Hannun ta ya ajiye a hankali hade da fitar da ajiyar zuciya, ya d'an kauda kansa gefe ya kuma sake kallon Billy wacce har yanzu idon ta yana kanshi.
Idanun ta ne suka ciko tap da qwallah sbd rad'ad'in bala'in da take ji a qasan ta, ta shiga kallon yananyin d'akin cike da mamaki yayinda hawaye ke qoqarin gangarowa kan kumatun ta,cike da damuwa Hakeem ya d'an matsa kusa da ita tare da riqo hannun ta kamar mai son cewa wani abu.
Billy kuwa cikin muryar kuka tace"Bobby me yake faruwa da ni ne?
Shiru Hakeem yayi ya rasa me zai ce da ita, domin ko kad'an baya son tasan dalilin faruwar hakan.
Hannun ta da yake riqe da shi ya ke faman murzawa a hankali cike da tunanin me zai ce mata.
Sautin kukanta ne ya dawo dashi,
yayi saurin kallon ta hade da girgiza mata kai alamar ta daina kuka.
Cike da shagwa6a ta fizge hannunta da yake faman murza tace"to ni ka sanar dani me ya faru dani har ka kawo ni asibiti?
cikin muryar lallashi abinda bai ta6a yi mata ba yace"shi kenan kukan ya isa haka kiyi shiru idan kina son na sanar da ke kinji, nan ta share hawayen ta kamar wata er baby tace"to fad'amin ina jinka, um um ni bazan gaya miki ba sae kinci abinci tukun, yayi maganar ne tamkar da qaramar yarinya yake magana kuma yana sane yayi hakan just bcs ya samu ya lalla6a ta.
Bata ce da shi komai ba har ya tashi ya fita daga d'akin.
Bai wani jima ba ya dawo dauke da leda a hannun sa,ya sami Billy sae qoqarin tashi zaune take cike da son tayi kuka,cikin hanzari Hakeem ya qarasa gurinta yace"mene ne?ina so na zauna amma inaji kamar bazan iya ba,
lumshe idonshi yayi a hankali ya ajiye ledar da ke hannun sa,ya taimaka mata ta zauna.
Sannan ya dauko ledar da ya shigo da ita ya bud'e ba wani abu bane face snacks da danqwaleliyar gasasshiyar kaza yakai gaban ta ya ajiye ta tsure abincin da ido kawai ba alamar zata ci.
Ganin haka yasa ya gutsura naman kaza ya kai mata a baki bata bud'e bakin ta ba sae kallon sa take kamar mai magana cikin ranta,can ta bud'e bakin ta a hankali ya saka mata.
Da haka yaci gaba da ciyar da ita har sae da tace ya ishe ta.
Nan ya tsiyaya ruwan lemu fresh one ya bata,wad'an da dama akan kawo ma patients su had'e da abinci amma sanin bata cin abincin ya siyo mata wani .
A hankali ta koma ta kwanta yasa top bedsheet ya rufa mata har zuwa qirjinta.
Billy sae kallon sa take kamar wani baqon ta tace"Bobby baka gaya min ba,bari kiyi bacci tukun kinji.
Kamar zata ce wani abu sae kuma ta fasa.
Sannu sannu kuwa ta fara jin bacci na fizgar ta har ta rufe idonta.
Hakeem kuwa yana tsaye a kanta kamar wani bodyguard sae can ya zauna wanda yayi dai dai da shigowar doctor.
Doctor yace ya ake ciki ta koma bacci ne? Eh, ok inace ka sanar da ita dalilin zuwan ta asibiti domin nasan da tashin ta ta buqaci jin hakan,
Ban sanar da ita ba domin bansan a ya zata d'auki abun ba... Kaga ka sanar da ita kawai meye a ciki,matar ka ce fa, sae dae kuskuren ka d'aya girman kan da kasa na qin sanar da ita buqatar ka kaje ka saka mata maganin bacci a ice cream domin ka biya buqatar ka, ba tare da ta sani ba, wanda nasan jin hakan ne kad'ai zai 6ata mata rai, amma ai kai namiji ne zaka iya shawo kanta idan kaso,, sae da ya nisa sannan yace haka ne doctor zan gwada yin hakan.
Duk maganar nan da sukeyi sak a kunnen Billy wanda ta tsinci kanta cikin tashin hankali har ta qagu doctor ya fita.
Fitar sa keda wuya ta yaye bedsheet d'in jikin ta ta jefar da shi,ta kalli Hakeem cikin tsananin tashin hankali hawaye wani na bin wani bakinta na rawa tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Bobby cin amanar da kamin kenan!
ka rabani da budurci na domin kawai ka lalata min rayuwa!
Cike da son yi mata bayañi ya tashi yayinda
ta wani sauka kan bed da qarfi kamar ba wacce akayiwa aiki ba.. Hakeem yace"No ba fa haka bane saurare ni kiji....a fusace taci kwalar shi tace"me zanji! me zaka ce dani! bayan ka lalata min rayuwa!why Bobby! why baka kashe ni ba a lokacin da ka gama keta min haddi!?why!?
da sauri Hakeem ya rungumo ta sbd yanda take jijjiga jikin ta sosai, gashi yana gudun ta jiwa kanta ciwo, yace"nifa ban kusance ki ba ki saurareni kiji.... Qarya ne!
ta fad'i haka ne yayinda ta fizgi jikin ta daga nashi taci gaba da cewa"bcs wannan rad'ad'in da nake ji a qasa na bazai ta6a bani damar yarda da zancen ka ba!azzalumi macuci wlh sae Allah ya isar min
domin bazan ta6a yafe maka ba!
"Ya salam"
cewar Hakeem wanda yaji komai ya cakud'e masa,
Sae ga wani tashin hankali wato hango jini na sauka a qafafun Billy, domin da qarfi ta fizge kanta daga jikin Hakeem.
Kafin Hakeem yace komai sae ga doctor ya shigo cikin sauri sbd jin hayaniya,doctor yace"subhannallah! Hakeem ya akayi haka ta faru? cikin rud'u Hakeem ke kallon doctor ya rasa me zai ce da shi,doctor ya kalli Billy wacce ke kuka sosai mai tsima zuciya,jini na faman sauka a qafafunta,cikin kuka ta durqusa kan guiwoyinta ba tare da ta damu da jinin da ke fita a jikin ta ba,
sae maganganu take kan Hakeem ya cuce ta.
Wanda nan Doctor ya fahimci komai,yaje gab da ita yana so ya mata bayani yanda abun yake....tayi saurin sa hannu ta rufe kunnuwanta tace"bana son jin kamoi doctor! bana so!domin naji komai a kunne na kuma naji a jikina da gaske ne abun,domin inajin zafin rad'ad'in abinda ya min!
Tana gama fad'a ta share hawaye da takaici ta nufi hanyar fita daga d'akin kamar wata zautacciya, Hakeem yayi saurin kamo ta,doctor Yace"dora ta kan bed ayi mata allurar bacci"
Da qyar Hakeem ya d'ora ta domin sae fizge fizge take tana kai mai cizo ta koina wanda da qyar doctor ya samu ya mata allura.
A tare suka sauke ajiyar zuciya cike da damuwa.
Nan doctor ya fita sae gashi ya dawo tare da wata baindiya wato likitar da tayiwa Billy aiki,
Nan doctor yaja Hakeem suka fita waje.
Zaune Hakeem yake amma kwata kwata hankalin sa baya gurin sae halin da Billy take ciki yake tunani..... Wayar sa ce tayi qara koda ya duba Naini ne,maida ta kawai yayi a aljihu domin baya jin zai iya receiving call a halin da yake ciki,yana ji tana ta faman ruri har ta tsinke.
Docta na fitowa Hakeem ya miqe da hanzarin sa ta dakatar da shi kan cewa bazai sami shiga yanzu ba domin ana buqatar Billy ta sami hutu sosai.
Jiki sanyaye yaje ya zauna sae dai ya kasa zama ya kasa tsayi har sae da yaje nan wani guri da ake hango mutum ta jikin glass ya leqa inda yaga ancanza mata uniform din jikin ta ancire wad'an da suka 6aci da jini har bedsheets d'inma duk an canza,ya jima yana kallon ta sannan ya koma ya zauna tare da zaro wayar sa ya kira Naini sukayi magana.
Sai gashi ba a wani jima ba yazo hankali tashe duk yabi ya shiga damuwa.
Da qyar Hakeem ya samu ya kwantar mai da hankali kan cewa ba wani abu bane.
Sae da ta tashi daga bacci ne aka basu damar shiga wanda a lokacin har Hakeem yaje ya d'auko Mimi daga school.
In banda kuka ba abinda Billy keyi,
Naini yayi iya qoqarin sa na ganin ta daina kuka tayi magana amma taqi haka ko Mimi,
bare shi Hakeem da baya ko son yayi magana ta hau shi da masifa kan abinda bai riga ya aikata ba.
Washe gari aka sallame ta,suka koma gida.
Har akayi kwana biyu Billy bata da aiki sae kuka duk tabi ta rame lokaci d'aya.
Sosai Hakeem ya shiga damuwa ya rasa ta yanda zai yi ya rarrashi Billy domin ya samu ya fahimtar da ita.
Guraren qarfe biyu na dare Hakeem ya fito daga d'akin shi sbd yaji fitowar Billy,
yana kallo taje kan two seater ta zauna wacce yaga har yanzu tana cikin qunci sosai,sae faman share hawaye take domin yanzu aikin kenan,kamar daga sama yaji ta fashe da wani sabon kuka ta hade kai da guiwa.
Sosai kukan ya ratsa jikin Hakeem,ya koma dakinsa cike da damuwa ya d'auko wasu takardu kamar na asibiti.
Ya sauko downstairs gaban Billy ya durqasa kan guiwoyinsa kafin yace komai ta d'ago sbd motsin da taji ta kalli Hakeem da yayi kneel down a gaban ta,sae kawai taga ya kama kunnen sa yace"please am sorry *Pinky*,am so sorry.
*Billy girotruncated by WhatsApp]
[9/22, 6:58 PM] +234 810 038 8117: [8/12/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na*
*Billy giro😊*
*Page*
*👛29&30👛*
Ya sameta taña gyaran tufafin ta da ke cikin wardrobe,
yayi seconds 5 a tsaye yana kallon ta sae yaji wani irin abu yana qara fizgar shi har dai yanda ya ganta d'aure da towel, ganin kansa kawai yayi rungume da ita, Billy kuwa a firgice ta juya domin ganin wanda ya rungume ta, sbd bata koji shigowar shi dakin ba.
sosai ta firgita ganin Hakeem kuma gashi ya damqi towel d'inta yana qoqarin raba ta da shi,hannu tasa ta riqe towel d'in gam tana kallon Hakeem da duk ya fita hayyacin sa, tace"Bobby lafiyar ka meye haka?please Bobby stop it"Hakeem kam sae qara matse ta yake a qirjin sa kamar wanda ke shirin mayadda ita cikin jikin shi ga towel d'in ta da yake ta faman ja wanda Billy ta jimqe gam taqi yarda ya raba ta da shi,bakin ta yake qoqarin lalubowa ya had'a da nashi,
tayi saurin kauda fuskar ta sae kawai taji harshen sa cikin kunnen ta yana yawo da shi cike da qwarewa har wani abu take ji kamar bacci mai dad'i na fizgarta,hakan yasa ta fara jin wani yanayi a jikin ta wanda bata ta6a samun kanta a ciki ba, nan jikin ta ya fara rawa tana fitar da numfashi slowly slowly kamar yanda take jin harshen Hakeem yana yawo a cikin kunnen ta,kuka ta fashe dashi sbd wata irin matsa da yayi mata Hakeem ya tsaya cak ya daina lasar kunnen ta ba tare da ya sassauta matsar da yayi mata ba.
