🧣🧣 *DAURIN BOYE* 🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)✍
*_Dandano daga littafin DAURIN BOYE_*
0⃣1⃣
Sake gyara tsaiwarshi yayi jikin machine din nasa samfurin lifan kirar MOTO B,agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla yana sake qiyasta mintocin daya kashe tsaye a qofar gidan,tabbas banda wani babban dalili babu abinda zaya sanyashi zaman jira har kamar haka,babu abinda ya tsana a rayuwarshi kaman jira,mutum ne shi mai kiyaye qa'ida wanda bai yarda da samfurin wannan maganar da hausawa ke bawa lokaci ba na african time.
Sauke hannun nashi yayi ya maida dubansa ga madaidaicin get din dake maqale da katangar gaban gidan wanda ya kasance shine kofar da zai sadaka da ainihin cikin gidan,kaman jiran hakan kuwa ake qofar ta soma yunkurin budewa,cikin sakannin kadan matashiyar dake yunqurin bude qofar ta bayyana.
A hankali take takowa zuwa inda yake,sanye cikin dinkin atamfa riga fitted da skert wanda ya zaunawa jikinta das,ta lullube jikinta da mayafi wanda baikai matsayin medium ba,a hankali yayi kokarin mamaye fuskarshi da murmushi duk da yadda fuskarta take kadaran kadaham hakan bai dameshi ba duk da yana ankare,ba fara'a sannan ba kuma a daure take can ba,kallo take kare masa tun daga nesa kaman yadda ta saba masa duk sa'ilin da ya ziyarceta,shirt ce jikinsa ruwan makuba da bakin wando jeans mai matsakaicin kudi,kafafunsa saye da takalmi budadde dinkin hannu na kasuwar kofar wambai,fes yake hakanan kayan sun masa kyau babu laifi,sumarshi kanshi zuwa sajensa a gyare a taje wanda hakan ya sake bayyana sirrin kyan da Allah ya bashi,ba shakka banda wani abu guda tak muhammad ya cika mijin aure wanda za'a iya nuna shi a ko ina,saidai wannan abun daya rasa din ya sanya ta cireshi daga tsarin mutumin daya cancanci aurenta.
"Barka da fitowa gimbiya zulaiha" ya fada cikin sassanyar muryarsa wadda na daya daga cikin abinda ke burge zulaihan tare da shi,duk da bata jin zata iya bashi damar kasancewa cikin rayuwarta,yana ci gaba da nazarin yanayin fuskarta a fakaice sanda ta amsa masa
"Barkan ka" ta fada cikin wani salon shan qamshi da basarwa
"Har na fidda rai ai,na tsammaci yau bazan samu ganinki ba"
"Kusan da hakan ce ta kusa faruwa,saboda zamu fita ne da maama,sannan ma kuma bansan zaka zo din ba,yanzun ma zuwa nayi na gaya maka.....don Allah ya kamata ace duk sanda zaka zo ka fara sanarmin tukunna kafin kazo din"ta fada kanta tsaye tana yamutsa fuska murmushi ya saki gami da dan duqar da kanshi qasa yana wasa da duwatsun dake shimfide a qofar gidan,baice komai ba sai murmushin da yaci gaba da fitarwa yana tattaunawa shi da zuciyarsa,tabbas yasan wannan rana na nan tafe,fiye da haka kuma na nan zuwa nan gaba kadan,wannan ba baqon lamari bane a gareshi,zulaiha ba itace mace ta farko da makamancin hakan ta faru tsakaninsu ba,saidai bazai yanke mata hanzari ba,zai jirata har zuwa ranar da zai zata furta kota yanke alaqar dake tsakaninsu da bakinta,sai bayan daya kammala wannan tunanin sannan ya dago ya dubeta
"Shikenan....babu damuwa...kiyi hakuri" ba tare data tanka ba ta juya tana niyyar komawa cikin gidan nasu
"Ki gaida maaman idan kin shiga"
"Zata ji" ta fada gami da jan qaramin tsaki can qasa ta shige gidan gami da rufe qofar gidan garam.
Kai ya girgiza bayan shigewarta cikin gidan yana sakin murmushi tare da cije lebansa na qasa,cikin qwarewa ya haye saman babur din bayan ya tadashi ya figeshi cikin gudu ya fice daga layin,zuciyarsa cike fal da tunani da mamaki,mamakin da har yau yaqi barinsa,tsahon shekaru kenan wannan abu na daure masa kai,da gaske haka rayuwa ta koma?,ya gode Allah da baiyi gaggawar yiwa hukunci wa rayuwarsa ba.
Titi ya hau ba tare da yayi wata doguwar tafiya ba ya soma sauka daga kan kwaltar zuwa gangaren titin,daf da wasu jeran baqaqen motoci da farare a qalla guda biyar ya soma qoqarin tsaiwa,wanda tun kafin ya kai ga tsaiwar wasu matasa kimanin su bakwai sanye da coat baqi da fari suka doso shi,kowanne fuskarshi manne da baqin gilashi wanda hakan ya sanya baka iya ganin qwayar idanunsa,ya kuma qara musu kwarjini qwarai,daya daga cikinsu shi ya riqe babur din sanda ya sauka,yayin da dayan ya matso kusa da shi yana bude masa qofar daya daga cikin motocin wadda duka ta fisu kyau da girma,sai da yaga ya shiga sannan ya rufe masa qofar,sauran suka zagaya suka shige ragowar motocin nasu,yayin da daya daga cikinsu shi kuma ya haye babur din ya bisu a baya.
"Ya dai,akwai wani sauyi ko ci gaba kuwa yau?" Wani kyakkyawan matashi wanda aqalla zaiyi shekara talatin da hudu dake zaune daga corner motar riqe da magazine ya fada yana dubanshi,fuskarshi na nuna alamun dariya yakeson yi,takalman qafarsa ya soma yunkurin cirewa gami da agogon hannunshi ba tare daya dubeshi ko ya amsa masa ba,ya dannan wani madanni dake gaban sit dinshi,wani qaramin akwati ne ya fito ya zuba agogon takalmin harda wayar dake hannunshi qirar VIVO bayan ya kasheta,ya maida akwakwun muhallinsa ya jingina da makarin kujerar sannan ya waiwaya ya dubeshi
"Me kake tunani mahmoud?,ita dinma kaman sauran,abun ma kamar yana sake lalacewa ne" ya qarashe maganar yana lumshe idanunsa tare da sauke numfashi
"Duk inda xaka je ka dawo dai shawarata ce kan hanya,na sha gaya maka ka sauqaqewa kanka walaha,ka laluba cikin familynka,akwai gomayyar 'yammatan dake sonka ka zabi daya cikinsu ka huta,kaga wannan babu wani fargaba tattare da kai,duka ana tare". Kansa yaci gaba da girgizawa ba tare daya bude ido ya kalli mahmoud ba,tsahon sakanni tamkar bazai amsa mishi ba sannan ya ware idanunsa yana duban sit din dake gabansa
"kana tunanin qaramin abu ne ya sanya na guje musu dukkaninsu na xabi inbiyo ta wannan hanyar?,su dinma kusan duka abu guda ne,babu wani banbanci,halayyar daya ce dai kaman yadda sunansu yake daya,abu guda dukkaninsu suke wa,manufarsu guda ce......" Maganar tashi ta katse sakamakon shigowar kira wayar tasa,ya maida qwayar idanunsa ahankali kan wayoyin dake zube a gefansa,kusan lokaci guda idanunsu shida mahmoud suka sauka kan wayar RAMLA sunan dake yawo kenan bisa screen din,murmushi mahmoud ya saki ganin ya kau da kanshi tamkar ba cikin wayarshi kiran ya shigo ba
"Yallabai ka daga mana?"
"Qyaleta kawai" ya bashi amsa kai tsaye gami da danna wani madanni,wani dan qaramin abu mai kama da fridge ya bayyana,cikinsa nau'ikan abubuwan sha ne masu sanyi da duka duka basu wuce gwangwanaye da kwalba goma sha biyu ba,daya a ciki ya dauka hadi da cup ya maida abun muhallinsa ya koma ya jingina da kujera ya tsiyaya yana kaiwa bakinsa ba tare da yabi ta kan qorafin daga waya da mahmoud ke masa ba,a maimakon hakan ma sai ya maye gurbin qorafin nasa da tambaya
"Jirgin qarfe nawa zamu bi ne?" Tunda ya masa hakan yasan bai bukatar xancan,saboda haka shima ya tayashi
"Yanzun airphort din muka nufa ai,tunda duka duka awa guda da 'yan mintuna ya rage lokacin tashin jirgin ya cika"
"Ok,kafin nan mu biya na sauya kayan jikina"
"Ba matsala" ya fadi yana gayawa driver inda zasu fara zuwa kafin su isa airphort din.
🧣🧣🧣🧣
A nutse ta miqe daga saman abun sallar tana sakin 'yar qaramar hamma tare da furta "a'uzu billahi minash shaidanir rajim" gami da ninke daddumar ta mata ma'ajiya a muhallinta,zare hijabin jikinta tayi tanayi tana duba agogon dake maqale a bango saboda gudun makara,qarfe shida na safiya ya nuna mata,hakan ya mata dadi ta tabbatar kafin lokacin tafiyarsu makaranta ta kammala dukkan abinda zata yi din,gyara dankwalin kanta tayi wanda ke niyyar zamewa saboda santsinsa da kuma santsin sumar kanta,sannan ta zura slippers ta bude qofar dakin nata ta fita a hankali.
Makekan falon nasu shiru yake tamkar babu halittar kowa cikin gidan,bugu da qari mamaye yake da dan sauran duhun asuba da bai gama yayewa ba,babu motsin kowa,don hatta da masu aikin gidan basu tashi ba,kunna qwayayen falon tayi take haske ya game ko ina ya kuma bayyana asirin kyan da falon ke da shi,sannan taci gaba da takawa a hankali ta doshi wani corridor wanda a nan kitchen dinsu yake.
Kitchen ne na alfarma wanda ya mallaki dukkan wani nau'in kayan amfani da kitchen ka iya buqata,kai tsaye ta nufi jikin wani dan qaramin Allo wanda ke dauke da timetable na abincin da gimbiyar gidan ke buqata kowacce rana,alhamis ce saboda haka ta sauke idanunta kan THURSDAY dake rubuce baro baro,ta kuma karanta abincin dake qarqashin ranar,kanta ta jinjina saboda yau aikin nata kaman mai yawa ne,gashi a jiya bata samu ta duba me zata girka ba yau sakamakon bacci fa yayi nasarar saceta tana tsaka da karatun test da zasuyi a safiyar yau,cikin hanzari ta bude freezer ta fiddo dukkan abinda zata buqata,sannan ta wuce store dake cikin kitchen din ta fiddo kayan amfani,sannan ta soma aikinta cikin hanzari da qwarewa.
A qalla ta shafe kusan mintina talatin sannan ta jiyo motsi alamun ana niyyar shigowa kitchen din,fuskarta qunshe da murmushi wanda ya sanya dimple dinta dake dukka kumatunta lonawa,tunkan ta qaraso tasan wacece,ita kadai ke tashi ta kama mata aiki,ita daya ce matar da hakanan Allah ya hada jininsu take qaunarta,ita daya ce take ganin qauna daga idanunta,irin qaunar data rasa,irin qaunar da take buri da fata ta ganta daga wajen wadda tayi silar kawota duniya saidai har yau abu yaci tura,a wajenta ne kawai take ganin kulawa qauna da kuma sassauci.
Ita dince kuwa,daya daga cikin masu aikin gidan ce inna laraba,fuskarta fadade da fara'a tace
"Yanzu inna laraba yau dinma ba zaki kwanta ki huta ba?,ina cewa jiya da qyar kika samu ciwon qafar nan ya barki?" Itama fuskarta qunshe da fara'ar tace
"Banda abinki shatu ai kema kinsan ban saba da wannan baccin bayan sallar asubar ba,kuma na tabbatar kina nan ke daya kina fama da kacaniya" ta fada tana qarasowa kusa da ita,murmushi ta saki sannan cike da girmamawa ta gaida innar kaman yadda take kiranta tare da tambayarta ya qafar tata,amsa mata tayi itama cikin kulawa kafin ta matso da niyyar kama mata aikin,duk yadda taso hanata amma innan sam taqi,haka ta sakar mata suka ci gaba da aikin tare suna hira.
Bata ankara ba taga lokaci ya ja,har qarfe tara saura na safiya,idanu ta zaro don tun jiyan da daddare anty asma'u ta ja mata kunne cewar qarfe tara zata fita,kuma driver ba tsayawa jiranta zaiyi ba,ruwanta ta shirya da wuri ruwanta karta shirya ta samu mai ajjiyeta makaranta"hakan ya sanya ta tattare komai a gurguje ta soma shiryawa saman qawataccen teburin cin abincin dake sashe na musamman dake cikin falon.
Plates da spoons suka rage suta dauko ta dawo da niyyar ajewa daga nan ta shiga ciki ta shirya itama,duk da cewa ita sai goma zata fita,amma dole ta shirya tabi asma'un koda qarfe bakwai asma'un zata fita,tsaye ta tadda ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar material,ta zuba makeup sosai,hannunta maqale da 'yar madaidaiciyar hand bag mai azabar kyau,kafadarta rataye da mayafinta wanda wanda haka qa'idar saka mayafinta yake,qwayar idanunta saye da tafkeken sun glasses wanda ya kusan cinye rabin fuskarta,table din take qarewa kallo har sanda aysha ta qaraso wajen tana dora plates din saman teburin gami da gaida asma'un.
Bata damu da amsa gaisuwar da take mata ba saima tambayar data jefo mata
"Waima baki shirya ba?" Ta fada cikin bacin rai tana zare glass din fuskarta kasancewarta mace wadda qanqanin abu sai ya bata mata rai ko ya tunzurata
"Yanzun zan shirya in sha Allahu" ta fada a tausashe,cikin hasala asma'un tace
"Kada ma ki shirya wannan ya rage naki,ni dama na soma gajiya da tafiya dake gaskiya,ya kamata daddy ya barni haka nan ya raba mana tafiya tunda babu dole.....ina cewa tun jiya na sanarmiki lokacin da zan fita,amma saboda tsabar raini da salon ki jawa mutum fada baki tashi kin gama komai a kan lokaci ba"
"Kai...kai me yake faruwa haka da sassafen nan kuma lafiya?" Cikin bacin rai asma'u ta juya tana kallon mahaifiyarta dake saukowa daga stairs,shirye cikin tsadajjen lace na alfarma,hannayenta da wuyanya duka sanye da jewels da banguls masu tsada
"Mommy nida yarinyar nan ne mana,wai ki duba fa jiya gabanki na gaya mata when zan fita shine wai har yanzu bata shirya ba"
"Garin yaya ke ayshatu?...." Jin tambayar tayi banbarakwai,tunda dukkaninsu sunsan me ya tsaidata,hidimar abincin safen asma'un ne,wanda dukkansu sun kwana da sanin cewa don ta itama a soke abincin safe,totally ma ba damuwarta bane abinci
"Ya kuma kika tsaya,jeki ki shirya,idan kuma har ta gama baki fito ba sai ki samu napep ya kaiki" ta fada itama tana jan daya daga cikin kujerun dining din da alama karyawa zatayi akwai muhimmiyar fita kenan.
Juyawa tayi a hankali ta doshi corridor din da dakunansu suke,sam batayi mamaki ba tunda ba yau bane farau,hajiya sa'adatu irin matan nan ne da basu cika ganin aibu ko laifin dansu ba,bugu da qari tana da attitude na idont care kan lamuran da ba nata ba,tayi ma rawar gani yau data tanka,idan da taso Allah ya kyauta kawai zata ce tayi zamanta ta hau hidimar gabanta ya tasu koma ya zasu qarke ohon mata,indai hakan bazai shafi shalelen tata ba ko kuma ita bazai kawo mata wani cikas ba.
Duk da cewa a gurguje ta shirya amma hakan bai sata ta samu nasarar tadda asma'un ba,saima hajiya sa'adatu data samu tana yunqurin bude murfin mota zasu fita ita da drivanta,kallo daya tayi mata tace
"Gashi har asma'un ta wuce tun dazun,saidai ki qarasa titi kibi ta haya" ta qarashe maganar tana shigewa motar tare da yunqurin rufewa
"Ba komai zan qarasa din mommy,a dawo lafiya"
"Allah yasa" ta masa sanda drivern ya fara jan motar suna niyyar ficewa daga gidan ba tare data damu da yadda ayshan zata kai kanta makarantar ba.
Tana nan tsaye har motar mommy ta fice sa'annan ta soma takawa a hankali cike da nutsuwar data zama tambarinta tabi bayan qurar motar ta fice daga gidan ta 'yar qaramar qofar dake maqale jikin get din.
Duk da yake akwai 'yar tazara kadan tsakanin gidan nasu da bakin titi amma sam bata ji tafiyar ba,hakan ya faru ne sakamakon yadda qwaqwalwa da zuciyarta baki daya sukayi zurfin tare da nisan kiwo wajen tunani,tunani qwaya daya da ko yaushe bata gajiya da shi,hakanan batasan randa babin tarihin rayuwarta zai rufe ba,hakan batasan meye qarshen nasa ba,yaya qarshen nasa zai kasance?,wata iriyar cukurkudaddiyar rayuwa da tayi take kuma kanyi ita ke mata kai kawo cikin qwaqwalwarta.
Sam ta sha'afa sai data tsaida mai napep sukayi cinikin nawa zai kaita sannan ta laluba jakarta cikin fargabar ta fito da kudi?,Allah ya taimaketa jakar a ciki ta sanya kudaden da daddy ya bata sanda zaiyi tafiya,ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana hamdala cikin zuciyarta.
