Nan ta tashi ta koma daki.
Washe gari ta hada masa lafiyayyen break fast kamar yadda ta saba.
Sannan taje tayi wanka ta shirya cikin wasu kaya riga da skirt.
Taje kan dining ta dibi quaqer oats ta zuba madara da sugar tayi zaune tana shan abinta cike da natsuwa.
Tana cikin sha Hakeem ya fito kallo daya ya mata ya kauda kai ya fita daga cikin gidan.
Cike da tsana ta bishi da kallo a wahalalle mai girman kai domin tasan tabbas da yunwa ya fita kasancewar kuku baya nan.
Bayan ta gama taje ta gyara masa dakin sa tsaf ta kuma wanke masa inner wears din sa da sukayi datti ta goge ta feshe su da turare ta saka a cikin wardrobe.
Guraren 3:pm kwance take tana baccin da tun 12 ta fara shi.
cikin baccin ta ne taji Hakeem nata faman knocking cike da jin bacci ta tashi ta bude qofa wanda yayi dai dai da Hakeem ya watso mata inner wears d'in sa da ta wanke mishi.
Cikin masifa yace"this is d last warning kar ki sake ta6a min kaya! Idan ba haka ba duk abinda na miki ke kika ja.
kuma se ki san yanda zakiyi da kayan domin ba abinda zanyi dasu!
_"calm down pinky,kar ki yarda plan dinki ya watse._wani 6angaren zuciyar ta ne ke tausar ta, sbd Hakeem ya kaita qololuwa ta yanda ya watso mata kayan, hakan ta dake ta qirqiro hawayen
qarya,cikin muryar kuka mai ban tausayi ga duk wanda yaji.
tace"haba Bobby meyasa baza ka haqura mu ajiye qiyayya, mu koma tamkar yanda iyayen mu ke so..... qarya kike sam ba hakan a ranki kawai don wata banzar manufa ce yasa kike min haka.
_Lallai kayi gaskiya da wata manufa nake maka duk wadannan abubuwan ba don kyautatawa ba ko kuma don na kasance mata a gare ka, sae dae manufar da kake tunani sam ba ita bace_
Tayi maganar ne a zuci kafin take cewa a fili"Bobby sam abinda kake tunani ba shi bane kawai dai yanzu na fahimci cewa qiyayya ba abu ce mai kyau ba shiyasa nake son kaima ka fahimci hakan.
Kuma duk abubuwan da nake ma ina maka su ne a matsayin matar ka,domin samun dinbin ladar da ke tattare da hakan.....qarya kike!kuma koda da gaske kike ki sani tun ranar da aka daura auren mu na rubuta na ajiye ke ba mata ta bace sam ba aure tsakani na da ke!
Billy taji zancen Hakeem tamkar wanda ke sanar da ita an mata bushara da gidan aljannah.
Hakeem yaci gaba da cewa amma tunda kika ce haka daga yau duk wani aikin da ke cikin gidan nan ke zaki riqa yinsa tun daga aikin kuku har kan gate man zasu ajiye aikin su ki dora inda suka tsaya, don haka tun yanzu kije ki dora min indomie na baki nan da minti goma!
_"this guy wan kill me but zan amince da hakan bcs hakan zai qara ma plan dina qarfi domin na fahimci plan dina ya fara aiki a kansa sbd alamu sun nuna tunda ya fita ya kasa cin ko wane irin girki a waje ya kuma dawo gida ya tarar da banyi ba shi ne ya wani dora min aikin gidan gabadaya just bcs ya riqa cin girki na!Brovo alaiki ya Billy u have really got dis drama_
Can ta dago ta kalle shi tace"shike nan zanyi duk abinda kace amma kayi haquri ka kar6i kayan nan da na wanke ma domin shima yana daga cikin aikin da zanci gaba dayi as ur wife.
Nan ta bashi kayan a maimakon ya kar6a sae ma ya maida hannyensa baya yana kallon cikin idanun ta domin kawai ya gano ainihin abinda ke cikin ranta,Billy ta fahimci hakan shiyasa tayi saurin kauda idon ta, yace"idan da gaske kike meyasa zaki bani kayan, ai ke ya kamata ki shigar da su da kanki.
Shiru tayi ta fahimci lallai idan tayi wasa Hakeem zai gano ainihin plan dinta, ya zama dole ta kiyaye.
Tace"Afwan but nayi haka ne sbd naga baka son ina shiga ma d'aki anyhow,bata jira me zai ce ba tabi ta gefen sa ta mayarda kayan a mazaunin su ta fito, Hakeem kuwa yabi ta da ido yace a ransa
_"duk abinda kike shiryawa baza ki ta6a cin ma burin ki ba_ domin ko da kuskure bazan sake ta6a ko yatsar ki ba bare har nayi kuskuren wuce gun"
*Billy gir[truncated by WhatsApp]
[9/22, 6:27 PM] +234 810 038 8117: [8/7/2016] Billy giro😊:
*```👛BILLY PINKY DURLING ```👛*
*```Na Billy giro```😊*
*```page```*
*```👛19👛```*
Washe gari da asuba ta sallame sallah kenan taji Hakeem na mata knocking.
Koda ta fito ta same shi sanye da kayan exercise yace"kije ki wanke min mota kuma kar ki 6ata min lokaci domin zan fita da qarfe takwas.
Yana gama fada ya wuce Billy ta bishi da ido tace"da gaske yake son wahalda ni na ganin na kasa cimma burina,amma zan jure domin kaima naka lokacin zai zo da zaka shiga yanayin da baza ka iya fitar da kanka ba sae idan Allah ne ya fitar da kai,gwara ni kenan da in yanzu naso zan yakice wahalar.
Fitowa tayi harabar gidan da niyar tasa gate man yayi saurin wanke motar kafin Hakeem ya dawo daga gurin exercise.
Tsaye tayi cak tana kallon dakin gate man a rufe,
kenan Hakeem ya sallame shi, tace" laillai in yasan wata bai san wata ba ina da numbar gateman i will call him ryt now!....Hakeem ne ya katse mata hanzari da taga ashe cikin gidan ne yake exercise inda yake zagaye gidan da jogging.
_No prob pinky just go an wash d car zaki ci ribar hakan wata rana_.
Zuciyar ta ce ke bata hakan ta furta "OK"a fili,
ta shiga tunanin ta ya ma zata fara aikin da bata ta6a yi ba.
Komawa tayi daga ciki ta cire hijab ta dawo taje gurin motar ta dad'e tsaye tana kallon ta,
se can ta hango tiyo taje ta dauka tare da kunna fanfo ba shiri ta fara jin saukar ruwa a fuskar ta sbd kafin ta kunna fanfo bata lura da cewa bakin tiyon na facing din fuskar ta ba,a razane ta buga ihu tana ja baya yayinda ruwan ke ci gaba da watso mata a fuska har zuwa qirjin ta nan take ta jiqe kafin take fahimtar tiyon hannun ta ne ke watso mata ruwan domin ta manta cewa tana riqe da shi,
Jefar da tiyon tayi a qasa tana sauke numfashi hade da kallon tufafin ta da suka jiqe wato riga da wando na bacci,
rigar mai d'an siririn hannu wacce ta kai mata har guiwa wandon kuma dogo ne har qasa.
Guntun tsaki ta buga ta kama gashin kanta ta dunqule,sannan ta duqa tana nad'e qafar wandon ta,
sae dai tashin ta keda wuya qafar wandon ya walwale sbd sul6i ne da yadin.
A shagw6e take kallon qafar wandon fuskar ta kamar wacce zatayi kuka tace"oh no!
Duk abin nan da take Hakeem na kallon ta yana dariya cike da mugunta.
Suna hada ido tamkar bashi ke dariyar ba yayi mata kamar sam bai ma lura da abinda ke faruwa ba yaje kan resting chair ya zauna yana sauke gajiyar execise.
