LAST PAGE
Washe gari Sarki Hasheem yasamu karfin jikinshi, da
misalin karfe 10, gaba dayansu suka taru a babban falo,
bayan anbude taro da addu,a anan aka fada ma Sarki
Hasheem duk abinda yafaru jiya, sosai ya tausaya ma
Medaki.
Malam yace to Alhamdulillahi, muna godiya ga Allah
daya nuna mana wannan rana, inafatan wannan abu da
yafaru agidan nan ze zame ma kowa darasi, abinda
yarage mana shine mucigaba da neman tsari daga
sharrin masu sharri, kuma kowa yadage da addu,a, kada
kuyi la'akari dacewar wani yana maku addu'a.
Idan har zaka iya saka wani yamaka addu'a to kai
meyasa bazaka iya rage wani abu daga cikin darenka
katashi karoki mahaliccinka ba? Allah da kanshi yake
fada akwai wani lokaci acikin dare wanda yake sakkowa
daga sama yazo ya karbi addu'ar bayin da sukayi
awannan lokacin. Da aka tambayi manzon Allah wane
lokacine wannan? Yace daga karfe hudu zuwa asuba.
Duk wanda yatashi awannan lokacin yayi sallah tabbas
Allah ze karbi addua'arsa. Ina me maku nasiha da ku
daure kurage jindadin duniya kusami lokacin ganawa da
ubangijinku acikin dare, ibadar rana kadai bazata isheka
ba, saboda duk yanda kaso kebewa da rana kace zakayi
ibada ta tsawon minti 30 kadai, dole se wani abu yashigo
maka katashi.
Amma idan akace maka da dare ne, kana da lokaci me
yawa. Kuduba manzon Allah, shifa yariga dayasan anyi
mashi albishir da aljanna, amma duk da haka yakan
tashi cikin dare yayi ta ibada. To kai waye dabazakayi
koyi dashi ba? Wanda aduk cikinmu babu wanda yakeda
tabbacin shiga aljanna. Dan manzon Allah yace akwai
wadan da zasu dade suna aikata aikin alkhairi, amma
karshen wuta ce makomarsu. Kamar yanda wasu zasu
dade suna aikata zunubi amma aljannace mako marsu.
Dan haka aduk lokacin da kukaga wasu suna aikata
alfasha, kada kabata lokacinka gurin aibantasu, kai zaka
cinye ladar daka tarama kanka, amai makon haka kayi
masu wa'azi idan har kaga zasu dauka, idan kuma abin
yafi karfinka to kabisu da addu'a.
Manzon Allah yace aduk lokacin da wani bawa ze
rokama wani dan uwanshi abu agurin Allah, batare da
sanin wancan ba. Mala'iku zasuyi rika yimashi addu'ar
duk abinda yarokama wancan shima.
Daga karshe, ina kara maku nasiha dakuji tsoron Allah,
kuma kucire son zuciya a zukatanku, Allah ze temakeku
aduk inda kuke, kuma kuzauna da kowa da zuciya daya,
idan shi bahaka yake zaune daku ba, wata rana Allah
zetonashi kowa yaganshi, kamar yanda yayi ma wadan
da suka wuce. Ina fatan kowa zerike duk abinda nafada
maku.
Gyaran murya Sarki Qaseem yayi yace, hakika munji
dadin irin fadakarwar da malam kayi mana, akwai
abubuwa da dama daka tunatar damu, wadanda
munshagala dasu abaya, hakika mutum yatashi yaroki
Allah da kanshi shine abinda yafi, domin idan kadogara
da wani, wata rana Allah yana uya daukeshi, shiyasa
akace daka bama mutum kudi yasayi abinci. Gara ka
bashi gona yayi noma, haka kuma daka bashi kudi gara
ka sakashi makaranta.
Wata rana seya temaki kanshi da al'umma. Mungode
kwarai da kulawarka agaremu, Allah yabar zumunci,
kuma insha Allahu zamu kawo gyara sosai amasarautar
nan, ta yanda zamu temaki sauran bayin dasuke cikin
masarautar nan, suma susami ilimin addini kada
rayuwarsu takare abauta.
Malam yace idan kukayi haka tabbas zaku kawo cigaba a
masarautarku, kuma yin hakan zesa wannan masarauta
ta daukaka, harma wasu masarautun suyi koyi daku. Ni
kuma nayi alkawarin turo manyan yarana suzo suma
subada tasu gudunmuwar, kaga ahakane, suma bayi
zasu gane cewa suma mutanene, kamar kowa. Ina rokon
Allah ya amshi wannan niya taku, kuma yasama abun
albarka. Ina ganin ayau zanzo in koma.
Waziri yace mungode sosai Malam, Allah yasaka da
alkahairi, kuma ina ganin kafin kawuce, zamu zabeka
amatsayin wanda ze daura mana sabon Sarkin Fada.
Malam yayi murmushi yace, to inaganin yakamata
abama wanda yakamata abama sarautar tun farko, kafin
aci amanarshi. Koba komai, zeji dadin hakan, kuma
sauran mutane zasu kara yarda dacewa duk zakaran da
Allah yanufa da cara, to ko ana muzuru ana shaho
seyayi, yasha wahala ta dalilin sarauta, ya kwashe
shekaru dayawa acikin kurkutu. Tabbas babu wanda ya
dace da wannan sarauta se shi.
Kallon Sarki Hasheem yayi yace, inaso inji wane suna
kasama diyar tawa, kafin inkoma? Murmushi yayi yakara
kallon Fulani sannan yace agaskiya tunkafin a haifeta
dama nazaba mata suna, badan komai nazaba mata
sunan ba, sedan inyi godiya ga Allah abisa kyautar da
yayi mani nasamun karuwa.
AMATULLAHI, shine sunan dana zaba mata. Lumshe ido
Areef yayi jin yanda sunan ya burgeshi. Malam yace
Alhamdulillahi wannan suna yayi dadi, AMINTATTAR
ALLAH kenan, to Allah yasa albarka acikin sunanki da
rayuwarki gaba daya. Kowa yace amin.
Waziri yace Malam inaganin zaka kara dawowa nan kusa
domin kadaura mana aure amasarautar nan, Murmushi
yayi yace lallai kam nima naga alama, dan tunkafin inzo
nasan da wannan labari, zuwana kuma yakara tabbatar
mani da hakan, dan Yarima yafi kowa kaffa kaffa da
diyar tawa, yanda kasan ance za'a kwace mashi ita.
Dariya suka saka gaba daya. Anan Baban Fulani shima
yayima Malam godiya sannan yakara yima Baba na
Darazo godiya.
Sarki Qaseem yace ai basu kadai ba, gawasu masoyan
nan agefe, dan haka tare za,a yi muhuta gaba daya. Kowa
dariya yayi. Malam yace to Allah ya nuna mana, amma
banaso asaka danisa, gara tazauna da mijinta, hakan ze
sa tasamu kwanciyar hankali. Anan aka rufe taro da
addu'a.
