*Waiwaye*
_A shafin da ya gaabata munji abin da ya faru da daya daga cikin ‘yan fashi na rasa rayuwarsa, wnda ya yi snadiyyar firgitar sauran ‘yan fashin guda biyu har suka ja da baya domin neman matsera daga daga wannan *BAKIN JEJIN*. Haka munji cewa har yanzu su Ameer ba su sami cinma abokani tfiyrsu ba, mun kuma ji kadn daga cikin hatsaruka da wannan Jejin ya kunsa._
*Ci gaba*
Si gudu suke yi har suka wurgar da bindigoginsu ba tare da su sani ba, firgice cikin tsoro na tashin haankalin da idanuwansu suka gane musu, haka tuni ‘yan fitilun da ke hannayensu suka fadi, sai gudu suke cikin surkukin jeji ba tareda sanin ina za su aza kafafuwansu ba, wani sa’in su kauri ice, wani sa’in su fadi, a haka dai suka yiwa jikinssu rauni sosai. Suna cikin gudu sai suka kawo daf da wani kogi, kogin ba ya da yawan ruwa, amma ruwan suna wucewa ne da karfi, kasncewar ba haske, saura kiris su fada ciki, sai suka taka birki, danfashin da ke gaba, sai ya fara taka duwarwatsu da ke cikin ruwan da niyyar ya tsallaka, ai ko kafarsa na tab ruwan, abokinsa da ke kusa yana jiran idan ya tsallake ya biyo baynsa, gani kawai yayi ya bata, kamar a film, ganin haka kuwa, ya ce kafa me na ci bambaki ba, gudu ya dawo sabo, gaba daya gajiyar da yake ji ta kau, ya sake dawowa baya a gigice a guje, sai waiwaye yake cikin gudunsa.
Shigowarsu a kogon Fate cikin rawar muryar sanyi ta ce “kun gansu ne?” “ko kusa, muma dawowa mukayi gudun kar ayi biyu babu” inji dattijo ya fada daidai lokacin da yake kokarin dube-dube da lalube-lalube kasancewar a kogon iyaka k hango duhun mutum, saboda dare da ya shigo kuma gas u a kogo. “baba me kake nema haka” Saddam ya fada, “yaro ina neman duwatsu ne domin na hasa muna wuta ko ma rage jin sanyi, ku je waje ku nemo mana itace, watakil ta sandiyyar wutar abokaninmu su dawo idan suka hango hasken” “ba damuwa Saddam yaa fada” a daidai lokacin da yake jan hannun abokinsa, suka fita suka dawo da itace, dattijo ya hada kawunan itacen da suka kawo sai ya dinga buga duwatsu guda biyu da ke hannunsa ta hanyar hada su da juna, bayan ya cika tsakiyar itacen da yanga (ciyawu da suka fara zama ice) bayan wani lokaci sai wuta ta kama, ai ko nan suka zagaye wutar. Nan suka zagaye wutar domin su duma jikinsu, nan fira ta fara kamar ba wadanda ke cikin damuwa ba. Tsohon ne ya nemi kowa da ya bayar da tarihinsa ta yadda zasu debewa juna kewa da mantar da kawunansu hadarin da suke ciki, inda Fate ta soma.
Su Ameer kuwa sai tafiya suke yi ga tsoron ‘yan fashi, g tsoron abind suka gani na mutuwar danfashi daya, ga takaicin rashin ganin abokanin tafiyarsu ina za su nufa ma basu sani ba, suka nutsa cikin jeji, sai dingishi Aseeya ke yi, ga masifafr ciwo, har kafr ta fara kumbura, suna cikin tafiya suka jiwo kukan da gurnani, cikin muryar tsoro Ameer ya ce, “muyi ta kanmu wannan muryar Damisa ce” ai ko nan gaban Aseeya ya yanke ya fadi sai ta ji kamar wacce aka sakawa super glue a kafafuwa, ta kasa ko motsi kan rudewa, kamar mahaukaciya, sai sambatu take kan firgicewa, gnin haka, ya ja hannunta suka ci gaba da tafiya duk da a cike yake da tsoron kar Damisar ta tarar da su, ba yadd zai yi domin ba zai iya barinta a wannan yanayin ba. Suka ci gaba da tafiya har suka karaso kan wani dan hayi, sai ya taka hayin domin ya ga ko zai iya hango wani abu, ai ko nan ya hango haske na fitowa daga cikin wani kogo, nesa da su, cikin murna ya juyo wurinta wacce dole k tusaya mata idan ka kalleta, ya ce da ita “Alhamdulilah, kin ga zo ki ga” da kyar ta samu ta haye hayin, t hango hasken ita ma, si y ce “inshaAllahu abokaninmu ne a wurin, sai mu hanzarta domin ganin mun isa gare su” “taff! Lallai mutuminnan ko kadan ba ka da tunani, kai imbanda rashin