*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
RIJF Mama A'i, ke da kika tafi ba ki yi sauri ba, mu da mika rage ba mu yi nawa ba. Allah kasa mutuwa ta zama hutu gareki Allah ya miki rahama ya gafarta miki kurakuranki. I will never forget you. Allah kayi mana kyakkyawan ƙarshe.
1⃣2⃣
Na kai hannu na karɓi cati na duba, sunanta ne da kuma hotonta a jikin catin hakan ya tabbatar min da cewar lallai ƴar jaridar ƙwarai ce. Na mayar mata da katinta.
“Ba mu san komai a kai ba, waya faɗa miki nan gurin kuma?”
“Jama'a ne suka kwatanta min, kuma na tabbatar min da cewar ƴan sanda suka duki margayin har ya mutu”
Na nuna mata ƙofar fita raina a ɓace.
“Fita ki bar mana gida, mutanen da suka labarta miki abunda ya faru ki je can su ƙarasa miki, mu bamu san komai ba”
“Haba Baiwar Allah...”
“Ki fita Wallahi ko na sa taɓarya na fasa miki kai yanzu”
Da gudu ta juya ta fice daga gidan. Ni kuma na cigaba da aikina zuciya na zafi har na gama gyara komai, ciki na shiga na samu Inna har lokacin tana bachi Hijabina na saka na ɗauki kuɗin da suke ƙarƙashin filo na fita neman mai ruwa.
Karo na ci da Dpo dake tsaye jikin motarsa yana kallon ƙofar gidanmu, ban gama tabbatar da shi ɗin ne ko a'a ba saboda yau a cikin kayan gida yake.
“Assalamu Alaikum Malama”
A maimakon na amsa masa sai kawai na watsa masa wata muguwar harara.
“Ni ba gurinki na zo ba, matar gidan na ke son magana da ita”
“Bachi ta ke”
“Ki taimaka ki tashe ta kuma ki nema minlH izinin shiga cikin gidan”
“Saboda?”
Ya gyara tsayuwarsa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa.
“Na ga dai ke ba ƴar jarida ba ce, be kamata ki tsare ni kina min irin waɗannan tambayoyin ba, beside ni ba gurinki na zo ba gurin Inna na zo”
“Gida mallakinmu, mahaifiya bachi take baƙincikin kashe mahaifinmu da ka yi take ragewa saboda hawan jini”
Ban tsaya jiran abunda zai ce ba, na cigaba ta tafiyata. Sai ya zagayo ta gaban motarsa ya sha gabana, cikin ɗaga murya ya fara magana.
“Miyasa kuke rayawa zuciyarku cewa ni na kashe mahaifinki? Mi mahaifinki ya yi min da zan kasheshi? Idan na kashe shi wace riba zan ci?”
Nima cikin zafin rai na zaburo masa.
“Saboda zalincin ƴan sanda, yayarka ta laƙaba masa sata bayan kuma be sata ba, kuka yi ta dukansa har sai da kuka kasheshi akan kawai sai ya amsa laifinsa, wannan ba halinku ba ne? Saboda yayarka tana taƙamar kai dpo ne yasa kuka wulaƙanta mana mahaifi cika tozarta shi sannan kuka ɗauki gawa kuka kawo mana, yanzu kuma kana raina mana hankali har kana wasa da hankalinmu”
Ya matso kusa da ni ya nuna ni da yatsa yana magana cikin jin zafin kalaman da na yi masa, har haƙoransa na ƙasa na haɗuwa da na sama yana cizonsu tare da zaro min ido.
“Karki sake saka bakinki a akan aikina, karki sake yin furucin akan abunda kika jahilta, i hate nonsense, na zo nan ne dan na faɗa muku karku kuskura bada bayanin mutuwar mahaifinku ga ƴan jarida”
Na yi baya-baya ina hawaye, tare da murmushin da ya fi kuka ciwo.
“Kamin ta zo nan ashe sai da ta bi ta gurinka, ka yi nasara ban faɗa mata komai ba, amman yanzu kan ni zan tara ƴan jarida da kaina na labarta musu irin zaluncin da kuka mana, wato so kuka a rufa muku asiri kar kowa ya ji ko? Ta yadda muma zaku samu damar ɓatar da mu, Wallahi Allah ba zai barku ba azzalumai macuta-”
Ya ƙara matsowa kusa da ni har sai da na matsa baya.
“Ki tara ƴan jarida, ki faɗa muku ƴan sanda sun kama mahaifinki sun masa duka har ya mutu, za su tambaye ki dalilin hakan, kuma ki faɗa muku komai karki ɓoye, ni da ke za a ga waye zai ji kunya, idan ba ki yi haka ba to baki haifu ba!”
Yana kaiwa nan ya haɗa hannunsa na dama da na hagu ta taɓa saitin fuskata, har sai da na rufe ido. Sannan ya buɗe motarsa ƙirar 406 ya shiga ya fisgeta kamar zai tashi sama, ko da na ɓuɗe idona ƙurar motar kawai na gani hawaye ya sauko daga idona, lallai wannan shi ne a dakika a hana kuka, kuma a mareka a ƙwace maka jaka!
Kasa zuwa kiran mai ruwan na yi saboda kuka da ya ci ƙarfina, na koma cikin gida da sauri. Bana son na tashi Inna balle har ta ga hawayena hakan yasa na shige ɗakinmu na kwanta saman tabarma, na ci kuka na sai da na ƙoshi sannan bachi ya yi gaba da ni.
Motsin shigowar su Habiba ne ya tasheni daga dogon banchin da ya ɗaukeni, babu komai a mafarkina sai wacan tashin hankalin da ya faru, Baba ne kawai na ke ta gani sai kuma irin zamantewar da muka yi a gidan kamin rasuwarsa.
Ko da na fito na samu Inna ta farka har suna fira da Habiba ma da ke cire safa.
“Nawwara kin tashi?”
Inna ta tambaya tana kallona, sai na zauna bakin ƙofar ina amsa mata.
“Eh ashe rana ta yi”
“Tun ɗazu su Noor suka dawo na ce kar ya tasheki kin gaji da yawa, ƙara ki samu bachi ki ɗan huta”
Kallo ɗaya Habiba ta yi min ta ɗauke kai, kamar ba ta ganni ba, hakan ya karatar da ni da akwai wani abu a ƙasa, sai dai ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauki bula na shiga banɗaki, bayan na fito na yi alwala na shiga ɗakinmu dan Sallah.
A ciki na sameta tana ɗaura zane, naje kusa da ita na tsaya.
“Habiba kamar akwai abunda ya ke damunki?”
Ta ɗaga kai ta kalleni a maimakon ta yi magana sai ta kawar da kai ta soma magana.
“Nawwara ɗazu da zanje makaranta na haɗu da Mustapha, na tsayarda shi na bashi haƙuri akan abunda kika masa, sai yake tambayata ke yayata na ce eh, shine ya ce wai tun da yake a rayuwarshi wata mace bata taɓa ɗaga hannu taareshi ba ko da uwarsa ce sai ke, akan me zaki mareshi, bayan da ke yake magana ba, kawai ya buga motarsa ya yi tafiyarsa. Nawwara miyasa kika mareshi? Zaki ƙara ja mana matsala”
“Shiyasa kike jin haushi na? Babu abunda zai faru Habiba, kuma bari kiji na faɗa miki ko da Mustapha zai yanka ni ya dafa namana ya soma ya ci, ba zan bashi haƙuri ba, ke ma kuma kinyi kuskure da kika tunkare shi kika ba shi haƙuri wannan ba halinki ba ne Habiba”
“To ya kike son na yi? Bamu da wani gata sai na Allah mutane kamar jiranmu suke su yi mana abu, yanzu idan wani abu ya sake samun family mu ban san ya zan yi ba, Allah kasa ni ce zan fara bin Baba na gaji da wannan rayuwar”
Ta fashe da kuka. Ni kuma na riƙeta muka zauna tare ina rarrashinta.
“Babu abunda zai sake faruwa inshallahu, na miki alƙawari, share hawayenki kar Inna ta ji”
Ta ɗaga min kai tana share hawayen.
Haka muka zauna cikin jiran tsamanin abunda zai same ni daga Mustapha domin na san ba zai bar ni ba, Habiba ma kullum cikin tunanin wannan abun take, bata ƙaunar ko waje na leƙa saboda gani take kamar zan iya haɗuwa da shi ya yi min wani abu. Wasa-wasa muka kwashe sati uku babu abunda ya faru sai dai tunanin abun zai faru ya hanani sukuni ni da Habiba, a cikin satin ne su Murja da Hajiya Umaima da Hasana suka zo min gaisuwa tun ɗaga Kebbi. Wato Yayar tsohon mijina da kuma ƙannensa, mahaifiyarsa kuma ta yi min aike ni da Noor. Ba su kwana ba ranar da suka zo ranar suka koma bayan mun yi ma Noor tsaraɓar kayan maƙulashe da kuma tufafi, Inna kuma suka kawo mata atamfa da buhun kishinka ƙarami.
Ranar da suka kwana biyu da tafiya ina zaune tsakar gida misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe wayata ta yi ƙara alamar saƙo, ban kulata ba dan na daina ɗaukin aikin a yanzu tunani ba zan samu ba, tun da kullum ina sa ran ganin saƙon kamfanin amman sai na samu saƙon mtn. Sai da na gaji da kwancin da nake na tashi zaune ya miƙa hannu na ɗauki wayar da ke kusa da ni ina dubawa. Ina ganin sunan Kamfanin One-On-One jikina ya fara rawa, cikin zumuɗi na buɗe saƙon Congratulations na ga an rubuta a sama.ban iya tsayawa karanta sauran ba na buga tsalle ina ihun daɗi.
WHO IS READY FOR THE NEXT CHAPTER?
I can't wait to see Nawwara in One-On-One limitless company. 😍
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣1⃣
Tun da na baro kamfanin sai komai na titi ya riƙa burgeni, idanuwana har yanzu kallon komai suke kamar kamfanin wata ƙila saboda labarin da ke ƙumshe a bakina ina son na labarta musu Habiba da Inna yadda gurin ya ke da kuma aikin shi kansa.
Tunawa da zancen Bilal ya sani dariya tare da furta sunansa a fili.
“Bilal kenan wai zan sha fama da kishi”
Ajiya zuciya na sauke ina tuna irin kallon da Mutune yake min ɗazu, lallai da akwai abunda Bilal ya faɗa masa akaina.
“Sauke ni a nan”
Na faɗa ganin Mai Napep ɗin yana ƙoƙari wucewa ta har cikin unguwarmu, ba kasafai na ke son napep ko achaɓa ya sauke ni ƙofar gida ba.
“Ba ni canjin”
Ya buɗe akwatinsa na kuɗi dake cikin napep ɗin ya ɗauko ɗari uku ya miƙa min, ni ko na ƙi karɓa.
“Haba Malam ya zaka ɗauko ni daga Koko road ka kawo nan kawo nan arƙila kuma ka ce zaka cire har ɗari biyu”
“Haba Hajiya kuɗin nan fa Mai gidane ya bada su ba ke ba, miyasa ku mata kuke son tauye mu ne wai”
Hannu ya kai ya ɗauko naira hansin ya miƙa min, ina ƙoƙarin karɓa na ji takun mutun a bayana yana katsawa mai napep ɗin tsawa.
“Kai wane irin mahaukaci ne zaka kawo mashin ɗinka a nan ka tarewa mutane hanya nonsense mtssssss”
Juyowar da zan yi sai idanuwana suka yi arba da Mustapha, mutun na biyu da na tsana a duniya, ba da ni yake maganar ba amman sai na ji kamar da ni yake saboda tsanar da na yi masa da kuma sanin yadda baya ɗaukar kowa da mutuncin a unguwarmu.
Tassss na wanke masa fuska da mari sannan na katsa mashi tsawa kamar wata uwarshi.
“Haka kuke ba ku ganin kowa da mutuncin, kowa a gurinku wulaƙantaccene, uban kowa baka ganin mutuncinsa a unguwarnan, sha-sha-sha marar tarbiya”
Mamaki da al'ajab ya kafe shi a gurin ya kasa ko da motsa idonsa balle ya yi wani motsi. Ni ko a zuciyata tsoro fal marata har ta cika da fitsari, amman a zahiri kallonshi na ke kamar yadda shi ma yake kallona sam ba zaka kalli fuskata ka gano akwai alamar tsoro a tare da ni ba.
Matsowa ya yi kusa da ni ya ɗaga yatsansa ya nuna kamar zai yi magana sai kuma ya cige bakinsa ya yi ƙwafa ya juya koma cikin motarsa, ribas ya yi ya koma inda ya fito da alama ya fasa shiga unguwar ma.
Sai a lokacin na samu sa'idar sauke ajiyar zuciya na juyo gurin mai Napep ɗin na karɓi hansin ɗin da yake miƙa min.
“Kai amman ke wannan ƴar bala'i ce, Allah ya raba mu lafiya”
Ba shi kaɗai ba ko mutanen da ke kusa da mu sun yi mamakin yadda na wanke mutun kamar Mustapha da mari, ni ba mafaɗaciya ba, kuma kowa yasan halin Mustapha a unguwarmu, ni kaina sai a yanzu na ke jin kamar ba ni ce na mareshi ba, wata ƙila kuma saboda na tsane shi ne shiyasa har idona ya rufe haka.
Sai dai mamakina yadda ya ƙyale ni be rama ba, yaron da harararsa ma baka isa ka yi ba saboda yana taƙama ubansa wani ne a cikin garin sokoto. Da wannan tunanin da kuma mamakin dalilin ƙyaleni da ya yi na iso gida, duk wani ɗuki da na ke na labartawa su Inna gurin aikin sai ya kau saboda wannan abun da ya faru tsakanina da Mustapha ya tsaya min a rai.
Ko da na shiga na samu Habiba tana da fa shimkafa da wake, Sakina na daka barkono (Yaji) Inna kuma na ɗaki kamar kullum.
“Har kin dawo ashe ba a daɗewa”
Cewar Habiba tana ƙara tura itacen murhu.
“Eh kin san da yake ba aikin ba ne, takardun ne kawai za a kai”
“Allah ya baki sa'a ya sa su ɗauke ki”
“Amman Babban Kamfanine Habiba, ba lallai ne su ɗauke ni aiki ba”
“Zan riƙa tufa musu fatiha a tsakar dare”
Na yi murmushi, kana na doshi ɗakinmu dan cire mayafina. Bayan na fito na doshi ɗakin Inna, ita na fara labartawa yadda kamfanin yake kamin Habiba ta shigo mana da abinci mu soma ci gaba ɗayanmu, ko lokacin da Baba na dai baya ƙwanar ya ga mun raba abinci daga manyan mu har ƙanana, sai dai kowa ya wanke hannunsa a ci a guri ɗaya, yana yawan faɗa mana cin abinci tare yana saka zumuncin da nishaɗi da kuma son juna, kuma ta nan zaka iya karantar halin mutun da lurar shi irin cin abincin da ya dace ya yi. Hakan yasa suka muka saba bama iya raba abinci inda wanda za a ci ne, ko da ɗayan mu baya nan sai mun jira ya zo ko da kuwa Jamila ce ita da ta kasance ƙaramarmu, balle kuma Noor da ko ina muka je baya cin abinci sai da ni matuƙar ina gurin.
Na bijiro musu da zancen marin da na yi ma Mustapha, a take hankali Inna da Habiba ya tashi har ma da Sakina
“Ina ruwanki Nawwara ai ba da ke yake ba, kuma ko da ke yake ai kya shafa kanki lafiya ki bashi haƙuri, yanzu wannan abun da ya faru da mahaifinku be isheki ishara ba? So kike ki ƙara jawo min wani?”