Kwana 3 aka dauka a masarauatar ana zaman jimami,
jikin Sarki Hasheem yayi sauki, sede haryanzu yana cikin
damuwa, kuma befara takawa da kanshi ba, dole seda
sanda, hakan yasa Sarki Qaseem da Waziri suka nemi
shawarar likita, shine yace idan ze yarda afitar dashi
waje.
Zasuyi mashi wani gashi, insha Allah ze dawo dede.
Bayan sun sameshi da maganar babu musu ya amince,
hakan yasa Waziri yace dashi za,a tafi. Sarki Hasheem
yace amma da Fulani zamu tafi ko? Murmushi sukayi
sukace ai badamuwa.
Lokacin da Sarki Qaseem yasamu Gimbiya Suhailat da
maganar cewa tayi suyi hakuri abarta akwai abinda
zatayi mata kafin sudawo angma. Yace a,a kinsan Yaya
baze yarda ba, kawai kibashi matar shi. Da to kawai ta
amsa mashi.
Amma azuciyarta tayi alkawarin bazata bari sutafi tare
ba, dan Fulani tana bukatar gyara sosai, shekaru 18
acikin hauka, kuma har haihuwa tayi. Dole ma tayi duk
yanda zatayi tahana atafi da ita.
Zaune suke afalo ana tashirin tafiyarsu, dan anjima
kadan zasu tafi,Fulani datake zaune agefen Sarki, tayi
saurin rike cikinta. Dasauri Gimbiya Suhailat tace lafiya
de Fulani?
Nana hankalin kowa yadawo kanta, Sarki Hasheem yace
adauketa muje asibiti mana. Gimbiya tace a,a inajin
baciwon asibiti bane,birin ciwonmu ne, na mata bari
muje cikin gida. Sarki Hasheem yace ina ganin za,a daga
tafiyar nan kafin tasamu lafiya.
Waziri yace a'a Memartaba, kada wannan yadameka,
tafiyarmu bazata wuce kwana 10 ba, inaganin kayi
hakuri tunda har angama komai kuma agobe za,a fara
gashin nan, kaga likitan yace akwai inda zeje, saboda
kaine yadaga tafiyar.
Kayi hakuri muje domin neman lafiyarka, nasan ayanzu
kanajin babu dadi kowa yana hidimarshi amma kana
zaune, guri guda, idan zajayi tafi seda sanda. Sarki
Qaseem ya matso kusa dashi yace dan Allah Yaya kada
kaki yarda ayi tafiyar nan, wlh Allah kadai yasan halin
damuke ciki akan rashin lafiyarka. Shiru yayi, hawaye
suna zuba daga idonshi.
Hannunshi Sarki Hasheem yakama shima idanunshi
sunyi ja, yace karka damu dan uwa na, acigaba da
shiri,Allah yasa ayi asa'a. Murmushin jindadi yayi
yarungume Yayanshi yace nagode Yaya. Sarki Hasheem
yakalli Beauty yace zo Amatullah mu gaisa mana.
Murmushi tayi ta tashi tanufi gurinshi tana zuwa tazauna
kusa dashi ta dora kanta saman kafarshi. Hannu yasa
yashafi fuskarta tace yauwa Amatullahi, Allah yabaki
lafiya kema kirika magana kamar kowa. Areef yace
Amma Baffa tayi magana so daya a asibiti.
Waziri yace insha Allahu wata rana zata yi magana, dan
likita yace matsalarta ne sauki ce, kuma base an kaita
asibiti ba, zata iya yin magana akowane,lokaci, yace idan
har taga wani abu daya tsora tata bakinta ze iya budewa.
Sarki Hasheem yace insha Allahu zata samu lafiya. Kuma
da mun dawo za,ayi maganar bikunku, Yarima seka
fadama abokinka dan ahada tare, ko Ayman? Murmushi
tayi ta tashi tafita.
Lokaci yana cika suka fito domin tafiya, seda aka kai
Sarki Hasheem gurin Fulani sukayi Sallama, sannan suka
nufi air pot. Suna zuwa aka fara kiran sunaye, haka suka
rungume juna shida Kaninshi, har kua seda sukayi. Yana
kallonsu har jirginsu yadaga sannan suka dawo.
Dariya Gimbiya Suhailat da jakadiya Safeeya sukayi,
Gimbiya tace ai nadauka Fulani bazakiyi yanda nace
maki, ba, dan kina tausayin mijinki. Fulani tayi
murmushi tace, duk yanda nake tausayinshi ai gara
inzauna indawo da martabata ni kaina wani lokacin kyan
kyamin kaina nakeji, kiduba fa kigani duk wata kazanta
damuke fitarwa haka zanyita ingama babu wani wanka.
Kai gaskiya mutanen nan sun cutar dani.
Jakadiya Safeeya tace wai ahaka ma kinsamu bakar da
ba, kuma kinga acikin kwana goma zaki samu gyara
sosai, wanda Sarki zeyi farin ciki da haka. Gimbiya tace ai
wannan gyaran na musamman zakisha, suma Yarana
nasu nadabanne.
Kallon Jakadiya Safeeya tayi tace akwai wani abu danake
so inhada, amma anjima idan hubby yadawo zamuyi
maganar, kema yakamata, ai ko? Jakadiya tace bangane
ba? Murmushi Gimbiya tayi tace a'a bakomai dama gani
nayi Waziri tunda matarshi ta mutu be kara aure ba,
kuma dama diyarshi daya sunyi mata aure. Shine naga
kema mijinki yarasu ai.
Dariya Fulani tayi tace kai amma wlh Aunty kin iya
hangen nesa. Tashi Jakadiya tayi tana murmushi,
Gimbiya tace, ina kuma zakije? Fita tayi bata cemata
komai ba. Gimbiya tace Allah da gaske nakeyi, kuma
insha Allahu wannan abu seya tabbata, zansa Hubby
yafadama Malam, kinga se ayi tare dana su Amatu.
Fulani tace Allah yasa.
Zaune suke acikin lambu, beauty Amatullah tana zaune
agefen Areef yana koyamata karatu, su Haisam suma
suna gefe guda suna firarsu. Areef ya kalli Haisam yace
wai abokina ya kukayi da Dady akan maganar Ayman?.
Murmushi yayi yace yafi kowa mafarin ciki shida Momy
dasukaji maganar, yace idan Baffa yadawo zasuzo. Areef
yace ai gara azo a aurar damu kowama yahuta ko Beauty
na? Kai tadaga mashi tana murmshi. Haisam yace Beauty
bahaka zakice ba, a,a zakice.
Hararshi Areef yayi yace todan bukulu ai seka hanata,
kuma wlh wannan sunan yafita abakinka, tunda de
ansamata suna kawai ka kirata da Amatullahin ta.
Haisam yace bazan kiraba, ni nariga dana saba.
Murmushi Areef yayi yace shikenan, nina zanrika kuran
Ayman da Angel. Apple din dayake kusa da Haisam
yadauka ya jefeshi dashi, dasauri ya cabeshi yana dariya,
Haisam yace wlh baka isa ba. Areef yace tokaima kadena
fada mata beauty. Haisam yace nayarda, dannaga alama
nizakafi kwara.
