Masarautar BUBAYERO, babbar masarauta ce mecike da
tarihi, ashekaru 18 dasuka wuce Sarki HASHEEM shine
Sarki amasarautar, yana da Kani wanda suke Uwa daya
Uba daya, su 2 iyayensu suka haifa, kafin iyayensu
surasu mahaifinsu shine Sarkin agarin.
Sakamakon hatsarin jirgi dasukayi shida mahaifiyarsu
wadda ita kadai ce matarshi kuma uwar yaranshi, shine
yayi sanadiyar mutuwarsu. Bayan kwana biyu da
rasuwarsu .Waziri wanda shine mahaifin wazirin sarki
Qaseem, shine yatara jama,a domin anada sabon sarki,
ananne aka zabi Hasheem yayan Qaseem aka nadashi
Sarkin masarautar Bubayero. Kuma shima Waziri
yasauka daga mukaminshi yamika ma babban danshi
wato Wazirin Sarki Qaseem.
Alokacin Sarki Hasheem yanada Matarshi 1 mesuna
Zakiyyah, diyace ga Sarkin Yobe, kuma abokine ga
mahaifin su Qaseem, shiyasa suka hadasu auren
zumunci, duk da Sarki Hasheem baya sonta haka yayi
biyayya ya aureta. Mahaifiyar Zakiyya takasance su 3 ne
agurin mijinsu Sarkin Yobe, amma dayake macece
wadda tasan kissa da iya tuggu hakan yasa tazamo yar
gaban goshi agurin mijinsu, baruwanta dabin boka ko
malam, tayarda da kanta.
Hakan yasa Zakiyyah tadauki duk wasu halaye nata.
Kuma da wannan halinne tajawo hankalin Sarki
Hasheem har yabata babban matsayi azuciyarshi.
Alokacin da aka nada mijinta Sarki bakaramin dadi taji
ba, sede babbar matsalar datake damunsu haryanzu
basu sami haihuwa ba, ko batan wata bata tabayiba.
Sede yanda takeyima Sarki yasa baya nuna damuwarshi
akan haka.
Jakadiya itace babbar baiwa datakema Sarki Hasheem
hidima tunkafin yazama sarki, ita kadai yabama amana
aduka bayin gidan, hakanne yasa lokacin dayahau
kujerar mulki yanadata Jakadiyarshi, ko Matarshi
batasan wasu sirrinkanshi ba kamar yanda Jakadiya
tasani, shiyasa kwata kwata basa shiri.
Bayan kaninshi yagama karatunshi akasar misrah
yadawo gida, alokacin Sarki yasa aka gyara mashi part
dinshi anan cikin gidan, kuma alokacin yazo mashi da
maganar matar dayakeso ya aura, Yayanshi bakaramin
dadi yaji ba, dan yana son kanin nashi kamar yanda
shima yakesonshi. Daya tambayeshi wacece yace mashi
diyar Sarkin Misra ce, atare sukayi karatu.
Babu bata lokaci yasa waziri yashirya masu tafi sukaje
neman auranta, koda sukaje sunsami tarba me kyau,
kuma anan take aka bama Qaseem auran Gimbiya
Suhailat, Bayan sundawo aka fara shirin biki.
Sati 1 akasa yanazuwa akaje akadaura aurensu, suka
taho Gombe, sede Sarki Hasheem yace base anbasu bayi
ba suna da isassun bayi, haka aka kawo amarya akasata
part dinta. Tunda suka hadu da Gimbiya Zakiyya taji ta
tsaneta, hakan yasa bata sakan mata fuska, kowa yanaji
da kanshi, ita Zakiyyah tana ganin ita diyar Sarki ce,
kuma matar Sarki, hakan yasa mulkin yayi mata yawa.
Ita kuma Suhailat tana ganin masarautarsu tafi tasu
Zakiyyah.
Bayan kwana 2 Sarki yasa Jakadiya tadebi bayi masu
yawa takaima Gimbiya Suhailat tazabi wanda takeso,
bayan tazaba Jakadiya tace tazabi amintattar baiwa
acikinsu, wani kallo tamata tace aini bana zabar
amintattiyar baiwa alokaci guda, dan haka ki kama
gabanki idan ina bukatar hakan basekin fadamun ba.
Jakadiya taji zafin maganar haka tajuya tawuce ranta
abace, sede dayake ta iya duniyanci bata nuna mata
afuska ba. Tsaki Gimbya taja, dan ita duk wanda befito
daga gidan sarauta ba gani take beda wani matsayi,
shiyasa ra'ayinsu da mijinta yazo daya, dan shima
sarauta tashiga jikinshi dayawa yana bata muhimmanci.
Sarki Hasheem yakasance mutum ne mesaukin kai
sosai, sede shima yana daraja sarautarsu sosai, kuma
baya son kai acikin masarautarshi, duk wanda ya aikata
laifi ana yanke mashi hukunci dede dashi.
Dalilin aurenshi da matarshi ta 2 kuwa yasamo asaline,
wata rana yafita rangadi shida Waziri da Kaninshi da
fadawa, sunzo wajen gari nesa da cikin gari, se suka
hadu dawasu bayin Allah agefen hanya uwa da diyarta,
yarinyar bazata wuce shekaru 17 ba, tana zaune kusa da
uwar tana ta kuka. Tsayawa sarki yasa akayi yasa aka
kirawosu, sede yarinyarce kawai tazo dan matar tana
cikin halin rashin lafiya bazata iya tashi ba. Tanazuwa
tafadi kasa, Waziri yatambayeta meyasa suke zaune anan
haka?.
Tana kuka bata basu amsa ba, Qaseem ya daka mata
tsawa yace waike ba magana ake makiba kin tsaida
mutane, Kallonshi Sarki yayi dan yasan abinda
kaninnashi ya tsana kenan, murmushi yayi yamaida
kallonshi kan yarinyar. Ihun matar dasukajine yasa babu
shiri Sarki da Waziri da sauran fadawa suka sauka daga
dokinsu suka nufi gurinta, yarinyar tarigasu zuwa
gurinta.
Jinine yake fita daga hancinta da bakinta, haka tarike
hannun yarta hawaye suna fita daga idonta, akusa da ita
Sarki ya tsugunna, fuskarshi cike da damuwa, yayi bakin
cikin dabasu fito da mota ba, kallon Waziri yayi yace
yazamuyi da ita, yakamata akaita asibiti. Hannun matar
yaji takamo babbar rigarshi, dasauri fadawa suka matso
dansu cire, amma yadakatar dasu. Kara dukawa yayi
yace baiwar Allah kibari mukaiki asibiti kina zubar da
jini.
