Har ya samu ta rage damuwar da ke ranta.
A nn ta d'ago daga kan qirjinsa tana tambayar sa yaushe zai koma,yace mata idan anyi sllr zuhur.
Tace"yaya da ka bari da yamma dai dai rana tayi sanyi se ka d'au hanya yafi"
Yace"um um da dai ace Abdallah na nn in samu abokin fira,junaid kuma basa nn bare in tafi gidan shi.
Bintu tace"to amma idan ka koma a can gidan mami zaka riqa kwana koh"
Yace"Aa a gida dai zan riqa kwana har ki dawo"
Cikin damuwa tace"um um dan Allah yaya ka riqa zuwa gurin mami kana kwana a d'akin ka wlh hankali na ze fi kwanciya,banna son ka kwana a wancan gidan kai kad'ai a d'aki ina tsoro"
Waheed dake kallon ta yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta yace"ki kwantar da hankalin ki Inshaa Allah ba abinda zae sake faruwa dani,ko inje d'akin gateman na riqa bacci tare dashi?
Dariya bintu tayi tace"A'a ai duk inda mutum yake Allah yana tare dashi kawai ka riqa baccinka a d'akin ka,as usual zanci gaba da roqon Allah ya tsare min kai.
Waheed da har ransa yaji dad'i yace"nima Allah ya tsare min ke fatima,bari in shiga bathroom inyi arwala in tafi masallaci nasan ba'a nesa da yin sallah.
Ba tare da ya jira me zata ce ba ya tashi ya shiga bathroom ita kuma ta kwashe kwanikan abincin da suka ci ta fito dasu.
Bayan anyi sallah ne waheed yazo yayi sallama da umma dasu anti hafsa acewar zai koma suka masa Allah kiyaye ya tsare hanya yace Amin.
Bintu ta raka shi har mota ya tafi se bye bye take mishi har ya wuce snn ta koma daga ciki.
Kwanan su biyu a garin se ga Abdallah shima yazo ae kuwa gidan se ya qara yiwa bintu dad'i se murna take da dawowar shi,kullum tare suke cin abincin su ita dashi har ma dasu anti hafsa duk tare suke ci su duka hud'u,su ilham da 'ya'yan anti nafee suma a kwano d'aya ake sa musu abinci suci tare dan ba kad'an ba hakan na qara danqon zumunci.
Shiyasa umma sosai take jin dad'in had'in kan 'ya'yan nata,se ka gansu sunyi zaune se fira suke tayi suna kekkewa,dan Abdallah idan yana ga guri gwanin son a zauna ayi ta fira ne ana raha,ae kuwa da lokacin komawar su sokoto yayi suka ji kmr su qara kwanaki akan sati d'ayan da sukayi amma ina sun san ko sun fad'a umma bazata yarda da wnn iya shegen ba,dole rnr lahadi da yamma suka shirya suka koma amma wnn karon a mota d'aya suka koma wato mortar anti Hafsa da Anti nafee ta biyo suka zo tare.
Duk da cewa waheed da kansa yaso yazo ya d'auki bintu tace masa a'a ya barshi kawai motar anti Hafsa da akwai enough space.
Da isar su garin sokoto bintu suka fara saukewa sbd tafi kusa.
Su anti Hafsa na wucewa bata ko shiga gidan ba sae ga waheed ya fito tarbonta sbd suna isowa bakin gate d'in gidan dai dai kiransa ya shigo dmn yaji shin suna ina,wanda tasowar su ya kirata kusan sau uku,ana hud'un ne tace mishi ai gasu har ma sun iso shine ya fito ya tarbe ta cike da murna ya rungume abar sa qyam kyace wanda yayi wata d'aya rabon shi da ita.
Haka ya shiga da ita gidan manne da ita a jikinsa yayinda gateman ya biyo su da akwati.
Da suka shiga ciki bintu taga komai tsaf tsaf se qamshi ke tashi ko wata mace albarka dan waheed akwai tsafta sosai sam baya son qazanta.
Ga abinci kala kala jere kan dining wanda duk mami ce ta girka mata shi da kanta ta aiko hajjo ta kawo.
Kasancewar a lokacin magrib tayi bintu bata tsaya cin komai ba sae da sukayi sallah snn waheed da kanshi ya d'ibar musu abinci sukaci.
Bayan sun kammala cin abinci har ma sunyi sllr isha sukayi zaune a falo suna fira yayinda waheed ke zaune kan doguwar kujera 3seater bintu kuwa na kwance kan qafafuwan sa tayi pillow dasu se wasa yake da kalabar kanta.
A cikin firar su ne bintu ke cewa"yaya wai yaushe ne hajiyar Husna zata maida maka saif ya dawo hannu mu da zama wlh ina son yaron sbd kunyi kama ba kad'an ba"
A hnkli Waheed ya numfasa yace"saif kam bazai dawo hannun mu ba fatima"
Bintu ta tashi tana kallon sa tace"meyasa?
Yace"yana nn hannun mami ya dawo da zama"
Cikin jin dad'i tace"yes! kaga ma shikenan se kayiwa mami magana nasan zata bamu shi"
A hankli ya girgiza kansa alamar a'a
Bintu tace"meyasa?
Yace"baza ki iya da lalurar sa ba fatima"
Nan take gabad'aya farin cikin bintu ya koma tace"sbd ni ba mahaifyar sa bace zaka gaya min haka"
Da sauri Waheed yace"ba haka bane Fatima"
Qwallah tap a idonta tana kallon sa tace"to idan ba haka bane mene ne,idan ni na haife shi ai bazaka gaya min haka ba wlh"
Tana kaiwa nn ta bar gurin ba tare da ta jira me zae ce ba waheed se kiranta yake amma taqi ta tsaya se kuka ma da yaji ta fashe dashi ta shiga d'akinta.
Jiki sanyaye waheed ya tashi ya bita ya same ta kwance ruf da ciki tana ci gaba da kuka.
Yaje gab da ita ya zauna tare da janyo ta zuwa jikinsa cike da son ya rarrashe ta amma taqi saurarar shi se qwacewa tayi daga jikinsa ta tashi zata bar masa d'akin.
Cikin muryar rarrashi yace"fatima yi haquri kar ki fita zo muyi magana kinji"
Bata fita ba d'in ta tsaya tana ci gaba da kukan ta,waheed ya taso ya jata ya tafi da ita suka zauna kan bed.
A natse cikin muryar rarrashi yace"kiyi haquri fatima ba haka nake nufi ba,ganin nayi gobe goben nn nida ke duk a bakin aiki zamu koma ba qaramar lalura bace dawo da saif hannun mu,snn ba kad'an ba mami tana son yaron ya kasance a gurinta ganin haka yasa hajiyar husna ta maida mata shi da kanta.
Amma kar ki damu kinji duk lokacinda kk off hajjo zata riqa kawo miki shi ya maki yini da dare se a maida shi koh?
A hankli ta gyad'a masa kai waheed yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta kana yaja karan hancinta d'auke da murmushi yace"iyayen rigima ba kya bari ki fahimci mutum se ki d'auki laifi ki d'aura mishi koh"
Murmushi bintu tayi tare da shigewa jikinsa tana fad'in yi haquri kasan mai kaza a aljihu baya jiimirin has se inga kmr dan bai haifu bane"
Waheed da har ransa ya fita damuwa yaga cewa ta haifu yace"hm my lady knn ae kema kin kusa ki haifu da yardar Allah.
Amin Allah ya kar6i bakin ka.
Cewar bintu wacce ta d'ago daga jikinsa tace"yaya ya kamata muje muyi wanka mu samu mu kwanta da wuri kar muyi lettin tashi"
To waheed yace snn ya taya ta cire kayan jikinta ta d'aura towel suka tafi d'akin shi.
Da fitowar su wanka gogan ya kasa haquri ko mai su shafa,se jan bintu yayi zuwa bed ya kwantar tare da zare mata towel d'in jikinta shima ya zare nasa ya jefar suka shiga ba juna haqqin su cike da zallar so.
Washe gari da wuri suka tashi suka shirya bayan sunyi breakfast suka fita waheed ya shiga tashi motar ya wuce gurin nasa aiki,itama bintu ta shiga sabuwar motar ta da waheed ya canza mata,ta wuce gurin nata aiki farin ciki fal a ranta se murna take dan da sassafen nn ne ya mata surprise d'in sabuwar motar.
Wacce kafin su bar gidan se da ta kira umma dasu anti Hafsa ta gaya musu se tayata murna suke,ta kuma ba waheed waya suka mishi Allah ya qara bud'i.
Koda sati ya zagayo bintu ta gama morning tana off hutu take kafin ta fara evening.
Shiyasa rnr waheed kawai ya fita aiki to ten se ga hajjo ta kawo mata saif kmr yanda waheed yayi mata alqawarin duk rnr da take free bata zuwa gurin aiki za'a kawo mata shi ya mata yini da dare se a maida shi.
Sosai bintu taji dad'i dan dagaske har ranta take son saif ji take kmr ma ace ita ce ta haifeshi sbd saif yaro ne mai shiga rai ga jikin sa d'an du6ul du6ul abun sha'awa kuma sam baya da kukan banza se idan yaji yunwa yake yin kuka.
Duk da saif bai yi wani wayo ba amma haka bintu zata tasa shi gaba tayi ta mishi wasa tana cilla shi sama shi kuma yana ta yi mata er dariyar shi da ya fara iyawa.
Idan kuma ta fahimci ya fara jin yunwa yana son yin kuka se ta had'a mishi madarar shi ta bashi yasha har se ya qoshi snn ta goya shi idan da akwai aikin da take son yi.
Har bayan isha saif na nn ba'a maida shi ba,bcos hajjo da ta kawo shi kai tsaye ta koma,kuma dama waheed ne ze maida shi bai dawo ba se 9,wanda koda ya dawo duk a gajiya yake seda yayi wanka yaci abincin snn yayi zancen maida shi.
Nan fa bintu ta marairaice mishi bata son a maida shi tace"yaya dan Allah ka barshi tunda dare yayi kuma gashi na mishi wanka ya samu yin bacci, gobe da safe idan zaka je aiki se ka ajiye mu gidan mami idan ka dawo gurin aiki se ka d'auko ni mu dawo,inshaa Allah mami zata amince ka kirata ka gaya mata kaji yaya.
Waheed dake ta kallon d'an qaramin bakinta dake koro masa bayani,har ransa yaji dad'in soyayyar da take yiwa saif yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta yace"shikenan naji kar ki min kuka ba cewa zanyi a'a ba"
Cike da jin dad'i bintu ta rungume shi tana mishi godiya.
Tana manne a jikinsa ya tafi da ita kan bed suka zauna se kallon saif yake da yake ta sharar bacci abinshi,ya tambayi bintu ko ya mata kuka ta ce mishi a'a,kana ya zaro wayar sa a aljihu ya kira mami ya snr da ita tace ba komai ai da yau da gobe duk d'aya ne,bintu kuma ai mahaifiyar sa ce ta wuce ace kan saif ta nemi alfarma.
Sosai bintu taji dad'i da jin zancen mami ta d'auki saif suka tafi d'akin waheed,kmr yanda waheed ya buqata.
Washe gari da waheed ze je gurin aiki saida ya sauke su a gidan mami snn ya wuce gurin aiki.
Nan ta yini har se guraren six na yamma snn waheed ya dawo daga gurin aiki ya biyo ya d'auke ta suka koma gida.
Bintu ta kwana cikin kewar saif dan kwana d'ayan da yayi a hannunta da kuma yinin da tayi tare dashi a gidan mami yasa ta qara jin qaunar sa a ranta,sai dai bata sa damuwa a ranta ba tuna cewa za'a riqa kawo mata shi duk ranar da bata zuwa aiki.
3months later
Sosai saif ya shaqu da bintu kmr ita ta haife shi sbd kawo mata shi da akeyi duk lokacinda take free bata zuwa gurin aiki,wanda ya shaqu da ita ne sosai sbd irin kulawar da take bashi tana mishi wasa ko kad'an bata son taga cewa yayi kuka,hkn yasa musamman har d'aki ta ware mishi a gidan ta cika d'akin maqil da kayan wasa se abunda babu.
Waheed da mami ba kad'an ba suna matuqar jin dad'in irin kulawar da take bawa saif musamman hajiyar husna wacce ta tabbatar ko husna ce a raye iyakar kulawar da zata bashi knn.
Wayar bintu in ka duba duk fotunan saif ne,wani shi kad'ai,wani ita dashi da kuma wanda sukayi su duka uku tare da waheed,duk koina in ka ganshi bakinsa a washe se dariya yake dmn yaron akwai son fara'a sbd irin wasar da bintu ke mishi dole yaro ko kum kum kum ne ze sake ya fara sabawa da dariya.
Abunda ke damun bintu har yanzu ciki shiru duk wata bata fashin al'ada,ae kuwa duk lokacinda yazo mata ta shiga damuwa knn wani lokacin ma har kuka take se waheed ne zae zauna yayi ta rarrashin ta yana bata magana.
Da karshe ma har asibiti sai da suka je aka dubata ba wata matsala da mahaifar ta take d'auke da ita yanzu lokaci ne kawai bai yi ba.
Bayan wata d'aya da zuwan su asibiti ne,ranar wata assabar da dare waheed na zaune a d'akin shi yana kishingid'e kan bed yana kallon labarai.
Se ga bintu ta turo qofar d'akin a hankali tayi tsaye qwallah tap a idonta tana kallon shi kmr zatayi kuka.
Waheed da ya maida duban sa gareta da kulawa yace tazo.
Ba musa ta qarasa gurin shi ya tashi daga kishingid'en da yake ya kama hannunta ya zaunar da ita kusa dashi hannun sa kan cikinta yana kallonta yace"har yanzu gudawar ce cikin bai daina miki ciwo ba"
Muryar ta can ciki cike da son tayi kuka tace"har yanzu yaya abun ba sauqi se qaruwa yake kmr ma bana shan magani"
Cike da damuwa waheed yace"to Fatima me kikaci ne wai ya 6ata miki ciki haka?
Tace"ni yaya ba wani baqon abunda nasan naci face wnn new chocolate d'in da muka siyo kwanakin nn kuma bana tunanin shine tunda kaima kaci amma bai maka komai ba"
Yace"duk da haka dai fatima ki daina cin sa mu gani kinji"
A shagwa6e tace"yaya bafa shi bane yau two days knn rabona da cin sa amma ciwon cikin se qaruwa yake tayi"
Ta qarashe mgnr ne tare da fashe masa da kuka.
