*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣1⃣
JIBRIL POV (Point of view).
Sanyi da yaji a tafin hannunta ya tabbatar masa da ita ɗin ce, hawaye ke zuba a idosa ba tare da ya san suna zuba ba, baya-baya take tana hawayen da yake jin ɗigarsu har cikin ransa, a hankali ya ke maye duk wani footsteps nata da take backwards, ga wani irin abu da ke jansa na ɗimaucewa da al'ajab ɗin ganinta kamar zai fita hayyacinsa he just can't believe Nawwara ce yau a gabansa.
Shigowar Siraj ya bata damar fita da gudu, shi kuma ya yi hanzarin binta sai Siraj dakatar da shi, ta hanyar ɗora hannunsa saman ƙirjin Jibril.
“Calm down Jibril”
Be saurari abunda ya ke faɗa ba ya ƙwala ma Nawwara kira da dukannin muryarsa yana mai jin kamar ya yi tsalle ɗaya na fisgota. Ya sauke idonsa da suka yi ja suka rine akan Siraj yana ambatar sunan Nawwara cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai.
“Nawwara ce fa”
“I know”
Siraj ya amsa masa yana ta matsar da shi baya har ya zaunar da shi saman tebur burinsa.
“Nasan zaka haɗu da ita tun ranar da na yi arba da ita tana aiki a kamfanin nan, ni ma dan bata san ni bane yasa ta zauna da ace ta san kamfaninka ne ba zata yi aiki a nan ba”
Cewar Siraj Hannayensa akan kafaɗar Jibril, sai ya ture masa hannaye yana masa kallon mamakin furucin da ya taɓa masa a can baya.
“Miyasa ka ce min ta mutu? Kasan iya shekarun da na ɗauka ina nemanta? Saboda ita na aminta na yi aiki nan saboda kawai ta taɓa rayuwa a nan garin, Siraj kasan yadda take da muhimmanci a gurina kuwa?”
“Na sani wannan dalili ne yasa na ce maka ta mutu, saboda ka yi focusing akan abubuwan da ke gabanka, na yi nemanta har na gaji ban samu ba, amman tun daga lokacin da na ganta a kamfanin tana aiki nasan wata rana zaku haɗu”
“So kasan tana aiki a nan kuma ka ƙyale baka faɗa min ba? Ban taɓa sanin kai maƙiyina ba ne Siraj sai yau”
“Na ganta sau ɗaya lokacin da muke duba ɗakunanan ni da Zinatu”
Miƙewa Jibril ya yi cike da ɓacin rai, ya nufi ƙofar zimmar fita, sai Siraj ya bishi da kallo yana faɗin
“Ina keka tunanin tafiya? Gurinta? Ai ba zata taɓa saurarenka ba ko ka manta irin wulaƙacin da ka yi mata?”
Tsayawa ya yi cak hawaye na ta cigaba da masa zuba kamar ba shi ba, abun ka da farin mutun har fatar idonsa ta yi ja. Tabbas ba zata saurareshi ba ba ma cancanci Nawwara ta kalleshi ba balle har ta saurare abunda zai fito daga bakinsa.
‘What can i do now? Oh God...’
Ya juyo cikin rashin kuzari ya zauna saman kujerasa ya dafe kansa yana lilo da kujerar.
“Take this”
Siraj ne ya yi maganar yana aje masa farar takarda mai ɗauke da Cocaine saman tebur. Jin ƙamshinta yasa ya buɗe ido ya kuma sauke idanuwansa akan cocaine ɗin, hannu ya kai ya yagi gefen takardar ya fara mata aiki kamar ba gobe, sosai ya shaƙeta ko da ya ɗago ƙasa da kuma gurin tsinin hancinsa ya yi ja sosai.
Yana san cocaine ne kawai saboda ta zame masa jiki ba wai dan tana masa aiki ba, tun lokacin da tunani Nawwara ya sashi gaba ya addabe shi yasa ya fara shanta, saboda ta ɓatar masa da hankali, da wasa-wasa ta kamashi har ta zame masa jiki ta yadda idan ransa ya ɓace sai ya shata yake jin sawaba, izuwa yanzu kan ta daina masa aiki ajiki saboda sabon da ya yi da ita, ko ya sha baya jin komai sai dai kawai ya sha dan ta zame masa kamar a abincin.
Miƙewa ya yi tsaye yana tsotsar pink lips ɗinsa sai wani numfashi yake kamar zakin da ya yi faɗa ya gaji, hannu ya ɗaga ya daki teburin da ke gabansa iya ƙarfinsa.
“Ya za'ayi na sake ganinta Siraj?”
Siraj ya ɗauke ragowar cocaine ɗin ya mayar a wani ɗan ƙaramin box yana faɗin.
“Malam ka fa koreta daga aikin ko ka manta?”
Wani dogon tsaki yaja ya fice daga office ɗin yana ciro wayarsa dake cikin aljihu, wata number ya nemo bugu ɗaya aka ɗaga.
“A fito min da mota waje”
Yana fitowa sekaterinsa ya miƙe tsaye yana faɗin.
“Sir akwai meeting tsakaninka da Managen Daherr Global Prints yanzu”
Juyowa Jibril ya yi a fusace zai jefa masa baƙar magana sai Siraj da ya fito daga office ɗin Jibril yanzu ya yi aurin karɓa masa.
“I will attend the meeting”
A fusace Jibril ya juya ya fuskanci ƙofar sai ta buɗe masa da kanta. Da ya fito be iya tsayawa Excavator ya sauko da shi ƙasa ba ya riƙa tattakowa ya sauko da sauri, kai tsaye ya fita daga harabar gurin, kamar zai tashi sama haka ya nufi lifted, Already sun saba indai zai shiga babu mai matsowa kusa da gurin har sai ya shiga ya sauka.
Kamin lifted ta dawo dashi hawa na ɗaya har ya matso sosai, sai gumi yake kamar wanda yake kusa da wuta, lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya, babu komai a cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalsa sai Nawwara. Ina zan ganta ta ina zai fara nemanta shine abunda yake ta tunani har ya isa gurin motarsa da aka fito masa da ita aka kawo masa har gaban kamfanin, duk gaisuwar da ma'aikatan gurin suke masa be ji ko ɗaya ba saboda hankalinsa kwatakwata baya jikinsa, su kan basu kula ba tun da sunsan halinsa ayi masa magana ya ƙi amsa tun da ya maida kowa maƙasƙanci saboda kawai suna aiki a ƙarƙashinsa, idan har ka gaisheshi ya amsa maka lallai kuwa ka isa irin sosai ɗin nan a gurinsa.
Direban na tsinkayarsa ya yi saurin fitowa ya buɗe masa mazaunin baya, a tunaninsa zasu fita tare ne sai yaga ya ɗaga masa hannu ya nufi driver seat. Da sauri ya rufe masa motar ya matsa can baya yana kallon yadda ya fisgi motar kamar zai tashi sama, abun har tsoro ya bashi.
Tun kamin ya ƙaraso security guard suka buɗe masa gate, domin sun san halinsa ba tun yau ba, shi baya jira a buɗe masa gate sai dai gate ya jirasa. @360 yake gudu kamar ba a cikin gari yake ba. Minti ɗaya zuwa biyu yake furta sunanta zuciyarsa na wani irin bugawa kamar zata filo.
“Nawwara Where are you?”
Titi yake bi zuciyarsa nata raya masa zai ganta, bayan kuma be san inda ta bi ba, haka ya yi yawonsa na neman Nawwara amman har aka kira sallah azahar be haɗu da ko da sawonta ba balle ita.
“I'm very stupid human being, taya za ayi ta bi titi? Tana gidansu by this time”
Ba bawa kansa da kansa amsa, sannan ya bugi sitarin motar iya ƙarfinsa, sannan ya juya akalar motarsa zuwa sama road. Tuna hannunta da ya riƙa yasa jin relief har miskilin murmushi ya bayyana a fuskarsa murmushi da ya kasa gushewa har ya isa ƙerarren gidansa end of discussion da ke sama road.
Yau kan be yi parking a inda ya saba ba sai ya fito cikin wani irin yanayi shi ba farinciki ba kuma ba akasinsa ba ya nufi ƙofar Babban falonsa, yana shiga idonsa suka sauƙa kan ƙaton hoton Nawwara dake tsaye a falon yana fuskartar ƙofa, matsawa ya yi kusa da hoton ya kai hannu yana shafa fuskarta kamar ance masa ita a gabansa tsaye.
“I love you Nawwara i love you so much”
Hawaye ne suka zubo masa, sai ya nufi bedroom ɗinsa yana buɗe maɓallan rigarsa, saman bed ɗinsa ya zauna ya buɗe bedside drawer ya ɗauko wani madaidaicin diary mai zaganen zuciya ya yi masa kiss sannan ya bude shi. Pages da yawa ya wuce a cikin diary sannan ya bude new page da ba ayi ma rubutun komai ba ya ɗauki biro ya zana zuciya a saman zuciyar ya rubutu. _Finally i meet her today she's still alive _ a kasan zuciyar kuma sai ya rubuta _Naj_ ya zagaye shi da biron ya yi ma yatsunsa biyu kiss ya liƙa hawayensa sannan na manna a jikin sunan da ke ƙasan heart ɗin, a take gurin ya jiƙe. Rumgume diary ya yi ya kwanata rai-rai yana bin ɗakin nasa da kallo kamar wani baƙon. Daga bangon gaban na ɗakin zuwa yamma babu komai sai hotunan Nawwara, dagana kudu zuwa arewa babu komai sai horunan Nawwara.
“After the game, the king and the pawn go into the same box, every step I took since the moment I could walk was a step towards finding you, and i find you Naj ba zan iya rasa ki ba i can't lose you again”
Ya tashi zaune ya fiddo wayarsa daga aljihu ya kira waya number.
“A cikin waɗanda aka kora akwai wata Nawwara wacce ta zo yau, ka aika mata da saƙon neman ta dawo aiki yau, kuma ka duba addreshinta ka aiko min da shi right now”
Yana faɗar haka ya kashe wayar, yana wani irin nishi shi ba na wahala ba, ba kuma na fushi ba, ba na jindaɗi ba, kansa ya shafa yana faɗin.
“Ina son ki Nawwara, ina son ki har cikin zuciyata, idan na rufe idona ke nake gani, idan kuma na buɗe ke nake da buƙatar gani kece ruhina Nawwara ina son ki matuƙa”
Magana yake da kansa yana kallon hoton, zuwa can idanuwansa suka sauka kan gmt ɗin dake ɗakin sai ya yi hanzarin tashi ganin uku saura kwata be yi sallah azahar ba.
NAWWARA POV.
Ƙoƙarin buɗe ido nake sai na ji sun min nayi sosai, bana iya tuna abunda ya faru da ni balle har na gane inda nake har sai da nayi ƙarfin halin buɗe idona dake ciki da danshi domin bana iya gani da su sosai.
“Sannu”
Bana iya tantance mai muryar amman tabbas na taɓa jin wannan muryar ko a ina ne, da sannu idanuwana suka buɗe wasai har na iya tantance a asibiti na ke, yanzu kan na tuna abunda ya faru amman waya kawo ni asibiti? Kamar ance na kalli gefena sai idanuwana suka sauka kan Mustapha idonsa narai-narai kan nawa. Unƙurin tashi na yi amman babu wani kuzarin kirki a jikina.
“San..nu..”
Ya faɗa murya na rawa, kansa ƙasa-ƙasa kamar mai saunata. lallai ma wannan mutumem ya raina min da hankali miya kawo shi a inda na ke ma? Tambayar da na kasa amsawa kaina kenan, cikin ƙarfin hali na ɓalle drip ɗin da aka saka min a hannu, na sauke ƙafafuna ƙasa, hannun da na ɓalle cannula yana ta jini na ɗauki Hijabina da ke saman durowa na saka.
“Nawwara....”
Ya faɗa yana miƙewa tsaye idonsa a razane kan hannuna dake ta zubar da jini. Da hannun na nunasa ina masa wani mugun kallo.
“Kar sunana ya sake ziyartar laɓɓanka, kar kuma ka sake ƙoƙarin furta wata kalmar a gareni, ban taɓa tunanin kai hasararren ɗa bane sai yau, zakka marar tarbiya, Zahili dan gantali haihuwar hasara”
Tun da na fara wannan maganar kansa na ƙasa ya rumtse ido yana ta saurarena, mi kuma tuni na fara takawa zuwa gurin ƙofa to my surprise sai ga Jidda ta shigo rike da kaya niƙi-niƙi a hannunta.
“Har kin farka?”
Da ni take magana amman idonta yana kan Mustapha da kamar akwai wani abu a ƙasa. Ƙarasa ta yi ta aje kayan da ke hannunta ta zo ta dafani, sai na kaɓe mata hannu idanuwa cike da ƙwalla zuciyata kuma har wani fisga take kamar zata fito.
“Me kuke yi a nan”
“Suma kika yi a hanya, sai Mustapha ya ganki ana neman inda za a kaiki shine ya kwaso ki ya kawo asibiti”
Kai tsaye ta bani amsar, Mustapha kan tuni ya yi mutuwar tsaye saboda kalaman da na masa.
“Ya akayi kika sani?”
Na tambaya yayinda da hawaye suka sauko daga idona suka wanke min fuska. Sai da ta kalli Mustapha sannan ta kalleni ta ce
“Mustapha ne ya faɗa min”
Dauƙe kai na yi na cigaba da tafiyata na ƙi kula kiran da take min har na fice daga ɗakin.
‘Taya Mustapha yasan alaƙar da ake tsakanina da Jidda? Miyasa be kira wani daga cikin gidanmu ba kira Jidda?’
Shine abunda na ke ta saƙawa a raina ina tafiya, Jidda na bina da kira.
‘Amman kuma ai bata san illar da Mustapha ya yi mana ba, bata san aibunsa a garemu ba’
Tuna wannan yasa na tsaya har na saka Hijabina na danne Hannuna ina jiran ta ƙaraso.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣2⃣
“Haba Nawwara abunda kike ba shi da kyau Wallahi na san kin tsani masu kuɗi amman wannan mutumen fa taimakonki ya yi ban san abunda bawan Allah nan ya yi miki ba duk kin bi kin tsaneshi, haka sam be dace ba, ni kaina na tuhumesa lokacin da ya zo har gida ya faɗa min na ce miyasa be faɗa ba gidanku ya ce yana gudun zargin ne kuma da na zo nan asibitin na tarar mutun biyu da suka kawo ki tare, Wallahi babu wani abu Nawwara dan Allah ki kwantar da hankalinki”
Shine abunda Jidda ta faɗa lokacin data ƙaraso kusa da ni. Mustapha kuma na daga can nesa da mu ya sako min ido kamar zai cinye ni. Kallo ɗaya na yi masa na ɗauke kai ba tare da na ce da ita komai ba na cigaba da tafiyata, zuciyarta na mugun bugawa kamar zata faɗo. Tare muka fito da Habiba a har bakin gate ɗin Specialist hospital dake sokoto, motar Mustapha ce ta sha gabanmu be ce komai ba ya miƙa hannu daga inda yake zaune ya buɗe mazaunin baya. Jidda ce ta iya riƙa ganbun motar ni kan ko kallo bata isa ban na kauce mata na cigaba da tafiyata har na tsada mai adaidaita na shige ina faɗa masa inda zai kaini, yana ƙoƙarin tashi sai ga Jidda ta dakatar da shi ta shigo tana min masifa wai abunda na ke bana kyauwa, ni dai ban kulata ba saboda na san bata san zafi da irin ƙiyayyar da raina ta Mustapha ba, tun da ban taɓa faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi sanadiyar muturwar ƴar'uwata ba.
A gurin da aka saba saukeni na ce ya ajeni na saka hannu aljihu na ciro kuɗi a bashi sai a lokacin na tuna da hoton Habiba da na baro a wacan baƙin kamfanin da bana fatar ko a mafarki na sake zuwa, gaskiya na ji babu daɗi sosai domin shine kaɗai hoton Habiba da nake da shi a yanzu wanda take da girmanta, ta ɗaukeshi ne lokacin da zata yi canjin makaranta daga Hafsatu zuwa Nana girl's, abunka da takala ba hotone a gabanmu ba sai idan wani abun ya tashi na dole sannan muke zuwa yin hoto.
“Ina wayata?”
Na tambayi Jidda bayan mai adaidaita ɗin ya bamu canji, hannu tasa cikin jakarta ta ɗauko wayar ta miƙa min.
“Gashi”
Ina karɓa na sa kai gabana muka cigaba da tafiya tare.
“Gaskiya halinki bashi da kyau Nawwara, idan har baki yabawa Mustapha ba to ba zaki zageshi ba”
“Ce miki ya yi na zageshi?”
“Ko baki zageshi ba kin faɗa masa magana marar daɗi domin alamu sun nuna haka, ban san abunda bawan Allah ya yi miki ba, ko dai akwai wani abun ne?”
Na tsaya ina kallonta
“Wai miyasa kika damu ne Jidda?”
“Saboda ya taimakeki, da be kawo ki asibiti ba da Allah kaɗai yasan halin da zaki kasance akan hanya”
“Da barina ya yi akan hanyar mota ta takani ko kuma mutane suka ɗaukeni suka jefar a bola, da ya fi min farinciki sama da ɗauko da ya yi ya kawo asibiti, dan Allah ki tattara duk wani abu da ya danganci maganar nan ki ajeta a gefe”
Na tada kai na cigaba da tafiyata har na isa gida ban waiga na kalli Jidda dake gefena ba. Ita ce ta faɗawa Inna abunda ya faru da kuma irin abunda na yi ma Mustapha har Inna da kanta ta dinga ganin rashin kyautawa da kuma faɗar abunda na yi ba halina ba ne.
Ni dai ban iya cewa Inna komai ba tun da nasan ita ma ban faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi ma Habiba aika-aika ba. Tufafin jikina na cire na saka a murhu na ƙone tare da Hijab ɗin duka na haɗa na ƙone saboda mutun biyu Mustapha da kuma Jibril tsakanin su ba zan iya banbance wanda zuciyata ta fi tsana ba. Ina gaban Murhu Inna ta fito daga ɗaki jin ƙauri ta saka salati.
