*waiwaye*
_A shafin da ya gabata munji yadda suks yanke shawara kan inda zasu nufa domin fita wannan jejin_
*ci gaba*
Nan suka dugunzuma gaba daya da zinmar fita wanna *Bakin Jeji* sai tafiya auke yi suna keta surkuki da kwazazzabai tun safe har rana tai zafi sosai, mafi tashin hankali shi ne, mutum biyu ne kadai sanye da takalmi a cikinsu, daga Ameer da ke sanye da sneekers sai Fate da ita ma sneekers ne a kafarta.
Suna cikin tafiya zafi ya yi zafi har ranar ta fara kunar kafafuwansu, sai suka nemi da a yada zango karkashin wani ice makeke na Dorawa, suka zauna gaba dayansu, sai dube-dube suke suna kokarin ko za su iya hango wata alama ko wani abu da zai iya taimaka musu wurin kudurinsu. Driver daga kishingida barci ya daue shi, Absulsamad ya fara korafi kan shi yunwa yake ji. Ai ko nan Aseeya ta bude idanu ta haushi da masifa. 'Me kake nufi? Rabon har mutum biyu fa ka ci kuma kace yunwa kake ji? Wai rudu kenan, su sauran da suka ci rabo daya kacal fa, da ni irina da komai ban ci ba fa?'
Tsoho ne ya katseta ya ce 'haba diyata, kowa fa da yadda ubangiji ya yi shi, zai yiwu wani rashin lafiya yake dauke da shi ko kuma halittace kawai kinga bai dace ki dinga kushe shi haka ba'
'Ba kushewa ba ne, gaskiya ce Baba...'
Saddam ne ya gabata ya ce; 'ku zo mu tafi neman abinda zamu ci'
Suka tashi shi da wasu daga cikinsu suka shiga jeji neman abinda zasu ci.
Ice bayan ice sai nema suke amma basu sami komai ba, haka suka daure suka dawo. Daga dawowarsu, sai Ameer ya mike ya fara hanya, sai Aseeya tace 'ina zaka tafi?' 'Zan yawato ne naga ko zansami abinda zamu iya ci' 'jira ni ta fada' da kyar ta samu ta mike saboda raunin da take da shi a kafa, bayan ta mike ta biyo shi, suka nusa cikin jejin.
Sun jima suna tafiya, har suka karaso wurin wni icen kaiwa, kasancewar lokacin rani ne, suka yi sa'a kuwa icen a cike yake da 'ya'ya, duk da 'ya'yan basu nuna ba, A haka ya hau icen ya dinga tsinko 'ya'yan yana wurgowa a kasa ita kuwa tana tattarawa wuri daya, har suka tara wani adadi mai yawa sai ya sauko ya cire rigarsa ya tsaya daga shi sai singlet, ya saka kaiwar a rigarsa, ya dauko suka nufo hanyar inda suka baro ayarin nasu.
Suna cikin tafiya take tambayarsa me ye wana kuma, bayan yayi murmushi ya karba mata da cewa ice ne da yayansa keda dadi sosai, galibi a farkon rani yake yin yaya, wasu sukan jira har yayan su nuna, inda wasu ke rubawa su ci baya nunar, icen amfi samunsa a dazuzuka masu yawan yashi kamar muce masu makotaka fa Niger Republic, ba abin mamaki ba ne samun wadannan itacen a jejin Kamba ko muce jejin garin Geza, kasancewar makota ne da Niger.
Suka ci gaba da tafiya suna fira tsakaninsu har suka cinma ayarinsu, ba karamar murna sukayi ba ganin Ameer ya ciko rigarsa da abinda zasu ci musamman Absulsamad
Suka jibge kaiwar gabansu, suka fara tsinta daya bayan daya suna ci, Aseeya kuwa tana kai daya a bakinta ta furzar, tace wannan ba zai ciwu ba.
Saddam ya ce 'yaruwa kar ki ci, mu ao gaba ta kai mu, ba sai muci iya cikinmu ba'
'Idan kuka cin sai ku fi ni kiba mana, kalla duk cin da kake kuri da shi gakanan a tsuge ba jiki.....'
Dariyar Abdulsamad ce ta katseta inda ta juyo shima ta azamasa masifa
Ganin masifar tata ba za ta kare ba Ameer ya ce 'malam Saddam kai dan wani gari ne?'
'Ni haifaffen garin Birnin Kebbi ne a unguwar Takalau, nayi primary a Tudun Wada model da ke unguwar tudun wada, nayi secondary a nan tudun wadar inda nake karatu a polyechnich tareda Abdul Samad. Dalili daya zai kai mu garin Kamba.
