A gidan nn me ya kawo ku to?
D'aya daga cikin su yace"tsohuwar matar waheed wato bintu da aka shaida mana cewa qanwarki ce ita muka zo zamu tafi da ita a bisa mummunan laifin da ta aikata....what! wane laifi ne ta aikata!?
Kallon ta yayi kafin yace komai sae ga bintu tazo muryar ta a sanyaye tana fad'in"Anti lafiya me yake faruwa?
Fuskarta d'auke da rashin fahimta tace"nima bintu bansan me yake faruwa ba wae ke suka zo nema kinyi laifi"
D'auke da mamaki Bintu ta kalle su tace"ni kuma me nayi?
Kallon kin ma raina mu ya mata snn yace"idan munje can kyaji"
kana ya umarci er sandar da take tare dasu kan ta sa mata ankwa su fice.
Anti Hafsa tayi saurin tarewa tana fad'in"Aa dan Allah kuyi haquri kar ku tafi da ita ku gaya mana tukun laifin me akace muku ta aikata"
Nan kai tsaye d'an sandan bai musa mata ba ya mata bayanin laifin da ake tuhumar bintu dashi.
A rud'e anti Hafsa tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!mun shiga uku wlh sharri ake mata ba ita ta aikata ba.
Yayinda Bintu fad'ar yanayin da ta shiga a lokacin abu ne da bazai yiyu ba ta zama kmr wata statue komai nata ya tsaya cak baya motsi sae hawaye dake fita a idonta, shikenan mafarkin ta ya zama gaskiya,gashi kuma anzo ana tuhumar ta wae ita ta aikata,innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahuma ajirni fi musibati wa akhlifni khaira minha.
Ta fad'i hakane a ranta amma a zahiri tana nn still kmr statue wacce tana ji tana gani aka sa mata ankwa suka tafi da ita,Anti Hafsa ta bisu har gate sae kuka take tana roqon suyi haquri kar su tafi da ita wlh sharri ne ba ita ta aikata ba amma ina basu saurare ta ba suka wuce da ita.
Hankali tashe Anti Hafsa ta dawo cikin gida da niyyar taje ta kira Abban ilham a waya ta snr dashi abinda ake ciki sae ga jabir yazo yana tambayar anti lafiya me yake faruwa?
Cikin kuka ta masa bayanin abinda ya faru.
Dafe kansa yayi tare da fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un!kana ya tafi da sauri ya d'auki mashin d'in sa ya fita a cewar zai bisu.
Sosai Anti Hafsa taso su tafi tare amma tuna cewa su ilham na nn basu wuce school ba kuma ba kowa wanda zae kula dasu yasa ta haqura har se ta kai su school snn daga can ta same shi.
Bayan ta same shi a can ba irin magiyar da basuyi wa en sanda ba kan sharri akeyiwa bintu bata aikata laifin da ake tuhumar ta dashi ba,suka nuna sam maganar su ba hujja bace tunda en fashi sun furta da bakin su cewa bintu ce ta tura su dan haka su tafi su basu guri idan har da wanda suke zargin ya mata sharrin suna iya su sashi qara.
Ba yanda suka iya suka baro bintu sae kuka take.
Hakama ma anti Hafsa kuka take har suka zo gida jabir sae rarrashin ta yake yana bata magana wanda shima qarfin haline kawai yake.
Anti Hafsa ta kira Abban ilham ta gaya mishi halinda ake ciki shida yaya Abbas wa enda dukkan su ba qaramin tashin hankali suka shiga da jin zancen ba yayinda yaya Abbas yace da Anti Hafsa kar ta snr da su umma halin da ake ciki tukun ta bari in sun zo zai san abinyi.
6angaren mami kuwa abun ba acewa komai dan bansan ta yanda zan misalta muku tashin hankalin da take ciki ba dmn waheed na can rai ga hannun Allah likitoci bila adadin a kanshi suna bashi taimakon gaggawa.
Husna kuwa koda aka kawo su asibiti abinda ke cikinta kawai aka iya ceto ransa amma ita Allah ya kar6i ranta wacce hajiyar ta tayi kuka sosai da baqin ciki marar misaltuwa yayinda ta qudiri lallai baza a bar bintu ba sae an yanke mata hukunci dai dai da abinda ta aikata.
*Kebbi*
6angaren su zeenah kuwa wa enda musamman jiya a garin sokoto suka kwana sosai sukayi murna da farin ciki amma beauty kam se kuka take sbd halin da taji waheed na ciki wacce su zeenah suka sata a gaba sae rarrashin ta suke kan tayi haquri ta daina kuka.
Tace"haba dan Allah ku barni kawai inyi kuka wlh en fashin nn sun 6ata min rai ashe kwata kwata ma basu san aikin su ba,suda aka ce kar su ta6i lafiyar shi amma shine duk suka hahharbe min shi,shegu en iska naga wanda ze fidda su to.
Zeenah tace"calm down beauty harbin da suka masa duk a qafa ne fa hakan ya nuna da akwai dalili bada niyar kisa suka harbe shi ba.
Hm! zeenah a gaban idona fa asibiti aka wuce dashi duk sunbi sun doddoke shi kanshi se fitar da jini yake taya zaki ce min bada niyyar kisa suka doke sa ba!
Ki fahimce ni beauty ga dukkan alama kokawa ya shiga yi dasu shiyasa suka kai ga ta6a lafiyar sa tunda gashi ogan nasu ya mutu d'ayan kuma yana asibiti.
Duk da haka zeenah wlh duk waheed ya mutu sae na tura har cell an kashe min su da ma wanda ke gadon asibiti dukkan su bazan qyale su ba sae na nuna musu kuskuren su wlh.
Zeenah tace"Aa beauty ki kwantar da hankalin ki da yardar Allah waheed bazai mutu ba kuma ko a birnin sin ne na tabbatar mami zata fitar dashi na ganin cewa ya rayu bai nakasa ba.
Snn ina baki shawara ki janye zancen cewa wae baza ki fidda su ba in kika yi haka sun ga damar su fad'i gaskiyar komai damu harke mu shiga uku, dan haka haquri zakiyi mu cika musu alqawarin da muka musu tunda suma sun cika mana alqawarin mu sa6ani ne kawai da aka samu wanda suma nasan ba haka suka so al'amarin ya kasance ba.
A sanyaye tace"Shikenan naji amma ya zama dole in sake komawa sokoto in ci gaba da zuwa asibiti a matsayin aikina ke kawo ni dmn in riqa sanin halinda waheed yake ciki.
Suka ce shikenan ba matsala.
A nn kai tsaye ta harhad'a kayanta ta shirya ta tafi cikin motar ta sabuwa fil da ta siya a en kwanakin nn.
Bayan ta wuce ne Sarah ke cewa kina ganin dan ta fita harakar su bata fidda su ba za'a iya samun matsala har muma mu shigo ciki kmr yanda naji kince?
Zeenah tace"hm na fad'a ne kawai dmn in nuna mata matsalar ta tamu ce amma mu meye namu a ciki muda rakiyar ta kawae mukayi gurin su sai en shawarwarin da muka basu ta yanda aikin zai yi yanda ake so ba tare da an sami wata matsala ba.
Sarah tace"Gud shiyasa nake sonki yanzu game d'in mu da bintu tazo qarshe we have won,beauty kawai ta rage mana danni na matsu inga dukiyar handsome gabad'aya ta dawo hannun mu.
Zeenah tace"itama kar ki damu nata na zuwa very soon!
A nn sukayi dariya tare da ba juna hannu suka tafa.
*Sokoto*
Su Abbas da Abban ilham suna sauka garin ko gida basu je ba kae tsaye suka wuce police station d'in da aka je da bintu kasancewar Anti Hafsa ta snr dasu.
Koda suka je Abbas yaga ashe d'an sandan da case d'in yake hannu sa abokin sa ne.
Hakan ba qaramin dad'i yayi wa Abbas ba yayinda abokin nasa ko kad'an baiji dad'in da hakan ta faru ga wani nashi da ya sani ba,gashi ba yanda zaiyi ya basu belin bintu kmr yanda suka buqata acewar zasu sa qarar wa enda suke zargi in yaso suci gaba da case d'in can kotu har a biwa bintu haqqinta.
Sosai ya kwantar da kai ta hanyar fahimtar dasu cewa wnn babban case ne da bazai iya bada belin bintu ba amma dai suje su sa qarar wa enda suke zargi tukun.
Duk da basu ji dad'i ba suka ce masa ba komai sun gode amma suna son a fito da bintu su ganta.
Nan yasa aka fito da bintu kmr yanda suka buqata wacce tazo sae kuka take.
Cike da tausayi Abbas ya soma rarrashin ta yana bata magana shida Abban ilham kan ta kwantar da hankalin ta zasu sa su zeenah qara abi mata haqqinta dan sun san ba makawa wnn sharrin su ne.
A nn ta d'an sassauta kukan da take amma da za'a koma da ita sosai ta riqe hannun yaya Abbas cikin kuka bata son komawa wanda cikin rarrashi ya samu da qyar ya sa6ule hannun sa aka koma da ita.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*Aminci writers association*
*_page 38_*
Cikin rashin kuzari suka tafi gida,Abban ilham ne ya fara shiga cikin gidan wanda kai tsaye d'akin Anti Hafsa ya nufa d'auke da sallama a bakin shi.
Anti Hafsa dake zaune gefen gado tallabe da goshinta irin na alamar damuwa,ta d'ago kanta a hnkli tare da amsa masa sallama kana ta taso tazo gunshi jiki sanyaye ta mishi sannu da zuwa.
Ya kama hannunta suka je kan bed suka zauna sae kallon sa take dan ta fahimci da akwai damuwa sosai a tattare dashi kafin tace komai yace"kiyi haquri Hafsa da saukar mu garin nn kai tsaye muka wuce police station amma bamu samu yanda muke so ba.
Anti Hafsa dake kallon shi tace"dama nasan irin wnn babban case da kmr wuya su bada beli"
Tayi mgnr ne cikin muryar kuka har hawaye na sauka akan kumatun ta.
Abban ilham ya tafi da ita a hankli zuwa jikinsa yasa tafin hannun sa yana share mata hawaye yana fad'in"kiyi haquri hafsa komai zae zo da sauqi inshaa Allah dmn inspector d'inda case d'in yake hannu sa abokin Abbas ne wanda ko kad'an baiji dad'in da bazai iya bada belin bintu ba amma dai yace musa qarar wa enda muke zargi tukun.
A hnkli ta d'ago daga jikin sa tace"shikenan yanzu ina ka bar yaya Abbas?
Na barshi a mota yana waya amma ina jin kmr ya shigo.
Tace"to muje kuci abinci sae ayi shawarar yanda za'ayi.
Nan Abban ilham ya tashi suka fito suka samu Abbas zaune kan doguwar kujera yana yiwa jabir bayanin yanda abun ya kasance inda jabir yayi shiru cike da damuwa a nn anti Hafsa keyi wa Abbas sannu da zuwa wanda ya kasa cewa komai sae mgnr belin bintu ya mata kan tayi haquri ga yanda abun ya kasance tace"haka Abban ilham ya snr dani yanzu damuwa ta d'aya shine yanda bintu zata yi ta zama a gurin en sanda har se an gama shari'a.
Abbas dake kallonta yayi shiru wanda yanzu wani irin tausayin bintu yake ji a ransa,kana yace"ki kwantar da hanklin ki bana jin shari'ar nn zata jima tunda kunce da kunnen ku kunji irin mugayen furucin da su zeenah sukayi kan se sunga bayan bintu.
Tace"tabbas nida Nafee munji da kunnen mu wanda a lokacin ne ma muka musu tsinannen duka.
Yace"shikenan zan samu qwararren lauya da zai tsaya mana"
Tace"to yaya su umma fa still baza'a gaya musu ba?
Dole zasu sani Hafsa amma ki bari nida kaina zan gaya musu ta yanda hankalin su bazai tashi sosai ba.
"To"
Cewar anti Hafsa wacce ta nemi da su taso suci abinci.
Bayan sun kammala cin abinci ne Nafee tazo gidan tare da mijinta ya jajanta musu kasantuwar abinda ake ciki snn ya koma.
Anti wlh har kuka nayi a yanayin da naje na sami bintu kafin muzo nn,se dai ince Allah ya isa tsakanin mu dasu zeenah,ba kuma zamu ta6a barin su ba wlh,baqin nufin su akan bintu se ya koma kansu wlh shegu en iska wa enda baza su ta6a ganin manzon rahama ba inshaa Allahu.
Anti Hafsa tace" hm bari kawai ni na matsu inga an fara shari'ar nn dmn ina tsoron kar suzo da wani tuggun kuma"
Anti Hafsa addu'a zamu dage da ita ba dare ba rana sam kada musa wasa,da yardar Allah wnn karon baza suyi nasara ba komai tuggun su kuwa.
Anti Hafsa tace"to Allah ya shige mana gaba yasa ayi shari'ar nn cikin sauqi"
Nafee tace"Amin".
*Kebbi*
Dasu zeenah suka ji ansa qarar su sun d'an girgiza amma daga baya abin se ya basu dariya har su za'a sa qara suda yanzu burin su yana gab da cika na kar6e dukiyar handsome daga beauty,da ko nawane zasu iya zubewa na ganin cewa shari'ar ta daqushe bintu ta dawamma a fursun.
A cewar Sarah,zeenah kuwa tace"ke ni Sarah wlh ko kaf duka dukiyar zata qare a kan case d'in nn bani da baqin ciki dmn nafi buqatar inga bintu ta dawamma a fursun kan dukiyar nn,mu zuba muda su shege ka fasa zamu ga tsakanin 6era da giwa wa zae janye wani.
Sarah ta fashe da dariya tace"inafa kin ta6a ganin inda 6era ma yace zai ja da giwa"
D'auke da dariya Zeenah tace"ah to naga zancen suke so zamu ga ko 6era zae cinye gasar ne oho.
*Sokoto*
Abdallah ne yazo gun bintu tare da jabir wacce tana ganin Abdallah ta nemi tayi kuka Abdallah yayi saurin girgiza kansa alamar a'a dan yasan tana fara kukan bazai iya hana fitowar hawaye a idon sa ba,wanda cike da tausayi ya janyo ta jikinsa yana bata magana cikin rarrashi kan tayi haquri na d'an qanqanin lokaci ne wnn inshaa Allah a cikin kwanakin nn da anyi shari'a komai zai dawo kmr ba'ayi ba.