Kusan babu wanda ta tarar cikin ajin,sakamakon akwai tazarar awa guda daga lokacin da za'a shiga lacture din da sanda tazo,guri ta samu na musamman inda tafi sha'awar zama ta zauna,sa'an nan ta zaro handout dinta taci gaba da dubawa kafin lokacin da zasu zana test din ya cika.
*mrs muhammad ce*👑
🧣🧣 *DAURIN BOYE* 🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)✍
0⃣2⃣
Kusan rabi da rabi take karatun,fiye da rabin hankalinta ya ta'allaqa ne akan wayarta,wadda ba komai take kalla ba sai wasu numbers wanda ke rubuce da sunan MAMA NA,ta kallesu yafi sau shurin masaki,ta kwatanta kira fiye da irgen yatsun hannunta saidai ta kasa hakan,ba wani abu bane ya jawo haka ba illa tsoro da fargabar abinda kiran zai biyo baya,taji ance bata ji dadi ba,tana so ta kirata ta mata sannu da jiki,saidai bata da wannan damar,ba qaramin qunar baqin wake take ba duk sanda tayi jarumtar kiranta,wanda hakan daga qarshe baya haifar mata da d'a mai idanu.
"Qawata sarkin sammako" taji an ambata ta gefanta,wayar ta rufe ya dago kai fuskarta qunshe da murmushi tana duban Aliya dake sauke jakarta daga kafada kana ta yiwa kanta mazauni kusa da ayshan itama tana murmushi
"To ya za'ayi" ayshan ta maida mata amsa tana gyara zamanta
"Hala yauma uwar masu gidan zata fito da wuri ne kika kwaso qafa kika biyota?" A maimakon ta bata masa murmushi ayshan ta saki,tasan halin rigima sarai irin na Aliya.
'Yar tsama suke qwarai da asma'u,basa hada hanya da ita,saboda banbancin halaye qwarai dake tsakaninsu,bugu da qari tana jin haushin yadda take mu'amalantar ayshan wadda ta zame mata qawa kuma aminiya a dui fadin makarantar,sosai Aliya keson aysha sabo managartan halayenta,nutsuwa haquri gami da kunya,uwa uba ayshan na daya daga cikin daliban da sukayi fice a duk fadin department dinsu,kai bama iya tsangayar tasu kadai ba a duka makarantar ma.
Kai Aliya ta kada cikin takaici,saidai ayshan bata bata damar cewa komai ba ta tareta
"Kinso yau ki makara qawata,ya akai haka?"
"Hmmm,wlh yau mama ta tsaidani sai dana hadawa ya khalil breakfast,Allah ne ya soni na masa sharp sharp na fece,da Allah ne kadai ya san makarar da zanyi" duka tana zancan ne sanda take ciro handout dinta daga jaka,kafin su sake cewa komai lacturer din ya shigo ajin.
Qarfe uku na rana ta kammala duk abinda zatayi cikin makarantar,hakan ya sanya ta tattara komai nata ta fito don ta qarasa inda zata samu asma'u,saidai koda taje wayam taga wurin babu alamun motarta,hakan ke nuna bata cikin makarantar,bata wani damu ba ta soma takawa da qafa don zuwa bakin get din makarantar don ta sami abun hawa,don yau Aliya ta rigata tafiya gida,ita ta tsaya ta dudduba wasu karatuttuka.
Jin qarar mota a bayanta ya sanyata sake rabewa don bawa motar damar wucewa,a sannan idonsu ya hadu da drivern,asma'u ce,ita da wasu mutum biyu a motar,da alama qawayenta ne,dauke kai asma'un tayi tamkar bata ganta ba,sai tama qarawa motar wuta tayi hanzarin wuce ayshan,sam hakan bai dameta ba,saboda ba yau farau ba,babu abinda asma'un ta tsana nan gidan duniya irin alaqar da zata bayyanar da cewa ayshan jininta ce,gida daya suka fito ko suna da dangantaka,tunda ayshan ta fahimci hakan sai itama take baya baya da duk wata alaqa da zata hadata da asma'u cikin bainar jama'a.
Kai ta jinjina kawai taci gaba da takawa zuwa qofar makaranta,wannan abun na asma'u zata iya cewa bai bata ranta ko kadan,idan ma ya bata din bai wuce digo daya cikin dari ba,a yanzu qyamatar da take fuskanta take kuma bata mamaki ta shafe ko wacce iriyar qyama da qiyayya da dukkan wata halitta zata nuna mata a doron duniya,dukkan wata tsana saidai ta biyo bayan waccar,da wannan tunanin ta tsaida wani dan sahu dake niyyar gifatata ta masa kwatance inda zata ta fada ciki.
Kamar kullum yauma a qalla ya kusa shafe mintuna ashirin yana tsaye yana jiranta,har sai data kaishi ga qosawa ya haye saman babur din da yazo da shi ya zauna,saboda rashin sabo saura kadan babur din ya tuntsira da shi Allah ya taimaka cikin zafin nama yayo gaba ya dawo ya zauna dai dai,mahmoud dake zaune cikin motarsu dake fake a wani layi ya tuntsire da dariya harda duqawa,ba don ba dabanba da ya fito ya masa vedio ya ajjiye saboda tarihi,saidai yana tsoron tashin balli tilas ya zauna cikin motar kamar yadda yayi masa umarni.
Sake duba agogonsa yayi yana qissimawa ranshi mintinan da zai qara wanda matuqar bata fito ba zai qara gaba,a gajiye yake,daga airphort yake ko gida bai isa ba ya sauya kaya ya canza akalar tafiyar tasa zuwa gidansu,bayan ya yiwa daya daga cikin yaranshi waya ya kawo masa babur din,kwanaki goma ya kwashe a qasar da yaje,bai kuma samu damar kiranta ba tunda ya tafi saboda gudun tonuwar asiri,don kada ta tsammaci ya janye hakan ne ya sanyashi tahowa kai tsaye gidansu.
Kamar ko yaushe yauma haka fuskarta take,ta qaraso inda yake saidai a yau waya take amsawa,ganin ta iso gareshi yasa ta bada uzurin zata sake kira ta kashe wayar ta lanqwasheta a hannunta yauma tana sake qare masa kallo a kaikaice
"Allah ya baka kyau na nunawa sa'a,saidai hakan ba zaiyi tasiri a raina ba saboda kana da babban naqasu na rashin hatimin nasara" duka take wannan maganar a ranta,sama sama suka gaisa tamkar baqin juna,shi kansa yana jin wani irin cikin ranshi,duk yadda yaso kawo sabo da shaquwa tsakaninsu zulaihat taqi bashi dama.
Shiru ya ratsa tsakaninsu bayan ya gama iya maganganun da yaga sun kamata,saidai rashin samun gamsashshiyar amsa yasa maganganun nashi basuyu tsaho ba
"Ammm...dama akwai abinda nakeson gaya maka" ta fada tana gyara yafen mayafinta
"Uhmmm...babu damuwa,yi maganarki"
"Cewa nayi don Allah daga yau ina son ka janye daga zuwa wajena da kake....saboda ina da buqatar space"qaramin murmushi ne ya subucewa fuskarsa,abinda yake zato yau zai tabbata kenan
"Amma wani laifi na aikata ne haka" kai ta kada tana dan tabe baki
"Ko daya,kawai na gaji da alaqarmu ne haka.....har yau jiya iyau,kai ba qaruwa ake da kai ba" ta qarashe furucin qarshe can qasan maqoshinta,saidai abinda bata sani ba shine,yana daga cikin jinsin mutanen da Allah ya musu kaifin ji matuqa,murmushi ya kuma saki mai dan sauti,ga mamakinta taji yace
"Shikenan....in sha Allahu daga yau din zan janye....amma" ya fadi yana sanya hannunsa cikin aljihun trouser dinsa,american dollers ya ciro daga aljihun nasa wanda baisan ko na nawa bane,takawa yayi a hankali har ya isa inda take jingune rungume da hannayenta ya soka mata su tsakanin hannayenta yana ci gaba da jifanta da murmushi
"Na gode da lokutanki na baya da kika aramin.....sai wara rana" ya fadi yana juyawa,binsa tayi da kallo galala,duk wata tasha ta tunaninta ta dauke tsaf,har ya isa bakin wata baqar mota wadda bataji sanda ta iso inda suke ba,gidan baya ya bude ya shige kana ya rufe,sai data ga motar ta bar layin nasu sannan hankalinta ya dawo jikinta,tabi dollers din dake liqe a jikinta da kallo,sabbi kar suna fidda wani irin qamshi dake cakude da sassanyan qamshin turarensa da har rana irin ta yau ta rasa gane wanne irin turare yake amfani da shi,cikin sauri kaman wadda aka yiwa allura ta juya cikin hanzarinta shige gidan su,bata tsaya ko ina ba sai parlourn gidansu,inda tabar qawarta barratu na jiranta
"Ya akayi,kin sallami dan anacen naki" maimakon ta amsa mata saita miqa mata dalolin dake hannunta
"Wadannan fa daga ina?" Barratu ta fada tana zakudawa gami da gyara zamanta tare da tattara dukkan hankalinta kan zulaiha,mayafinta ta yage sannan ta zauna hannun kujera tana baiwa barratu labarin abinda ya faru,ta rufe da cewa
"Tsoro na daya barratu,kada ya kasance irin mijin da nake muradi ne na koreshi da kaina,kinga irin motar daya shiga kuwa" ta fada fargabarta na fitowa fili qarara,murmushi barratu ta saki tana karkada kudaden
"Kinga malama....kwantar da hankalinki....tundan yau kin gano haka ai baki makara ba,waskewa zakiyi,ai kiransa zakiyi kawai ki nuna ke bakison kudinsa yazo ya amshi abinsa,ke gwadashi dama kike yi" bata tsaya ta gama jinma qarshen zancan ba ta zaro wayarta cikin hanzari ta soma laluba inda ta jefa lambar tasa,can cikin black list ta ganota,cikin hanzari ta cireta daga black list din sannan ta soma kiransa.
Dai dai lokacin yana lafe a bayan motar suna tafe, mahmoud nata tambayar sa ya akayi a gefe guda kuma yana sheqa masa dariya,qarar wayar ita ta sanyashi bude manyan idanunshi da suke a rufe,waya ce da ita daya keda number,wadda dama dominta ya siya wayar da layin,hannunshi ya kai ya daga wayar ya kara a kunnensa ba tare da yace komai ba
"Ka dawo ka amshi kudinka,ni basu nake so ba,gwadaka dama nake,kuma alamu sun nuna kaci wannan jarrabawar" irin maganganun data ringa jerowa kenan duk a niyyarta nason amintar da shi da gamsar da shi,murmushi kawai ya sake mata wanda ya ratsa kunne da qwaqwalwarta
"Am sorry to say,ida na wuce aji bana maimaita shi.....sai wata rana" ya qarashe fada yana cire wayar daga kunneshi,bai tsaya a nan ba sai daya cire layin ya karyashi gida biyu,ya sauke glass din motar qasa kadan ya watsar ta window sannan ya maidashi yadda yake ya koma jikin kujerar motar ya sake lafewa ba tare daya bi ta kan dariyar mahmoud ba,hannayensa ya saka ya rufe kunnuwansa saboda yadda mahmoud din ya hanashi sakat,daga bisani da yaga baida niyyar barinshi ya huta ya shammaceshi ya kai masa naushi,Allah ya taimakeshi ya kauce yana cewa
"A'ah,karka lahantani,haka kawai bani na kar zomon ba ai,danma ka samu wai ina rakoka,tunda an kasaka ba shikenan ba sai ka sake sabon lale....amma fa ka riqr a ranka,'yammatan zamani indai zaka ci gaba da zuwa musu a haka za'a dade ana kasaka" dariya ce ta subucewa khalipha ba tare saya shirya ba,suka dan dara tare da mahmoud din,shi kansa lamarin na bashi mamaki gamibda daure masa kai,karo na uku?,karo na uku duk tafiyar ta kasance iri guda?,sai yaushe?,sai yaushe zaiga sauyi,zaya so yaga wannan rana qwarai.
*mrs muhammad ce*👑
*_HUGUMA_*
0⃣3⃣
Tsaye yake cikin tafkekan dakin taron a gaban wani hamshaqin teburi wanda yake dauke da aqalla ma'aikata kimanin mutuk arba'in,hannunsa guda dafe yake da gaban teburin yayin da daya hannun yaketa wulwulgashi cike da gwanancewa duk da baisan yana yi ba,da alama bayanin da yakewa ma'aikatan da suka bashi dukkan nutsuwarsu ya dauki zafi,lokaci lokaci yana daga daya hannun nasa dake dafe da teburin yana duba agogon hannunsa,wannan kadai ya isa ya nuna maka mutum ne mai kiyaye lokaci da kuma alfanunsa.
"Is there any problem?...." Ya qarashe jimlar tasa ta qarshe yana duban fuskokin ma'aikatan,saidai kowanne ya gamsu girgiza kai suka dinga yi daya bayan daya,ganin haka ya sanya shi ya soma tattare kayanshi dake saman teburin tare da bada umarnin a rufe taron da addu'a kaman yadda yake a qa'idarsa.
Shine mutum na farko da ya soma fita,shahid ya rufa masa baya suna magana qasa qasa,a bakin hall din daya daga cikin mutanen dake tsaye a wajen ya karbi kayan hannunsa sannan yabi bayansa har cikin elevetor wadda bata saukesu ko ina ba sai hawan qarshe na kamfanin inda office dinsa yake.
Mahmoud ne kawai zaune cikin office din ya tasa computer a gaba da alamu wani aiki yake ragewa mai muhimmanci Hannu mahmoud ya baiwa shahid suka gaisa cike da alamun cikakkiyar sanayya a tsakaninsu bayan security din dake riqe da kayan khaliphan ya aje ya fice,yayin da khalipha ya wuce kai tsaye bakin freezer ya dauki ruwa ya sha bayan ya rage suit din jikinsa kana ya shige toilet,alwala ya daura sannan ya dawo cikin office din ya tadda shahid da mahmoud suna hira,wadda fiye da rabinta abinda ya shafi kasuwancinsu ne,daya daga cikin wayayoyinshi wadda ke dauke da lambobin dukkan mutanen daya baiwa muhimmanci a rayuwarsa lambarsu ke ciki,kai tsaye ya nufi bakin daya daga cikin windows din dake cikin dakin office din wanda kai tsaye zaka iya kiransu da qofa saboda kadan ne ya rage basu kai girman qofar ba,saidai glass ne zalla a jiki wanda hakan zai baka damar gano ainihin farfajiyar companyn daga sama har qasa.
Bugu biyu aka daga wayar,ya sauke ajiyar zuciya sallamar matar na ratsa kunnensa,cikin sanyin murya kaman yadda halittar muryarshi take ya amsa sallamar sannan yace"Anni...barka da warhaka"
"Barka kadai khalipha,kun fito daga taron ne?"
"Mun fito ammi,saidai aci gaba da yi mana addu'a Allah yasa mu dace"
"Ubangiji ya dafa,ya shiga lamarinku,ya zama jagora a gareku,ya albarkaci rayuwarku". Cike da jin dadi yaketa amsawa da ameen,idanunsa lumshe yana shafa qirjinsa yana jin zuciyaraa wasai
"Ya jikin anni?,kinsha maganinki na rana,naga lokaci yayi"murmushi ta saki cike da qaunar yaron nata
"Khalipha kenan baka gajiya?,kaman ba awannin da suka shude muka gama waya da kai ba,jiki alhamdulillah,magani kuma ina gama sha kiranka ya shigo"cikin murmushi ya amsa
"Ya za'ayi na gaji da jinki anni....Allah ya qara miki lafiya mai dorewa"
"Allahumma amin khalipha,Allah yayi albarka"
"Ameen anni...sai na dawo"
"Allah ya tsare" ta sake ambata cikin nuna kulawa da qauna,ya amsa sannan ya kashe wayar yana murmushi,abubuwa da yawa na dawowa cikin kwanyarsa game da annin tasa,zai iya cewa baiga uwa irin tashi ba,kuma baya zaton za'a samu,anninsa da taban ce ko cikin halittun ubangiji,da wannan zancan zucin ya qaraso inda su mahmoud suke.
🧶🧶🧶
Zaune yake gaban annin tashi cikin shigar qananun kaya na t shirt da trouser,qafafunshi tanqwashe gabanshi kuma plate ne wanda ke dauke da tuwon shinkafa miyar water leaf da ogu wadda ta wadata da ganda busashshen kifi da kuma tsokar nama,a nutse yake cin abinci gefe guda suna hira da anni,hirar dake nuna tsantsar shaquwa dake tsakaninsu,kallo daya zaka yi musu ka tabbatarwa kanka lallai akwai saboda da shaquwa mai qafi tsakaninsu
"Khalipha..." Ta ambata a hankali wanda hakan yasa ya dago kanshi yana dubanta sannan ya amsa
"Wai sau yaushe zan daina jiran ganin zuwam surukata?" Murmushi ne ya subuce masa,sai ya aje cokalin hannunsa ya fasa kai lomar da yayi niya,cikin kulawa da qauna yake dubanta sannan yace
"Kwanan nan anni,karki damu....addu'arki nake buqata kawai...ina son na kawo miki surukar da zata kulamin dake,surukar da zata daukeki a matsayin uwa....surukar da zakiji dadin zama da ita fiye dani yadda zanji" murmushi ya subuce mata,sai ta kada kai tana dubanshi
"Allah ya baka mace ya gari wadda zata zame maka majingina.....amma banda abin khalipha kana tunanin akwai irin wannan surukan yanzu?" Ta qarashe managanar tana dariya qasa qasa,don har ga Allah bata dauki burinta ta cillashi har haka ba,kullum dai addu'arta Allah ya bashi wadda zata soshi tsakani da Allah,nagartacciyar matar aure,dan marairaicewa yayi kadan sannan yace
"Anni,kin sha gayamin ba'a fidda rai da rahamar Allah"
Kai ta jinjina cike da gamsuwa tace"wannan haka yake,ubangiji ya maka zabi ja gari"
"Ameen" ya amsa yana daukar cokalinsa dinci gaba da cin abincinsa sannan yace
"Cikin sati na gaba haidar zai dawo gida hutu" murmushi tayi kaman ko yaushe
"Sun kammala jarabawar kenan"
"Eh sun samu hutu na wata biyu"
"Allah ya kai mana rai"
"Ameen" ya amsa yana daukar cup din daya cika da ruwa ya soma sha.
