_THE DARK FOREST_
0⃣1⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
*Godiya*
godiya da yabo sun tabbata ne ga Allah mabuwayin sarki, wanda iyawarsa da ikonsa suka kewaye zarce tunanin duk halittu, ba shakka shi ya mallaki duk wani abu da yake samamme, wanda muke iya gani da ma na fake.
salati fiye a kirga nayo gun manzon tsira, Muhammadu wanda ya tarwatsa kafirci, wanda ta sanadiyyarsa musulunci ya habaka bayan jahiliyya ta masa rarrakar gara.
ka dada tsira da aminci ya Allah gun iyalan gidansa hadi da sahabbansa da suka sayar da rayukansu domin nuna soyayyarsu gareka da kuma manzonka, tareda duk wanda yabi turbar manzonka ys zuwa ranar tsayuwa.
ina mika godiya ga mahaifiyata da ta sha dawainiya da ni har na kawo wannan matakin, ya ubangiji ka sada ta da gidan aljannarka amin.
masoyana kuma ina dada yabo da mika godiya gareku, kun zamo wasu bangare na rayuwata, dabazarku ce nake taka rawa, inajin dadin addu'o'i da shawarwarinku, Allah ya bar mu tare amin.
```Tsokaci```
mai karatu wannan labarin kagagge ne, ko kadan ba wani abu da ya faru a iya nawu sani da ya faru da gaske, labari ne da ke dauke da ilmantatwa kan littafin ~Bible~ da kuma nuna illar daukar kai ga jama'a da nuna koma rintsi ko wuya, ubangiji na nan, haka littafin ya karkata wurin nishadantarwa ta fannin abubuwan da zasu gudana a _Bakin jeji_. wannan jejin sam babu shi a wannan hanyar garin _Kamba_ na kirkireshi ne kawai.
labari ne na _Ameer_ marubuci tareda wata yar jarida mai masifa maisuna _Aseeya_, tateda wata mabiya addinin kirista da wasu samari guda biyu da kuma wani tsoho sai driver.
zamu ga yadda suke tafiya a mota daga Birnin Kebbi zuwa Kamba, inda a hanyarsu zasu ci karo da 'yan fashi, inda zasu runtuma cikin _Bakin jeji_, zasu rayu? me zai faru da su?
duk zaku sami amsoshinku a cikin labarin.
08034840276
Kamba......Kamba......Kamba.....Kamba kawai ke fita daga bakin _conductor_, a guje ya sheka lokacin da ya hango mashin dauke da _passenger_ mashin din kirar Bajaaj ne ja a kala, tun kafin mashin din ya saukar da ita ya fara kokawar karbar Jakarta da dayan _conductor_ da ke saka lodin Yauri.
''Haba meye haka malamai? So kuke Ku tsinkamin jaka ne?'' Ta fada a dai dai lokacin da take saukowa daga kan mashin din.
''Nawa ne kudinka'?' ta fada a yayin da ta mayar da hankalinta ya zuwa D/Acaba da ya dauko ta.
''Naira 60'' ya fada ba tareda ya kalleta ba, kasancewar hankalinsa yana gun masu kokawa kan wace mota za a saka Jakarta.
Maganar da ta jefo ita ta mayarda hankalinsa zuwa gateta. ''Unguwar *BADARIYA* fa ka dauko ni, idan akayi magana sai kuce dollar ta tashi, haba Ku dinga kimantawa mana, ba domin kaya da nake dauke da su ba wallahi sai in tako kasa,'' cikin murmushi yace 'Hajiya ai kayan sune
suka Kara tsadar kudink'
''ba damuwa'' ta fada a dai dai lokacin da take kokarin dauko kudi cikin yar karamar Jakarta, ta mikamasa naira Hamsin da naira goma.
''Allah ya kiyaye hanya' 'ya fada a yayin da yake kokarin buga mashin dinsa.
Ba tareda mayar masa ba, ta juyo wurin Jakarta a lokaci daya tace, ' *Kamba* zanje'
''Kaji ba'' dayan _conductor_ ya fada tareda kokarin kwace jakar daga hannunsa rike da hannu daya.
''Kudinki #1000'' ya fada a lokacin da yake kokarin daukar jakar zuwa bayan mota golf 3 wacce suke cikawa da mutum shida
'Mu nawa ne a motar'? Ta fada dai dai lokacin da take dauko kudi daga jakarta tana kirgawa.
