*ci gaba*
Yanayin wurin abin sha’awa, kama yadda wurin ya kawatu da yashi mai masifar sanyi, kasancewar da subahin ne, gaba daya wuria ya yi tsit, hatta kukan tsuntsaye daukewa ya yi, sai wani sanyayayyen iskan hunturu da ke ratsa bargon mutum har ya ji sanyin ya kamashi ta ko’ina, suna zaune cikin wani kware wanda ke cike da yashi, sai suka jiwo abu ya tinkro su a guje, ba tareda tsayawa su duba me ye ba, suka ranta a na kare, sai gudu suke suna waiwayar baya, amma har suka share awa daya suna gudu ba su ga me ye ke biyar su ba, ganin haka suka sami wuri karkashin wani ice suka zauna, bayan sun huta gajiya suka ci gaba da tafiya ciki wannan *BAKIN JEJIN*
Sai tafiya suke suna fira tsakaninsu, cikin firar ne Fate ke cewa, “ku musulmi kuna birge ni musamman a wannan tafiya da ta hadamu, yadda kuke nuna soyayya ga junanku, yadda baku kyamace ni ba duk da cewa ba addininmu daya ba, nasan cewa da musulma ce mace ke tareda tawagar kiristoci, da tuni sun nemi keta mutuncinta, amma ku ga shi, har taimakamin kuke yi, ba ma wanda zai iya bambanta ni da ku, gaskiy na ji dadi sosai, hujjojinka suna gamsar da ni, amma ina tsoron a karbi addininku, idan naje gida bansan da wacce fuska zan kalli ‘yan’uwana ba, domin na sha ganin yadda ake mu’amalantar wadanda suka sauya addininsu”
Ameer ya karbe, zacen, “amma ko suna zaluntarsu ne kawai, domin ko constitution a wanan kasar ya aminta mutum ya sauya duk addinin da yake so, ki duba chapter iv sakin layi na 38 a 1999 constitution, kinga mu addininmu ya yiwa duk masu shigowa cikinsa gata, ta hanyar kankare zunubai, ga duk wanda ya karbi addinin”
“yanzu kana nufin idan na amshi musulunci, duk zunuban da na aikata sun tafi ke nan?”
“kwari kuwa,” ya fada cikin sakin fuska
Haka suka ci gaba da tafiya suna zantawa kan musulunci da kuma addinin kiristanci, har suka karaso wurin wani zugu sosai, nan suka dinga nema ko za su sami abinda za su ci ganin rana ta fara zafi, amma jirai kadai suka samu, suka debo mai yawa suka sami wuri suka zauna, suna ci suna fira.
Ganin ta dauki lokaci mai tsawo ba tareda ta fara cin nata ba, Ameer ya ce “’yar Jarida, ai ko gaara ki ci, domin zai yi wu wanan jiraa shi kadai zamu gani, a wunin yau”
Ba tareda ta ko kalleshi ba ta saki wani dogon numfashi, dai dai lokacin da cikinta ya fara rurin yunwa, ganin haka, ta dauki wani jirai babba daga cikin wadanda aka ajiye mata a gabanta, ta fara tsotsawa.
Tsoho ya kada baki yace, “yanzu abu daya ya rage muna, shi ne mu dage da addu’ah, domin ko yunwar cikinmu da kishirwa kadai sun isa su karar da rayukanmu,”
“haka ne” Ameer ya fada, yana kallon sauran mutanen da ke zaune wurin.
“Aseeya ya kamata musan wa cece ke” tsoho ya fada, idanuwans kyam a kanta
Cikin mamaki ta saki baki, ganin idanun kowa a kanta, ta tabbatar sun kosa su ji daga gareta, sai ta fara. “sunana Aseeya Abubakar, ni haifaffiyar Birnin Kebbi ce a unguwar Rafin Atiku, amma a halin yanzu muna zaune ne a unguwar Badariya, asalina ni ‘yar Niger state ce a wani kauye da ake kira Shwaga kusa da garin Nasco, gidanmu mata uku ne, wurin mahaifiyarmu mu uku ne, ni ce ta biyu, inada yaya mace sai kani, ina karatu a FUBK ug3 inda nake karatun sociology. Aikin Jarida da ziyara za su kai ni garin Kamba”
Cikin mamaki suke kallonta, suna tunanin yadda take hada karatu da wannan aiki mai wahala.
Bayan wani lokaci, da suka ga rana ta fara yin sanyi sai suka dugunzuma suka ci gaba da tafiya domin neman mafita daga wannan jejin.