Nan taja tiyo ta tafi dashi gurin mota ta shiga watsa ma motar ruwa da taga koina ya samu taje ta kashe fanfo acewar ta gama wankin motar,domin tana kashe fanfo ta nufi qofar shiga gidan Hakeem yace ke zo nan,ba musu taje,yace me kike nufi da zaki fice baki gama wankin motar ba? Ai na gama wankin motar baka ga koinan ta ya sami ruwa ba... tsaki ya buga hade da jefa mata key yace dallah malama jeki bude gate man room ki dauko car wash da sosu ki wanke min mota!
Nan ta duqa ta dauki makullin ta 6oye damuwar da ke qoqarin bayyana a fuskar ta, ta qirqiro murmushi tace"sorry na manta ne.
Haka taje ta bude gate man room ta dauko abubuwan wankin mota har da qyallen gogewa.
Taje tana wankin motar cike da wahala sbd ta cika kumfa sosai,ga gashin kanta ya walwale sae faman wahalar gyaran sa take.
Da qyar ta kammala tayi tsaye riqe da qugu tana sauke numfashi,Hakeem da ke kallonta yace"indai wahala ce yanxu kika soma.
Bayan ta mayarda abubuwan wankin mota a gate man room ta rufe ta kawo masa key zata fice yace"kin manta da bawa flowers ruwa ne.... cak Billy ta tsaya tana jin kamar ta fashe da kuka domin bata ta6a wahala irin ta yau ba"tace a ranta"my plan gonna kill me amma wlh sae na jure domin bazan fara wahala a banxa ba.
Nan taje ta bawa flowers ruwa tana gamawa ta fice kitchen ta hada masa break fast dinsa sbd tayi zama d'aya ta huta.
Tana gamawa taje ta cire kayan jikinta ta bawa gado amana sae sha biyu ta tashi ta shiga toilet tayi wanka taje kitchen ta dora abincin rana.
Tana gamawa taje falo tayi zaune tana kallo.
Bata jima da zama ba ta shiga jin oda ba qauqautawa,
tsaki tayi sbd ta rasa inda oda ke fitowa.
Ba jinawa se ga Hakeem ya shigo gidan ransa baqiqirin ya kalli Billy da ke kwance tana hutawa Yace"be carefull kina wasa da aikin ki! kafin na bar gidan nan akwai abu biyu da bakiyi min ba,wato bani abinci da kuma bude gate sannan yanzu na dawo ina faman oda kika share ni!,, kayi haquri mantawa nayi bai ce da ita komai ba ya fice cikin 6acin rai.
Billy abin dariya ma ya bata tace"game din nan tamu da ban dariya take.
Hakeem kuwa da shigar sa daki ya fada toilet yayi wanka,ya shirya cikin kayan shan iska
Tana kwance taji fitowar sa ya wuce dauke da laptop yaje kan dining ya zauna ba 6ata lokaci ta bishi.
Hakeem ya wani hakince kamar wani Prince yana aiki da laptop Billy kuwa har ta zuba abinci a plate ta fara bashi a baki sae dae hankalin ta baya ga bashi abinci yana kan waya tana chat da qawayen ta.
Haka Hakeem kar6ar abincin kawai yake amma hankalin sa na kan laptop bai ankara ba yaji spoon kan hancin sa,
kai tsaye ya buge spoon cike da 6acin rai duk abincin ya watse yace"dama nasan qarya kike ba gaskiya a cikin zancen ki wace mace ce zata ce tana neman lada a gun mijinta amma tana bashi abinci hankalin ta na wani gun....sorry sorry please calm down, tabbas zance na da gaske ne,ka daina tunanin wani abu, fatana mu kasance kamar yadda iyayen mu ke so, amma kayi haquri da kuskuren da nayi a yanzu bada niya bane" ta fadi hakane yayinda ta langwa6ar da kai ta wani marairaice kamar da gaske.
Hakeem bai ce mata komai ba yaci gaba da aikinsa inda yake furta cewa a ransa
_"ai kuwa kaud'in bakin ki zai ja miki domin zan maida ke tamkar house girl_
Billy kuwa cewa take
_na fahimci kana min tsanani ne sbd na fara gajiya da hakan har ka samu ka gano ainihin plan dina ni kuwa bazan baka wannan damar ba duk abinda zaka min zan jure bazan yarda na nuna maka gajiyawa ta ba,domin nasan sannu sannu zaka nutse a cikin plan dina_.
Nan ta dauki wani spoon taci gaba da bashi abinci,
da ya gama ta kwashe kwanika ta kai kitchen bata fito ba sae da ta wanke su tas.
2 days latter .
zaune take kan bed daure da towel tana waya.
Hakeem ne ya shigo dakin ba ko sallama tayi saurin gyara daurin towel dinta sbd yanda ta daura shi da farko ana ganin rabin mamman ta.
Fuskar ta daure ta kalle shi bcs bata son ana shigo mata daki kai tsaye bai damu da yanayin fuskar ta ba yace"kije na fitar da kayan datti ki wanke ki goge.
Ya fita ba tare da ya jira amsar ta ba haka ita ma bata bashi amsa ba sae ma wayar ta da taci gaba dayi.
Bayan ta gama ta saka tufafi ta dauki waya ta nemo numbar gate man ta kira shi domin yazo ya wanke mata kayan in yaso ta biya shi.
Domin bata jin zata iya duk da kuwa suna da washing machine.
Bai jima ba yazo ta miqa mishi kayan dattin tace yayi sauri ya wanke ya goge kafin Hakeem ya dawo.
*Billy gir[truncated by WhatsApp]
[9/22, 6:38 PM] +234 810 038 8117: [ 8/8/2016] Billy giro😊:
*```👛BILLY PINKY DURLING```*👛
*```Na Billy giro😊```*
*```Page```*
*```👛20&21👛```*
Gate man ya wuce ita kuma ta koma ta kwanta a nan falo daga nan sae bacci.
Tana cikin bacci ne gate man ya kawo mata kayan har ya kammala,ta kar6i kayan ta bashi kud'i ya qi kar6a!tayi tayi yaqi kar6a,
bata yi mamaki ba sbd tasan sabon da sukayi ne yasa yaqi kar6ar kud'in bcs duk xuwan da suke dasu umma shine gate man d'in su.
Nan taje daki ta dauko wata had'addiyar sarqar indiyawa sabuwa dal wacce da gani zata yi tsada ta hado mishi da set din en hannu ta kawo mishi tace"ya kar6i ko wannan ya kai ma matar sa, ba musu kuwa ya kar6i kayan yana ta godiya cikin harshen turanci kamar yadda ita ma take masa magana a harshen turanci.
Da ya wuce ta wuce kitchen ta duba store duk kayan abinci sun qare indomie kawai ta rage.
Tsaki kawai tayi taje tayi kwanciyar ta domin bata jin zata iya fita ta siyo, ta maga kayan sun jima basu qare ba bcs ta siyo su ne a iya sati biyu,domin ta zaci two weeks zasuyi su koma sae taga har yanzu basu koma ba,inda ta rasa dalilin da yasa Hakeem ya wani zauna a garin kamar wani ma'akacin garin.
Daga haka ta koma bacci abinta.
Hakeem ne ya shigo riqe da hannun wata yarinya er 6 yrs,da gudu yarinyar taje kan jikin Billy tana fadin"didi"
Hakan yasa Billy ta farka tana ganin yarinyar ta sake mata murmushi tace"mimi keda waye? nuna mata Hakeem tayi dake qoqarin haurawa upstairs,sannan tace"da kuma yaya Naini ya tsaya a boys quarters zai saka kayan sa,ni kuma ga nawa a bakin qofa.