“Lafiya kike ƙone kayan aikin kuma Nawwara mi yake damunki?”
“Inna sun koreni dan haka bana da buƙatar wannan kayan”
“Garin ya wani abun kika yi?”
“Ban yi komai ba, saboda kawai na daɗe ban je ba”
“Ba kince Bilal ya faɗa musu baki da lafiya ba?”
“Wai basu yarda ba shugaban Kamfanin ne bashi da mutunci”
“Allah ya kyauta ya baki wani”
Ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata jidaɗin haka ba. Ƙarasowa ta yi kusa da ni ta riƙani ta tayar tsaye.
“Tashi gaban hayaƙi, bari na saka miki ruwa ki yi wanka”
“A'a zan iya Inna”
“Babu ƙarfi jikinki Nawwara baki ga yanxu kika dawo daga asibiti ba”
Da kanta ta haɗa min ruwan na shiga banɗaki na yi wanka, bayan na fito na ɗauki buta na yi alwala na shiga ɗakinmu sai na samu Inna zaune tana yanka min albasa a wake da shinkafa, saboda ta san ina son na saka albasa da tumatur idan zan ci wake.
“Gashi nan idan kin gama sallah sai ki ci, bari na kawo miki ruwa”
Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita ni kuma sai na yi saurin dakatar da ita.
“Haba Inna kina ta min abu sai kace ƙaramar yarinya ni ya kamata ace ina hidima dake ba wai ke ki yi da ni ba”
Tsayawa tayi jikin ƙofa tana murmushi tare da wasa da wuƙa da kuma ragowar albasar dake hannunta ta ce.
“Nawwara ji nake kamar da nayi wani sakaci kaɗan rasaki zanyi, ɗazun da baki dawo a lokacin da kika saba dawowa ba hankalina ya tashi sosai, ba san yadda zanyi ba idan har na rasaki bayan na rasa Habiba, kuma kina a matsayin RAI BIYU a yanzu ni da kuma ɗanki, shi ma ya damu da be ganki ba lokacin da ya dawo daga makaranta, yana ta tambayar ina Momy nace mishi kina gurin aiki amman daker ya yarda ya tafi islamiya, ɗanki yasan zafin rabuwa da mutun yasan idan aka tafi ba a dawowa shiyasa saboda ya rabu da Habiba dan haka ba zamu iya jure rashinki ba”
Tana faɗar hakan tasa kai ta fice idonta cike da ƙwalla, ni kuma na jingina na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, wani irin tausayinta ne ya rufe ni. Jin wayata tayi ƙara yasa na buɗe ido na nufi inda wayar take, tun kamin na ɗauka gabana na faɗi saboda saƙone daga One-On-One Limitless Company, ji nayi bana da buƙatar sanin abunda saƙon ya ƙumsa, dan haka na danna delete na goge shi ba tare da na karanta ba.
Sai da na gama rama sallah azahar sannan na gabatar da sallah la'asar, sai na zauna na ci abincin sai ba sosai ba saboda bana jindaɗin abinci a yanzu, sai dai shigowar Inna yasa na zage dantse na yi ta auna abinci domin nasan zata damu idan ta ga banci da yawa ba. Na yi ƙoƙarin ganin na danne damuwata amman mahaifiya ta fi gaban wasa ita da kanta ta tsinkayi hakan a cikin idona.
“Nawwara kamar akwai abunda yake damunki, idan dai dan maganar aikin nan ne ki kwantar da hankalinki Allah zai sake baki wani kamar yadda ya baki wannan”
Kai kawai na iya ɗaga mata domin na gansu maganar aikince kamar yadda take hasashe, domin idan har ta tiƙe ni ban san mi zan faɗa mata ba. Tashi tayi ta fita jin wata maƙociyarmu ta shigo, ni kuma na rafka uban tagumi ina kallon ƙasa amman hankalina yana can gurin rayuwata ta baya.
FLASH BACK.
_“Yau za'ayi ina fatar zaka samu zuwa kai da madam, tau ya yi sai kun ƙaraso”_
_Haka na ji ya faɗa a waya, sannan na miƙe tsaye yana min wani gumun kallo ya ce._
_“Wallahi duk kika sake abokaina suka zo gidan nan kuma kika fito sai na halakaki, kinji ni ko?”_
_Da sauri na ɗaga masa kai hawaye na zuba a idona, sai ya kaɗa kai fuska babu annuri ya nufi ɗakinsa yana wani irin jinkansa, ni kuma na zube a gurin ina kuka saboda zafin ruwan zafin da ya watsa min a hannu kuma ya hanani kuka saboda tsabar zalumci. Ina a gurin ina aikin kuka har ya shirya ya fito sai ƙamshin turare yake ya tsaya a kaina ya nuna ni da yatsa_
_“Ki shiga cikin ɗaki ki kulli kanki karki yarda ki fito”_
_Na amsa masa da tau jikina na rawa ina ta ƙoƙarin haɗe kukana nasan idan har na yi kuka a gabansa zai iya dukana, kamar yadda ya umarce ni haka na shiga cikin ɗakin na rufe kaina wanda hakan ya bani damar tausayawa kaina da kaina. Can zuwa dare na soma jin hayaniyar abokansa ta hirar da suke na iya gane ashe muƙamine ya samu amman ya gagara faɗa min saboda ƙiyayyar da yake min, haka yake duk lokacin da wani abun ya sameshi sai dai na ji a waje ba dai ya faɗa min ba. Har suka yi abunda zasu yi suka gama ban fito ba, bayan fitarsu da minti ashiri na ji an buga ƙofar ɗakina, yanayin yadda aka banki ƙofar ne ya fahimtar da ni cewar Jibril ne yake buga ƙofar, cikin hanzari naje na buɗe saboda na san baya son jira, sai nayi arba da yatsunsa biyar a kuncina, ma'ana wanke min fuska da mari yana faɗin_
_“Ke kiƙa faɗawa Abbah zanje meeting ba dake ba ko?”_
_Baya-baya na yi ina girgiza masa kai_
_“Na rantse da Allah ban faɗa ba, Wallahu ba ni bace”_
_Na faɗa cikin kuka, sai ya watsa min harara, yace na canja tufafi muje amman duk na masa kuka cikin mutane sai ya ɓanlani, jin wannan yasa hawayena ya yanke tun kamin ma mu fita domin na san haƙinsa ne sarai zai iya ci min mutunci a gaban kowa, sai dai ban daina jin zafin marinba har muka isa gurin da ake tare, gurine dake cike da manyan mutane an ƙawata gurin anyi masa kwalliya gwanin sha'awa. kowa da mazauninsa, an kasa mutane daban-daban wasu na tare da matansu wasu kuma na tare da familysu. Tare muka shigo da shi amman muna shiga harabar gurin sai yayi kamar be sannin ba tare da gargaɗina akan karna yarda na nuna cewar ni matarsa ce. Guri na samu kusa da wasu baƙin na zauna, bayan an gama jawabin da akeyi aka kirashi aka karramashi, sai yaje ya karɓi Award ya yi jawabi godiya, a lokacin Abbah da Hajiya basa nan dan haka babu wacce zai kira bayan su sai ni da nake matarsa, amman abun mamaki sai ya kira sunan budurwarsa Asiya ko kuma ma nace karuwarsa, haka ta miƙe tsaye tana ta karairaya ta haura gurin tana taya shi murna. Ni kuma ina daga nan zaune ina hawaye_
_Wani mutun ne ya miƙo min tissue yana min kalaman da mijina abokin rayuwata be taɓa min ba_
_“Kuka be cancanci kyakkyawar fuskarnan taki ba dan Allah karɓi ki share hawayenki”_
_Kallonsa na yi amman na kasa karɓa saboda idon Jibril na kaina, haka mutumen ya matsa min amman naƙi kula shi har aka tashi taron, a gurin da zamu shiga mota ya tare mutumen ya riƙa bugar masa baki wai ya yi magana da matarsa, babu kalar baƙar maganar da saurayin be faɗa masa ba, sannan aka rabasu ni kuma ya sakoni gaba muka dawo gida, kamar jira yake mu iso ya sakani gaba da duka wai na kula wani namijin har wani huci yake kamar zaki..._
BACK TO STORY
Shigowar Noor ne ya katse min tunani, sai ya yi saurin aje allon dake hannunsa ya nufo yana share min hawayen da ban san sun zubo ba.
“Momy miyasa kike kuka? Shiru shiru shiru kinji Allah ya miki albakar, yi shiru shiru faɗa min waya taɓa ki?”
Shine abunda yake faɗa tare da saka haɓar rigarsa ya goge min fuska, ina kallonsa gabana ya faɗi fuskar Jibril ce shimfiɗe a fuskarsa babu inda ya ragoshi tun daga kan hancinsa har ido da baki da fari komai na ubansa ne, rumgumeshi nayi muka kwanta saman kafitar da nake zaune.
_“Ba cikina ba ne...!”_
Shine abunda ya faɗo min a rai, sai na ƙara ƙanƙame Noor kamar ance za a rabani da shi. Bachine ya kwashemu ni da shi bamu farka ba sai da Sakina ta shigo tana tashina wai anyi magariba.
Bayan Sallah isha'i Bilal ya kirani a waya yace min yana ƙofar gida, nasan daman zaizo tun da yau ban karɓi kuɗin da ya saba bani ba. Sai dai na sha mamaki lokacin da fita muna fira da shi.
“Miyasa kika fita Kamfani ɗazu kina kuka?”
Shine abunda ya fara tambayata, nasan wata ƙila wani ne ya faɗa masa, ni kuma sai na masa ƙarya da cewar saboda sun ƙoreni yasa ni kuka, ya nuna min damuwarsa sosai har ma ya yi alƙawarin zai yi wani abu wajen ganin an maidani aikin, amman na nuna masa bana so. Sai tara da rabi muka rabu ban faɗa masa cewar na suma a titi ba duk na san nan gaba kaɗan zan ji a gurin Jidda domin bata ɓoye masa komai da ya dangance ni.
Ko da na shiga gida wayata na ta ringing ko da na duba sai naga baƙuwar number, kamar kar na dauka sai kuma na ɗauka tare da sallama, sai na ji ba a amsa min ba kuma ba a ce komai ba har na tsawon lokaci, hakan yasa na sake sallamar nan ma shiru har sai da na duba wayar naga mai kiran be kashe ba, na sake karawa nayi sallama a karo na uku ba amsa min ba kuma ba a ce komai ba, hakan yasa na kashe wayar dan da alama mai kiran yana son sauraren muryarta ne kawai duk da ban san ko wanene ba.
WASHE GARI...
Misalin bakwai da rabi saƙon kamfanin ya sake shigowa, nan ma ban karanta ba na goge, na shigaba da haɗa abun karinmu da nakeyi. Sallamar baƙuwar murya yasa na ɗago daga gaban murhun da nake na amsa mata ina mata kallon rashin sanin, sai da ta gaisheni sannan ta matso kusa da ni ta aje min leda biyu dake hannunta ta ce
“Wai gashi inji Ya Mustapha ya ce abawa Nawwara, kuma wai yana mata sannu da jiki”
Har na buɗe baki zance mata ta ɗauki kayan ta koma da su sai ga Inna ta fito daga ɗaki tana amsawa kamar tasan ni ba zan amsa ɗin ba.
“Mashallah ki ce an gode Allah ya saka da alheri, jiki kuma ya yi sauƙi sosai”
Da wannan budurwar ta juya ta koma wacce nake san ran riƙonta ake a gidansu Mustapha domin iyayensa shi kaɗai suka haifa. Tana fita na ɗauki kayan na fice na bar Inna tsaye tana kallon ikon Allah domin nasan idan har na ce yarinyar ta ɗauki kayan ta koma dasu a gabanta ba zata bari ba, amman yanzu bata san mi zanyi ba dole ta saka min ido.
Ina fita na yi karo da shi a ƙofar gidanmu sai ya ɗanyi nisa da gidanmu kaɗan yana sanye da jallabiya, daga inda nake tsaye na jefa masa ledodin na juyo abuna.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣3⃣
“Me kika yi kenan?”
Ina shigowa gida ta jefo min wannan tambayar, da fari na tsaya tunanin abunda zan ce mata sai kuma daga baya na yanke shawarar faɗa mata gaskiya.
“Mayar masa da abunsa na yi, bamu da buƙatar taimakoshi”
“Amman Nawwara ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mutumen da ya tsinceki gefen titi ya taimaka miki ya kaiki asibiti garin Allah ya waye kuma ya aiko ganinki shine zaki mayar masa da kayansa? Wannan wace irin rayuwace Nawwara? Mi yake damunki? Wulaƙanta ɗan'adam? Kuma mutun kamar Mustapha yaron da babu wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa amman har kike ƙoƙarin ci masa zarafi?”
Yanayin fuskarta da kuma lamanta na fahimci ranta ya ɓace sosai akan abunda na yi, ni kuma na marairaice mata kamar zanyi kuka.
“Inna kin san waye Mustapha ana yaba masa da neman matan banza, dan me zai kawo min abu na karɓa, bayan ban san manufarsa a kaina ba”
Ta ƙaraso kusa da ni
“Shiyasa na ke son ki lallaɓa da shi ku rabu lafiya, da baki watsa masa kayansa ba sai ki amsa ki masa godiya in yaso daga baya sai ki nemi ya rabu da ke”
“Zan kiyaye nan gaba”
Da wannan muka raba na nufi murhu na cigaba da hura wuta, ita kuma ta koma ɗaki tana cewa Sakina ta zo ta siyo mana ƙosai. Har na dama kumun tunani ɗaya ne a raina, na faɗawa Inna gaskiya game da Mustapha ko kuma na barwa cikina, idan ma na faɗawa Inna amfanin me zai mata? Idan kuma na bari ban faɗa ba ni amfanin me haka zai min?
Ina cikin wannan tunanin naji muryar Namiji yana sallama a ƙofar gidanmu, bayan naji tsayawar mota da kamar minti huɗu, dakan uku-uku gabana ya yi duk da ban san ko wanene ma. Ko da na bar gaban murhun Jamila har ta kai waje, sai gata ta dawo da sauri tana kirana.
“Anty wai ki zo ana kira a waje”
“Waye?”
“Wanine”
Mustapha na fara kawowa a raina, amman da shi ne ai Jamila ta sanshi da shine ai ba zata ce wani ba. Miƙewa na yi tsaye na tare da bokitin da na dama kunun na nufi ɗakin Inna na aje mata sannan na ɗauki Hijabinta na saka na nufi ƙofar gida gabana sai faɗuwa yake musamman da na yi arba da mutumen dake sanye da rigar kamfanin da kuma hularsu, tun kamin na masa sallama shi ya fara min tare da faɗin sunana.
“Khadija Musa Kafinta”
“Sunana ne”
“Zaki saka hannu a nan sai na baki saƙon da aka aiko miki”
“Bana da buƙata ka mayarda saƙon, kuma ka faɗawa shugabanku ya dakatar duk wani saƙo da suke aiko min bana da buƙata”
Sakin baki mutumen ya yi yana kallona, kamin ya barshi tsaye a gurin nayi shigewata, zuciyata cike da tunanin abunda ke cikin saƙon a lokacin na riƙa da na sanin ƙin karɓa da na yi domin sosai na so naga abunda aka rubuta, sai dai kuma ta wani babin bana da buƙatar duk wani abu daya dangancin Jibril idan har na saka masa fuska tabbas zai sake nuna wasa da ni kamar yadda ya yi a baya.
Wani mugun murmushi na samu kaina da yi lokacin da na tuna hawayen da na gani a fuskar Jibril, ashe zai iya zubar da ƙwalla saboda ganina har ya riƙa hannuna ya shafa a fuskarsa, mace da ya ce kashe yafi ta daraja a gunsa, lallai akwai babban labari a cikin hawayensa, domin ba kasafai Jibril ya ke nadama akan abunda ya aikata ba.
“Kee... Lafiya kike murmushi ke kaɗai kuma?”
Tambayar da tayi min ta dawo dani daga duniyar tunanin da na tafi har na yi dariya na matsa kusa da ita na rumgumeta.
“Ina sonki sosai Mamana”
“Waye ya zo yanzun kuma?”
“Daga kamfanin da nake aiki ne, suka aiko saƙo amman ban karɓa ba”
“Saboda me?”
“Nasan babu komai a ciki sai wulaƙanci”
“Ai da kin karɓa kin duba wata ƙila zai miki amfani”
“Ya riga ya tafi”
“Allah ya kyauta”
Sai duk muka amsa da Amin. Bayan mun gama karyawa, su Sakina suka shirya suka tafi makaranta tare da Noor, sai dai gabana nata faɗuwa saboda ina ganin kamar wani abu zai faru da ɗana. Sai da suka je makarantar suka dawo sannan hankalina ya kwanta.
Can da yamma sai ga Jidda ta shigo gidanmu da manyan ledoji, daman ta saba a duk lokacin da nake rashin lafiya sai ta riƙo min wani abu take zuwa gidanmu dubani, sai dai abunda ya ban mamaki siyayar da ta yi min ta fi ƙarfin Jidda duk da nasan sun fimu rufin asiri. Bayan sun gama gaisawa da Inna ta ƙasaro inda nake zaune ta dire min ledojin tana zolayata kamar yadda ta saba.
“Gawa ta ƙi rame, kin ƙi ki mutu mu ci gado”
“Mutuwata ba yanzu ba yarinya sai ke da danjinku kaf kun ƙare”
Sai duk muka saka dariya har Inna dake ninkar kayan da na wanke ɗazu na su Jamila. Mun sha fira sosai da Jidda daga bisani na tambayeta inda ta samo wannan kayan domin ita kanta tasan na san wannan kayan yafi ƙarfinta, bata ɓoye min komai ba ta faɗa min daman can Jidda bata ɓoye min komai.
“Wallahi Mustapha ne ya kawo ya ce idan zanje na riƙa miki wannan, wai kar nake hannu sake, daman ina ta tunanin abunda zan riƙo miki dan bani da kuɗi kuma bana son zuwa haka nan”
“Daman kuna waya da shi?”