Cewar Inna. Habiba kuma ta ɗora da cewar
“Da ma ba ki mareshi ba Nawwara, kar ya ce kuma zai miki wani abun, kin san halinsa idan ma ya ƙyale iyayensa ba za su ƙyale ba”
Ganin yadda hankalin Inna ya tashi ƴasa ni yin ƙarya.
“Ke wasa na ke daman kawai ina son naga yadda zaku yi ne, ban mare shi ba kuma da ya zo yana faɗa da mai Napep ɗin ma na bashi haƙuri”
“Da Gaske?”
Na gyaɗawa Inna kai ina dariya saboda ta yarda. Sai dai na lura da Habiba kamar bata yarda da ni ba, har muka gama cin abincin ban ga yanayin Inna ya dawo dai-dai ba.
Bayan sallah la'asar Jidda ta shigo gidanmu, a lokacin ina zaune waje ni da Habiba Inna kuma tana ɗaki, Sakina da Noor da Jamila suna islamiya. Kusa da ni ta zauna ina kallin bakinta na san da akwai magana, sai dai tana tsoron furtawa ganin Habiba na kusa da ni. Murmushi na yi na ce
“Saki jikinki Jidda faɗa min ko minene ai Habiba kamar ni ce, dukan abunda kika sani nawa to Habiba ta rigaki saninsa, abunda duk na ke iya faɗa miki to Habiba ce ta fi cancanta na fara faɗawa, ni da ita abu ɗaya ne bama ɓoyewa juna abu”
Sai ta yi ƴar dariya.
“To ai ban sani ba ko gidan ba su ji ba ne”
“Minene?”
“Cewa aka yi wai kin mari Mustapha”
Habiba ta yi min wani kallo tana jiran ta ji abunda zai fito bakina.
“Ba wai ba ne na mare shi ɗin ɗazu”
Habiba ta riƙe baki
“Ashe da gaske ne”
“Na ɓoye ne saboda na ga kamar ran Inna ya ɓace”
Jidda ta kama hannuna.
“Ke ko miya kaiki? Miya haɗa ku?”
Shiru na yi ina tunanin irin amsar da zan bawa Jidda, domin bata san shine mutumen da ya yaga rigar mutuncin Habiba ba, a lokacin da abun ya faru ban labarta mata ko wanene ba kawai dai na faɗa mata cewar Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin.
“Ba komai kawai wai dan Mai Napep ya tsaya a bakin hanya shine ya zo yana mana rashin mutunci, ni kuma na mare shi”
“Aka ce mari har uku wai, ai ƙara da kuka mareshi basa ganin mutuncin kowa a unguwar nan”
Na zaro ido
“Ɗaya ne kaji mutane da canja magana kuma, wai yanzu zancen nan har ya kai miki”
“Wallahi ina zaune gida aka kawo min shi, wai ƙawata ta mari Mustapha, ai ko ni kika mara sai zancen ya zagaye unguwa balle kuma Mustapha guda”
Dariya na yi, domin a yanzu duk wani tsoro da ke raina na ɗazu ya gushe. Labarin kamfanin na ɗaukowa Jidda ina ta faɗa mata yadda abubuwan suka, ita kanta da bata je gurin ba sai da abubuwan suka burgeta saboda yadda na tsaya na tsara mata komai kamar anyi a gabanta.
Har muka ci firarmu da Jidda muka suɗe Habiba bata saka bakiba, Jidda kuma bata bar gidanmu ba sai da ta yi sallah magariba sannan na rakata sannan na dawo.
Shikafar ɗazun na ɗauko na ɗumana na zuba mana muka zauna gaba ɗayan mu muka ci, ban da Inna da daman nata daban ake zuba mata balle kuma yau da ta ce ba zata ci ba. Muna cikin cin abincin nokiyar da ke gefena ta yi ringing, abun ka da wanda ya daɗe ba shi da waya tun da na saka layin ba a taɓa kirana da shi ba.
Number Waje ma'ana ba nunber nigeriya ba ce, cikin rawar jikina na ɗauka dan nasan mace ɗaya zata iya kira na da wannan layin wato Salima
“Hello Ƙawata”
Sai ta amsa min daga ɗayan ɓangaren.
“Ƴar'uwata, kin jefar da ni kullum ina kiranki bata shiga”
“Wallahi bana da waya ne a yanzu, wannan ma ara min aka yi na saka layina”
“Allah sarki ya gida? Ina Baba da Inna?”
“Sai dai Inna tana nan lafiya ƙalau, Baba kan Allah ya yi ikonshi”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yaushe? Miya same shi”
“Rashin lafiya kwana biyu”
Na yi ƙarya saboda ba kowa zaka iya faɗawa dalilin mutuwar Baba ya gasgata cewar Baba be yi satar ba, duba da yadda muke fama da rashi. Bayan ta yi min gaisuwa ta yi ma Inna sannan ta yi ma Habiba, Sakina da Jamila sannan suka maido min da wayar.
“Kin rasa RAI BIYU masu muhimmanci Nawwara mutuwa mai ɗaci , kin rasa Abban Noor yanzu kuma Babanki Allah ya baki ikon ɗaukar wannan lamarin”
“Amin Salima na gode”
“Inshallah idan na dawo Nigeria zan zo har nan na yi miki gaisuwa”
“To Allah ya yarda”
Daga haka muka yi sallama, na amsa mata da to ne kawai ba dan na gamsu zata zo ɗin ba, duk tsawon zaman da muka yi da ita bata taɓa tako ƙafarta sokoto ba ai ba zata taɓa zuwa ba.
Da gudu Noor ya zo gurin yana ƙoƙarin karɓar wayar.
“Momy waya baki waya? Momy kira min Gwaggota Murja kin ji”
Haka yake idonsa idon ganin waya, baya da magana sai ta a kira masa Murja wato Ƙanwar mijina wacce ya shaƙu da ita sosai.
“An ya ma sun ji maganar rasuwar baban ku kuwa?”
Maganar Inna tasa na ɗago kai na kalleta.
“Ina zasu ji tun da ba a nan suke ba kuma babu waya a lokacin”
“Ya kamata dai kan ki faɗa mata”
“Bari na mata please Call me dan ba ni da kati gaskiya”
A take na aikama mata please Call, ko minti biyu ba a ƙara ba sai gata ta kirani, mun gaisa sosai sannan na bata Inna, ita ta labarta mata cewar Baban mu ya rasu, ta shiga ɗimuwa da kiɗima sosai, har da kukanta kamar Babanta ne ya rasu.
Bayan ta yi min gaisuwa ta faɗa min zata shaedawa sauran ƴan'uwan margayi Sadiq zasu zo har sokoto su yi min gaisuwa, duk ƙoƙarin dakatar da ita da na yi akan zuwan sai ta nuna min sam ba zai yiyu sai ta zo, ai daga sokoto zuwa Kebbi ba wani nisa ba ne. Sun daɗe suna waya da Noor sannan bashi yaranta suka yi magana sai ta kashe.
Takwas da rabi wayar Bilal ta shigo, ina ɗauka ya shaida min yana waje. Sai da na faɗawa Inna sannan na tashi na saka Hijab ɗina na fita. Jikingine da ƙofar gida na same shi, ina masa sallama ya amsa fuskarsa da murmushi har wani ƙyali take.
“Nawancy”
“Bilal”
Sai yasa dariya.
“Ina jin daɗin ki kira sunana yana mugun daɗi a bakinki”
Na yi murmushi ina rausayar da kai. Bayan mun gaisa ya bijiro min da fira cikin har da zancen marin da na yi Mustapha, sai na nuna masa ya yi min ba dai-dai ba ne shiyasa. Sai tara da rabi muka yi sallama.
WASHE GARI....
Yau kan ba laifi dukanmu mun tashi cikin walwala, Sakina da Jamila tuni suka wuce makaranta, Habiba ma shirin makarantar ta ke, ni kuma ina gyaran gida, Inna kuma na ɗaki tana bachin safe.
“Nawwara canjin kuɗin Koko yana nan ƙarƙashin fillo, Inna ta ce a siye ruwa”
Cewar Habiba tana tsaye riƙe da littafan makarantarta.
“Yau Fanfan ba zai zo ba ne hala?”
“Yau kwana biyu be zo ba, ruwan da muke amfani da su sun ƙare, ƙara a siya da wuri idan ma ya zo kin ga kaɗan kawai za mu ɗebo”
“Allah ya bada sa'ah”
“Amin na tafi”
Fitarta da kamar minti biyar, wata matashiyar yarinya ta shigo sanye da dogowar rigar atamfa da wani minafukin gyale a kafaɗa, sallama ta fara yi na amsa mata.
“Assalamu alaikum”
“Wa'alaikissalam”
“Sannu ina kwana?”
“Lafiya ƙalau”
“Dan Allah nan ne gidan Musa Kafinta?”
“Nan ne, lafiya?”
“Lafiya ƙalau, Sunana Shafa Ibrahim ni ƴar jarida ce ina aiki da jaridar Arewa a yau, tare da abokin aikina na ke ina son mu tattauna da iyalansa ne akan abunda ya faru”
Ta ƙarasa tana miƙa min katin shedarta.
CANDY ✍️
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣5⃣
Habiba ce kwance tsakar gida amai na gefenta da alama yanzu ta gama shi, domin Inna ta ɗauki makwashi da tsintsiya ta je ɗebo ƙasa. Da sauri na ƙarasa kusa da ita jikina a mace na dafata.
“Sannu Habiba mi ke damunki”
“Wallahi kaina ne ke ta ciwo ban ma iya dawowa daga makaranta ba sai da malaminmu ya kawo ni, sai faman aman na ke, kuma bakina babu daɗi”
Samun kaina na yi da kuka marar sauti, hawaye na bin fuskata kamar babu gobe. Na samu kaina cikin wani irin tashin hankali wanda ban taɓa samun kaina a ciki ba.
“Ai zata samu sauƙi ina jin malaria ce bata sake ta ba”
Inna ta faɗa ganin ina kuka, sai faman rufe aman take.
“Allah yasa malaria ce, Allah yasa ta tabbata malaria ce ba ciki ba”
Maganar ta fito daga bakina kamar antseni. Hakan yasa Inna ta kalleni
“Nawwara, akwai abunda ya kamata na sani ne?”
Na yi saurin girgiza mata kaina hankalina a tashe.
“Babu babu komai”
Ta saki tsintsiyar hannunta, ta kalli Habiba da ta soma kuka daga inda take kwance.
“Akwai abunda kuke ɓoyewa ne?”
Na girgiza mata kai alamar a'a. Amman bata yarda ba. Ta soma ƙirga da hannunta.
“Tsaya dakata, Habiba tana da ciki kenan?”
Habiba ta yi saurin tashi zaune ta matsa gefena kamar zata shige jikina tana girgiwa Inna kai.
“A'a Inna”
Ta faɗa cikin kuka, kamar yadda nima na ke kuka. Sai ina ta kalleta idonta cike da hawaye ta nunata da yatsa.
“Kina da ciki Habiba, na lura da haka domin yanayinki ya canja gaba ɗaya, amman saboda karna munana zato a gareki yasa ban bari zuciyata ta ƙawata min wannan ba, ashe yaudara kuke ke da ƴar'uwarki, na shiga uku na lalace ina kika samo shi?”
Ta ɗora hannu saman kai ta nufi ɗaki tana kuka. Hakan yasa na cire Hijabin da ke jikina na aje a gurin tare da wayata na rufe mata baya. Safa da marwa na tarar tana yi a cikin ɗakin tana kuka, kamar jira take na shigo sai ta rufeni da maganganu marar daɗi.
“Kun cuce ni Nawwara, wannan ba tarbiyar gidan nan ba ce, ina kuka ɗaukota? Kun ƙara shafa mana baƙin fenti acewa mahaifinku ɓarawo ku kuma a kiraku ƴan iska, wayyo Allah na”
Ta faɗi tsakar ɗaki tana kusar kuka. Kusa da ita na ƙarasa na ɗafa ina kuka na ce
“Wallahi ba mu watsar ba Inna, ita ma yaudararta aka yi”
“Waya yaudareta? Faɗa min waya rusa mana ɗan farincikin da ya rage mana?”
A nan na feɗe mata daga biri har wutsiya akan abunda ya faru, sai dai ban labarta mata cewar Mustapha ne ya aikata mata haka ba, saboda bana tabbacin cikin nasa ne ko ba nasa ba ni dai abunda na sani ba shi kaɗai na ya yi lalata da ita ba, nasan kuma duk na faɗa mata cewar shi ne zata iya zuwa ta samu iyayensa wanda hakan na san ba zai mana daɗi ba, domin zasu iya ɗauka ko wane irin mataki a kan ɗan su ƙwalli ɗaya da suke ji da shi.
Can ƙasa-ƙasa na hango muryar Inna tana cewa.
“Habiba ta ci amanata kuma ta ci amanar kanta, ta zubarda ƙima da duk wani mutuncin da yake gidan nan, a yau na yi nadamar haihuwarta, baƙincikinta zai kasheni, ni ma nice na tafi ba mahaifinku ba, Allah be ƙaddara ya ga wannan abun kaico da wayyo a rayuwarsa ba sai ni, Habiba kin cuce mu...”
Duk wannan furucin da Inna take akan kunnuwan Habiba saboda tana jikin ƙofa tsaye ne, sai da Inna bata iya ganinta saboda ta bata baya ne. Muna haɗa ido da ita sai ta bar jikin ƙofar ta nufi ɗakinmu. Da sauri na tashi na bita saboda irin hawayen da na hango suna zuba a idonta.
Ko da na shiga na tarar tana ta saurin cire uniform ɗin jikinta ta saka wasu tufafin. Jin motsina yasa ta juyo da sauri ta kalleni.
“Nawwara guduwa zan yi, ba zan zama dalilin mutuwar Inna ba, ba zan rasa Baba kuma na rasa Inna ba-”
Ta juyo ta cigaba da haɗa kayanta. Ƙarasa na yi kusa da ita ya miƙar da ita tsaye na kama hannyenta da ke zafi sosai saboda zazzaɓi na riƙe gam, ina kuka kamar yadda itama take yi har ɗayanmu baya iya yiwa ɗan'uwansa magana.
GOOD NIGHT.... 🤧
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣3⃣
Ihun da na yi ne yasa Inna fitowa daga ɗaki da sauri tana kallona.
“Na samu aikin Inna sun ɗauke ni”
Murmushin haukan da na ke ta yi, tana girgiza kai for first time bayan rasuwar mahaifinmu yau na ga murmushin Inna. Zuwa na yi da gudu na rumgumeta ina ta murna kamar babu abunda ke damuna. Haka na wuni cikin farinciki da jindaɗi kamar wacce aka yi ma kyautar kujerar makka. Ban san farincikina kaɗan ne har sai da Habiba ta dawo na sanar mata da labarin sai ta yi kamar zata haɗe kanta dan murna kai kace ma ita ta samu aikin ba ni ba, a ranar Habiba bata iya cin abincin rana ba dan tsananin murna, da maraici ta siye alawa da kuɗin Inna ta yi sadaka. Haka ta ke nunawa kulawarta da damuwa a duk lokacin da wani abun ya sameni, ta kan zauna ta labarta min abunda Inna bata sani ba, zata iya ɓoyewa Inna abu amman ni bata ɓoye min ba, mutune har mamakin yadda muke son junanmu suke, ganin ita take bina amman bama taɓa samun saɓani, ko ma mun samu tun anjima kaɗan zanje na rarrasheta ko kuma ita ta zo ta bani haƙuri ko da kuwa ni ce bana da gaskiya, irin tsabanin da ake samu tsakanin mabiyi da mabiyi ni ban cika samunsa da Habiba ba, muna son junanmu sosai, ko ciwo ɗayan mu yake sai ɗayan ya ji kamar ya cirewa ɗan'uwansa ya sakawa kansa.
