Waheed ya tashi zae fita mami tace"zo mana waheed kaja hannunta ku tafi gida ka rarrashe ta kaji"
Waheed ya tsaya ba tare da ya juyo ba mami da kanta ta taso riqe da hannun bintu ta rakosu har mota suka shiga snn tace da bintu"kar ki damu inshaa Allah a cikin satin nn zamuje India a duba matsalar ki daina kuka haka ya isa kinji.
Ta qarashe mgnr ne cikin share mata hawaye snn ta rufe mata ganbun mota waheed ya tashi mota suka tafi wanda koda kuskure bae yarda ya kalli gefen bintu ba har suka isa gida.
Kae tsaye d'akinsa ya nufa bintu na biye dashi a baya yana kai bakin qofa ya juyo cikin 6acin rae yace"wae lafiyar ki kike faman bibiyita sae kace wata mayya!
Kallon sa tayi jiki sanyaye ta durqusa kan guiwoyin ta kanta qasa cikin muryar kuka tace"komai zaka ce min kace yaya waheed na cancan ci haka amma dan Allah ina son ka yarda cewa wlh ba wani magani da nake sha bayan......da saurin sa ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu yace"bana son jin komai daga gare ki na tsaneki ki tashi ki tafi i dnt wnt see u any more!
Wasu hawaye masu zafi ne suka gangaro kan fuskar ta tana kallon shi tace"dan Allah.....ya daka mata tsawa ki tashi nace bana son ganin ki!!
Bintu ta tashi cikin kuka ta bar gurin waheed ya shiga d'aki ya rufe ganbun sa da qarfi, ya manna bayan sa jikin qofar qwallah tap a idon sa yana jin wani irin zafi a cikin zuciyar sa kmr ana hura masa wuta meyasa Bintu zata masa haka bayan ya yarda d'ari bisa d'ari cewa tana son shi nn kawai ya fashe da kuka ya durqushe gurin kmr wani qaramin yaro wae yau shida kanshi yasa hannu ya mari bintu ya kirata mayya ya kuma ce ya tsaneta baya son ganinta,
inama mafarki ne bintu bata aikata haka a gare shi ba.
Bintu kuwa tana zuwa d'aki ta fad'a ruf da ciki kan bed tana ci gaba da kuka yau abinda takeyiwa gudu ya faru shike nn yaya waheed ba zae qara ganin ta da daraja ba gashi har yana furta cewa ya tsane ta baya son ganin ta.
Babban kuma abinda yafi d'aure mata kae shine maganin da aka ce tana sha dan kar ciki ya zauna ita da tun rnr da ta zubar da cikin farko tayi nadama ta kuma d'auki alqawarin baza ta sake kuskure irin wnn ba amma sae gashi bata tsira ba inama bata aikata na farkon ba da duk hkn bata faru ba.
Tashi tayi ta share hawayen fuskar ta snn ta d'auki wayar ta ta kirasu zeenah ta gaya musu duk matsalar da take ciki suka ce mata kar ta damu suna nn zowa yanzun nn zasu shirya suzo skt.
Hkn yasa ta d'anji sanyi sanyi a ranta.
Su kuma su zeenah suna ajiye waya zeenah ta ba sarah hannu suka tafa tace"lokaci yayi tarkona ya fara kama er banza kmr yanda muka ta6ar6are a yawon banza ba aure haka itama sae tazo tanayin shi tashi maza shirya mu d'au hanya yau skt tayi kira bari in kira my guy yazo ya kaimu.
Bintu na kwance kan darduma kmr wata mara lafiya ta soma jin sallamar su zeenah da saurin ta ta kalli agogon bangon d'akin, yaushe yaushe ne tayi waya dasu awa biyu bata ko cika ba amma gashi har sun iso Allah sarki en uwa masu qaunar ta su kam sam basu gado halin iyayen su ba shiyasa take son su.
Ta tashi a hankli ta bud'e musu qofa suka shigo suka zauna ta kawo musu ruwa da lemu ta zauna sae kallon ta suke kmr masu jin tausayin ta da gaske har zeenah na fad'in"Allah sarki bintu duk kin rame lokaci d'aya"
Bintu tace"dole ne zeenah ni kad'ai nasan irin tashin hankalin da nake ciki abinda nayiwa gudu tun farko kuka ce min ba abinda zae faru"
Sarah tace"kiyi haquri mu kanmu bamu d'auka hakan zata faru ba shiyasa amma ae sauqin abun kince bai gaya ma mahaifiyar sa ainihin abinda ya faru ba koh.
Eh 6oye mata yayi shine ma har take cewa a cikin satin nn zamu tafi India a duba matsalar yanzu babbar damuwa ta shine maganin da Dr Khalid yace wae ina sha dan kar ciki ya zauna byn ni wlh ban san ina shan wani magani ba shine kaina ya d'aure gabad'aya gashi yaya waheed yaqi ya saurare ni.
Zeenah tace"ke kanki kinsan ba zae saurare ki ba a yanayin da yake ciki yanzu kin ma ci sa'a da wani ne da ba haka ba kuma duniya duk sae tasan abinda kika mishi amma shi gashi har mahaifiyar sa ma bai yarda ya gaya ma ba"
Qwallah ne suka ciko tap a idon bintu tace"ni kaina nasan nayi sa'a amma yau nasan na kaishi karshe tunda har ya iya d'aga hannun sa ya mareni ya kuma ce ya tsaneni baya son gani na.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka ta yanda duk wani mae sauraren ta dole yaji tausayin ta sae dai kuwa in babu sauran imani a zuciyar sa.
Idanun zeenah ne suka ciko tap da qwallah har suna gangarowa kan kumatun ta ta rungume bintu sae rarrashinta take tana bata haquri.
Kana ta d'agota sae share mata hawaye take tana fad'in"kiyi haquri bintu ki daina kuka inshaa Allah a yanda waheed yake sonki kika ci gaba da lalla6a shi yau da gobe zae saurare ki ya fahimce ki ya kuma yafe miki har komai yazo kmr ba'ayi ba.
Cikin kuka bintu tace"to idan mahaifata ta sami matsalar da baza a iya magancewa ba fa ya zanyi kunsan dai bazai zauna dani haka ba dole zae qaro aure"
Zeenah tayi saurin rufe mata baki tana fad'in"ki ma daina fad'ar haka inshaa Allah hkn bazai faru ba.
Da suka fito zasu koma suna tsaye suna jiran wanda ya kawo su bai riga yazo ba sarah ke cewa"nifa zeenah kin tsoratani naga har taya ta kuka kike kaddai kin fara jin tausayin ta ne?
Zeenah ta le6ace baki tace"hm wane tausayi nayi ne kawai dmn ta qara yarda mu masu qaunar ta ne"
Sarah ta sauke ajiyar zuciya tace ae ca nake tausayin ta ne ya kamaki sae duk naji jikina yayi sanyi sae tunani nake kaddai har game d'in tazo qarshe cikin sauqi haka.
Zeenah tace"cabd'i ae wlh game kam yanzu aka fara in gaya miki.
Kafin sarah tace komai sae ga wanda suke jira yazo suka shiga mota suka wuce.
Bintu kuwa har dare bata sake sa waheed a idon ta ba sbd tun lokacin da ya shiga d'akin sa bai sake fitowa ba,washe gari kuma koda ta fito har ya shirya ya tafiyar shi gurin aiki.
Da yake tana da motar kanta da ya saya mata ta shirya ta tafi asibiti gurin nata aiki amma ta fita ne kawai ba dan zata iya aikata komai ba.
6angaren mami kuwa tun jiya da tausayin bintu ta yini ta kwana ganin yanda duk bintu ta damu sae kuka take shiyasa ta yanke shawarar yau zata sa ayi komai na tafiyar su zuwa gobe se su tafi.
Cikin d'aki take ta fito falo ta sami hajjo sae gyaran gida take tace"hajjo d'an ajiye aikin nn kizo akwai mgnr da nake son muyi"tana kaiwa nn ta zauna kan doguwar kujera hajjo tazo da sauri ta zauna qasa cike da ladabi tana sauraren me mami zata ce.
Mami tace"hajjo ba wani abu bane dama tafiya ce ta kama mu gobe inshaa Allah zamu tafi India nida waheed da kuma bintu shine nace kema yau idan kin gama aikin da kk ki harhad'a en kayanki ki tafi qauyen ku har sae mun dawo.
Hajjo ta numfasa tace"Allah dae yasa tafiyar ta lafiya ce"
Mami tace"eh to lafiya ba lafiya ba bintu ce zamu kae asibiti a dubata"
Hajjo tace"Subhanalillahi me ya same ta?
Mami tace"wlh tana d'an fama da wata matsala a mahaifar ta ne shiyasa ma kika ji en jikokin nawa shiru har yanzu amma inshaa Allah muna sa ran idan muka je india za'a magance matsalar kidae ta taya mu da addu'a Allah yasa muje a nasara.
Hajjo bata iya cewa Amin ba sae jinjina kanta da ta shiga yi.
Mami tace"yadai hajjo lafiya?
Tace"Wato hajiya wata magana ce da naji jiya har ma ban yarda da ita ba nace kodae ba bintun da na sani bace amma inko har mgnr da naji da gaske ce meyasa zaku d'auke ta ku kaita asibiti byn korar kare ma ya kamata ace kunyi mata ba zancen ku taimaka mata ba..hm mts inaga dae mgnr nn ba gaskiya bace ko kuma ince wata bintun dai ce ta daban bata gidan nn ba kmr yanda na zata.
Cikin d'aurewar kae mami tace"wae hajjo zancen me kike yi bangane ba fayyace min ta yanda zan fahimta.
Um um hajiya tunda har baki ji zancen nn a bakin waheed ba to ba gaskiya bane.
Kinga hajjo gaya min insan abinda ake ciki ,
halin waheed na sani duk abinda yasan zae 6ata min rai ba zai yarda ya gaya min ba.
Hajjo ta nisa tace"wlh hajiya abin ne ba dad'i ban so ace daga bakina kika fara ji ba"
Koma mene ne hajjo gaya min ba komai ae zaman tare ya kawo haka idan baki snr dani ba wa zae gaya min tun da shidai waheed ba fad'a yake yi ba.