Ta gyad'a masa kai cikin muryar ta mae cike da jin kuka tace"to yaya,yaya waheed fa ance yana asibiti unconscious"
Yace"ki kwantar da hanklin ki inshaa Allah zai sami lafiya Husnah kuwa da ta rasu Allah yaji qanta yasa aljannah firdausi ce makomar ta.
Bintu tace"Amin" tare da sa hannu ta share hawayen da suka zubo mata dmn har ranta taji zafin mutuwar Husna ba kad'an ba.
Abdallah yasa tafin hannun sa ya qara share mata hawayen snn yace"mu zamu koma anjima Barrister usman Ali zai zo ya d'an tattauna dake kinji"
A hnkli ta gyad'a masa kai ba tare da tace komai ba.
Bayan sun tafi da d'an jimawa se ga barrister Usman Ali yazo d'in kmr yanda Abdallah ya gaya mata.
Da kulawa barrister d'in ke kallonta wanda ya kira sunanta a natse ta amsa mishi snn yace"suna na Barrister Usman Ali nine wanda zae kare ki a zaman kotun da za'ayi ina son ki fad'a min haqiqanin gaskiyar cewa shin kece kika tura wa en nn en fashin dmn su kashe waheed da matar sa Husna?
Bintu ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace"wlh bani na tura su ba sharri ake min na rantse"
Shikenan kar ki damu ki kwantar da hanklin ki ki kuma dage da addu'a dmn kinsan shari'a sa6anin hankali ce.
Muryar ta a sanyaye tace"ina kanyi kuma zan ci gaba"
Yace"to shikenan ina son koda anje gaban kotu kar kiji tsoron komai ki fad'i gaskiyar abinda kika sani kinji.
Gyad'a masa kai tayi tare da share hawayen da suka zubo mata sae ga er sanda tazo ta jata suka koma,Barrister Usman Ali da yabi bintu da kallo ya girgiza kansa d'auke da tausayin ta a ranshi.
*Kotu*
Kowa ya Hallara ba wanda bai zo ba hatta su umma dama iyayen su zeenah kama da mami da kuma hajiyar Husna.
Bayan mai gabatar da case d'inda za'ayi shari'a a kansa ya gabatar ya miqa takardun case d'in zuwa ga alqali snn ya zauna.
Alqali ya umarci Barrister's da su gabatar da kansu.
Barrister Usman Ali ya miqe tare da fad'in "ya mai girma mai shar'ia suna na Barrister Usman Ali nine lauyan da zai kare wacce ake tuhuma da laifi.
Kana d'ayan barristern ya miqe"yace ya mai girma mai shari'a suna na Barrister Abubukar Qasim nine lauyan da zae kare wa enda ake qara.
Bayan sun zauna Barrister Abubukar Qasim ya miqe dmn fara shari'a kmr yanda alqali ya buqata.
Yace"ya mai girma mai shari'a ni a gani na dama kutu bata tsaya wahalar da kanta da sauraren wnn qara ba dmn shaidu da dama sun tabbatar da cewa bintu ce ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi amma tasa qarar wa enda basu ji ba basu gani ba dmn kawai ita ta samu ta ku6utar da kanta.
Muna da hujjoji da zasu tabbatar wa kotu da haka in kotu ta bani dama zan gabatar da hujjojin d'aya bayan d'aya nagode.
Kana ya zauna Barrister Usman Ali ya miqe yace"ya mai girma mai shari'a"ina son tabbatar wa wnn kotu mai adalci cewa bintu baza ta iya aikata laifin da ake tuhumar ta dashi ba dmn a tahiri ko kiyashi bintu bata ta6a kashewa ba bare har ta iya tura en fashi su kashe en Adam ko en Adam d'in ma wae harda mijinta da take mutuqar so sam wnn ba gaskiya bane kuma na tabbatar idan wnn kotu mai adalci taji shaidu da hujjojin mu zata fahimci cewa tabbas ba bintu ce ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi ba sharri ne kawai.
A nn yayi godiya ya zauna.
Alqali yace"Barrister Abubakra ko da akwai tambayoyin da zakayiwa wacce ake tuhuma?
Eh ya mai shari'a.
Nan bintu ta fito wacce kallo d'aya zakayi mata kasan cewa tayi kuka har hawayen ta sun qafe.
Yace"Bintu kowa yasan cewa kin auri waheed ne dan dukiyar sa shiyasa baki ta6a yarda ma kin haifu dashi ba jira kawai kike lokaci yayi ki kawadda shi ki kwashe dukiyar ki gudu sea gashi kafin ki aiwatar da nufin ki asirin ki ya tonu mahaifiyar sa tasa ya sake ki wanda hakan yasa kika ji baqin ciki da takaicin rashin cikar burinki shine dan kar a zargi kece kika bar se da akayi watanni abun ya lafa kika tura en fashi dmn a kashe shi dashi har matar sa dan kawai ki samu ki kwashe dukiyar dmn ki cimma burinki koh.......objection my lord bai kamata Barrister Abubukar ya riqa yanke hukunci haka kai tsaye ba bayan kaine alqalin bashi ba wnn izgilanci ne dan haka aja hankalin Barrister Abubukar ya gyara.
Alqali yace"Barrister Abubukar ka gyara kalaman ka tambayoyi zaka mata ba yanke hukunci ba.
Yace"A gafarce ni ya mai shari'a snn ya maida duban sa gun bintu wacce gabad'aya kalaman sa sun sa ta soma kuka.
Kuyi haquri da wnn Wlh kwana biyun nn ban zauna ba.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 39_*
Yace"Bintu ko zaki iya gaya mana babbar hujjar ki ko ince dalilin ki da yasa kike zargin su zeenah.
Bintu ta share hawayen fuskar ta wacce cikin muryar kuka tace"eh zancen cewa na auri waheed dan dukiyar sa ba gaskiya bane duk sharrin su ne hujja ta ita ce da bakin su suka gaya min haka ba'a gun wani naji ba"
Kina nufin kice duk cikin da kike samu qarya ne knn ba gaskiya ba?
Aa ina samun ciki amma bani ke zubarwa ba na farkon ne kawai nasan nayi kuskuren zubarwa a bisa qaddara da kuma gurguwar shawarar da suka bani.
Yace"Ma'ana bayan na farkon duk cikin da kike samu knn haka kawai kk ganin yana zubewa ba tare da kin san dalili ba?
A gaskiya da farko bansan dalilin zubewar su ba se bayan munje gun doctor ya fad'i dalilin da yasa ciki baya zama jikina sanadiyar shan wasu pills da basa bari ciki ya zauna wanda nayi mamakin haka matuqa dan bansan na ta6a shan wani magani ba sae gashi daga baya su zeenah da kansu suka gaya min suke samin magani a ruwan sha na idan naje school ko kuma sun sameni a gida.
Hm naji amma ya mai girma mai shari'a ina so wnn kotu mai alfarma tayi duban tsanaki ta fahimci cewa zancen nn na bintu ta fad'a ne kawai dmn taji dad'in bakinta ta kuma yiwa kotu yawo da hnkli sbd ba wani wanda zai maka sharri yazo haka kawai da kanshi ya gaya maka,nagode kana ya zauna.
Alqali yace"Barrister Usman ko kana da tambayoyin da zakayi wa wacce ake tuhuma?
Eh ya mai girma mai shari'a ina da tambayoyin da zan mata.
Bintu"kince su zeenah ne da kansu suka gaya miki sune suka miki duk wani qulle qulle shin ko zaki iya gaya mana ta yanda akayi har suka gaya miki?
A nn bintu ta gaya masa zuwan su zeenah gurinta wato nn gidan anti hafsa da duk yanda akayi har suka kai ga gaya mata.
Yace"to ya kika ji a lokacin da suka gaya miki?
Da farko nayi baqin ciki sosai dmn ban ta6a tunanin zasu iya cutar dani ba a matsayin su na en uwana da muka taso tare,amma kuma bnyi mamakin jin haka daga bakin su ba dmn kafin su gaya min na fahimci sune sukayi qulle qullen sbd a lokacin da muka dawo asibiti nida yaya waheed bai gayawa mami gaskiyar abinda ake ciki ba 6oye mata yayi sae gashi daga baya kwatsam mami taji komai byn ba wanda yasan da mgnr se su zeenah kawai da na gayawa wanda a tunani na en uwana ne masu qaunata dagaske da zasu bani kyakkyawar shawara ashe ba haka bane cike suke da mugun nufi akaina.
Yace"to a lokacin da suka gaya miki sune ke miki qulle qullen ke kad'ai ce ba wani wanda yaji?
Anti Hafsa da Anti nafee duk sunji.
A nn ya nemi alqali da ya bashi dama yana son yiwa su Anti Hafsa tambayoyi.
Bayan sun fito d'aya bayan d'aya kowaccen su ta mishi bayanin tabbas da kunnen su sunji lokacin da su zeenah ke fad'a ma bintu irin sharrin duk da suka qulla mata har ma daga baya suka fad'i mugayen kalamai akan se sunga bayan bintu.
Bayan sun koma sun zauna Barrister Abubukar ya nemi kotu ta bashi dama yana son yiwa wa enda ake zargi tambayoyi.
Alqali yace"kotu ta baka dama"
Bayan su zeenah sun fito d'aya bayan d'aya ya tambaye su shin ko da gaske ne abinda bintu ta fad'a hakane?
Suka ce sam ba gaskiya bane su kam basu ta6a bata muguwar shawara ba asalima cikin farko da zata zubar ba irin yanda basuyi ba kan kar ta zubar amma fafau tace ita bata shiryi kar6ar cikin ba se ta zubar.
Nan ya basu damar su koma su zauna.
Barrister Usman Ali ya nemi yana son zai yiwa mami tambaya.
Alqali ya bashi dama mami ta fito yace"mami shin ko zaki iya gaya mana a bakin wa kikaji cewa bintu ta auri waheed ne dan dukiyar sa?
Mami tace"naji mgnr ne a bakin mai aikina hajjo.
Nan Barrister Usman Ali ya kira Hajjo da izinin alqali.
Bayan mami ta koma hajjo ta fito yace"Hajjo shin ko zaki iya gaya mana ke kuma a bakin wa kika ji mgnr"
Eh nazo zan shiga gida se naji mgnr a bakin wasu en mata da suka zo a kusa da gidan da nake aiki suna kallon gidan suna magana cikin jimamin abunda ya faru.
Yace"to hajjo shin ko zaki iya gane fuskokin wa en nn en matan ko kuwa?
Eh to a gaskiya duk da rnr ne na fara ganin su bazan manta fuskokin su ba dmn na jima ina kallon su ina sauraren abunda suke fad'a.
Yace "knn yanzu idan nace muje ko'a ina ne zaki iya gano min su?
Ae ba se ma anje koina ba suna nn cikin kotun nn wato wa en nn en matan da ake zargi tabbas ba makawa sune ba wasu ba.
A nn ya numfasa d'auke da alamar murmushi a fuskar sa yace"ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta sake bani dama in yiwa d'aya daga cikin en matan tambayoyi.
Nan Alqali ya bashi dama hajjo ta koma zeenah ta fito wacce gaban ta se dukan uku uku yake ganin asirin su na neman tonuwa.
Yace"zeenah kunce duk abinda bintu ta fad'a ba gaskiya bane, mgnr hajjo kuma fa ko shima qarya ne bata kangu ba?
Ae kam qarya ne yaxa ace sau d'aya da ganin mutum bata san shi ba bata ta6a ganin shi ba amma tace wai zata iya gane shi da akwai dai wa enda ta gani bamu ba.
Kuna nufin kuce baku kad'ai ne bintu ta gaya ma halinda take ciki ba da akwai wa enda ta gayawa bayan ku?
Oho mu dai ta gaya mana kuma mun riqe mata sirrin bamu san mun gayawa wani ba.
D'an shu'umin murmushi Barrister Usman Ali yayi wanda qyar idon sa akanta yace"idan gaskiya kika fad'a meyasa to gabad'aya kin tsorata se zufa ke karyo miki har muryar ki na rawa alamar duk jikin ki ma rawa yake....objection my lord bai kamata ace Barrister Usman Ali yana mata irin tambayoyin nn ba! kuma ae gaskiya ta fad'a bazai yiyu ace kaga mutun sau d'aya tak kuma da jimawa snn kace in ka ganshi zaka sake gane shi,sam wnn ba gaskiya bane ya mai girma mai shari'a,
kuma ina son wnn kotu mai alfarma ta d'aga wnn shari'ar har izuwa wani lokaci dmn mu samu damar qara yin bincike dmn gano gaskiyar al'amarin.
Alqali yace"shikenan Barrister Usman ko akwai abinda zaka ce?
Eh ya mai shari'a ina son wnn kotu mai alfarma ta taimaka ta bani belin bintu.
Kotu ta baka belin bintu amma da sharad'in en sanda zasu kasance tare da ita har zuwa lokacin da za'a sake wani zama wato nn da bayan mako biyu masu zuwa.
Cikin girmamawa ya d'an russunadda kanshi yace"Nagode ya mai shari'a"
Ana fitowa bintu tazo jikin umma ta rungume ta sosai sae kuka take tana fad'in"Dan Allah umma kuyi haquri ku daina fushi dani ku yafe min wlh yafiyar ku kad'ai zata sa nayi nasara akan komai umma.
Umma da gabad'aya tausayin er tata take ji tace"ba komai bintu na yafe miki kije ki roqi Abbanki shima"
Bintu ta kalli Abban nata dake tsaye yana kallon su tayi tsaye sae kallon sa take cike da fargabar yanda zata je ta same shi ko ya zai kar6e ta.
Abban nata dake kallonta da kanshi ya mata alamar tazo,ba musu taje gareshi ta tafi a hnkli zuwa jikinsa tana bashi haquri.
Komai baice ba sae shafa gadon bayanta da yayi a hnkli alamar ba komai ya wuce sbd yana cikin yanayin da baya son cewa komai dan gabad'aya al'amuran su zeenah sun matuqar d'aure masa kai,dan kwata kwata baisan da sa hannun su ne abubuwan nn keta faruwa ba sae karon nn umma ta gaya masa komai.
Kana ya d'agota daga kan jikinsa tare da sa tafin hannun sa ya share mata hawaye snn yace"ki dage da addu'a kinji mu zamu koma"
Ta gyad'a kanta tare da fad'in"nagode Abba"
Duk abin nn da yake faruwa su zeenah na tsaye suna hango su baqin ciki kmr zae kashe su wa enda suna fitowa beauty ta wuce da sauri ta barsu sbd uzurin gaggawa da ya kamata na zuwa asibiti.
Takaici yasa suka kama hanya dmn barin gurin suna tafe sarah ke fad'in"Nifa zeenah nayi mamakin da kae tsaye alqali ya bada belin bintu bayan laifin da ake tuhumar ta dashi babban laifi ne.