Kai tashiga girgizawa, ahankali tafara magana, babu
inda zanje dannasan rayuwata tazo karshe, sede ina
neman wata alfarma agurinka. Sarki yace inajinki,
kadubi girman Allah, kamar yanda Allah yadauka kaka,
yafifitaka sama da sauran bayinshi badan yafisonka ba,
nasan matsayinka ya girmi alfarmar dazan fada maka,
sede inason kayi jahadi domin ka ceci marainiyar Allah
daga fadawa wata rayuwa.
Sarki yace inajinki, kifadi koma menene nikuma namaki
alkawarin zanzamo mecika makishi. Waziri, Qaseem
sukayi saurin kallon Sarki jin abinda yafada batare
dayasan me matar zata fada ba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 35⚜40
Zaune suke a falon Malam Bello na Darazo, Sarki ne, se
Qaseem da Waziri. Malam Bello babban malami ne,
kuma attajiri, duk da yamanyanta amma sbd ilimin
dayake dashi idan kaganshi zaka dauka shekarunsa basu
kai nashi ba. Shine babban malamin garin Darazo
malamin sosai, yana temakon mutane dayawa agarinsu,
mutanen garin suna matukar sonshi da girmamashi.
Hakan yasa yagina katon gida me bangarori dayawa, ko
yaranshi maza 2 dasukayi aure acikin gidan suke zaune
da matansu, da yaransu, dama kuma beda yara dayawa
yaranshi 4, maza 3 mace 1, itama tayi aure acikin garin
bauchi. Matarshi daya uwar yaranshi, se kanwarshi
kuma autar gidansu, tunda mijinta yarasu bata kara aure
ba, dama kuma bata taba haihuwa ba, hakan yasa tace
bazata kara aure ba, itama ta manyanta akalla zatayi
shekara 35.
Mutane dayawa idan sukazo garin basuda masauki yana
basu guri acikin gidanshi, ko idan ya musuluntar da
wasu yana basu gurin zama, yana da dalibai dayawa
dayake karantarwa. Haka kuma baya aiki da aljanu, sede
yana fitar dasu kuma suma sunajin tsoronshi, kuma duk
wanda aka kawo marar lafiya yana temaka mashi, hakan
yasa mutanen garin dana wajen gari suke girmamashi.
Yadade yana yima masarautar Bubayero hidima tun
lokacin mahaifansu Qaseem, dan masarautar bata yarda
da malamin duba ko boka ba, hakan yasa koda iyayensu
suka rasu basu yarda shiba, duk wani temako kowata
shawara sukan zogurinshi, kuma Sarki baya aiko kowa
gurinshi kode yazo tare dasu Qaseem da Waziri ko kuma
ya aikosu su 2, yauma sunzo domin neman wani
temako.
Bayan sungama gaisawa, Malam yasa ankawo masu
kayan motsa baki, dan sunyi waya da Qaseem tun jiya
yafada mashi suna hanya. Qaseem ne, yafara magana
cike da ladabi. Allah gafarta malam, kamar yanda muka
fara magana dakai jiya awaya. Dama bawani abu bane
akan matsalar rashin haihuwar Yaya, tun tuni naso muzo
shine yake hanawa, shine nace ai koma menene yanada
magani, shine mukazo muji daga gareka.
Gyara zama malam yayi yacire glass din dayake idonshi
yace, hakika nima nadade ina tausaya ma, memartaba,
kuma dama tun kwanakin baya damukayi magana dakai,
nafarayin istahara akan al'amarin. Kuma alhamdulillahi
dama kobakuzo ba nayi niyar kiranka, infada maka
abinda nagani.
Sede inaso kusani bakomai ne, ake fada ba dan kayi
istahara, amma tabbas akwai abinda nagani amma
nabarma kaina, kuma insha Allahu abinda ake so ahana
za,a sameshi, sede muyita rokon Allah, babu abinda
yagagareshi. Kamar kullum abinda nake fada maku kuyi
hankali da mutanen da kuke tare dasu bance kuyi
bincike ba, amma kada kayarda dakowa kuyarda da
kanku, shine zaku zauna lafiya.
Abinda nakeso kusani insha Allahu memartaba yanada
rabon samun haihuwa, sede abinda zan fada maku agsky
ayanzude rabon dana gani zesamu ba'a agurin matanshi
yake ba. Amma koma menene nasan zesamu haihuwa
insha Allahu, sede adage da addu'a inafatan kunfahimci
bayanina? Waziri yace munfahimceka malam, kuma
mungode Allah yasaka da alkhairi, muzamuzo mukoma.
Malam yace tonima inada wata alfarma danakeso kuyi
mani, Qaseem yace haba malam ai kawuce komai
agurinmu kafadi koma menene. To kamar yanda kuka
sani akwai kanwata kuma autarmu, kunsan mijinta
yadade da rasuwa kuma taki yarda tayi wani auren,
shine nakeso dan Allah kozaku tafi da ita can tarika
temaka ma matan sarki dawasu aiyuka inaganin yafi
zamandatakeyi anan tunda can akwai jama,a dayawa.
Sarki zeyi magana Qaseem yayi saurin fadin agaskya
malam naji dadin wannan magana taka, kuma inaso
abani ita inkaima Suhailat, dan mundade muna neman
wadda zata zama mekusanci agurinmu, kasan ni bakowa
nake yarda dashi ba, itama haka, amma tunda daga
gareka tafito, kuma jininkace nayarda da ita sosai. Kuma
dama tana da tsohon ciki inata tunanin wadda zata
zauna mata. Mungode Allah yabamu zaman lafiya. Ya
sunanta? Malam yace sunanta Safeeya.
Murmushi Waziri yayi yace mungode malam Allah
yasaka da alkhairi. Sarki yace mungode malam, kuma
insha Allahu zamu riketa amana. Malam yace nikeda
godiya, bari inje infada mata tashirya.
Daki yakira Safeeya, sundade suna tattaunawa banji
abinda suke fada ba, haka tafito tashirya tayima Matar
malam sallama da sauran matan gidan, hada kukansu,
haka suka shiga mota suka dauki hanya.
Gimbiya Suhailat taji dadin zuwan Safeeya, dan tanajin
labarin malam agurin Qaseem, shiyasa tajata ajikinta
sosai, dan har karatu take kara mata, hakan yasa suka
saba dawuri, duk wata shawara Gimbiya Suhailat tanayi
da Safeeya, haka kuma baruwanta dashiga part dinsu
Gimbiya Zakiyyah, asalima basu san dazuwanta ba,
kamar yanda babu wanda yasan tana da ciki harya tsufa,
shiyasa taji dadin zuwan Safeeya. Dan Waziri yahana
anuna Safeeya acikin gidan, har seda Sarki yace meyasa
Waziri yace yallabai dan Allah abarta, Qaseem yace
shikenan yanda kace Waziri.
Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya, Cikin Gimbiya
Suhailat harya shiga watan haihuwarshi, Qaseem da
Sarki suna farin ciki da cikin, dan kamar Sarki yafi
Qaseem farin ciki da Cikin, kuma betaba fadama
matanshi ba, dan gani yake kamar sun sani kuma beso
suga kamar shima yadamu darashin haihuwar.
Jakadiya dasu Gimbiya sun hada kansu, Gimbiya Zakiyya
babu abinda takeso kamar haihuwa, ayanzu bata da
abokiyar shawara se Jakadiya, duk wani sirrinta Jakadiya
tasani, sede haryanzu bata karbi gurguwar shawarar
Jakadiya ba. Ita ko Gimbiya Nafeesa dama tasan bazata
kara haihuwa ba, dan tunzubar da cikin datayi har so 3,
likita yace mahaifarta tasamu matsala. Shiyasa bata da
damuwa agidan, itade burinta kawai tasamu ta tara abin
duniyarta, shiyasa takebin Gimbiya Zakiyya soda kafa,
sede tabangare guda kuma sun hade kansu ita da
Jakadiyya.
Zaune Jakadiya take afalon Gimbiyar Babbar Gida,
kallonta tayi tace inajinki Jakadiya wace shawara kika
kawo? Gyara zamanta tayi takara rage murya tace
Gimbiya bawata shawara bace dama wata dabara
nakawo, nace meze hana kicema Memartaba kina da
ciki. Saurin tashi Gimbiya tayi tace bangane mekike nufi
ba. Wace irin magana kikeyi haka, dama ana cikin karya
ne? Murmushi Jakadiya tayi tace Allah yahuci zuciyarki,
bahaka nake nufiba. Kinga yanzu ku 2ne matan Sarki,
kuma kece Babba taya za,ayi muyarda wata tashigo daga
baya ace ta haihu ke baki samu naki ba.
Jiya mukayi magana da Sarkin Fada kinsan mutumina
ne, agurinshi nasamu labarin Sarki yace daya samu da
namiji tofa lallai shine zegajeshi, shine nace meze hana
kawai kice mashi kinada ciki, idan yaso sekirika saka
tsummuna idan lokacin girman cikin yayi, kinga semuje
gidan marayu mudauko yaro namiji kinga kema kinyi
na..... marin da aka dauketa dashine yasata tayi shiru.
Dasauri tamaida kallonta gurin Gimbiya datake ta huci
sbd tsananin bacin rai, cike da tsawa tace kitashi
kibacemun daga nan. Kuma ina me tabbatar maki da
duk ranar dana kara ganin kafarki acikin part dina wlh
sekinbar masarautar nan.
Cike da bacin rai Jakadiya tafito, hanyar lambu tanufa
inda suka saba haduwa da Sarkin Fada, wata baiwace
tafito dagudu zata wuce, dasauri Jakadiya ta tareta dan
tagane baiwar Gimbiya suhailat ce. Ke lafiya kike gudu
haka? Wlh dama sauri nakeyi inje inyima Sarki Albishir
Gimbiya tasauka lafiya tasamu da na miji. Kara goge
kunnanta Jakadiya tayi tace bangane mekike fada ba.
Dama Gimbiya ciki gareta? Kwarai ma kuwa, aiko Sarki
yasan tana dashi. Wani mugun murmushi Jakadiya tayi,
tace ki koma za'a isar mashi da sako.
Dasauri Jakadiya tanufi gurin Sarkin Fada, sundade suna
magana daga baya tafito tana dariya tanufi bangaren
Sarki. Bakaramin dadin Sarki yaji ba, nan take yayima
Jakadiya kyauta metsoka, Qaseem ma seda yabata
kyauta, dan yana gurin aka fadi haihuwar.
Kafin wani lokaci gidan Sarki ya sheda haihuwar Gimbiya
Suhailat, Qaseem boye farin cikinshi yarikayi, dan
bayason Yayanshi yashiga damuwa. Bakaramin tashin
hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba lokacin da labari yazo
mata. Har kuka seda tayi, gashi takori Jakadiya, haka tasa
aka kira Gimbiya Nafeesa ita tarika bata hkr, dan ita ko
akanta.
Duk wata hidima Safeeya ce take mata, yaronta me kyau
sosai, tun yana jariri dayayi kuka se dimple dinshi ya fito.
Bayan kwana 7 akayi suna, Sarki da kanshi yasama yaron
suna, dan Qaseem yaso yasaka sunan Yayanshi amma
Sarki yace yabari zesa mashi suna, shikuwa yayi haka ne,
dan yabama matar kaninshi hakkinta ko akwai sunan
datakeson tasama yaron. Lokacin dayasa Safeeya ta
tambayeta sunan datakeso asama yaron tace tanason
asamashi Areef, dan sunan kaninta ne, daya rasu. Sarki
yaji dadin tambayr dayasa akayi mata, koba komai yasan
ba,a shiga hakkinta ba.
Qaseem yayi mamakin sunan da Sarki yasama yaron,
koda yabincika yagane shine yasa atambayi matarshi,
bakaramin jin tausayin Yayanshi yayi ba, kuma yakara
jinjina adalci irin nashi.
Bakaramin taro akayi ba, hatta da yan uwanta seda
sukazo suna, su gimbiya Zakiyya sunga yanda ake mulki
da kuma dukiya, haka suka saki jiki kamar bakomai akayi
suna lafiya, se alokacin suka san da zaman Safeeya, dan
sunga komenene Gimbiya zata sa sede takirata, gashi
kuma ita batada uniform bare suce baiwace, alokacin
sunan ne Gimbiya Zakiyya tashirya da Jakadiya, dan
tasan koba komai tana mata amfani sosai.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, duk yanda suka so
susamu wata hanya dazasu kunta tama Gimbiya suhailat
babu dama. Jakadiya da sarkin Fada kuwa kansu ahade
yake, dan sarkin fada seda yasan yanda yayi yarika shiga
bangaren Qaseem, yanuna yana matukar son Areef
hakan yasa yashiga jikin Qaseem sosai, duk lokacin da
aka kawo Areef Fada, Sarkin Fada shine yake karbarshi
yayita renonshi harseyayi kuka sannan amaidashi.
Bayan shekara 1 Areef yakara wayau sosai, kullum afada
yake wuni tare dasu Sarki, kowa yasan irin son da Sarkin
fada yakema Areef, hakan yasa itama Gimbiya suhailat
take mashi kyauta akai akai.
Lokacin da Areef ya cika shekara 1 da rabi aka yayeshi,
dan baya zama agurin Gimbiya yafi zma afada shiyasa
kawai ta yayeshi. Duk wani makircin Jkadiya da Sarkin
Fada babu wanda yasani, wata rana suna cikin lambu
suna makircinsu, Sarkin fada Yace wlh Jakadiya idan har
muka bari wannan yaron yagirma kashinmu yabushe,
Jakadiya tace meze hana mukawar dashi kowa yahuta.