sani ciwon kai, duk masifarnan da muka fada, kuma so kake mu sake kai kawunanmu a hallaka? Ina mukasan su waye a cen, yanzu idan ‘yan fashi ne fa da ke biyarmu ko wasu mugaye?” “ba ‘yan fashi ba ne, domin mumbaro su a baya, idan kuwa mugaye ne kaddararmu kenan, ba mu isa mu tsallaketa ba, bari in tambayeki, hala fitowar da kika yi daga gida, kin tsarawa kanki cewa hakan za ta faru da ke? Amma sai ga shi ta faru, kuma baki isa ki hana faruwar hakan ba, ke bar wa ubangiji komai mu je mu duba” “wannan fa ganganci ne, a tsakiyar jeji fa muke kake tunanin wadancen wai mutanen kirki ne, me yasa wai ku marubuta bakwa da tunani ne? ni fa ba inda zan je” ta fada daidai lokacin da take kokarin zaunawa. Sai ya ce da ita “ba damuwa, ki zauna a nan, ni zan je in dibo ko ma meye ko su waye, sai in dawo in sanar da ke” “kaji wani rashi hankali, wa za ka bari a nan shi kadai? Wallahi ko kusa, ba in da za ka je, muna nan tare, muyi kwanciyarmu nan kawai” “wai ke wacce iri ce? Nan fa ko sanyinsa kadai zai iya illata mu, dubi yanayin kafarki, wasu lokuta fa sai ka gwada aikata abu mai hatsari kafin kayi nasarar cinma burinka” “kai ake ji” ta fada bayan da ta kara gyara zamanta. Ya kalleta cike da haushi, ga shi ba zai iya barinta nan ba, dole ya hakura.
Dayan danfashin kuwa sai gudu yake kamar ransa zai fitaba tareda sanin ina zai nufa ba, yana cikin gudu yayi kicibis da Damisar da su Ameer suka jiwo kukanta, ai ko ya sake dora sabon gudu, amma ina kafin ya je ko’ina ta kama shi, kuwwar da ya saka, ita ta farkar da Aseeya daga angaje (gyngyadi) da ta fara, cikin rashin ida wartsakewa ta kalli Ameer ta ce “kuwwar wan a ji haka?” ya ce “ya zakimin wannan tambayar, in ce tareda ke muke wuri daya tun fitowarmu daga tasha? Kawai dai naji kukan Damisa, sai kuwwar wani” cikin tsoro ta mike tsaye, “don Allah tashi mu tafi” ba tareda ya ce da ita komai ba, ya tashi suka tafi, tinkis-tinkis har suka karaso a kogon, shigarsu gaba daya ‘yan wurin suka kaure da murna, suka sami wuri suka zauna, sai Ameer ya kalle su, ya ce “kun yu sallah kuwa?” suka amsa da “a a” sai ya ce “ku tashi muyi sallah” “ina ruwan alwala”? in ji Saddam. “taimama za mu yi abokina” suka tashi sukayi taimama har da Aseeya suka gabatar da sallar Isha, Fate ce ta tamabye su daga kammala sallar ta su, “wai ku me nene wannan sallar da duk da kuna cikin wannan hadarin sai da kuka yi ta?” Ameer ya karbe, “sallah ita ce rukuni na biyu a addinin musulunci, wajibi ce kan duk wani musulmi matsawar yana bisa hankalinsa, inaga wannan kadai ya ishi tambayar ta ki” “yawwa tsoho ya fada, kun zo dai dai lokacin da muke gabatar da tarihin junanmu, Fate muna saurarenki”.
Wa cece Fate?
Za mu ji a shafin gaba
DR zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣3⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
08034840276
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
*Quote of the day*
_Any man who reads too much and uses his own brain too little falls into lazy habits of thinking_
*SHAFIN MASOYA*
_Fa’iza A Umar Keffi_. Ina godiya kuma Allah ya kawo maki mafita
_Maryam Mustapha Borno_. Ubangiji ya baki lafiya na gode, duk da rashin laafiyaarki kina bibiyar littfaina
_Qurratul Ayn_
_Zuwairat Madara_. Sarkin surutu
_Raheem Jega_
*Waiwaye*
A shafin da ya gabata, mun ji yadda duka yan fashin suka rasa rayukansu cikin wannan jejin, haka munji abinda ya sami Aseeya na sake jin ciwo a cikin raunin da ta yi, munji yadda ayarin driver da mutanensa suka yada zango cikin kogo a tsakiyar jeji har suka yanke shawar kowa ya bayar da tarihi game da kansa ko Allah zai sa hankulansu su kwanta, wanda daf da fara haka sai ga su Ameer sun iso, inda hasken wutar da suka kunna ya masu jagora.