''Ke ce ta uku,'' ya fada a lokacin da yake soke kudin da ta bashi a aljihu.
Leka motar da zatayi sai taga wata mabiyiya addinin kiristanci a cikin kujera zaune ta baya, kusa da ita kuwa wani dattijo ne da zai iya kaiwa shekaru 50, bayan ta gaisa da su, ta nemi wuri ta gaba ta zauna, sai ta fidda littafin *laifin waye... Ni ko yarena?* na _zainuddeen Zain_ ta fara karantawa.
Gaban stadium wanda yafi shahara da Haliru Abdu Mini Stadium Birnin Kebbi, wuriv ne da aka mayar tamkar tasha inda duk garin da ke kudanci ko yammaci da Birnin Kebbi to zaka sami motarsa a gurin.
Kamba, Yauri, Minna, Kalgo, Jega da dai sauransu, garuruwa ne da duka zaka Sami motocinsu a wurin, abinda yav kawo cigaban wurin baifi yadda motoci suke saurin cika ba.
Nan wasu mazaje matasa suka zo bayan mintuna kadan sai ga wani saurayi ya karaso, ba tareda bata lokaci ba direba ya fara hanya.
Tun fara hanyarsu ba wanda ya cewa wani uffan.
Nan christian mai suna FATE ta rufe idanuwanta ta karanto wasu addu'o'i daga littafin ~BIBLE~ dattijon da ke kusa da ita tun ba aje ko'ina ba ya fara tsarguwa da ita. Sai abokani biyun da suka zo tare Saddam da Abdul-Samad, gaban mota mutum biyu ne da 'yar unguwar BADARIYA wacce sunanta Asiya Abubakar sai na kusa da ita mai Suna Ameer.
Ba Wanda yaji bakin Ameer tun saukarsa a kabu kabu fuskarsa a daure kamar Wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
Aseeya doguwa ce chocolate ce, tanada diri sosai me Jan hankalin duk wani lafiyayyen namiji, amma ko kusa bata daukar raini, duk abinda ke ranta takan fadeshi komai zafi ko dacinsa.
Kyakkyawa ce sosai kuma ga murya mai dadi.
Ameeer fari ne matsakaici, kyakkyawa ne ko kusa bayason surutu ko hayaniya.
Yana a duniyar tunaninsa ji kawai yayi ASEEYA ta takashi, cikin bacin rai tace ''malam baka gani ka takani? Ko ni dutsi ce da zaka taka ba ko sannu?''
''Yi hakuri' 'ya fada cikin sanyin murya ba tareda ya ko kalleta ba.
Ta soke kanta taci gaba ta karatun littafinta.
Labarin ba fara ba
ku biyoni
dr.zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣2⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
08034840276
*waiwaye daga shafin baya*
kar maikaratu ya manta, mota ta cika, inda Ameer da Aeeya suke a kujerar gaba, a baya kuwa; mutum hudu ne, da kirista mai suna Fate, sai Abdulsamad da Saddam da tsoho.
sun dauki hanya ba tareda wani tsaiko ba.
_cigaba_
daga fitarka a tashar laulaya daya kadai zaka wuce wacce zata baka damar ficewa barka da zuwa ko ka dauki hannun hagu zuwa unguwar filin sukuwa.
Daf da laulayar ta hannun damma akwai gidajen mai guda biyu, da direba yazo gidan mai na farko sai ya tsaya domin ya karawa tankinsa mai.
Ai kuwa sukayi sa'a ba layi motoci uku ne kadai a gabansu sai masu mashin su biyar.
Bayan direban ya tsayarda mota sai Aseeya ta cewa Ameer 'Malam kayi hakuri inaso in fita insha iska'
Kamar baiji me ta fada ba, sai da ya dauki lokaci kafin ya motsa, a ranta tace, 'kar ma ka fita wallahi da sai in taka ka in fita'
Nan ta dinga zagayo gidan mai din, sosai fasalin ginin ya birgeta, abinka da mace bata ko kula da dinbin mutane da ke wurin ba, sai faman daukan hoto take.
Ameer kuwa ba abinda yakeyi in ba dannar waya ba, idan ya fita wannan shafin ya shiga wannan, sai bincike bincikensa yakeyi.
Bayan an kammala saka musu mai, suka koma cikin mota direba ya fara hanya.
