu suna cin abinci ma. Wani murmushin jin dadi
Gimbiya tayi tace ai nasan Yarima zeso Ayman, gashi
lokaci guda har sun saba, wato kunyata sukeji shiyasa
suka tafi can. Jakadiya tace emana agida na za,ayi firar ai,
kinsan Yarima. Naguri nane, ai, gimbiya tace aise suyita
ta tafiya nima haka nakeso, Allah yabama Yaya lafiya
musha biki. Kallon agogo Jakadiya tayi tace bari inje gida
seda safe Gimbiya.
Kallonta tayi tace haba de tunyanzu sallar isha,i ma
yanzu za,ayi, wai meyasa yanzu bakison zama anan sosai,
musammamma da dare? Gaban Jakadiya yafadi, aranta
tace nasan Fulani tana can takusa tashi ai dole inkoma
kada su Yarima suganota. Dasauri tayi murmushi tace ai
dole intafi inje inji inda aka tsaya amaganarsu,
murmushin jindadi Gimbiya tayi tace hakane fa,
Jakadiya tace nikam yanzu ai nasamu yan fira tunda de
kunya tahanasu zama anan, dan yarima ma cewa yayi
bayaso kusani harse Sarki yasamu lafiya yasan dayayi
maku magana za,a sa rana. Gimbiya tayi dariyar jin dadi
tace kibarni dasu, zamu gwada masu bamusan komai ba
dakanshi zezo mana da maganar, bari hubby yadawo
infada mashi, sosai Jakadiya taji dadin maganar Gimbiya,
sallama tayi mata tafita.
Koda taje kowa yana zaune tare da masoyiyarshi, Areef
yanata koyama beauty rubutu da karatu, kitchen ta
wuce ta dauko abinci tace sannuku da aiki, Yarima yace
Aunty har kindawo? Tace bari inshiga ciki inci abinci inyi
wanka sukace to afito lafiya.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya babu wanda yasan
abinda yake tafiya atsakanin masoyan. Abangarensu
kuwa soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, akoda yaushe
suna part din Jakadiya Safeeya, Areef yadage sosai yana
koyama beauty karatu da rubutu, suna dawowa office
beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira
beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira
kome yakoyamata take daukeshi, ayanzu har rubutu ta
iya, dan tana hada kalmomi.
Ganin haka yasa hankalin Jakadiya yafara tashi, samunta
tayi tafada mata kome Yarima ya tambayeta kada
tabashi amsa, idan ba haka ba, duk ranar da yasan
labarinta bazata kara ganinshi ba kuma zesa akoresu,
kada kisake kice mashi A MAKABARTA AKA HAIFEKI,
kawai kifada mashi abinda nafada mai, kinji ko? Ta daga
kai, da wannan hankalin Jakadiya Safeeya yadan kwanta,
kuma akaci sa,a shima be cika yimata tambayoyi ba.
Abangaren Gimbiya Zakiyya kuwa ta kwace ma Medaki
Sarkin fada, dan duk dare agurinta yake kwana, wani irin
sonshi takeyi, har bataso yayi nisa, sosai Medaki tashiga
damuwa sede tunda Jakadiya Karima tayi mata bayanin
komai, shima Sarkin Fada yace mata yayi hakane dan
kawai yarama irin cin mutuncin datayi masu ne, kuma
kudinta yakeci sosai, kuma yana kawoma su Medaki,
hakan yasa hankalinta ya kwanta idan yasamu lokaci
kuma yana zuwa gurinta.
Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya Waziri akullum
yana kara sakama Sarkin fada ido, dan sunyi waya da
malam yace mashi yayi kokari yagama hada duk wata
sheda daza,a fara tuhumar Sarkin fada yana nan zuwa
tunda jikin Sarki yafara sauki, yanaso akawo karshen
matsalar gidan.
Gimbiya Suhailat ce tafito tana neman Ayman, ganin
bata ganta ba, wata baiwa tace sunfita bagaren Jakadiya
Safeeya. Murmushi tayi tace yaude bari inje da kaina
inga wata wainar ake toyawa, kuma in nuna masu nasan
abinda suke boyemun, ai gara azo ayi bikin nan kowama
yahuta. Allah nagode maka da zaka cikamana burinmu,
bari indawo in bama Yaya albishir medadi, itama nasan
zataji dadi ace Ayman dinta zatayi aure. Fita tayi wasu
bayi suna take mata baya, suka nufi bangaren Jakadiya
Safeeya.
Zaune suke afalo, Areef da beauty suna zaune bisa
doguwar kujera, sungama karatu, yana bata biscuit
abaki, suna ta firar su gwanin ban sha,awa, Haisam da
Ayman suma suna zaune kasa yana bata ice cream tana
ta zuba mashi shagwaba.