Billy da bata san makari ba ta kalli mimi a rashin fahimta tace"tare da ku zamu koma Nigeria?no didi zamu dai zauna a nan ne har su Abba su dawo... Ina suka je, cewar Billy wacce tayi maganar ne yayinda wani d'an saurayi ya shigo ta sakar mai murmushi tace"su Naini manya ba a ganin ku duk da muna gari d'aya, ba haka bane pinky kinsan karatu muke kuma lokacin exam ya matso ko yanzu karatun ne yaja mana baza a je da mu Nigeria ba...lah su Abba Nigeria sukayi? sosai kuwa....cike da shagwa6a tace"oh no ina ma za'a je dani,wlh Allah na matsu naje naga umma,,,
sosai shagwa6ar Billy ta bawa Naini shawa har ya jima yana kallon ta,
haka shima Hakeem dake saukowa ya kalle ta sau daya ya kauda kai tare da komawa upstairs.
Billy tace"zasu jima sosai kenan naga har akwati mimi tazo dashi kaima kuma ka shigar da kayan ka a boys quarters?eh to baza su jima a Nigeria ba daga can sae su wuce umrah, domin tun a last month suka so suje se wani aiki ya tsaida Abba,wanda shine ya kawo muku tsaiko kan komawar ku nigeria da wuri,
bcs baku jima da zowa ba Hakeem yaje gida yaji Abba na magana kan yana son suyi tafiya kuma baya son su bar mu,
mu kad'ai a gida nida Mimi to anan Hakeem yace da Abba ba matsala zaku jira har su Abba suje su dawo in yaso mu kuma mu dawo gurin ku da zama.
kenan can ne Hakeem ke zuwa kullum domin naga kamar kusan kullum sae ya fita?eh gaskiya kullum yakan je sbd wani aiki da yake taya Abba,, ok inace dai umma bata ga laifin rashin zuwa na ba?eh to bata ga laifin ki ba, sbd cewa tayi wai ke amarya ce baki isa fitowa ba...uhm umma kenan, Allah na dai ji kunya bcs tun zuwan mu fa sau daya na kira ta a waya,ta fadi haka ne yayinda ta haura sama naini kuwa ya bi ta da ido cike da so.
Zan muku d'an taqaitaccen bayani game da Mimi da Naini.
Wato sun kasance 'ya'yan aminin Abban Hakeem,asalin su en kaduna ne,suna zama new Delhi ne sbd nan mahaifin su ke aiki,suna jimawa sosai kafin su je Nigeria sbd karatun su da kuma aikin mahaifinsu wato Babban likita na fannin zuciya.
Naini abokin wasan Billy ne sosai,amma shi ba abokiyar wasa kadai ya dauki Billy ba,soyayya mai tsanani yake mata, sae gashi kwatsam yaji tayi aure duk da yaji hakan bai daina jin sonta ba.
ita kuwa Billy bata ma san yanayi ba,domin har yanzu a matsayin abokin wasa take daukar shi.
Wannan kenan.
Tana haurawa sama ta nufi dakin Hakeem tare da danna door bell sae da ya jima sannan ya bud'e,
tabi ta gefen sa ta shiga tare da rufe dakin,
Hakeem sae kallon ikon Allah yake kai tsaye ta shigo mai daki har da wani rufewa,
ta fahimci hakan amma ta basar tace"ba wani abu bane dama ba kayan abinci gashi anyi baqi,,,to me yasa da kika ga ba kayan abinci bakije kin siyo ba? koda naga hakan lokaci ya qure,indomie kadai tayi saura kuma kasan Naini baya cin indomie....sae kisan yanda zakiyi da shi,
ni kije ki hado min indomie nida Mimi,bafa komai a gidan nan da zan bashi kamata yayi kaje ka siyo kayan abinci....wani banzan kallo ya mata yace nayi miki kama da d'an aike....oops sorry zanje d'in da kaina but kudin hannu na sun kusa qare min,bai ce mata komai ba yaje ya zaro kudi ya jefo mata, nan ta duqa ta dauka, tana dagowa suka had'a ido inda ta dawo mishi Billyn da,
wato shaye da toka tana masa kallon kafa raina ni da yawa, a nan take kuma ta dawo Billyn yanzu tace"to yanzu zan dafa ma indomie kafin na tafi ko? Da a tunanin ki zaki bar gidan nan baki dafa min ba!...... Mtsw! ya buga tsakin ne yayinda Billy ta fita daga d'akin yace"oh God! meyasa su Abba suka had'a ni da ke,
bayan baki dace da rayuwa cikin mutane ba face cikin dabbobi domin kullum daqiqancin ki sea abinda ya qaru!
Sak Billy taji abinda ya fada sbd bata riga ta rufe qofar ba tace a ranta
_"ni da kai za a ga wanda zai qare a daqiqi marar fahimta fatana kawai Allah ya kaimu lokacin da plan dina zai gama had'uwa_
nan ta qarasa rufe qofar ta wuce.
Taje ta had'a mishi indomie shida Mimi.
Naini kuma ta kai masa abin motsa baki kafin su sayo kayan abinci a dafa mishi.
Bayan sun gama ne Billy taja Mimi da Naini suka je shopping inda suka bar Hakeem shi kadai a gida ya fito balcony yana karatun jarida.
Sun jima sosai kafin su dawo.
Suna isowa ta fada wanka tayi shirin shiga kitchen.
White rice ta had'a da stew wacce taji naman kaji,koda ta kammala anyi magrib.
Sae da akayi isha'i sannan suka zauna ma cin abincin,
Billy ce ta zuba musu abinci wanda kallo d'aya Hakeem ya masa yaji ransa yayi mugun 6aci,ta gefen ido Billy ke kallon shi inda take dariyar mugunta cikin ranta sbd tasan ya tsani white rice da stew, wanda tayi hakan ne da gayya sbd qin zuwan da yayi na siyo kayan abinci.
Komai ya kasa cewa ya tashi ya bar gurin.
Nan naini ya shiga tambayar lafiya?Billy tace"no kar ka damu may be lalura ce ta kama shi,,"ok" cewar naini daga nan yaci gaba da cin abincin sa.
Bayan sun gama cin abinci sun huta,Naini yaje 6angaren sa domin ya watsa ruwa haka Billy da mimi suka tashi domin zuwa shirin kwanciya.
Hakeem kuwa yana shiga d'aki ya dauki makullin mota ya fita.
Koda ya dawo ya sami Billy da Naini kowannen su da shirin bacci, ya kalli tufafin da ke jikin Billy riga ce handless iya guiwa sae ihu take cike da murna sbd wata game din tserar mota da suke ita da naini,
Nainin da sam hankalin sa baya kan game sae Billy yake kallo wacce keyin komai cike da sha'awa.
Nan Hakeem yaje ya kashe TV Billy tayi saurin kallon shi yace"ki tashi ki koma daki kin bar Mimi ita kadai,
tashi tsaye tayi hade da bubbuga qafafun ta a qasa cike da shagwa6a tace"uhm uhm oh Bobby why!? ya zaka zo ka kashe mana tv bayan kaga yanda hankalin mu ya karkata a can, indai akan Mimi ne fa bacci ma take,but please Bobby kaga yanzu 9:30 tayi idan 10:00 tayi Allah zan koma daga ciki please Bobby kar kace a'a.
Hakeem kam shiru yayi yana kallon yanda take zuba mai shagwa6a tamkar umma ce a gabanta har da wani buga qafa a qasa.
Kauda idon sa yayi cike da ganin yarintar Billy ya kalli Naini wanda ya mato gun kallon Billy har ma wani murmushi ke bayyana a fuskar shi.
Nan ma ya kauda idon shi ya kalli Billy wacce har yanzu begging dinsa take.
Cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa yace"ki wuce daga ciki bana son ganin ki a nan!
Tap idanun ta suka cika da qwallah domin ba qaramin takura ta Hakeem yayi ba, wanda duk shagwa6ar nan da ta masa tayi ne don ta samu ya barta ta qarasa game d'in ba wai don plan d'inta ba bcs at all 6acin rai ya mantar da ita kan plan d'in da take had'awa bare har ta fahimci wani abu a ga me da Bobby kan abun da ya mata yanzu.
Sae da ta wuce ya kalli Naini wanda ransa bai masa dad'i ba kan ganin ran Billy ya 6aci.