A kujerar baya Abdul samad da Saddam sai gulma suke suna kus kus kan Aseeya lallai kyakkyawa ce, sai dai kash akwai ta da tsiya ga masifa, dukkansu har sun fara tsoronta.
Fate kuwa tun fara tafiyarsu bayan ta kammala addu'a irin nasu ta bude ~Bible~ ta ci gaba da karantawa.
Dai dai isowarsu barka da zuwa (welcome to) nan Ameer ya fara magana, yace 'tabbas canji ya fara duk da mu talakawa mun kasa hakuri yadda ya kamata'
''Me yasa ka fadi haka?" Aseeya ta fada dai dai lokacin da take juyowa ta fuskanceshi.
''A gwannatin da ta gabata'' Ameer ya cigaba, ''a nan barka da zuwa da zarar ka karaso hannunka a gaba, sojoji da 'yan sanda ba za ka wuce ba har sai ka bayar da wani abu na kudi, naira 20 ko 50, idan kaki ka fuskanci wulaqanci, amma ji yanzu duk sun kama aikin da ya dace, ko wannan ai ci gaba ne.'
'
''Haka ne'' Dattijo da ke baya ya fada, a daidai lokacin da yake kokarin gyara zamansa kasancewar a matse suke a baya.
Da zarar ka wuce barka da zuwa garin Sabon gari ne zakayi kicibis da shi wanda dama da hangun titi duk shi ne, sai dai a bangaren hagu garin yafi yawa a dama makaranta ce kawai sai gidaje marasa yawa.
Muatanen garin sun kware ne a noma da kamun kifi kasancewar suna makotaka da ruwa.
A titin bakin garin mutane ne cike da sana'o'insu kala kala.
Haka suka ci gaba da tafiya sai fira akeyi da juna cikin motar.
Lafiya lau suka karaso junction na garin Kalgo, junction ne da idan ka mike tsaye zaka isa Basaura sai Jega, idan ka shiga ta dama zaka iya karasawa zuwa Bunza ya zuwa Kamba.
Suka shiga kwanar dama kasancewar Kamba suka nufa.
Abin sha'awa yadda titin ya kawatu da shaguna da sana'o'i daban daban a hagu idan zaka wuce kasuwar garin ce, wacce ke ci duk ranar alkhamis.
Direba ya taki motarsa suka kara nutsawa cikin jeji, har suka karaso inda aka gina parmanent site na FUBK ( _federal university birnin kebbi_)
Ku biyoni har yanzu labarin bai fara ba
dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣3⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
*Shafin masoya*
Queen (fake queen)
Rabeauty (gwauruwa)
zeety
Nordeen Amrabat
Maimartaba
*waiwaye*
_shafin da ya gabata, munji firar mahayan motar ta cigaba da akasamu fannin tsaro da sauransu, haka munji cewa motar ta cigaba da tafiya har suka karaso a ginin makarantar FUBK, har yanzu da saura, labarin bai fara ba_
*cigaba*
'Kai makarantarnan gaskiya ta ginu, sai dai akwai courses da dama wadanda basa cikin tsarin makarantar har yanzu'
Maganar da ta fito daga bakin Abdul-Samad kenan; 'kasan sabuwa ce' dattijo ya fada.
'Sai nake ganin kamar gate din school din yayi kusa da titi sosai lura da wannan titin babba ne'
inji Abdul-Samad.
'Kai malam injiniyoyin da sukayi aikin ne takkwalai ko me kake nufi? In ce, sai da aka tara manyan injiniyoyi kafin a fara wannan aikin, daga sama zaka zo kace gate din baiyi ba; duk wanda ya raina tsayuwar wata ai sai ya hau ya gyra'
Asiya ta fada a lokaci daya kanta na sunkuye sai karatu take zabgawa.
'Hahahahahaha'! Saddam ya fashe da dariya, ya dinga tokarar abokinsa da yatsa yana tsokanarsa.
Cike da tsarguwa Abdul samad ya ko kasa iya furta wata kalma, duk da a ransa ji yake kamar an tsoma shi a dakin dahuwar biredi.