Hajjo ta jinjina kanta cikin jimami tace"Wato hajiya jiya da kika aike ni ne na biyo zan wuce naga wasu en mata kusa da gidan nn sun tsaya sae jimami suke suna magana kan wae mugun nufin da bintu taso aiwatarwa akan waheed Allah bai bata sa'a ba asirin ta ya tonu.
Da mamaki mami tace"Bintu kuma me aka ce tayi?
Hm wae cewa sukayi ba tsakani da Allah ta auri waheed ba ta aure shi ne dan suci dukiyar shi shiyasa duk cikin da ta samu bata bari take zubarwa lokaci kawai suke jira su kawadda shi su kwashi dukiya su gudu daga qasar nn gabad'aya.
Er dariya mami tayi tace"kae wannan zancen ba gaskiya bane hajjo, bintu dako 6atan wata bata ta6ayi ba ina zancen tana samun ciki tana zubarwa da akwai dae ko wace ce suke magana akanta ba 'yata bintu ba kam.
Hajjo tace"nima dae haka nace hjy shiyasa koda kuskure ban miki zancen ba amma hjy ji nayi fa suna cewa wae waheed da kanshi ya d'auke ta suka je asibiti dmn a duba waye mae matsala a cikin su koda aka duba bintu ce keda matsala sbd yawan zubar da cikin da takeyi ya haifar da matsala a mahaifar ta har ma ana ganin baza ta ta6a iya haifuwa ba sbd mahaifar ta riga ta samu matsala,naga dae a rayuwata mae suna waheed d'aya na sani wato na nn gidan sae gashi kuma yanzu kin kirani kince zaku kai bintu asibiti sbd matsalar da mahaifar ta take dashi shine naji gabad'aya kaina ya kunce kaddai mgnr da naji gaskiya ce.
Shiru mami tayi tace"ikon Allah wnn zancen naki ya soma rikita ni Hajjo koni nn babu wani mai suna waheed da na sani face d'ana waheed kuma jiya nice na tura su asibiti dmn a duba waye mae matsala a cikin su da suka je ya dawo cikin damuwa shi kad'ai ba tare da bintu ba sae tmbyr sa nake lafiya ina yabar bintu ya min shiru sae gata ta shigo ita har kuka ma take da na nemi ta fad'a min waye mae matsala a cikin su zatayi magana knn waheed ya kar6e wae ba wata matsala lokacin haifuwar ne kawai baiyi ba nace ya gaya min gsky bana son 6oye 6oye dmn wnn damuwar da nagani a fuskar sa ya nuna akwai matsala snn ne fa yake cemin eh fatima ce akace tana d'an da er matsala a mahaifar ta.
Kinga ko nn abun dubawa ne amma duk da haka zancen nn bae kamani ba gsky dmn bintu yarinya ce mae qaunar waheed bana tunanin abinda aka fad'a akanta gaskiya ne, sae dai waheed yazo zan tuntu6e sa inji,tashi kawai kije kici gaba da aikin ki.
Hajjo ta tashi ta wuce mami na nn zaune mgnr sae dawo mata take tana mamaki bintu kae ba gaskiya bane wata bintu ce ba 'yata bintu ba.
Yini mami tayi tana tunanin mgnr da hajjo tazo mata da ita, ta kira waheed tace idan sun tashi daga gurin aiki koina kar ya tsaya yazo tana son ganin shi.
Haka ko akayi tun daga banki waheed bai zarce koina ba yazo gidan mami.
D'aki suke ita da dashi tana zaune kan sofa yana zaune qasa ya sadda kansa qasa yana sauraren me zata ce.
A natse tace"waheed kar ka kuskura kace zaka 6oye min abinda zan tambaye ka, gaya min shin da gaske ne bintu tana samun ciki amma zubarwa take wanda dalilin hkne yasa mahaifar ta ta sami matsala iye?.
Da saurin sa ya d'ago yace"wa ya gaya miki wnn mgnr mami?
Mami tace"kaga waheed ba ruwanka da wnn gaya min eh ko a'a kuma in ka 6oye min ka sani ban yafe maka ba"
Qwallah tap a idon sa yace"eh mami amma na kasa gane dalilin da yasa fatima ta min haka"
Tace"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! amma waheed dama kasan bintu tana samun ciki tana zubarwa shine baka ta6a gaya min ba ko kuma kaima sae jiya ne da kuka je asibiti kake ji a bakin khalid?
Mami nasan tana samun ciki amma ban san ita ke zubarwa da kanta ba na farkon ma banko san ta same shi ba har ta zubar.
Mami ta dafe kanta tare da fad'in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!mgnr nn gskiya ce knn kae!me mutane suke son maida kansu ne wae cabd'i!banga ta zama ba maza tashi muje ka gaggauta rubuta mata takardar sakinta ka bata.
A rud'e waheed ya kalli mami yace"mami saki fa kika ce"
Mami tace"yanzu yanzun nn ma kuwa tashi maza muje"
Girgiza kansa yayi da sauri muryar sa na rawa yace"mami wlh bazan iya sakin fatima ba na rantse amma ki fad'i ko wane irin hukinci kike son in mata zanyi wlh,amma banda na saki dan girman Allah mami"
Mami tace"waheed umartar ka nake ba wae ina baka shawara ba dan haka kar in sake jin kayi wata magana wlh!
Nan ta jawo mayafinta ta yafa tana fad'in"muje yanzun nn ka rubuta mata takadar sakinta ka bata tayi gaba can ta qarata da mugun halinta"
Komai waheed bae sake cewa ba asali ma jikinsa ne ya mutu liqis ya kasa yin komai har sae da mami taja hannun sa suka fito yana biye da ita kawai kmr wani gunki har tasa shi cikin mota ta zagaya ta shiga gefen driver ta tashi mota suka tafi.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 22&23_*
Bintu na d'aki dawowar ta knn daga asibiti ko uniform d'in jikinta bata cire ba tana dae batun cirewa ne ta soma jin mami na qwala mata kira,
duk inda hankalin ta yake sae da ya tashi dan bata ta6a jin mami tayi mata irin wnn kiran ba sae yau.
Fasa cire uniform d'in tayi ta fito jiki sanyaye ta same su falo gaban ta sae dukan tara tara yake shike nn ita ma mami taji me ya faru dan daga kallon yanayin fuskarta ta san cewa ta gama jin komai, jikinta na rawa ta durqusa har qasa zata gaida mami,da sauri mami ta d'aga mata hannu tace"riqe gaisuwar ki bana so snn ta maida dubanta gun waheed dake zaune qasan tilse yayi zaman tahiya kmr wani mae neman gafara ta miqa mishi biro da takadar tace"ungo gata nn maza rubuta mata takadar sakinta yanzun nn ka bata.
Kmr saukar guduma bintu taji zancen wacce a rud'e ta d'ago da sauri ta kalli mami dake tsaye tana miqawa waheed biro da takarda ya kasa amsa sae marairaice fuska yayi zae yi magana tace"kar ka kuskura kace zakayi wata magana kaji na gaya ma maza kar6i takardar nn da biro ka rubuta min abinda na umarce ka.
Waheed ya kar6i takarda da biro bintu tayi saurin girgiza kanta tana kallon mami qwallah tap a idonta ta had'e tafukan hannayen ta tace"Dan Allah mami kiyi haquri kar ki sa ya sakeni wlh na yarda kumin ko wane irin hukunci amma banda na saki"
Mami tace"au in yaso sae ki sami damar aikata mugun nufin naki akan shi koh"
Cikin muryar kuka Bintu tace"mugun nufi kuma mami"
Mami tace"au a tunanin ki bamu san abinda kk shirin aikatawa ba,to bari kiji duk abinda kuke shirin aikatawa na jishi a kunne na dan hk dake har iyayen naki baku isa ku rabani da d'an nn qwaya d'aya tal da Allah ya bani ba idan ku mayu ne can kuci kanku Allah bazai ta6a baku nasara ba koma a ina kuka je.
Waheed ya miqe tsaye yace"haba dan Allah mami wnn wane irin zance ne kikeyi haka banbarakwai ba dad'in ji"
Cikin d'aga murya tace"yi min shiru waheed! kuma idan naji ka sake cewa wani abu a nn zan maka abinda baka ta6a tsammani ba wlh,shashasha kawai wanda bai san abinda yake yi ba! Ka rubuta mata takardar sakinta nace ka bata ko kuwa sae ka gama 6ata min rae ne iye!
Waheed yayi shiru kawai bai ce komai ba sae kallon takarda da biro yake da kmr ba zae iya rubuta abinda ta umarce shi ba.
Tace"ban isa ba koh!?
Yace"ko d'aya mami wlh ba haka bane amma dan Allah kiyi haquri na mata wani hukuncin ba wnn ba.
Cabd'i lallai inaga baka san abinda wnn yarinyar take shirin aikatawa akan ka ba shiyasa,ta nuna bintu tace"ka ganta nn bata aure ka dan komai ba sae dan dukiyar ka shiyasa duk cikin da ta samu bata barin shi take zubarwa kai d'in ma lokaci kawai take jira ta kawadda kae ta kwashi dukiya su gudu.
Waheed yace"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!mami a bakin wa kk ji wnn mgnr wa ya gaya miki da har kika yarda cewa fatima zata iya aikata haka a gareni bayan kinfi kowa sanin irin qaunar da take min.
Au qaunar da take maka ne yasa duk ta sami ciki take zubarwa.
Kansa ne ya kunce lokaci d'aya qwallah suka ciko masa ido haqiqa mami tayi magana a nn amma baya jin bintu zata iya cutar dashi ko nn da can da akwai dai dalilin da yasa take zubar mai da ciki dashi kansa ya kasa gane dalilin.
Idanun sa jajur ya kalli bintu wacce ke kuka cikin tashin hankali da jin zancen mami da ya qara rikitata.
yace"fatima ashe dama dalilin da yasa kika aure ni knn ba sona kikeyi dagaske ba!?
Cikin kuka tace"yaya waheed wlh na rantse maka ba haka bane ban aure ka dan komai ba sae dan qaunar da nake maka"
Yace"qarya kike ba kya qauna ta fatima kan me zaki ta zubar min da 'ya'ya na to gaya min ko duk cikin so ne!