Ganin lokaci ya gabato sai sukayi taimama sukayi sallah, fate dai ba mujiya ne kawai nata.
Daga idar da salla suka ci gaba da tafiya cikin masifar tsananin rana, ga kishir wa musamman a bangaren Aseeya da har yanzu bata sawa ckinta komai ba.
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣8⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
*quote of the day*
_be who you are and say what you feel, because those who mind don’t matter and those who matter don’t mind_
*waiwaye*
_a shafin da ya gabata, munji yadda suka ci ‘ya’yan itacen kaiwa, haka munji sa’insa da ya gudana tsakanin Aseeya da Abdulsamad, munji asalin Saddam, haka munji cewa sun dauki hanya domin ci gaaba da neman mafita a wannan jejin, har yanzu kuma Aseeya ba ta sakarwa cikinta da komai ba_
*ci gaba*
Haka suka ci gaba da tafiya ga tsananin zafin rana abinka da jeji mai makotaka da kasar Niger, kuma ga matsananciyaar kishirwa, bugu da kari Ammer ne sai Fate kadai ke sanye da takalmi.
Suna cikin taafiya Fate ta matso kusa da Ameer ta ce.”Wai ita wannan sallah me kuke nufi da ita ne, naga kun bata muhinmanci sosai, duk da muna cikin wannan masifar ku sai kun tsaya kun yi?”
Bayan ya murmus cikin jin dadin wannan tambaya tata, sai ya soma, a didai lokacin da Aseeya ke kara matsowa kusa da su, jin tambayar, itama tanaso ta karu. “kamar yadda na fara gaya maki, ita sallah ita ce rukuni na biyu a addininmu na musulunci, wata bauta ce da ta sanadiyyarta ubangiji yakan yafe zunuban bayinsa ya kuma albarkaci rayukansu ya daukaka su a sama da duk wasu da ba sa yinta, sallah dole ce kan duk musulmin da ya balaga kuma ya mallaki hankalin kansa, mukanyi alwala kafin muyita”
“kanaso ka gayamin cewa, ubangiji ne ya umarce ku da kuyi ta?”
“sosai, yin sallah cika umarnin ubangiji ne, har a kanku ku kirista”
“ban fahimta ba” ta fada cikin mamaki
“Ina nufin har cikin littafinku, an yi umarni da ayi sallah irin wacce muke yi”
“irin taku fa? Ku nakan ga har dora goshinku kuke yi a kasa, mu kuwa ba wannan a nau’ukan ibadunmu”
Shiru na tsawon second talatin da ya yi, shi ya baiwa Aseeya damar dagow ta kalleshi, abin mamaki sai ta ga fuskarsa cike da fara’a duk da bai bude baki ya furta komai ba. Murmushi kawai ya saka, sai ya ce, “duk annabawan da aka aiko, ba wana baiyi sallah irin wacce kika ga munayi ba, kuma cikin littafinku duk akwai wadannan sallolin da yadda ko wanne annabi ya yi ta hanyar dora goshinsa a kasa domin ya yi sallah”
“ko za ka iya nunamani?” ta fada a daidai lokacin da take kara gyara Bible da ke hannunta.
“sosai kuwa” ya fada
“Munkarnta inda annbi Musa tareda annbi Haruna (moses and Aoron) suka yi sujda a cikin littafinku,”
Numbers 20:6 “ *and Moses and Aoron went from the presence of the assembly unto the door of the tarbancle of the congregation, and they fell upon their faces: and the glory of the Lord appeared unto them.”* (KING JAMES VERSION)
“Annabi Musa ma mun karanta yaadd yayi sujada”
Exodus 34:8 “ *Moses quickly bowed down to the ground and worshipped”* (GOOD NEWS BIBLE)
“Annabi Ibrahim ma yayi sujad cikin littafinku”
Genesis 17:3 “ *Abraham bowed down with his face touching the ground…”* (GOOD NEWS BIBLE)
“Bawan Annabi Ibrahim ma yayi sujada da fuskarsa a kasa kamar yadda kika ga munayi”
Genesis 24:52 “ *when the servant of Abraham herd this, he bowed down and worship the lord”* (GOOD NEWS BIBLE)
“Akwai annabawa daga cikin Bible da suma duk sunyi sallah ta hanyaar dora goshinsu a kasa da dama daga cikin Bible, kamar”:
Joshuah 5:14
“Ke har sallar jumuah da mukeyi dauke d huduba a cikin littafinku”
Nehemih 8:1-6 1 *By the time the seventh month arrived, the People of Israel were settled in their towns. Then all the people gathered as one person in the town square in front of the Water Gate and asked the scholar Ezra to bring the Book of The Revelation of Moses that God had commanded for Israel*.