Jakadiya kam tana dakin Fulani tagama yimata wanka
tana sa mata kaya, tayi kyau sosai, hutun datake samu
kyanta yafito har kiba tayi. Jakadiya tace insha Allhu
komai zezo karshe da malam yazo kema kije gurin
mijinki koze samu sauki.
Wazirine da Sarki Qaseem suka fito zasuje bangaren
sarki Hasheem, dede gurin part din. gimbiya Zakiyya
zasu wuce, sega Jakadiya da Sarkin Fada sunfito daga
gidan, Sarkin Fada se gyara wando yakeyi, suna fitowa
suka kwashe da dariya, hannu yamika mata suka kashe,
yace kai wlh yau nasha roman Gimbiya, sosai, kinsan
tundazu naso infito ta hanani, ashede haka Sarki yakejin
dadinshi. Jakadiya tace ba dole sunemeka ba, tunda kana
dauke masu nauyin abinda musakin mijinsu yakasa ba,
ai wlh..........
Maganar ce ta makale sakamakon idanu data hada dasu
Waziri. Hannu tasa ta tabo sarkin fada dayake shirin yin
magana. Wata irin zabura yayi alokacin da idanunshi
sukaga abinda take nuna mashi, wani irin kallo Sarki da
Waziri suke binsu dashi,,,, kuttt suka hadiyi wani miyau
me daci, ga wata irin zufa datake fito masu.
Shinko su waziri sunji firarsu? Kubiyoni anext page
danjin abinda yafaru.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 85 ⚜90
Idan ran Sarki Qaseem yayi dubu to yabaci dajin irin
kalaman Sarkin fada da Jakadiya Karima, Waziri ne,
yajuya ya kalli Sarki Qaseem, shi kanshi ya tsorata da
ganin yanayinshi. Cikin sauri yataboshi, yana kallonshi
yayi mashi alamu da ido.
Juyawa yayi murmushi dauke afuskarshi yakalli su Sarkin
fada yace dama gurin memartaba zamuje kuma segashi
munhadu, ko kuma daga can kuke? Dasauri Sarkin fada
yace wlh kuwa shinema mukashiga gurin Gimbiya muyi
mata albishir naganin halin da Sarki yake ciki.
Gaskiya munji dadi sosai, jikinshi yayi kyau, yanzun nan
nashiga ko kinti 2 banyi ba, shine ma muka fito da
Jakadiya. Amma ai kuma yanzu kukazo nan, ko kun dade
tsaye anan? Waziri yayi murmushi yace ai ko second 2
bamuyi anan ba, kuka ganmu, bari mukarasa. Wata irin
ajiyar zuciya suka saki, har suna hada baki gurin fadin to
adubashi, Jakadiya Karima tajuya tanama Sarki Qaseem
kirari, hannu yadaga mata tare da kakalo murmushi
sannan suka wuce.
Sarkin Fada yace wai! Allah yasomu damun kama kanmu
ashema basujimu ba, Jakadiya tace kaide bari, nidama
nasan dakyar idan sunjimu, dan Sarki Qaseem mutum
ne wanda beson jin abinda bedameshi ba. Sarkin Fada
yace haka ne, shima ai Wazirin na Allah ne, babu
ruwanshi dajin gulma, akwai addini, muje gurin Medaki
itama inkwashi rabona. Jakadiya tace to amma gaskiya
yau nima inaso muje dakina.
Wani kallo yayi mata, sannan yace haba Jakadiya da
girmanki kike fadin haka, ai kibarma Gimbiyoyin Sarki,
ke kam yanzu ai kinwuce wannan matsayin. Hade rai tayi
tace amma ai duk tsufa na ban kaika ba ko? Dariya yayi
yace haka ne, amma kinmanta namiji baya tsufa? Kawai
kibar wannan maganar muje inyi abinda zefishsheni.
Wani guri kafin akai part din Sarki Hasheem suka samu
suka zauna, idanuwan Sarki Qaseem har rufewa sukeyi
sbd bacin rai, da kyar ya iya daga baki yace, dan Allah
Waziri kace abinda naji ba gsky bane, nabama mutanen
gidan nan amana musamman wadannan 2, acikinsu
Yaya yafison Jakadiya Karima, nima haka, dan Allah
Waziri. Wani irin tausayinsu ne yakama Waziri, ganin
idanun Sarki Qaseem sunyi ja yasashi matsawa kusa
dashi tare da dafashi yace.
Memartaba wane irin matsayi kabani azuciyar ka?
Kallonshi Sarki yayi yace aduk gidan nan kaine mutumi
nafarko damuka fara aminta da kai, kawuce kowane irin
matasayi agurinmu har ka kai matsayin dan uwa
agurinmu. Bari kaji aduk fadin duniyar nan kai kadai
muke iya fadama sirrinmu, shiyasa bama jayayya da duk
wata shawara dazaka kawo mana.