Hakeem kuwa duk haushin naini yake ji amma haka ya da ke yace"sorry Naini i dnt mean to hurt you kasan halin ta bata san me take yi ba.
*```Billy giro😊```*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 6:41 PM] +234 810 038 8117: [8/9/2016] Billy giro😊:
*```👛BILLY PINKY DURLING ```*👛
*```Na Billy giro😊```*
*```page```*
*```👛22&23👛```*
Washe gari da safe Billy ce da Mimi suka sauko downstairs suka sami Hakeem da ke jiran fitowar Mimi domin ya kai ta school.
Kallon Billy yake wacce yaga idanun ta sun kumbura da alama kuka tayi kan game d'in da ya hana ta qarasa.
Girgiza kanshi yayi yace a ransa"wai ko dai yarinyar nan ta manta cewa tare da Hakeem take ba umma ba.
Mimi ce ta kula da kallon da yake ma Billy tace"yaya kai ma ka fahimci didi bata da lafiya ko?
ta6a jikin ta ma kaji yanda yayi zafi.
Ta fadi haka ne yayinda ta riqo hannun Hakeem zata kai jikin Billy.
Cikin hikima ya hana faruwar hakan bai yarda ya ta6a jikin Billy ba sae break fast din Mimi ya kar6a a hannunta da ke cikin lunch box.
Yaja hannun Mimi suka fita.
Yayinda Billy ta bi bayan su taje ta bude musu gate sannan ta dawo cikin gida ta fada toilet zuwa wanka.
Ta fito ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu zubin ta kamar arabian gown.
Saukowa tayi downstairs wanda yayi dai dai da shigowar Hakeem shida Naini suka nufi dining.
Ta same su a can ta d'an saki fuska suka gaisa da Naini.
Sannan ta zuba musu abinci.
Ta zauna kusa da kujerar Hakeem zata fara ciyadda shi ya kar6i spoon din yace jeki yau bana buqatar hakan.
Kallon sa tayi tace a ranta"ai dama don ka wulaqanta ni ne kace na riqa baka abinci ammà baya daga cikin aikin gidan nan...
Me kika ce?
Da mamaki Billy ta kalle shi domin tasan maganar ta bata fito ba bare ace yaji me tace, tace"ai banyi magana ba... Kinyi magana man a cikin ranki domin yanayin fuskar ki ya nuna hakan, sanin kanki ne tun farko ke kika fara dorawa kanki lalurar gidan nan ba wani yace kiyi ba, wanda kinyi haka ne don wata banzar manufar ki.
Bobby ka fahimce ni mana har ga Allah manufar da kake tunani ba ita bace.
Abinda na gaya ma d'in dai ne....
naji da Allàh kar ki cika mu da surutu.
Nan Billy ta d'ibi quaker oats ta zuba madara da sugar ta wuce.
Naini ya bi ta da kallo har ta shige daki bai janye idon shi ba.
Hakeem da ke kallon shi yace"ya dai Naini ko wani abu kake buqatar ta kawo ma ne?
Ajiyar zuciya ya sauke yace"no ba komai"
Daga haka sukayi shiru basu sake cewa komai ba,Hakeem sai kallon naini yake kamar wanda ke son ya fahimci wani abu.
Suna kammala cin abinci naini ya wuce school.
Guraren qarfe biyar Naini da Billy ne ke volleyball cike da nishadi yayinda kowannen su ke sanye da games wears sbd dama haka suke da sun had'u guri d'aya basu da aike sae volleyball.
Suna cikin wasar ne suka ji oda Billy ta tafi cikin jogging ta bud'e gate da suka shigo ta rufe,ta koma kan wasar su.
Naini yace ina gate man dinku da kika bude gate?
Baya nan,
tayi maganar ne a taqaice taja hankalin sa suka ci gaba da volleyball.
Mimi wacce Hakeem ya dauko daga school taxo da gudu billy na ganin ta ta tarbe ta tana mata wlcm.
Nan suka ajiye wasar suka shiga daga ciki akasin Naini da ya wuce 6angaren shi.
Bayan Billy tayi ma Mimi wanka ta bata abinci taci kuma bata fito ba sae da ta tabbatar bata buqatar komai.
Tana fitowa ta sami Hakeem zaune a falo yana waya,
ta fita haka yace ina zuwa?
Ta d'an yi mamaki amma ta basar otace"zanje mu qarasa Volleyball nida Naini.....so kike ki bar Mimi ita kad'ai bayan yanzu ne dawowar ta. Game take bata buqatar fitowa.
Ki dai koma daga ciki ba inda zakije.
Ba musu ta koma bcs bata son ranta ya 6aci irin na jiya.
Sae dae wani abun yau kusan kwana uku Hakeem na mata abu d'aya wato yana hana ta fita suyi volleyball ita da Naini wanda ta kasa gane dalilin hakan,gashi tasan cewa ba yau ya saba ganin tana wasa da Naini ba duk zuwan da suke da su umma shine abokin wasan ta hakan yasa ta shiga dogon tunani can tace"kodai plan d'ina ya kama shi ta 6angaren da na fison ya kama shi, wata zuciyar ta ce da wuri haka?
haka ne but ba mamaki amma yanzu xan gawada wani abu naga idan haka ne.
Nan ta fad'a toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wasu en iksan tufafi, sae dai tayi matuqar kyau.
Ta fito tana tauna chewing gum cike da natsuwa.
Qamshin turaren ta ya bawa Hakeem damar kallon ta inda ya shiga qarewa suturar jikin ta kallo.
Riga ce iya guiwa mai dogon hannu sae dae gabadayan ta net ce tsaf ake hango er fincikar rigar ciki wacce iya mammanta ta tsaya bata da mara ba da bz sae dan guntun wandon da ya tsaya mata iya cinya yayi mata d'as a jikin ta.
Wani hair style ne tayi ma gashin ta mai kyau kamar wacce taje saloon.
Tana sanye da takalma masu tsini.
Bai yi mamakin ganin dressing din ta ba sbd haka ko gida haka take abin ta idan bata fita,ma'ana iyakar ta ta zauna da shi a cikin gida domin shaqatawa.
Tana saukowa ta nufi gun center table ta dauki key zata fita Hakeem yace"ajiye min makullin mota.
Ba musu ta ajiya ta nufi hanyar fita yace"ina zaki je bayan kinsan Mimi awa daya ta rage naje d'auko ta daga school,
wa kika ajiye wanda zai kula da ita?
Ai bazan jima ba tana gama fada ta sa qafa ya sake dakatar da ita Yace"ina zaki je da en iskan kayan nan sae kace wata arniya!
Wani irin farin ciki taji amma ta nuna 6acin rai a fili.
Ta shagwa6e fuskar ta sosai tace"Oh Bobby city beach fa zan tafi idan bansa kayan nan ba wanne kake so na sa, domin kasan ko rigar nan ta sama idan naje cire ta zanyi domin naji dadin shiga ruwa, please ka bar ni naje nan da 30mnt zan dawo.
Wani mugun kallo Hakeem ya sakar mata wanda yasa ta bar gurin cike da shagwa6a tana kuka.
Hakeem bai daina kallon ta ba sae da ta shige daki ya tashi ya rufe qofa hade da zare key ya tafi da shi dakin sa.
Billy na shiga daki ta fada kan gado cike da murna tace"tabbas gayen nan ya fara sona bai sani ba that's my plan yanzu abinda ya rage na fara nuna maka so kamar da gaske but not now zan dai ci gaba da shagwa6e ma sannan daga bisani na fara nuna ma so sannu sannu kamar yadda nawa son ke shigar ka.
Bazan qarasa plan d'ina ba har sae ka fahimci kana sona ka kuma zurfafa a ciki ta yanda rashi na zaiyi iya illata ka, ni kuma a lokacin zan zille ma na nuna ma sam ba sonka a cikin zuciya ta basaja ne kawai, na kuma had'a ma sharrin da su Abba zasu raba auren mu kai tsaye bcs abinda zan fad'a da kuma shaidar da zan bayar qwaqqarar shaida ce wacce da a raba auren da kar a raba ba aure a tsakanin mu.