2-3 *So Ezra the priest brought The Revelation to the congregation, which was made up of both men and women—everyone capable of understanding. It was the first day of the seventh month. He read it facing the town square at the Water Gate from early dawn until noon in the hearing of the men and women, all who could understand it. And all the people listened—they were all ears—to the Book of The Revelation*.
4 *The scholar Ezra stood on a wooden platform constructed for the occasion. He was flanked on the right by Mattithiah, Shema, Anaiah, Uriah, Hilkiah, and Maaseiah, and on the left by Pedaiah, Mishael, Malkijah, Hashum, Hashbaddanah, Zechariah, and Meshullam.*
5-6 *Ezra opened the book. Every eye was on him (he was standing on the raised platform) and as he opened the book everyone stood. Then Ezra praised God, the great God, and all the people responded, "Oh Yes! Yes!" with hands raised high. And then they fell to their knees in worship of God, their faces to the ground.*
“nasan za ki ce ai duk wadannan hujjojin daga tsohon alkawari ne (old testament) ga hujja daga sabon alkawari (new testament)
“Munkaranta lokacin da annabi Isah yana rokon ubangiji domin ya tsare shi daga sharrin yahudawan da ke so su kashe shi, yayi sujada”
Mathew 26:39 “ *he went a little farther on, threw himself facedownwards on the ground, and prayed…”* (GOOD NEWS BIBLE)
Nan zufa ta fara karyo mata, domin ita sam bata taba cin karo da wadannann hujjojin ba, ga shi duk ta karanto tag a hakanne ba halin ta ja ko ta karayata.
“naji dazu ka ambaci cewa kukanyi alwala kfin kuyi sallah, idan da gaske ne, abinda ka fada na cewa umarni daya ne mu da ku, me yasa mu ba wannan alwar a cikin littafinmu?”
“sosai akwai alwala a cikin littafinku, ( _masu karatu kuyi hakuri ba da son raina ne nake kawo hujjojinnan da yawa ba, duk da sum sun da matukar amfani so zn rage kawo su gudun ku gundura)_
Exodus 40:31-32 “ *and Moses and Aoron nd his sons washed their hands and their feet thereat. When they went into the tent of the congregession, and when they came near unto the altar, they washed as lord commanded moses.”* (KING JAMES VERSION)
“Kinga su kalar tasu alwalar ke nan”
Cikin rashin sanin me za ta fada, sai faman shafar zufa take yi, bugu daa kari ga zafin rana sai karawa yake yi.
Jin su Ameer sun yi shu, dam tun fara tambaya da Fate ta yi suka maido da hankulansu ya zuwa wurin su Ameer, sai tsoho ya ce, “driver ya kamata musan kai waye”
Firgigit ya yi ya fara wuki-wuki da idanu, ga shi mutum ne baki wulik kamar ni, sai dai shi irin ginjima ginjiman mutanennan ne da suka fito daga kasar Niger kamar yadda ya fada, shi haifaffen garin ‘Aqadas’ ne (Agadaz) (turawa ne suka canja sunan daga asalin wanda Usman Danfodio ya sakawa garin) Buzu ne gaba da baya, amma gaba daya rayuwarsa a Nigeria ya yi ta, shi yasa har ya iya karfin halin zama ba rakumi, ko ya yawata ba rawani a kansa (hahaha) ayi hakuri Buzaye kunsan bakwa iyawa sai da rakumi da rawani yalla.
Haka suka ci gaba da tafiya cikin wannan Jejin har dare ya yi musu, amma sam ba hanya ba alamunta, dole suka nemi wuri suka yada zango.
Suka hura wuta domin su duma jikinsu su kuma sami tsaro ko fatan wasu su hango wutar su kawo musu dauki, ( Allah sarki, basusan wannan jejin ba ne shi yasa suke wannan tunanin)
Tsakiyar dare ta raba, sai kawai wutar da suka kunna ta mutu, sai ga wani sauti mai firgitarwa ya fara tinkaro su, a lokacin mutum biyu ne kadai a farke, domin sun raba ne, idan wasu suka yi gadi na wani lokaci sai su kwanta su tada wasu suma su taba gadin, haka har safe, Fate da Driver sune a farke sai ga wannan lamarin ya fara faruwa. Ganin haka suka yi sauri suka tayar da sauran.