Kawai kafadi abinda ke ranka namaka alkawarin
komenene zankarbe shi, nasan bazaka taba fada mana
abinda ze cutar damu ba. Gyaran murya Waziri yayi,
fuskarshi cike da annurin kalaman dayaji daga bakin
Sarki Qaseem, ahankali yafara fada mashi duk irin
abubuwan daya fara gani agurin Sarkin fada, har firar
dasukayi seda yafada mashi, daga karshe yace zakayi
mamakin idan nafada maka Gimbiya Fulani tana cikin
gidan nan tsawon watanni 3?.
Seda Sarki yakusa kwarewa saboda firgita, kai waziri
yadaga alamun da gaske yake, sannan yacigaba, akwai
abubuwa da yawa wanda bakusansu ba, daga ni se
Malam, se Jakadiya Safeeya kadai muka sansu, amma
inaso abari se gobe idan Malam yazo zeyi maku bayanin
komai, sede abinda nakeso kasani bawai munboye
Fulani da wata manufa tamu bane, a,a wannan umarnin
Malam ne.
Kuma alokacin da muka kawota gidan nan, babu wanda
yasan itace, dan tun lokacin data bace tsawon shekaru
18, har zuwa yanzu tana cikin yanayi na hauka, kuma
wahala data sha ne yasa muka kasa ganeta, acikin yan
kwana kin nan dayake tana samun kulawa agurin
Jakadiya Safeeya, dan agurinta take zaune, tofa alokacin
ne, tafara dawowa kamanninta, sbd tana samun tsafta,
shine Jakadiya ta ganeta.
Bayan tafada ma Malam, yace kada tafada ma kowa,
kuma yakirani yafada mun, nima yace kada infada ma
kowa, dan wadan da suka aikata mata wannan laifin
suna cikin masarautar mu, dole semunbi asannu zamu
iya ganosu.
Ajiya mukayi waya dashi yace mun zezo gobe domin
yanaso yakawo karshen halin da masarautar mu take
ciki. Babban abin farin ciki tahaifi cikin dake jikinta, Allah
ya azurta ta dasamun diya mace, aranar data bar gidan
nan kamar yanda su Malam suka sami labari daga gurin
wadan da suka tsinceta, to aranar ta haihu, kaga yanzu
Yarinyar tana da shekara 18 da watanni.
Babban abinda yasa nataboka alokacin damu kaji abinda
su Sarkin fada suke fada shine, kasan idan baka iya kama
barawo ba, to shine zekama ka. Nadade dasanin halin da
Sarkin fada yake ciki shida matar Sarki Medaki, suna
aikata kazamar harka, kusan kullum agurinta yake
kwana, nasamu wannan bayanin ne daga gurin daya
daga cikin bayin dana sa ya kular mun da duk wani
motsi na waziri.
Dan haka ayanzu base gobe ba, inaso kabani dama nasa
akama Sarkin Fada da Jakadiya akullesu har zuwa gobe,
idan Malam yazo se afito dasu, nasan idan aka maimaita
masu laifin dasukayi, zasu tona duk abinda sukayi.
Hawayen dake idanun Sarki Qaseem yagoge, saboda
bakaramin kaduwa yayi dajin labarin Waziri ba.
Da ace beji abinda suka fada dazu ba, kuma ace ba
waziri bane yafada mashi dabaze taba yarda da abinda
aka fada ba, kallon Waziri yayi yace ayanzu bani da
sauran bakin magana, da kai da Malam nabaku damar
ku aiwatar da duk wani abu da yayi dede da hukuncin
masarautar nan, sede abu daya nakeso, inaso akawo ma
Yaya Fulaninshi yagani, kila ta silar haka yasamu sauki,
banaso afadi wani abu harse yasamu sauki, dan yaji duk
irin abinda mahintan makusantanmu suka aikata. Waziri
yace godiya nake, bara inje insa akama su, kafin wani
tunanin yashige su sugudu. Sarki Qaseem yace shikenan
bara inshiga gurin Yaya kada yaji shiru.
Da sallama su Gimbiya Suhailat suka shiga falon Jakadiya
Safeeya, adede lokacin da Beauty tana karbar biscuit
ahannun Areef shi kuma yana ta mata wasa da hankali,
se dariya sukeyi, hannu tasa zata karba, cikin rashi sa,a
tafada jikinshi. Kwanciya tayi saman cinyarshi tana ta
dariya shima haka.
Cak Gimbiya ta tsaya da sauran Sallamar data fara,
tsayawa tayi tana kallonsu cike da mamaki, da takaici,
sam bata kula dasu Ayman ba, sede kawai taji dariya
agefenta, saurin kallon gurin tayi, ai jitayi kamar tazube
dan takaici, Haisam ne, yake kokarin saka ma, Ayman
sweet abaki, sunata dariya abinsu.
Kamar daga sama sukaji wata irin tsawa, wadda tasa
beauty saurin kankame Areef, tayi,wani Uban ashar
Gimbiya tasaki, wanda ita kanta batasan ta iyashi ba.