Lokacin da Baba na da rai idan ya tashi zolayarmu har cewa yake yadda muke son junanmu bama sonsa haka, wani gurin ma idan mukaje ba dan kamanni ba da mutane za su ce Habiba ƙawata ce ba ƙanwata ba.
Ba zan iya misalta irin son da take yi ma Noor ba, tun da na haifeshi ita ce da ɗawainiyarsa har ya kawo yanzu, babu kuma wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa a unguwarmu ko ma a cikin gidanmu ni kaina ban isa na hukunta Noor ba indai a kan idon Habiba ne. Ni kaina shaƙuwar ta kan ba ni mamaki, wata ƙila dan akwai tazarar shekara bakwai a tsakaninmu.
Duk farinciki da ɗaukin aikin da nake idan na tuna Baba ba ya raye sai na ji babu daɗi, na so ace na samu aikin yana da rai na san zai yi farinciki sosai, sai dai kuma ƙaddara ta riga fata abunda Allah ya rubuta dole shi zai samu bawa. A daren ranar da na samu aiki sai ga Bilal ya kirana ni a waya na yi zaton zai ce na fito ne sai ya ce na aiko masa Noor yana bakin ƙofar gida, ba musu na miƙawa Noor wayar, ban san mi suke tattaunawa ba kawai dai na ga Noor yana dariya yana ɗaga kai sai kuma ya wulgumin wayar ya tashi ya fita da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.
“Falfala da gudu ɗan gidan Bilal sai in be kiraka ba”
Cewar Habiba tana dariya. Nishaɗin dake fuskarta shine a fuskar Inna da Jamila har ma Sakina da kuma ni kaina.
“Bilal ɗin nan yana son Noor kuma na tabbatar son da yake miki ne ya shafe shi”
Na ɗago na kalli Inna da furucin da ta yi.
“Ba fa so na yake ba, mutunci ne kawai a tsakaninmu, be taɓa cewa yana so na ba”
Habiba ta watsa min harara.
“Ji matar nan muna-muna munafuka, Wallahi son junansu suke amman shi ba zai iya faɗa ba ita ba zata ba shi dama ba, ai da yanzu an wuce gurin, duk alamun da yake nunawa ai na son ki ne, ke kuma kina kauce masa”
Na yi dariya ina girgiza kai.
“To ya kike son na yi?”
“Ya dai kamata ki bashi dama, zama haka ba zai yiyu ba, Allah kaɗai yasan iya gulmar da ake muku a unguwarnan, kin kore kowa kin zauna a gida gashi har mahaifinki ya rasu be ga wani auren na ki ba”
Wannan karon Inna ce ta yi maganar, kuma maganar da ta yi ta ɗan taɓani, tabbas mutuncin ƴa mace da kuma darajarta a gidan aurenta ne, sai dai ba kowa ne zai maka son tsakani da Allah ba, wasu kan zo so na saboda sha'awata da sun gwasa sun gano ni ba ƴar iskar barawarar nan ba ce sai su gudu, wasu kuma su nuna maka ba zasu yarda da je da yaron ka ba, wasu kuma basa da wani sana'ar kirkin da za su iya riƙe sauran iyalansu ma balle kuma a haɗa da ni, kowa da irin matsalarsa. Bilal ɗin ma laƙe min ya yi da sunan abota, sai dai ko da wasa ban bashi alamun da zai iya nuna min so ba, saboda na san iyayensa ba zasu yarda ya auri mace da taɓa aure har biyu ba kuma har da ɗa ma.
Uffan ban ce ba, Inna da Habiba kawai ke ta nanata maganar. Muna nan zaune Noor ya shigo da ƙatuwar leda a hannunsa har biyu a hannunsa baki har kunne.
“Momy kalli abubuwan da siyo min, kuma ya ce Mama Habiba kawai zan bawa kar na sammi ki, kuma ya ce yana kiranki yana ƙofar gida”
Shi da Habiba suka riƙa kokuwar buɗe ledar, ni kuma na zari Hijabina na nufi ƙofar gida. Tsaye na sameshi yana kallon ƙofar gidanmu da alama dai yana jiran fitowata ne.
“Ina ta zuba ido na ganki yau a kamfaninmu ban ganki ba”
Ban bashi amsa ba sai da na yi masa sallama ina murmushi.
“Assalamu alaikum”
Sai ya amsa min da murmushi.
“Wa'alaikissalam Nawancy, na zo na taya ki murnar samun aiki, ai na faɗa miki zasu ɗauke ki”
“Ɗazu na samu saƙon, na jidaɗi sosai”
“Mutane na ta zuwa karɓar uniform amman ke ban ganki ba”
“Uniform kuma?”
“Yes ai Uniform zaku saka, tun safe ake zuwa ƙarɓa kin ga ɗaga yau zuwa gobe ne kawai ake bada uniform ɗin, on monday zaku fara zuwa aiki, kuma idan kunje karɓar uniform ɗin za a nuna muku irin aikin da zaku yi”
“Gobe zanje Inshallah, ai ban san ana zuwa yau ba”
“Sai dai matsala ɗaya, Nawancy bana son ki saka wando, ina ganin kamar ba be dace ba”
‘Musamman ga irina masu manyan mazaunai’
Na faɗa a raina. A fili kuma sai na ce.
“Ai zan iya saka Hijabi ko abaya a sama”
“Amman baya son haka, sai idan kin tashi aikin ko kuma idan zaki shigo, shi be yarda ma ko hula a saka a gurin aikin ba balle kuma Hijabi”
Cike da mamaki na ce
“Ba musulmi ba ne hala?”
“Wallahi musulmi, amman mutumen sai a hankali, haka zaki ga tattoo a jikinsa, ina jin ya zauna waje ne”
Na taɓe baki cike da ƙyamar halin mutunen duk da ban san shi ba
“Allah ya kyauta amman abun baƙinciki ne ace musulmi ya rinjaya wani addini sama da nasa, ga shi ka ce ya cika tsanani”
“Yana da tsanani sosai, amman tsananinsa yana burge ni wani lokacin, kin ga dole kowa ya riƙe aikinsa da muhimmanci, kuma kin ga wacan da aka canja baya damuwa da duk waɗannan abubuwan shiyasa duk ƙarshen wata sai an siyo kayan abincin da cups da aikatan gurin suke aiki da su, amman zuwan wannan ya saka dokar duk wanda ya fasa masa cups za a cire cikin albashinsa, dole kowa ya riƙa taka tsantsan da abubuwan gurin”
“Amman daman ba a biyan kuɗin abincin ne?”
“No ana biya restaurant ɗin da ke cikin kamfanin ai nasa ne, amman idan ba restaurant ba kin ga ma'aikici zai buƙaci shan ruwa ko wani abun ko kuma tea musamman ga masu zuwa tun safe, ko kuma idan aka yi baƙi, to duk da wannan cups ɗin ake amfani. Bayan ma wannan kamfani suna da Sabuwar Asibiti da aka buɗe nan by pass, One-On-One Special Hospital, amman ance ta masu kuɗi ce dan katin ganin likita ma ɗari takwas da hasin ne”
Na jinjina kai ina faɗin.
“Kamfanin ma akwai girma, ni Allah yasa ma har na yi aikin na gama ba zan ganshi ba”
Sai kawai yasa min dariya.
“Kina tsoro ne Nawancy?”
“A'a ba tsoro ba ne, kawai ba zan iya jurar wulaƙanci ba ne, kaga ƙara ma ace bamu haɗu ba”
Mun daɗe muna fira yana ta labarta min kamfanin da kuma wasu abubuwa na cikinsa da kuma yadda aikinsa yake, kamin hirar siyasar ƙasar nan ta shigo ciki, sai tara da rabi muka yi sallama ya tafi ni koma na cikin gida.
Ko da na shiga su Habiba sun ci sun ciye an gutsura min ɗan tsiton cake da nama ƙwara ɗaya an aje min sai kuma ice cream a cibi.
“Yanzu wannan abun kawai zaku bar min?”
“Eh mana dan kin samu ma mun rage miki”
Cewar Habiba, tana bani amsar tambayar da nayi, sai Noor yasa dariya yana cin namansa ya ce
“Momy ƙyale Mama Habiba sai ta yi bachi zan ƙara miki karki kuka kinji?”
Sakin baki Habiba ta yi.
“Au ni zaka watsawa ƙasa a ido?”
Ta kai masa dudu. Inna tasa dariya, yau kan ba laifi muna cikin farinciki farincikin da muka daɗe ba mu yi ba tun bayan rasuwar Baba, sam ba zaka gan mu a yanzu ka ɗauka akwai wata damuwa a ranmu ba. Daman can talauci baya hana mu walwala ko kuma farinciki, idan ka ganmu a damuwa to muna jin yunwa ne, da kuma mun samu mun ci sai mu gode Allah da wannan ni'imar, mu kuma roƙi na anjima.
*** *** ***
Kamar yadda muka kwana cikin farinciki haka muka tashi da shi, abun ka da sabon shiga su Noor na wucewa makaranta nima na shirya muka fita tare da Habiba ita ta wuce tata makarantar ni kuma na ɗauki hanyar gurin mu a Napep.
Yau ma da na isa ban shiga ba sai da na ƙira Bilal na sanar masa ina bakin gate, shi ya fito ya shiga da ni, sai mita yake wai ya kamata ace na shigo ciki da kaina tun da Monday zan fara aiki, ni kuma ina taka tsantsan ne gudun ƙar na yi wani abun da ba daidai ba, shugaban ya ce zai hukunta tun ban fara aikin ba.
Ciki ya shiga da ni har muka isa cikin wani ƙaton haɗi inda na faɗa musu sunana suka duba sannan suka ɗauko uniform ɗin dake cikin leda suka ba ni, sai kuma wasu takalmi masu kama ta da malaman lafiya na asibiti, suka miƙa min wasu takardun na saka hannu sai suka buƙaci idan zan dawo na zo da ƙaramin hoto na guda biyu, wai zasu saka a file ɗayan kuma a kuma na saka a catin zan rayata a wuya na shedar aikina.
Ɗaya daga cikinsu ne ya yi min ja gaba har gurin da zan yi aikin nawa, kitchen zan riƙa gogewa da kuma da ake aje files kusan ɗaki biyar, sai dai ba ni zan yi sharar ba aikina Mopping ne kawai, kuma idan zamu yi mopping ɗin sai mun saka safar hannu idan mun gama mu jefar, sai kuma goge kofuna da jerasu a muhallinsu, shi ma sai mun saka safa, tsarin kamfanin kamar na turawa, lallai sai a yanzu na tabbatar da zancen Bilal na cewa Kamfanin yana takara da kamfanonin duniya. Mai nuna min aikina ya jaddada min kamin na jera kofunan sai na ƙirga ko guda nawane na rubuta a file ɗin gurin da kuma time da na fara da time ɗin da na gama, da kuma ko kofi nawa na tarar, daga ƙarshe Bilal ya kai ni reception ya nuna min gurin da zan saka sunana da kuma lokacin da na shigo, idan kuma na gama sai na saka sunana da kuma lokacin da na fita, ƙarfe bakwai zan fara aikin na ƙare tara, hakan na nufin bakwai ta yi min a can kenan.
Irin yadda tsari da dokokin kamfanin suke sai duk na ji aikin ya fara fita raina kamar ba zan iya ba, sai dai babu yadda na iya tun da nema na ke yi kuma ba anan zan dauwamaba. Har bakin titi Bilal ya rakoni, muna tsaye da shi na hango motar Zinatu ta shiga kamfanin, na tabbatar da ita ɗin ce saboda hangota da na yi ta gilashin motar da ke sauke. Bilal ya tara min Napep na hau sannan ya koma ni kuma na kama hanyar gida ciki da mamakin tsare-tsaren wannan kamfani, gaskiya ba dan ina son aikin ba da na haƙura da yinsa, a gurin da na saba sauka na ce mai Napep ɗin ya aje, sai na karɓi ragowar canjin kuɗin da Bilal ya bashi na nufi cikin unguwarmu.
A hanya na haɗu da mai gidan da muke haya, wata irin kunyace ta mamaye mu nasan yayi mana karamcin tun da be mana magana tun baya rasuwar Baba ga shi har Inna zata gama wanka takaɓan ta cikin wannan satin. Sun-sun-sun na gaisheshi ya amsa min yana murmushi tare da tambayar ya haƙuri.
“Mun gode Allah dan Allah ka yi haƙuri akan maganar kuɗin nan, inshallah za a kawo”
“Kuɗin me? Ai Bilal ya biya be faɗa muku ba ne? Tun Margayi be yi sati da rasuwa ba ya kawo kuɗin dubu arba'in cif”
Na saki baki ina mamakin ikon Allah.
“Wallahi ba mu sani ba”
“Wallahi ya biya sai dai ayi masa godiya”
Sallama na masa na wuce zuciyata cike da hauƙin Bilal, bakina kuma har rawa yake naje gida na labartawa Inna wannan labarin. A hankali wata mota da ta fito ɗaga gidansu Manjo ta doso inda na ke, mai maotar na kawowa daidai ni sai ya sauke baƙin gilashin motarsa.
Ashe Mustapha ne, cikin shigar manyan kaya wato farar shadda da kuma barar hula sajensa na kwanta sai sheƙi yake, da alama jumma'a zai je tun da yau friday, fuskarsa cike da annuri, sai dai bana mutanen kirki ba, na kuɗi da kuma kyawun hallita da suka nuna isa a fuskarsa. Kallona yake ba ko ƙyafta ido, ni kuma na bawa banza ajiyarsa sam babu tsoro a tare da ni saboda na shirya tarbar ko minene daga gareshi.
Haka nasa kai na wuce na barshi a gurin zuciyata har wani zafi take min saboda da tsanarsa.
Da sallama na shiga gida, Inna da dpo suka haɗa baki gurin amsa min, hakan yasa naji kamar na janyo sallamar na mayar da ita a bakina, yau ma ya taki sa'a na sauke idona cikin nasa hakan yasa ni jin kamar na ƙarasa a inda yake zaune gaban Inna na shaƙe wuyansa.
THE GAME IS ABOUT TO START...
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣4⃣
Na ɗauke kaina kamar ban san da zaman mutun a gurin da Inna take ba.
“Har kin dawo?”
Inna ta tambaya, ni kuma na nufi ƙofar ɗakin mu ina amsa mata domin bana son na juyo idona ya haɗu da na azzalumin mutunen nan.
“Eh Inna”
Na ɗaga labulen ɗakin mu na shige zuciya cike da abubuwa guda biyu farincikin abunda Bilal ya yi mana da kuma baƙincikin ganin dpo a gidanmu. Kayan da ke hannuna ma saman katifa na jefasu, na zauna ƙasa raina a jagule.
Jidda ce ta faɗo min a rai, ya kamata ace na tabarta masa samun aikin nan da na yi, har na unƙura zan tashi na fita sai na tuna dpo yana tsakar gida, hakan yasa na koma na zauna, sai tunanin Bilal ya dawo min rai. Lokaci zuwa lokaci na kan samu kaina da murmushi tuna irin abubuwan alherin da Bilal yake mana, wanda na san har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa saka masa da abunda ya yi min, ya sadaukarda abubuwa da dama saboda farincikina.
Kiran da Noor yake min a tsakar gida ne ya katse min tunani, ina unƙurin tashi na fita sai ya shigo ɗakin da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.
“Momy duba aka raɓa mana sabon littafi a makaranta”
Na faɗaɗa fuskata da murmushi ina karɓar littafi tare da buɗewa ina dubawa, littafi rubutu ne mai hoton ciyaman, da alama ya kai musu ziyara ne, daman naji a rediyo ana cewar zai ziyarci makarantu.