Sautin kuwa sai kara karasowa yake wurinsu, dauke da wani iska marar karfi, amma iskan shi ke kara firgitar da zuciyoyinsu, ganin haka sai rabon idanu suke, kuma suka kasa tashi su gudu kamar wadanda aka rikiye.
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
1⃣9⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*quote of the day*
_remembering that you are going to die, is the best way I know to void the trap of thinking you have something to loose_
*waiwaye*
_a shafin da ya gabata munji hujjoji kan sallah ma ta zo a cikin littafin ~Bible~ haka munji ita kanta alwala abin umarni ce a cikin addinin kiristoci, munji asalin Driver. Munji inda ayarin ya yad zango cikin dare, da wani sauti da ke tinkaro su hadi da iska mai kadawa a tsorace_
*ci gaba*
Sautin da ba za ka iya bambance shi da na dabba ba, ko na iska mai karfi, shi ya ci gaba da tinkaro su, ba shakka komai jarumtar mutum, dole y razana, musmman da yake iskan yana kara tayar wa mutum da hankali.
Cirko-cirko suka yi inda zuciyoyinsu suke dukan uku-uku, idanuwansu kuwa kawar wadanda aka baiwa gashi aka kwace, duk da zaune suke amma ji suke kamar kafafuwansu ba a jikinsu suke ba.Ganin har yanzu abinda ke tafe da wannan sautin bai bayyana gare su ba, sai kallon-kallo suke tsakaninsu cikin firgita, nan Fate ta fara runtse idanu tana karanto wasu ayoyi daga cikin littafinsu, tun tanayi a hankali har ta fara yi da karfi. Cen sai ga abin ya bayyana, ai kuwa daga fitowarsa Fate ta juyo a guje, sai ta yi tuntube da wani guntun ice da aka hura wuta da shi ta fadi, sauran da suka yi yunkurin suma su arta a na kare, suka yi tubtube da Fate suka fermata, sai ihu take kurmawa.
Ameer kuwa, kamar sam ba wani abin tsoro a kusa da su, nan ya gabata ya tinkari halittar, Aseeya ce da ke kasa bayan an taushe ta sanadiyyar faduwar da sukayi ta tsura masa na mujiya domin ta ga me yake shirin aikatawa, a ranta tana cewa lallai marubuta mahaukata ne, shi wannan ba y tsoron wannan dodon ya illata shi…
Ameer sai da ya je daf da halittar, shi ya bni damar kallon sifofin halittar sosai: halitta ce mai masifar tsawo, za ta fi tsayin Chabe (pole) guda uku, sam ba ta da fuska amm zaka iya hango jajayen idanuwanta daga wani farin lullubi da ya zagaye kanta, jikin halittar jajur yake, amma tan dunkul ne cikin farin kyalle, batada kafafuwa, idan za ta yi tafiya, sai dai tayi amfani da jikinta gabaa daya ta tafi, tana dauke da hannaye guda uku, wadanda da su take aman wuta domin ta kona mutum, idan ta taba ka, ba abinda za ta bari sai kwarngwal (skeleton).
Ameer ya kusa ya isa kusa da ita, sai ta yo masa aman wuta daga hannayenta sai ya goce cikin zafin nama, ya fadi cen gefe, ganin haka su Driver suka mike cikin kidimewa suka fara gudu, amma kasancewar hankulansu ba sa jikinsu, suka sake karawa da juna suka fadi, wannan ya hau kan wannan wannan ya hau kan wannan, har suka yi wa kawunansu rauni.
Ganin haka sai halittar ta daga hannayenta sama, sai ga wani abu ya fito kamar walkiya daga sama, sai ta nuna su da shi, walkiyar ta farwa Saddam a kahon zuci, ya fadi ba tareda ya ko shura ba, ganin haka suka karaa kidimewa.
Ameer kuwa, ya kara yi cikin halittar ya suri daya daga cikin itacen da suka hura wuta da su, ya rafkamata a jiki, amma sai ya ji icen ya wuce bai taba ta ba, ganin haka ya san ba wani tasiri da duka zai yi a kanta, sai ya fara karanto ayoyin Kur’ani, yana karantawa tana wani kuka mai ban tausayi, amma ya ki ya saurara har sai da hlittar ta fadi ta kone gaba daya.
Cikin sauri suka yo kan gawar Saddam, Abdulsamad sai kuka yake rusawa, da kyar suka samu suka rrrashe shi, ya hakura, suka yi wa gawar abinda y dace a wannan lokacin, suka haka rami suka rufe gawar. Gaba daya suka sha jinin jikinsu, alamu da suka gani na ketowar alfijir na farko, na fatsi-fatsi da ya fara fitowa a sararin samaniya, suka fahimci cewa lokacin sallar subahi yayi, suka yi sallah bayan sun yi taimama, suka ci gaba da tafiya neman mafita a cikin wannan jejin, gaba dayansu a firgice suke.