Kar mai karatu ya manta, an yi musu barazanar rashin fita daga jejin, haka, jejin ance yanada hadari sosai, ga shi har yanzu manyan hadaruruka basu fara faruwa da su ba. Allah sarki, Fate za ta musulunta kuwa, talents na Ameer duk a jeji za su kare, Aseeya fa munga ta rage zafi kodai lokaci take jira, Datiijo zai sami daidaita auren ‘yarsa kuwa???? Duk ku biyo ni cikin wannnan labarin
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣3⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_put your hand on a hot stove for a minute, and it seems like an hour. Sit with a pretty girl for an hour, and it seems like a minute. That’s relativity_
*shafin masoya*
AUTAR
PRINCE UMAR IDRIS ASADA
JAMILA
PRINCE ZA’EED
HURUL’EEN
FARUQK
Haka suka ci gaba da tafiya, sai jan kafafuwansu suke, kasancewar suna cikin matsananciyar yunwa da kishi, gaba daya wunin jirai kadai suka sakawa cikinsu, haka har jikinsu ya fara furi da bashin rashin wanka, tufafinsu kuwa ba a ko magana, domin wurin gudu ba wanda bai yaga tufarsa ba daga cikinsu, sai tafiya suke suna fira abinsu har rana ta fadi, bayan sun kammala sallah, suka ci gaba da tafiya, ga matsananciyar gajiya, amma har yanzu ba alamun fita daga wannan *BAKIN JEJIN* cen sun yi nisa da tafiya, da awanni wuce uku da kammala sallar isha, suka fara jiwo sautin ganguna dauke da kuwwace-kuwwace na mutune nesa da su sosai, hakan ta sa suka ajiye hankulansu wuri daya domin jiyo daga inda sautin da kuwwar ke fitowa, a cewarsu sun sami mafita. Sun dauki lokaci suna dube-dube, kafin su hango hasken wuta nesa da su kusa da wani babban dutse, ganin hakaa, da kuma tsammanin samun mafita da ke kwance a zukatansu, suka bige da murna, nan take kuma duka gajiyar da suke ji ta kau, yunwa kuwa suka manta da ita. Suka dauki hanya gaba daya suka tinkari inda hasken yake, Abdulsamad ne ya kada baki ya ce, “inaga fa wancen kidin mafarauta ne, sai mu hanzarta ko za mu sami abinda zamu sakarwa cikinmu, wallahi yunwa naa batun illata ni” Aseeya ta kalle shi a yatsine, ta ce, “ai wannan kidan ba na mafarauta ba ne, zai yi wuya ka ga mafarauta sun yi farauta da dare, idan ba da lalura ba, ga shi ko hasken wata babu, zai yi wu dai wasu mutane ne na daban, ko kuma gari ne mai zaman kansa, kunga idan muka karasa ta gaarin sai su dora mu a kan hanya, na kosa wallahi in koma makaraanta, kar ayi lectures ba na nan” “wa ya gayamaki wannan ba kidan mafarauta ba ne?Ke duk yadda mutum ya yi magana sai kin gwale shi” Abdul ya fada cikin fushi. Dattijo ya karbe, “sosai dana wannan kidan ba na mafarauta ba ne, naso na gane wanne iri ne domin musan kalar mutanen da zamu tarar, amma sam na kasa gane kidan, a rayuwata ban taba jin kalar wannan kidan ba, kuma wannan kuwwar, daga ji majiya karfi ne, domin ku saurara, har ta nan za ka iya bambance ta namiji da ta mace”
Lokaci daya sukayi ajiyar zuciya, kamar programming na computer, “tau me ye abin yi?” Fate ta fada cikin tsoro, “me ko zamu yi illa mu je mu shaidawa idanuwanmu” inji Abdul samad “ni fa ko yunwarnan kadai illata ni zatayi”
“kai da ke cewa mu tafi, muka sani ko aljanu ne ke wasa, muje mu kai kanmu mahallaka” inji Aseeya. “da rashin kira fa Karen kurma ya bata, haka da rashin tayi sai ki ga an bar arha, kuyi hakuri mu ajiye tsoro gefe, daya, mu fuskanci gaskiyar cewa yunwa fa muke ji, haka, idan ma aljanu ne, ai addu’ah ta ishe su, zamu iya yin karatu daga Qur’ani, dole su gudu”
Ameer ya ce, “zancenka aboki gaskiya ne, amma ko kusa ni hankalina bai kwanta da muje wurin ba, tunda munji Dattijo yace baisan kalar kidan ba, kuma kasan tsofaffi su sukasan abubuwa da suka shafi gargajiya da al’ada, mu hakura kada mu jawowa kawunanmu wata jangwangwama”
“haba sai kace wasu mata, ni fa banga abin tsoro ba a nan, kawai mu murje idanuwwanmu mu tafi, wa ya sani ma ko nan ne mafita daga wannan *BAKIN JEJIN*”
“idan ba mafita ba dai zai iya zame muna mahallaka” inji Aseeya, “amma ku zo mu tafi, in ce ai tare da shi zamu je, sai kayi muna jagora, dama ai ka fada yunwa za ta kaika wurin, shin wai kai wanne kalar ciki kake da ne? naga duk abinda ke cikinka shi ne a namu, ga shi kan masifar cinka za ka kaimu ka baro”
“idan kum nan ne mafita, sai ku ce me, kun bi kunata surutaai marasa kai, bari in gaya maki ki iya bakinki kinfara kai ni bango fa, na fara gajiya da kaifin bakinnan naki”
“me zaka iya yi ne, kai ba abin kunya ba ne, ga mata ba wacce ta yi kukan yunwa sai kai, hatta tsoho ya jure amma kai ka kasa jurewa woooo!”