Dattijo ne yace 'wai ke diyata wace iri ce? Sai angama fira da ke lafiya, lokaci kadan sai ki birkice? Gaki kyakkyawa wannan fadan zai kore maki samari fa'
Ameer tuni ya suku sai murmushin dole ke fita a lallausan kumatunsa
'Ai kai baba, duk wanda yace ya goya samarin zamani ai bansa hujewa zaiyi, ba abinda ya ragewa samari idan ba karya ba, bokonnan shi kadai mazajen nan kebbi suka dogara da shi, sai su gama aiki yazo yayi tsaye, gwannati tayi dasu su koma noma da kiwo, Ball da ji da kai da gayu sun hana, sun manta sam a farkon wannan kasar ta noma muka habbaka, wallahi baba mannan da kake gani zai baka mamaki, nomannan da kiwo da muka raina su ne dai abin kamawa'.
'Diyata zancenki dutse, gaki karama amma da tunani....'
Abdul ya kado bakinshi,
'ai matan yanzu ne basada alkibla, in banda kwadayi ba abinda suka saka a gabansu, shaye shaye da lesbianism sunyi yawa a cikinsu har basa ko kula samari...'
'Kajika tau shaye shayen tareda wa sukeyi? Wa ke dauko musu abubuwan da zasu sha? Mace zaka gani 'yar Islamiyya amma duk yadda za a lalata ta gayu sun sani.'
'Lallai da sauran ki 'yaruwa, mata ai yanzu sune diloli na miyagun kwayoyi, kedai Allah ya shigemuna gaba.'
Fate tace, 'hmmmm ai bantaba ganin masu yaudarar kansu irin miutanenku (musulmi) ba, kunce ku salihai ne, kuma kuke shan kayan maye'.
Cikin sauri Ameer ya waigo kamar dama jiranta yakeyi yace 'in banda ke ai gara mu littafinmu yasan matsayar da yayiwa shaye shaye, mutane ne a ko wanne addini sai ka sami bata gari wadanda basa biyar karantarwar addininsu, bari in karantomaki wasu ayoyi daga littafinku kiji kwamachalar da ke ciki'
A littafin *BIBLE* _in the book of_ ```Isaiah chapter 55 verse 1-2``` *Ho, every one that thirsteth, come ye to the waters, and he that has no money, come ye, buy, and eat; yea, come, buy wine and milk without money and without price.*
*2. Wherefore do ye spend money for that which is not bread? And your labour for that which satisfieth not? Hearken diligently unto me, and ear ye that which is good, and let your soul delight itself in fatness*
Wannan daga *KING JAMES VERSION* ne na *BIBLE*
'idan kika lura sun zargi sayen giya a cikin wannan ayar.'
'Ki duba kuma _book of_ ```Isaiah chapter 56 verse 10-12```
*his watchmen are blind : they are all ignorant, they are all dumb dogs, they cannot bark; sleeping, lying down, loving to slumber.*
*11. Yea, they are greedy dogs which can never have enough, and they are shepherds that cannot understand; they all look to their own way, every one for his gain, from his quarter.*
*12. Come ye, say they, i will fetch wine, and we will fill ourselves with strong drink; and tomorrow shall be as this day, and much more abundant.*
_KING JAMES VERSION_
'a nan ma an zargi shan giya idan kika natsu kika karanta.'
'Ga wasu'
*ISAIAH 5:12-13*
*PROVERBS 23:29-33,35*
*PROVERBS 23:30-31*
*PROVERBS 31:4-7*
Duka wadannan ayoyin sunyi kashedi ne da hannunka maisanda kan shaye shaye
*bible* bai barku ba har sai da yaimaku gargadi kan shaye shaye.
```Book of Isaiah chapter 28 verse 1```
*woe to crown of pride, to the drunkards of Ephraim, whose glorious beauty is a fading flower, which are on the head of the fat valleys of them that are overcome with wine.*
_KING JAMES VERSION_
Ki duba
*romans 13:13*
*luke 21:34-35*
'Idan har haramtawa ce gashi kin gani a littafinku, a yau a Birnin Kebbi ke a ma wurare daban duk inda ake shangiya zaki tararda *Pastors* ne kan gaba, me yasa ba za su hanu ba?
Ko wanne addini dole zaki zaki tarar da mashaya, amma ki daina kyamar wani addini shi kadai.'
Duk wadannan hujjojin yana fada tana buda littafinta na *bible* domin gasgata ko karyata shi, inda ta ga duk ayoyin haka ne.
'Kai musulmi ne kuwa' Asiya ta fada a lokacinda take kallonsa.