“A'a ɗazu dai ne ya zo yake tambayata jikinki kuma ya bani number wayarsa wai idan zanje dubiyarki na faɗa masa, shine fa ya kwaso min wannan kayan”
Bana son Jidda ta zargi wani abu, hakan yasa ban ƙara masa wata tambayar ba, sai kawai muka ɗauko wata firar. Sai da aka kira sallah magariba sannan na rakata ƙofar gida ta wuce tana mintar rashin adalci na mai kamfanin da nake aiki, domin na labarta masa cewar ya koreni.
Tun daga wannan ranar kullum sai Mustapha ya aiko da saƙon a gidanmu da sunan ganin lafiyar jikina, wasiƙar gurin aiki kam kullum sai tazo gidanmu bayan ta waya da ake aiko min, tun Inna na lallaɓa na koma aikin har ta gaji ta zuba min ido domin ta fahimci ba zan koma ɗin ba, na kan faɗa mata ni bana son aiki a kamfanin ne saboda dokokin kamfanin. Bilal ma ya yi mamaki matuƙa ji da ganin yadda kamfanin yake neman na koma aikin bayan ance an koreni, shi da kansa yake faɗa min ko da harkar kasuwanci kanfanin zai ƙulla da kai da zai ci riba matuƙar suka koreka ba zasu nemeka ba balle kuma ma'aikaci, babu irin tambayar da bai min ba akan ko nasan wanine a kanfanin amman na nuna masa ni bansan kowa ba har ma na yi masa iƙirarin cewar ai na fada cewar ban yafe Haƙƙina ba wata ƙila shiyasa suke son na dawo aikin.
Sam ban taɓa ɗaukar lamarin Mustapha azimun ba ne sai yau da mahaifiyarsa ta zo dubani, ita kanta Inna mamaki ya cikata kuma ta ɗan tsorata da lamarin kamar yadda nima nake ta almarar abun tare da tunanin abunda yake ƙoƙarin aikatawa. Kana ganinta kasan zuwan cilas ne domin ƙyamar gidanmu take sosai, zama na sai ya gagareta sai wani kallon gidan take a hankaɗe a tsaye ta yi min ya jiki ni kuma na bawa banza ajiyarta har sai da Inna ta amsa ta tana ta ƙoƙarin kareni, saboda ta tsarku da yadda na share Hajiyar a tsaye ko gefenta ban kalla ba balle har na iya gaisheta.
“Iska ne da ita abubuwan ne sai a hankali”
Ta taɓe baki tana gyara tsayuwar gilashin idonta.
“Daman Son ne ya faɗa min akwai yarinyar da kai asibiti yana son na zo na dubata, ni zan wuce”
Ko sakon biyar bata ƙara a gidanmu ba ta fice tana wani irin taku na ƙasaita Inna ta bita tana masa godiya, ni kuma na bita da harara, daman ba zan lissafata a cikin mutane mn da suka mana gaisuwar Habiba ko Baba ba duk da bana iya tantance kowa da kowa amman da tazo da dole wasu zasu ganta ko da ba ni ba, gashi tsanar ɗanta ya dasa nin tsanarta musamman yanzu dana fahimcin bana sha'awar mutane irinmu.
Inna na dawowa daga rakiyarta ta cire takalmin ta buga min a kai, kana ta nuna ni da shi tana faɗin
“Allah ya canja miki wannan baƙin halin da ya taso miki, ai ba ita kika kunyata ba ni kika kunyata”
Tana faɗar haka ta nufi ɗaki ranta a ɓace, rabon da Inna ta ɗauki wani abu ta dakeni tun ina junior high school lokacin da na zo wani hutu, amman yau gashi ranta ya ɓace har ta buga min takalme a kai saboda ɓacin rai. Tashi na yi na bita ɗaki na bata haƙuri tare da shaida mata ba zan sake sannan muka shirya da ita har ma tayi min bitar zaman da mutane da kuma taka tsantsan na ka samu ka rabu da kowa lafiya.
Haka muka zauna muna ta fira har su Noor suka dawo daga makarantar allo na tura masa karantunsa ya wanke allon yana ta murna wai malaminsu ya ce ya iya idan yaje gida ya wanke allo gobe yi masa wani rubutun. Bayan sallah magariba Bilal ya sallamomin kamar yadda ya saba sai dai yau sallamar tasa ta musammance domin firar kansa yake min wai mutane nata maganar ya kamata ya yi aure har da ƴan gidansu, ni dai murmushi kawai nake inda kuma ya kamata na yi dariya sai nayi dariya, har muka rabu beji wata kalma da yake zato daga bakina ba, hasalima ban barshi ya daɗe kamar yadda ya saba ba ganin inda akalar labarinsa ya dosa a yau.
Misalin tara da rabi muka kulle gidanmu bayan mun gama fira da Bilal, na bawa Sakina ta kai min wayata maƙota saboda na samu caji, sai na alwalar na shigo ɗakin Inna na yi sallah isha'i, sannan na shiga na gyarawa su Sakina gurin kwanansu, ni kuma na dawo ɗakin Inna domin a yanzu na daina barinta tana kwana ita kaɗai.
Saman gado muka haye ni da Inna Noor na bayana daman duk inda nake kwana a nan yake kwanan, na yi matashin kai da fillon Habiba kamar yadda na saba sannan na yi Noor addu'ah bayan wacce ya karanta ta shiga bachi, ni ma na yi muka kwanta cike da aminci da salama.
Can cikin bachi naji Inna na tashina a hankali, ina buɗe ido hankalina ya tashi sosai, sakamakon jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidanmu da muka ji ana yi, ashe nice bachi ya lula da ni sosai ban ji ba har sai da aka tasheni su Sakina da Jamila kan tuni suka ji har sunyo ɗakinku sun ta ɓoya bayan Inna suna kuka, Noor ma yana ƙanƙame da Inna jikinsa sai rawa yake.
“Ku shige ƙarƙashin gado”
Inna ta faɗa kaɗan-kaɗan, ni kan araina na ce wane irin ƙarƙashin gado kuma ƙarƙashin gadon da itace ne muka saka a ƙasa ni da Habiba, saboda a samu yabuɗaɗɗiyar katifar ta tsaya. Kamin mu yi wani unƙuri sai dirowar mutane muka ji cikin ɗakinmu, daman ƙofar ɗakin ta cire ta can farkon shigowa gidace kawai ta rage muke rufe gidan da ita. Fitila mai haske sosai ɗayansu ya dallo min ba shiri na rumtse ido jikina na rawa na rumgume Inna ina saki fitsari abunka da mai mugun tsoro...
TO SU WAYE KUMA WAƊANNAN😨😱
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣4⃣
Sakina da Jamila ne suka saka da Noor ne suka ihu ganin bindiga nikan dabam idanuwana a rufe suke addu'a kawai nake karantowa.
“Ku yi mana shiru..”
Ɗaya daga cikinsu ya faɗa a tsawace cikin wata murya mai kamar doro, sai duk suka yi tsif kamar babu su a gurin.
“Dan Allah dan Annabi karku cutar min da yara ku yi haƙuri”
Shine abunda Inna take ta roƙo muryarta na rawa alamar tsoro yana tare da ita.
“Ki kwantar da hankalinki ba zamu miki komai ba ba zamu taɓa kowa na ki ba, kuɗi muke so ko abun kuɗi”
Jin wannan yasa na sassauta riƙon da nayi wa Inna na buɗe ido tare da ɗagowa na kalli fuskokin waɗannan mutane da suka zo neman kuɗi a gidanmu, ina ɗagowa ɗayan ya dalla min fitila a ido gashi ba shiri na sake rumtse ido.
Ɗan abunda Inna ta san tana da shi na canji taje ta ɗauko ta kawo musu jikinta sai rawa yake tana faɗin
“Shikenan na ke dashi a gidan nan Wallahi ba muda komai mu talakawa ne”
“Kina da ɗan kunnen zinari ko azurfa?”
“Wallahi bamu da shi”
Ta bashi amsa ciki kuka mai cike da tsoro. Ban sake jin sun ce komai ba sai kawai na jin nayi suna da bincikar kayan da ke ɗakin wasu kuma suka nufi ɗakinmu wacan dake waje suna bincika, hakan ya bani damar buɗe idona a karo na biyu na kalli mutun huɗu da suke ɗakin suna mana bincike, daga ganinsu manyan ɓarayi ne domin ɗauke suƙe da manyan bindigogi fuskarsu sanye da fuska irin ta manyan ƴan fashin nan dukansu danye suke da baƙar riga da jean banƙi.
Mun ga ikon Allah a wannan ranar domin komai sai da suka bincike, sam basu yarda bamu da komai ba, har tufafinmu sai da suka bincika suka tsince masu kyau, ragowar shinkafar da ta rage mana mana dafawa har da ita suka haɗa, wani abun ɗaure kai har da tukunyar da muke dafa abincin sannan suka ce duk mu rufe idonmu kuma mu kwanta, sannan suka fice suna cewa duk wanda ya ɗago sai sun halbeshi. Ni dai ba buɗe ido ba ko motsi ban sake yi ba har na kusan minti talati saboda kawai tsoro.
A daren babu wanda ya sake runtsawa daga ni har Inna da Sakina, Jamila da Noor ne kawai suka yi bachi, Noor ma sai da na rumgumeshi. Abu ɗaya ne ya tsaya min a rai har garin Allah ya waye, miyasa basu shiga gidan manyan masu kuɗi ba sai gidanmu? Beside waɗanne irin ɓarayi ne ma da zasu ɗauki tsofin sutura da ragowar shinkafa da ƴan canjin da basu kai dubu biyu ba da sunan sata da alama mu fa manyan ɓarayi ne ba ƙananan ba.
‘Turosu aka yi’
Shine abunda zuciyata take ta yawan nanata min, sai dai kuma waya turo su?
Washe gari mutane suka yi ta shigowa suna mana jaje tare da fatar allah ya tsare gaba ciki har da ƴan babban gida, sai dai wannan besa ɗayansu ya yi tunanin cewa mu koma can ba, duk kuwa da kasancewar rayuwarmu tana cikin hatsari saboda suna ganin idan muka koma zama tare da su lalurar mu ce zata hau kansu, kai tirrr da wasu ƴan'uwa!
Da yamma Jidda ta zo ita da mamanta suna jajanta mana take labarta min abunda ake faɗi a unguwa, wai gurin dai suka zo har wasu na cewa ba zasu rasa min fyaɗe ba sai dai ba zan faɗa ba, maganar ta ɓata min rai daman nasan dole mutane su zargi haka ganin bamu da Komai kuma ace sun zo gidanmu.
Baba Sulaiman ne ya kira mai gyara ya gyara mana tsohon ganbun na ƙofar gida da mutane suƙa ɓalle suka shigo. Tun da yamma muka bar gidan saboda ƴan'uwan Inna da suka sha kai akan sai dai mu dawo can da zama, ranar a tudun wada muka kwana gangaren tallatu sayin salamatu mai tuwo. Sun nuna mana mana kulawa sosai aka wuni ana firar ta nan na fahimcin Inna ma ta gano turosu aka yi, sai dai ita ta allaƙa abun ne ga Mustapha har take min faɗan wai na lallaɓa mu rabu lafiya da shi.
Bayan sallah isha'i Bilal ya kirani na kwatanta masa inda nake, ko minti arba'in ba a ƙara ba sai gashi ya iso tudun wada, na fito titi na shigo da shi cikin lungun na mu. Gaisawace first abunda muka fara yi sai yasa na kira masa Inna ya gaisheta tare da yi mata jaje sannan ya ce an gidansu suna gaisheta. Bayan Inna ta shige ya dawo kaina sai bugun cikina yake yana ta son ya ji idan sun min wani na san wannan ba zai rasa nasaba da maganganun mutane da yake ji ba.
“Kaima ka yarda da abunda mutane duke faɗa kenan”
Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara tsayuwarsa ya ce.
“Yarda ta da rashin yardata duka suna gurinki, Wallahi komai kika faɗa min zan yarda da shi Nawancy”
“Idan har ka yarda da ni toh ka yarda da duk abunda zan faɗa maka, Wallahi basu min komai ba ko hannuna basu riƙa ba, babu wanda suka taɓa a gidanmu”
Sanyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jinginawa jikin iccen tarbejiya dake ƙofar gidan yana hamdala.
“Allah na gode maka, Wallahi Nawancy da sun taɓa ki ban san yadda zan yi ba ban san iya halin da zan shigaba”
“Da ba zaka iya aurena ba ko?”
Hakan yasa shi ɗagowa daga jinginen da yake da sauri yana kallona fuskarsa da ɗauke da murmushi.
“Nawancyta da gaske kike maganar nan da kika yi?”
Ya tambaya yana matsowa kusa da ni kamar zai haɗa numfashinsa da nawa, hanzarin matsawa baya nake sai ya yi caraf ya cafke min hannun yana cigaba da matsosa kusa da ni.
“Kin san waye ni babu abunda zan miki, kawai ina son na tabbatar ne, Wallahi Nawancy i'm ever ready to marry you dan Allah ki taimaka min”
“Mutane fa zasu gani”
Na faɗa a tsawalle ina kawar da fuskata, sai na yi sa'a ya sake ni, ina ganin hakan na juya da gudu na shige gida.
Babu irin kiran da be min ba ta waya amman na ƙi ɗagawa har ya gaji ya tafiyarsa.
Kwanan mu biyu a can muka dawo gida saboda tsallawa da muka yi saboda gidan gidan taro ne babu sakewa sosai, ga yaran gidan basa da ragowa a gaban idona suke buge Noor ba damar nayi magana ace na yi rashin ta ido su kuma ba zasu iya yi ma yaransu magana ba.
Ranar da muka dawo ma mutane sun ta zuwa yi mana jaje mutanen da basu samu zuwa mana washe garin da abun ya faru ba, saƙon kamfani kan kamar ƙa'ida ko da muka dawo mun tarar da wasiƙa biyu wacce aka kawo yau ita ce ta uku ban da ta waya da nake ta karɓa ko wace safiya da kuma yammaci.
Bayan na gama gyare-gyaren gida na shinfida tabarma na zauna tsakar gida ina ta nazarin abubuwan rayuwa ciki har da wannan abun da ya same mu, da kuma maganar ƴan sanda da suka yi mana izgilanci amman shiru har yau babu dpo babu labarinsa, ga kuma Jibril da ya sakoni a gaba yanzu.
Wai shi Jibril me yake nufi ne ya yi nadama ko kuma so yake na koma aiki ƙarƙashinsa ta yadda zai sake gallazamin ya ɗauka kamar da ne?
“Kut”
A fili na yi ƙwafa, kana na ɗaga kaina dake ƙasa na kalli Inna wacce ta fito daga ɗaki tana maganar aikina.
“Ni fa wannan lamarin har tsoro yake bani Nawwara, ban taɓa ganin wanda aka matsawa ya koma aiki kamar ki ba, anya babu wani abu?”
Na yi dariyar da ni ƙaɗai nasan abunda yake nan.
“Babu komai Wallahi kawai dai kin san abu idan aka ce maka da turawa ne, shiyasa”
“Amman ke miyasa kika tsaya kai da fata akan ba zaki koma ba, nifa ina jin da kamar akwai wani abu”
“Babu komai kawai ina musu jan ajine saboda susan ba ko wanne mai neman aiki ba ne wulaƙantacce, zan koma aiki Inna ai dole ma ne na koma aikin ko dan na bawa marar ɗa kunya! Kuma ni kaina ina da buƙatar aikin saboda zai taimaka mana mi tallafawa kan mu da kan mu”
Na faɗa ina sauke ajiyar zuciya Inna kuma tana amsa sallamar Malam Haruna mai gidan da muke haya...!
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣5⃣
Bayan Inna ta amsa sallamar ta je ta ɗauko hijbinta ta saka sannan ta ƙarasa ƙofar gida suka gaisa da shi. Sama-sama na ke jiyo firar da suke har Inna na faɗin Innalillahi, kamar na unƙura na tashi sai kuma wata zuciyar ta ce na zauna tunda maganar manya ce ake ko ma minene idan ta zo ai zanji, sai dai jikina na ta raya min ba abun daɗi ba ne.
Sun ɗan ɗauki lokaci suna maganar daga bisani na ji muryar Inna tana roƙon a tausaya mana shi kuma yana faɗin babu yadda zaiyi. Bayan sun gama maganar Inna ta dawo cikin gida jikinta a sanyaye fuskarta kuma na nuna alamun damuwa.
“Lafiya Inna miya faru?”
Zama ta yi kusa da ni tana nuna min kuɗin dake hannunta.
“Wai an sai da gidan ya kawo mana ragowar kuɗin hayarmu na wata takwas kuma wai sati ɗaya wanda ya siye gidan ya bamu”
Kamar daga sama aka jefo maganar haka na jita cikin kunena, zuciyata ta hau bugawa da hauri na zaro ido hannuna a ƙirji na ce
“Sati ɗaya kuma? Waya siye gidan ne?”
“Oho”
Ta faɗa idonta cike da ƙwalla, furucin da na yi na ɗazun ne ya fito da Sakina, Jamila da kuma Noor da gudu suka nufo inda muke zauna suna ta rabon idon da son jin abunda muke tattaunawa.
“Inna miya faru?”
“Tashi zamu yi Sakina an saida gidan”
Inna ta amsata cikin wani irin kalar murya marar daɗi.
“Tau ina zamu koma, waya siye gidan hala?”
Jamila ta tambayi Inna.
“Allah masani”
Dukansu ɓata fuska suka yi da alama suma maganar tashin be musu daɗi ba domin sun saba da unguwar anan haifesu ga ƙawaye da ƴan'uwa kusa da su taya zasu jidaɗin tashin? Idan muka tashi ina zamu koma ? Babban gida ko ina?
“Haya yanzu tsada take ina ma zamuje a bamu ɗaki ban sani ba, babban gida ma idan muka ce zamu zauna babu guri tun da duk sun kame ɗakunan waya ma zai bamu haya da dubu ashirin datara da suka rage mana na ragowar kwanakinmu kai Innalillahi wannan rayuwa daga wannan sai wannan”
Cewar Inna hawaye na zuba a idonta, ni kuma na kalleta na ce
“Ko dai karin kuɗin hayar yake so?”