🧶🧶🧶
Da sauri sauri take tafiya hadi da duba agogon hannunta,qarfe tara da rabi na safe dai dai,mintuna talatin zata qara ta makara wanda hakan dai dai yake da rasa lacture dinta har na tsahon awa biyu.
Turus tayi gabanta na dan dokawa ganin asma'u zaune dafa'an cikin falon sanye da kayan barci wanda hakan ke nuna ko wanka bata yi ba bare a kai ga shirin fita,hannunta daya riqe da cup na tea tana kurba a hankali,daya hannun kuma wayarta ce samfurin iphone 8 take latsawa,jikinta sanyaye ta qaraso gefanta ta tsaya
"Ashe baki shirya ba anty asma'u?" Sai data shaqi iska kafin ta amsa
"Eh....sai eleven"
"Gashi goma lacturer din yake shiga..." Ta fada adamuwance,saboda daddy yana gidan,kusan yasan lokutan fita lactures dinsu daya ne,tare suke fita su kuma dawo tare a iya saninsa kenan,idanu ta daga ta kalleta ta watsa mata wani kallo
"Naga alamun raini na son soma shiga tsakaninmu aysha duk don saboda sharing abun hawa da muke ko...to ki shiga taitayinki,ke kanki kinsan wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,banda game game irin ja daddy da sunan zumunci saidai ki dinga hangoni ta cikin glass,to banson zura kai in zaki wuce kije ki hau abun hawa na haya ki wuce,dama dashi kika fi dacewa kuma dashi kika saba" tana kaiwa nan ta maqala earpiece a kunnenta da alama kira ne ya shigo mata zata amsa.
A kasalance take takawa a harabar gidan,zuciyarta cike fal da tunani,tana tsammanin kyautatawa na sanyawa kaso mutum koda baka sonshi,saidai ta gefan asma'u sam ba haka bane,mommy kuwa har yau ta kasa fahimtar a wanne aji take?,banbancin rayuwar data baro da wannan baya wuce sauyin muhalli,sutura da ilimi data samu ba,amma baya ga haka zata iya kiran yanayin da SAMMAKAL a wajenta
"A'ah,ina zaki a qafa aishatu?" Ta tsinkayi muryar daddy dake fitowa daga babban falonshi da yake ganawa da baqinsa,wanda sam bata lura da shi ba saboda zurfin tunanin da tayi,cikin hikima tayi qoqarin saisaita yanayinta,ta qaraso cike da girmamawa
"Ina kwana daddy..." Ta soma da gaisheshi,don yau duka basu samu damar haduwa ba,kasancewar jiya wajen goma na dare ya dawo qasar,ya kuma buqaci mommy ta tasota saidai tanajin sa'adda da tace masa ai ayshan tayi bacci,bayan idanunta biyu a sannan litattafanta ne a gabanta take dubawa,har lokacin data shiga dakin asma'u ta tadata kan ta fito daddynsu ya dawo amma asma'un tayi qememe tace ta gaji sa gaisa gobe,haka mommyn ta fito tace masa itama din tayi bacci
"Ina zaki aysha?" Ya sake jeho mata tambayar bayan sun gama gaisawa,bata da wata qarya da zata masa don kare asma'un wannan karon,saboda haka kai tsaye tace
"Makaranta" agogon wayarsa ya duba sannan yace
"Ina asma'un.....ina kuma drivern naku?"kanta ta duqar qasa sannan tace
" yau akwai banbancin lokacin fitar namu ne"
Kai ya jinjina,tun da can shi ba mutum bane mai yawan sanya ido da takura ba,hakan ya sanya abubuwa da dama kan gudana cikin gidan ayi musu kwaskwarima a sauya musu salo a bashi a haka ya karba ba tare da ya sani ba.
Dai dai sannan usama drivansa ya turo get din gidan ya shigo,saboda ga tsammaninsa a sannan zasu tafin,hakan ya sanya daddyn ya sallameta bayan ya miqa mata sabbin 'yan dubu dubu guda biyar da sukayi saura a hannunsa wanda da alama ya gama sallamar masu neman taimako ne wadan nan suka rage,tasan baya kyauta a dawo masa da ita hakan ya sanya tasa hannu biyu ta amsa tana jero masa godiya.
Ko cikin motar tunanin karamci irin na daddyn take,har abada kuma har ta mutu ba zata taba manta alkhairinsa da karamcinsa gareta ba,qarar wayar usama ta dawo da ita hayyacinta,daga jin yadda yake amsa wayar cikin daburcewa tasan akwai magana
"Kiyi haquri ranki ya dade,yanzu zan ajeta na dawo,na dauka yau bazaki fita bane...kiyi haquri" kalmar yayita maimaitawa,saidai hakan bai hana asma'u yi masa tas ba harda alakoron zagi ta kuma katse wayar
"Kaga....ajjiyeni usama kaje ka daukota saina qarasa wani abun hawan" yana bala'in ganin qimar ayshan saboda yadda take girmamashi tamkar yayanta,hakan ya sanya yace
"Barshi kawai na qarasa dake aishatu,koda na ajekin ma na koma daukota ba tsira zanyi ba" kai ta kada
"Ka ajenin babu komai...laifin ai zai ragu idan kace mata ajjiyeni kayi ba kamar ka kaini ka dawo ba" haka ya gangara gefan titi bada son ransa ba ya ajeta ya juya ya koma,ta tsaida adaidaita sahu ya qarasa da ita,idan da sabo ta jima da sabawa da halayen asma'u,ta haddacesu tsaf,shi yasa ba komai ke bata ranta ba.
*mrs muhammad ce*👑
🧣🧣 *DAURIN BOYE* 🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)✍
0⃣4⃣
Qarfe daya ta fito daga library dake cikin makarantar don ta qarasa masallaci tayi sallah,tattaunawa suka sakeyi da sauran dalibai 'yan uwanta kan lacuture din da suka gama yi,qoqarinta da yadda kanta keja yasa yawa yawan dalibai ke maqale mata saboda ta sake ganar da su abinda basu fahimta ba,ta kammala alwalar tana gab da shiga masallacin wayarta tayi tsuwwa,dakatawa tayi ta ciro tana duba mai kiran,gwaggwo asabe ce take kiranta qanwa ga mahaifiyarta,mace daya tak da ko a baya tayi qoqari wajen ganin ta taimaki rayuwarta,tana daya daga cikin jerin jama'ar da bazata mance da su ba cikin rayuwarta,gefe ta samu ta jingina da wata bishiya dake wajen bayan ta katse kiran ta kirata da kanta don kada ta cinye mata kudi,gaisawa sukayi bayan 'yan tambaye tambayen lafiyar juna da suka biyo baya tace da ita
"Indo hala bakisan malam baida lafiya ba ko?"
"Kai haba?,tun yaushe gwaggwo?"
"Sati kusan biyu kenan,har a asibitin cikin gari ya kwanta,amma alhamdulillahi yanzu jikin nasa da sauqi an sallamoshi yau kwana uku yana gida ma"
"Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bashi lafiya,in sha Allah zan shigo garim cikin qarshen satin nan,kiyi masa sannu kafin na iso"
"Zaiji,saikinzo Allah ya kawoki lafiya"
"Ameen gwaggo na gode,ki gaishemin da su lami"
"Zasuji" daga haka ta kashe wayar ta maidata cikin jakarta tana sauke ajiyar zuciya,ta tabbata ba don gwaggwo asaben ba babu lallai tasan da rashin lafiyar malam din,ta rasa wanne irin baqin abu ta aika har baqin jini yake bibiyarta wajen danginta na uwa da uba?,me tayi musu haka da kowa ma bai damu da rayuwarta ba?,a hakan ma takan iya cewa alhamdulillah da yadda ta tsinci kanta a yanzu akan shekaru kusan bakwai zuwa goma baya da suka shude,wanda abun yayi tsananin da har bata marmarin tunawa?,saidai har yau akwai wawakeken tabo da gibi cikin rayuwarta wanda batasan ranar da wannan gibin zai cike ba,batasan randa wannan babban jigon zai rabeta ba,batasan yaushe zai waiwayo ya dubi rayuwarta duba irin na idon rahama ba kaman yadda sauran 'ya'ya ke samu daga wajen uwayensu,da wannan tunanin ta qarasa cikin masallacin ta tada sallarta.
🧶🧶🧶🧶
Cikin nutsuwa ya kammala sanya maballan t.shirt dinsa wadda kudinta ya kama naira dubu biyu ita da wandon jeans dake jikinsa,har ya dauki turarensa zai fesa sai ya tuna,maidashi yayi wajensa,ya sake miqa hannu ya dauko wani daban wanda kallo daya zaka masa ka qiyasta kudinsa bazai wuce naira dubu guda ba idan yayi wuta ya fesa a jikinsa,duk da qarancin kudin turaren kuma bai cikin jinsin irin turarukan da yake mu'amala da su amma hakan bai hanashi jin dadin qamshinsa ba,saboda turare ne sanyi dake fita a hankali ba tare da ya daga hankalin wanda yake shaqa ba.
Gaban mudubi ya qarasa yana duban kansa,sai murmushi ya subucewa fuskaraa,duk da arhar kayan amma sun masa kyau
"Gwanjo" ya fada yana shafa gaban rigar dake jikin nasa zuwa saman cikinsa,yana tuna can wani lokaci baya daya shude,wani zamani da yayi tafiyar ruwa da dukkan farincikin rayuwarsu,wani qarni wanda basu taba tsammanin zaya wuce babinsa ya shafe kaman bai taba wanzuwa ba cikin littafin qaddararsu ba,tunanin ya saka ya zarce da sake gyara sumarshi da tayi matuqar yi masa kyau.
Kafin ya kai ga aje comb din hannunsa aka turo qofar dakin hade da sallama,mahmoud ne ya shigo idanunsa na kan khalipha,daga gani tambayoyi ne fal cikin qwaqwalwarsa wanda tun kafin ya zauna ya jefo masa daya
"Me haka ne malam?,ban fahimceka ba" juyawa yayi yana ci gaba da gyara kansa kafin ya bashi amsa
"Na zaci shigata kawai ta isa ta baka amsar abinda yake faruwa ko?"
"Wai har yau baka haqura ba?,baka kuma daina ba?" Ajjiye comb din yayi ta tako kusa da mahmoud din ya dauki qaramar vivo din dake aje kusa da shi ya bude bayanta ya soma qoqarin sanya mata layi
"Na sake haduwa da wata,kuma na fuskanci kaman wannan karon ina tare da nasara" dariya sosai mahmoud din ya bushe da ita harda kwantar da gadon bayansa saman gadon khaliphan,san dariyar mahmoud din bata dameshi ba saima yunqurin kunna wayar da yake bayan ya kashe nashi tsadaddun guda uku ya jefa cikin wata 'yar kyakkyawar briefcase dake nuna alamun da ita zai fita
"Me yasa kake wahalar da kanka ne babu gaira babu dalili my man.....ka saki kudi kawai ka auri duk kalar macen da kakeso kada ba jinsinka bace ba 'yar qasarka ba,kowa ya sani cewa mata yanzu kudi kawai suke so,mai kudi suke nema koda baida hali koda bai cancanta,koda ba saurayi bane koda ba kyakkyawa bane,koda jahili ne,to bare kai da babu abinda Allah bai baka ba,c'mon muhammad khalipha ka aje wannan game din a gefe ka fuskanci reality,ba irin matan da kaketa serching a yanzu,baka gani duk inda ka soma farauta daga qarshe sai kaga no signal?".
Hannu yasa ya dauki briefcase dinsa tamkar bada shi mahmoud ke magaba ba ya doshi qofar fita ba tare da yace masa ci kanka ba,hakan ya sanya shi miqewa da dan tsallensa ya biyo bayansa,saidai bai sake biyo ta kan wancan maganar ba ya sauya topic,yasan ko yaci gaba ma ba amsa zai samu daga gun khaliphan ba
"ka rakani mu shiga na gida anni"
"Daga nan ni sai inda na nufa,idan ka fito daga wajenta ka kwashe su jibril duka ku wuce kamfani na tadda ku a can,ni da mota daya zan fita,bana buqatar gayya" ya fada yana gaba yana ci gaba da dubo lambar sabuwar budurwar tashi don ya sanar mata da tahowarshi.
Yana fita duka suka taso inda yake,da hannu ya tsaidasu kafin ya daga kai ya dubesu
"Mota daya ta isheni da driver,zaku jira mahmoud tare zaku tafi,zan taho daga baya" kai auka jinjina suna janyewa,yayin daya bude motar da kanshi ya shige gidan baya,drivan motar ya shiga ya tasheta suka bar harabar makeken gidan.
Layuka biyu suka rage kafin ya qarasa layin gidan nasu ya bashi umarnin ya saukeshi ya kuma jirashi a nan,ba musu ya tsaya kaman yadda ya umarceshi,ya bude ya fice.
Sannu a hankali yake takawa,shi kansa yana jin dadin takawar da yake,saboda ko banza ya motsa gabbansa,ba kamar baya ba da motar ita ta zame masa qafafunsa,sauqin abun daya bai da lalaci,duk safiyar duniya sai ya shiga dakin dake bangarensa,wanda ke cike sa nau'in qarafuna da na'urori na motsa jiki da qara lafiya.
Plashing yayi bugu biyu ya katse,shi kansa sai da dariya ta subuce masa
"Shame on you khalipha,wai yau kaine da yin plashing,Allahu yahdik" ya furta a zuciyarsa yana sakin murmushi gami da ranqwashin tsakiyar kansa,fitowarta ita yasa ya maida hankalinsa ga qofar gidan,tayi kwalliya sosai cikin atamfarta
"Sannu da zuwa" ta furta tana wuwwulga ido kaman mai neman wani abu,amma sai ta basar saboda jin kanta da take a mace mai aji
"Yauwa barka da fitowa"
"Ina kuma abun hawan yau?" Ta tambaya kai tsaye tana dubanshi,wani abu mai kama da mamaki yaso mamayarsa amma sai yayi hanzari kau da shi yace
"Kinsan qarfen nasara bashi da tabbas,yau yaqi tashi kawai sai na yanke na taho a na haya"
"Kan bala'i,ana wata ga wata" ta furta qasa qasa,sarai ya jita amma sai yace
"Na'am,me kika ce?"
"Babu komai,shigo daga ciki" ta fada ranta a alamun bace,bai musa ba yabi bayanta har setting room din gidan,duk da cewa ba baqonsa bane gidan da zuwanshi kusan na uku kenan,kallon farko zuwa na biyu zaka yankewa maxauna gidan ajin rayuwar da suke ciki,ba alamun suna cikin talauci,dukkan wata alama ta rufin asiri akwaita a gidan,kaman yadda ya tsammaci akwai tarbiyya gwargwado gidansu khadijan.
Nan ta masa sauki ta gabatar masa da abun motsa baki kamar kullum,saidai abinda ya fuskanta abinda aka kawo masa jiya idan ya sake zuwa yawansu da tsadarsu kan ragu,idan cake da doghnout da lemo yaci to zuwa na gaba doughnout da lemo kawai zai samu,yasan bai taba baiwa khadijan komai ba,haka itama bata taba roqarsa ba,saidai amma ya lura duk sanda sukayi sallama zai tafi ba tare da ya miqo komai ba yakanga bacin rai qarara a fuskarta,har idan ya koma gida ya kirata da zummar gaya mata ya iso bata dagawa,saidai duk ya share wannan bai sanyashi a babin komai ba.
Tun kafin aci talata da laraba a hirar tasu ta gyara zamanta tare da sake lanqwashe murya
"Ammm....dama muhammad akwai maganar da nakeso muyi"
"Ina saurarenki" ya fada yana harde qafafunshi waje guda tare da zuba mata idanunsa,haka nan taji ya mata kwarjini,abinda take yawan tunani kenan,me yasa yake yawan cika mata ido,wanda wannan dalilin yasa tun zuwansa na farko dana biyu data fuskanci ba kalar wanda take lalube bane ta kasa masa bayani,janye qwayar idanunta tayi cikin dakiya tace
"Dama.....biki zamuyi na wata qawata,so an fidda anko nakeso ka yimin" janye yatsansa dake saman lebansa yayi ya dan motsa jikinsa kadan sannan yace
"Kaman nawa ne kudin how much?" Sai da tayi rolling qwayar idanunta sannan tace
"Dubu talatinma is enought,idan son samu ne kuma 40k" murmushi ya qwace masa saidai iya shi da zuciyarsa,ba kudin data tambaya bane suka bashi mamaki don ba matsalarsa bane,don a yanzun haka akwai ninkinsu a wajensa,wanda ya fito da su ne yau dan ya mata kyauta matuqar ta sake tsallake yau din bata nemi komai daga wajensa ba,mamakinsa shine yadda yarinya budurwa da bata rasa ci sha da sutura daga gidansu ba take iya duban qwayar idon namiji ajnabinta ta roqeshi kudin da zata dinka suturawa jikinta haka kanta tsaye ba kunya,tamkar ta bashi ajiya ne,kai yake kadawa a hankai zuciyarsa na gaya masa bata gama cin jarabawa ba ba shakka
"Ya naji kayi shiru ne?" Ta tambayeshi tana dan bata rai gami da fiddo ido waje
"A'ah babu komai,kawai....gani nayi kudin basuyi yawa ba?" Tsaf ta dinke girar sama da qasa
"Just 30 to 40k dinne sukai yawa?,ko iyawa ne ba zaka yi ba?,thank god da ba'a gaban qawayena bane da nake cika musu kanka da naji kunya" murmushi ya saki yana miqewa tsaye
"Ba zakiji kunya ba in sha Allahu zan shiga na fita,amma sai kin danmin haquri kadan kinsam abinka da almajiri mai nema"
"Ba damuwa indai zasu samun,amma kar su wuce nan da one week don Allah" ta qarashe maganar a shagwabe,kai kawai ya iya jinjinawa mamaki na kasheshi,haka tayi masa rakiya har qofar gida yau cike da kulawa sannan ta juya ta koma,shi kuma yaci gaba takawa yana juya abinda ya faru tsakaninsa da khadijan har ya isa bakin motar,wanda tuni driver ya bude masa ya shige shi kuma ya maidata ya rufe sannan ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar unguwar.