Bayan kwana biyu kwance take kan bed sae juyi ta ke duk taji ba dadi tana son tayi volleyball amma tasan Hakeem zai iya hana ta tunda yana gida gashi yanzu take son suyi kafin Naini yaje lectures bcs yàu evening lectures ne da shi.
Tana nan kwance taji oda tsaki ta buga sae kuma taji dad'i Hakeem zai fita ta samu suyi wasar kafin ya dawo.
Nan ta tashi taje tana zuwa ta same shi har ya cika fam yana jiranta cikin hanzari ta bud'e mishi gate ya fita ta rufe ta tafi 6angaren naini bata jima ba suka fito.
Suka fara volleyball.
Sun jima sosai suna yi sae taji odar Hakeem ya dawo nan taje ta bud'e mai gate ta dawo suka d'ora inda suka tsaya.
Hakeem ya fito daga cikin mota ya kalle su sau d'aya ya wuce daga ciki.
Billy ta bishi da ido domin tayi tunanin zai ce mata wani Abu.
Falo yaje ya zauna yana hutawa sae yaji yana son fitowa waje ya sha iska.
Da jaridar shi ya fito yaje kan resting chair ya zauna iska mai dad'i na buso masa.
Su Billy kuwa na ci gaba da wasar su sai ihun murnar ta ake ji duk Hakeem yaji ta fara damun sa
Hakan yasa ya dago ya kalle ta tana gudu zata d'auko qwallo cikin gudun ne accidentally qafar ta ta bugi d'ayar qafa ta fadi had'e da sakin ihu.
Da gudu Naini yazo zai kama ta, isowar Hakeem ya dakatar da shi da cewa"barta kawai"
sannan ya kalli Billy shaye da toka wacce ke ihu had'e da kuka yace" da Allah malama rufe mana baki duk kin bi kin cika gidan nan"cikin muryar kuka tace"Bobby wani abu ya shige min a qafa.... naji tashi muje daga ciki...shagwa6e mai tayi kamar yarinya er shekara hud'u tace"uhm uhm Bobby bazan iya tashi
ba ji nake kamar qafata ta karye, kuma gurin da wani abu ya shiga yana
fitar da jini sosai"
ta fadi hakane yayinda ta nuna mai yaga tabbas ba wasa jini ke fita a gurin.
Ya durqusa gab da ita yana qarewa gurin kallo kamar wani doctor, nan ya fahimci d'an wani dogon kare ne kaurin sa da tsayin sa zai kai stick d'in ashana,gashi kad'an ya rage ya qarasa shigewa cikin qafarta.
A hankali yakai hannun sa gun,
Billy ta jaye qafar da sauri tana kuka had'e da yarfi da hannu ta kalle shi da idanun ta da ke ta zubar da hawaye tace"Bobby Allah ciwo nake ji sosai muje daga ciki tukun ko za a cire"
Kauda idon sa yayi gefe yana tunanin to ya zai yi,kallon naini yayi kafin yake maida duban sa gun Billy yana kallon ta kamar mai wani shawara a ransa.
A hankali naga yakai hannun sa ya d'auki Billy cak,wanda yayi dai dai da saukowar ruwan sama, bai yi mamaki ba domin yasan da hadarin, kallon Billy yayi wacce tayi saurin cusa fuskar ta a qirjin sa, sbd ko kad'an bata son jin saukar ruwan sama a jikin ta, yayi second biyar yana kallon ta sannan ya kama hanya.
Naini kuwa kallon su yake kamar wanda zai yi kuka har suka shige daga ciki.
*```Billy giro😊```*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 6:44 PM] +234 810 038 8117: [9:14PM, 8/11/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na Billy giro😊*
*Page*
*👛25 to 28👛*
Da dare bayan har sunyi shirin kwanciya ba su riga sun kwanta ba,sbd zaune suke kan bed amma Billy har ta kwanta Mimi kadai ce a zaune tana shan cornflakes sbd yau Billy bata iya dafa musu abincin dare ba.
Knocking suka ji,
Billy tace "yes come in"
A hankali Hakeem ya bude qofar ya shigo dauke da leda biyu a hannun sa,
Yakai d'aya kan drawer ya ajiye sannan ya bawa Mimi dayar"ya shafo fuskar ta tare da fadin sorry Mimi Allah na manta cewa yau baza mu sami dinner ba"no ba komai yaya.
Nan ya bude ledar gasasshiyar kaza ce da fresh milk yace sae ki fara ci ko, kallon Billy tayi tace"Didi zo muci"
no bacci nake ji bazan iya cin komai ba yanzu, amma didi fruits kawai naga kinsha fa,don't worry ci kawai kinji"
ta fadi haka ne yayinda ta juya musu baya ta qara jan blanket d'in jikin ta.
Mimi tace"pls yaya muci tare domin bana jin dad'in ci ni kad'ai.
Ba musu yasa hannun sa suka ci.
Bayan sun gama ne Mimi ta tashi ta nufi toilet, shi kuma ya tashi zai bar dakin ya kalli Billy wacce tuni baccin ta yayi nisa yaje ya dauke ledar da ya ajiya kusa da ita kan drawer,
ya saka a fridge yayinda Mimi ta fito toilet ta kwanta.
shi kuma ya fita hade da kashe wutar d'akin.
Washe gari da asuba Hakeem ne ya dawo daga masallaci,
yaje dakin Billy yana knocking bai shiga ba sae da Billy ta bashi izini.
Ya shigo yayinda Billy ta 6alla wutar d'akin had'e da yaye blanket dinda ke jikin ta.
Ta tsure qafar ta da kallo kamar yadda Hakeem ke kallon,
qafar nan yagà ta qabe sosai.
Kauda idon sa yayi yace"kinyi sallah kuwa?
shiru ta mishi domin tasan fashin sallah ta ke haka shima bai ce mata komai ba face"idan kin gama bacci anjima doctor zai zo ya duba qafar, ta gyada mai kai kafin yake fita.
Ta koma ta kwanta.
Da yake yau weekend ba zancen tada Mimi tayi shirin zuwa school.
Sae guraren qarfe goma ta farka ta samu ta lalla6a ta shiga wanka ta shirya sannan ta tada Mimi ita ma tayi wankan.
Gabad'ayan su gidan da tea sukayi break fast,suka had'a da d'umamen leda biyu na gasasshiyar kazar jiya wacce Billy bata ci ba da ta kuma Hakeem.
Bayan sun gama ne Hakeem ya kira doctor, koda doctor ya duba qafar ya fahimci tayi targad'e.
nan doctor yace da Hakeem sae fa anja qafar,no ba komai kayi duk abinda kake ganin ya dace.
Duk suna magana a harshen hausa ne kasancewar doctorn bahaushe ne aiki ya kawo shi new Delhi asalin sanin sa da sukayi shine doctorn Abban Hakeem,tun a Nigeria.
Nan doctor ya kai hannu yana qoqarin fara jan qarfar,
Billy tayi saurin kallon Hakeem tace"please Bobby ni kawai ya ban magani gurin ya warke ba sae an ja ba, Hakeem bai ce mata komai ba yayi kamar ma bada shi take magana ba face doctor da ya ce, dole sae anja domin daidaita qashin da yaje inda bai dace ba.
Ba yanda ta iya amma ji take kamar ta fara kurma ihu kafin aja qafar.
Nan ya fara jan qafar a hankali tun tana jaquri har ta fara sakin ihu,ta kama pillow ta matse sosai kamar wacce ke shirin raba shi biyu,kuma duk ta wani cusa fuskar ta a ciki yayinda ta shiga roqon a barta ta huta tukun.
Hakeem yace da doctor barta d'in ta huta but idan zaka sake jan qafar ka mata zama d'aya domin ka huta da ihun ta....no Bobby kar ya min zama d'aya Allah zan iya mutuwa,Hakeem bai ko kula ta ba sae ma fita yake qoqarin yi daga d'akin.
