*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee*
3⃣2⃣
A ranar Jibril ya maidani cikankiyar mace, da safe ni na taimakawa kaina na shiga banɗaki da kaina na haɗa ruwa na yi wanka sannan na ɗora da alwala na fito a wahalce na yi sallah.
Da safe be shigo ya tambayi ya na tashi ba duk da yasan halin da ya barni, ban fito daga ɗakin ba sai tara da rabi na safe kai tsaye na nufi kitchen sai na samu ya aje min makaroni da mai da tumatir da sauran kayan da zan sanrafa na dafa makaroni ɗin, cike da tausayin kaina na dafa makaronin ɗin ne na dawo ɗaki ina ta aikin kuka.
Haka nake wuni na kwana babu ruwan Jibril da ni a gidan, tun daga ranar kuma be saki kuni da sunan zamantakewar aure ba, idan baya nan gidan Ummu Faisak na ke zuwa na zauna musha fira ta haka nake samu na cika cikina da abincin gidanta, ban taɓa labarta mata irin yadda Jibril yake azabtar da ni ba, sai dai tasan irin zaman da nake a gidan ko da yaushe tana ƙoƙarin koya min abubuwan da zan yi na burge Jibril ko kuma na janyo hankalinsa akaina.
Ranar wata lahadi yana zaune gida na same shi a garden inda yake zaune yana hutuwa na risina har ƙasa na roƙoshi akan ya taimaka ya sake ni, amman ya ƙi har ma ya soma iƙirarin shi yanzu ya fara zama da ni, sai dai ya taimaka min ya ba ni makullin kitchen, daga ranar kullum abinci kala uku na ke girkawa wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ko kallonsa ba ya yi.
Yana zaune falo shi da abokinsa ni kuma na nufi kitchen saboda miyar da na ɗora karta ƙone, ina nufar kitchen ina jin yadda yake faɗawa abokinsa wai Aisha tana da ciki and he's so happy and excited akan cikin da aka samu babu aure, ina kitchen ɗin na tarar da ni ya shaƙe ni yana tambayar ina Hijabina taya zan fito haka babu mayafi a gaban abokinsa, da kansa yaje ɗakina ya ɗauko min Hijab na saka sannan na wuce ta gaban abokinsa, har abokin yana zolayarsa wai shi yana ganin matan wasu amman shi ba a ganin nasa.
Ma samu sasauci sosai daga lokacin da ya bani makullin kitchen ɗin saboda kullum zan girka na ci, sai dai wata rana sai na gama girkin na ji bana so ko kuma na ji wannan na ke so bana son wannan abu a kaɗan sai amai, nan da nan zazzaɓi ya rufeni haka na kwashe kwana uku ina fama da rashin lafiya kamar zan mutu amman ko da rana ɗaya Jibril be taɓa shigowa ya duba lafiya na ke ba.
Ranar da na samu sa'ida na ɗaure na fito falo saboda na gaji da zaman ɗaki, ranar sai ya shigo ya sameni falo yadda ya ga na rame shi kansa ya bashi tsoro, da kanshi yana zo yana tambayar me ke damuna cikin nuna halin ko in kula saboda kawai na ce be damu ba.
Bayan na faɗa masa ya ɗauko min roba ya ce na yi fitsari sai kuma ya ɗibi jinina, ya bani wasu magunguna. Washe gari sai gashi ya dawo cikin gidan a rikice kai tsaye ɗaki na ya nufa.
“Ina kika samu ciki?”
Shine abunda ya fara tambayata fuskarsa na nuna tsantsar ɓacin rai da ke tare da shi, ni kuma na ɗago kai a hankali na kalleshi na maida kaina domin bana iya amsa masa.
“Ni ban shirya haihuwa yanzu ba, saboda haka ki san yadda zaki yi da cikin nan, daga yin abu sau ɗaya sai ace ciki ya shiga, zubar da shi zan yi ko kuma ya zama ƙarshen auren mu”
Ni dai uffan ban ce da shi ba ina ta aikin kuka, ban san miya aikata ba bayan kwana biyu ya shigo ɗakina ya bani lemu ina sha hankalina ya ɓace ban farko ba sai da aka kira assalati. A week later ya ɗauki ni zuwa gidan Daddynsa ashe ya kira Baba ni ban ma sani ba sai da muka isa, a falon ya yi min tozarci da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ya tozarta ya yi min ƙazafi a gaban Mahaifina da mahaifinsa ya fiddo wasu hotuna na tsiraici tare da wani ya nuna musu kuma ya yi min ƙazafin cewar na aikata zina da wani a waje kuma da aurensa.
Ban iya cewa komai ba sai aikin kuka, har ga Allah ban san inda ya samo wannan hoton ba amman ni dai nasan babu wani namiji da wata mu'amala ta taɓa shiga tsakaninmu sai shi amman ya juya baya ya murje ido ya ce ba nashi ba ne, a ranar na riƙa hannunsa na riƙe shi akan ya karɓi cikin nan sai ya tureni yana faɗin taya zai karɓi cikin da ba nasa ba.
“Ni kan ban haifi ƴar iskaba kuma na san irin tarbiyar da na bawa ƴata”
Shine abunda Baba ya faɗa, Shi kuma ya sakeni saki uku mahaifinsa ya ce idan an saki mace a lokaci ɗaya kamar saki ɗaya ne dan haka ya maida aurensa ya yi haƙuri, sai kawai ya ce ya sani saki ɗaya ya sake ni saki biyu ya sake ni saki uku saboda kawai kar na koma gidansa sai Baba ya kama ni muka fito daga gidan, gidan aurana na koma na ɗauke duk abu na wa mai muhimmanci daga nan kai tsaye muka nufi tashar mota, sai dai ba mu kawo sokoto ba sai washe gari saboda ko da muka taso yamma ta yi sosai a zaria muna kwana, dawowata ta bawa kowa mamaki musamman da aka fahimcin ina da ciki sai aka fara zancen cewar ba aure na je yi ba iskaci naje yi wasu kuma su ce daman haka sai ya faru tun da Baba ya nuna kwaɗayinsa a kan abun duniya, har ma da masu cewa babu makarantar da na tafi. Baba ne yake ta dawainiya da ni shine ci na shana har na haihu da ƙarma ƙarama ya samo aka yanka rago ranar suna, yaro ya ci suna Muhammad Noor.
Bayan na haihu Inna ta ce ya faɗa masa sai azo a auna jininsa da na yaron amman Baba ya ce ba zai yi ba, ai namiji idan ya girma shi zai nemi ubansa, kuma yasan komai daren daɗewa sai Jibril ya dawo gurin ɗansa. Da wannan na zauna a gida ina rainon ɗana har ya cika shekara biyu da wasu watanni, a lokacin ne muka fara sabo da Bilal saboda gaisuwar arziki da take haɗa ni da shi, abotarmu da Jidda kuma ta ƙullu sosai, a gunta na ke jin labarin ai mahaifin Zinatu yana ɗaukar aikin local government har da masu ssce, haka na ɗauki takarduna naje gidansu Zinatu neman ta yi ma Babanta magana akan aikin amman sai ta tsaya tana kallona har ma da zolayata wai ina karatun da aka ce ina yi a waje har tana dariya, daga baya take faɗa min cewar mahaifinta ya ce sai masu degree yake ɗauka.
A hanyata ta dawowa daga gidansu na haɗu da da Faruk, tun daga unguwar yake bina har sai da na iso gida sannan ya yi min magana, ya kuma gabatar min da kansa ni kuma na faɗa masa ko wacece ni ban ɓoye masa komai.
Daga nan sai alaƙa mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninmu har ta kai ga neman aure duk da ban so haka ba Baba da Inna suka buƙaci na aureshi tun da har ya nuna yana son aurena. Faruk mutum ne mai hallaci da kawaici yana so na tsakani da Allah, da kansa ya ce na daina cewa Noor babansa ya mutu saboda na yi masa ƙarya tun farƙo na faɗa masa cewar Baban Noor ya rasu ne, wasu mazan basa yarda mace ta yi aure da ƴaƴan wasu a gidansu amman shi kan ba zaka taɓa gane cewar ba shine ya haifi Noor ba, duk abunda ya kamata uba ya yi ma ɗansa shi yake ma Noor ba dan kuma baya da ƴaƴanba, domin yana da aure har da yara biyar, sai dai yana aiki ne a sokoto amman mutumen kebbi ne, acan yake zaune da duk familynsa, sai ya bar ni nan, ita kuma yana zuwa can inda take a kebbi. Iyayensa basa jindaɗin zama da matarsa irin matan nan da basa ragawa uwar miji da ƴan'uwanta ko kaɗan duk da ba guri ɗaya suke ba, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa ta buƙaci ya maidani kebbi kusa da ita saboda ta yaba da tarbiyata a ɗan zuwan da muke ina gaisheta.
Sai ya tattara ya maida ni a kebbi tare da Noor, su kansu family ɗinsa suna son Noor kamar ɗansa yan'uwansa haka, ga mahaifiyarsa tana mugun so na ni da ɗana saboda ina kyautata mata sosai, ɓari na biyu a gidan Faruk amman Allah be bani haihuwa ba, aiko ranar na ga gata a gurin danginsa da shi kansa kamar su haɗeni saboda tausayi. Muna haka kwatsam labarin mutuwarsa ta same mu sanadiyar haɗarin motar da ya yi a hanyarsa ta zuwa sokoto gurin aikinsa.
A ranar nima sai da na yi kamar zan mutu saboda kuka, a nan gidan na yi taƙaba na gama familynsa suka riƙe Noor kamar yaron da muka haifa saboda sun ga babu yaro a tsakaninmu kuma basa son alaƙarmu ta yanke gashi Noor ya ɗaukesu a matsayin yan'uwan mahaifinsa. Bayan na gama wankan taƙaba na dawo gida.
A duk lokacin da suka samu lokaci sukan kirani ko kuma su zo duba Noor, bayan na dawo sai Bilal ya maida Noor kamar abokinsa kullum zai zo gidanmu kiran Noor da wannan alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu muna girmama junanmu sosai ni da shi, sai dai iyayenaa basa son alaƙar da ke tsakaninmu ko ƙaɗan saboda sunan ganin ni bazarawa ce kuma da ɗan da ake zargin shege ne shi kuma saurayi mai mutunci, wannan dalilin yasa na ƙi bashi wata dama da zai nuna min soyayya.
Har kuma tsawon lokacin Momy bata taɓa kirana ba, ni ma kuma ban kira ta ba, Ya Jamal ma sau ɗaya ya taɓa kirana be ƙara ba, Salima ce kawai muke yawan gaisawa akai akai ita kaɗai ta san na haifi Noor kuma na nemi ta min alƙwarin ba zata faɗawa kowa ba, duk da nasan sai ta faɗawa Momy amman Jibril be san yana da ɗa ba da ni ba.
BACK TO STORY....
Tuna irin rayuwar da na yi aba ya hanani bachi har garin Allah ya waye.
‘Baka cancanci yafiya ba Jibril kuma hanyar da zan rama abunda ka yi min ita ce ta hanyar yin aiki tare da kai kamar yadda ka buƙata’
Shine abunda zuciyata take ta raya min ni kuma ina nanatawa kaina cewar ba zan taɓa yafe masa ba...
YANZU LABARIN ZAI FARA...😄
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
3⃣1⃣
A nawa tunani Momy tayi min haka ne tun farko saboda kar na auri ɗanta, yanzu kuma bata son a kashe auren ne saboda dukiyar gidansu Jibril tasan duk wulaƙancin da zai min ni ba ƴarta ba ce saboda haka wannan ba zai taɓa damunta ba, babu wanda zai fi jin zafi jin zafin ɗa kamar uwar da ta haifeshi, ni kaina da Mahaifana ne ce zan iya fahimtar da su kuma su fahimta, amman wannan duk abunda zan yi sai dai su kalleshi a a matsayin butulci.
Duk da maganar da Daddy ya ce yi ya sai da aka kwashe wata ɗaya har da kwanaki rana ɗaya Momy ta kirani wai na je na shirya yau Jibril zai zo ganina, gabana ya faɗi sosai har na ji ina ma ba zai zo ba har abada domin na san zuwan nasa ba alheri ba ne.
Wanka na sake na saka wasu tufafin kwaliya kan ban yi ba, mai ma dan ya zamin ne jikine yasa na shafa, daman ta saka mai aikinmu ta shirya masa abinci da lemu haɗin gida. Haka na zauna tun sha biyu na rana har magariba be zo ba kuma be kira ba, misalin goma sha na dare Momy ta shigo ɗakina wai na taso gashi can ya zo, Ba musu na tashi na cire kayan bachi dake jikina na ɗauki atamfa na saka da mayafi na saka takalmi na fito jikina a sanyaye na nufi part ɗin baƙi.
Tun a bakin ƙofar falon ƙamshin turarensa ya daki hancina hakan yasa gabana faɗuwa, da sallama na shiga falon amman be amsa min ba sai dai idonsa na kaina har na zauna a kujera na soma miƙo masa gaisuwa a kufile, nan ma be amsa ba, sai wani shan ƙamshin yake ya tsare fuskata da kallo kamar mai neman munina.
“Saboda ke Daddyna yasa na dawo garin nan, saboda ke ya cilasta min dawo wa da aiki a nigeria gaba daya, ke dan Allah ba ki jin kunyar yadda ake ta turaki gurin namiji kamar ni?”
Ɗagowa na yi na kalleshi kallon mamaki da takaici ina ma zai san abunda ke zuciyata da ya taimakamin ya rabu da ni, akwai tsantsan tsoro da fargaba a tare da ni a wacan lokacin shine abunda yake ta cutar da ni sai kuma zurfin ciki da ya zame min hali.
“Zuwanka da rashin zuwanka duka ɗaya ne a gurina, ni dai ina neman izininka zan koma makaranta”
Be ci komai daga abunda Momy tasa aka kawo masa ba, sai ya tashi tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni har jikinsa na shafar nawa ya matso da fuskarsa kusa da tawa ta yadda ni kaɗai zan iya jin abunda zai fito bakinsa sannan ya kalleni ya na ƙara haɗe fuska ya ce.
“Ba aure kika zaɓa ba? Tam zaman aure zaki yi babu ke babu karatu har a bada, ai baki san waye Jibril ba kina da butaƙar sanin wanene tuƙunan”
Yana kaiwa nan ya tashi tsaye na saka hannunsa aljihu ya ciro kuɗi ya watsa min.
“Ga tsiyarki nan”
Ni kuma na miƙe tsaye ina kallonsa na ce
“Tsiyarka dai, tsiyar da ta saka baka ganin kowa da mutunci, na ji ni ƴar talaka ce kuma ni talaka ce amman haka ba zai baka damar ka yi min duk kalar wulaƙancin da ka ga dama ba, kuɗi kawai kake da shi Jibril ni kuma na ɗara ka da tarbiya da biyayya”
Murmushin gefen fuska ya yi ya taɓe baki.
“Fine, zamu gani”
Daga haka ya fice, ni kuma na koma cikin gida ko inda kuɗin suke ban kalla ba, zuciyata cike da ƙuna.