"Ashe duk kanwar jaa ce?" Ya fada qasa qasa cikin sigar tambayar kansa da kansa bayan ya ciro sabbin kudaden dake aljihunsa ya qare musu kallo ya watsasu cikin wata ma'ajiyar dake motar ya maidata ya kulle yana sauke ajiyar zuciya,kansa ya shafa sau biyu yana kiran sunan Allah sannan ya maida idanunsa ya lumshe yana aje numfashi
*mrs muhammad ce*👑
*DAURIN BOYE*
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)
0⃣5⃣
A hankali take takowa bayan fitowarta daga kitchen dauke da babban tray data shiryo abincin daddy a kai zuwa inda yake zaune yana faman rubuce rubuce cikin wasu takardu,yayin da gimbiyar tasa hajiya sa'adatu mommy ke zaune gefanshi cikin kwalliya tana aikin duba tashar da zata dace da kallonta.
Duk da yawan ma'aikatan dake gidan hakan sam bai damu ayshatu ba ko ya tsone mata idanu,takan bata lokaci aduk sadda take da dama tayi girkin da zata ciyar da mutanen gidan,musamman daddy mutumin dake da qima a idanunta,mutumin da take masa kallon mahaifi,kai tana iya cewa abinda yayi mata ko mahaifin da yayi silar kawota duniya baiyi mata shi ba,don ba zata iya cewa yau ga dadin da mahaifi yake da shi ba.
Gabansa ta aje tray din cikin nutsuwa a ladabce,ya dan daga kansa ya dubeta fuskarshi washe da fara'a
"Sannu indon baffale" murmushi ta saki saboda kiranta da wani suna daya shude can baya cikin tarihin rayuwarta,sai ta duqad da kanta ta koma can baya ta rabe daura da momy,tana jira ya bata dama ta sanar masa tafiyarta qauye da takeso tayi gobe asabar ta dawo litinin tunda bata da makaranta ranar litinin din.
Asma'u ce ta fito daga dakinta sanye da dogon wando da riga 'yar qarama mai gajeran hannu,sai ta dora top wadda takai har saman gwiwarta,kunnenta sanye da earpiece kaman yadda yake kusan al'adarta kenan ko da yaushe,kanta babu dankwali sai yalwataccen gashinta mai tsaho dake fake cikin ribbom,a shagwabe ta qaraso gaban iyayen nata ta zube a gaban daddyn
"Daddy....tun shekaran jiya ka dawo har yau zuwa fa banga alqawari na ba"
"Hmmm,bake kadai ba,nima shiru nake ji har yau ba'a cemin komai ba,safina ma tayo waya tana jira amma duk daddy ka mana shiru"inji mummy sa'adatu ta fada tana ci gaba da sauya tasha,takaddun ya tattara gefe daya kana daga bisani ya cire gilashin idanunsa yana murmushi
" kowa sai daya min qorafin saqonsa shiru,ayshatu ce har yau banji ta fadi komai ba"murmushi aysha tayi tana sadda kanta qasa,ita awa?,wanne saqo ma ta baiwa daddyn?,iya alfarmar da ya yiwa rayuwarta kadai ta isheta har abada,ta gefan asma'u kuwa fuska ta kwabe tana dan bata rai,ta tsani daddy ya dinga hada yarinyar da su sam,tana ganin bata cancanci jerawa da su ba,yayin da hajiya sa'adatu ta dan tabe baki gami da dauke kai a fakaice,wanda ba kowa bane zai kula da hakan,bai sake cewa komai ba ya kira waya ya bayar da umarni,cikin mintina biyu daya daga cikin amintattun yaran gidan ya shigo jaye da akwati da kuma wata babbar jaka ya dire a falon ya juya ya fice.
Saukowa yayi qasa carfet din ya janyo jakar ya soma kici kicin zugeta hadi da fadin
"Ai gwara na sallameku na huta kada ku cinyeni danye" dukkansu sai da sukayi dariya,kasancewarsa mutum mai barkwanci a wasu lokutan,amma fa idan ya murde sam bashi da dadin sha'ani.
Wayoyi ya fito da su guda biyu irin wanda asma'un ta zaba tace tana so iri daya sak komai da komai,wayace sabuwar shigowa mai dan karen tsada da kyau ya miqawa asma'un,cike da murna da zumudi ta amsa tana jujjuyata ranta fari qal,saidai tuni murnarta ta koma ciki sanda taga ya miqawa aysha irin tata wayar sak,farincikin dake kan fuskarta ya koma bacin rai,ya sake fito da wasu dogayen riguna masu azabar kyau guda shida ya raba musu uku uku,cikin sanyin jiki da fargaba aysha ta miqa hannu zata amsa,yayin da idanunta ya sauka kan mommy da asma'u,mommyn dai ta share kaman bata gani ba,yayin da asma'u idanunta ke kan ayshan,haka ta amsa cikin sanyin jiki tana jerama daddyn godiya da addu'ar Allah ya qaro budi,wasu kayan ya sake fitarwa ya turawa mommyn yana cewa
"Ga kayan su safina nan,saiki san yadda zaki gobe ki aika musu da saqonsu nima na huta"
"Tohm" ta amsa wanda ga duk wanda yai tsai da hankalinsa zai fuskanci ranta a bace yake,muqullin mota sabuwa dal ya ciro ya miqa mata yana fadin
"Ga taki tsarabar saiki barni na sarara" sai a sannan fuskarta ta washe ta koma kaman da,cike da murna tasa hannu biyu ta karba tana masa godiya
"Ta wajenki saiki barwa su asma'u da aysha su ajje tasun ko?"
"Kan uba" kalmar data subuce daga bakin asma'u,motar data jima da ciwa burin daddyn nata yasa mommy ta bar mata shine yanzun zaice wani wai ita da aysha?,wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata yi sharing motar nan da ita ba
"Me kike fada asma'u?" Daddyn ya tambayeta yana mai zuba mata ido don yaso yaji kalmarta ta farko
"A'ah mamaki nake daddy,mun gode Allah ya qara budi"
"Ameen" ya fada yana rufe jakarsa,aysha na gefe baki daya a takure
"Alla ya qaro arziqi daddy mun gode,Allah ya saka da alkhairinsa" ta furta a sanyaye
"Amin aisha....amin" ya fada cikin jin dadi,a tajure take,saboda ji take kaman idanun mommy da asma'u na kanta har yanzu,hakan ya sanya ta miqe tare da fakewa da cewa zata duba farfesun naman kan ragon da takewa mommy a kitchen tayi shigewarta kitchen din,zamanta tayi a can tana duba farfesun tare da sake gyara freezer din da suke zuzzuba kayan girke girke da suke da saurin lalacewa har naman ya nuna,zuwa sannan bata jiyo muryar kowa a falon,hakan ya tabbatar mata sun bar gurin kenan,don haka ta juye naman a warmer ta gyara wajen ta baro kitchen din.
Asma'u kadai ta taras ta nutse cikin kujera,idanunta saman t.v saidai ba ita take kallo ba,ta cika tayi fam,ta soma gajiya da yadda daddyn ke dai daita da 'yar qauyen yarinyar a komai nata,da kafin zuwanta duka batasan irin wannan ba,ita kadai ta rage a gabansu sai abinda ta zaba ake mata,komai nata daban yake ba tare da an hadata da kowa ba,kallon baqin ciki tabi aysha da shi wadda ta giftata ta nufi dining ta dora warmer din.
Tana saukowa daga wajen mommy na shigowa falon,cikin hanzari asma'u ta miqe ta gyara zamanta sosai cikin bacin rai ta soma fada kaman zata saki kuka
"Yanzu fisabillilahi mommy ni an kyauta min kenan?,babu dama nace ina son abu sai daddy ya hadani da yarinyar nan,yanzu kaman ni ace in saka kaya iri daya da nata,na riqe waya irin tata,mu shiga mota daya tayi driving nayi,mu shiga makaranta a gani ai wallahi sai friends dina su rainani" mommyn dake shirin zama nan wajen tace
"To ya zakiyi husna,sarai kinsan halin mahaifinku,idan yayi niyyar abu babu kai hanashi" ta sake narkewa kaman mai shirin fidda qwalla tace
"Ni wallahi na fahimci kawai daddy ya shurya zubda min mutunci na da ajina,ke ba sai kiyiwa tufkar hanci ba mommy,gaskiya bazan yarda ba nidai kawai ki karbi wayar kya siya mata wata,koni na saka hamid ya kawo mata dai dai ita daga kamfaninsu tunda sun fara qananun wayoyi daga 50k zuwa sama"
"To ai shikenan indai kinsan zaki kawo mata watan,banson ne daddynku ya fuskanci bata hannunta ya daga ma mutane hankali....aysha" mommy ta qwala mata kira wadda ita tuni har ta isa dakinta ma tana shirin daura alwala tayi shafa'i da wutiri,sai ta fasa ta fita kiran mommyn
"Wayar da daddynku ya baku dazu zaki kawomin na ajjiye miki wajena,za'a kawo miki wata wannan bai kamata ki fara amfani da irinta ba tun yanzu" cike da rashin damuwa ta nunawa mommyn inda kayan suke,don tunda aka soma dramer tasan akwai abinda zai biyo baya shinyasa ma bata debe kayan ba,asma'un ita taje ta birkita kayan ta dauko wayar tana jifan ayshan da harara kamar ita ta cewa daddyn ya aikata hakan ko tana da masaniyar zai aikata din
"A'ah dawo ki debi sauran kayan mana ya zaki barsu nan?" Mommy tace da aysha wadda take niyyar komawa dakinta,bata ce komai ba ta dawo ta kwashesu tana fadin
"An gode".
" ke kawo....zonan mu ga"asma'u ta fada cikin hargagi,ba musu ta dawo da baya ta sake zube kayan a gabanta,hannu ta saka ta bibbirkita ta ciro doguwar riga guda daya wadda bata da kalarta cikin wadda daddyn ya raba musu,gefanta ta jefa tana cewa
"Jeki wannan ta yimin,kamar ma tafi tawa tsada,ina da wata idan na shiga daki zan dauko miki a amadadinta" Tsaki asma'u taja bayan ayshan ta shiga dakin
"Rigima ce fa kawai irin ta daddynku,ita kanta yarinyar na fuskanci rayuwa bata dameta ba,yarinyar data taso a qauye saika dinga siyan kaya na manyan kudi kana bata,harda abinda batasan darajarsa ba ma....miqo min wayar" mommy ta fada tana miqawa asma'u hannu,saita noqe
"Namecy zan bawa ita mommy please" dan zare ido mommy tayi
"Ke bana son sakarci bani nace" cikin shagwaba tace
"Habba mana mommy,kinsan 'yar waye ne cikin garin nan?,wallahi nasan na bata wannan wayar as a gift ba qaramin daga min aji kyautar zatayi ba" harara mommyn ta watsa mata
"Yar banza,sai shegen son suna da tara qawaye"
"Thank you my mommy,i love you so much" ta fada tana tsalle hadi da faduwa saman kujerar cikin farinciki,ta tabbata gobe zatayi abunda kowacce saita kalleta cikin qawaye,haka nan husna zata sake ganin darajarta da yadda da irin kudin nasu gidan,duk da qawaye ne amma gasa ce sosai a tsakaminsu,kowacce so take tayi abinda zata burge daga,kowacce so take 'yar uwarta taga ta fita,kowacce so take ta ganta itace a gaba ta baro daya a baya,su kansu basu san cewa abota suke mara ma'ana ba,har hassada da qyashi da kishi ya shigo cikin tarayyarsu yayi kane kane ba tare da sun sani ba,abu daya ne ya hana mommy amshe wayar jin cewa 'yar wani za'a bawa,kasancewarta mace mai son mu'amala da manyan mutane,tana son a ganta tana mu'amala da wani,wanin ma da yayi suna ya kuma shahara,haka dabi'arta take a jininta take,kusan ba'a qasa yaranta suka dauki wannan dabi'a,za'a iya cewa duk cikinsu mutum daya ce ta banbanta da su,halayenta kusan irin na mahaifinta ne,hakan ya sanya babu jituwa ko alaqa mai qarfi tsakaninta da asma'u,saboda banbancin ra'ayi da hali.
A hankali yake kurbar lemon dake cikin tambulan din qarau na glass sake gabanshi,yayi kyau cikin shigar da yafiyi shigar suit musamman idan ranakun aiki ne,yanayin zamanshi a wajen da yadda yake kai lemon bakinsa lokaci lokaci kadai ya isa ya gaya maka nutsuwar da yake sa ita uwa uba aji da kyau da Allah ya bashi,kusan babu budurwar da zata shigo wajen bata kalleshi ba,masu rawar kan cikinsu kanyi sha'awar dosar sa su taya hajarsu saboda alamun malasa da suke hangowa tattare da shi,saidai basu iya qarasawa saboda kwarjinin da yake da shi suke karya kwana su sauya hanya.
Agogonsa ya sake dubawa ya yarfar da hannu gami da jan tsaki,banda haduwarsu da mas'ood yau ta zama dole baiga abinda zai sashi zaman wajen ba,sam wajen baiyi masa ba,akwai yawaitar cakudedeniyar maza da mata abinda yafi tsana,yana da kishi qwarai duk da cewa kuwa baida qanwa mace,a zahiri zaka ce bai damu da motsin dake faruwa a wajen ba,saidai a badini yana zaune ne yana sake.nazarta da karatun halayyar 'yammatan zamani,abubuwa da yawa sun faru da suka bashi mamaki suka kuma sake sa mishi tsanar zaman wajen,yana mamakin yadda yammatan ke shigowa,wata tsakiyar maza biyu wata namiji daya,ba wani kunya ko takatsantsan da aka san diya mace da ita,ta zauna cikinsu suci abinci ko abinsha suna hira kaman zasu tafa,wasunsu ma sukan kebe can baya suje susha shisha,wanda shi a wajenshi bata da maraba da taba wiwi da sholisho,hakan take ko a wajen malaman lafiya,zuqa daya ta shishar dai dai yake da ka zauna kasha karan taba sigari guda dari biyu,yana da yaqinin mafi yawansu ba nan suka cewa iyayensu zasu ba,suna iya qarya da sunan mabanbantan wurare da sunan cewa can suka nufa,su binne iyayen har su zo su koma basu fuskanci komai ba.
Dogon tsaki ya kuma ja yana niyyar dauke kanshi wata mota ta shigo wajen,hakanan yaji ta dauki hankalinsa,bawai don kyanta ko bai taba ganin irinta ba,a'ah,hasalima shekararsa uku da hawanta,duk da ba ita yake kallo kai tsaye ba amma hankalinshi na wajen.
kaman a mafarki yaga khadija na fitowa daga gaban motar bayan matashin dake tuqa motar ya zagayo ya bude mata,yana iya ganin sanda ta sauya hijabin jikinta da mayafi sannan ta fito,tare suka jero har zuwa kan daya daga cikin kujeru da teburan dake wajen suna wa juna magana.
Sosai mamaki ya kamashi,don bai tsammaci ganinta a ire iren guraren nan ba tare da wani namiji,da kuma shiga irin ta jikinta,aljihunsa ya laluba sai yaji wayarshi da yake kiranta da ita,yaji dadin hakan,don dama ya taho da ita ne saboda yana da plan din daga nan ya leqa wajenta.
Miscal wajen hudu yana hangota daga inda yake,tana ganin kiran take dauke kanta,daga bisani ta soma tsaki,yana hango saurayin na mata magana kan ta daga,sai a kira na shida sannan ta daga din,sallama ya soma mata ta amsa da qyar tana wani basarwa
"Hala na katse miki wani abu mai muhimmanci...."
"Kusan haka ne,don bacci nake...na dawo daga makaranta na gaji ina buqatar hutu don Allah....ko kudin sun samu ne?"
"A'h...muryarki dama kawai nake da muradin ji"
"Ohk....idan sun samun zaka iya kirana saika gayan ranar da zaka zo" ko kafin ya kashe tashi wayar tuni ta datse nata layin,yana iya hango yadda take yatsina fuska sannan daga bisani ta wurga wayar jaka ta sake tattara hankalinta ga saurayin.
Yana shirin dauke idanunsa ya hangi sanda ya amshi jakarta ya saka mata kudi a ciki,kanshi ya kawar sannan ya miqe tsaye bayan ya ciro wayarshi yaba laluben number mas'od ranshi a bace,shi yasa ya tsani jira,badon mas'ood din ya tsaida shi da alqawarin yana hanya ba da bai zauna wajen har idanunsa sun gane masa abinda ya gani din ba
"Afwa boss,afuwa don Allah"
"Is too late....nayi cancel schedules dina na yau na zauna jiranka duk da muhimmancin da lokacina yake da shi.....saidai wani lokaci kuma idan na samu chance....na kiraka ne na gaya maka karka qaraso baka kuma sameni ba" ya qarashe fada yana shigewa bayan motarshi da jibril ya bude masa sannan ya kashe wayar ya ajeta gefanshi,idanunshi na kansu har sanda driver ya soma jan motar suka soma barin wajen,idanunsa ya lumshe sanyin A.cn dake cikin motar yana ratsashi,sosai zuciyarsa na zafi...dukkan wani hope nashi yana sake raguwa sosai fiye da kowanne lokaci,sunayen Allah yake jerowa daya bayan daya cikin zuciyarshi kamar yadda ya saba duk sanda yaji bacin rai,bai yadda ya zauna zuciyarshi na soyuwa hakanan ba tare daya kira Allah ba.