A fusace ya taso da niyyar kai mata duka, sai da Fate da Ameer suka shiga tsakani, Fate na kokarin rike Aseeya da ita ma tasowa ta yi da niyyar su bai wa hamata iska, Ameer ya rike Abdul, ya ce, “haba abokina kar ka bata wa marubuta suna, ansanmu da hakuri fa, yanzu idan ka yi fad da mace, a ce maka me? Idan ma kashi ka bata, me za ka karu da shi? Idan kuma reshe ya juye da mujiya ka ga girma faduwa zai yi”
Tsoho ne ya karbe zancen, “ku in banda kuruciya, ina mu ina fada da juna cikin wannan tashin hankali, da me za mu ji? Da faman neman mafita ko da kokarin daidaita ku, ku zo mu tafi mu gani me ke faruwa”
Suka ci gaba da tafiya, su Abdul sai hararar juna ake da abokiyar fadarsa, inda kowa ya yi tsit ba wanda ya sake furta ko kalma daya har suka kawo daf da wabi babban taro, ganin alamun mutane ne sai suka karasa, amma daga isarsu, sai labarin ya canja ga shi ba halin su koma ta baya, domin sun rigaya sun zo daf da su, wadannan mutanen Maridai ne, masu cin naman mutane, sun hura wutar ne suna shagulgulansu na cin naman mutane, a saman wutar tareni ne na mutane har uku, da suke gasawa, za a ci, a cen bayan taron kuma wata mutum ce da suka kamo suka daure, a ka’idarsu , idan suka kama mutum za su daure shi ne tsawon kwana uku ba tareda sun bashi abinci ba, ruwa kawai suke ba shi, sai su yanka shi su yi farfesun kayan cikinsa sauran naman jikinsa kuwa a gasa a cinye, gaba daya ba mai tufafi a cikinsu a zindir suke tun daga kananan yara har tsofaffi, ba sa aure tsakaninsu, duk wacce ka ga ta maka, ko a gaban kowa ne, za ka kamata ne ka biya bukatarka, rayuwarsu dai kamar dabbobi, sukan yi magana, amma da wasu sautuka marasa tsawo, wadanda su suka san ma’anoninsu, suna dauke da makamai da suka yi ta hanyar amfani da itace manya, da kibau, wurin farauta ba za ka bambanta mace da namiji ba a cikinsu.
Nan su Ameer suka fara kallon juna zuciyoyinsu sai dakan uku-uku suke, musamman Abdulsamad, cikin murya mai ban tausayi da tsoro Aseeya ta kalle shi ta ce, “wallahi Allah ya isa…”
Kafin ta rufe bakinta, suka zageye su, ga su tsakiyar masu cin mutane, tirkashi, me zai faru da su kuwa, ku biyoni cikin labarin, yanzu muka fara
Ni ne naku
ZAINUDDEEN JIBRIL ZAIN
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣4⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_it does not matter who has the title or who gates the glory_
*shafin masoya*
ASEEYA LAME
AISHA A MUHAMMAD
MAMAN SUDAIZ
ADAM DAN MAMA
SAFWAN AGAJI
80K
MUSTAPHA MUSTY
UMMU SAYYEED
“ai ba Allah ya isa zakimun ba, ki zo ki dake ni mana” ya fada a fusace
“wai ku wanne rashin hankali ne da ku, bakwa ganin abin da ke gabanmu, har kuke kokarin fada da juna, sai kace wasu yara?”
“baba kana fa ji, Allah ya isa take min, ni na dauramata tafiyar zuwa garin *KAMBA* ne? Ai da sai tayi zamanta a gida mana”
Suka ci gaba da musanyar magana, cikin salo irin nasu, suka cafke su gaba daya, suka tafi da su a wasu kejuka suka daure hannayensu suka saka su, kowa a cikin nashi kejin daban, duk da kejukan suna kusa da juna. Kejin an yi shi ne da itace masu kauri, inda aka kafe su daga cikin kasa, a samansa ma itace ne da suka yi amfani da wasu igiyoyi da suka yi daga saiwu na itace, suka daure, kejin ba ya da kwari kasancewar ya bushe sosai, haka suka daure hannayensu gaba daya, ta baya.
A bangaren wadannan maciya mutane kuwa, sai kade-kadensu suke yi suna raye-raye, a lokaci daya kuma suna zagayar wutar da suka hura, wacce ke da masifar zafi, zuwa wani lokaci naman mutanen da ke kan wuta ya nuna, sai aka saukar da shi, haka suka dinga wawason tarenin wanda yafi karfi, shi ke samun babban kaso, inda yara kanani saidai kuka domin manyan sun cinye komai, haka suke cin naman da zafinsa.