Da sauri ta tashi daga durqushen da take taja da baya ganin yanda yake matsowa kusa da ita kmr zae duke ta bata iya cewa komai ba sae wani sabon kuka da ta fashe dashi dan bata san ma ta yanda zata mishi bayani ba.
Waheed sae kallon ta yake zuciyar sa na masa wani irin zafi da quna ba dan komai ba sae dan baqin cikin quncin rayuwar da ta jefa su a ciki suna zaman su mai dad'i tazo ta 6ata musu komai wanda shi ya tabbatar abinda mami ta jiyo ba gaskiya bane bintu bazata iya aikata shi ba amma ba yanda zai yi tunda bintun taqi tayi bayani.
Mami tace"kaga waheed bana son wani 6ata lokaci yi abinda na umarce ka kawai tayi ta bar gidan nn in daina ganinta idan kika tafi can kya yiwa iyayen naki bayanin bakuyi nasara ba Allah ya tonu asirin ku.
Waheed ya runtse idanun sa ko kad'an baya jin dad'in yanda mami ke sako iyayen bintu a ciki yafi son koma mene ne ta tsaya akan bintu.
Komai bai sake cewa ba ya rubuta takarda ya ba bintu ta kar6a sae kallon takardar take tana hawaye.
Mami tace"kuma kisani a cikin satin nn waheed aure zai yi dan haka ki tabbatar kin kwashe duk wasu komastsanki da kika san naki ne ki tafi dasu bana da buqatar ganin su a gidan nn"
Bintu dake kallon mami wasu hawaye masu zafi suka gangaro kan fuskar ta tasan dole abinda zae biyo baya knn,bata ce komai ba ta juyawar ta zuwa d'aki.
Mami ta kalli waheed wanda gabad'aya hankalin sa ya gama tashi da jin zancen ta dan yasan tun da har ta furta ba makawa haka ne d'in zae faru wanda cike yake da son ya mata magana amma bata bar yace komai ba taja hannun sa suka bar gidan.
Itama bintu ba 6ata lokaci ta bar gidan sae kuka take janye da akwati a hannun ta.
Motar kasuwa tabi cikin mota ta yanke shawarar ko taje gida baza ta bar umma ta sani ba zata ce kawai ganin gida tazo,ba don komai ba sae dan bata son ganin irin baqin cikin da umma zata shiga a ciki da kuma irin maganganun habaici da zata sha agun iyayen su sarah wa'enda burin su knn ko yaushe su gansu cikin matsala.
Byn isha'i suka isa garin birnin kebbi ta samu napep ta kaita gida, bata yi sallama ba dan bata son kowa yaga shigowar ta, taci sa'a kuwa har ta shiga d'akin su ba wanda ya ganta kowa babu a falo ta shiga daga ciki ta sami umma ta fito daga bathroom knn.
Da mamaki umma tace"bintu kece da daren nn da kuma uwar akwati haka ga kuma uniform a jikin ki ko cirewa bakiyi ba lafiya me yake faruwa?
Duk yanda bintu taso 6oye ma umma damuwar ta ta kasa ta saki akwati taje da gudu jikin umma ta fashe mata da kuka.
Umma taja ta suka je gefen gado suka zauna tana kallon ta da kulawa tace rashin jinki yasa kunyi fad'a da waheed koh?
Girgiza kanta tayi
Umma tace"to mene ne?
Ba komai yaya ne zae yi tafiya.
Umma ta girgiza kanta tace"to shine kike ma kuka haka awa wacce akayiwa mutuwa ina waheed d'in yake tare kuka zo ko kuwa"
Aa ba tare muka zo ba yana can.
To wace irin tafiya ce zai yi da bazai barki gidan mamin sa ba kmr yanda ya saba.
Zai jima sosai shiyasa.
To komai jimawar da zaiyi bintu ae bai kamata ace kin dawo ba keda kike aiki.
Na d'auki hutu ne....shi aikin asibiti ake d'aukar hutu haka kawai,hm mts ni narasa meyasa waheed yake biye miki da galihun nn ae gwanda kiyi aiki tuquru ki san halalinki kike ci.
Bintu tace"umma wlh ni tun lokacin da na fara aiki rana d'aya ban ta6a tsallakewa ba ko yanzu lalura ce ta kama.
Umma tace"to naji shi drivern da ya kawo ki yana ina ko a motar ki kika zo?
Aa ba a mota ta nazo ba, yunwa nake ji umma banci komai ba nazo"
To ae kinsan hanyar kitchen sae ki tashi kije ki sami abinda kika ci.
Nan ta tashi ta fita umma taja akwatin ta takai ta inda ta dace.
Bintu kuwa tea ta had'a tazo falo tayi zaune tayi shiru qwallah tap a idon ta sae motsa tea take tana tunanin duk rnr da umma ta gano gaskiya ya zatayi tasan kashin ta ya bushe gashi ko yanzu sae tambayoyi take ta mata wanda hkn ne yasa ta qirqiro cewa yunwa take ji dan ta samu ta ku6uta daga tambayoyin da umma ke mata amma halin da take ciki sam bata jin zata iya cin komai duk da irin yunwar da take ji kuwa.
Motsin da taji ne yasa tayi saurin share hawayen da suka gangaro kan kumatun ta.
Umma ce ta fito sae da taje ta kunna tv snn tazo ta zauna ta kalli bintu had'e da fad'in"keda kika ce yunwa kikeji baki ci komai ba shine baki ga abin had'awa ba sae tea byn akwai abinci"
A sanyaye bintu tace"umma ko tean ma naji kmr bazan iya shan sa ba"
Umma tace"ae tunda kika had'a shi sae kin shanye shi tas in gaya miki, nn ba irin gidan ki bane da kike 6arnar da kika ga dama.
Umma wlh ba 6arna bace shan sa ne bazan iyaba kuma so nake inje ko ruwa na watsa in cire uniform d'in nn duk sun isheni.
Umma tace"to sha ko kad'an ne sae ki tafi"
Yanayin fuskarta kmr zatayi kuka tace"Umma dan Allah bari in tafi.... ba inda zaki je fa sae kin sha ko kad'an ne idan kuma d'ure kike so in miki to a shirye nake.
Kan dole bintu ta kur6a kad'an ta ajiya ta tafi acewar zata dawo ta qarasa shanye sauran idan ta cire uniform wacce ta fad'i hkne kawai dan kar umma tace tazo sae ta qara sha.
Umma dae bata ce mata komai ba sae binta tayi da kallo dan ta fhmci duk ta fad'a ta rame.
Dama labarun Kebbi TV tazo kallo ana gama labarun ta kashe Tv ta d'auki tean da bintu ta ajiye ta tafi d'aki riqe da shi a hannunta, ta sami bintu cikin shirin ta na bacci zaune kan bed ta had'e kae da guiwa.
Kan bedside drawer ta ajiye tean snn ta zauna gefen gado kusa da bintu wacce sae a lokacin taji shigowar ta tayi saurin sa hannu a 6oye ta share hawayen fuskarta snn ta d'ago a hnkli ba tare da ta iya kallon umma ba.
Umma tace"ke shike nn dan waheed zai yi tafiya kibi kisa damuwa a ranki kmr wanda in ya tafi ba zae dawo ba"
A sanyaye bintu tace"umma zae jima sosai ne shiyasa "
Umma ta numfasa tace"duk da haka bintu kukan nn yayi yawa ki duba fa koda kika zo gidan nn duk idanuwanki a kumbure suke sbd kuka sae kace kece farau tafiyar miji ko da yake banga laifin ki ba waheed mutumin kirki ne da ko kwana d'aya kayi tare dashi bako so ya tafi ya barka, kece dai yini d'aya ma kin ishi mutum.
Komai bintu bata ce ba sae kallon umma tayi ta sake maida kanta qasa.
Umma tace"tsawon wane lokaci zae d'auka kafin ya dawo?
Hawaye ne suka silalo mata ta share hawayen snn tace"nima bai gaya min lokaci ba ya dai ce zae jima"
Cikin yanayin tausayi umma taja ta zuwa jikin ta tana shafa bayanta cikin rarrashi da haka har bacci ya kwashi bintu.
Umma ta kwantar da ita taja blanket zata rufa mata jikinta sae ta hango hannun ta dunqule da wani abu,a hankali ta ware hannun taga takarda ce ta ciro takarda ta bud'e zata karanta.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 24_*
Ta bud'e takardar zata karanta knn sae taji qarar wayar ta tana ringing sae kawai ta linke takardar ta jawo bedside drawer ta saka snn taje ta d'auki wayarta.
6angaren waheed kuwa suna isa gidan mami,mami ta zaunar dashi kan doguwar kujera taje ta d'ebo mishi abinci tayi zaune kmr wani qaramin yaro zata fara bashi a baki.
Bae kar6a ba yace mami ki barni inyi magana dan Allah.
Mami ta sake kae spoon a bakin shi tace"ci abinci tukun zamuyi magana kaji"
Yace"Mami bazan iya cin abinci nn ba wlh so nake kawai naji shin zancen aure nn kin fad'a ne kawai ko da gaske kike?
Mami ta numfasa tare da maida spoon a plate tace"ba wasa nake yi ba waheed da gaske nake kuma a cikin satin nn inshaa Allah nake so ayi komai dmn so nake ka manta da bintu kwata kwata a rayuwar ka ko tunanin ta bana so inga kanayi.
Waheed yayi shiru kawai dmn abinda mami ke fad'a ita kanta tasan ba zae yiyu ba,ba zae ta6a iya manta bintu a rayuwar sa ba har abada sae dae kuwa idan qwaqwalwar sa ce ta sami matsala.
Ya kalli mami cikin yanayin begging yace"Mami ki taimaka min dan Allah ki janye zancen auren nn wlh gabad'aya aure ya fita a raina nafi so in ci gaba da rayuwata ni kad'ai bana da buqatar wata abokiyar rayuwa.