“Momy da idona na ga Ciyaman yana jawabi har da godiya ya yi mana, sai aka raba mana littafai”
Na kai hannu na shafa fuskarsa ina dariya
“Amman Ciyaman ya kyauta da ya bari Noor ya ganshi”
Sai ya ƙyalƙyale da dariya ya rumgume ni. Haka ɗa na yake, masu kuɗi da ƴan siyasa suna burgeshi ko a mota ya ga mutun sai ya tsaya kallonsa har sai ya daina hangoshi sannan hankalinsa ya kwanta, a ranar kan labari sai abunda ya manta.
Zaunar da shi na yi saman jikina, na soma cire masa talkamin makaranta tare da safa, shi kuma yana duba littafin tare da karantawa. Habiba ce ta shigo ɗakin babu ko sallama, kana ganinta kasan a gajiye take jikar littafanta ma a bakin ƙofa ta sakesu ta kwanta kusa da ni tana ƙoƙarin cire hijabinta.
“Lafiya kike kuwa?”
Na tambaya ina kallonta, Noor kuma ya tashi da sauri ya fita waje. Ɗan guntun tsaki taja irin na wanda baya son magana kana ta ce
“Wallahi bana jindaɗi, amai na biyu makaranta kuma kaina ciwo yake sosai”
Dukan shida-shida gabana ya yi tsaɓanin uku-uku da na kowa keyi, a take nima na ji ciwon kan ya kamani, dafe kaina na yi na lumshe ido yana sauraren yadda zuciyata take bugawa. Ƙoƙarin kawarda abunda ke zuciyata nake, yes cikin zai iya nunawa a sati biyu amman ba ko wanne ba, cikin Noor ma a sati biyu aka gano ina da ciki balle kuma Habiba da ke da wata ɗaya har da sati ɗaya, tunda ranar litanin Inna zata cika wata ɗaya da sati biyu cikin taƙaba.
‘No ba ciki ba ne, maleriya ce inshallah ba ciki ba ne’
Zancen da nake a zuci shi Habiba take a zahiri.
“Nawwara na ce ƙila maleriya ce, saboda idona har nauyi yake”
Na buɗe ido na kalleta tare da ɗaga mata kai alamar ‘Eh’
“Ita ce, bari na aika Sakina ta siyo miki Anti-Malaria shago”
“Tau”
Ta juyo min baya tana dafe da kai, hakan ya bawa hawayen da ke maƙƙale a idona saukowa zuwa kumatuna, ban taɓa tabbatar da hawaye na da zafi ba sai a wannan lokacin, gumi ne ya soma keto min ta ko ina kamar wacce ta yi rashin gaskiya. Cikin hanzari na kai hannu na share hawayena saboda motsin Sakina da na ji zata shigo ɗakin, sai na miƙe tsaye na nufi ƙofar fita. Ashe magana take min ban ji ba har sai da ta riƙoni.
“Anty Nawwara, wai ɗan sanda nan yana kiranki a waje”
Da kai na iya amsa mata, daman Hijabin da na shigo da shi yana jikina sai kawai na zarce ƙofar gida, har ga Allah ba dan ina cikin ruɗu ba babu abunda zai sa dpo nan ya kirani kuma har na tafi. Tsaye na yi masa idona a ƙasa ina ta tunanin makomarmu, idan har ta tabbata Habiba na da ciki mun shiga uku, lallai mutane zasu gasgata cewar Mahaifinmu ya yi sata, tun da ga ƴar'uwata da cikin shege, duk wani yabo da ganin mutuncinmu da ake a unguwarnan zai zube, ya Inna zata yi idan ta ji Habiba na da ciki? Ita kanta kanta Habiba ya zata kasance? Ni kaina da suka san na yi aure lokacin da na haifi Noor sai da suka kira shi shege balle kuma Habiba.
“Nawwara”
Kiran sunana da dpo ya yi na yasa na dawo hayyacina har na kalleshi, ashe tun da na zo gurin magana yake min amman ban fahimtaba saboda tashin hankalin da ke zuciyata.
“Ki yi haƙuri dan Allah, ki share hawayenki, duk abunda na faɗa miki zanyi ki yarda da ni”
Sai a lokacin na kula da hawayen da ke ta zuba a idona, cikin sauri na sa Hijabina na gogesu ina jan magina. Sai ya ɗora da zancen da ban gane masa ba, ba dan kuma yana min wani yaren ba sai dan hankalina baya gurin, babu komai a zuciyata sai fargaba tunani da kuma zullumin abunda zai je ya dawo, na tabbatar da za'a auna jinina a lokacin za a tarar ya haura ɗari uku da wani abu bama ɗari biyu ba.
A gurin na barshi tsaye na shige gida ba tare da hawayen sun tsaya min ba, haɗa ido da muka yi da Inna yasa idona ƙara cika da ƙwalla, tausayinsa ne ya kamani tabbas Mahaifiyata ba zata iya ɗaukar wannan ba, duka-duka yaushe ta rasa mahaifina kuma yanzu ta ji Habiba na da ciki.
“Lafiya?”
Tambayar da ta yi min ne yasa na share hawayena ina ƙoƙarin ƙirƙiro ƙaryar da zan mata.
“Ba komai kawai mun yi magana kan Baba ne”
“Nawwara ki yi haƙuri idan ma a duniya ba a yi komai ba, lahira za'ayi domin Allah baya zalumci kuma zai ƙwatar mana haƙƙinmu”
“Haka ne, Inna kina da kuɗi a siyowa Habiba maganin Malaria?”
“Duba a cikin jakata ba za'a rasa ba, tace kanta ke ciwo”
Ban iya tsayawa amsa mata ba, na nufi ɗakin na ɗauko kuɗin na aiki Sakina ta je siyo mata, bata daɗe ba ta dawo da kuɗin wai sunje masallaci.
Kayan jikana na tuɓe na koma gaban murhu ina hura wuta domin ɗora girkin rana, har na yi girkin na gama kuka nake a boye saboda bana son Inna ta gano ina kuka hakan zai raunana mata zuciya kuma dole zata tambayeni dalilin kukan wanda ba zan iya faɗa mata ba.
Bayan na gama na shiga banɗaki na yi wanka tare da kuka a can, domin a nan babu wanda zai san da damuwata, bayan na fito na raba abincin na sake aikin Sakina ta je ta siyo mata maganin. Da kaina na ɓalla na bata ta sha na zuba mana abinci sai ita ta kasa ci saboda zazzaɓin ya rufeta sosai, jikinta ya yi zafi sosai. Ni kaina kasa cin abincin na yi, sai mutuwar Baba ta dawo min sabuwa, da ace ƴan sanda nan ba su masa duka ba, da be mutu ba da Habiba da ni da Inna duk ba mu shiga wannan halin ba. Bana son kowa yasan kukana hakan yasa na ɗauki buta na shiga banɗakina na ci kukana sao da na ƙoshi sannan wanke fuskata na fito, a lokacin ana kiran sallah la'asar.
Ba laifi Habiba ta samu sauƙi bayan shan maganin da ta yi, da muƙa gama sallah magariba ba har waje ta fito muna ɗan taɓa fira da ita, har ma ta ci ciwon masarar da na yi, hakan ba ƙaramin faranta min rai ya yi ba, gar na samu sakewa na labartawa Inna zancen Bilal, babu irin ruwan albakar da Inna bata sa mishi ba, Habiba ma sai yabonsa take. Inna ce ta cilasta ni kiransa a waya na sanar masa tana son ganinsa.
Bayan Sallah isha'i ya zo Inna tasa na shigo da shi har cikin gida ta yi masa godiya, bayan mun fito ni nake masa godiya duk da nasan cewar ba da sanin mahaifiyarsa ya yi mana wannan abun ba, da ba zata bari ba domin ta ƙi jinin ta ganmu tare ma balle kuma har kyauta ta shiga tsakaninmu, mun daɗe muna fira shi sannan muka yi sallama.
Bayan na dawo nake labartawa Inna yadda gurin aikin yake da kuma irin ƙa'idojinsa sai kuma zancen yadda kace min Shugaban ya ke, ta yi murna sosai ita da Habiba sun ƙarfafa min gwuiwa kuma suka min addu'ar samun nasara.
Washe gari naje na sanar da Jidda zancen samun aikina, ita ta yi murna sosai kusan sai na ce ta fini farinciki, haƙiƙa Jidda ta wuce ƙawa a gurina mun zama ƴan'uwan juna ni da ita, mun sha fira sosai yadda na ke labarta mata gurin aikinmu ita abun ma burgeta ya yi, wai ban sanar mata da wuri ba da ta kai takardunta na diploma sun ɗauke ta aiki a guri.
Sai yamma na baro gidansu bayan na haɗu ni da kwanon shinkafa da miya, abincin da na ke marmari.
*** *** ***
MONDAY MORNING...
Hankalina ya kwanta sosai a kwanan biyu da Habiba ta yi bata sake ko da ciwon kai ba, hakan ya gamsar da ni lallai malaria ce take damunta.
Dukan mu shiri muke bayan mun gama karyawa, ni ina shirin zuwa gurin aiki su kuma suna shirin zuwa makaranta, ban shafa hoda ba bayan na shafa mai, domin kawaliya bata dame ni ba, balle ni da zan fita tun 6:30am. Uniform ɗin na ɗauko na cire daga cikin leda, dogon wando ne ash color da farar riga, sai kuma wata ƴar ƙaramar riga marar hannu da za a ɗora saman wacan farar rigar ita ma ash, sai da na gama kallo ni da Habiba sannan na saka.
Cas na fito kamar wata ma'aikaciyar banki musamman da na saka baƙaƙen takalmin nan masu kama da cover shoes.
“Wow Nawwara kin wanku”
Cewar Habiba tana kallona, ni kuma na yi dariya ina mai jindaɗi a raina. Ba Habiba kaɗai ba har Noor da Inna sai da suka yaba ni, ni kaona na san shigar ta yi min kamar wata ma'aikaciya, idan ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce aikin Mopping zan yi. Wata ƴar ƙaramar baƙar hula na ɗauka na saka a kitson da ke kaina, sannan na ɗora ƙaton Hijabi yaɗi huɗu da rabi na saka, a gaggauci na fito daga gida gudun kar na yi lattti gashi yau ne farkon zuwana, duk yadda Habiba ta so na tsaya mu fito tare ƙiyawa na yi gudun kar na ɓata lokaci. Sai da na kawo bakin titi sannan na tuna da hoton da aka ce na kawo, da gudu na koma gida na ɗauko na sake fitowa ina ɗan jin kunya saboda mutane da ke kai da kawo a unguwat sun ɗan fara fitowa, duk da yake ba za'aga uniform a jikina ba amman sai na samu kaina da jin kunya saboda ban saba saka wando na fita da shi ba.
Ko da na isa kamfanin bakwai sauran minti biyar, yau kan sun tare a bakin ganin suna ɗan bincikata, sai na faɗa musu komai har ma na nuna musu uniform ɗin da ke jikina da kuma katin sheidata, sannan suka bar ni na wuce. Kamar yadda Bilal ya nuna min sai da na fara isa na saka sunana da lokacin da na shigo da kuma rana sannan suka nuna min gurin da zan aje Hijabi da wasu kaya idan na zo da su, na nufi gurin na na cire Hijabina na aje a lokar da suka ba makullinta, na samu kaina da jin kunya sosai ganin babu komai a jikina sai uniform ɗin da kuma ƴar ƙaramar hular da ke kaina, sai da na ɗan jima tsaye a gurin sannan na juyo na fara takowa, sai ɗaya ɗaga mutanen da ke reception ya ɗaga hannushi yana nuna min hular da ke kaina, a dole na juya na je na cire na aje, na juyo ina wani taku kamar wacce bata son saka ƙasa babu komai a tattare da ni sai kunya, shi kanshi ya lura da yanayina, hakan yasa ya sakar min murmushi, nima na sakar masa kaɗan idona a ware, ina kalle-kalle ala-ala na ke kar naga wanda na yasan ni har na nufi Lifted na danna ta buɗe na shiga sai na danna number 3 ta rufe ta soma tafiya da ni, zuciyata sai bugawa take da ƙarfi irin bugarwa nan na ɗoki da kuma tsoro a lokaci ɗaya.
Muna isa number 3 ta buɗe na fito sai na samu masu irin uniform ɗina suna ta aikin gyara gurin, ganin duk mata ne yasa ni na ɗan saki jikina na nufi gurin da aka nuna min da zan ɗauki kayan aikina. A ciki na tarar da wata yarinya mai far'a da son mutane domin ita kaɗai ce ta amsa min sallamar da na yi har ta yi min kyautar murmushi.
“Da alama ke baƙuwace a nan”
“Haka ne, yau zan fara”
“Haba shiyasa”
“Mi kika gani hala?”
“Naga kin yi sallama ne, ai a nan ba a sallama ba a gaisuwa saboda mai Kamfanin baya buƙata, idan kika ga ana fira da juna tau angama aikine ko kuma an fita can waje”
“Tau shi kuma haka yake”
Ta yi dariya tana nuna min camera.
“Ki yi a hankali, Camera tana ɗaukar komai”
Security camera ce daga gabanmu tana ɗaukar komai, sai na yi saurin gumɗe bakina na ɗauki kayan aikina na yi gaba.
Na ji wuyar aikin sosai wata ƙila saboda ina farkom farawa ne, ko kuma saboda ɗakunan da aka haɗani da su suna da girma sosai, ga kuma gyara kofuna da jerawa bayan na gama ƙirgasu, sai da na gama sannan naje gurin da ake rubutawa na rubuta ko nawa na tarar sannan na nufi gurin aje kayan aikin na aje, na aje na kaiwa mutumen jiya wanda yace na kawo mashi ƙananan hotona, ɗaya ka karɓa ya saka a file sannan ya karɓi ɗayan na saka min a katin sheidata na rataya a wuya sannan ya ce min.
“Idan kina da account ki rubuta a nan, idan kuma baki da shi zan cika miki wata takarda sai ki riƙa karbar albashinki hannun kashiya”
“Gaskiya na daɗe ban yi amfani da shi ba, ina tunanin yanzu ma baya aiki”
Wata takardar ya ɗauko ya yi rubuce-rubuce sannan ya bani na saka hannu sai ya maida takardun ya aje, ya ce
“On 25 zaki riƙa zuwa gurin kashiya kina amsar kuɗin albashinki 12k”
“Tau na gode”
Na juyo duk da ban tambaye shi iya kashinyan yake ba, na fito daga gurin gaba ɗaya. A ƙaton agogon da ke reception na ga 12:14pm, lallai na daɗe ina aikin nan, sai da na saka hannu kuma na rubuta lokacin da na gama aikin sannan na nufi gurin da Hijabi yake na ɗauka, ina sakawa na ji mutun a bayana.
“Nawancy”
Da sauri na juyo na kalleshi.
“Ka ganni ne kamin na saka Hijab?”
Sai kawai ya ƙyalƙyale da dariya ya ɗora min ɗari biyar a lokar dana ɗauki Hijabina.
“Allah dai ya bar min ke, ga wannan ki hau Napep, a sauka lafiya”
Sai ya kama gabanshi ya yi tafiyarsa. Cike da kunya na fito na daga cikin kamfanin ita tunanin anya zan iya aikin nan zuwa?
“Sannu ƴar'uwar yau nima na ti latti gama aiki”
Na kalli mai min maganar da ke gefena na dama fuskarta ɗauke da murmushi, yarinyar ɗazun ce, sai dai wannan karon ita ma tana sanye da Hijabi, hakan yasa nima na yi mata murmushi.
“Da wuri kike gamawa kenan?”
“Eh gaskiya ten na ke gama aikina. Sunana Amina ke fa?”
“Nawwara”
“Suna mai daɗi”
Sai duk muka yi dariya, muna ta ɗan taɓa fira da ita kamin motar da ta wuce mu ta dawo dai-dai mu ta tsaya.
“Nawwara”
Jin muryar Zinatu yasa na yi saurin kallon motar, ita ce hakimce a motar idonta sanye da baƙin gilashi.