Cikin murmushi yace 'hala ke 'yar jarida ce? '
Naga duk nayi magana sai kinyi tambaya
Ba tareda tace komai ba sai ta mikamasa Id card inda ya tabbatar ita 'yar jarida ce da ke aiki karkashin *JARIDAR DIMOKURADIYYA* da ke da cibiya a garin kaduna.
'Ni musulmi ne, rubutu da bincike ne aikina.'
A dai lokacin suka karaso a junction da zaka dauke zuwa garin *diggi*
har yanzu labarin bai fara ba
dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣4⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
*Waiwaye*
_A shafin da yagabata, mun ji yadda shaye-shaye ya zamo har a cikin mata, da ake tunanin sune jigon tarbiyya, haka munji yadda ~Bible~ da addinin musulunci suka haramta wannan mummunar dabi'a. haka munji ashe masifaffiya Aseeya 'yar aikin jarida ce, munji Ameer da ke zaune tare da ita a kujerar gaba, marubuci ne kuma mai bincike._
*Ci gaba*
Junction din garin Diggi zai iya sadaka da garin Tilli idan ka tsallaka ruwa haka zuwa Zogirma har zuwa Bunza da sauransu.
''Tunanina 'yan Jarida basada masifa amma a naki labarin daban ne''
Ameer ya fada daidai lokacin da yake kokarin ajiye wayarsa a aljihun rigarsa na gaba.
''Ni kuma tunani Marubuta akwai su da surutu da iya feso karya.''
Ta fada ba tareda ta ko kalleshi ba.
''Ai abubuwan da muke rubutawa a littafai ba karya ba ce.''
''Okay now tell me, labaran da kuke yi na yaki, ya ma za ayi ya zama gaskiya, mutum daya sai kaga ya tarwatsa rundunar sadaukai dubu. Ko wai kaga mutum yana tashi a sararin samaniya.''
''Hmmm! 'yar Jarida; labaru da muke yi na rayukan jama' a hasashe ne, sau tari wasu are based on true life. Na yaki kuwa domin nishadi ne da kuma haskowa mai karatu wani abu da zai fadada tunaninshi.
Amma kinga ana zarginku da labarun kage ko sauya labari idan aka cika maku aljihunku..''
''Haba ai cin hanci na wadanda basusan aikin Jarida ba ne, amma ai Dan Jarida muryar al'umma ne, idan ya sayar da kansa talakawa ne ya sayar.''
''Hakane diyata'' tsoho ya fada
Haka suka ci gaba da tafiya har suka karaso garin DANGOMA
Abdul Samad ne yace 'yanzu idan inaso in zama marubuci ya zanyi abokina?
Ina sha'awar rubutu amma sai nake ganin kamar bazan iya ba'
''Ba abinda ba ya ke da wuya aboki matukar mutum zai bi daki-daki na ka'idoji na yadda aka tsara komai. matsawar za ka iya jure biyar dokoki zama marubuci abu ne mai sauki,
Misali akwai wanda shi da rubutu aka haifeshi a jininsa rubutu yake, irin wannan idan ya fahimci kansa sai yayi kokarin neman shawarwari wurin manyan marubuta da kuma dagewa wurin bincike
Akwai wanda koyon rubutu yake ba a haifeshi da shi ba, idan ya fahimci kansa sai ya yi kokarin gurfanawa gaban manyan marubuta suyi masa bita.
Inaga kana cikin kashi na biyunnan''
''Nagode abokina zan karbi lambarka idan mun sauka sai muji yadda ya dace infara domin inada labarai da nakeso na rubuta''
'Idan kuwa haka ne, kar ka saka wasa, yanada kyauka hanxarta, domin baiwar rubutu ba abin wasa ba ce.'
''Allah ya taimaka''
Driver ya fada dai dai lokacinda yake canja wakar da ya saka a motar
''Subhanallahi!''
Driver ya fada
Cikin nuna damuwa da matsanancin tsoro suka hada baki
'me ya faru'?
''Wallahi faci ne muka yi,''
a dai dai lokacin da yake parking na motar a gefen titi rabin kilometer daga fita garin DANGOMA.
'yanzu ya kakeso muyi, shi ne ake cewa 'yan tasha bakusan darajar mutane ba'
''Bauyar Allah ya kikeso nayi ne, ai ni ba Ubangiji ba ne da zan iya hana wani abu ya faru, kuma dai kowa shaida ne ba gudu nake yi ba
Ya kina magana kamar ba musulma ba, ko wannan aljihun bayar ai bazata fadi haka ba''
ya fada cikin bacin rai, kamar ya kai hannunsa kan ta.