Cikin damuwa waheed ya shiga rarrashinta yace ta tashi suje asibiti, tace mishi um um ya bari taci gaba da shan magunguna tukun idan ciwon cikin bai daina ba snn suje.
Bai musa mata ba sae kwantar da kanta yayi zuwa faffad'an qirjinsa yana shafa gadon bayanta a hankli har tayi bacci.
Washe gari koda suka tashi gabad'aya jikin bintu ya gashe yayi zafi sosai wacce kwata kwata cikin dare ciwon ciki bai bar tayi bacci ba,safiya na wayewa kuma sae amai komai taci kai tsaye take amaryar dashi baya tsayi,shiyasa waheed duk yabi ya damu ga bintu ta sashi a gaba se kuka take mishi yunwa take ji,ya rasa me zai mata tunda ba abinda take ci ya tsaya mata,se mami ya kira ya snr da ita halin da suke ciki,tace mishi gata nn zuwa su tafi asibiti.
Kasancewar bintu jiri take gani bata iya miqewa tsaye da kanshi ya mata wanka ya shirya ta mami na zowa suka tafi asibiti.
Cike da farin ciki suka dawo gidan sbd kyakkywan labarin da suka dawo dashi wato juna biyu ne da bintu na tsawon wata d'aya.
Duk da irin jin jikin da bintu keji kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsantsar farin ciki, sam ta kasa 6oye murnar ta bare shi waheed uban aiki duk yafi su farin ciki dan babban burin sa shine yaga fatimar shi ta haifar mishi.
Da dawowar su ne mami na cike da murna ta cire mayafinta ta ajiye ta fad'a kitchen dmn girkawa bintu abinda zata samu ta d'an saka a cikinta.
Faten dankalin turawa ne ta mata da aka watsa wake a ciki sai qoda da aka yanyanka gutu gutu yayi kyau har ya gaji se qamshi ke tashi tazo da kanta tayi zaune tana bata har se da tace ya isheta.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 47_*
Cikin ikon Allah kuwa se bata amaryar da abincin ba,mami ta 6alla mata magunguna tasha.
Snn ne fa akayi zancen kiran kowa aka sanar dasu,ae kuwa kowa se murna yake yana fatar Allah ya bada rayayye mai albarka.
Kowannen su:
Umma,su anti Hafsa,Abdallah da Abbas duk se da suka kira bintu suna taya ta murna tare da mata kyakkyawar addu'a.
Bayan nn ne mami ta tafi gida.
Tunda mami ta bar gidan bintu ke bacci kan jikin waheed se zuhur snn ta tashi sukayi sallah sukaje kan dining dmn cin abincin da mami ta aiko musu dashi.
Dambun shinkafa ne da yayi matuqar kyau,wanda yaji ganyen zogale sosai da kayan lambu had'a da fried meat da akayi cutting d'insa gutu gutu aka watsa akai se qamshi ke tashi.
Ai kuwa sosai bintu taci danbum dan ba kad'an yayi dad'i da taushi har ya gaji.
Kmr kar su kammala cin abincin ko kan dinning basu sauka ba bintu ta soma jin wani bacci,a d'an shawa6e ta kalli waheed dake share bakin sa da tissue,kafin tace komai ya ajiye aikinda yake,da kulawa ya shafo gefen fuskarta yace"amai?
Tace"um um wai bacci"
Kike ji?
Waheed ya tambaya.
Ta gyad'a masa kai yace ta tashi muje d'akina koh.
Ya fad'i hakane tare da kama hannunta tana manne a jikinsa har suka isa d'akin shi,dashi har ita sukayi baccin su suna rungume da juna har sae la'asar snn suka tashi.
Da dare bayan isha'i guraren qarfe tara waheed ne ya shigo d'akin bintu ya same ta zaune kan bed d'aure da farin towel a jikinta,ta d'auko rigar bacci bata riga tasa ba tana ajiye kan cinyoyin ta tana waya d'auke da alamar jin kunya a fuskarta.
Yana tsaye har ta gama waya snn ya qarasa gurinta ya zauna gab da ita tare da kai hannun sa kan cikinta yana shafawa a hnkli cikin natsuwa yana kallonta yace"da wa ake waya ana jin kunya haka?
Murmushi tayi tare da fad'in"Abba ne fa ya ma ce a gaida ka"
Yace"ina amsawa snn ya d'aura da cewa"ya jikin naki to?
Sai da ta rufe fuskarta da tafukan hannayen ta snn tace"ae murna da farin yasa komai ya tafi yaya,bana jin duk wani ciwo a jikina yanzu"
Waheed dake kallonta d'auke da murmushi ya janye hannayen ta daga kan fuskarta yana kallonta yace"har da ciwon ciki duk ya tafi?
Tace"eh ya tafi"
D'auke da jin dad'i ya shafi fuskarta snn yakai hannun sa kan towel d'in jikinta ya kwance d'aurin snn a hnkli ya yaye towel d'in daga kan qirjinta idon sa qyar kan albarkatattun qirjinta da suke tsaye qyam a jikinta gasu sumul sumul masu kyau da fad'i,yasa tafin hannun sa a natse yana shafa su kana ya kalle ta yace"my lady na fahimci duk cikinda kikayi samu a baya kina ciwon qirji mae wahala Allah yasa wnn karon kar kiyi"
Amin cewar bintu wacce tana kallo waheed ya qarasa zare mata towel d'in jikinta ya saka mata rigar bacci snn ya kama hannunta suka tafi d'akin shi.
Washe gari tunda suka tashi sukayi sllr asuba bintu ta koma bacci,a cikin baccin ta ne ta soma jin gwalanniyar saif yana rairafawa kan gadon ze zo gurinta.
Nan ta tashi daga baccin ta miqe zaune d'auke da murmushi tana kallon sa ta tara masa hannu,shi kuwa da saurin sa ya rairafo ya qaraso gurinta,ta d'auke shi ta d'aura shi kan cinyoyin ta se kallon sa take tana shafa kansa cike da zallar so,kana ta maida duban ta gun waheed dake tsaye hannuwan sa kan qugunsa yana kallon su d'auke da d'an murmushi a fuskar sa,
tace"Hajjo tazo knn ina bacci?
Yace"um um naje kar6o mana breakfast ne ya ajiye min kuka se nazo dashi,shine da shigowar mu yana ganin ki kwance kina bacci ya matsa min se na sauke shi yaje gurin ki.
Murmushi bintu tayi tare da kallon saif wanda ya kama zaren rigar baccin jikinta se wasa yake dashi,ta rankwafa gab da fuskar sa ta lotsa en yatsun ta kan kumatun sa cikin dadda d'ar murya me jan hankalin yaronda ake yiwa wasa tace"my saif habibee i really miss u jiya duk ba'a kawo min kai ba"
Ta qarashe mgnr ne tare da d'aura masa kiss kan goshi snn tasa tsinin hancinta tana goga shi a hnkli kan nashi.
Nan kawai ya shiga gwalanniya yana mata dariya hannun sa kan fuskarta yana son ta6a tsinin hancinta da take mishi wasa akan nashi.
Waheed dake kallon su wani tsabar sonta ne yaji ya qaru a cikin ranshi,ya qarasa gurin su d'auke da murmushi ya zauna gab da ita yace ta kawo saif se taje tayi wanka suci abinci.
To tace mishi, yakai hannu ze d'auki saif da saurin sa ya maqalqale bintu bazai je ba da qyar bintu ta lalla6ashi yaje snn ta tashi ta shiga bathroom.
Saif dake hannun waheed ya le6ace baki yana kallon bathroom d'in cike da son yin kuka yana son zame wa daga jikin waheed ya sauka ya tafi.
Hakan yasa waheed ya fita dashi yana lallashin sa suka bar d'akin dan yasan idan ta fito bazai barta ta shirya a natse ba.
Falo ya tafi dashi ya d'auko masa kayan wasan sa ya zube masa su a nn tsakiyar falon,ya ajiye shi sae wasa yake tayi abinshi,
waheed yaje yayi zaune kan doguwar kujera 3seater se kallon sa yake yana jin kmr ace bintu ce ta haifar masa shi, take kuma yaji tausayin Husna baiwar Allah bata ji ba bata gani ba sun rabata da duniya,a hnkli ya girgiza kansa yayinda a ransa yake mata addu'ar Allah ya ji qanta yasa aljannar fiddausi ce makomar ta Amin.
Ba 6ata lokaci bintu tayi wanka ta shirya ta fito ta sami saif se jefawa waheed kayan wasan sa yake waheed na maida mishi yana ta dariya wanda yana ganin ta da gudun sa ya rairafo yazo gurinta, ta d'aga shi cak se wuntsil wuntsil yake da en qafafuwan sa cike da jin dad'i yana qyalqyatar dariya.
Cilla shi ta ci gaba dayi tana mishi wasa har ta qaraso gun waheed ta zauna kusa dashi tare da d'aura saif kan cinyoyin ta ta zaunar.
Fuskar ta d'auke da shagwa6a tana kallon waheed tace"waih! yaya kaji irin yunwar da nake ji kmr an min yaso bayan cikin dare zuwa asuba tashi na uku ina shan fresh milk amma se gashi ji nake kmr nayi sati banci komai ba wlh,babyn nn naka koh in ya fito nida shine ko ita.
Ta qarashe mgnr ne cike da shagwa6a.
Waheed dake kallonta cike da so ya shafo cikinta yana fad'in"babyna er gold ce me kama dake ba wanda ya isa ya ta6a min ita kiji in gaya miki"
Ya qarashe mgnr ne tare da jan karan hancinta snn ya d'auki saif yace tashi muje muyi breakfast kar yunwa ta illata min ke.
D'auke da murmushi bintu ta tashi suka je sukayi breakfast.
Suna kammala breakfast ne waheed ya fita agurguje zuwa aiki dan ya makara,bintu kuwa off take satin ta gama night tana hutu kafin ta fara morning.
Da dare suna kwance kan bed a nn d'akin waheed da ya kasance luf luf ba wani haske sosai,cikin shirin su na bacci,bintu na manne jikin waheed hannunta cikin rigar shi se shafa faffad'an qirjinsa take sannu a hnkli har taje da hannunta inda yafi matuqar so ta ta6a a jikinsa tana ci gaba da shafar shi a hankli cikin natsuwa kmr mai shafa qwai,waya waheed keyi amma gabad'aya ya rasa natsuwar sa dan salon da bintu taci gaba da mishi a gurin ya wuce sanin mai karatu,ae kuwa a gaggauce ya gama wayar ya kifadda ita kan bedside drawer.
Jikin sa na rawa ya janyo bintu ya had'e bakin sa da nata, tare da mirginawa kan jikinta ya mata rumfa ya tura hannun sa cikin rigar ta yana wasa da dukiyar fulanin ta,d'akin yayi tsit qarar komai baka ji se saukar numfashin su da ke fita a hankali suna ci gaba da romancing d'in juna cike da qwarewa har suka je ga babban aiki.
Bayan sun samu gamsuwa ne bintu na kwance kan faffad'an qirjin waheed idanuwanta a lumshe se sauke numfashi take a hankli tana shafa jikin shi yayinda take qara jin wani irin qaunar sa a ranta sbd ba kad'an ba a fagen kwanciya waheed cikakken namijin gaske ne da iya sarrafa mace fiye da tunanin me karatu.
Haka shima waheed idanuwan sa a lumshe yana shafa gadon bayanta cike da natsuwa yana ji a ransa kaf duniyar nn babu wata macen da takai mishi fatimar shi dan sosai take mishi yanda yake son mace ta kasance mishi,shiyasa duk lokacinda ya kasance da ita wani irin nishad'i yake ji a cikin ransa.
"Ina sonki My lady"
waheed ya fad'a a natse cikin dadda d'ar murya,bintu ta bud'e idanunta ta a hankli ta d'ago daga kan jikin sa kad'an tana kallon shi d'auke da murmushin jin dad'in kalmar da ya fad'a,ta d'aura masa kiss a hankali kan lips d'insa snn tace"Luv u more"
Kissing d'inta yayi shima kan lips d'inta snn ya maida kanta kan faffad'an qirjinsa ya kwantar yana shafar gadon bayanta d'auke da murmushi a fuskar sa,itama fuskar ta d'auke da murmushi take shafa jikin shi a haka har sukayi bacci abin su.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 48_*
Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwar su cike da qaunar juna,kullum mami ke aiko musu abinci,bintu iyakar ta ta gyara gidan ta tafi zuwa asibiti gurin aikinta,sam cikin baya bata wahala se yawan bacci da take yi da kuma saurin jin yunwa.
shiyasa har asibiti mami ke tura hajjo ta kai mata abinci da duk wani abinda mai ciki ke so na qwalama bintu bata rasa shi ba,a gida take ko asibiti duk mami na aika mata.
Ba kad'an ba bintu na jin dad'in yanda mami ke bata matuqar kulawa haka,shiyasa kullum qaunar mami se qaruwa take a ranta yayinda take jin kaf cikin mata tafi kowa sa'ar uwar miji mai qaunar ta da gaske da ta d'auke ta tamkar er ta ta cikin ta.
Ranar wata juma'a da yamma bintu na kwance kan doguwar kujera a nn falo tana fmn sharara bacci,can a cikin baccinta ta soma jin knocking da qyar ta tashi cike da jin bacci taje ta bud'e qofa,ihun murna ta saki ta qanqame Fadila dake tsaye a bakin qofar,suka shigo ciki se murna bintu keyi da ganin ta taje ta kawo mata ruwa da lemu bayan tasha bintu ke tambayar ta ina Humaira cewa da er ta.
Fadila tace"hm humaira na can gida tare da Abbanta na bari kinsan tafi liqe mishi a kaina"
Bintu tace"yayi su Humairan dady har da zaki fito anguwa ma baza ta biyoki ba"
Tace"um um ai ita ta daban ce Abbanta dai in zai fita take liqe mishi se yaje da ita amma in nice ba ruwanta.
Bintu tace"Allah sarki,shikenan kuna can bauci kun bar mu nn sokoto se yanzu aka leqo mu saukar yaushe to?
Wlh jiya muka zo shine yau nace ya kamata inzo in qara janjanta miki kan abubuwan da suka faru.
Bintu tace"wlh kuwa ae yanzu Alhmdlh komai ya wuce"
Fadila tace"Hm ai ni su zeenah sun bar ni da mamaki matuqa wlh"
Bintu tace"Hm bari kawai ae suna can Allah ya nuna musu abinsu"
Fadila tace"wlh kuwa shine aka ce idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi kad'an dan wata ran zaka iya fad'awa,gashi kuwa sun fad'a tsumbul"
Bintu tace"ai kuwa Allah de ya kyauta ya qara tsaremu da maqiyan mu na kusa da na nesa"
Fadila tace"Amin, waheed fa ya qarin lafiyar jikin nashi?