Tun daga wannan lokacin be kuma sake zuwaba sai da aka sake yin wata ɗaya sannan ya kira Momy a waya yana tambayar lafiyata shi ma kuma na san cilasta masa aka yi, bayan ya tambayi Momy aka kawo min wayar sai ya kashe ba tare da ya ce da ni komai ba, a ranar n samu Momy na yi mata bayani akan bana son Jibril kuma bana son zaman aure da shi sai ta muna min na yi haƙuri komai zai wuce da zarar na tare a gidansa, ganin bata goya min bayan rabuwa da shi ba yasa na samu Daddyda kaina na kuka masa halin Jibril da abunda na ke hangowa a zamantakewar auren da zamu yi, amman sai ya bani haƙuri saboda a tunaninsa saboda na daɗe a gidana ne yasa nake wannan tunanin shi ma sai ya kasa fahimta ta, wannan ƙorafin da na kaima yasa ya kira mahaifin Jibril ya yi masa magana akan tarewar mu.
A cikin watan nan aka yi kawo lefena kayan masu kyau da tsada, bayan sati ɗaya aka yi walimarta Daddy ya aika da ƙaramar mota aka ɗauko Mama da wasu daga ƴan'uwanta da kuma ƴan'uwan Baba.
Ranar da akayi walimar aka kaini gidansa bayan anyi min huɗuba sosai ciki har da Mama da take ta kukan rabuwa da ni, ni kaina ba zan iya misalta irin kuka da na yi a wannan ranar ba. Tun tara na dare aka kaini gidansa amman abokansa basu shigo da shi ba sai ƙarfe goma sha biyu, su kansu kamar sun sam baya son auren suka mana addu'a suka fice tare da wasu ƙawayena.
Misalin ƙarfe ɗaya na dare ya bar gidan, ban saka shi a ido ba har garin Allah ya waye, haka na kwana na wuni be shigo gidan ba har sai da aka kwana huɗu tsoro duk ya kamani saboda ƙaton gida ne gashi ni kaɗai ke ciki sai ƴan aiki da safe ne kawai ake aiko mana da abinci daga gidan Momy, yau ma da yake rana da huɗu ne ba a kawo ba ni na girka da kaina. Sai a ranar na biyar ya shigo shi ma kuma tare da budurwa Aisha, a gidan suka wuni suka kwana idan yana buƙatar wani abun ko kuma tana buƙata sai ya aiko min da saƙo a waya na tashi na yi musu, ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba zan taɓa nuna masa ina jin zafin abunda yake ba, ba kuma zan taɓa saɓa umarnin iyayena na cewar na yi duk abunda ya saka ni.
Ranar da na gaji da zama gida na fita maƙota, gidan wata matar na shiga wacce gidanta ke kusa da nawa sosai, ba laifi matar tana da son mutane da far'a Cikin ƙanƙanen lokaci muka sabu har ta kai gidan naje gidanta sai dare zan dawo shi ma kuma idan mijinta ya dawo, ita da kanta ta fara fahimtar irin zaman da nake da miji har ta tambaye ni na labarta mata kaɗan sai ta bani shawarwari akan na daina biye masa kuma na nuna wayeta sosai saboda shi yana shiga ƙasashen turawa ne dole idonsa zai buɗe da yawa.
Gaskiya Ummi Faisak na da kirki na koyi abubuwa da dama a gunta ciki har da girki da kuma iya kwalliya, sai dai ban taɓa gwada ko ɗaya ba saboda na san irin mijin da na ke aure.
Wata rana ina gidanta har dare sai gashi ya kira ni na ce masa ina maƙota yanzu zan so, ko da na fito sai na same shi bakin titi yana jiran ƙarasowata shi da wani abokinsa, ina isowa ya wanke min fuska da mari da har sai da na ga wasu ƙananan taurari, har abokinsa ya yi ƙoƙarin riƙeni saboda tangal-tangal da na yi zan faɗi, abun mamaki sai ya fara faɗa da abokinsa kamar zai cinye sa wai taya zai yi ƙoƙarin riƙa masa mata ai ko baya so na yasan zafina na matarsa kar an ya sake masa haka.
A ranar na wuni da zugin marin shi kuma ya wuni yana ta mitar fitar da na yi, hakan yasa ya kulle kitchen kuma ya karɓe wayar da ke hannuna, wai naje gurin matar da nake zuwa ta bani abinci. Daga lokacin kullum da yunwa na ke wuni na kwana sai ya ga dama zai dauko wani abun ya bani jiki na rawa na karɓa na cinye, sai na koma abar tausayi, da na masa laifi kaɗan sai ya dakeni kamar wata ƴarsa, yana yawan shigowa da Aisha ta kwana a gidan ko ta wuni yasa na dafa musu abinci na kai musu ruwan wanka idan sun gama sai naje na ɗauke kwanukan, sai dai duk da haka ko da wasa be taɓa sakewa Aisha fuskar da zata rainani ba baya bari ta sakani aiki ko ta faɗa min wata maganar marar kyau idan ma an wulaƙanta a gidan to shi ne kawai yake da wannan damar.
Wata rana ina zaune falo cikina na kukan yunwa, shi kuma yana ɗaki sai gashi ya fito ya jefo min wayata wai zan yi waya da Mama, sannan ya juya ya fice daga falon.
“Babanki ba lafiya Nawwara, kuma bamu da komai, shine na ce idan da wani abu a hannunki ki aiko mana dan Allah, ko abinci sai mu siya”
Shine abunda Mama ta roƙa ni kuma na ce mata zan aiko mata, bayan na kashe wayar na soma raira kukan da ban san ta inda yake fito min ba, ina haka abokinsa ya shigo hakan ba ƙaramin ɓata ran Jibril ya yi ba saboda ƙananan kayana ne jikina kuma abokin nasa ya ganni, ya yi min masifa sosai har da dukana ya yi akan haka.
Muna cikin wannan halin Daddy ya yi rashin lafiya ya rasu, sai komai ya koma min sabo domin ganin Babu Daddy ya bawa Jibril damar azantar da ni da kalar azabar da yake so, sai dai bayan rasuwar Daddy sai Mahaifinsa ya kira ta wayarsa ya riƙa tambayata ko da wani abun ni dai ban taɓa faɗa masa ba.
lokacin da Ya Jamal zai koma Jos sai ya biyo inda na ke dan mu gaisa, kamar ƙaddara sai ga Jibril ya dawo a ranar na sha duka wai akan me zan shigo masa gida, ya yi faɗa da Ya Jamal sosai har Ya Jamal yake masa faɗa akan yadda ya maidani kamar wata tsohuwa saboda wahala.
Na sha fama a gidan Jibril ga shi baya son Sallah akan lokaci idan kuma na tasheshi sai ya yi ta masifa da ni, wata rana sai kamo tashar musulunci dake cikin receiver wa'azi wani babban malami yake akan irin azabar da ake ma masu wasa da sallah da kuma halin da suke shiga tun nan duniya, da gangan na cika murya dan yaji ashe kuwa saƙon ya isa dan tun daga wannan lokacin be sake wasa da sallah ba, wani lokacin da asuba har tashi na ke na tarar da ya riga ni tashi.
Abun da na lura da shi Jibril yana da rayuwar turawa saboda zama da ya yi a can tun yana da ƙurciya har girma, gaba ɗaya rayuwarsa ta turawace, sai dai a wannan lokacin Jibril ba ya cin goro ma balle taba, rashin ilmin addinin islamiya ne yake ta cutar da shi, idan ina karatun ƙur'ane ya kan natsu yana saurarena musamman da asuba, akwai ranar da ya taɓa tambayata wai waya koya min karatu manyan surori haka na ce makarantar islamiya, daga ranar kuma be ƙara tambaya ba, ni kuma na maida tashar wa'azi ta zamo abar saurarena kullum, sai dai hakan be hana shi zalunta ta ba, be kuma hana shi yin fasiƙanci da Aisha ba, be kuma sanya shi ciyar da ni ba, ni dai iya abunda zan iya shidunsa da shi shine kishi, Jibril yana kishina sosai dan ko abokansa baya bari su gan ni, idan kuma wani ya yi magana da ni ko ya nuna kulawarsa akaina ranar zai wuni yana masifa kamar ya cinye kansa.
Haka na bi na lalace ba ƙarfin yau bare na gobe, wata rana mahaifinsa ya aiko da mota aka ɗauko ni aka kaini gidansa, muka gaisa ya ɗauki wayarsa ya kira Jibril yana zuwa ya fara masa akan yadda ya ga na lalace sai Jibril ya yi tunanin ko na faɗa masa wani abun ne, bayan ya sallame ni da kuɗi mai yawa muka fito ni da Jibril na shiga motarsa muka kama hanyar gida.
Sai da ya tabbatar na yi nisa da gida sannan ya faka motarsa ya fisgoni da ƙarfi ya jefar a gefen titi ya koma cikin motar ya yi tafiyarsa ya bar ni a gurin. Haka na zauna a gurin har aka kira magariba sai da wani mutun ya zo zai wuce ya tsaya ya tambayeni na nemi ya taimaka min ya taimaka ya ɗauko ni a motarsa ya kawoni gida, a ranar sai da Jibril ya mareni kuma ya yi min duka mai kyau. Washe gari sai ga Momy ta zo gidan ta karɓu kuɗin da Daddynsa ya bani, ni dai na roƙeta akan ta raba biyu ta aikawa Baba rabi duk da nasan ba zata yi ba.
Jibril ya kan kirani da ko wane irin suna, idan na yi masa wani abu ba dai'dai ba sai ya ce min annoba ko baƙin maciji, yana yawan faɗar cewar ya fi son mutuwarsa da ni. Tun da ya aureni be taɓa bari naje gida ganin Baba ba, gidan momy kawai na yake kaini shi na kuma da dare yake kaini bayan ƴan mintuna ya ce na taso mu dawo gida.
Ranar da zamuje raka daddynsa zuwa airport ya mareni a bainar jama'a saboda kawai na zubar da ice cream ba da gangan ba, aiko ranar ya sha faɗa a gurin mahaifinsa har sai da ya raina kansa.
Bayan mun dawo gida ya wuce ɗakina na yi kuka har na gode Allah, daga nan bachi ya yi gaba da ni ina cikin bachin na soma jin ana shafani, hakan yasa na farka a firgice ina ihu, sai ya ji haushin ihun da na yi ya mare ni ya riƙa ya jefar ƙasa har sai da kaina ya bugu da madubin gadon, sai kuma ya taso ya doso inda na ke gadan-gadan ya dake fiskgata ya jefa saman gadon.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee ❤*
3⃣4⃣
Tare da Siraj suka shigo a lokacin Jibril na zaune saman kujerarsa yana kallon ƙofar shigowa office ɗin.
Tun da suka haɗa ido da Mustapha zuciyarsa take ta raya masa wani akansa, Siraj ne ya nuna masa gurin zama a cikin kujeru dake gaban teburin Jibril suna facing ɗinsa, domin Jibril in banda kallonsa babu abunda ya ke. Mustapha ya miƙa masa hannu.
“Sunana Mustapha Faruk Turaki”
Jibril ya daɗe yana kallon hannunsa sannan ya miƙa masa.
“And...?”
Mustapha ya yi mamakin ganin yadda yake amsa masa kamar baya maraba da mutane, sai dai be nuna masa komai ba ya ɗora akan abunda ya kawo shi.
“Na zo ne akan wani gida da yake guiwa, wanda ka siya ta hannun Malam Haruna”
“Me gidan ya yi maka?”
“Be min komai ba, ance min ka siye gidan ne milion ɗaya ni kuma zan baka 1.5 million ka mallaka min gidan”
Jibril ya yi murmushi tare da kwantawa saman kujerarsa yana lilo tare da wani shegen murmushi.
“Waya faɗa maka ni na siya gidan?”
“Malam Haruna ne ya faɗa min, naje gunsa ina son na siye gidan sai yace min wani ne ya siya sunansa Jibril, amman ya ce be san waye Jibril ɗin ba, yaro ne ko babban na buƙaci gani ka, yace bashi da number ka sai da ta wanda suka yi cinikin domin ya bar number akan idan mutunen gidan su tashi a faɗa masa, na buƙaci ya bani number wanda suka yi cinikin ne sai ya bani number wannan Siraj ɗin, ni kuma na kirashi sai ya yi min bayanin ba shi ya siye gidan ba kai ka siya kuma shi baya da wani abu da zai yi sai dai na yi magana da kai”
Hannu Jibril ya kai yana wasa da wata ƙwallo da ake saman teburinsa mai ruwan zinari wance aka ɗora saman wani abu mai kama da turmi.
“Amman miyasa zaka siya gidan har 1.5 million?”
“Saboda kai da ka siye gidan ka bawa waɗanda suke cikin gidan kwanaki su tashi, that's why na ke son siye musu gidan”
Siraj ya haɗa ido da Jibril sannan ya kalli Mustapha ya ce
“Kana da alaƙa da ƴan gidan ne da har zaka siye gidan da kuɗi da yawa haka, gidan da be wuce dubu ɗari shida ba?”
Mustapha ya watsa masa wani shegen kallo tare saboda yadda yaga sun maida shi ƙaramin yaro.
“Mr gida na zo siye ba bincikar alaƙata da ƴan gidan na zo ku min ba”
Jibril ya yi murmushi yana ciagaba da juyawa saman kujerar.
“Come on tell me boy maybe i can help”
Mustapha ya maida dubansa gurin Jibril jin irin isgilancin da yake masa, yanzu kan zuciyarsa ta fara raya masa akwai dalilin da ya sa Jibril ya siye gidan.
“Ban girmi ka karani boy ba? Name what ever you want zan baka am not here to play a game”
Jibril ya miƙe tsaye yana dariyar ƙeta ya nufi gurin window sa yana faɗin.
“In banda kai daƙiƙi ne baka taɓa tsayawa ka yi tunani ba, baka taɓa tambayar kanka dalilin da yasa ka na siye wannan gidan ba? Taya zan zuba har milion ɗaya na siye gidan dubu ɗari biyar sannan ka zo ka ce na fansar maka ni ba a min wasa da kuɗi sai dai ni na yi ma wasu wasa! Mu kamfaninmu baya siye da siyar da gidaje ni ma kuma ba sana'a ta ba ce, so wannan gidan akwai dalilin da yasa na siye shi, so walk out of my office ba zan siyar ba”
Mustapha ya tashi tsaye yana murmushi.
“Zuciya na raya min ka siye gidan nan ne saboda wata manufa is that the reason yasa ka basu lokacin tashi? Kuɗin ka be amfane ka ba Mr Billionaire, tun da har zuciyarka zata raya maka siye gidan talakawa kuma ka takura musu bayan kasan babu su da inda zasu koma me suka maka ne?”
Jibril ya ƙyalƙyale da dariya daga inda yake tsaye ba tare da ya juyo ba ya ce.
“Na siye gidan ne saboda na isa na siya, ni mijin Nawwara ne idan ma akan ta kake wahalar da kanka so ka daina yaudarar kanka”
Mustapha ya yi murmushi tare da zuba hannayensa aljihu.