Hm waheed knn bari kaji in gaya ma aure kam anyi an gama kuma a cikin satin nn inshaa Allah idan kae baka da buqatar abokiyar rayuwa ni inada buqatar inga en jikokina snn dan mace d'aya ta cuceka ae bashi zae sa ka tsani duka matan duniya ba dmn kowace mace da irin halinta kuma wacce nake son in had'a ku aure ka santa yarinya ce mae natsuwa da hankali wato Husna er gidan Hajiya binta wacce akae akae take zowa gidan nn tana kawo min ziyara ina ce ka gane ta?
Shiru kawai waheed yayi wanda ko kad'an baya son mami na masa zancen auren nn shi abinda yake matuqar damun sa ya kuma d'aure masa kae shine shin a ina ne mami taji cewa bintu ta aure sa ne dmn taci dukiyar sa"
Mami tace"wae waheed baka jina ne ina maka magana kamin shiru.
A hnkli ya numfasa yace"kiyi haquri mami so nake ki gaya min dan Allah a bakin wa kika ji cewa bintu ta aure ni ne kawae dan taci dukiya ta.
Mami tace"waheed meyasa kake son sae kasan wanda ya gaya min?
Sbd nayi mamakin yanda akayi har kika yarda da zancen nn mami.
Tace" Waheed ni kaina da farko nayi matuqar mamaki da jin zancen nn sbd nafi kowa sanin irin qaunar da bintu ke maka snn kuma a iya sani na ko 6atan wata bintu bata ta6a yi ba hkn yasa nace ba bintu 'yata ba kam sae dai ko wata can ce suke mgnr ta amma in kazo zan tuntu6e ka inji,sae gashi da kazo na tambaye ka kamin bayani dae dae yanda naji mgnr kaga kuwa dole in yarda tunda kae kanka kace baka san dalilin ta na zubar ma ciki da take yi ba,ko kun ta6a wani fad'a ne ka 6ata mata rae da yawa shiyasa take ramawa da hakan?
Ko d'aya mami a zaman da mukayi ban san munyi wani fad'an azo a gani ba.
To ko ta ta6a ce maka tana son kuyi planning sbd karatun ta kace mata a'a?
Aa mami asalima duk ta samu ciki ya zube sosai tafi ni shiga damuwa se tayi ta kuka sae ni zanyi ta rarrashin ta.
To ka gani duk nn zaka fahimci na munafurci ne kawai tunda cikin farko ma baka san ta same shi ba har ta zubar,dan haka nake son kar ka bani kunya waheed ka yarda ayi auren nn kmr yanda na buqata.
Idanun waheed ne sukayi jajur suka ciko tap da qwallah sam a tsarin rayuwar sa bai ta6a kawo zaiyi rayuwa da wata 'ya mace ba bayan bintu koda kuwa ace mutuwa ta rabashi da ita sae dai yayi rayuwar sa shi kad'ai amma yanzu ya zama dole yayi biyayya ga mamin shi ko dan kasancewar sa shi kad'ai ne d'anta a duniya da zata kalla taji sanyi wanda idan bai bi umarnin ta ba ya tabbatar zatayi matuqar baqin ciki shi kuma baya da burin da ya wuce ya ganta cikin farin ciki ko yaushe.
A hankali ya kwanta kan laps in ta tare da fashe mata da kuka ta d'ago shi sae share masa hawaye take tana fad'in "haba waheed kaifa namiji ne bai kamata ace kanayin kuka da hawaye irin haka ba komai na duniyar nn haquri akeyi ba kuka ba kaji yi haquri.
Yace"Dole inyi kuka mami dmn fatima ta cuce ni bata kyauta min ba meyasa zata min haka bayan tasan irin qaunar da nake mata.
Cike da tausayi Mami ta maida shi kan laps d'in ta ta kwantar sae shafa kansa take tana rarrashin sa.
6angaren su bintu kuwa washe gari da safe umma ta tashi bintu tayi sallah,bintu ta tashi taje bathroom bata wani jima ba ta fito tazo tayi zaune qasa gefen gado ta had'e kai da guiwa.
Umma da ta sallame sallah tace" zo nn bintu"
Bintu tazo jiki sanyaye kmr wata mara lafiya ta zauna kusa da umma wacce ke kallonta da kulawa tace"gaya min gskyr abinda ke damunki dmn bazai yiyu ace damuwar tafiyar waheed kad'ai ce ke damunki da har kika kasa yin baccin kirki.
Bintu tace" ba komai umma"
Umma dake kallonta muryar ta natse tace"bintu duk wanda ya kalle ki lokaci d'aya yasan akwai damuwa a tattare dake,ki gaya min idan har matsala kika samu da waheed inji in sasanta tsakanin ku kafin Abban ki ya dawo ki samu ki koma dan in yazo ya tarar dake a gidan nn zaku kwashi en kallo ne keda shi dmn muddin yaji ba zuwan gidan lafiya ne kikayi ba tofa mai qwatar ki a hannun shi sae Allah kin sanshi sarai soja ne mae baqar zuciya ba sae an gaya miki ba kuma gab yake da dawowa yau ko goben nn.
Shiru bintu tayi haqiqa tafi kowa sanin halin Abbanta shiyasa take matuqar jin tsoran sa dmn kan rashin jinta akwai wani d'an karan duka da ya ta6a yi mata har sae da aka fidda ran zata rayu.
Amma kuma tana jin tsoran snr da umma gaskiyar abinda ke faruwa dan ta tabbatar ba abinda bazae faru ba idan suka ji,Abba zae duke ta dukan tsiya umma kuma zatayi baqin ciki marar misaltuwa.
Tace"Umma bani da wata damuwa kawai ina jin kewar yaya waheed ne kuma baccin da na kasayi ciwon kae ne ya hana min.
Umma ta numfasa tace"to Allah ya sauwaqe tashi kiyi sallah ki sami abinda kika ci sae kisha magani"
A sanyaye tace"Fashin sallah nake umma kuma kaina ya daina min ciwo".
Umma tayi shiru tana kallonta tace"wae bintu har yanzu dae shiru ko 6atan wata"
Bintu ta sadda kanta qasa qwallah cike a idonta.
Umma tayi shiru tana kallon yanda hawaye ke silalowa a hnkli kan kumatun bintu ta fhmci duk tayi mata zancen haifuwar nn sae tayi kuka se taji dama bata d'auko zancen ba sbd bata son bintu tana saka damuwa a ranta.
Ta jata zuwa jikinta cikin rarrashi tana fad'in"ke yarinya ce bintu wacce kwata kwata ko shekara ashirin bakiyi ba har yanzu dan haka ki daina saka damuwa da yawa a ranki haifuwar nn ta Allah ce lokaci ne kawai bai yi ba idan lokaci yayi zaki haifu da yardar Allah kinji ki daina kuka.
Bintu ta gyad'a kanta tare da share hawayen fuskarta sae kuma da saurin ta ta kalli umma tace"umma jiya da nayi bacci baki ga wata takarda dunqule a hannu na ba?
Umma tace"na ganta tana cikin bedside drawer na saka miki"
Ajiyar zuciya bintu ta sauke ta tashi taje ta d'auki takardar ta 6oye a cikin akwatin ta umma dai sae kallonta kawai take tayi bata ce mata komai ba.
Guraren qarfe goma zaune suke suna break fast inda bintu cin abinccin kawae take cikin tunani can muryar ta a sanyaye tace"umma wae su zeenah na gidan nn kuwa naga tun jiya banji alamun su ba ko dan basu san nazo bane"
Umma tace"Ae yanzu su zeenah basa zama gidan nn haya suka kama can kusa da asibitin da suke aiki sae jefi jefi suke shigowa"
Cikin mamaki bintu tace"Haya kuma umma da wane dalilin?
Umma tace"Hm wae yafi masu sauqi ko a qasa sae suje asibiti ba sae sun hau mashin ba.
Amma umma wnn ba hujja bace shi kawai kud'in mashin zae sa abar su su kama haya a matsayin su na en mata kuma iyayen su suna a cikin gari gaskiya hakan bae dace ba kuma ba mutunci bane.
Umma ta nisa tace"ba yanda Abbanki bai yi ba bintu amma fafur iyayen su suka ce su sai dai abinda 'ya'yansu suke so za'ayi,ya kawo na gani ya saka musu,dan haka kema bana son inji kin musu wata magana da sunan shawara dmn bana son anyi ance.
Bintu tace"to"snn tace"yaya Abdallah fa yaushe zae zo?
Baice min ga yaushe ba yadai ce min idan ya sami lokaci zae zo.
Shiru kawai bintu tayi bata ce komai ba tana tunanin lallai idan ya dawo zata gaya mishi matsalar da take ciki ko zata sami mafita dan tasan shi kad'ai ne zae iya fahimtar ta har iya bata shawara.
*Sokoto*
Waheed ne kwance shiru yana jin gabad'aya gidan ya masa fad'i ba dad'i qunci da tunani fal a ransa duk ya rame kmr wanda ya jima kwance yana ciwo.
Doorbell d'inda yaji ne yasa ya tashi sannu a hnkli yaje ya bud'e qofa. maminsa ce ta shigo ya gaida ta suka je suka zauna takai hannun ta kan goshin sa tare da fad'in"ya jikin naka da sauqi koh"
Muryar sa can ciki yace"da sauqi "
tace"to Allah sauwaqe kaci abinci kuwa?
Kae ya gyad'a mata ba dan yaci ba sae dan baya son ta tasa shi gaba kan sae ya ci.
Tace"Alhmdlh zancen auren ka dai yana tafiya dai dai dmn nayima hajiya binta magana kuma ta amince ayi komai a cikin satin nn kmr yanda na buqata snn na gaya musu komai mu zamuyi da kanmu har kayan d'aki dan haka nake son duk wani abu na bintu zan turo a kwashe ae aikata mata komastsanta can bama da buqatar su.
Waheed ya gyad'a mata kae kawai dan ko magana ma baya sonyi
Mami ta numfasa dmn ko kad'an bata son ganin waheed cikin damuwa shiyasa ma take son ayi auren nn da wuri ko zae rage damuwar da yake ciki.
Tace"bari in tafi sauri nake amma dan Allah ka rage damuwar nn kaji"
Still kae ya gyad'a mata ta tashi ta tafi ya d'ago kansa sae kallon hoton su yake shida bintu inda suke sanye da qananun kaya iri d'aya ya goyata a bayan shi suna dariya, ya sauke idon sa a hnkli yasa tafin hannun sa ya share hawayen da suka gangaro kan kumatun sa.
