'sakon cewa ubangiji daya ne, ya zo ne daga dukkanin annabawa da unangiji ya aiko, kasancewar akwai ayoyin ubangiji a littafinku mai tsarki, shima, yana dauke da wadannan sakonni na kadaitar ubangiji.'
'kana nufin a ~Bible~ akwai ayoyi kan cewa, ubangiji daya ne?'
'sosai akwai, ke ba wani annabi da ubangiji ya aiko, face ya isar da wannan sakon na zaman ubangiji daya, bari mu leka littafin naku.'
Exodus 20:1-5 ' *and God spake all these words, saying 'I am the Lord thy God which have brought thee out of the land of Egyp, out of the house of bondag. thou shalt have no other gods before me. thou shalt not make unto thee any graven image, or any likeness of anything that is in heaven above or that is in the earth beneath or that is in the water under the earth. thou shall not bow down to them nor serve them: for I the Lord thy God am a jelous God........* (KING JAMES VERSION)
'Kinga wannan yankakkiyar hujja ce, domin kuwa ubangiji da kansa ne ya furta cewa shi kadai ne, har ya tsoratar ya kuma hana a dauki wani a matsayinsa, ko a bautawa hotuna kamar yadda kuke yi a yanzu.'
yana bayaninsa ita kuma tana kokarin karanta ayar da ya karanto mata.
'idan kuma muka tsallaka kadan ga abin da littafinku mai tsarki ya ce';
Deuteronomy 4:39 ' *know therefore this day, and consider it in thine heart, that yhe lord He is God in heaven above, and upon the earth beneath; there is none else'* (KING JAMES VERSION)
'kin ji ko a wannan ayar ~Bible~ ya tabbatar da cewa ubangiji ne kadai ba wani a sama ko a kasa. ina zancen su Annabi Isah kuma'?
'cikin wannan littafin an maimaita abinda na kawo maki daga littafin Exodus a sama, duba Deuteronomy 5:6-7'
'haka a wannan book na Deuteronomy 6:4 munkaranta daga bakin annabi Musa cewa ' *Hear or Israel, the lord our God is one Lord* (KING JAMES VERSION)
'Annabin Allah kenan Musa ke gaya muna cewa ubangiji daya ne'.
'ga wata hujja ta gaba.'
1chronicles 17:20 ' *o lord ther is none like thee, neither is there one God beside thee, acvording to all that we have heard with our ears*' (KJV)
'kinji daga littafinku, cewa ba wani ubangiji tare da Allah.'
'ga wata hujja ta gaba.'
Isaiah 43:10-13 ' *ye are my witnesses saith the lord and my servant whom i have chosen; that ye may know and believe me, and understand that i am He, before me, there was no god formed, neithet shall there be after me. I even i am the LORD and beside me there is no saviour.......*' (KJV)
'ubangiji da kansa ya sanar da mu cewa tun farko shi kadai ne, idan ba shi ba wani Allah, haka ba wani a tare da shi, kuma shi kadai zai yi ceto.'
tuni fuskar Fate ta jike da zufa duk da tagogin motar a bude suke kuma ga iska na shigowa sosai. cikin rawar murya, ta ce, 'wadannan hujjojin da ka kawo daga tsohon alkawari ne, ba aya ko daya da ta zo daga sabon alkawari'
cikin nuna alamar damuwa Aseeya da ke tun dazu saurarsu bayan da ta mayar da littafin da take karatu a kan cinainanta, ta ce, 'sabon alkawari kuma? me take nufi ne'? ta fada idanuwanta cike da kwadayin me zai fito daga bakin Ameer da ta kurawa idanu.
~'Bible~ an kasa shi ne gida biyu, duka littafin ~Bible~ yana dauke ne da littafai 66 daga cikinsu 39 na farko sune tsohon alkawari, su aka turowa Yahudawa, 27 ragowar kuwa su ne sabon alkawari, wadanda galibinsu malaman yahudawa masu fada da addinin annabi Isah ne suka rubuta.'
'na fahimta, amma sunada bambanci ne?'
'ko kusa, sai dai su kiristoci idan suna so su ratsewa gaskiya sukan ce sai abinda suka gani a sabon alkawari (new testament) kadai za suyi imani da shi. amma ai annabi Isah yayi maganin wannan matsalar.'