*Ci gaba*
Gaba daya kogon sai ya yi tsit, ba abinda kake iya jiyowa sai numfashi da karar kararuwa da ke konew a cikin wuta, a dayan bngare kuma zukatansu sai bugawa suke yi a hankali, Aseeya da ke jingine a kogon ta mike kaffuwanta gaba daya hankalinta ya dawo kan Fate da ke shirin fara magana bayan ta dauki wani lokaci kan ta kimtsa.
“sunana Fate, ni haifaffiyar garin Fakai ce, mu uku mahaifinmu maisuna Danladi ya Haifa ni ce ta karshe, na girma ne a garin Birnin Kebbi sanadiyyar mutuwar mahaifiyata tun inada shekaru tara, wannan shi yasa kulawa da yaro zai samu yadda ya kamata na rasa ta, amma wannan bai hana na sami ilimi ba ta fannin boko da addininmu na kiristanci, na karanci Diploma a fannin accounting haka ni mace ce mai son addinina sosai. Na bambanta da sauran yayyena guda biyu, micheal da Richel, Richel ta fi karkata da sana’ar waka, inda mike yake harkar kasuwanci na saye da sayarwa, ksancewar mu haifaffun zuru ne da mahaifiyata da mahaifina duka dakarkari ne, muma da wannan muka tashi.
Aseeya ce ta karbe, “ashe kin iya dakarci?”
“sosai na iya, in banda ke ai Barewa ba za ta yi gudu ba ‘yarta kuma tayi rairafe, bare mu Dakkarawa, ba ma sake yarenmu, mumba shi muhimmanci sosai.”
“me za ki je yi a garin Kamba?”
“eh tau, bn yi niyyar sanar da ku ba, amm tun da haka abin y zo, yanad kyau kusan me zai kai ni garin Kamba, mu kiristoci munada bangare uku na kiristanci, amma gudu biyu ne suka fi shahara a duniya da aa nan Nigeria, akwai catholic (katolika) akwai protestant, ni ina daga cikin protestant, an turo ni ne domin na cika aikin missionary, na kokarta wurin samun zama har a aminta da ni sai gayyarmu ta zo a hankali mu dinga yada addininmu, kafin a ahama ‘yan kauye sun karbi kiristanci sosai, mukan yi haka ta fuskar baiwa talakawa kudi da tufafin sakawa ko abinci”
Aseeya taa yi ajiyar zuciya, ta mayar da kallonta ya zuwa ga sauran jaama’ar da ke cikin kogon, wadanda ke zaune zugum kowa yaa rasa abin furtawa, sai ta ce, “abin mamaki, aikin da ya kamata a isko mu musulmi muna yi, yau shi kuke yi, shi yasa wani wanda ba ya da addini ya ce, “da ace musulmi ne ke kashe kudi domin su rusar da kiristanci yadda kiristoci ke kashewa domin su rusar da musulunci, da yanzu ba kirista ko daya a doron duniya”, kirista kuna kokari wurin bata dukiyarku da lokacinku wurin abinda ba gaskiya ba, amma mu musulmi gamu kan gaskiya, sai dai mun kasa mu nuna hakan”
Fate bayan ta nisa cikin murmushi sai ta ce, ‘me kike nufi da ba ma kan gaskiya? Ki kalla ki ga duk inda aka ce ga ‘yan ta’adda a duniya, zaki ga musulmi ne, kalli Saddam Hussaini, kalli Osama ki kalli kungiyoyi irinsu Alqa’ida irinsu Boko Haram da sauransu, idan addininku addinin gaskiya ne, me yasa kuke ta’addanci da kisan wadanda ba ruwansu?”