Zafin rana ya yi zafi, ga yunwa, ga kishirwa, wannan wunin ko abin kalaci ba su samu ba, Aeeya kuwa tun shigowarsu a jejin har yau ba abinda ta saka a bakinta, mafi muni kuma har yau ba wanda ya watsa ruwa a jikinsa.
Sun dade suna tafiya bayan da suka kammala sallar Azahar, kwatsam sai suka ci karo da wani babban kogi, ai kuwa murna wurinsu tafi a bayyana, da yake kogin babba ne sosai, matan suka zagaya inda ba wanda zai gansu suka wanke jikinsu da tuffinsu suka shanya, sai suka koma cikin ruwan suk cig b da wasa suna jiran tufafinsu su bushe, suma mazan haka suka yi a nasu bangaren, bayan sun saka kayansu, suk taru gaba dayansu a gabar kogin, suka fara shawara.
Wasu suka bayara da shawara kan su zauna a wurin ko ba komai akwai ruwan sha kuma akwai kifi da za su dinga kamawa suna ci, iyaka su dinga daukan lokaci suna zagayawa ko Allah zai sa su dace da samun mafita, suka ajiye shawara a kan hakan, nan suka shiga jeji suak nemo itace da ganye, suka kafa dakuna guda biyu, duk da shun fuskanci kalubale ta wurin Aseeya, haka dai suka hakura da juna suka gina dakunan, su matan su suke da daya, maza kuma su ke da daya
Shi kenan a nan zasu rayu?
Ko zasu sami mafita?
Hujjojin na tasiri kan fate kuwa?
Amsoshin na cushe cikn labarin.
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣0⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*quote of the day*
_i know nothing, except the fact of my ignorance_
*waiwaye*
_a shafin da y gabata, munji rasa rayuwar day daga cikinsu, haka mun ji artabon da y gudana tsakaninsu da halitta marar fuska, munji inda ayarin ya ayada zango a bakin wani kogi, da dakunan da suk gina har guda biyu_
*ci gaba*
Da maraice, mazan suka dugunzuma gaba daya cikin wannan kogin domin su sami abinda za su sakawa cikinsu, Fate da Aseeya kuwa suka nemi wuri suka zauna a bakin kogin, sai wasa suke yi da ruwa, duk da Aseeya tana cikin jin matsananciyar yunwa, hakan bai hanata fara’a ba. Sai Fate ta kada baki ta ce; “me yasa naga sun raba muna wurin kwanciya, ba sa gudun wani mugun abu ya faru da mu, ku musulmi a koda yaushe sai ku dinga nuna innocence da rashin wayewar cakuduwar maza da mata, ni fa ban ga illar yin hakan ba” har ta juyo a fusace da niyyar ta fara yi mata masifa, sai ta tuna kirista ce, kuma yin tambayar ya nuna musuluncin ya fara ratsa ta, gudun kar ta sakamata shakku ko dar kan musulunci, sai ta yi ajiyar zuciya tareda sakin murmushi, a lokaci daya kum ta dafa kafadarta, ta ce; “musulunci addini ne mai tsafta wanda kuma ya tsarkaka daga duk wasu gurbatattun halayya, namiji da mce ubangiji ya halicce su ne domin su zamewa juna jinkai da kwanciyar hankali, amma hakan tana halatta ne kadai idan suka mallaki juna a matsayin ma’aurata, ki kalli irin kira da ubangiji ya halicci mace da su, tun daga shape na jiki, zuwa kirji da kunkuru, zaki ga ita ta daban ce, ko ‘yaruwarta ta kalleta dole ta hadiye yawu, bare namiji da aka halitta da cikakkiyyar sha’awa zuwa gareta, kan wannaan ne ubangii ya umarce su da su kauracewa juna gudun su afka hadari, shi kuwa namiji, ubangiji ya halicce shi da iya sarrafa harshe da tsara zance, musamman idan yana yunkurin mallakar abinda zuciyarsa ke muradi, ita kuwa mace, ubangiji y halicce ta da son saurarar zance, kasafi zuciyarta ke karkata idan zance ya tsaru, shi yasa daga hikimar ubangiji sai ya umarci su kauracewa juna idan ba aure tsakani. Addinimu yayiwa mace gata ne, sai ta zama kamar wata ‘yar sarauniya mai mulki…..”