'ya fada a cikin sabon alkawari cewa, 'kar kuyi tunanin nazo ne na soke abubuwan da wasu annabawa suka zo da su, na,zo ne domin na cika su' a duba Mathew 5:17. kinga,kenan annabi Isah yayi umarni da ayi aiki da tsohon alkawari, amma har wa yau zanmata adalci, bari na bata hujjoji daga sabon alkawarin.'
duk wannan muhawarar da ke gudana, mahaya motar kowa ya kasa kunnuwansa ne yana saurara, sai mamakin Ameer suke yi.
har yanzu labarin bai hau hanya ba, saura kiris mu shiga labarin
ku biyo ni kawai
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣8⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
*Qoute of the day*
_Coming together is the beginning. Keeping together is progress. Working together is success._
*Shafin masoya*
_my partner Ummu Aleesha marubuciyar 'Yan Kwaleji da Wuya ba ta kisa, Allah ya baki lafiya, ya kuma barmin ke, ya kuma sa a rage fushi da ni, ameen_
_masoya wannan littafin ina jin dadin addu'o'inku hadi da shawarwarinku gare ni, ba shakka ni takarda ce kawai a kan iska, ku ne borina, Allah ya bar mu tare nagode da nunamin kauna da kuke yi_
*Waiwaye*
_A shafin da ya gabata, munji cewa ubangiji daya ne ko littafin ~Bible~ ya tabbatar da haka, haka mun ji yadda tsare-tsaren ~Bible~ yazo ta fuskar littafan da ke cikinsa, cewa 66 da shida ne, tsohon alkawari ke dauke da 39 sabon alkawari kuwa 27, munji yadda kiristoci ke kokarin bijirewa hujjoji daga tsohon alkawari idan suka sabawa abinda sukayi imani da shi, haka munji annabi Isah yayi umarni da a bi hukuncin da ke a tsohon alkawari_
*Ci gaba*
Daga cen Abdul Samad ya jefo tambaya; 'shin dama duk marubuci dole ne yasan ~Bible~ kamar yadda naji kana zuba da shawagi cikinsa haka?'
bayan Ameer ya murmusa, sai ya dan kara gyara zamansa kasancewar dama ya juyo daga kujerar gaba domin jin dadin yiwa Fate bayani yadda ya kamata.
'Ba dole ba ne kan marubuci yasan ~Bible~ amma shi ilimi kan duk wani abu dake doron kasa, yanada kyau a isko marubuci da abin fada kansa, ta yadda idan rubutu ya ja akalarsa a cen, zai yi bayani yadda ya dace.'
'idan inaso na ilmantu nasan ~Bible~ kamar kai ya zanyi'?
'ko kadan abokina ba wuya, da farko dai idan kana so ka san littafin kiristoci sosai, ka fara da hardace Qur'ani da harda mai karfi, ta yadda zaka iya fadar lambar sura da aya a ka, sai ka tabbatar kayi zurfi a karatun addini, musamman ulum da tauhidi, a isko zaka iya yin fira ta awanni da harshen larabci, sai a isko a kalla ka karanta ~Bible~ daga farko har karshe a kalla sau goma, kuma ka mallaki a kalla kalar ~Bible~ biyar, sai ka kokarta wurin hardace wurare masu muhimmanci daga gare shi, kuma ka jure wurin saurarar lectures na Ahmad Deedat, HUssaini Yusuf Mabera, Zainuddeen Zain, Dr. Zakir Naik da rubuce-rubucensu kan ~Bible~, Misali Deedat ya rubuta _The choice_ Yusuf Mabera ya rubuta _Muhammad in the ~Bible Zainuddeen Zain ya rubuta who was Jesus_Dr. Zakir ya rubuta _concept of God in major religions_ haka kowannensu ya gabatar da lectures da yawa kan ~Bible~. sai ka dage wurin research na rubutun manyan mutane irinsu Dr. Jamal Badawi da sauransu.'
