"Ohhhh nikuka maida mahaukaciya ko inacan hankalina yatashi bansan Inda kake ba ashe kananan kuna abinda nahaneku to wallahi tallahi kukiyaye ni ke kuma nadawo kanki wato baki dauki zancena da muhimmaci ba nafadamiki idan nakara ganinki da ghailan kuna soyayya ban yafe amma kinki jina ko to wlhy zan dauki mummunan mataki akanki" momy ce keta wannan masifan anty Shafa kuwa jin hayaniya yasata fitowa ta tsya tana sauraren fadan da momy keyi cikin kuka jawaheer tafara magana
"Anya kuwa momy kekika haifeni?babu uwarda zataso ganin danta cikin damuwa bata nemi mafita domin ganin farincikin danta momy idan kece uwar data kawoni duniya meyasa bazakiso farincikinaba? Meyasa bazaki nemarmin hanyar dazan sami farincikina ba momy farincikina a hannunki yake basekinsha wahalar nema ba zanyi matukar bakinciki idan kece uwar data kawo niduniya amma bakya kaunar farinciki na"
"Ke kikama min bakinki wlhy tun ban karairaya kiba kuma kije kihado kayanki aikinsami lafiya muwuce gida"
Dagudunta takarasa bayan anty Shafa "ni wallahi momy bazan bikiba tunda bakya sons"anty Shafa tajanyota tadawo da ita gabanta "jawaheer kiyi hakuri kinji kibi mamanki tanasonki"
"Haba umma yazakice tanaso na? Momy bakisaniba tun ranar damukazo fadamiki zancen soyayyarmu kika koramu tun ranar nasan manufarki akan hanani auren Yaya ghailan hakika nayi matukar bakin ciki kuma banxo da Sa'a ba arayuwata wai ace uwa da yarta ke takarar soyayya akan saurayi Wanda ya dauketa tamkar mahaifiyarsa munajin labari munagani da idanunmu dayawa iyaye suke sacrificing farincikinsu saboda yayansu amma momy banda ke saboda zancenki ko kadan ba abin hawa azauna bane kuma daga ni har shi wallahi munfi kaunar mutuwar mu akan ki aureshi"durqushewa tayi awurin tana dirzar kuka
Ghailan ne yadawo gaban momy ya tsaya kafin yafara magana "momy tabbas ni Dane awurinki bazan taba son na saba mikiba kece kika fitar dani daga rayuwar kunci kika maidani cikakken dan Adam kamar kowa amma momy hakurina yasoma karewa akan abubuwan dakike ATM card dinsa yaciro daga aljihu ya ajiye agabanta hadi da karanto mata pin dinsa duk abinda kikayimin nagode zan fita daga rayuwarki da yayanki kamar yadda kikeso duk abinda nasamu ta sanadiyyarki zan ajiye miki abinki ilimin dake kaina ma da inada yadda zanyi naciroshi dasena damka miki abinki kokuma nayi tariyar baya namaida rayuwata kauyenmu daduk sena yi domin nafita daga rayuwarku tafiyata zanyi basekin yi wahalar nemana ba garinmu zani inxauna da iyayena kuma zan fada musu abinda yasa nadawo saboda ta boye boye takare tunda baki rufawa kanki asiri ba mu meye amfanin rufeshi? Nagode sosae da muhimmiyar rawar dakuka taka arayuwata" hawayen dayake kokarin tarewa ne tundazu suka shammaceshi suka zubo dan haka beyi kokarin taresu ba illama kukan daya kwace masa ya durqushe awajen wani kukan suka jigo daga bakin kofa adnan ne da tundazu yake tsaye yana saurarar su karasowa yayi palon "ada munyi tunanin babu Wanda yakaimu sa'ar uwa ashe ba haka bane seyanxu muke ganin halayen