Yayi minti biyar matse da ita kafin yake bude idanun sa da sukayi jajir tare da fizge towel d'in ta da qarfi ya jefar,
Billy ta buga ihu hade da kare qirjinta tana Bobby stop it!
Hakeem kuwa tunda ya jefar da towel ya tsure gurin da ya jefa towel da ido sbd hango pad da yayi a gurin,
wanda hakan yasa ya fara sassauta riqon da yayi mata nan ya saki jikin ta gabad'aya ya fita daga d'akin kamar wani zautacce.
Billy tayi saurin sama d'akin key taje ta fad'a kan bed ruf da ciki tana qoqarin ganin ta saisaita kanta, amma tayi minti ashirin kafin take samu jikin ta ya daina rawa.
Tashi tayi ta dauko towel d'inta anan taga pad wanda garin gyaran wardrobe ne ya fad'o bata sani ba, dauke shi tayi ta mayar.
Ta daura towel taje kan bed ta zauna ta dafe kanta da take jin yana mata ciwo yayinda ta shiga tunnin me yake faruwa da Hakeem haka,sae kace wanda ya shiga convulsion,but ai ba haka yanayin convulsion yake ba,amma tabbas da akwai abinda ke damunsa sbd sam ba a hayyacin sa yake ba,ko kuma doctor ne ya bashi maganin da yafi qarfin jininsa,haka ta qaraci saqe saqen ta bata gane komai ba,
Kallon agogon dakin tayi taga lokacin d'auko Mimi daga school ya kusa gashi tasan Hakeem bazai iya zuwa ba,
jiki sanyaye ta fad'a toilet.
Bayan ta shirya taje ta d'auko Mimi.
Har dare Billy bata sake ganin Hakeem ba kuma bata nemi sanin halin da yake ciki ba asali ma bata da tabbacin yana gidan ko baya gidan.
Zaune suke kan dining suna dinner nan Naini ke tambayar Billy,cewa"har yanzu Hakeem jikin ne da bai samu ya fito cin abinci ba?
mimi tace"nima yaya naini tunda na dawo banga yaya Hakeem ba na dauka ko yayi tafiya ne.
Billy sae jin su take bata ce dasu komai ba.
Kallon ta kawai naini yayi wanda ya fahimci tunda ya shigo suka suku yake ganin yanayin ta ko magana bata cika son yi ba.
Nan ya tashi ya nufi d'akin Hakeem yayi ta knocking ba alamar za a bude,
nan ya bude dakin a hankali ya shiga ya sami Hakeem qundundune cikin blanket sae rawar dari yake,koda Naini yaje kusa da shi yaji jikin sa yayi zafi sosai har blanket din da ya rufa dashi ya d'auka.
Sosai Naini ya shiga rud'u domin kallo d'aya zakayi Hakeem ka hango mutuwa kusa da shi sbd yanda ya fita hayyacin sa gabad'aya,
Naini bai tsaya wata wata ba ya kira wani doctor abokin mahaifin sa.
Ba jimawa yazo sae sauri yake sbd akwai inda zaije hakan yasa bai yi wani qwaqqwaran bincike kan Hakeem ba yace typhoid'fever ke damun shi nan ya rubuta mishi magunguna,yayi mishi
allurai biyu ya wuce.
Da safe Billy ta fito ita da Mimi suka same shi kwance ya d'an ji sauqi bisa ga jiya, amma duk da haka kallo d'aya zaka yi mishi ka fahimci yana jin jiki sosai.
Naini ne ya shigo da sallamar sa yayi ma Hakeem ya jiki sannan ya ja hannun Mimi domin zuwa kai ta school.
Bayan sun fita ne ita ma Billy ta juya zata fice sae kuma ta tsaya ba tare da ta juyo ba tace na kawo ma breakfast d'inka yanzu?
shiru yayi bai ce da ita komai ba domin baya jin buqatar komai face ya kasance da ita, shiyasa ya matsu ta bar gurin domin baya son ya sake samin kansa a cikin yanayin da ya sami kansa jiya wanda shi kadai yasan azabar da yaji na rashin samun ta.
Ganin bai ce da ita komai ba ta wuce.
Yau kusan kwana biyu Hakeem na faman jure azabar da yake ji har ma baya son ganin giftawar Billy,
shiyasa ma ya fara kulle kansa a daki.
Da ya gaji da zaman dakin ne ya fito waje domin ya sha iska,sae ga Mimi tazo ta same shi riqe da ribbon a hannun ta tace"please yaya ka samin didi sallah take koda na fito gurin wanka,shiru Hakeem yayi yana tunanin kenan Billy tayi wanka,
bcs duk a tunanin sa pad d'in da ya gani ranar ya zaci fashin sallah take shiyasa ya barta.
Nan ya ci gaba da tunanin yau zai kawo qarshen azabar da yake ji kullum ba sassauci,
kuma fa baya son zubar da ajinsa na nunawa Billy buqatar sa,sae dae kuwa idañ tana cikin bacci zai kusance tunda ba virgin bace bare in ta farka ta fahimci wani abu,amma kuma wane irin bacci ne da har zan kusance ta bata farka ba.....kawai ka bata maganin bacci mai qarfi tasha, zuciyar sa ke gaya mishi hakan, yace"ta yaya?... ta hanyar sa mata a abun sha....but a yaya zanyi wannan aikin,
Wannan karon zuciyar sa bata ce mishi komai ba sae tunani ya shiga yi da kanshi.... Mimi ce ta katse shi da cewa please yaya,,,sorry Mimi ban iya sa abun nan ba,nan ta koma daga ciki ya ci gaba da tunanin yanda zai yi.
Da dare guraren qarfe 9:00 Mimi ce tazo ta sami Billy ta fito daga wanka ta bata ledar ice cream tare da fad'in yaya yace a kawo miki sannan idan kin gama sha kije ki gyara mishi d'aki.
Tana gama fad'a ta fita taje suka sha nasu ice cream ita da Hakeem.
Billy kuwa sae da ta shirya sannan tasha nata ice cream ta tashi taje d'akin Hakeem domin gyara mishi.
Tunda ta shiga Hakeem ke faman dubin agogo da yaga tayi minti goma da shiga ya kalli Mimi yace "je ki kwanta kinsan akwai school gobe",
ba musu ta tashi,
haka shima yabi sayunta,
Mimi ta shiga d'akin Billy shi kuma ya shiga nashi.
Bai yi mamakin ganin Billy kwance tana bacci kan bed d'insa ba sbd yasan hakan zata faru.
Sae da yaje ya saka key sannan ya rage hasken d'akin amma duk da haka akwai d'an haske.
Kayan jikin sa ya fara cirewa kafin yake hawa kan bed,ya tsure Billy da kallo yana mai jin tsananin baqin cikin kusantar ta da zai yi sbd bai ta6a kawo hakan zata shiga tsakanin sa da ita ba,sae dae kuma ya gwammaci ya kusance ta kan yaje ya aikata zina.
Yana gama tunanin sa ya cire mata rigar da ke jikin ta ya jefar,ya zamo daga ita sae pant,nan yabi surar jikin ta da kallo cike da ban sha'awa har dai qirjinta da yafi daukar hankalin sa, a hankali ya kai hannu ya zare pant d'in jikin ta tare da rungomota jikin sa ya fara wasa da sassan jikin ta ta koina, musamman qirjinta da yafi maidawa hankali.
*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 7:00 PM] +234 810 038 8117: [ 8/13/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na Billy giro😊*
*Page*
*👛31&32👛*
Haka Hakeem yaci gaba da aikin shi na ganin ya cimma burin shi amma yayi 1hour yana fafutukar cimma burin sa ya kasa,
kansa ne ya d'aure sosai domin shi dai ba daga gareshi matsalar take ba sae dai ko Pinky da ya kasa samun hanyar shigarta.
Sauka yayi kan bed yaje jikin window yana so ya gano meye matsalar inda ya shiga tunanin ashe mace kan rufe ruf koda kuwa tasha had'uwa da maza.
Zuciyar sa tace "may be haka ne don haka kaje kayi da gaske ko zaka sami hanyar cimma burinka.
Nan ya koma kan Billy inda yayi mata ta qarfin tsiya wanda yasa ta farka cikin nannauyan baccin da take ta saki qara sosai sau d'auya bata sake ba,haka kuma komai nata bai motsa ba.
Tatta6a ta ya shiga yi yana d'an girgiza ta amma ba alamar zata sake motsawa,
ajiyar zuciya ya sauke sbd baya son ta farka ta ganshi tare da ita a cikin wannan yanayi.
Kayan ta ya dauko yasa mata,shi kuma ya d'auki jallabiya ya saka, ya dauke ta cak ya kaita d'akin ta ya kwantar har da wani kwantar da teddy kusa da ita ya dora hannun ta kan teddy ya fita daga dakin.
Yaje dakin sa yana ta faman kai komo yayinda yake jin komai ya kunce masa na kasa cimma burin sa da yayi.
Washe gari har lokacin zuwan Mimi school yayi Hakeem bai ji d'uriyar su ba bai kuma ji alamar zasu fito ba.
Hakan yaje yayi ta knocking sae can Mimi ta farka tazo ta bud'e mai.
Ya shiga d'akin yana mai mamakin ganin Billy yanda ya ajiye ta.
Kallon Mimi yayi yace yi sauri kiyi wanka lokaci ya qure.
Bayan tayi wanka agurguje ta shirya Hakeem ya dauke ta zuwa school wanda har yaje ya dawo yana tunanin ya kamata ace Billy ta farka haka sbd ruwan allurar da ya tsirga mata a ice cream lokacin gama aikin su yayi.
Falo yake zaune yana ta kallon agogo har sha biyu bai ji motsin ta ba,
haka kuma naini bai shigo ba sae dai ba Naini ne damuwar sa ba kamar farkawar Billy.
Tashi yayi yaje dakin ta still tana a yanda take,
6angaren Naini yaje ya same shi sae bacci yake,
yayi tsaye yana tunanin me ma Naini zai mishi,
shi da baya son kowa ya sani.
Amma kuma dole ya kira doctor in yaso yace mai taqi farkawa ne tun baccin jiya.
Hakan ya yanke shawara ya kira doctor ya sanar da shi.
Da yazo suka je har dakin Billy,
Yana duba ta ya fahimci doguwar suma ce tayi,doctor ya kalli Hakeem yace ai ba bacci take ba doguwar suma ne tayi but garin ya haka ta faru Hakeem?fuska daure yace "Doctor ta ya zan fahimci hakan tana dakin ta ina nawa dakin,
doctor bai ce da Hakeem komai ba sae binciken Billy da ya shiga yi,
can ya nisa tare da fadin ka shirya ta muje asibiti.
Asibiti doctor? Of course zan yi qwaqqaran bincike ne domin na gano ainihin abinda ya sumar da ita.
Yana gama fad'a ya fita yace kayi sauri ina jiran ka a waje.
Ba yanda Hakeem ya iya haka ya nemo suturar kirki ya sakawa Billy ya fito dauke da ita suka shiga mota.