'taff! Ashe aikin ja ne'
'kar ka sarye aboki, da xarar ka fara, za ka ji abin da sauki fiye da hadiyar tuwo'
Fate ce ta karbe zancen da su ke yi, ta ce; 'ku musulmi, bakwa ganin girman Yesu ko kadan, sai ku dinga yin magana kuna manta matsayinsa gaba daya, ga shi bakuyi imani da shi ba domin baku yarda da mu'u'jizojida ya nuna a rayuwarsa, wadanda su muke kallo har mu kira shi da ubangiji'
sai da ya yi shirun rabin minti kafin ya nisa, sai kuma ya saki murmushin da hakoransa ba wanda ya bayyana, sai ya mayar da kallonsa ya zuwa gareta, wacce, take sanye da guntun skirt iya cinyoyinta, duk da a zaune take, sarai cinainanta sun fito a fili, sai wata 'yar riga iya cibiya, wacce ake kira da arm less, ta gefe za a iya hango rabin mamanta, kanta kuwa cike yake da gashin kanti har gadon baya, ba dankwali a kanta. sai ya ce;
'kiristoci bakwa adalci a zancenku, da farko mu musulmi munyi imani da annabi Isah, mun yarda cewa mahaifiyarsa Maryam ta haifeshi ba tareda uba ba, mun yarda ya nuna mu'ujizoji da dama a rayuwarsa, musulunci ne kadai ya saka daga cikin Rukunnan Imani dole ayi Imani da annabawa, ba musulmin da zai cika musulmi matsawar bai yi imani da annabtar annabi Isah ba, muna girmamashi, shi yasa idan aka ambaci sunansa dole muce 'tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi' amma bamu yarda cewa shi ubangiji ne ko dan unangiji ba, kamar yadda kuke fada'
'kaji ai, shi yasa nace, ba kuyi imani da shi ba'
'dakata' Ameer ya fada yana kokarin fiddo mata da bayanai domin ta gamsu, 'mumfa yi imani kan cewa annabi Isah ya nuna mu'ujizoji da dama a rayuwarsa, amma ko kusa mu'ujizojin basu isa dalilai da za su sa mu kira shi da matsayin Allah ba, domin kuwa akwai annabawa da suma sun nuna mu'ujizoji wasu ma fiye da na shi, kinga kuwa idan mu'ujiza ce ma'aunin zama ubangiji, akwai 'yan takara, da yawa. misali; ga wasu daga mu'ujizojin Annabi Isah daga Littafinku:
John 11:38-44 mun karanta yadda annabi Isah ya tayar da Lazarus daga mutuwa
John 2:6-9 mun karanta yadda ya mayar da ruwa giya (abin mamaki)
Mark 6:30-44 mun karanta yadda ya ciyar da mutum dubu biyar da gurasa biyar da kifi daya
Mathew 8:14-17 mun karanta yadda ya warkar da mutane da dama
Mathew 9:27-31 mun karanta yadda ya warkar da makafi.
“mu musulmai munyi imani da duk wadannan mu’ujizojin, kuma mun yarda cewa annabi Isah ya aikata su duka, amma ko kusa basu isa su kai shi matsayi na zama Allah ba, saboda shi da kansa ya gayamuna a cikin littafinku cewa ba yin sa ba ne, Mathew 28:18 da John 5:30, haka peter a cinkin acts 2:22 ya tabbatar yin Allah ne ba annabi Isah ne yayi da kansa ba. Me za ki ce gameda wadannan?''
Ezekiel 37:1-14 ‘ *I felt the powerful presence of the loed, and his spirit took me and set me down in a valley where the ground was covered with bones. He led me all round the valley; an I could see that there were very many bones and that they were very dry. He said to me, “mortal man can these bones come back to life?” I replied “sovereign lord, only you can answer that!”. He said prophesy to the bones. Tell these dry bones to listen to the word of the lord. Tell them that I the sovereign lord am saying to them; I am going to put breath into you and bring you back to life, then you will know that I am the lord. So I prophesied as I had been told, while I was speaking, I heard rattling noise and the bones began to join together. While I watched, the bones were covered with sinews and muscles, and then with skin. But there was no breath in the bodies. God said to me “mortal man, prophesy to the wind, tell the wind that the sovereign lord commands it to come from every direction, to breath into these dead bodies and to bring them back to life. So I prophesied as I had been told, breath entered the bodies and they came to life and stood up. There were enough of them to form an army. God said to me “mortal man, the people of Israel are like these bones they said that they are dried up, without any hope and with no future so prophesy to my people Israel that I the sovereign lord I am going to open their graves, I am going to take them out they will know that I am the lord. I will put my breath in them bring them back to life and let them live in their own land. Then they will know that I am the lord I have promised that I will do this and I will, I the lord have spoken.*
Ga wani ya tayar da mutum sama da dubbai daga mutuwa, me yasa ba ku kira shi Allah ba?
1kings 17:21-22 ‘ *then Elijah stretched himself out on the boy three times and prayed “o Lord my God, restore this child back to life.!” The lord answered Elijah’s prayer; the child started breathing again and revived.*
Ga wani shima ya tayar da yaro daga mutuwa, me yasa kuka fidda shi daga takarar Allantaka?
2kings 4:32-35. Elisha ma ya tayar da yaro daga mutuwa.