Zeenah tace"Hm! ni bada belin ta sam bai dameni ba Barrister Usman d'in nn ne matsala ta dan na fahimci ya cika qwalailai cewa da saurin gano yanayin da mutum yake ciki.
Sarah tace"ki cire duk wani tsoro da damuwa zeenah, indai Barrister Abubukar Qasim ne ba kad'an ba yasan aikin sa yanda muke son shari'ar nn ta kasance ba makawa haka za'ayi ba tare da an sami matsala ba,yanzu muna fitowa ma ya turo min text a waya yace mu same shi guest house d'inshi da akwai magana.
Zeenah tace"ok da akwai ma wata idea da ta fad'o min akai yanzun nn matso kiji in gaya miki shima in munje sae mu gaya mishi ko idean tawa zata qara taimakawa.
Nan zeenah takai bakinta kunnen Sarah ta gayawa sarah magana,take Sarah ta bata hannu suka tafa had'e da fad'in"wuhuu! ai wlh zeenah wnn idea tayi ta koina ma mun gama lallata shari'ar nn amma muje muji me Barrister zae ce tukun daga can se mu wuce gun beauty.
Bayan su umma sun wuce tare da Abdallah dake driving d'insu.
Abbas yaje ya sami abokin sa inspector yana gode masa kan belin bintu da aka bada.
Yace"ba komai kasan halin kawun nawa (cewa da Alqali)da qyar wlh na samu ya yarda zai bada belin ta dmn ko kad'an baya son wata matsala ta shigo idan yana yin shari'a komai yafi son yayi shi kan gaskiya shiyasa nace ku kwantar da hankalin ku indai har bintu nada gaskiya to ba makawa se gaskiyar ta fita bare barrister Usman yasan aikin sa sosai.
Abbas yace hakane kam nagode sosai mu zamu tafi kaga en sandan da kawun naka ya had'a mu dasu sae jiran mu suke.
Er dariya inspector yayi yace"kuyi haquri fa da tsarin kawun nawa"
Yace"ah haba ba komai ae tamkar escort ne a gare mu dan koda wa en can en iskan yaran nada niyyar wata mugunta wa bintu an toshe musu hanya ba suda yanda zasuyi sae da nace Allah ya tsare kowa da sharrin su yasa a kammala shari'ar nn lafiya.
Inspector yace"Amin"
Nan sukayi sallama inspector ya wuce shima Abbas ya tafi suka wuce gida.
*Asibiti*
Mami ce zaune a gaban waheed kansa da qafar sa ta hagu duk bandage ne wanda kwata kwata bai san inda yake ba ya shiga coma.
Tayi shiru se kallon sa take amma tunanin ta yana kan abubuwan da suka faru kotu kan shaidar da Hajjo ta bayar wacce da fitowar su court ta tambaye Hajjo wae gaskiya ne abinda ta fad'a ko tausayin bintu ne yasa ta fad'i haka?
Hajjo ta rantse mata tace wlh Allah Hajiya kan gaskiya ta sune na gani suna wnn zancen.
Tun daga lokacin mami ta qara shiga tunani har suka zo asibiti ta kasa dainawa.
6angaren bintu kuwa itama zaune take shiru a d'aki ita kad'ai dan en sanda basu wani takurata ba a iya gate sukayi zaman su.
Ga abinci a gabanta ta kasa ci tunanin ta wane hali waheed yake ciki ya farfad'o ko kuwa.
Anti Hafsa ce tazo ta same ta a haka,ta zauna cikin lallami da rarrashi har ta samu taci abincin.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 40&41_*
1 Week later
Har yanzu dai su zeenah basu samu sun kar6e dukiyar handsome daga gun beauty ba sbd sunyi iya nasu wayon sun kasa amma ko yaushe suka zauna sae qara tsara yanda zasu kar6e dukiyar suke kafin a sake wani zama a kotu.
Wannan karon duk tsare tsaren su yana kunnen beauty kasancewar tana la6e a bakin qofa tana jinsu ba tare da sun sani ba wacce sae da ta gama sauraren su kaf snn ta shigo da sakin fuska kmr ba abinda taji.
Haka suma da sakin fuska suka tarbe ta suna mata ya hanya dan isowar ta kenan ta fito daga sokoto.
Bayan ta zauna suke tambayar ta ya mai jiki
tace"to da dama dama za'ace dan har yanzu yana nn kmr wani gawa bai farfad'o ba amma yana samun kulawa sosai dan ko qasar waje albarka likitocin sun san aikin sosai.
Sukace to Allah ya bashi lafiya ya nuna mana kun angwance.
Er dariya tayi tare da fad'in amin.
A ranta kuma mamakin su take yanzun nn ta gama jin mugun nufin su akanta na yanda zasu tura mata mugaye su kar6e dukiyar handsome daga gare ta koma ta kashe ta ne su kashe ta a dai samu dukiyar ta fito amma se gashi a zahiri suna nuna mata tamkar ba wani abu a ransu lallai zata nuna musu ko gaba da gabanta.
Zeenah tace"beauty ya mgnr mu ta zuwa gurin wnn hatsabibin bokan da kika ce kinji labarin aikinsa tamkar yanka wuqa yau zamu tafi qauyen ko sae gobe?
Beauty wacce dama abinda ya kawota knn suje wnn qauyen,
tayi shiru kmr baza tayi magana ba can ta numfasa tare da fad'in"zeenah nayi tunani da mun bar zancen zuwa gurin bokan nn dmn bana jin yanda mutanen nn suke tsaye da kansu boka zai iya convincing Alqali ya yanke hukunci dai dai yanda muke so ba tare da an tsaya wata doguwar shar'ia ba.
Zeenah tace"amma beauty kince fa bokan nn ya shahara gagarumin matsafi ne ba wani aiki da yake masa wahala kawai ya mana convincing kowa mana ta yanda idan an yankewa bintu hukunci ba wanda zai iya musawa bare suce zasu d'aga qarar izuwa wata kotu snn asa kowa ya fita harakarta su manta ta gabad'aya a rayuwar su kmr ma ba a ta6a yinta a duniya nn ba.
Beauty dake sauraren ta tasan a yanda taji labarin bokan ba makawa zae iya yin duk yanda zeenah ta tsara.
Amma bazata yarda ayi aikin ba so take ta musu muguntar da har su mutu baza su manta ta ba,ta girgiza kanta tare da fad'in"zeenah ba wai naqi bane ina son ki fahimci cewa mutanen nn su bintu tsaye suke ko yaushe cikin addu'a shiyasa nace miki kawai a bar zancen zuwa gurin boka ko yanda Barrister Abubukar qasim ya tsara yayi ba sae anyi wani abun nn ba ko kuna tantamar kmr bazai iya ba?
Aa we trust him yana da ilimin da zai iya yin komai yanda ya tsara, kawai cece kuncen da akeyi a kotu ne yake d'an bani tsoro dan naga Barrister Usman Ali d'in nn da gaske yake son ganin ya qwatarwa bintu haqqinta.
No kar ki damu ki cire duk wani tsoro a ranki ba abinda zai hana muyi nasara akan shari'ar nn.
Tace"ok to zakiyi kwana nawa a nn kafin ki koma sokoto?
Eh to gaskiya bazan koma ba sae a daren da za'a sake wani zama a kotu sae mu had'u daku a washe gari ko zamu tafi tare da kune gabad'aya?
Zeenah tayi saurin cewa"A'a kije kawai zamu zo daga baya"
Beauty tace"ok to ni zan fita da akwai inda nake son inje"
Zeenah tace"baxa kici abinci ba kafin ki fita?
Aa sae na dawo tukun daga haka ta tashi ta fita ba tare da ta jira me zasu ce ba.
Kmr jira sarah keyi tace"zeenah kinji ta wae sae daren da za'a sake wani zama zata koma ya za'ayi knn muda keson komai ya kammala kafin lokacin?
Zeenah tace"kar ki damu indai har zata koma a rnr ba matsala komai zaiyi yanda muke so kafin washe gari, Barrister kuma ko bayan an gama shari'ar ne se mu cika masa kud'in aikin sa gabad'aya.
Sarah tace"olryt shikenan"
Beauty da ke la6e a bakin qofa bata riga ta wuce ba ta girgiza kanta d'auke da shu'umin murmushi snn tabar gurin wacce da gangan tace har se daren da za'a sake wani zama zata koma sbd tarkon da take shirin had'a musu.
Ranar da beauty zata koma sokoto da wuri ta koma sbd so take ta kammala duk wani tarkon da take shirin had'awa su zeenah ba tare da an sami matsala ba kafin gobe.
6angaren su zeenah kuwa suma sun kitse magana da wa end zasu kwato musu dukiyar handsome gun beauty sun musu misalin gidanta da ta siya a nn sokoto da yanda zasu shiga gidan a sauqaqe duk sun musu bayani dare kawai suke jiran yayi su kai mata farmaki.
Washe gari ne za'a sake wani zaman kowa ya hallara a kotu an kammala duk wani abu da ya kamata ayi kafin a fara shari'a.
Barrister Usman Ali ne ya fara magana acewar yana son kotu ta bashi dama yana son zai yi tambaya wa en fashi.
Alqali yace kotu ta baka dama.
Bayan sun fito barrister Usman Ali ke cewa bincike ya nuna cewa a lokacin da en sanda suka tuhume ku sam baku tsaya wani kwana kwana ko ja'in ja na qin fad'a ba,kai tsaye kuka fad'i cewa bintu ce ta tura ku hakan ya nuna cewa ba makawa sharri ne wato sa akayi ku fad'i cewa ita ta tura ku dan haka kotu na buqatar kuyi mata bayanin gaskiyar wanda ya tura ku ba tare da kun wahaladda shar'ia ba.
Shiru sukayi wa enda basa jin zasu iya yiwa beauty rashin alqawarin da suka d'aukar mata jiya da dare da taje gurinsu cikin 6adda kama izuwa namiji wacce da zuwanta takarda kawai ta miqa musu ta wuce yayinda takardar ke kunshe da tsarin yanda take son su fad'a idan an tambaye su a kotu gaskiyar wanda ya tura su.
Basu tsaya wahaladda shar'ia ba kmr yanda Barrister Usman Ali ya buqata suka fad'i cewa gaskiyar wa enda suka tura su sune wa enda ake zargi wato su zeenah.
Bansan ta yanda zan gaya muku irin razanar da su zeenah sukayi ba wa enda suka miqe tsaye zumbur cikin tsananin tashin hankali kafin su iya cewa komai,kae tsaye sae ga beauty ta shigo wacce cikin muryar kuka tace"tabbas hakane ya mai girma mai shari'a,ni shaida ce akan abinda suka fad'a sam bintu bata da laifi ko d'aya a kan laifin da ake tuhumar ta dashi kuma duk abunda bintu ta fad'a a gaban kotu su zeenah sun mata gaskiya ne sun qaryata ta ne kawai dmn su cimma burin su na ganin cewa bintu ta qare rayuwar ta a lalace,amma ina son kotu ta bani dama in qara mata gamsasshen bayani.
Alqali ya jinjina kansa tare da fad'in kotu ta baki dama.
Nan beauty taje ta tsaya gaban a kotu(bar).
Wacce sae da ta fad'i ainihin sunan ta snn ta fara bayanin cewa ni qawar su zeenah ce sosai na yarda dasu na basu amana da duk wani sirrina bana iya 6oye musu haka suma wasu abubuwan su duk basa 6oye min har ma abinda suke son aikatawa ga wanda suke hassada suna gaya min,amma kasancewar ko kad'an bana son halin nn nasu na kan zauna na basu magana kan suji tsoron Allah abinda sukeyi su daina ba kyau, amma sam basa jin shawara ta har ya kasance ma sun daina gaya min, ni kuma se na d'auka ko sunji shawara ta ne ashe ba haka bane suna nn hassadar su se qaruwa take kan duk wanda suka ga cewa yafi su da wani abu ko jin dad'in rayuwa se sunyi duk yanda zasuyi suga cewa rayuwar ta lalacewa mutum ya daina jin dad'in ta kwata kwata komai shaquwar su dashi kuwa,mutane sun fi aqirga wa enda suka cutar suka raba su da duk wani farin cikin su,sae dai na bintu nn duk yafi muni dmn sun jima suna son ganin cewa rayuwarta ta ta6ar6are amma burin su ya kasa cika a lokacin da suke so, shine suka qulla mata wnn sharrin na ganin cewa sun gama da ita har abada a manta da wacece ita kwata kwata har iyayen ta ma su manta ta,yayinda ni kuma zan zamo next target d'insu dmn sunga alamun na fara wuce su.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka.
Barrister Abubukar qasim da duk ko'inan sa zufa se karyo masa take yayi qarfin halin cewa"zainab ta yaya akayi kika san komai bayan da kanki yanzun nn kince tuni sun daina gaya miki duk wani tsaren tsaren su hakan na nuna kin shirga qarya ne dmn kiyiwa kotu yawo da hankali koh"
Cikin kuka Beauty ta girgiza kanta tare da fad'in"ko d'aya bana da nufin nayiwa kotu yawo da hankali sae dai na gaya mata gaskiyar abinda yake faruwa.
Alqali yace"ci gaba da bayanin ki, kotu na sauraren ki gaya mana yanda akayi kika san komai"
Tace"naji komai ne a lokacinda nazo zan shiga d'aki yayinda isowa ta knn na fito daga sokoto naje Kebbi.
Ban riga na shiga d'akin ba naji suna magana cikin murna da farin ciki kan irin nasarar da sukayi a rayuwa, suna labarin duk wanda suka cutar da irin nasarar da sukayi akansa har suka zo gun bintu ina jin duk wani bayanin cutar da ita da sukayi da kuma zancen cewa ta auri waheed dan dukiyar sa ne, duk su suka qulla har en fashin da suka kashe Husna duk su suka tura a kashe ta kuma da sanin su suka kira police su kama en fashin dan kawai idan an tuhume su suce bintu ce ta tura su wa enda en fashin sun yarda da haka ne a bisa alqawarin da suka d'aukar musu na cewa zasu fitar dasu kuma ko nawa suke so zasu basu bayan sun fitar dasu.