*mrs muhamma ce*👑
*D B*
*0⃣6⃣
*Wannan littafin na kudi ne meso ya karanta ya nemi wannan number 08030811300*
Washe gari ita mommy ta baiwa tsaraban yaran nata dake aure ta hadata da driver ta kai musu,duk da cewa tana da makaranta amma ita sam wannan ba matsalarta bace,damuwarta shine ta idar mata da nata aiken koma ya zatayi ba matsalarta bace,hakan ya sanya a gurguje taje ta miqa musu,ba wani zama tayi ba,ko dama can ba wani sabo ke tsakaninsu ba,tsakaninsu da ita idan bautarsu da tashi,gidan anty safiyya kawai ta dan zauna har ta sha ruwa,kasancewar duk ta fisu sakin fuska da janta a jiki.
Ranar bata shigo gida ba sai qarfe biyar na yammaci,duk da haka bata zauna ba sai data shiga kitchen ta shiryawa daddy abincin dare da taimakon inna laraba,data gama dinma dai ba zama tayi ba,kayanta ta soma hadawa wanda zata je gida gobe da su,tsaf ta shirya kayan nata cikin matsakaiciyar jaka,kaman yadda ta saba ta tsinci wasu daga cikin kayan nata ta zuba daban da niyyar yin kyauta da su kaman yadda ta saba.
🧶🧶🧶🧶
Tafe suke shida drivansa cikin motar tasa baqa wul,wadda kallo daya zaka mata kasan ba qananun kudi aka sanya aka sayeta ba,yana lafe bayan motar sanyin raba na kadashi,sanye yake da suit suma baqaqe wadanda suka dace da kalar fatarshi wadda ainihin hutu da jin dadi suka ratsashi,dirarsa kenan cikin qasar,wanda a yanzu haka yana hanyarsa ne ta isa gida,lokaci lokaci yakan lumshe kyawawan idanunsa dauke da zara zaran gashin ido,hakanan yake jin kasala da gajiya sun masa dabaibayi,Allah Allah yake ya isa gida yaga anninsa ya kuma kwanta ya huta.
A hankali qaramar wayarshi da bai wuce mintuna goma da kunnata ba ta dauki qarar qaraurawa,ko bai daga ba yasan wacece,ita kadai zata kirashi ta cikin wannan wayar,saboda don ita kadai ya saka layin ciki,hakanan daya bude yaci karo da tarin saqonninta tun na kwanaki bakwai da suka wuce,wato kwananshi biyu kenan da barin gidansu,kwana daya kuma da ganinta da yayi a wancan eatery din,wanda yayi dai dai da tafiyar data kamashi zuwa china sai a yau ya samu dawowa,a kasalance ya saka hannu ya daga wayar gami da karata a kunnesa
"Na gode da wulaqancin da ka yimin,duk ni na saiqa kaina koma meye ka yimin khalipha" idonsa ya sake lumshewa ya bude yana jin yadda taratsin maganarta ke ratsa kwanyarsa
"Afwan dija na"ya fada cikin qarfi halida danne bacin ranshi a kanta wanda ya haifar da sanyi a muryarsa,sanyin muryar da ta kashe mata jiki tare da sauke kaso hamsin cikin darin bala'in data so yi
"Ni baka da abinda zaka gayamin,wannan wanne irin cin fuska ne,tun ranar da kazo gidanmu na qarshe gaba daya aka daina samunka a waya,kuma kai baka neme ni ba,haka ake soyayyar?"boyayyen murmushi kawai ya saki,shi yasan ba wannan ne maqasudin fadanta ba,a baya bata taba nemansa ko damuwa da duk kwanakin daya dauka baije gidansu ko ya nemeta ba,idan ya nemeta falillahil hamd,idan ma bai nemeta ba duk daya wai mamaci ya karye
"ai nace kiyi haquri ko?,wayar tawa ce ta samu matsala,sai yau na samu na karbo daga wajen mai gyaran" ya qarshe maganar yana istigfari cikin zuciyarshi,daga can bangaren khadija dummm tayi,tana sake ji cikin zuciyarta da jikinta lallai muhammad din bai dace da ita ba sam,baiwar kyau kawai Allah ya masa,wanda bazata bari kyansa ya rudeta ba ta shiga gidan da bashi take da buri ba,wanne irin gyaran waya fisabillilahi,wayar tashi da ko tata wayar ta fita tsada,don ranar farko data fara ganin wayar sai data sake kallonta,gaba daya ba zata wuce dubu goma ba
"Kawai ka fadi me ya hanaka dawowa,ko babu waya ai qafafunka zasu iya kawoka,ko kudinne ba zaka iya bani ba shi yasa ka janye jiki?" Maganarta ta bashi dariya,baisan murmushin da yayi ya fito fili ba sai data ce
"Dariya na baka?" Cikin waskewa yace
"A'ah....ba haka bane,gani nayi kin kusa canko abinda ya hanani dawowa.....kawai dai kudin ne basu samu ba,kuma ina kunyar nazo miki haka" ranta yayi qololuwar baci,a haka zata aureshi?,mutumin da ya kasa mata kyautar naira dubu talatin kacal ina zai samu kudin aurenta,a gabanta kowacce cikin qawayenta suka dinga karbar alert na kudade daga samarinsu,mai qaramin kudi cikinsu itace wadda aka turowa dubu talatin,sai ita zata tashi a tutar baya?
"Kana nufin duk jiran da nayi ya tashi a banza kenan bazan samu ba?" Sake gyara kwanciyarshi yayi bayan motar sanyin A.C na ratsashi,cikin kwantar da murya kaman gaske yace
"Ni bance ba zaki samu ba,ai Allah shine mai bayarwa,shike kuma azurta bawa a duk sanda yaso,ina nan ina qoqari cikin satin nan ina saka ran Allah bazai hanani ba" shiruuu tayi bacin rai na ratsata
"Ai shikenan" abinda ta iya fada kenan ta katse kiran,wayar ya cire a kunnensa yana kallonta,ya sake sakin murmushi kawai yana girgiza kai,baiyi ko yunqurin nemanta ba ya aje wayar gefanshi saboda baison sauran hayaniya hutu yake nema kuma,har suka isa gida yana tunanin rayuwa da irin darussan daya samu masu tarin yawa dangane da halayyar 'yammatan zamanin nan.
A nutse yayi sallama cikin parlourn alfarma wanda yake mallakin mahaifiyarsa,parlour ne daya wadata da dukkan wani nau'i na kayan morewa rayuwa,dattijuwa anni na zaune cikin daya daga cikin kujerun tana sauraron hadisai saga tashar talabijin ta saudi sunna tare da kallon masallacin ma'aiki da suke nuno lungu da saqonshi,a hankali ta cira kai tana amsa sallamar tashi fuskarta qunshe da fara'a,yayin da bakinta ke furta masa marhaban lale,cikin qauna irin ta d'a da mahaifi ya iso gabanta,suka shiga gaisawa cikin nunawa juna kulawa
"An dawo lpy"
"Lpy alhmdlh anni cike da nasara"
"Alhamdulillahi rabbil Aalamin" ta fada tana hade hannayenta waje daya kaman mai addu'a,kansa ya sake dagawa ya dubi saudi sunnah sannan ya kuma duban anni cikin murmushi
"Ko yaushe cikin shauqin wajen nan kike anni" murmushi ta sake masa mai sanyi irin na manyan dattijai sannan tace
"Banda abinka khalipha wannan waje ko sau nawa musulmi zaije ai bazai rabu da shauqinsa ba,ba zaiqi ya dawwama a nan ba har ranar mutuwarsa"
"Gaskiya ne,inaga ki soma shiri zan sa khalid ya shirya miki komawa can cikin watan nan,ko sati hudu kije ki sake yi" murmushi ya sake yalwata kan fuskarta,farinciki tare da alfahari da tilon dan nata ya sake mamayarta,bai wasa da duk wani abu data nuna tana muradi ko da iya kan fuskarta ya fuskanci haka,kwata kwata watanta uku cikin na hudu da dawowa daga umrar
"Ba matsala khalipha?" Murmushi ya saki
"Har abada anni ina fata mun tserewa matsala,ko sau nawa mike da buqatar zuwa ki fadi kawai,yaronki a shirye yake da ya kaiki,uwace ke da ba kowanne d'a yake dace sa irinta ba,har abada bazab manta sadaukarwarki garemu ba"
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi ta timmus salihat,Allah yaci gaba da yiwa rayuwa albarka,ya tsareka ya maka jagora,Allah ya zama gatanka kaida 'yan uwanka,ya hadaka da mace ta gari"
"Amin ya Allah anni,Allah ya qara lafiya da nisan kwana"
"Amin amin" ta fada tana murmushi,ya bude bakinsa zai sake magana yaga shigowarta falon,hannunta riqe da wani kyakkyawan kwando kwanon tangaran,tana sanye cikin shadda gezner ruwan hanta wadda aka yiwa dinkin buba da ado mai kyau tun daga sama har qasa,tayi daurin zamani tare da buga kwalliya sosai,suna hada idanu ta soma jifansa da murmushi,janye idanunsa yayi a hankali ya maida kan anni yayin da take qarasowa kusa da su,ta aje kwanon gaban annin sannan ta zauna tana fadin
"Barka da dawowa ya khalipha"
"Yauwa,sannunki amal"
"An dawo lpy ya hanya?" Ta fada tana murza yatsunta kanta a qasa alamun jin kunya,ya sake dubanta ya dauke kai sannan ya miqe yana cewa
"Alhamdulillah,yasu momma?"
"Lafiyarsu qalau suna gaidaka"
"Ma sha Allah,anni zan shiga nayi wanka na huta" daga kanta amal tayi da sauri tana dubanshi
"Ya khalipha ga abinci can na shirya maka fa" ta fada a narke tana dubanshi
"Am ok,nafi buqatar na huta" ya fadi yana soma motsawa alamun zai wuce ne
"A'ah ai ba'ayi haka ba,kaje kayi wankan saita miqo maka ko a can sai kaci" cewar anni wadda bata so amal din taga kaman ya gwasale qoqarinta ne,saboda tunda ya kira annin yace mata sun taso take rawar qafa
"Ba damuwa anni" ya fada yana daukar safarshi daya cire yayi gaba.
Sai daya kashe wayoyinshi kaf sannan ya rage kayan jikinsa ya fada bandaki,mintina talatin yayi sannan ya fito,ya shirya cikin jallabiya mai gajeran hannu,yana cikin fesa turarensa ya jiyo knocking daga can qofar falonshi,ya aje turaren yana daukar wayarsa qwaya daya ya kunnata sannan ya fita zuwa falon.
Amal ce ita da mai aikin anni raliya,wadda ke dauke da kwanukan abinci,sakin qofar yayi,amal ta amshi kayan abincin daga hannun raliya ta shigo ciki,kasancewar ta sani baiso kowa na shigo masa bangare barkatai,a gabanshi ta dire kwanukan abincin a sanda yake waya da P.A dinshi,kafin ya kammala harta gana zuba masa komai ta samu gefanshi daya daga cikin kujerun ta hakimce tana satar kallonshi,ba qaramin so takewa khalipha ba,ji take kaman ta bude ido taga ya zama nata,komai nashi yayi mata,sak irin mijin data sha zanawa a mafarkinta,kyakkyawa mai qirar qarfi,mai aji mai kudi kana mai dimbin ilimi.
Hada idanu sukayi sanda ya dauki plate din data cika da fried rice da gasashshiyar kaza a gefe,daga cikin dabi'unsa sam baison kallo,a nutse yana juya abincin yace da ita
"Akwai wani abu da yayi saura ne amal?,kina iya tafiya" shagwabe masa tayi tana noqe hanci
"Haba ya khalipha,wanne irin na tafi bayan hira nakeso na tayaka?yaushe rabon da mu hadu don Allah,amma kai ko irin nunawa ma baka yiba" fararen idanunsa ya watsa mata yana tauna abincin bakinsa a hankali,sai daya hadiye sannan yace
"Indai zaman hira kika zo yi yanzu kam bazan iya ba,kinsan ban iya cin abinci ana min surutu ko?"kai ta sadda qasa
"Kayi haquri to" sai ta dan bashi tausayi kadan,banda ya riga ya gama da farke layarsu ita da mahaifiyarta bai tunanin zai iya tsallakewa tarkon ita yarinyar a yadda take binshi sau da qafa
"Is ok,kije ciki idan nayi bacci na tashi zan shigo,sai muyi hirar ko?"
"Tohm" ta fada tana miqewa tare da ficewa daga parlourn bayan ta ja masa qofar,kai ya girgiza yana ci gaba da cin abincinsa a hankali,har yau bai manta da mahaifiyarta ba wato momma zinat,har yau bai mance irin kyara tsana tsangwama da kallon qasqanci da ta dinga jifansu da shi shida mahaifiyarsu ba a wani zamani baya can da ya shude,sai gashi cikin qanqanin lokaci momma zinat din ta koma daya daga cikin gagga gaggan masoyansu,abun da mamaki da kuka daure kai a wajenshi,saida ga duk wanda baisan abinda ya faru shekara kusan goma sha biyar baya ba zaiyi zaton soyayyace daga Allah momma zinart din ke musu,da wannnan tunane tunanen ya kammala,a nan kan doguwar kujerar da yake kai ya miqe,kan wani lokaci bacci yayi awon gaba da shi kasancewar tafiyar da yayi bai samun isashshen baccin da ya kai awa hudu ko biyar
🧶🧶🧶🧶
Tunda suka shigo siririn titin da zai sadaka da ainihin qauyen nasu tunaninta ya rarrabu kashi kashi kaman yadda ta saba kowanne lokaci,ina zata sauka?,a wanne gida zata fara yada zango?,gidansu mahaifinta ko gidansu mahaifiyarta?,ko kuma gidan gwaggwo lami?,ason ranta gidan gwaggwo lami tafi sha'awar ta sauka,saidai hakan ka zama tamkar ta aikata wani laifi ne aduk sanda labarin zuwanta ya iske gidansu mahaifiyarta harma dana mahaifin nata,zasuyita mata fassara daban daban kaman yadda suka saba,duk da cewa ada bawai sun damu da rayuwarta bane,saidai a yanzun suna son nuna sun damu da rayuwar tata ko don dan qaramin alkhairin da take riqowa tazo musu da shi,wanda hakan ya dan sauya yanayin mu'amalarsu da dangantakarsu,sauyin da bai taka kara ya karya ba,sauyin kuma da bashi da wata ma'ana ko alfanu a gareta.
Itadai a baya tasan ba wanda ya damu da rayuwarta,babu wanda ya damu data rayu kota mutu,ba wanda keson ta rabeshi,kowa gani yake rab'uwarta da shi wani kayan nauyi ce,idan kuwa ya zama dole ta rabi mutum din yana ganin ya yiwa rayuwarta gagarumar alfarma ne,koda kuwa babu wani abu da yake iya tsinanawa rayuwartata
Umarni ta baiwa mai motar da ya daukota tun daga tashar takai saboda asma'u ta fice da motar da daddy ke fadin wai ya basu,wai mana tunda bata taba shigarta ba itakam,hakan kuma bai dameta ba,mommy kuma ta kasa bada koda qarama cikin motocinta biyu a kawota kasancewar babu idon daddyn,tun da sassafe ya sallameta sukayi sallama ya fita,tace drivan ya sauketa qofar gidansu mahaifinta,tunda duk tsiya da uba ake ado,yaran da sukayi tsaye gaban motar su suka daukar mata jakarta zuwa cikin gidan,sai data biya direban sannan tabi bayan yaran zuwa cikin gidan,lokaci lokaci gabanta na faduwa tare da tunanin me kuma zata taras wannan karon.
Kamar ko yaushe,kamar kuma kowanne lokaci irin wannan,dukkan matan sassa sassa dake gidan na gindin qatuwar bishiyar dake tsakar filin gidan,wadda kusan itace ta zama wajen hutawarsu a duk sadda rana ta qwalle a sararin subhana,nan ne dai wajen zaman,masu sana'a nayi,masu gulma da sa'ido ma duka suna yi,masu ayyukan gida ma duk sukan jibge a nan,wasu bisa shimfidar tabarmar kaba,wasu kan kujera 'yar tsuguno,yayin da wasu ke a tsaye suna surfe ko wani aikin ma daban,bishiya ce da Allah ya mata yalwar inuwa da kuma iska,har wani bai takurawa wani,wajen zaman ya ishesu a wadace.
Tunda aka shigo da jakarta yanayin hayaniyar dake wajen ta ragu,kowa ya maida hankalinsa kan ganin shigowarta,mata ne a qalla sun kusa su goma kowacce idanunta a kanta tana qare mata kallo,ta saba da wannan kallon tun a sanda yake muguwar guba ce a rayuwarta,balle yanzu da kaifin wannan gubar ya ragu saidai abinda ba'a rasa ba,fuskarta a washe ta zauna gefan tabarmar da tatuwa take kai ita da faccalarta karime ke kai suna irga soyayyar tunkuza wadda da alama basu jima da kammala aikinta ba,saboda yanayin maiqon dake jikin zannuwansu da rigunansu,kowacce da yanayin data amsa mata,zuciyar kowannensu da abinda take saqawa.