Dariya suka saka Areef yace dade yafi maka, amma ni
inkirata. Beauty kaima haka, ai bazeyuba. Haisam yace
towai kai yamaganar fitarku waje bayan aure? Areef yace
wlh har yanzu banyi maganar dasu Abba ba, amma yau
zanje insamesu. Idan har sukaki zan hadasu da Malam.
Haisam yace insha Allah ma zasu amince, duk da nima
bazanso kamun nisa ba, amma saboda cigaban Amatu
kawai zan hakura, nima inaso inga tadawo kamar kowa.
Gimbiya Suhailat tana kwance ajikin Sarki Qaseem suna
fira, tace Hubby, dama wata shawara ce, nace bara
infada maka kafinsu Yaya su dawo se afada masu aji
mezasu ce. Kara yawota yayi yace fada inajinki. Anan
tafada mashi abinda takeso.
Murmushi yayi yace wlh kamar kinshiga zuciyata, na
dade ina wannan tunanin, kawai ciwon Yaya ne,
yahanani fada amma tabbas idan suka dawo zansamu
Waziri da Yaya da maganar. Wannan abu ne me kyau.
Kema Allah yabiyaki da kika kawo wannan shawarar.
Sallamar Areef ce ta katsesu, abakin kofa ya tsaya, dan
dama al'adarshi ce duk inda yaje baya shiga se anbashi
izini kida gidansu ne. Murmushi Sarki yayi yace Allah yayi
maka albarka Yarima, hakika ina farin ciki da irin
halayenka da kuma tarbiyarka, ace mutum yaje kasar
waje yayi karatu amma duk da haka tarbiyarshi bata
lalace ba, asalima karuwa tayi. Babu abinda zanma Alkah
se godiya, domin nasani shine ya tsare bawansa.
Bayan sun gyara zamansu ya amsa Sallamar yace shigo
Yarima, shigowa yayi yazauna kusa da Abbanshi tare da
dora kanshi saman kafarshi yace sannunku da hutawa
Abba. Shafa kanshi Gimbiya tayi tace yauwa sannu
Yarima. Sarki yace zanga ranar dazaka girma Areef, ace
haryanzu kana hawa cinya.
Dariya yayi yace ai babu rana Abba, yace akwai mana,
nan da wata daya kam ai zaka zama megida. Kafin kaima
kasamu naka dan, kaga saka barmashi ko. Gimbiya tace
ai anan zasu zauna ko? Abba yace emana, ai bama son
muyi nisa da juna, zamansu cikin masarautar nan zefi.
Tashi Areef yayi yana sosa kai yace Abba dama wata
alfarma nazo nema, yace fadi duk wata alfarmarka, ni
kuma zanyi maka. Anan yafada masu abinda yakeso.
Shiru sukayi, yace dan Allah Abba.
Sarki yace bawai naki bane, ina duba yanda Yaya zeji,
kasan yanada bukatar ganin Amatu akusa dashi, amma
se ace ana daura aure zaku tafi. Areef yace wlh Abba
koni dole ce zata sani yin nisa daku, kuma ina me
tabbatar maku shekara 3 zamuyi, niba burina beautytayi
zurfin karatu ba, kawai inaso tasamu karatu me kyau,
dan koda tayi karatun ni bazan barta taje wata University
ba, kawai tasamu karatu kodan sbd rayuwarta data
yaranta.
Gimbiya tace gaskiya kayi magana me kyau, kuma nima
nagoy bayanka son dazamu nuna mata kenan mubarta
tasamu ilimi me kyau, kuma tunda saudiya zakuje, nasan
zata samu ilimi me kyau, kaga daga kai har ita kunje kusa
da gida, kafin kudawo zaku zagaya dangi.
Sarki yace shikenan, idan Yaya yadawo zamuyi maganar
dashi. Areef yarungume Abbanshi yayi yana dariya.
Gimbiya tace ammafa zaku rika zuwa bawai zama zakuyi
harseta gama ba. Sarki yace dama ai baza,ayi haka ba.
Haka suka cigaba da shirye shirye, Amare suna shan
gyara, dan masu gyara na musamman daga meduguri
aka dauko, Fulani daki guda aka ware mata ita da ne
gyaranta, tunda tashiga bata fito ba, akoda yaushe suna
cikin gyara, sallah kadai da cin abinci suke tadasu.
Bakaramin kyau takarayi ba, tadawo tamakar wata
yarinya, komai nata yadawo kamar da. Beauty kuwa
masu gyaran har mamakin kyanta sukeyi, gashi dama
tunda aka fara gyaransu su Areef suka dena ganinsu, duk
ya gama shuga damuwa.
Ayaune, masarautar BUBAYERO tacika da mutane, anata
gyara da shirin tarbar Sarki Hasheem. Kowa kagani cikin
masarautar cikin farin ciki yake. Fulani tasha kwalliya
kamar meshirin zuwa zaben sarauniyar kyau, tayi kyau
harta gaji, haka suka kaita dakinta dayasha gyara har yafi
ranar da aka kaita kyau.
Motoci harma da mashina ne, suka je dauko Sarki. Ana
bude kofar jirgi mutane suka fara fitowa, sarki Qaseem
yazuba id kawai yaga ta yanda yayanshi zefito. Waziri
yafara hangowa, daga bayanshi ya hango Yayanshi cikin
shiga ta alfarma yayi matukar kyau, kamar bashi bane
yayi ciwo abaya ba.
Da kafafuwanshi 2 yarika saukowa daga jirgi, ai Sarki
Qaseem kasa hakura yayi ya karaso, cike da murna ya isa
gurinshi uka rungume juna. Kowa na gurin seda suka
burgeshi. Haka suka nufi gida cike da farin ciki.
Suna zuwa Sarki Qasee yajashi zuwa part dinshi, yace
Yaya kashiga kashirya kada kafito seda dare, Fulani tana
daki tana jiranka, nasan kagaji dayawa. Murmshi yayi
yace shikenan nagode, sena fito. Har falo yakaishi
sannan yafito fuskarshi dauke da annashuwa.
Tura kofar dakin Fulani yayi, lumshe ido yayi dan wani
da daddan kamshine ya bugar mashi hanci. Da sallama
yashiga, ai cak ya tsaya ganin Fulaninshi, da gudu tarugo
ta rungumeshi, hannuwanshi 2 yasa ya rungumeta, wani
irin farin ciki sukeji dukansu.
Sun dade ahaka kafi tajashi zuwa cikin dakin, riketa yayi
yana kallonta, yace anya ba masanye akamun da
Fulanita dana sani ba? Murmushi tayi tace kila, jawota
yayi, yace gaskiya nagodema Allah dayasa bantafi dake
ba, gashinan an maidomun da mata kamar yar shekara
18. Murmushi tayi tacire jikinta daga nashi tana fadin
sannu da hanya, muje kayi wanka kaci abinci.