Bayan sun kammala ciye-ciyensu, sai wani tsoho ya gabata daga cikinsu, tsayuwarsa a tsakiyar filin shi ya dakatar da kidan da ke tashi, haka maraya da suka cika tsakiyar filin gaba daya suka fita suka koma gefe, nan ya fara rabon idanu yana kallon taron, cen zuwa wani lokaci, sai ya nuna wata mace daga cikin taron, ai ko daga nuna ta, wasu majiya karfi guda biyu suka je suka fito da ita, ita kuwa sai kokarin kubucewa take yi daga hannunsu, amma sai da suka kawota a gabanshi, sai rawa jikinta ke yi, ya mata alama da hannu cewar ta kwanta, kamar wacce aka tsafe ta kwanta, yayi masha’a da ita. Daga kammalawarsa suma sauran kowa ya fara neman wacce zai tara da ita. Bayan sun kammala sai suk fara watsewa, a lokacin dare ya raba sosai.
Su Ameer kuwa duk abinda ke faruwa, a saman idanuwansu ne, gaba daya suka shaa jinin jikinsu, kusa da kowanne keji akawai mutum daya da ke gadinshi, rike da katon ice a hannu. Ganin duka sun waste, tsoho ke tambayar wacce suka tarar an daure a wurin, ita ba a keji aka saka ta ba, sun daureta ne a jikin wani babban ice, inda suka daure hannayenta ta sama a jikin icen, suka kuma daure kafafuwanta, da alamun yunwa a tattare da ita, kuma da alama ta sha wuya sosai, tsoho ya tambayeta.
“ke kuwa me ya kawo ki wannan jejin har kika fado hannun wadannan mutanen?”
“gaskiya labarina mai tsawo ne, amma asalina ni ‘yar garin Gaya ce a Niger Republic, yawon dibar Jirai ya jawo ni har na fado wannan wurin, abu daya na sani shi ne, gobe wa’adina zai cika, dama sukan ajiye mutum ne har tsawon kwana uku suna gana masa azaba kafin su kashe shi daga baya,gobe ne kwanakina za su cika, kuma kwankinku uku ne a wannan kejin, idan lokaci ya yi, zaku zama namansu”
“nama fa kika ce?” Abdul ya fada idanuwansa a bude
“sosai, ko tausayi ba sada ga su sunma fi dabbobi rashin hankali, ni banmasan wadanmi kalar halittu ba ne”
“Da ikon Allah za mu kubata daga sharrinsu” Ameer ya fada a daidai lokacin da yake mayar da hankalinsa a kan Fate. Ya ce da ita; “yanada kyau ki karbi musulunci, kin ga idan nan ne Allah ya nufi rayuwarmu za ta kare, za ki ribata, idan ma mun tsira, dadinki ne, za ki tafi da imaninki”
“ni fa ba kin karbar addininku nake yi ba, har yanzu ina bukatar hujjoji da za su gamsar da ni”
Aseeya ce ta karbe zancen, “lallai Fate; yanzu duk hujjojin da bawan Allahn nan ya kawo maki kina nufin baki gamsu ba? Bansan irin hujjojin da kike bukata ba kuwa kafin ki karbi musulunci”
“ki bar ta, idan ubangiji ya nufe ta da karbar addini ai za ta karba, idan kuma bai nufeta ba, duk hujja da z a bata ba za ta yi imani ba, akwai zance makamancin wannan a cikin Qur’ani, kum shi musulunci ba a yi wa mutum dole kamar yadda ubangiji ya sanar da mu a cikin Qur’ani, amma har wa yau Bible ya sanar da mu cewa ku nemi sanin gaskiya, ita kuwa gaskiya za ta dora ku saman hanya madaidaiciya John 8:32 “ *And ye shall know the truth, and the truth shall set you free*”(KING JAMES VERSION) ki bar ta, idan ta gamsu sai ta karbi musulunci.”
Tun da sanyin safiya, suka zo suka kwance wacce ke kan ice, tana kuwwa tana kiran “ku cece ni”, amma ina, suka kwantar da ita, bayan sun yaga tufafin da ke jikinta, suka taru a kanta sama da mutum goma, kowanne sai da ya yi lalata da ita, suka Burma cikinta sai ihu take, a haka suka fara fiddowa da kayan cikinta, tana kallo tana kuwwa har rayuwarta ta fita, suka fidda kayan cikin nata suka fara ci danyenshi, sai suka fara yanke kanta, suka fidda shi gefe daya suka yiwa naman gunduwa gunduwa suka dauka suka dora kan wutar da ke ci tun tahowar su Aseeya, ashe wutar ba a kasheta, ko me ya sa oho. Suka gasa naman, haka suka dinga wawason naman suna ci har suka cinye gaba daya, suka wurgar da kan, cen cikin kanun da sun haura dubu, wasu sai wari suke, inda wasu da dadewa sun zama kashi zalla.