“Her ex-husband dai Nawwara bata da wani miji a yanzu”
Jibril ya juyo yana kallon Mustapha murmushin da ke fuskarsa yana dusashewa, can kuma sai ya fara dariya.
“Yeah yeah it Funny am laughing, amman bari na faɗa maka wani abu ka bar irin wannan wasan i don't play when it comes to Nawwara”
Mustapha ya nufo kamar yadda Jibril yake doso inda yake.
“Kana son zaka saketa? Ƙarya so kake mata tun da har ka iya siye gidan da suke ciki dan kawai ka takura mata, a haka ake so? Ko dai jikinta kake so ne huh? Da nine na samu damar auren Nawwara ko ƙuda ba zan bari ya taɓa ba balle har ya kai ga na saketa ko da kuwa kullum ruwan zafi take zuba min a jiki, but look at yourself ka yi arzikin aureta amman ka saketa ooph so sad maybe rabona ce shiyasa ka saketa”
Cewar Mustapha yana wani abu da fuska kamar mai magana da ƙaramin yaro yana murmushi, cikin zafin rai Jibril ya kai masa bugu a fuska ya sake kai masa wani a gefen baki, cikin zafin nama Mustapha ya ɗago zai rama sai Siraj ya yi saurin riƙeshi ya jashi baya, hakan ya bawa Jibril ƙara kai amsa wani dukan a baki sai jini ya fara zuba.
“Abraham”
Siraj ya ƙwalawa PA ɗin Jibril kira sai gashi cikin ɗakin da sauri.
“Riƙe min wannan”
Da sauri ya Siraj ya saku Mustapha ya nufi Jibril ya riƙe shi yana faɗin.
“Take him out”
Ganin Abraham ɗin ba zai iya fitar da shi shi kaɗai ba, yasa Siraj ya saki Jibril ya nufi Mustapha suka fitar da shi tare.
Juyowa Jibril ya yi ya nufi teburinsa ya buge System ɗin da ke saman ta faɗi ƙasa.
“I need to see her, we need to talk zan bata haƙuri zan yi komai akan ta, ba zan bari wani ya ɗauki muhallin na a zuciyarta ba”
Komawa ya yi gaban teburin ya ɗauki wayarsa ya danna number Abbah, yawo ya riƙa yi cikin office ɗin zuciyarsa na mugun bugawa, a ƙarshe ya samu tsayawa jikin window saboda Abbah ya yi picking.
“Afternoon Abbah”
“Afternoon Jibril ya aiki?”
“Alhamdulillah, Abbah we need talk”
“About?”
“Nawwara Abbah na gano inda take”
“Ai nasan zaka gano inda take, shiyasa na ce ban yafe maka kaje ƙofar gidansu da sunan neman gafararta ba, kai yanzu dan baka da kunya sai kaje ƙofar gidansu har ka iya haɗa ido da ita? Mu muka zaɓa maka ita lokacin da zaka aureta ka butulce ma umarninmu ka ce kai ba haka ba yanzu kun rabu miye na bibiyar yarinyar mutane?”
“Na tuba Abbah Wallahi na tuba”
Ya duƙa har ƙasa kamar yana gaban Abbah.
“No ban yarda ba”
“Abbah ko dan na nemi gafararta ba, ina da buƙatar na tambayi abunda yake cikin maybe ta haihu, you know how i love to see my carbon copy Abbah kasan yadda na ke son haihuwa”
“Sai ka ƙara aure ka yi haƙuri har Allah ya baka”
“Abbah kasan na yi aure ba ɗaya ba amman Allah be bani haihuwa ba, taya Allah zai bani haihuwa bayan na yi masa butulci”
“Sai ka yi haƙuri"
Abbah na faɗar haka ya aje wayar. Sai Jibril ya miƙe tsaye yana cizon lips ya wulgarda wayar ƙasa iya kar ƙarfinsa, kamar mahaukaci ya fara bugun ginar gurin da duka hannayensa har sai da jini ya fitowa ko wannensu sannan yaja baya yana haƙi.
Zinatu ce ta shigo office ɗin da sauri hankalinta tashe ta doso inda Jibril ya ke.
“Miya same ka haka?”
Zata taɓashi sai ya yi baya yana ɗaga mata ɗayan hannunsa.
“Don't touch me, na yi ma kaina alƙawarin ba zan sake taɓa wata mace ba sai Nawwara, wata mace kuma ba zata sake taɓa ni sai ita”
Mutuwar tsaye ta yi a gurin ta, kamin ta juyo ta kalli Siraj da ya shigo yanzu.
“Miya faru kuma? Zinatu go and call doctor please”
Kainta kaɗa sannan ta juya ta fice jikinta a sanyaye. Siraj ya nufo Jibril yana faɗin
“Be kamata ka tada hankalinka akan wannan gayen ba”
“You don't know what Love is you have no idea how i feel so karka faɗa min wannan maganar”
“Ina ƙoƙarin faɗa maka wannan gayen be isa ya ƙwace Nawwara daga hannunka ba har sai idan kai ka so”
“Kasheshi zan yi Siraj babu wanda ya isa ya so Nawwara sai ni kaɗai ne wanda Nawwara zata so sai ni”
Siraj ya kai hannu ya dafa ƙirjinsa.
“Baka buƙatar kashe shi, sai idan kasheshi zaka yi da ranshi babu wanda ya isa ya yi gasa da kai Jibril sai idan ka so”
Wata kujerar da ke gefe Jirbil ya nufa ya zauna yana ta sauke ajiyar zuciya, wani haushi yake ji da baƙincikin da be shaƙe Mustapha ba.
*** *** ***
Misalin huɗu da rabi ina zaune tsakar gida ni da Inna muna tattauna abunda ya faru a ɗazu. Kamar daga sama sai muka ji sallamar Zinatu daman na ji tsayar mota a waje sai dai ban ɗauka mai motar nan zata shigo ba.
Na yi mamakin yadda na ganta fuska a sake kamar ba ita, cike da walwala ta gai da Inna sannan ta kai min duka irin na wasa.
“Ke ƴar gari gurinki na zo”
Cike da mamaki na tashi ina dariya na nufi ɗakinmu sai ta biyoni, bayan ta zauna saman katifar mu sai na fita na ɗebo mata ruwa na dire mata gabanta.
Sai ta ɗauke ruwan ta maiyar gefe ta fuskance ni ta ce.
“Nawwara ranar da kika mari Ogan mu, abun ya ban mamaki, abu na biyu kuma ya matsa akan yana son ki dawo aiki wai sai ya mugun wulaƙantaki, shine na ke son na san wace irin gaba ce a tsakaninku har haka duk da yake na ji ya kiraki da matarsa amman abun ya ɗaure min kai”
Murmushi na yi a zuciyata ina cewa ki ce gulma ce ta kawo ki kenan. A fili kuma sai na ce
“Babu wata alaƙa fa, kawai ya taɓa hannuna ne ni kuma bana son yadda maza suke taɓa ni shiyasa na mare shi”
“Amman miyasa ya kira ki matarsa?”
Ido na ƙura mata ina ta tunanin abunda zan ce mata, ban sani ba ko shine ya aikota ko kuma ta zo ta san wani abun ne.
“Shi ya kamata ki yi ma wannan tambayar, ai na yi zaton ke ɗin budurwarce ko ƙanwar da har kika yi unƙurin rama marin da na masa”
Ɗan murmushi ta yi.
“Nawwara kenan, ai ban za ci akwai wata alaƙa tsakaninki da shi ba shiyasa na yi hakan domin be kamata ki mari babban mutun kamar shi ba”
“Gaskiya ne, ke ma be kamata ace kin biyo ƴar talaka har gida kina bugun cikinta ba”
Miƙewa ta yi tsaye tana cigaba da murmushi ta dafa ni.
“Anyway daman na zo ne akan na baki shawara akan karki yarda ki koma aikin nan domin kuwa Jibril na shirya wulaƙantaki ba kaɗan ba”
Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleni
“Da ni ce ke ba zan taɓa yarda na haɗa ido da mutumen da ya wulaƙanta ni ba balle har ya kirani kariwa kuma na yarda na kula shi, Wallahi ba ayi irin wannan mijin ba”
“Sai kuma aka yi rashin sa'ah zuciyar Nawwara da ta Zinatu ba iri ɗaya ba ce”
“Ai ba zasu taɓa zama ɗaya ba har a bada ni dai shawara ce kawai na baki domin bana son ya cutar da ke”
“Tau na gode Ummu ta gaida Aisha”
Daga haka ta juya ta fice, ni ɗauki ruwan da bata sha ba na fice da su daman na san ba zata sha ba tun da ƙyamarmu take.
MUSTAPHA POV.
Gudu ya ke kamar zai tashi saman ko da ya iso gida kamar baya cikin hayyacinsa saboda ɓacin rai. Shi kansa be san iya adadin horn ɗin da ya yi ba kamin a buɗe masa gate, abunda ya tashi hankalin Hajiya ta fito a firgice tana kallon yadda ya faka mota kamar wani mahaukaci.
“Son what happen to you?”
Ta faɗa tare da nufar inda yake tana kallon fuskarsa hankalinta a tashe.
“Wani ne ya yi min haka saboda Nawwara Mom”
Hannayenta biyu ta kai ta riƙe fuskarsa tana kallon yadda gefen bakinsa ya soma kunbura ga fuskarsa ma tayi ja sosai abunka da mai farar fata.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee*
3⃣3⃣
MUSTAPHA POV.
Bayan ya baro part ɗin Hajiya sai ya dawo ɗakinsa ya zauna saman kujera ransa a jagule ya dafe kansa yana sauke ajiyar zuciya.
Shi kansa yasan Nawwara ba zata taɓa kula shi ba, yasan ba zata taɓa ƙaunarsa ba, gani yake ya cancanci ko wace irin jarrabawa amman ban da ta son Nawwara, yarinyar da ya wulaƙanta ƙanwarta sai kuma yanzu ya zo ya ce yana son ta.
Miƙewa ya yi tsaye ya nufi gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa, tunani yake abunda zai aikata wanda zai cire masa son Nawwara amman ko sunanta ya tuna sai gabansa ya faɗi.
“Allah na san na aikata laifi mai girma Allah kaine mai yawan gafara mai tausayi Allah ya yafe min, Allah ka musanya min wannan jarabar ta son Nawwara zuwa wata Allah indai wannan ba ita ce ajalina ba”
Shine abunda ya ke faɗa idonsa cike da ƙwalla.
“Son...”
Ya juyo da sauri jin motsin mahaifiyarsa, sai ya zauna gefen gado, ita ta ƙaraso kusa da shi ta zauna ta dafa shi
“Son ka yi haƙuri da abunda Daddynka ya yi maka ka kwantar da hankalinka ka ji?”
“Bana da kwamciyar hankali Mom tun daga lokacin da Allah ya jarrabe ni na zama silar mutuwar wata kuma Allah ya jarrabe ni da son macen da ba zata taɓa so na ba, kullum kuma ina tunanin abunda zai faru da ni gaba, ina jin kamar ajalina yake kusa da ni saboda wannan tunanin da rayuwar da na shiga ba zata taɓa bari na rayuwa mai tsowo ba”
Ta yi saurin rumgume shi tana ƙoƙarin kuka.
“No Son no ka daina zancen mutuwar nan, ka daina saka kanka damuwa akan abunda ba kai ka aikata ba, yarinyar nan ba kai ka akasheta ba su suka kashe ƴarsu so stop blaming yourself, Nawwara kuma ka cireta a ranka ba ta dace da kai ba, so kawai take ta yi amfani da wannan damar ta wulaƙanta ka”
Be damu da hawayen da ke zuba a idonsa ba ya ce.
“Mom Wallahi ba ni na sakawa kaina son yarinyar nan ba, ban san yadda aka yi son ta ya shiga raina ba duk wata hanya da zata cire min son ta nemanta na ke amman na kasa samu”
“Zamu samu Son ka kwantar da hankalinka”
Ya ɗago yana share hawayensa tare da ɗaga mata kai.
“Bari Ikram ta kawo maka abinci ka karya anjima za mu yi magana”
Nan ma kai ya gyaɗa mata, sai ta shafa masa kai cike da so da kuma ƙaunar ɗan ta.
“Allah ya maka albarka”
Ta tashi tayi ta fice, bayan kamar mintuna goma sai ga Ikram ɗauke da kwanonin abinci ta shigo ɗakin da sallama ta aje masa a gabansa.
“Ba zan iya cin abincin nan ba Ikram”
Ya faɗa yana kwantar da kansa saman gadon saboda zazzaɓin da yake jin ya fara taso masa.
“Idan baka ci Mama zata damu”
Cewar Ikram tana buɗe wasu plates, sauƙowa ya yi ƙasa ya zauna ya tsurawa Ikram ido kamar mai karantar abu a fuskarta.
“Ikram zaki iya aurena...?”
Ɗago kai ta yi da sauri ta kalleshi har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta yi shiru ta ɗaga masa kai alamar Ee.
“Amman miyasa Nawwara ba zata iya so na ba”
“Ni da ita akwai banbanci, ni na rayuwa a cikin gidan nan ita kuma ta rayu a gidansu, kana da kyau da isar da kowace mace zata ce tana son ka, sai dai ita a halin yanzu ba soyayyace a gabanta ba, duk macen da aka yaudareta ko aka yaudari wani nata ita ma zata ga kamar wani zai yaudareta ne, babu yadda za ayi Nawwara ta kula balle ma har ya kai ga ta so ka, saboda abunda ka aikata ma ƙanwarta, kullum da wannan abun zata riƙa kallonka ko da kuwa wata mace ka yi ma balle kanwarta.
Sannan akwai banbancin tarbiya a tsakanin kai da ita da kuma gata, kaga duk wannan abun da aka aikata iyayenka goyon bayanka suke suna ƙoƙarin nuna maka baka da laifi, i'm sorry to say idan har ka biyesu zasu iya rabaka da Ubangijinka duk da kuwa suna iyayenka, saboda suna kallo kana aikata zina kuma suka ƙyale saboda gudun ɓacin ranka, ƙara ma Momy wata rana tana maka magana amman baka ji, Allah ya ce kar mu kusanci zina balle har mu aikata ta, kai ko ya aikata adadin da baka san iyaka ba, kasancewar nan da muke ɗaki ɗaya ba shi da kyau Ya Mustapha domin idan mace da Namiji suka kasance su kaɗai suka kaɗaice to sheɗan ne na ukunsu, amman wannan be taɓa zuwa a ran Momy ba balle kuma kai da ace hankali ko kuma sha'awarka ta kwaɗaita maka ni da yanzu ka gama da ni kuma ba za ayi komai ba saboda kai ɗan gata ne.
Ka misalta kanka Ya Mustapha da ace kana aikata zina da wannan yarinyar ne Allah ya karɓi ranka mai zaka faɗawa Ubangijinka? Kamar kaina da bawa ka ce karya aikata abu kaza wata rana sai ka sameshi da tsabama Umarninka har ma ya yi maka sata kuma ka kamashi dumu-dumi wane irin hukunci zaka yanke masa?”