“Na tambayeshi yace aa shi ai ya riga ya siyar da gidan”
Na yi shiru inata nazari wannan wane irin saida gidana ne ba a shigo ciki anga yadda gudan yake ba kawai sai muji labarin an siye shi kuma wai sati ɗaya mu tashi? Lallai wannan daga gani shiri ne, kuma ba zai wuce Mustapha ba shine kawai na ke zargi.
“Inna ki kwantar da hankalinki zan koma aiki idan aka biyani kuɗin aikin sai mu haɗa da wannan mu kama wani gidan haya, zan roƙeshi ya yi mana haƙuri har ƙarshen wata zamu tashi mu bar masa gidansa”
Na faɗa ina kallon Inna sai Sakina ta ce
“Ko kuma a faɗawa Ya Bilal”
Na katsa mata tsawa.
“Ke wane irin Bilal kuma Wallahi duk wacce taje cikinku ta faɗa masa sai na ɓata mata rai, haka kawai sai mu ɗauki lalurar duniya mu aza masa, shi ma ai yana da tashi lalurar”
Haka muka wuni gidan shiru-shiru kamar wanɗanda aka yi ma mutuwa duk jikinmu ya yi sanyi, tsoron kwana da muke ji a gidan sai ma ya cire mana saboda hankalinmu ya karkata kan wannan matsalar.
Bayan sallah magariba Inna tace naje Babba gida na faɗa musu halin da ake ciki, ba musu na tashi na ɗauki Hijabin da na cire wanda na yi sallah da shi na saka na kama hannun Jamila muka nufi ƙofar fita.
Abun mamaki muna fitowa muka dami Mustapha a tsaye kamar daman can mu yake jira, kallon kallo muka riƙayi da shi, idonsa narau-narau fuskarsa abun tausayi kamar mai shirin yin kuka, ni ko babu komai a idona sai wuta mai tsananin ci a lokacin da ta ga maƙiyinta.
“Guri....guri...gurin.. inna na..zo Daddy ne ya aiko...ni-”
Haka maganar ta riƙa taƙe mishi kamar marar gaskiya, ni kuma abun sai ya bani mamaki kuma ya sakani murmushin takaici.
“Like seriously? Wai Mustapha ko baka san gidansu Habiba ba ne? Baka san ni yayarta ba ce?”
Sai ya amsa min da sauri.
“Na sani! Zan iya rantsewa da Allah ni ban taɓa kula kina cikin unguwar nan ba sai da kika mareni, daga lokacin da kika mareni sai na sa aka min bincike kanki a maimakon na tsargu sai na samu kaina da tausayin halin rayuwar da kuke ciki kuma na yi nadamar abunda na yi ma Habiba kasancewarta ƙanwarki, a lokacin da ta sameni ta bani haƙuri akan karna cutar da ke ina ta shirya abunda zan miki na rama abunda kika min amman sai zuciyata ta hanani saboda tausayinki da take, kin fini kwarjini da ƙima Nawwara kuma ke jaruma ce na gano haka ne daga lokacin da kika ɗaga hannunki kika mareni bayan kuma ba dake nake faɗan ba siya kika yi, wannan ya karantar da ni wani abu a rayuwata lalle ni a idon wasu ba kowa bane tun har mace kamarki zata iya ɗaga hannu ta mareni a bainar jama'a, bayan ko ƴaƴan masu kuɗi basu taɓa unƙurin nuna min ko da yatsa ba balle kuma harara.
Na rasa natsuwata daga lokacin da labarin mutuwar ƴar'uwarki ya same ni, mutuwar Habiba ta canja ni Nawwara, ta tunatar da ni abubuwa da dama da na manta i understand the distance between right and wrong, ta kuma ta sanar da ni abubuwan da ban sani ba a rayuwar duniya, if i begin to tell you how terrible i feel for what I did to your family Nawwara you will find a place in your heart to forgive me, da ace kun sanar da ni tana da ciki da na karɓi cikin kuma na ɗauki nauyin komai na ta, but it too late labarin mutuwarta kawai ya sameni ba a faɗa min dalilin mutuwarta ba amman ni na san cikine saboda ance ta yi zubar jini, Nawwara i'm looking forward to corrected all my mistakes, i made a mistake because I am only human dan Allah Nawwara ki yafe min”
Ta yanayin muryarsa nake fahimtar hawayene suke zuba a idonsa, domin duhu ya sauko bana iya ganin fuskarsa da kyau, sai dai na fahimci hawaye yake kamar yadda nima nake tunawa da ƴar'uwata.
“It's too early to ask my forgiveness Mustapha, i know you are here to play a game with me too”
“No don't get me wrong, i know it too early i'm sorry i shouldn't talk about this, ga wannan ko zaku buƙaci yin wani abu da shi”
Jamila na ganin damin kuɗin da ya miƙo min ta juya da gudu ta koma cikin gida. Ni kuma na yi murmushi ina share hawayena.
“Baka ba kanka dariya ba? Tsayawa kana magana da ni be isa yasa ka ji kunyar kanka ba? What kind of stupid are you Mustapha? What make you think zamu karɓi wani taimako daga gareka? Wannan ne yasa ka turo aka kwashe mana komai kuma ka siye gidan da muke ciki just to humiliate us? Or to force us accept your apology? What kind of person are you?”
Na faɗa cikin kuka, har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya yi shiru kamar mai nazari, isowar Inna ce tasa ni saurin share hawayena.
“Lafiya Nawwara?”
“Lafiya ƙalau daman Zakkace aka fitar shine Daddy ya ce a kawo muku”
Shine ya amsata yana miƙa mata kuɗin, ni kuma na yi karaf na ce.
“Karki karɓi kuɗin nan Inna, kuɗin maƙiyinki ne, shine mutumen da ya yi ma Habiba fyaɗe ya yi sanadiyar rabaki da farincikinki kuma shi ya turo mana ƴan fashin nan ya siye gidan da muke ciki saboda kawai mu karɓi taimakonsa...”
Mutuwar tsaye Inna tayi na ɗan wasu mintuna sannan taja hannun Jamila da Sakina ta mayar da su cikin gida ni kuma ta ce da ni.
“Nawwara shiga gida”
Ba musu na juya na shige cikin gida sai ta maida ƙofar ta rufe, duk muka yi ɗaki har ita, na yi tsammanin zan ga hawaye ko makamancin haka a idon Inna amman ban ga komai ba muryarta ce kawai take iya karantar da ni damuwarta.
“Daman na yi zaton shine ya aiko da ƴan fashin nan, kuma na san babu wanda zai saye wannan gidan sai shi, amman ban taɓa tsamanin shine ya lalata min rayuwara ƴa ba...”
Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciyata, daga ni har ita bamu kwana cikin daɗi ba a wannan daren gashi zuciyata na ta saƙa min zuwa gurin aikin ko kuma na haƙura.
*** *** ***
JIBRIL POV.
Jingine yake jikin kujerar dinning hannunsa saman kofin tea yana ta zagaye bakin kofin ya gagara sha, babu abunda yake tunani sai rayuwarsu ta baya da Nawwara.
Yana jin lokacin da take waya da Inna Inna na faɗa mata zata so har Abuja ganinta ita kuma tana ta ɗauki da murna, amman sai ya haya ya nuna mata sam baya son sanin family ta.
“Kina jindaɗi kin auri mai kuɗi ko? So that ki kawo min su a gida ko? Ni ke na aura ba iyayenki ba dan haka bana buƙatar ganin kowa a gidana”
Matsowa ta yi kusa da shi kamar zatayi kuka.
“Jibril ya kamata ka san iyayena suma kuma su sanka, ko lokacin da za ayi aurenmu ƙin zuwa ka yi ka gaishesu, bayan kuma an yi auren sau ɗaya suka taɓa ganinka ba zasu tantance ka ba...”
Tsawa ya katsa mata ya shaƙe wuyanta.
“Na faɗa miki bana buƙatar ganin kowa anan, ba iyayenki ba har abokanki bana da buƙatar ganinn kowa karki kuskura kawo min kowa a nan, annoba kawai...”
Tuna wannan yasa shi sauke wani dogon numfashi har yana buɗe baki.
“Taya zan tunkaresu yanzu? Ya Allah help me”
Ya faɗa yana kallon Siraj da ya shigo yanzu riƙe da file a hannunsa.
“An gama komai mum nika masa kuɗin gidansa ya sayar mana ya bamu takardu mun bashi kuɗi kuma mun faɗa masa sati ɗaya muka ba ƴan hayan”
“What...?”
Ya ture kofin tea ɗin ya miƙe tsaye.
“Sati ɗaya ya yi nisa Siraj a basu kwana biyu ko uku, miyasa baka da tausayi ne baka san halin da nake ciki ba i can't live without her”
Siraj ya matso kusa da shi ya dafa kafaɗarsa.
“Cool down my friend, Nawwararka ta dawo aiki yau da safen nan”
Jibril ya juya baya yana lumshe ido tare da jan sauran cocaine ɗin dake hancinsa.
“Joke apart Siraj”
“i'm not joking, yanzu aka kirani wacce ake aikawa saƙon ta dawo aiki ta dawo amman bata da uniform na ce a bata sabo”
“Oh my God”
Ya furta ya nufi bedroom ɗinsa da sauri yana cire vest ɗin dake jikinsa. Siraj kuma ya bishi da kallo yana taɓe baki.
*** *** ***
MUSTAPHA POV.
Yafi ƙarfin waya ɗaya a tsaye ƙofar gidan bayan Inna ta rufe gidan, sannan ya kama hanyar gidansu yana tafiya da ƙafa kamar yadda ya zo zuciyarsa cike da mamaki, daman sai yanzu Nawwara take faɗawa Inna kenan Habiba Nawwara kawai ta faɗawa bata faɗawa Inna ba.
Ko da ya isa gida jikinsa a mace ko part ɗin mahaifiyarsa be leƙa ba ya yi shigarwasa part ɗinsa, sallah isha'i a cikin ɗakin ya yi ta. Tunani Nawwara ne ya tsaya masa a rai har garin Allah ya waye be bachi be ko zo kusa da idonsa ba balle ya ɗauke shi, be taɓa samun kansa cikin irin wannan halin ba sai a yanzu.
Kamar sallah isha'i itama sallah asuba a cikin ɗakinsa ya yi ta, yana ta roƙon Allah ya yi masa sauƙin abunda yake ji a zuciyarsa. Misalin sha ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta shigo ɗakin sai ya yi saurin juyawa kamar mai bachi. A aladar shi tara na safe yake fitowa su yi breakfast goma ya shirya ya wuce gurin aiki amman yau ga shi har shaɗaya na safe bata ji ɗuriyar ɗanta ba dole ne ta duba tun da taga motarsa ta tabbatar da yana gida.
“Son...”
Ta kira sunansa a hankali tana zama saman gadon kusa da shi. Juyowa ya yi ya kalleta ba tare da ya amsa ba. Jan da idonsa suka yi suka kumbura ya tashi hankalinta sosai, da sauri ta kai hannu ta taɓa kansa.
“Baka da lafiya ne your temperature is so high, miyasa same ka, bari na kira likita”
Tana miƙewa tsaye sai ya riƙa hannunta.
“Please tell me Mom ya zakiji idan kika rasa ni?”
“What...?”
Ta dawo ta zauna tana masa wani razanannen kallo, shi kuma ya tashi zaune yana kiran amsarta.
“Zan haukace Son, ƙara dai ni na mutu kai ka rayu, kai kaɗai gareni fa bani da kowa sai kai i can't afford to lose you, don't talk about this please, you have no idea how mother could feel if she lose her own child, her happiness, kai kaɗai gareni Son ka daina kawo zancen mutuwa a yanzu”
Razani, tsoro da fargabar da ya ganin a fuskar mahaifiyarsa ta karantar da shi halin da mahaifiyar Habiba take ciki.
“Ba zasu taɓa yafe min ba losing a father, mother, child is unforgettable pain ba zasu taba yafe min ba”
Ya furta idonsa na kallon window ɗakinsa. Sai mahaifiyarsa ta kama hannayensa.
“Su wa?”
“Ƴan'uwan Habiba”
“Wace Habiba?”
“The woman i raped”
“When... How”
“Yarinyar da tazo gurinki neman kuɗi kika hanata, ni na yi mata fyaɗe na bata kuɗi and now she's dead”
Hankalinta ya ƙara tashi.
“Fyaɗen da kayi mata ne silar mutuwarta? Taya?”
“Ciki tayi iyayenta suka je zubar da cikin garin zubar da cikin ta rasu”
Ta yi saurin riƙa fuskarsa dan bata son tashin hankalin ɗanta ko kaɗan.
“That's the point Son ba kaine silar mutuwarta ba karka matsawa kanka, su sukaje zubar da cikin ƴarsu suka kasheta”
“Amman ni ne silar cikin”
Shiru ta yi tana ta tunani babu yadda ba tayi ba akan ya daina neman mata amman yaƙi ita kanta abun yana damunta amman gudun ɓachin ransa yasa take ɗaga masa ƙafa ga kuma ubansa da ya tsaya masa kai da fata akan yadda duk yadda yake so a gari ga taka wanda duk ya yi masa ba dai-dai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗora hannayenta saman kafaɗarsa ta ce
“Son kai ne Sila amman idan ka roƙi Allah zai yafe maka, kuma hukunci za a masa sai dai ayi maka mukuncin wanda ya yi zina su kuma iyayenta ayi musu na kisan kai, zan toƙa maka Allah ya yafe maka kuma kaima ka roƙa Allah ya yafe maka”
“Amman Mom su iyayenta ba zasu yafe ba, musamman yayarta Nawwara”
“Idan Allah ya yafe maka ko da su basu yafe maka ba babu komai, kawai ka natsu na daina wannan halayyar”
“Na daina Wallahi Mom, amman idan Nawwara bata yafe min ba i will never ever being in peace and happiness, because i love her...”
Kamar wacce akayi ma shocking haka ta ɗauke hannayenta daga kafaɗar Mustapha tana kallonsa baki sake.
#RAI BIYU #RB
#TEAM MUSTAPHA
#TEAM BILAL
#TEAM JIBRIL
Bari mu ga TEAM ɗin wa suka fi yawa....? 😁
CANDY ce 👌
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣6⃣
Bayan su Sakina da Jamila sun wuce makaranta ni kuma na shiga gyaran gida, ina tsaka da wanke-wanke wayata ta ringing kamar ba zan ɗaga ba saboda bana son tashin idan ina aiki har sai na kammala, sai kuma na cire kuiya na miƙe tsaye na nufi saman window inda wayar take na ɗauka, Bilal ne ke kira da gangan na tsaya masa yanga har sai da ta kusa tsinkewa sannan na ɗaga cikin muryata mai nuna tsatsan babu ruwana.
“Assalamu Alaikum”
“Nawancy i'm glad muryarki na fara ji yau da safen nan”
“Baka je aiki ba?”
“Yanzu zan wuce ɗan leƙo waje na ganki”
“Bilal duk na yi datti aiki nake yi”
“Ai nafi son ganinki da dattin kin fi kyau, leƙo mana ke kaɗai nake jira”
Babu yadda na iya dole na amsa masa da tau na ɗauki Hijabi na saka na leƙa waje da fuskata a she yana nan daf da ƙofar gidan jikingine yana jiran fitowata.
Murmushi na sakar masa ina kallon yadda suit ɗin jikinsa ya karɓesa ya fito da kyausa chocolate skin ɗinsa sai shining take kamar wani sabon ango. Shi ma murmushin yake min yana nuna min wani bafulatani dake tsaye da jarkokin ruwa a wheelbarrow.
“Ragowar ruwan da aka zuba mana a cikin gidane Mama ta ce a kawo muku”
“Na gode sosai Allah ya saka da alheri”
“Amin”
Ya faɗa ni kuma na juya da nufin komawa cikin gidan domin nunawa mai amalanken inda zai zuba ruwan, sai kawai na ji Bilal ya kirani.
“Nawancy”
Ina juyowa sai kawai ya kanne min ido ɗaya sannan ya kama gabansa yana tafiya kamar ba shi ba.
Nikan dariya ma abun ya bani wani lokacin Bilal yana min abu kamar wani ƙaramin yaro, hakan kuma ba ƙaramin ƙara min son kasancewa da shi nake ba. Komai na cikin gidanmu sai da aka ciki har muka bada sauran jarka biyu maƙota kasancewar ruwan ya yi mana yawa, hakan ne ya tabbatar min da cewar ba Mahaifiyarsa ce ta siye ruwan ba shine dai ya siya ya yi mata kamfen, taya ma zata siya mana ruwa haka kawai.
Bayan mai ruwan ya gama juyewa na koma na cigaba da wanke-wankena zuciyata na ta shauƙin begen Bilal, alƙairinsa nake ta tunawa da kuma irin son da yake yi ma Noor da kulawar da yake bamu, lallai idan har rayuwarsa zata kasance a haka har abada to kuwa matarsa ta yi dacen mijin da zai taimaka mata ta tashiga aljanna, domin ni kan nasan ba ajina bane domin babu yadda za'ayi mahaifiyarsa ta barshi ya auri bayan ta yi iƙirarin wayo kawai nake masa wai na yi aure har biyu kuma da yaro kuma na ce zan auri ɗanta shi da yake saurayi ƴan uwansa ma basa so mahaifinsa ne kawai be ce komai ba shi ma kuma ina tunanin baya ra'ayin haka.
‘Amman tun da shi yana son ki ina ruwanki? Ai da shi zaki zauna ba da iyayenshi ba’
Wata zuciyar ta tambayeni, har ga Allah idan har na ƙi auren Bilal saboda iyayensa zai iya ɗaukar na yi masa butulci ne kawai domin shi baya la'akari da wannan shi di kullum maganar ɗaya ai shi dai yana so na, na san ko da na aureshi ba zai taɓa bari kowa ya wulaƙantani ba kuma zai maida Noor kamar ɗansa.
Haka nake ta saƙe-saƙe na ina aikin har na gama na shiga wanka na fito ina ta tunanin alfanun auren Bilal domin ni dai har yau ban hango wata illa auren Bilal ba idan har iyayensa zasu amince ya aureni ɗin, sai dai kawai na shirya fuskarta familynsa masu uban yawa da cecekuce.