Gaba dayansu hankalinsu atashe suka juyo suna
kallonta, cike da kaduwa Haisam da Ayman suka sauko
kasa, shikam Areef sam abun be daga mashi hankali ba,
kara rungume Beauty yayi saboda kukan datasa mashi,
sam bata taba jin wata aba wai ita tsawa ba, tunda take,
hakan yasa tayi mugun tsorata.
Gimbiya cike da bacin rai tace kai dan Ubanka bazaka
saketa ba, kabani hankalinka? Jakadiya ce tayi saurin
fitowa daga dakin fulani, dan dama tayi bacci ta tsaya
gyara mata dakinne kafin tafita, tana cikin gyara taji
wannan hayaniya.
Alokacin data fito saura kadan tazube saboda kaduwa,
cak ta tsaya bakin kofa tana zaro ido tare da kallon
Gimbiya. Areef yakama beauty suka sauka kasa, dan
shima alokacin da Gimbiya tamashi wannan zagin
bakaramin kaduwa yayi ba, dan tunda yake betaba jin
irin zagin abakin momynshi ba, ko fada bata taba
yimashi ba.
Wani irin murmushin takaici Gimbiya tayi, ta kalli
Jakadiya, rai abace tace sannu munafukar Allah,
mayaudariya, maha inciya, ashe dama abinda kike
kullawa kenan? Kinaso ki batama yarona tarbiyya tunda
ke baki dashi? Wato duk ginin da nakeyi kece kike rushe
shi? Kinje kinsamo wata matalauciyar yarinya kin hadata
da Yarima, ita kuma diyata kin hadata da abokinshi.
Ashe dama duk zaman damukeyi zaman munafurci ne ?
Wai meyasa duk wanda be fito daga gidan sarauta ba,
zaka sameshi maci amana ne? Lallai zamanki yazo karshe
agidan nan, bazan kara amincewa da banzan halinki ba.
Kai kuma Haisam kake kowa? Inaso kasani Ayman
Yarima zata aura, garama ka tattara soyayyarka kayi
waje da ita, ko kuma kaima kaje kasamu diyar dan siyasa
ka aura, danmu bama auratayya da yan siyasa, domin
Sarauta gado ce, kuma ajininmu take, kufa?.
Mulki ne, da lokacinku yacika ko kunaso ko bakwa so,
dole kusauka kubama wanda yaci, dan haka kada inkara
ganinka agidan nan, bare kuma tare da Yarima ko
Ayman. Ke kuma kisaurari hukuncinki, matsawa tayi ta
ture beauty wadda tundazu take kuka.
Hannu Areef yasa yariketa sosai shima hawayene suke
zuba a idonshi, da kyar yace Momy dan Allah kiyi hakuri
wlh beauty itace rayuwata, idan kika rabani da ita
mutuwa zanyi, ture ta tayi takama hannunshi dana
Ayman wadda itama kukan takeyi, Haisam ne kawai
medauriya acikinsu, amma har jakadiya kuka takeyi.
Jansu tarikayi kamar yara har suka fita daga falon,
dasauri Jakadiya ta matsa takamo beauty ta dagata zasu
shiga daki, kuka kawai, takeyi harda sheshsheka, tana
tashi takoma tazube kasa sumemmiya.
Abakin kofar falon Areef ya toge, duk yanda Gimbiya
taso tajashi kasawa tayi, hannunshi ya fisge alokacin
dayaji Jakadiya tasa wani irin kuka tana fadin munshiga
3 Yar Baba dan Allah kitashi, dasauri yakoma falon,
Gimbiya tabishi tana fadin kadawo nace maka ko. Yana
zuwa yaga beautynshi kwance akasa babu alamun rai
atare da ita, wata irin kara shima yasaki tare da dafe
kanshi yazube kasa asume.
Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 90⚜95
Da gudu Gimbiya da Haisam sukayi kansu, tana zuwa
takama Areef hankali tashe tafara jijjigashi tana kuka,
Jakadiya Safeeya ma beauty tarika jijjigawa tana kuka.
Haisam ne yayi kokarin fita waje yakira wasu bayi maza,
suka dawo tare.
Su suka dauki Areef shi kuma yadauki beauty suka fita,
Jakadiya, Gimbiya da Ayman suna binsu abaya, cikin
mota yasakasu, Jakadiya tashiga tare da Ayman ya kulle
kofar ko kallon Gimbiya beyi ba yaja motar suka barta
nan tsaye dan babu halin tabisu, tunda Sarki Qaseem
besani ba.
Komawa tayi part dinta tana kuka, kara tunano kalaman
Areef tayi,,,, Momy wlh kika rabani da beauty nima
mutuwa zanyi. Hannutasa tarufe duka kunnuwanta tana
fadin bazaka mutu ba Yarima, kaine farin cikina, dan
Allah kar kamun haka. Saman kujera tafada tana kuka
bayinta se hakuri suke bata.