A cen gaba a 2kings 13:20-21. Bayan Allah ya karbi rayuwar Elisha, shekaru da dama har ya zama kasusuwa zalla, sai aka zo za’a rufe wani da ya mutu, ashe a kabarin Elisha ne za’a sakashi ba tareda sanin mutane ba, ai ko ana sakashi a ramin yana taba kasusuwan Elisha sai ga shi ya taso daga mutuwa. Me yasa baku kira Elisha Allah ba, ko ba ya da galihu ne?'
Exodus 4:1-5 mun karanta yadda sandar Annabi Musa ta zama katon maciji. Idan mu’ujiza ke sa a kira mutum Allah annabi Musa fa?
2kings 6:18 mun karanta yada Elisha ya makantar da wasu mutane.
2kings 6:20 kuma ya bude masu idanuwansu, shi me yasa baku kira shi Allah ba?
ko wacce hujja ya kawo sai ya bata lokaci domin ta karanta a nata ~Bible~ din, ba Fate ba hatta mahayan motar jikinsu yayi sanyi, sai faman shafar zufar rashin gaskiya take yi, ganin ba tada abin fada, sai Ameer ya ce; ga hujjojin cewa ubangiji daya ne daga sabon alkawari kamar yadda kika nema.
har yanzu da saura kan labarin ya warware, saura kiris mu shiga labarin.
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣9⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
08034840276
*Quote of the day*
_In any situation, the best thing you can do is the right thing; the next best thing you can do is the wrong thing; the worst thing you can do is nothing._
*Shafin masoya*
Sumayya Musa
Prince Abdullahi
Sadie Smart
Subby
Star nucy
Aliyu Miko
*Waiwaye*
_A shafin da ya gabata, mun Ji cewa, marubuci yanada bukatar sanin fannoni da dama yadda sai Ji saukin yin bayani kan komai, haka munji wasu daga cikin matakai da ya kamata Maison ya ilmantuwa kan Bible sosai zai bi domin cinma burinsa. Haka munji daga littafin Bible mu'ujizoji da annabi Isah ya nuna, haka munga mu'ujizojin wasu annabawan, Wanda ya zama hujja kan Annabi Isah ba ubangiji ba Ne, sai dai hujjojin duka sun fito Ne daga tsohon alkawari, wato old testament._
*Ci gaba*
Ameer ya soma, 'Yahudawa sun tambayi annabi Isah a cikin ~Bible~ kan lokacin da kiyama za ta tsayu, sai ya basu amsa kamar haka; *'But of that day and hour, knoweth no man, no, not the angels of heaven but my father only. '*Mathew 24:36. (KJV)
'Tambaya a nan ita ce, idan da gaske shi ubangiji ne, ya aka yi baisan lokaci KO ranar da kiyama za ta tashi ba, idan kuwa ya sani tau karya ce ya yi musu da ya ce KO shi bai sani ba, ubangiji na fadar karya kuwa???'
Akwai lokacin da annabi Isah aka tambaye shi, kan wanne umarni na farko ya kamata a kiyaye, sai ya amsa kamar haka. ' *and jesus answered him, "the first of all the commandments is, hear o Israel, the Lord our God is one Lord"* mark 12:29 (KJV)
'Kin Ga nan Yesu ne da kansa Ke fadar ubangiji days ne. Ga wata hujja daga sabon alkawari'
'Annabi isah ne Ke yiwa mabiyansa addu'ah daga ciki Ga abinda ya ce';
*And this is the real and eternal life:*
*That theya know you,*
*The one and only true God,*
*And Jesus Christ, whom you sent* John 17:3 (HOLY BIBLE MESSAGE)
'Akwai ayoyi da dama da sukayi magana kan kadaitar ubangiji daga sabon alkawari'
'Bugu da Kari , hankali MA ba zai dauki cewa Annabi Isah ubangiji ba ne, misali; munkaranta a ~Bible~ cewa shi fa ubangiji ba mutum ba ne: Hosea 11:9 " *I will not execute my fierceness of mine anger, I will not return to destroy Ephraim. For I am Got not man...* (KJV)
numbers 23:19 " *God is not a man that He should lie, not the son of man that He should repent...* (KJV)
'awadannan ayoyin ubangiji ne ke gaya muna cewa shi ba mutum ba ne, Ki saurari wannan ayar;'
Acts 2:22 ' *Ye men of Israel, hear these words, Jesus of Nazareth, a man approved of God...* (KJV)
'Wannan sahabin annabi Isah ne Mai suna Peter ke gayamuna cewa Annabi Isah mutum ne, idan kuwa annabi Isah mutum ne kamar yadda muka ji daga ~Bible~ kuma muka ji daga ~Bible~ din cewa Ubangiji ba mutum ba ne, ta wacce hanya Annabi Isah zai zama ubangiji?'