Doctor yace"da dai ka barta a mata a sannu d'in sbd qafar ta kwana ba a ja ba, akwai zafi sosai.
kawai kayi yanda nace.
yana gama fad'i ya tafi d'akin shi ya dauki laptop ya zauna ya bud'e haka sae ya tsaya cak sbd ihun Billy da yaji sau d'aya bata sake ba.
Tashi yayi yaje d'akin ya sami Billy ta sauka kan bed tana faman yarfi da hannu tana wahalallen
Kukan da ko sautin sa baya fita.
Hakeem ya maida dubansa gun doctor yace hope ka kammala?yace eh tare da rubuta masa maganin da zai siyo mata tasha sannan ya tarkata kayan sa ya bar gidan.
Hakeem ya kalli Billy da ke jingine jikin bed ta dora kai kan guiwoyinta tana ci gaba da kuka.
Har zai fita daga d'akin sae kuma yaje gab da ita ya durqusa har yana shaqar qamshin turaren ta wanda yasa ya d'an ja baya kad'an sbd wani dalili nashi.
Yace kinga malama kukan ya isa haka idan ba so kike kija ma kanki wani ciwon ba.
Dagowa tayi tana kallon shi da idanuwan ta da suka cika tap da qwallah yana kallon cikin idon ta,
yayi saurin jaye idon shi a hankali sae kuma ya sake kallon ta yace"mene ne?
le6ace baki kawai tayi ta fashe mishi da wani sabon kuka mai cike da shagwa6a.
Sauke ajiyar zuciya yayi a hankali ya tashi ya fita daga d'akin.
Ya fito falo ya sami Naini da Mimi tana zuba mishi surutu shidai ko kula ta baya yi,bcs yanayin sa suku suku kamar mai wani tunani.
Yana ganin Hakeem yace ko zan iya zuwa naga pinky? Ba yabo ba fallasa ya kalle shi kafin yake cewa "eh".
Nan suka haura sama shida Mimi shi kuma Hakeem ya fita daga gidan.
Bai wani jima ba ya dawo ya zarce sae dakin Billy d'auke da magunguna a hannun shi,ya ajiye maganin kan drawer yace ki duba kowanne da akwai yanda zaki shashi a rubuce.
Sannan ya kalli Naini wanda ke kallon Billy tana share hawaye zata koma kan bed ta zauna.
Yace"Mimi kuzo muje falo"nan suka tashi suka bar Billy ita kadai,wacce bata bi ta kan magani ba sae kwanciyar ta da tayi.
Haka ta yini kwance sae da dare ta d'an ji sauqin qafar ta,ta tashi kenan mimi tace "Didi tun dazu fa yaya ya kawo wata leda inaga abincin ki ne,sbd mu har munci namu"ok bari nayi brush.
Tana shiga toilet,sae ga
Hakeem yayi knocking Mimi ta bud'e mai tare da fad'in "didi ta tashi amma ta shiga toilet zata yi brush"
no nazo ne naji ko kinci naki abinci eh yaya nayi jiran ka har na gaji shine mukaci nida yaya Naini,yace "ok" ya juya zai bar dakin.
Ita kuwa Billy Koda ta shiga toilet se taji tana buqatar ta watsa ruwa a nan toilet corner ta cire kayan jikinta
ta daura towel ta qarasa shiga toilet tare da yaye towel ta ajiye a mazaunin shi,
zata shiga gurin wanka kenan sae kawai wutar toilet d'in ta d'auke ihu ta saki tana mai lalabar towel d'in ta.
Hakeem da ke qoqarin fita daga d'akin ya tsaya cak yana sauraren yanda billy ke faman ihu kamar wacce taga abin tsoro bcs akwai wuta a dakin ta toilet kad'ai ta d'auke.
Toilet d'in ya shiga domin ganin mene ne sae kawai wutar ta kawo.
Yayi tsaye yana kallon Billy wacce ta rufe fuskar ta da towel wanda ya sauko tun daga kan fuskar ta har zuwa cinyoyinta ya rufe,
sae ihu take saki taqi d'agawa koina kuma taqi bud'e fuskarta bare ta fahimci wutar ta kawo sae can taji kamar mutum ya shigo ta fara jaye towel d'in a hankali har ta bud'e fuskar ta.
Tana ganin Hakeem ta qara danne towel d'in da ke kan qirjinta had'e da turo baki tace"to ni ka fita ka wani tsaya kana kallo na"
Kauda kansa yayi yayinda d'an guntun murmushi ke son bayyana a fuskar sa,yace a ransa"wai meyasa nake son childish behavior nata.. bcs hakan na mata kyau sosai,
cewar 6angaren zuciyar sa,yace"no ba haka bane nida komai nata baya birge ne bare naga tamin kyau har nayi sha'awar hakan, its just bcs inajin nishadi a yau.
Nan ya gama zancen zucin sa ya fice Billy tayi murmushi had'e da girgiza kanta tace"za dai ka gano ne nan gaba.
Bayan ta fito daga wanka ta d'auko Vaseline tana shafawa,Mimi tace"didi kar ki shafa mai kan qafar ki mai ciwo bcs akwai wani magani da naga uncle ya shafa miki kina bacci"
Billy tayi fari da ido tace
_"a ranta amazing yanzu har hakan ta fara faruwa tsakani na da Bobby"_
Sannan tace da Mimi a u sure? Allah kuwa didi, kingan shi ma,
ta bude ledar magungunan da Hakeem ya ajiye a dazu ta dauko mata maganin,
tube ne d'an qarami da shi,ta dubi instruction nashi sau uku ake shafa shi a rana ta matsa maganin ta fara shafawa yayinda fuskar ta ke d'auke da murmushin da ita kadai ta baiwa kanta sani.
Bayan ta gama shiri ne ta bud'e ledar abincin ta,
snacks ne a ciki da gasasshiyar kaza.
Ta tashi da d'an d'ingishin ta taje ta bud'e fridge ta dauko freshmilk tayi sanyi har ta gaji taje ta zauna taci abinci tasha magani.
Bayan kwana biyu da faruwar haka qafar Billy tayi sauqi sosai domin har girki ta ci gaba da dora musu.
Hakeem,Naini,Mimi sune zaune kan dining Billy na zuba musu abincin dare.
Fried rice ce wacce taji spices taji komai yanda ya kamata sae qododi dake yawo cikin ta.
Hakeem ya kalli abincin sau d'aya ya kauda kai"yace wai ke meyasa long time kin daina min favourite food d'ina?da mamaki ta kalle shi domin tasan ko wannan favourite food d'insa ne tace"kamarya?i mean tuwon shinkafa da miyar ganye... oh yes naga baka son ayi maka tuwo da wata shinkafa face er gote kuma dama er goten da kaga ina yi maka tuwo da ita a kwanaki wacce su umma suka ta6a bari ce wani zuwan da mukayi kafin wannan,
kuma ba wani yawa ne da ita ba bcs kasan its just bcs of u ake zowa da ita.
Ajiyar zuciya yayi cike da damuwa Yace olryt.
Nan yaja plate suka fara cin abinci shida Mimi.
Naini kuwa shi kadai yake cin abinsa haka ita ma Billy amma farfesun kaji ne take sha.
Haka rayuwar su taci gaba yayinda yanzu Hakeem komai yaga Billy tayi sae yaga hakan ya bashi sha'awa amma yaqi yarda da abin da zuciyar sa ke son raya masa na cewa he is in love wit her,,, just ya d'auki abun a zaman da suke guri d'aya ne ya kawo hakan.
Sbd yanzu duk inda Hakeem yake,sae Billy tayi qoqarin ganin tana gurin,sbd qarawa plan d'in ta qarfi wanda
ko school Hakeem zai kai Mimi sae Billy tayi ta begging d'in sa cike da shagwa6a kan zata yiwa Mimi rakiya.