Abaya na saka na ɗauki ɗankwalin abayar na yafa akai na, na saka baƙaƙen talkami sai dai fuskata bata da wata kwalliya domin ko hoda ban shafa ba bayan man da shafa, na ɗauki jar jakata na saka wayata a ciki na nufi ɗakin Inna, ina shiga sai na sameta har yanzu tana bachi, daman na san za a rina tunda jiya ta raya dare da tunanin Habiba a duk lokacin da na farko zaune na ke ganinta saman carpet ta rafka tagumi nasan wannan ba zai rasa nasaba da maganar da na faɗa mata ba jiya lokacin da Mustapha ya zo. Tashin na ta ya zame min dole ne domin bana son na je aiki ba tare da ta sani ba, dan haka na taɓata a hankali na tasheta har ta buɗe ido sannan na faɗa mata zan tafi, addu'a tayi min da fatan nasara ni kuma na fice ina amsawa da Amin.
Kamar ni ake jiran an fito sai na samu motar kamfaninsu Jibril a tsaye direban yana neman yaron da zai aika, yana ganina ya yi saurin fitowa cikin ladabi ya miƙa min wasiƙar ni kuma na karɓa ina wani shu'umin murmushi na yi sighing sannan ya wuce ni kuma na jefa takardar a jakata na kama hanyar zuwa gurin aikin.
Ko da na isa bakin gate ɗin kamfanin, ƙarfe tara ta yi har da rabi, da fari guards ɗin dake bakin gate ɗin sun tareni a da na nuna musu id cart ɗina da ya rage ban ƙone ba a cikin kayan aikim kamfanin sai suka bani dama na shiga bayan sun tambayeni dalilin saka Uniform ɗin sai nan faɗa musu uniform ɗin ya ƙone ne, da na shiga kamfanin sai na nufi gurin da aka tanada domin aje wasu abubuwan da mutun yake shigowa da su wato wani ɗan katon cabinets ne da aka tana domin ma'aikatan gurin su riƙa aje komai na su idan sun rufe sai su tafi ta makullin. Wayata da jakata na aje bayan na kulle na nufi reception na rubuta sunana da kuma lokacin da na shigo sannan na yi musu complain ɗin bana da uniform sai suka ce na wuce kawai.
Da kunnena na ji lokacin da ɗayan yake sanar da zuwana a telephone da halshen nasara wato turanci.
Yadda na tarar da gurin ya tabbatar min da wata ta fanshe a aikin, domin alamu sun nuna wata ta yi mopping ɗin kamin zuwana. Amman hakan be dame ni ba na ɓa ɗaure mayafin abayata a kaina na ɗauki bokiti da mop na fara aikina mutane dake ta kai kawo a gurin na ta kallona domin sun san an yi mopping ɗin gurin ni kima na zo ina ƙara yi.
Irin ƙamshin turaren da naji lokacin da muka zo tare Bilal irinsa na ƙara ji a wannan karon, ƙamshin turaren dana tsana a duniya wanda ke haddasa min ciwon kai a duk lokacin da na jishi.
Ko da wasa ban yarda na juya ta baya da nufin ganin mai ƙamshin ba, duk da jikina ya bani akwai mutun tsaye a bayana. Mutane dake gurin da waɗanda zirga-zirga na ga duk sun fice ɗaga gurin kamar ƙyabtawar ido wata ƙila da kai ya yi musu magana da su fita domin ni ban ji kalma ko ɗaya ba, kawai dai na hango yadda duk suke shiga natsuwarsu daga bisani kuma naga sun tashi sun fice da sauri kamar wanɗanda aka kora.
Hakan yasa na juyo sai idanuwana suka sauka cikin nasa, hakan yasa ni haɗe fuska kamar baƙin hadari, na wulgarda abunda ke hannuna na nufi ƙofar fita, sai ya biyoni da sauri yana kiran sunana. Juyowa na yi a fusace ina jiran jin dalilin kiran sunan, shi kuma ya gagara cewa komai bakinsa sai rawa yake idonsa na yawo saman fuskata. Ganin ba shi da abun cewa yasa na juya na cigaba da tafiya lifted na nufa shi kuma yana biye da ni sai kiran sunana yake mutane dake gurin kowa yaja baya ganin ya nufo lifted waɗanda suke cikin office's kuma na kallonmu kasancewar duk office's ɗin glass door ne na ciki yana hango na waje kamar yadda na waje zai iya hango na ciki, kallon mamaki suke ganin yadda ya biyoni yana kirana ni kuma naƙi na tsaya.
Daf da zan shiga Lifted ya miƙa hannunsa ya riƙoni.
“Nawwara ki saurare ni mana....!”
Tassss na yi ƙarfin halin wanke masa fuska da mari mai kyau, har sai da ya lumshe ido, komai da ke hawa na uku sai da ya tsaya kasancewar ma'aikatan dake aikin gurin suka ɗauke hannayensa masu tafiya kuma suka tsaya cak suna kallon ikon Allah.
“Karka sake kuskuren kai Hannunka ka taɓa min jiki, ka ɗauka nima kamar sauran ƴan matanka nake ko? Karuwai masu binka? To ni ba ƴar iska ba ce kar hannunka ya sake taɓa jikina shashasha kawai”
Har lokacin da nake masa wannan furucin be buɗe ido ba, ni kuma ban fasa faɗa masa abunda nake so ba, a gurin baka jin ƙarar komai sai na muryata da kuma sautin takun talkamin Zinatu wacce ta doso inda muke rai a ɓace, tana ƙarasowa kusa da mu ta ware hannu zata rama marin da na yi ma Jibril sai ya yi saurin buɗe ido ya yi karaf ya riƙe mata hannu.
“Don't...”
Ya faɗa cikin muryarsa dake amsa amo biyu. Cike da tsananin mamaki Zinatu ta kalleni da kalleshi ta ce.
“Baka ga abunda ta yi maka ba?”
“She's My wife....”
Ya faɗa rinannun idanuwansa da suka kaɗe suka yi ja suna kaina, ni kuma na yi murmushin takaici na tattara yawun bakina na tofa masa a fuska.
“Tuuff Allah ya tsare Nawwara da zama matar Jibril, matar da ka kira da annoba yau ita kake kira da matarka? Matar da kace ganin baƙin maciji ya fi maka ganinta, matar da ka ce baka ƙauna bata dace da kai ba yau ita kake kira da matarka? Matar da ka wulaƙanta ka fifita karuwa akanta? Matar da ka kira mashiririciya ƴar talakawa ita kake kira da matarka? Matar daka zalumta ka dannewa haƙƙi ita kake kira da matar da baka son abokanka su ganta yau ita kake kira..”
“Enough....!”
Ban ƙarasa ba ya katsa min tsawa idonsa cike da ƙwalla wasu kuma sun ganganro zuwa kumatunsa. A maimakon na yi shiru sai hakan ya bani damar cigaba har ma da nuna shi da yatsa.
“Ba irin da bane Jibril, Nawwara da ka sani a baya ba ita ba ce a yanzu, tirr da kai Jibril, tirr da haihuwar ɗa irinka, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata, azzalumi macuci maha'inci, wanda be san komai ba sai zalinci da cin amana”
Hawaye nake ina faɗin wannan maganar kamar yadda shi ma yake hawaye kamar ba gobe, a ada ne na faɗa masa wannan maganar dukana zai yi har sai na faɗi uban da ya aikoni, amman abun mamaki sai ya faɗi saman gwuiyoyinsa ya fashe da kuka yana ƙoƙarin riƙa ƙafafuna abunda ya bawa kowa na gurin mamaki.
“Ki yi haƙƙuri Nawwara dan Allah ki yafe min...”
Da gaske hawaye yake kamar yadda nima nake hawaye na tsanarsa da kuma tuna irin zalumcin da ya yi min. Mutume nan ne ya shigo wanda ya taɓa shigowa a wacan lokaci da nake cikin office ɗinsa, shi ne ya yi ma duka ma'aikatan dake gurin magana suka fice da sauri ciki har da Zinatu da jikinta ya gama yin sanyi da mamaki.
Sai kuma rage daga ni sai Jibril sai kuma wannan mutumen, baya baya nayi sai Jibril ya matso da sauri ya rumgume min ƙafafu yana kuka kamar ba shi ba.
“I'm sorry Nawwara i'm so sorry”
“Haƙuri kake bani da gaske ko Jibril?”
Ya yi saurin ɗago kansa yana gyaɗa min kai a tunaninsa zan haƙura ne.
“Waya faɗa maka zan yafe maka? Miyasa zaka yaudari zuciyarka da abunda ba zai taɓa zuwa maka ba? Nawwara will never ever ever forgive Jibril for what he did to her, indai har wannan ne yasa ka riƙa aikamin wasiƙar aiki to ka daina wahalar da kanka”
Ya yi saurin miƙewa tsaye ya riƙa fuska yana girgiza min kai.
“No no no ba haka ba ne Nawwara i just want be close to you i need..”
“Close to epidemic? Close to black snake...”
Ya yi saurin rufe min baki yana kuka kamar ƙaramin yaro.
“Nawwara please...”
Hannu nasa na janye hannunsa ɗaga baki na ce
“Na tsaneka Jibril na tsani duk wani masoyinka, na tsani farincikinka kukanka shine farincikina na tsaneka Allah ya wandaranka”
Na juya cikin kuka na danna lifted ta buɗe na shiga, ina jin yadda yake ƙoƙarin riƙoni abokinsa ya hanashi. Ko da na fito reception kowa kallona yake nasan baya rasa nasaba da hawayen dake zuba a idona. Gurin dana aje jakata na nufa na ɗauka ina hawaye na fice.
#RB
#TEAM MUSTAPHA
#TEAM JIBRIL
#TEAM BILAL.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣7⃣
*MUSTAPHA POV.*
A hankali ya yi parking ya fito daga motar kamar marar lakka ya nufi part ɗin mahaifiyarshi.
Tana hakimce saman kujeara ya shigo jiki ba ƙarfi kamar marar lafiya, gaba ɗaya sai ta tattara hankalinta ta maida gunsa tana kallonsa har ya zauna a kujerar dake gefenta na dama.
“Son na yi ta kiran wayarka kashe, tun da ka fita baka dawo gida ba sai yanzu hankalina duk ya tashi, kuma ka kashe duka wayoyinka”
“Ina Office”
Ya amsa mata cikin muryar dake nuna tsantsar damuwarsa. Tashi tayi takoma kusa da shi ta zauna tana ɗaga bayansa.
“Duk tsawon lokacin nan kana office? Haba son miyasa zaka riƙa wahalar da kanka kana damuwa ga abunda har ga Allah baka da laifi? Bafa kai ka kashe yarinyar nan ba dan mai zaka damu kanka su suka kashe ƴarsu da kan su”
Juyowa ya yi ya kalleta.
“Momi ke kika siye gidansu Nawwara?”
“What why would i?”
“Lokacin da naje gidansu Nawwara ta yi wani furuci da ke nuna an siye gidansu kuma an basu kwanaki kaɗan su tashi ke ce ko Momi?”
“Wato Mustapha har gidansu yarinyar nan kake zuwa fira? Yarinyar da basu da tarbiya ga shegen hassada ya yi musu yawa, dan Allah ka cire yarinyar nan a ranka Wallahi ba ajinka ba ce”
“Da ace ni na sakawa kaina son ta da na cire shi cikin sauƙi ba tare da kanki kin sani ba, na yi iya ƙoƙarina na ganin cewar na gujewa soyayyarta amman sai na kasa, babu yadda za'ayi na sakawa kaina ƙaunarta Momi Allah ne ya saka min”
Ya miƙe tsaye ya zuba hannayensa a ajihu.
“Please Mom ki maida musu da gidansu, kuma karki sake yin wani abu da zai takurawa rayuwarsu, idan har baki tayani neman yafiyarsu ba to be kamata ki ƙara ɓata min suna a gurinsu ba”
Yana kaiwa nan ya nufi ƙofar fita cikin yanayi marar daɗi, Hajiya ma miƙewa ta yi tsaye ta bishi da kallo har ya fice sannan ta ce
“Wato revenge ɗin da zata ɗauka ta haɗa ni da ɗana ko? Uhmm Wallahi Nawwara kin deɓo ruwan dafa kanki, duk kika ce zaki shiga tsakanina da ɗana bake ba kaf ɗanginku sai na hana musu zama lafiya, kuma Wallahi ɗana ba zai taɓa aurenki ba ƴar matsiyata kawai”
faɗa take tana huci tsabar jin zafin ɗanta ya kamu da son Nawwara. Ɗakin ta nufi tana da bala'i har su Zarah da Ikram suka fito ɗaga ɗakinsu jinyo muryarta tana matsifa.
*** *** ***
Around eight am kowa ya hallara a dinning ɗin cin abincin safe ban da Mustapha, hakan be damu Hajiya ba domin ta san halin da ɗanta yake ciki, sai kawai ta cigaba da jera kayan abincin tare da su Ikram da kuma Ma'u mai aikinta. Fitowar Alhaji ne yasa Zara dake ɗaki fitowa domin yin breakfast ɗin, ganin babu kowa a kujerar Mustapha yasa Alhaji ya kalli uwargidansa ya ce
“Yau ma ba zai yi breakfast ɗin ba?”
Ikram ta yi karaf ta ce
“Ai daman sai tara yake karyawa”
Hajiya kuma ta taɓe baki tana cigaba da haɗawa Mijinta tea ta ce
“Ai ina ganin tsakanin jiya da yau in ban da ruwa babu abunda Mustapha ya ci, ko jiya be fita aiki ba sai sha biyu na rana be dawo gida ba sai da isha'i”
Kallon rashin fahimta Alhaji ya yi mata yana ɗaukar tea da ta aje masa ya kurɓa
“Saboda mai?”
“Uhmm saboda yarinyar nan mana”
Wani dogon tsaki Alhaji yaja ya kalli Ikram a fusace ya ce
“Jeki kira min shi wannan ai iskancin banza ne”
Da sauri Ikram ta tashi ta nufi ƙofar fita, bata ɗauki dogon lokaci ba sai gata ta dawo falon tare da Mustapha dake cikin shigar kayan bachi.
“Good morning Dad”
Ya faɗa murya can ƙasa-ƙasa kamar wanda baya son magana.
“Seat”
Alhaji ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar da ya yi masa ba, ba musu Musyapha yaja kujera ya zauna yana fuskarta Daddynsa, mahaifiyarsa taja kujerarta ta zauna tana kallon ɗanta a natse Alhaji ya fara magana ta yadda ɗan nasa zai fahimta.
“Mustapha ka daina damunka kanka nayi imani har ga Allah baka da laifi akan wannan lamarin, saboda ba kai ka kasheta ba iyayenta ne silar mutuwarta. And a part from her sister ka aje shi a gafe domin ba tsararka ba ce, idan ma aure kake so ka nemo ko ƴar wani gidace ni zan aura maka ita amman ba dai wannan yarinyar ba”
Sauke idonsa ya yi ya kalli tea ɗin da Ikram ta aje masa a gabansa sannan ya sake data kai ya kalli mahaifinsa ya ce
“Dady ita kaɗai ce macce da nake so”
“No Look Son yarinyar nan ba ƴar gidan mutunci ba ce sannan aurenta biyu fa kai kana sauranyinka ka ce zaka aureta, after that yaron dake hannunta yanzu ana zargin shege ne fa bashi da uba, wasu ma na cewa babu wani aure da tayi zaman banza ta yi abuja ta dawo da ciki sai wannan auren da ta yi na biyu, ba ƴar gidan tarbiya ba ce Mustapha ƙara ka auro ƴar mutunci kuma ƴar gidan mutunci”
Mahaifiyarsa ya kalla domin yasan ita kaɗai ce zata iya faɗawa Daddynsa wannan maganar, kallon mahaifinsa ya sake yi
“Amman ina fatar Momi ta faɗa maka ni na lalata ƙanwarta ko?”
Alhaji ya yi saurin girgiza kai.
“No no son ba kai ka ɓata ta ba, daman can yarinyar lalatacciya ce, mahaifinta ma ance sata ya yi da aka mashi aka masa shegen duka har ya mutu....”
Zarah dake aikin tsire baki tayi karaf ta ce.
“Wallahi sam yaran gidan nan basa da mutunci ko kaɗan”
Tsawa Mustapha ya katsa mata.
“Idan ana maganar tsakanin Uba da ɗa ki daina saka bakinki a ciki”
Momi ma ta katsa masa tsawa.
“Ta daina saka bakinta iya ba ƴar'uwarka ba ce? Wai mi yake damunka ne Mustapha?”
“Nima ban sani ba, kawai ni dai abunda na sani zuciyata na son Nawwara”
Ya amsa mata da cikakiyar gaskiyarsa, shi kansa a yanzu ba zai iya ayyana abunda yake damunsa ba, kawai dai yana samun kansa cikin wani kalar yanayi da be taɓa samun kansa a cikinsa ba. Alhaji ya buga tebur ɗin da ƙarfi
“Ba zaka aureta ba Mustapha, ana nuna maka hanya kana ba haka ba, ka bar ganin kai kaɗai na haifa zan iya shafe labarinka a doron ƙasa matuƙar ka zaɓi yarinyar can ƴar nasara mutunci”
Miƙewa ya yi tsaye ya nufi ƙofar fita ba tare da wata kalmar ta ƙara fitowa daga bakinsa ba.
“Could you see this?”
“Na gani, ni gani nake kamar ba banza suka barshi ba, dan ni ban taɓa ganin yarimyar da Mustapha ya zo ya ce min yana so ba duk wanda na gansu tare zai ce abokiyar aikinsa ce ko abokiyarsa, amman be taɓa buɗe baki ya ce min ga wacce yake so ba sai wannan zagalar, duk yabi ya canja saboda wata ƴar iskar yarinya, jiya ma haka ta zugoshi yazo ya rufeni da masifa wai na siye gidansu, ni kuma ban san na siye wani gida ba wata ƙila so take ya ɗauki maƙudan kuɗi ya ɗanka mata”
“Bari ai zamu saka ƙafar wando ɗaya da shi”
“Da shi kuma? Sai dai da su ai su suka susuta naka yaro, shi kaɗai fa Allah ya bamu idan ka saka ƙafar wando ɗaya da shi ai abun akan mu zai koma”
Ƙwafa ya yi ya cigaba da shan tea ɗinsa yana ta huci.