Tsahon mintuna tayi a cikinsu tana tattambayar 'yan uwanta dake gidajen aure da iyayenta maza wasanda dama ta tabbatar suna goba suda yaransu maza wadanda suka tasa sai qananu da aka bari a gida,matan kuwa matasan da basuyi aure ba na wajen talla,kana daga bisani ta tambayi kakarta wadda take mahaifiya ce ga mahaifinta hafsatu wadda suke kira da inna yelwa
"Tana rumfarta tana hutawa" cewar lami wadda ta maida tabaryarta cikin turmi bayan ta watsa dawar da zata surfa,tasan dama a rina,kasancewarta mace mai shegen mulki ga duk wanda ke qasanta da nuna isa,bata cas bata as cikin gidan,yawanci irin wannan lokutan tana rumfarta zaune saidai ta wurgo umarni kuma dole abi,walau 'ya'yan nata ko matansu ko su kansu jikoki.
Ilai kuwa a sanda ta daga labulen dake rumfartata sai ta sameta zaune saman tabarmar karauninta,falon nata a share qal wanda tasan aikin daya daga cikin surukan nata ne,wanda duty duty suke,qafafunta miqe abinda,haule daya daga cikin surukanta tana murza mata goro a magogin qarfe tana watsawa bakinta,bawai don bata da haqora ba a'ah da saura,tsabar mulki ne da ganin dama.
Fuskarta a sake tayi sallama yayin da inna kululu ta dago kai tana dubanta
"Hala kinji zuwan waccar uwar taki shine kika kwaso qafa kika taho,bayan kin san babu abinda zai sauya,zuwanki banza zamanki banza" sosai kalaman suka soki zuciyarta,duk da cewa ta jima tana jin ire iren wadan nan kalaman daga bakin inna kululun,saidai har yau ta kasa sabawa,ta rasa sai yaushe wannan DAURIN BOYEN zai warware?,sai yaushe komai zai gyaru?yaushe zatayi dariyar farinciki da zata ratsa har qasan zuciyarta kamar kowacce 'ya?.
Bata amsa mata ba har ta zauna gefan tabarmar da take kai tana gaida haule,ta amsa tana miqewa tare da gyara daurin zaninta da alama ta gama murza goron,kallonta inna kulu tayi
"Ki kiramin karime"
"Toh" ta amsa tana ficewa,sai data fitan sanann innar ta maida kallonta kan aysha
"Uwarki kika biyo ko?" Ta sake maimaitawa bayan ta amsa gaisuwar da ayshan ta mata,kai ta kada ranta na tabuwa
"Kibar wannan maganar inna yelwa,ni baffa nazo dubawa ance min baida lafiya"
"K'nnnnn,lallai Allah yasa da gaske kike,ya kika baro su sa'adatun,ince dai bakya musu wani mugun halin naki ko?" Ta fada tana tsareta da ido,ya ilahil Aalamina,daga durowarta?,ba'a tambayeta komai daya shafeta sai zancan su mommy?,koda yake hakan ba komai bane,abinda yafi hakan ma zata iya gani
"Suna lafiya lau,tana gaisheki"
"To madalla".
Shiru ne ya biyo baya kaman wadansu baqin juna,ita innar bata ga damar sake magana ba har karime ta shigo ta fita,yayin da ayshan ta rasa abun cewa saboda ba wani sabo bane tun fil'azal tsakaninsu,bugu da qari tunanin daya rinjayi zuciyarta ta gefe guda najin mahaifiyara dake aure a lagos wai tazo,ba zata iya tuna yaushe rabon data sanyata a idanunta ba,idan zata tuna tun sanda zata bar qauyen zuwa gidan daddy rabonta da ita,shekara aqalla kusan takwas kenan,rabuwar da har yau tana tuna yadda suka yita,a duk sanda ta tunada lokacin sai qwalla ta cika mata idanu
Ta tafi tana roqon ta kalleta sau daya,ta tafi tana kukan ta kira koda sunanta sau daya taji da kunnenta,ta tafi tana kwadayin taji tayi mata addu'a ko sau daya ne tak a rayuwarta,saidai dukka wannan burin nata bai cika ba.
Sai qarfe biyu saura ta miqe daga zaman kuramen ta rataye mayafinta ta dauki butar inna kulun ta zagaya don kama ruwa da daura alwalar sallar azahar
*mrs muhammad ce*👑
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER ( 08030811300)_*
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
0⃣8⃣
Kebantaccen waje ne da yake ganawa da muhimman mutanensa,wanda a siffa yafi kama da lambu.
Waje ne mai kyau daya qawatu da shuke shuke da kujeru irin na kaba,daga gefe guda wani magangarar ruwa akayi mai kama da qorama,zakayi zaton ba cikin companyn yake ba saboda yadda aka tsarashi,kallo daya zaka ma wajen ka fuskanci dan qaramin taro aka gama yi a wajen,saboda yadda grass carfet din wajen ya baci da robobin kayan ci da na sha,khalipha na tsaye cikin mutanen wanda baqi ne daga qasar waje wanda zasuyi hadin gwiwa wajen bude wani kamfani,da sauri daya daga cikin yaranshi wanda ke riqe da wayoyinshi ya matso inda yake tsaye,ya tsaya daga bayanshi kadan cikin girmamawa
"Sir,ana kiranka" hannunshi kawai ya miqa ya amshi wayar yana ci gaba da magana da mr james,vivo dinsa ce yasan mai kiran koda bai duba ba,amma duk da haka saiya duba screen din,khadija ce kamar yadda ya zata,bai samu damar daga wayar ba har sai da suka kammala maganarsu da su mr james sukayi sallama da su suka shiga motocinsu suka fice daga companyn baki daya.
Da sauri daya daga cikin yaran ya sake matsowa da niyyar amsar wayar ya adana ta,daga masa hannu khalipha yayi sanda ya danna kiran khadija sannan yaja baya jikin wasu flowers da aka yiwa ado mai kyau
"Muhammad...ni kake qin dagawa waya?" Abinda ta soma fada kenan,kadan ya cije lips dinsa kana yace
"Afwa....ina wani uzuri ne....mun tashi lafiya?"sai data ja iska kafin ta amsa masa
"Lafiya lau.....ya ake ciki ne wai?,gaskiya jiran fa yayi yawa...har yau kana nufin kudin basu samu ba?" Danne bacin ranshi yayi cikin dakiya yace yana kada kai tare da tabbatarwa kansa itama khadijan ta fadi,bata kai labari ba,bata kuma cinye jarabawar ba
"Su naketa qoqarin hadawa basu samu ba....dubu goma ce kawai ta samu" can qasa yaji ta ja tsaki tana qunquni sannan tace
"Ka kawon dubu goman na toshe wata kafar,da babu gwara babu dadi"
"To shikenan"
"Kar ka wuce qarfe hudu saboda inason in fita"
"To babu damuwa" qit ta kashe wayar,ya cirata daga kunne yana kallonta gami da kada kai,har yau dai jiya iyau,dukkansu kaman tare aka haifesu tsabar kamanceceniyar hali,ya talaka yake wanda baida komai kafin ya samu macen aure a wannan zamanin?,ya talaka mara abun hannunsa yake kafin ya samu soyayyar gaskiya?,da wannan maganar zucin ya miqawa jibril wayar,ya amsa yana miqo masa daya daga cikin kebantattun wayoyin nashi wanda kira yake ta shigowa tun dazun,bai bashi bane ganin wata wayar yake amsawa,karba yayi ya kara a kunnesa kana ya soma takawa yana barin wajen,yana fita ma'aikata suka shigo suka soma kintsa wajen da kawar da duk wata dauda ko shara komai qanqantarta.
♦♦♦♦♦
Kusan jiran da ya saba yi mata na yau ya wuce na ko yaushe,bai damu sosai ba saboda maganar da yake cikin waya tun dazun ta dauke masa hankali,ya jima tsaye qofar gidan sanye da wani yadi mai sauqin kudi wanda aka yiwa dinkin riga iya gwiwarsa da gajeran hannu,irin yadikan nan ne da ake saidawa kan farashi mai sauqi,duk da haka yadin ya masa kyau saboda baiwar qira da Allah yayi masa,daga takalmin qafarsa har zuwa hularsa masu qaramin kudi ne duka baqaqe,mota uku ce ta masa rakiya saidai yau sun shigo har cikin layin,amma suna tsaye bayanshi qofar wani gida wanda a qalla daga gidan zuwa gidansu khadijan gidaje hudu ne a tsakanisu,waya ya daga ya kirata
"Gani nan" ta fada sannan ta kashe tana jan tsaki
"Kaman wani kudin arziqi ya kawo min,sai kyau iya kyau amma babu abokan tafiya,wannan da kyan da yake da shi da shine kudin shi kuma mummuna da da sauqi,kyau ba kudi ai wahala ce tunda ba dashi zaku rayu ba,ba kuma kyan zaka loqa a goshi kayi yawo da shi ba" ta fadi ita kadai tana mita sanda take gyara yafen mayafinta.
Babu wata cikakkar fara'a a fuskarta haka ta iso
"Mun yini lafiya"
"Lafiya lau ya mutanen gidan"
"Suna lafiya....." Ta amsa ciki ciki
"Ina saqon?" Ta buqata kai tsaye saboda tana tantamar idan ka ya kawo din
"Gasu nan" ya fada hannayensa na harde a qirjinsa ba tare da ya motsa ba yana karantar yanayinta lamarin na sake bashi tsoro da mamaki,sai ya cire hannunsa daya ya saka cikin aljihun wandonshi,ganin haka ya sanyata tadan saki ranta sannan tace
"Ok....mu shiga daga ciki mana" ta fada tana duban qofar gidan sannan ta maido idanunta kanshi,kafadunsa ya daga duka biyun yana ci gaba da qoqarin zaro kudin,ba tare daya dubeta ba yace
"Ba sai na shiga ba,abinda kika fi buqata na kawo miki kawai muyi sallama na wuce" bata fahimci komai ba haka bata ce komai ba,saboda hankalinta dukka yana kan kudin daya ciro a aljihunsa,wanda kai tsaye bata ce ga adadinsu ba,bandir bandir ne sababbi kar a miqe na 'yan dubu dubu guda biyar,sai 'yan dari biyar biyar kuma daban,wadan can ya maida aljihunsa ya irga 'yan dari biyar biyar din dubu goma ya miqa mata yana kallonta
"Lissafa kiga sun kai?" Amshewa tayi,cike da zumudi qasan ranta tare da fatan samun qari ta lissafa cikin qwarewa sannan tace
"Sun cika" sai ya kada kai ya sake ciro wadancan bandiran yana dubanta yace
"Nawa kika ce kina buqata a baya?" Farrrr tayi da ido dadi na ratsata,addu'arta ta karbu cikin zumudin daya kasa boyuwa tace
"40k kawai nake buqata,ina zaton zata isheni komai da komai" sai ya miqa mata dukkan kudaden hannun nasa yace
"Zaki iya gane nawa ne nan ko?" Cikin zumudi bakinta a washe tace
"Yes,duk bandir daya dubu dari ce,duka wannan five hundred thousand kenan"kai ya gyada hannayensa soke cikin aljihunsa,ya dan shaqi iska sannan yace
"ki riqe duka na baki" idanunta ta waro baki daya tana jujjiya kudin cikin rudewa tace
"Kai muhammad please da gaske kake?,dama ka samu kudin kake ta min wasa da hankali haka,oh my god sweetheart na gode na gode,dama ni na sani ba zaka barni naji kunya ba,dama ashe wasa kake min"
"Eh....gwadaki nake.....kuma kinyi failing....baki ci wannan jarabawar ba khadija,kin fadi warwas har abada" sai kuma ta dan saurara daga murnar da take tana dubansa cikin mamakin kalamanshi
"Kamar yaya wacce iriyar jarabawa?"murmushi ya fidda mai kyau wanda ya sake fitar da kyan surarshi,sai taga yau taga yafi kullum yi mata kyau,ya zaro wayarsa yana dannawa wadda khadijan ta bita da kallo,idan bata manta ba wancan satin ta taba tambayar kudin wayar taji tafi qarfin kanta,don har saurayinta ta tamnaya ya siya mata ita a sannan yace bata da hankali,ashe ba qananun kudi ta baro masa ba, cikin burgewa take bin wayar da ido,idanunsa na kan screen din wayar yace
"Kudi kike so khadija bani ba,kudi sunfi miki soyayyata,sune gaba da komao a wajenki....gasu nan na baki su a madadina...as from today ki saka a ranki baki taba sanin wani mai suna muhammad ba a rayuwarki ko mai kama da shi,kisawa ranki kamar a mafarki alaqarmu ta taba wanzuwa....." Ya qarashe maganar yana kashe wayar tare da maidata aljihunsa fuskarsa qunshe da murmushi wanda take cakude da mamaki,haushi al'ajabi da takaicin halayyar 'yammatan yau,yayin data saki baki kawai tana binsa da kallo saboda lissafinta dake neman dagulewa lokaci guda.
Kunya da tsoron rasashi a sanda ta fahimci wayeshi suka dabaibayeta,tsoron subucewarsa daga hannunta a sanda ta gane cewa type dinta ne shi suka cikata,cikin qoqarin kare kai ta bude baki da niyyar bawa kanta kariya,saidai isowar motocinsa wajen yasa ta kasa furta komai,a gabanta ilyas daya daga cikin yaranshi ya bude masa bayan motar ya shige ba tare da ya sake koda waiwayarta ba,tana kallo suka janye motocin suka fice daga layin suka barta tsaye riqe da rafas din kudi.
Har suka bace daga layin tana tsaye tana bin kyawawan baqaqen motocin da kallo mamaki ya daskarar da ita,da gaske wannan shine ainihin muhammad ba wanda ta sani ba?,shin mafarki take ko gixo idanunta ke mata,saita maida idanunta kan kudin tana jujjuyasu tare da qare musu kallo,qwaqwalwarta a daure take tamau,ta rasa me zata aiwatar,takai hancinta ta shanshanasu,wani irin lallausan qamshi suke fitarwa irin mai kwantar da zuciya,take nadama da dana sani suka lullubeta,ya akayi ta kasa boye zalamarta?,ya akayi ta kasa gane cewa muhammad ba qaramin mutum bane?,iya motoci kawai data gani na biye da shi da kyautar daya mata a yanzu sun isa bata amsar cewa shi din wani ne,shi din isashshe ne,sam bata jin zata iya haqura da shi,asarace da ba zata iya jurewa ba,samun irinsu muhammad a wannan zamanin tamkar gudun yada qanin wani ne ga 'ya mace,mai rabo ke samu,zata san yadda zata lallabashi ta dawo da shi cikin rayuwarta,tabbas sai ya zama mallakinta cikon burin rayuwarta kenan,jiki a salube ta juya ta shige gidan tana gyara riqon kudin a hannunta zuciyarta cike da zulumi da fargabar kada ta rasa muhammad daga rayuwarta.
*mrs muhammad ce*👑
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
09
A gaggauce ta tsame hannunta daga cikin flour din da take kwabawa ta dauraye hannunta ta goge jikin towel sannan ta fita a kitchen din don amsa kiran da mommy sa'adah keta qwala mataba tare da tayi la'akari da aikin data sanyata take yi ba
Cikin bedroom dinta ta taddata,tana zaune gefan gado,daga daura da ita kayan turarukan wuta ne lodi guda da alama lissafinsu takeyi,yar lelen nata kuma na gaban madubi tana ta shafe shafe da qalqale qalqale,saboda yau fita ce ta musamman zatayi,dinner ake na wata cikin qawayenta na makaranta da take aure,qawaye ne irinta 'yan ji da kai da daukar duniya da fadi,su kansu kayan da zata sanya a ranar order dinsu aka yi mata bayan an musu dinki na musamman,ba'a maganar jaka da takalmin da zata sanyawa qafafunta na kudade masu yawa.
"Mommy gani" aysha ta furta tana rusunawa gefan mommyn,wayarta ta aje sannan ta dubeta
"Saura me da me ki kammala ne?,qarfe shida na yamma fa zasu soma taron,kuma nasan tana can tana jira"
"Mommy na gama komai da komai,doghnout din ne naga kamar bazai isa ba shine zan dan qara yawanshi"
"Zaikai kamar nan da minti nawa?" Ta tambayeta bayan ta kalli agogo
"Awa daya ko minti hamsin"
"To kiyi sauri ki gama din,saboda ke zan aika ki kai matan"
"To mommy" ta fadi tana miqewa tare da qoqarin ficewa daga dakin
"Idan kin gama ki debi komai kimin packaging,ki hada masa dambun kazar nan da kika ma daddy last week,yau nake xaton hamid zai dawo gobe zai shigo waje na" cewar asma'u dake goga jambaki kan lebanta,wanda ta bada umarni ne kawai ba tare data waiwayo ta dubi wadda ta bawa umarnin ba
"Toh" shine abinda aysha ta fada tana ficewa daga dakin cikin ranta tana fadin autan maza,hamid shine saurayin asma'u data zaba cikin dubban samarin da Allah ya bata a matsayinta na budurwa 'yar qwalisa wadda har ranta takejin duniya na damawa da ita,me ji da kyau aji ado da gata takowanne fanni,hamid ya yiwa asma´u dari bisa dari,tana jin ya dace da tsarinta ya kuma yi dai dai da ra´ayinta,hamid matashin saurayin dan kasuwa ne maiji da gata da kuma dukiya,mutum ne shi mai shegen son girma,son matsayi da qyamatar mu'amala da duk wani wanda baikaishi arziqi ba,tafiyarsu tazo dai dai da asma'u saboda katarin hali da akayi yazo guda,soyayya ake bugawa sosai,wani irin so asma'u take masa wanda yake baiwa kowa mamaki,irinson da ba'a taba ganinta ta yiwa wani d'a namiji shi ba,saboda ta jima tana jan maza a qasa,tana daga musu kai da hura musu hanci saboda baiwar kyau da Allah ya bata da iya kwalliya,uwa uba gata data samu daga wajen uwa da uba kasancewarta auta a gidansu,saidai tashin farko ta matowa hamid,ya rushe duk wani plan nata ya tafi da zuciyarta,a yanzu haka babu wanda baisan da zaman soyayyarsu ba,haka nan ta tsaidashi a matsayin wanda zata aura,saidai iyaye duka basu shiga ciki ba,saboda tana da plan din sai ta gama degree dinta sannan a soma maganar aurensu,shi dinma hakan ya masa shi yasa komai ke tafiyar musu dai dai,suke kuma gudanar da soyayyarsu hankali kwance.