'Munkaranta a littafin _Zabura_ da ke cikin ~Bible~ kamar haka;
' *Behold, He that keepeth Israel shall neither slumber nor sleep.'* Psalms 121:4 (KJV)
'A dayan bangare Kuma sai muka karanta kamar haka;
' *And behold, there arose a great tempest in the sea, insomuch that the ship was covered with the waves, but he (Jesus) was asleep*' mathew 8:24 (KJV)
'Idan har ubangiji ba ya barci kamar yadda ya zo a littafinku, shi kuwa annabi Isah ga shi yana barci, ashe hujja ce kan shi ba ubangiji ba ne'
'Ga hujja ta gaba'
Mathew 28:50 ' *Jesus, when he had cried again with a loud voice, yielded up the ghost*
'Ma'ana ya mutu kamar yadda kuke fada'
1timothy 6:15-16 ' *which in his time he shal shew, who is the blessed and only potentate, the king of kings, and the lord of lords. Who only hath immortality, dwelling in the light...*
~Bible~ ya ce Annabi Isah ya mutu, kuma ~Bible~ ya ce ubangiji ne kadai ke da rayuwar har abada, ashe ba hujja ba ce, kan shi Yesu ba ubangiji ba ne?
Munkaranta
Isaiah 40:18
Isaiah 40:25
Psalms 89:6
Cewa ba wani abu ko wata halitta da tayi kama da ubangiji.
Mathew 21:18-20
Mun karanta yadda yake jin yunwa har ya la'anci wani ice (fig tree) kan ya hango shi daga nesa ya zata akwai yaya a kansa da ya zo sai ya tarar ba komai. Shin ubangiji yanajin yunwa kuwa?
Munkaranta
Luke 23:41-43
Mathew 11:19
Cewa ya ci abinci, ubangiji na cin abinci ne?
John 11:35 munkaranta cewa yayi kuka, a ina ubangiji ya taba yin kuka?
'Ki nutsu sosai kafin lokaci ya kure maki, annabi Isah bawan Allah ne kuma manzonsa kamar yadda littafinku ya fada.'
Cikin murya ta rashin makama, ga idanunta sunyi ja sosai, ta ce, 'bab fahimta ba, a ina aka kira shi da bawan Allah kuma?'
'Ki duba wadannan ayoyin'
Acts 3:13 ' *the God of Abraham, Isaic and Jacob, the God of our ancestors, had given divine glory to His servant Jesus* (GOOD NEWS BIBLE)
cikin Saudi, muryarta na rawa ta ce, 'ba haka aka rubuta ba' ta fada dai dai lokacin da take kokarin nuna masa yadda ayar ta ke a nata littafan, kamar haka, _the lord of Abraham and of Isaic and of Jacob, hath glorified His son Jesus_ (KING JAMES VERSION) KJV
Bayan yayi murmushi, sai ya ceda ita, duba wannan sai ya bata GOOD NEWS BIBLE ta karanta ta Ga servant akarubuta, sai have tau wanne Zamu dauka cikin biyun?
Ki duba
Acts 4:27
Acts 4:30
Duka daga good news bible
Ko ki duba AMPLIFIED BIBLE
Kinga kuwa shi bawan ubangiji ne, bawa kuwa ba ubangiji ba ne.