Da suka je asibiti cikin 15mnts doctor ya gama binciken sa ya kira Hakeem a office d'insa yace"Pinky ta suma ne a dalilin jin zafin rad'ad'in wani abu,Hakeem mene wannan abun? Doctor ta yaya zan sani... no kar ka min gardama ka fito ka gaya min gaskiyar mene ne,domin ta haka ne aikin zai min sauqi,
shiru Hakeem yayi yana tunanin ta yanda zai sanar da doctor,har dai da ya tuna cewa yayi masa gardama ba wata sha'awa da ke damunsa to ya zai ce mishi garin kusantar ta ne ta some.
Doctor ya katse shi da cewa Hakeem daka sanar dani da kar ka sanar da ni zan iya gano koma mene ne but bana son nayi wa matar ka wannan binciken ba tare da naji wani solution daga bakin ka ba sbd wani dalili, idan kuma kaqi sae na kira Abban ka naji koda akwai wani ciwo da pinky ke d'auke da shi wanda idan ya motsa ya kan iya sumar da ita.... no doctor kar ka kira Abba bana son suji wannan abun ko kai don ba yanda zanyi ne,, olryt fadi ina jin ka.
Nan Hakeem ya sanar da shi,wanda ko kad'an doctor bai yi mamaki jin bayanin hakeem ba sbd a nan take ya gano matsalar,kallon Hakeem yayi cike da tausayi domin yasan maganin da ya bawa Hakeem ba zai daina azazzalar sa ba sae idan ya sami mace ko kuma sai idan anyi masa allurar kashe maganin.
Yace Hakeem matsalar pinky hallita ce wacce ubangiji ke hallito wasu mata da ita wanda koda za'a haife su suna dauke da ita,ma'ana wata tsoka ce da ke toshe gaban mace wacce idan ba a cire mata ita ba d'a namiji ba zai ta6a iya kusantar ta ba,ko mai kuwa qoqarin ganin ya same ta ba zai same ta ba sae dae ya illata ta.
Kan Hakeem ne ya daure yace doctor nifa bangane ba, abinda nake son ji shine shin dama ita mace idan aka jima ba a kusan ce ta ba ta kanyi wuyar kusanta ne ta rufe ruf?me kake son cewa ne Hakeem ko kana nufin ka ta6a kusantar pinky but ta yaya ka kusance ta bayan tana d'auke da wannan lalurar? No doctor ni ban ta6a kusantar ta ba kawai dai nasan she is not virgin koda na aure ta...ba gaskiya bane Hakeem bcs idan har yanda kamin bayani gaskiya ne kuma abinda nake tunani shine, tabbas ba wani namiji da zai iya kusantar pinky komai jarumta kar sa kuwa dick dinsa ba zai ta6a iya shiga ba bare har ya iya moving,kawai zargin ta kake amma pinky she is virgin,domin ba wata mace da za a ce an ta6a kusantar ta,ta kuma dawo virgin, never,
bare pinky da ke dauke da wannan lalurar, amma tunda kace haka zan sa likitar mata tayi min bincike akan pinky ni kuma na bincike ka domin a gano wanda keda matsala cikin ku.
Nan Hakeem ya gyad'a wa doctor kai yana cike da tunani kala kala a ransa.
Doctor bai jima ba ya dawo,a nan yayi binciken da zai yi akan Hakeem inda ya gano ba wata matsala da yake d'auke da ita ma'ana lafiyar sa qalau.
Koda ya gama binciken sa yayi ma Hakeem alurar kashe qarfin wannan maganin ba tare da Hakeem ya nemi sanin ta mece ba kamar yadda doctor bai sanar da shi ba.
A nan doctor yace da Hakeem baka da wata matsala Hakeem lafiyar ka qalau bari naje naji result d'in pinky.
yana gama fad'a ya fita.
Sae gashi ya dawo cikin qanqanin lokaci ya zauna tare da furzadda iskan bakin shi yace"tabbas kuwa wannan abun shine pinky take d'auke da shi wato angurya,
yanzu kasa hannu domin aiki za'ayi mata a cire shi... But doctor kana ganin yi mata aiki ba zai kawo matsala har su Abba su ji ba?no Hakeem ai ba wani aiki bane bcs ba aikin da idan anyi ace za'ayi dinki bane, kuma idan an cire mata wannan abun she is stiil virgin,
kuma a cikin sati d'aya zata warke sumul kamar ma ba ayi ba.
OK doctor but pls bana so idan ta farka taji dalilin da yasa aka yi mata aiki na fiso nayi mata bayani da kaina, nan doctor yace "ba damuwa"
sannan ya bashi takarda domin yasa hannu.
Sosai jikin Hakeem yayi sanyi yayinda yake sa hannu a takarda,Doctor yace
"kar ka sa kanka a damuwa ba abinda zai same ta inshaAllah,
Hakeem bai ce da shi komai ba bcs ba aikin da za'a yiwa pinky ne ya sashi sanyin jiki ba irin jin cewa virgin ce.
Bayan an kammala yiwa pinky aiki doctor yaje yaja Hakeem zuwa d'akin da aka kaita.
Hakeem yaje yayi tsaye yana kallon fuskar ta da tayi fayau tayi haske ta qara kyau kamar wata matatta,
long time Hakeem yana kallon ta sae bacci take,
yayinda yake jin kansa cikin wani shauqi na daban wanda ya kasa gane cewa son Billy ne.
Zama yayi kan kujerar da ke kusa da bed d'in da Billy ke kwance, tare da riqo hannun ta yana murza shi a hankali inda ya sami kansa da lumshe idonsa ya dorawa hannun kiss,d'agowar da zai yi ne suka had'a ido da Billy.
*Billy girotruncated by WhatsApp]
[9/22, 7:03 PM] +234 810 038 8117: *👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na Billy giro😊*
*Page*
*👛35&36👛*
Sosai tayi mamaki har dai sunan ta da ya furta abinda bai ta6a yi ba a rayuwar sa,sae dae bata nuna mishi mamakin ta ba sae tashi tayi zata bar gurin yayi saurin riqo hannun ta yace"for God sake ki tsaya ki saurare ni.....ai da kasan Allah da baza ka cuce ni ba,koda yake bazan yi mamaki ba don ka cutar da ni sbd kai maqiyina ne ko maqiyin ma na qarshe domin yanzu na qara tabbatar da hakan ko......Kuka ne ya hana ta qarasa zancen, Hakeem ya tashi tsaye yaja hannun ta suka zauna ya miqa mata takardun asibiti yace"ki duba kiga abinda aka cire miki wanda har yasa kike jin rad'ad'i a gun amma wlh ba kusantar ki nayi ba, sae dae gaskiya nayi niyar aikata hakan amm sae na kasa samunki sbd lalurar da kike d'auke da ita, kuma banyi niyar kusantar ki don haka kawai ba sae don babbar lalurar da nake d'auke da ita wacce ke qoqarin kaini ga aikata zina..... Kaga malam zancen ka ba alamun gaskiya a cikin sa sbd sanin kanka ne nasan zinah ba komai bace a gurin ka,abu ne wanda ka riga ka saba aikatawa.... Pinky ni kuma?....qarya nayi ko kaman ta cewa na ganku da ido kai da Jennifer
Kin gan mu but..... Shiii!that's all.
Nan ta tashi zata bar gurin ya jawo ta da qarfi har sae da ta fado kan jikin sa tayi saurin tashi tare da fad'in"wai lafiyar ka me kuma kake so ka sake min a rayuwa bayan ka riga ka gama da ni....baza ki bar gurin nan ba har sae kin fahim ce ni domin ni kad'ai nasan yanda nake azabtuwa kan rashin fahimta ta da kikayi, na rantse miki ni ban kusance ki ba kuma ban ta6a aikata zeenah a rayuta ba!
Shiru Billy tayi tana kallon Hakeem tace"hm Bobby kai fa namiji ne bazan ta6a yarda da zancen ka ba domin ku ba abin yarda bane,
don haka ka daina 6ata yawun bakin ka a banza!
Hakeem yayi shiru ya rasa me zai ce da ita, sae duk yaji haushin kansa sosai har ma yaji ina ma ace bai yi yunquri biyan buqatar sa da ita ba,koda kuwa ace wannan lalurar zata kashe shi ne,a hankali ya saki hannun ta yace"ina so ki min alfarma d'aya ki duba tarkadun asibiti kafin ki bar nan,
Yana gama fad'a ya tashi ya bar gurin,
ba musu kuwa ta shiga duba takardun wanda a nan ta fahimci komai amma baza ta yarda da hakan ba har sae taje asibiti domin ayi mata binciken da zata fi yarda da hakan.
Nan ta tashi ta koma d'aki.
Washe gari ta fito tayi break fast kamar yadda ta saba.
Bayan Hakeem ya kai Mimi school ya dawo suna kan dining su uku zaune suna break fast,Naini sae yi yake yana kallon Billy wanda tun zaman ta ta fahimci hakan, sae dai ta kàsa gane na mene ne,sbd kallon yayi yawa? Nan dai ta basar.
Suna gama break fast Naini ya tafi school Hakeem kuwa ya shiga d'akin sa.
Billy kuwa makullin motar Hakeem ta dauko ta fita zuwa asibiti domin ayi mata binciken da zata fi yarda cewa Hakeem bai kusance ta ba.
Ba yabo ba fallasa ta dawo,amma da alama taji bayanin da take son ji.
Koda ta shigo ta sami Hakeem kwance a falo idanuwan sa a rufe sae dae kamar ba bacci yake ba, tayi tsaye tana kallon shi tace a ranta
_"yanzu zamu d'ora inda muka tsaya sae dae dole na kiyaye duk wani abu naci ko na sha da zai fito daga hannun ka,domin kare mutuncin kaina"_
Ta wuce haka yace"Pinky"
ta tsaya cak tana kallon shi yace"meyasa kika kashe wayar ki umma da Abba sunyi ta kira basu same ki ba? ni at all na manta inda na ajiye wyr 3days a go.
Olryt se kije ki nemi wayar bcs umma na son magana da ke nan ta gyad'a mishi kai ta wuce ya bi ta da kallo cike da so wanda yanzu shi kanshi tabbas yasan ya fara sonta.
Tana shiga d'aki ta cire doguwar rigar da ke jikinta,
ta saka wata riga handless iya qugu da d'an guntun wandon da bai wuce cinyar ta ba.
Sae da tayi waya da umma kafin take fitowa tazo gab da Hakeem ta zauna fuskar ta na d'auke da shagwa6a,Hakeem sae kallon ta yake yanda tayi kyau sae duk yaji ta qara shiga ran shi yace"me akayi ne pinky?wai ni Bobby yaushe zamu koma ne ka san fa a school anyi resuming har anyi nisa, kar ki damu saura kwanaki kad'an mu koma,ihun murna ta saki had'e da rungumo shi ta bashi peck a kumatu tace gud story Bobby! ta tashi tare da fad'in ina zuwa, Hakeem kam dasqarewa gurin yayi cikin yanayin mamaki yanda tayi hugging d'insa ta kuma bashi kiss sae dae kuma haka Billy take idan ta sami gud story a gun umma ko Abba wanda yanzu ya fahimci rashin umma da Abba ne yasa abubuwan suka fara dawo wa kanshi.
Billy kuwa tana shiga d'aki tace"cab na makara fa, lallai dole na gaggauta nuna ma soyayya ta a cikin en kwanakin nan,na kuma sake da kai sosai tamkar dama can mun saba.
Pringles ta d'auko ta fito.