Tun da ta fara maganar jikinsa ya yi sanyi hankalinsa ya tashi tun da yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa ya faɗa masa gaskiya kamar Ikram, yana sauraren wa'azi amman be taɓa natsuwa ya yi aiki da shi ba. Hawaye yake hawayen da ke nuna nadama da tashin hankalin da ke fuskarsa.
“Miyasa baki faɗa min wannan ba tuntuni? Da kin tunatar da ni da yanzu ban faɗa wannan halin ba”
“Ko da na faɗa maka zaka faɗa saboda ƙaddaraka ce a haka, kuma a lokacin na san ba zaka saurareni ba saboda ba zaka taɓa ganin munin abunda kake aikatawa ba, ban ga sha'awa ga abincin da zan wanke hannu na ci ba wani yazo hannunsa da datti ya ci wani ma yazo hannunsa da datti yasa ya ci ni kuma na zo na sake saka hannu na ci, sam babu kishi kuma babu imani ga duk mutumen da yake aikata Zina, ban san miye daɗinta ba balle kuma ribarta, saboda yawan mata da kuma yawan wasu ɗabi'u na ɗan adam Allah ya halattawa maza auri mace sama da ɗaya amman kai kaba ma yi auren ba ka faɗa a zina kana neman hallaka kanka, a wannan halin da ka shiga a yanzu ina tunanin shiriyarka ne yazo, dan haka ka yi ta istigifari kana neman Allah ya yafe maka abunda ka aikaka kuma ka yi ma Allah alƙwarin ba zaka taɓa komawa a cikin wacan ƙazamin halin ba, ka yi ta aikata dik wani abin da ka san zai kusantar da kai ga Ubangijinka”
Ya gyaɗa mata kai alamar gamsuwa.
“Amman Nawwara ba zata yafe min ba ko?”
“Zata yafe maka matuƙar kana kyautata mata, kuma kan tuba tuban gaske sai Allah ya dafa maka ta yafe maka har ma ta so ka idan ƙaddarar sonka yana cikin ƙaddararta”
“Idan kuma so na baya cikin ƙaddararta fa?”
A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce.
“Zai iya zama son ka yana cikin tawa ƙaddarar...!”
Da sauri ya miƙe tsaye ya share hawayensa daman tun ba yau ya lura da take-taken Ikram da ke nuna alamar tana son shi.
“Ki ɗauki abincin idan na fita waje zan ci, na gode sosai Sis”
Yana faɗar hakan ya nufi banɗakinsa dake cikin ɗakin, murmushi ta yi murmushin da ke nuna rashin jindaɗinta sannan ta kwashe kayan ta fice.
bayan ya fito wankan ya ɗauki wayarsa ya nemo number Jidda bugu uku ta ɗaga muryar a sake har wani zaƙi take ƙara mata.
“Hello Mustapha”
“Ya kike?”
“Lafiya ƙalau”
“Kina gida?”
“Ee ina gida lafiya?”
“Lafiya ƙalau, kawai ina son ganinki ne akwai wata magana mai muhimmanci da na ke son mu yi da ke idan babu takurawa kuma idan kina free”
“Aiko bana free dole zan samu time dominka, faɗa min yaushe zaka zo i mean time?”
“Yanzu nan gani nan har na yi wanka”
“Okay sai ka shigo”
Yana aje wayar ya nufi gurin da tufafinsa suke ya buɗe, cikin ƙanƙanen lokaci ya shirya cikin manyan tufafi riga da wando na shadda, sannan ya fito ya nufi gurin motarsa ya shiga sai ƙofar gidansu Jidda.
Waya ya buga mata sai gata ta fito ba ɓata lokaci fuskarta ɗauke da kwalliya sai ƙamshin turare take kamar sabuwar amarya, motar ta buɗe ta shiga kasancewar be fito ba ne yana daga ciki zaune. Front seat ta zauna tana ƙara miƙa masa gaisuwa ciki kashe murya fuskarta ɗauke da murmushi, bayan sun gaisa ya koro mata da bayanin da ke tafe da shi.
“Jidda ko kin san wanda yake da gidansu Nawwara da suke haya?”
“Ee Malam Haruna ne yana nan gaba da su kaɗan, ya aka yi?”
“Na je gurinta ne sai take zargin ko nine na siye gida na saboda ance an siye gidan”
“Haka nima na ji amman ban san waya siye ba”
“Ai nasan Malam Haruna zan masa magana na ji wanda ya siya sai ya fansar min. Am Jidda ina son ki faɗa min duk wani abu da Nawwara take so da wanda bata so da kuma taimaka min akan duk wani abu da zai ƙara kusancina da ita na san ke zaki iya daboda kinfi kowa saninta”
Ta kalleshi Jiki a sanyaye.
“Saboda me?”
“Saboda ina ƙaunarta son ta na ke Jidda wannan dalilin yasa na ƙulla abota da ke”
Tafiyar daƙiƙu biyar zuwa shida numfashinta ya yi sannan ya dawo jikinta har ta iya jiyo bayanin da Mustapha yake koro mata. Be ɓoye mata komai ba daga irin son da yake yi ma Nawwara da kuma abunda ya aikatawa Habiba, ko da ya ƙarasa bata labarin kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro. Lumshe ido ta yi ta haɗeye yawu sai hawaye suka sauko mata, hawayen da ita kanta ba san na minene ba na tausayin Habiba ko Nawwara ko kuma kanta ko Mustapha, wani baƙon al'amari ya ziyarceta labarin ya zo mata banbaragwai domin Nawwara bata taɓa labarta mata wannan ba, sai dai yanzu ne ta gano dalilin tsanar da Nawwara take yi ma Mustapha.
“Please help me...”
Ya faɗa cikin muryar kuka. Sai ta kalleshi tana kukan kamar yadda shi ma yake yi.
“Zan yi tunani akwai, ina da buƙatar natsuwa bana iya banbance komai a yanzu”
Tana faɗar hakan ta buɗe motar ta fita ta shiga gida da sauri tana kuka. Ya kusan minti talatin sannan ya bar ƙofar gidan zuciyarsa na mugun ƙona ya nufi gidan Malam Haruna.
*** *** ***
Anya zan iya aiki tare da Jibril kuwa? Mutumen da ya wulaƙanta ni zan iya bashi wannan damar ta kusanci da ni?
Yes zaki iya, ga dukan alamu ya gane kuskurensa yanzu kan ya san ƙimarki tun da har zaki maresa a gaban jama'a ya ƙyaleki, yanzu ne ya fi dacewa ki nuna ko wacece ke, yana da kyau yasan ba wacan Nawwarar ba ce this is the time da zaki rana abunda ya yi miki kuma the same time da zaki nunawa Bilal son gaskiya kike masa, kuma idan har ban yi aiki da shi ba na gallaza masa hakan zai bashi damar da zai riƙa bibiya ni da familyna.
Da wannan tunanin na tashi yau ina ta son tsayarda matsaya ɗaya akan na yi ko kar na yi. Su Sakina sun kama hanyar makaranta Inna kuma na bachinta kamar yadda ta fara dabuwa kanta a yanzu da bachin rana, ni kuma na fito na gyara tsakar gidan na yi wanka sai na shirya cikin koriyar atamfata ta roba, jin na yi bana ƙaunar zama gidan dan haka na saka Hijabina na ɗauki wayata na nufi Babban gida daman na kwana biyu ban leƙa ba.
Ina cikin tafiya wayata ta yi ƙara alamar saƙo, da fari na yi zaton mtn ne ashe Bilal ne ya aiko min da saƙon barka da safiya.
_Morning text does not only mean good morning. It also means, I think about you when I wake up, I love you._
Wani kalar farinciki ne da annashuwa suka nemi inda zuciyata take suka mamayeta, at that time phone ɗin ta nokia @360 ta yi ringing da number nan da aka saba kirana da idan wacce sai na ɗauka sai ayi shiru aƙi magana. Kamar ba zan ɗauka ba sai kuma na daure na ɗauka a tunani na Mustapha ne ashe Jibril.
“Kai wai wane irin shashasha ne? Akan ne zaka riƙa kirana ne wahalalle”
“Dan Allah ki yi haƙuri Wallahi na kira ne kawai na tambaya idan zaki zo aikin saboda na ga baki shigo ba yau”
“So kai ne ko? Daman kai ne kake kirana ka ƙi magana ko?”
“I just want to hear your voice”
Ya faɗa muryarsa a ɗaƙile, ni kuma na ja tsaki na kashe wayar ma gaba ɗaya, saboda ya ɓata min rai. Ban wani daɗe Babban gida ba kasancewar ban tarar da Yakunbo ba domin a ɗakinta na ke shiga na kwanta saboda rashin hayani, mun ɗan yi fira da wasu cousins ɗina mata, sannan na taso na nufo hanyar gida.
Ina shigowa gida na tarar da Inna ta rafka uban tagumi tana kallon ƙofar shigowa, da sauri ma ƙarasa kusa da ita.
“Inna lafiya”
“Mahaifiyar Mustapha ta zo gidan nan ta min cin mutunci, kuma ta gargaɗe ni matuƙar baki ƙyale ɗanta ba sai tasa an ci mana mutunci, har tana iƙirarin wai mun yi ma ɗanta magani mun zugashi yaje ya ci mata mutunci”
Faɗuwa na yi zaune shi ƙenan mu dan muna talaka ba mu da gata kowa ya ɗauko shararsa sai ya juye akan mu wai mai muka yi mutanen nan ne...?
JIBRIL POV.
Lilo yake ta yi da kujerarsa hannunsa dafe a kai ya lumshe ido, sai shaƙar ragowar cocaine ɗin dake hancinsa ya ke.
Siraj ne ya turo ƙofar office ɗin ya shigo riƙe da wasu takardu a hannunsa.
“Kana ta takurawa kanka Jibril yarinyar ba zata zo ba, ɗazu fa nan ka kirata amman ta kashe maka waya, akwai mata da yawa fa a garin nan da ma wajen gari be kamata ace kana damun kanka akan ƴar talakawa ba...!”
Da mugun ƙarfi Jibril ya daki teburin dake gabansa har wasu abubuwan suka zube ƙasa, ya kalli Siraj cikin wani irin ɓacin rai ya ce.
“Oh s*** how many times do i have to tell you ka daina faɗin wani abu marar daɗi akan yarinyar nan ne, baka san wacece ita ba ka daina saka bakina a kan maganarta, you're just my friend so stay where are you”
Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya nufi window yana huci tare da busar da iskar bakinsa. Siraj ya tsorata sosai da yanayin Jibril duk zamansu tare be taɓa masa haka ba sai yau, cikin sanyin jiki ya ce.
“Akwai wanda yake son ganinka”
Ba tare daya juyo ba ya ce.
“Yana da appointment da ni ne? Idan yana da ayi cancelling bana buƙatar ganin kowa a yanzu sai NJ, na faɗa maka idan ma wani abun ne akan aikin nan zaka iya wakiltata”
“This one is important too, ya zo ne akan maganar gidan nan da ka siya na su Nawwara, ni ya kira na faɗa masa inda kake ya zo PA ya hana shi ganinka, so shiyasa ya ƙara kirana ya matsa yana son ganinka”
Da sauri Jibril ya juyo yana kallonshi da idonsa da suka kaɗe sukayi ja.
“Waye shi?”
“Ban sani ba ya ce dai sunanshi Mustapha”
“Bar shi ya shigo”
“Ka faɗawa PA ɗinka ya barshi ya shigo domin yana reception yana jira”
Daga haka Siraj ya juya ya fice, Jibril kuma ƴa nufi telephone ɗinsa.
WHAT DO YOU EXPECT NEXT ....?
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee ❤*
JIBRIL POV.
Bayan an gama wanke masa hannun aka bashi wani magani da zai sha, sannan likitan ya ɗauki box ɗinsa ya fice daga office ɗin zuwa chemist ɗin dake kamfanin kasancewar yana aiki a ciki ne.
“Siraj ka sake aikawa yarinyar da saƙo ko kuma ka kirata”
“Ya kamata mu bata time Jibril, idan har kana son Nawwarar nan ta yi aiki tare da kai kuma ta yarda ta yi aikin dole ne sai ka nuna mata cewar kai ma Namiji ne, rayuwarka ta baya dole sai ta fara aikin a kanta ya yadda zata gamsu aikinne dai kuka yi ba wani abu ba, matuƙar ka ce zaka kwanta ta hau ta takaka zata yi maka abunda baka tsammani kuma daga ƙarshe mu zo bamu samu abunda muke so ba”
Shiru ya yi tana nazarin kalaman Siraj yasan yana da gaskiya wani ɓangaren, a halin yanzu ya san Nawwara ba zata taɓa yarda ta yafe masa kai tsaye ba, kuma taya zata gane ya canja da gaske yana sonta idan har kusance ba idan kuma har be bi shawarar Siraj ba yasan babu kusanci a tsakaninsu domin zata yi ta nesantarsa ne.
Ganin Yadda Jibril ya natsu ya bawa Siraj damar cigaba da bayaninsa.
“I zuwa yanzu ya kamata mu dakata daga tura mata da saƙon neman ta dawo aiki ko kuma kiran da kake mata mu ɗaga mata ƙafa na ɗan wani lokaci”
“Baka san yadda na ke ji ba Siraj idan naji sunan yarinyar nan ji na ke kamar na runtse ido na buɗe na ganta a gabana, Siraj ina neman duk wata hanya da zan nuna mata da gaske na gyaru kuma ina sonta, abu na ƙarshe ba zan bari wannan wawan ya shiga zuciyarta ba”
“Ka yi haƙuri da sannu komai zai wuce, ka bata ɗan lokaci kaɗan, amman fa dole sai ka zama namiji domin ba zai yiyu ta riƙa maka wannan cin kashin ba”
“Idan kuma bata dawo ba fa?”
“Zata dawo na tabbatar zata dawo saboda tana tunanin ɗaukar fansar abunda ka yi mata ta hanyar wulaƙanta a gaban ma'aikanta, ai ta yi na ɗaya ka ƙyaleta dole zata yi ƙoƙarin yin na biyu har zuwa adadin da take ganin zata gallaza maka, idan kuma ba ta dawo ba sai mu bi wata hanyar ta dabam”
Ya saka hannunshi aljihi ya ciro ƙaramin hoto ya miƙawa Jibril.
“Ga wannan Abraham ya bani wai Nawwara ta manta shi lokacin da ta shigo office ɗin nan, ina tunanin yana da muhimmanci sosai a gareta”
Hannu Jibril ya miƙa ya karɓa yana duba, yasan ba Nawwarsa ba ce amman wacce ke cikin hoton tana kamada ita sosai, ajiyar zuciya ya sauke ƙana ya ce.
“Idan har Nawwara ta furta kalmar so gurin wannan yaron ko? Ba makawa kisa ya tabbata akansa”
Miƙewa ya yi tsaye ya fice daga office ɗin maganganun Mustapha na ɗazu suna ta masa yawo akai, yanzu kan bashi da babban maƙiyi kamar Mustapha domin duk mai son Nawwara a gurinsa maƙiyinsa ne indai namiji ne.