*** *** ***
JIBRIL POV.
Be bar kamfanin ba sai tara na dare, ko da ya isa gida jikinsa da mugun nauyi kamar wanda ya yi wani aiki, bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower ya lumshe ido yana sauraren yadda tsanyin ruwa ke ratsa jikinsa.
‘Nawwara will never ever ever forgive Jibril for what he did to her’
Shine abunda ke ta masa yawo a cikin kai, zuciyarsa na wani irin zafin, sai goma har da kwata sannan na bar bathroom ɗin cikin yanayi marar daɗi.
Vest ya saka da ɗan guntun wando, be shafa mai ba amman ya shafa turare, sannan ya fito parlour ya haɗa ma kansa tea ya zauna saman cushion yana kallon hoton nawwara Tea ma sai ya gagara sha. Yana zaune gurin har shaɗayan dare ta buga be ko motsa daga inda yake ba. Siraj ne ya turo ƙofar falon ya shigo hannunsa riƙe da takardu masu yawa, ɗakin karatun Jibril ya nufa ya aje takardun sannan ya dawo ya zauna kusa da shi yana faɗin.
“Gaskiya yau Jibril ka bani mamaki, wai su waye iyayen yarinyar nan ne da har zata wulaƙanta a gaban jama'a ka ƙyaleta?”
Sai a yanxu ya gincira saman kujerar yana cigaba da kallon hoton Nawwara.
“Maruƙar haka zai sa ta yafe min, zan jure har sai ta yarda da na yi nadama kuma na tuba”
“Wannan ba revenge ba ne, it's an embarrassment, ko ma mi kayi mata baka cancanci ta yi maka wannan tuzarcin ba, su fa mata ba a ƙyalesu hakan ya bata damar cigaba ne, gaba ɗaya yau ak kamfanin nan kai aka wuni ana magana wannan ai tozarci ne”
Murmushi Jibril ya yi ya kalli Siraj ya ce.
“Data mareni a gaban mutane na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta airport, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a gaban iyayena, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a bakin titi na jefar da ita na yi tafiyata, at least now na san yadda mutun yake ji idan aka disgashi gaban jama'a”
Siraj ya juyo yana fuskarta shi da kyau ya ce.
“Kana da banbanci da kowa Jibril be kamata ka auna kanka da sauran jama'a ba, weather you like or not abunda yarinyar nan ta yi maka bata kyauta ba”
Miƙewa Jibril ya yi tsaye ya nufi window falon yana faɗin.
“You're my new tight friend Siraj, bana son kana faɗar wata kalma marar daɗi a kan nawwara, saboda hakan zai sa na tsane ka ita kuma na ƙara ƙaunarta, zan iya jure ko wani kalar wulaƙanci daga Nawwara matuƙar hakan zai sa ta yafe min, soyayyata da ta rasa a can baya ita nake son nuna mata a yanzu, kulawar da na gagara bata a da, ita na ke son bata a yanzu.
Na wulaƙanta yarinyar sosai Siraj irin wulaƙanci da ban taɓa tsamanin Allah zai jarrabeni da son kamar haka ba, a gaban idonta na ke shigowa da budurwa a gidanta kuma ta dafa mana abinci ta haɗa mana ruwan wanka, ta san fasadi muke aikatawa amman haka be taɓa damunta ba, ko da yana damunta bata taɓa nuna min ba. Idan ta dafa abinci sai ta kawo min tana jiran na yaba mata amman sai na kushe wani ko ci ba zan ba, idan ta yi kwalliya tana jiran na yaba mata ba zan kalleta ba, ban taɓa riƙa hannunta da nunan sha'awaba sai idan zan hukunta ko kuma na doketa, idan mahaifina ya tambayeta ko akwai wata matsalar sai ta ce masa babu komai muna zaune lafiya...”
Hawaye ya zubo masa sai yasa gefen hannunsa ya shafe yana cigaba da kallon titi kasancewar window yana fuskantar titi ne.
“Lokacin da na gano tana da ciki, sai na saka mata maganin bachi a lemu ta sha, da tayi bachi sai na cire mata tufafi na ɗauki hotonta na kai ayi editing aka haɗa da na wani, da gangan na sa aka ɗauko min mahaifinta aka zo da shi garin abuja na tarasu da mahaifina na ce cikin da ke jikinta ba nawa ba ne ga wanda ya yi mata shi nan, i'm very fool Siraj can you imagine na ɗauki hoton mamata na haɗa da hoton wani saboda kawai bana son ta kuma ban shirya haihu da ita ba a wannan lokacin...”
Ya zuba hannayensa aljihu hawaye na ta masa zuba, sannan ya sauke ajiyar zuciya.
“A gaban mahaifinta da mahaifina na nuna waɗancan hotunan kuma na ce na saketa saki uku, sai mahaifina ya ce min saki uku idan aka yi su a take a matsayin saki ɗaya suke dan haka na yi haƙuri na maida matana, jin wannan yasa nace na sake tsaki ɗaya tsaki biyu tsaki uku, a ranar Nawwara ta riƙe min hannaye tana roƙon na rufa nata asiri na karɓi cikin nan, wannan roƙon da ta yi min sai yasa mahaifina ya yarda cewar ba cikina ba ne.
A ranar mahaifina ya tabbatar min da sai na yi nadamar abunda na yi mata, saboda yana ganin ta bi maza ne domin kawai na kasa bata kulawa, ashe da gaske zan yi nadama. Bayan na rabu da ita mace huɗu na aura suka kasa zama aure da ni, wasu basa mutunta ni kamar yadda take, wasu kuma su nuna min suma ƴaƴan manya ne ba zasu iya abu kaza da kaza ba, daga lokacin na fara kewar Nawwara, kuma duk wannan auren da nayi babu wacce ta taɓa samun ciki da ni, kuma ba dan bana haihuwaba ba dan ina da wata matsala ba sai dai isgilancin da na yi Allah ya jarrabe ni, sai bayan na yi aure na biyar ashe ita ba ɗana ba ne ban ganr haka ba sai da na auna jininsa, gudun afkawa cikin wata matsalar sai step mom ɗita ta aura min ƙanwarta, sai da tafiya ta tafi sai na gano kasheni take son yi ta ci gado tun da bana haihu ita kuma tana son haihu amman bata son fita ta bar ɗaular gidana, sai ta saka min guba a abinci shine ciwon da har yanzu yaƙi warkewa a jikina, bayan na rabu da ita na dawo na cewa mahaifina ina son naje gidansu Nawwara, sai ya ce min shi ba babu ruwansa kuma ba da yawun bakinsa ba, saboda na kunyatashi na tozarta shi kuma na ci amanarta bayan shi ne silar aurena da ita, daga ƙarshe ya ce be yafe min na taka ƙafata ƙofar gidansu Nawwara ba, tun daga lokacin sai tunaninta da halin damuwar da na saka ta ya riƙa damuna, wani lokacin na kan rufe kaina ni kaɗai a ɗaki ina kukana amman babu mai bani haƙuri saboda mahaifita bata raye.
Komai nawa sai ya tsaya cak, idan naje asibiti bana iya komai sai tunani da damuwa, wannan ne ƴasa Abbah ya dawo da ni kamfaninsa na nan sokoto saboda na rage damuwa, na jidaɗi da Abbah ya yi min haka ko ba komai ni ma zan yi rayuwa garin da Nawwara ta taɓa rayuwa, lokacin da na zo na haɗu da kai, na saka nemanta sai ka ce min ta mutu kuma iyayenta ma sun mutu, daga lokacin na yafe farinciki da walwala a tare da ni.”
Ya juyo ya kalli Siraj sannan ya ce
“Nawwara ce kawai macce da ta samu ciki da ni ta hanyar halak, Nawwara ce kawai take kula da ni kamar mahaifiyar da ta haifeni, Nawwara ce kawai zuciyata ke ƙauna, ko a can baya ba ƙaunarta ne bana yi ba kawai dai ina ganin ta shigo rayuwata ne a lokacin da be kamata ta shigo ba. Dan haka karka sake faɗin wata mummunar kalma akan Nawwara, na zan iya tukararta kai tsaye ta yafe min ba, amman idan muna zama a guri ɗaya ita da kanta zata fahimci halin da nake ciki ta yafe min, i need to work with her, i need to be close to her”
Yana kaiwa nan ya share hawayensa ya nufi Bedroom ɗinsa, ya bar Siraj a tsaye yana jinjina lamarin.
*** *** ***
Kukana ya yanke tun kan na iso gida, sai dai hakan be hana mahaifiyata fahimtar ina cikin damuwa ba, ga shi na dawo da wuri ban daɗe ba.
“Lafiya kika dawo yanzu?”
“Lafiya ƙalau kawai faɗa muka yi da wani na mareshi sai suka ce na dawo gida”
“Faɗa kuma? Da namiji miya haɗa ku”
“Na goge gurin ne sai yazo yana min masifa har da riƙa hannuna na ni kuma na mareshi”
“Tau kin kyauta kin yi abun a yaba miki kowa ya yi miki ba dai dai ki riƙa hannu kina marensa kinji Allah ya miki albarka”
Na san baƙar magana ta yi min wacce ke nuna bata jidaɗin abunda na yi ba.
“Amman Inna ni ce nai gaskiyafa”
“Idan kina da gaskiya sai ki ɗaga hannu ki mareshi wata ƙila ma ya girmeki, duk wani hali da ba naki ba Nawwara yanzu kin ɗauka kin ratawa kanki, wannan zabin zuciyar na Habiba ke aka saukewa shi? Ita tafi sai masifar ta dawo kanki, wannan ba halinki ba ne Nawwara, kuma ba tarbiyar gidan nan ba ce”
“Yi haƙuri Inna na miki alƙwari ba zan sake ba”
Na faɗa idona cike da ƙwalla, domin ni kaɗai na san halin da nake ciki, ita kanta da tasan wanda na mara da bata min wannan masifar ba. Ɗakinmu na wuce na ci kuka sai da na gode Allah sannan na fito.
Bayan sallah magariba, Bilal ya kirani a waya ya sanar min yana waje, na ɓata lokaci kamin na fita saboda na san maganar da zai min ba zata wuce ta abunda ya faru yau ba, sallama na yi masa amman be amsa min ba sai ya jefo min tambaya.
“Ance min kin kirashi da azzalumi, shi kuma ya baki haƙuri har ya yi iƙirarin kiranki da matarsa, shine Baban Noor ko Nawancy”
Na gyaɗa masa kai
“Shine”
“Daman kin san nan kamfaninsa ne kike aiki?”
“Ban sani ba sai yau”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke.
“Na yi farinciki da ya gane kirkurensa, ko ba komai Noor zai san mahaifinsa na gaskiya”
Na yi saurin girgiza masa kai idanuwa cike da ƙwalla.
“Ba zai sani ba Bilal ba zan iya bashi Noor ba, be san zafin ɗana ba, be san yadda na yi na haifi ɗana ba, be san wahalar da na sha kamin da bayan na haifi ɗana ba, ko sau ɗaya ƴan'uwansa ba su taɓa biyo sawunna su duba lafiyar ɗana ba, Noor be cancanci Uba irin Jibril ba, Dan Allah dan girman Allah karka faɗa masa ina da ɗa zai iya raba ni da ɗana Bilal”
“Ba zan faɗa masa ba, amman dole wata rana zai gano, lokaci yana zuwa Nawancy zaki koma ke da shi kamar ba ayi ba”
Ya faɗa muryarsa na nuna tsantsar damuwar dake cikin ransa.
“Ba zamu koma ba Bilal, babu wanda zuciyata take so take ganin ƙimarsa kamar kai, kai kaɗai ne mutun da zan tuna na yi murmushi, Wallahi kai kaɗai zuciyata take ƙaunara Bilal”
“Ina jin tsoron faruwar wani abu Nawancy”
“Babu wani abun da zai faru, sai idan ba son aurena kake ba, ba son ƙwarai kake min ba, daman can zaka biye abunda mutane suke cewa ka gujeni”
“Ba zan taɓa gudunki ba Nawancy, ina ƙaunarki sosai”
Ya faɗa yana ƙoƙarin kai hannu ya share min hawayena sai na yi saurin saka nawa hannun na share, sai kawai ya saka min dariya.
“Na jidaɗin wannan abun ko ba komai kin nuna min yadda kika so na”
Ni kuma sai na cire talakmena na gwaɗa masa a hannu har sai da ya yi ƙara.
“Ka daina taɓa ni da wannan hannun”
“Nima ba son raina yake taɓa ki ba, kawai dai shi ɗin ne ya damu sai ya taɓa ki, amman ranar da zai taɓa halalinsa zan ga bakin da ya isa ya hana shi”
Na zaro ido ina mamakin kalaminsa, sai ya kannemin ido ɗaya yana murmushi. Mum yi firar da ta ɗebe min kewa fira irin ta masoya firar da ta gusar min da duk wani tunani da damuwa har sai da na dawo cikin gida. Bayan na yi sallah isha'i na ci abincin dare kaɗan saboda kar Inna ta gano abunda yake damuna.
Dakimmu na dawo da zimmar bachi amman sai na kasa rayuwar da na yi a abaya ta dawo min...
FLASH BACK.......
_______________________________________
I can't wait na ji tarihin Nawwara zamanta da Jibril.. 💃
#RB
#TEAM MUSTAPHA
#TEAM JIBRIL
#TEAM BILAL
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣8⃣
Khadija shine sunan da mahaifina ya saka min, sai ya yi min alkunya da Nawwara, duk da kasancewar ba ni ce ta farko ba, ƴaƴƴuna hudu maza duk basu tsayaba sai ni da nazo a ta biyar kuma mace.
Bayan ni sai da mahaifiyata ta shekara biyar sannan ta haifi Habiba, a lokacin Mahaifina yana ta faɗi tashin rayuwa na nema mana abunda zamu ci.
Ba zan kira kaina da kyakkaywa ba, sai nasan ni ba mummuna ba ce, abunda kawai zan iya shaidar kaina da shi shine na ɗauko fari da kuma dogon hancin mahaifiyata kasancewarta fulani, gashin kan ba a magana na girata ma askewa nake balle kuma na gadon bayana dake ƙayatarda mai kallo.
Siye da siyarwar na fatoci, Sana'ar iyaye da kakkanina ce sana'ar wacce mahaifina ya buɗe ido ya samu kansa a cikinta har muma muka zo muka tarar anayi, kowa ya tashi a gidan ana buɗa masa shago ko kuma a haɗashi da wanda zai riƙa masa ja gaba kan sana'ar har ya kafa tashi.
Kusan zan iya cewa sana'ar bata karɓi mahaifinmu ba, tun lokacin da ya fara ba riba ba kuɗi, wani lokacin har kuɗin wani sai sun shiga ciki su ƙi fita, duk lokacin da mahaifinmu ya siyo fata da zimmar saidawa sai karaya ta sameshi wacce zata zama silar da ba zai iya maida kuɗin ba, yayyunsa da Yakumbo da kuma Hajiya Lamtana Allah ya jiƙanta sai suka ɗauki karan tsana suka ɗora ma Ramatu wato mahaifita, a ganinsu ita ce bata da ƙashin arziki, sukan ce wai can kamin ya aureta a lokacin da yake saurayinsa yana sa'arsa lafiya sai da ya aureta sannan komai yaso ya lalace.
A lokacin ina ƙarama amman abun yana min zafi sosai saboda yana damun mahaifiya sosai, har na riƙa kallonsu a matsayin maƙiyanmu wanda har yau shine a zuciyata, domin a lokacin a gaban idonmu suna faɗa wai uwarmu mai farar ƙafa ce wanda hakan suke tunanin ba komai bane ko kuma mu bamu kula ba alhalin yana mana zafi sai dai bamu isa mu nuna ba kasancewar gidan taro ne, ko tari kayi sai anji, Babban gida irin gidan nan ne da kakanni suke siye sai iyaye da jikoki su taru a gidan kowa ya keɓe wani ɓangare nasa ya kafa nasa iyalin.
Lokatuta da dama takan keɓe ita kaɗai ko kuma da mu tayi ta kuka tana roƙon Allah ya bawa mahaifina wani aikin duk da bashi da wani karantun zamani a wacan lokacin, muna haka wani maƙocinmu Malam Buba kuma abokin Baba da yake yawan zuwa Abuja ya faɗa ma Mahaifimu cewar wani attajirin mai kuɗi a garin Abuja yana neman mai masa gadi kuma ya ce baya buƙatar kowa sai bahaushe ɗan'uwansa, Malam Buba ya kasance yana masa gadin wani babban kamfanin siyer da kayan alatu ne dake can garin Abuja.
Muna zaune gida ranar wata talata, bayan mun gama cin kwaɗon ƙanzo, sai Baba ya shigo da far'arsa yana labarta mana abunda Malam Buba ya faɗa masa, Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta, a nan suka yanke shawarar ba zasu sanar da Yakumbo da Hajiya ba saboda sunsan ba zasu bari yaje ba, sai suka haɗa kai da Malam Buba ya faɗa musu Babanmu zaije Abuja ya kai fatune saboda ana bukatarsu a can, sun yi na'am suka masa addu'ah da fatan nasara, sai Baba ya karɓi fatun bashi da sunan idan yaje can zai aiko da kuɗin.
Ranar da zai tafi munyi kuka sosai ni da Inna har ma da wasu mutanen gidan saboda muna ganin kamar ba zai dawo ba, tafiya nisa kuma har garin Abuja garin da a wacan lokacin muke ɗaukarsa kamar wata ƙasar dabam.
Bayan wata ɗaya da tafiyar mahaifinmu sai gashi ya dawo cikin shigar mutunci da kamala, sai dai ya ɗanyi rama kaɗan ya kuma yi haske, ya labarta mana komai yake muna nan cikin ranshi wannan tunanin ne ya hanashi ƙiba, har ma yake faɗa mana cewar mai gidansa ya ware masa wani ɓangare na gidansa ya bashi ya ce ya ɗauko iyalansa su dawo nan kuma ya zo mana da kuɗi mai yawa.