*KEBBI*
Washe gari bintu ce zaune shiru riqe da magani a hannunta tana kallon umma dake harhad'a kayan wanki sae fad'uwar gaba take taji da ta rasa dalili ga kuma kanta dake mata masifar ciwo sbd damuwar da take ciki da kullum qaruwa take jin tana yi.
Umma ta gama had'a kayan wankin tace"bintu kisha magani mana ki kwanta kiyi bacci ko ciwon kan nn zae rage miki ni zan tafi inyi wanki bana son Abbanki ya dawo ya sami kayan dattin nn.
Bintu tace"umma ae naji sauqi bari in wanke miki kayan"
Umma tace"sha magani kawai ki kwanta zan iya da kaina kinji"
Komai bintu bata ce ba ta d'auki koko dake ajiye cikin cup kan bedside drawer tasha magani.
Bata kwanta ba sae kayan wankin da umma ta d'auka taje ta kar6a tace"umma bari in kai miki bana son ki d'auka da kanki".
Umma bata musa mata ba suka fito tsakar gida nn gurin fanfo inda kowa ke wanki bintu ta ajiye wankin dama da akwai kujeru gurin na tsakar gida ta d'aukowa umma ta zauna snn ta d'ebo ruwa a fanfo suka fara wanki umma keyin sa6in farko bintu nayin na biyu ta kuma d'aurewa ta shanya ba don umma taso ba sbd ciwon kan da bintu ke fama dashi amma bintu ta dage kan saita taya ta.
Suna cikin wankin ne suma iyayen su sarah suka d'auko nasu wankin sunayi dan kawai suyi su cika gurin shanya kar umma ta samu yanda take so ba don sunyi niyyar yin wankin ba.
Da bintu har umma ba wanda ya kulasu suna jin su sae fira suke a tsakanin su suna kekkewa da kuma habaice habaicen su da suka saba na neman magana.
Can kowannen su na cikin wankin sa kmr daga sama suka ga mutane sun shigo gidan bako sallama sae jefo kaya suke ta koina.
Cikin tashin hankli umma ke kallon kayan ta sa6ule hannunta daga ruwa kana ta kalli bintu tana fad'in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un! bintu me nake shirin gani kmr kayan d'akin ki!?
Bintu dake riqe da bocket zata je shanyi ta kasa cewa komai sae sake bocket d'in tayi tare da gurfanawa gurin kanta qasa ta saki kuka a hnkli marar sauti hawaye masu zafi suka soma gangarowa kan kumatun ta.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 25_*
Kwatsam sae ga Abban bintu ya shigo gidan sae masifa yake tayi da masu jefo kayan wanda sam bae kula da kayan waye ake jefowa ba yana fad'a ne sbd rashin mutuncin su da ya gani,su kuma gabad'aya take suka shiga taitayin su sbd ganin uniform d'in sojawa dake jikinsa suka daina jefo kayan suka ci gaba da sauke komai yanda ya kamata.
A zuciye Abban bintu ya qaraso ciki yana tambayar kayan waye ake watsi dasu haka daga ina suka fito?
Bintu dake gurfane kan guiwoyinta ta tashi ta tafi da gudu d'aki tana kuka.
Duk zuciyar da Abba ya d'ebo take ya sauko ganin yanda hawaye ke fita a idon umma.
Yace"subhanallah umman abdallah yau ke kike yin kuka lafiya me yake faruwa?
Komai umma bata iya ce masa ba ta tafi d'aki da sauri yabi bayanta.
Suma iyayen su sarah da saurin su suka zo a bakin qofa suka la6e domin jin me yake faruwa.
Umma kuwa da shigar ta d'aki a nn falo ta zauna kan doguwar kujera tasa ha6ar zaninta sae share hawaye take wasu na sake zubowa Abba da ya zauna kusa da ita yace"umman Abdallah gabad'aya kun tashi hankalina ki gaya min me yake faruwa kuke ma kuka dake har bintu?
Umma ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace"ni kaina ban san ainihin abinda yake faruwa ba amma na tabbatar rashin jin mgnr bintu ne yasa ta kashe aurenta ta dawo gashi har kayan d'akinta sun korota dashi wacce tun shekaran jiya da tazo gidan nn da uwar akwati nake tambayar ta gaya min me yake faruwa amma yarinyar nn ta 6oye min wae ba komai ashe ja'irar yarinya aurenta ne ta kashe ta dawo.
Abba ya numfasa yace"bari in kira waheed inji me yake faruwa amma na tabbatar tun da har suka mata haka laifin da ta musu yana da girman gaske.
Ya qarashe mgnr ne tare da ciro wayar sa a aljihu ya kira waheed ya jima sosai yana waya da waheed d'in kana ya kashe waya sae jinjina kansa yake yana fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Umma dake kallon sa ta matsu taji me yake faruwa dan abinda taji kawai shine irin haqurin da waheed keta bawa Abba kan komai bae faru a son ransa ba ba yanda zaiyi ne kawae tunda bintu ta riga ta aikata abinda bazai iya kareta ba.
Abba da gabad'aya ransa ya gama 6aci ya miqe cikin rawar jiki ya zaro qaton belt d'insa ya nufi d'akin umma,umma tayi saurin shan gaban sa tace"ka gaya min me yake faruwa tukun"
Abba yace"ki barni in fara dukan ta tukun dmn abinda ta aikata ko kashe ta zan iya yi yau sbd bata da wani amfani a gare mu ta 6ata mana mutunci mu da sunan mu gabad'aya.
Kafin tayi wani yunquri tuni ya fad'a d'akin ta, bintu dake kwance ruf da ciki kan bed tana rusar kuka sae saukar duka ta fara ji ta koina a jikinta,a gigice ta tashi sae ihu take tana ba Abba haquri,haka umma dake biye dashi sae haquri take bashi kan ya saurara ya gaya mata me yake faruwa tukun amma ina kmr qara tunzurasa suke dan baji ba gani yake dukan bintu tamkar Allah ne ya aiko shi.
Su umman sarah dake nn la6e a bakin qofar falo suka tafa hannayen su sae murna suke yau ga rnr da suke jira tazo.
Da saurin su suka bar gurin ganin yanda bintu ta fito aguje Abba na biye da ita har ta fita wajen gidan,
Abba da ya tsaya a qofar gida ya nunata yace"har abadah kar in sake ganin kinzo ko qofar gidan nn ki tafi duk inda zaki je mu bama da buqatar ki kuma ko a hanya kika ganni ban yafe ba idan kika nuna kin sanni.
Wani irin kuka bintu ta fashe dashi ta zube qasa kan guiwoyin ta sae haquri take bashi bai kulata ba ya juya zae koma cikin gida umma tabi shi sae roqon sa take tana bashi haquri, iyayen su sarah kallon su kawae suke murna fal a ransu ko na munafurcin nn dae su sa baki su bada haquri basuyi ba mazajen su ne keda d'an dama kuma duk basa nn ga Abba fir yaqi saurarar umma shifa lallai sae bintu ta bar gidan.
Bintu kuwa tana can waje qofar gida sae kuka take,
kawae sae ga su sarah napep ta ajiye su wa enda dama iyayen su ne suka kirasu kan suyi sauri suzo suga abinda ke faruwa burin su ya cika.
Bintu na ganin su taje da gudu jikin zeenah tana kuka tana fad'a musu Abba ne yace sae ta bar gida.
Sosai suka nuna alamar tausayi a fuskar su har zeenah ta cire gyalen ta da takalmi taba bintu snn kuma ta bata kud'in mota tace taje sokoto gidan anti Hafsa idan komai ya lafa snn.
Ba yanda bintu ta iya ta kar6i kayan sae kuka take ta shiga napep d'inda ta ajiye su yaja suka tafi zuwa tasha kmr yanda su zeenah suka snr dashi.
Wucewar su keda wuya sae ga umma ta fito a babbarkace gabad'aya ta rasa mafita riqe da hijabin bintu da takalmi da kuma en kud'in mota da ta riqo wacce itama niyyar ta ta tura ta sokoto gurin anti Hafsa kafin ta samu ta shawo kan Abba duk da bata ma ji me bintun ta aikata ba.
Dama su zeenah basu riga sun shiga gida ba suka mata bayanin cewa sun tura ta sokoto gurin anti Hafsa idan komai ya lafa snn.
Nan umma ta d'anji sanyi sanyi a ranta ta koma cikin gida gun Abba taji shin me bintun ta aikata da ya yanke mata wnn irin hukunci haka har yana fad'in bae yafe mata ba idan ta ganshi ko a hanya ta nuna ta san shi.
Umma na wucewa su sarah da zeenah suka tafa hannu irin tafawar da sauti baya fita snn suka shiga cikin gidan sae murna suke a ransu babban burin su a rayuwa ya cika wa enda qarin farin cikin su yanzu sun samu mazajen aure har anyi magana rana kawai ta rage a sa.
Bintu abin tausayi kuka take har ta isa garin sokoto wacce da saukar ta mota sae ga Anti Hafsa tazo d'aukar ta acewar su zeenah ne suka snr da ita halin da ake ciki.
Tun a cikin mota anti Hafsa taso tambayar bintu ainihin me yake faruwa sbd su zeenah basuyi mata wani bayani ba amma ganin yanda bintu ke kuka yasa tayi shiru har suka isa gida.
Da shigar su gidan ilham da Abba da daddy suka zo aguje sae murnar ganin bintu suke wacce bata iya kula su ba sbd halin da take ciki sae Anti Hafsa ce taja hannun ta suka tafi d'aki ta zaunar da ita kan bed snn itama ta zauna tasa hannu tana share mata hawaye tana fad'in"bintu gabad'aya hankalina a tashe yake ki daina kukan nn haka ki gaya min me yake faruwa gashi tun kafin ki iso sae kiran umma nake tayi amma wayarta a kashe bana samu su zeenah kuma basu min wani cikakken bayani ba,
ki gaya min ina so inji me ya faru tsakanin ki da waheed da har kika je gida Abba ya koro ki?