Basu san ina nn ina sauraren su ba suka ci gaba da bayanin yanda suke son shari'ar nn ta kasance wato zasu je gun wani shaharraren bokan su da ya saba musu aiki ya musu convincing kowa har Alqali dmn ya yankewa bintu hukunci yanda suke so wato d'aurin rai da rai a gidan kaso ba tare da kowa ya iya musawa ba haka kuma kowa ya manta ta gabad'aya tamkar ma ba'a ta6a yin ta a duniyar nn ba,bansan lokacinda kuka ya qwace min ba sbd tausayin bintu da naji,nayi saurin hana fitowar sautin kukan nawa sbd maganata da naji sun d'auko acewar idan sun gama da bintu nice next target d'insu na ganin cewa sun qwace min dukiyar da iyayena suka mutu suka bar min.
Nan kawai na shiga d'akin ba tare da nayi wani tunani ko shawara ba wa enda suna gani na suka san cewa na gama jin komai, amma sam basu damu da hakan ba hankalin su a kwance suke kallona,ban nemi nayi fad'a dasu ko wani abu ba sae ma roqon su da nayi da su tausaya su janye qudurin su a kan bintu ko dan kasancewar ta er uwa a gare su,snn ni kuma ko nawa suke so a dukiya ta su fad'a nayi alqawarin zan basu.
Fafau suka ce ban isa na hana su abinda sukayi niyya ba,ganin haka yasa nace muddin basu janye qudirin su a kan bintu ba tofa lallai zan toni asirin su,suka ce tabbas baza su fasa abinda sukayi niyya ba kuma muddin na toni asirin su sae sun sa an kashe ni,nace sae dai su sa a kashe ni, idan baza su fasa ba nima bazan fasa ba.
Har abun ya zamo mukayi fad'a kaca kaca dasu,na dawowa ta sokoto na kasa zama na kasa tsayi cike da tunanin lallai tunda suka furta zasu sa a kashe ni ba qaramin aikin su bane zasu iya turawo a kashe ni da dare kar washe gari na toni asirin su a kotu nn na yanke shawarar kiran en sanda dmn suzo su bani taimako,hakan kuwa da nayi shi ya taimake ni dmn a cikin dare sae ga qarti kusan su uku sun zo kashe ni ba tare da sun san da akwai en sanda a gidan ba,kafin su min komai en sanda suka zo suka kama su,suka kuma sa su kira su zeenah su gaya musu cewa sun kammala aikin su da suka sasu gobe da safe idan an gama shari'a zasu had'u,shiyasa su zeenah sam basu tashi hankalin su ba suka zo kotu cike da murnar burin su zae gama cika.
A nn ta kawo qarshen zancen ta tare da fad'in idan kotu na son tabbatar da cewa abinda na fad'a gaskiya ne a shirye nake da nasa police su shigo da wa en nn qartin.
Nan kotu ta buqaci ganin su sae gashi kuwa en sanda sun shigo dasu d'aya bayan d'aya tare da inspector Bashir wato abokin Abbas hakan yasa Alqali ya qara tabbatar da zancen beauty gaskiya ne dan yasan inspector bashir mutum ne mai gaskiya babu wani cin hancin da ke tsone masa ido.
Babu wani 6ata lokaci Alqali ya yankewa su zeenah hukuncin d'aurin rai da rai a gidan kaso snn kuma za'a cisu tarar naiar dubi d'ari biyar dmn bintu ta magance matsalar mahaifar ta da suka so hallakawa da gangan.
en fashi kuma hukuncin kisa aka yanke musu ta hanyar rataya haka suma wa en nn qartin ba'a barsu ba aka yanke musu nasu hukunci.
D'auke da murna beauty ke kallon su zeenah wa enda tun lokacinda ta shigo ta fara bayani ita kawai suke kallo hawaye wani na bin wani a idon su, cikin tsananin rud'u da tashin hankali na jin yanda duk tabi ta lauye su ta d'aura duk wani laifi akan su da wanda sukayi da ma wanda basuyi ba.
Suna ji suna gani en sanda suka sa musu ankwa suka tafi dasu iyayen su kmr wasu zautacci suka bi en sandan sae kuka suke suna basu haquri.
En fashi kuwa da za'a wuce dasu kallon beauty sukayi wacce a kafaice ta musu signal kan su kwantar da hankalin su zata fitar dasu kafin a yanke musu hukunci wacce a ranta sam ba haka bane sun mata ganin qarshe knn ba wani fidda su da zatayi idan buqatar en fashi ta taso mata ta nemi wasu dan har yanzu haushin su take ji kan abinda sukayiwa waheed.
6angaren Bintu kuwa farin ciki fal taji a ranta wacce taje cikin kukan farin ciki tana godewa beauty.
cikin sakin fuska beauty ta kama hannyen Bintu tana fad'in ba komai ae yiwa kaine.
A hnkli Bintu ta sa6ule hannayen ta daga riqon da beauty ta mata tana kallon mami da ta qaraso gurin tana kallon ta wacce a hnkli ta ware hannayen ta cikin kuka tana son bintu tazo gareta,hawaye ne suka silalowa bintu a hnkli,ba tare da ta musa ba taje jikin mami wacce ta rungume ta sae haquri take bata kan yarda da abubuwan da taji bayan ta fi kowa sanin irin son da take yiwa waheed,komai bintu bata iya cewa ba sae haquri itama take ba mami kan zubar da cikin farko da tayi bayan tasan waheed ne kad'ai d'anta da take matuqar son ganin jika daga gare shi da shima yake matuqar son haifuwa amma bata dubi hkn ba tabi son zuciya da rud'in su zeenah.
Mami ta d'agota tana share mata hawaye cikin nuna cewa ba komai ae kuskurene na yarinta kana taja hannun ta suka je gun su umma dasu Abba dake tsaye suna kallon su,farin ciki fal a ran kowannen su na yanda shar'iar nn ta kasance.
Cike da nuna rashin jin dad'in abinda mami ta aikata a gare su ta basu haquri suka nuna ae ba komai komai ya wuce asalima su basu ga wani laifinta ba tunda ga yanda abun ya kasance,mami tace duk da haka dai bata kyauta ba suyi haquri suka ce ba komai wlh sun haqura.
Nan suka d'unguma su dukan su gabad'aya zuwa asibiti dmn dubo waheed.
Beauty kuwa gida ta wuce kai tsaye wacce da isar ta motar Barrister Abubukar ta fara cin karo da ita yana tsaye jikin motar tasa yana jiran isowar ta.
D'an shu'umin murmushi ta saki snn ta fito daga cikin mota taje gab dashi tana masa wani kallo kana tace"me kuma ya kawo ka ko kaima so kake in toni asirin ka a yanke ma naka hukunci?
Barrister dake kallonta yace"haba beauty me yayi zafi da zakiyi wa su zeenah haka bayan naga kanku a had'e yake.
Su suka ware ni suna son cutar dani shiyasa na musu haka.
Me suka miki?
Wannan ba damuwar ka bace kuma ina son ka sani kaima ba wai nabar ka bane,dan ina son kamin wani aiki ne yasa ban tona maka asiri ba idan kuma kaqi kamin aikin wlh zan toni asirin ka na fad'i har ma abinda baka yi ba kmr yanda nayiwa su zeenah.
Ba yanda Barrister ya iya yasan zata iya dan ya fahimci ta fishi bala'i.
A sanyaye ya gyad'a kansa tare da fad'in"ina jinki gaya min me kike so in miki.
Waheed nake son kaje ka sato min a asibitin uduth mu bar garin nn dashi cikin daren yau....what! meyasa?
Bana da buqatar ka sani yanzu, kawai dai anjima da dare ka zama cikin shiri zanzo in d'auke ka mu tafi a mota ta.
Yace"no wlh kinsan satar waheed da kmr wuya ko kin manta da sojawan da ke tsare dashi ne"
Ban manta ba Barrister amma banyi tunanin za'a ci gaba da tsare shi ba bayan an gama shari'a.
Duk da haka dai kije da yamma ki duba duk abinda ake ciki sae ki snr da ni.
Tace"ok to"
Kana ya shiga motar sa ya wuce ita kuma ta shiga daga ciki.
Yamma nayi ta shirya taje asibiti mami bata yi mamakin ganin ta ba sbd tasan asibitin take aiki kuma akai akai ta kan zo ta duba waheed wacce sam bata san dalilin hakan ba ta d'auka ko dan tana ma'aikaciya ne take d'an zuwa duba shi, kuma ko kotu a zuwan farko bata lura da ita ba sae wnn karon.
Bata wani jima ba tace zata koma mami ta mata godiya da irin kulawar ta.
Beauty na fita bata zarce koina ba sae inda ta faka motar ta bata shiga motar ba sae jingina jikinta tayi a jikin motar,ta kira Barrister wanda da d'aga wayar yace ya ake ciki sojawan na nn ko kuwa?
Tace"eh still sojawan na nn tsare a bakin qofar d'akin amma kar ka damu zamu iya aiwatar da aikin mu ba tare da an sami matsala ba"
Ta yaya beauty?
zan baka kaya kayi shiri kmr wani doctor ni kuma se nayi shirina a matsayin nurse, kaga hakan zai sa baza su hana mu shiga ba bare ni sun san aiki nake a nn dan haka ka shirya sae dare yayi sosai zan zo har gidan ka in d'auko ka muzo, na tabbatar a lokacin mami tayi bacci amma duk da haka zamu fesa mata wata powder da baccin nata zae qara nauyi ta yanda har mu fita dashi baza ta farka ba yayinda su kuma sojawan zasu d'auka ko zamu canza masa d'aki ne sbd ba haka kawai zamu fita dashi ba akan bed zamu keka shi,hope get it?
Na fahimce ki amma meyasa zakiyi haka bayan kinada hanya mafi sauqi da zaki mallake shi?
Hakane amma wnn hanyar da kaga na d'auko zata fimin dad'i inci kare na ba babbaka.
Kamar ya?
Wato Barrister jiya ne naji wata magana a bakin doctorn da nake samun rahoton lfyr waheed dan yana d'aya daga cikin masu kula dashi,wanda ya gaya min cewa waheed ya sami er matsala a qwaqwalwar sa sakamakon dukan da en fashi suka masa aka wanda ba lallai bane in ya farka ya iya regaining rayuwar sa ta baya shiyasa nake son d'auke shi na tafi dashi can inda nake so,ya farka hannu na kaga bai san kowa ba sae ni ya fara gani,se inyi training life in sa a yanda nake so na aure shi muyi rayuwar mu daga ni sae shi ba wani mai takura mu.
Barrister ya numfasa tare da fad'in to idan qwaqwalwar sa bata sami matsala ba yanda ake tunani ba fa?
Wnn ba matsala bane sae inyi using kwalli na in kuma sa boka yasa ya manta kowa har mahaifiyar tasa.
Amma to meye dalilin ki na taimakawa bintu na d'auka ko kin tausaya mata ne kin haqura da waheed zaki bar mata shine suci gaba da rayuwar su?
Haba dai Barrister kmr baka da fahimta,nifa ba dan tausayin bintu bane yasa na toni asirin su zeenah sae dan ganin cewa nima so suke su hallaka ni dan haka kama fita harakar zancen bintu ko mutuwa zatayi wlh sae na rabata da waheed, kai zan dai rabashi da uwar sa bare ita.
Yace"to shikenan ina sauraren ki anjima se kinxo"
Tace"olryt bye sae nazo d'in,but plz ka zama cikin shiri dan wlh bana son wani 6ata lokaci da mun d'auke shi nake son mu bar garin nn dashi kae tsaye.
Yace"kar ki damu komai zaiyi yanda kike so"
Daga haka suka tsinke wayar ta juya knn zata bud'e ganbun motar ta,se sukayi ido hud'u da mami wacce tun lokacinda beauty ta fara waya tun daga farko har qarshe taji komai amma sae mami ta had'iye duk wani yanayin da ta shiga bata nuna mata taji ba,sae wani tsadadden bracelet na gold ta miqawa beauty tare da fad'in"abun hannun ki ne da ya sa6ule ya fad'i baki sani ba shine na biyo ki na kawo miki"
Beauty wacce da farko har ta tsorata da ganin mami girshi,amma da ta fahimci kmr mami bata ji komai ba, ta sauke ajiyar zuciya a hankali snn ta kar6i abun hannun tare da mata godiya.
Cikin sakin fuska mami tace"ba komai a gaida mutan gida"
D'auke da murmushi Beauty tace"to zasu ji snn ta shiga motar ta ta wuce"
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 42_*
Cabd'i!
cewar mami wacce ta fad'i hakane tare da fitar da nannauyan ajiyan zuciya,ta jinjina kanta had'e da fad'in"lallai wato yarinyar nn dalilin da yasa take yawan zuwa duba waheed knn,shi kuma doctor a tunanin sa duk tausayawa ne yasa har ya gaya mata matsalar da waheed ke d'auke da ita ni bai gaya min ba,
hm! innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Kana ta wuce office d'in likitan qwaqwalwa dan tasan ba makawa a bakin sa ne beauty taji matsalar da waheed ke d'auke da ita a cikin qwaqwalwar sa.
Da shigar ta office d'in cikin girmamawa ya gaida ta tare da nuna mata kujera ta zauna.
Mami ta zauna tana mai kallon sa muryar ta a natse tace"Haba doctor sa'id ashe dama waheed ya sami matsala a qwaqwalwar sa shine baka gaya min ba, sae da na jiyo a shanun talla, meye dalilin ka na qin gaya min a matsayina na mahaifiyar sa da ya zama dole in san da wnn matsalar"
Dr sa'id ya numfasa tare da fad'in"kiyi haquri hjy bana son in gaya miki ne damuwa tazo ta qara miki yawa shiyasa na bar zancen har sae ya farfad'o tukun inga ya yanayin sa zai kasance,amma dan Allah hjy a bakin wa kika ji cewa waheed ya sami matsala a qwaqwalwar sa?.
Mami tace"Har ka manta wacce ka gayama?
Doctor yayi shiru kana yace"Zainab beauty ita kad'ai nasan na gayawa amma bada wata manufa na gaya mata ba wlh sae dan ganin yanda take tausayin waheed ta damu dashi sosai.
Mami tace"shikenan ba komai,amma ina son dan Allah kayi shiru da bakin ka kar ka tuntu6e ta da wnn mgnr"
Yace"inshaa Allah hjy"
Nan mami ta tashi ta fito,ta dawo d'akin da aka kwantar da waheed.
Ta sami sojawan da ke tsare a bakin qofar d'akin ta nemi da su shigo da akwai mgnr da zatayi dasu.
Bayan sun shigo d'akin ta gaya musu duk abinda yake shirin faruwa anjima da dare,dan haka tana son su kula da kyau kuma su zama cikin shiri,zata kira police ta snr dasu suzo dmn so take a kama su red handed.
Beauty wacce gabad'aya ta gama yarda cewa mami bata ji komai ba, dare nayi guraren qarfe 2 taje har gidan barrister ta d'auko shi suka zo asibiti cikin shirin su kmr yanda beauty ta tsara.