uwar tamu dabasu dace da itaba na tabbata saboda wannan abinci dakike shirinyi momy shiga cikin jama'a seya mana wuya saboda kinanemane ki ruguza mana rayuwa musamman jawaheer she's still young kuma kinji abinda Dr yace mana kalli yadda takoma kowa yasan da ba haka takeba amma kinki kitausaya mata kinaji kina gani hawan jini naneman yamata dole ta tambayeki kokece Mahaifiyarta" hawayene suka cigaba dazuba daga idon adanan momy kuwa atsaye take tana tunani hakika maganganun yayanta sunaso suyi tasiri kwanta saboda dukansu gaskiya suka fadan sedai shedan dazuciyar ta nacigaba da ingizata saboda idan takalli ghailan setaji takara son sa koda ta Ankara bakowa a Palon se ita kadai miqewa tayi dan ganin anty Shafa da jawaheer zasu fita "anty ina zaku?" Ta tambayeta batareda ta kalletaba tace ganinayi kinaneman haukacewa donhaka gun abbanmu zani nasanar dashi halinda ake ciki"
Zuciyar momy ce tayi wani irin bugawa DUM DUM dasauri tasha gaban umma "don Allah anty kiyi hakuri zanyi tunani kinsan halinda Abba yake ciki karki Sanar dashi don Allah" tagefenta umma ta bi zata wuce tana riqe da hannun jawa momy tasake shan gabanta "ke wallahi idan kika sake taremin hanya zakisha mamaki banza me budurwar zuciya"
Daga haka tabi gefen momy suka wuce momy kuwa tasan idan abbansu yaji zancennan takade har ganyenta gashi anty shafa ta yimata abinda baya tana yimataba lallai kawai matsala to mema zakayi haka ta tsaya agurin tana tunani mezatayi yanxu.
_(To hell with you momy)_
*wannan shafin nakune matan Exquisite Allah yabarmu tare ameen*
*I love u*💋
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*© Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
40/41
"Kawu inaga kawai zanje na fadawa su Abba ne don wallahi abubuwan er baba sun fara yawa"umma ce ke magana da kawu dama bada niyyar zuwa gun abbansu tayiba zuwa wurin kawu tayi don Neman shawarar sa,
"A'a shafa'atu kibarta tunda tace zata sake tunani ninasan er baba Nada hankali amma lamarin nata yana daure min kai yanzu abinda za ayi kije gida kawai mubata sati biyu idan tanememu ta chanja tunani shikenan idan kuma tananan kan bakanta to semuje gun abbanku domin musanar dashi yasan halinda ake ciki yanzu yakamata muduba yanayin rashin lafiyarsa karmuje sauri ya haifar da nawa my qyaleta muga iya gudun ruwanta"kawu ke wannan zancen saboda shi aganinsa zuga momy ake saboda yasan tanada hankali koda suna yara sunfita rawar kai don ita batama cika magana ba se idan takama dole,
"To shikenan kawu Allah ya kyauta"ya amsa da ameen
"Bari na kira wannan shashashan daga zuwanmu ta shige ciki tanacan zata kashe mana kafafun uwa" kawu yai dariya kafin yace
"Kibarta ta hau abinta ai itama hajaran ita ke biye mata" sukasa dariya suduka
"Ke meye haka kika zauna tana baki fura abaki sekace wata ta goye?"
"Umma ita tace nazo tabani"
"Sannunki shine sekika zauna tana baki don bakida kunya?"
" kinsan kamun kafa take dani dan kwanaki hanawa mijina yabata cefane nayi shine take kula masa da amaryar tasa ko er tsohuwa?"