''Dakata malam''
Fate ta fada cikin rashin iya Hausa sosai
''Meye aljihun baya kuma naga sai da ka nuna ni kafin ka fadi hakan?''
Saddam ne ya sarbe maganar da cewa
''Kafiri ne aljihun baya wanda bai yarda da Allah ba''
''TO ai mu kirostoci mun yarda da Ubangiji''
ta fada cikin izza
Ameer ne ya kwace maganar
''wane irin imani kuka yi da Ubangiji?''
''Don Allah ku fita''
Driver ya fada
''ku karasa cen a waje taya zan canja''
kamar fama jiransa take ta sarbe cikin fushi, 'Ai dole mu fita malam, domin ba zamu tsaya ba zafi ya illata mu''
Duka suka dugunzuma waje
Nan Ameer ya matso kusa da Fate yace
'' inajinki baki bani amsar tambaya ta ba''
Ku biyo ni har yanzu labarin bai fara ba
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣5⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
08034840276
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
*Waiwaye*
_A shafin da ya gabata, mun ji yadda ya dace 'yan jarida su kasance, haka mun ji kalar marubuta da matakan farko da ya dace sabon marubuci ya bi domin ganin ya zama marubuci_
*ci gaba*
```
'mu kirostoci mun yi imani cewa Ubangiji shi ya halicci sammai da kassai da dukkanin halittu a cikin kwanaki shida. Kamar yadda yazo a littafi mai tsarki ```book of genesis``` *1:1-29*
Haka kamar yadda yazo wurare har bakwai a naku littafin'
'Eh naji wannan amma har yanzu baki sosa inda ke yin kaikayi ba.'
'Me kake so kace ne?' ta fada a lokacin da take kallonsa cikin idanu
'Kuna fadar cewa Annabi Isah Allah ne ya sauko daga sama in flesh domin yazo ya wanke zunuban duniya ta hanyar mutuwa kan cross'
'Sosai hakane, Isah Allah ne kuma ya mutu ne domin ya wanke zunuban duniya bayan kwana uku ya taso daga kabari'
'Idan haka ne a lokacinda Annabi Isah ya mutu din, wa ke kula da lamurran duniya?'
'Ubangiji mana. Allah uku ne amma daya ne, baka taba Jin trinity ba ne? Akwai God the father God the son da kuma God the holy spirit amma abu daya ne'
'Ko zaki iya kawo ayar da ta fadi haka a littafinku na ~Bible~?'
'Sosai zan iya
```first epistle of John 5:7```
*for there are three that bear records in heaven, the father, the word and the holy ghost and these three are one*'
'Wannan ayar da kika karanto daga littafin king James version ne'
'Eh daga gare shi ne'
'Ina zuwa ya fada a dai dai lokacinda yake komawa a mazauninsa ya dauko yar jakarsa ta ratayawa ya fara tono littafai da su Kadai ne sai laptop a cikinta. Cen ya fiddo da wani ~Bible~ na daban da wanda ke hannun Fate.
A jikin Bible din anrubuta *REVISED STANDARD VERSION OF THE BIBLE* bugun 1957
Sai ya budomata daidai first epistle of John 5:7 yace 'karanta'
Sai ta karanto kamar haka...
'there are three that bear witness'
Cikin damuwa da matsanancin sauri ta juya littafin ta sake karanta sunansa da ke jikin bango ta kuma kalli Ameer. Ta kasa hakuri tace 'anya kuwa wannan ~Bible~ ne'?
' kar dai ki gayamin cewa ko sunayen littafanku musawa kuke yi '?
Ya fada cikin murmushi
'Ki karanta shimfidar littafin wato preface zaki gamsu'
Bayan ta karanta sai yace 'me aka rubuta'?
'Sunce King James version na ~Bible~ yanada kurakurai kuma kurakuren sunyi yawa ta yadda dole sai anyi gyara shi ne aka yi shi wannan Revise standard version of the Bible domin fassararsa tafi kusa da ainihin ~Bible~ na asali'
'Haka ne' Ameer ya fada 'a littafai da dama manyan malaman kirostoci Sunce wannan ayar sam babu ita a ~Bible~ na asali.