Har Aseeya za ta amsa mata, sai t yi shu, ji da ta yi Ameer ya yi gyaran murya, sai ya ce. “ba zan ga laifinki ba saboda abinda aka sanar da ke kenan game da musulmi, amma bari na tambaye ki, wa ye ya fi kowa kisan mutane a duniya? Idan baki sani ba shi ne Adolf Hitler, Adolf Hitler ya kashe yahudawa kadai sama da miliyaan shida, bakya bukatar na sanar da ke cewa ba musulmi ba ne kirista ne wanda ya girma hannun manyan kiristoci. Mutum na biyu da ya ya fi kowa kisan mutane a duniya shi ne Mussoliyni, shima kirista ne, me yasa ba ku jingina abubuwan da suka aikata da addininku na kiristanci ba, kuke kokarin kirkirawa wasu sharri? Bazan yi musu da ke ba, a musulmi akwai ‘yan ta’aadda, haka a kiristoci ma akwi ‘yan ta’adda, amma a kur’ani babu aya ko daya da ta karfafa ayi ta’addanci a surah ta 6 aya ta 151 a cikin kur’ani maigirma mun karnta inda Ubangiji ya harmta kisan rai, haka a sura ta 17 ay ta 33 nan ma ubaangiji ya haaramta kisan rai……” “dakata” Fate ta fada baayan ta daag masa da hannu, “littafinku kuwa yayi umarni da ayi kisa” cike da mamaki su Abdul samad sai kallonta suke yi. Ameer ya ce “ina saurarenki, ina ne littafinmu ya yi umarni da ayi kisa?” “ ka duba littafinku sura ta 9 aya ta 5 inda ubangijinku ya ce duk inda kuka ga mushriki ku kashe shi..” Ameer ya yi murmushi ya ce ”tabbas akwa wannan bangaren a ayar, amma baki karanto abinda ke bayan ayar ba, sai kuma ki hada shi da zancen da ke gaba ba, abin da ya faru shi ne, alkawari akayi tsaknin musulmi da kafirai kan yaki, shi ne kafirai suka karya alkawarin, tunda mushrikai sun karya alkawarinsu, shi ne ubangiji ke cewa idan kuka gan su ku yakesu din ku kashe su, a aya ta 6 cewa yayi ai idan mushriki yanaso ka ba shi kariya ka bashi kuma ka jiyar da shi zancen Allah, sa’annan ka rikaye shi har inda zai sami aminci. Idan kika saurara sam musulunci ba addinin da yakai shi adalci da nuna tausayi, ana karaantomaku ayoyi ne ba bisa ka’ida ba. Amma idan kika duba littafinku, kika ga yadda ake umarni da ta’addanci sai ke da kanki kin tsani littafin naku”
“me kake so ka fada?”
Ta fada cikin firgita
“inaso ince da ke, duk duniya baa littafi da ya kunshi ayi ta’addanci kusa ma da yadda littafinku ya yi umarni”
“ko za ka iya nunamin?”
“sosai kuwa. Ki duba a cikin Bible Ezekiel 9:5 ‘ *pass through the city after him, and smite; your eyes shall not spare, and you shall show no pity; slay old men outright, young men and maidens, little children and women*……(REVISED STANDARD VERSION) kinji yadda littafinku yayi umarni da a kashe tsofaffi da yara da mata, mu a musulunci ko yaki ta kama ayi, ba a kashe tsofaffi ko yara ko mata, sai idan suma sun dauki makami suna kisan mutane, ga ta’addanci karara a littafinku, a aya ta 7 munji yadda ya cika umarnin da aka ba shi.
Ga wata hujja. A cikin littafinku book of Numbers 31:1-7 mun karanta yadda ubangiji a fadar littafin naku ya umarci annabi Musa da ya je ya yaki Madians, inda ya je kuma ya kashe su har sarakunansu, ashe kisa takan kama ne, ko kuwa duk inda akayi kisa ta’addanci ne malama FATE?
Ga wata hujja. Munkaranta a book of Joshua 6:16-20 cewa ubangiji ya basu kasa, saboda haka su je su kashe duk wanda ke ciki banda wata mata da mabiyanta. Shi kuma wannan kisa na meye?
Ayoyin sun da yawa, bana so naa tsawaita, kinga kuwa mu musulmi ke da bakin kiranku ‘yan ta’adda ba ku ku kiramu da sunan ba, matsalar da aka samu, ku kunfimu bakin yayata maganganu koda kuwa bakwad a hujja, amma kisani ba wani addini da yakai musulmi son zama lafiya”
Ta yi murmushi, sai ta ce “naji duk abinda ka fada, amma idan addinku na gaskiya ne, me yasa binciken kimiyya (science) bai zo ba a littafinku?”
Ameer ya saki murmushi, a lokac daya suka had idanu da Aseeya mai kokarin gyar zamanta, sai ya ce” sosai littafinmu yana dauke da kimiyyar zamaani, ke ba wata ingantacciyar kimiyya face tana cikin littafinmu……..