Kae tsaye suka nufi d'akin da aka kwantar da waheed kmr wasu masu gaskiya.
Sae dai a zuciyar Barrister sam hankalin sa ba a kwance yake ba,wanda kafin su isa yake cewa beauty"wae beauty kina ganin ba matsala har mu fito da waheed mu wuce dashi a gaban sojawan da ke tsaron shi su kalle mu kawai ba tare da sun ce mana komai ba.
D'an guntun tsaki tayi tare da fad'in "kai ka cika tsoro wlh kaman ba namiji ba,ae nasan yanda zanyi dasu ka kwantar da hankalin ka kawai ka biyo ni muje.
Nan Barrister yayi shiru bai sake cewa komai ba har suka isa,sosai beauty taji dad'in ganin ba sojawa a bakin qofar d'akin,ta kalli barrister tare da fad'in"kaga ma basa nn,dan haka sae ka kwantar da hankalin ka muyi aikin mu yanda ya kamata,amma ka bari in fara shiga tukun inga ko mami tayi bacci,dan matar akwai ibadah,rnr cikin dare nazo a sace dan in ga waheed na same ta sae nafilfili take bayan ta idar kuma tayi zaune a gaban shi sae tofe shi take da addu'o'i.
Barrister yace" shikenan je duba d'in"
Nan beauty ta bud'e qofar d'akin sannu a hnkli ta leqa se taga d'akin duk duhu ne ba haske,ta kunna fitilar wayarta ta yada,
a nn ta hango mami kwance kan sofa tana bacci.
Murmushi ta sakarwa Barrister a cewar ya shigo.
Barrister ya shigo yayinda beauty taje gun waheed tayi tsaye sae kallon sa take cike da so d'auke da d'an murmushi a fuskar ta ta kai tafin hannunta a hankli tana shafa gefen fuskar sa,muryar ta a hnkli tace"am sorry my guy zan rabaka da mahaifiyar ka ba dan in quntata maka ba sae dan in nuna maka tsantsar soyayyar da nake maka kaji.
Daga haka ta janye hannun ta daga kan fuskar shi,ta maida dubanta gun barrister ta masa alama da hannu, acewar ya shaqawa mami wnn powder suyi su kama gaban su.
A nn kae tsaye Barrister ya nufi gun mami ya ciro powder a aljihun sa ya bud'e knn zae shaqa mata,kawai haske ya bayyana a d'akin mami dake kwance ta miqe tsaye yayinda police da sojawa suka firfito a bayan curtains duk suka zagaye d'akin.
Hankali tashe barrister da beauty ke kallon su kowannen su yayi arresting nasu da bindiga,
nn take a rud'e suka d'aga hannayen su,beauty ta kalli mami tare da saurin zubewa qasa kan guiwoyin ta tana ba mami haquri.
Mami ta qaraso gurinta tace"gaya min me na miki a rayuwa kike son rabani da d'ana qwaya d'aya tal da nake da shi a duniya?
Beauty muryar ta na rawa tace"Wlh mami ba abinda kika min tsananin qaunar sa ne yasa nake son in tafi dashi,amma wlh Allah na haqura da son shi zan barwa bintu abunta,kar kisa a kamani dan Allah wlh nayi alqawarin zan tafi nesa daku bazan sake waiwayar ku ba har abada.
Mami bata kula ta ba tace da police su kama su su tafi dasu.
A rud'e barrister yace"Aa dan Allah police kar ku tafi dani wlh itace ta tursasa ni banyi niyyar aikatawa ba"
D'aya daga cikin police yace"da yake kai wawa ne mai qwaqwalwar jaki se ka yarda mace ta tursasa ka kayi abinda bakayi niyya ba ko!
Yace"wlh Allah halinta ne na sani zata iya qulla min mummunan sharrin da ban aikata ba, dan ko su zeenah ta qara akan abinda basu aikata ba.
Nan barrister ya tona mata asiri kaf har kashe handosme da tasa akayi bai rage komai ba.
(Sbd komai gaya masa sukayi a lokacin da za'ayi shari'a dan yasan yanda zaiyi ba tare da an sami matsala.)
Cike da alajabi mami ta shiga jinjina kai lallai su zeenah sun had'u da gamon su in taqamar su ba mutun muguwar shawara.
Barrister se roqon ta yake ta yafe mishi kar tasa a tafi dashi,beauty kuwa se kuka take tana fad'in sharri barrister yake mata,mami bata kula su ba,police suka jasu suka tafi dasu kmr yanda ta buqata.
Washe gari da safe bintu na kwance kan darduma wacce tun lokacin ta ida sllr asuba take kwance a gurin bata tashi ba, sei tunanin waheed take tayi wanda tun jiya da suka je duba shi taji gabad'aya ya bata tausayi a yanayin da ta ganshi.
Anti hafsa ce ta shigo d'akin d'auke da sallama a bakin ta,hkn yasa bintu ta tashi zaune tare da amsa mata sallama snn ta mata ina kwana.
Anti Hafsa ta amsa gaisuwar wacce cikin yanayin damuwa da mamaki tace"hm kin san me bintu?
A hnkli bintu ta girgiza kanta tana mai kallon Anti Hafsa wacce tace"yanzu nn yaya Abbas ya kira Abban ilham yake gaya mishi abinda ya faru jiya da dare, wae ashe wnn beauty d'in baqar muguwa ce halin ta d'aya dasu zeenah koma ince tafi su.
Nan Anti Hafsa ta gayawa bintu duk abinda ya faru.
Bintu wacce idanun ta suka ciko tap da qwallah cikin muryar kuka tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku!yanzu idan yaya waheed ya manta waye shi ya zanyi....nan kawai ta fashe da kuka,Anti Hafsa taja ta jikinta sae rarrashin ta take tana bata magana,amma bintu ta kasa daina kukan.
Nan Anti Hafsa ta janye jikinta a hnkli ta tashi taje ta bud'e qofa sbd knocking d'in da taji anayi.
Abban ilham ne ke knocking d'in wanda anti Hafsa na bud'e qofa yace"kin tada su ilham kuwa?
Tace"Aa yanzu dai nake shirin tada su.
Yace"to kiyi ki tada su kar suyi latti.
Anti Hafsa tace"to"
Kana Abban ilham ya juya zai tafi sae kuma ya tsaya yana sauraren sautin kukan bintu dake fitowa a hankli.
Ya kalli Anti hafsa tare da fad'in"me nake ji kmr kukan bintu kaddai kin gaya mata matsalar da waheed yake d'auke da ita ne?
Tace"ya zanyi Abban ilham tunda abu ne da ya zama dole ta sani"
Ransa a d'an mace yace"haba hafsa meyasa, iyakacinki ki gaya mata abinda ya faru bai kamata ace kin gaya mata har matsalar da waheed yake d'auke da ita ba,fisabilillah ba kya jin tausayin ta,duka duka yaushe ne ta fita waccan damuwar da zaki zo ki d'aura mata wata damuwar kuma.
Muryar ta a sanyaye tace"kayi haquri Abban ilham zan rarrashe ta".
Abban ilham dake kallon ta komai bai ce ba ya tafiyar shi.
Anti hafsa ta koma daga ciki jiki sanyaye ta sami bintu taci gaba da rarrashin ta har ta samu bintu ta daina kuka.
Da yamma bayan sallr la'asar sae ga Abbas yazo daga kebbi sbd jiya tare suka koma kebbi shida su umma da Abdallah.
Bayan ya gama gaisawa dasu Abban ilham da Anti hafsa ya nemi ganin bintu,Anti Hafsa taje ta kira mishi ita tazo muryar ta a sanyaye ta mishi sannu da zuwa,ya kama hannunta ya zaunar da ita kusa dashi yana kallon ta da kulawa kana yace"Bintu ance gabad'aya kin shiga damuwa akan matsalar da kika ji waheed na d'auke da ita a qwaqwalwar sa,to ki cire damuwa a ranki kinji inshaa Allah waheed zai sami lafiya bazai manta rayuwar sa ta baya ba da yardar Allah,su umma na kan addu'a haka nima zan taya ki kema ki qara dagewa sosai da addu'a kinji.
A hnkli bintu ta gyad'a kanta.
Abbas dake kallonta yace"dama abinda yasa nazo mami ce taje can kebbi gun Abba da umma ta nemi alfarmar dan Allah idan har ba saki uku waheed ya maki ba tana son a maida auren ki keda waheed a cikin kwanakin nn dmn so take ta fitar da waheed waje dake dmn magance matsalar da kike d'auke da ita.
A nn bayan ta gama bayanin ta su umma suka gaya mata cewa ae ba ma saki a tsananin ku kmr yanda na gaya musu kin min bayani dan haka sae ki shirya a cikin satin nn zaku tafi India inshaa Allah.
Bintu ta kalle sa tace"amma yaya baka ce bazan koma ba kwata kwata?
Abbas yace"Dalilin da yasa knn nazo dmn har umma zata kiraki a waya ta gaya miki buqatar mami nace ta bari kawai inxo in gaya miki dmn dama da akwai bayanin da nake so inzo in miki.
Bayanin shine ni sam ba da gaske nake shirin rabaki da waheed ba,ina hora ki ne sbd ki gane kuskuren ki ta yanda ko maqiyin ki ba kya fatar ya aikata kuskure irin wanda kikayi.
Abban ilham da jabir duk sun san cewa hora ki kawai nake amma sun damu sosai da wnn horon dan ganin suke yayi tsanani musamman jabir wanda da naji zancen yana sonki sosai na lallashe shi na bashi magana kan ya haqura dake yazo ga peeya zan shige masa gaba in yana so(cewa da qanwar mtr shi).
Bintu wacce da gani tausayin jabir take ji tace"to me yace?
Abbas yace"Na nuna masa photon ta tuni ya amince gobe goben nn ma tare zamu tafi dashi Abuja ya ganta suga juna idan ta amince sae ayi magana manya su shigo ciki,bare ma nasan peeya bata da matsala inshaa Allah zata amince ta so shi ko danni da na kawo shi, fatan mu Allah yasa wnn had'i alheri ne a tsakanin su da mu baki d'aya.
Bintu tace"Amin"kafin Abbas ke cewa tashi kije ki gaya wa Hafsa su shirya yanzu muje mu qara dubo waheed.
Nan bintu ta tashi taje ta snr dasu suka shirya gabad'ayan su har jabir suka tafi,da zasu dawo mami ta nemi da su bar mata bintu da dare zata maida ta.
Bayan sun tafi bintu na zaune kan kujera kusa da waheed da still yake kwance kan bed kmr wani gawa, idon ta akan shi sae kallon sa take tayi musamman qafar shi da tasha harbi, da take tsoron kar ita ma qafar azo ace ta sami matsala dan dai ba kad'an ba sun masa rauni a qafar.
Zar taji saukar hawaye a kumatun ta tayi saurin share hawayen kar mami ta gani.
Mami dake kallonta ta girgiza kanta cikin tausayawa,ta matso kujerar ta kusa da bintu ta kama hannayen bintu ta riqe a hnkli snn tace"kiyi haquri bintu ki daina kuka inshaa Allah waheed zai sami lafiya kinji"
A hankli bintu ta gyad'a kanta mami dake kallonta tace"ina kuma roqon Allah ya shiga tsakanin ku da maqiyan ku yasa sun tafi knn har abada baza su fito ba.
Amin cewar bintu wacce tana gama fad'ar haka ne tayi saurin kallon waheed sbd yatsun hannun sa da taga sun motsa.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 43_*
mami kinga yatsun yaya waheed suna motsawa!
Bintu ta fad'a yayinda tayi saurin matsawa gab dashi ta kama yatsun nasa tana kallo.
Mami jikinta na rawa ta matso gab dashi itama tana kallon yanda yatsun nashi ke motsi a hankli.
Suna kallon sa har ya fara bud'e idanun sa sannu a hnkli har ya bud'e su gabad'aya.
Bishi bishi ya gansu kmr wasu katun suna juya mishi dasu har d'akin kmr zasu fad'o mishi aka.
Ba shiri yasa hannuwan sa duka biyu ya dafe kansa da sauri ya kuma rufe idanun sa gam yana jin kansa na masa wani irin masifaffen ciwo tamkar zae tsage ya rabu biyu
Nan mami ta fita da sauri taje ta kira Dr sa'id yazo ya nemi da su bashi guri yana son zae duba shi.
Ba yanda suka iya haka suka fita sae safa da marwa suke a bakin qofar d'akin.
Bayan minti sha biyar dr ya fito ya nemi da su shiga.
Da mami har bintu cikin fargaba suka shiga d'akin,a ransu suna tunanin shin waheed zae tuna su ko kuwa?
Da shigar su Dr ya kalle su snn ya maida duban sa gun waheed dake zaune kan bed bayan sa jingine da pillow yace"to waheed ko zaka iya gaya min su waye wa en nn?
Waheed da tun lokacin da suka shigo idon sa ke kansu,ya kalli dr fuskar sa d'auke da alamun jin jiki muryar sa can ciki ta marasa lafiya yace"wae meye haka ne Dr ka tambayeni sunana da waye ni na gaya ma,kuma shine har mami da fatima sae ka tambaye ni su waye.
Da mami har bintu wani irin dad'i suka ji a ransu,washe da baki mami ta kalli dr da ke d'auke da murmushi a fuskar sa tace"kae Alhmdlh amma naji dad'i wlh ya akayi haka Dr?
Dr sa'id da still fuskar sa ke d'auke da murmushi yace"ikon Allah ne wnn dan nayi mamaki byn na mishi allura ya samu relief na mishi tambayoyi se naji kae tsaye yana bani amsar abinda nake son ji,dan fatana knn inga bai manta rayuwar sa ta baya ba,amma a gaskiya still da akwai er matsala a qwaqwalwar sa, dmn wnn ciwon kan da yazo mishi da farkawar shi shine ke barazanar son mantar dashi rayuwar sa ta baya, amma ba matsala idan aka ci gaba da yi mishi allurar da na mishi d'in nn zae rabu da matsalar inshaa Allah,dan inaga ma koda aka d'auki photon qwaqwalwar sa,qwaqwalwar tasa na cikin wnn yanayin shiyasa naga matsalar,Allah dai ya qara tsare gaba ya kuma bashi lafiya.
Mami tace"Amin"
Nan Dr ya fita wanda kafin ya fita sae da ya rubuta magungunan da waheed zae sha bayan yaci abinci.
Bintu ce ta kar6i takardar ta fita dmn siyo magungunan.