MUSTAPHA POV.
“Sai yaushe zaka ga ne Nawwara nan ba ajin ka ba ce Son? Dan me zaka bar wani ya yi maka haka akan macen da ko a mafarki be kamata ta zama budurwarka ba balle matarka ba, na je ɗazu na ma mahaifiyarta jan kunne akan karta sake bari ƴarta ta kula ka idan ma wani maganin ne tau ta yi gaggawar karyashi”
Ya janye hannayenta dake fuskarsa ya riƙe yana nuna mata tsantsar damuwa a fuskarsa.
“Haba Mom a maimakon ki taimaka min gurin neman soyayyarta sai kuma ki ɓata abun? Kin ce kina so na miyasa ba zaki so abunda na ke so ba? Wallahi yarinyar nan bata min komai ba, kawai Allah ya ɗauki sonta ne ya ɗora min dan ya jarrabe, dubi ki ga fuskata kin san dalilin da yasa na dawo gida yanzu? Saboda na nuna miki wannan abun ki san ba ni kaɗai na ke son Nawwara ba, kuma ki taimaka min wajen neman yafiyarta da soyayyarta, na je gurin wanda ya siye gidan da suke ciki ne akan ya fansar min amman sai yake nuna min kamar ya fini son Nawwara saboda shi mahaukaci, ni kuma na yi alƙawari ba zan taɓa bari ya auri Nawwara ba, ba zan hanata Nawwara son wanda zuciyarta take ƙauna ba, amman ba zata taɓa zaman aure da wani ba sai ni, saboda ta haka ne kawai zan iya gane cewar ta yafe min”
Hawaye ya fito a idanuwan Mahaifiyarsa ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallonshi.
“Shikenan sun gama juye min kan yaro, s8n gama da kai Mustapha ba zaka taɓa jin abunda zan faɗa maka ba”
“Ke kuma ba zaki taɓa gane abunda na ke nufi ba...!”
Yana kaiwa nan ya sake mata hannu ya nufi part ɗinsa.
*** *** ***
Bayan na aje ruwan da bata sha, sai tambayarta da kuma abunda ta faɗa min ya dawo min a rai, ya aka yi ta san Jibril ya wulaƙanta har haka? Ko dai shi ya faɗa mata ne? Idan har shi ya faɗa mata wannan yana nufin shi ya turota kenan? Amman taya zai turo ta bani shawara akn karna koma aikin kuma.
“Lafiya kuwa Zinatu ta zo?”
Ya ɗago daga tunanin da na ke na kalli Inna ina ƙirƙiro murmushi tare da nufar inda take zaune na zauna.
“Ba komai ta zo ne akan aikin nan wai yau ban je ba na faɗa mata se gobe shine wai bata son ina wasa da aikin ne”
“Nawwara be kamata ace kina ɓoye min wani abu ba, ni fa mahaifiyarki ce, bana son noƙe-noƙen nan da kike haka kuka yi ke da Habiba har ta Allah ta kasance”
Rumgumata na yi ina murmushi.
“Wallahi Inna maganar aikice ta zo ta bani shawara, babu wani abu kin ji na rantse miki”
Hakan yasa hankalinta ya kwanta, ni kuma na zari Hijabi na nufi gidansu Jidda.
A tsakar gidansu na sameta kwance saman tabarma ta yi rufa da zane da alama bata jindaɗi duk ta rame kamar ba ita ba. Da mahaifiyarta muka fara gaisawa sannan na nufi inda take hankali a tashe, hannu na kai na taɓa jikinta sai na jishi da ɗan ɗumi.
“Tun yaushe ne baki da lafiya?”
“Shekaranjiya, maleria ce ke damuna”
“Allah ya baki lafiya, Wallahi ban sani ba sannu”
Kai ta gyaɗa min sai ta miƙo hannunta ta kama nawa hannu ta jimƙe a sosai ta lumshe ido sai hawaye, a take hankalina ya tashi ji nayi kamar itama tafiya zata yi ta barni ban san lokacin da na fara nawa kukan ba, sai Maman Nura tasa mana dariya wai daman mu ƴan raki ne idan muna ciwo. Ban bar gidan ba sai da na yi sallah magariba a nan, ko da na dawo gida kaina na ta ciwo saboda kuka da na yi a gidansu Jidda.
Da kaina na labartawa Inna rashin lafiyar Jidda, ita ma kanta bata jidaɗi ɓa domin ta san yadda na ke da Jidda kuma ta san irin halin da Jidda take shiga idan bani da lafiya.
“Zata ji sauƙi ai kin san maleria yanzu yadda take ma mutane balle Jidda da rakin tsiya, Allah ya sauwaƙe sai gobe zanje na dubata”
“Amin amman gaaskiya tana jin jiki domin ta rame sosai jikinta kuma da zafi kamar ba a mata allura ba”
“Allah ya bata lafiya, ai malaria yanzu sai an sha allura sosai ake tashi”
Na tashi cikin rashin kuzari na nufi ɗakinmu. Washe gari da wuri na tashi kamar kullum bayan su Sakina sun tafi makaranta ni kuma na shirya cikin wata doguwar rigar yadi na yi ma Inna sallama tare da faɗa mata zanje gurin aikin sannan na saka Hijabi na fice. Gidansu Jidda na nufa dan duba lafiyar jikinta, una tafe ina ta mamakin tun jiya ba mi yi waya da Bilal ba be kirani ba ni kuma ina tsoron kiransa saboda ban saba ba kuma ban san hali da yake ciki ba, sai dai gaskiya a kwana biyu nan da ya saba min da kiran yasa ni jin babu daɗi.
Na yi mamakin ganinta ƙofar gidan tare da Mustapha suna magana duk da ban san mai suke magana akaiba na samu kaina da tsoro sosai saboda sanin wanene Mustapha.
Daga ita har shi ido suka ƙura min ganin irin kallon tuhumar da na ke musu, ba ma kamar shi da natsu guri ɗaya kamar na rikice da ganina.
“Kin san waye Mustapha a unguwar nan Jidda karki yarda ya yaudareki”
Na faɗa ina kallon Jidda da idonta ke cike da ƙwalla, shi kuma sai ya yi saurin girgiza kai yana faɗin
“Wallahi ba abunda kike tunani ba ne Nawwara”
Ni kuma na watsa masa wani shegen kallo.
“Mi na ke tunani miye bana tunani? Kasan na san waye kai ka gwadani baka samu ba shine zaka dawo gurin ƙawata? Ko kuma bayan ka gama da ita ne ka dawo kaina?”
“Babu komai a tsakanina da shu Nawwara nan ma ya zo ne saboda ke...”
Cewar Jidda hawaye na mata zuba.
“Saboda ni ko? Ki cigaba da biye masa har ya kaiki ya baro, waya sani ma ko ya lalata miki rayuwa kema”
Ina faɗar haka sai na juyo na kamo hanyar dowowa, zuciyata cike da zargi kala-kala. Sai da na yi nisa sosai na kai bakin titi ina ƙoƙarin tare Napep sai ga Mustapha ya sha gabana da Mota ya fito da sauri ya fuskance ni.
“Wallahi ba abunda zargi ba ne, na canja na Nawwara Wallahi na miki alƙwari ba zan sake yin wani abu marar kyau ba”
“Ka dawwama a cikin abunda kake aikatawa ko kuma ka tuba babu ruwan Nawwara a ciki wannan farincikin iyayenka ne da kuma masoyanka, Kuma dan Allah ka fita daga hanyata mahaifiyarka ma ta yi mana cin mutunci saboda kai tace muna zugaka kana ci mata mutunci akan gida, dan Allah ka ƙyale karka sake jamin wani bala'in gida dai zamu tashi mu bar maka abunda very soon In Shaa Allah”
“Ba ni na siye gidan ba Nawwara, wani ne ya siya sunansa Jibril ya ce shi mijinki ne”
Mamaki ne ya cikani.
“Ina ka ganshi?”
“Malam Haruna ne ya faɗa min na je na sameshi yace shi mijinki ne”
“Daga kai har shi baku da hankali, Kuma na faɗa maka ka fita hanyata”
ina kaucewa ya sake shan gabana.
“Nawwara mi zan yi ki yafe min mi zan yi ki yarda da ni? Faɗa min ko minene zan yi Nawwara ki yafe min?”
“Zaka iya dawo min da Habiba?”
“Wanda ya mutu baya dawowa kuma...”
Sai na tari Numfashinsa.
“Tau ba zan taɓa yafe maka ba”
Ina faɗar hakan na kauce na cigaba da tafiyata na bar shi nan tsaye yana kallona fuskarsa kamar wanda zai fasa kuka.
Na yi sa'ar samun Napep da wuri, ko da na isa gurin aikin takwas da ƴan mintuna, tun a bakin gate na haɗu da Amina abokiyar aikina, a tare muka ƙarasa ciki muka rubuta suna tare har tana cemin yau kan munyi latti ita tama daina ganina kwana biyu ina wasa da aikina, nikan dariya kawai na yi na ɗauke kai na nufi gurin aje Hijabina sannan na muka shiga ciki tare.
“Khadija Musa Kafinta”
Daf da za mu shiga lifted na ji an kirani sai muka waigo tare, wata ƙabila ce ta kira sunan nawa tana sanye da suit.
“Please Follow me”
Sai da muka haɗa ido da Amina sannan na bita ita kuma ta shiga Lifted, wata lifted muka nufa muka shiga tare sannan ta danna 5 lifted ta rufe muka fara tafiya. Ni dai ban kalli inda take ba itama bata ce da ni Uffan har muka isa sannan ta fita nima na fita muka doshi wani gurin daban.
Ina hango inda na bi shekaranjiya na shiga office ɗin Jibril na yi tunanin kalwaɗowa zata yi mu shiga office ɗin sai naga mun iso wani ƙaton ɗaki mai cike da computers da kuma files.
Muna shigowa sai matar ta juya ta fita wannan abokin nasa ya miƙe tsaye yana ɗaukar documents ɗin dake gabansa ya yi min magana ba tare da ya kalleni ba.
“Congratulations Miss Nawwara, kin samu baban promotion zuwa office ɗin Oga Jibril you're now his new PA, Rabi zata zo ta miki bayanin komai”
Mamaki ne na cikani new pa haka kawai bayan bana da dogon karatu?
“Amman ban yi wani zurfin karatun da za a bani wannan matsayin ba”
Kamar daga sama na ji muryar da nafi tsana a duniyar nan wato muryar Jibril ashe yana bayana ta gurin kujerar da ke farkon shigowa, ni ban ma san da shi ba kasancewar ban kalli gurinba tun da na shigo idona yana kan abokin nasa.
“Shi kuma ga damar baki idan kuma ba zaki yi ba you can leave”
Ba yabo ba fallasa ya faɗi haka ya kana ya miƙe tsaye suka fice tare da abokin nasa suka barni nan tsaye ina mamaki.
__________________________________________
Kalamaina sun yi ƙaranci su gode muku fans akan irin soyayyar da kuke nunawa littafin nan.
#Team RB
#Team Nawwara
#Team Jibril
#Team Mustapha
#Team bilal
Na gode na gode sosai Nawwara ta ce a gaishe da masoyanta.😜 Soyayyar da kuke nunawa littafin nan a yanzu Allah yasa ku nuna min irinta a littafi na gaba mai suna HAFSATU MANGA labarin ƙauye. Ina muku son so Fisabilillah a duk inda masoyin littafin nan yake. 😍
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
3⃣6⃣
Wata kyakkyawar mace ce ta shigo mai far'ar fuska da kuma ta ruhi domin kuwa muna haɗa ido da ita sai naji kamar na santa, hannu ta miƙa min.
“Sannu sunana Rabi Ismail”
“Nawwara”
Na faɗa ina miƙa mata nawa hannun.
“Zo muje zan nuna yadda aikin naki yake”
Tana gaba ina biye har muka isa office ɗin Jibril, a gaban computer ta fara isa ta nuna min yadda zan danna na buɗe ƙofar farko ta shigowa, sannan muka ƙarasa ciki ta nuna abubuwan da zan yi da zarar na iso da safe, sai kuma abubuwan da Jibril yake buƙata da kuma tsarin yadda zan jera masa komai.
“Aikinki ne ki sanar da shi idan zai yi meeting kamin lokacin ya cika, da zarar ya shigo da wuri saki sanar shi duka abubuwan da zai yi, wayarsa da ke nan office ke zaki riƙa amsa ta, idan wani na buƙatar ganawa da shi ke zaki tabbatar da tsaro kuma ke saki saka time, yanzu kan ba zaki tashi aiki ba sai 4:00pm, kuma dole ne ki shigo 8:00am, masu kowa ƙorafi ko wani bayani na cikin kamfanin nan ke zaki kula da su shi kuma sai kije ki masa bayani a tsanake, aikinki ne gogewa da kuma gyara ɗakin nan, idan na shigo dole ne zaki tashi ki gaishe kuma ki tambayeshi abunda yake buƙata”
Ya juya ta ɗauko wata leda dake saman teburinsa ta miƙa min.
“Wannan kuɗi ne naira dubu ɗari biyar zaki siye tufafin da zaki saka masu kyau saboda Oga baya son ana saka tufafi marar rsada musamman yanzu da kike new PA ɗinsa, wannan kuma makullin gida ne dake Abdullahi Fodio Road a gidan zaki zauna komai akwai a ciki”
Na sauke ajiyar zuciya ina kallon makullin data fiddo daga aljihunta tana miƙa min.
“Daman idan mutun ya fara aiki haka kuke masa a wannan kamfanin?”
“A'a Karamci ne kawai irin ya Oga Jibril ina tunanin kina da muhimmanci a gareshi sosai shiyasa”
“Ki bar kuɗin ki aje makullin kuma ki faɗa masa ba zan yi aikin ba”
“Amman miyasa?”
Ban bata amsa ba na juyo na yi tafowata zuciyata na ta raya min abubuwa da dama, idan har na yarda na yi aikin nan tau Jibril ya ƙwareni kuma duk wulaƙancin da ya yi ya tashi a banza kenan, taya mutun zai wulaƙanta ni sai kuma na dawo na fara aiki a tare da shi? Ya samu danar wulaƙanta ni saboda kuɗin da yake da su, yanzu kuma sai na yarda ya yi amfani da kuɗin ya maye gurbin abunda ya aikata? Lallai ni wawuya ce.
Haka na ke ta tunanina har na iso reception na ɗauki wata a inda na aje tare da Hijabi na saka na nufi ƙofar fita ba tare da na saka lokacin da na tashi ba.
“Nawancy”
Da sauri na juyo jin muryar Bilal, sai na sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake min.
“Ashe kin shigo?”
“Ee amman yanzu zan koma”
“Har kin gama aikin ne?”
“Ee yau baka kirani ba, duk na damu”
Ɗan murmushi ya yi muna fara takawa tare yana faɗa min akwai abunda ya ɗauke masa hankali.