Duk da tana gudun irin 6acin randa Anti hafsa zata shiga bata iya 6oye mata komai ba tayi mata bayanin duk abinda ya faru.
Sosai ran Anti Hafsa ya 6aci wacce cikin fad'a tace"amma sae yau na tabbatar ke qatuwar wawuya ce wlh wacce baki san abinda kikeyi ba kan me zaki nemi shawara a gun su zeenah wa enda ko kad'an kinsan iyayen su basa qaunar mu ta yaya kike tunanin suma da gaske suke qaunar ki har da wani gaya musu banzan ra'ayinki kina biyewa shawarwarin su gamu mu en uwanki na jini muna gari d'aya kin kasa tuntu6ar mu ki sanar damu sbd kinsan ba abin qwarai ne kike shiryawa ba koh,
to ae yanzu sae kije suda suka baki shawara har kika shiga matsalar sae su fidda ki a cikin matsalar tunda su masu qaunar ki ne da suka fi mu.
Daga haka anti Hafsa ta fita rae 6ace ta bar mata d'akin.
Bintu ta kwanta sae kuka take ci gaba dayi shikenan ta aikata kuskuren da har abadah baxa ta ta6a iya gyarawa ba wanda kowa yaji sae yayi tir da abinda ta aikata.
Haka ta yini ita kad'ai a d'akin wacce tun lokacin da anti Hafsa ta fita bata sake dawowa d'akin ba sae ilham ta turo ta kawo mata abinci da ruwa amma ko ruwa bata iya sha ba bare taci abinci.
Da dare guraren bayan isha'i bintu na d'akin su ilham wato d'akin yara,tana zaune kan bed ta had'e kai da guiwa wacce gabad'aya jikinta ya gashe sosai yayi zafi sbd zazza6in da ya mata mugun kamu kan kukan da tasha da kuma rashin cin abinci.
Sae ga Anti Hafsa ta shigo d'akin ita da Abdallah yana janye da akwatin bintu a hannun shi wanda sallamar da yayi ne yasa bintu ta d'ago kanta da sauri jiri na d'ibar ta tazo jikin sa cikin kukanta da baya ko fita sosai.
Cike da tausayi Abdallah yaje da ita kan bed suka zauna anti hafsa ta kar6i akwatin hannun sa takae ta inda ta dace snn itama tazo ta zauna dan magana suke son zasuyi da bintu.
Abdallah ne ya fara magana cikin natsastsiyar muryar sa yace"bintu banji dad'in abinda naji ance kin aikata ba ko kad'an,na kuma yi baqinci sosai musamman da nazo na sami umma har kuka take kan abinda taji kin aikata a bakin Abba wacce ba abinda yafi qona mata irin yanda akace wae sun sa kin auri waheed ne dan dukiyar sa, fisabillillah bintu meyasa kika 6atawa iyayen mu suna gashi gabad'aya anguwar mu kowa yaji abinda ya faru wa enda qalilan ne masu taya mu baqin ciki sauran duk ala gwai suke mana kan irin qarya da gaskiyar da iyayen su sarah suka had'a suna ta yad'awa gida gida sae kace wani abun farin ciki,koda yake su agun su abun farin ciki ne kece dae kika kasa fahimtar cewa ba qaunar ki su sarah keyi ba suna nuna miki so ne kawai a fuska wanda yaci ace kin fahimci haka tun lokacinda suka baki shawara kan abinda duk wani masoyin ki na gaske bazai ta6a baki wnn shawarar ba sae dai ya saki a hanya kan kar ki aikata amma sukace kiyi kika kuma yi and still kina ganin wai su masoyanki ne, me yake damunki ne bintu, ina wayonki ya tafi da har kika bar ra'ayin zuciyar ki yayi tasiri akan ki bayan kinsan ba abune mae kyau zaki aikata ba,abun haushi da takaici wae da kanki kike ta kashe 'ya'yanki na halal kina hana su zowa duniya wae ke baki tashi ba Allah ya miki gaggawa knn koh?
Da saurin ta girgiza kanta cikin dasashiyar muryata da tasha kuka tace"kayi haquri yaya Abdallah wlh ba haka bane rashin wayo ne ya d'ebe ni kuma tun a rnr da na aikata wnn kuskure nazo inayin nadama na kuma d'auki alqawarin bazan qara aikata kuskure irin wnn ba amma ban san ya akayi ba da muka je asibiti Dr Khalid yace wae bayan na zubar da cikin farko ina shan magani dan kawae ko na sami ciki ya zube byn ni a sani na wlh bana shan wani magani.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka
Abdallah yace"bintu idan mu mun yarda cewa baki shan wani magani su baza su yarda ba sbd khalid ne ya duba ki,Khalid kuwa aminin waheed ne sosai da sosai da bazai fad'i abinda bashi bane qarin matsalar kuma maganar da mami tajiyo kan kin auri waheed ne dan dukiyar sa har ma akace dalilin hakane yasa kike zubar da ciki kinga kuwa koda sharri ake miki su baza su iya ganewa ba tunda kin riga kin aikata kuskuren farko wanda da ace baki aikata ba da duk hakan bata faru ba kuma koda ace shi waheed yaqi yarda da zancen cewa kin aure sa dan dukiyar sa ne mami zata yarda sbd soyayyar d'anta qwaya d'aya tal ta rufe mata ido dole tayi duk wani abu na ganin ba'a rabata dashi ba dan haka kar kiga laifin abubuwan da ta aikata a gare ki ke kika ja koma mene ne.
Bintu tace"ae ni yaya banga laifin ta ba sbd duniyar nn komai yardar ka da mutum zae iya cutar da kae akan abun duniya amma ina so ta yarda cewa ni yarda ta da ita ta har abadah ce bazan ta6a iya cutar dasu ba duk abinda sukaji sharri ne kawai ake min kuma na tabbatar ba kowa bane sae su zeenah da suka zo rnr su sukayi koma mene ne sbd da muka dawo asibiti yaya waheed bai gayawa mami ainihin abinda ya faru ba haka nasan Dr khalid haka kawai bazae kirata ya gaya mata ba, da haka nake son dan Allah yaya ka taimaka min kaje ka fahimtar dasu ka kuma basu haquri.
Abdallah ya numfasa yasa hannun sa ya share mata hawaye snn yace"naji zan tafi d'in amma sae kinci abinci kinsha magani dmn jikin nn naki yayi zafi da yawa"
Ba musu ta gyad'a masa kae
Anti Hafsa tace"Allah yasa su yarda su saurare ka"
Yace"amin"
Snn ta fita ta kawo ma bintu abinci abdallah da kanshi yake bata abincin har sae da tace ya isheta ya bata magani tasha snn ya fita.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 26_*
Wanka bintu ta nemi zatayi Anti Hafsa ta shiga bathroom ta had'a mata ruwan d'umi a bahon wanka wacce koda ta fito ta sami bintu ta tu6e tana d'aure da towel,bintu ta shiga bathroom
Anti hafsa kuma ta fita d'akin riqe da plate d'inda bintu taci abinci dashi wanda ke d'auke da sauran ragowar abinci akai.
Bata wani jima sosai a bathroom d'in ba ta fito tayi shirin bacci tazo tayi kwance kan bed sae addu'a take a ranta Allah yasa mami ta saurari Abdallah ta kuma yarda da bayanin da zae yi musu.
Ta jima kwance a gurin tana ta fmn addu'a a ranta can kmr daga sama taji sallama kmr ta waheed da saurin ta ta tashi zaune ga mamakin ta kuwa waheed d'in dae ne shida Abdallah suka shigo ae kuwa bata san lokacin da ta miqe tsaye ba bakinta ya kasa rufuwa sae kallon waheed take wae shi d'in dai ne ko kuwa gizo yake mata gashi sae kallonta yake yana murmushi ya kuma ware mata hannayen sa alamar tazo kmr da tsoro ta girgiza kanta dan gani take in taje 6ace mata zai yi.
Yace"kar ki ji tsoro my lady nine ba gizo nake miki ba zo kinji"
Kuka da dariya ne suka su6uce mata lokaci d'aya sbd farin ciki taje da gudu jikinsa ya rungume ta qam a qirjinsa sae fad'in yake"na yafe miki duk abinda kika min fatima dan Allah kar ki koma tafiya ki barni i cnt be with out u.......firgigit ta tashi daga mafarkin da take sae dube dube take dae dai anti Hafsa ta shigo d'akin ta taso da saurinta tazo gun anti Hafsa tana fad'in"anti Hafsa ina yaya waheed ya tafi yanzun nn shida yaya Abdallah, yanzun nn fa na gansu anti har ya rungume ni a jikinsa sae kawae naga ban ganshi ba ko sun tafi su dawo ne Anti?
Anti Hafsa tace"bintu mafar...bintu tayi saurin girgiza kanta tace"dan Allah kar kice min mafarki nake wlh da idona na gansu anti har ma ya rungume ni a jikin sa yana fad'in ya yafe min duk abinda na mishi.
Anti Hafsa ta sauke numfashi tana kallon ta cike da tausayi taja ta suka je kan bed suka zauna tace"naji ba mafarki kikayi ba amma na tabbatar gizo ya miki dmn Abdallah bai ko dawo ba tun lokacinda ya fita.
Qwallah tap a idon ta tace"Anti wlh ba gizo bane shida kansa ma ya fad'a har yace min inzo na kuma je ya rungume ni ba tare da ya 6ace min ba kawae dai ki ce min sun fita su dawo ko anti.
Anti Hafsa tayi shiru tana kallon ta dmn ta fhmci mafarki dae ne bintu tayi,
yanzu idan Abdallah ya dawo basu saurare sa ba ya knn.
Tana kaiwa nn kuwa sae ga Abdallah ya shigo d'auke da sallama a bakin shi,cikin murna bintu tace"kin gani ko anti na gaya miki ba mafarki bane sun fita ne su dawo may be baki san lokacin da suka shigo bane.
Bata jira me anti Hafsa zata ce ba tazo gun Abdallah da ke tsaye a bakin qofa jiki sanyaye ya kasa qarasa shigowa tace"yaya Abdallah ina kuma yaya waheed ba yanzu kuka shigo tare ba?