Tayi maganar tana yiwa hajiyar dariya
"Ke nidai tashi ja'ira kificemin duk ta shanyemin fura daga zuwanta"
Fizge kofin jawaheer tayi tana fadin "kinga da wannan ma zani bazan bar miki ba zancewa angona yakawo miki wata"tanagama fadar haka tafice sallama Anty Shafa tayi musu suka nufi guda ,
Bangaren momy kuwa gidansu takoma tazauna adaki tama rasa me zatayi kawai ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya seda tayi me isarta kafin ta hakura tayi shiru dan idanunta har sun soma ciwo gashi dama tun tana karama haka take fama da ciwon ido,
Adnan kuwa iyakacinsa da momy gaisuwa bayan haka ba wani abu ko abincin gidan bayaci abinda yasa baze bar gidan ba kawai dan kar yaba momy ita kadai gida domin ita uwa uwace bame chanja ta,
Ghailan kuwa yana fita yaje gun sadeeq yace aramai 20k insha Allah zebiyashi befada mai halin dayake ciki ba amma sadeeq yalura da yanada damuwa amma tunda be fada masaba baze tambayeshiba don ghailan bayason shishshigi "abokina zandai baka kyauta kafi karfinsu agurina"yadauki kudin yabasa yayi godiya wani boutique yashiga yasiyo riga da wando yanufi gidan momy,
Duk abinda yadanganceta kama daga takardunsa,motarsa,wayoyinshi,system daidai dakayan sawa be dauka ba yasaka wayanda ya siyo yabar gidan tasha yanufa yahau motar silami,
Da zuwansa be boye musu komaiba ya fayyace musu lamarin hakika sun girgiza da jin wannan batun inna ce tafara magana cikin kuka "wlhy malam tun farko Kaine kanace se anbata yaronnan nahakura badason raina ba saboda shikadai gareni namiji kace tunda tazo da iyayenta suka roqa se an basu gashinan ashe badon Allah takarbar min yaroba"tana magana tana kuka
"Haba Hauwa kinsandai lokacin datazo bama tunann dawata manufa tazo kuma ga iyayenta da mijinta sunxo karki manta da aurenta akanta fa tazo ina tunanin dai akwai wata akasa"
Ghailan kam zaune kawai yake yana kallonsu bayama fahimtar me suke cewa yanacan yana tunanin halinda princess take ciki
"Koma dai menene yanxu kotaxo bazai komaba tabar min Dana nafijin sanyi idan yana kusa dani Jurewa kawai nake idan bayanan"
"A a hawwa baxamuyi hakaba ba ni inaso ma tazo akwai abinda nakeson fada mata"
Kqllonsa kawai takeyi tana tunani anya kuwa malam sanin bayason musu yasa ta kyaleshi,
Yau kwana coma sha daya da barin ghailan gidan gabadaya momy bata hayyacinta duk ta chanja kamanni,
"Hajiya murja kin kwanta asibiti ne bansaniba"?
"A a wlhy Hindu shiyasa nakiraki inacikin matsananciyar damuwa ne" gyara zama hajjiya hindu tayi nan momy ta labarta mata duk abinda yafaru hadi from A to Z,
"Amma wlhy murja kinban kunya kina abu sekace wacce bataje islamiya ba kokuma bata waye ba ? Kobadan yana danki ba aikya janye kudrin kodan ganin suna soyayya da auta to wlhy ina baki shawara tun wuri ki kama kanki wannan abin kunyar dame yayi kama ni yadda kila koma tsabar rashin kwanciyar hankali yarama sungano badaidai kikeba amma ke kin to she kunnenki ana ga annabi kina runste ido ai dole su guje ki yarinya har cieo tayi likita yacemiki tana dab dakamuwa da hawan jini amma ki shakulatun bangaro da batunsa? Yarinya dududu shekarunta sha Tara fa sekace bakida imani kokuma bakyasonta? Kisake tunani kawata"
Momy tafitar da huci me zafin gaske ita kadai tasan metake ji azuciyarta
_Allah ka rabamu da budurwar zuciya_ameen
*kuyi hakuri da wannan kwanabiyu dinnan lazyness dinane ya motsa se ahankali luv u oll*💋
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
*wannan shafin nakiñe miemiebee Allah yakara miki basira*
*ILYSVM*❤
42/43