Murmushi sarkin fada yayi yace shawararki tana kan
hanya. Shiru yayi jin motsi akusa dasu, saurin juyawa
yayi yanufi inda motsin yake, caraf yariko hannun wata
baiwa wadda tazo wucewa taji suna magana ta labe tana
jinsu.
Kuka tafarayi tana fadin wlh, banji komai ba, kuyi hkr,
dankwalinta yacire yashaketa dashi harseda ta mutu
sannan, Jakadiya tace kaga shegiya, muzaki tonama asiri.
Yo da asirinmu yatonu ai gara kowa yamutu. Sarkin fada
yazamuyi da gawar, kasande idan aka duba ba,a ganta ba
dole ashiga nemanta. Murmushi yayi yace kada kidamu
mubarta anan ko anzo anganta babu wanda zece
kasheta akayi, daukarta yayi yajefata cikin swimming
pool din gurin suka tafi.
Da gudu Jakadiya tashiga bangaren sarki tana kuka,
Waziri yace lafiya ke kuma zakishigo mana haka? Tana
kuka tace wlh nazo wucewa naga kamar mutum acikin
ruwa shine nazo infada maku, ai dasauri suka mike suka
nufi gurin, fadawa waziri yasa suka cirota, koda suka
duba suka iske tamutu.
Sarki da Qaseem sun shiga damuwar abinda yafaru,
haka akayi mata wanka aka rufeta, koda akayi bincike
wata kawarta baiwa take fadin dama tana tsoron ruwa
lokacin da aka aiketa lambu daga lokacin bata kara
ganinta ba, sese akace ta mutu. Sarki yace kila zamewa
tayi tafada kuma babu wanda yaganta. Da haka akarufe
maganar, hankalinsu Jakadiya ya kwanta.
Wasu mutanene guda 2, tare da wani Dattijo daka ganshi
zakaga beyi kama da hausawa ba, yafi kama da larabawa,
gefenshi. Kuma wata kyakkyawar matace, fara tasss da
ita, itama babbar macece, gefenta wata santaleliyar
budurwace kyawunta yawuce afadeshi, daka gansu kaga
larabawan asali, yarinyar bazata wuce shekara 19 ba,
tare suke da kayansu suna tsaye ajikin wani dankaramin
gida me kyau.
Mutane 2 dasuke tare dasu daya daga ciki yace to Baba
yakaga gidan yayi maka? Cikin hausarshi wadda bata
goge ba, yace e gida yayi tunda akwai dakuna 3 aciki
kuma kowane da bandaki nashi aciki ai yayi dede. Dayan
yace yauwa Baba kamar yanda muka fada maka zaka
rika bamu dubu 50 ashekara sune kudin hayar gidan.
Baban yace shikenan babu damuwa, amma akwai wutan
nefa ko? E Baba akwai komai har ruwa bamuda
matsalarshi.
Baban yace toyanzu kaine zakazo kadaukemu anjima
muje cikin kasuwa muyi siyayyar kayan amfani ko? E
Baba kome kakeso zanyi maka, kuma zan kaika inda zaka
samu kaya masu kyau. Yace toshikenan yaro nagode bari
mushiga daga ciki mu huta.
Wadan nan mutanen bawasu bane kamar yanda kukaji
ankira dattijon da Baba. Asalin sunanshi ABRAHAM ne,
kuma shi mutumin saudiya ne, yatabayin zaman Nigeria
har so 2, yayi aiki da hausawa agarin Bauchi, bayan
yakoma saudiya ne, ya yanke shawarar dauko iyalinshi
yadawo dasu Nigeria, kasancewar yaji dadin zamanshi
ABauchi gurin wani mutumin kirki, bayan yatafi seda
yayi wata 2 bedawo ba, se wannan dawowar dayayi tare
da iyalinshi, sede yayi rashin sa,a yana zuwa Bauchi
yasamu labarin rasuwar mutumin.
Yayi kuka sosai, dayake akwai Babban yaron Alhajin
atare sukayi aiki, kuma shi dan Gombe ne, hakan yasa
yanemi address dinshi yazo nan yasameshi, kuma shine
yayi mashi hanyar samun gidan dazasu zauna, dan yace
tund yariga da yabaro garinsu baze koma ba, shiyasa
yace zezauna agurinshi sucigaba da kasuwancin tare.
Matarshi daya da yarsu daya, mesuna Rayhana, suna
matukar sonta sosai, tana da ilimin boko dana addini,
gata da natsuwa baruwanta da hayaniya, tanason
iyayenta sosai. Bayan sun huta, dayamma akazo
akadaukesu suduka suka tafi kasuwa.
Jerin motocin Sarki ne suka shigo cikin gari suna jiniya
sundawo daga Yobe, tacikin gari suka shigo dansu gaisa
da jama'a mutane se daga masu hannu sukeyi, dan
mutanan Gombe suna son Sarki Hasheem sbd yana
masu adalci.
Rayhana ce da Umminta suka fito daga wani store na
kayan kitchen, Mahifinta kuma yana daga dayan
bangaren tare da wanda sukazo suna siyan wasu kaya,
Rayhana takamo hannunn Umminta dansu tsallaka titi,
yaran dasuka dauko masu kayan suna binsu abaya.
Wata irin kara da Baba yaji ne, tasashi saurin juyowa
dashi da mutanen dake gurin. Innalillahi Wainna
ilaihirrajiun, shine abinda mutane suke fadi da gudu
Baba yarugo dan ganin abinda yake faruwa. Dasauri
sauran motocin suka samu guri sukayi parking suka fito
domin ganin abinda yake faruwa.
To jama'a muje zuwa anext page danmuji meyafaru.
Tnx alot for ur concern to me, my luvly friends.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 40⚜45
Rayhanace rike da Umminta akasa ta rungumeta tana
wani irin kuka yayinda jini duk yabata mata jiki. Babanta
ne, yakaraso gurin ganin abinda yake faruwa shima
yaduka ya rungumo matarshi yana kuka, babu alamun
rai ajikinta, dan tunda motar tabigeta nan take tacika.
Driver daya kadeta ne, ya iso gurin, abayanshi kuma su
Sarki ne da tawagarshi suka nufo gurin dan yana daya
daga cikin motocin gidan sarki. Isowarsu tayi dede da
Rayhana tamike tana kuka tanufi drivern motar
tashakeshi tana kaimashi duka tana kuka. Dasauri Waziri
dasu sarki suka karaso gurin, Waziri ne yayi kokarin
cireta daga jikinshi yana bata hakuri, komawa tayi gurin
Umminta tazube tana kuka gwanin bantausai.
Qaseem da Wazirine suka isa gurin, shikuwa Sarki tunda
yadora idonshi akan Rayhana yaji wani abu ya soki
zuciyarshi, da kyar yasamu ya dedeta kanshi ya karasa
gurin, amma duk da haka yakasa dauke idonshi akanta.