“Zinatu Ya kike?”
A maimakon ta amsa min sai kawai ta jefo min tambaya.
“Me kike a nan?”
“Aiki”
“Aiki aiki aiki wane irin aiki?”
“Mopping”
“Nice amman yau kika fara ko?”
“Eh”
“Good kowa zai ji muna aiki a guri ɗaya Sai dai ba level ɗaya ba, and people may not know the different, congratulations”
Ta tashi gilashin motarta ta kunna kai zuwa harabar da aje motoci. Maganar ta sosa min rai har Amina ta lura da hakan.
“Kin santa ne hala?”
“Eh tare muka yi primary school”
“Allah sarki”
Kamar ta ce wani abu sai kuma ta yi shiru, muka cigaba da tafiya. A gurin hawan Napep muka rabu ni na ɗauki hanyar gidanmu ita ma ta kama hanyar na su gidan.
Kamar kullum a inda aka sake sauke ni na sauka na ƙarɓi canjina na nufi gida, zuciyata cike da tunanin kalamin da Zinatu ta yi min, bana son fassarata da wata fuskar da kuwa da kasancewar na san halin na tsanar mutane irina da ta yi wato talakawa, haka kawai na samu kaina da faɗuwar gaba wata ƙila na tunanin da nake ne, sai da na shiga gidanmu na fahimcin faɗuwar gaban bana tunani ba ne na abunda zan tarar ne.
______________
SHARE, COMMENT AND VOTE.
Sauran na ji wani ya ce short page ne na buge masa baki 😎
BEST REGARDS 🌹
Khadeeja Candy💜
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣6⃣
Haƙiƙa akwai ƙurciya a rayuwar Habiba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta aikata abunda ta aikata, wanda take tunanin kamar mafitane, sai gashi ya zame mana matsala, yanzu kuma tana ganin kamar guduwa ta bar gida shi ma mafita ne, ni ko nasan duk yarinyar da ta gudu ta bar iyayenta lallai tana tare da na sani da kaico a rayuwarta.
Ba zan bari ƴar'uwata ta aiwatar da wannan ƙudirin nata ba, ko da kuwa haka yana nufi salwantar rayuwar mahaifiyata ne, ba zan bari ta sake aikata wani kuskuren ba. Ƙoƙari nake na tsayarda kuka ta yadda zan ƙarfafa mata guiwa da rarrashi amman hawayen da ke min zuba sun ƙi bani haɗin kai.
Idan har ban yi ƙarfin halin shiga tsakaninta da wannan kuɗirin nata ba, lallai zamu iya rasata wanda na san hakan zai iya sama sadiyar rasa Inna.
Hannayenta na saki na share hawayena ina kallonta, cike da ƙarfin hali na ce
“Babu inda zaki je Habiba, irin wannan tunanin na ki ne yaja miki kika jefa mu cikin wannan halin, yanzu kuma zaki sake aikata irinsa? Kina tunanin aikata wannan abun shine mafita? Ba zai canja komai ba, sai dai ma ya ƙara ɓata ran Inna har ta kasa yafe miki, mu kuma ki ja mana ɓacin suna, haka kike so?”
Ta girgiza kai alamar a'a, muryarta a shake ta ce.
“Ta ce ta yi nadamar haihuwata ni ce ajalinta, ba zata yafe min ba”
Hannu na kai na sake riƙe hannayenta.
“Zata yafe miki Habiba, ni ma uwace na san halin da Inna take ciki, akwai zafi idan wani abu ya samu ɗanka musamman mace, idan wani abu ya sami Noor bana iya yafewa kaina, bana iya controlling kaina bana iya juriya, kin san saboda me? Saboda Ina ƙaunar Noor, a duk faɗin duniya babu wacce zata gwadawa ɗa so kamar uwarsa, duk abunda Inna ta yi miki saboda tana ƙaunarki ne ke kanki kin san Inna tana son ki, karki yarda ki gudu idan har kika gudu babu ni babu ke har abada!”
“Ba zan gudu ba, ba zan je ko'ina ba na miki alƙawari, ko da kuwa Inna zata yanka ni ne”
Ya faɗa cikin kuka. Sai na zaunar da ita ina share mata hawayenta, tare da yi mata wasu kalaman da zasu ƙarfafa mata guiwa.
Ban bar ɗakinba sai da na tabbatar kuka da take ya tsagaita, sannan na fito na shiga ɗakin Inna.
Gurin da barta a nan na sameta sai wannan karon tana daga kwance ne, gurin da fuskarta take ya jiƙe da ruwan hawaye kamar an zuba ruwa a gurin. Daga inda na ke tsaye na soma mata magana ciki da ƙarfin hali.
“Habiba ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin kamar hakan shine mafita, ta aikata abunda ta aikata saboda Baba da ke da kuma mu duka, kin yarda da ƙaddarar da ta samu Baba har kika riƙa bani haƙuri, shin miyasa ba zaki yarda da wannan ƙaddararba...?”
Tashi tayi zaune ta kalleni a tsawace ta amsa min
“Saboda ita ta kai kanta”
Na matsa kusa da ita
“Akwai ƙurciya da tare da ni balle kuma Habiba, hankalinta da tunaninta be kai inda kike tunaniba, babu banbanci tsakanin wannan ƙaddarar da kuma wacan dukansu ƙadarori ne, babu wanda ya dace ya nunawa Habiba soyayya a yanzu fiye ke, babu wanda zai mata magana hankalinta ya kwanta fiye da ke”
“Habiba ta ɗauko wata rayuwa wacce bata gidan nan ba, sam wannan ba tarbiyarmu ba ce”
“Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar ƙaddarace, ashe ko haka ya isa yasa ki rumgumeta ki nuna mata kina tare da ita”
Ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalleni
“Kina da ƙarfin zuciya Nawwara, haƙiƙa Muhammad Noor ya yi sa'ar uwa”
“Ƙarfi guiwata taki ce Inna, kin rigani zama uwa kin fini sanin komai a rayuwa”
Wani dogon numfashi taja ta sauke tana cige baki ta ce.
“Wani lokacin kaina ya kan kulle har na yi tunani ba dai-dai, Allah ya kan jarrabi bawa da abubuwa da dama har bawa ya ga kamar Allah baya sonshi”
“Zamu jarrabeku da yunwa da tauyewar ƴaƴan ittatuwa da rayukan da dokiyoyi, ka yi bushara ga masu haƙuri (Masu jure waɗannan jarabce-jarabce) Waɗanda idan masifa ta samesu sai su ce (Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un) Mu ɗaga gurin Allah muka fito kuma a gare za a maida mu, kyakkawar yabo ya tabbata agaresu daga Ubangijinsu, haka Allah ya faɗa a ciki alƙur'ane mai girma, akwai kuma inda Allah yake cewa ‘Ko wane tsanani yana tare da sauƙi har ya sake maimaitawa Haƙika ko wane tsanani yana tare da sauƙi, sai kuma ya ce Fasbir sabaran jaamila wato ya kai Annabi ka yi haƙuri haƙuri mai kyau, Allah yana tare da masu a haƙuri. Inna duka waɗannan Allah ne ya faɗa.
Kin tuna lokacin da na yi aure? Na fuskanci wulaƙanci da ƙalubale kala-kala a gidan aurena, har na fito na haifi Noor cikin baƙinciki da damuwa, na sake wani auren har na fara jindaɗi sai Allah ya karɓe abunsa, na sake dawowa cikin wannan wahalar, sa'anina da wanɗanda muka yi makaranta tare da su, duk sun zama manyan mutane har basa son abota da ni, ni kuma ina nan, amman hakan be taɓa saka ni na yi tunanin ko Allah baya so na ne ba ko da sau ɗaya, da ace Allah ya yi ni kafira da zan yarda Allah baya so na saboda komai na tara a duniyarnan zan mutu na bar shi naje ƙiyama na shiga wuta, amman kin ga yanzu zan iya sha wahala a nan idan har na aikata aiki na ƙwarai ina zuwa ƙiyama kai tsaye aljannah zan wuce, kuma kin ga can ba a mutuwa ba a baƙinciki balle tsufa.
Ki rumgume ƙaddarar nan Inna, karki yi Habiba abunda zai ƙara mata baƙinciki, ta ce min zata gudu ta bar gidan nan saboda kar ta zama silar ajalinki”
Da sauri Inna ta miƙe tsaye da sauri hankalinta a tashe.
“Ina take?”
“Tana ɗakinmu”
Da gudu ta nufi ɗakin, ni kuma na rufa mata baya. Ko da muka shiga ɗakin sai muka samu babu kowa a cikinsa, daga ni har Inna sai da gabanmu ya faɗi, Inna ta juyo ta kalleni nima na kalleta.
“Habiba”
Na kira sunanta da ƙarfi, sai ta amsa min daga bayan gambu da take ɓoye, a zatonta Inna zata faɗa mata wata maganar marar daɗi ne ko kuma ta daketa hakan yasa ta ɓuya a nan. Da sauri Inna ta duba gurin domin ta fini kusa da shi sai ga Habiba a tsaye tana hawaye jikinta na rawa tana jiran sakamakon Inna.
“Zo nan ƴata na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yi miki albarka, ya isar miki”
Inna ta faɗa tana miƙa hannu taja Habiba jikinta ta rumgume, sai suka fashe da kuka, sai nima na fara nawa kukan da daga inda na ke tsaye, a raina kuma ina ta godiyar Allah.
*** *** ***
Haka muka wuni a cikin gidan kamar waɗanda akayi wa mutuwa, Sakina da Jamila ma sun lura da haka su kansu basa wani sakewa saboda ganin kamar muna cikin damuwa, Noor ne kawai yake ta sha'aninsa shi kan be ma damuba.
Washe gari kasa zuwa aiki na yi saboda na tashi jikina da kuma zuciyata babu daɗi, duk yadda Inna ta so naje sai na ƙi, su Sakina kawai suka je makaranta, mu kuma muna gida shiru-shiru babu wani motsin kirki da ɗayanmu ke yi, misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bilal ya kirani ina ɗauka sai ya fara tambaya miyasa ban je aiki ba, ni kuma na amsa masa da cewar babu komai, sai dai ban yarda ba yana ganin kamar ɗan ya ganni babu hijabi jiya ne yasa na yi fushi.
Jikin Habiba ya ƙara tsanani da yamma, har na ke bada shawarar mu kaita asibiti sai Inna ta ƙi saboda aganin asiri mu zai tonu.
“Idan mukaje asibiti zasu faɗa mana ciki ne, wanda nasan nan da nan za a ji a unguwar nan, ya kike so acewa Yakumbo da kuma mutane babban gida? Da wane ido zamu kallesu, yanzu zasu ce dan margayi ba shi da rai ne na ƙyale Habiba ta aikata wannan abun ni zasu ɗorawa laifi”
“Da ido da muke kallonsu Inna, tun bayan da aka gama amsar gaisuwa kin saki ganin ƙafar wani a gidan nan? Ba mu da nisa da su amman basu taɓa ɗauko ƙafa suce bari su leƙo mu suga ya muke ba, kowa harkar gabansa yake”
Ta yi shiru kamar ba komai kamar mai tunani can kuma ta kalleni
“Ni da wai na ce ko zubar da cikin zamu yi?”
Gabana ya faɗi, naji maganar kamar saukar aradu.
“A'a Inna idan muka je zubar da cikin ai dole za'aji”
“Ba asibiti ba wai gida”
“Taya zamu zubar da ciki gida?”
“Ƴan kayan ɗacin nan da ake badawa mana, tun da kin ga yanzu be yi ƙwari ba kuma a iya busa masa rai ba, idan har be zube ba sai mu ƙyaleta”
Na kasa cewa komai saboda na lura ranta ya kwaɗaitu da a zubar da cikin, duk da ina ganin zubar da cikin yana daga cikin alamomin rashin yarda da ƙaddara. Tausayin Habiba ne ya kamani sai na ji ina ma nice ba ita ba, hawaye suka zubo min sai na yi saurin tashi tsaye ina faɗin.
“Bari naje na siyo mata maganin zazzaɓi”
Inna ta amsa min da tau cikin yanayin damuwa, ɗaki na nufa na ɗauko Hijabina ina kallon Habiba take kwance malala kamar lakka.
Kamar na fasa kuka haka na fito ɗaga ɗakinmu bayan na ɗauko ƴan canjina na fita zuwa siyo mata magani, har na isa tunanin maganar Inna nake, ta yadda zan yi na hanata kawai na ke nema.
Bayan mum gaisa da mai shagon maganin sai na miƙa masa ɗari biyu na ce ya haɗa min maganin zazzafi kala-kala. Ya haɗa min kusa kala takwas cikin har da na malaria da na ciwon kai da na zafin jiki, ya ɗora min a saman gilashin da suke ɗora magani ni kuma na karbi leda na saka ina jiran canji.
Sai kawai na ga Mustapha cikin shagon kamar an jefoshi, matsawa yayi kusa da ni sosai yana min magana ta yadda babu wanda zai ji
“Ki yi haƙuri da abunda ya faru ranar nan, Wallahi ba da ke nake ba da mai Napep ɗin daya ɗauko ki na ke”
Ji na yi kamar ace akwai wuƙa kusa da ni na daɓa masa a ƙirji, wani ɗogon tsaki naja wanda ya jawo hankalin duk wanda ke shagon zuwa garemu, na ɗauki canjina na fice zuciyata na bugawa kamar zata fito saboda ɓacin rai.
NOT EDITED ⚠️
SHARE, COMMENT, VOTE.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣7⃣
‘Ba a banza ya baki haƙuri ba, taya zai baki haƙuri mutumen da ba ya ganin kowa da mutuncin, ba dake yake ba kika mareshi sai kuma yanzu ya zo ya baki haƙuri, lallai akwai abunda yake nufi da ke’
Shine abunda na ke ta saƙawa a zuciyata, a zahiri kuma sai nan nemin tsarin Allah akansa.
“Allah ka min tsari da sherinsa”
Har na iso gida ina ta saƙe-saƙen abubuwa biyu a raina, maganar zubar da cikin Habiba da kuma haƙurin da Mustapha ya ba ni. Na samu kaina da faɗuwar gaba sakamakon hango Bilal da na yi a tsaye ƙofar gidanmu, cikin rashin kuzari na ƙarasa daman can babu kuzarin a tare da ni. Lokacin da na ƙarasa kusa da ƙofar gidanmu sai na tsaya dai-dai inda yake tsaye ina masa sallama.
“Assalamu alaikum”
A maimakon ya amsa min sai kawai ya ɗaga idonsa dake ƙasa ya kalleni.
“Miya hana ki zuwa aiki yau?”
Ajiyar zuciya na fara saukewa sannan na haɗe yawun da ke bakina na fara magana a daƙishe.
“Bana jindaɗi ne”
“Miyasa baki kira kin sanar min ba?”
Yanzu kan bansan mi zan ƙara ce masa ba, shirun da na yi ne ya bashi damar fassara ni da abunda yake hasashe.
“Saboda kin yi zaton na ganki ko? Wallahi Nawancy ban ganki babu Hijab ba, lokacin sa kike aikinki ina can ina nawa aikin, ba zan miki alƙawari ba amman zan yi ƙoƙari na kawar da idona daga kallonki idan kina aiki”
“Wallahi ba saboda haka ba ne Bilal, kawai akwai abunda ya ke damuna”
“Ko zan iya sanin minene?”
“Sanin ba shi da amfani, barin wannan sirrin a cikina zai fi min amfani”
Magana nake kamar zan fara kuka saboda damuwar da ke raina. Shi kansa ya fahimci haka saboda be saba ganina cikin irin wannan yanayin ba.