Bintu tace"Wlh tuni yaji sauqi yana ma gurin aiki yanzu haka,amma ya kusa ya dawo.
Tana kaiwa nn suka ji knocking Fadila tace"ko shine ya dawo?
Bintu tace"um um bana jin shine dan banji shigowar motar shi ba.
Nan bintu taje ta bud'e qofa,hajjo ce tsaye a bakin qofar yayinda basket d'in abinci ke ajiye a gefenta wanda ta ajiye shi ne a lokacinda zatayi knocking,sbd d'auke take da saif a hannunta wanda yana ganin bintu ya tafi jikinta ta amshe shi tana fad'in"my saif habibee"
suka shiga ciki se wasa take mishi,hajjo ta bisu d'auke da basket d'in abinci wacce saida suka gaisa da Fadila snn taje ta ajiye basket d'in kan dinning ta wuce.
Nan bintu ta miqawa Fadila saif tace"kinga d'ana da Husna ta haifarwa yaya"
Fadila ta kar6i saif tana kallon sa tace"Allah sarki kamar sa sak da waheed a hannun ku yake zama?
Um um a hannun mami yake zama nasan da yaga hajjo zata kawo mana abinci ya ajiye mata kuka se tazo dashi, dan haka yake in yasan gidan nn zaka zo tofa se kazo dashi se dai idan baiga lokacinda zaka fita ba ko kuma yana bacci.
Fadila tace"Allah sarki duk da ba gurinku yake ba amma ya saba daku haka"
Bintu tace"wlh kuwa kawo shin da akeyi ne yana min yini rnr da nake free bana fita aiki.
Fadila tace"au kin san na manta sam da aiki kike fita ashe naci sa'a da nazo na same ki a gida"
Bintu tace"wlh kuwa yau morning nayi shiyasa ma kika sameni da yamman nn"
Fadila tace"Allah sarki ina sha'awar aikin asibiti,amma kuma meyasa mami take aiko muku da abinci ba kyada lafiya ne?
Bintu tace"lafiya ta qalau kawai tunda na sami ciki ta d'auke min yin abinci tana aiko mana"
Fadila tace"haba dan Allah!yanzu ciki ne dake shine baki gaya min ba"
Er dariya bintu tayi tace"ramawa ce ke ba kya kiran mutum sae da lalura shine nima nace sai na haifu snn ko zaki ji"
Hm lallai bintu kinso ki shammace ni da yawa,wae dan Allah da gaske kike ko wasa kk min?
Hm fadila knn wlh Allah da gaske nake gaya miki yanzu cikin ma har ya kai 4months.
Kai amma mami na son ki da yawa shine ta d'auke miki yin abinci tana ta aiko miki.
Bintu tace"wlh kuwa ba yanda banyi ba kan ta daina d'awainiya dani haka zan iya tunda cikin baya bani wahala,amma sam taqi amincewa wai aiki yamin yawa ga ciki ga gyaran gida ga zuwa gurin aiki.
Fadila tace"Allah sarki gaskiya ke kam kinyi sa'ar uwar miji me sonki,ba kmr mu ba da kan masifar ta ne yasa na bisa can bauci gurin aikin sa, amma kuma yanzu Alhmdlh na fara sayeta dan duk zamu zo ganin gida se kinga tsarabar da nake tilo mata kmr bansan ciwon kud'i ba,ai kuwa tayi ta murna tana jin dad'i har da su samin albarka.
Murmushi bintu tayi tace"kinyi dibara Allah ya qara dai dai ta tsakanin ku"
Fadila tace"Amin"
Nan sukaji qarar bud'e gate waheed ya dawo,da murna bintu ta fita taje ta tarbo shi suka shigo,se bayan ya gama gaisawa da fadila ne snn ya wuce daga ciki janye da saif a hannun shi sbd yana ganin waheed ya shigo ya sauka kan jikin fadila ya tafi gurin shi wanda yanzu watannin sa 8cikin na9 amma tun yana da 7months ya iya tafiya abinshi.
Bintu dake rataye da jakar waheed bata riga ta bisu ba tace"fadila ina zuwa dan Allah"
Fadila ta tashi tare da fad'in"Aa aini tafiya ma zanyi yanzun"
Bintu tace"haba fadila meye haka nida nake son da na kai masa jakar sa na dawo na d'ibar mana abinci muje d'akina muna ci muna fira,indai yaya waheed ne wlh yanzu fita zaiyi da anyi sllr magrib bazai dawo ba se bayan isha'i.
Fadila tace"kar ki damu ai karon nn zamu jima kafin mu koma bauci,a duk lokacinda kk free waheed baya gida zan sake dawowa amma fa se in kinje tukun dan bazai yiyu ina yawon hanya ni kad'ai ba.
Murmushi bintu tayi tace shikenan da yardar Allah kuwa zaki ganni in miki yini zungur.
Fadila tace"Allah yasa da gaske kk"
Bintu tace"Allah da gaske nake miki"
Tace"to shikenan Allah ya kaimu ina sauraren zuwan ki"
Nan suka fita bintu ta rakata wacce tana dawowa bata zarce koina ba se d'akin waheed.
Ta sami waheed zaune kan sofa yana rage kayan jikin sa,yayinda saif ke zaune gefen sa yana cin biscuit wanda waheed ne ya bashi.
Kai jaka tayi a mazauninta ta ajiye snn ta d'ebo masa fresh milk mai sanyi a cup kmr yanda yake buqata idan ya dawo se yasha fresh milk snn yaje yayi wanka.
Dai dai ya kammala rage kayan jikin sa ta bashi fresh milk d'in ya kar6a,snn ta d'auke kayan da ya cire takai su a muhallin su,ta dawo ta zauna nn kan sofa kusa dasu.
Saif ya d'aura kansa kan cinyoyin ta ya kwanta abinshi yana ci gaba da cin biscuit d'inshi,ita kuma se shafa kansa take a hankali tana kallon shi.
Bayan waheed ya gama shan fresh milk ne yake tambayar bintu hln fadila ta wuce ne?
Tace masa eh ta wuce,ina ma son dan Allah ka barni inje gidan ta kafin su koma"
Yace"ba matsala duk lokacinda kk free kina iya kije"
Tace"olryt thank u"
A nn waheed ya shafi gefen fuskarta ya tashi ya fad'a bathroom yayi wanka ya fito ya shirya cikin farar jallabiya yaja saif suka fita zuwa sllr magrib.
Wa enda kafin su fita sae da bintu ta tambayi waheed ko zae dawo kafin sllr isha'i suci abinci dan yunwa take ji yace mata eh ze dawo.
Bayan har sun dawo sunci abinci waheed ya koma fita tare da saif wanda bai dawo gidan ba se qarfe tara dan daga masallaci da yayi sallr isha'i ya wuce gidan mami ya maida saif suka d'an ta6a fira da mami snn ya dawo.
Se bayan sati biyu da zuwan fadila gidan ne snn bintu ta sami lokaci taje gidanta ta mata yini kmr yanda tace,se da yamma snn ta dawo.
Ta sami waheed a farfajiyar gidan yana kwance kan kujerar hutawa me kmr camp bed yana shan iska.
Da murnar ta ta fito mota ta isa gurin shi ta zauna,waheed da koda ta qaraso gurin shi ya tashi zaune,yana kallonta d'auke da murmushi yace"wnn murnar ta mece ce haka my lady?
Leda ta miqa mishi tare da fad'in"duba kaga abunda na samo shine nake ta murna na matsu ban dawo gida na fara sha ba"
Koda waheed ya duba ledar,qanqarar nono ce cike a ciki, ya girgiza kansa yace"oh oh my lady a ina kika samo wnn?
Tace"gidan fadila mana da naje"
Yace"haka kawai take yin qanqarar tana sha ko me?
Aa saidawa ake a maqotan su,mun fito ne ta rakoni zan shiga mota naga Humaira ta dawo da siyen qanqarar tana sha,shine nace ina so ina ake saidawa, shine tasa aka siyo min mai yawan nn dan in zuba a fridge duk lokacinda nake buqata in riqa d'auka kawai ina sha.
D'an guntun tsaki yayi yace"Haba my lady shine har da murna wai kin samo qanqara a lokacin sanyin nn,bayan kinsan ba ke kad'ai bace da baby a jikin ki"
Tace"yaya to ai babyn ne yasa naji ina ra'ayinta,dan wnn kwad'ayi ne kawai irin na masu ciki ka sani.
Yace"To kiyi haquri ki had'iye kwad'ayin,dan nikam bazan barki kisha wnn qanqarar ba ki illata min baby"
Sosai ta marairaice fuska tana fad'in"haba yaya dan Allah kar ka min ka wlh Allah ba kad'an ba na sata a raina"
Yace"kiyi haquri fatima bazan iya barin ki kisha wnn qanqarar ba gaskiya"
Nan kawai ya shiga kiran gateman,gateman yazo da hanzarin sa waheed ya miqa masa ledar qanqarar gabad'aya yace je ka kyautar.
Kafin gateman ya kar6a Bintu ta riqe ledar tana kallon waheed kmr zatayi kuka tace"dan Allah yaya ko kad'an ne ka sammin inji sauqi.
Waheed bai saurare ta ba se janye hannun ta yayi daga riqon da tayiwa ledar ya miqawa gateman,qwallah tap a idonta tabi gateman da ido har ya fita daga gidan.
Nan kawai ta kalli waheed tare da fashe masa da kuka ta tashi ta bar gurin se kiran ta yake tazo ta gaya mishi me take so ya siyo mata,amma bata saurare shi ba taqi dawowa dan haushi ma ya qara bata.
Zaman sa yayi bai bita ba dan yasan ko yaje ba saurarrar shi zatayi ba se da akayi sllr magrib snn ya tashi ya shiga ciki yayi arwalla ya wuce zuwa masallaci.
Bashi ya samu ya dawo gidan ba se kusan qarfe tara.
Kai tsaye gun dining ya wuce sbd yunwa yake ji,koda yaga abincin bintu bata ci ba.
Tashi yayi dmn yaje ya lallaso ta tazo suci,se ya samu d'akin nata a rufe,haka da yaje d'ayar qofar wato ta cikin d'akin shi ya samu itama a rufe take,yayi knocking taqi ta bud'e mishi.
Ba yanda ya iya haka ya dawo yaci nasa abinci,bayan ya gama yaje yayi wanka yayi shirin bacci snn ya sake komawa a nn qofar da ke cikin d'akin shi yana ta mata knocking cikin rarrashi yana lalla6ar ta yana bata haquri kan ta bud'e qofa tazo taci abinci amma har ya gaji bata bud'e ba.
Jiki sanyaye yaje kan bed ya kwanta idanuwan sa a lumshe yana jin kansa cike da buqatuwar son kasancewa da ita, dan a yanda yake jin dad'in kasancewa da bintu,duk dare idan ba ya neme ta ba sam baya jin dad'i,lalura ko rashin lafiya kawai kesa dole ya haqura.
Haka yayi ta juyi shi kad'ai kan bed ya kasa bacci yana ta sauraren ko zata fito taci abinci amma shiru har 11 ba alamar zata fito,hkn yasa duk yabi ya qara shiga damuwa ya janyo wayar sa yayi ta kiran layinta amma taqi d'agawa,da qarshe ma se ta kashe wayar ta gabad'aya.
Sosai ransa ya 6aci wanda da qyar yaga safiya ta waye mishi.
Da gari ya waye se guraren qarfe goma Bintu ta fito riqe da er travelling bag a hannun ta zata fita, waheed dake zaune a falo zata wuce shi yace"ina zaki je?
Cak bintu ta tsaya a ranta tana mamakin wace irin tambaya yake mata wnn bayan yasan da mgnr yau kebbi zasu je ita da su anti Hafsa bikin auren wata er uwar su da za'ayi.
Tana kallon sa ya taso yazo gurinta shaye da toka yana kallonta yace"ina zaki je nace?
D'auke da mamaki tace"yaya kmr ya ina zanje ka manta yau ne zamu je kebbi nida su anti Hafsa bikin auren wnn er uwar tamu da za'ayi"
Yace"to ba inda zaki je,tunda kin nuna min ni ban isa inyi abinda yake dai dai akanki ba,shikenan se ki d'auki yin fushi dani.
Cikin muryar kuka tace"Haba yaya wane irin abune ka daki mutum kuma ka hana mishi kuka, gaskiya bazai yiyu kace bazan je bikin nn ba wlh.
Yace"ok tunda bazai yiyu ba ai kagi ga hanya se kije d'in,idan kuma har kina ganin da akwai wanda ya isa yasa na barki dole kije se kije ki gaya mai"
Bintu dake kallon sa kuka ta fashe dashi,ta saki jakar hannun ta a fusace ta fita daga falon taje taja motar ta ta bar gidan bata zarce koina ba se gidan mami.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 49_*
Tana shiga gate d'in gidan shima waheed na kunnowa da tashi motar dan biye yake da ita.
Blocking d'insa tayi bata bar ya qarasa shigowa gidan ba dan ta fahimci sauri yake ya hanata isa gurin mami.
Shiyasa tana blocking d'in sa bata tsaya wata wata ba ta fito cikin mota da sauri ta shiga cikin gida,dai dai mami ta fito daga kitchen ta tafi jikinta tana kuka.
Kafin tace komai se ga waheed ya shigo gidan d'auke da dariya yana fad'in mami dan Allah kar ki saurare ta rigima ce kawai take ji yau.
Bintu dake jikin mami tana kuka ta d'ago tace"wlh mami ba wani rigima shine dai yake jin fad'a tun jiya,na samo qanqarar nono ya hana min insha snn yau har na fito zan tafi gidan anti Hafsa mu wuce kebbi yace ba inda zanje kuma bansan me na mishi ba.
Mami ta kalli waheed tace"gaya min meye dalilinka me ta maka,ko shikenan dan ka fita waje an 6ata maka rai se ka dawo gida kana saukewa akanta haka aka ce maka anayi.
Waheed yayi murmushi yace"calm down mami abinda ta fad'a bafa haka bane,ni jiya ba wani fad'a da nake ji,ita dai kejin rigirma se kinga qanqarar nonon da ta kwaso cike tap da leda ba sauqi,wai zata zuba a fridge ta riqa sha bayan tasan ba ita kad'ai bace da baby a jikin ta,shine dan na hanata sha ta zo tana fushi dani har ma taqi taci abinci tun jiya har yau,wato tunda nace bazata sha qanqara ba kar ta illata min baby shine taqi cin abinci babyn ya dad'e bai illata ba!.