Bugu da kari a littafinku an nuna Allah daya ne'
'Ko zaka iya nunamin'
'Sosai kuwa
Amma kafin imfara kawo maki nawu hujjoji bari infara rusa wadanda kika kawo.
Kikace Annabi Isah yazo nan duniya kuma a surar mutum a matsayinsa na Ubangiji ya kuma mutu domin ya wanke zunuban duniya ma'ana zunubin da Annabi Adam ya aikata na cin haramtacciyar itaciya cikin aljanna?'
'Sosai haka ne
Mun karanta a ~Bible~ cewa Ubangiji ba ya mutuwa
Misali
```Habakkuk 1:12 "are u not from everlasting, O. Long my God, my holy one who never dies"? ```
```1 Timothy 6:15-16" *and this will be made manifest at the proper time by the blessed and only sovereign, the king of kings, long of lords who alone never die. And dwells in unapproachable list whom no man has ever seen nor can see. TO him belong honour and eternal dominion Amen".*
(Jerussalam Bible)
'Wadannan ayoyin suna kokarin hasaso muna cewa lallai Ubangiji ba ya mutuwa. Kinga ko idan har Annabi Isah ya mutu ya taso to ba Ubangiji ba ne, nasan kinji cikon dayan ayar da tace ba wanda ya taba ganin Ubangiji kuma ba wanda zai iya ganinshi, Annabi Isah ba ganinshi Kadai ba ~Bible~ ya gaya muna har marinsa anyi.
Tambaya anan itace da ya mutu din wa ya tada shi?'
Har yanzu labarin bai fara ba Ku biyo ni
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0⃣6⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
08034840276
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
*Qoute of the day*
_Frog's eyes never stop a cow from drinking_
*Waiwaye*
_A shafin da ya gabata, mun ji cewa Annabi Isah ba ubangiji ba ne, haka hujjar da kiristoci suka dogara da ita, ba makama ba ce, domin ayar sam ba ita a ~Bible~ na asali_
*Ci gaba*
'Ubangiji ne ya ya tada shi mana,' ta fada cikin nutsuwa da izza.
'idan da gaske shi ubangiji ne kuma ya mutu har na tsawon kwanaki uku, duniya a lokacin wanne hali ta shiga? me zai faru da sauran ubangizai guda biyun, inaga tun da kince duk daya ne dole suma mutuwa za su yi, kinga kuwa duniyar ta rayu ba ubangiji, maganar hankali ba zai dauka ba.'
Abdulsamad ne ke gayawa abokinsa Saddam cewa shi ko kusa ba zai iya jure yunwa ba, ya nemi abokin nasa da ya raka shi cikin garin domin ya samo dan abinda zai saka a ciknsa, 'abokina, dama nasan kai mai mugun ci ne, duka ko awa daya fa ba muyi ba da muka ci abinci a tasha kafin mu taso', 'wai ina ruwanka?'
Abdulsamad ya fada, 'idan za ka raka ni kazo mu tafi tun kafin lokaci ya kure, kaga driver ya fara aikin sauya tayar', 'ba inda xani, azo a kammala bana kusa.'
'haba abokina, zo muje mana', 'okay naira nawa zaka biya'? 'wallahi zan ci...don..ka manta yadda na samo kudin mota da kyar? sai da na sayar da wayata daya'. 'Na fasa, da nayi niyyar rakayar taka,' 'haba tau zo muje idan na hau kujerar shugaban kasa zan biya.' 'hahaha! muje, amma bari mu sanar da su', 'kar kayi, wadancen firarsu suke masifaffiya kuwa kaga kallonsu ne aikinta, duka ba zamu wuce minti goma ba, nasan zamu dawo kafin a kammala. ba damuwa.'
Dattijo da Aseeya sai suka dawo 'yan saurare da kallon Ameer da fate, inda driver yake kokarin saka jack ta kasan mota domin ya fitar da taya, bayan a jibge sifanu a gabansa.