Da murmushi Hakeem ya tarbe ta domin yana son pringles sosai tashi yayi zaune inda suka fara cin pringles d'in a tare suna kallon TV can Billy ta kalli Hakeem cike da jin bacci tace"Bobby bacci"ok je daki ki kwanta, um um ni anan zanyi bacci"
ta fad'i haka ne yayinda ta samarwa kanta gurin kwanciya a jikin sa ta hanyar yin pillow da cinyoyin sa ta wani qudundune qafafunta kamar wata er baby, kallon ta yake inda ya sami kansa da shafar gashin kanta har tayi bacci.
Ta jima sosai tana baccin ta, Hakeem kuwa yana kallo,yana ci gaba da cin pringles ,sae ga Naini ya shigo yana ganin Billy kwance a jikin Hakeem yayi saurin juyawa zai fita, Hakeem yace yadai Naini?yace no ba komai,but ina so zamuyi magana" sae kawai ya fita ya tsaya a bakin qofa,shiru Hakeem yayi shifa ya fara hango wani abu a game da Naini but ko dai kayan da ke jikin Billy ne ya hana shi shigowa,kallon Billy yayi yana tunanin yanda zai yi domin baya son garin tashi ya tashe ta daga bacci gashi da alama baccin na mata d'ad'i sosai,a hankali ya tashi ya d'auke ta cak ya kaita d'akin ta ya kwantar.
Ya dawo yace da Naini shigo muyi magana ba musu ya shigo domin yaga lokacin da Hakeem ya maida Billy d'aki sae duk quncin da yake ciki ya qaru.
Ya sami guri ya zauna yace dama ba wani abu bane ina so zan koma hostel da zama,meyasa naini?shiru Naini yayi domin shidai abinda ya sani ko kad'an baya son ganin jikin Billy na haduwa da na Hakeem,
se can yace"sbd zamu fara exam...but Naini ai duk d'aya ne bcs nan ba mai takura ka, I know but kawai dai nafi son can, Naini ko dai wani abu aka ma wanda bai ma ba ka fad'a min sae mu gyara kaji,ba abinda kuka min kawai dai ina son na tafi can domin ganin nake kamar zan fi karatu a can,olryt but please kar ka tafi yanzu ka bari idan pinky ta tashi daga bacci,
ba musu yace shikenan zan koma school dama abu nazo d'auka.
Guraren qarfe biyar Hakeem ya shigo gidan ya dawo daga dauko Mimi,Billy wacce ta bude musu gate,ta qarasa da gudu ta tarbo Mimi taje ta riqo hannun Hakeem cike da shagwa6a tana d'an shillo dashi a hankali,ta wani turo baki tana kallon shi tace"shine kaje d'auko Mimi baka je dani ba,bayan da safe kasan bada ni aka kaita school ba,, am sorry kinji na jima da fita domin koda na fita duk kina bacci ban kuma dawo ba sae yanzu...maqale kafad'a tayi tace"um um ni bazan haqura ba sae an fita dani domin na jima ban fita ba, cike da murmushi Hakeem ya lakuta hancinta yace"kin manta yau da safe kin fita"to ai wannan ba yawo bane.. Olryt naji amma yau nagaji da yawa sae dai gobe,
ya fad'i haka ne yayinda suka shigo falo,ta saki hannun Hakeem,
ta tafi da sauri gurin Naini sbd dama game ce suke bugawa taji odar Hakeem.
Hakeem yayi tsaye yana kallon ta yace da Mimi wacce ke qoqarin zuwa gurin su"no mimi je kiyi wanka kizo kici abinci ba musu ta wuce ya kalli Billy da har ta fara sake ihun murna yace"pinky je kiyi ma Mimi wanka"oh oh Bobby ba kace taje tayi ba,
kallon ta kawai yayi bai ce mata komai ba ya bar gurin, da sauri ta tashi tabi bayan shi, Naini kuwa ya bita da kallo har suka shiga d'akin Hakeem,suna shiga tace wai Hakeem meye haka kasan fa Naini baya jin dad'in abinda kake yi may be ma akan shi ne yace zai koma hostel sae da na lalla6a shi ne yace ya fasa komawa kuma yanzu kazo..... maganar Naini ta ishe ni haka fa!
Ta kalle shi cikin fushi ta fita daga dakin.
Hakeem ya bi ta da ido shi ba abinda ke 6ata mai rai irin qananin kayan da take zama da su a gaban Naini.
Tun lokacin Billy fushi take da Hakeem har sukayi dinner.
Bayan tayi shirin kwanciya sae ga Mimi tazo tace"didi yaya Hakeem yace kije yana kira"yana a ina? yana a falo,
ba tace komai ba tayi kwanciyar ta tana chat,
sae can ta tashi taje falo bata same shi ba taje d'akin shi ta samu yana toilet zata fita kenan ya fito tayi saurin juya bayan ta shaye da toka,Hakeem Yazo gab da ita ya rungumota ta baya,tayi saurin kame jikinta tace"Bobby ka saka towel d'in mana, ai akwai towel a jikina.... a wuyan ka ba,pls ka saka shi inda ya dace ,gaban ta ya dawo tayi saurin rufe idon ta tace "ah ah Bobby bakada kunya ko zan fita fa"
bud'e idon ki kiga Allah da towel a jiki na,
a hankali ta bud'e idonta,taga kuwa yana d'aure da towel a qugunsa sae kuma d'an qarama da ke kan wuyansa tace"uhm ashe da gaske kake na zaci ka fito a yanda ka saba,
Shiru yayi domin tabbas yayi niyar fitowa a yanda ya saba sae dai jin shigowar ta ya hana hakan can yace"amma ya akayi kika san yanda nake fitowa wanka?
Hannu ta kai taja kumatun sa duka biyu tace"bayan ganin farko da na ma sae gashi ranar na shigo zan gyara ma d'aki,
naga ka fito daga wanka sae kayi sauri ka koma sae nayi kaman ban ganka ba nayi ma wayon manya"
ta fad'i haka ne had'e da yi mishi gwalo, murmushi yayi tare da jawo ta jikin sa,,
da wasa ya riqi d'an sirin hannun rigar ta yayi kamar zai zare hannun daga jikin ta yace"ai kuwa sae na rama yanzun"Billy tayi shan tokar en yara tare da buge mishi hannu tace"ni ka daina ta6a ni ka manta fushi nake da kai"
to ai ke kika fara ta6a ni, cike da kunya ta cusa fuskarta a qirjin sa tana dariya ciki ciki sbd yanda yayi magana kamar wani yaron goye, nan Hakeem ya shiga yi mata cakulkuli yace"ai sae kin fitar da dariyar ta fito, dariya ta shiga yi sosai tana fadin ka daina mana,bai daina ba sae zille zille take har suka je kan bed Hakeem yayi mata rumfa yana ci gaba da mata cakulkuli can ya dakata ya kai hannu a hankali yana share mata en guntayen hawayen da suka fito mata kan dariya,kallon shi ta shiga yi long time sae kawai ta tuna da qawar ta Feenah a lokacin take sanar da ita cewa
*"Bobby baya da matsala ta koina matsalar sa d'aya ita ce qiyayyar da yake nuna miki*.
*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 7:14 PM] +234 810 038 8117: [8/18/2016]
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na Billy giro😊*
*page*
*👛39 to 41👛*
Dasqarewa Billy tayi komai nata ya kasa motsi sae hawaye da ke faman zarya a kumatun ta, qoqarin sulalewa take ta fadi Hakeem yayi saurin tarbo ta ta fad'a jikin sa, tace"na shiga uku Bobby na kashe Nai....saurin rufe mata baki yayi ya girgiza mata kai yayinda idanuwan sa suka ciko tap da qwallah yace"nine na kashe Naini,
ni na kashe shi da hannu na kar ki sake yunqurin d'orawa kanki.
Tsananin mamaki ne ya bayyana a fuskar ta tace"ya zaka ce haka Bobby bayan ba kasan yanda abin ya faru ba,wlh Allah nice....shiii! na sani amma ki barshi a yanda nace,why Bobby....police suka gani kai tsaye sun zagaye su,duk Billy tabi ta qara rikice wa kamar yadda shima Hakeem ya shiga rud'u domin bai san ya akayi en sanda suka sani ba har suka biyo su asibiti.... Doctor ya dafa Hakeem yace Hakeem nine na kira su domin bansan daya daga cikin Ku ne yayi kisan ba,sbd kayi min bayani a rikice inda ka nuna min kamar wani ne ya aikata aikin shiyasa nayi gaggawar kiran police,amma don Allah kayi haquri wlh...
no doctor ko baka Kira su ba nayi niyar hakan sbd kisan mutum ba abune da za'a iya rufe shi ba,bare mahaifin Naini mutum ne mai tsananin bincike akan komai, shiyasa ya zama dole tun wuri na miqa kai na ga hukuma.
Nan ya miqa kanshi ga police suka sa mishi handcuff,kuka Billy ta fashe dashi tana kallon doctor tace"doctor wlh ba shi yayi kisan ba nice,don Allah kar ka bari aje da shi"
Hakeem yace"pinky banyi haka don komai ba sae don fitar da ke daga qunci,sbd haka ki daina kuka kinji domin zan iya jure komai indai akan ki ne.
Yana kawo nan police suka jashi, Da gudu Billy ke binsu cikin kuka sae kuma ta tsaya cak"inda ta
shiga magana a cikin ranta
_"meyasa zan damu da yawa haka bayan ba son Bobby ko d'as a cikin zuciya ta da har zanji tausayin shi,kuma hakan da yayi tamkar ya samar min wata dama ce da zan ku6uta da auren sa har abada....._
No ba haka naso ya faru da kai ba Bobby ko don hallacin da kamin a yanzu,,ni dai kawai fatana na rabu da qaddararren auren ka shi kawai nake buqata a rayuwa ba mutuwar ka ba.
Tayi maganar ne a fili kuma cikin kuka kafin take durqushewa gurin tana ci gaba da kuka tana kallon su Bobby da sukayi nisa har suka 6ace mata shima kallon ta yake.
Mimi ce tazo ta fada jikin ta ita ma kukan take sosai.
Cike da tausayi doctor yazo yana lallashin su,tace doctor don Allah ka fitar da Bobby wlh Allah bana so ya mutu.
Doctor bai ce da ita komai ba,domin ya shiga mamakin zancenta da yaji yanzu ace duk hallacin nan da Bobby yayi mata tana kan bakar ta na ganin auren su ya rabu,nan dai ya basar da zancen ya ci gaba da lallashin su.
Wanda da qyar ya samu ya lallashe ta ya maida su gida.
Haka suka kwana cikin kuka,
Mimi ce kadai ta samu bacci ya d'auke ta Billy kuwa tunda suka dawo take faman kiran number umma da Abba amma ta kowannen su taqi shiga.
Tashi tayi ta d'oro arwala,tayi ta nafilfili tana roqon Allah kan ya taimake ta yayi gaggawar fitar da Hakeem.
Daga qarshe ta hade kai da guiwa tana ta rusar kuka inda ta sami kanta da jin wannan hallaci da Hakeem yayi mata,da ace Allah zai ku6utar da shi da kuwa tayi rayuwar zaman aure da shi har abada duk da kuwa ko kadan bata jin son Hakeem a cikin ranta.
Washe gari tunda safe taji door bell da sauri ta fito har tana had'awa da gudu ta bud'e qofar tare da fad'in "Bobby".