Waziri ne, tare da wasu manyan bayi maza suna binshi
abaya, hanyar lambu suka nufa dan yafi zaton suna can,
koda sukaje basu same su ba, tunawa yayi da Medaki,
hakan yasa suka nufi can.
Alokacin Sarkin Fada da Medaki suna cikin daki, ita ko
Jakadiya Karima tana zaune falo tana kallo ta tasa
farfesun kaji tanaci. Wata baiwa ce tashigo falon, ai
dasauri Jakadiya tace Uban wa yabaki izinin shigowa?
Bana hanaku idan muna gidan nan kushigo ba?.
Dukawa tayi tace Allah yabaki hakuri, dama Waziri ne, ya
tambayeni ko keda Sarkin fada kuna ciki, shine nace
masa kuna nan, shine yace amaku magana. Cikin
Jakadiya ne yayi wani kara, nan take zufa tafara keto
mata, batasan lokacin data saki cinyar kazar datake
hannunta ba.
Cike da tashin hankali tace ubanwa yace kifada masa
muna ciki? Innalillahi wainnailaihirraji,un. Munshiga 3
kada de ace asirinmu ne yake shirin tonuwa? Tashi kiba
mutane guri munafuka. Hanyar dakin Medaki tanufa, har
tuntube takeyi, tana zuwa tafara bubbuga masu,alokacin
sunyi nisa cikin harka, dade sukaji bugun yayi yawa,
shine Sarkin Fada yayi saurin zira babbar rigarshi, ko
wando besa ba, haka yaje yabude.
Ai yana fitowa Jakadiya tajawoshi tana fadin munshi 3
gasu Waziri can abakin kofa suna jiranmu. Zaro ido yayi
yana fadin waya fada masu muna nan? Tace kaide
kawuce muje, bawannan bane agabanmu, yanda zamu
kare kanmu bakamar ma kai, danni wlh tawa mesauki
ce, tunda ni macece kuma kowa yasan inada hakkin
shiga duk inda nakeso amasarautar nan.
Sarkin fada yace kiwa Allah kije kice ke kadai ce, bakisan
inda nayi ba, nasan zasu kyaleki. Zaro ido tayi tare da
dafe kirji tana fadin Jar Uban nan, ai wlh baka isa ba, ai
gara ma kai, kome akayi maka kasha dadi, nifa?
Menasha, kun hadani da naman kaza da kallo kunshige
daki, ai wlh inde nafita kaima seka fita.
Bugun kofar falo ne, ya sasu saurin kallon gurin alokacin
Medaki tayi saurin fitowa da daurin gaba ajikinta, kanta
ko dan kwali babu, tana fadin wai meke faruwa haka?
Shigowar Waziri ce tasata yinshiru, idanu 2 suka hada
dashi, hakan yasa yayi saurin kauda kanshi, ai dasauri
takoma daki, kallon Sarkin Fada yayi wanda ko rawani
babu akanshi, dagashi se babbar riga,, jikinshi kam ko
wando babu.
Hannu Sarkin Fada yadora akanshi yana fadin shikenan
yau kuma ahaka tazo mani. Waziri cike da bacin rai yasa
fadawa sukamashi, Jakadiya Karima tace ai dama kullum
ina fada maku kune bakwaji, yau ga irin ta nan, nikam
baruwana, Allah yakara, hanyar waje tanufa tana shirin
fita. Wani kallo da Waziri yayi mata yasa dole taja burki
tana raba idanu.
Wazirin yace ku kamosu dukan su akaisu kurkutu zuwa
gobe, kuma inaso kusaka kwakkwaran tsaro agidan nan,
yanzu zan fadama sauran masu tsaro, kada abari kowa
yafita daga gidan nan koda kuwa matar Sarki ce, koma
waye dole akirani kafin yashigo ko yafita. Haka aka tasa
keyarsu zuwa kurkutu. Medaki kuwa tana daki tarasa
inda zata sa ranta.
Suna zuwa asibiti aka karbesu akayi emergency dasu,
kowa aka fara bashi temakon gaggawa, cikin lokaci
kankani Areef ya farfado, sede beauty ko alamun motsi
batayi, hakan yasa likita yace akai Yarima dakin hutu,
nan suka cigaba da duba Beauty.
Tunda Areef ya farfado yafara kiran beauty, kuka
yasakama Haisam da Jakadiya Safeeya, se lallashin shi
sukeyi, Areef yace wlh idan wani abu yasami beauty na,
nima Momy zata rasani. Haisam yace kadena fadin haka
Areef insha Allahu zata warke. Karar wayar Haisam ce ta
katsesu, Areef yace idan Momy ce kace mata ban farfado
ba dan Allah.
Yana dagawa tace Haisam yaya jikin Yariman? Wani irin
haushi yaji, wato ita ta danta ma kawai takeyi. Ahankali
yace Momy Areef yana cikin wani yanayi, addu,a kawai
zakitayashi. Cike da tashin hankali tace ina likitan banishi,
yace suna can akanshi suna bashi temako.