Bintu dake kallon sa kwallah tap a idon ta cikin jin ciwon abinda ya fad'a tace"haba yaya wace irin magana ce kuma wnn....rai 6ace waheed ya nuna ta da yatsa yace"wlh yi min shiru me kk nufi idan ba haka ba!
Bintu da hawaye suka silalo kan kumatun ta ta kalli mami tare da girgiza kanta tace"wlh ba haka bane mami,koda na dawo gidan ciki na a cike yake naci abinci a gidan fadila da naje snn kafin na kwanta sai da nasha tea haka ma da safen nn,kuma fushin da nayi dashi ko kad'an banji dad'in da ya hanamin shan qanqarar nonon nn ba sosai na sa ta a raina,naso ko qwara d'aya ce de ya bani insha amma yaqi ina kallo ya bawa gateman wai yaje ya kyautar.
Mami tace"Haba waheed baka kyauta ba,ka kuwa san irin abinda mai ciki ke ji idan aka hanata abinda taso,fisabilillah dan baka sani ba se ka hanata tana ji tana gani ko qwara d'aya dai kabata taji sauqi amma kaqi"
Cikin damuwa yace"mami halin fatima ne na sani in na barta ta fara shan qanqarar na tabbatar zata liqewa shan qanqarar knn ba sauqi har taje ta cutar min da yaro ko 'ya"
Mami tace"uhm to me yaro ko 'ya naji wnn,se ka gaya min meye dalilinka na cewa bazata je kebbi ba bayan kasan biki ne zasu je kuma kasan da bikin tun ba yau ba.
Yace"mami a gabana fa yarinyar nn dan ta raina ni ta fito zata wuce ko gefen da nake zaune taqi ta kalla wai fushi take dani"
Mami tace"to yi haquri ka barta ta tafi kaji ba dad'i en uwa kowa yaje bata je ba"
Yace"mami dan Allah ki barni da ita kawai zan ga in rainin wayon ta zai sa in barta taje"
Kallon sa bintu keyi qwallah tap a idonta.
Wanda yana kai qarshen zancen sa yasa qafa ya bar falon ba tare da ya tsaya jin me mami zata ce ba.
Mami ta kalli bintu dake share hawayen da suka zubo mata tace"kar ki damu jeki kebbi kawai abinki ni na baki izini banni dashi.
Bintu tace"Aa mami ki barshi kawai zan zauna tunda baya so inje, inaga haka shine yafi alkhairi"
Mami tace"Aa bikin nn fa inshaa Allah se kinje jeki kawai gida da kanshi zai zo ya kaiki har kebbi kinji.
Godiya bintu ta mata yayinda mami da kanta ta rakata har mota ta shiga ta wuce snn ta koma cikin gida ta kira waheed a waya tace ya dawo tana son ganin shi.
Waheed da har ransa ba da gaske yake son hana bintu zuwa kebbi ba,ya mata hakane kawai dan ya rama fushin da tayi dashi jiya ta barshi ya kwana cikin matuqar buqatuwa da kewar ta,bai musa ma mami ba ya koma, ta sashi a gaba tana lalla6a shi tana bashi magana dan tasan halin d'an nata ya kan jima kafin yayi fushi irin wnn amma kuma duk rnr da yayi abun ba sauqi sei da lallami ake shawo kanshi.
Bayan Bintu ta koma gida tana zaune a d'akin ta kan bed ta had'e kai da guiwa,tana jin wayar ta se faman ringing take amma taqi d'agowa bare ma zancen ta d'aga kiran,dan anti Hafsa ce keta faman kiranta bata kuma san me zata ce mata ba idan ta d'aga.
Qarar bud'e qofar da taji ne yasa ta d'ago kanta a hankli, waheed ne ya shigo d'akin riqe da er wata leda a hannun shi ya qaraso gab da ita ya zauna yana kallon ta,ta kauda fuskarta tare da saurin share hawayen da suka zubo mata.
Waheed yakai hannun sa kan wayar ta da ke ta ringing,ya d'aga yaji anti Hafsa se fad'a take bintu ta 6ata musu lokaci,sosai ya bata haquri yace su tafi kawai shi zai kai Bintu kebbi.
Bayan sun gama wayar ne ya janyo ledar da ya shigo da ita ya bud'e,qanqarar nono ce da akayi sealing mai dad'in gaske.
Bintu se kallon qanqarar take a ranta tana mamakin ina ya samo.
Kmr waheed yasan meye a ranta yace"mami na tambaya inda zan samo miki qanqarar nono shine ta gaya min naje na siyo miki"
Yayi mgnr ne yana mai kallon ta snn ya d'auki qanqara d'aya yasa bakin sa ya bud'e mata inda zata tsotsa tasha ya bata.
Bata kar6a ba se kallon sa kawai take kmr yau ne ta fara ganin sa.
Waheed dake kallonta a natse ya janyo ta zuwa jikinsa se rarrashinta yake har ya samu ta yarda ta kar6i qanqarar tasha,snn suka shirya suka kama hanyar zuwa kebbi.
Kan hanya cikin mota se fira suke suna wasa da dariya irin na mata da miji tamkar ba abinda ya faru a tsakanin su har suka isa garin kebbi.
Koda suka isa sun samu Anti Hafsa tuni sun iso har sunci abinci.
Bayan an gama murnar ganin juna da gaishe gaishen da ake na bayan rabuwa umma ta bawa bintu abincin su ita da waheed suka je d'akin Abbas.
A nn tsakiyar d'akin kan center carpet bintu ta jiye musu abincin suka zauna suna ci cike da nishad'i.
Suna kammala cin abincin waheed ya tashi yaje ya rufe musu qofar d'akin da makulli.
Bintu da bata riga ta tashi daga inda suka ci abincin ba, ta bisa da ido dan bata san dalilin sa na rufe d'akin ba,tana kallo yaje ya zauna kan bed ya cire rigar sa da singlet,hannun sa kan zip d'in wandon sa ze cire wandon ta tashi ta qarasa gurin shi ta zauna gab dashi tare da kama hannun sa tana kallon sa d'auke da alamar dariya a fuskarta tace"wae me zakayi ne yaya ka rufe d'aki kana faman cire kaya ko lafiya?
D'auke da murmushi yaja karan hancinta yace"ae se ki zuba ido ki ga me zanyi"
Komai bata ce ba se murmushi ta mishi tana kalo ya rage hasken d'akin snn ya qarasa cire kayan jikin sa,ya d'auke ta ya d'aura kan cinyoyin sa ya zaunar tare da kai hannun sa kan zip d'in rigar ta zai cire mata rigar.
Nan bintu ta d'aura tafukan hannayen ta a hankali kan kumatun sa tana kallon sa a natse tace"No yaya kayi haquri ba lokaci ka sani"
Shima tafukan hannayen sa ya d'aura kan kumatun ta yana kallon ta idon sa a cikin nata yace"bazan iya haqura ba my lady inada buqatar ki sosai kinga komawa zanyi ki tausaya min.
Zata sake magana knn taji harshen sa a cikin bakin ta ya hana ta cewa komai sai tsutsar lips d'inta da yake.
Tana ji ya cire mata tufafin jikinta hannun sa kan nonuwanta se shafa su yake,kana ya zare bakin sa daga nata ya maida kan qirjinta yasa harshen sa kan albarkatattun qirjinta yana mata wani irin salo mai wuyar fassarawa.
Bintu ta lumshe idanun ta tana jin kanta a cikin wani irin yanayin da ita kad'ai tasan yanda zata iya fassara abinda take ji,wacce tana son hana shi amma ina ta kasa se numfashi ta soma fitarwa a hankali cike da jin dad'in abinda yake mata,hannunta bayan kansa se shafa shi take har izuwa gadon bayan sa tana masa tafiyar tsutsa,ga qirjinta da take qara tura mai a hankli ta yanda zai fi jin dad'in ci gaba da abinda yake mata.
Ae kuwa gogan cikin kid'imewa yaci gaba da mata nashi salon yana kissing d'in jikinta ta koina,ita kuma se shafa jikin sa take snn a hnkli tana zamewa daga kan cinyoyin sa ta sauka ta gurfana kan guiwoyinta tare da rankwafadda kanta zuwa cikin sa tasa harshen ta cikin ramin ci biyar shi,a hnkli cikin tafiyar tsutsa ta tafi dashi zuwa tsakiyar cinyoyin sa tana masa wani irin salon da ya soma mantar dashi duniyar da yake,wanda a rud'e cikin kid'ima ya kwanta rigingine yana fitar da wani irin numfashi yana sambatu cike da jin dad'in abinda take mishi.
Da haka suka ci gaba da romancing d'in juna cike da enjoying har suka je ga babban aiki.
Suna cikin hutawa sun kammala abinda suke knn anti Hafsa ta soma musu knocking cikin kiran sunan bintu,bintu dake kwance jikin waheed tana sauke gajiyar da suka d'ebo,ta tashi ta nemi abu ta rufa jikinta snn taje ta tsaya a bakin qofar ba tare da ta bud'e qofar ba tace"Na'am Anti"
Anti Hafsa tace"wane irin abu ne daga cin abinci kin shantaqe kin bar mu tun d'azun muna jiranki muje kasuwa kinsan da hud'u tayi no African time lunch za'a wuce gashi har uku ta kusa,ko ba kya zuwa kasuwan ne mu wuce kawai?
Tace"Aa ina zuwa anti dan Allah ku d'an jirani gani nn zuwa yanzu.
Anti Hafsa tace"ok to dan Allah kiyi sauri"
Bintu tace"to"tare da saurin barin bakin qofar taje gun waheed dake kwance kan bed tace"yaya tashi fa wai har anyi zuhur uku na batun yi bamu sani ba"
Waheed da shima bai san lokaci ya tafi haka ba,ya tashi da hanzarin sa suka je sukayi wanka.
Suna fitowa wanka ne suka maida kayan jikinsu waheed ya kabbarta sallah,bintu kuwa kasancewar bata tare da hijab a gurin sai da taje cikin gida tayi tata sallr.
Tana ida sallah ta tofa addu'a waheed ya kirata a waya zai koma kebbi tazo yana son ganin ta.
Koda ta fito ta same shi a nn falo yana zaune kan doguwar kujera 3seater taje gab dashi ta zauna.
Envelope ya miqa mata mai cike da d'auri d'auri na sabbin kud'i a ciki dubu d'ari biyar yace ta bawa umma ta qara tayi hidimar biki dasu.
(sbd wacce za'a yiwa auren er qanwar umma ce kuma mahaifiyarta ta rasu,a can gurin mahaifin ta take zama wanda bawani qarfi ne dashi ba)
Bayan ya bata na umma snn ya koma bata wasu kud'in dubu d'ari uku yace ita kuma ga nata.
Duk da bintu tasan kud'in sunyi yawa bata nemi ya rage ba dan tasan halin sa ko kad'an baya son ta mishi haka har fad'a suna iya yi,shiyasa kawai ta masa godiya cikin matuqar jin dad'i dan sosai taji dad'i a ranta ba kad'an ba.
Tashi tayi taje ta kaiwa umma,umma tazo har nn falon ta mishi godiya tare da kyakkywar addu'a.
Bayan ta tafi ne bintu tazo ta rakashi har mota ya wuce snn ta koma suka shirya suka tafi kasuwa dmn siyo abubuwan da suke son siyo wa.
Saida sukayi kwana biyu ana events snn a rana ta uku aka d'aura aure da qarfe 12,su Abbas,Abdallah har waheed ba wanda bai zo d'aurin auren ba.
Sbd bikin se yayi kmr er umma ce ta cikinta ake yiwa auren dmn duk wani abu na hidimar da uwa ke yiwa erta shi umma tayi.
Sai da aka gama hidimar biki da komai snn su bintu suka dawo sokoto.
A rnr da suka dawo da dare bintu na kwance jikin waheed,dashi har ita ba komai a jikin su se farin bedsheets da suka rufa jikin su dashi yayinda d'akin ya kasance ba wani haske luf luf dashi.
Bintu da ke kwance jikin waheed tuni tayi bacci tana faman sauke gajiyar da waheed ya saukar mata.
Waheed kuwa bai riga yayi bacci ba se aikin shafar gadon bayanta yake a hankli cikin natsuwa,idanuwan sa a lumshe se tariyo dadd'ar zumar da suka fito yake,cike da qara jin son bintu a ranshi, yarinya da ita amma tasan duk wata hanya da zata gamsar dashi a fannin kwanciya,in ta mishi wani salon ma ji yake kmr zai zauce har ihu yi mata yake,se bayan sun kammala abinda suke se yayi ta tariyo abubuwan da suka faru a lokacin,yayi murmushi kawai cike da nishad'i a ranshi.
Ko yanzun ma da ya gama tariyo abubuwan da suka faru murmushi kawai yayi tare da d'aura mata kiss aka snn ya gyara mata kwanciyar ta, hannun sa kan d'an cikinta da ya fara tasawa yana shafawa a hankali har bacci ya d'auke shi.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 50_*
Guraren asuba yunwa ce ta farkadda bintu wacce ta tashi a hnkli ta zare jikinta daga na waheed ta lalubo rigar baccinta ta saka snn taje bathroom ta wanko bakinta ta dawo taje ta bud'e fridge ta d'auko fresh milk zata tsiyaya a cup,se jin tayi waheed ya rungume ta a hankli ta baya,ta d'an karka tadda kanta kad'an ta gefen sa ta kalle shi d'auke da murmushi,shima murmushin ya mata tare da d'aura hannun sa kan nata ya kama mata suka tsiyaya fresh milk d'in a cup.
Yana riqe da fresh milk d'in ya kama hannunta da d'ayan hannun sa ya tafi da ita suka zauna kan sofa,ya bata fresh milk ta kar6a tana sha se kallon ta yake har ta shanye ta ajiye cup,kana ya janyo ta zuwa jikin sa cike da so yana shafa cikin ta a natse yana kallonta yace"babyn nn nawa ya kyauta min"
D'auke da murmushi Bintu ta kalle sa tace"Dame?
Yace"Da yanda yasa kika daina wasa da cin abinci se kikayi 6ul 6ul kika qara wani kyau sae qyalli da sheqi kike ba kmr daa da cin qwalama ne kawai aikin ki ba.
Murmushi bintu tayi wacce ita kanta tasan hakane d'in,er qibar nn da ta qara ba qaramin kyau tayi ba duk wanda ya ganta se yayi magana.