Tana ganin doctor ne kuka kawai ta fashe da shi,cikin dasasshiyar muryar ta da tasha kuka tace"doctor tun jiya bana samun wayar su Abba don Allah ka fitar da Bobby,nasan zasu baka shi tunda ba d'an qasar su ya kashe ba, pinky ko ba d'an qasar su ya kashe ba zasu hukunta shi a bisa kisan kai da yayi cikin qasar su kafin suke miqa shi ga hukumar qasar mu.... Haba doctor don Allah ka taimaka mana, nidai ko yaya ne ka fitar da shi please doctor,
ta fadi haka ne yayinda ta durqusa kan guiwoyin ta tana kuka mai ban tausayi.
Da sauri doctor ya bar gurin yaje cikin motar sa ya zauna hade da jinginawa cike da damuwa,yace "sae dai kiyi haquri pinky domin ba yanzu ne ya dace na bayyana cewa Naini yana raye ba,bare har na fito dà Hakeem har sae na fahimci ra'ayin ki ya canza gabad'aya kema kin fara son Hakeem kamar yadda ya fara sonki.
D'agowar da zai yi ne ya hango pinky ta jikin mirror ta wuce cikin sauri nan ya fahimci tabbas pinky taji zancen sa, idan kuwa haka ne ta 6ata mai tsari.
Cikin rashin jin dadi ya fito mota ya shiga cikin gidan rai 6ace Billy ta kalle shi taja hannun mimi suka haura sama,tana tunanin lallai doctor nan ya akayi har yasan ba da gaske take son Hakeem ba.
Shi kuma doctor ba yanda ya iya domin ya fahimci ta ji sak me yace.
Nan ya fita bai dawo ba sae tare da Hakeem,wanda tun cikin mota yake tambayar doctor ya akayi ne.
Bai ce da shi komai ba sae tunanin abinda zai ce da shi yake bcs baya son yasan tun farko Naini bai mutu ba,sbd shi kad'ai yake tsarin shi na ganin ya daidaita tsakanin su kafin su koma Nigeria.
Sae da suka fito cikin mota sannan yace"ina taya ka murna sosai Hakeem bcs doguwar suma ce Naini yayi yau da safe ya farfado wanda hakan yasa nayi matuqar farin ciki marar misaltuwa.
Cike da tsananin murna Hakeem ke kallon doctor yace to ai doctor gurin shi ya kama ta ka fara kaini tukun, a'a gabadayan ku nake son muje don haka kaje ka fito da su pinky.
Duk maganar nan da suke pinky na hango su ta jikin window sae duk ta d'auka da hadin bakin Hakeem ciki,inda ta shiga tunanin kenan Hakeem ba soyayyar gaskiya yake mata ba ko hallacin da yayi mata don kawai ta so shi ne yayi, wato kenan shine ya gano plan d'inta ya sanar da doctor shine suke son plan d'in ya koma kanta,to me ya kamata nayi yanzu?
Tana cikin haka ne taji alamar zai shigo da sauri ta haura sama ta shiga d'aki.
Cike da murna Hakeem ya shiga d'akin ta ya same ta ruf da ciki kamar mai bacci"yace bacci kike pinky ki tashi gani na dawo bcs naini is alive, shiru tayi tana sauraren shi da mamaki wato doctor bai fahimci taji ba kenan lallai zata nuna bata ji ba,in yaso taci gaba da bin su har taga iya gudun ruwan su.
Tashi tayi tana kallon Hakeem cike da murna tace"da gaske Bobby da gaske Naini yana raye!?cike da murmushi ya gyad'a mata kai yace "ashe ba mutuwa yayi ba doguwar suma ce.... ihu ta saki ta qanqame shi sae kuma ta fashe da kuka tace"inace basu ma komai ba ko?ba abinda suka min,nan ta share hawayen ta yace ina Mimi? wanka take,kefa kinyi wanka domin yanzu asibiti xa muje gurin Naini, Bobby ta ya zan ji qarfin wanka bayan kana cikin wani hali,olryt ba gani na dawo ba ai sae kije kiyi wanka yanzu, maqale kafada tayi tare da qara mannewa a qirjin sa tace"ni sae na gama ganin ka tukun,cike da jin dadi yake kallon ta sae ga Mimi ta fito daga wanka, yace"kinga Mimi ta fito je kiyi wanka nima zanje nayi amma kiyi sauri domin doctor yana jiran mu fa.
Nan ta tashi ta fad'a toilet shi kuma ya fita.
Mimi cike da murna take shiri domin kafin Hakeem ya fita ya sanar da ita komai.
Tsaye yake jikin mirror ya fito daga wanka har ya saka tufafi yana sanya buttons d'in rigar shi sae ga Billy ta shigo cikin shiri,
taje a hankali ta rungumo shi ta baya inda suke hango juna ta jikin mirror, a hankali ya sauke ajiyar zuciya domin qamshin turaren Billy da ya shiga hancin sa tace"nayi ma wayo na riga ka fitowa har na shirya kai sae yanzu kake shiri,,uhm ai don ba kya kwalliya ne kika riga ni,,au to kai kana yin kwalliyar ne? eh mana baki ga kullum se kyau nake qarawa kamar mace,murmushi tayi yayinda take qarewa fuskar shi kallo ta jikin mirror tace"haka ne fa amma ba wata kwalliya a fuskar ka,kuma fuskar ka ba kyau sae muni kamar tawa,
saurin kallon ta yayi ya girgiza kansa kawai domin shidai yanzu baya ganin munin ta ta koina da ne kawai. yace"ke muni ne dake?eh mana ji hanci na kamar zai ta6o bakina, ga d'an qaramin baki kamar wacce aka emma, idanu kamar wata mai jin bacci,yace"kenan baki gode Allah ba, ya fadi haka ne yayinda ya juyo yana kallon ta,tace"a'a wlh na gode Allah fiye ma da yanda kake tunani,to meyasa kika ce haka? Sbd kawai naji dad'in bakina amma da wasa nake.
Nan yaja hannun ta suka zauna kan bed yace"ina so naji shin me ya had'a ki da Naini har hakan ta faru"shiru tayi tana kallon shi kafin take sanar da shi yanda abin ya faru.
Kansa ne ya d'aure sosai yace"pinky ko dai akwai wani abu tsakanin ki da naini kike 6oye min?a'a wlh,to Ko kun sami sa6ani ne? ko d'aya, ok zo muje nama ji kamar Mimi na kiran ki.
Nan suka fita suka tarar da doctor cikin mota.
Tafiya suke yayinda doctor ke hango Billy ta jikin mirror ta wani narke a jikin Hakeem sae labari suke bawa junan su suna dariya,hakan yasa ya d'anyi mamaki yaushe hakan ta fara faruwa tsakanin Bobby da Billy domin duk a tunanin sa ko kusa da Hakeem bata zama bare zancen had'a jiki,nan ya kawad da zancen sbd sun iso asibiti.
Koda suka shiga sun sami Naini idanuwan sa a lumshe sallamar su ne yasa shi bude ido inda ya sauke su kan Billy wacce ke riqe da hannun Mimi.
Doctor ne ya taimaka mishi ya tashi zaune wanda har yanzu idon shi na kan pinky kafin yake kallon Hakeem yace"am sorry to say Bobby and u pinky i am really sorry, i dnt mean to hurt u, ni kaina ban san meyasa nayi yunqurin aikata abinda nayi niyya ba kawai dai na tsinci kaina da tashi aikata hakan sbd son da nake miki.... saurin kallon shi tayi yace"of course ina sonki pinky ina sonki sosai, tun muna yara bani da burin kasancewa da kowa face ke, ban ta6a tunanin zan rasaki ba pinky, shiyasa ban furta soyayya ta a gare ki ba,
wanda nayi hakan ne har sae idan mun kammala school nida ke ko zan sanar da ke sae gashi kai tsaye naji auren ki wanda ya ritikita min tunani gabad'aya amma idan na tuna wanda aka had'a ki aure da shi sae naji kamar nan kusa zan same ki matsayin mata sbd sanin cewa ba kwa son junan ku ko kad'an,
sae dai zaman da nayi daku ya fahimtar dani wani abu wanda na fara cire ran zan same ki a matsayin mata, shine zuciya ta tayi ta ingiza ni kan na d'auke ki naje dake can inda zamuyi rayuwar mu mu kad'ai gurin da ba wani d'a namji da zai kalle ki bare har naji zafi a raina,amma kiyi haquri da kuskuren da nayi sharrin so ne da kuma sharrin shaid'an.
Pinky a yanzu bani da wani buri a rayuwa da ya wuce na sami mace mai irin hallayar ki da ma komai naki domin idan ban sami haka ba bana jin zan ji dad'in rayuwar duniya har na koma ga mahallici na.....kar ka ce haka Naini ka tuna fa Allahn da yayi ka shiya d'ora maka sona kuma kai tsaye zai iya yaye maka sona ya kuma baka mace wacce ta fini da komai kuma ka daina cire ran ka rasa ni ba mamaki watarana zan zamo taka.
Tayi maganar ne cikin muryar kuka sbd sosai Naini ya bata tausayi domin duk a cikin kuka yayi zancen shi.
Hakeem kam duk kishi ya rufe mishi ido shiyasa ko kad'an bai ji tausayin Naini ba sae ma haushin sa da ya ji.
Da dare bayan sun koma gida pinky ta fito daga wanka tayi shirin kwanciya cikin rigar ta pink iya guiwa.
D'akin Hakeem ta nufa sbd tun a asibiti ta fahimci fishi yake da ita.
Tana shiga ta same shi riqe da glass cup zai sha ruwa yana ganin ta ya fasa shan ruwan.
kafin ta qaraso ya isa gurin ta fuskar shi a daure Yace"lafiya me ya kawo ki d'aki na?kallon shi tayi sau d'aya ta kauda kai ta rasa meyasa take jin ba dad'i sbd fishin da Hakeem keyi da ita,duk da kuwa tana ganin kamar plan ne bada gaske yake kishin ta ba.
Magana nake miki kin min shiru!idanuwan ta ne suka ciko tap da qwallah tace"Bobby meyasa kake fushi dani?in dai akan Naini ne sanin kanka ne mutum baya d'orawa kanshi so.... Naji mutum baya d'orawa kanshi so domin naga hakan a tattare dani amma meyasa kika kama mishi kuna ta kuka har kina ce mishi kar ya cire ran wata ran zaki zamo tashi...ai gaskiya na fada Bobby sbd ba wanda yasan gobe....nasan da hakan ba sae kin sanar da ni ba, amma ke ba don haka kika gaya masa cewa wata ran zai same ki ba ki gaya min meyasa kika ce masa haka?.....sbd na fahimci yana sona sosai shiyasa nake son kwantar mai da hank....kafin ta qarasa zancen ta se kawai taji qarar fashewar glass cup d'in da ke hannun shi, ya kuma jefo shi kusa da ita har sae da tayi saurin matsawa.
A tsorace ta
fashe da kuka tana kallon hannun shi da ke fitar da jini, shima Hakeem kallon ta yake cike da nadamar jefo mata cup,cikin muryar lallashi yace"pinky na same ki ne?girgiza mai kai tayi yayinda ya ware hannyensa alamar tazo,
da sauri taje ta shige jikin sa tana kuka sosai sae haquri take bashi,,,is ok pinky amma don Allah kar ki sake furta cewa wani yana sonki a gabana kinji.
gyada mishi kai tayi hade da share hawayen ta taje ta dauko first aid kit taja hannun shi ta zaunar da shi kan bed,a hankali take cire mishi glass d'in da ya soke mishi hannu wanda har ta gama treatment din shi kallon ta yake,d'ayan hannun sa ya kai yana share mata hawaye domin har lokacin kuka take.