Dan Allah Haisam kace ma likita yayi duk yanda zeyi kada
dana yarasa ranshi, ko wani abun yasameshi dan Allah.
To kawai yace mata, yakashe wayar. Runtse ido Haisam
yayi yana karajin haushin kalaman Momy, Areef yace
hankalinta yatashi ko?.
Kai kawai yadaga mashi, yace ina ganin matsalar mu
zatazo cikin sauki, sbd Momy tana sonka sosai, dan haka
dole muhada mata plan. Murmushi Areef yayi yace haka
ne, abokina nagode, yanzu muje inga jikin beauty na.
Jakadiya Safeeya tace a,a Yarima ka kwanta jikinka babu
kwari, likitoci suna kanta suna nema mata sauki.
Komawa yayi yakwanta zuciyarshi tana zafi.
Sarki Qaseem ne, afalonshi hankalinshi tashe da abinda
Waziri yafada mashi sungani apart din Medaki, haka
yazauna yadafe kanshi da hannu 2, jin haryanzu shiru
bega Gimbiya Suhailat tafito ba, yasa yatashi yanufi
dakinta, kwance yasameta tana ta kuka, cikin sauri
yakarasa gurinta tare da kamota ya rungume.
Kara rungumeshi tayi tasaki wani sabon kuka, shafa
bayanta yafarayi yana fadin meyafaru kike kuka haka?
Kanta tadago, tana share hawaye tace shikenan
munshiga 3 Hubby, zamu rasa danmu guda 1 da Allah
yabamu. Cike da tashin hankali Sarki yace bangane
mikike nufi ba, meyasamu Areef din ? Ko hadari yayi? Kai
tashiga girgiza mashi, tace yana can asibiti likitoci ma
sunkasa samo kanshi. Sarki yace dan Allah kitashi
kifadamun abinda yafaru, wlh zuciyata gab take da
bugawa, bakisan irin tashin hankalin daya sameni ba,
kifadamun abinda yafaru tunkafin nima kirasani.
Ai dasauri Gimbiya ta tashi tana kallonshi, se alokacin ta
kula da yanayinshi, idanunshi sunyi ja sosai,cike da
kaduwa tace hubby dan Allah meyafaru, kallonta yayi
dan yafara kulewa da ita, tureta yayi cike da bacin rai,
yace ya ina tambayarki kina tambayata dan kin rai nani,
kawai kifadamun abinda yafaru idan bahaka zanbar
maki gidan. Matsowa tayi ta rungumeshi tana kuka, dan
tunda suke betaba yimata irin wannan ba, asalima bata
taba ganinshi cikin irin wannan yanayin ba.
Dagowa tayi tajawoshi suka zauna bisa gado, kanshi
tajawo tadora saman cinyarta tana ta shafa kanshi,
lumshe ido yayi, yana sauke ajiyar zuciya. shiru sukayi
nawani lokaci, jinyayi shiru yasa tadagshi ta tashi takawo
mashi ruwa mesanyi, dakanta tabashi, kofi guda ya
shanye, sannan takara jawoshi yakwanta akan cinyarta.
Ahankali tana shafa kanshi tace hubby karika fadin
Innalillahi Wainnailaihirraji,un, kayi haka harso 5,
sannan infada maka abinda yafaru, amma ina fatan
bazakamun fada ba idan kaji abinda nayi?
Cike da fargaba Medaki tashiga falon Gimbiya Zakiyyah,
alokacin tana zaune tana hutawa, kallonta tayi tace
kekuma lafiyarki zaki shigo mani gida ahaka, ko Sarki ne
ya mutu? Medaki tazauna tace ai da mutuwa yayi zefi
sauki da halin dazamu shiga nida ke, da su Jakadiya,
cinkin lokaci kadan.
Tashi tayi daga kishingiden datake tana yamutsa fuska
tace bangane abinda kike nufi ba? Anan tafada mata duk
abinda yafaru, har halin datake ciki ita da Sarkin Fada
seda tafada mata, dan ita tariga da tagama yarda da ita,
tunda taga halinsu daya ne. Wani irin miskilin murmushi
Gimbiya Zakiyyah tayi, tayi mata wani irin kallo, tace.
Lallai bansan ke Jahila bace se yau, wato keda Sarkin
fada kundade kuna aikata alfasha, saboda kinga Sarki
beda lafiya, kai, wama yasan tun lokacin da kuke tare?
Hmmmm dama nafada, shiyasa duk abinda yafaru daku
wlh bazanji tausayinku ba, kema kijira sammaci anjima
ko gobe, dan tunda Waziri yakamaku da kanshi, kema
kinsan hukuncin kisane akanki.
Tir da ke, kina matar Sarki kinabin maza, mazan ma wai
Sarkin Fadan Mijinki. Kodayake ba laifinki bane, dama
shi talaka kome akayi dashi, seya baka kunya, yanzu
tayaya wanda yafito daga jinin sarauta ze aikata irin
abinda kikayi?