Momy takalli Hajiya Hindu "Hindu Na janye batuna na auren ghailan dama shedan ne yake rudani amma wlhy haryanxu jinake duk bayan second daya sonsa nakaruwa cikin zuciyata akwai abubuwan danayi tunani daga baya bansan me yake damuna ba"tana maganar ne tana kuka
Hajiya Hindu ta tausayawa kawarta"tun farko murja kece bakiyi tunani ba kawai kikayi wa al'amarin hawan kawara"
Kuka momy tafashe dashi data tuno da kalaman jawaheer *anya momy ke kika haifeni?* *momy farin cikina a hannunki yake basekinsha wahalar nemaba* *momy idan kece uwar data kawoni duniya meyasa bazakiso farincikinaba munajin labari kuma muna gani da idonmu dayawan iyaye ke sacrificing farincikinsu saboda yayansu*
Tana zuwa nan ta runtse idonta "what kind of a mother i am? Dawane ido zan kalli Yaya na musamman ghailan Hindu na tafka babban kuskure bangane yayana sunada muhimmaci arayuwata ba seda suka nisanceni"
"Kiyi hakuri yanzu tashi zakiyi muje gun Anty Shafa da kawu kibasu hakuri saboda sam Bali kyauta ba abinda kikayi"
"Banajin zan iya fita jikina banajin dadinsa"
"Daurewa zakiyi murja kiyi hakuri"
Anty Shafa seda ta firgita ganin yadda er uwarta ta komade "er baba meyasameki haka"tafada tana riqo hannunta
"Anty kiyi hakuri don Allah seyanxu Nagano bankyauta mukuba Anty kunyar hada ido da ghailan da auta nakeji"hawaye ke zuba daga idonta ahankali
"Babu komai murjanatu ninasan akwai abinda yake damunki shiyasa mukayimiki uzuri"tajanyo hannunta suka zauna a Palo
"Yi hakuri Hindu munbarki a tsaye"
"Babu komai antyn mu"
"Murja meye haka naji jikinki da tsami tsami damuwar har takai kikasa yin wanka ga jikinki da zafi"
"Anty komai kasa yi nake rabona da abinci tunjiya gidan babu dadi"
Jinjina kai Anty tayi "to tashi gsky kiyi wanka kafin nan angama abinci hajiya hindu mushiga daki"
"Allah sarki autanmu bacci take"
"Aifa aikin kenan Dan yauma ba islamiya suna hutu "
"Allah sarki"
Momy kuwa kallonta take tadanyi kiba da haske akan lokacin datake gida Allah sarki auta wlhy inasonki Anty Shafa ta katsemata tunani
"Murja kije ga ruwan wanka can nahada miki kar lokaci ya kure mana"
Jawaheer ce tafarka daga baccin datake taga momy kusa da ita amma tajuya mata baya kasancewar kayan Anty Shafa momy tasaka se jawa tayizaton umma ce miqewa kawai tayi ta rungumeta "umma yunwa nakeji"tafada cikeda shagwaba momy kuwa juyowa tayi tana kallon jawa sekuma ta rungumeta hawayene suka fara fita daga idanunta ahankali tafara magana
"Jawaheer wlhy inasonki haqiqa natafka babban kuskure kiyi hakuri kiyafemin bansan dawane ido zan kalleku ba keda shalele nashiga damuwa da kuka nisanceni don Allah kuyi hakuri"
Jawa takara matse momynta ajikinta tana kuka "momy nima inasonki nasan abinda kikayi badason rankibane kuma kidaina jin kunyarmu my yayanki ne munfi kowa sanin halinki da fahimtarki kidaina kuka"tadago tana sharrwa momy hawayenda ke fuskarta da hannunta suna yiwa juna murmushi,
"Babu komai er baba nafahimceki Allah ya taimaka" fadin kawo bayan yagama jin bayanan momy da Anty Shafa
Yaci gaba da magana"yanzu se batun zuwa bikon ghailan amma kafin nan semun fara zuwa gun abbanku Susan halinda ake ciki saboda ina tunanin iyayen ghailan baxasu yadda susake bamushiba se anyi magana tafahimta sosae akuma basu hakuri akan abinda yafaru"
"Kawu Dan Allah kar afadawa abbanmu kasan halinsa"momy tafada muryarta kamar me shirin yin kuka
Anty Shafa tafara magana"murja yakamata suji saboda susaka baki iyayen ghailan subarshi yadawo kinfa San wannan maganar bekamata mu ringa rufa rufa akantaba tunda iyaye na Raye yakamata suji hakuri zakiyi insha Allah zasu fahimce mu"