“Amman ko minene ai ya kamata ka min ko da massage ne”
“Haka ne am sorry my dear ba zan sake ba”
Hango Jibril da na yi a tsaye a gate ɗin garden yasa na washe haƙura ina kallon Bilal.
“Ma yafe maka ammam karka yarda ka ƙara”
“Allah ya Huci ran sarauniya ba zan ma sake ba”
Haka mike tafiya tare muna firarmu sai dai yadda na ke dariya sai ka ɗauka wani labarin ban dariya ne yake ba ni.
Muna dosar gate Jibril kuma ya doso cikin kamfanin tare da mutumen da suke magana tare.
“Good Morning Sir”
Bilal ya faɗa cikin girmamawa a lokacin da Jibrilya kawo kusa da mu, ni kan ko kallonsa ban yi ba har sai da na ji maganar da ke fitowa daga bakinsa.
“Miye tsakaninka da wannan yarinyar?”
Ƙasa Bilal ya yi da kansa ya kasa amsawa kamar mai tsoro sannan ya buɗe baki xai yi magana sai na yi karaf na karɓe duk da ba ni ya tambaya ba.
“Wanda zan aura ne”
Sai ya juyo kaina ya kalli fuska a ɗaure ya ce
“Bamu gina wannan kamfanin domin masoyaba, idan zaku yi soyayyarku sai ku yi ta a can waje nan kam domin aiki muka ɗaukeku dan haka bama buƙatar ganin wani abu daya alaƙancin soyayya a nan. Ku wuce gurin aikinku”
Kallona Bilal ya yi ya sakar min murmushi.
“Sorry Nawancy zan kira ki”
“Okay Dear I love you”
“I love you too”
ya mayarmin da martani sannan ya juya ya koma ciki. Ina kallon yadda Jibril ya ɗauke kai ya haɗe yawu da ƙarfi, ya saka hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma ya jimƙeshi sosai.
“Wuce kije office”
“Ba zanyi aikin ba”
Na bashi amsa kai tsaye, sai ya ɗaga kafaɗunaa alamar ko a ajikinsa. Ni kuma na kama hanyar fita daga harabar kamfanin.
Ina cikin Napep kira ya shigo wayata da fari na ɗaukar Jibril duk kasancewar baƙuwar number ce, hakan yasa na ƙi ɗauka, sai dai har na isa gida ba a daina kiran ba da zarar ta tsinke sai a sake kira ni kuma na ƙi na ɗaga. Ko da na shigo Inna na wankin tufafinta na sakawa, da sauri na cire Hijabina na aje na tsuma hannayena cikin wanki ina faɗin ta cire nata.
“Amman dai yau ma kin yi saurin dawowa”
“Na gama aikin ne da wuri”
“Bayan fitarki Ɗansandan nan ya zo be tararda ke ba ya ce zai sake dawowa”
“Ya yi wata magana ne?”
“Cewa Ya yi suna nan suna cigaba da bincike amman yana son ganawa da ke, ya kuma tambayeni akan yadda muka tararda Babanku lokacin da muka je duba shi”
“Uhmm su dai suka sani”
“Wayarki tana ƙara”
“Barta a can kiran bashi da muhimmanci”
Na faɗa ina ɗauraye kayan da ta fara wankewa, a hankali na ji ta kira sunana.
“Nawwara? Kwana biyu nan kin chanja kamar akwai abunda ya ke damunki, ki daina barin damuwa a ranki ki riƙa sanar da ni abunda ya kamata na sani tun wuri”
Na tsayar da abunda na ke na kalleta.
“Babu komai Inna, kawai ina tunanin Noor ne da makomarsa”
“Makomar Noor tana hannun Allah da kuma shi kansa, ki daina damuwa da matsalarsa idan ya girma zai nemi mahaifinsa da kansa ko kuma shi mahaifin nasa ya nemeshi, amman ki daina damuwa arzikinki Noor na mijine ba mace ba”
“Amman ni Inna ina ganin kamar ba zan iya ƙyale Noor yaje gurin mahaifinsa ba, bayan wulaƙancin da ya masa ya yi min sai kuma ace na yarda na bada ɗan gaskiya ba zan iya bari Noor ya kusanci wannan mugun mutumen ba”
“Ko da ya gane kuskurensa ya nemi yafiyarsa? Ba a shiga tsakanin ɗa da uba Nawwara yanzu kin ga duk wannan abun Noor be san da shi ba aiko abun farincikin ki idan har yau Allah ya kawo babansa ya nemi ɗansa da kansa”
Idona ya cika da ƙwalla.
“Amman Inna kamar akwai ƙwaruwa a ciki, ku kuka raini yaron nan sai kuma a ɗauka a miƙawa uban bayan uban be san darajarsa? Gaskiya ni ba zan iya yafe masa ba”
“Ban ce ki yafe masa ba kuma ban ce karki yafe masa ba, amman bashi ɗansa kan dole ne indai har ya buƙaci haka, yara su tashi a gidan iyayensu maza yafi daraja da ƙima fiye da iyaye mata, ke kanki zaki fi jindaɗi na san ba zaki so Noor ya yi agolanci ba, saboda ba ko wane uba ne yake son a kawo masa ɗan wani a gida ba, ba duk miji ba ne zai so ki ya so ƴaƴanki, ni kuma ba burina ki yi ta zama a gida ba bana da natsuwa Nawwara har sai kinyi aure kin zauna ɗakin mijinki”
“Amman ai be zo karɓan ɗansa ba kwata-kwata be taɓa sakashi a ido ba, kuma irin wannan mutumen kike goyon bayan na bashi ɗansa?”
Na faɗa ina kuka, ji nake kamar da gaske rabani za'ayi da ɗana.
“Misali ne kawai na ke baki, ba wai na tabbatar zai zo ba ne, amman zuwansa yana da muhimmanci Nawwara domin zai wanke zargin da mutane suke miki, kuma Noor zai san waye ainahin ubansa na gaskiya”
“Ni gaskiya zan maida Noor gurin Gwaggonsa”
“Wace Gwaggonsa kuma? Zumuntar uwa suka haɗa ko ta uba da zaki ɗauki yaro ki kai mata saboda kawai kin auri yayanta? Faɗa min abunda kike ɓoyewa Nawwara ko shine yake kiranki?”
“Ni ma ban sani ba, amman Inna Noor zai iya rayuwa ko babu babansa a kusa da shi ko da ma ace Ubansa ya mutu”
“Allah ya kyau”
“Amin”
Na amsa ina kuka sosai har da mazina. Ban gama wankin ba sai da aka yi azahar, a lokacin su Sakina suka dawo makaranta, Noor da ciwo a ƙafarsa wai yaje buga Boll ya buge da dutse har jini ya fita.
A ranar ba tare da shi suka je Islamiya ba saboda ciwon ƙafan, da suka dawo ne suke labarta mana wai yau sun yi babban baƙo a makarantar su har ya saka gasar karatun sirratul nabiy wacce ta yi ta ɗaya za a bata gida ta biyu kuɗi dubu ɗari biyar ta uku kuma dubu ɗari biyu da hansin, kuma su uku kawai aka zaɓa Sakina sai wasu ƙawayenta biyu.
Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta har tana addu'ar Allah yasa Sakina ta ci, ya yinda ni kuma na ke ta tunanin kamar ba gasar Allah da Annabi ba ce.
JIBRIL POV.
Shi kansa ya san ya cancanci a yaba masa akan namijin ƙoƙarin da ya yi na ɗauriyar sauraren kalma mai tsada da Nawwara ta furtawa Bilal. Sai dai tun daga lokacin baya jin sukuni har yanzu, kalmar kawai yake ta ji a kunnensa tana masa yawo kamar wanda zai haddace sautinta.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Shine abunda ya fi furtawa a duk lokacin da yaji abun ya haye masa zuciya. Safa da marwa yake ta yi a ɗakin ya kasa natuwa guri ɗaya.
“Am so so sorry Naj am so so sorry please forgive me”
Ya furta yana janye hannun rigarsa sai ga sunanta shimfiɗe a ɗamtsensa da tattoo, shafa gurin ya shigayi ya lumshe ido sai ga hawaye.
“I love you so much bana son na zama wani kalar mutum Ya Allah help me”
Zaunawa ya yi bakin gado yana ta tunanin abunda zai fissheshi, can ya miƙe tsaye ya saka hannunsa ɗaya ya saka aljihu ya fiddo wayarsa ya danna number Nawwara, haka ya jera mata kira biyar bata ɗaga ba sai ya sake kira na shida ya bar wayar saman madubi ya fita zuwa kitchen ɗan haka wa ƙansa tea.
“Hello Momina tana banɗaki idan ta fito zan faɗa mata”
Noor ne yake maganar sannan ya katse kiran jin ba a amsa masa ba, a daidai lokacin Jibril ya dawo ɗakin ɗauke da kofin tea, wayar ya sake ɗauka ya duba sai ya ga anyi picking, da sauri ya sake kira sai aka kashe ya sake kira aka sake kashewa sai kawai ya yanke shawarar aika mata da saƙon karta kwana wato sms.
Da kansa ya tsara rabutun ya tura mata sannan ya jefar da wayar ya miƙe tsaye ya nufi window yana ta kurɓa tea ɗin zuciyarsa na mugun zafi, ji ya yi ba zai iya jurewa ya aje kofin ya nufi wani ɗakin, da shigarsa ya ɗauko wani akwati ya buɗe ya ɗauki ƙwanƙwaƙo ƙarami ya buɗe sai ga cocaine cikin wata farar leda da sauri ya ɓasge ledar ya zuba garin a hannu yana shaƙa kamar ba gobe.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee*
3⃣8⃣
MUSTAPHA POV.
Be taɓa tattabar da cewa yana son Nawwara ba sai yanzu, wani irin abun yake jin yana dibarsa masar misaltuwa, kalamar da ta furta ga waninsa na masoyin da ta kira Bilal yake jin kamar ace shi ne.
Kai tsaye ya wuce part ɗinsa sai ya kwanta rairai ƙasan carpet ya lumshe idonsa, babu abunda yake tunani sai halin rayuwar da ya jefa kansa, da ace be kasance mazina ci ba da babu abunda zai hana Nawwara ta so shi, tunani yake abunda zai faɗawa Allah idan har ya mutu a yau ba tare da ya tuba, son nawwara yasan jarabawace Allah ya ɗoro masa gashi tana da ɗawainiya da shi ta hanashi sukuniina ga ya mutu? Tabbas zai yi ƙoƙarin juye rashin Nawwara amman azabar Allah fa zai iya jureta? Wacan azabar da za'ayi ma mazinata ba da irin wannan jarabawar ba ce da wuta mai kamar kunu za a ƙona fatarsa bayan azabar da za a gada masa cikin ƙabari.
Buɗe ido ya yi sai ya ɗaga hannunsa sama yana kallon farar fatar hannunsa, sai ga hawaye sun gangaro daga idanuwa zuwa gefen kuncinsa, unƙurawa ya yi da zimmar tashi zuwa alwala ya yi sallah ya ƙara nemi yafiyar Ubangijinsa, sai dai hango Mahaifiyarsa da yayi jikin ƙofa tana kallonsa tana hawaye yasa shi yin zaune tana share nasa hawayen.
Ƙarasowa ta yi kusa da shi ta zauna kana ta riƙa hannunsa tana kallon fuskar ɗanta cike da tausayinsa.
“Son kuka kake yi?”
Ya yi shiru be ce komai ba.
“Zan je na nema maka yafiyarta, in har hakan zai faranta maka rai, damuwarka damuwata ce a duniyar nan bana da wani farinciki sai naka, amman ina son ka sani ba kai ne ka kashe yarinyar nan ba”
“Ba ni na kasheta ba Mom na sani, amman ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sannan Allah ya jarabeni da abunda ban taɓa tsamani ba, son yayarta, kuma kun kasa fahimtar hakan balle ku goya min baya”
“Na yi magana da mahaifinka zamu nema maka yafiyar Nawwara, da kuma aurenta matuƙar hakan zai kwantar maka da hankali”
Ya yi saurin kallonta kamar be yarda ba.
“Mom da gaske?”
“Kai kaɗai na ke da a duniyar idan ban faranta maka ba wa zan farantawa? Bana son na rasa ka”
Ya kwantar da kansa jikinta yana murmushi tare da sauke ajiyar zuciya.
“Thank you so much Mom i love you”
“Love you more”
Ta faɗa tana hawaye, har ga Allah ba dan tana son nawwara zata nema masa ita ba sai dan kawai ɗanta ya samu salama hankalinsa ya kwanta, amman ita har gobe gani take ɗanta be dace da nata kamar Nawwara ba.
Sun daɗe a haka sannan ta sake shi ta fita shi kuma ya shiga banɗaku dake falon ya wanke fuskarsa ya canja Jalabiyar da ke jikinsa ya zuwa wata jalabiyar black sannan ya fito a compound ya nufi gurin da motarsa take ya shiga horn ɗaya mai gadin ya buɗe masa gate ya ɗauki hanyar gidansu Jidda.
Tun kamin ya ƙarasa ya kirata ya faɗa mata ta fito gashi ƙofar gida, sam ba zaka ganshi a yanzu ka ce mutumen ɗazu ne ba, farinciki ya mamaye masa zuciya ji yake kamar da Momy taje ta bawa Nawwara haƙuri haƙura zata yi ta kulashi.
Yana zaune cikin motar har Jidda ta fito sanye da Hijab tana tafiya kamar marar laƙƙa, jinginawa ta yi jikin motar yana miƙa masa gaisuwa shi kuma sai ya kashe motar ya fito yana murmushi.
Gabanta ya faɗi zuciyarta ta fara bata wani tunani na daban kar dai ya cutar da ƙawarta, mutumen da tasan yana cikin damuwa yanzu kuma har da murmushi a fuskarsa.
“Naje na yi magana da Nawwara amman har yanzu bata fahinta ba, har na faɗa mata maganar da be kamata ba, amman na san nan gaba zata gane kuma zata yafe maka ni dai abunda na ke fata karka cutar da ita dan Allah”
Ya sake yin murmushi yana kallonta fuskarsa da annuri.
“Zan iya cutar da kaina ban cutar da Nawwara ba, da kin san yadda na ke sonta da baki min wannan zargin ba, amman na san duk mutumen da yasan wanene dole zai zargeni, faruncikin da kika gani a fuskata na zo ne na faɗa min cewar Mom ta yarda har ma ta ce zata taimaka min wajen neman yafiyar Nawwara”
“Wow amman na yi farinciki, Allah ya shiga cikin lamarin kuma ya sa ta kula ka”
“Amin nima fatana nan”
Ya faɗa yana kallon hawayen da suka zubo mata, wanda hakan yasa shi wani tunanin na daban.
“Hawaye kike?”
“Ni?”
Ta yi saurin kai hannu ta share hawayen, da alama bata san sun zubo mata ba.
“Kawai ina farinciki ne”
Ya mata murmushi as respond ba dan ya gamsu hawayen nata na farinciki bane, ita kanta bata san hawayen mi take ba, iya abunda ta sani zuciyarta na yaudararta ne da son cuta mata abunda ta san ba zai taɓa yayuwa ba.