“Allah ya yaye miki damuwarki Nawancy, Allah ya zama gatanki, ƴa shiga dukan lamarinki ya tsareki daga dukan sheri, ya jiɓɓanci lamarinki, kada Allah ya barki da kanki”
“Amin”
Na amsa hawaye na bin fuskata. Ya lumshe ido ya buɗe.
“Ki shiga ciki, ni zan wuce, daman na rubuta wasiƙa a gurin aiki amadadakin cewar baki da lafiya”
“Zan shigo gobe”
Na faɗa ina share hawayen idona.
“Karki dakurawa kan ki, and if you need someone to talk to i'm here”
“Thank you Bilal you have encouraged me every time, Without you I don't think I could ever be fine”
Na faɗa kuka na cin ƙarfina sosai. Har ga Allah ina jindaɗin zama da Bilal yana ƙarfafan min guiwa, yana damuwa da damuwata ko kaɗan baya son ganin ɓacin raina.
“Get some rest”
Na gyaɗa masa kai sannan na shiga cikin gida ina jin kamar na rafke na faɗi. Ɗakinmu na nufa jiki babu ƙwari, sai na samu Habiba a zaune tare da Inna kwanon ruwa na gaban Habiba jiƙe da magani. Na zauna nima ina buɗe ledar maganin.
“Gashi ya ce wannan uku zaki sha, wannan kuma biyu biyu sai wannan shi ma uku”
Na faɗa mata yadda ya rubuta a jikin kwalin maganin, sauran kuma duka na ɗiba ne, wasu biyu wasu huɗu.
“Tau ki bari har a jima ki sha, yanzu na jiƙa mata tagargade da gishiri ta sha”
Cewar Inna ni kuma na kalleta cike da mamaki.
“Tagargade da gishiri kuma Inna?”
“Ee yana yanke mara, wai ko za a samu cikin ya zube”
Wani dogon numfashi naja na sauke, na san ko na yi magana ba lallai ne Inna ta fahimta ba, idan har kuma nasa ta bar cikin a can gaba wani abun ƴa faru zata ɗora laifin a kaina.
“Bani maganin na sha ko zan samu sauƙin zazzaɓin nan”
Habiba ta faɗa tana miƙo min hannu. Tashi na yi na ɗebo mata ruwa na miƙa mata maganin ta sha, sannan na je na yi alwala har na yi sallah tunani ne a raina.
A tare da ita muka kwana a ɗakin, duk bayan minti biyu zuwa uku Inna sai ya miƙa mata tagargaden ta sha, haka ta kwana wulle-wulle sai abun ya zame mata biyu ga zazzaɓi ga ciwon ciki. Ita ke ciwon amman ni na kwana kuka ina jin zafin ciwon kamar a jikina ya ke, can kusan asuba Allah ya bata sauƙi har ta samu bachi.
Ni kuma na tashi da ciwon kai na yi alwala na yi sallah, ina zaune saman carpet ɗin ina karatun ƙur'ane har rana ta soma huduwa. Tashi na yi cikin ƙanƙanen lokaci na shirya na aika Sakina ta siyo kunu suka sha domin ni ko ruwa bana iya kaiwa a bakina.
Haka na kama hanya zuwa gurin aiki ba tare da na saka komai a cikina ba, duk kuwa da kasancewar ana cewa fita ba a karya ba bashi da kyau. Har na isa gurin aikin jina nake kamar ba ni ba, sai nake jin kamar ba ni nake motsa jikina ba, wata ƙila saboda nauyin da na tashi yana min yau ne. As usual sai da nayi duk abunda ya dace tun daga kan rubuta suna da time na yi komai sannan na shiga cikin kamfanin na soma aikina.
Ina daf da ƙarewa a ɗaki na ƙarshe, Amina ta shigo tana min magana kaɗan-kaɗan.
“Ƙawata ana kiranki, wai kin yi mopping da ruwa da yawa, matar nan sai masifa take”
“Wacece?”
“Wata mai'aiki a nan ce amman ita babba ce dan har office tana da shi”
Ba musu na bita muka tafi inda ta ce ana kirana ɗin wato a ɗakin dana fara mopping, abun mamaki sai na samu Zinatu tsaye a ɗakin tana sanye da suit da baƙin gilashi hannunta riƙe da wani ƙaramin akwati.
“Nawwara ke kika yi mopping ɗin gurin nan?”
Na ɗaga mata kai alamar Ee.
“Amman fisabilillahi haka ake mopping? Wai miyasa idan zaku yi abu baku yinsa tsakani da Allah, yanzu idan gidanku ne haka zaki yi, aikin nan fa biyanku za'ayi amman kuka abu da kissa kamar kyauta kuke yinsa haka sam be dace ba, yau da safen nan meeting zamu yi da manyan mutane yanzu idan suka shigo suka duba yadda kamfanin nan yake ai sai kuja mana ɓacin suna”
Yadda ta runtse ido take min masifa kamar bata san wacece ni ba, tabbas na bar ruwa saboda ga gurin nan har yanzu be bushe ba, sai dai ba da gangan na yi haka ba, na yi mopping ɗin ne a lokacin da hankalina baya gurin, sai dai ban jidaɗin yadda take ɗaga min murya ba kamar wata uwata.
“Ki yi haƙuri zan kiyaye a gaba”
Na faɗa abunda yake har a zuciyata shine, ƙawata sai dai a nan kuma ita ce babba a gurin aikina, kuma dole ne na bita idan har ina son cigaba da aikin.
“Better”
Ta furta tana ƙoƙorin juyawa sai ga wani mutun ya shigo shima cikin shigar suit sai dai na shi blue ne tsaɓanin nata da suke baƙaƙe. Har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya fasa sakamakon idonsa da suka sauka a kaina. Bakinsa a sake yake kallona fuskaraa na nuna alamun mamaki, hakan yasa kunya ta rufe ni domin tun da na shigo kamfanin a yau ban samu kaina da jin kunyar tufafin da ke jikina saboda damuwata ta mantar da ni komai.
Sai dai kallon da yake min ya ya karantar da ni da akwai wani abu, wata ƙila ya daba ganina da Hijabi yau kuma ya gan ni babu Hijabi ko kuma dai yana mamakin yadda na ke aikin ne, tau tsaya ma wai ni ina na san shi balle na yi tunanin haka ni dai fuskarsa bata min kama da wanda na sani ba, wata ƙila dai shi ya sanni ne kai sai ka ce wata ƴar film ko mawaƙiya.
Ni kaɗai na ke ta tsaƙe-tsaƙe na domin kuwa Zinatu ta daɗe da ficewa ɗakin, yanzu daga ni sai shi ne sai kuma Amina.
“Newcomer?”
Ya tambaya ni kuma sai na gyaɗa masa kai.
“Your Name?”
Ya sake tambaya.
“Nawwara”
Ya rausayar da kansa sannan ya sake kallon na from head to toe sai ya juya ya fice.
“Shine mai kamfanin?”
Ma tambayi Amina bayan ya fice, sai ta zaro ido.
“Tab mai kamfanin zai tsaya tambayar sunanki, ai yana zuwa gurin nan zai ɗaukeki mari sai kin manta hanyar garinku”
“Saboda me?”
“Saboda wannan kuskuren da kika yi”
Na taɓe baki.
“Ni kan ba zan yarda ya wulaƙanta ni ba, saboda kawai ina aiki ƙarƙashinsa”
“Aiko idan baki ɗauki wulaƙanci ba, baki shirya aiki a kamfanin nan ba, amman na ga mutumen kamar ya san ki”
“Ni ban ma taɓa ganinsa sai yau, da alama shima a nan yake aiki ko?”
“Shi ma babba ne a kamfanin nan, kuma ance suna shiri da mai kamfanin sosai wai amininsa ne, ko meeting ne idan be samu damar zuwa ba shi yake turawa”
Haka muka fito tana ta labarta abubuwa da dama akan kamfanin da kuma ma'aikatan gurin cikin har da Zinatu da take ita sabuwar zuwa, sai dai ita ta rigani zuwa da wata huɗu, yadda take ta yabon kirki da kuma halin Zinatu har sai da abun ya ban tsoro wata ƙila duk wannan mugun halin nata mu take yi ma shi mu da muke tsofin ƙawayenta.
Komawa na yi ɗakin na gyara sannan na dawo na cigaba da aikina, bayan na gama na fito na nufi gurin da ake rubuta suna na rubuta duk abunda ya kamata ina kamawa sai ɗaya daga cikin mutanen da suke reception ɗin ya miƙa min wata farar takarda, ya bani wani file wai na saka hannu, bayan na yi karɓa na nufo gurin da na aje Hijabi na ɗauka na saka sannan na kama hanyar fita daga kamfanin ina warware takardar.
Naira ɗari biyar ce a ciki sai kuma sunan Bilal a jikin wata ƙaramar takarda, na san ya yi haka ne saboda na nuna masa bana son na ganni babu Hijabi. Ƙasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskata murmushin da na manta rabon da na yi irinsa. Ƙamarar takardar mai sunansa na ɗauka na jeta a bakina na taune zuciyata cike da shauƙi Bilal.
Wannan shauƙin shi ya kawar min da komai na damuwata har na isa gida. Da sallama na shiga Jamila da Noor suka amsa min domin sune a tsakar gida, Inna tana ɗaki tare da Habiba.
“Miya hana ku zuwa makaranta?”
“Noor ne ya ce ba zai je ba”
Cewar Jamila kamin Noor ya karɓe mata.
“A'a Wallahi ita ta fara cewa ba zata je ba, Anti Sakina ce kawai ta tafi”
“Daman haka kuke so, idan bana a cikin gidan nan babu mai matsa muku kuje makaranta”
Da faɗan na shiga ɗakinmu, sai na samu Habiba ita kaɗai kwance ƙasa ƙafafunta lulluɓe da ƙaton kuma tsohon Bedsheet ɗin Inna.
“Habiba”
Na kira sunanta a hankali, sai ta ɗago ta kalleni amman da dukan alamu kamar bata cikin hayyacinta, domin alamu sun nuna hakan. Hannu na kai na buɗe bedsheet ɗin dake rufe da ƙafafunta sai ga jini a gurin kamar an juye jalkar manja, ba shiri na saki bedsheet ɗin na yi baya-baya dafe da baki ido a waje, zuciya mugun bugawa kamar an ce min ga mutuwata nan kusa da ni.!
NOT EDITED
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣9⃣
Inna ta kai hannu ta kwanto da fuskarta zuwa saman hannayenta tana murmushi. Haske sosai fuskar Habiba take goshinta ya soma taruwa da gumi.
“Allah ga yata nan, ta aikata kurkure kuma na yafe mata, ina roƙon ka Allah ka yafe mata, ka karɓi baƙuncinta, Allah ka zama gatanta bata da gata sai naka, yau ƴata ta koma gareka Allah kuma nasan ba ka yi dan ƴata ba, kuma ba kayi ƴata dan ni ba, Allah ga ƴata nan ta dawo gareka, ƴata mutuminyar kirki ce dukan abunda ta aikata ta aikata ne saboda mu, Allah ka yafe mata, haƙiƙa kai mai yawan gafara ne”
Inna ce take maganar tana shafa fuskar Habiba, hawayen idonta na zuba a fuskar Habiba. Sai kuma ta ɗago ta kalleni.
“Kin ga abunda na aikata ko Nawwara? Saboda gudun kunya na kashe ƴata, ba a tambayar Allah miyasa ya aikata abu, abunda ya ga dama shi yake aikata a sanda ya so ga kuma wanda ya so, amman da ace ni ce na mutu a wannan lokacin zai fi, ko ba komai ni naga duniya Habiba ko yanzu take tasowa, Habiba ƴarinyar kirki kin samu rana, mutane da yawa suna fatar mutuwa a cikin wannan ranar ta jumma'ah-”
Tsakanin Habiba da Inna sai na rasa wanda zan tausayawa, Habiba da ta bar duniya da ƙirciyarta ko kuwa Inna da zata shiga wani tashin hankalin a dalilin rashinta?
“Na rasa *RAI BIYU* Ran mahaufinku da kuma na ƴar'uwarku, na mahaifinku saboda zalinci na ƴar'uwarku kuma saboda talauci, Allah na gode maka”
Mai napep ɗin ya juyo ya kalletaa dai-dai lokacin da ya faka napep ɗinsa bakin ƙofar emergency,idonsa cike da ƙwalla ya ce
“Ta mutu ne?”
Sai ta ɗaga masa kai.
“Juya mu koma gida daman ta ce karna kawo ta asibiti”
“Da kin bari an dubata ko dogon suma ta yi”
“Jikina ya bani ƴata ta tafi har a bada, sai idan na iskota”
Shi ne ya matsa har aka fita da ita aka shiga da gawarta emergency, likitoci biyu suka dubata suka tabbatar mana da cewar ta mutu, sannan suka saka mana ita a motar ɗaukar gawa na asibiti saboda tausayin halin da suka ga muna ciki, mai Napep ɗin kuma ya ƙi karɓar kuɗinsa sai kuka yake kamar ƴar'uwarshi ce ta mutu. Ni dai bana iya aikin komai sai na kuka har muka iso gida. Jiniyar motar asibitin ce ta ɗago hankali kowa izuwa gidanmu, kan kace kwabo maza da yawa sun taru ƙofar gidanmu cikin har family Babanmu na babban gida, sai kuma family Inna maza da mata wanɗanda suke unguwar da kuma waɗanda bama da wata tazara mai nisa tsakanin unguwarmu da ta su.
“Miyasa ta? Tun yaushe ne bata da lafiya?”
Shine abunda kowa yake ta tambaya, masu kuka na yi, ciki har da kawayenta na makarantar islamiya da boko, tsakanin Sakina da Jamila bana iya banbance waye ya fi kuka a tsakaninsu, babu abunda ya fi bani tsoro kamar Noor da ya koma gefe ɗaya ya zauna ya natsu sosai ya kasa ko da guntun hawaye. Jidda ce ta shigo gidan da gudu tana ihu kamar zata tashi gidan, kuka take sosai tana kiran sunan Habiba kamar zata dawo da ita. Inna kan hawaye kawai take iya yi kamar yadda nima nake. Can kuma sai muka ji muryar Noor ya saka kuka ya yi waje da gudu yana kiran sunanta.
“Wayyo Mama Habiba-”
Ɗana ƙarami ne amman yasan mutuwa, yasan duk wanda ya tafi baya taɓa dawowa yasan ya yi rashin uwa har abada...!
Ƙanwar Bilal ta biyu ce Zulaihatu ta shigo tana kuka sai ta kama hannuna.
“Taso muje gida Bilal ya ce na zo da ke”
Bana iya uh bale uh uh tana jan hannuna na bita kamar babba da yaro ina ƙwalla ita kuma tana kuka, har muka isa gidansu. Gidansu Bilal irin babban gidan nan ne mai yalwa amman ba sosai ba, ba kuma irin na masu kuɗi ba na masu rufi asiri dai-dai gwagwado, gidane da ke cike da ƴan mata daga ƙanensa da kuma cousins ɗinsa da ake riƙo gida wasu saboda suna makaranta a sokoto wasu kuma zaman ne kawai, sai kuma Mahaifiyarsa da kishiyar mahaifiyarsa, da ƙanwar babansu wato Gwaggo Rabi.
Sun tausaya min sosai sun nuna kulawarsu a kaina, daga iyayen har ƴan matan da suke gida, a falon kishiyar mamansu aka fara shiga da ni na zauna sai kuma wata cousin ɗinsa ta shigo ta fita da ni zuwa ɗakin Bilal dake can gefen ɗakunan mazan gidan kuma a farkon shigowa gidan.
Kamshin turarene ya fara yi mana murhbun sai kuma lallausan carpet, ya gyara ɗakin kamar na mata komai akan tsari kamar na wani babban mai kuɗi. Wutar daƙin da kunna duk da kasancewar ɗaya da rabi na rana ya yi.