"Shikenan anty Allah yasa karsu dau zafi dani"ameeb
Washe gari tunda sassafe suka tafi bayan sunbar jawaheer kan adnnan yakaita gidansu rufaida,
Momy ce durkushe agaban abba tana kuka bayan tagana yi musu bayanin abinda yafaru"abba Dan Allah kuyi hakuri wlhy rudin shedan ne da sharrin zuciya"
"Er baba abu daya zesa namiki uzuri wlhy saboda tun farko kece me natsuwa acikin Ku kuma baki taba samun sabani da uban yayankiba Dan bantaba zaman sulhu a tsakaninku ba badan hakaba saboda wannan abinda kikayi zan iya cireki acikin jerin yayana amma kisani wlhy kinbani kunya"
"Abba ataimaka ayi hakuri don Allah tunda tagane tayi kuskure kuma tabada hakuri aimata afuwa" maminsu kuwa batace komaiba aikinta kallo amma akwai abinda takeji game da ghailan tanasonsa kamar tafadiwa duniya adduar ta batawuce Allah yasa iyayen ghailan suyi hakuri subasu shi yadawo (nace ameen Dan koni kaina nan banason zamansa kauye),
"Shikenan kutashi yanzu karfe Tara nakegani kafin sha daya mun isa silami kukira adnan idan bekai jawaheer ba karsu tafi yaje yadauko marwan dasu zamu tafi duka"
Atake sukayi yadda yace larfe 9:40 suka dauki hanyar silami,
Zazzaune suke a tsakar gida suka jiyo sallama ganin su momy ne yasa dukansu suka miqe aka gaisa fuska ba yabo ba fallasa,
"Malam kuyi hakuri nasan kunji abinda yafaru akan abinda murjanatu taso tayi abin kunya kuma Mara dadin sauraro shiyasa mukazo dakanmu mubaku hakuri itama kanta tagano abinda take shirinyi ba daidai bane"
Momy dake zaune kanta akasa tafara magana muryarta Na rawa alamun kuka take "malam don Allah kuyi hakuri najanye batun danakeui abaya naso natafka babban kuskure idan nice uwar jawaheer nabashi ita duniya da lahira"
"Hajiya a gaskiya bamuji dadin abinda yafaru ba senaga kamar ba don Allah kika karbar mana yaro ba amma idan natuna da aurenki akanki kikazo to se abin yadaure min kai"
Kawu ne yafara magana "don Allah kuyi hakuri kowa yana mamakin wannan abin datayi saboda beyi kamada ita ba "
"Shikenan amadu amma akwai abinda nakeaon fada muku naji dadin zuwan Ku kuduka"
Kowa yakasa kunne yaji me malam keson fda musu inna kuwa jikinta yadauki rawa har tafara hada gumi kamar wata Mara gaskiya,
"Abinda nakeso kusani shine........."😜
_se Ku biyoni domin jin abinda malam keson cewa_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writers*
_sofiyyah galadanchi_
_in dedication to sha'awa Ibrahim_
44/45
'Ghailan da kuke gani ba Dana ne ba hasali ma bansan koshi wayeba Ma'ana bansan asalinsa ba"
Rufe bakinsa keda wuya sukaji faduwa abu kowannensu yakai dubansa ga ghailan dayafadi ya suma a rikice momy tayi kansa tana kiran sunansa inna ce tayi karfin hali debo ruwa aka yayyafa masa,
Jawaheer kuwa jitayi marar ta tayi wani irin murdawar da seda ta riqo hannun anty Shafa sosae ta runtse idonta,
Ghailan kuwa yana farfadowa ya fara sambatu "baba don Allah karkace haka menayi maka dazaka guje ni"
Dakayar suka samu yayi shiru amma idonsa sunyi ja yazama abin tausayi,
Abba ne yafara magana "malam to kayi mana bayanin ya akayi ghailan yazo hannunka"