Tace"ni kaina naji dad'in er qibar nn da nayi amma cin ne bana so wlh,shiyasa na cika shan fresh milk,bcos tauna ka had'iye d'in nn se inji ya zamar min wani aiki"
Waheed dake kallon ta d'auke da murmushi yaja karan hancinta yace"tunda ba qwalama bace ai kya fad'i haka"
Komai bata ce ba se murmushi tayi tare da qara shigewa jikinsa,tana jinsa se ci gaba yake da shafar cikinta,can yace ta tashi suje suyi wanka.
Ba musu ta tashi suka je sukayi wanka koda suka fito se kirayen kirayen sallah ake,waheed ya zira farar jallabiyar sa ya wuce zuwa masallaci.
Bintu kuwa ta nemi er doguwar riga mara nauyi ta saka, ta janyo hijabinta na sallah me kai mata har qasa tasa,snn ta shinfid'a darduma ta kabbarta sallah.
Bayan wata biyu da faruwar haka,cikin bintu ya fito sosai kana ganin shi, wacce ba kad'an ba ya mata matuqar kyau har kuri take da abinta in ta zauna ita kad'ai bata da aiki sai dai tayi ta shafar cikin cike da so d'auke da murmushi a fuskarta,yayinda kullum addu'ar ta Allah ya sauke ta lafiya ya kuma bata rayayye mai albarka.
Haka mami ko yaushe addu'ar ta knn wacce har yanzu ita ke aiko musu abinci,breakfast, lunch,dinner.
Kuma akai akai ta kan zo kawai ganin bintu duk da cewa kullum se ta kirata a waya taji lafiyar ta.
Da dare bayan isha'i,bintu ce zaune a falo ita da saif wanda ya d'aura kunnen sa kan cikinta se gwalanniya yake cikin maganar sa da ya fara iyawa wai yana magana da qanin sa ne,bintu kam se dariya take dan gwallaniyar sa akwai ban dariya,dagaske yake dagewa se yayi magana gashi kuma bai iya ba se yamin baki da yake.
Waheed ne ya qaraso gurin su ya zauna yana kallon saif yana dariya yace"kai baka iya magana ba kana cewa dole se kayi magana da qanin ka se damun mommy kake,tashi muje ka rakani yawo"
Ya qarashe mgnr ne tare da miqa masa hannu alamar yazo.
A shagwa6e saif ya maqale kafad'a bazai je ba,dan ganin yake kmr wayo waheed ke masa gida zai maida shi gun mami,dan yau kwanan sa uku knn gidan bai yarda an maida shi ba kullum yana maqale jikin bintu rungume da cikinta yake bacci baya son rabuwa da qanin shi.
Duk maitar waheed na son kasancewa da bintu duk dare haka yake haqura dan duk yanda yaso janye shi daga jikin bintu farkawa yake ya qara maqalqale ta.
Gashi yau kam waheed ko kad'an baya jin zai iya haqura shiyasa yake son fita dashi yawo daga can ya maida shi gun mami.
Nan ya nemi bintu da ta lalla6a mai shi ko zai yarda suje,bintu ta samu da qyar cikin lalla6i ya yarda,wanda har sun kai qofa zasu fita ya dawo da gudu ya d'aura mata kiss kan ciki ya wuce yana mata bye bye tana maida mishi d'auke da murmushi a fuskarta har suka fita.
A hankli ta jingina bayan ta da jikin kujerar da take zaune,ta lumshe ido tana shafa cikin ta a hankali cikin natsuwa,can ta tashi taje ta bud'e fridge ta d'auko yalo qwara d'aya,da mami ce ta aiko mata dashi me yawa,tayi zaune tana yanyanka qwara d'ayan da ta d'auka slice by slice tana ci.
Koda waheed ya dawo gidan bai same ta a falo ba,ya tafi d'akin ta ya samu ta fito daga wanka knn tana zaune gun dressing mirror tana shafa mai.
Qarasawa yayi gurinta ya rungume ta suna kallon juna ta jikin mirror,ta kai hannun ta ta shafo gefen fuskar sa tace"Saif fa ya kayi dashi?
Yace"garin yawon mu na samu yamin bacci a mota na maida shi gun mami nasan se ya farka ya ajiye mata kuka.
A sanyaye cikin nuna rashin jin dad'i Bintu tace"Ae kam nasan se yayi kuka dama ka dawo dashi kawai yaya"
Waheed yace"hm lallai my lady da kin san me nake ji ko na rana d'aya idan ban same ki ba da baza ki fad'i haka ba,amma idan na damqe ki yau zaki gane.
Yana kaiwa nn ya janye jikin sa daga nata d'auke da shu'umin murmushi ya kama hanya zai fita daga d'akin.
Bintu ta tashi ta riqo hannun shi ya juyo ta kalle sa a shagwa6e cikin marairaice fuska tace"plz yaya um um"
Maqale mata kafad'a yayi alamar yaqi d'in,snn ya zare hannun sa daga nata ya wuce abinshi,ta bishi da ido cike da so,ta rasa me yasa duk waheed yayi yanayin shagwa6a wani irin kyau yake qara mata,dan bata ta6a ganin namijin da shagwa6a ta masa kyau irin sa ba.
Se bayan ta gama shirinta na bacci snn taje d'akin shi,wacce da shigar ta d'akin taji alamun ze fito gurin wanka,nn kawai taje da sauri ta kwanta kan bed ta rufe ido kmr me yin bacci da gaske.
Waheed da ya fito daga bathroom riqe da d'an qaramin towel yana share jikinsa,yazo gab da ita ya zauna ya kalle ta se kawai yayi murmushi tare da girgiza kansa,dan se ta tuna mishi da lokacin farkon auren su rnr da aka kawo ta daga kawai yaje raka abokanan shi ya dawo ya samu tayi bacci,bai tashe ta ba dan a tunanin sa ko baccin gaske ne,dan ya d'an jima a waje abokanan shi na ta mishi tsiya.
Duk yanda yaso ya same ta a rnr haka ya haqura ya barta har kusan sati d'aya yana wahala da tsananin buqatuwar son kasancewa da ita,dan tun da taga tayi nasara a daren farko bai tashe ta ba,se taci gaba da yi mishi haka da zarar dare yayi taji zai shigo d'akin ta se tayi sauri ta kwanta ta rufe ido tayi baccin qarya,se ya fita snn ta tashi tana tsalle tana murna.
Rnr da ta cika sati tana cikin tsallen murna se ganin waheed tayi ya koma dawowa,ashe a lokacinda yazo ya samu tana bacci, yana fita daga d'akin se yaji ihun murnar ta shine ya dawo,ae kuwa sosai taji kunya tana tsaye ta kasa d'agawa ko ina sae sadda kanta tayi qasa har ya qaraso gurinta d'auke da murmushi ya jata zuwa jikin shi,wacce ba kad'an ba a daren rnr ta sha wahala a hannun shi dan seda ya kar6i haqqin sa.
Bayan ya gama tariyo hakan ne,still murmushi na kan fuskar sa yana kallonta yace"uhm gwanda ma ki tashi en mata idan kuma kinfi so se na fita ki tashi kina yin tsalle to"
Bintu ta bud'e idanun ta ta tashi zaune tana dariya tace"lah yaya ashe baka manta ba"
Yace"inafa zan manta kin tashi illata ni"
Bintu dake dariya ta bud'e ido tace"kae yaya na tashi illata ka ko dai ka tashi illata ni nida kasa nayi kwana uku ina faman shiga ruwan zafi,ba dan inada jiki mai kyau ba ai a yanda kaje min d'in nn da se ammin d'inki"
Waheed yayi dariya yace"kiji tsoron Allah fa my lady ni ba wata wahala da na baki raki ne kawai irin naki,kuma koma mene ne ai duk ke kika ja har na baki wahala"
Tace"hm bari kawai yaya rnr koh ji nayi kmr zan mutu wlh,baka ji irin zafin da naji ba,har na d'auka ma baka sona kwata kwata ka aure ni ne kawai dan wnn abun shiyasa baka tausaya min ba duk da kukan da nake ta maka"
Ta qarashe mgnr ne cikin turo baki tana kallon shi.
Waheed yayi murmushi dan yana iya tuna lokacin har fushi tayi dashi tana ta mishi kuka ita se ya maida ta gida,sai da qyar ya samu ya lalla6a ta ta haqura.
D'auke da murmushin da ke kan fuskar sa yaja karan hancinta yace"se ki shirya yau zamu mai mai ta irin wnn rnr"
Tace"kai ma dai da wasa kake yaya,idan ka min irin na wnn rnr ai se babyn mu ya fito ba shiri"
Yace"Ae yanzu duk yanda nabi dake kin saba babyn mu bazai fito ba se lokacin fitowar sa yayi"
Ya qarashe mgnr ne yana mai shafa cikinta.
Tace"hm ba wani sabo in ka min da zafi wlh Allah zafi zanji bare wnn.....nn kawai ta zira hannun ta a hnkli cikin towel d'inshi had'e da qarashe mgnr a cikin kunnen shi.
Waheed ya fashe da dariya haka ma bintu wacce ta tashi da sauri zata bar gurin,bai barta ba ya janyo ta suka fad'i kwance kan bed,bintu da tasan ta tsokano shi da yawa bata bar ya mata komai ba se saurin had'e bakin ta tayi da nashi,daga nn mgnr ta canza salo,ya bada kai bori ya hau.
Tun da cikin bintu ya shigo cikin wata na tara ta soma exercise kullum safe da yamma,a nn d'akin exercise d'inda suke da.
Ba ta ko sani waheed yaje yana ta kallonta,se tayi wani exercise d'in da ya bashi tsoro ne zata ganshi kai tsaye yazo da sauri ya hanata wai kar ta jiwa babyn su ciwo,dariya kawai take mishi dan tasan ba abinda exercise d'in ze yiwa babyn dan bai san makarin abun bane kawai.
Ranar wata assabar gabad'aya yinin su a gidan mami suka yishi,dan bintu duk da cikin ta ya tsufa bata jin wata wahala ko nauyin shi koina tana iya zuwa abinta.
Bayan isha ta ida sallah tana kwance kan darduma
waheed ya dawo daga masallaci yace ta tashi su tafi gida.
A hankli ta tashi zaune tana kallon saif dake kwance gefe kusa da ita yayi bacci,wanda tun da suka zo yana liqe da ita gudun kar su tashi tafiya basu je dashi ba,se gashi yana jiran ta ida sallah bacci ya kwashe shi.
Mami dake zaune can nata gefe kan darduma tana cazbi tace"Saif duk liqewar nn dai gashi yayi bacci"
Bintu bata ce komai ba se d'an murmushi da tayi.
Mami dake kallon ta tace"Bintu kodai za kiyi kwanciyar ki a nn ne naga kmr tashin yana so ya miki wuya"
Kafin bintu tace komai waheed yace"zata iya mana mami ai kinsan Alhmdlh bata jin nauyin cikin"
Kallon sa bintu tayi d'auke da murmushi dan tasan halin gogan nata ko tana jin nauyin cikin bazai yarda ba,ko d'aukar ta zaiyi se dai ya d'auke ta su tafi,kan yaje ya kwana shi kad'ai ba tare da ita a kusa da shi ba.
Haka ma mami kallon sa kawai tayi had'e da murmushi dan ta san halin d'an nata ba yarda zai yi ba ta fad'a ne kawai.
As usual da kanta ta tashi ta rakasu har mota suka wuce snn ta koma daga ciki.
Da isar su gida kowannen su ya nufi d'akin shi.
Bayan waheed yayi wanka yayi shirin bacci ya nufi d'akin bintu ya same ta zaune qasa gefen gado kanta kan bed ta kwanta bata ko je tayi wanka ba.
A hankli yaje ya zauna qasa kusa da ita yana kallon ta da kulawa muryar sa a natse yana shafa kanta yace"my lady lafiya ko wanka baki tashi kinyi ba"
Bintu ta tashi d'auke da murmushi tana kallon sa tace ba komai waya na gama yi da umma shine ban tashi ba.
Ta qarashe mgnr ne had'e da yunqurin tashi zata koma kan bed,waheed ya kama ta ya zaunar da ita kan bed d'in snn ya tayata ta cire kayan jikin ta,taje tayi wanka bayan ta fito ta shirya suka tafi d'akin shi.
Da isar su d'akin sa kai tsaye kan bed suka je,tana manne a jikin shi yake tambayar ta ko zata sha fresh milk,sbd mostly se tasha kafin su kwanta amma se tace mishi a'a tare da qara lafewa a jikinsa,ta kuma rufe ido kmr me son yin bacci,a nn ya rage musu hasken d'akin snn a hankali yakai hannun sa kan jikin ta se shafa jikin nata yake ta koina,bintu dake jinsa ta bud'e idanun ta a hankli tana kallon shi,da kmr baza ta iya ba yau sbd abinda take ji,amma kuma se bata ce masa komai ba tana kallo har ya had'e bakin sa da nata ya ci gaba da sarrafa ta,tabi dashi duk yanda yake so bata nuna kasawar ta ba har suka je ga babban aiki.
Sai dai yana gab da samun gamsuwa ne idanuwan sa a rufe ya riqe ta gagam yana fitar da wani irin nishi,nn kawai se taji marar ta ta wani irin tsinka mata,ba shiri ta rirriqe shi sosai cike da jin zafin ciwon,duk da yanayin da waheed yake ciki bai hana ya fahimci ta shiga wani hali ba,ya bud'e idanun sa yana kallon ta dai dai lokacin da abu ke fita a jikin shi bai kula ba,se saurin zare jikin sa yayi ya mata rumfa yana tambayar ta fatima mene ne?
Komai bintu bata iya ce masa ba se hannunta ta kai kan marar ta,a nn ya janye jikin sa daga rumfar da ya mata ya zauna ya tallabo ta jikin sa hannun sa kan marar ta ya d'aura se jin yake abinda ke ciki na motsawa,a rud'e ya kalle ta fuskar sa kmr ze yi kuka yace"fatima na shiga uku na ji maki ciwo ne?
Girgiza masa kanta tayi,yace to gaya min mene dan Allah,qara riqe shi tayi ta samu da qyar tace"yaya ciwo zan mutu ka taimake ni"
Ta qarashe mgnr ne tare da fashe masa da kuka tana yarfi da hannu.
Waheed duk yabi ya rud'e ya qara janyo ta jikin sa se rarrashin ta yake cike da damuwa yana bata haquri dan ganin yake kmr laifin sa ne shi ya janyo mata ciwon, sam bai fahimci cewa naquda ce ta zo mata ba.
Cikin rarrashin ta ya d'aura hannun sa kan marar ta se murza mata gurin yake a hankli,a tunanin sa ko ze daina mata ciwo,amma ina abun se dad'a qaruwa yake dan bintu duk tabi ta rikice masa tana kuka.