Nan ya matsa gab da ita ya lumshe idon shi yayinda ya kai lips dinsa a hankali kan nata ya zira harshen sa wanda yayi 3mnt kafin yake zarewa, ba yabo ba fallasa pinky ke kallon shi ta kwanta a hankali kan qirjin sa tare da sauke ajiyar zuciya,shiru sukayi na d'an wani lokaci d'akin yayi tsit kamar ba kowa Hakeem sae shafar sumar kanta yake, can ya katse shirun da cewa ki fara shiri domin gobe ne kad'ai muke cikin qasar nan.
*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 7:18 PM] +234 810 038 8117: [8/20/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na Billy giro😊*
*Page*
*👛42 to 44👛*
Ba tare da ta d'ago ba tace"su umma zasu dawo ne gobe? tana nufin iyayen su Naini.
Yace "inshaAllah"
tace "Allah ya kawo su lafiya yace"Amin"
Daga haka sukayi shiru.
Yayinda Billy ta qara narkewa a jikin sa kamar mai jin bacci,ba wai don tana jin baccin ba sae don yau taji dad'in kwanciya a jikin shi sosai fiye da kullum,
koda yake kullum duk ta6a jikin sa da take bata ta6a jin wani abu makamancin haka ba sae yau wanda har ma ji take tamkar su tabbata maqale da juna don kar ta daina jin dad'in da take ji a yanzu.
Shi kuwa Hakeem a matse yake gurin domin har zufa ya fara sae Allah Allah yake ta tashi domin shi kad'ai yasan azabtuwar da yake dama kullum ta6a ta da yake yana yi ne sbd idan bai ta6a jikin ta ba har wani zazza6i yake ji idan kuma suka jima a maqale shi kad'ai yasan azabtuwar da yake amma hakan yake jurewa kullum.
Duk da kuwa ba ita ce macen farko da ya fara ta6i ba amma a kanta kad'ai ya fara jin hakan.
A hankali yake d'aga ta kan qirjin sa, ta kalli yanda ya matse qafafun sa kamar mai jin fitsari tace"Bobby zaka je toilet ne?da qyar yace"no pinky tashi kije daki kiyi bacci kinji, bcs bacci nake ji sosai, ba musu ta tashi kan jikin sa ba don taso ba domin da bai ce komai ba sae dai ta lafe kan jikin sa har safe.
A daren ranar kowannen su sae juyi yake da qyar suka samu bacci ya d'auke su.
Washe gari ta fito daga wanka kenan tayi kici6is da Hakeem ya shigo d'akin,
saurin kauda idon shi yayi domin daurin towel d'in ta kamar wanda ke shirin sa6ulewa a qirjin ta ba wani daurin kirki take yiwa towel ba sae duk tabar rabin mama a waje kamar d'aurin en boarding school,sae duk yaji sh'awar ta sosai har dai yanda yaga d'igo d'igon ruwa a jikin ta.
Sae da ta gyara d'aurin towel d'in sannan ya iya kallon ta yace"yau da wuri zaki had'a break fast sbd da wuri su umma zasu dawo.
Yana gama fad'a yasa qafa zai fita tace"Bobby"ya juyo a hankali yana kallon ta, tazo gab da shi ta riqo hannun sa da ya jiwa ciwo jiya,cike da damuwa har tana ji kamar tayi kuka sbd ganin yanda hannun ya kumbura sosai,nan taja shi suka zauna kan bed, sannu a hankali take walwale mishi bandage har ta cire taje ta d'auko first aid kit,a hankali take wanke mishi gurin da kad'a da sprit.
bayan ta gama ta sa mishi wani sabon bandage.
A natse ta d'ago tana kallon shi taga ashe ita yake kallo tace"sannu ko?ya lumshe idon shi tare da fad'in kema sannu,ba tace da shi komai ba domin ganin take taci ya mata sannun sbd ita kad'ai tasan zafin da taji a lokacin da take wanke mishi gurin sae taji abun har cikin ranta tamkar ita ke dauke da jin ciwon.
Nan ya tashi ya fita ita kuma taje ta shirya sannan ta fito zuwa kitchen ta sami Mimi da Hakeem zaune a falo mimi na biya karatun qur'ani.
Sae da ta gama had'a break fast ta jera abun da duk za'a buqata kan dining.
Suka ji oda da gudu pinky taje ta bude gate cikin murna.
Koda suka fito cikin mota har su Hakeem sun fito,
Mimi taje da gudu ta fad'a jikin umman ta kafin take zuwa gurin Abban ta.
Haka Billy da Hakeem suka je suka tarbe su sannan suka shiga daga ciki.
Bayan sun gama cin abinci ne suka je asibiti domin Hakeem ya sanar da su tun kafin su dawo.
Da dare guraren qarfe goma da rabi Hakeem ne kwance sai juyi yake kan bed baya da muradi irin yaji pinky kwance a qirjin sa har ma jin yake kamar ya kira ta a waya tazo ta taya shi bacci tunda Mimi bata nan.
Yana cikin haka ne yaji knocking da hanzarin sa ya tashi ya bude dakin.
pinky ya gani rungume da qatuwar teddyn ta,ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya bata hanya a natse ta shiga daga ciki,tayi tsaye ba tare da ta nemi guri ta zauna ba,yaje gab da ita har suna jin qamshin turaren juna yace"ya baki zauna ba ko wani abu kike so? shiru tayi tana kallon shi domin ita kanta bata san me ya kawo ta dakin ba, kuma gashi a daki ta kasa bacci sae faman juyi take wanda duk ta juya ba abin da ke fad'o mata a rai sae Hakeem.... Ki min magana kinji pinky,
still kallon shi take yayinda hawaye suka ciko tap a idon ta har suna qoqarin zubowa, da sauri Hakeem ya dafa kafàdar ta yace"pinky mene ne gaya min kinji"sautin kukan ta ne ya fara fitowa yayinda ya kar6i teddy ya ajiye.
A hankali ta fad'a kan jikinsa yayinda sautin kukan ta ke qara fitowa,duk Hakeem yabi ya damu sosai sae tambayar ta yake lafiya?cikin kuka ta d'ago tana kallon shi tace"uhm uhm nima ban sani ba"no pinky kodai wani abu aka miki, gaya min waya ta6a ki? ya nuna kanshi da yatsa yace "nine?girgiza mai kai tayi yace"ko Abba? umma fa?abokannan ki? duk girgiza mai kai tayi tare da fad'in nifa ba abinda aka min,
bai ce da ita komai ba sae jan hannun ta yayi suka zauna kan bed yakai hannu ya shafo cikin ta da ya lafe sosai yace"kina jin yunwa?gyad'a mishi kai tayi,ya tashi ya dauko fresh milk da cup ya tsiyaye yaje yana bata har sae da tace ya ishe ta sannan ya bata ruwa tasha ya zaro tissue ya goge mata d'an qaramin bakin ta yace"ki daina zama da yunwa kinji bcs bana so"gyada mishi kai tayi sae kawai ya dauke ta cak ya kwantar da ita ya rufa mata blanket yaje ya kwanta tare da rage hasken d'akin.
Har guraren 11:30 bacci ya kasa d'aukar su kowa nason yaji d'an uwan sa manne dashi.
Hakeem ne ya kasa haquri ya juyo ya kalli Billy yace"meyasa kin kasa bacci tun d'azu ko so kike ki koma d'akin ki?saurin girgiza mai kai tayi tare da fad'in tsoro nake ji Bobby"abu ga mai jira da sauri ya matsa gab da ita tare da rungume ta yace"yi baccin ki haka ba abinda zai same ki kinji"bata ce komai ba sae qara shigewa tayi a jikin sa shi kuma yana faman bubbuga bayan ta kamar wata er baby wai so yake tayi bacci,
daga haka ya fara shafar bayan ta sannu sannu har ya soma zuwa koina na jikin ta,duk pinky naji ta fara jin wani iri amma ta kasa hana shi,duk da kuwa taji yanda ya rikice har yana qoqarin raba ta da rigar jikin ta, bai cire mata rigar ba sae hannun sa taji kan qirjin ta yana wasa da dukiyar fulanin ta son ransa,
nan jikin ta ya d'auki rawa duk tabi ta tsorace muryar ta na rawa tace"Bobby....saurin d'ora yatsan sa yayi a bakin ta yace "Shiiii!pinky wasan yana min dad'i sosai pls kar ki katse ni"
nan ya had'e bakin su gam yana tsutsar lips d'in ta kamar wanda ya sami alawa,nan ya samu cikin hikima ya raba ta da rigar jikin ta ya bar ta da d'an pant haka shima boxer kadai ya bari a jikin sa,kuka ta ajiye mishi sbd yanda ya haukace yana shan mamman ta, cak ya tsaya domin jin kukan ta yake tamkar ana hura mai wani zafin bala'i cikin kunne.
Rungume ta yayi sosai a qirjin sa yana fitar da wahalallen numfashi yakai bakin sa gab da kunnen ta yace"pinky zan mutu please kimin abu d'aya ko zan iya bacci"muryar ta na rawa tace me zan maka Bobby? nan ya gaya mata abinda zata mishi wanda take ganin kamar yafi qarfin ta amma tsabar tausayi yasa ta mishi inda cikin 15mnt yaji sauqin komai sai qara rungume ta yayi a jikin sa suka shiga bacci.
Koda ya farka da Asuba bai ga pinky ba but bai yi mamaki ba domin ya tuna lokacin da yaji ta zare jikin ta daga nashi.
Tashi yayi yaje yayi arwala yayi sallah yaje ya murd'a qofar pinky yaji ta gam nan ya koma d'akin sa domin baya so ya tashe ta.
Pinky kuwa tana jin lokacin da Hakeem ya maurd'a qofa amma ta share shi ba don taso ba sae don ta hana zuciyar ta abinda take ji game da Hakeem wacce tun lokacin da ta sato jiki ta dawo d'aki sae haushin kanta take ji kan ta kai kanta d'akin Hakeem ta sake mishi jiki ya ta6a ta duk inda yaso abinda mai son ta da gaske kad'ai ya kamata ta bawa wannan damar ba Hakeem ba da take ganin son plan ne yake mata.
Kuka ta fashe dashi sosai tana tambayar kanta meyasa ta fara son Hakeem a lokacin da ta fahimci ba da gaske yake son ta ba❓.
Bata da amsa nan taci kuka har ta gode Allah tana cikin kukan ne taji Hakeem na mata knocking da sauri ta share hawayen ta taje ta bude qofa kad'an bcs bata son ya ganta kar ya fahimci kuka take.
Yace "je kiyi wanka time zai tafi kinsan a 12am zamuyi tafiyar" gyad'a mishi kai tayi tare da rufe qofar bata d'aga gurin ba sae manna bayan ta tayi jikin qofa tana kuka marar sauti nan ta zame jiki ta zauna qasa ta hade kai da guiwa tana ci gaba da kuka sbd tuna mata tafiyar tamkar ya tuna mata zasu rabu sbd bata jin zata barshi ya aiwatar da plan d'in shi kafin ita.
Da qyar ta hana kanta kuka ta fad'a toilet tayi wanka tana gama shiri taji knocking taje ta bude ta sami Hakeem a tsaye cike da kulawa ya riqo hannun ta yace"zo muje kiyi break fast.
Tafiya suke kan staircase sae kallon shi take inda ta fahimci fuskar nan tashi d'auke take da farin ciki fal.