Shi kuwa Hakeem shagwa6ar da Billy keyi mishi kesa ko yayi niyar dizgata se ya sami kansa da kasawa hakan yasa yake zuwa da ita wanda har suje su dawo ba mai ce ma wani qala sae idan Billy ce tayi magana.
Kwance yake a falo kan sofa sanye da singlet da three quarter da alama bashi da lafiya domin alamu sun nuna hakan.
Billy ce ta sauko downstairs sanye da riga pink handless wacce tsayin ta bata qarasa kai mata a guiwa ba,
tazo ta zauna qasa kusa da kujerar da Hakeem ke kwance idanun sa a lumshe suke amma Billy na zama ya bude su a hankali,ta sakar mai sexy eyes d'inta tace"zakaci wani abu kafin doctor yazo?um um bana jin yunwa ruwa kawai nake son sha.
Nan ta tashi ta kawo mishi ruwa bai kar6i ruwan ba sae da ya tashi zaune yayinda Billy ta bashi ruwan,sai da yasha sannan ya koma ya kwanta.
Billy ta wani nuna damuwa sosai a fuskar ta tana mishi sannu kamar da gaske.
Kallon ta kawai yayi bai ce da ita komai ba Yace"ki tashi kije daga ciki doctor na kan hanya kuma kinsan bai kamata yazo ya ganki da kayan da ke jikin ki ba"
Ba musu ta miqe yayinda Hakeem ya shiga tsananin mamakin kansa da furta hakan, meye damuwar shi koda a tsirara doctor zai ganta,wata zuciyar tace ka furta haka ne kawai sbd ita musulmace haramun ne wani wanda ba muharramin ta ba ya ganta haka.
Billy kuwa cike da sh'umin murmushi ta shiga d'aki sbd ta fahimci yanda Hakeem ya shiga mamakin kansa sosai.
Zuge zip din rigarta tayi ta cire rigar ya zamo daga ita sae pant ta jawo towel ta daura sbd wanka take so tayi amma bata shiga wankan ba ta tsaya gyaran d'aki.
A 6angaren Hakeem kuwa Billy na tashi sae ga doctor.
Sai da suka d'an gaisa
yace da Hakeem me kake jin yana maka ciwo a jikin ka? Kawai ka duba ni doctor bcs bansan ainihin abinda ke damuna ba.
Nan ya shiga dube duben shi a jikin Hakeem inda yake mishi wasu tambayoyi yana bashi amsa.
Bayan dube duben shi da jin amsoshin Hakeem,
sae yayi shiru kamar mai mamaki har yana d'an jinjina kan sa,
can dai ya dafi kafad'ar Hakeem ya fara magana cike da natsuwa yace"Hakeem ba wani abu ne ke damunka ba face tsantsar sh'awa!
da mamaki Hakeem yace as how doctor? I mean kana buqatar kasancewa da mace!
Hakeem ya qara jin
zancen wani iri yayi murmushin yaqe yace"doctor bancin matar da nake da,
sae na nemo wata macen? Hakeem kenan kar ka manta kana tare da doctor ne,domin a binciken da nayi na fahimci sha'awar da ke dauke da kai ba alamar ka kusanci mace nan kusa ma'ana ka jima sosai baka kusanci matar ka ba!
kan Hakeem ne ya kunce domin shi a iya sanin sa bai ta6a jin yana buqatar mace ba, bare shi da ke tare da Billy ta ya zai sakawa kansa buqatar mace bcs Billy fanko ce ba abin sha'awa bace,kawai dai yasan idan ya shaqi qamshin turaren ta yakan ji wani yanayi a jikin sa har dai idan tana kusa da shi, haka idan tana mishi shagwa6a ji yake kamar ya rungomo ta yana lallashin ta...doctor ya katse shi da cewa Hakeem ya kamata ka ajiye wata qiyayya da girman kai,ka kar6i abinda kake buqata a gurin matar ka,idan ba haka ba sha'awar nan zata kai ga illata ka..... Pls doctor ka daina wannan zance bcs even yesterday night I slept with my wife ta ya zaka ce wani sha'awa ce ke damuna!
D'an guntun
murmushi doctor yayi yace a ransa.
_nayi boko kayi boko baza mu nuna wa junan mu wani abu ba,but zan nuna ma nafika yawan shekaru na kuma nuna ma ba abu d'aya muka karanta ba_
Yace "shikenan kayi haquri da nayi ma rashin fahimta amma ina zuwa,
nan ya tashi ya fita bai wani jima sosai ba ya dawo,
yace da Hakeem ga wannan magani kasha,
magani ne wanda idan an kasa gane ainihin matsalar mutum idan ya sha shi inshaAllah zai ji sauqi,
Ba musu Hakeem ya kar6i tablet d'in yasha.
Yayi minti d'aya da shan maganin,
yace doctor maganin nan jiri yake sawa ne?
sorry ba jimawa zaka daina jin haka but idan ba damuwa ko zaka kira min pinky nayi mata en wasu tambayoyi a game da ciwon ka?
Da qyar Hakeem ya iya ce mishi ba damuwa" sbd wani yanayi da ya fara jin kanshi,
nan ya tashi ya tafi sae tangad'i yake kamar wani mashayin da yasha ya fara buguwa a haka har ya shiga d'akin Billy.
Doctor ya girgiza kansa yace a ransa"lallai Hakeem da pinky duk da had'a ku auren da aka yi bai sa kun haqura kun shirya kanku ba,
amma ba komai na kusa kawo qarahen abun,domin wannan maganin da kasha ba zai ta6a baka damar fitowa a dakin pinky ba har sae ka kusance ta!
Yana gama fad'ar haka ya fita daga gidan.
Hakeem kuwa yana shiga d'akin Billy....
*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 6:47 PM] +234 810 038 8117: [ 8/15/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na*
*Billy giro😊*
*page*
*👛33&34👛*
Hannun ta ya ajiye a hankali hade da fitar da ajiyar zuciya, ya d'an kauda kansa gefe ya kuma sake kallon Billy wacce har yanzu idon ta yana kanshi.
Idanun ta ne suka ciko tap da qwallah sbd rad'ad'in bala'in da take ji a qasan ta, ta shiga kallon yananyin d'akin cike da mamaki yayinda hawaye ke qoqarin gangarowa kan kumatun ta,cike da damuwa Hakeem ya d'an matsa kusa da ita tare da riqo hannun ta kamar mai son cewa wani abu.
Billy kuwa cikin muryar kuka tace"Bobby me yake faruwa da ni ne?
Shiru Hakeem yayi ya rasa me zai ce da ita, domin ko kad'an baya son tasan dalilin faruwar hakan.
Hannun ta da yake riqe da shi ya ke faman murzawa a hankali cike da tunanin me zai ce mata.
Sautin kukanta ne ya dawo dashi,
yayi saurin kallon ta hade da girgiza mata kai alamar ta daina kuka.
Cike da shagwa6a ta fizge hannunta da yake faman murza tace"to ni ka sanar dani me ya faru dani har ka kawo ni asibiti?
cikin muryar lallashi abinda bai ta6a yi mata ba yace"shi kenan kukan ya isa haka kiyi shiru idan kina son na sanar da ke kinji, nan ta share hawayen ta kamar wata er baby tace"to fad'amin ina jinka, um um ni bazan gaya miki ba sae kinci abinci tukun, yayi maganar ne tamkar da qaramar yarinya yake magana kuma yana sane yayi hakan just bcs ya samu ya lalla6a ta.
Bata ce da shi komai ba har ya tashi ya fita daga d'akin.
Bai wani jima ba ya dawo dauke da leda a hannun sa,ya sami Billy sae qoqarin tashi zaune take cike da son tayi kuka,cikin hanzari Hakeem ya qarasa gurinta yace"mene ne?ina so na zauna amma inaji kamar bazan iya ba,
lumshe idonshi yayi a hankali ya ajiye ledar da ke hannun sa,ya taimaka mata ta zauna.