Ganin haka hankalin Aseeya ya yi matukar tashi, musamman ganin yadda karti har goma suka keti haddin wannan bauyar Allah, kuma suka rabata da tilon rayuwarta, Fate ba abinda take yi sai kuka. Ameer ne ke kwantar musu da hankali da kokarin nuna musu cewa addu’ah ce mafita a gare su, ba shakka ubangiji ya yi alkawarin cewa duk wanda ya roke shi zai karba masa, saboda haka su dage da addu’ah da ikon Allah za su kubuta.
“ganinka za mu iya kubuta daga wannan tarkon kuwa? Ji fa yadda muka shiga hannun wadannan marasaa imani, ba na tunanin akwai mafita kan wannan”
“haba Abdul sai kace ba musulmi ba; ubangiji ne fa da kansa yace ‘ya ku wadanda suka yi imani, kar ku yanke tsammani daga Rahamar Allah….’ Kuma shi ya ce; ‘wa ye yake jin wanda yake a matse (cikin neman bukata) idan ya kira shi…?’ duk halin da bawa ya shiga, da ma wanda zai shiga, ubangiji yana sane, kuma a shirye yake da ya taimake sa, matsawar bawannan bai manta da shi ba, inada yakini kan tabbas ubangiji zai kubutar da mu”
Cikin shesshekar kuka fate ta karbe zancen. “yanzu kana nufin ubangijinku zai iya fidda mu daga wannan tarko? Ba shakka, idan ubangijinku ya aikata haka, ya nunamin cewa ya fi kowa, kuma zan aminta da cewa shi ya fi cancanta da a bautawa”
“kada ki ce da ni sharadi ki ke baiwa ubangiji, mu namu ubangiji, yakan aikata duk abinda ya so, zai yi wu ya bar mu mu mutu a nan, da wata hikima ta shi da ba musan da ita ba, zai yi wu ya raya mu domin ya nunamaki buwayarsa”
“Ni fan a tsorata, saura kwanaki biyu kacal fa, ayi wawason namanmu” Abdul ya fada cike da tsoro.
Tsaki kawai Aseeya ta rafka, tareda shiga dogon tunani a lokaci daya.
A bangaren maciya mutanen kuwa, da dare ya yi, suka ci gaba da raye-raye hadi da kade-kadensu, kasancewar ba naman mutane a daren yau, suka gabatar da namun dabbobin jeji da suka kashe, dama munsan cewa gwanaye ne a farauta, mazansu da matansu, bayan sun kammala, suka gabatar da masha’arsu yadda suka gabatar jiya, duk a idanuwan su Ameer, suka waste aka bar su Ameer da masu gadinsu.
Aseeya ta kada baki, cikin rawar murya da ke nuna dauke ta ke da yunwa ta ce; “kar fa mu manta gobe ne wa’adin zamanmu a wannan keji zai cika, ya kamata a ce mun attaka wani abu, idan ma nasara ce ba mu yi ba, yafi mu zauna haka, ko ba komai Bahaushe ya ce, wai ubangiji ya ce, ‘tashi in taimake ka’, ya kamata mu dan yi yunkurin kubuta, idan mun kubuta, shi kenan, idan muka mutu, duk daya ne wai makaho ya fito yawon dare”
Cikin ajiyar zuciya dattijo ya ce; “ba shakka zancenki yarinya haka ne”
Nan suka tsara duk yadda za su yi. Da dare ya raba suka fuskanci wasu daga cikin masu gadin nasu sun fara barci, sai Ameer ya kokarta ya kwance kansa, dama kofar kejin wani kara ne aka sakada a makullin, tunaninsu ba wanda zai iya kubuta, ya swance karan, ya kiwaci hankalin wanda ke farke, ya fito daga kejinsa, ya sami wani ice ya buga masa a ka, ya mutu, cikin sauri, ya je ya kwance Abdul, tare suka kwance sauran, wurin rawar jikin tsoro Fate ta taka daya daga cikin masu gadin, ya farka, ganin su duka sun fito daga kejukansu, ya rafka ihu, inda sauran duka suka tashi, ai ko suna ganin haka suka runtuma cikin jeji, su kuwa suka ce da wa aka hadamu idan ba da ku ba, daya daga cikinsu, ya dauki wani ice ya fara dukan wata katuwar ganga da ke wurin, inda sauran suka farka, suma suka biyo su a guje bayan ya nuna musu hanyar da suka bi.
Sai gudu suke, suna haki tare da waiwayen baya, a duk lokacin da suka waiwayo sai su hango har yanzu fa a biye suke da su, su kuwa sai kururuwa suke suna biyarsu. Wasunsu da kibau wasu dauke da manyan itace, a jikinsu kuwa ba mai tufafi.
Za su tsira kuwa?