Abdallah dake kallon ta qwallah ne ke son ciko masa ido yayi saurin had'iye hawayen yace"mafarki kike yi bintu ni ban dawo ba tun lokacin da na fita se yanzun"
Cikin rashin fahimta tace"nifa yaya banyi bacci ba kwanciya kawai nayi ina jiran dawowar ka sae kawae naji sallamar yaya waheed da farko nayi mamaki ko gizo yake min amma da kanshi ya gazgata min cewa shine.
Abdallah ya numfasa yace"bintu kiyi haquri mafarki ne kikayi inaga bacci ya kwashe ki ne baki sani ba"
Bintu dake kallon sa tayi qasa da idonta hawaye suka silalo a hnkli kan kumatun ta,Allah sarki knn d'an kwanciyar da tayi bacci ya kwashe ta a gurin bata sani ba.
Ta share hawayen snn ta d'ago tace"to yaya da kaje ka same su kayi musu bayani sun kuma fahimce ka ko kuwa?
Abdallah dake kallonta ya qara jin tausayin ta a ranshi sbd ba yanda baiyi ba amma mami taqi ta saurare shi.
Bintu dake kallon sa tace"mami bata saurare ka ba ko yaya?
Yace"A'a ban same su bane sun fita"
Tace"Aa yaya kasani koda ka 6oye damuwa a fuskar ka idanuwan ka baza su 6oye ba,ka gaya min koma mene ne zanyi haquri da qaddarar da ta sameni"
Yace"bintu damuwar da ke idona damuwar da kike ciki ce ke damuna dan haka jeki ki kwanta kiyi bacci kinji"
Tace"to gobe da safe zaka sake komawa gurin su?
Ya gyad'a mata kae qwallah nata son ciko masa ido yana had'iyewa.
Bintu kuwa ba musu taje ta kwanta anti Hafsa tasa mata blanket ta rufa mata jikinta ta kuma kashe mata wutar d'akin snn suka fito falo ita da Abdallah.
Bayan sun zauna Anti Hafsa tace"Abdallah na fahimci kmr ba'ayi nasara ba koh?
Yace"hakane anti ba yanda banyi ba taqi ta saurare ni bare ma taji bayanin da nazo mata dashi dmn ganin take kmr duk yaudara ce kawai so muke muyi galaba akan su.
Anti Hafsa tace"har da waheed d'in bae saurare ka ba ko kuwa?
Gidan waheed na fara zuwa dmn nasan shi mutum ne mae sauqin kae da zae fahimce ni lokaci d'aya amma sae ban same shi ba akace yana gidan mami,sae gashi da naje gidan mami bata saurare ni ba har tana cewa idan ban gaggauta fita gidan ba zata kira min police su tafi dani ba yanda na iya dole na fita gidan ba tare da nako ga waheed ba asalima bai ko san abinda ke faruwa ba.
Anti Hafsa tace"ae ko ka ganshi ba yanda za'ayi tunda mami taqi ta saurare ka amma meyasa ka 6oyewa bintu baka snr da ita gaskiyar abinda ke faruwa ba?
Anti Hafsa banso na 6oye mata ba amma tausayin ta yasa na kasa gaya mata dan nasan idan taji bazata iya yin bacci ba sae dai tayi ta kuka.
Anti Hafsa tace"hakane amma mami ta bani mamaki da lokaci d'aya tayi watsi da duk wata yardar da mutuncin da ke tsakanin mu.
Abdallah yace"ki daina mamakin ta anti Hafsa sanin kanki ne mutanen duniyar nn sun lalace qalilan ne masu aminci sae kiga sbd kud'i uwa zata iya saida d'anta,haka d'a zae iya saida uwar sa koma ya kashe ta da hannun sa to meye abin mamaki dan ta yarda da abinda taji wanda abun yazo a sarqaqe ta yanda dole ta yarda.
Anti Hafsa tace"hkne yanzu gobe da safe me zamu cewa bintu?
Zamu gaya mata gaskiya dan abune da bazai 6oyu ba sae dai tayi haquri da qaddarar da ta same ta.
Anti Hafsa tace to shikenan bari in kawo maka abinci kaci.
I cnt eat any more Anti kawae ki bani ruwan Lipton insha,
nn Anti Hafsa ta tashi ta had'o masa ruwan Lipton ta kawo masa.
Washe gari guraren qarfe goma Anti Hafsa ce riqe da hannun bintu suka je kan dining suka zauna dmn yin break fast Anti Hafsa ta d'auki plate ta fara zubawa bintu arish da soyayyen qwai had'i da plantain.
Bintu tace"Anti ya naga mu biyu kawae zamuyi break fast ina su ilham da Abban su?
Anti Hafsa tace"su ilham na kaisu school Abban su kuma kinsan yanzu Abuja yake aiki sae weekend yake dawowa.
Tace"to yaya Abdallah fa?
Yana BQ na kirashi yanzu nn yace zae zo.
Daga haka bintu tayi shiru bata sake cewa komai ba, jim kad'an Abdallah ya shigo sukayi ina kwana snn ya zauna suka fara break fast.
Suna gamawa Abdallah ya tashi zae fita bintu tace"yaya ya zancen mgnr mu ta zuwa gurin mami ko can ne zaka tafi?
Abdallah yayi shiru bae so ace shi zae gaya mata ba yaso ace anti hafsa ce dan shi baya son ganin yanayin da zata shiga ciki idan taji mami bata saurare sa ba amma ya zama dole ya gaya mata da kanshi.
Bintu dake kallon sa tace"yaya kayi haquri na takuraka koh?
Abdallah ya zauna had'e da riqo hannayen ta yace"ko d'aya baki takurani ba bintu amma ina son kiyi haquri da abinda zaki ji daga bakina jiya da nace miki naje ban same su ba na 6oye miki ne sbd bana son ki kwana cikin damuwa amma gaskiyar magana shine da naje mami bata saurare ni ba asalima ganin take kmr wata yaudara ce naje musu da ita amma kar ki damu wani lokaci zan sake komawa koda Allah zae sa idan naje ta saurare ni.
Qwallah ne suka ciko a idon bintu tace"ba komai yaya nagode qwarai da kulawar ka a kaina"
Daga haka ta tashi da sauri ta bar gurin sbd kukan da take ji sosai.
Anti Hafsa ta tashi zata bita Abdallah yace"Kar ki bita anti Hafsa ki barta tayi kukan ko zata ji sauqin abinda ke ranta"
Anti Hafsa tace"wane kuka ne batayi ba Abdallah tayi kuka tayi kuka har da su zazza6i to kan me za'a barta taci gaba dayin kuka bayan kukan bazae mata maganin damuwar da take ciki ba.
Hakane Anti Hafsa amma idan kin lura kukan nn yazo mata ta yanda bazata iya controlling d'insa ba ki barta kawai tayi ni zan tafi gidan Anti nafee sae na dawo"
Anti Hafsa ta masa a dawo lafiya snn ya fita.
Baifi awa d'aya da fita ba sae gashi ya dawo shida Anti Nafee,Anti Hafsa taja su suka tafi d'akin su ilham gun bintu kmr yanda Abdallah ya buqata sbd birnin kebbi zae koma.
Zaune suka same ta kan bed ta had'e kae da guiwa sallamar su ne yasa ta d'ago kanta a hankli fuskar ta fayau kmr wata mara lafiya ga idanuwan ta da suka kod'e kan kuka,waya riqe a hannunta ta kira umma yafi a qirga amma taqi d'agawa.
Abdallah ya zauna kusa da ita yana kallonta cikin muryar rarrashi yace"bintu ni zan koma birnin kebbi abu d'aya nake so dake shine ki rage damuwar nn da yawan kukan nn kar kije ki jama kanki wani ciwon abinda ya kamace ki shine ki roqi Allah yafiyar abinda kika aikata ki kuma riqa yin addu'a dmn itace waraka akan komai.
Bintu ta share qwallar da suka zubo mata snn tace"hakane yaya zanyi duk abinda kace amma ni nasan rayuwata ta lalace banida wani sauran amfani a duniyar nn na rasa yaya waheed Abba ya koreni umma tana fushi dani yarda da mutuncin da ke tsakanin mu da mami sun watse duk a sanadin abinda na aikata,nn ta fashe da kuka tace"meyasa kuma bazaku fita harakata ba tunda ni wawuya ce bansan abinda nakeyi ba.
Abdallah ya girgiza kansa kmr zae yi kuka yace"ki daina fad'ar haka bintu kuma ki daina kukan nn ko da gaske so kike muma muyi fushi dake mu fita harakar ki gabad'aya"
Da sauri ta girgiza kanta yace"to daina kuka share hawayen nn bana son ganin su"
Ba musu tasa tafin hannu ta share hawayen fuskarta.
Ya tashi riqe da hannun ta suka fito harabar gidan su dukan su sbd tafiyar knn,driver ma sae jiran sa yake su tafi a motar Anti Nafee da tasa akai shi.
Kafin ya shiga mota ya kalli bintu wacce still yana riqe da hannun ta yace"ki kwantar da hankalin ki qanwata inshaa Allah zan shawo kan umma har da Abba kinji"
Gyad'a masa kae tayi tare da masa godiya snn ya shiga mota tare da saurin share hawayen da suka zubo masa kana driver ya tashi mota suka wuce.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 27_*
Snn su kuma suka koma daga ciki inda kae tsaye bintu ta wuce d'akin su ilham, Anti Hafsa da Anti nafee kuwa a nn falo suka zauna.
Anti hafsa ta tashi da niyyar kawo ma Anti nafee ruwa da lemu.
Anti nafee tace"uhm Hafsa zauna kawai ba sae kin kawo min komai ba ni abunda ke damuna kad'ai ya ishe ni wae ace duk shirin nn da su zeenah keyi da bintu tun suna yara zasu iya cutar ta abin ya bani mamaki.