“dakata, gata fa? Ai ko ba addinin da ya raina mace, irin adddininku na musulunci. A addininku, mace ba ta da halin ta saka tufafin da ranta ke so, a addininku mace bata da wani sakewa a koda yaushe tan karkashin namiji sai yadda ya g dama da ita.”
Bayan Aseeya ta murmusua, ranta take cewa, ashe Ameer yana hakuri da tambayoyin wannan arniyar, sai taa ce, “ai ko idan kikayi zancen gat, ba adinin da yyiwa mace gata kamar namu addini na musulunci, haka, a duk fadin duniya, ba addinin da ya wulakanta mace kamar addininku na kiristanci”
Suna cikin wannan musanyar zance sai ga su Ameer sundawo dauke da kifaye manya-manya kuma masu yawa, ganin haka suka yi sauri suka karba, suka fara gyarawa, inda mazan suka shiga daji domin nemo itacen da za a gasa kifin da su, sai da duhu ya fara shigowa suka dawo, suka hura wuta bayan sun ida sallah, suka zagaye wutar, inda tsoho ya fara gasa naman, su kuwa suka dora daga inda suka tsaya kan zancen, gatan mace a addinin kirista da n musulmi.
Fate ta fara, “inajinki, kince addininku yafi yiwa mace gata kai gaa namu addinin kinada hujjoji?”
Sosai inada hujjoji da zan kawo maki, amm tunda ga abokin zantawarki nan yazo, ku ci gaba n tabbata ba zai rasa abin gayamaki ba, kin ganni nan ban cika son surutu ba”
“haba diyata, kina aikin jarida kuma za ki ce ba za ki iya dogon surutu ba? Ko da yake aikin jarida kala-kala ne, amma duk da haka, dole surutu ya shigo”
“baba gajiya dai na yi, ai ina ganin kokarin marubucinnan ta yadda yake jimawa suna surutu yana amsa tmbayoyinta”
Suka kwashe da dariya gaba daya
Bayan Aseeya ta yi masa bayanin zancen da suke yi, si ya soma.
“da farko musulunci ya yi wa mace gata, ta yadda ya yi umarni da a kula da ita tun haihuwart har komawarta gareshi, idan tana karkashin mahaifinta, anyi umarni da ya bata kulawa, idan karkashin mijinta ne shima haka, idan kan ‘ya’yanta ne a lokacin da ta tsufa, suma haka, amma a naku addini, an nuna mace sam ba ta da hurumin yin magana ma a cikin jamaa’a ki duba 1 timothy 2:12
“kuma a addininku, mutum yanada damar ya sayar da diyar cikinsa a matsayin bauya, ki duba exodus 21:7
“Sai ki gayamani wanne gata ne a inda mutum zai sayar da diyar cikinsa?”
“A littafinku, annuna ba mace daya d take da dattako, ki duba Ecclesastes 7:28”
“An ambaci mace a matsayin marar ilimi jahila a littafinku ki duba proverbs 9:13”
Mu musulmi, idan mace tan jinin haila, haramun ne mijinta ya yi jima’I da ita, haka ba za ta yi sallah ba, amma mijinta nada damar ya taba duk inda yake so a jikinta, ya mata sunbata ya rungumeta, su ci abinci tare da sauransu, amm ku addininku, idan mace na jinin haila, gaba daya kauracemata kuke yi, baka tabinta bakwa cin abincinta, duk wanda ya taba ta, zai zama cikin rashin tsarki na wuni daya, ki duba
Leviticus 15:19-22 ‘ *when a woman has her monthly period, she remain unclean for seven days, everyone who touches her remain unclen till eveninganything on which she sits or lles during her monthly period is unclean*”
Wannan kadan ke nan daga kyama da ddininku ya ke nunawa zuwa ga mata, nasan abinda ya ja ki har kike tunani irin wnnan, kila mu addininmu ya hana mata cakuduwa da maza da sunan neman ‘yancin mata. Wanne ‘yanci mace zata kwata fiye da gatan da ubngiji ya mata, kullum mata suna banga kan Gender Equality, basusan duka wannan shirin yahudawa ne ba domin ganin sun raunana tarbiyyar yara da ke tasowa ba, lokacin da kike amfani da shi wurin halarta manyan taruruka, tarbiyyar diyarki ko danki a lokacin tanacen tana lalacewa, a lokacin bakaya kula mijinki, kila wata ta dinga biya masa bukatarsa, amma mata sun kasa hankalta………..