Murmushi yayi yace nikam bazan iya cin abinci ba,
tunda naganki, dariya tayi tace a,a muje de. Haka tajashi
zuwa bandaki. Bayan yafito ya shirya takawo mashi
abinci, da kanta tarika bashi yana jingine jikinta, kamar
karamin yaro, yahanata sakat. Da haka tagama bashi
abinci, yaje yayi brush yadawo yana fadin taho kimun
tausa, bacci zanyi.
Murmushi tayi tanufo gurinshi, yace amma kicire
wannan kayan zasu damenim tace amma naga bacci
zakayi, ina ruwan kayana da kai, kanne mata ido yayi
yace e sonake musami AMINULLAH. Dariya tayi yajawota
shima yana dariya.
Koda Sarki Qaseem sukaje fada da dare, Sarki Hasheem
befito ba, ganin haka Waziri yace abari se gobe, azauna,
akwai gajiya atare dashi, Sarki yace a,a amarci kawai
yakesha. Waziri yace kaima ai sekaje kasha naka.
Murmushi Sarki yayi yace kaima nan da wani lokaci kaza
fara shan naka. Dariya Waziri yayi yace seda safe, Sarki
yace to Allah yakaimu.
Areef ze zaune afalon Jakadiya kamar zeyi kuka ya kalleta
yace haba Aunty dan Allah sokukeyi inshiga wani hali,
kinfi kowa sanin damuwar danake ciki, shikenan ace
kullum so daya zanga beauty gaskiya bazan iya ba.
Ina gyaran nan danni akeyishi? To nide abarmun ita haka
banaso. Dariya Jakadiya tayi tace yi hakuri bara inturo
maka ita karkamun kuka, fita tayi sega beauty tafito.
Tsayawa yayi yana kallonta, tana zuwa tazauna kusa
dashi tana murmushi, yakamo hannunta yace haba
beauty nan shikenan sekirika guduna.
Kema bakison ganina ko? Girgiza mashi kai tayi, yace
yauwa kokefa beauty na, hannunta yasaki, yace jeki
dauko mani abinci yunwa nakeji, tashi tayi tadauko
mashi, akasa tadameshi, nan tazauna tazuba mashi.
Atare suka fara cin abinci, yana bata tana bashi, har suka
gama sannan suka zauna yana mata fira.
Washe gari se bayan azahar sannan aka taru afada, atare
Sarki Hasheem da Fulani suka fito, daka gansu kasan
suna cikin farin ciki. Bayan angama gaisawa, aka bude
taro da addu'a.
Sarki Qaseem yace Alhamdulillahi, munama Allah godiya
daya kawomu wannan rana Yaya yasamu lafiya, komai
na masarautar nan yazama dede, ina rokon Allah daya
kara tsaremu damu da yaranmu baki daya. Dan haka
inaganin zanmika ma Yaya kujerarshi, dama amatsayin
rikon kwarya na amsa.
Sarki Hasheem yayi murmushi yace, a,a ai kuma nida
mulki har abada, wanda nayi abaya ya isa, kaine zaka
cigaba da mulkarmu, kafin Yarima yakawo karfi se
abashi, amma wannan maganar ma kabarta.
Waziri yace wannan magana haka take, munriga da
munyanke zaka cigaba da zama Sarkin Gombe, har Allah
yakaimu lokacin dazaka sauka. Allah yatayaka riko.
Waziri yace magana ta 2 akan maganar bikinsu Yarima
ne, munsami labarin mahaifin Haisam zezo gobe da
jama'arshi neman auren Ayman, dan haka nan da sati 2
za'ayi bikinsu in Allah yakaimu.
Kallon Baffan beauty yayi yace akwai wata magana da
Yarima yazo mana da ita, jiya Sarki Qaseem yake
fadamun. Anan yafada masu alfarmar da Yarima yake
nema. Shiru Baffan beauty yayi bece komai ba. Can
yadago kai yace ai hakanma yana da kyau, Se ayi magana
acan kasar asama mashi aikinyi kafin itama tagama
karatun nata. Allah yasa aje asa'a akuma samu abinda
akeso.
Sarki Qaseem yace kuma akwai dayar maganar, aure
danakeso inyi, dama akan Waziri ne da Jakadiya Safeeya,
ina ganin insha Allah nan da sati 2 tare danasu Yarima
za,a daura. Dago kai Waziri yayi yasaki baki yana kallon
Sarki Qaseem. Baffan beauty yayi murmushi yace lallai
kamar kashiga zuciyata.
Dan Allah Waziri kada kace komai, kawai kayi fatan
alkhairi, kasan baza zaba maka abinda zakayi dana sani
ba. Sunkuyar da kai Waziri yayi yana murmushi. Sarki
Qaseem yace ai ya amince, Allah yakaimu musha biki.
Shirye shirye ya kankama agidan su Yarima, iyayen
Haisam sunzo anyi magana, kuma har can misra an fada
masu, kuma sunce zasuzo. Baba Fulani ma yakira yan
uwanshi yafada masu, wasu daga cikinsu sunce zasuzo.
Duk wani shirin tafiyarsu Areef angamashi, anyi masu
visa, da takardar shedar zama akasar, kuma an sama ma
Areef aiki acan har gudan dazasu zauna ansamu. Dayake
abun namasu sarauta ne. Babu wani bidi'a dazasuyi
abikin, hakan yasa aka kira me wa'azi yazo yayi masu.
Ayau ne dubban jama,a suka halarci daurin auren
mutane, 3 nagidan sarautar BUBAYERO. Daurin aure ne
daya tara mutane dayawa, daga garuruwa daban daban,
harma daga kashashe. Bayan daurin aure akayi babbar
walima, anci ansha, kowa seda ya yaba da irin auren
wannan Masarauta. Gashide auren yaransu, abin sonsu
akeyi amma kuma babu wata bidi'a da akayi. Mutane
dayawa abin ya burgesu.
Adaren ne kafin azo daukar Ayman, Sarki yatarasu duka
domin ayi masu nasiha. Nasiha meratsa zuciya sarki yayi
masu, bayan yagama Baffan beauty ma yayi masu. Yace
Amatullahi, kiyi hakuri kinga gobe da safe zaku tafi, babu
ruwanki da kowa, bakisan kowa ba se mijinki.
Kada kiyarda wasu suzo maki dawani abu, yanda baki
magana, karkiyarda kibiyema kowa, kuma kimaida
hankali akan karatunki, inhar kinaso kidawo kusa damu,
amma idan bakiyi kokari ba, acan zakuyi tazama. Ko
kinaso kuzauna acan? Kai ta girgiza yace yauwa, Allah
yayi maku albarka. Kema Ayman, kindega abinda yafaru
azuwanki gidan nan, damma kinci sa,a gidanki daban ne,
amma duk da haka bana son kisaki jiki da mutane,
dangin mijinki kirikesu da hannu 2, kowa kizauna dashi
da zuciya daya, Allah zetemakeki akan makiyanki. Allah
yabaku zaman lfy. Anan Waziri shima yayi masu tashi
nasihar, se yan uwan Ayman da dangin Fulani dasukazo,
kowa seda yayi masu nasiha.