Sam jinin aysha da hamid zan iya cewa bai hadu bane ko kuma banbancin halayya ya sanya hakan,tsakaninta da shi gaisuwa,sai ko idan yazo ta miqa masa kayan maqulashen da asma'u ke sawa ta hada masa ta kama gabanta,yana da ji da kai girman kai da kuma daga kai da jin shi wani ne,wannan halayyarsa ce a jininsa.
Cikin awa gudan ta kammala komai ciki harda wanka,ta shirya tsaf cikin lace bayan ta nannade jikinta da laffaya wadda ta dace da shigarta,ita ba ma'abociyar son kwalliya bace,hakan ya sanya kaso hamsin na kyawunta ke boyewa idan ba ka mata kyakkyawan kallo ko kyakkyawan sani ba,ita dai barta da qamshi,tana son qamshi,kuma dukkan turaren da take amfani da shi ba mai hayaniya bane,saika matsa kusa da ita zaka dinga jin tashinsa,kuma a hankali,yawanci tafi ta'ammali da turaren kaya haka sai rollon body spray masu kyau da dadi tamkar wata babarbariya.
A parlour ta tadda momy tsaye tana amsa waya,dai dai sanda asma'u ta fito,ba banza ba ta kashe awa guda tana kwalliya,ba qaramin kyau tayi ba,duk wanda ya ganta kuma dole ya sake juyawa ya kalleta,ankon lace din yayi masifar karbarta,uwa uba make up din da tayi
"Hey momy sai na dawo" ta fada tana ficewa cikin hanzari tana kada muqullin mota,itama hannu mommyn ta daga mata cikin dan daga murya take cewa
"Kiyi qoqarin dawowa kafin daddynku ya dawo kinji na gaya miki" daga haka ta maida wayarta taci gaba da yi,hannun kujera aysha ta samu ta zauna idanunta kan film din da ake haskowa a tashar zee world hannayenta rungume a qirjinta tana jiran mommy ta gama wayar ta bata umarnin tafiya,sai data gama din sannan ta dubeta
"Na saka usama ya sanya komai a cikin mota,a motar asma'u zakuje saboda ta fita a tawa,na mata bayanin komai ki gaisheta idan kinje"amsa mata tayi ta miqe ta fice daga falon yayin data bar mommy na zama saman kujera tare da qwalawa daga cikin 'yan aikinta kira ta kawo mata drinks.
Hajiya laraba qawa ce ta qut da qut ta momy,saidai akwai banbancin halaye tsakaninsu,hajiya laraba macace mai kirki da mutunci qwarai da jan mutane a jiki,faran faran da rashin girman kai duk da arziqin da suke da shi,sanda ta isa da kayan ba qaramin murna ta nuna ba ta bubbuda tana cewa
"Kai ma sha Allah,wannan da gani aikin indo aisha ne ko?" Murmushi aysha tayi cikin jin kunya har fararen haqoranta na bayyana bata ce komai ba
"Sannunki da aiki,lallai hajiya sa'adatu na morar mai girki"
"Yauwa mama" ta amsa mata tana matsa yatsunta
"Gashi dukka su muslima tun shekaran jiya suka gudu gidan bikin suka barni a gidan saini kadai sai 'yan mazan,maza kuma kinsan ba zama suke ba,gidan babu dadi duk saini daya" ta fada sanda mai aikin mama ke aje mata kayan motsa baki,ruwa kawai ta zuba tasha tana sauraren maman data daga waya tana kiran yaronta,sai data gama wayar take dan jan ayshan da hira,bata da saurin sabo a wasu lokutan amma tayi qoqarin sakewa maman suna dan taba hira.
Sallamar matashin saurayin ce ta katse musu hirar da suke jefi jefi
"Banda abin ahmad kuma saika zauna,kasan amfani za'ayi da kayan,ka hanzarta don Allah ka miqa mata" ta fadi tana miqa masa muqullin mota bayan ta miqe ta nufi dakinta tana cewa
"Bari na baka wadan nan kudin ka kai mata,ni inajin sai wajen gobe zan samu shigowa qafar nan yau ta matsanta min" amsa mata yayi yana gyara zamanshi saman kujerar idanunsa kan aysha wadda ta gaidashi a sanyaye kamar yadda haka yanayinta yake,ya amsa mata yana tambayarta mommy,daga haka falon ya sake daukan shiru har mama ta fito ta sallameshi ya wuce.
Sam hanata tafiya maman tayi har sai data yi sallar isha'i ta kuma tilastata taci abinci,kyautar turare maman tayi mata da agogon hannu mai kyau kafimn su wuce,hannu biyu tasa ta karba tana mata godiya,hakanan aishatu ke burge maman saboda yanayin nutsuwarta da tarbiyyarta.
Suna gab da shiga unguwarsu wayarta ta soma ringing,da mamaki ta cirota daga jakarta tana duba mai kiran,saboda tasan bata da wani mai kiranta a irin wannan lokacin,bama wannan lokacin ba,da wuya ka zauna da ita kaji kira ya shigo wayarta,saboda bata da mai kiran nata bata da wanda ya damu da ita baya ga Aliya a cewarta,idan kaga kiran mommy kona asma'u cikin wayarta to qaruwarsu ce.
Ilai kuwa asma'un ke kiranta,tana shirin sallama saidai bata tsaya ta saurari sallamar ba bare ta amsa ta soma magana,da alamun bacin rai cikin muryarta
"Mommy tace min ta aikeki gidan mommy laraba,ki bar abinda kike ku sameni keda usama a meena event" qit ta kashe wayar daga haka,wayar aysha ta sauke daga kunnenta tana qoqarin maidawa cikin jakarta tace da usama
"Usama meena event center zamu je,kasan wajen?" Dariya ta bashi har ya dan murmusa cikin sautin murmushin nasa yace da ita
"Na sani mana aisha wanne dan kano ne baisan wajen ba....sai irinku kifin rijiya" itama murmusawar tayi,tana ganin meye hadinta da wajen me zata jeyi?,a yadda ma taji Aliya na fadin haduwar wajen tasan ba tsarar shigarta bane
"Amma me zamuyi a wajen?" Usama ya jeho mata tambayar
"Yaya asma'u tace muje,halan daukota zamuyi"
"Amma da motarta ta fita ai,me zamuyi a can"
"Ban sani ba nima usama" ta bashi amsa tana dan dafe kanta tare da maida kanta ga titi,ba ma'abociyar son doguwar magana bace sam,hakan yasa sau tari asma'u kan soketa da kalmar macijin sari ka noqe,taqi yarda har yau cewa a halittarta ne.
Ba wanda ya sake cewa komai har suka isa wajen taron,wajen adana motoci usama yayi parking sannan aysha ta soma kiciniyar kiran asma'u,jifa jifa tana bin wajen da kallo wanda yake da haske saidai ba tarwai ba,amma hakan bazai hanaka ganin yadda hadaddun maxa da mata ke kaikawo a wajen ba cikin ado da qawa.
Kusan sau biyar tana katsewa ba tare da asma'un ta dauka ba,sai ana shidan ta daga,shima kunnuwanta cike da kidan dake tashi daga cikin ainihim rufaffen dakin taron taje tsinto muryar asma'un
"Wai meye ne?" Abinda ta soma cewa kenan
"Muna wajen mun iso" tsaki ta doka
"Bana son qauyanci fa,daga zuwanku sai nabar abinda nake...ku jirani malama" daga haka kashe wayar,itama kashe tata wayar tayi sannan tace
"Ammm...usama tace muyi jiranta"
"To,bari na zaga nima nadan kama ruwa"
"Ba damuwa" ta furta tana bude data din wayarta,cikin qanqanin lokaci ta soma browsing tana duba abubuwa masu amfani dake da alaqa da karatunta.
Jira sukayi na tsahon awa biyu,har a sannan ba asma'u ba dalilinta
"Tayar motar nan kamar tayi faci aishatu,ko zaki fito na sauya wata kafin ta fito?"taji usama na fada saitin window din da take zaune
"Toh ba matsala"ta fadi tana maida wayarta jaka sannan ta bude murfin motar ta fito,idanunta ta sake sanyawa tana qarewa filin kallo,komawa tayi jikin motar ta jingina tana ci gaba da kallon wajen jifa jifa.
Cikin minti goma usama ya gama canza tayar yace ta koma ciki,amma sai tace ya barta anan saboda ta gaji da zaman cikin motar.
A gurguje yake takowa daga bangaren nasa zuwa bangaren anninsa,shigar baqaqen kaya yayi gaba daya har takalminsa hight top sai ratsin ja jifa jifa,agogon hannu yake daurawa hakan yasa sam bai lura da zeenart ba,qiris ya rage suyi gware,da sauri ya ja da baya yana ci gaba da daura agogonsa,yayin da zeenart ke qare masa kallo cike da sha'awa da burgewa,ya mata kyau sosai haka shigarshi ta burgeta matuqa
"ya khalipha badai fita zaka yi ba"murmushi ya saki kadan bayan ya dubeta yana ci gaba da gyara wuyan rigarsa
"Xan dan leqa dinner din wani abokin kasuwanci na"a shagwabe tana dan buga qafa tace
"Kai ya khalipha,amma ka sani already na hada maka dinner yana kan dining ko?"
"Dont mind,bazan jima ba zan dawo"
"Kayi alqawari?" Ta fada tana langabar da kai,murmushi ne ya qwace masa,yaran na bashi mamaki matuqa,wai sun mata baya ne?,ko sani ne basuyi ba saboda qanqantar shekaru?,ko sun sani takewa sukayi
"Nayi" kawai ya fada,binsa tayi suka jera har zuwa bangaren anni.
A parlour suka taddata kamar ko yaushe tana zaune saman kujera sanye da hijabi hannunta riqe da carbi,haka al'adarta take musamman da yake ba'a jima da gama sallar isha'i ba,amal ce zaune gefanta tana shan fruits,idanu suka hada ta sakar masa murmushi,bai iya disgi ba hakan ya sanya ya maida mata ya qarasa gefan anni ya zauna a qasan carfet kamar yadda al'adarsa take idan annin na sama bai zama a sama shima
"Ka fito khalipha"
"Eh anni na fito......ina su haidar ne?"murmushi annin ta saki tana dan tabe baki
"Nan yaci wanka ya fice,yace yaga alama saiya kawomin surukata har gida sannan zaka farka" murmushi ya saki shima yana shafa sumarsa cikin jin kunya,yasan jirwaye annin ke masa me kama da wanka,bai maida amsa ba yace
"Anni zan leqa wajen bikin mus'ab"
"Ikon Allah....lokacin har yayi kenan?"
"Eh wallahi...."
"To Allah ya sanya alkhairi,ka miqa masa saqon taya murnata"
"Zaiji in sha Allah...sai nadawo"
"Allah ya tsare hanya" amsawa yayi da amin sannan ya miqe zai fice,zeenart ce ta rufa masa baya,tsam amal ma ta miqe ta biyosu.
Gab da zasu isa jikin motocin ya jiyo muryar amal na tsaidashi,dakatawa yayi yana dubanta har ta qaraso,bata damu da zeenart dake wajen ba cikin shagwaba tace
"Yaya...amma nace ka kaini shopping kace baka da lokacin fita da dare..kuma...."
"Wannan uzuri ne daya kama dole...later ma fita ko" ya katsi qorafin data soma jerowa
"Yauwa yaya na na gode" ta fada cikin farincikin,tasan cikin ruwan sanyi ta rama abinda zeenart din tayi mata dazu na karbe girkin da ita tayi niyyar yiwa khaliphan.
Har motoci ukun da zasu fitan tare suka bar harabar gidan suna tsaye,sai da suka gama ficewa sannan zeenart taja tsaki tayi gaba zuwa cikin falon cikin gudu gudu sauri sauri,amal ta bita da harara sannan tabi bayanta suka shige ciki.
Ranta a bace ta hau step ta yiwa amarya sallama da niyyar sai gobe,don sam ba yanzu taso barin wajen ba,amma mommy ta katse mata hanzarinta ta kirata kan lallai ta biyo su aysha su dawo gida yanzu yanzu,saboda daddynsu ya dawo yana tambaya ta masa qaryar ta aikesu su duka gidan hajiya laraba.
Cikin takunshi dake nuna baiwar da Allah yayi masa ya hawo mazaunin ango da amaryan don ya shigo a makare,mus'ab din kuma yaqi karbar uzurinsa ya kafe lallai sai ya qaraso nan ya bada uzurinsa wajen amarya.
Sakkowa take a hankali saboda yanayin tsinin takalmin dake qafarta,dab da zasu gota juna idanunsa ya sauka a kanta,yanayin hade ranta abu na farko daya soma jan hankalinsa,tafiyar nutsuwa da adonta,da hanzari ya qarasa wajen ango suka gaisa sannan ya juya yace masa yana zuwa.
Ita kadai ke sakin tsaki jifa jifa saboda komawarta gida da bataso ba,yana biye da ita tare daci gaba da karantarta a haka har suka kusa isa parking space din dake wajen sannan ya qara hanzarinsa har ya cimmata,a bayanta ya tsaya sannan yayi mata sallama,ta dan tsorata hakan yasanya ta waiwayo tana dubanshi,da fari taso gaya masa magana ne saboda yadda ta tsorata,amma tashin farko sai ya mata wani irin kwarjini,kyan fuskarsa ya dakushe tsiwarta,saita sake ajiyar zuciya tana dubanshi tace
"Meye haka malam?,haka kawai ka tsorata mutane" murmushi ya saki cikin sassauta tsare gidansa da ragewa kwarjininsa kaifi
"Kiyi haquri ranki ya dade,banyi zaton zaki tsorata ba"
"Naji...lafiya?"kai ya girgiza
"ba lafiya ba" ido tadan fiddo waje
"Ba lafiya ba kamar yaya?"
"Idan ba zaki damu ba ko zamu matsa daga gefe?"
"Ba buqatar hakan don ni sauri nake,fadi matsalarka"
Cikin nutsuwa ya soma fadi mata sunanshi da abinda ke tafe da shi,kallo ta dinga qare masa tun sanda ya soma maganar har ya gama
"Kai din waye?" Ta furta tana son sanin waye shi din har zuciyarta,shafa kanshi yayi kamar wani mara gaskiya
"Ba kowa bane ni,hasalima qarqashin wani nake,shine ubangidana kuma shi na rako nan wajen" dariya ta saki cikin ranta tana jin haushi da takaici,tana ganin ya gama raina mata wayo,ya kuma fado da ajinta,ta yaya yaron wani zaice yana sonta?,maici a qarqashin wani?,me na sama yaci ballantana na qasa,toko gashin kanshi yake ci ai bata jin zai samu soyayyarta ta sauqi bare yaron wani,abu guda ne zai hanata ci masa mutunci,tsantsar kyau da kwarjinin da yayi mata,sai kawai taja siririn tsaki ta juya ta soma takawa a hankali da niyyar barin wajen
Cike da hanzari da zafin nama ya sake binta,daf da zasu isa inda su aysha ke jiranta ya sake shan gabanta,tsam tayi tana dubansa har ya gama maganarsa,tsiwa takeso ta masa amma ya mata kwarjini,yayi mata tako ina ya hadu,kai tsaye ma zata ce yafi hisham
Kyau kwarjini da cikar zati,namiji ne mai irin kyan da takeso,mai surar da takeso,saidai bai mallaki abinda zai bashi damar shiga jerin masoyanta ba,abu guda tak daya fada yasa taga sam bai dace tayi tarayya da shi ba,wato lafazin uban gidansa ya rako
"Kar ka sake bina pls,ka saurara min" lafazin da aysha ta iya jiyowa sun fito daga bakin asma'u kenan,tana iya hangoshi tar ta cikin hasken,a hankali ta janye idanunta daga kansu tana yunqurin komawa cikin motar ganin asma'un ta doso su tun kafin tazo itama ta sauke mata nata kason,tana matuqar mamakin yadda asma'un keda zarrar tsayawa gaban maza tana musu yadda taga dama ba tare da damuwa da shekaru ko darajar koma waye ba.
Garam ta rufe murfin motar ba tare data dubi usama ko aysha ba tace
"Muje" kai tsaye
Ita daya ta dinga mitar biyotan da akayi aysha na jinta bata ce komai ba,tana ganin kamar ya rage mata aji ne daya biyoya ma,kiran wayar hamid ita ta janye hankalinta har suka je gida suna waya,a cikin mota ita dai ta barta ta wuce ciki.
Kan dining ta samu daddy shi da mommy suna cin abincin dare,a nutse ta qarasa,tana shirin gaida daddy mommy tayi caraf cikin salon data saba amfani da shi koda yaushe tace
"Ina kuka tsaya tun la'asar sai yanxun?" Kanta a qasa tace
"Hajiya ce tace sai munci abinci zamu taho"
"Ina ita husnar?"