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣5⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_you don’t have to fear me, may be if you take your time to hear me, am sure you would learn to cheer me. It aint about me being a writer or a hip hop artist, I just hope that you could see the light before it is ruined_ Dr. Zain
*zuwa ga masoyana*
_ba shakka ku ne kwarin guiwata wurin rubuta wannan labarin, ina godiya sosai da addu’o’I da fatn alkhairi da kuke yi mani, haka ina jinjina maku da kauna da kuke nuna mani, inaso kusan cewa kuma kun zama wata gaba a rayuwata, soyayyarku tana yawo sosai a jiyoji hadi d jinina, kar ku barni domin ni ko da wasa ba zany ad ku ba, d inada zabi da a madubin rayuwata ku zan saka domin na dinga ganinku ko zan sami kwanciyar zuciya, ku nawu ne, ni kuma naku, irin ana mugu mugun tarennan_
*ci gaba*
Sai kokarin bace musu suke, amma abin y ci tura, duk lokacin da suka boye masu na wani lokaci, cen sais u gan su, a haka har safiya taw aye rana ta haur tsakiya si gudu suke, su kuwa ko alamun gajiya babu a tattare da su sai biyar su suke yi. Cen tsoho ya fadi ya kas tashi, suk tsya domin su bashi dauki, amma ya umarce su da su tafi kawai su bar shi, da kyar hadi da kukansu suka aminta suka bar shi, kasancewar ya nuna musu shi ba wata attaka da zai iya tabukawa, idan kum suka tsay, suma rayukansu za sui ya karewa, da ayi haihuwar guzuma, gar shi su barshin, ko ba komai zai rage masu saurinsu. Kan haka suka barshi suk ci gaba da gudun nemn kubuta daga mutuwa, tun basuyi nis ba, suka jiwo kararsa, almun sun farmsa ne, ko da suka waigo suk gay add suke cin namansa danye, tausayi ya hana sui ya kallon wannan rashin imani na wadannan mutanen, ko mu ce halittun. Suka ci gaba da gudu, ba treda sanin ina za su nufa ba.
Suna cikin gudu har suka zo wurin wani dutse mai kogo a jikinsa, ba tareda tsaiko ba suka runtuma ciki, haka suka cig ba da gudu a cikinsa, duk da kogo ne, a ciki ynada girma da fadi sosai, kamr dai wata katuwar hanya, ba abinda suke haduwa da shi idan ba kashin manyan dabbobi ba, gawarwakin manyan tsuntsaye, sunfi gudun awa biyu kafin su fita daga wannan kogon, da suka fita, kuma ba su tsaya ba a haka suka ci gaba da gudu, har sai da suka tabbatar da wadannan mutanen sun daina biyarsu, sai suka tsaya, suka rasa me ke damuwarsu, dattin jikinsu ko yunwar cikinsu ko gajiya da suka kwaso ta wannan gudun ceton rai.
A bangaren halittun kuwa, da suka g sun nema basu gan su ba, dole suka hakura suka koma mazauninsu.
“kai lallai mun kuru, wadannan marasa imanin da sun sami kama mu ai da tuni mun zama gawa, ji fa yadda suke tazgar naman dattijo, lallai duk wanda ya tashi a jeji dole ya yi dabi’u irin na dabbobi” Fate ta fada cikin muryar shessheka, Abdulsamad kuwa sai harararta yake yi a ransa yana cewa, kanku ake ji, ni yunwar cikina ita t dame ni.
“ba shakka ubangiji ne ke nuna buwayarsa garemu, yana kuma so mu kara gode masa da sanin cewa shi kadai zai iya kubutar da mu daga wannan ala’in, sau da yawa ubangiji yakan yi abu domin y jarraba imanin bayi, mu tamu jarabawa ke nan, sai mu dage mu cit a sosai, duk da haka, Fate ki kara tunani kan hujjoji d abubuwa da ke gudana, kisn cewa musulunci ne kadi addinin gaskiya, ki sallama, bakisani ba ko nan ne karshen rayuwarki” Ameer ya fada.
“har yanzu in bukatar hujjoji da za su gamsar da ni fiye da wadanda na mallaka”
Aseeya ta karbe, “ai kuwa ki tsaya wurin jiran hujjoji har lokaci ya kure maki, kinga gwanda ke, ni bari inyi sallolin da ke kaina” ta fada dai dai lokacin da take kokarin gyaran wurin da za ta yi taimama”
Bayan sun kammala sallolinsu, Ameer ya gabata domin ya gabatr da kansa. Sunana Shaheed ni haifaffen garin Kangiwa ne a nan Kebbi state, amma an haife ni a garin Sokoto a a unguwar ‘Yar Marina, a nan na far girma, si dag baya muka dawo nan Kebbi, nan nayi karatuna gaba daya, bancin university inda na karanci Pharmcy a UDUS. Ni kadai ne a wurin mahaifina da mahaifiyata, hakn ta san a taso cikin kulawa, duk abinda nake so ina samu dag mahaifiyata musammn, ia wani rubutu ne da ya shafi, boarder ta garin Dole kaina, shi ne dalilina n zuwa Kamba”
“taff! Yanzu kan rubutu shi ne za ka taso tun daga uwa duniya? Ai da sai ka rubuta duk abinda y zo maka a kai, naga galibi mrubuta hake kuke yi, ya fi maka wahalar bata lokaci da kashin kudin mota”
“hmmm! Abokina kenan, shi rubutu, daga cikin abubuwan da ke inganta shi, akwai kwakkwaran bincike, ba haka kawai ake rubuta duk abinda ya zo wa mutum ba, hakan ke sa marubuci ya fuskanci zagi da makamancinshi a wurin makaranta, yanada kyau, duk abinda za ka yi rubutu a kai, ka tabbatar haka abin yake, idan ma a kirkirarren labari ne, wurare da kayi amfani da su ko garuruwa, ka tabbatar yadda ka rubuta hak abin yake, duk da kai marubuci kanada damar kirkirar gari ka sk ms suna da kanka, amma idan ka yi amfani da gari sannne, dole ka rubutashi yadda yake.”