Suna zuwa kan dining ya zauna tare da d'ora ta kan cinyar shi ya bude kula soyayen dankalin turawa ne da soyayyen qwai se plantain sunyi kyau sosai,
kallon shi tayi da mamaki tace"Bobby kuku ya dawo ne? A'a nine kukun mu na yau, kallon shi ta shiga yi domin tasan Hakeem bai iya komai ba,idon ta ya kai kan hannun sa inda taga ruwan mai ya qona shi har da yankan wuqa, kamar zata yi kuka tace"Bobby jibi yanda ruwan mai ya qona ka kuma har da yankan wuqa"forget about it, me yake damunki naga idon ki har ya soma kumbura kamar wacce tayi kuka"
ya fad'i hakane yayinda yake qarewa fuskarta kallo,duqar da kanta tayi tare da fad'in bacci ne"a u sure? gyada mishi kai tayi,nan ya sauke ajiyar zuciya ya fara ciyadda ita a hankali, kar6ar abincin take cike da damuwa bcs sae kallon hannun sa take da ya qone.
Yana cikin ciyadda ita ne ta kai hannu zata qarasa shigar da arish d'inda bai kammala shiga bakin ta ba, Hakeem yayi saurin dakatar da ita yace "kar ki 6ata hannun ki"
Shi ya shigar da arish d'in a hankali cikin bakin ta,Billy sae kallon shi take kamar mai neman wani abu a fuskar shi yace"me yake faruwa ne pinky ko wani abu kike so? girgiza mishi kai tayi tana qoqarin tashi kan jikin sa tace"na qoshi".
Sallamar doctor suka ji Hakeem ya amsa sallamar yayinda ya bawa Billy ruwa tasha ya zaro tissue ya goge mata bakin ta.
Gaban ta ne ya fad'i lokacin da ta hada ido da doctor sae duk jikin ta yayi sanyi domin ganin take yazo ne su tattauna kan plan d'in da suke shiri.
Tafiya take zata haura sama doctor ya kalli Hakeem yace"kamar pinky bata jin dad'i fa"saurin kallon ta Hakeem yayi yace "me ka gani doctor? Baka ga jikin ta a sanyaye ba fuskar ta fayau kamar mara lafiya,wlh na tambaye ta doctor tace min wai bacci ne, a'a ba gaskiya bane akwai abinda ke damun ta.
Hakeem na jin haka ya dakatar da ita ya jata suka zauna kan kujera sae kallon ta yake yace"pinky me yake damunki kike 6oye min? shiru ta mishi,Yace"please pinky say something.... may be ko ita bata san me yake damun ta ba,amma da alama zazza6i ke son kama ta bari naje cikin mota na d'auko allura ayi mata,ok doctor, nan doctor ya fita, Billy ta kalli Hakeem idanun ta cike da hawaye tace"Bobby bana son allura kuma ni lafiya ta qalau"no pinky da ganin ki ba kya jin dad'in jikin ki ki bari a miki allurà kinji,kuka ta fara mishi ya shiga lallashin ta.
Doctor yazo ya same ta duk ta shagwa6ewa Hakeem tana kuka bata son allura.
Yace doctor a ajiye zancen allurar nan bata so,, Hakeem... Please doctor wlh bana son jin kukanta ne da ace bana kusa da zan iya haqura domin in na tuna a gabana zaka soka mata allurar ina kallo to kuwa wlh ba mamaki zaka ji ina taya ta kukan,hmm shi dai doctor komai kasa cewa yayi sae kallon su yake cike da sha'awa yanda Hakeem ke lalla6a Billy kan ta daina kuka inda yake share mata hawaye cike da kulawa.
Sae da tayi shiru yace"kin qarasa packing?girgiza mai kai tayi yace"to je ki qarasa kafin muyi break fast nida doctor sae muje asibiti mu duba Naini kafin mu tafi,
nan ta tashi Hakeem ya bita da kallo cike da so har ta shige d'aki.
ya maida duban shi gun doctor da ya saki baki yana kallon shi sae kace statue, Hakeem ya 6allah hannun shi tare da waving fuskar doctor,doctor yace "ai ina qasar banje koina ba kawai dai na zama speechless ne,kana abu kamar ba soja ba....kai doctor ajiye zancen soja koma nace ka ajiye zancen komai idan ana zancen so, na rantse maka doctor na bala'in kamuwa da son pinky abinda ban ta6a tunanin zai faru tsakani na da ita ba.....gaskyr ka Hakeem domin ba wanda zai sanku a da yayi tunanin zaku zamo haka,kuma kasan Allah,tun farko fa Naini bai mutu ba nine na tsara hakan sbd na samu na sasanta ta ku kafin ku koma Nigeria,domin nasan tabbas baza ka bari a kama pinky ba zaka d'ora laifin a kanka se nayi tunanin in taga hakan zata fara sonka... Au haba? Allah kuwa,oh no doctor ai tun farko ita ta fara sake min kafin ni amma naqi bata dama domin na d'auka wani abu take shirin yi,,eyyah nifa duk a tunani na kai ka fara sake mata kuma tun lokacin da aka mata aiki na d'auka fishi take da kai bata daina ba,ashe kenan ko wata magana da naji tayi lokacin da police suka je da kai har na shiga mamakin ta, nasan ta fad'i haka ne sbd ganin kaqi sake mata bare ta sa ran zaku ci gaba da rayuwar aure... bari kawai doctor wlh yau cike nake da farin ciki zamu koma ga iyayen mu muna masu son juna duk da kuwa ba wanda ya furta ma wani so a cikin mu amma mun san muna son juna,
har ma na qagu mu koma gida domin kawai na furta cewa ina son pinky a gaban iyayen mu sbd na sasu farin cikin da ban ta6a sasu ba a rayuwa,har surprise nake son bawa Billy na pink mota da nasa aka qera mata hadaddiya, kuma 6angaren mu gabadaya kwalliyar pink nasa akayi har da daki na kuwa,ba wanda yasan da hakan hatta su umma da Abba,
Amjad kad'ai ya sani shida nasa aikin na kuma roqe shi kan kar ya fad'a ko su umma sun dawo sbd koda akayi aikin sunyi tafiya.
Amma fa gaskiya Hakeem sae dae nace Allah ya d'ore soyayyar nan taku har jannatul Fiddausi,amin doctor na gode sosai fa domin kayi min addu'ar da tun da na fahimci ina son pinky nakeyin ta wacce nake matuqar fatar ta zama kar6a66iya sbd soyayya ta da pinky ina ji a jikina ta daban ce ba ko wace irin soyayya bace... But doctor muje muyi break fast kasan na qagu mu koma Nigeria domin dole a sake bikin auren mu ayi wanda muke cikin farin ciki ba kamar wancan ba... Au haba? Allah kuwa kuma dole kaje domin na gayyace ka tun yanzu,,,inshaAllah kuwa zanje.
Nan suka je kan dining suna break fast cike da nishad'i Hakeem sae fad'in yake yanda zai tsara bikin har yana fad'in kaf abokanan sa da sukayi karatu a turai sae sun zo.
Pinky kuwa tana d'aki sae wani sabon kuka yazo mata domin ganin take suna can suna qara tsara plan d'insu na ganin Hakeem ya wulaqanta ta idan suka je Nigeria hakan yasa ta qudiri sae ta riga Hakeem aiwatar da plan d'in ta kafin shi.
Tafiya suke cikin mota sun fito asibiti zasu je airport sae kuka take ji sosai tana ta faman hana kanta domin duk jin take kamar su fasa tafiyar suyi zaman su har sae Hakeem ya fara son ta da gaske ko zasu koma.
Hakeem ya fahimci yanayin ta sae duk yaji ba dad'i nan ya shiga bata labarai masu ban dariya har ya samu ta fara sakewa har tana dariya.
Fara'a take abinta har suka shiga jirgi.
zaune take a 6angaren window jirgi na tashi ta kalli Hakeem cike da zolaya tayi pointing out of window tace"see Jennifer sae faman gudu take tana kiran ka,da wasa ya buge yatsar ya saka yatsar a bakin sa ya d'an ciza har sae da tayi er qara yace"idan kika sake nuna min Jennifer ko sae na mird'e yatsan, shi kuma bakin da ya sake furta Jennifer zan kama shi na tsotse tas tamkar alawa....a cikin jirgi mutane na kallon ka... to wa zai hana ni nida mata ta,bari ma kiga...dariya take ciki ciki tayi saurin 6oye fuskar ta a qirjin sa, a nan take se hawaye suka zubo mata sbd ko kad'an bata son ta tuna zata aiwatar da plan d'in ta har jin take kamar ta fasa taga shin me Hakeem zai yi amma gudun kar na Hakeem yasa ta baqin ciki da yawa zai sa ta fara nata kafin shi.
Hakeem kuwa cike da farin ciki yakai hannu ya qara rungumota tare da d'ora mata a kiss a ka yayinda ya furta a ransa
_"Allah ka nuna min mun isa gida lafiya domin na sanar da iyayen mu tsananin farin cikin da nake d'auke da shi a zuciya ta sannan na bawa Billyta surprise"_
To masu karatu muje muga shin wa zai riga wani a cikin su.
Nidai nace.....🙊oh no Nana saca only tace kar na fad'a😉 sae dae munga wa zai riga wani.
Luv u😘.
*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 7:22 PM] +234 810 038 8117: : [ 8/22/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na Billy giro😊*
*Page*
*👛45&46👛*
A washe gari suka sauka guraren qarfe goma na safe kasancewar sun kwana a garin abuja.
Suna fitowa Billy sae rarraba ido take ta inda zata hango su umma ai kuwa tana ganin su ta saki jakar hannun ta tafi da gudu ta fad'a jikin umma,Hakeem ne ya d'auki jakar ya biyo ta da ita inda ya same ta sae rungumar su Abba take wato mahaifin Hakeem da nata sannan ta jewa qawar ta Feenah da ita ma tana gurin.
Shima zuwa yayi cike da murna gurin iyayen shi suna tarbon shi,sae dad'i suke ji a ransu ganin Hakeem da Billy kowanen su yayi kyau ya qara haske kuma kallo d'aya zaka yi musu kasan suna son junan su sosai.
Nan suka tattara zuwa gida sae nan nan ake da su,sukayi zaune suna kwasar lafiyayen girkin da aka musu,gabad'aya kowa na kan dining sai santi suke zubawa sbd umman Hakeem mace ce wacce ta iya girki sosai.
Suna cikin cin abincin ne Abba sae kallon Hakeem yake wanda bakin sa yaqi rufuwa duk ya qagu su kammala cin abincin ya sanar da su albishir d'in da yake d'auke da shi.
Abban Hakeem yace"wai Hakeem
wannan wane irin albishir ne da kake son sanar da mu, naga tun kuna Abuja ka kira ni ka sanar dani akwai albishir,kuma naga da alama ka qagu ka fada, eh wlh Abba amma dai nafi son mu kammala cin abincin tukun....gaban Billy ne ya bada ras _me Hakeem ke shirin sanar da su da yake farin ciki haka shine har da gaya musu kafin ya iso,koma mene ne ya kamata na riga shi,_
Nan ta ajiye farfesun kifin da take ci sbd ta daina jin dad'in abincin gabad'aya har wani d'aci take ji a cikin bakin ta kamar wacce tayi zazza6i .
Abban Hakeem yace mamanah ya akayi kar dai kice kin qoshi?eh na qoshi....oh wai ke har yanzu kina nan da rashin cin abinci"
umma ce ta fad'i hakan.