A daidai lokacin suka karaso garin Bunza, garin fulani zan ce ko garin Gurumada (bayin fulani)
Fejin gaba zamu so labarinmu inshaAllah
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣0⃣
*the story is on the verge to start*
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza and Aseeya Abubakar Imam~
*Quote of the day*
_Throughout life people will make you mad, disrespect you and treat you bad. Let God deal with the things they do, cause hate in your heart will consume you too._
*Waiwaye*
_A shafin da ya gabata, munji cewa ubangiji daya ne daga sabon alkawari, haka munga hujjoji a hankalce daga ~Bible~ da za su tarwatsa tunanin cewa Yesu ubangiji ne, haka mungani daga littafin cewa shi bawan Allah ne, wanda wadannan hujjojin sun saka Fate cikin kogin tunani, mota ta karaso garin Bunza, daf da ana kiran magariba, kasancewar sun kamo hanya ne kusan karfe shida na yammaci, kuma ga tsaiko da suka samu na faci da tayarsu ta yi_
*Ci gaba*
Sai kallon gadar Bunza suke yi cike da ta'ajjubi, gada ce da dole ta kanta za ka bi kafin ka shiga garin, karkashin gadar ruwa ne masu gudu rani da damina, nan galibi mazauna garin ke kamun kifi, a kusa da ruwan kuwa a nan 'yan makarantar kawan (GTC) da (GWANDU BUNZA) ke yin wanki a ranakun karshen sati, akwai dadi sosai a rayuwar garin. Suka ci gaba da tafiya har suka karaso tasha, suka iso a junction wanda zai iya sadaka dagarin Zogirma da Tilli, a nan suka ajiye mota, da cewar za suyi sallah, Fate ba tada abin fada ganin ita kadai ce ba musulma ba, nan ta fito bakin mota domin ta jira dawowarsu, Aseeya kuwa sai ta shiga unguwar fulani da ke kusa da wurin ta nemi wani gida ta shiga domin ta sauke farali, inda mazajen sai sauri suke yi. Domin samun jam'i ganin an kusa tada salla, a massalacin da ke hannun dama da junction din.
Shigar Aseeya gidan da ta nufa, ta yi sallama, amma shiru, sai cen wata yarinya karama ta karba sallamar, sai ta ce; 'ina mahaifanki?' 'Suna ciki' yarinyar ta fada cikin muryar fulani, Hausar na kokarin subuce mata, 'je ki ce ga bakuwa a waje' bayan mahsifiyar yarinyar ta fito, sai ta gayamata dalilin zowanta, cikin murna ta tarye ta, ta umarci yarinyar da ta dauko mata ruwa a buta, ita kuwa sai ta shiga daki ta dauko tabarma da sallaya bayan da ta nuna mata kujera ta ce ta zauna kafin ta fito, tana yin shimfidar sallar ita kuwa tana yin alwala, daga kammala alwalar sai ta fara sallah.
Fate kuwa da ke tsaye a jikin mota, sai dube-dube take, wurin ya burge ta yadda masu saye da sayarwa suka cika wurin, kama daga 'yan talla masu sayar da fura da ma masu tireda, ta juyo ta kara yiwa hanyar Zogirma kallo, a ranta tana cewa, 'yo ina wannan hanyar kuma za ta bula?' Sai zuccin hadin kan musulmi take na ganin ba wanda ya musa cikinsu da zancen sallah ya zo, harda masifaffiya Aseeya kuwa, a ranta ta ce lallai za ta tambayi Ameer gameda wannan sallar.
Bayan Aseeya ta kammala sallah, matar gidan ta ajiye mata fura da nono make da wata kwarya, sai wani ludayin karfe da bakinsa ba girma, ko kadan ba ta so ta tsaya ba, amma furar ta ja hankalinta domin har wani tsam ke kaiwa a tsukakken bakinta. Tana shan furar suna fira. 'Ke kuwa me za ki je yi Kamba?' 'Aiki ne zai kai ni, tareda ziyara, kasancewar munada 'yan uwa a cen' 'kin burge ni ne, domin yanzu mata ba su cika kula sallah ba, amma ke a halin tafiya ga shi kin kyla, haka muje ta fama da su, har mu da ke kauyen chatting duk ya karbe musuluncin' 'Allah ya kyauta ta fada a dai dai lokacin da take kai ludan a baki.
Da ta kammala shan furar, ta wanke bakinta, da gefen zanenta inda furar ta bata, cikin sakin fuska, ta kira karamar yarinyar da ta aika farkon shigowar ta gidan, ta rike ta a jijinta, 'me ye sunanki?' 'Hauwa' ta fada sai faman wasa take da kafafuwanta, ta saka hannu a jaka ta dauko kudi ta mika mata, yarinyar ta kalli mahaifiyarta, sai ta galla mata harara, ganin haka, yarinyar ta sunkuyar da kai, sai Aseeya ta juyo gun mahaifiyar ta ce; 'haba ya za ki hana ta karba, ai kyauta ce na bata' 'kina dai so ne ki biya kudin fura da kika sha' 'haba ya za ki fadi haka?' Da kyar ta samu ta aminta diyar ta karba, suka yi sallama ta dawo inda aka ajiye mota, ta yi sa'a kuwa Fate kadai ta tarar tsaye jingine a jikin motar, bayan wasu mintuka sauran suka dawo driver ya dauki hanya.