Waziri yaduka kusa da Baba yakamoshi yana fadin kayi
hakuri Baba muje akaita asibiti. Dago kai Baba yayi yana
kallonshi yace wane asibiti kuma, bayan tarasu. Cak
numfashi Rayhana ya tsaya jin abinda Babanta yafada,
nan take tasume. Mamaki ne, yakama mutanen gurin
lokacin dasuka ga Sarki yadauki Rayhana yayi hanyar
mota da ita, ganin haka Waziri yace ma Baba yatashi
sutafi asibitin, Waziri da kanshi yadauketa suka nufi
mota, Qaseem dayake bin Yayanshi da kallon mamaki
shima yanufi mota suka nufi asibiti.
Suna zuwa aka karbesu, dan danan aka fara bama
Rayhana temakon gaggawa, Umminta kuwa koda suka
aunata anan suka gano ta jima da rasuwa, anan sukayi
masu bayani, Seda Su Waziri suka rike Baba lokacin
dayaji bayanin likita, abisa kujera suka zaunar dashi,
anan Waziri da Qaseem suka shiga bashi hakuri. Baba
yace ashede kasarki anan take, jiya mukazo garin nan
ashe bazaki rayu damuba. Haka yayita sambatu, suna
bashi hakuri.
Sarki kam hankalinshi yana kan Rayhana, yakasa tsaye ya
kasa zaune, Qaseem ya maida kallonshi gurin Yayanshi,
tausayinshi ne, yakama shi, dan tunda yake betaba ganin
Yayanshi cikin wannan yanayin ba, tashi yayi yanufi
gurinshi. Kafadarshi yadafa, juyowa yayi, yana kallonshi,
hannunshi yakama suka nufi wata kujera suka zauna.
Qaseem yace Yaya kanutsu Fadawa da mutanen gari
suna kallonka, kuma kowa yasan bamuda alaka dasu
kada suyi tunanin wani abu. Sarki yace Matar tarasu ko?
Kai Qaseem yadaga mashi, Sarki yace Allah kaceci
baiwarka kada itama ta tafi. Qaseem yayita bashi baki.
Mintuna 30 Rayhana tadauka kafin tafarfado, alokcin har
antafi da Umminta gidan Sarki, dan Sarki dayaji cewar
bakine agarin shine yaroki Baba akan suje masarautarsu
ashiryata ayi mata sallah acan se arufeta. Baba yaji dadin
yanda yasamu mutanen kirkin dazasuyi jana'izar
matarshi. Suna zuwa gidan Qaseem yawuce part dinshi
yacema Safeeya tafito akaita asibiti zata zauna da wata
kafin sudawo, haka yasa driver ya kaita yarakata har
dakinta shi kuma yakoma.
Koda Rayhana tafarka wata mata tagani akusa da ita,
cikin Hausarta marar dadi wadda suka koya agurin
Babanta danshi zaman dayayi anan yasa ya iya hausa,
kallonta tayi tace Ina Ummi na? Matsawa Safeeya tayi
takamota tace kiyi hakuri tana daki, kai Rayhana tashiga
girgizawa tana fadin ance ta mutu ai. Kuka tasaka marar
sauti, sede daka jishi zakasan yana ci mata zuciya. Ahaka
aka turo kofar dakin, tana daga kanta taga Babanta ne da
wasu mutane, shima idonshi yayi ja sosai. Dasauri
yakaraso gurinta ya rungumeta shima yasa kuka, tsaya
su Sarki sukayi suna kallonsu cike da tausayi.
Ganin tasamu sauki likita yasallamesu. Bayan sunfito
Rayhana tana jikin Babanta hawayene kawai suke fita
daga idonta, Baba yakalli Sarki yace Yallabai inaganin
Zamu koma garinmu gobe, banga amfanin zamana anan
ba, dama nazo daniyar zama anan, amma tunda narasa
matata gara mukoma nida yarinyata. Mungode Allah
yasaka da alkhairi, kuma munyafe ma wanda ya banketa,
sede yaje yayi azuminshi.
Shiru Sarki yayi yanajin wani zafi aranshi, kasa magana
ma yayi ya tsaya yana kallon Rayhana. Qaseem ne yayi
saurin fadin a,a Baba yanzu kaga dare yafarayi, muje
gida koma menene semu tattauna.
Part din Gimbiya Suhailat Qaseem yace Safeeya tawuce
da Rayhana, shikuma Baba suka nufi bangaren Waziri
dashi, Part din Sarki Qaseem yawuce dan tunda suka
shigo yawuce part dinshi. Kwance yasameshi abisa
gadonshi yana kallon sama. ( Niko nace Kadde ace su
Sarki anshiga layi ne😉).
Zama Qaseem yayi yadafashi cikin sanyi murya yace
Yaya tundazu naga kashiga cikin damuwa, wanda kuma
bahaka muka taho da kai ba, damuka dawo Yobe,
kafadamun damuwarka, idan baka fadamun ba, wazaka
fada mawa? Tashi Sarki yayi yakalli Qaseem yace
shikenan yanzu Qaseem tafiya zasuyi? Ai yakamata ace
tunda harsunzo daniyar zama garinmu kuma sukayi
rashi tadalilinmu yakamata ace mubasu muhalli akusa
damu suzauna, wlh Qaseem haka nan araina naji banaso
sutafi. Murmushi Qaseem yayi yace kada kadamu Yaya
munyi magana da Waziri bazamu bari sutafi ba. Sarki
besan lokacin da wani Murmushi ya kwace mashi ba.
Tashi Qaseem yayi shima yana murmushi yace Yaya bari
inwuce seda safe. Harya kai bakin kofa yajuyo yace Yaya
Allah tabbatar da alkhairi. Dasauri yafita yana dariya.
Murmushi Sarki yayi ya girgiza kai yanajin wani sanyi
yana ratsashi.
Rayhana kuwa tana falon Gimbiya Suhailat sunata
lallashinta. Cike da tausayi Gimbiya tace kiyi hakuri kinji,
daga yau munzama yan uwanki, bazakiyi maraicin Uwa
ba, kinga nima ba'a nan kasar nake ba. Daga yau kinga
nasamu yar uwa, haka sukayita lallashinta hartasamu
taci abinci tayi wanka suka nufi dakin Safeeya suka
kwanta.
Washe gari Baba yasa aka kira mashi Rayhana tana zuwa
suka fara kuka, Waziri yace suje fada Sarki yanason
ganinsu. Bayan Sungama gaisawa Sarki yakara yimasu
ta'aziya. Anan waziri yafada ma Sarki sunyi magana da
Baba yace ya hkra zasu zauna, sede yafiso yakoma gidan
daya kama yazauna aciki.