'mun karanta a cikin littafinku,' Ameer ya cigaba, 'cewa Yahudawa da aka aika Annabi Isah a wurinsu, sun bukaci da ya xo masu da mu'jiza idan yana so suyi imani da shi, sai ya ce zai zo masu da mu'jiza irin ta Annabi Yunusa. Annabi Yunusa ya yi wa mutanensa wa'azi tsawon lokaci, amma mutane kalilan suka karba kiransa, sai ya fusata yayi yunkurin ya bar garin ya zuwa wani gari, kasancewar ubangiji bai bashi dama ba, akan hanyarsa sai kifi ya hadiye shi. yayi kwanaki uku a cikin cikin kifi (dare uku da wuni uku) yanayin addu'ah kana ubangiji ya fiddashi inda kifin ya amayo shi.'
tace 'eh! Haka labarin yake ko a namu littafin' (book of Jonah)
'bari na karanto daga littafinku.' Ameer ya fada
MATHEW 12:38-40. (Mathew chapter 12 verses 38 to 40). “ *Then certain of the scribes and of the Pharisees answered, saying”, ‘master we would see a sign from thee’. But he answered and said unto them, ‘an evil and adulterous generation seeketh after a sign; and there shall no sign be given to it, but the sign of the prophet Jonas: for as Jonas was three days and three nights in the whale’s belly; so shall the son of man be three days and three nights in the heart of the earth.’* (KING JAMES VERSION)
LUKE 11:29-30. “ *And when the people were gathered thick together, he began to say” ‘this is an evil generation: they seek a sign; and there shall no sign be given to it, but the sign of Jonas the Prophet. For as Jonas was a sign unto the Ninevites, so shall also the son of man be to this generation’* (KING JAMES VERSION)
'kinga idan Annabi Isah zai cika wannan, dole yayi wuni uku da kwana uku kan cross, kuma dole a isko shi a raye, kamar yadda Annabi Yunusa yake raye ba a mace ba.'
'a sharhin ~Bible~ munkaranta cewa ranar jumu'ah ce da misalin karfe shida na maraice abin ya faru, ~Bible~ ya sanar da mu cewa tun da safe ne ranar lahadi ya taso daga mutuwa, idan haka ne dare biyu kadai sai wuni daya yayi kan cross, kuma dole ya kasance a raye. wannan hujja ce kan lallai annabi Isah bai mutu kan cross ba.'
Nan ta dauki lokaci tana karatun hujjojin daga littafinta mai tsarki, a dayan bangaren kuwa Aseeya ce, sai daukar hotuna take yi, duk da hankalinta sarai yana kan firar da suke yi.
driver kuwa tuni ya cire tayar har ya fara canja wata.
Dattijo ne ya fahimci cewa su Saddam basa kusa, nan ya duba su ta gefen hanya kasancewar mai motar yayi parking ne a gefen titi daf da ciyawu, bai gan su ba, nan zuciyarsa ta darsa masa cewa a garin Dagoma suka shiga, ba tareda ya sanar da kowa ba ya sake dawowa,inda muhawara ke gudana tsakanin Ameer da Fate, wacce tuni jikinta yayi sanyi.
wasu mintuka driver ya kammala saka tayar, ya mayar da tayar da ta yi faci da sauran kayan aiki a bayan mota, sai ya umarci mutanen da su shiga, sai a lokacin suka fahimci cewa su Abdulsamad fa basa kusa, sai duban ta ina zasu fito ake yi. inda Aseeya ke cewa kawai su wuce su bar su nan, a cewarta ya zaayi kan su biyu a batawa mutum kusan biyar rayuwa. driver yayi murmushi yace 'kiyi hakuri, ba zan iya barinsu ba, daga gareji, amanarsu ce aka bani, kuma alkawari ne na dauka cewa zan saukar da su a garin Kamba, kaddarar ubangiji kadai ta isa ta canja haka', bayan ta saki murmushi a cikin yanayi na hadiye fuska, tace, 'ai kaddarar ce yanzu ta hau kansu'...suna cikin musanyar zance, sai suka hango su tafe cikin gudu.
daga karasowarsu, suka bada hakuri, duk da Aseeya ta fara masifa, Dattijo ya shiga tsakaninsu. suka shiga, mota ta fara hanya.
bayan sun nutsu ne dajjijo ke nuna,musu kuskurensu na tafiya su bar mutane cikin irin wannan yanayin. suka kara bada hakuri.
ganin kowa a natse, sai Ameer ya juyo yace da Fate, 'ga hujjoji kan Ubangiji daya ne daga littafinku.'
'inajinka' ta fada, jikinta a sanyaye.
har yanzu labarin bai warware ba bare ya fara, ku biyoni kawai.
Dr. Zain
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
0 comments:
Post a Comment