Waheed da yabi Bintu da ido har ta fita,ya kalli mami yace"mami ya na ganki tare da fatima?
Kallon sa mami tayi a natse ta shafo gefen fuskar sa snn tace"zamuyi magana anjima ba yanzun ba kaji"
Yace"To Husna fa sun kashe ta koh?
A hnkli ta numfasa tace"duka duk zamuyi magana anjima,bari na had'a ma tea kasha kafin hajjo ta kawo abinci.
Bata jira me zai ce ba ta tashi taje ta had'o mishi tea ta kawo ta ajiye a nn kan drawer.
Snn ta zubo ruwan gora mara sanyi a cup had'e da er wata tasa dmn ya wanke bakin shi.
Rawa hannun sa ya soma yi bazai iya kar6ar cup d'in ruwan ba sbd gabad'aya jikinsa ya masa nauyi sosai ta yanda gab6an jikin sa baza su iya wani aiki ba.
Hakan yasa mami ta wanke mishi bakin da kanta ta kuma yi zaune tana bashi tea yana sha,a nn sae ga Bintu ta dawo,mami ta kar6i ledar magunguna,bintu taje can kan sofa ta zauna kanta qasa dan sae jin kunyar had'a ido da waheed take,shi kuma shan tea yake yana kallonta jefi jefi.
Bayan ya gama shan tean ne,mami ta bashi magunguna yasha,ya sake tuntun6ar mami amsar tambayar da ya mata d'azun dmn ya qagu yaji dalilin ganinta tare da bintu lafiya lau kmr wani abu bai faru a baya ba.
Haka kuma yana son yaji yanda Husna ta kasance da ma yanda akayi yazo asibiti.
Wannan karon Mami bata musa mishi ba ta nemi bintu da taso tazo kusa dasu.
Bayan Bintu tazo ta zauna kusa dasu ne mami tayiwa waheed bayanin duk abinda ya faru da duk wani sharrin da su zeenah suka qullawa bintu har labarin beauty wacce sai da akayi bincike aka tabbatar da gskyr abinda barrister ya fad'a hkne snn aka yanke mata hukunci d'aurin rai da rai,barrister kuma shekara d'aya a gidan kaso.
Duk haka ta gaya masa komai ba abinda ta rage.
Wani irin yanayi waheed ya shiga na jin tausayin bintu da kuma kashe Husna da akayi.
Idanuwan sa sukayi jajur suka ciko tap da qwallah, yana kallon bintu da hawaye suka shiga silalowa a hnkli kan kumatun ta dan labarin da mami ta bayar se taji komai ya dawo mata sabo.
Mami ta jata jikinta tasa tafin hannun ta tana share mata hawaye.
Bayan sallar isha tuni hajjo tazo ta kawo abinci har ta koma wacce ba kad'an ba tayi murna da farin cikin ganin waheed ya sami lafiya bai kuma manta waye shi ba.
Mami da kanta ta ciyadda waheed abinci har saida yace ya ishe sa.
Bayan ya gama cin abincin ne ya nemi yana son ya watsa ruwa ko jikin sa zae d'an qara sake mishi dan da yaci abinci ya d'an ji sauqin jikin sa ba kmr d'azu ba.
Tare da taimakon mami ya sauko kan gadon ta d'aura shi kan wheelchair ta tura shi zuwa bathroom.
Har zata fita ta barshi sae tayi tunanin kmr wankan zai masa wahala dan ko d'azun da zai yi sllr magrib da isha'i da taimakon ta ne ya samu yayi arwala.
Tace mishi"zaka iya wankan da kanka ko na kira ma bintu tazo ta taimaka maka?
Kansa qasa muryar sa a hnkli yace"eh tazo ta taimaka min"
Nan mami taje ta kira mishi bintu wacce tazo tayi tsaye kawai a bayan shi ba tare da tace dashi komai ba.
Waheed ya juyo da keken gabad'aya yana kallonta kanta qasa se wasa take da en yatsun ta.
A natse yace"Fatima gaya min meyasa kike jin kunyata?
Kallon sa tayi se kuma tayi saurin maida dubanta qasa ta bud'e bakinta a hnkli tace"ina jin nauyin ka ne sbd rashin kyautatawar da na maka kayi haquri dan Allah "
Waheed dake kallon ta cike da so yace"ba komai fatima na yafe miki duk abinda kika min dama wanda baki min ba"
Fuskarta d'auke da d'an murmushi jin dad'i tace mishi ta gode,snn ba 6ata lokaci ta had'a mishi ruwan wanka a bahon wanka.
Tace"na had'a ma ruwan,me kuma kake buqata?
Yace"se kayan jikina zaki tayani cirewa kimin wankan"
A hnkli tazo ta durqusa tana cire mishi kayan jikin nashi har ta cire mishi komai gabad'aya,amma cike take da jin kunya dan se taji kmr yau ne ta fara ganin sa a haka.
Waheed dake kallonta tana durqushe a gaban sa taqi yarda su had'a ido,
yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta snn yace"to tashi ki rage hasken wutar tunda kunyata kike ji yau.
Bintu ta d'anyi murmushi ba tare da tace komai ba ta rage hasken wutar bathroom d'in snn tazo ta taimaka mishi ya shiga bahon wanka.
Nan ta shiga yi mishi wanka cike da kulawa,ba tare da ta bar gun da aka harbe shi a qafa ya sami ruwa ba kmr yanda ake buqata har ta kammala mishi wankan ta d'aura mishi towel suka fito.
Basu sami mami a d'akin ba ta fita, wacce ta basu guri ne sbd ta fahimci ba kad'an ba bintu taji kunya a lokacin da tace taje ta taya waheed wanka, shiyasa ta basu guri har sai ta kammala taimaka mishi ya shirya snn ko zata dawo.
Amma kafin ta fita sae da ta fitar musu da komai da tasan zasu buqata har tufafin sawar shi wato farar riga mai guntun hannu da farin wando 3quarter,wa en da dama an tanade su ne sbd irin wnn rnr koda ya farka.
Haka waheed ya zamowa bintu tamkar wani qaramin yaro komai ita ta mishi, har gashin kansa da sajen fuskar sa duk ita ta taje mishi ta kwantar da sumar tsaf se yayi kyau yana zuba qamshi kmr ba majinyaci ba.
Wacce har qafar sa ma sae da ta sake masa dressing tasa bandage ta rufe masa miki ya fito tsaf tsaf.
Mami kuwa sae da ta tabbatar sun kammala snn ta dawo.
Cikin fara'a tayi wa bintu sannu da qoqari tare da snr da ita cewa ta shirya ta maida ta gida kad dare yazo ya qara yi.
Ba musu bintu ta shirya,mami ta kalli waheed dake zaune kan bed ya jingina bayan sa da pillow tace masa zata je ta dawo,yace mata a dawo lafiya snn suka fita.
Da murna anti Hafsa ta tarbi bintu tana mata congratulation sbd tun asibiti bintu ta kirata ta snr da ita cewa waheed ya farka kuma bai manta rayuwar sa ta baya ba.
Wacce nan take bintu na gama snr da ita ta kira su umma da kowa ta snr dasu har Abdallah dake school,dan ana gama yanke shar'ia ya koma a washe garin rnr.
Washe gari guraren qarfe goma sha d'aya se gasu Abbas dasu umma sun zo,bintu bata yi mamakin zuwan su ba sbd Anti Hafsa ta snr da ita cewa zasu zo duba waheed cos gobe gobe ne tafiyar su india,shine suka ga tunda ya farka ya dace ace sunzo sun ganshi kafin su tafi India d'in.
Tare suka je asibiti gabad'ayan su wato umma da Abba,Anti Hafsa,Abban ilham,jabir,Abbas,Bintu,da kuma Nafee.
Da murna sosai mami ta tarbe su dan bata ko san da zuwan nasu ba se ganin su da tayi, yayinda su kuma fuskar su a sake suka gaisa tare da yiwa waheed sannu da jiki wanda ya amsa cikin girmamawa da mutuntawa.
A nn suka sami hajiyar Husna itama taje duba shi,yana d'auke da d'ansa da husna ta haifa wanda aka saka wa suna saif.
Qwallah ne suka ciko a idon Bintu a lokacin da take kallon saif kamar sa sak da waheed ba inda ya rago shi.
Da kanta ta kar6e shi daga hannun waheed ta ba su umma dasu Anti Hafsa suka ganshi.
Kyakkyawar addu'a suka mishi kan Allah ya raya shi akan sunna Husna kuma Allah yaji qanta yasa ta huta.
Mami da Hajiyar Husna suka ce Amin.
Waheed kuma a lokacin magana suke shida Abbas har yana tambayar sa Abdallah fa yace masa shekaranjiya ya koma school.
Basu kai awa d'aya ba suka ce zasu koma,mami ta raka su tana musu Allah tsare hanya tare da qara yi musu godiyar hidimar da sukayiwa waheed mai yawa,duk da sun san cewa gobe ne tafiyar su india amma basu gaza gurin kawo masa abubuwan da mara lafiya zai buqata ba,wanda mami taji dad'in hkn ba kad'an ba ta kuma yaba da qoqarin su.
Su umma da Abba kai tsaye kebbi suka koma,Abbas,Abban ilham da jabir suka bi jirgin sha biyu zuwa abuja, yayinda Nafee tabi Anti Hafsa zuwa gidan ta,ya kasance Bintu kad'ai suka bari a asibiti tare da waheed dan hajiyar Husna ta ma riga su umma wucewa tare da saif dan a hannun ta yake,mami kuwa bayan sun raka su umma ita da bintu sun dawo ta d'an tafi gida.
Qatuwar darduma bintu ta shinfid'a a nn tsakiya wato tsakanin sofa da bed kmr yanda waheed ya buqata dan so yake ya sauko daga kan bed zaman gadon ya ishe shi.
Bayan bintu ta taimaka mishi ya sauko ya zauna tasa mishi pillow a jikin gina ya jingina bayan shi tare da d'aura mishi wani d'an qaramin pillow ya d'aura qafar sa dake masa ciwo, snn ya buqaci ta d'auko mishi grapes da apples biyu a cikin fridge wacce ta d'auko tazo tayi zaune a gaban shi ta lanqwashe qafafu tana yanyanka apples d'in a plate kmr yanda yace ta mishi.
Yanka apples d'in take ta d'ago taga ya hard'e hannuwan sa a qirji se kallonta yake d'auke da d'an murmushi a fuskar sa,cikin kyakkyawan salo ta d'aga mishi gira had'e da masa wani kallo da kyawawan idanuwanta na alamar kallon fa, kafin yace komai ta d'auki slice d'in apple ta kai bakin shi wai koshi yake so yaci.
Bai bud'e bakin nasa ba sae hannu yasa ya kama apple d'in had'e da lallausan hannunta duk ya kama ya riqe yana kallonta yace"shagwa6ar me naga kina yiwa umma a d'azun harda yi mata kuka me kike so ne?
Sai da ta zare hannun ta a hnkli daga riqon da ya mata snn muryar ta a natse tace"Ban san cewa da wuri zasu tafi ba shine da tace zasu koma nake roqonta karsu tafi yanzu su bari se da yamma,shine tace min a'a komawa zasuyi nace to zan bisu in dawo da yamma,nn ma tace min a'a,shine nayi kuka tace idan ganin gida nake so inje na bari sae mun dawo daga india dai dai jikinka yayi sauqi se naje.
Waheed dake kallonta ya girgiza kansa d'auke murmushi yace"shagwa6a66iya shine kike yima kuka ni nama d'auka ko wani abu kk so ashe rigimar kice kawai ta tashi"
Turo baki kawai tayi tana kallon sa,dan ta san bata da abun cewa ya fita gaskiya,dmn bai kamata ace a yanayin da yake ciki tayi zancen wani zuwa gida ba sae ya sami lafiya tukun,duk da dai tana da buqatar zuwa ganin gida d'in.
Grapes waheed ya d'auka ya tura mata a bakin nata da ta turo se jin yayi ta cije masa yatsa,a take yayi saurin zare yatsan nasa yana yarfi dashi yayinda ya 6ata fuskar sa yana kallon ta kmr wani qaramin yaro,bintu dake masa dariya ta kama hannun sa tana hura masa yatsar had'e da murza masa gurin a hankali.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 44_*
Suna cikin hakane sae ga abokin sa dr khalid yazo shida matar shi da d'ansu.
Basu qarasa shigowa ba Waheed yace"karma ka qaraso nayi fushi ku juya bana so tunda se yau kaga damar zowa"
Cak khalid ya tsaya d'auke da murmushi a fuskar sa yace"haba dai wa ya gaya maka?
Waheed yace"bakinda baya qarya"
Yace"to mami ai tasan bana nn"
Ce maka nayi mami ce?
To koma waye wlh bana nn nayi tafiya bana qasar nn gabad'aya ma se jiya na dawo ko Honey?
Ya qarashe mgnr ne tare da kallon matar sa Zainab wacce tayi murmushi kawai,waheed kuwa d'an le6ace baki yayi yace"kaji baban soyayya koma bitter zaka kirata bazan yarda ba ai bakin ku d'aya"
D'auke da dariya khalid ya qaraso shida matar sa dake riqe da d'ansu abdul suka zauna kan sofa,
Bintu taja hannun abdul ta zaunar dashi kan jikinta ta d'ibi grapes da apple ta bashi yayinda suka shiga gaisawa da Zainab.
Khalid kuma yana magana da waheed kan cewa"wlh Allah da gaske nake gaya maka bana nn mami bata gaya maka bane?
Waheed dake kallon sa d'auke da murmushi yace"ina ma wasa ne ae mami ta gaya min har ma tace akai akai kana kiranta a waya kana tambayar ta ya jikin nawa,da dai ace baka zo ba har muka wuce India gsky da nayi fushi"
khalid yace"ashe na kuru to ya jikin naka?
Yace"Alhmdlh naji sauqi"
Nan itama matar shi Zainab ta mishi ya jiki kana suka jajanta musu abubuwan da suka faru,snn daga bisani bayan sun d'an jima suka ce zasu koma.
Bintu wacce dama ba yau ne suka fara had'uwa da mtr khalid ba har ziyara suna kaiwa junan su kan abotakar da ke tsakanin mazajen su.
Ta tashi ta d'anje ta rakasu ta dawo,ta sami waheed yana qarasa aikinda ta bari na yanka apple, murmushi tayi tare da girgiza kanta taje ta kar6e ta qarasa abunta snn ta soma bashi yana ci,shima ya d'auka yana bata tana ci amma bata wani ci sosai ba tace ya isheta,sbd dama dan ya matsa mata kan se taci ne yasa taci.