Se kuka sukeyi, bayan angama masu Sarki Qaseem yace
kuje, yanzu za,azo adaukeki. Bayan suntafi, Sarki yace
Waziri kaima yanzu zamu kawo maka taka amaryar.
Dariya suka saka, gaba daya. Da misalin karfe 9 aka dauki
Ayman, wanda Areef shima yadauki beautynshi amota
suka tafi rakasu.
Bayan kowa yatafi yarage daga amarya da ango se su
Areef. Haisam yace abokina yakamata muje inrakaku.
Duka Areef yakai mashi yace wlh kai dan iska ne, wlh se
ince ba inda zani, Haisam yace da kyau, ai akwai wani
dakin, indarabon asamu dan gidanmu kuma shikenan.
Areef yace a,a ni baruwana kaine dan iska nikam nafison
dan saudiya. Haisam ya kalleshi yace wlh abokina
banason tafiyar nan taku, shiyasama bazan je rakiya ba,
amma zamu zo dan acan zamuyi honey moon dinmu,
Areef yace bakomai nasan sanda zamu tafi ma baku
tashi daga baccin gajiya ba.
Dariya Haisam yayi yace ammade ai munyi sallah ko,
Areef yace tobara mutafi nasan beauty na tagaji gara
muje ta huta, mike wa sukayi, Haisam ya rungume shi
idanunshi har yakawo ruwa. Shima Areef seda yazubar
da kwalla, sun dade ahaka, kafin suka saki juna.
Har bakin mota suka rakasu, Ayman da Beauty se kuka
sukeyi,da kyar Areef yacire beauty daga jikin Ayman.
Ayman tace Yaya yanzu shikenan gobe zaku tafi? Kallonta
yayi zeyi magana kuka yataho mashi, kawai jan beauty
yayi suka shiga mota.
Amota yayi ta lallashin beauty, da kyar tayi shiru, haka
suka nufi gida shima duk bayajin dadin rabuwarsu da
Haisam dan bakaramin sabo sukayi ba. Beda wani aboki
se shi, dashi kadai yasaba. Har dakinta na bangaren
Jakadiya Safeeya ya kaita sannan yatafi.
Kwallan data zubo mata ta goge, takalli Jakadiya Karima
tace yanzu kalli yanda duniya tajuya mani baya, kamar
ni da mulki na da matsayina amma kalli yanda kowa
yamanta ni acikin gidan nan, biki akayi ayau amma
banida damar fita inje gurin. Jakadiya Karima tace,
Zakiyya kenan, idan zakiyi hakuri ki aje wata sarauta ki
rungumi kaddara kiyi.
Har garama ke, zaki iya kirga kwanakin ki,nifa? Sede
afitar da gawata. Saboda haka kinganni nan namaida
gurin nan kamar gidana, idan harzaki rika yimani
maganar wata sarautarku, ina me tabbatar maki zanbar
maki dakin nan, kuma bazaki kara ganina ba, dan kinsan
babu wanda zezo yazauna tare dake. Shiru Zakiyya tayi
tana jinyanda Jakadiya take fada mata maganganu.
Murmushin takaici tayi tace duniya kenan.
Washe gari tunda safe aka fito rakiyarsu Areef, idanunshi
sunyi ja sosai, dan tunjiya yakema iyayenshi kuka,
Abbanshi har cewa yayi kode afasa tafiyar ne, yace a,a
Abba, nasan damun tafi komai ze wuce.
Haka suka shiga mota aka nufi air pot dasu, ko acan da
kyar aka ciresu daga jikin iyayensu, suma seda sukayi
hawaye, suna kallo har jirginsu yadaga, sannan suka juya
zuwa gida. Acikin jirgi kam lallashin beauty Areef yayi
tayi, mutane se kallonsu sukeyi, dan sunga suna kama
sosai, gashi dama beauty da kyar tashiga jirgin, shiyasa
tashige jikin Areef, ko ido takasa budewa. Shiyasa kukan
nata yazama 2.
Suna sauka dama mota tana jiransu,daukarsu tayi suka
nufi gidansu, gida ne, mekyau, yaji komai, kayansu aka
shigo masu dasu. Wanka Areef yace suje suyi, rufe fuska
beauty tayi tana murmushi. Cak yadauketa bema tsaya
jiran yardarta ba. Haka sukayi wanka suka fito, dakanshi
yashiryata aka kawo masu abinci.
Da dare ma kawo masu abinci akayi, bayan sungama
yadauketa suka nufi toilet, wanka sukayi tare da alwala,
sallah sukayi sannan yajawota suka nufi gado.
Washe gari da safe dakanshi yashiga kitchen yahada
masu break, bayan sungama yajata zuwa daki suka
koma bacci, seda azahar suka tashi, wanka sukayi sukaci
abinci suka fito falo, takarda da biro yadauko yajawota
suka zauna falo, yace beauty yau labari zamuyi fa.
Haka yayita rubuta mata yana bata tana rubuta mashi
abinda tasani, idan ta manta ya tuna mata.
Haka suka cigaba da rayuwarsu acikin gidan gwanin ban
sha,awa, akullum suna yin waya da yan gida, satinsu
guda sannan suka fara fita, aranar yakaita makaranta shi
kuma yawuce gurin aiki, seda yayita lallashinta kafin ta
hakura, yace dasun tashi zezo yadauketa.
Rayuwar Areef da Amatullah gwanin ban sha,awa, suna
matukar son junansu, akullum tare suke fita ya kaita
makaranta, shikuma ya wuce aiki, se da yamma suke
tashi, dayake makarantar hade take da islamiya, shiyasa
sesun kai yamma, kuma Beauty tana gane karatun sosai,
babu ruwanta da kowa, karatunta tasa gaba.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, suna da wata 3 dayin
aure, ciki yafito ajikin beauty, bayan sunje asibiti akayi
test aka gano ciki dan wata 2, bakaramin murna Areef
yayi ba, haka yakira gida ya fada masu, suma sunyi
murna sosai. Tunda suka koma gida yake riritata,
damma cikin beda laulayi,
Haka yakira Haisam yayi mashi albishir, shima alokacin
yake fada mashi Ayman ma tana dauke da ciki itama
wata 2, Areef yace amma naji dadi, zamu fara cika ma su
Abba gida da jikoki. Haisam yace idan muna da rai
muma semu hada zumunci. Areef yace Allah ya kaimu.
Amma wai yaushe zaku zo, kasanfa muna son zuwa
ziyara gurin yan uwa, gurin dangin su beauty, danasu
Momy. Haisam insha Allah zamu shirya muzo. Yace to
Allah yakaimu
Baffan beauty ya kalli Fulani, datake kwance ajikinshi,
dawowarsu daga asibiti kenan, fuskarshi dauke da
murmushi, yace babu abinda zance maki Fulanita, sede
godiya, tabbas ke haske ce acikin rayuwata.