Billy dai bata ce komai ba sae qoqarin tashi take domin ta matsu ta bar gurin.
nan ta wuce Hakeem sae kallon ta yake yana murmushi yayinda Feenah ke kallon shi sae duk taji soyayyar su ta fara bata sha'awa domin ta fahimci akwai so a tare da su.
Billy na shiga d'aki cikin sauri ta nemo takarda da biro hannun ta na rawa take rubutu yayinda hawaye ke ta faman zarya a fuskar ta d'agowar da zata yi taga mutum tsaye a kanta har sae da taji faduwar gaba
da sauri ta share hawayen da ke kan fukar ta tace"haba Feenah ya zaki shigo min daki ba sallama ni har kin tsorata ni wlh ... Hmmm lallai pinky me kike shirin yi ne haka naga kin wani rubutu saki kuma har uku...ba ruwan ki! ido ne kawai naki idan baza ki iya ba sae kisa kai, kuma wlh duk kika sanar da su Abba ni na rubuta shi kin san sauran... Meye sauran? Oho miki amma wlh se kinyi nadamar sanar da su da zakayi.
Tana gama fad'a ta nad'e takardar zata fita Feenah ta jayo ta tace"pinky ya kamata ki tsaya kiyi tunani kafin ki aikata komai domin zakiyi babbar nadama idan kikayi hakan,meye matsalar ki da Hakeem bayan kallo d'aya za a yi muku a san kuna son juna.... Hm baki san komai ba Feenah don haka ki barni kawai nan tasa kai zata fice Feenah ta fizgo ta da qarfi tace"pinky kar kiyi haka fa!cikin tsawa tace"Feenah!wai so kike sae ya riga ni aiwatarwa kafin ni!da Allah sake ni na wuce!
nan ta fizge hannun ta wanda yayi dai dai da shigowar umma tace"meye haka pinky me yake faruwa? Pinky tayi saurin 6oye takardar hannun ta tace"it's just about banci abinci ba take takura ni"to ya isa kizo Abbanku yana kira,
nan umma taja ta aka bar Feenah tace"tabbas pinky idan kikayi kuskuren bada takardar nan sae na nuna miki kuskuren ki domin zan aure Hakeem kina ji kina gani dama abinda najima ina nema ne.
Billy kuwa tafiya suke kan staircase gaban ta sae dukan uku2 yake zuciyar ta nata hana ta.
suna isa falo pinky ta sami guri ta zauña Abban Hakeem ya kalle ta yace"mamàna da alama kema akwai magana fal a bakin ki?eh Abba,,,to bari muji abinda yasa Hakeem ya tara mu a nan sannan kema ki fad'i taki ko,nan ta kalli Abba cike da damuwa,Hakeem ya lura da hakan yace"Abba ta fad'a muna jin ta,a'a kafa riga ta"Abban Billy ne yayi maganar,
Hakeem yace"ba komai ta fad'a kawai Abba, yayi maganar ne yayinda yake kallon Billy cike da murmushi yace"talk pinky kinji muna sauraren ki,kalloñ sa take sosai tace a ranta
_"kamar alamu sun nuna da gaske Hakeem ke sona har dai da na kalli qwayar idon shi but zan aiwatar da plan d'in naga bcs idan gaske ne yana sona to kuwa tabbas zai qaryata ni_
Da qyar ta samu ta sai sai ta kanta ta fara magana cikin natsuwa tace"Abba dama ba komai bane face abinda ya zama dole na sanar da ku, wanda nasan zakuyi baqin ciki da jin sa sae dai nace kuyi haquri domin nima ban so hakan ta faru ba,don ba yanda zan yi ne kawai.
Ba mu jima da zuwa new delhi ba, naso ace Hakeem ya bani dama mu kasance tamkar yadda kuke so ma'ana mu ajiye qiyayyar da muke yiwa junan mu, amma sae bai bani damar hakan ba ya nuna sam ba hakan a ransa kuma baya buqatar hakan, a nan ne yake sanar dani cewa na ma ajiye wannan zancen domin tun ranar da aka d'aura auren mu ya rubuta ya ajiye ni ba matar sa bace sam ba aure tsakani na da shi,da farko na d'auka ya fad'a ne kawài se na basar da zancen inda nake ta qoqarin ganin mun dai daita tsakanin mu amma yana zille min.
To da haka ne wata rana ina gyara mishi d'aki ,
a cikin drawers din sa ina tsara mishi wasu takardu se na had'u da wannan takardar wacce ta nuna min tabbas ba aure tsakani na da Hakeem wato da gaske yake tun ranar da aka d'aura auren mu ya raba wannan auren domin har date ya saka........ Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Abba ne ya fad'i zancen yayinda ya zare hular kanshi yana kallon takardar wacce ke rubuce da saki d'ai d'ai har uku.
Hakeem kuwa zumbur ya miqe cikin tsananin mamaki hannun sa na rawa ya kar6i takardar da ke hannun Abba yaga sak rubutun shi ne, kallon Billy ya shiga yi wacce ta tashi tsaye tana kallon shi sae fatar take ya qaryata zancen ta, shi kuma mamaki ya cika shi inda ya fahimci kenan dalilin da yasa pinky ta yaudare shi tasa ya koya mata rubutun shi,kenan soyayyar da take nuna mishi bada gaske bane,
_no!no!no pinky!_
Yayi maganar ne a cikin ranshi yayinda yake kallon pinky idanun sa sunyi jajir duk jijiyoyin kansa sun tashi,kansa ne yayi mugun sara mishi yayinda rayuwar shi da pinky ta new delhi keyi mishi yawo cikin kai,
nan ya dafe kansa yana ja baya yana magana a ranshi cewa _"if yes i can't life any more with out u pinky!d only thing i will just go n kill my self!i will kill my self ryt now!_
nan ya fita gidan kamar wani mahaukaci su Abba suka bishi suna kiran shi, pinky kuwa kuka ke qoqarin zo mata ta tafi da sauri zata haura sama gabadaya idon ta ya rufe bata ganin komai tafiya kawai take kan staircase wanda har ta kai matakalar qarshe sae kawai jiri ya debe ta ta zube, nan ta shiga gangarowa kan staircase.
Hakeem kuwa yana fita ya fad'a mota ya fige ta a haukace inda ya buge gate d'in gidan da qarfin tsiya ya fita.
Umma wacce bata riga ta fita ba tayi saurin zuwa gun Billy tana taslima duk hankalin ta ya tashi domin koda ta gama gangarowa ta some goshin ta sae fitar da jini yake.
Feenah ce ta fito da gudu jin yanda umma ke qwala mata kira.
Hakeem kuwa a bar zancen kawai domin yana fita ba ruwan sa da komai da ke kan hanya duk inda ya samu kad'a motar sa yake nan ya had'u da katuwar mota tayi cilli da motar shi wacce sae da tayi juyi uku kafin take tsayi.
A rikice su Abba dake biye dashi cikin mota suka tsaida motar su suka fito.
Tuni gurin ya cika da mutane akayi gaggawar fitar da Hakeem cikin mota ,nan aka tafi dashi *Hakeem Specialist hospital*
wanda koda suka je Amjad yana kan Billy wacce su umma suka kai hakan yasa wani likitan ya kar6i Hakeem.
Nan aka had'u su umma da Abba kowanen su cikin damuwa.
d'aki d'aya aka aje Billy da Hakeem d'aki ne na mutum biyu kacal sae dai kowanen su bacci yake.
Su Abba na zaune a d'akin ba mai cewa komai sae jiran farfad'owar su ake,kuma Alhmdlh ba wani jin ciwo Hakeem yayi ba.
Har akayi sallar zuhur ba wanda ya farfad'o a cikin su,nan su Abba suka tashi zasu je masallaci ita ma umma tace bari taje gida ta had'o musu abinci kafin su farfado,nan suka fita ya zamo Feenah kad'ai aka bari cikin d'akin.
Tana nan zaune ta fara ganin Hakeem na motsi cikin sauri taje ta kira doctor koda suka shigo Hakeem sae faman dannar kansa yake da ke mishi ciwo nan ya duba shi jiki sanyaye ya kalli Feenah wacce ya zaci er uwar hakeem ce yace"ki same ni office akwai wani abu da zan gaya miki a game da Hakeem.
Ba musu ta bishi ta samu guri ta zauna, nan ya cire gilashin da ke idon sa tare da furzadda iskan bakin shi yace"am sorry to say sae dai kuyi haquri da tsarin ubangiji domin a binciken da nayi kafin Hakeem ya farfado na same shi da matsala guda biyu da ya samu a sanadiyar buguwa, amma ban fad'a ba sbd ina so na qara tantancewa idan ya farfado,koda ya farfado naga haka d'in ne a bisa wasu tambayoyi da na masa.
Matsalar farko ita ce Hakeem ya manta komai wanda ya faru wata biyu da suka wuce ma'ana duk abinda ya faru a wata biyu da suka wuce bazai tuna su ba.
Cike da damuwa Feenah ke kallon shi inda ta shiga wani lissafi cikin qwaqwalwar ta, tace doctor don Allah ina so kar ka sanar da kowa wannan matsalar,sbd zaka d'aga hankalin iyayen mu don Allah doctor,,,gsky wannan matsala ba abin 6oye wa bace dole a sanar da iyayenku ko yanzu don ina sauri zan fita yasa nace kizo na sanar da ke amma mahaifin ku ne ya dace nayi wa wannan bayanin ba ke ba..but doctor na fi so na musu bayanin da kaina Allah bana so hankalin su ya tashi, tayi maganar ne cikin marairaiwa,yace to shike nan nayi miki alqawari bazan sanar da kowa ba, nan ta mishi godiya ta fita cike da jin dad'i a ranta kan ta sami wata damar da ta barwa kanta sani.
Da sauri doctor ke qoqarin kiran ta sbd bai gaya mata matsala d'aya ba sae dai kuma ya basar domin d'ayar matsalar ta wuce ya sanar da feenah ita sae dai mahaifin su.
koda ta koma dakin ta samu Billy ta farka sae kallon Hakeem take da ya juya bayan shi wanda takaici ya cika shi yana tunanin me ya faru da shi da har yazo asibiti aka kuma had'a shi da pinky d'aki d'aya.
Shigar Feenah keda wuya sae ga su umma sun dawo har da su Abba.
Nan Hakeem ya juyo domin ya tambayi abinda yasa aka kawo shi asibiti sae dae ganin fuskar Abba a d'aure yasa yayi shiru.
Gurin Billy Abba ya nufa yana mata sannu kafin yake maida duban shi gun Hakeem wanda yace"Abba wai me yake faruwa ne...kar ka raina mana hankali ai kafi kowa sanin abinda ya faru.
Nan Abba ya fitar da takardar saki yace gaya min gaskiya kai ka rubuta takardar ko kuwa?Abba ban fahimce ka ba ita wannan takardar a ina ta fito....a gidan ku ta fito d'an rainin hankali!ka gaya min wa yayi wannan rubutun nace!?
Nan Hakeem ya kar6i takardar yana kallo yaga tabbas rubutun sa ne kan cewa ya saki Billy wani irin dad'i yaji har cikin ransa,amma kuma bazai iya tuna lokacin da yayi shi ba shidai kawai abinda ya sani yasan an d'aura aure tun daga haka ba zai iya tuna wani abu ba.
Nan ya d'ago yana kallon Abba yayinda Billy ta tsare shi da kallo domin taji me zai ce.
Yace"Abba wannan ai rubutu na ne kuma ni nayi shi.
0 comments:
Post a Comment