"Tana mota" ganin tambayoyinta sun qare yasa ta waiwaye bangaren daddyn ta gaidashi cike da ladabi da girmamawa,shima ya amsa mata cikin kulawa,tana shirin miqewa ta wuce asma'u ta shigo,a shagwabe take qarasowa zuwa wajen
"Ke ba zaki ci abinci ba?"mommy sa'adah ta fada ganin ayshan na niyyar wucewa,ga idanun daddy a wajen
"Na qoshi,naci wajen hajiya"har ta soma takawa daddy ya kira sunanta,sai duka hankalinsu ya koma kansu daddyn duk da magana suka soma yi a tsakaninsu,a ladabce ta dawo ta durqusa
"badai wata matsala ko?" Murmushi ta saki dan kadan,to wacce matsala ita din take da bakin cewa tana da ita?,a yanzu bata ganin wata matsala tattare da rayuwarta idan ta kwatanta da rayuwarta ta baya
"Eh daddy babu"
"Kin tabbatar?" Ya sake jaddadawa don har ga Allah yana qaunar yarinyar yana tausayin rayuwarta,sam bata da marsala tunda har yau duk abu irin na sa'adatu bata taba kawo masa qararta ko qorafi a kanta ba,duk da cewa bata taba yabonta ba,amma hakan ya alamta masa bata da wata matsala,yqsan halin matarsa sarai,da tana da damuwa yarinyar tofa duk sanda suka zauna hira ta dinga sakin qorafin akanta kenan,duk da ba zata fito kai tsaye ta kawo masa qararta ba,haka nan nutsuwarta ta daban ce
"Na tabbatar daddy" ta amsa masa muryarta can qasa idanunta na duban tiles din dake shimfide a qasan falon
"To Allah yayi albarka ya kuma yi jagora"
"Ameen daddy na gode,Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen" ya amsa cikin jin dadi,miqewa tayi bayan ya sallameta,asma'u na zabga mata harara a fakaice tana ayyana munafuka cikin zuciyarta,yayin da haushi da takaici ya tuqe mommy sa'adatu,saidai sam ba zaka ce haka ba don ko kan fuskarta bata nuna ba,sai abinci da take diba kadan kadan.
A gajiye take liqis,cikin kasala ta dinga warware lafayar jikinta sannan ta shiga bayan gida ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,mai ta shafa ta feshi jikinta da turare sannan ta zira rigar bacci doguwar mai taushi da kauri,bacci kawai take buqata tayi,saidai qarar wayarta ta dakatar da ita,ta qarasa ta cire wayar daga chargy tana duba mai kiran,asma'u ce,ta shafa ta kara a kunnenta
"Fito ki daukomin kayan da nace ki ajemin" ta fada da salon muryar data saba yi mata magana,aje wayar tayi ta zira hijabinta ta fice zuwa kitchen.
*mrs muhammad ce*👑
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(Home of expert and perfect writers)
10
A tsaye ta sameta cikin kitchen din riqe da cup tana shan yoghourt,fuskar nan a hade,fridge din ta bude ta ciro mata kayan,saidai bata ga dambun kazar ba
"Ina dambun?" Ta tambayeta tana duban kayan
"Ban sani ba nima cikin freezer din na ajjiye"
"Wacce iriyar banzar magana kike fada,banson iskancin banza waye zai dauka?" Ta fada a dan zafafe,da alama dai akwai wata a qasa,cikin sanyin muryarta kamar yadda yake a halittarta tace
"Wallahi ban sani ba anty asma'u,dana gama na saka a ciki mummy ta aikeni gidan mummy laraba", shigowar mummy cikin kitchen din shi ya katse muhawarar
" hayaniyar me nake ji?"ta tambayesu tana aje warmers din abincin da daddy ya gama ci
"Wannan yarinyar mummy nason ta fara rainani,sumumu kasau macijin sari ka noqe,na sata ta hadamin kaya amma tace wai bata ga dambun da nace ta yimin ba?"
"Banson tashin hankali da daren nan ki kira mana hankalin babanku,ta sake miki wani,wancan nayi baqi na basu" ta fadi tana ficewa a kitchen din,shiru tayi kafin ya kwashe kayan ta fice itama bayan ta aje mugun tsaki.
A qalla ta shafe kusan minti goma kafin itama ta soma takawa a hankali tana ficewa daga kitchen din,bata san me ya taba zuciyarta ba batasan tana hawaye ba saidata shafi fuskarta,tana goge hawayen tana addu'ar bacci da haka ta kwanta bayan taja bargonta zuwa kafadunta.
Ta jima a kwance tana nazarin rayuwa kafin ta tattara dukka lamuranta ta sake miqawa Allah.
Ya dan jima tsaye shida drivansa yana qarewa gidan kallo,haka kawai yaji zuciyarsa ta nutsu ta aminta da gidan,yana jin gamsuwa da nutsuwa har cikin zuciyarsa,yana son mace mai kamun kai da jan aji,yana ganin kamar akwai alamun hakan tattare da ita,yanayin arziqin gidansu yana ganin kaman bazai sanyata qyamatar mai qaramin qarfi ba,kamar zata amsheshi haka yakeji,amma hakan bazaizama dalilin da zai sanya ya kasa jarraba ta ba kamar sauran,a nutse ya yiwa drivern nasa umarnin su wuce.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe biyu na rana suke takowa zuwa cikin layin nasu daga bakin titi zuwa gidansu ita da asma'u dake qunquni kamar zata fashe,taci alwashin bata sake hawa motar,duk da ba tsufa ne yasata yin hakan ba,uban motar da take ci ne kawai da kuma halin tsiyar qarfen nasara,inda Allah ya taqaita saida sukazo kwanar gidan nasu ta kakare musu a nan,itakam aysha na gefanta,baki daya bata ga abun bacin rai ba,don dai yau kadai.
"Malam ka cikani,Allah bazan biya ba"
"Wallahi saika biya kaji na gaya maka,ba inda zan sakeka kaje" hayaniyar mutum biyu kenan data cika kunnensu gab da zasu qarasa qofar gidansu,hayaniyar na tashi ne daga wani dan case dake maqale da gidan maqocinsu dake kallon nasu gidan,case ne da mai gadin gidan ya bude yana saida katin waya da sauran 'yan qananun abubuwa da ba'a samu cikin unguwar sai sunje waje mai nisa saboda yanayin unguwar tasu,dukkansu hankalinsu yakai wajen,asma'u ta ganeshi tsaf,yayin da aysha taso ta shaida fuskar,da sauri asma'u ta dauke kanta,hakanan taji gabanta na faduwa,ta yaya akai yasan gidansu?,me yake a layinsu?,fatanta daya kada Allah yasa ya nuna ya santa,don ta fuskanci yana da wata zarra da rashin fargaba.
Saidai ko daya addu'arta bata ci ba,don kafin tayi qwararan taku guda goma ya samu isa gabansu,murmushi yake jifanta da shi wanda ya haddasa mata faduwar gaba,babu shakka ba qarya yana da kyau wanda ko gasa ya shiga idan baizo na daya ba zaiyi na biyu,saidai baida makamin da zai tayashi yaqin shiga inda yakeso
"Ranki ya dade....ashe nan ne gidanku?" Ya fadi yana qarewa gidan nasu kallo kamar da gaske yau dinne ya soma tozali da shi,itama gidan ta kalla kaman yau ta soma gani sannan ta maido dubanta gareshi,cikin tsiwa da tsaurin ido tace
"Nan ne,sai yaya?" Murmushi ya saki sannan yace
"Nayi farinciki sosai.....hakan ya nuna Allah yana sona" tana niyyar maida masa habu mai trader da suka tarar suna taqaddama ya qaraso yana sakw fadin
"Mallam ka sallameni ka biyani kudina zan koma bakin aikina"
"Karka damu yanzu za'a biyaka...." Sai ya dubi asma'u dake dubansu galala tana tabe baki
"Ranki ya dade taimaka ki ranta min wasu kudi mana 'yan kadan ba masu yawa ba" kallon banza tayi masa,wani bacin rai na tokare wuyanta,yanzu ita asma'u har tayi arahar da saurayi mai cin bashi wajen masu qananun akurkin shaguna zai tsaya kafada da kafada da ita yana magana?,baqinciki yasa ta kasa magana illa dogon tsaki da taja ta wuce zuwa bakin wangalelen get din gidansu kamar zata saki kuka,koma meye motarsu ce ta jawo mata,da bai isa ya ganta ba bare ya tsaya da ita.
Binta sukayi da kallo duk su ukun har ta shige cikin gidan kafin kowanne ya maido idanunsa inda suke,idanu suka hada shida ayshan,sai kuma ta danyi turus cikin rashin sabo ganinta gaban maza har biyu abinda bata saba da shi ba,sai a sannan ta soma tuhumar kanta name ta tsaya yi a wajen,a hankali ta ciro jakar ta dake rataye a kafadarta ta bude tana fatan samun wani abu a ciki,cikin sanyin muryarta ta daga idanunta ta dubi habu mai trader
"Nawa ne kudin naka?"
"Eh...ammm....dari biyar.....dari biyar ce" dubu daya ta ciro ta miqa masa
"Gashi bani da canji....ka bashi canjin dari biyar din ya riqea hannunshi" tana gama fadi ta maida jakarta kafadarta ta nufi cikin gidan,tana ganin rashin kyautatawarta qarara,tana gani tunda har ya karya billensa ya tambaya buqata gareshi,bai kamata kana da shi ka hana wanda baida shi ba,batasan dalilinsa na tambayarta ba.
Tun kan ta isa parlour din take jiyo banbamin fadan asma'u,tsaye ta sameta gaban mommy sa'adah da alamu labari take bata da kuma nuna bacin ranta
"Sannu da gida mummy..." Aysha ta furta tana dan rusunawa cikin girmamawa
"Yauwa.....ina ke kuma kika tsaya?" Ta tambayeta tana dubanta
"Ta tsaya tana kallonmu salon ta sake samun damar rainani.....munafuka....waya sani ma ko kin sanshi....koma kece kika turoshi?" Bata ce komai ba ta juya ta nufi bangaren da dakinta yake,tana iya jiyo muryar asma'un tana ci gaba da cewa
"Banza baqauya kawai....Allah mommy cikin satin nan indai daddy bai sauya min mota ba Allah na bar zuwa school,ai ba girma na bane a ganni mota tana bani matsala...haba don Allah mommy...sau biyu fa tana min haka" kai ta kada kawai,sau tari tana mamakin halayya irin ta asma'un,itakam har yau cikin duniyar nan bata ga wani abu da zai burgeta ya shiga zuciyarta da yawa har irin haka ba,me ta nema?,meta rasa?,amma ko yaushe qari take nema,ko yaushe so take taga ta zama perfect,ko yaushe so take taga komai nata yafi na kowa,ko yaushe yadda ta tsara ma kanta haka takeso taga ya kasance,tafi dukkan sauran 'yan uwanta mata uku buri da kai kanta can wata uwa duniya,duniyar da ma'abota buri da hangen duniya da tsaho suke yunqurin isa.
Dukka tana wannan tunanin ne tana cire kayan jikinta don wanka take da buqatar yi saboda tsananin ranar da ake kodawa,da wannan tunanin ta shiga bandaki ta sakarwa kanta ruwan shower mai sanyi ba tare data sirka da ruwan dumi ba,koda sanyi ake indai ba tsananta yayi ba tana iya wanka abinta da ruwa mai sanyi,saboda sabo da tayi da wata iriyar rayuwar da tayi can a baya.
Dari biyar din habu mai gadi ya miqa masa yana cikin rusunawa tamkar bashi ya gama cin kwalarsa dazu ba yana cewa
"Gashi yallabai...." Daga kai khalipha yayi ya dubi kudin sannan hannayensa zube cikin aljihun wandon jeans din jikinsa 'yan gwanjo wanda ya ara wajen habun ya dora kan t.shirt dinsa da ainihin wandon jikinsa
"Bakai aikin da kyau ba habu" cikin fargabar ko kada yadda ya ringa cacimarsa ne ya bata masa rai yace
"Tuba nake yallabai...." Murmushi khalipha yayi ya amshi dubu dayan da yake miqa masa yana cewa
"Nan gaba kayi da gaske,ka daina tuna waye ni,kayi kaman ka kama mutumin da yaci bashinka shekara guda ya tsere yau ka kamashi" dariya ya bawa habun har sai daya dara,yana mamakin sauqin kai irin na khalipha,dama akwai masu kudin dake da sauqin kai haka,amma mamakinsa meye dalilin da yasa khaliphan ya maida kansa talaka a idanuwansu?.
Isowar wani matashi cikin shigar coat baqaqe dauke da briefcase wajen ya sanya habu tsagaita dariyar da yake,briefcase din mutumin ya zuge ya miqowa khalipha,dubu dayan daya karba ya jefa cikin sabbain bandiran kudin dake cikin jakar,sannan ya zaro bandir din 'yan ashirin ashirin ya miqawa habu,cikin rawar jiki da murna yace
"Duka wannan nawa ne yallabai?" Kai ya gyada masa sannan yace
"Next term zanci bashin credit....karka manta"
"Allah ya kaimu yallabai...yaushe zakazo"
"Ba lokaci....saika ganni kawai" ya fada yana amsar wayoyinsa daga hannun matashin tare da duba miscal din daya tara zaman da yayi wajen habun,sannan ya soma takawa a hankali zuwa wajen motocinsa dake can bakin layin suna jiransu.
Mai kawai ta shafa ta zura doguwar rigar atamfa a jikinta,bacci takeji sosai saboda jiya bata samu tayi isashshen bacci ba,tayi karatu sosai hakan ya hanata bacci da wuri,kan gadonta ta koma ta janyo wayarta ta soma lalubar lambar aliya wadda bata jin dadi bata samu ta shigo ba,ringing uku aliyar ta daga tana fadin
"Yanzu nake zancanki cikin raina" murmushi ta saki mai dan sauti,tana jin dadin yadda aliyar ke nuna mata qauna
"Nima kina raina,lactures ne yau sunyi zafi da yawa aliya,kaina har ciwo ciwo yake wallahi" ta qarashe maganar da sanyin muryarta,dariya aliya tayi
"Tofa....alhuda huda yau da kanta take fadin haka?,lallai yau kun gasu" 'yar dariya itama tayi
"Eh lallai jiki yayi kyau tunda har kike da bakin tsokanata....to Allah ya qara lafiya"
"Amin sashin(haka take kiranta wasu lokutan),naso na shigo makarantar yauma,mama ce tace na bari na qara jin dama zuwa jibi da muke da lacture"
"Allah sarki mama...ki gaidamin ita don Allah"
"Keee....wai me kike nufi?...banfa dauke miki dubiya ba" dariya ce ta qwacewa aysha ba tare data shirya ba
"To kuma me kika ji nace?"
"Baki ce ba amma i know you in and and out eesha....bakyason zuwa gidanmu bakison zuwa gidan kowa....bansan me yasa ba..ko kina tantamar qaunar da nake miki" tabbas ba qarya aliya take ba,hakanan take jin kaman bata dace data rabi kowa ba,bata kai matsayin hada alaqa da kowa ba tunda har uwarta mahaifiya ma bata da buqatarta
"Kiyi haquri sashin...gobe zan shigo in sha Allahu"zaro ido aliya tayi kaman tana gabanta cikin mamaki da doki
"What...da gaske kike?"
"Na taba miki qarya?" Ta amsa mata cikin dariya dariya
"Heee....Allah ya nuna mana gobe....breaking news yau a kunnen mama...kinga bari naje na soma shiri tun yau...sai anjima" ta fadi cikin zumudi gami da katse wayar tabar aysha da dariya,tasan dole aliya taji dadi saboda yadda take qaunar ayshan,bugu da qari tunda suke zuwanta gidansu daya sanda mamanta bata da lafiya wannan shine na biyun.
Wayarta ce ta sake ruri a karo na biyu,sake jawo wayar tayi tana tsammanin aliya ce ta sake kira,idanunta ta zaro zuciyarta na bugawa ganin sunan wadda ke yawo saman screen din wayarta,a zabure ta miqe ta zauna sosai saman gado bugun zuciyarta na qaruwa,UMMI NA sunan data yi serving number mahaifiyarta dashi shike yawo saman wayar,tunda take karo na farko da lambar wayar ummin ta soma yawo akan wayarta ba tare da ita tayi gangancin kiranta ba,cikin zumudi farinciki cakude da wani irin tsoro ta amsa kiran tana mai cike da fatan ummin tata ce da gaske.
Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke sanda tajiyo muryar Basma
"Anty indo...basma ce" ta fada cikin zumudi
"Wai...yau kin tuna ni basma" ta fada tana jin dadi cikin ranta,ko banza yarinyar na sonta cikin 'yanuwanta
"Anty bani da waya shi yasa bana kiranki.....yanzu ma ummi na wanka na dauka bata sani ba"
"Ina ummi basma...tana tunawa da ni?...tana zancena?...." Ta fada cikin karyayyiyar murya
"Ummi bata son ana........."
"Basmah!" Aysha ta jiyo murya ummin na kiran sunan basman cikin tsawa,da alamu ma kusa da ita take
"Uban wa kike kira?"ta sake tambayar yarinyar cikin hargagi
"Kiyi haq....haquri um...mi..." Abinda aysha ta jiyo kenan wayar ta katse,sauke wayar itama tayi daga kunnenta cikin fargaba,muryar mahaifiyarta Kawai data jiyo da fadanta ya sanya jikinta yin laushi tare da tsoro tamkar tana gabanta,zuciyarta ta karye sai hawaye ya soma sintiri saman kuncinta
"Ya Allah" ta furta a sanyaye tana kwantar da kanta saman pillow,fatanta daya Allah yasa kada ta yiwa yarinyar irin mugun dukan data saba,bata taba mance yadda dukan ummin nasu yake,bata mancewa da irin fushinta,bata manta yanayin hukuncinta,gefe daya zuciyarta na saqe saqe kala kala irin wanda ta saba,tasha qaryata mutane da kanta cewa ummin mahaifiyarta ce,saidai an sha gaya mata,kowa ma hakan yake gaya mata itace mahaifiyarta sau shurin masaki,ita ta tsugunna ta haifeta,saidai garin yaya?,me yasa?me ya faru?me tayi mata?,Allah masani har yau bata samu wannan amsa tata ba,ta dade tana kuka saman gadon ita daya har baccin data kwanta dominsa yazo ya sureta
*mrs muhammad ce*👑
0 comments:
Post a Comment