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣4⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_A life spent mking mistakes is not only more honorable, but more useful than a life spent doing nothing_
*waiwaye*
_A shafin d y gabata, munji a gurguje wa cece fate, haka munji hojjoji kan cewa musulunci ba addini ne na ta’addanci ba, hasali ma addinin kiristoci shi yake da wannan a cikinsa._
*ci gaba*
Fate cike da mamaki ta kura masa idanu, a lokacin ne Saddam ya kara itace cikin wuta, ganin wutar t fara yi kasa, driver kuwa tuni ya fara angaje, daga waje kuwa, ba abinda zai cika kunnuwanka irin kuka na mugayen kwari da dabbobi
“Bincike mai dauke da mamaki wanda yaa girgiza duniyar kimiyya shi ne, THEORY OF RELATIVITY OF TIME ba shakka wannan thery din ya daga duniyar kimiyya”
Cikin fuskar rashin sani, Aseeya ta tambaya, “me ye kuma theory of relativity of time, me ye alakarsa da firar da ake yi?”
Sai da ya yi murmushi sai y amsa
“ *RELATIVITY OF TIME*: shi ne, bambancin lokutta saboda banbancin wurare, ina nufin lokaci yakanyi gudu a wasu wurare da sauri fiye da wadansu wuraren, inda zaka ga kwanaki kaza a wasu wurare sune kila rabin yini a wani wuri, binciken zamani ya tabbatar da haka saboda wasu dalilai (mass and velocity). Nasan muna sane da planets da muke da su, zakaga a wadansu planets kwanaki da yawa su ne kwana daya a wadansu saboda lokaci yafi gudu a wadansu planets fiye da wasu. Kamar haka: MERCURY tafi kowacce planet zama kusa da rana kwanaki 88 ne kwana daya a tamu planet (EARTH). VENUS kwanaki 243 ne kwana daya na EARTH. EARTH kwana daya ne awa ashirin da hudu. MARS awanni 24.6 ne kwana daya a EARTH. JUPITER shekaru 12 ne kwana daya a EARTH. SATURN ita ma shekaru 12 ne kwana daya na EARTH. URANUS shekaru 84 ne kwana daya a EARTH. NEPTUNE shekaru 165 ne kwana daya na EARTH. PLUTO shekaru 248 ne kwana daya a EARTH.
A farkon karni na ashirin (early 20th century) Albert Einstein ya kawo wannan binciken har duniyar kimiyya ta bashi matsayi na (greatest thinker of the twentieth century) ya kuma samu daukaka ta (second best scientist in the world). Amma ni a wurina ana ci ne ana mantawa da hannu.
Sama da shekaru 1400 Qura’ni yayi bayani mai gamsarwa kan wannan theory na relativity of time har da kawo misalai.
Qurani 22:47 “ *…………..kuma lallai ne, yini daya a wurin ubangijinka kamar shekaru dubu yake daga abinda kuke kidayawa”*.
Wannan ayar ta sauka ne lokacin da mushrikan makka ke hurawa annabi wuta kan lallai a gaggauta kawomusu azaba, shi ne ubangiji ya basu martini. “kuma suna neman kayi gaggawa da azaba, alhali kuwa Allah ba zai saba wa’adinsa ba….” Su sani wunin da Allah yayi musu alkawari shekaru dubu ne a nasu kirgin (kidaya). Anan muka fahimci kenan akwai inda shekarunsu dubu shi ne wuni daya a wani wuri.
Qur’ani 32:5 “ *yana shirya al’amari daga sama zuwa ga kasa sa’annan ya taka zuwa gare shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shekaru dubu ne ga abinda kuke lissafawa”*
Qur’ani 70:4 “ *mala’iku da ruhi (Jibrilu) suna takwa zuwa gare shi, a cikin yini wanda gwargwadon shekaru dubu hamsin ne”*.
wanan bambancin lokacin ya bambanta da biyun farko, duk da shi yana bayani ne kan wani yini da mala’iku zasu sauko kuma Allah baice a namu kidanyawa ba, shike nuna wurin ya banbanta da tamu duniyar.
Bayanai makamanta wadannan za’a’iya nemansu a littafan tafsiri irinsu Ibn Kasir, Dabari da sauransu.
Wannan ba karamar mu’ujiza ce ba da kur’ani ya mallaka domin duniyar kimiyya basu gane wannan ba har sai da suka mallaki ababen bincike masu karfi sosai, ashe suna wahalda kanunsu ne kawai bayanin yana jibge a Qur’ani. Allahu Akbar!
Wannan shi ke nuna Qur’ani littafi ne da ya fito daga buwayayye Allah mahalicci.
Kinga ashe akai kimiyya a littafinmu.