“na fahimta” Abdul ya fada.
Suka ci gaba da tafiya har suka tarar da wata ‘yar bukka a tsakiyar Jeji, cikin fari ciki, suka leka bukkar, amma ba kowa a ciki, kuma ba alamar mutum na zama a ciki, hakan yasa suka ci gab da tafiya, yunwar cikinsu kadaai tai she su. Sai faman jn kafafuwansu suke, shi Abdul a bangrensa kawai ayi shu, domin har hawaye ya zubar kan yunwa, Fate kuwa sai faman hasaso hujjiji take daga zuciyarta tana kwatantawa da addininta.
Tambaya a nan ita ce, shin za su tsira a wannan jejin kuwa ina suka nuf yanzu?
Labarin ya kusa karewa, gangarewa kawai ta rage muna….
DR.ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣6⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_a person is a person because of other persons_
*shafin masoya*
_wannan shafin naku ne musamman, *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*, muna godiya sosai da soyayya da kauna da kuke nunamuna, *UMM HANAN* ga tawu gaisuwa, haka ina mika gaisuwa tareda jajintawa abokiyar aikina *AUNTYMUMMY* FATIMA MALAMI LIMAN, Allah ya baki lafiya, ya kuma sa kaffara ce. ‘yan kungiyar *PEN WRITERS ASSOCIATION* na mika sakon gaisuwarsu sai mun zo cin kajin jinya_
Haka suka ci gaba da tafiya, ba tareda sanin ina ne gabas ko yamma ba har suka karaso wurin wani kudiddifi, suka ttsaya suka wanke jikinsu suka sha ruwa, sai a lokacin suka sami damar tattaunawa kan zuwa neman abinda za su sakawa cikinsu, Ameer ne ya nuna, sam bai dace su tsaya ba, domin shi wanda maciji ya sara, raga (tsumma) ma idan ya gani sai dai a cinmasa saman kafafuwansa. Dole suka daure suka ci daba da tafiya wacce ba tabbacin tsira a cikinta.
Kan hanyarsu ne suka hadu da barewa, ga shi ba wanda ke da ko kara a hannunsa, ganin bata gan su ba, suka umarci su Fate da su kwanta a kasa, da kyar Aseeya ta aminta ta kwanta, inda su mazan suka dinga lababenta har suka sami nasarar cafke ta, da kyar suka sami abu mai kaifi suka yanka ta suka gyara suka hura wuta suna fira suna gasa nama, Abdul kuwa sai faman hadiyar yawu yake yi, inda Ameer yake kokarin koyar da su addu’o’I da ya dace su karanta kafin su kwanta domin su sami kariya daga miyagun aljanu da dabbobi da ke kirshe cikin wannan jejin.