Qaseem yace Baba dan Allah kayi hkr kazauna tare damu
kaga Rayhana zatafi jin dadin zama anan saboda akwai
mutane, amma acan daga kai se ita, kuma daka fita zata
zauna ita kadai, kaga kadaici zeyi mata yawa. Baba yace
shikenan naji zanbarta anan amma nikam nafiso
nazauna acan. Waziri yace shikenan Baba munyarda,
amma zakayi hkr kadawo kusa damu, kaga can yayi nisa
kuma zakayi nisa da 'yarka, akwai wani gida nesa kadan
da masarautar nan za'a gyara makashi se asaka maka
wadan da zasu rika yimaka hidima seka zauna, kaga koba
komai kana kusa damu. Baba yace to nagode sosai, Allah
yakara budi.
Kallon Rayhana yayi wadda tayi lamo ajikinshi, cikin
larabci yayi mata bayanin komai, shiru tayi tana kuka,
kai tashiga girgizawa tace ita bata yarda ba, da kyar
yasamu yashawo kanta. Haka yayi masu bayani ta
amince, bakaramin dadi Sarki yaji ba, tagefen ido
Qaseem yakalleshi shima yayi murmushi ganin farin ciki
kwance afuskar Yayanshi.
Haka aka gyarama Baba gidan aka zuba komai, yakoma
ciki, Qaseem da kanshi yazabi bayi maza da mata dazasu
rika yimashi aiki. Rayhana kuwa ankawo mata kayanta,
kuma Gimbiya Suhailat da Qaseem sunce agurinsu zata
zauna.
Gimbiya Zakiyya da Gimbiya me daki bakaramun jin
haushin abinda akayi sukai ba, baram ma Gimbiyar
Babbar Gida, gani take kamar anmaidata saniyar
ware,Jakadiya wadda itace take kawo masu duk wani
labari daga fada. Kallon Jakadiya Gimbiya tayi tace
agskiya jikina bebani zaman wannan balarabiyar agidan
nan akwai alkhairi ba. Kawai ni tunkafin inganta wlh naji
na tsaneta, tsana ma ta sosai, dan haka dole musan wane
irin kulli zamuyi mata tabar gidan nan.
Jakadiya tace Gimbiya da ace Gimbiya suhailat tana
daukar zuga kuma tana bani fuskar shiga gurinta danaje
mata dawani kaidi wanda na tabbata setayi sanadiyar
fitar wannan yarinyar agidan dan sena nuna mata
mijinta akwai dalilin dayasa yakawota gidanshi tazauna.
Gimbiya medaki tace kai amma Jakadiya kinkawo
shawara me kyau, kuma dole sekin san yanda zakiyi
kisamu kishiga jikinta. Gimbiya Zakiyya tace ni nasan me
za'ayi, ina Sarkin Fada, ai mutuminta ne, dan haka
tagurinshi zamu samu damar aikata abinda mukeso.
Jakadiya tace angama ranki yadade. Murmushin farin
ciki tayi takoma ta kwanta tana fadin seyanzu nafara
jindadin aiki dake, dan kinfara kawo shawara irin tamasu
tunani, wato yan gidan sarauta. Kallon Gimbiya medaki
Jakadiya tayi, suka hada ido, su duka sunji zafin maganar
data fada masu, amma haka nan suka hadiye bacin
ransu.
Kwance Gimbiya Suhailat take ajikin Qaseem yana wasa
da gashinta, Gimbiya tace Hubbi kasan mene? Yace sekin
fada, wlh naji dadin zuwan Rayhana gidan nan, naji dadi
sosai daka kawomun ita part dina, inajinta ajikina sosai.
Qaseem yace nasan zakisota, shiyasa nakawo maki ita,
kinsan nasan duk wani abu daya dace dake. Kinma san
menene? Tace a,a inaso kikara kula da ita sosai, dan inaji
ajikina Yaya kikema kiwo. Dariya suka saka tace kai
Hubbi da gske? Yace sosai ma, kodazu munyi maganar
da waziri, shima ashe yagane abinda Yaya yake ciki. Kai
amma naji dadi, aikuwa zankoya ma Rayhana yanda zata
kwace Yaya daga gurin wadan can matan nashi.
Jinjina ta musamman gareku masoyana. Nagode sosai,
sekunjini a next page😘
.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 45 ⚜50
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 45 ⚜50
Sarkin Fada ne zaune afalon Gimbiya Suhailat, Areef
yana bisa cinyarshi yanata wasa yanacin biscuit,
Murmushi Gimbiya tayi tace Sarkin Fada kaida mutumin
naka ne? Washe baki yayi yace barka da fitowa ranki
yadade uwargidan Yallabai.
Zama tayi, bayan sungaisa Areef ya mika hannu alamun
tadaukeshi, murmushi tayi tace a,a nibazan dauke ka ba,
ai nadauka kamanta dani, kara wangale baki yayi kamar
yaji abinda tafada. Hannu tamika mashi segashi yataho.
Lafiya de Sarkin fada naganka awannan lokacin? Kanshi
yadan sosa ahankali yace lafiya lau, dama wani dan
labarine naji awaje shine nace bari inzo inji daga uwar
dakina ko haka zancen yake, dan abun yashafeki, nikuma
aduniya babu abinda zanji dangane dake ace nabarshi.
Inajinka, E to, to dama de akan wannan bakuwar
balarabiyar ne datake zaune agurinki, shine naji mutane
suna cewa wai yallabai Qaseem ne yakawota, koshima
zebi sahun Memartaba ne yabi Sunnah. Kuma da alama
itace ze aura ko? Wani murmushi Gimbiya tayi takara
kallon Sarkin Fada, gaba daya babu natsuwa atare dashi,
kozama yakasayi.
Kara murmushi tayi tace tonagode, amma nibani da
labari, sede kazauna inaji yakusa shigowa semuji daga
gareshi, zaro ido yayi yace haba Gimbiya rufamun asiri,
ina ni ina zama inyi irin maganar nan da Yallabai, nifa
dama ban tabbatar ba, kawai kinsan bazanso arika
maganarki ina guri ba, shiyasa nace gara inzo inji da
kunnena. Murmushi tayi tace gaskiya kam ka kyauta, to
bahaka maganar take ba. To harnaji dadi, aini bazanso
ayima uwar dakina abokiyar zama ba. Tonizan koma,
ahuta lafiya. Mikama Areef hannu yayi nan yataho suka
fita.