"Shekaru ashirin da Tara dasuka wuce gidannan yakasance shine farko farko idan aka shigo gari kasancewar mune nafarko dana fara zama anan unguwar duka duka bamuwuce mu hudu damuke zama anan unguwar ba shiyasama aka saka mata suna gidan daji wata rana na dawo daga kasuwa har zan shiga gida senajiyo nishi mutun daga gefen gidana hakan yasa nayi addua naje Dan naga kowaye mace nasamu akwance da tsohon ciki kamar zata mutu tana naquda dagudu nashiga gida na kirawo hawwa'u muka kinkimeta muka shiga gida da ita domin tana bukatar taimako akofar daki na tsaya ina riqeda Sha'awa domin lokacin shekararta daya da wata biyu ko awa daya Matar batayiba ta haifi yaronta Hauwa tazo takirani bayan ta gyara wurin amma kash munyi juyin duniya Matar taki magana sedai wasu abubuwa data bani daure acikin Dan kwalinta Kalmar shahada kawai tayi rai yayi halinsa hakika bamuji dadiba hakan yasa naje dakaina wurin sarkin garinnan batareda kowa yasaniba na labarta masa abinda yafaru se yacemin nakawo yaron ze riqeshi nanunamai inada ra'ayin riqe yaron na tabbatar dame dakina bazata wulakantashi ba dahaka dai muka rufa wannan sirrin mutanen gari kuwa mukace musu muntsinci mata cikin halin rashin lpy a bayan gidana kafin muyi yunkurin yin wani abu rai yayi halinsa kowa ya tausaya mata haka mukayiwa gawa duk abinda yadace aka kaita makwancinta"
Kowa yayi shiru yana sauraren malam harni na saki bakida hanci ina sauraro
"Dare yayi naje gun mai gari nafada masa bansan mezancewa mutanen gari gameda yaro ba seya bani shawara kan cewa dama inada ra'ayin zama cikin garin sokoto kasuwanci mexe hana nakoma chan bayan wani lokaci sena dawo kan cewar a can matata tahaihu daidai yaron yagirma saboda gudun kar mutane suji aringa yi masa gori",
"Haka nabi shawarar me gari dama iyayena basuda rai sekanwar mahaifina naje nafada mata kudurina Jason komawa sokoto kasuwanci nata hananiba saboda tasan tanacin anfanina washe gari na tura Hauwa tayiwa iyayenta sallama seta bar min ghailan alokacin ne naimasa huduba nasa masa sunanan saboda inasonshi haka muka ringa boye boye ha muka bar garinnan mun is a lpy nakama mana madaidaicin gida",
"Kasuwancina Allah yasa masa albarka ghailan kuwa dama Hauwa batayaye Sha'awa ba setacigaba da shayardasu subiyu shekara kwana munsamu shekaru uku agarinnan wata rana Allah ya jarrabemu da gobara duka Rabin kasuwa takone gashi lokacin ankawo mana kaya duk mun kwashi kudi munsiyi kaya bamufita dakomai ba se rai gwamnati tace zata taimaka mana haka mukaita zata tsawon wata shida ba labri game gidan damuke ciki yagfar damuna hakan yasa kuka dawo silami kowa yayi mamakin ganin mu dayaro amma se muka ce bayan tafiyar mu ta haifeshi ashe tanada shigar ciki bamusaniba har yakai wata biyar shkearun ghailan uku kenan kasanceawar Hauwa fara kyakkyawa yasa suka yadda Dan ghailan badai farin fata da kyauba,
"Abincin dazamuci yan nema ya gagaremu hakan yasa muka tura ghailan *Almajiranci*gun wani malamin almajirai dake can sokoto Dan garinanne a can ne kika ganshi"yakareshe magana tana zubar da kwallah
Jawaheer kuwa murdawar da mararta tayi yazo mata da period dinta kafin lokacin sa yayi
Kowinnalillahi wa'innq laihirraji'un yakefada ghailan kuwa zaune kawai yake yana kallonsu,
Malam ne yakatse musu tunani da fading
"Ga abinda ta bani na ajiyeshi harse ghailan ya girma na ajiyeshi kamar raina"
Abbansu ne ya karba anty Shafa da momy suka kara matsowa kusada abbansu Dan ganin meye acikin jakar gabansu ne yafadi ganin Dan kwali
*JAWAHEER* sukafada atare cikin daga murya ganin sarka da zobe acikin dankwalin abba tsarabar dakamana lokacin dakaje maka momy ta janyo Jakarta ta dauko sarkarta anty Shafa ma Ciro tata tayi daga wuyanta suka hada komai iri dayane take suka fashe da kuka gun ghailan sukaje suka rungumeshi suna kuka,
Jawaheer kuwa tasowa tayi taje kusada momy "umma naji kunkira sunana"
"Bake muka kiraba sunan mahaifiyar ghailan ne" inji umma
Su maman kuwa mamakine ya cikasu sunkasa cewa komai balle marwan da adnan dasuke kamar hoto,
0 comments:
Post a Comment