Cike da mamaki fate ta ce, “tabbas nasan wannan theory din amma ko kadan ban taba tunanin za a same shi a littafinku ba”
“littafinmu yana dauke da abubuwan mamaki sosai. Nan suka ci gab da fira har barci ya kwashe su, da safe sukayi sallah, sai suka taru wuri daya d zancen samun neman mafit cikin wannan bakin jejin
Abdulsamad ne ya nuna ya kamata a ce sun nemi abinda za su ci ne kafin komai, inda abokinsa ya kwabe shi, si dattijo ya nuna zancen nasa gaskiya ne, ya kamata su shiga cikin jejin domin su nnemo abinda za su ci, daga baya sais u tattauna kan mafita.
Aseeya kuwa kafar tata ba wani babbaan ciwo take yi ba, amma bt iya takata yadda ya kamata, it d fate sai suka zama ‘yan saurare kawai
Nan mazan sukaa fntsama cikin jejin domin yin frautar abinda za su ci, inda aka bar Fate da Aseeya a cikin kogo.
Duka wannan abin ya faru ne kafin fitowar rana
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣5⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
*Quote of the day*
_to withdraw is not to run away – and to stay is not a wise option – when there is more reason to fear than to hope_
*waiwaye*
_A shafin da ya gabata, mun ji cewa akwai binciken kimiyya a cikin kur’ani, haka mun ji cewa mazan sun fita yin farautar abinda za a ci, inda aka bar matan zaune cikin kogo suna jiran dawowarsu._
*ci gaba*
Gudun kar daya ko wasu daga cikinsu su rabe daga ainahin ayarin, sai suka yanke shawara kan duk inda za su a tare zasu tafi.
Sai kara nutsawa suke yi cikin jeji, amma ba abinda suke haduwa da shi sai fara, kasancewar da saura kafin rana ta fito kuma ga shi lokacin sanyi, abinka da jejukan Kebbi, gudun kar su yi biyu babu, sai suka kama adadi mai yawa daga fara da suke haduwa da ita, saninmu ne mu ‘yan kebbi, fara dama da sanyin safe ake kamata domin a lokacin sanyi ya doketa sosai ba ta iaya tashi sama. Suka ci gaba da tafiya har suka tarar da sawu sababbi na zomo da inda ya shige cikin wata Biga (Biga: ita ce, inda itace suka yi zugu ko taro a wuri daya, kuma aka sami wurin da rami ko kuma kasa yake), nan suka zagaye Bigar, sai Abdulsamad ya gabata ya fara dukan wurin domin Zomon ya fito amma shuru, hakan tasa suka fara neman inda za su kutsa ciki, da kyar suka sami wata ‘yar kusurwa wadda mutum ba zai iya shiga ba saboda sarkakewar itace, nan suka yi amfani da hannayensu suka karya itacen da suka rufe kusuwar, sai tsoho ya shiga, duk da sun gyara kusuwar, da kyar ya samu ya shiga, har sai da ya jiwa guiwowin hannayensa ciwo. Ba da jimawa ba da shigarsa, sai suka ga Zomo ya fito a guje, suka yi tara-tara, amma ina sai ya gudu, sun juyo domin su bi shi sai ga wasu sun ffito, ganin haka sai suka dawo suka bi su, amma ko kusa suka kasa kama ko da daya, abinka da masifar gudun Zomo. Da kyar da bone tsoho ya samu ya fito, a hannunsa ba abinda ya kama, ba tareda ya ce da su uffan ba, ganin su a hannayensu ba abinda suka kama, ya musu alama da hannu cewa su kara gaba. Suka bi shi kowannensu rai a bace, kuma ga shi rana tuni ta fito har jejin ya haskaka sosai.
Sai a lokacin na sami damar kawo maku yadda fsalin wannan jejin yake.
Jeji ne da galibinsa duwarwatsu ne manya-manya wadansu jajaye wadansu kuwa da alamar baki a jikinsu, kamar dai muce irin duwatsunnan masu aman wuta (volcano), duk da haka akwai itace irinsu Muruci Sabara da su Anza da dai sauran itace da ke nuna tabbas wannn wurin yana dauke da hadari, iyakar kallon mutum ba abinda zai yi tozali da shi face kungurumin daji, gabas da yamma gudu da arewa duk inda ka duba iyakar ganinka jeji ne fallau. Wasu wurare a jejin suna dauke da yashi, kasancewar akwai itace a wurin shi ya hana jejin ya zama sahara. A wdanan duwarwatsun akwai koguna, inda manyan namun jeji ke zama, wasu ma anan suke haihuwa, kamar yadda muka fada, a tarihi, ba wanda ya taba shiga jejin ya fita da rayuwarsa, saboda hadari da manayan aljanun da ke cikinsa.