A saman gadonsa ta zaunar da ni har ta juya sai kuma ta juyo ta dawo ta kwantar da ni saman gadon kaina akan matashin kai, sannan ta ce
“Ya Bilal ya ce a kawo ki nan saboda gudun hayaniya”
Ta juya ta fice. Ƙaton hoton Bilal da ya yi da Noor nake kallo, a zahiri hoton na ke kallo amman hankalina yana can gurin Habiba da Inna. Zuwa can na lumshe ido bachin wahala ya yi gaba da ni.
Ko da na farka dishi-dishi na fara gani kamin na ga dai-dai, Bilal ne zaune gurin kaina idonsa na kaina Noor kuma na bayana yana bachi sai faman sauke ajiyar zuciya yake yana wani ɗaukar numfashi, da alama ya yi kukan ne har ya gaji.
Kallo kallo muka riƙa yi ni da Bilal ni na kasa tashi daga kwance da nake, shi kuma ya gagara motsawa har sai da yaga idona ya fara zubar da ƙwalla.
Sai ya yi saurin kai hannunsa for the first time ya riƙa ya tayar da ni zaune, babu wani kuzari a jikina ko ƙire ji na ke kamar ba ni ce ba, fashewa na yi da kuka sai ya yi min masauki a ƙirjinsa ya rungume tsantsan.
“Shiiiiiiiii”
Rarrashina ya ke amman ji nake kamar yana ƙara min ƙarfin kuka, ban lura da shafa baya da yake alamar rarrashi ba sai da kukan ya tsagaita min, sai na yi saurin barin jikinsa na miƙe tsaye, shi ma ya miƙe tsaye yana kallona.
“Ina zaki je?”
Ban iya amsa masa ba na juya ina kuka, sai ya y hanzarin kai hannu ya juyo da ni ya rumgume a karo na biyu, a nan na rushe da kuka muka durƙushe da a ƙasa tare ni ina kuka shi kuma yana hawaye suna sauka saman kaina.
Wata irin natsuwa da kwanciyar hankaline suka ziyarce ni, na ji daɗin rumgumar da ya yi daman i need some shoulder to cry, har ga Allah na san ba dan wani abun Bilal ya rungume ni ba sai dan rarrashi da kuma tausayi, hakan yasa na sake jiki na yi kuka iya yadda zan iya sannan yasa handkerchief ɗinsa ya goge min fuska yana shafa saman kaina kamar wata yarinya.
“Shiiiiiii karki tashi Noor, daker na samu ya yi bachi”
Gunɗe bakina na yi na lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata, yanayin Bilal yana min kamar na tsohon mijina wato Margayi Faruk, yau a bayar tafiyarsa wani namiji mai natsuwa da kamala ya rumgume da har na samu natsuwar da na kasa samu a farkon aurena, sai dai wannan ba da ijiya uku ya rumgume ni ba. Tuna wannan yasa na yi hanzarin barin jikinsa, duk yadda ya so ya tsayar da ni sai na ƙi a dole ya biyo bayana yana min magana amman ban kula shi ba har na bar gidan.
JUMMA'AT MUBARAK...😘
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣8⃣
Na yi saurin rufe bakina idona cike da hawaye na nufi waje da gudu, ɗakin Inna na shiga ban sameta a ciki ba, ina fitowa waje Inna na fitowa daga banɗaki tana riƙe da buta. Kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai ta nufi ɗakinmu, ni kuma na rufa mata baya hankalina a tashe.
“Inna kin ga halin da take ciki kuwa?”
Ya gyaɗa min kai.
“Ko minti talati ba ki yi da fita ba, ta fara zubar jini ina jin cikin ne yake zubewa”
Tsugunawa na yi a gurin na dafe kai ina hawaye.
“Inna bata cikin hayyacinta”
“Dole ne zata yi haka saboda wannan ne na farko kuma kinga yarinya ce, amman zata warke zata dawo lafiya ƙalau”
“Inna dan Allah mu kaita asibiti”
Na faɗa ina fashewa da kuka, sai ta ce
“Babu inda zamu je Nawwara, zata warke”
Ta janye bargon ta soma gyara mata jiki ni ko ina duƙe a gurin ina aikin kuka. Haka muka wuni muka kwana babu wani canji sai ma ƙari, tun ina ganin tausayinsa har zuciyata ta fara raya min wasu abubuwa marasa kyau. Ita kanta Inna ta soma tsorata ganin mun kwana da ita a haka babu wani canji, ni ko na kasa zuwa aiki saboda ina ganin kamar idan na je na barta zan dawo na tarar ta mutu, ina jin kamar idan ina kusa da ita babu abunda zai sameta.
Can da yamma abun ya fara zuwa da sauƙi da har ina maganar ko Inna bata so sai na ɗauke ta na kaita asibiti saboda gudun kunya ba zan bar ƴar'uwata ta mutu ba.
Jikin nata babu ƙarfi amman hankalinta ya dawo, har ma ta ɗan jiro hannunta kaɗan ta ɗora saman nawa, kasancewar ina zaune ne kusa da ita saman tabarma. Numfashi take wahalce gaba ɗaya idanuwanta sun canja kamar wata tsohuwa.
“Sannu Habiba”
Na faɗa cikin muryar kuka ina mai tausayin ƴar'uwata, sai ta yi min murmushi hawaye ya fito daga gefen idonta.
“Ina Inna?”
Ta tambaya daker cikin muryarta na marar lafiya.
“Taje maƙota zata samo miki lafiya dubu”
Ta yi shiru tana lumshe ido, hakan yasa na tashi na ɗebo mata ruwa, na ɗan ɗaga kanta na kai mata kofin a baki, ba laifi ta sha da yawa kamar zata haɗe kofin har mamaki na yi na ce.
“Na ƙaro miki?”
Sai ta girgiza kai alamar a'a, sai ta rufe idonta tana numfashi a hankali. Ganin haka yasa na miƙe tsaye domin naje na kira Inna sai na ji ta kira sunana.
“Nawwara...”
Sai na koma na zauna ina kallonta.
“Na'am”
Na amsa ina kallon idonta dake rufe.
“Ance mace data mutu gurin haihuwa ana kyautata mata zaton samun aljanna saboda ta yi shahada, tau idan kuma mace ta muru gurin zubar da cikin banza fa?”
Ji nayi kamar jiri ya ɗibeni, hawaye uku-uku ya soma sauko min, ta farkon ido da kuma tsakiya, sai kuma ta gefen ido. Me Habiba take nufi ne? Wannan wace irin tambaya ce take min haka? Bakina a sake nake kallon yadda take numfashi. Ina haka Inna ta shigo, da fari gabanta ya faɗi ganin hadda hawaye suke min zuba sai dai ganin Habiba ta buɗe ido yasa ta ɗanji sanyi har ma da yin murmushi ta zauna kusa da ita tana nuna mata kulawa irin ta ƴa da uwa. Ta tsorata lokacin da takai hannu ta gwale idon Habiba, ya yi ɗorawa kamar marar jini, sai ta kalleni.
“Kamar bata da jini”
Kai kawai na iya gyaɗawa mata, sai ta miƙe tsaye da sauri tana kiran Sakina.
“Sakina zo ki siyo mata maltina da madara ta sha kamin muje asibiti”
Da gudu ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta bada a siyo mata maltina uku da madara ta bata, sai kuma ta dawo ta zauna kusa da ita tana kuka.
“Na yi wauta Habiba yanzu zan kai ki asibiti, ban ɗauka abun har ya kai haka ba, kin zubar da jini da yawa”
A wahalce Habiba ta soma magana.
“Karki kai ni asibiti Inna, ko kin kaini mutuwa zan yi, kuma mutane zasu ji, na barku da damuwa, ƙara baki je ɗin ba domin Wallahi mutiwa zan yi-”
Na yi saurin kai hannu na rufe mata baki, sai ta lumshe ido, Inna ta tashi a firgice ta fita daga gidan tana kuka, kamar jira take na janye hannuna daga bakinta sai ta ce.
“Nawwara zan tafi na barki ke kaɗai...”
Na sake rufe mata baki ina kuka. Sai ga Inna ta shigo.
“Riƙata ga Napep can na na tsayar zamu kaita asibiti”
Kamar waɗanda suka ɗauki takarda haka muka ɗaga Habiba, jikinta ya yi sanyi sosai ƙwayar idonta baƙar ta ɓata ɓat sai farin kawai kake gani. Cikin hanzari muka saka mata wasu tufafin muka saka mata Hijabi muka ɗauketa sai gurin mai Napep.
Muna shirin shiga Napep ɗin Sakina ta dawo daga siyen madara da maltuna, tsabar hankalin Inna ya ɗauku bata ko iya karɓa ba muka kama hanyar asibitin uduth dake gawon nama, duk da da kasancewar mun san asibitin ta kuɗi ce.
Gudu sosai mai napep ɗin ke yi amman kasancewar tsakanin unguwarmu da asibitin uduth akwai ƴar tazara sai da tafiyar ta yi mana nisa. Muna isa bakin gate ɗin asibitin, Habiba ta sauke wani irin ajiyar zuciya ta kwanto da kanta dake jikina zuwa jikin Inna, rai ya yi halinsa ƴar'uwata ta amsa kiran mahaliccinta...!
I will updated 19 tomorrow morning.
RIJF Habiba😭
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣0⃣
I dedicated this chapter to each and every RAI BIYU fan's, especially RAI BIYU CONVERSATION and RAI BIYU FAN'S GROUP together with KHADEEJA CANDY NOVELS. Thank you so much for your lovely and meaningful Comments. Son So Fisabilillah 😘
•••~•••
Ko da na isa gida na tarar ƴan'uwa da masu karɓar gaisuwa suna Sallah la'asar, ashe huɗu ta yi ni ban ma sani ba kasancewar na kwanta ne a lokacin da ba a fara zuwa masallaci ba. Ba zan iya kwatantan yawan mutane da na tarar a gidanmu ba, daga ɗakinmu har ɗakin Inna da tsakar gida cike ya ke da ɗan adam, hakan ya tabbatar min da an kaita gidanta na gaskiya kenan. Duk yadda na so na danne kukana sai na kasa saboda raunin zuciyata, kuka na ke haƙuri ake ba ni amman kamar wuta da fetur na zama, haƙuri na ƙara min kuka, daker mutaneɓ suka rarrasheni har wasu suka samu damar yi min gaisuwa, da yawa na ji suna faɗar dole zan yi kuka saboda shaƙuwar da ke tsakaninmu da Habiba.
Bana iya kwatanta yawan mutane da ke ta zuwa gaisuwa ba, tsakanin ita da Baba bana iya banbance waya fi yawan jama'a, tun daga maza har mata, ta samu addu'ah da yabo sosai, kowa ya ji mutuwar Habiba har ma da waɗanda basu danta ba gani ko kuna jin ta rasu haka kawai babu wani ciwo. Ban tabbatar da na yi rashin ƴar'uwa ba sai da dare ya yi naga inda take kwantawa babu kowa sai matashin kanta, da kuma komatsan kayanta a gefe, ban san lokacin da na fashe da kuka ba sai kuma dariya ta biyo baya, wata ƙanwar Inna ce ta shigo ɗakin ta fita da ni zuwa ɗakin Inna, amman har lokacin ban bar kuka da dariya ba, ni kaina zan iya cewa na kusa na haukace ne a wannan lokacin.
Addu'ah suka riƙa min suna tofa min har sai na dawo ina kukan kawai babu dariya, kuka ne ya saka Inna kuka, ni da ita aka rasa mai rarrashin wani. Ni da Inna ba mu runtsa ba sai dai ƙannenta ne suka samu suka yi bachi, ni kuma na tashi na raya dare ina tayi ma Habiba da Baba addu'ah da kuma Faruk, sai mutuwar ta dawo min ta yi min tsaye, duk mutanen da suka da muhimmanci a rayuwata ina ta rasa su.
Ka rasa mahaifina sai kuma na ƴar'uwata, na rasa RAI BIYU masu muhimmanci a rayuwata, kuma duk a cikin shekara ɗaya.
Har aka yi kwana ukun Habiba aka gama bana aikin komai sai kuka, bana iya cin komai sai ruwa, a wannan babin kan na yarda Inna ta fini tawwakkali domin da kanta tana kan zauna na bani haƙuri tana min maganganu masu tausasa zuciya, amman na kasa jurewa wannan ƙaddarar kan na saka ɗaukarta, a kowa ne dare gani nake kamar Habiba zata dawo, bana da mafarki sai nata, da naja numfashi na sauke addu'ah nake mata, ƙiriƙiri bachi ya gagareni duk dare bana iya bachi har garin Allah ya waye, wani lokacin Bilal ya kan shigo har cikin gidan saboda bana fita ya riƙa min nasiha yana jana da hira wai ko zan sake amman ina na kasa kai zuciya nesa, Jidda ma ta yi iya yinta har ta gaji ta sa min ido.
Haka na kwashe sati biyu babu wani canji tsakanin ni da Noor domin shi ma idan yana bachi kiran sunanta yake, idan zai ci abinci sai ya ambaci sunanta saboda mun saba cin abinci tare, da an taɓa shi ya buɗe baki yana kiran Mama Habiba. Ranar da ta cika kwana goma shabiyar a ƙabarinta ina zaune waje ina karatun ƙur'ane Noor ya kwanto jikina yana kuka.
“Momy miyasa idan aka mutu ba a dawowa?”
Kallonsa na yi, da farko rasa na yi mi zaɓ ce masa sai kuma na yi ƙarfin halin ba shi amsa.
“Haka Allah yaso, kuma duk wanda ya samu lahira baya ƙaunar dawowa duniyar nan, sai dai mu iskeshi”
“Momy nima ina son na mutu naje inda Mama Habiba, kullum ina mafarkinta bana jindaɗi idan bata nan”
Ya faɗa yana kuka, sai na rufe ƙur'ane na aje gefe na kwantar da kansa saman cinyata ina shafa kansa, shi kuka ni kuka.
Na yi kuka sosai har sai dai na jawa kaina ciwon kan da ban taɓa irinsa ba, domin har cikin ƙashin bayana yaƙe sauko min, a ranar bana iya ko da motsin kirki har sai da aka kira wani nurse ya duba ni ya bani magani. Wasa wasa ciwo ya fara min yawa yau ciwo gobe lafiya tun abun be kama Inna ba har ya soma bata tsoro, sau biyar ana min ƙarin ruwa amman kamar zubarwa ake, duk nabi na rame na lalace farar fatata ta soma ɗuhu, gashi bana iya cin komai.
Haka Inna zata saka ni a gaba tana kuka tana cewa ni ma rasa ni zata yi, damuwar da nake ganin tana ciki ne yasa na ragewa kaina tunani ta yadda zan samu na riƙa cin abinci ko da kaɗan ne, domin nurse ɗin ya faɗa min matuƙar ban daina tunani ba ba zan taɓa jin sauƙi ba, kuma ba zan taɓa iya cin komai ba, idan zan kwanta sai na shimfiɗa zanen da Habiba take shinfiɗawa na yi matashin kai da fillonta hakan yasa sai ma ji kamar tana kusa da ni.
Da addu'o'i da ƙarfin hali na fara samun sauƙi, cikin sati ɗaya na koma normal sai dai ban iya maida jikina ba, lafiyata ma bata dawo gaba ɗaya ba, amman Alhamdulillah na dawo cikin hayyacina ma miƙa lamarina ga Ubangijina, har na kan fita naje gidansu Jidda saboda rage kewa, Bilal kuma ya yi min sallama na fita mu gaisa na tattara komai na adana a zuciyata, na tabbatar da ace ana buɗe zuciya da tawa zuciyar idan aka buɗe ba za a tarar da komai ba sai damuwa, baƙincikin, tunani, da kuma hudu na rashin RAI BIYU da na yi.