‘i'm very stupid taya zan so mutunen da ke son ƙawata?’
A fili kuma sai ta kalli Mustapha ta ce
“Zan shiga ciki”
Nan ma kai ya ɗaga mata yana murmushi da iya fatar baki kawai ya tsaya masa. Har ta juya sai ya kirata.
“Jidda...”
Ta juyo tana kallonsa
“Thank you”
“Anything for Nawwara”
Sai da ta shiga gida sannan ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa na raya masa wani abu da baya son kawowa akansa, he's happy at first amman yanzu sai ya nemi farincikin ya rasa tunanin hawayen da Jidda take ya tsaya masa a rai.
Ko da ya isa gida part ɗin Mom ya fara shiga sai dai be sameta ba saboda bata gidan, Ikram ce kawai a falon tana game, yana shigowa hankalinta ya dawo kansa.
“Mom taje zata yi magana da Nawwara abunda ka daɗe kana jira amman kuma sai naga kamar baka farinciki”
Ya kalleta irin kallon nan na sai yanzu ya lura da maganar da take.
“Ofcourse am happy i was just thinking of something else”
“Like?”
Sai yayi murmushin da ya bayyana haƙoransa ya miƙe ya shiga kitchen yana faɗin
“Manta kawai ba wani abu bane mai muhimmaci”
Freezer ya buɗe ya ɗauko gorar ruwa ya kai a bakinsa ya sha sai kuma ya nufi gurin window yana ta tunani.
“Impossible”
Ya sake cika bakinsa da ruwa, sai kuma ya yi murmushi yana sauke ajiyar zuciya.
“I love you so much”
Ya daɗe a kitchen ɗin sai da yaji motsin shigowar Mom sannan ya juyo ya fito riƙe da gorar ruwan ya nufo falo.
“Mom ya kuka yi?”
Ya tambaya tun kamin ta cire mayafin da ke kanta, sai dai bata bashi amsa ba sai da ta zauna saman kujera fuskarta da murmushi.
“Sun ce ba zasu yafe ba”
“You must be joking Mom”
“Ka ci gidanku, ni zan maka wasa”
Ya zauna kusa da ita yana kallon murmushin da ke fuskarta.
“Na yi magana da su kuma sun ce sun yafe maka, baka ga yadda mahaifiyarta ta tarbeni ba kamar daman can babu komai”
“Da gaske? Amman Nawwara fa?”
Ta ɗanyi shiru sannan ta ce
“Ita ma ta yafe maka har ma tace a gaisheka”
“Mom da gaske”
“Sai kaje ka tambaya idan baka yarda ba”
Wani irin tsalle ya yi ya dare kamar mahaukaci.
“Mom i love you so much”
Mom ma tana farinciki ganin farincikin ɗanta, cikin zumuɗi ya fice daga falon ya nufi part ɗinsa. A ranar kasa bachi ya yi saboda farinciki, sai ya kwana yana istigifari da hamdala ga Ubangijinsa, a zatonsa da gaske Nawwara ta yafe masa har ma ta miƙo gaisuwar gunsa.
Around eight o'clock in the morning Mustapha ya fito part ɗinsa zuwa part ɗin Mom, sai dai hango motar abokinsa da ya yi yasa shi tsayawa baƙin ƙofar yana jiran ya ƙaraso.
NAWWARA POV.
Cikin rashin daɗin rai na shiga gida, Inna ma ta lura da haka sai dai bata cemin komai a zatonta tsakanina da Bilal ne wani abu ya faru. Misalin takwas da rabi na dare muka ji sallama a ƙofar gida, Inna ce ta amsa ni kuna idona na kan Noor take ta faman game baya gajiya. Sarai muryar Hajiya mahaifiyar Mustapha a ɗaki kunnena a sallamarsa ta biyu, gabana ya faɗi ba dan tsoro ba sai dan tunanin abunda yake tafe da ita. Inna ce ta unƙura ta fita sai kuma ta dawo ta ɗauki tabarma ta sake fita, sama sama nake jiyo firar da suke da dukan alamu yafiya take nemawa ɗanta abun mamaki har da su wa'azi da nuna ƙaddara, zuwa can kuma dai na ji Inna ta kirani daga inda na ke na amsa mata sannan ya miƙe na fita.
Hajiyar ce zaune saman tabarma yayinda Inna take zaune saman kujerar mata ta tsakar gida.
“Nawwara ce”
Hajiyar ta faɗa tare da kunna fitilar wayarta ta haska fuskata.
“Ina wuni?”
“Lafiya ƙalau, ayi ta haƙuri kinji haka abubuwan duniya suke zuwa”
“Allah ya bamu haƙuri”
Daga haka ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsaye na dawo ɗaki. Bata ɗauki tsawon lokaci ba tayi ma Inna sallama ta fice. Inna kamar jira take tana shigowa cikin ɗaki ta hau ni da masifa.
“Wannan halin ba na ki ba ne Nawwara ba irin wannan tarbiyar muka baki ba, yafiya da afuwa ga wanda ya yi maka ba daidai shu aka fi ga musulmi, duk yadda zaki so Habiba ko ki nuna baƙincikinki akan mutuwarta be kai ni uwarta, tun da har na yafe kema ya cancancanta ki yafe, Ƙaddarace ni da ke duk ba mu wuce faɗawa a cikinta ba, yanzu da ace ɗan uwanki ne ya faɗa a wannan halin ko kuma ɗan ki Noor yaje yana neman yafiyar wata ba ta yafe masa ba zaki jidaɗi? Komai zaka yi ka riƙa kwatantawa da kanka”
Tun da take maganar na ke hawaye, Inna ta min fahimta baibai, ta kasa gane irin zafin da ɓakincikin rashin yar'uwata da nake, ko da Habiba tana raye dole na ƙyamaci Mustapha saboda ya yaga mata rigar mutunci, tana ɗora min laifi akan Jibril saboda tana ganin kamar na zufafa da yawa, ni kou na san irin zafin da na ke ji idan na tuna wulaƙancin da ya yi min ya yi min ƙazafin zina a gaban iyayensa da iyayana yasa mutane unguwa suka kira ɗa na da shege ni kuma aka kira da karuwa, irin waɗannan mutanen ne take ganin na zufafa ƙiyayyata a garesu?
“Ki yi haƙuri Inna, zan yi iya abunda zan iya na danne zuciya daga abunda take ji, dan Allah ki yi haƙuri kuma ki roƙa min Allah ya sassauta min abunda nake ji”
Na faɗa ina ta kuka kamar zan haɗiye zuciya na mutu, sai Inna ta zauna kusa da ni ta dafani tana lallashina.
Sama sama na samu bachi a daren ranar saboda kuka da na kwana ina yi ga kuma tunani ƴar uwata da ya dawo min sabo. Washe gari da wuri na farko bayan na gama raka'atayal fajir sai na jira aka tayar da sallah na masallaccin da ke kusa da mu bayan na gama na karanta azkar na safe, da ayatul kursiyu na fara
A 'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem. Allaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwal-Hayyul-Qayyoom, laa ta'khuthuhu sinatun wa laa nawm, lahu maa fis-samaawaati wa maa fil-'ardh, man thai-lathee yashfa'u 'indahu 'illaa bi'ithnih, ya'lamu maa bayna 'aydeehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay'im-min 'ilmihi 'illaa bimaa shaa'a, wasi'a kursiyyuhus samaawaati wal'ardh, wa laa ya'ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal- 'Aliyyul- 'Adheem.
sannan ɗora da ƙula'uzai
Allahu ahad, Allahu assamad, Lam yalid walam yoolad, Walam yakun lahu kufuwan ahad.
Qul a'aoothu birabbi alfalaq, Min sharri ma khalaq, Wamin sharri ghasiqin ithawaqab, Wamin sharri annaffathatifee al'uqad, Wamin sharri hasidin itha hasad.
Qul a'aoothu birabbi annas, Maliki annas, Min sharri alwaswasi alkhannas, Allathee yuwaswisu fee sudoori annas, Mina aljinnati wannas.
Sai kuma na karanta hasbiya ƙara bakwai
Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa
Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem
Sai kuma na karanta
Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem.
Ƙafa uku.
A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa
Sau uku
Waɗannan addu'o'i ne na neman tsari matuƙar ka karantasu babu abunda zai same ka daga iska har tsafi har ma da wasu ƙwari masu cutarwa, bayan na gama na ɗora da azkar ɗin godiya ga Allah waɗanda ake son musulmi ya karanta safe da yamma. Sannan na rufe da shugabar istigifari wato
Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta.
Yana na gama na yi salatin annabi ɗari istigari ba ɗari, sannan na yi hasbiyalahu sau ɗari huɗu da hansi, wacce ake karantawa a duk lokacin da mutane yake cikin matsala na halin rayuwa ko neman mafita, kamar neman aure warwarewa al'amura duk ka lamuncin karantawa zaka samu mafita cikin gaggawa.
Ko da na fito har Sakina ta dama kamu, Inna kuma ta aiki Jamila da Noor su siyo ƙosai da suga, bayan sun dawo muka sha kunun har Inna sannan na kama kan Noor na yi mas addu'a irin wacce Annabi yake yi ma jikokinsa Hasan da Husaini
U'eethukumaa bikalimaatil-laahit-taammati min kulli shaytaanin wa haammatin, wa min kulli 'aynin laammatin.
Bayan na gama da Noor na karantawa Jamila sannan na suka kama hanyar makaranta tare da Sakina. Ni kuma na tashi na shirya cikin wata atamfar roba na saka Hijab ɗina mai kama da atamfata, sannan na zo yi ma Inna sallama da karɓar kuɗin Napep.
“Inna zan tafi aikin”
“Allah ya tsare Nawwara Allah ya miki albarka, ban miki faɗa jiya dan wani abun ba sai dan ki gyara”
Ta faɗa tana miƙo min ɗari biyu.
“Ko babu komai kika min faɗa ba zanga laifinki ke uwace kina da damar ki yi duk yadda kike so da ni, kuma abunda kika min faɗa akai kina da gaskiya, ni kaina na san ina da buƙatar ganin na canja ta yadda zan cigaba da rayuwa na manta komai, ni dai fatana ki kasance mai min addua da kuma haƙuri da hali na miki alƙwarin zan canja”
“Addu'a ai wajibi ce ga dukan uwa ta yi ma ƴaƴanta, Allah ya miki albarka ya baki miji na gari wanda zaki ji daɗin zama mai son ki tsakani da Allah”
“Amin Inna”
Na faɗa ƙasan zuciyata na ta kira min Bilal, tun jiya be kirani ba kuma be dawo ba ni kuma ban kira ba.
Sai da na fito daga gidan sannan na soma kiran Bilal amman wayarsa a kashe, hakan yasa ni jin babu daɗi zuciyata na raya min kamar fushi yake da ni, daman na san dole sai ya zargi wani abu ganina tare da Mustapha.
Na yi sa'ar samun napep da wuri amman sai da ya sauke mutun biyu sannan ya ƙarasa da ni inda zai kai ni, koda na isa tara saura kwata tunda na doshi kamfanin zuciyata ta soma rayamin wasu abubuwan sai sai tunawa da maganganun Inna yasa na kawar da komai na nutsa kai cikin kamfanin, na yi mamakin yadda kowa yake kallona kamar wace suka ga baƙuwar fuska, wataƙila an faɗa musu wani abun ne akai na ko kuma dan na yi latti suke kallona oho, ban damu da cire Hijabina ba a ganina yanzu ai an canja min aiki dan haka bana buƙatar cire Hijabi duk kuwa da kasancewar ban taɓa ganin kowa da Hijabi ba a kamfanin.
Har na doshi lifter tunani na ke irin kallon da Jibril zai min da kuma irin wanda zan yi masa idan har na yi aiki a gurin. Ina dosar office ɗinsa gabana ya shiga faɗuwa, ba faɗuwar tsoro ba ko fargaba ba faɗuwa irin ta maƙiyi zai yi arba da maƙiyinsa.
Kamar wacan zuwan nawa na farko haka na yi saka buɗe min, yau ma sai da aka tantance ni a cikin ɗan ƙaramin gilashin nan mai bayyana komai na jikin mutun sannan aka bani damar shiga Office ɗin, ban ji ya ce na aje wayata da ƴar ƙaramar jikar da ke hannuna ba, ni kuma ban aje ba na shiga da abu ta, shi ɗin ne dai mutumen da na taɓa tararwa wacan karon. Tun kamin na yi magana ya rigani.
“Please go in”
Ya doshi ƙofar da ya nuna min gabana na ƙara faɗuwa, ajiyar zuciya na sauke sannan na kai hannu ya tura ƙofar, ba tare da na waigo ba na maida ƙofar na rufe ina kallon bayansa, kasancewar ya bani bayana ne domin shi yana tsaye ne jikin window ya maido hannayensa baya yana kallon waje.
Har yanzu akwai tattoo ɗin taurari a bayansa, mamaki ya kamani sosai ganin sunana rubuce cikin style ɗin wasu harufa tattoo a hannunsa, nasan be san da shigowata ba ko da yake yaji an buɗe ƙofa, ni kuma na gagara kiran sunansa sai kawai na ce
“Excuse me”
Da sauri ya juyo ya kalleni, irin kallon nan na mamaki sannan ya yi hanzarin warware hannun rigarsa ya nufi ƙasaitacciyar kujerarsa ya zauna.
“Kin zo latti, ba a faɗa miki 8am zaki riƙa zuwa ba?”
Na yi shiru ban amsa masa ba. Sai ya soma kallona daga sama zuwa ƙasa.
“Ba a saka mana Hijabi a nan next time ki san irin tufafin da zaki saka”
“Ba za'a saka muku Hijab ba saboda ku ba musulmai ba ne?”
Ya yi murmushin gefen fuska sai ya taso daga inda yake ya doso ni yana faɗin.
“Aiki muke a nan ba addini ba”
“Da wannan aƙidar ka cuci kanka, kai kana ganin kamar babu ruwan addini ko Allah a cikin abunda ya shafi aikinka ko rayuwarka ko? Kana da mummunar aƙida Jibril”
“Ko?”
Ya tambaya yana ta matsowa kusa da ni ni kuma ina matsawa baya, har sai da na kai jikin ginin ɗaki, sosai ya matse ni yana kallon fuskata idanuwa cikin nasa idon, har na buɗe baki na yi magana sai ya duƙa ya kama zanen atamfata ya murja.
“Me kake ƙoƙarin yi ne?”
Ya miƙe tsaye bakinsa kusa da nawa kamar zai haɗe bakinmu.
“Dirty mind, ni ba ɗan iska ba ne”
Ya faɗa kaɗan kaɗan kamar mai raɗa, sannan juya ya doshi kujerarsa. Hakan ya bani damar lumshe ido na sauke ajiyar zuciya, jin abunda yake faɗa yasa ni buɗe idon ina kallon yadda ya haƙimce saman kujerarsa mai juyawa yana min magana cikin isa.
“Dan me za ki saka min tamfar roba?”