Murmushi tayi ta girgiza kai, kallon wata baiwa tayi tace
takira mata Safeeya. Bayan tazauna ta fada mata abinda
Sarkin Fada yace mata. Shiru Safeeya tayi nadan lokaci,
sannan tace nifa Gimbiya dama nafada maki banyarda
dashi ba, ina yawan ganinsu tare da Jakadiya, amma
kikace kinyarda dashi. Gimbiya tace bakomai Safeeya ki
kyaleshi ni haryanzu ina mashi kallon mutumin kirki, kila
da gaske yaji maganar, kinsan gidan nan akwaisu da
gulma, bare sunga ankawo yarinya mekyau dole surika
tsegumi. Safeeya tace amma duk da haka kirika kula
sosai Gimbiya, ba'a saurin yarda da mutum, nasan kuma
wannan halin kine, amma naga kinyarda dashi. Tace
shikenan Allah yashige mana gaba, tace amin.
Haka suka cigaba da rayuwa, su Gimbiya Zakiyya duk
yanda sukaso su hada tuggu akori Rayhana sunkasa.
Sarki kuwa Son Rayhana yayi girma azuciyarshi, gashi
baya ganinta dan bata fitowa sede idan zataje gaida
Babanta ita da Safeeya, ganin abun zedameshi ya yanke
shawarar fadamasu Qaseem.
Waziri ne da Qaseem Zaune afalon Sarki, su dukansu
cike suke da murnar abinda Sarki yafada masu, dama
kuma abinda suke jira suji yafada kenan, dan Waziri
yace ma Qaseem yabari shida kanshi yayi masu
maganar.
Waziri cike da murna yace agskiya naji dadin wannan
labari, nima tunda naga yarinyar kawai naji ta kwanta
mun arai, duk da bata fito daga gidan sarauta ba, amma
inaganin aurenku akwai alkhairi aciki. Amma mekace
Qaseem? Murmushi yayi yace aini nakasa magana sbd
farin ciki.
Duk da inada ra'ayin kin auren wadda bata fito daga
gidan sarauta ba, amma nikam nayima Yaya sha'awar
auren Rayhana, sbd mune muke tare da ita nasan halinta
mekyau gashi babu ruwanta, tana da addini, Allah ya
tabbatar da alkhairi.
Sosai Sarki yaji dadin maganarsu, kallon Waziri yayi
seyayi shiru. Waziri yace to ai ba tsayawa zamuyi ba,
zanyi magana da Malam domin yayi mana addu'a akan
al'amarin, kome yafada semuyi magana da Baba.
Qaseem yace wannan yayi dede, Allah yate maka. Waziri
yace amma inaso abar maganar anan, harse komai ya
tabbata, kasan halin mutane. Sarki yace wannan yayi
dede.
Bayan kwana 2, malam yakira Waziri suka yi magana
akan istaharan dayayi. Waziri yaji dadin abinda malam
yace, sundade suna kara tattaunawa akan masarautar,
sannan sukayi sallama. Qaseem yakira yafada mashi
komai, sannan suka fadama Sarki. Sosai yaji dadi, waziri
yace zasuje suga Baba.
Gimbiya Suhailat da Safeeya sunji dadin maganar, sede
Rayhana batasan abinda akeyi ba. Da dare Gimbiya
Suhailat takirata, bayan tazo Gimbiya ta sheda mata
dalilin kiranta. Sunkuyar da kai tayi tana murmushi bata
ce komai ba, Safeeya tace Rayhana kiyi magana mana
kin amince? Da gudu ta tashi tana dariya tashige daki.
Dariya Gimbiya tayi tace Allah mungode maka, gaskiya
naji dadi sosai. Allah yashige mana gaba. Safeeya tace
amin, amma ina tausaya mata gata karama babu
ruwanta zata shiga cikin matan Sarki.
Gimbiya tace kinsan yanda Yaya yake sonta kuwa?
Betaba auren Soyayya ba seyanzu zeyi, kinsan baze bari
wani ya wulakanta taba, kuma akusa dashi za'a ajeta,
bakiga ana kara gyara part dinshi ba? Nasan de kawai su
Gimbiya Zakiyya zasu sha kayan haushi sede suyi hakuri.
Nikam yanzu zan kara koyama Rayhana zama dasu,
kuma dole ayi mata gyara na musamman, nasan dawuri
za'ayi bikinta amma duk da haka daga gobe zata fara
amsar gyara.
Bayan su Waziri sunje gurin Baba sukayi mashi bayanin
daya kawosu, sosai Baba yaji dadin maganar, nan take ya
amince, masu suka bada kudin neman aure dubu dari
biyar. Anan aka yanke rana sati 2. Godiya sukayi mashi
kuma suka fada mashi basu bukatar komai.
Zaune Jakadiya take afalon Sarki, Bayan sungama
gaisawa yakalleta cike da girmamawa, danshi yana
matukar girmamata, dan sunyi sabo sosai, komatanshi
bayajinsu kamar yanda yake jinta, sun share shekaru
tare tun farkon zuwanta gidan, take mashi hidima,
shiyasa yabata amana sosai. Kallonta yayi yace dama
nakiraki ne dan inbaki sako kifada ma su Gimbiya
Zakiyya da Nafeesa maganar aurena nan da sati 2.
Akwai Yarinyar da take zaune gurin Suhailat wadda
mukazo da mahaifiyarta nan akayi mata sutura wadda
driver na ya kade harta rasu. To itace nakeso na aura.
Washe baki tayi tace amma naji dadi sosai, kallonshi tayi
tace Rankai dade da alama naga kana son Rayhana sosai,
bantaba ganinka cikin wannan farin cikin ba alokacin da
zakayi aure ba, se wannan karon. Ko aurenka na farko
banga wannan farin cikin atare da kaiba. Murmushi yayi
ya sosa kai, dan yanajin Jakadiya kamar mahaifiyarshi
dan tagirmeshi, yace wlh Jakadiya ina mata son daban
taba yima wata mace ba. Dariya tayi tace Allah ya shige
mana gaba, kuma anan danaga ana gyara za'a ajeta ko?
Yace haka ne.
Murmushi tayi tace gskiya nafi kowa farin ciki da
wannan al'amari, sbd yanzu Uban gidana zesamu abinda
ranshi yakeso. Dan haka zan daukota domin akoya mata
zama agidan sarauta. Kallonta yayi yace ai inaganin
kamar Suhailat tana koya mata, babu damuwa nasan
zata kula da ita sosai. Jakadiya tayi murmushin yake tace
toshikenan bari inje infada masu Gimbiyar. Check
yadauko guda 2 yace takaimasu kowa dai dai. Wasu kudi
yadauko yamika mata yace ga wannan kema kirike
ahannunki. Godiya tayi mashi tafita.
Gurin Sarkin fada tawuce, abinda yafaru tafada mashi,
sosai suka shiga tashin hankali. Sarkin Fada yace kina
ganin Sarki baze iya samun haihuwa da wannan yarinyar
ba kuwa? Kinsan fa ance larabawa albarka garesu.