Aka saukar da kifi, kowa aka ajiye masa nasa a gabansa, suka fara ci, suna cikin ci ne, tsoho yayi gyaran murya ya soma, “Ni sunana malam Tanko, ina zaune ne a garin Jodu da ke makotaka da grin Kola kusa da unguwar Badariya, garinmu garin zabarmawa ne, hakan ta sa, nima bazabarmne ne gaba da baya, inada diya shida sai jikoki sha uku, da matata daya, wacce muka yi aure tun da kuruciyarmu, inada diya da ke aure nan garin Kamba, sun sami matsala ne da maigidanta, shi ne nazo na sasanta su, kunji dalilin fitowa ta daga gida
Nan suka myi cirko-cirko suna kallon tsoho cikin halin tusay masa.
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣1⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_the people may be made to follow the path of action, but they may not be made to follow it_
*waiwaye*
_a shafin da ya gabata, munji asalin dattijo Tanko da kuma dalilin fitowarsa zuwa wannan tafiyar Ajali, kamar yadda Bahaushe yake fada ‘idan ajali ya kira ko babu ciwo aje’, munji inda suka ci kifi da kuma hujjoji kan addinin musulunci ya yi gata ga mata, da kuma wulakanci ko kaskanci da ke tattaare a addinin kiristanci a kan mata_
*ci gaba*
Bayan sun kammala sallar isha, driver ya buge da barci, Ameer ya shiga jeji domin ya mike kafafuwansa, inda Abdulsamad da Aseeya suka bi bayansa, domin su yawata tare da shi, ya rage daga Fate sai Dattijo sai driver da tuni ya yi nisa a duniyar barci. Ganin barcin driver ya fara nauyi, Dattijo yaa je bakin kogin da yake da fadi sosai, ga ruwan cikinsa sai gudawa suke a gurguje, ya sami wani dutse da ke wurin ya zauna, ya ci gaba da ka;;on ruwa, duk da da mamaaki abin, kasancewar da dare ne kuma ga shi ba hasken wata sosai. Fate kuwa ta nei wuri ta kishiingida tana jiran dawowar Aseeya domi su je su kwanta a dakin da aka gina musu, daga nesa sai kokarin hango Dattijo take, a ranta kumaa si taraddudin hujjojin da Ameer ya tula a kanta take, a ranta tana cewa, ba shakka wadannan hujjojin sunada kaarfi, amma yanzu idan na koma addinin Msulmi zan tsira kuwa, ji yadda ya kona dodo ta hanyar amfaani da karatu daga cikin littafinsu…….
Sai nusawa suke yi cikin jeji suna fira tsakaninsu, Abdulsamad ne ya bude baki ya ce; “dan’uwa har yanzu dai ina kan bakana na zama marubuci, domin zamanmu kadai a wannan jejin akwai abubuwa da dama da nake so nayi rubutu a kai”
Sai da ya yi murmushi tukun ya amsa masa “zamaa marubuci abu ne mai matukar sauki, galibi marubuta sabaabbi sukan faraa ne da laabarai da suka faru a kusa da su a kan idanunsu, ka ga kaima hakan kake kokarin yi, matsalar da ke faruwa it ce, marubutan yanzu ba sa tsayawa su bai wa rubutu hakkins, ta hanyar snin abubuwa da ke kewaye da shi rubutun d bubuwa da ya dace marubuci ya sni kfin y fra rubutu, shi yasa yanzu usaan online ka ga littfan baatsa sun yi yawa, kuma marubutan sun kasa tsay susan cewa duk fa abinda k rubuta, zai tabbat hr bayn ranka, inda sharri ka dora jama’a a kai zaka sami nka kaso na zunubi, haka idan alkhairi ka shuka shi din za ka girba a ranar tsayuwa. Ina I bak shawara, idan rubutu za ka yi, kayi wanda mutane za su amfana, b domin nemn sun ba, shi suna zai iya zowa ki tsaye, tsarin ubangiji ne”
“nagode aboki, insha Allah z yi kokari kn wannan”
“ke ‘yar jarida na g kaf t warke sosai, shi yasa kika biyo mu ki mike kafa ko?”