Bayan ya cinye taje ta tsiyayo mishi fresh milk mai sanyi a cup.
Takai a bakin sa zai sha knn ya kasa sha se idanuwan sa da ya rufe tare da kai hannu ya dafe qafar sa da alama ciwo take masa.
Bintu ta ajiye fresh milk dake cikin cup,ta qara matsawa gab dashi ta gefen sa,idon ta akansa tace"yaya mene ne?
A hnkli ya bud'e idanun sa ya sauke su akanta yace"qafata ce take min ciwo fatima tunda na farka haka take min lokaci lokaci ciwon se yazo yana ta qaruwa shiyasa duk naji na qagu mu tafi indian nn su duba min ita,idan ma taci a sake min wani aiki su sake min ko zanji sauqin qafar.
Cike da tausayi Bintu ke kallon shi dan ta fhmci ba kad'an ba yake jin zafin qafar tasa.
Muryar ta a sanyaye ta mishi sannu tare da fad'in"inace wnn ciwon kan bai sake zo maka ba"
Yace"Aa bai sake zo min ba da safen nn ma dr sa'id yazo yamin allura"
Tace"raunin bayan kanka fa naga kmr gurin ya warke ba zafi ko?
Yace"eh tunda na farka bana jin wani zafi a gurin,bani fresh milk d'in insha.
Bayan ta bashi yasha yace ta taimaka mishi ya kwanta bacci yake ji.
Nan ta taimaka mishi ya kwanta kan sofa snn tayi zaune a gefen sa se shafa kanshi take a hnkli har yayi bacci.
~~~~~~~~~~~~~~~
Agurguje plz.
Washe gari ne jirgin su ya sauka zuwa qasar India a garin Mumbai city.
A cikin satin da suka tafi ne aka sake yiwa waheed aiki a qafar shi,haka ma bintu an mata aiki snn aka d'aura ta akan magungunan da zata riqa sha.
Sosai mami ke ba kowannen su kulawa duk da cewa ita bintu aikinta ba aiki ne da mutum zae kwanta jinya ba, dan a cikin kwana biyu ta dawo ras abunta,kawai dai mami na kula da ita sosai na ganin cewa tasha magani akan lokaci.
Waheed kuma Alhmdlh tunda aka mishi aiki ya fara jin sauqi nazo mishi sannu sannu wanda koda sukayi sati d'aya da en kwanaki a garin, ya fara iya taka qafar shi amma sai da walking stick ne yake d'an samu yana taka qafar.
Duk da cewa tuni an sallami waheed a asibiti mami bata yarda sun dawo ba sae da waheed ya qara samun sauqi snn suka fara shiryen shiryen dawowa.
Amma kafin nn sae da mami ta tafi da bintu gurare daban daban na bud'e ido,har ma da waheed duk tare suka tafi duk da cewa shi ba wnn ne karon farko da ya fara zuwa garin ba ya saba zuwa tun kafin yayi aure shida mami suna zuwa haka kawai dmn hutawa.
Ranar da suka cika sati uku cur jirgin su yayi landing a 9ja.
Koda suka iso garin sokoto goma da rabi 10:30pm tayi.
Drivern waheed ne yaje ya d'auko su wanda bai zarce dasu koina ba sae gidan mami kmr yanda aka umarce shi.
Da murna hajjo ta tarbe su tana musu sannu da zuwa,wacce tunda sukayi tafiya itama ta tafi garin su sae yau ta dawo kmr yanda mami ta umarce ta kan tazo ta gyara gida ta kuma shirya musu abincin da zasu ci idan sunzo.
Sae da sukayi sllr da ke gaban su snn suka ci suka sha, bayan sun kammala ne waheed yace bintu ta tashi su tafi gida.
Mami tace masa a'a waheed ba inda zaku je cikin daren nn,kaje ka kwana a d'akin ka tunda shima a gyare yake, ita bintu se ta kwana a tare dani in yaso gobe da safe sae ku tafi.
D'auke da er shagwa6a a fuskar sa ya kalli mami yace"um um mami plz ki bari mu tafi kawai wlh....se kuma bai qarasa ba se d'an sosa bayan kansa da ya shigayi irin na jin kunya d'in nn"
Mami dake kallon sa ta girgiza kai d'auke da murmushi a fuskarta dan ta fahimci inda ya dosa.
Tace"in banda abinka waheed wnn gajiyar da muka kwaso haka ina kai ina d'auko wani zance kayi haquri mana ku kwana a nn,koma mene ne gobe da safe sae ku tafi gida.
fuskar sa a 6ace kmr qaramin yaro yace"wlh mami bazan iya bane shiyasa"
Mami ta numfasa tace"to naji shikenan Bintu tashi tafi d'aki ki d'auko mayafinki kizo ku tafi kinji"
Bintu da tun lokacinda waheed ya fara zancen sa ta soma jin kunya ta tashi a natse ta tafi d'aki.
Mami ta kalli waheed da yabi Bintu da ido a ranta tace"hm ikon Allah yaron nn da na hana shi zuwa gida dana shiga haqqin sa da yawa knn.
Waheed ya kalleta d'auke da murmushi yace"thank u mami da kin hana mu zuwa gida da bazan ji dad'i ba wlh"
Tace"uhm to ka dai bi komai a hnkli kaga dai Bintu a gajiya take snn har yanzu kasan still qafar ka nada saura se ka riqa walking stick ne kake iya tafiya dan haka duk wani movement naka ya kasance sannu a hnkli kaji.
Cikin jin kunya waheed ya sosa bayan kansa tare da fad'in "inshaa Allah mami zan bi komai a hnkli"
Nan bintu ta fito suka wuce gida.
Koda suka isa gidan,bintu sae kallon gidan take cike da sha'awa kmr wani gidan turawa ya qara kyau fiye da daa,an sake yin komai sabo tamkar wata sabuwar amarya ce zata shigo wanda anyi gyare gyaren ne bayan tafiyar su.
Waheed da kanshi ya kaita har bedroom d'inta yace idan tayi wanka ta same shi a d'aki,snn ya wuce nasa bedroom dmn shima ya samu yayi wanka.
Bayan minti ashirin se ga bintu ta shigo d'akin nasa se zuba qamshi take ta koina gashi tayi masifar kyau cikin er fincikar farar rigar ta ta bacci mai lafewa a jiki da tsokano sha'awar dukkanin wanda ya kalla ko mace ce kuwa in ta ganta se taji yar a jikinta,Lol.
Waheed dake tsaye jikin mirror ya tsaya cak da taje gashin kansa da yake yana kallonta ba ko qyaftawa har ta qaraso kusa dashi ta hura masa iskan bakinta kan idanuwan sa da yake ta faman kallonta da su.
A hnkli ya lumshe idanunsa ya koma ware su akanta,kana ya ajiye comb brush d'inda ke hannun sa ya zagaya da hannun sa ta bayan qugunta ya manna ta a jikin sa yana kallon fuskarta yace"kin min kyau my lady"
Bintu tace"nima ka min kyau amma ya baka sanya kaya a jikinka ba har yanzu kana nn da halinka knn ko?
Tayi mgnr ne yayinda ta d'aura tafukan hannayen ta akan kumatun sa tana kallon sa da kulawa.
Yace"dama ba kyaso ne?
A hnkli ta lumshe kyawawan idanun ta tare da gyad'a masa kai alamar eh.
Snn a natse ta janye jikinta daga nashi ta nufi wardrobe in shi,ya bita da ido se kallon yanda rigar baccin jikinta take cak a jikinta wacce ta fito mata da ainihin shape d'inta wato figure8.
Yanda take tafiya haka jikinta ke juyawa yana karkad'awa cike da jan hankali shiyasa sam ya kasa d'auke idonsa akanta har ta d'auko abunda zata d'auko ta dawo.
Guntun wandon sa ne fari tas a hannun ta,taja hannun sa suka je kan bed ta zaunar dashi yana kallo har ta saka mishi wandon ta zauna gab dashi tare da sa en yatsun ta ta lotsa kumatun sa d'auke da murmushi tace"kai ba yaro bane yaya u have to be matured ka daina fitowa wanka zir d'in nn kaji"
Tsadadden murmushi ya sakar mata snn yace"towel d'in ne yake min nauyi kin sani amma tunda kince in daina zan daina"
Ya qarashe mgnr ne yayinda yakai hannun sa kan santala santalan cinyoyin ta yana shafawa.
Snn a hnkli yaje da bakinsa kan d'an qaramin bakinta ya had'e da nashi ya kama lallausan harshenta yana tsotsa haka itama ta kama nasa harshen tana tsotsa cike da natsuwa.
Sun d'auki lokaci a haka kowannen su baya son yaji bakin sa ya fita daga na wani se shafar jikin juna da suke ta koina suna ci gaba da tsotsar bakin juna zaman ya gagare su har suka kai kwance bakin su yana still a had'e.
Se can da qyar suka iya rabe bakunan su tare da bud'e idanuwan su a hnkli se sauke numfashi suke suna kallon juna d'auke da idanuwan su da suka soma canza kala,kana waheed yakai hannu ya kashe musu wutar d'akin snn ya cirewa bintu rigar da ke jikinta yakai bakin sa gefen wuyanta yana kissing d'in jikinta ta koina wanda tunda ya d'aura harshen sa kan albarkatattun qirjinta ya shiga yi mata wani irin salo mai wuyar fassarawa,bintu duk tabi ta narke masa se fitar da numfashi take a hnkli tana qara manna mishi qirjinta nata a jikin shi, ta kuma sa hannun ta a jikin wandon shi tana shafa shi cikin wani irin salon da ya soma rikitar dashi jikin sa na rawa ya ci gaba da romancing d'inta tamkar wanda zae had'iye ta.
Koda suka je ga babban aiki gabad'aya waheed ya manta da wani ciwon qafar da yake d'auke dashi sae aikin sa yake baji ba gani cikin tsananin kewar ta da yayi na tsawon watanni,haka itama bintu sosai ta bada kai bori hau.
Wa enda ba kad'an ba sun faranta ran juna a daren rnr.
kwanan dad'i bintu tayi wanda rabonda tayi irin shi tun rabuwarta da waheed.
Washe gari suna yin sllr asuba suka koma kwanciya se guraren sha biyu snn suka farka sbd knocking d'inda ake,waheed ne ya tashi ya d'auki walking stick d'insa da ke kusa da bed yaje ya saka jallabiya ya fita.
Breakfast ne umma ta aiko musu dashi,ya kar6a yakai kan dining ya ajiye snn ya koma daga ciki,ya sami bintu ta tashi tayi zaune ta had'e kai da guiwa,ya qarasa kusa da ita ya zauna kan bedside drawer tare da shafo gadon bayanta a hankli yace"mene ne my lady?
A natse ta d'ago tana miqa a hnkli had'e da fad'in"ba komai bacci ne kawai"
Yace"to tashi muje muyi wanka mami ta aiko mana da breakfast.
Nan Bintu ta miqe tsaye se qara yin miqa take dan baccin yaqi ya sake ta yanda take so, waheed dake kallonta wani yarr yaji a ajikinsa sbd a lokacinda take miqa bedsheets d'in jikinta ne ya zame ya fad'i nonuwan ta da suke tsaye qyam suka bayyana.
Kafin bintu ta maida bedsheets a jikinta sae ganin tayi waheed ya miqe tsaye yazo gab da ita yasa hannun sa ya kama albarkatattun qirjinta yana shafawa,kana yakai bakin sa a hankli zai tsotsa,bata barshi ba ta rufe abunta da duka hannayen ta biyu tare da maqale kafad'a tana masa murmushi,shima murmushin yayi tare da had'iye yawun bakinsa da suka tsinke mishi.
Da suka je bathroom sam kasa had'iye kwad'ayin sa yayi se da ya neme ta,a nn cikin bahon wanka suka kashe juna da soyayya.
Sae zuhur snn suka kammala abinda suke suka fito suka shirya snn sukayi sallah suka je suka ci breakfast d'insu da ya zamar musu lunch.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 45_*
Da yamma liqis sae ga anti Hafsa tazo gidan,bintu na zaune a farfajiyar gidan tana hutawa kan kujerar shan iska,tana ganin Anti hafsa ta tashi da murnar ta taje tayi hugging d'inta tana mata oyoyo,wacce dama tasan da zuwan nata dan ta kirata a waya kafin tazo.
Ciki bintu ta nemi su shiga Anti Hafsa Tace"Aa nifa komawa zanyi yanzun,akwatin ki kawai nazo kawo miki gidan Nafee zanje in kar6o d'inkuna na da na bayar telan ta ya min"
A shagwa6e Bintu tace"lah haba anti wai dama akwatina ce zaki kawo min knn kin gaji dani har korata ma kike"
Ta qarashe mgnr ne had'e da turo baki.
Anti Hafsa tace"Au daa idan ban kawo miki akwatin naki ba komawa zakiyi knn"
Bintu tace"ba haka ba anti ae kya bari har inje da kaina in d'auko ko,amma haka kmr dama can kin matsu dani"
Anti Hafsa tace"yi haquri ba haka bane bintu gobe goben nn abuja zamu tafi nida Abban ilham dasu ilham sbd wani abokin Abban ilham ne zai yi aure kuma se munyi kwana biyu kafin mu dawo shine na kawo miki akwatin kar kije se bama nn ki buqaci akwatin,dan tun lokacin kafin ku dawo da waheed yace inzo inga gyaran gidan da aka miki ko yayi idan ba wani abinda ake buqata,naso inzo miki da akwatin se na manta.
Bintu tace"ok to ya batun zuwan mu kebbi kinsan fa ending of dis week ne zamu tafi har ma d'azun na gayawa Anti nafee itama tace zata tafi.
Anti Hafsa tace"ba matsala ko daga baya ne idan mun dawo zan biyo ku daga baya dani har su ilham dan yanzu kinsan hutu suke ba sai na kaisu gun kakar su ba,ko kuma tunda on Friday ne za'a gama bikin ku jirani in na dawo Saturday, Sunday se mu tafi
Bintu tace"yayi ba matsala,amma Anti ki shiga ciki mana ko gaisawa kuyi da yaya waheed ki masa ya qarin lafiyar jikinsa"
Aa ba d'azun da mukayi waya kince min baya nn ba ya tafi gurin mami?
Eh ya dawo yanzun nn ma tare muke dashi ya d'an shiga daga ciki ne,ko kinfi so in kira miki shi yazo ku gaisa?
Aa mu shiga daga ciki kawai ae na d'auka baya nn ne.