Ashe inada rabon ganin yarana, aduniya. Ina rokon Allah
ya saukeki lfy. Murmushi tayi tace amin. Yace ina ganin
Gimbiya Suhailat zata rigaki haihuwa ko? Kai tadaga
mashi, tace wlh ni kunya nakeji, yace kunyar me kuma?.
Tace haba dan Allah, yanzu kana ganin Amatu ciki gareta,
Ayman ma haka, ga Aunty, yanzu kuma ace nima haka,
kuma suk kusan tare zamu haihu. Dariya yayi yace kin
manta dayar ai, tace wa kuma? Yace matar Waziri mana.
Tashi tayi fuskarta dauke da mamaki, tace da gske Aunty
Safeeya tana da ciki? Yace da gske mana, dazu yake
fadamun, nace kinga ikon Allah ko? Tace gaskiya kam,
wama yayi zaton Aunty zata haihu, yanda ta dade bata
taba haihuwa ba.
Yace aishi Allah babu ruwanshi, yana yin abunshi aduk
sanda yaso,babu ruwanshi da tsufanka ko yarintarka.
Fatanmu Allah yasa mugama da duniya lfy. Tace amin.
Amma de ba gida su Yarima zasu dawo ba idan zata
haihu ko? Dariya yayi yace wai naga duk kinbi kin damu,
ina ruwanki dasu?.
Kinsande muna da inda zamu ajesu ko? Kuma zamu
sami masu kula dasu, dan haka ki kwantar da hankalinki.
Shiru tayi bata ce komai ba. Jawota yayi yace dazu
Yarima yake fadamun zasu je ziyarar yan uwa.
Murmushi tayi tace kagani ko,
Nibanje ba, ga jikarsu nan har zataje, yace karki damu
kema zakije, Allah yasaukeki lafiya. Tace Amin.
Zaman Haisam da Ayman, zama ne na so da kauna, yana
kula da ita sosai, itama haka, kuma tana daraja yan
uwanshi. Acikin satin ne, yagama shirya masu visa suka
daga zuwa saudiya domin zumunci.
Bakaramin dadi su Areef sukaji ba, da ziyarar dasuka
kaimasu, kuma agidansu suka sauka, ko abinci basa
tsaywa girkawa, sede sufita suci awaje, dagacan suwuce
gurin shakatawa. Dayake Beauty suna hutu.
Sun zagaya gurare dayawa, sannan suka shirya dukansu
suka nufi misra, yan uwansu bakaramin dadi sukaji ba.
Kwanansu 3 sannan suka wuce garinsu Fulani, suma sun
tarbesu sosai, sun sha gata, kwanan su 3 acan ma,
sannan suka dawo gida.
Kwana 2 su Haisam suka kara sukace zasu wuce, har
kuka sukayi dasuka rakasu, da kyar Areef yacire beauty
daga jikin Ayman, haka jirginsu yadaga suka dawo gida
yana lallashi.
Bayan wasu watanni Gimbiya Suhailat ta haifi diya mace,
ansha hidima sosai, sede su Areef basu jeba, dan beauty
tana Exams. Yarinya taci sunan mahaifiyarsu Sarki
Qaseem Fatima, ana kiranta da NOOR.
Bayan wata 2 da haihuwarta Fulani ma tahaihu yan biyu,
mace da namiji,gaba daya gidan seda kowa yasan anyi
haihuwar yan 2, Sarki Qaseem bakaramin dadi yaji ba,
ganin Yayanshi yana samun haihuwa yanzu. Alokacin
beauty tagama Exams dinta, shima yadauki hutun
shekara.
Hakan yasa suka nufo gida, bakaramin farin ciki
mutanen gidan sukayi ba, apart dinsu da aka gina masu
anan suka sauka, wata dattijuwa aka kawo ma beauty
wadda zata rika temaka mata, ana cemata Ladingo.
Ranar suna akasama namijin sunan Mahaifinsu Sarki,
macen Kuma sunan Mahaifiyar Fulani. Ana kiransu da
AMEER DA AMEERA. Anyi shagali sosai, su beauty da
Ayman da Jakadiya Safeeya sunata fama da tsohon ciki.
Bayan suna da sati daya Ayman da Jakadiya Safeeya suka
haihu, Ayman ta haifi Namiji itama Jakadiya Namiji.
Beauty kuwa kuka tasaka dataji ance Ayman ta haihu.
Areef yatambayeta lafiya awayarta ta rubuta mashi ita fa
tsoro takeji, dariya yayi uajawota yace ki kwantar da
hankalinki, babu wata wahala kinji ko? Kai tadaga mashi
tana murmushi.
Adaren itama ta tashi da nakuda, dama beauty ga tsoro,
gaba daya taki sakin jikinta se kuka takeyi, tun Ladingo
tana kokari harta gaji, Areef kuwa kamar shine yake
nakudar, kallonshi Ladingo tayi tace agaskiya Yarima ina
ganin sede fa akaita asibiti, idan bahaka ba, za, iya rasa
abinda ke cikinta.
Cikin rudewa yace to kihada kayan bara infada ma su
Momy. Cikin lokaci kankani aka nufi asibiti da ita,
hankalin kowa yatashi ganin yanda beauty tafita
hayyacinta. Suna zuwa aka nufi labour room da ita.
Kowa yakasa zama, Areef kuwa kuka yasaka, Haisam ne
yajashi suka fita waje yana lallashinshi.
Areef yace kasan Allah daga wannan haihuwar beauty
tagama haihuwa. Dariya maganar tabama Haisam sede
ya dake ganin halin da akeciki. Haisam yace addu,a zaka
rika yimata, yace haba Haisam kalli fa yanda take shan
wahala, baiwar Allah wlh da ana karbar haihuwa dana
karbar mata. Amma anyi na farko anyi na karshe,
banason yaran dayan dazata haifa ya isa.
Haisam yace duk wannan ma bata taso ba, kaide muyi
Addu,a Allah yasauketa lfy. Areef yace amin. Amma.........
sunanshi yaji ankira cikin wata irin murya da Yaya Areef,,
cak ya tsaya da magana dazeyi, yajuya yana kallon inda
yaji muryar tafito. Ai dasauri yanufi cikin asibitin Haisam
yabi bayanshi.
Suna zuwa kusa da labour room din suka jiyo kukan
jariri, da gudu Areef yanufi dakin, cikin sauri Haisam ya
rikeshi, yana fadin maza basu shiga, kajira afito da ita.
Areef yana hawaye yace kasakeni, wlh duk da bansan
muryar beauty ba amma nasan ita ce ta kirani, kasakeni
inje inga beauty na.
Da kyar su Waziri suka hanashi shiga, Momynshi ta
matso tace haba Yarima kayi hakuri mana, kallifa yanda
ake kallonmu. Zonan kazauna kaji, yanzu za,a fito da ita.
Wani likita ne yafito fuskarshi dauke da murmushi
yanufo gurin. Sarki Qaseem ya tarbeshi yace yaya jikin
Amatullah?.