Ganin ba yanda zai yi ya kira mami ya gaya mata cewa ya jiwa bintu ciwo gashi se kuka take bai san me zai mata ba,hankali tashe mami take tambayar sa garin me ya ji mata ciwo kuma a ina,bai 6oye mata ba ya gaya mata abinda ya faru har ta fara masa kuka,taslima tayi cikin fad'a tace"wae kai waheed wane irin mutum ne!
kai baka gani tun kafin ku tafi ta fara jin yanayin naquda shiyasa ma naso ta kwana a gurina amma sbd rashin haquri da rashin tausayi irin naka shine sai da ka neme ta!"
Waheed dake rungume da bintu se juyi take tana ci gaba da mishi kuka,ya kalle ta idanun sa cike da qwallah yace"wlh mami ban sani ba sam ban fahimta ba"
Tace"yi min shiru! sha sha sha kawai marar haquri! yarinya ciki ya tsufa ai ka barta ta huta very stupid!maza da Allah yi sauri ka shirya ta gani nn tafe mu tafi asibiti sha sha sha!
nn ta buga tsaki tare da tsinke wayar.
Waheed ya ajiye wayar sa snn ya tashi da sauri yaje ya nemowa bintu tufafi ya saka mata snn shima ya nemi nasa tufafi yasa a jikinsa.
Ba 6ata lokaci se ga mami tazo ya d'auki bintu agurguje suka tafi asibiti dan sosai naqudar ta taso mata ko kukan da take ma ta daina bata iya yi.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 51_*
Da isar su asibiti ana shiga da ita labour room bata sha wata wahala ba nn take ta haifo santalelen d'anta jawur dashi tamkar ka kwanta jini ya fito.
Koda nurse ke nuna wa bintu abunda ta haifa wani irin farin ciki bintu taji ganin yaron ba inda ya rago waheed tamkar saif d'an qaramin bakin nn ne kawai nata.
Cike da so ta shafi kansa tare da d'aura masa kiss kan goshi.
Snn nurse ta wuce dashi dmn shirya shi sae kallon sa take d'auke da murmushi a fuskarta dan ya bata shawa ba kad'an ba,d'an du6ul du6ul dashi renon madara.
Bayan an gama shirya shi aka kaiwa su mami shi,mami ta kar6e shi washe da baki sai murna take bakinta ya kasa rufuwa,bare shi waheed uban gayyar kwatan ta murnar sa ma wani aiki ne.
Bayan an fito da bintu labour room ne aka kaita d'akin da zata d'an huta kafin a sallame su,yayinda d'akin ya kasance na mutum d'aya ne ba hayaniya.
Bintu na zaune kan bed tana shan tea tamkar ba ita ce ta haifu ba lafiya lau abunta ba wani alamun jin jiki a tattare da ita.
Bayan ta gama shan tea ne,
Mami taje zuwa miqa mata jaririn dmn ta shayar dashi,waheed yaje da sauri zai kar6e shi dmn ya bawa bintu.
Mami bata bashi ba se hararar sa da tayi,a shagwa6e ya langwa6ar da kansa kmr qaramin yaro yace"plz mami dan Allah kiyi haquri ki barni in d'auki jaririn nn tun d'azu kin hana min ko sau d'aya ban d'auke shi ba"
Murmushi kawai mami tayi tare da miqa masa jaririn,waheed ya kar6e sa jikin sa na rawa se kallon jaririn yake cike da so snn ya baiwa bintu shi,wacce ta kar6e shi se kallon sa kawai take ta kasa fidda mamma ta bashi sbd tana jin kunyar ta fidda nonon ta a gaban mami.
Mami wacce ta fahimci hakan tayi murmushi kafin tace komai se aka kira ta a waya ta d'aga kiran had'e da fita ta basu guri.
Waheed da kanshi ya ciro mamman yasa bintu ta d'ago kan jaririn a hankli ta yanda zai ji dad'in sha snn ya saka mishi mamman a baki ya soma sha.
Bintu da tasa en yatsun ta ta d'an kama mamman bata sakarwa jaririn gabad'aya ba,ta kalli waheed d'auke da murmushi wanda ya janyo farar kujerar roba yazo gab dasu ya zauna yana fuskantar su tace"yaya hln me ya faru ne da mami taqi yarda ta baka baby?
Waheed dake kallon ta take idanun sa suka kad'a suka ciko da qwallah muryar sa a natse yace"Haba Fatima meyasa kinsan cewa naquda kike baki gaya min ba kika bar ni na neme ki?
Bintu dake kallon sa a hankali tayi qasa da idanun ta snn ta sake maida su akan shi muryar ta a hankli tace"kayi haquri yaya bazan iya hana ka bane shiyasa"
Yace"wnn kasada ce fatima dan Allah kar ki sake kinji"
Muryar ta can ciki kmr zatayi kuka tace"zan kiyaye inshaa Allah hakan bazai sake faruwa ba.
Yace"kiyi haquri fatima kar kiyi kuka ba fad'a bane magana ce"
Tace"ba wai dan maganar ka bane yaya banji dad'i bane a yanda naga yanayin ka nasan sosai mami ta maka fad'a"
Ta qarashe mgnr yayinda hawaye suka silalo a hankali kan kumatun ta,waheed dake zaune ya tashi da saurin sa ya tafi yana share mata hawaye yana fad'in"haba fatima ya zaki min asarar hawayen ki a irin lokacin nn da ya kamata ace farin ciki muke yi"
Tace"to yaya ai kaine naga zaka yi kuka a lokacinda na tambaye ka,hkn ya tabbatar min ba kad'an ba mami ta maka fad'a sosai"
Yace"no fatima ni ba fad'an mami ne yasa kika ganni a wnn yanayin ba,neman ki da nayi kina naquda shine ya min zafi ko kad'an banji dad'i ba"
Hannun ta ta janye daga riqon da tayiwa mammanta snn ta shafo gefen fuskar sa tana kallon sa da kulawa tace"am verry sorry bazan sake ba kaji"
Cike da so ya rankwafadda kansa ya d'aura mata kiss kan goshi yace"ba komai my lady ai nine mai laifin nida na zamo jarababbe marar haquri kullum se takuraki nake"
A shagwa6e tasha masa toka cikin turo baki tace"uhm ni yaya kar ka sake kiranka da wnn sunan bana so"
Waheed yayi murmushi tare da jan karan hancinta yace"ae gaskiya na fad'a amma tunda ba kya so na daina"
Murmushi bintu tayi wacce bata ce komai ba se kallon baby boy tayi da ya soma kuka.
Waheed ya girgiza kansa had'e da murmushi yana shafa kan jaririn yace"wai fa nonon da kika saki ne yaji ya daina kai mishi a baki shine yake kuka se kace dama can ya saba sha.
Bintu da still murmushi na kan fuskar ta tana kallon jaririn tace"kasan jariran yanzu da wayo ake haifuwar su"
"Ae kam"
Cewar waheed wanda da kanshi ya maida mishi mamman yaci gaba da sha.
Tana gama bashi mamman ne se ga mami ta shigo tare da Anti Hafsa da Anti nafee,da ita ce ta kira su ta snr dasu cewa bintu ta haifu,wa enda murna da farin ciki sam bai bar sun iya haqura har se da safe snn su zo ba.
Suka kar6i jaririn cike da murna se barikallah suke ta fad'i,suna yiwa bintu barka da ta sauka lafiya,bintu dai se kallon su kawai take tana murmushi.
Kasan cewar bintu lafiya lau take ita da jaririn ta,take aka sallame su,suka koma gida.
Washe gari da safe mami da kanta ita da waheed suka tafi da bintu kebbi tare da baby boy,kmr yanda al'ada ta tanadar idan haifuwar fari ce gida ake komawa,amma shi waheed ko kad'an baiso hkn ba dan ba yanda ze yi ne kawai.
Cike da girmawa umma ta tarbe su wacce ta kar6i baby boy a hannun mami se murna take kyace jikanta ne na farko,wacce tun jiya da dare da aka haifu ta kira Abba ta snr dashi shima sosai yayi murna da farin ciki dan da safe ma har bintu ya kira suka yi waya.
Dasu mami zasu koma,saif wanda dama dashi aka zo,yayi ta kuka bazai tafi ba se da baby boy,da qyar aka samu aka rarrashe sa ya haqura.
Bayan wucewar su ne se ga Anti Hafsa ita da Anti Nafee sun zo,gida ya cika en barka se shigowa suke tayi.
A sokoto bayan su waheed sun koma,da dare yaji gidan nasa ya masa fad'i ba dad'i,kwata kwata ya kasa kwanciya se zagaye d'aki yake cike da jin haushin meyasa za'a ce idan mace tayi haifuwar fari gida take komawa, bayan yanzu ne ya kamata ace bintu na kusa dashi dmn ya bata kyakkywar kulawa mai cike da zallar so ita da yaron su.
Amma ina al'ada bata bar ya samu damar hakan ba,gashi yayi ta kiran bintu a waya bata samu ta d'aga kiran ba yasan tana can tare da en barka basu bar ta zauna ba.
Yana cikin hakane se ga kiran bintu ya shigo a wayar shi,bai d'aga kiran ba se kallon kiran yake d'auke da murmushi har kiran ya tsinke snn ya kirata suka dad'e suna waya cike da so tamkar saurayi da budurwa yayinda waheed se shagwa6a yake mata wai ya kasa bacci bata kusa dashi,ita kuma se lalla6a shi take kmr wani qaramin yaro cikin kalamai masu sanyaya rai.
Duk da haka washe gari da ya dawo gurin aiki kasa zama yayi sei da yaje har kebbi ya gansu.
Daga haka abun ya zamar masa jiki kullum da yamma idan ba yaje ya gansu ba sam baya jin dad'i har lokacin suna ya qarato.
Yayinda ranar suna baby boy yaci sunan muhammad (Arman).
Sosai akayi biki bidiri,qofar gidan ta cika tamqal da mutane tamkar wani d'aurin aure ake,su Abban ilham,Abbas, Abdallah,har jabir duk ba wanda bai zo ba har abokanan waheed duk sai da suka zo,dan kasaitacciyar walima waheed ya shirya ta gani ta fad'a dmn godewa ubangiji sabuwar qaruwar da suka samu daga gare shi.
Plz kuyi haquri da wnn.
Am totally busy.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 52_*
Bayan kwana biyu da yin biki ne Abdallah da bai riga ya koma school ba yana kwance kan doguwar kujera 3seater,idanuwan sa a lumshe se shafa jikin arman yake dake kwance kan faffad'an qirjin sa yana bacci.
Nan se ga bintu tazo ta zauna qasa kusa dashi tare da lanqwashe qafafunta tana fuskantar shi,idon ta a kanshi tace"yaya nasan ba bacci kake ba ka tashi dan Allah muyi magana"
A natse Abdallah ya bud'e idanun sa ya tashi zaune rungume da Arman a jikin shi,kana ya kwantar dashi kan kujera kusa dashi snn ya kalli bintu yace"ina jinki qanwata mene ne?
Tace"islam ta kirani wai kana fushi da ita?
(Islam cewa da yarinyar da yake nema)
Abdallah ya girgiza kansa d'auke da d'an murmushi a fuskar sa snn yace"dama maganar islam ce zaki min kika sa na tashi zaune har da ajiye Arman gefe,kinga idan kina da aikin yi gwanda kije kiyi"
Yana kaiwa nn ya kai hannu zai d'auki Arman dmn su koma su kwanta.
Bintu tace"plz yaya ka tsaya mana muyi magana wlh islam duk tabi ta damu tace kwana biyu fushi kake da ita ka daina kiranta kuma in ta kira ka baka d'aga kiran ta shine tace dan Allah in baka haquri.
Yace"ki barta kawai ni ba fushi nake da ita ba ina hora ta ne kawai,ae tasan laifin da ta min shiyasa ta biyo ta hanyar ki dan a sasanta"
Bintu tace"hln me ta maka?
Abdallah yace"qanwata kinfi kowa sanin irin yanda nake matuqar son islam,bani da burin da ya wuce na kammala karatu muyi aure nida ita,an mana engaged since amma abun haushi duk lokacin da naje qofar gidan su se na gaji da tsayuwa kafin take fitowa se kace wanda bata so,shekaran jiya da naje nafi awa d'aya a gurin ina jiran fitowar ta har se da na gaji na dawo gida abuna,shine nasan da ta fito bata ganni ba tayi ta faman kirana a waya ni kuma na fita harakar ta, wacce a tunanin ta taga ina matuqar sonta bazan iya share ta ba.
Bintu dake kallon sa ta sauke numfashi a hankli snn tace"calm down yaya sanin kanka ne yanda islam ke sonka wlh bada son ranta take maka haka ba,laifin matar uban ta ce da taso ace erta fati ka nema ba islam ba.
Ko dan kaji haushi kace ka fasa auren islam,mugunta zai sa ta hana islam fitowa cikin lokaci idan kaje.
Shiru Abdallah yayi shi kansa yasan abunda bintu ta fad'a haka ne,anguwar kusan kowa yasan halin matar uban islam sam bata qaunar islam ko kad'an,se dai islam 6oye mishi take bata fad'a mishi komai,dan duk lokacinda yaje gidan su in ta fito ya tambaye ta meyasa ta barshi tsawon lokaci yana jiranta, se tace yayi haquri an sata d'an wani aiki ne bata samu ta kammala ba se yanzu,kuma firar tasu bata ko wani tsayi lokaci kad'an ta ce mishi zata koma,in ya tambaye ta meyasa se tace mishi Abban ta ne baya son tana jimawa a waje, hakan kesa dole yake haqura ya tafi ba dan yaso ba.
Amma a zahiri matar uban ce ke d'ibar mata lokaci wacce idan ta qara akan lokacin da ta d'ibar mata dukan tsiya take mata,shiyasa firar tasu se yi take tana duba lokaci a wayarta yayinda Abdallah ya d'auka ko Abban ta ne kesa mata lokaci kar ta jima,dan ba kad'an ba mahaifin ta na sonta duk muzguna matan da ake se idan ya fita ne baya gida baisan wainar da ake toyawa ba,kuma islam ba gaya mishi take ba dan yarinyar akwai haquri tamkar mahaifiyar ta da ta rasu.
Bintu dake kallon Abdallah tace"yaya kayi shiru tun d'azu komai baka ce ba"
Cikin sauke numfashi yace"qanwa ta ina tunani ne duk se naji tausayin ta ya kamani.