Nan suka shiga sun sami waheed har ze fitowa ya koma suka gaisa da Anti Hafsa dake tambayar sa ya hanya da kuma qarin lafiyar jikin sa yace duk Alhmdlh ya muka dawo muka same ku,su ilham kowa lafiya?
Tace wlh lafiya qalau kowa.
Bayan sun qarashe gaishe gaishen su ne tace zata koma bintu ta had'o mata kayan tsarabar su da tayo musu har na Anti nafee duk ta bata snn ta kar6i akwatin ta.
Da dare bintu ce ta shigo d'akin waheed cikin shirinta na bacci ta same shi shima cikin shirin sa na bacci yana tsaye gun fridge yana tsiyaya fresh milk a cup. Murmushi ta sakar mishi kmr yanda ya sakar mata ta qarasa gurinsa tare da shigewa jikinsa yayi hugging d'inta tare da bata peck kan goshi snn hannun sa kan gefen fuskarta yana shafawa se yaba irin kyawon da tayi yake.
Bintu da har ranta taji dad'i ta d'aura masa kiss kan gefen kumatun sa d'auke da murmushi tace"thank u"
Komai waheed bai ce ba se murmushi yayi had'e da jan karan hancinta snn ya kama hannunta suka je kan sofa suka xauna,yana riqe da fresh milk d'inda ya tsiyaya a cup yana sha yana bata tana sha suna kallon film har suka shanye suka ajiye cup suka ci gaba da kallon su.
Kallo suke amma waheed se yawo yake da hannun sa kan jikin bintu yana shafata,wacce ke rungume jikinsa tana wasa da hannun ta kan faffad'an qirjinsa kasancewar rigar baccin tashi mai budadden qirji ce.
Tana jinsa se ci gaba yake da shafar jikinta a hankli har ya shigar da hannun sa cikin rigar ta yana matsa dukiyar fulanin ta cike da natsuwa yana motsa su.
Bata hana shi ba sae shafar qirjinsa taci gaba dayi itama.
Sannu sannu har abun ya wuce sanin mai karatu dan a nn kan sofa suka kashe juna da soyayya.
Sanan bayan sunyi wanka suka kwanta kan bed sukayi bacci.
Washe gari sun fito daga bathroom gurin wanka kowannen su d'aure da farin towel,bintu da fitowar su bathroom ta tafi da saurinta zata bar d'akin tana yima waheed dariya, waheed dake tsaye a bakin qofar bathroom ya kasa biyota se saurin danna wani abu yayi a jikin qofar bathroom d'in,ae kuwa gabad'aya doors d'inda ke cikin d'akin suka rufe, wato da ta fita zuwa falo da wacce ke sada shi zuwa d'akin bintu da kuma ta bathroom duk suka rufe.
Bintu najin lokacinda doors d'in sukayi locking ta murd'a key taga aikin banza ne bazata iya bud'ewa ba.
Ta juyo a shagwa6e tana kallon shi tace"plz yaya ka barni in fita"
D'auke da dariya waheed yace kije mana ba kinga banada qafa ba.
Tace"ba haka bane"
Yace"to idan ba haka bane rowa kike so kimin knn"
Girgiza kanta tayi alamar a'a snn ta qarasa gurin shi kmr da gaske ta amince da buqatar shi.
Tana isa gurin kawai tasa yatsar ta da sauri ta danna gun da waheed ya danna ta bud'e qofofin ta kuma kwasa aguje zata bar gurin,
se jin tayi towel d'in jikinta ya rabu da ita sbd damqar da waheed ya mishi,wacce kafin ta iya yin komai tuni ya cafko ta suka fad'a kan bed ya mata rumfa,se dariya take tana son qwatar kanta,shima waheed se dariya yake wanda kai tsaye ya zare towel d'in jikinsa ya jefar tare da kai bakin sa kan nata ya had'e,tun tana zille mishi har ta bada kai bori ya hau,wacce dama kissa ce kawai irin tamu ta mata take mishi.
Dan yanda waheed kejin tsananin kwad'ayin ta na jimawar da sukayi basa tare haka itama take ji a ranta.
Haka suka ci gaba da rayuwar su cike da zallar so duk dare idan ba ya neme ta ba sam baya jin dad'i haka da safe idan suka je wanka ko kad'an baya iya had'iye kwad'ayin sa se ya neme ta yake samun gamsuwa. Bintu kuwa bata hana shi se dai ta bada kai bori ya hau.
A daren rnr da zasu tafi kebbi ne guraren qarfe tara na dare waheed yazo d'akin bintu,wanda yanzu Alhmdlh ya samu sauqi da qafar sa yake takawa ba sai da walking stick ba.
Yayi tsaye yana kallon bintu wacce keta harhad'a kayan tafiyar ta zuwa kebbi da duk wasu en tsarabar da tayi wa su umma duk ta had'a cikin er akwatin ta da zata tafi da ita.
Bintu dake harhad'a kayanta ta kalle shi d'auke da murmushi tace"yaya ya kayi tsaye se kallona kake tayi"
Numfashi waheed ya fitar a hnkli tare da sanya hannuwan sa cikin aljifan wandon sa,cikin nuna damuwa yace"wato fatima bansan ta yanda zan miki bayani bane"
Bintu dake kallon sa jiki sanyaye ta ajiye aikinda take tazo gab dashi cikin damuwa tace"me yake faruwa ne yaya?
A hnkli waheed yasa tafukan hanneyen sa ya riqo kumatun ta yana kallonta yace"Ba wani abu bane fatima ina son kiyi haquri ki bar tafiyar nn se wani sati kinji"
Kmr zatayi kuka tace"meyasa?
Yace"ni ke buqatar haka Fatima"
Tace"to yaya baka ganin tare zamu tafi dasu anti dan Allah ka bar ni inje tunda dai yanzu kana iya yin komai da kanka"
um um fatima bazan iya bane kiyi haquri ki bar su Hafsa su tafi kawai ke kuma wani satin se kije kinji"
Maqale kafad'a tayi cike da qwallah a idon ta tace"ni wlh nafi so in tafi tare dasu dan Allah tunda kaji sauqi ka barni inje"
Yace"Fatima ko naji sauqi ae inada buqatar ki a kusa dani wani sati idan na koma bakin aiki sae ki tafi"
Kuka ta fashe mishi dashi taja baya tana doddoka qafafunta a qasa cike da shagwa6a tana fad'in"haba yaya gaskiya ni tare nake son in tafi dasu,ka tausaya min dan Allah nafa jima rabona da gida"
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka sosai ta kuma kama hanya zata bar d'akin.
Cikin dariya waheed ya janyota jikinsa yana fad'in"ikon Allah nifa da wasa nake miki wlh na gwada ki ne kawai inga ya zakayi"
Bintu ta d'ago shaye da toka tana kallon sa,se kuma taci gaba da kukan ta cike da shagwa6a tana kai masa duka a qirji tana fad'in"wlh se na rama"
Waheed dake mata dariya ya kama hannayen ta ya riqe ya kuma kai bakinsa a nata ya had'e.
Se can ya zare bakin sa,bintu bata kalle sa ba se zuwa tayi kan faffad'an qirjinsa ta kwanta tana sauke numfashi a hnkli,waheed ya rungume ta sosai a jikin sa yana shafa gadon bayanta muryar sa a natse yana bata haquri.
Se jin yayi ta mintsile shi a gefen cikin sa har sai da ya saki er qara,bata kula shi ba se zuwa tayi da gudu kmr wata qaramar yarinya taje ta d'aga wayarta dake fmn ruri.
Waheed ya saki d'an wani tsadadden murmushi yana kallon ta cike da so wanda har ta gama waya bai daina kallonta ba.
Kana yaje ya tayata ta qarasa shirya kayanta.
Washe gari koda qarfe goma na safe tayi tuni bintu ta kammala shirin tafiya ita da waheed dan zasu tafi tare ne sbd yana so yaje ya gaida su umma ya dawo.
Waheed ne ke tuqa mota inda kai tsaye gidan mami suka je bintu ta mata sallama snn suka tafi gidan anti Hafsa ba 6ata lokaci suka wuce zuwa kebbi dan dama tuni nafee tazo da yaranta isowar bintu kawai suke jira,duk da cewa ba a mota d'aya zasu tafi ba kawai dai sunfi son su tafi lokaci d'aya.
Basu qarasa awa biyu a hanya ba suka isa garin kebbi, murna a gurin bintu ba'a magana rabonta da garin kusan watanni goma sha d'aya koma ace kusan shekara.
Bintu taga gidan nasu an sauya masa tsari dan yanzu umma ita kad'ai ce a 6angarenta an ke6ance ta da iyayen su zeenah duk da cewa basa ma gidan dmn tun da abun ya faru mazajen su suka kora su da saki uku uku.
Wa enda mazajen nasu ba kad'an ba sunyi nadama da baqin cikin abubuwan da suka faru,dan suna biye musu ne kawai ba tare da sun san ainihin mugun abunda suke shiryawa ba shiyasa sosai suke son ganin sun shirya da d'an uwansu wato baban bintu da kwata kwata sun kasa samun fuska kuma sam ya fita harakar su.
Basu sami Abba a gidan ba baya nn ya koma jos,se umma suka samu wacce ta tarbe su da murna tana musu sannu da zuwa,en jikokinta wato su ilham da 'ya'yan anti Nafee duk suka maqalqale ta suna murnar ganin ta, qwallah ne suka ciko a idon bintu,da yanzu itama da er ta ko yaronta a cikin su.
Waheed ne kad'ai ya lura da yanayin da ta shiga a ciki, yayinda bintu a tunanin ta ba wanda ya lura da ita dan kai tsaye ta had'iye hawayen da suka cika mata qwallah taci gaba da murnar ta kmr a ranta ba komai.
Gabad'ayan su ciki suka wuce suka bar waheed zaune a falo,umma ta fito riqe da makullin d'aki a hannunta wacce bata bashi makullin d'akin ba se zama tayi suka qara gaisawa tana tambayar sa ya qarin lafiyar jiki yace"Alhmdlh jiki yayi sauqi sosai"
Tace"to Allah ya qara baka lafiya ya kuma tsare gaba ya muku katangar qarfe da duk wasu miyagun mutane"
Yace"Amin"
Snn ta bashi makullin d'akin da yake sauka wato d'akin Abbas da yake kira d'akin shi dan haka suke shida Abbas abun waheed nasa ne haka waheed abun sa na Abbas ne,haka amintakar su take abun sha'awa har iyayen su sun biye musu,se dai Abbas bai sake sosai da mami ba kmr yanda waheed ya sake da umma.
Sbd Abbas aikin sojan shi bai barshi ya cika yin ziyara kmr yanda waheed keyi ba.
Kuma ko ganin gida ma se can yake zowa wanda tunda yayi aure ko yazo a gidan sa yake fara sauka shida iyalin sa snn suzo su gaida su umma.
Koda waheed yaje d'akin ya sami d'akin tsaf tsaf se qamshi ke tashi kai tsaye kan sofa yaje ya zauna tare da zaro wayar sa a aljihu.
Umma kuwa tana baiwa waheed makulli,kitchen taje ta shirya masa abincin sa a tray ta kira bintu ta bata tace ta kai mishi.
Koda bintu tazo ta same shi zaune kan sofa se waya yake cike da fara'a yana dariya.
Tasan ba kowa ne yake waya dashi ba face yayanta Abbas dan tasan dashi kadai' yake irin 6arkar dariyar nn idan suna waya.
A nn gaban shi ta jawo stool ta d'aura masa trayn abincin snn ta dibar masa abincin a plate, white rice ce da miyar stew wacce taji naman kaji se cucumber salad da ta sa mishi a gefe,snn ta zuba mishi lemu a cup ta miqa mishi dan a lokacin ya gama waya.
Waheed ya kar6i lemun tare da kama d'ayan hannun ta ya zaunar da ita kusa da shi ya kurma lemun ya bata itama dmn tasha,
a hnkli ta girgiza kanta tace"Aa kasha kawai"
Waheed ya ajiye lemun yace"to muci abinci"
Nan ma tace"Aa kaci kawai naka ne wnn ni zanje inci dasu anti Hafsa"
Yace "No muci kawai ae zai ishe mu har ma mu rage"
Bintu bata musa mishi ba ta yarda suka ci abincin.
Bayan sun kammala bintu ta zari tissue tana share bakinta se kallon ta waheed keyi.
D'auke da d'an murmushi bintu tace"yaya lafiya?
A natse ya kama hannayen ta yasa a cikin nashi ya riqe yana kallonta kmr zai ce wani abu se kuma yace"ba komai"
Maqale kafad'a tayi tare da fad'in ban yarda ba da akwai abinda zaka fad'a ka fasa"
Ta qarashe mgnr ne tare da d'an doddoka qafafunta a qasa tana kallon sa cikin shagwa6a,tace"uhm dan Allah yaya ka gaya min mene ne wlh bana son ayi niyyar gaya min abu kuma a fasa"
Waheed dake kallonta a natse ya shafo gefen fuskarta yace"ba wani abu bane my lady dama d'azun ne naga kinsa damuwa a ranki a lokacinda su ilham suka je jikin umma suna murnar ganin ta, tunanin me kike kuma meyasa kika tashi yin kuka a lokacin?
Qwallah ne suka ciko a idon bintu tana batun fashe masa da kuka,da sauri waheed ya girgiza kansa yace"kin gani koh shiyasa kawai naso in fasa mgnr dan nasan zaki iya min kuka,maida kukan idan baso kike muyi fad'a ba"
Ya qarashe mgnr ne yana kallon bintu wacce bata fashe masa da kukan ba amma ta kasa maida hawayen da ke cike a idonta,se hannunta ta d'aura kan cikinta muryar ta a sanyaye tace"yaya ina son in haifu nima inga 'ya'yana"
Waheed dake kallonta yaja ta zuwa jikinsa yana shafa bayanta a natse cikin muryar rarrashi yace"ki kwantar da hankalin ki my lady meye na damuwa duka duka yaushe ne aka miki aiki wata qil ma yanzu haka akwai babyna a jikin ki lokacin bayyanar sa ne kawai baiyi ba.
Bintu ta d'ago hawaye still cike a idonta kmr zasu zubo cikin muryar kuka tace"babu baby a jikina yaya am in on"
waheed yace"yaushe?
Tace"muna isowa cikin gidan nn naji isowar shi"
Yace"kin duba kuwa shine?
A hnkli ta gyad'a masa kai tare da sa hannu ta share hawayen da suka zubo mata.
Waheed da gabad'aya jikin sa yayi sanyi ya sake maida ta kan faffad'an qirjinsa ya kwantar se shafa bayanta yake cike da natsuwa yana bata magana.
0 comments:
Post a Comment