A bangaren su Fate kuwa tun fitar mazajen farauta, suma suka ce bari su dan fito bakin kogon domin su mike kafafuwansu, su kuma morewa idanunsu, hakan t faru ne da suka g hasken rana ya fara bayyana. Suka fito a kofar kogon amma gudun kar su yi nisa hanyar dawowa ta baciye nusu, sai sukaa tsay iya inda zasu iya hango dutsen da kogonsu yake, ba abinda ya birge su irin kukan tsuntsaye da kumaa wulgawarsu a kan kawunansu, duk da suna cikin damuwa ta kasancewa cikin wannan *Bakin Jejin*, sun tsinci kawunansu a cikin nishadi, wanda har ta kai suka fara sakin murmushi, Aseeya kuwa har yanzu dingishi take da ‘yar kafarta.
Zuwa wani lokaci, sai gaa mafaarauta sun dawo, sai dai ba abinda suka kamo fache fara sai Bushiya guda hudu. Hango dawowarsu da su Fate suka yi shi ya sa suka yi sauri suka koma cikin kogon, bayan sun karaso, suka ajiye abubuwan da suka kamo, nan take wasu suka fita nemo itace, inda wasu suka fara gyara nama domin a dora kan wuta, Aseeya ce ta fara magana. “wannan kuma me ye kuka kamo” “fara ce sai kuma Bushiya, da kyar muka samu muka kamo bushiyoyinnan” “fara fa da Bushiya? Sai ka ce wasu mayunwata? Ta ina kuka taba ganin an ci dayaa daga cikin wadannan?” tsoho ne ya yi murmushi a daidai lokacin da yake gayara fari da aka jibge a gabansa, ya kalli Driver da Saddam wadanda suke kokarin gyara Bushiya, ya ce “mu abinda muka iya samowa kenan diyata, kuma ai komai da kike gani dan lokaci ne, wasu awanni da suka shude, baki taba tunanin zaki kwana a kogo ba, haka ba ki taba tunani kiyi kalaci da irin wannan ba, tafiya fa mabudin ilimi ce, kinga yanzu kinsan cewa za’a iya cin fara da Bushiya, Karin dadin labarin ma ga shi za ki ci da kanki.” Ya fada cikin sakin fuska. Sai ga su Ameer sun dawo da makamashin wuta, suka fara hasa wutar, kafin su kammala su Dattijo sun jima da kammala gyaran kalacin nasu, sai suka dora a kan wuta, gaba daya suka zagaye wutar ksnacewar duk da rana da fito akwai sanyi sosai. Nan tsoho ya kada baki ya ce, “ya kamata wani daga cikinmu ya dan bamu tarihinsa a takaice, kafin abincinmu ya nuna” Aseeya ta galla masa harara, a fakaice, a ranta sai kwankwanto take na ya za ta ci wannan abun da ko wankewa da ruwa ba ayi ba.
Saddam ya gabata, “sunana Saddam Alhassan Masama, ni haifaffen garin masama ne, amma a garin Gwandu na tashi a hannun yayan mahaifina malam Akilu, a unguwar Kofar masama, mutum ne ma aboci neman ilimi da koyarwa, amma hakan batasa na dauko halinsa ba, illa dai na sauke kur’ani kuma na dan san abubuwa iya gwargwado a musulunci, haka ina kulawa da addinina ba na wasa ko kadan, da Marikina ya fahimci bana biyar abokanin banza kuma na fi mayar da hankalina kan sana’a da kokarin dogaro da kaina, sai ya dinga bani shawara da goyon baya, ni dalibi ne a WAZIRI UMARU FEDERAL POLYTECHNICH BIRNIN KEBBI, ina karatun estate management a ND2 nake yanzu. Mu biyu ne mahaifinmu ya Haifa, ni sai kanwata Zaraa’u, dukkaninmu a garin Gwandu muka tashi, sai dai ita daliba ce a UDUS inda take karatun Hausa”
“me zaka je yi garin Kamba?”
Aseeya ta tambaya
“akwai wani project da nake yi, ya hada ne da gine-gine da suka shafi garin, shi yasa nazo domin na iya rubuta yadda abin yake, gudun kar na yi copy, nayi karya”
“gaskiya ka birge ni, ka ga mutanen yanzu, sun dauki project kamar rubutun bango a aji, da za su dinga copy kawai, ba tareda sun tashi tsaye sunyi bincike ba da kawunansu, Allah ya sa albarka” Aseeya ta fada
“amen nagode”
Suka ci gaba da zantawa kan project har ya zuwa lokacin da breakfast nasu ya nuna, suka saukar da Bushayen, sai suka fara gasa fara, kasancewar ba tukunya ko mai da zasu toya ta, Dattijo ne ke gashin, inda yake jefa farar daya bayan daya a cikin wuta, sai ya dinga amfani da kara yana juyata har sai ko ina ya gasu, sai ya fitar ya sake jefa wata cikin wutar, a haka har ya kammala gashin gaba daya, ya raba naman ya ajiyewa kowa a gabansa. Abdulsamad ne ya far cin nasa, duk da ba ko gishiri a ciki, sam shi bai damu ba, kawai dai ya ji cikinsa ya dauka. Aseeya ce kadai ta ajiye nata a gabanta, sai kura masa ido take, duka namun sunyi baki, a tunanint ita fa cuta ce zata sakawa cikinta, maatsalar kuma ga shi tanajin yunwa sosai, mafi tashin hankalin, shi ne, batasan yaushe za a sami wani abincin ba.