Likita yace Alhamdulillah tasauka lafiya, tasamu baby
girl, kuma duk suna cikin koshin lafiya. Sarki yace
Alhamdulillah. Likita yace yanzu za,a kaisu dakin hutu,
idan kungama kusameni office, akwai wani albishir din.
Godiya sukayi mashi, yawuce. Areef yariga kowa shiga
dakin da suke, kotakan jaririyar be biba, gurin
beautynshi yanufa.
Hannunta yakama yarike sosai yana sannu beautu na,
nine ko? Murmushi tayi mashi, yace sannu bazan karaba
kinji? Kamar daga sama yaji tace Yayana ga babynmu.
Surin dago kai yayi yana kallonta. Itama shi take kallo,
cikin farin ciki yanunta yama kasa magana, kai tadaga
mashi.
Ai yama manta da mutanen dakin kawai ya rungumeta
da karfi, harseda tayi dan kara. Momy tace lfiyarka
Yarima? Saurin sakinta yayi yajuyo yana sosa kai yace
wlh Momy beauty tayi magana.
Suma mamaki ne yakamsu, suka nufi gurinta. Murmushi
tayi tace Momy. Cike da farin ciki Momy ta matsa kusa
da ita tace da gaske ne, ashe? Ikon Allah, lallai Fulani
zatayi farin ciki. Allah mungode maka. Sarki yace Sannu
Amatullah, cike da kunya tace yauwa Abbah, yace bari
muje gurin likita mudawo.
Zaune suke a office din likita, bayan yagama rubutunshi
yacire glass dinshi yace albishir din dana ce maku kilama
idanunku sungane maku? Sarki yace tabbas yau munga
abin farin ciki, sede muyi ma Allah godiya. Likita yace
haka ne, dama nafada maku, akowane lokaci maganarta
zata iya budewa, sbd akwai irinsu, kasan akwai wani
zakaga kurma ne, bayaji baya magana amma sakamakon
wani tashin hankali bakinsu yana budewa.
To itama Allah yasota gashi ta dalilin haihuwa bakinta
yabude. Kuma jikinta babu wata matsala, zuwa anjima
idan tahuta zaku iya tafiya, ga magungunan dazatayi
amfani dasu anan. Allah yabada lafiya. Godiya sukayi
mashi suka fita.
Segurin karfe 11 na dare suka koma gida, gaba daya
murna tacika gidan, Ayman jitake kamar itama tadawo
gida, dan Haisam yace tazauna tunda hidima tayi masu
yawa, agidan. Kowa cewa yake yarinyar tana kamada
Areef, shiko bakinshi yaki rufuwa, yamaki fita daga
dakin, seda Momy tayi mashi da gaske sannan yafita.
Haka akayita shirin suna, Momy tace ma, Haisam
yamaido Ayman gidan ayi suna gaba daya,daga baya
sesu koma. Aranar suna bakaramin taro akayi ba, diyar
Beauty aka samata Khairat, dan Areef da kanshi yace
babu sunan wanda zesa, shi khairat yajeso.
Yaron Ayman shima Haisam be tsaya saka sunan kowa
ba,yasa mashi Fahat. Waziri kuwa sunan Baffan beauty
yasaka ma yaronshi wato Hasheem, ana kiranshi da
Karami. Bakaramin dadi Baffan beauty yaji ba da irin
karar da waziri yamashi ba. Sarki Qaseem shine yasayi
komai na jariri harda ragunan suna.
Gaba daya masu laifin gidan aka fiddo haka aka raba
masu aiki, kowa danashi, Zakiyya abangaren masu abinci
aka kaita, tanayi tana kuka, ahaka suka gama, aka
sallamesu kowa aka bata nata.
Bayan kwana biyu mahaifiyar Zakiyyah ta kawo mata
ziyara, sunsha kuka sosai, ayanayin data ganta, kallonta
tayi tace Zakiyyah kinga irin abinda nake fada maki ko?
Yanzu ina sarautarki da mulkinki gashi nan kinkare a
gidan kurkutu, acikin talakawa marasa galihu. Cikin kuka
tace wlh Umma nayi dana sanin shiga wannan bakar
rayuwar dana shiga, kuma insha Allahu na dauki darasi.
Umman tace bakomai ai kin kusa fita kema kidawo gida.
Allah yayi maki sauyi da miji nagari. Ta dade kafin ta tafi,
takawo mata abubuwa dayawa. Zakiyyah se kuka takeyi.
Seda suka sami wata 2 kafin sukayi shirin tafiya, visa
Sarki yasa akayima Ladingo yace sutafi da ita seta rika
temaka mata. Haka beauty tacigaba dazuwa makaranta
tare suke tafiya da Ladingo, idan zasu shiga aji seta
barmata Khairat. Yanzu karatun yana mata sauki sosai,
dan har larabci tanaji tana maidawa.
After 2 years. Beauty ce tafito hannunta rike da takardu
tana ta farin ciki tanufo gurin Areef da khairat dasuke
tsaye jikin mota suna jiranta. Khairat tayi wayo sosai,
sede haryanzu ba,ayi mata kanwa ko kani ba. Tana zuwa
tafada jikinshi tana murna. Kara rungumeta yayi yace
congratulation my beauty na. Allah yanufa yau kingama
karatunki.
Khairat tace Dady nima kadaukeni, dariya suka saka yace
yi hakuri yau ranar Mimie ce, janta yayi suka shiga mota
suka nufi gida. Party sosai suka shirya aranar, dan
beauty hada qur'ani tasauke, gashi aharkar boko yanzu
sede takoyama wani.
Bayan kwana 2 suka fara shirye shiryen komawa gida
dama tuni yagama hada komai na aje aikinshi. Bayan
suje sunyi tsaraba washe gari suka dira a nigeria. Kowa
yayi farin ciki da dawowarsu. Haisam kamar ze zuba
ruwa akasa dan farin ciki. Beauty ta kalli Ayman wadda
cikinta har yafito kadan tana dariya tace Aunty yanaga
haka?
Hararta tayi tace kema zakiyi ne ai, haka suka nufi gida.
Babbar tarba, kowa yana cikin farin ciki.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya acikin masarautar,
Areef yakoma aikinshi, suna zuwa cikin wanciyar hakali
shida Haisam.
Iyalen Baban darazo sunajin dadin zaman gidan
sarautar, babu abinda basa samu ta ko ina.
Ayanzu cikin masarautar karatu akeyi sosai, dan Malam
ya aiko da malaman dasuke koya masu karatu, gaba
daya bayin dasuke gidan, harma da masu laifi, ana fidda
masu ranar karatu. Sosai suke jin dadin abinda ake
masu, gaba daya canji yasamu agarin Gombe, duk
wanda ya aikata wani laifi, ana yanke mashi hukunci
dede dashi.
Bayn shekara 2 beauty takara haihuwar da namiji, ana
kiranshi da Faisal, Ayman ma yaranta biyu, mace da
namiji, macen sunanta Labiba.
Ayau ne Zakiyya tafito daga kurkutu, rungume suke da
juna ita da Jakadiya Karima, kuka kawai sukeyi. Zakiyyah
tace Allah yada fuskokinmu, da ace ba,a gidan nan kike
ba, dazanyi maki alkawarin kawo maki ziyara.