Ba ƙaramin yaƙi akayi ba kamin Hajiya ta yarda ta barmu aka tafi da mu, a nan ma sai da ya yi mata wata ƙaryar cewa ya canja sana'a yanzu yana siye da saida takalma ne na fatu har ma ya ce mata hayan gida ya kama a ƙauyen Abuja acan zai zauna da mu ya cigaba da sana'arsa.
Amaina huɗu a mota kamin mu sauka zaria, aka siya min abinci da ruwa na cika cikina ni da Habiba sannan muka cigaba da tafiyar, ko da muka shiga garin Abuja ina bachi, sai da motar ta tsaya sannan Inna ta tasheni muka koma can wani ɓangare na tashar, Baban mu ya ari wayar wani ya kira Alhaji ya sanar masa mun iso domin ba a shiga da wani abun haya a unguwar.
Dare ya yi sosai har Baba ya yanke shawarar zuwa gurin abokinsa Malam Buba mu kwana a can sai ga ƴan komisho sun zo suna neman Malam Musa Kafinta, a nan suka haɗa mu da mutumen yanayin yadda Baba ya gaisa da shi sai ya tabbatar da cewar ya sanshi, ashe direban Alhajin ne.
Ni da Inna duk da tsoro muka shiga motar saboda ganin Babbar motar kamar wannan wacce ni dai zan iya rantsuwa hannuna ma be taɓa kaiwa akanta, amman yau zan shigeta. Ina ta rabon ido har muka iso wata kyakkyawar unguwa. Idona be ƙara buɗewa har sai da muka iso cikin ƙaton gidan dake cike da ababen more rayuwa.
Iyalan mutumen ne da Alhajin shi kansa suka fito suna tarbonmu, har yake bawa Baba haƙuri akan rashin ɗaukoshi da wuri wai yaje meeting ne kuma sai ya manta sai da ya dawo gida sannan ya tuna.
Cikin Falonsu muka shigo sai suka saka mai aikinsu ta kwashi kayanmu ta kai BQ, mu kuma suka kawo mana abinci da abin sha.
Cikin sati ɗaya muka sake da ƴan gidan kasancewarsu mutane da suka san darajar ɗan'adam tun daga Hajiyar gidan har yaranta, Ƴaƴanta maza biyu manya sannan mata uku ɗayar tana aure sauran biyu kuma a lokacin suna karatune, sai ƴar ƙaramar ƴarta Salima, wacce ta kasance ta shida a cikin yaranta takwas.
Shaƙuwa sosai da sosai ta shiga tsakanina da Salima, har ta kai zuwa makaranta ne boko ne kawai yake rabamu, kasancewar ni bana zuwa bokon sai dai islamiya Alhaji Dahiru wato mahaifinta ya sakani Islamiyarsu.
Duk ƙarshen wata Baba yake zuwa gida duba Hajiya, wani lokacin kuma sai dai ya yi mata aike a haka muka kwashe shakara ɗaya a gidan Tsohon ambasadan nigeria a ƙasar London, muka zama kamar ƴan gida, shaƙuwa sosai ke ƙara shiga tsakanina da Salima, da kuma Babban yayanta Jamal, shi yake koya min karatu duk da ba a sani makaranta ba a lokacin, Jamal mutum ne mai son jama'a da far'a, har ta kai idan be ganni ba sai ya aika an kirani, bayan ya gama koya min karatu sai ya ce na yi masa gatana, ba laifi a lokacin na iya zuba gatana har da wacce ba'a taɓa yi ba, haka zai zauna ya yi ta saureren shirme na wani lokacin har da Hajiyarsu. Shi ya fara yaba ƙwazo na sai ya yi ma mahaifinsu magana aka sakani a makarantarsu Salima, na kashe kuɗi sosai gurin samo transfer dake nuna daga wata makarantar na ke, sannan aka samu sa'a aka sakani aji ɗaya da Salima, Habiba kuma aka sakata wata maƙarantar wacce ƙannen Salima suke yi.
Tare muke zuwa mu dawo, mu tafi islamiya tare, wasa-wasa sai na tattara kayana suka na koma ɗakinta da zama, a lokacin Inna na da cikin Sakina, komai a iri ɗaya muke da Salima bana da ƙawa sai ita itama bata da ƙawa sai ni, idan ba a ganta ba sai an tambayeni haka itama.
Ta ɓangaren Jamal kuma soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk a lokacin ban san miye so ba, na kan samu kaina da tunaninsa da kuma rashin jindaɗi a duk lokacin da baya gida.
Muna daf da ƙare makarantar secondary school ni da Salima Hajiya ta samu labarin cewa Baba gadi yake a wani gida, babu irin bala'in da bata mushi ba cikin har da zance zata tsine masa gidan be dawo ba, wai Inna zata kaishi ta baro yana biye zancen mace. A dole tasa Baba ya tattara ya koma gida sai dai be zauna gidan ba sai ya kama haya kusa da su inda muke zaune har yanzu.
Ni kuma a aka barni nan da sunan idan na gama zana jarabarwar za a maidani gida, bayan mun gama jarabarwa ta fito ta yi kyau, a lokacin ne ɗan wani mai kuɗi ya fito neman auren Salima, Alhaji Dahiru ya yi na'am ya sallama masa bisa sharaɗin zai jirata ta yi karatu na gaba, a lokacin shi kansa yaron be kammala karatunsa da yake ba.
Bayan sati ɗaya da faruwar haka sai Ya Jamal ya fara min zancen aure, ni kuma ina ta tsoro saboda ina ganin kamar iyayensa ba zasu yarda ba, sai na nuna masa bana son shi, duk abunda muke a tsakaninmu ne iyayensa basu sani ba, har Salima ma tada zame min jinin jiki ban taɓa labarta mata ba, shi ma kuma be taɓa nunawa kowa ba.
Bayan takadun mu sun fito sai Alhaji Dahiru wanda muke kira da Daddy ya turo mu gida ni da Salima, bayan ya cika mana bayan mota da abinci, a lokacin an haifi Sakina har ta soma wayo.
Watan mu ɗaya muka garin Abuja saboda sabo sai zaman sokoto ya yi ma Salima wuya, ni kan ban so haka ba, sai dai babu yadda zan yi tun da mun zo tare dole mu koma tare, bayan mun koma sa sati ɗaya na sake dowa, Alhaji Dahiru ne yasa ka Ya Jamal ya rakoni har gida, sai dai wannan karon tafiyar Jirgi muka yi saboda Ya Jamal ya ce ba zai iya bin mota ba zuwa sokoto.
Kwanansa ɗaya ya koma, ni kuma na zauna a nan har na tsawon wata uku a lokacin Mahaifina yana sana'ar siyar da itace a ƙofar gida, wata rana mu cinye ribar wata rana kuma Allah ya buɗo mana, haka muke ta faɗi tashin rayuwa ga masu neman aurena sai fitowa suke. Kwatsan Alhaji Dahiru ya kira ya ce a sanar min ya samo mana gurbin karatun lafiya a ƙasar burtaniya wato London, cikin sati ɗaya na shirya na koma Abuja, duk wani shirye-shirye ina can aka yi shi, bayan kamar wata ɗaya da ƴan ƙwanaki aka kammala komai, sai da na koma gida na yi bankwana da su Inna a lokacin ne Yakunbo ta so tanani zuwa saboda a ganinta kamar za a siyar da ni ne ko wani abu makamancin haka.
Kamar na mafarki na fara karatu a City, University of London, a ƙasar da ban taɓa mafarkin zuwa ba, ƙasar da nake ji a labarai da kuma jaridu, burtaniya ƙasar turawa ce wacce bata da matsatsi akan addinin kowa a wacan lokacin, ba ko yaushe nake irin shigarsu ba wato shigar ƙananan kaya, nafi saka doguwar rigar atamfa ko abaya sai na samu ƙaramin ɗankwali ko hula na yi rolling kaina da shi.
Ɗakin mu ɗaya da Salima da kuma wata tsohuwar ɗaliba makarantar wato Farida, wacce ƴar asalin hijar bauchi ce, cikin ƙanƙanen lokaci muka saba da Farida duk da kasancewar ba gurin karatun mu ɗaya ba. Ranar da muka fara zuwa lab wani babban likita muka tarar ɗan Nijeria dan asalin garin Kaduna, wato Doctor Jibril Bashir Makama, sai da ya fara gabatar mana da kansa sannan na soma bamu darasi tare da nuna mana wasu abubuwan a zahiri.
Tun da idona suka sauka akansa sai ya tafi da imani da duk wani tunani da natsuwata, Jibril na da kyau da ba zaka iya tantanshi aa cikin ƴaƴan turawa ko larabawa, fatarsa fara ce fes ga shi da tsaye hancinsa ya sauko a ƙasan hancin an yanka masa madaidaicin baki, fuskarsa na ɗan faɗi, yana da manyan ido sai dai ba fararene ba, suna da surkin ja ƙaɗan, a gefen wuyansa tattoo ɗin taurara ne aka jera masa har cikin bayansa.
Hankalina baya kan abunda yake ƙoyar da mu yana kansa, duk wani ƙyabtawar idonsa ƙirgawa nake, ina haɗɗace yadda bakinsa yake motsi da turansa da yake watsowa kamar baturen burtaniya, duk bayan daƙiƙu sai na lumshe ido saboda ƙamshin turarensa da ya cika lab ɗin. Murmushi nake masa ba tare da na san ina yi ba, har sai da ya katsa min tsawa.
“You deaf...”
A firgice na dawo hayyacina cike da kunya, ƙasa-ƙasa na ke kallon wata abokiyar karatuna Katherine Williams wace ke sonim dariya ita da wasu da dake kusa da ni.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
2⃣9⃣
Tun daga lokacin bana da tunani sai na shi, mafarkina ma nasa ne, duk wani abu da zai kusantar da ni gareshi na kanyi ƙoƙarin aikatashi, duk hanyar da zan ganshi ita na ke bi, duk da na lura da babu ruwansa da sha'anin kula wasu matan na daban hakan yasa na fara tunanin ko yana da mata ne.
Salima kanta ta lura da yadda nake ta rawar jiki da son ayi zancesa, idan kuma wata macen ta kalleshi sai naji kamar naje na shaƙeta, a gurin Salima na ke samun labarinsa, kasancewar ta sanshi farin sani wai ɗan abokin Daddy ne, na yi mamakin da ban san shi ba duk tsawon zaman da na yi a gidan, duk da kasancewar na san Mahaifinsa amman ban taɓa kawowa zuciyata cewar shine ɗansa ba, sai dai duk wani mummunan hali nashi na wulaƙanci da rashin son mutane ta hanyar Farida na ke jinsa saboda ta rigamu zuwa makarantar duk wani abu da ya danganceshi ta san shi sosai.
Salima ce take labarta min cewar Jibril shine ɗa na uku a gurin Mahaifinsa, kuma ɗa na farko a gurin mahaifiyarsa kasancewarta Amarya, yana da Step mother wacce ita ce ke da ƴaƴa da yawa kuma ita ta riƙashi a hannunta ya tashi, a gurin haihuwarsa Allah ya karɓi ran mahaifiyarsa wannan yasa mahaifinsa yake sonsa kuma yake tausayinsa domin ko da Jibril ya buɗe ido be san mahaifiyarsa ba sai step mother.
Wata ranar da muka yi practicing akan thigh surgery, ya yaba min sosai kuma ya nuna jindaɗinsa akan yadda na maida hankali sosai, a ranar kasa bachi nayi saboda farinciki duk bayan minti ɗaya zuwa biyu uku fuskarsa na ke gani.
Hakan yasa na ƙara maida hankali akan karatuna, da muka samu hutu sai muka soma shirin ziyarar gida kasancewar dkanmu munyi marmarin gida saboda haka muna samun hutun muka shirya muka dawo gida.
Bayan mun dawo Abuja da kwana biyu na fara shirye-shiryen zuwa gida sokoto domin ganin iyayena, ranar da anje gurin kitso na dawo sai Daddy ya aiko yana kirana.
A ɓangaransa na sameshi tare da Momi Aisha wato Hajiyarmu, da sallama na shiga bayan na gaishesu sai na maida kaina ƙasa ina wasa da carpet zuciyata cike da son jin dalilin kiran nawa, da farko na yi tunanin akan tafiyata ne sokoto ko kuma karatu.
‘Wata ƙila zai ce na haƙura har sai mun sake samun wani hutun ne ko kuma wani abun’
Haka na yi ta saƙe-saƙe na kamin na ji abunda Daddy yake faɗa.
“Nawwara ko akwai wani wanda kike so? Ko kuma iyayenki suke son haɗa ki da shi?”
Na yi mamakin da ya yi min wannan tambayar, a take Jamal ya faɗo min a raina na fara tunanin ko ya faɗawa Daddy wani abun ne, ko shiyasa tun da na zo ban ganshi ba. Cikin natsuwa da ladabi na ɗaga kai na kalleshi na ce
“A'a babu Daddy”
“Mashallah”
Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciyar da ke nuna ya jidaɗin hakan, ya gyara zamansa yana fuskanta ta sannan ya ce
“Alhaji Bashir Makama aminane a tare muka taso tare muke duk wani abu da ya shafi siyasa ko kasuwanci, sai dai shi be cika zama a garin Abuja ba shiyasa ba ki wayeshi sosai ba, yafi zama Kaduna wato mahaifarsa sai kuma garuruwan da yake gabatar da kasuwancinsa.
Few days ago mun tattaunada shi akan ɗansa, yana son haɗa zuri'a da ni, ni kuma na duba a cikin ƴaƴana na ga babu wacce ta dace da shi sai ke, na yi hakan ne ba dan komai ba sai dan sama miki rayuwa mai kyau da nagarta, na san idan har kika auri ɗansa zaki ji daɗi sosai, saboda yaron yana da aiki ba irin ƴaƴan masu kuɗin nan ba ne shashashu kuma yana son yaronsa sosai, matsalar sa ɗaya baya son zaman da yake a waje kuma baya son yarinyar da yake tare da ita”
Sosai na ji babu daɗi duk da bani da wanda zan iya fitar a lokacin na ce gashi shi nake so, amman hakan yasa ni jin babu daɗi, sai dai ban yarda na nuna masa ba domin na san ba zai min abunda zai cutar da ni ba.
“Ai kin san Alhaji Bashir ko? Ɗan sa da yake waje yana aiki, ta hanyarsa ma Daddy mu ya samo muku gurbin karatun, ba zaki rasa sanin Jibril ba dan ance makarantar ku yake koyarwa, kuma a can zamu zauna sai kin gama karatun sannan ku dawo gida gaba ɗaya”
Wannan karon Momy ce take maganar da ta kwantar min da hankali kuma ta saka ni farinciki, cikin nuna tsantsar ladabi na ɗago na kalli Daddy na ce
“Ba zaka taɓa yi min abunda zai cutar da ni ba, ni kuma ba zan taɓa butulce maka ba, ko wuta ka kunna kace naje na shiga zan iya shiga na ƙone kaina balle aure, fatana Allaj yasa haka shine alheri”
Ya ji daɗin farucina har ma yasa min albarka shi da Momy sannan na taso zuciyata cike da farinciki fal na dawo sashenmu, jikin har rawa yake na labartawa Salima abunda ake ciki, ita ma tayi farinciki sosai sai da nayi mata alƙawari karta faɗawa kowa kuma karta nunawa Daddy ina sonsa, ita kuma ta yi min alƙwarin haka.
Bayan kwana ɗaya muka yi shirin zuwa sokoto ni da Salima wannan karon ma jirgi muka bi, Inna ta yi farinciki ganin sosai ni kaina ban san na canja ba sai a wannan lokacin na yi mamaki da Inna ta ƙara haihuwa ba tare da ƙara wasu shekaru biyar ba, kuma ace har anyi sunan Jamila ba a faɗa min ba.
Dare muke rayawa ni da Salima muna labarta Inna da Baba rayuwar waje, Habiba kan ta shige cikina tare muke kwana a shinfiɗa ɗaya, a wannan lokacin ne na samu damar ziyarar abokaina da muka taso tare ciki wasu kuma da muka yi makarantar islamiya da boko a tare kamin tafiyata Abuja, cikin har da Zinatu da Baraka da kuma Jidda a lokacin duka muna unguwa ɗaya kamin su Zinatu su koma kware road gawon nama.
Wasu basa yarda ina karatu a waje saboda suna ganin mahaifina ba kowa bane, kuma ba kowa ne mai arziki ba ne zai iya yi mana yadda Daddy ya yi mana. Inna ta labarta min yadda ake ta tsigumi a unguwarmu wai saboda kwaɗayin abun duniya zai siyar da mutuncin ƴarsa ya yarda naje na yi karatu bayan na secondry da aka ce na yi, a cewarsu wai yaƙi ya yi min aure jira yaƙe sai na gama karatun sai mai kuɗi ya zo ya aureni.
Ni kaina maganar bata min daɗi ba kuma daman nasan za a samu haka, mutane ba zasu taimakeka idan kuma wani ya tallafawa rayuwarka sai koma gefe suna zagi da ganin hakan be dace ba.
Sai da muka yi sati biyu a sokoto ana sauran kwana uku mu koma Abuja, Baba ya shigo ya same ni a ɗaki a lokacin ina ni kaɗai ya soma labarta min maganar da Daddy ya yi masa, ganin na ƙi cewa komai yasa ya kira Inna suka sakani a gaba akan ina son haka ko bana so domin shi ba zai yarda ayi min auren dole ba.
Ni kuma na yi shiru ban amsa ba, hakan ne ya tabbatar masa da ina so ɗin kamar yadda Annabi ya faɗa shirun budurwa shine amsarta.
“Amman yasan ke ba ƴar Alhaji ba ce ko? Saboda bana son ayi abu daga baya ya dawo na rashin daɗi”
“Wallahi Baba ban sani ba, amman na san ba zai rasa faɗa masa ba”
“Idan ma be faɗa masa ba ni zan buƙaci.ya faɗa masa, ƙara yasan ko wacece gudun kar sai anyi abu wani abu ya biyo daga baya, kuma ina son yasan mu talakawa ne iyayenki ba masu kuɗi ba, idan ya ji zai iya aurenki a haka walillahil hamdu idan kuma ya ce ƴar mai kuɗi yaƙe so sai mu jira Allah ya kawo miki na gari”
“Hakan shi yafi Allah ya zaɓa miki alheri”
Cewar Inna, ni dai ban ce komai ba, Allah kawai na ke roƙo ya zaɓa min abunda ya fi alheri. Bayan mun koma Abuja Momy take faɗa min wai cikin satin nan Jibril ɗin zai dawo dan haka na shirya tarbonsa a kowane lokaci, a lokacin hutunmu sauran sati uku ya ƙare.