“hahhaha! Na biyo ku dai saboda ina sha’awar mike kafaafuwana, musamman a lokacin daanake cikin damuwa, haushi nake ji yaanzu haka, ace har wuce kwanaa biyu ban dora hannuna ka takarda ba, gaba dya bana yi si da rubutu”
“lallai kina kokari, ni kin ganni, marubuci ne, amma ina kyamar doraa hannuna kan takarda, ia jin kasalar typing, musamma yanzu da rubutun an janye na online kaan takardu, ya dawo ka laptops da wayoyi”
“shi yasa ai ku marubutan yanzu, idanuanku ba sa da kwari, hasken scree duk yaa kashe su”
“tau kin ji ai Bahaushe ya ce ‘akan sana’ar mutum amfi so ya adage a san sa’”
Suka ci gaba da tafiya suna fira, har suka yawato sai raha suke, ko da suka dawo suka tarar da Dattijo ne kadai a farke, a bakin kogi yana karatun wasikar Jaki, a gefe kuwa Fate ce da barci ya yi wa satar ba tsammani, shi driver ba a ma ta tashi, domin da jimawa ya buge. Da kyar suka sami tada driver daga barci d y dauke shi, baayn y tashi, ya bi su zuwa nasu dakin da suka zagaye da itce tareda gnyayyaki na itace, sumaa matan suka shiga nasu dakunan. Ce da dare ya raba, suka fara jiyo motsi na tinkaro dakin nasu, Dattijo e y fraa jiyo motsin, yayi sauri ya tada saurn, amma kasncewar driver mutum ne mai nauyin barci, shi bai farka a, suka fito tgaba daya, gnin motsin bai dain ba kuma sai kar tinkaro su yake, Dattijo ya hanzarta ya tada su Aseeya, ai ko fitowarsu ke da wuya, sai mace Ayu ta bayyana t gabansu, jikint daga cibiya zuwa sama a mutum ne, inda dag cibiya zuwa kasa yake na kifi, mace ce wacce kirjinta cike yake da mama, ga gashi mai tsawo har gadon baya, hka take jan jikinta ya zuwa gare su, gin hak suka ranta a a kare, wurin gudun su tsir da rayukansu, suka manta da driver, ta buge gab daya dakuan da suka gi, sai a lokacin da t fara rusa dakunan suka tuna cewa fa driver yana ciki, juyowa da za suyi, suka gat a dauko shi tamkar wacce ta dauki sosu ta rab shi gida biyu karma mai yag takarda, al’amarin da ya kara tad musu da hankali kenan, suka kara gudu domin su tsira da rayukansu. Su jima suna guddu kafin su tsaya, sai haki suke.
Aseeya ce ta kad baki ta ce,”wai kun ga abinda ya fru kuwa, ko ni kadai ce idanuwana suka shaida”
“sosai muma mun shaida, ai hakaa macen ayu take da masifar karfi, komai karfin abu yaa shiga hannunta tau karyarsa ta kare” tsoho ya fda cikin haaki
“wallahi ni daukana zancen Ayu duk karyaa ce, da wani ne y gayamin cewa hakan t fru, zai yi wuy na gaskgata shi, amma sai g shi abin ya faru a saman idanuwana” Abdulsamad ya fada ciki tsoro.
“duk ba wanan ne abin da y kam ce mu ba, wannan jejin wwallahi ba wurin zamaa ba ne, kawai mu hanawa idanuwamu barci, mu ci gaba da kokarin neman mafita, ba dare ba ran, idan ba hka b, duka rayukanmu z su kare ne a wannan *BAKIN JEJI* Ameer ya fadaa
Suka amsa gaba daya “hakaa ne wallahi.
Suka ci gaba da tafiy, duk da da barci a idannuwansu dole a haka suka hakura, su ne basu yadaa zango ba sai da suka faraa jin sanyin subaa y faraa dukan su, a daidai wani kwadarko da ke tsakanin wasu manyan duwarwatsu gud biyu, d kyar suka samu suka wuce wurin saboda hdrin tsallakewa da yake da, daga tsallake wurin sai suk jiwo wata murya mai sautin amao n tinkaro su, suka rasa sanin daga ina ne muryar ke fitowa, baka iy tantce mutum nnawa ne ke magana cikin muryar, aka ce da su “me ya kawo ku cikin wannan *BAKIN JEJIN* inaso kusa da cewa ko da wasa ba wanda ya taba shigowa wanna jejin ya fita da rasa, haka ba za a fara ba daga kanku”
Cikin rashin sanin ina ne muryar ke fitowa, Ameer ya karba, “musa da cewa ba ta yadda zamu tsallake shirin da ubangiji ya yi a kanmu,duk abinda za ku fada ku fada, Jeji dai na ubangiji ne, tabbas kuma sai munfita daga gareshi, sai ida dama a ne ubangiji ya uf rayukanmu za su kaare, shi kuwa ba yinku ba ne haka ya tsara kenan” ya rafka tsaki.
Muryar ta rafke da dariyar keta.
Fate sai kallon Ameer take cike da mamaki
0 comments:
Post a Comment