Sai firarsu suke yi, har suka wuce garin DUTSEN KURA suka wuce BALU KARAMA, daf da shiga garin GEZA, suka hango fitillu sai haskaka Jeji ake yi da su, tsohon da ke tare da su ne ya ce su dakata yana fa ganin wadancen fitillun ba na lafiya ba ne, Aseeya ta kece da dariya, tace 'Baba, me yasa ku dattijawa kuke tsoron mutuwa' 'diyata ai kinsan wanda ya riga ka kwanciya ana tunanin ya riga ka tashi, ku yarda da ni wadancen fitillun ba na lafiya ba ne,' driver ya katse zancen, 'ya kuke ganin ya dace mu yi' ya fadi haka ne bayan ya sami wuri ya ajiye motar, daga cen suka hango masu fitillun aguje zuwa wurinsu, bude hasken mota da zai yi, suka gansu dauke da manyan bindigogi kuma ga su kartin gaske, ya so ya tada mota ta ki,wurin sauri makulli ya fita ya fadi, ganin haka ya fada da karfi 'wallahi muyi ta kanmu' wannan ya fadawa wannan, wannan ya hau jikin wannan, da kyar suka fita motar, suka runtuma cijin *JEJI* sai gudu suke ba tareda sanin inda za su nu fa ba, haka suma 'yan fashin suka biyo su cikin *JEJIN*
Aseeya ta kama hannun Ameer gam dama tun fitowa motar ta cakumi rigarsa, sai gudu suke suna waiwaye, kamar wadanda rayukansu za su fita.
Kusan gudun minti arba'in suka yi na fitar rai cikin jeji gaba daya tufafin jikinsu sun bice da turba hadi da kayoyi, suna cikin gudu, kafar Aseeya ta fada cikin wani karamin rami, fizgawa da zatayi, ta sami targade kafar ta gusde, ta rafka ihu wanda komai rashin imanin mutum dole ya tausaya mata, ta fadi sai sharbar kuka take.
Cikin tausayawa Ameer ya duka domin ya taimakamata, ya umarci sauran mutanen da su wucewarsu kawai, za su same su a gaba.
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣1⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza and Aseeya Abubakar Imam~
*Quote of the day*
_Start by doing what is necessary, then what is possible, and suddenly you are doing the impossible._
*Waiwaye*
_A shafin da yaa gaabata munji yadda suka tsaya sukayi sallah a garin Bunza, daga bisani suka ci gaba da tafiya har Allah ya karaso da su kusa daa gaarin Geza, inda suka kicime da ‘yan fashi, wanda hakan ta yi sanadiyyar suka runtuma cikin jejei da cikinsu a wanda yasan ina za a nufa, munji cewa Aseeya ta sami gusdewa a kafa, sanadiyyar kafarta da t shige a wani karamin rami, hak munji sauran sun ci gaba da gudu, inda Ameer ya tsaya domin ya taimakawa Aseeya._
*Ci gaba*
“kiyi hakuri” Ameer ya fada cike da tausaya mata, ya dauke ta ya karaso da ita daf da wani ice mai girma sosai, ya jinginar daa ita, ita kuwa sai faman zubdaa hawaye ta ke, shi kuwa ba abinda yake yi sai kokarin rarrasarta, ya ja mata kafar sai ihu take rusawa, wanda yayi sanadiyyar karkatowar ‘yan fashin ya zuwa gefen da suke, ‘yan fashin dais u uku ne, ko wanne majiyi karfi, kuma rike da bindiga, a haannu dayaa kuwa fitila mai masifaffen haske, da idan aka dalla maka it a idanu, zak daina gani na tsawon minti talatin idan cikin dare ne. ‘yan fashin suka fara biyu sautin kuwwar Aseeya har suka zo daf da su, jin sautin tafiyarsu sai Ameer ya sa hannu ya taushe mata baki, ya yi mata alaama da hannu daya kan tyi shu, gyada masa kaai kawai tayi cikin matsanancin jin zafi, ga idanunta sunyi jajur hawaye kuwa har a kumatu. Daya dgaa cikin ‘yan fashin ya karaso kusa da su, ya hango su, yana dariyar mugunta tareda nunawa Ameer bindiga, yace “idan ka daga zan harbe ka,” nan Ameeer ya dg duka hanneyansa biyu sama, alamar y mika wuya. Ganin haka said an fashin ya karaso, Allah da ikonsa, yana zowa daf da su, sai wani haske ya fito daga cikin wannan babban ice, ya tsinkewa danfashi kai, ya fadi matacce sai shure shure yake, jini kuwa y dinga tsartowa daga wuyansa, ganin haka Ameer ya suri Aseeya ya goya, ya ci gaba da gudu, sai haki yake yi, ga nauyinta ga tsoron ‘yan fashi g rudewa kan abinda ya faru, ga shi baisan ina ne hanya ba, ina zai cinma ‘yan uwansu duk bai sani ba. Sauran ‘yan fashin da suka ga abinda ya faaru da dan’uwansu suka runtuma da gudu, da zinmar su fita jejin, domin sun ji a trihi cewa ba wnda ya taba shiga jejin ya fita da ransa, shi yasa aka yiwa jejin lakabi d suna BAKIN JEJI, nn suka fara da na sanin kawo kawunansu cikin wannan masifa, hk suka dinga gudu domin neman hanyar fita, tuni sun fit baatun su aseeya.