Shiru-shiru Jibril be zo ba, da sunan ganin matar da zai aura, hakan ya tabbatar min da cewar shi ma baya son auren wata ƙila shi ma an masa yadda aka min ne, wato haɗi.
A week later Momi ta ce na shirya ni da Salima zamu je area 1 gurin abokin Daddy mu ƙarɓo saƙo, duk kalar tufafin da na saka sai Momy tace ba su yi ba naje na canja, kuma ni kawai take cewa ba da Salima ba, daga ƙarshe sai ta shigo ɗakinmu da kanta ta zaɓa min tufafin da zan saka kuma tasa na canja kwaliyar fuskata na feshe jikina da turare sannan ta kira direba ta ce ya kaimu.
Na samu kaina da faɗuwar gaba sanin gidansu Jibril ne zamu je, sai dai ko da wasa ban kawowa raina cewar zan je mu gaisa ba ne, iya abunda na zata zamuje karɓo saƙo ne wata ƙila yana nan shiyasa take son na yi kwalliya ta yadda ko da ya ganni ba zai raina ni ba, amman abun mamaki bayan mun isa gidan mun gaisa da Hajiya Zainab Step mother ɗinsa sai aka nuna min wani falo wai na shiga zamu gaisa da Jibril.
Na ji babu daɗi duk da kasancewar ina sonshi amman sai nake ganin kamar hakan be dace ba, shi da yake namiji ya kasa zuwa ya ganni sai ni da nake mace za a ce naje mu gaisaz, ba zan iya mata musu ba tunda ita a tunaninta Momy ta faɗa min haka tun gida.
Da sallama na shiga muryata can ƙasa-ƙasa, amman be amsa min ba kuma be ɗago ya kalleni yana ta aikin dannar wayarsa fuskarsa a haɗe kamar baƙin hadari, his perfume make me feel comfortable har na zauna duk da be min izinin zaman ba.
From head to toe ya kalleni sannan ya jinginar da kansa yana taɓe baki ya ce
“Ke kuma haka tarbiyar gidanku take? Mata su suke zuwa fira da kansu? What kind of woman are you, kin cika arha da yawa gaskiya abun har cikin gida”
“Ni ma ba a faɗa min da kai zan gana ba, saƙo aka ce min zan karɓa shiyasa yazo da ko mayafina baka isa ka gani a gidan nan ba”
Ba bashi amsa kai tsaye, sai ya tashi zaune yana taɓe baki tare da cigaba da kallona.
“Really? Kuma kika ci kwalliya haka? Kina tunanin zan ga kyauki ne ko? Mutumen da yake son ki zai yaba kyauki, amman ba ni ba dan ni kamar baƙin maciji nake ganin ki, ki taimaki rayuwata baiwar Allah ki ce baki so na, Wallahi zan biyaki ko nawa kike so”
“Kai miyasa ba zaka taimaki rayuwata ka faɗawa mahaifinka cewar baka so na ba”
Still bakinsa a mere ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa a aljihu ya nufi window.
“Ban san ko sau nawa zan faɗa masa ya yarda ba, Wallahi na faɗa na ƙara duk wata mace da ba Aisha ba bana son ta, amman mahaifina ya tsaya kai da fata akan sai na auro wata, ya neman min auren ƴar Alhaji Dahiru ne saboda yana yaba tarbiyar gidan kuma yana son zumuncinsu ya ƙara ƙulluwa, after that you're not his biological daughter, jin wannan yasa Mahaifina ya ɗaga min ƙafa, amman Alhaji Dahiru ya dage akan shi yana son ayi, har da cewar wai baya son auren ya ɗauki lokaci.
Aurena da ke baiwar Allah ba alheri ba ne, domin ni dai har ga Allah bana son ki, lemme ask you some questions, shin zaki iya auren namijin da ya taɓa kusantar wata mace kamin ke? Zaki auren Namijin da ya taɓa sanin wata mace kamin ke? Zaki iya zama da namijin da zuciyarsa da gangar jikinsa duk na wata macen ne? Could you?”
Na girgiza masa kai.
“No i couldn't, ba zan iya auren namijin da ba be san ƙimar zaɓin iyayenshi ba”
Ya matso kusa da ni cikin ɓacin rai, ya riƙa fuskata ya soma magana cikin murya mai amsa amo biyu.
“how dare you, ke iyayenki sun san ƙimarki ne zasu barki hannun wani saboda ƙwadayin abun duniya, bayan baku haɗa komai da shi ba daga gadi! Wallahi duk kika aure kin saka rayuwarki cikin matsala sai kin ƙwammace kiɗa da karatu, duk wanda ya ce zai raba ni da Aisha ba zai sha da daɗi ba”
Ya ciro wayarsa da ɗayan hannunsa ya nuna min hotonta da ke gaban wayarsa, yana matsar min fuska iya ƙarfinsa, a nan na fara kokuwar kuɓucewa amman na kasa.
“Wannan matar ta fiye min ke sau dubu ɗari, dan haka karki yaudari zuciyarki kar kwaɗayin abun duniya yasa ki salwantar da rayuwarki ni da ke kamar RAI BIYU ne wuta da ruwa ba zamu taɓa haɗuwa ba, you bitch...!”
Yana kaiwa nan ya wulgar da ni saman manyan cushion, ya yi ficewarsa cikin zafin rai. Ni kuma na tashi zaune da sauri ina taɓa bakina da nake tunanin yama fara jini saboda zogin da yake min.
Na kusan minti goma a falon sannan na fito ina ta ƙoƙarin ɓoye abunda ke fuskata. Ban tararda Salima a falon ba, sai Hajiya Zainab da yaranta ƴan mata da ke ta min kallon uku saura kwata.
“Direba zai maida ke gida, Salima ta koma tuni saboda an kira Daddy ku ba lafiya”
Gabana ya faɗi sosai, miya samu Daddy ina ta tambayar kaina har na fito harabar gidan na nufi inda direba yake, na shiga bayan motar sai ga wata budurwa ta zo da jakunkuna ta saka min a motar sannan direba ya kama hanyar gida da ni, tun kamin mu isa gida na fara hawaye saboda tunanin abunda ya sami Daddy da kuma baƙin cikin abunda Jibril ya yi min.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
3⃣0⃣
Ganin Motar Anty Mairo da Zubaida wato manyan ƴaƴansa guda biyu a harabar gidan ya ƙara tayar min hankali, cike da fargabar abunda ya samu Daddy na fita motar na nufi cikin gidan.
A falon Momy babu kowa sai ƴar aikinta Suwaiba, ban tsaya komai ba na nufi part ɗin Daddy. Mamaki ne ya maye gurbin tashin hankalina, sai ya zo akasin tunanina da kuma furuncin step mother ɗin Jibril cewar Daddy ba shi da lafiya.
A sanyaye na shigo falon idona kan Daddy dake making call yana murmushi, ban ankaro da ban yi sallama ba sai da Anty Zubaida ta hankarar da ni ta hanyar amsa min da.
“Wa'alaikissalam”
Saurin share hawayen fuskata na yi na yi sallamar duk da kasancewar na kai tsakiyar falon. Sai duk suka haɗa baki gurin amsa min ciki har da Momy. Cike da mamaki na zauna kusa da Anty Zubaida ina cigaba da kallon Daddy.
“Nawwara har kin dawo?”
Cewar Momy.
“Eh ko da na fito Salima ta dawo gida ko da na fito Hajiya tace min Salima ta wuce wai Daddy ba lafiya”
“Ee na kirata na ce ta dawo gida jikin Daddynta ya tashi amman da sauƙi daman jinin ne ya hau amman ya sauka”
Ajiyar zuciya na sauke na kalli Daddy da ya aje waya a kunnensa ina masa ya jikin.
“Alhamdulillah, ya kika baro can ina fatar kina son shi?”
Har na buɗe baki na yi magana sai Momy ta yi karaf ta karɓe.
“Kana maganar tana son shi Alhaji wace mace ce zata kalli Jibril ta ce bata son shi, ai Hajiya ta kirani ta faɗa min sun fahimcin junansu sosai kuma shima ya yaba da ita sosai”
Ƙasa na yi da kaina saboda bana son ƙaryatata ko kuma na kunyata ta a gaban ƴaƴanta akan wannan zancen da ba haka yake ba.
“Maa Sha Allah, haka muke so Allah ya tabbatar da alheri a ciki, mahaufinsa ma ya faɗa min yana son a ɗaura masu aure kamin ta koma makaranta albashi idan ta kammala sai ayi bikinsu”
Jin wannan maganar ta Daddy yasa idanuwa cika da ƙwalla. Anty Zubaida da Anty Mairo suka shiga tsokanata har ma da Salima, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na tashi da gudu na bar falon.
Ɗakinmu ma dawo na zauna bakin gado ina ta kuka, wata zuciyar na raya min na kira Baba na faɗa masa wata na cewa a'a, tabbas a lokacin ina son Jibril amman rashin aurensa shi zai fi min alheri tun da har ya nuna min akwai wacce yake so.
Ina ta tunanin mafita sai ga Momy ta shigo ɗakin tare da Salima tana faɗin.
“Kun saka min ƴa kuka bari na rarrashi abata”
Tana zaunawa kusa da ni sai ta kore Salima daga ɗakin da sunan zata rarrasheni, Salima na fita sai ta canja fuska ta kalleni
“Iyakar halacci Nawwara mun miki ke da iyayenki, ashe ko ba mu cancanci komai ba sai kyakkawan sakamako, kin dai san Alhaji ba zai miki zaɓin da zai cutar da ke ba, kuma wannan auren da kike gani idan har kika aureshi ke da danginku duk kun warke, ƙin yi wannan auren zai ɓata abotar Daddynku da shi na tsawon shekaru ashirin, idan kuma kika yarda kika aureshi tam kamar kin zuba babban jari ne a dukiyar gidan nan da kuma ta gidanku, domin mahaiɗinsa na cikin masu kuɗin da ake ƙirgawa da su a africa ba ma Nigeria kaɗai ba”
Na ɗaga kai na kalleta cikin muryar kuka na ce
“Amman Momy baya so na yana da wacce yake so, kuma ya faɗa min matuƙar na yarda na aureshi sai na yi nadama”
“Ai nasan baya son ki, daman taya za'ayi Namiji kamar Jibril ya so mace irin ki? Yaron da yake ganin ƴaƴan turawa da larabawa, kuma ɗan da magana kawai zai yi ma kuɗi su faɗo ƙasa sai kalli ƴar talaka irinki ya ce yana sonta? Ke ni fa Salima na so a bashi amman Alhaji yaƙi wai wani ya riga ya bada ita ba zai ce ya fasa ba saboda wannan, amman idan kika yi haƙuri da sannu zai fara sonki har ya kyautata miki, ke ko be so ki dole zai kyautata miki domin su masu kuɗi matuƙar suna auren mace dole ne su kyautata mata domin dukiya bata musu zafi.
Nawwara karki yarda ki faɗa ko ki nunawa Alhaji cewar baki son zaɓin da ya yi miki domin hakan zai iyasa zuciyarsa ta buga ya mutu gaba ɗaya, dan Allah ki yi min alƙawari zaki auri Jibril albashi idan daga baya kika ga zaki fito sai ki ce ya sakeki, kuma kin ga waje ma zaku zauna kina karatunki shi yana sha'aninsa”
Ta ƙarasa tana riƙe hannuna cike da magiya. Kai kawai na iya ɗaga mata alamar na amince ba dan raina ya so ba, har ga Allah ni kaɗaina ina ganin kamar idan ban auri zaɓin Daddy ba ban masa halacci ba.
Bayan fitarta Salima ta shigo tana zolayana, yadda ta ga ina kuka ya tsorata ta har ta soma tambayar ko wani abun ne ni kuma na amsa mata da ba komai.
A haka na jure na kauda kaina daga duk wani abu da zai nuna bana son auren saboda kar ran Daddy ya ɓace, su kuma sai hidimar ɗaurin auren suke har ana daf da ɗaura aure Baba be daina min magana akan idan bana sonsa na faɗa ba, amman na ƙi na faɗa, ni dai kawai na ɗaukarwa kaina alƙawarin zan jure ko ma minene saboda na zama ƴar halak a gurin Daddy da Momy.
Ana cikin haka ne Ya Jamil ya samu transfer gurin aiki zuwa Jos, ni kaina na jidaɗin haka nasan idan ya yi nisa da ni zan fi samun sakewa.
Sai da ana sauran kwana biyu ɗauren auren Jibril be taɓa kirana ko a waya ba, kuma be je ya gaishe da Baba ba, sai dai Mahaifinsa ya tafi tare da muƙƙarabbansa suka gaishe da Baba, komai a ɗaurin auren a nan Abuja aka yi saboda haka sai ranar da aka ɗaura min aure sannan mahaifina ya ga fuskar mijin ƴarsa kasancewar ya samu halarta tare da wasu ƴan'uwansa.
Na ji ni daban a cikin wani yanayi marar misaltuwa a wannan ranar, bana farinciki kuma bana baƙinciki ni dai kuka kawai na ke kukan da ban san dalilinsa ba, ganin haka yasa Momy ta kaini ɗaki ta ja min kunne akan na daina kukan kar mutane su zargi wani abu, haka na wanke fuskata na keɓe kaina a ɗaki har sai da ka ce na fito ga Baba can zamu gaisa.
Babu wata gaisuwa da na yi da dashi sai ta kuka kuka na yi sosai har sai da shi ma na saka shi kuka, ya yi min nasiha sosai akan rayuwa da kuma zamantakewar aure, ya faɗa min yanzu na tashi daga ikonsa na koma ikon wani, hakan yasa na ji ni cikin wani babban ɗaki mai nauyi.
Washe gari ma da zai koma sai da ya kirani shi da ƴan uwansa suka zagaye ni suna min huɗuba mai ratsa jiki.
Kwana biyu da ɗaura min aure aka kwantar da ni a babbar asibitin Abuja saboda rashin lafiyar da ya taso min, a wannan ranar ce Jibril ya hau jirgi ya bar ƙasar nan, har na yi jinyar na gama be taɓa kirana ba sai dai mahaifinsa da wasu Sisters na sa sun zo duba ni da kuma step mother ɗinsa, Mahaifinsa ne ya fi nuna min kulawa da damuwa, su kan kamar daman sun zo ne by force.
Bayan an sallameni da kwana biyu Salima ta fara shirin zuwa makaranta, ni kuma Daddy ya hana ni da sunan wai ba zan koma ba sai na ƙara jin sauƙi, ni kuma ban musa musu ba na amince, ina ji ina gani Salima ta koma makaranta ni ina nan.
Yana lura da yanayi na sosai, har ta kai wata rana ya kirani a ɗakinsa ya tambayeni ko dai bana son auren ne, sai an kasa amsa masa, ya yi min nasiha akan haƙuri da halin Jibril wai daman yasan za a samu haka saboda baya son auren kwata-kwata babu zancen aure a gabansa, wannan yarinyar ce kawai yake kulawa ita kuma ba ƴar mutunci ba ce zaman kanta take wannan dalilin ya saka mahaifinsa ya ƙi yarda ya aureta, a ranar yake labarta min cewar Jibril ne ya hana na koma makaranta wai ya ce be bada izinin na koma makaranta ba.
Ranar na yi kuka sosai har sai dai na raina kaina, mutumen da ba zai iya kirana ya tambayi tafiyata ba shi ne zai ce bada umarnin kar a barni na koma karanta kuma a ƙyaleshi saboda kawai yana taƙama da kuɗi.
A haka na kwashe wata shida a ban koma makaranta ba, idan kuma nunawa Momy ina son anje gida gurinsu Inna sai ta ce min ba haka ba, wai ba zata bari na tafi bada izinin mijina ba. Tun daga ranar da aka ɗaura min aure da Jibril duk wata sai Alhaji Bashir Makama ya aikowa da Momy kuɗi ya ce a bani amman bata taɓa bani ko naira ba, bata ma taɓa faɗa min ko nawa ba ne tana dai faɗan min ya aiko saboda kawai na yi masa godiya.
Tun da Jibril yasa ƙafarsa ya bar ƙasar nan be sake waigo Nigeria ba, kuma be taɓa ɗaukar waya ya kirani ba, wani daga familynsa be taɓa zuwa da sunan ganina ko duba lafiyata ba.
Da wannan baƙinciki na ke kwana na ke tashi ban taɓa nunawa kowa ba, sai dai hakan be hana Daddy damuwa ba, wata rana bayan na gama haɗa abun karyawa mun sai ya aiko yana kirana, ko da na shiga sai na samu Momy tare da shi, guri na samu na zauna na natsu ina ta sauraren abunda yake faɗa min.
“Na gaji da wannan halin na Jibril, ba zai yiyu ya ce ba zaki koma makaranta ba, kuma baki tare ɗakinki ba, tun da ya tafi be ma kira ya tambayi lafiyarki ba, dan haka na faɗawa mahaifinsa idan ba zasu iya tanƙwara ɗan su akan abunda suke so ba, ni ba zan cutar da ƴata ba, na faɗawa mahaifinsa idan har yana ganin rabuwa da ke shine maslaha tam mu muna maraba, kuma ina fatar wannan hukuncin ya yi miki”
Kamin na ce wani abu sai Momy ta yi karaf ta ce.
“Haba Alhaji yaran zamani ai sai an yi haƙuri, karka yi maganar raba auren su ko shekaran jiya na tambayeta ta faɗa min ita tana son mijinta, kawai ka yi ta musu addu'ah”
Kallo ɗaya na yi mata na ɗauke, wata ƙila tana min haka ne saboda ni ba ƴar ta ba ce, Daddy kan tuni ya gama gamsuwa da bayaninta, jiki a sanyaye na taso na fito daga part ɗin Daddy.
0 comments:
Post a Comment