Ku biyoni. Mun fara shiga labarin
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣6⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_if you have fear of some pain or suffering, you should examine, whether there is anything you can do about it, if you can, there is no need to worry about it, if you cannot do anything, there is also no need to worry._
*waiwaye*
_a shafin da yaa gabata, munji cewa; mataafiyan sun je sun yo farautar bushiya da fara, har wasu daga cikinsu sun ci nasu inda Aseeya ta kurawa nata ido, haka munji ina ne asalin Abdulsamad wato garin Masama, munkuma ji inda yake karatu da inda yake Zaune_
*ci gaba*
Har sai da kow ya kammala cin nasa, it kuwa manyan idanuwnta suna akan nata kalacin, duk da tanajin yunwa amm si t kasa ci, ganin haka sai Abdulsmad y gabata ya ce;”idan ba za ki ci ba, me zai hana ni ki bani na kara domin nawu bai ishe ni ba” ya fada a dai dai lokacin da yake mayar d hankalinsa gab daya kan guntayen naman Bushiya sai wasu kwarorin Fara da aka dora kan ganyaye na icen kalgo, tsaki kawai ta rafka, ba tareda ta ko kalle shi ba, tayi masa alama da hannu, cewar ya dauka kawai. Shi kuwa har da saurinsa ya dauka ya koma mazauninsa ya ci gab da cin binsa, haushi wurin bokinsa Saddam kuwa kamar y tso ya doke shi, ganin yadda y kayr da girmans hart a wulakanta shi.
Ganin sun sami nutsuwa sai Dattijo ya gabata ya ce “kamar yadda na sanar da ku kafin mu fita Farauta a dazu, ya kamat mu zauna me nemarwa kawunanmu mafita daga cikin wannan jejin, mundai g kalar hadaruruka da ya kunsa, bugu da kaari gidajenmu ba s da labarin a ina muke haka wadanda zamu tarar a Kamba basa da labarin komai a kanmu, ga shi ba wanda n gani da waya a hannunsa bare mu kokarta mu kira a kawomana doki, yanzu me ye shawarwarinku kan mafita daga wannan jejin”? ya fada a daidai lokaacin da yake mayar da hankaalinsa ya zuwa wurinsu.
Sun yi jim na wani lokci mi tsawo kana, Aseeya ta ce,”inaga idan har muna so mu fita annan hadarin, mu koma ta baya, inda muka fito ba shakka tanan ne kadai zamu iya tarar da babbar hanya, domin idan muk ce mu dauki wata hanya, wani sabon bal’I zamu jefa kawunanmu domin bamusan ina zamu dosa b, bmusan tsawon wanne lokaci zamu kai ba mun tafiya kafin mu isa inda zamu cinma gun ceto, amma nan munsan tsawon tfiya nawa zamu yi mu cinm babbr hany”
Daga cen Abdulsamad y katse ta y ce;”haba bauyar Allah har kinmnta da masifar da ta koromu, ‘yamfashin da suka koro mu fa suna t bayamu ne, kd wurin gyaran idanu a tsone shi, gaskiy mu dai dubi wata hnya kawai mu yanka sambai muyi t tfiya ba shkk nasan zamu cinma hanya, sai mu nemi hnyr is gida”
Fate tai murmushi ta ce;”shawarar ‘yaruwata fa ita tafi daceewa da a bi, idan muka dauki wata hanya bamuda masaniyar ina zmu dosa”
Haka di sukayita musanyr hujjoji har suka ajiye akan za su koma ta baya ne domin su gani ko za sui y cinma inda motrsu take.
Da yake ba sa da wasu kaya, suka tashi gaba dayansu suka far hanyar komawa gurin motarsu. Aseeya ta kama hannun Fate domin ba tai ya takawa sosai suka fara hanya.
BAKIN JEJI ke nan, wannan shi ne takon farko na shigrsu mnyn hdaruruk
Ku biyo labarin kawai
0 comments:
Post a Comment