To wlh bari infada maku dake dasu gaba daya, daga yau
babu ni babu ku, kuma koda kunbude baki kunfadi
abinda nasa akayima Rayhana, babu wanda zeyarda
daku, dan bakuda sheda, kuma ni daga gidan sarauta
nake, zan iya amfani da karfin mulkina inkwaci kaina,
dan kunsan atsari na sarauta ba,a yanke hukunci dole
seda sheda bayyanan na, ku kam bakuda wata shedar
dazata nuna akwai sa hannuna aciki.
Kitashi kibani guri tunkafin azo aganki agurina. Cikin
kuka Medaki tace dan Allah kada kinmani haka, nabaki
duka yarda, banda kowa aduniyar nan kece silar jefani
cikin wannan harka dan Allah kada kice zaki juya mun
baya, kinsani duk wani abu da muka aikata shawararki
mukebi, saboda kece babba. Hannu tadaga mata tamike
tsaye tace nace kitashi kibani guri kada inkara ganin
kafarki agidana.
Ni nabi shawarar kiyi zina da kaskantaccen talaka kuma
yaron mijinki? Kafin asirinku yatonu kintaba fadamun
halin dakuke ciki? Dan haka wlh kinji narantse maki
baruwana acikin harkarku, fita nace. Tashi Medaki tayi
tana kuka tafita waje. Wata irin dariya Gimbiya Zakiyya
tasaka tace, uhmm dani kuke magana, anfada maku
sarauta haukace? Kaima sarkin fada nasan kana tunanin
katona asirina.
Ni kuma zan nuna maka bakada wayau,duk duniyar nan
babu wanda zeyarda da kai dan kafada masu munyi
harka tare, domin kuwa babu wanda yasan munyi daga
ni sekai, kuma agidan sarauta ba,a karbar shedar mutum
daya, kuma shedar ma tabaki. Dariya tasa tashige daki.
Saurin tashi Sarki Qaseem yayi yana kallon Gimbiya
Suhailat, bayan tagama bashi labarin abinda yafaru. Kai
yafara girgizawa ta kalleshi tace dan Allah kayi hakuri,
wlh banyi haka dan in cutar dashi ba, kuma ni bansan
Son dayake mata ya kai haka ba, kuma gani nayi nida kai
munzaba mashi wadda ze aura shiyasa nayi haka.
Murmushi Sarki yayi yace kinzaba mashi de, kuma ita
Ayman din ai tasamu wanda take so, to koma bata samu
ba, yarinyar dayakeso ita zanbashi sede ita Ayman tazo
ta 2, domin kuwa kinso ki tabka babban kuskure, ko
rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, yarinyar da kika gansu
tare da Areef jinina ce, kuma shima jininshi ce, bari inje
asibitin inga halin dasuke ciki.
Kuma kisani tunda har Ayman tasamu wanda takeso to
bazata auri Areef ba, da ace tana sonshi, to zanbashi
shawara ya aureta, amma tunda haka tafaru, kowa ze
auri zabinshi. Kuma kisamu kalaman dazaki bama Jadiya
Safeeya hakuri dasu, dan kinci mata mutunci, matar da
ta sadaukar da jin dadinta domin takaremu.
Matar da tabaro kowa nata, badan tana cikin talauci ba,
a,a kawai dan tazauna damu da gaskiya. Juyawa yayi
yanufi kofa zefita, da gudu tarugo tarikeshi tabaya tana
kuka tace, dan Allah hubby kayi hkr kada kamun irin
wannan horon, naji nayarda da duk abinda kace, kuma
nahakura Yarima ya auri koma wacece amma dan Allah
kafitar dani duhu, kuma kada kayi fushi dani kasan
bamu saba haka ba.
Murmushin jindadi yayi, sede bejuyo ba, yace ki kwantar
da hankalinki, danki ze auri irin yarinyar da mukeso, yar
gidan sarauta, albishir daya zan maki, wannan yarinyar
da kika gani ba kowa bace se diyar Yaya da Fulani. Kuma
wani abun farin cikin yanzu haka Fulani tana cikin gidan
nan, sauran bayani sena dawo zakiji, yana fadin haka
yayi waje. Wani irin yanayi tashiga, gaba daya tarasa
mezatayi, ga kunyar abinda tayi yadameta, musamman
idan ta tuno kalaman data fadama jakadiya, komawa
tayi daki tana tunani.
Cikin sa,a da kwarewa tare da temakon Allah beauty ta
farfado, numfashinta ya dedeta, sede haryanzu bata
bude ido ba, kuma bugun zuciyarta be dedeta ba. Likita
yace sukaita dakin hutu, nan da wani lokaci zata dawo
dede akwai abinda ya tsoratata shiyasa tashiga wannan
yanayin.