Bintu tace"wlh yaya dama can ni tausayi take ban,dama zaka yarda ayi auren nn kawai ko baka kammala karatun ka ba.
Murmushi Abdallah yayi yace"bazai yiyu bane bintu nafi son se na kammala karatu tukun na fara aiki haniqam duk dai madecine ne.
Kuma ae islam ta gaya min Maiduguri zata tafi gurin kakarta ba kuma zata dawo ba se idan za'a yi auren.
D'auke da murmushi bintu tace"shike nn ma ta huta Wlh,kuma gashi watannin da suka rage ku kammala karatu ba yawa koh?
Yace"eh ba yawa wata biyu ne suka rage inshaa Allah.
Tace"Allah ya nuna mana kun kammala karatun lafiya musha biki dan Abba kam tuni ya kammala maka gini kuma umma tace har kud'in lefe da komai ya ajiye maka suna a save kai kawai ake jira.
Abdallah yace"Ae kam Abba ya matsu nayi auren nn ban san meyasa ba.
Bintu dake kallon sa kafin tace komai wayar ta ta shiga ruri koda ta duba islam ce,ta kalli Abdallah d'auke da murmushi tace"ga er halak ta kira taji idan na shawo kanka"
Abdallah yayi murmushi yace"kar ki d'aga kiran bari na kirata a wayata kar a cinye mata kati,d'auki Arman ki tafi dashi dan d'akina zan je mu kashe juna da soyayya"
Bintu ta fashe da dariya haka ma Abdallah wanda ya tashi ya fita,bintu kuwa ta d'auki Arman suka wuce daga ciki.
Bintu na yin arba'in ta soma shirye shiryen komawa sokoto sbd hutun da aka bata a asibiti ya qare zata koma bakin aiki.
Wacce a washe garin rnr da ta kammala shiryen shiryen tafiyar ta mami tazo ta tafi da ita sbd waheed baya nn tunda akayi biki yayi tafiya yana Germany kan wani course na harakan business da yaje yi for just 3months.
Shiyasa kai tsaye mami ta wuce da bintu gidan ta ta ware mata d'akin da zata zauna a ciki kafin waheed ya dawo.
Duk bintu zata je gurin aiki nn take barin Arman bata zuwa dashi idan yaji yunwa madara mami ke kad'a mishi ta bashi se idan bintu ta dawo snn tayi breast feeding nashi.
Har tayi wata d'aya da sati biyu a gidan waheed be dawo ba.
Se rnr bayan kwana biyu Bintu tana zaune a falo ita kad'ai tana kallo gabad'aya hankalin ta ya tafi gun kallo ko qarar bud'e gate bata ji ba se ihun murnar saif dake waje taji yana fad'in"daddy oyoyo!daddy oyoyo!
Nan ta tashi da sauri taje ta bud'e labulen window taga kuwa waheed d'in ne ya cira saif sama suna murnar ganin juna.
Bata damu da gidan mami take ba haka ta fita cike da murna taje ta maqalqale shi,suka shigo falo tana rungume a jikin sa, waheed sam ya kasa sakinta,ya tafi da ita kan doguwar kujera suka zauna se kallon ta yake kan yanda yaga ta wani canza mishi ta qara kyau da haske tayi 6ul 6ul abunta se sheqi take kmr ita ce ta fita waje ba shi ba.
Duk da cewa shima ya qara kyau sosai da haske amma ya d'an fad'a.
Cike da so yasa tafukan hannayen sa kan kumatun ta idon sa a cikin nata yana kallon ta d'auke da murmushi yana ji kmr ya had'iye ta se yaba irin kyaun da tayi yake.
Bintu da har ranta taji dad'i d'auke da murumushi ta shafo sajen fuskarshi muryar ta a hankli tace"kaima ba kad'an ba ka qara kyau my guy"
Fuskar sa a shagwa6e yace"inafa kin ganni duk na fad'a kewar rashin ki a kusa dani ya hana ni sukuni"
Murmushi tayi tare da kwanciya kan faffad'an qirjinsa tace"nima cike nake da kewar ka yaya, mami ce ke sani a gaba se naci abinci da zaka same ni na ma fika ramewa"
Cike da jin dad'in zancen ta ya d'ago ta ya d'aura mata kiss kan goshi yace"ina mami da yarona Arman?
Kafin tace komai se ga mami ta fito tare da saif wanda da shigowar su ya tafi aguje d'akin ta ya snr da ita dadyn sa ya dawo.
Waheed ya tashi da murnar sa yaje yayi hugging d'inta,mami wacce itama cike take da murna ganin sa ta d'ago shi tare ta jan karan hancin sa tace"shine se ka mana bazata ko ka snr damu"
Yace"to mami da ace na fad'a baza ayi murnar gani na kmr haka ba,ya kalli bintu da ta qaraso gurin su yace kin ganta aguje taje ta tarbo ni sbd bata san da dawowa ta ba,da ta sani se dai tayi tsaye kawai tana kallona se na qaraso snn ne zata min sannu da zuwa.
Bintu dake kallon sa murmushi kawai tayi tare da girgiza kanta.
Mami tace"sharrin da zaka mata knn"
Yace"ba wani sharri mami ni ina yarona Arman naga kowa ban ganshi ba"
Nan mami ta shiga qwalawa hajjo kira se ga hajjo tazo da hanzarin ta d'auke da Arman dake riqe da abun wasan sa na kwacan kwacan yana ta wasa dashi, dan yaron take yayi wayo kmr ba d'an wata uku ba.
Kafin hajjo ta qaraso gurin su waheed ya qarasa gurinta da saurin sa ya kar6e shi wanda sai da ya d'aura masa peck kan goshi snn ya iya amsa sannu da zuwan da hajjo ke mishi.
Ya koma gurin su mami se shafa kansa yake cike da so yana kallon sa kana ya maida duban sa gun mami yace"mami yarona fa se kyau yake qarawa gabad'aya fatima yake son komawa"
Kafin mami tace komai bintu tayi saurin kallon Arman tace"wlh a'a duk kaine ni bakin nn ne kawai nawa ba wani kama da mukayi dashi"
Waheed dake tsokanar ta ya fashe da dariya dan tayi mgnr ne shaye da toka tana kallon sa kmr zata mishi kuka,dan a yanda take son waheed ko kad'an bata son Arman ya sauya izuwa kmr da sukayi da shi.
Mami dake kallon su tayi murmushi tare da jan bintu zuwa jikinta cikin muryar rarrashi tace"fita harakar shi wasa yake miki je kitchen d'ebo mishi abinci ki kai masa d'akin ki yaje can yaci.
Nan bintu ta wuce zuwa kitchen waheed ya bita da kallo d'auke da murmushi,kana ya kama hannun saif suka wuce zuwa d'akin bintu kmr yanda mami ta umarce shi.
Wacce da kanta taje nn fridge d'in falo ta d'auko masa ruwa da lemu ta kai mishi.
Koda bintu ta kai masa abinci ta same shi zaune kan sofa yana shan lemu,d'ayan hannun sa na riqe da Arman da ya d'aura kan cinyoyin sa ya zaunar yayinda saif ke zaune a kusa dashi yana ta yiwa Arman wasa.
Ajiye abincin tayi kan stool snn ta zauna kusa dasu fuskar ta a d'aure tana faman fushi da waheed,waheed dake kallonta yayi murmushi tare da ajiye lemun da yake sha a cikin cup ya d'aura kan stool snn yace"fushin name kuma my lady bayan kinsan da wasa nake miki habibin ki Arman da d'an gatan mijinki da kike matuqar so yake kama"
D'auke da murmushi tace"to ai ni bana son irin wnn wasar ne,wlh bakaji yanda gabana ya fad'i ba a lokacinda kace Arman ya dawo ni.
Waheed yayi murmushi yana kallon ta cike da so yace"dan ya koma ke se akayi me aini haka nafi so wlh"
Bintu ta sakar masa wani irin kyakkywan kallo idon ta a cikin nashi tace"meyasa?
Yace"sbd ina sonki shiyasa nake matuqar son Arman kan d'an qaramin bakin nn naki da ya d'auko.
Ya qarashe mgnr ne tare da shafo lips d'in ta snn yakai hannun sa kan cikinta yace"amma duk da haka ki shirya yau zan saka miki babyna er gold me kama da ke sak ba inda ta rago ki"
Bintu dake kallon sa d'auke da murmushi ta ware masa kyawawan idanun ta snn ta saki dariya a hankli tace"komai rushing d'inta dai an rigata na gaba yayi gaba na baya se labari, kuma habibee Arman se ya girma tukun ya isa a mishi qanwa snn ko zata samu isowa"
Waheed dake kallonta yace"Au haka kika ce?
Tace"qwarai kuwa.
Yace"Ashe daren yau kuwa zaki ga aiki da cikawa dan zan saka qwan er gold d'ita a jikin ki,ta yiwa habibin naki over taking.
Dariya bintu tayi haka shima waheed dariyar yake kana ya soma cin abinci suka ci gaba da firar su cike da nishad'i.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*
*_Story n written by Billy giro😊_*
*_page 53,54&55_*
Koda ya kammala cin abinci an soma kiraye kirayen sallar magrib dan da yamma ne.
Nan bintu ta kar6i Arman,shi kuma yaja saif suka tafi zuwa masallaci bayan sun dawo kai tsaye d'akin mami ya tafi,bashi ya fito ba sai da akayi sllr isha'i,ya koma jan saif suka tafi masallaci,da suka dawo gabad'aya falo suka zauna suna fira cike da nishad'i.
Yayinda mami,bintu da saif suka baje nn tsakiyar falon kan center carpet suna cin abinci a plate d'aya,Arman kuma yana hannu waheed yana mishi wasa.
Se guraren qarfe tara snn waheed yaja Bintu da Arman suka wuce zuwa gida.
Da isar su gida kai tsaye bintu d'akin ta ta nufa ta shimfid'e Arman da yayi bacci kan d'an bed d'insa snn ta tafi zuwa wanka.
Tana fitowa wanka se ga waheed ya shigo d'akin a nn ta qofar d'akin sa dake sada shi da ita,bintu ta tsaya tare da ware idanu tana kallon shi,ba komai a jikin shi fitowar sa daga wanka knn ko ruwan jikin sa bai iya tsanewa ba yazo d'akin.
Bata iya ce masa komai ba tana kallo ya nufo ta gadan gadan ya kama kugunta ya tafi da ita jikinsa da sauri ya had'e bakin sa da nata yana tutsar lips d'in ta a gigice cikin kid'ima kmr wanda ze cire lips d'in ya cinye su d'anye.
Haka Bintu ta biye masa bata hana shi ba dan tunda ya shigo d'akin ta d'aura idonta akan tsakiyar cinyoyin sa tasan cewa ba qaramin cikin tsananin buqatuwa yake ba,sam ba wani abunda ze iya dakatar dashi.
Wanda nn kai tsaye yana had'e bakin sa da nata ya zare towel d'in jikinta ya jefar snn ya kama hannun ta ya d'aura kan tsakiyar cinyoyin sa bata sa wasa ba ta soma shafa shi kaman yanda yake buqata,haka shima yakai hannun sa a tsakiyar cinyoyin ta yana shafa ta cikin wani irin salo mai wuyar fassarawa,ae kuwa tsayuwar gagarar su tayi waheed ya kwashi bintu dake neman sulale mishi suka je kan bed,daga nn mgnr ta canza salo fiye da tunanin me karatu dan daren rnr waheed zaucewa ne kawai bai yi ba da salon bintu,haka ita ma gabad'aya ta fita hayyacin ta da irin nashi salon.
Washe gari da asuba waheed ya dawo daga masallaci yayi tsaye a bakin qofa yana kallon Bintu wacce ta linke darduma ta saka a wardrobe snn ta cire hijab da zanin da ta d'aura akan rigar baccinta duk ta linke su ta saka a ciki.
Daga nn ta nufi bed zata kwanta se miqa take me cike da jan hankali, waheed dake kallonta ya lumshe idanun sa a hankli tare da fitar da ajiyar zuciya har yana had'iye yawu snn ya qarasa gurin ta dai dai ta zauna kan bed ta kama blanket zata kwanta taji mutum ya zauna gab da ita,a tsorace ta juyo da sauri ta kalle shi dan sam bata ji shigowar sa ba,sauke ajiyar zuciya tayi ganin waheed ne yayinda shi kuma yake hura mata isakan bakin shi kan kyawawan idanun ta da suka nuna alamar jin tsoro yace"tsoron name ko kina nufin baki ji shigowa ta ba har da sallamar da nayi"
Sai da ta lumshe idanun ta a hankli snn ta ware su a cikin eyeballs d'inshi tace"wlh sam ban ji ba"
Yace"tunanin me kike to?
Tace"ba wani tunanin da nike banji bane kawai"
Sosai ya tafi da ita zuwa jikinsa fuskokin su gab har suna jin saukar numfashin juna,idon sa a cikin nata yana kallonta yace"ni kinga jiya gabad'aya cikin tunani na kwana,nishad'i bai bar na iya yin bacci ba se tariyo dadd'ar zumar da kika shayadda ni nake.
Ya qarshe mgnr ne tare da shafo gefen fuskarta cikin wata irin murya mai taushin gaske yace"my lady wai meye sirrin gabad'aya daren jiya kin rikitar dani kina neman zautadda ni da dadd'ar zumar ki dake sa in manta kowa da komai.
Tsaddaden murmushi me jan hakali bintu tayi tare da lumshe idanun ta a hankli ta koma ware su a kanshi,se kallon shi take ba tare da tace masa komai ba.
Waheed dake kallonta a hankali yaja tsinin hancinta cike da so yace"my lady zaki kashe ni da wnn salon naki,wnn murmushi da kallo haka kin kuwa san me naji"
Kafin tace komai ya kama hannunta ya d'aura kan tsakiyar cinyoyin sa ya ce ta6a kiji duk kin tayar min...
Bintu da hannun ta ke kan jikin shi tana shafa shi taji kuwa abinda ya fad'a hakane ba wasa a ciki,tayi murmushi tare da girgiza kanta tace"yaya knn shi d'an murmushin da kallon?
Idanun sa a kasale yana kallon ta d'auke da murmshi ya lakato hancinta yace"eh mana ae tsokanar ba biyu kad'ai bace,ta ukun duk tafi girma da tada min hankali,wato wnn miqar da kikayi a d'azun da na shigo ina kallon ki gabad'aya kin tada min da duk wata tsikar jikina,da qyar na iya qarasowa gurin ki na zauna dan haka ki shirya yanzu zan fashe.