Nan Fate ta kada baki ta ce; “wacce addu’a kuma kake cewa su yi? Kai kullum addini dai addini, kuma ni har yanzu addinin naka banga ya fitar da mu daga wannan jejin ba”
“me kike ci na baka na zuba? Na sha gayamaki, ubangiji idan zai nuna buwayarsa, aikatawa kawai yake yi, ba tareda ya sanar ba”
“hmm! Tau za mu jira muga abinda zai faru”
Cikin takaici Aseeya ta harareta, har ta yi niyyar ta mayar mata da amsa, Ameer ya daga mata hannu, domin ya fahimci kudirinta, “ki mata uzuri, inada tabbaci kan ubangiji ba zai bar ta a hakan ba, zai bude idanuwanta domin ta ga gaskiya, ko ba komai ta fara yabawa dabi’unmu inaga wannan kadai makama ce”
Suna musanyar zance har suka ci suka koshi, shi Abdul dama tun fara cin naman ya dauki azumin magana, ganin sun ci har sun koshi, sai suka dauki hanya, suka ci gaba da tafiya, ga matsanancin duhu, ga shi sam ba susan ina za su dosa ba, tafiya ta yi tafiya, suna cikin tafiya suka ci karo da wani katon dodo, idanuwnsa jajur, ya fashe da wata mahukaciyar dariya, ya ce da su; “daman na sanar da ku cewa, ba ta yadda za ku fita daga wannan jejin, kuna tinkaho da ubangijinku, tau ya fiddaku mana, kuma kusani, zan shayar da ku daga mafi daci daga mutuwa”
“ba abinda za ka iya yi muna, face abinda ubangiji ya kaddara a kanmu, idan ma cutar da mu ka yi, tau ba shakka haka ubangii ya tsara” Ameer y fada cikin jarumta da rashin tsoro
“kai bil’adama, na fahimci kanada taurin kai, kai ko tsorona ba ka ji, har kake tinkara ta ga-da-ga? Lallai bil’adama akwai karmbani’
Bayan Ameer ya murmusa, sai ya bashi amsa, “me zai sa naji tsoronka, tunda kai ka kasa jin tsoron ubangijin da ya halicce ka, har kake so ka cutar da mu, mu fa nan duka jemagu ne, ba daren da ba mu gani ba, mun sakankance cewa *wuya ba ta kisa* kuma da ikon Allah za mu fita daga wannan jejin, kai kuwa za ka koma wurin mahaliccinka ka fuskanci hukunci”
Dodon ya fashe da wata mahaukaciyar dariya, sai ya tada hannayensa sama, sai ga wuta ta bayyana ta tinkaro su, ganin haka, suka tsorata musamman Abdul da Fate, Ameer ya karfafasu ta hanyar umartarsu da su dinga karanto ayoyin kur’ani, wutar ta taba su amma Fate kadai wutar ta kona, nan suka ci gaba da karatun kur’ani, sai ga wata kara ta bayyana, mai masifar karfi, sai komai ya tsaya. Ganin haka suka yi sauri suka bar wurin, sai waiwaye suke, har suka yi nisa, ga duhu ga rashin sanin ina za su dosa.
Suna cikin tafiya Fate ke faman jinyar raunin da ta samu daga wutar da dodo ya turo musu, ta kuma kada baki ta ce; “ya akai naga ku ba wanda ya konu daga cikinku, amma ni ga shi wuta ta kona ni?”
“Saboda mu mun karanta ayoyi ne daga littafin ubangiji, ayoyi da za su kare mu daga dukkan sharrin wata muguwar halitta, ke kuwa ba ki karanta ba”
“amma ai nima na karanto ayoyi daga namu littafin, me yasa duk da na karanto su kuma wutar ta shafe ni?”
Ni namu kadai na sani, zai yiwu naku littafin akwai canje-canje a cikinsa, har ta kai ayoyi da dama ba daga ubangiji ba ne, amma mu namu littafin ya tsarkaka daga canji, duk kalma da kika gani a cikinsa daga ubagiji ne”
“ya za ku iya gane cewa daga ubangiji ne, zai yiwu kuma naku kur’anin an canja shi.”
“ko kusa, ba wanda ya isa ya canja kur’ani, inda za ki fahimci haka, shi ne, duk yawan ayoyi na kur’ani, ba ko daya da ta ci karo da daya, sabanin littafinku da lokacin da aka yi bincike daga Jehova witnesses, suka ce sun gano kurakurai sama da dubu hamsin, na tabbata da za su kara bincikawa, da sun sami fiye da hakan, a kur’ani ba kuskure ko daya, a littfinku akwa tufka da warwara a ciki, a ku’ani ba wannan, a littafinku akwai batsa a ciki, a nammu ba batsa, littafinku akwai plagiarism (plagiarism shi ne yin copy na abu kalma da kalma) a littfinmu babu duka wadannan, kadan ke nan dag ma’aunin da muke iya gane cewa wannan littafin ya zo ne daga ubangiji”
“yanzu za ka iya nunamin duka wadannan a cikin littafinmu?”
“sosai zan iya nuna maki”
Aseeya ce ta karbe zancen, ta ce “hmmm! Lallai so kake iska ya wahal da mai kayan kara, matarnan fa ba ta da niyyar yin imani, amma ka nace, wai kai dan anace, tau sai ka buga muna wakar shagon mafara…
“kar ki taba yanke tsammni daga rahamar Allah”
Suna cikin zance, Ameer ya ce ku dakata, mun fita daga wannan jejin”
Cike da mamaki suka fara kallonsa, duk bakinsu a sake, “me yasa ka ce mun fita daga wannan jejin?”
“haba ku bude idanuwanku mana sai kace makafi……
Da gaske ne sun fit daga jejin?
Ya akai Ameer ya san sun fita, idan da gasken sun fita?
Idan ba su fita ba, me ye karshensu?
Munji Ameer zai ba wa Fate hujjoji, shin za ta gamsu ta karbi Musulunci kuwa, ko dai zancen Aseeya zai gasgata, cewa wahalar banza yake?
Duka amsoshin suna kunshe cikin shafi na gaba
Saur kiris mu rufe labarin
0 comments:
Post a Comment