Adede lokacin Sarki da Waziri suka iso asibitin,kai tsaye
office din likita suka wuce, bayan sun gaisa yayi masu
bayanin halin da ake ciki. Sarki yace amma yaya jikin
yarinyar? Likita yace insha Allahu babu wata damuwa,
zata dawo dede. Amma Yarima jikinshi dasauki. Godiya
suka mashi yasa aka nuna masu dakin Areef da beauty.
Seda Sarki yafara shiga gurin beauty, kwance yasameta
kamar matatta, Jakadiya Safeeya tana gefenta se kuka
takeyi, sallamarsu ce tasa tayi saurin goge idonta, ta tashi
tana mika gaisuwa, da kyar ya amsa, hankalinshi yana
kan beauty, sak kamarta da Fulani da Areef yake gani
afuskarta, wasu hawayen farin ciki ne, suka zubo mashi.
Kusa da ita ya matsa, fuskarta ya shafa ya kalli Waziri
yace tabbas ita ce, ko ba,a fadamun ba nasan wannan
jinin Yaya ce, Allah sarki, Allah maji rokon bayinsa, insha
Allahu ayau Yaya zesamu babban albishir, ayanzu base
gobe ba. Kallon Jakadiya yayi yace kifadamun Ina Fulani
take, inje da kaina inkaima Yaya ita?.
Se alokacin Jakadiya ta tuna sunbarta agida, damma
tasan barci takeyi, sede tana duba agogo taga lokacin
tashinta yakusa, gashi basu kulle gidan ba, cike da tashin
hankali ta kalli Sarki tace Rankai dade tana gida kuma
yanzu zuwa wani lokaci zata iya farkawa, gashi bankulle
gidan ba, ina tsoron tafito, koza,a sa amaidani gida kada
tafito?.
Waziri yace babu damuwa, muje muga jikin Areef
semuwuce tare. Sarki yace a,a tunda ance jikin nashi
dasauki kawai. Muwuce, Jakadiya tace to bari inma
Ayman magana seta dawo nan tazauna kada tafarka.
Waziri yace rankaidade muje gaba daya muga jikinshi
semu wuce.
Areef da Haisam suna cikin tsara yanda zasu hada plan,
Ayman tana gefe duk tashiga damuwa se kallon Haisam
takeyi tana tunanin idan aka rabasu bazata iya. Hakura
dashi ba. Turo kofar da akayi ne. Tasa su saurin kallon
kofa, Areef suna hada ido da sarki yayi saurin komawa
ya kwanta tare da rufe ido.
Dariya yakusa bama Sarki, bayan sun shigo Sarki ya
matsa kusa dashi yace lallai yarona kai ragone tunda har
zaka iya kwanciya asibiti saboda mace, to danazo ince
maka na amince da zabinka amma tunda naga baka
warke ba, nafasa, ai dasauri yamike yariko hannun Sarki
yana fadin wlh nawarke koyanzu ma asallameni. Gaba
daya dakin seda suka sa dariya, hada Ayman me kuka.
Sarki yace ka kwantar da hankalinka babu wanda ze
hanaka auren zabinka, kuma jininka, bari muje gida
mudawo, kallon Haisam yayi yace ka kula dasu, ke kuma
me kukan soyayya sekiyi shiru tunda zaki samu abinda
kikeso, kitashi kije gurin Diyata kizauna zamu dawo
yanzun nan. Juyawa yayi yafita suma suka bisu abaya.
Cike da Mamaki Areef ya kalli Haisam yace Jinina, kuma
diyar Abba? Tome yake nufi? Kafada Haisam yadaga
alamun shima besani ba, yace mujira sudawo maji daga
garesu.
Jakadiya Karima se kuka take tana fadin tsakanina da
Gimbiya Zakiyya Allah ya isa, muguwar mata tasamu
cikin bala,i kuma gashi yanzu mune akulle, bamuda wata
sheda dazata nunama mutane tanada hannnu acikin
abinda muka aikata. Kaicona ni Karima, ban rike amanar
da mutanan nan suka bani ba, naci amanarsu, nima
kuwa Allah baze barni ba. Yanzu shikenan haka za,a
yanke mana hukunci muna kallo abar Gimbiya?.
Wata irin dariya Sarkin fada yayi yace kidena bata
hawayenki abanza, waye yace maki itama zata kubuta?
Aini bana barin baya da kura, inde zanyi aiki to dole se
nasamu madafa nake farashi, ko anfada maki nima irin
kwakwalwar jinin sarauta nakeda ita wadda bata da seti?
Kawai malama kizuba ido kisha kallo gobe.
Suna zuwa gidan afalo sukaci karo da ita tafito se raba
idanu takeyi. Cak Sarki ya tsaya yazuba mata ido, tabbas
ita ce, sede tarame, hannu yadaga sama yanama Allah
godiya, Waziri yace Jakadiya kamota muwuce. Hannunta
takama suka nufi waje.
Ur's.
0 comments:
Post a Comment