Walwalar da nake tasa Noor ma ya sake har yana sawarsa da yara, sai dai duk da haka idana ka masa wani abu sai ya shigo yana kuka ko ya ce da Mama Habiba na nan da yanzu ta rama masa, Sakina ce ta ɗauke halin Habiba a gidanmu duk wani aiki da Habiba take Sakina ce take yinsa a yanzu, Noor ma idan aka masa wani abun itace kan gaba wajen magana, sosai take ɗauke min kewar Habiba daman suna kama sosai da Habiba ta fuska da kuma ta magana, inda suke da banbanci Habiba tana da tsawo ya yinda Sakina take gajeruwa sai dai ba can sosai ba.
A kwana a tashi hasarar mai rai! Wasa-wasa kwanaki suka soma ja, har Habiba ta haura wata ɗaya da rasuwa, a zuwa yanzu kan mun fara sabawa da rashinta, sai dai duk da hakan kewarta bata bari na bachi har sai na kwantar akan shinfiɗarta. Ranar da Inna ta fita wanka, wato ta gama taƙaba sai mutuwar Habiba da ta Baba ta dawo mana sabuwa. Mutane da dama kama daga ƴan'uwa, maƙota abokan arziki suyi ta shigowa suna mana barka da fita wanka da Inna ta yi lafiya. Sai dai babu Family Bilal ko ɗaya da ya zo mana barka da fita wanka, hakan be bani mamaki ba daman can na san ƴan gidansu ba son alaƙar dake tsakanin mu suke ba.
Bilal kan sai dare ya zo, ya kawo ma Inna atamfa vilisco ta dubu biyar da kuma wax ita ta dubu biyar da Hijab mai kyau yadi huɗu, sai turaruka da man shafawa da kuma kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, abunda yan uwan Babanmu suka kasa yi, ko atamfar roba ka rasa wanda zai siyo ya kawo ma Inna da suna ta saka na fitar wanka saboda rashin haɗin kai da kuma halin ko'in kula nasu.
Duk yadda Inna ta so ta rage kaya sai Bilal yaƙi yarda wai idan har ta mayar masa hakan na nufin bata ɗauke shi ɗa ba. A bakin ƙofar gida muka tsaya muna fira da shi, a nan yake min zancen aikina wanda ni har na watsar da lamarin.
“Ya kamata ki koma kin ga idan kina fita zaki fi sakewa, kuma ita kanta Inna zata ji daɗi”
“Amman Bilal ni aikin ya fita daga raina ma”
“Aiko yanzu ne ya kamata aiki ya shiga kanki domin Sakina da Jamila da Noor suna da buƙatar taimakonki, ga kuma Inna”
Gaskiya ya faɗa tun da bamu da wasu ƴan'uwa masu son taimako dole ne mu tashi mu nemi namu, daman hausawa na cewa ‘indan ma ɗan'uwa nemi naka’
Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi duk da kasancewar ba zan iya ganinsa ba saboda babu hasken farin wata, ita kan wutar nepa na manta rabon dana ganta a gidanmu domin an daɗe da yanketa, sai dai idan maƙota sun kunna wuta hasken gulob ɗinsu na haska gidanmu musamman masu gidan samman nan dake kusa da mu, sai dai yau basu kunna ba sakamakon babu wutar gaba ɗaya a unguwa.
“Amman basu kore ni ba? Na daɗe ban zo ba”
“Na basu rahoton cewar baki da lafiya, dan haka idan kin shirya zuwa kije kawai”
“I will try”
Na faɗa ina tsotsa lips ɗina. Bayan zancen aiki sai kuma muka ɗora da wani zancen na daban, ba laifi na saki jiki mun yi fira har da dariyata kamar ba ni ba, da wannan na yarda cewar zuciyata ta fara zaurancin son Bilal domin ina jin nishaɗi a duk lokacin da muke tare da juna, ko sunansa na tuna sai na samu kaina cikin hauƙi da murmushi.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan na shawarci Inna akan maganar aikina, na yi zaton zata hanani ne ko tace wani abu sai naga ta nuna farinciki sosai har tana ce min wai na fara dawowa a mutun ɗinta, farincikin dana gani a tattare da ita ne ya ƙarfafa min guiwa na yi jimmar wanke uniform ɗina na zuwa aiki.
Washe gari na shirya tsaf na ɗauki Hijabina na saka, sai kuma na buɗe jakar da nake aje tarkace na na ɗauko ƙaramin hoton Habiba na saka a aljihu, hakan zai kwantar min da hankali kuma zai ƙarfafamin guiwa domin a duk lokacin da nake kusa da wani abu da ya danganceta ina jin kamar ƴar'uwata tana kusa da ni.
Sai da na yi ma Inna sallama sannan na fita bayan na yi addu'ar fita daga gida. Bana baƙinciki ba farinciki na isa gurin aikin, kamar yadda nake a baya, sai da na fara zuwa na rubuta sunana da lokaci na aje hijabina da wayata a inda aka tanada domin aje irin waɗandanan abubuwan sannan na domin sai sannan na nufi gurin aikina, ina cikin aiki na ji muryar wani namijin yana faɗin
“Khadija Musa Kafinta you're fired”
Da sauri na juyo na kalli mai maganar yana sanye da black suit hannunsa riƙe da file.
“Saboda me?”
Na tambaya cike da mamaki.
“Saboda rashin zuwa da kika yi, shugaba baya son haka, kuma ya ce be yarda da rahoton da aka bada cewar baki da lafiya ba”
A take raina ya ɓace sosai, taya zai ce be yarda ba shi beda uzurine hala! Sai da na fara aiki za a ce an koreni, ni ko ba zan yafe haƙƙina na kwana biyu da na yi ina aiki ba.
“Na ji an koreni amman a bani kuɗina na aikin da na yi na kwana biyu da rabi”
“Kwana biyu da rabi?”
Ya maimaita fuskarsa a haɗe.
“Ee ai na yi aiki sau biyu a wannan kamfanin kuma yanzu na yi rabin aikin, dan haka a biyani haƙƙina”
Ta yadda na yi masa maganar ya fahimci ina cikin zafin raine, domin a hasale nake ina katsa masa tsawa, yasan duk ya yi wasan sake ce min wani abu zan haukace masa ne.
“Kije hawa na biyar bi faɗawa mai kamfanin, ba ni zaki faɗawa ba”
Ya faɗa yana juya ya fice, ni kuma na bishi da bala'i ina cewa.
“Ai kai ya aiko dan haka kai zan aika”
Can kuma na soma tambayar kaina, wai shi wannan mai kamfanin wane irin mutun ne, miya ɗauki mutane ne? Aiko Wallahi ba zan iya yafe masa haƙkina ba ko da be bani kuɗin ba sai na faɗa masa marar daɗi sannan na bar kamfanin.
Haka na kuɗiri aniyar sai na nuna masa ahi ba kowa ba ne, kai ina ma son ganin shi wane irin hallita ne da yake wulaƙanta ɗan adam, wato shi wannan yana tunanin kamar ba zan iya ba shiyasa na ce naje ko?
“Aiko zan baka mamaki”
Na faɗa a fili, sai na saka ƙafa na yi shuri da bokitin da nake mopping ɗin ruwan suka watse a ƙasa na fice a fusace. Kai tsaye na nufi gurin da lifted take na danna ta buɗe sai na shiga na danna 5. Gadan-gadan na fita daga lifted babu tsoro ko kaɗan a tare da ni, wannan gurin ma kamar wacan yake sai dai wannan ko wane office a kulle yake, an yi rubutu an laƙa a saman ƙofar. Ɗaya bayan ɗaya na riƙa bin ɗakunan ina duba wai ko zan ga wanda aka yi wata alama ta mai kamfani amman ban samu ba. Har na juyo sai ga wani mutume ya fito daga wani ɗaki riƙe da files, tsaidashi na yi ina tambayar office ɗin mai Kamfanin.
“Lafiya kike nemansa?”
“Shi ya aika ya ce yana nemana”
Wani kallo ya yi min daga sama zuwa ƙasa sannan na kalli sunana dake rataye a wuyana.
“Sai kin hau Excavator can, zaki ga Office guda uku jera, a na tsakiyar zaki tsaya akwai wani maɓalli a gurin sai ki danna”
Sai da ya gama min kwatancen sannan na lura Excavator ɗin dake can gefen dama da offices ɗin.
“Na gode”
Na faɗa inanufar gurin, shi kuma ta bi bayana da kallo. Ni ban kula shi ba na hau Excavator ɗin. Ina kawowa sai na hauye saman tile ɗin na ƙarasa gaban offices dake jera, a na tsakiyar na tsaya, dama na ni na hango maɓallin da yake magana a kai na kai hannu na danna.
Wata ƴar tsuwa na ji sai wata fitila ta hasko saman kaina.
“What do you want?”
Muryar namiji ce mai tambayar, kaina na ɗaga saman ina kallon camera dake ɗaukata.
“Ina son ganin oganku ne”
“Ur Name?”
“Nawwara”
Bayan na bashi amsa da kamar minti biyu sai ya ce.
“You don't have an appointment with him”
“Amman shi ya ce yana son gani na”
Na faɗa a tsawa ce ina kallon camera kamar ance mutumem ne a gabana.
“Sorry Ma'am you're not in the list”
“But he's the one who tell me to come and meet him here”
Na faɗa cikin turancina na yan ƙaramar makaranta. Sai kawai ƙofar ta rabu biyu ta buɗe min, da ɗan tsoro na kutsa kai ciki sai na gano ashe cikin wani ɗan kumbo ne na ke ciki, sai da kumbon ya gama scanning ɗina sai muryar ta sake min magana.
“Keep your passport inside the box”
Muryar ɗazu dai ce ta yi min magana, sai na saka hannu na ciro hoton Habiba na saka cikin wani ɗan ƙaramin akwati dake gefena, sannan ƙofar ta buɗe min tana min WELCOME.
Wani ɗan madaidaicin Office ne na samu kaina ciki shi ba babba ba kuma ba ƙarami ba, an ƙawatashi da kayan alatu, da gangan na hana idona kallon wasu abubuwa na office ɗin saboda karna manta abunda ya kawo ni.
Matashin Saurayi ne zaune saman kujerar dake office ɗin, laptop biyu a gabansa a daga gefensa kuma desktop computer ce a aje, can nesa da shi kuma an jera wasu desktop computer har biyu da kujerarsu daban. Can a farko shigowa office ɗin an jera kujeru masu kyau na san ba zasu wuce na zaman baƙi ba. Matsawa na yi kusa da shi da jimma na fara masa masifa domin a haukana na ɗauka shi ne mai kamfanin, sai ya rigani magana.
“Stay where are you, i have to call him first”
Telephone ɗin dake kusa da shi ya ɗauka ya fara danna wasu numbobi, hakan yasa na yi janzarin ƙarasawa kusa sa shi sosai.
“Sir a young lady... ”
Yana fara magana na fisge telphone ɗin na fara tawa maganar domin nasan idan har ya faɗa masa zai ce shi be san da zuwana ba, ba zasu bani damar magana da shi ba.
“Azzalumi macuci, ka koreni ai sai ka bani kuɗin aikin da na yi na kwana biyu da rabi kuma kaima baka wuce Allah ya ɗora maka ciwon ba-”
“Nawwara...-”
Ɗaga can cikin wayar ya ambaci sunana. Tun da muryarsa take daki kunnena yawun bakina suka tsinke, kaina ya fara jiri wani abu na ji na tsikareni tun daga saman kaina har cikin ɗan yatsan ƙafata, gaba ɗaya jikina sai ya mutu. Mutunen nata ƙoƙarin fisge telphone ɗin daga hannuna sai na saka masar na juya da gudu na nufi inda na ke hango wata ƙofa dake can dama da teburin mutumen amman nesa da shi.
Da gudu na banki ƙofar na shiga, sai na samu kaina cikin wani irin ƙaton office mai cike da sanyin ac. Yana hakimce saman kujerar alfarma wani irin ƙaton tebur mai takardu da kayan kawata teburin office haɗi da system na gabansa.
Ji na yi kamar ana zooming ɗina a take hawaye suka fara bin fuskata, na san idona ba gizo suke min ba, ba mafarki na ke ba.
Daga saman kujerar da yake zaune ya ɗagawa secretary sa dake ta kokuwar fitar da ni hannu, ya yi masa alama da ya fita sai ya juya ya fice yana ja ƙofar office ɗin. Shi kuma ya taso da sauri ya doso inda na ke yana kira sunana muryarsa har rawa take.
“Naaa...Naww...Nawwarraa....”
Tafin hannuna na kama taɓa sai ya yi saurin kai shi gefen fuskarsa ya lumshe ido, sai hawaye suka zubo masa.
Fisge hannuna na yi ina yin baya-baya, Tabbas shine, shine mutumen da ya yi nasarar canja ni daga mutum zuwa mutum mutume, shine mutumen da ya ce yafi ƙaunar ganin mutuwarsa sama da ni, shine mutumen da ya kirani ƴar talakawa marar daraja, shine mutumen da daya wulakanta ni ya sani a rana kuma yasa duniya ta zargeni, shine muteme da ya yanke min duk wani jindaɗi ma rayuwar duniya, shine mutumem da ya fara saka ni a ɗakin kuka da baƙinciki.
Kai na nake girgizawa ina cigaba da yin baya-baya shi kuma yana matsowa kusa da ni, duk ya rikice kamar zai cinye ni, idonsa har sun soma canja kala, jikinsa na ta rawa hawaye kuma na ta aikinsu a fuskarsa.
Muna haka Mutumen da ya taɓa tambayar sunana a wacan lokacin da na ke aiki ya shigo, shi ya kai hannu ya dafe masa ƙirji saboda kar ya ƙaraso kusa da ni, ni kuma na juya da gudu na fice ina kuka, ina jiyo sautin muryarsa yana kiran.
Da kuka na sauko ƙasa na ban tsaya saka sunana ba na nufi gurin da Hijabi ya ke tare da wayata na ɗauka na saka na fice ɗaya ɗaga cikin mutanen da suke reception na ta kirana wai na zo ga saƙo amman nayi banza da shi ina ta aikin gudu da kuka.
Sai da na yi nisa da kamfanin sannan na fara tafiya ina hawaye, tare da tambayar kaina wasu tambayoyin da ba ni da amsar su.
‘Shi da yake likita miya kawo shi nan? Daman ƙamfanin na su ne? Daman shi ne mutumem da Bilal yake faɗa min, miyasa ban gane shi ba a lokacin da Bilal ya faɗa min suna da Asibiti? Na taɓa jin ƙamshin turarensa miyasa ban ga ne shi ba? Ya faɗa min yana da tattoo miyasa ban ga ne shi ba?’
“Lallai ke wawuyace Nawwara”
Na furta a fili hawaye na min zuba, yau kan ƙasa na kama hanyar gida duk kasancewar akwai tazara mai tsawo tsakanin unguwarmu da kuma inda kamfanin ya ke, amman baƙincikin da ke raina ba zai bari na iya tsayawa na tari abun hawa ba.
Ƙarar tsayawar motarsa ce ta riƙa ta dawo min kamar a yanzu ne abun ya ke faruwa, irin yadda ya fisgoni ya jefar gefen titi ne ya riƙa min yawo a ƙwaƙwalwa.
Wani irin jiri ne na ji na ɗibeni sai na ji ƙafafuna kamar an cankesu an ja ni, duhu na soma gani, ko kamin na kai ƙasa numfashina ya daɗe da barin jikina.
___________________________________
Dogon shafi kamar yadda kuke bukata 😂
Dan haka nima dogon comment na ke son ji idan ba haka ba next chapter sai nan da one week kuma short chapter 🤷
Ko wanenen wannan mutumen ne? Bari nima na bi Nawwara na sha labari 😉
#COMMENT
#VOTE
#SHARE
0 comments:
Post a Comment