Anti Hafsa tace"hmm kema kina son ki zama irin bintu knn, ae tunda iyayen su basa qaunar mu komai zasu iya yi akan mu"
Haba hafsa fisabilillah ki duba fa tun suna yara tare suka taso komai tare sukeyi cin abinci wanki wanke wanke sharar gida makarantar boko da ta islamiyya duk tare suke zuwa haka idan an aiki wani a cikin su tare suke zuwa snn duk fad'an da bintu take janyowa sune masu shiga mata su kama yaran anguwa su musu dukan tsiya koda kuwa bintu ce mae laifi to ta yaya zanyi tunanin zasu iya cutar da bintu har su bata gurguwar shawara kuma fa tun suna yara suka taso da rashin son abinda iyayen su keyi na rashin kyautawa waenda na d'auka har ransu hakane ba funafurci ba sae dai ko idan iyayen nasu ne suka canza musu ra'ayi daga baya.
Anti Hafsa tace"hm nifa tun suna yara ban yarda dagaske suke son bintu ba duk da basu ta6a nuna mata wani abunda zaisa inga haka ba kawae dai halin iyayen su ne yasa sam ban yarda dasu ba shiyasa na ga wautar bintu da ta biyewa shawarar su na kuma yi mamakin duk ina wayonta ya tafi wacce kan tsananin wayonta ne yasa tun tana er shekara biyu da en watanni aka saka ta school.
Nafee tace"Hafsa ni ban d'auka rashin wayo ne yasa bintu ta aikata haka ba nafi yarda cewa dan tana buqatar zubar da cikin ne ido rufe kuma ko ba haka ba su zeenah sun girme mata wayon su ba d'aya ba snn su kansu haka suka taso da shegen wayo tamkar wasu tom and jerry.
Anti Hafsa tace"To yanzu dae koma mene sun riga sun kaita sun baro sun sakata a matsaloli sun rabata da gidan mijinta su kuma suna batun yin auren su.
Nafee tace"Allah sarki hln saki nawa ne waheed ya mata?
Bata gaya min ba kawae dai tace ya bata takarda.
Anti nafee tace"Allah yasa ba saki uku bane"
Hm nafee ko ba saki uku bane ya za'ayi tunda mami bata ko saurarrar mutane mun fita a ranta gabad'aya ba muda wani sauran mutunci a gurin ta wacce a cikin satin nn ma take shirin kawo ma waheed sabuwar amarya,bintu kuwa ko wani auren tayi ba lalle bane ta iya haifuwa.
Shiru Anti Nafee tayi sae can ta girgiza kanta tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un! haqiqa bintu ta aikata babban kuskure wanda ko kad'an banji dad'in sa ba,ya Allah kasa mufi qarfin zuciyar mu ka kuma kare mu da sharrin maqiya na kusa da na nesa.
Anti Hafsa tace"Amin"
Bari inje inga bintu ina so zanyi magana da ita
Cewar Anti nafee wacce bata jira me anti Hafsa zata ce ba ta tashi ta nufi d'akin da bintu take.
Ta shiga d'akin d'auke da sallama a bakinta ta sami bintu kwance shiru sae yawo take da hannunta a hankali kan bed.
Sae da bintu ta tashi had'e da amsa mata sallama snn Anti nafee taje gab da ita ta zauna ta kama hannunta da kulawa tana kallon ta kafin take cewa"bintu so nake inji saki nawa ne waheed ya miki?
Bintu dake kallon ta ta d'auke idonta tace"kiyi haquri Anti nafee bazan iya gaya miki ba kawae dae ya bani takarda"
Anti nafee tace"ko meyasa ba kya son fad'a?
Kawae dae bana son in fad'a ne.
Anti nafee ta numfasa tace"shike nn bazan matsa miki ba fatana kawai Allah yasa ba saki uku bane dmn burina inga kin koma gidan waheed kuma inshaa Allah zaki koma da yarda Allah komai zae dawo kmr ba'ayi ba.
Anti wnn abu ba abu ne da zae dawo kmr ba'ayi ba na riga na janyowa kaina abinda har mutuwa bazan mantashi ba,Anti ko a mafarki ban ta6a kawo yaya waheed zae yi rayuwa da wata mace bayan ni ba amma gashi a dalilin kuskuren da na aikata zae yi auren sa ya mantani.
Har abada kinsan waheed bazai ta6a iya manta ki ba bintu,dan haka kima daina fad'ar haka.
Anti ko yaya waheed bai manta ni ba zae share dani a rayuwar sa ko dan abinda na masa wanda bae ta6a tsammani ba da har tasa ya furta tsana a gareni.
Bintu addu'a tana maganin komai dan haka kici gaba da yin addu'a kawae da yarda Allah komai zae dawo kmr ba'ayi ba.
Shiru kawae bintu tayi amma ta san ta riga ta cuci rayuwar ta ta janyo ma kanta matsaloli musamman matsalar mahaifar nn da bata san ko nn gaba zata iya haifuwa ba ga waheed auren sa zai yi ya soma hayayyafa abinshi ae dole ya manta ta tunda waheed mutum ne mae matuqar son haifuwa.
Anti nafee da ke kallon ta tace"nasan tunanin ki d'aya shine auren nn da waheed zae yi ,ki tunafa baya son auren nn a tilas zai yi shi.
Anti nasan baya son auren nn amma yaya waheed mutum ne mae son abinda mahaifiyar sa ke so wanda ko kad'an baya son ganin 6acin ranta nasan da sannu soyayyar da yake min zata koma gun wacce zai aura yayinda ta fara haifa masa 'ya'ya soyayya ta zata zamo masa tarihi.
Anti nafee tace"ki daina fad'ar haka bana so a ma daina zancen nn yanzu abinda nake so inji shine tun zuwanki gidan nn su zeenah sun kiraki?
Sun kira ni yafi a qirga amma ban d'aga ba dmn cike nake da mamakin su.
Ae da kin d'aga kiran ko mutuncin en iska kici dmn su san abinda suke shiryawa a 6oye ya bayyana.
Wato anti so nake sae sun zo tukun da akwai abinda na shirya musu.
Au cewa sukayi zasu zo knn?
Eh da suka ga sunyi ta kirana ban d'aga ba sae suka turo min text kan nayi haquri sun san halinda nake ciki bazan iya d'aga waya ba amma kar in damu zasu zo da akwai wata shawarar da suke son zasu bani.
Hm lallai yaran nn so suke suzo su sake guma miki wani knn Allah ya fisu baza su ta6a nasara akan abinda suke so ba en iska.
Shiru kawae bintu tayi bata ce komai ba amma ganin take wace nasara ce kuma basuyi a kanta ba sae dai fatar Allah ya tsare gaba.
Washe gari ne su zeenah suka zo suka sa bintu a d'aki wae su shawara suke bata idan ta amince tazo su koma kebbi can gidan da suka kama haya suci gaba da zama tare zasu smr mata aiki a nn asibitin da suke aiki su riqa zuwa tare tunda Abba dae ya cije kan lallai bazata dawo gida ba.
Bintu dae sae jin su kawai take wato dae sun maida ta wawuya sha ka tafi byn sun saka ta a wnn matsalar so suke su sata a muguwar hanyar da suke ciki in yaso sae ta fand'are tabi duniya.
Tace"hm lallai sae yanzu na qara tabbatar da cewa ba kwa qaunata da gaske,to bari kuji kuda kuka riga kuka bi hanyar lalaci ku zaku ci gaba da lalacewa ni nafi qarfin kuci gaba da sani a matsala wlh Allah bazai barku ba.
Zeenah tace"hm lallai kwanyar ki ta fara ja knn to kema bari kiji har abada munci gaba da saki a matsala knn har sae kin qare rayuwar ki a lalace idan kuma kina ja sae mu gwada muga mu dake waye zae yi nasara.
Bintu tace"uhm ae Allah bazai ta6a bawa azzalumi nasara ba dan haka se kusan irin ramin muguntar da zaku gina dmn kune masu shirin fad'awa tsumbul ba mai fidda ku.
Sarah tace"haba bintu daga shawara shine ke kuma zeenah zaki bar 6acin rae yasa ki biye mata kar fa ki manta bintu mufa en uwanki ne masu qaunar ki da baza mu ta6a iya cutar da ke ba.
Kafin bintu tace komai zeenah tace"sarah lokaci yayi da bintu zata san komu su waye dan haka kima daina wani 6oye mata,bintu kisani tun muna yara mu ba masu qaunar ki bane muna nuna miki qauna a fuskar mu ne kmr yanda iyayen mu suka umar ce mu snn kuma zan gaya miki abinda baki sani ba shine duk cikin da kk samu bayan na farko mune kesa baya zama ta hanyar sa miki magani a ruwan shanki idan kinje hostel gurin mu ko kuma idan munje gidan ki,ke bashi kad'ai ba ma mune muka shirya duk wasu maganganu da komai ta yanda mami in taji kae tsaye zata tsaneki tasa waheed ya sakeki kuma buqatar mu ta biya ko yanzu kasuwa ta watse d'an kola mae rabon ci ya ci.
Bintu ta girgiza kanta cikin jin ciwon abunda suka aikata a gare ta,ta bud'e baki ta fara ci musu mutunci sae abinda ta manta ta zazzage su ta musu tas har iyayen su bata ragawa ba.
Sarah da zeenah ransu yayi matuqar 6aci dan tunda suka zo duniya ba'a ta6a ci musu mutunci irin yanda bintu ta musu d'in nn ba inda cikin zafin nama zeenah ta d'aga hannu zata kaiwa bintu mari bintu ta riqe mata hannu tasa iya qarfinta ta kwad'a mata mari har saida zeenah tayi taga taga zata fad'i,sarah ta kafta wani uban zagi had'e da kukan kura zata ramawa zeenah sae jin saukar marin bintu taji a kuncenta har sae da ta nemi gigicewa kafin suyi wani yunquri dama Anti Hafsa da Anti Nafee a shirye suke suna la6e a bakin qofa suka shigo kowaccen su riqe da makaminta na duka suka taru su duka uku har bintu sae dukan zeenah da sarah suke baji ba gani tamkar Allah ne ya aiko,sae ihu suke suna neman ceto sun kasa qwatar kansu har suka musu zir sae dukan su suke ci gaba dayi ta koina can da qyar da sud'in goshi suka samu suka qwaci kansu suka fita aguje ba tare da sun tsaya d'aukar komai nasu ba sae d'ankwalayyan da suka tsira dasu.
Kuyi haquri da wnn.
0 comments:
Post a Comment