Ya qarashe mgnr ne tare da kai bakin shi kan d'an siririn hannun rigar baccinta ya kama yana sa6ule rigar da bakin shi,se kallon shi kawai take tana masa murmushi har ya cire rigar.
Wanda jikin sa na rawa yakai bakin sa kan albarkatattun qirjinta ze tsotsa,da sauri bintu tasa duka hannayen ta biyu ta rufe nonuwan ta,waheed ya kalle ta d'auke da murmushi me cike da kasala yace"ba kya so in sha madarar inji"
Bintu dake kallon sa cike da so ta girgiza kanta tace"um um milk d'in da ke ciki na Habibi Arman ne shi kad'ai ba me sha,alfarma d'aya da zan maka shine kayi wasa"
Yace"uhm yayi zan rama dmn idan baby na tazo da kaina zan tsotsi madarar in kai mata a baki tasha"
Bintu bata ce komai ba se murmushi da tayi,wacce tana kallo ya janye hannayen ta daga kan albarkattaun qirjinta yasa harshen sa se lasar su yake cikin wani irin salo.
Ta lumshe idanun ta kmr wata me jin bacci,hannunta kan jikinsa se shafa shi take a hankali cike da jin dad'in abunda yake mata,wacce da kanta ta zare mishi kayan jikinsa suka ci gaba da romancing d'in juna har suka je ga babban aiki.
Haka suka ci gaba da rayuwar su cike da qaunar juna.
Bintu na zuwa aikinta haka shima waheed wanda yanzu ya fara business d'in sa a online shida wasu aminatattun frnds d'inshi dake zama a Dubai ya janyo suka had'a hannu.
Kasancewar suna yin komai akan gaskiya ba mai cutar wani,se gashi Alhmdlh cikin watanni kasuwancin nasu ya fara ha66aka,waheed ya bud'e makeken mall d'insa a can garin su wato lAFIYA dan dama en asalin garin ne aiki ne ya kawo mahaifin waheed nn sokoto,da ya rasu se mami bata koma ba taci gaba da zamanta a nn,sbd kakannin waheed duk sun rasu basa raye,se en uwa da sam basu da wani qarfi talakawa ne shiyasa duk abu ya faru basa iya zowa garin ya musu nisa,rasuwar mahaifin waheed ne ya ta6a kawo su da kuma auren waheed,se dai duk abunda ya faru na farin ciki ko na jajantawa,suna kiran mami a waya,haka kuma duk lokacin da ta tura musu abun alkhairi suna kiran ta a waya suyi mata godiya.
Haka ma waheed akai akai yana qoqarin ganin ya musu alkairi shiyasa ma yasa akayi masa makeken mall d'in sa a can garin nasu ya zuba duk en uwan sa a ciki suna kula masa da gurin yana musu albashi mai tsoka.
A cikin watanin nn ne akayi auren Abdallah wanda koda shakera ta zagayo a cikin ta biyu Allah ya azurta shi da samun baby girl da ya sakawa sunan bintu wato Fatima.
Haka ma jabir sunan da ya sakawa er sa kenan wanda anyi bikin auren sa ne kusan lokaci d'aya da na Abdallah.
Bintu kuwa tuni ta yaye Arman har tana d'auke da sabon cikin ta d'an wata biyu da ta samu bayan dawowar su hajji da suka je ita da waheed da kuma mami,haka ma su umma da Abba duk lokaci d'aya suka je kuma duk waheed ne ya biya musu,ya kuma biya ma kawun nn shi dake can lafiya.
Ranar wata assabar Waheed ne zaune a farfajiyar gidan shida bintu kan kujerar shan iska ta zaman mutum biyu,yayinda waheed ya d'aura qafar sa kan d'aya yana karatun jarida,bintu kuwa tana rungume a jikin shi hannun ta a saqale ta zagayo dashi ta bayan qugun sa,snn kanta kan kafad'ar sa ta kwantar se kallon saif da Arman take dake cikin motar su ta wasa suna tuqawa cike da nishad'i suna wasa,yaran da in ka gansu tamkar en biyu sbd kmr da suke yi da juna gashi zama d'aya Arman ya cimma saif da komai kyace lokaci d'aya aka haife su,bintu dake kallon su har ranta take jin qaunar su a ranta tamkar su duka biyun ita ta haife su.
A hankli ta lumshe idanun ta tare da qara shigewa jikin waheed ta kuma qara kwantar da kanta sosai a jikin shi.
Waheed ya kalle ta d'auke da murmushi yasan ba makawa bacci zatayi dan ko wnn cikin haka yazo mata da yawan bacci da zarar ta jingina a wani guri to fa se bacci kmr wacce sleeping sickness ya ciza.
Komai be ce da ita ba se hannun sa ya d'aura kan cikinta cike da so yana shafa cikin a hankali cikin natsuwa,bata bud'e idon ta ba tana jinsa har tayi bacci.
Snn ya janye hannun sa a hankali yaci gaba da karatun jaridar shi, se ga su saif sun zo a guje zasuyi magana knn waheed yayi saurin d'aura yatsan sa kan lips d'in sa ya nuna musu bintu da ido alamar suyi shiru kar suyi magana mom d'in su na bacci.
Ae kuwa da mgnr kurame sukayi magana alamar suna son zasu d'auko ball suyi wasa,shima a yanayin mgnr kurame ya basu amsa kan suje su d'auko,cike da murna suka je suka d'auko ball suka tafi can filin ball d'in su da aka ware musu na mussaman suka soma wasar su.
Waheed kuwa yaci gaba da karatun jaridar shi wanda duk wani motsi na bintu yana kulle dashi.
Tunda cikin bintu ya tsufa ya shigo cikin watan haifuwa waheed ya haqura da neman ta dan har yanzu yana nn da halin shi na kullum idan ba ya neme ta ba baya jin dad'i,amma haka yake tauye kansa dan baya son ayi irin na wancan karon.
Wanda ba kad'an ba yana wahala matuqa kullum da qyar yake iya yin bacci rnr ma kwata kwata kasa bacci yayi,wanda tun yana juyi a hankli har ya zame jikin sa daga na bintu ya sauka kan gadon,ya durqusa kan guiwoyin sa yasa hannun su duka biyu a tsakiyar cinyoyin sa ya matse cinyoyin nasa sosai tare da d'aura goshin sa kan bed jijiyoyin kansa duk sun taso se goga goshin nasa yake kan bed yana fitar da wani irin wahalallen numfashi.
Cikin bacci bintu ta soma jinsa ta tashi wacce tana ganin halin da yake ciki,ba shiri ta sauko kan gadon a rud'e tazo gab dashi ta durqusa kan guiwoyin ta tare da tallabo kanshi,tasa hannayen ta kan kumatun sa tana kallon sa idanuwan sa sunyi jajur duk tabi ta rud'e se tambayar sa take abunda ke damun shi.
Komai waheed bai iya ce mata ba se cusa fuskar sa yayi gabad'aya cikin qirjinta yana ci gaba da goga fuskar sa a hankali kan jikinta.
Wanda still hannayen sa na kan tsakiyar cinyoyin sa bai janye ba se qara matse gurin yake, yana wani irin numfashi cike da buqatuwa kmr zai shid'e.
Se a lokacin bintu ta fahimci ainihin halin da yake ciki.
Tasa hannayen ta ta tallabo fuskar sa daga kan qirjin ta tana kallon sa da idanuwan ta da suka ciko tap da qwallah cikin muryar kuka tace"haba yaya meyasa kake son hallaka kanka da kanka ko na maka wani laifi ne da baka son kusan ta ta tsawon lokaci ina kule dakai ka gaya min me na maka?
Muryar sa da qyar yace"ba kin min laifin komai ba my lady ina tsoro kar in neme ki kina yin naquda bana son kina wahala fatima ko kad'an banji dad'i ba a wancan karon.
Bintu dake tallabe da kumatun sa idanuwan ta a cikin nashi muryar ta a hankli tace"kar ka damu yaya dan ka neme ni ina yin naquda ni naji zan iya ba wani abu bane se ma sauqin haifuwa da yake kawowa,take mace ta haifu ba tare da tasha wata wahala ba and now u are free bana jin komai kaji"
Girgiza kansa yayi almar a'a dan ko kad'an baya son takurata.
Bintu bata saurare shi ba se bakin ta ta had'e da nashi tare da zira hannun ta a cikin wandon shi tana shafa shi cikin wani irin salo mai wuyar fassarawa,sam waheed kasa hanata yayi gabad'aya ya kid'ime jikinsa na rawa ya cafki harshen ta ya kama mata suka ci gaba da romancing d'in juna har suka je ga babban aiki,wanda a hankali cikin natsuwa yabi da ita har suka samu gamsuwa.
Kana ya rungume ta qyam a qirjinsa idanuwan sa a lumshe yana jin wani irin sonta na qara fizgar shi a cikin ransa.
Washe gari da safe ba mai zuwa aiki a cikin su weekend ne,waheed baya fita aiki bintu kuma tana off.
Bayan sunyi wanka sunyi breakfast waheed ya tafi kai Arman gidan mami dan kusan kullum can yake yini.
Suka bar Bintu ita kad'ai zaune a falo kan doguwar kujera 3seater ta jingina bayanta idanuwan ta a lumshe hannunta kan cikinta tana shafa cikin nata a hankali sbd yanayin da ta fara ji na alamun naquda.
Tana cikin hakane waheed ya dawo wanda da shigowar shi kai tsaye gurin ta yazo ya zauna gab da ita tare da d'aura hannun sa kan cikin ta yana shafawa shima,
a hankli bintu ta bud'e idanun ta tana kallon sa d'auke da murmushi muryar ta a natse tace"er gold d'ikka Hanan she is coming very soon inshaa Allah!
Wani irin dad'i waheed yaji bakin sa a washe ya riqo kafad'un ta yace"kai haba dan Allah kin fara jin alamu ne?
A hankali ta lumshe idanun ta tare da gyad'a masa kai alamar eh.
Nan waheed yaje da hannun sa a hankali kan marar ta yace"da zafi sosai?
Tace"um um kad'an kad'an"
Yace"to na kira mami na gaya mata ta zama cikin shiri?
Tace"um um tukuna"
Yace"to me kk so ko kina son na tausa miki jikin ki?
Tace"um um fresh milk kawai nake so insha"
Nan ya tashi da hanzarin sa ya nufi fridge bintu ta bisa da ido cike da so wacce ta fahimci duk murna ta kid'imadda shi.
Da saurin sa ya dawo riqe da fresh milk da cup ya zauna ya tsiyaya mata a cup snn ya ajiye ragowar ya rungumo ta jikinsa yana bata da kanshi har sai da tace ya ishe ta snn ya ajiye cup had'e da er ragowar da ta bari.
Kana ya d'aura hannun sa a natse kan cikin ta yana shafawa d'auke da murmushi yana kallon cikin yace"ina maraba dake baby Hanan Allah ya kawo min ke lafiya kuma ina son dan Allah ki fito a hankli cikin sauqi kar kisa my lady na tasha wahala kinji ko"
Bintu dake kallon sa tayi murmushi tana kallon sa cike da so bata ce masa komai ba,se kwanciya tayi a jikinsa ta lafe tare da lumshe idanun ta a tunanin ta zata iya yin bacci amma ta kasa se jin take marar ta na ci gaba da juya mata tun tana jurewa har zufa ta fara tsattsafo mata.
Cikin hikima da dabara ta share zufar bata son waheed ya lura.
Waheed dake rungume da ita se shafa cikinta yake a hankali wanda a tunanin sa ma tayi bacci se da ta motsa ne snn ya fahimci ba bacci tayi ba.
Da kulawa ya kalle ta yace"mene ne ko kin fara jin zafi sosai ne?
qara shigewa jikin sa tayi tare da fad'in"um um"
Komai bai sake ce mata ba se ci gaba yayi da shafar cikin ta wanda yana kule da yanda take ta motsi ciwon marar se gaba gaba yake mata.
Farin handkerchief d'insa ya zaro a aljihu ya share mata zufar da ya gani kan goshin ta snn ya zaro wayar sa ya kira mami ya snr da ita acewar tazo suje asibiti bintu zata haifu.
Bintu na jin sa ta kasa ce masa komai dan takai matakin da ko magana bata son yi.
Ba 6ata lokaci se ga mami tazo,wacce koda tazo gadan gadan naquda ta tasowa bintu,ae kuwa basu tsaya wata wata ba suka wuce da ita zuwa a asibiti.
Ko wnn karon ana shiga da ita labour room bata sha wata wahala ba take ta haifo kyakkyawar er ta jawur da ita kmr ka qwanta jini ya fito.
Nurse tazo da murnarta ta snr dasu an haifu an sami 'ya mace.
Sosai waheed yayi murna wanda nan take ya ciro wayar sa a aljihu ya kira su umma da su anti hafsa ya snr dasu.
Haka mami sosai tayi murna se Alhmdlh take ta fad'i tana godewa Allah,d'anta qwaya d'aya tal amma gashi Allah ya albarka ce shi se tara mata jikoki yake.
Wacce itama nn take ta ciro wayar ta a jaka ta shiga kiran en uwa da abokan arziki tana snr dasu.
Bayan sun dawo gida mami na cikin bathroom tana had'awa bintu ruwan wanka. Waheed kuwa yana zaune kan bed shida bintu murna fal a ransa se kallon Hanan yake dake shan mamma wacce sak kmr ta d'aya da bintu tamkar an tsaga kara.
Cike da murmushi waheed ya shafo kan hanan ya kalli bintu yace"kinga ikon Allah ko,musamman da muka je hajji na dafa qa'aba na roqi Allah yasa ki haifa min 'ya mace mai irin kyakkyawar fuskar ki sak gashi kuwa Allah ya bani.
Ya qarashe mgnr ne tare da jan karan hancinta yana murmushi.
Bintu dake kallon sa d'auke da murmushi,takai bakinta kan nashi cike da jin dad'in mgnr sa ta d'aura masa kiss kan lips.
Pens up!!!.
ALHAMDULILLAH! A NAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA
*BINTUWAHEED* INDA NAYI KUSKURE INA ROKON UBANGIJI ALLAH YA YAFE MIN.
AND NA WALLAFAR DA LITTAFIN NAN NAWA GA MASOYIYATA AMINIYATA WATO SADIYA IBRAHIM ALIYU(SADIYA BURSAR)
WATO ILA'S WIFE😎.
KI SHAFA MIN KAN YARONA ABU-SIFYAN😍.
BANCE JIDDA BA FAH EHE😚
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
LUV U ALL MY FANS INA K'AUNAR KU HAR RAINA BA KUMA ZAN TA6A DAINAWA BA.
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
0 comments:
Post a Comment