Sannan ya dauko ledar da ya shigo da ita ya bud'e ba wani abu bane face snacks da danqwaleliyar gasasshiyar kaza yakai gaban ta ya ajiye ta tsure abincin da ido kawai ba alamar zata ci.
Ganin haka yasa ya gutsura naman kaza ya kai mata a baki bata bud'e bakin ta ba sae kallon sa take kamar mai magana cikin ranta,can ta bud'e bakin ta a hankali ya saka mata.
Da haka yaci gaba da ciyar da ita har sae da tace ya ishe ta.
Nan ya tsiyaya ruwan lemu fresh one ya bata,wad'an da dama akan kawo ma patients su had'e da abinci amma sanin bata cin abincin ya siyo mata wani .
A hankali ta koma ta kwanta yasa top bedsheet ya rufa mata har zuwa qirjinta.
Billy sae kallon sa take kamar wani baqon ta tace"Bobby baka gaya min ba,bari kiyi bacci tukun kinji.
Kamar zata ce wani abu sae kuma ta fasa.
Sannu sannu kuwa ta fara jin bacci na fizgar ta har ta rufe idonta.
Hakeem kuwa yana tsaye a kanta kamar wani bodyguard sae can ya zauna wanda yayi dai dai da shigowar doctor.
Doctor yace ya ake ciki ta koma bacci ne? Eh, ok inace ka sanar da ita dalilin zuwan ta asibiti domin nasan da tashin ta ta buqaci jin hakan,
Ban sanar da ita ba domin bansan a ya zata d'auki abun ba... Kaga ka sanar da ita kawai meye a ciki,matar ka ce fa, sae dae kuskuren ka d'aya girman kan da kasa na qin sanar da ita buqatar ka kaje ka saka mata maganin bacci a ice cream domin ka biya buqatar ka, ba tare da ta sani ba, wanda nasan jin hakan ne kad'ai zai 6ata mata rai, amma ai kai namiji ne zaka iya shawo kanta idan kaso,, sae da ya nisa sannan yace haka ne doctor zan gwada yin hakan.
Duk maganar nan da sukeyi sak a kunnen Billy wanda ta tsinci kanta cikin tashin hankali har ta qagu doctor ya fita.
Fitar sa keda wuya ta yaye bedsheet d'in jikin ta ta jefar da shi,ta kalli Hakeem cikin tsananin tashin hankali hawaye wani na bin wani bakinta na rawa tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Bobby cin amanar da kamin kenan!
ka rabani da budurci na domin kawai ka lalata min rayuwa!
Cike da son yi mata bayañi ya tashi yayinda
ta wani sauka kan bed da qarfi kamar ba wacce akayiwa aiki ba.. Hakeem yace"No ba fa haka bane saurare ni kiji....a fusace taci kwalar shi tace"me zanji! me zaka ce dani! bayan ka lalata min rayuwa!why Bobby! why baka kashe ni ba a lokacin da ka gama keta min haddi!?why!?
da sauri Hakeem ya rungumo ta sbd yanda take jijjiga jikin ta sosai, gashi yana gudun ta jiwa kanta ciwo, yace"nifa ban kusance ki ba ki saurareni kiji.... Qarya ne!
ta fad'i haka ne yayinda ta fizgi jikin ta daga nashi taci gaba da cewa"bcs wannan rad'ad'in da nake ji a qasa na bazai ta6a bani damar yarda da zancen ka ba!azzalumi macuci wlh sae Allah ya isar min
domin bazan ta6a yafe maka ba!
"Ya salam"
cewar Hakeem wanda yaji komai ya cakud'e masa,
Sae ga wani tashin hankali wato hango jini na sauka a qafafun Billy, domin da qarfi ta fizge kanta daga jikin Hakeem.
Kafin Hakeem yace komai sae ga doctor ya shigo cikin sauri sbd jin hayaniya,doctor yace"subhannallah! Hakeem ya akayi haka ta faru? cikin rud'u Hakeem ke kallon doctor ya rasa me zai ce da shi,doctor ya kalli Billy wacce ke kuka sosai mai tsima zuciya,jini na faman sauka a qafafunta,cikin kuka ta durqusa kan guiwoyinta ba tare da ta damu da jinin da ke fita a jikin ta ba,
sae maganganu take kan Hakeem ya cuce ta.
Wanda nan Doctor ya fahimci komai,yaje gab da ita yana so ya mata bayani yanda abun yake....tayi saurin sa hannu ta rufe kunnuwanta tace"bana son jin kamoi doctor! bana so!domin naji komai a kunne na kuma naji a jikina da gaske ne abun,domin inajin zafin rad'ad'in abinda ya min!
Tana gama fad'a ta share hawaye da takaici ta nufi hanyar fita daga d'akin kamar wata zautacciya, Hakeem yayi saurin kamo ta,doctor Yace"dora ta kan bed ayi mata allurar bacci"
Da qyar Hakeem ya d'ora ta domin sae fizge fizge take tana kai mai cizo ta koina wanda da qyar doctor ya samu ya mata allura.
A tare suka sauke ajiyar zuciya cike da damuwa.
Nan doctor ya fita sae gashi ya dawo tare da wata baindiya wato likitar da tayiwa Billy aiki,
Nan doctor yaja Hakeem suka fita waje.
Zaune Hakeem yake amma kwata kwata hankalin sa baya gurin sae halin da Billy take ciki yake tunani..... Wayar sa ce tayi qara koda ya duba Naini ne,maida ta kawai yayi a aljihu domin baya jin zai iya receiving call a halin da yake ciki,yana ji tana ta faman ruri har ta tsinke.
Docta na fitowa Hakeem ya miqe da hanzarin sa ta dakatar da shi kan cewa bazai sami shiga yanzu ba domin ana buqatar Billy ta sami hutu sosai.
Jiki sanyaye yaje ya zauna sae dai ya kasa zama ya kasa tsayi har sae da yaje nan wani guri da ake hango mutum ta jikin glass ya leqa inda yaga ancanza mata uniform din jikin ta ancire wad'an da suka 6aci da jini har bedsheets d'inma duk an canza,ya jima yana kallon ta sannan ya koma ya zauna tare da zaro wayar sa ya kira Naini sukayi magana.
Sai gashi ba a wani jima ba yazo hankali tashe duk yabi ya shiga damuwa.
Da qyar Hakeem ya samu ya kwantar mai da hankali kan cewa ba wani abu bane.
Sae da ta tashi daga bacci ne aka basu damar shiga wanda a lokacin har Hakeem yaje ya d'auko Mimi daga school.
In banda kuka ba abinda Billy keyi,
Naini yayi iya qoqarin sa na ganin ta daina kuka tayi magana amma taqi haka ko Mimi,
bare shi Hakeem da baya ko son yayi magana ta hau shi da masifa kan abinda bai riga ya aikata ba.
Washe gari aka sallame ta,suka koma gida.
Har akayi kwana biyu Billy bata da aiki sae kuka duk tabi ta rame lokaci d'aya.
Sosai Hakeem ya shiga damuwa ya rasa ta yanda zai yi ya rarrashi Billy domin ya samu ya fahimtar da ita.
Guraren qarfe biyu na dare Hakeem ya fito daga d'akin shi sbd yaji fitowar Billy,
yana kallo taje kan two seater ta zauna wacce yaga har yanzu tana cikin qunci sosai,sae faman share hawaye take domin yanzu aikin kenan,kamar daga sama yaji ta fashe da wani sabon kuka ta hade kai da guiwa.
Sosai kukan ya ratsa jikin Hakeem,ya koma dakinsa cike da damuwa ya d'auko wasu takardu kamar na asibiti.
Ya sauko downstairs gaban Billy ya durqasa kan guiwoyinsa kafin yace komai ta d'ago sbd motsin da taji ta kalli Hakeem da yayi kneel down a gaban ta,sae kawai taga ya kama kunnen sa yace"please am sorry *Pinky*,am so sorry.
0 comments:
Post a Comment