Jakadiya tace kada kadamu nasan abinda zanyi, damma
Sarki yace ba,a gurina zata zauna ba da tunkafin tashiga
gidanshi zanyi kokarin hanata haihuwa, amma kasan ni
amintattar Sarkice dan haka kome nakai zesata taci, dan
haka kada kadamu inde ina raye bazan bar Sarki yaga
kwanshi aduniya ba. Shekarata nawa ina mashi hidima
amma haryanzu nakasa zama wata acikin gidan nan,
haka zankare a Jakadiya?.
Sede inzama fitila ina haska wasu ni ina kona kaina, ai
rashin gata ba hauka bane, dan haka gara kowa yayita
zama ahaka, shima wannan yaron dande ka hanani
dayanzu na aiwatar mashi. Sarkin fada yace kiyi hakuri
wannan yaron yashiga rai na, Allah yasani badan so
nafara daukarshi ba, amma daga baya yashiga raina
sosai, dan haka kibarshi, ninasan ko Sarki yamutu sede
Qaseem yahau kujerarshi bade Areef ba, dan haka
mutsaya akan sarki da matanshi. Yanzu kije ki kaima
Gimbyar Baban Gida mugun labari, dannasan ita kadai
zata shiga damuwa, banda Medaki, itakam ai tamu ce.
Dariya Jakadiya tayi tace wlh bakada dama. Yace Allah
kuwa kinsan daza,a bani Gimbiya medaki ai dana more,
tun lokacin datazo gidan nan miyau na yabiya kawai
senaji wai Sarki ze aureta. Jakadiya tace ai naga alamar
itama yar hannu ce, amma matso kaji. Wata dariya suka
kwashe da ita Sarkin fada yace kina ganin haka za,ayi?
Tace sosai ma, amma bayanzu ba senan gaba idan komai
ya zama dede.
Wani uban gumi ne yake fitowa daga jikin Gimbiya
Zakiyya, kara kallon Jakadiya tayi tace yanzu jakadiya har
saurin zuwa ki kawomun wannan bakin labarin kikeyi?
Jakadiya tayi kasa da kai tace Allah yahuci zuciyarki,
shima Sarki ba sonta yake ba, kawai tallarta Babanta yayi
mashi, kuma kinsan Sarki dasaukin kai shiyasa ya amsa,
amma dakanshi yafadamun ke kadaice macen dayakeso
aranshi, duka sauran ya auresu ne abisa lalura. Dan haka
ki kwantar da hankalinki.
Komawa tayi tazauna, saurin zuba mata ruwa jakadiya
tayi tamika mata. Bayan tasha tace yanzu ya za'ayi
kenan? Jakadiya tace Ranki yadade kamar yanda kika
saba, hakan zakiyi, kinsan Sarki yana yabonki akan
halayyarki tarashin tada hankali aduk lokacin dazeyi
aure. Yace shiyasa yake kara sonki. Murmushi Gimbiya
tayi tace shikenan, amma wannan karon bazan kyale
wannan yarinyar ba. Jakadiya tace ai bazamu barita
dadeba.
Ita kuwa Gimbiya medaki duk da taji haushi kadan
amma ana bata magudan kudi tamanta da fushin.
Jakadiya tace dama nasan bazaki damu ba, se waccan
sarkin kishin, ita tana ganin kamar ita kadai sarki yakeso
dan tafito daga gidan sarauta. Medaki tace aisetayi tayi
nikam inde da kudi ya auri 10 ina ruwa na, nasan kawai
zanrasa kulawar danake samu duk bayan kwana 2 ,
nasan hakanne kawai zedameni dan Sarki akwai iya shiga
rai. Dariya Jakadiya tayi tace ai Gimbiya nasan
matsalarki, kuma wannan badamuwa bace kede kawai
kirikeni zaki samu yanda kikeso. Sarkin fada ma yanzu
yaganni zanshigo nan yace ingaisheki, kinsan ke kadai
yake gaidawa aduk matan gidan nan gaskiya yanaji dake.
Medaki tayi dariya tace ai yana da kirki damma kada ace
wani abu ai daya rika rakoki munashan labarai.
Murmushi Jakadiya tayi tace ah, tunda kinaso ai angama.
Sati 2 Gimbiya Suhailat tadauka tana gyara Rayhana,
takara kyau, sosai kyanta haryaso yayi yawa, tasha gyara
sosai. Duk wata kissa Gimbiya ta koya mata, dayanda
zata zauna da matanshi, babu abinda bata koya mata ba.
Duk wanda yakwana yatashi agarin Gombe babu wanda
besan Sarki zeyi aure ba, gaggarumin biki aka shirya
gidan kanshi yasha gyara, hankalin Gimbiya Zakiyya
bakaramin tashi yayi ba, dan tagano irin son da Sarki
yakema Rayhana, tun daga dukiyar dayake kashewa da
kuma irin hidimar da taga Qaseem yanayi, wanda tasan
shikanshi yana murna da bikin.
Taso ta tadama Sarki hankali akan auren, amma
mamanta tanaji tahanata, tace bakida hankali Zakiyya?
Kina ganin akan abinda yakeso baze iya wulakantaki ba?
Tunwuri idanma wasu ne suke zugaki togara kidawo
hanya, kina ganin nice karama acikin matan Abbanki
amma yanzu nice nazama babba, dan haka banyarda
kikara tada hankalinki akan auren nan ba. Kuma banyafe
maki ba, idan har kika yarda wata tajaki kukaje gurin
wani malami ko boka. Hakuri Gimbiya Zakiyya tayi ta
bata kuma tayi mata alkawarin bazata je gurin kowa ba,
kuma bazata kara tada hankalinta akan auren ba. Da
haka ta kwantar da hankalinta, sede tayi alkawarin idan
har tuggu da kissa suna sa mutum yaci riba zatayi
amfani dasu takori Rayhana daga gidan Sarki.
Ayau ne miliyoyin jama'a daga jahohi daban daban da
manyan sarakuna na garu ruwa suka halarci bikin Sarki
Hasheem da Rayhana, wanda aka daura akan sadaki
million 1, kowa yasheda wannan auren Soyayya ne Sarki
yayi, ankashe dukiya sosai, anci ansha maroka da
mawaka sun sami kyauta sosai. Adaren ranar Sarki da
sauran Sarakuna da manyan masu kudi sukayi kayatattar
walima ababban dakin taron masarautar Bubayero.
Bayan sungama kowa yanufi masaukinshi, kuma ranar
aka kai amarya Rayhana dakinta dayasha dukiya kamar
ba,a nigeria ba. Yayin da wasu suka cika da farin ciki
alokacin Gimbiya Zakiyya tarasa inda zata sa kanta sbd
tsabar bakin ciki. Jakadiya kuwa jan Sarkin Fada tayi suka
nufi part din Medaki acan suka zauna suna bikinsu.
Nima nace yakamata abar amarya da Ango su sha
amarcinsu.
0 comments:
Post a Comment