Su Fate kuwa da suka ci gaba da gudu basu tsaya ko’ina ba har sai da suka cinma wani babban dutse, mai kogo, dutsen yanada sha’awa sosai kuma ga shi da girma da tsayi sosai, a jikin dutsen ramu ne na manyan namun jeji da suk zauna a kogon shekaru d suka shude, ba tareda ko shawaraa ba su duka suka faada cikin kogon dutsen, sai haki suke, kamar rayukansu za su fita.
Dattijo ne ya ce “su wadancen da muka baro ko wanne hali suke yanzu” wannan jejin yana dauke da manyana aljanu da namun jeji, saboda haka dole mu kula idan muna so mu tsira”
Cikin tsoro Abdulsamad ya ce “kana nufin akwai namun jeji a wannan jejin? Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’un, mutuwarmu ce ta zo Saddam shi kenan ta mu ta kare” ya fada har da kukansa. Duk da dariya ta so ta kubucewa Saddaam ganin abokinsa da gske yake ya firgit sai ya shiga rarrashinsa da kwantar masa da hankali, d kyar ya samu ya shawo kansa. Driver da Fate kuwa kamar wadanda aka saka azumin magana, Fate dai gefe kawai ta koma ta bjingina jikinta a jikin wani dutse, ta rungume jikinta da hannayenta, duk da jikinta da zufar gudun da sukayi, masifaar sanyi ta kunnomataa kai, kasancewar fiye da rbin jikinta a waje ne, kuma gas shi lokacin sanyi ne, ganin sun share sama da minti hamsin a kogon, ga shi basu ji maaotsin su ameer ba, sai tsohon ya cewa Driver, “muje mu duba wadannan yaran ko lafiya” “haba dattijo, idan faa ana ta kai, ba a zancen ta kaya, ko mu ya muka isal bare mu ce z mu fita duba lafiyar wasu, naga alamun yaron ai yanada hazaka sosai b shakka zai kubutar da su” “haba driver kai fa ne ka fada dazu a lokcin daa ka canja taya, cewa amanarmu aka baka daga gareji, amanar kaa ajiye ne?” ba da son ransa ba dole ya bi tsoho suka fito nemansu Aseeya.
Gudu yayi gudu, Ameer ya gaji suka fadi, kafarta ta kar buguwa kasa, ta sake sakin wani sabon kuka, cikin kukan ta fara masa masifa “halaka ni kake so kayi ne, ji yadda ka zo k kadaa ni cikin wannan ciyawa mai masifr kaikayi, ga kafar twu kanaso ka ida hallakani, kai wanne irin mutum ne da baisan daraaja ko tausayin mutane ba?” cikin rashin sanin me zai ce da ita ya kalleta sai fada da masifa take zuba masa, ya sake treating kafar, duk da masifarta bai kula ta ba, zuwa wani lokaci ya ce, “tashi mu je” “mu je ina, kalli fa ynayin d naake ciki, an gayamaka zan iyaa takawa ne?” bayan ya saki murmushin da iya karsa labatansa, ya ce, “sosai za ki iya takawa, idan kika bari kafar taa rike ko tayi nauyi, muna cikin hadari domin za sui ya cinmuna, kuma kalla ki ga” ya nuna mata, duk da akwai duhu sosai, ta fahimci tabbas suna cikan jeji ne da ga alama jejin akwai hadari. “idan baki taso ba, namun jeji za sui ya tarar da mu” dole ta tashi ta bishi, sai dingishi take yi, da kyar take taka kafar.
Tsoho kuwa da ya ga basu gansu ba, suka dawo gudun kar suma su bata.
Me zai faru, ku biyo ni dai, yanzu labarin y fara………
0 comments:
Post a Comment