Amma yanda zanbar gidan nan bana fatan inkara
dawowa. Kiyafemun abinda namaki nima nayafe maki.
Jakadiya tace nayafe maki. Allah yabaki miji nagari kema
kiyi aurenki. Da kyar suka rabu sunata kuka. Sallama
tayima sauran mutanen gurin tafito.
Mahaifyarta ce, tazo daukarta, haka suka nufi fada kallo
daya zakama Zakiyya kasan tafita hayyacinta, gaba daya
tayi baki ta rame. Azaune suka iske iyalan masarautar,
kowa fuskarshi cike da annuri.
Kallonta sukeyi cike da tausayi. Zama tayi bayan
sungama gaisawa, ta kalli Baffan beauty, suna hada ido
ykara daure fuska ya dauke idonshi daga kanta. Wasu
hawayene suka zubo mata, ahankali tace
Nasan banida bakin dazan rokeka gafara, amma duk da
haka bazan yi kasa aguiwa ba, dan girman Allah kaya
femun abubuwan dana yimak. Hakika naga rayuwa,
kuma hakan kadan ya isheni darasi. Banaso in mutu da
hakkinka kayafemun.
Kuka ne yaci karfinta. Shiru yayi kamar bazeyi magana
ba, can yace bakomai nidama nadade da yafe maki.
Allah ya shiryeki. Matsawa tayi kusa da Fulani, takamo
hannunta, tana kuka tace Fulani dan .... saurin rufe mata
baki tayi tana girgiza kai, hawaye suna fita daga idonta
tace nayafe maki. Allah ya yafe mana baki daya.
Haka tayita rokon mutanen falon tana kuka, har seda
tasa wasu kuka. Tashi sukayi auka masu sallama, har
bakin mota aka rakasu, amma banda Sarki Qaseem,
Waziri da Baffan beauty. Seda suka tafi sannan suka
dawo.
Bayan kwana biyu da komawar Zakiyyah gida tadan
murmure, mahaifinta yakira Ummanta da ita suna zuwa,
ya kalleta yace, zakiyya ina tayaki murnar fitowa daga
gidan yari. Basena kara tunatar dake rayuwa ba. Nasan
azaman da kikayi kin kin koyi darussa da dama. To
Alhamdulillahi dama arayuwa ana son idan mutum yayi
kuskure yayi kokarin gyarawa.
Shiyasa Allah da kanshi ya saukar da hukuncin daza,ayi
ma masu laifi, domin yazama darasi agaresu. Mutane
dayawa ta dalilin wannan hukuncin suke shiryuwa. Naji
dadi sosai danaga kin koyi darasi.
Abunda yasa nakiraki dama kinsan nace dakin fito zan
aurar dake,somin zamanki agidan nan babu abinda ze
amfana maki, se tarin bakin ciki. Dan haka nazaba maki
miji, amma idan beyi maki ba, kinada ikon canza wani
ba dole zanyi maki ba.
Goge hawayen idonta tayi tace, babu wani zabi
dazakamun inki binshi, nayarda da duk wanda
kazabamun. Murmushi yayi yace naji dadi, kuma
bakowa bane se Wazirina. Shikadai ne, nasan zerikemun
ke da amana kobayan rai na. Sede kinsan matanshi 3,
sekiyi hakuri da abokanan zamanki. Wannan asabar din
za.a daura auren akaiki dakinki. Allah yayi maki albarka.
Tashi tayi tana hawaye tanufi dakinta. Zama tayi tabuga
tagumi, tana fadin kaicona dana kasa yin hakuri agidana,
Allah yamun ni,ima amma na butulce mashi. Yanzu
gashinan zan shiga cikin matan da suka haifeni inyi kishi
dasu. Allah kabani ikon cin wannan jarabawa daka
jarabceni da ita.
Kwance take ajikinshi sunata fira, Areef yace beauty na,
yakamata fa ace akamar yanzu kinada yaran 3.
Murmushi tayi tace a,a 2 ma sun isa, kaidama kace daga
daya bazan kara ba. Dariya yayi yace nima bansan yanda
akai kika karaba my beauty.
Kallonshi tayi tace habibina yakamata ka canzamun suna
haka nan, kanaji rannan Khairat tacemun beauty ko,
dana tambayeta ce tace wai Auntynsu ce itama take
cemata beauty, data tambayeta meyasa tace mata haka
setace ai tana da kyau ne, shine yan ajinsu suke cemata
beauty, ahine Fahad yaketa kuka wai meyasa zasu rika
cemata haka shine zerika fada mata haka ai.
Se nace mata tomiyasa tacemun beauty? Kasan metace?
Wai nima inada kyau shiyasa kake cemun haka. Dariya
yayi yace ai bata fadi karya ba. Kuma nibazan iya dena
cemaki beauty ba, domin sunan yadace dake, alokacin
dabansan sunanki ba, kawai naga beauty ne kadai
yadace dake. Kuma Fahad da gaskiyarshi, nima bakiga
lokacin da Haisam yana cemaki beauty ba nahanashi.
Ai sunan dakake kiran masoyinka dashi, kai kadai
yakamata ka fadeshi. Murmushi tayi tace Allah yanuna
mana muga girman su fahad, Areef yace aini tunyanzu
nabama Fahad Khairat.
Dariya tayi tace duniya komai mewucewa. Allah ne yayi
zanrayu, gashi yanzu wai harnice da yara 2. Kamar
banice aka haifa AMAKABARTA BA. Daure fuska Areef
yayi yace banaso inkarajin wannan maganar abakinki,
kinaso au Khairat su san wannan labarin ne? Duk wani
da nagari bazeso yaji wannan bakin labarin ba, kuma ace
da mahaifiyarshi yafaru. Daga yau na kashe wannan
labarin na AMAKABARTA AKA HAIFEKI.
Murmushi tayi takama kunnanta tace afuwan Habibina,
insha Allahu daga yau bazan kara cewa AMAKABARTA
AKA HAIFENI ba. Jawota yayi ya rungumeta yana fadin
yauwa BEAUTY NAH!!!!!!
ALHAMDULILLAH!!!
Ina godiya ga Allah (s.w.a) daya kawoni karshen wannan
littafi nawa na AMAKABARTA AKA HAIFENI.
Abinda nafada da kuskure Allah ya yafemani, kuma
banyi wannan labari ba, dan cin zarafin masu aikata irin
wannan laifi. Nayishine domin yazama darasi ga mutane.
Ina mika sakon jinjina da godiya ga duk kanin
masoyana, Allah yabar zumunci da kauna, nagode da
irin kaunarku agareni.
Se kunjini alittafina nagaba me suna . DARAJAR
MUHALLI.
SADAUKARWA GA FAMILIES OF LATE RABI'U IDRIS
ZANGO
UR'S.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
A MAKABARTA AKA HAIFE NI
Na Nabila Rabi'u Zango
Ebook creat by Shuraih Usman
0 comments:
Post a Comment