“Ba kai na sakawa ba, kaina na sakawa”
“Miyasa kika yi rejecting kuɗin da aka baki ki siye wasu tufafi?”
“Bana da buƙata, tufafin jikina sun isheni”
“Saka ƙananan tufafi marar daraja na zubarwa kamfanin da ƙima, ya kamata ki san wannan”
Ya faɗa fuskarsa babu alamun dariya, sannan ya danna telephone ɗin da ke kusa da shi ya yi magana da halshen nasara.
“You can go now”
Sannan ya kalleni.
“Tea please”
Tsaye na yi a gurin kamar an dasani, shi kuma ya bawa banza ajiyata yana ta aiki da system ɗin da ke gabansa. Waige-waige ɓa farayi har na hango teburin dake ɗauke da kayan tea na doshi gurin zuciyata na ta raya min maganar ɗazu, wai shi ba ɗan iska ba ne, wato ni ce ƴar iskar ko? Har na haɗa tea ya kawo masa maganar bata daina min yawo a kunne ba.
“Ƙarfe uku zaki tashi aiki, idan kuma har muna da meeting ko aiki da yawa zaki iya kaiwa har dare, kuma a shigo min office haka nan kawai, saboda karki tararda ni cikin wani yanayi, har sai idan ni na kiraki, idan wata magana ce akwai telephone a gurin dannawa kawai zaki yi ki kirani”
Ban ce masa komai ba na juya na fita, zuciyata na mugun ƙuna, anya zan iya jurewa na yi aiki a ƙarƙashin Jibril?
Sai da na ƙarewa office ɗin kallon sannan na zauna a saman kujerar mai juyawa, komai daki daki na bishi ina kallon da dubawa sannan na kula da ƴar danjar da ke ƙara a gefen teburina, sai kuma computer ta soma nuna min mutumen da ke waje, wato Bilal yana riƙe da wasu takardu.
Gabana ya faɗi sosai sai na soma tunani da wace fuskar zan kalli Bilal shi kuma wane irin tunani zai min.?
JIBRIL POV.
He's just can't believe Nawwara tana ƙarƙashinsa a yanzu, wani irin daɗi yake ji yana ta yi ma Allah hamdalla, cike da so da ƙauna yake kurɓa tea da ta haɗa masa yana wani lumshe ido.
Jin ya yi ba zai iya jure jin wannan farincikin shi kaɗai ba, ya ɗauki wayarsa ya danna number Siraj dan labarta masa.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee*
4⃣0⃣
JIBRIL POV.
“Ee kana da ɗa”
Shine kawai abunda Jibril yake son jin ya fito daga bakin Nawwara, wani irin bugawa zuciyarsa take da sauri, ido cikin ido yake kallon Nawwara tsantsar gaskiyarta yake son ganewa, yadda ta saki baki tana kallonsa shi kansa yasan subul da baka ta yi, yadda take numfashi yake karantar da shi irin faɗuwar gaban da ke ranta.
“Kana da ɗa mana ƴaƴama zan ce, ba ka auri Aisha ba ta haifa maka ƴaƴa, na tuna ai tun kamin ka aureta ma ta samu ciki, wanda kake labarwa abokinka farinciki fal a ranka, kuma bayan ita maybe ka ƙara auren wasu matan sun mahaifa maka ƴaƴa ko kuma ka musu cikin shege”
Lumshe ido ya yi ya haɗe yawun dake bakinsa ya dunƙula hannunsa ya matse sosai kamar zai dake, har ga Allah baya jindaɗin kalamanta, duk lokacin da ya tuna rayuwarsa ta baya yana jin babu daɗi ballr kuma ace ita ce da kanta take tuna masa da wannan, hakan na karantar da shi cewar ba zata taɓa yafe masa ba kuma ba zata manta ba.
“Ina cikin da na barki da shi?”
Ya faɗa yayinda da buɗe idonsa da suka rine suka yi ja sosai.
“Cikin da ka kace ba naka ba ne? Ai na zubar domin ba zan iya ɗaukar shege a cikina ba”
“Ba zaki iya zubarwa ba, ba zaki iya kashe rai ba ko da kuwa ɗan shegen ne da gaske”
Kallonsa ta yi sai ta yi murmushi.
“Ashe kai da kanka ka san ba ɗan shege na ɗauka a cikina ba, amman ka ce ba naka ba ne ka haɗa hotona da hoton wani namiji wanda ban taɓa sanin inda ya fito ba, saboda kawai kana neman rabuwa da ni? Da na dawo da ciki sai suka kira da karuwa wannan dalili yasa na zubar da cikin”
Ta faɗa hawaye na fitowa daga idonta fuskarta kuma ɗauke da murmushi.
Wani irin ƙuna yake ji a cikin ransa, zuciyarsa zafi take kamar an kunna masa wuta, yana jin rashin kyautawa a duk lokacin da ya tuna abunda ya aikata mata, tabbas yanzu ya yarda akwai wawanci, shashanci a tare da shi, duƙursawa ya yi ƙasan guiwoyinsa ya kama Hijabinta sa gashi yana hawaye.
“Dan Allah Nawwara ki yi haƙuri dan Allah ki yafe min”
“Daman na faɗa, saboda ka riƙa neman yafiyata yasa ka cilasta min aiki a tare da kai”
“Ba dan haka ba ne Nawwara, saboda na samu kusanci da ke, ina sonki sosai Nawwara”
“Ni kuma bana son ka, bana kaunarka Jibril”
“Na sani”
Ya fada yana hade maganarta ciki da dacin rai. Zaunawa ta yi shi kuma ya mike tsaye na koma office dinsa, sam be gamsu ba shi da tsakaninsa da Nawwara ba, tabbas ya bar ta da ciki kuma ya san ba zata iya zubar da cikin ba.
‘Ta haife shi, idan har babu haihuwa tsakamina da ita mi zai sa ta yi wannan maganar?’
Shine abunda zuciyarsa take ta raya masa, wayarsa ya dauka ya kira Siraj bugu biyu Siraj ya yi picking.
“Siraj ina son kasa a bincika min duk wani abu da ya shafi Nawwara, akwai da a tsakanina da ita Siraj kasa a abincika min”
“Okay”
Daga haka ya kashe wayar ya kira Abbah, sai da ta dade tana ringing sannan ya dauka yana kiran sunansa.
“Hello”
“Jibril”
“Abbah ina wuni”
“Lafiya kalau ya aiki?”
“Al-hamdilillah, Abbah akwai da tsakanina da Nawwara”
“Waya fada maka?”
“Ita ta yi subul da baka”
“Kaje gidansu ko? Bana fada maka karka je ba”
“Ban je ba, Abbah a nan kamfanin take aiki”
“How when?”
Ya kwashe komai ya fada ma Abbah amman be fada masa zance ya cilas mata aiki a tare da shi ba. Abbah ya yi shiru kamar mai tunanin abunda zai ce.
“Abbah we're meant to be”
“Kana son ta ka saketa? Bana son ka zama cikin irin mazan nan da ake fada Jibril ni yanzu ko wani aure ban yarda ka kara yi ba sai ka gane kuskurenka”
“Wallahi Allah Abbah na canja zan zauna da Nawwara zama na tsakani da Allah ba zan taba sakinta ba, Abbah ita kadai ce take so na tsakani da Allah”
“No ba yanzu, kuma na fada maka karka kuskura taka kafarka gidan nan”
“Tau Abbah ba zan yi ba, amman da Mahaifiyata tana da rai da ta roka min kai ka amince, rashinta ne yasa na rasa komai, ba ni da mata ba ni da ɗa sai kai kadai kai kuma ka kasa fahimta ta”
Yana fadar haka ya kashe wayar ya aje saman table, sai ya dora hannayensa saman table din ya dafe kansa ya dinga rusar kuka kamar karamin yaro.
Kuka yake sosai kuka ina zai saka kanshi, kuka neman mafita, be san mahaifiyarsa ba domin be tashi tare da ita ba, amman yana jin zafin rashinta kamar yanzu ta mutu ta barshi, ji yake ina ma tana raye da yanzu ta roka masa Nawwara ta yafe masa, ta shiga cikin lamarinsa ta gyara masa komai, be taba jin zafin rashin mahaifiya ba kamar yau.
Hannunsa yasa ya janyo aljihun table din da take zaune ya dauko hoton wata matashiyar mata mai kama da shi yana ta kallonta yana kuka kamar mace.
Kuka ya yi sosai har sai da ya soma jin kamar jiri yana dibarsa sannan ya tashi ya shiga bathroom ya wanke fuska ya dawo ya dauki ruwan freezer ya sha, sai ya dora gorar saman freezer ya nufi kofar fita.
Ko da ya fito Nawwara na zaune tana duba abubuwan da suke cikin computer, ya samu thirty seconds yana kallonta mugun burgeshi take gani yake a duk duniya babu wata mace da ta kaita daraja da kima da kuma kyau, ji ya yi kamar yaje ya rumgume kamkam a kirji, sai dai yasan ba shi da wannan damar. Karasa ya yi inda take yana kallonta da manyan idanuwansa masu kamar madara kamar zai cinyeta.
“Lokacin cin abinci ya yi, a nan zaki ci ko restaurant zamu je?”
“Ka ce min idan uku ta yi zan iya zuwa gida idan har babu aiki da yawa, kuma na ga yanzu uku sauran kwata”
Ta fada ba tare da ta kalleshi ba dan gaba daya ta tattara hankalinta ya maida kan computer.
“Ee amman a ka'ida karfe biyu da rabi zuwa uku ma'aikata suke zuwa cin abincin rana, taso muje restaurant”
Mike ta yi tsaye yana gaba tana biye har suka sauko kasa gaba daya, tare suke daga kafa kuma su aje tare har suka isa restaurant din dake cikin kamfanin, wani abun da ya bawa Nawwara mamaki suna shiga sai duk wanda ke gurin ya tashi ya fita, aka barsu su kadai daga ita sai shi. Karasa ya yi can guri wani teble wanda shi kadai yake zama akansa ya zauna ita ma ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa.
Waiter ne ya zo da sauri yana tambayar abunda za a kawo musu.
“Fried rice and chicken soup”
“And drink?”
“Fanta”
Ya juyo gurin Jibril.
“And you Sir”
A hankali ya juyo ya kalleshi ba dan yasan a abunda yake tambaya ba sai a lokacin ya kula da shi domin gaba daya hankalinsa yana gurin Nawwara.
“And you Sir”
Ya sake maimatawa ganin kamar be ji abunda ya ce ba.
“Just water”
Nawwara ta masa wani kallo
“Ni ladai zan ci abincin kenan?”
“No”
Ya yi saurin amsa mata sannan ya sake kallon mutumen ya ce
“White rice and pepper soup”
“Drink?”
“Lemun juice”
“Okay”
Ya juya da sauri ya koma inda ya fito. Cikin yan seconds sai ga abincin an kawo musu, Nawwara ce ta fara dan ta nuna masa ita fa cin abincin kawai ya kawota ba komai ba, shi kan kasa taba abincin ya yi ya tsura mata ido kamar mai kirga lomomin da take, zuwa can ta dago ta kalleshi, sai ya yi saurin daukar spoon ya soma wasa da abinci dan har ga Allah baya jin cin abincin, kawai saboda ita ta samu ta ci ne yasa shi zuwa ko ba komai hakan zai kara masa kusanci da ita, yadda take cin abinci mugun burgeshi take ya tattara hankalinsa gaba daya ya mika mata, har ta gama cin abinci be yi ko da loma daya ba.
Wani abun da ya ba waiters din mamaki biya bill din abunda be taba yi ba, idan ba ya ci abinci a guri sai dai pa dinsa ya biya ko da kuwa shi da wani suka ci, amman yau shi ya biya da kansa sannan suka fita.
A lifter ma kallota yake ta yi zuciyarsa na mugun fisgarshi kamar zata fasa kirjinsa ta fito.
“Can i hug you?”
Ta juyo da sauri ta kalleshi kamar yadda yake kallonta, idanuwansa sun yi fari kal har wani ruwa ya kwanta a ciki.
“Baka da hankali Jibril, ka rumgume ni muharramarka ce? Ko dai ka dauka kamar Aisha na ke ne? Gaskiya kana bukatar komawa makaranta ka fahimci addini sosai”
“Am sorry”
Ya furta yana dauke idonsa daga kallonta so zai samu sauki zuciya, tare da danke hannunsa ya matse sosai.
Suna shiga Office ya wuce Office dinsa ya zauna saman kujera ya dora hannunsa saman goshinsa ya rufe ido yana sauraren bugun zuciyarsa.
Bayan an mintuna Nawwara ta shigo Office din rike da jakarta.
“Ni zan wuce”
Bude ido ya yi ya kalleta sai ya dauki wayarsa ya kira direbansa, yana yin picking.
“Get ready”
Yana fadar haka ya kashe wayar, da kansa ya dauki akwatinsa ya saka laptop dinsa da tardunsa sannan ya mika mata jikar.
“Aje saman teble”
Sai da ya aje sannan ta dauka suka.
“Ni fa gida zanje fa naga garin hadari ma ya hadu”
“Na sani a ka'idar kamfanin nan as you are my pa dole ni zan saukeki gida ko kuma direban kamfanin nan”
Ya yi tunanin zata musa masa ne, sai dai shi ba ya yi ba ne dan kawai ya kara kusanci da ita, haka dokar kamfanin take.
Tare suka fito duk mai son kallonsu sai idan sun bada baya sannan ake daga ido a kallesu domin sun san abunda Jibril ya fi tsana shine kallo. Ko da suka fito daga cikin kamfanin har an fara yayyafi motar da Jibril zai shiga kuma tana fake daidai bakin kamfanin, direban na ganinsa ya bude masa gidan baya da sauri yana kara masa umbrella, shi kuma sai ya zagaya ta wacan bangaren ya budewa Nawwara dan baya son ta shiga gaba, abunda ya bawa direban mamaki, ba tare da tunani komai ba ta shiga ta zauna, sai ya maida kofar ya rufe sannan ya zagayo ya shiga direban ya rufe masa, sai ta dora akwatin a tsakiyarsu ta maida hankalinta gurin gilashin motar tana kallon yadda ruwan sama ya soma sauka da karfi.
“Guiwa locos”
Ya fada yana kallonta, sai direban ya fisgi motar kamar ba ruwa sama ake ba, har aka shiga cikin unguwarsu bata juyo ta kalli inda Jibril yake ba, shi kuma idonsa na kanta, a hankali ya kai hannu zai taba hamnunta sai a ya yi dai dai da juyowarta tana fadawa direban inda zai aje ta.
Hakan yasa shi saurin janye hannunsa ya danke ya maida kallonsa gurin gidajen da suke unguwar da yadda mutanen suka fake saboda ruwa.
“Ya isa”
Direban na tsayawa ta bude motar zata fita sai ya yi karaf ya ce
“Akwai ruwa sosai ki dan jira a rage”
“A'a”
“Tahir kara mata lema”
“A'a”
Haka ta bude motar ta saka kafafunta cikin cabon da ke gurin tana tafiya ruwa na dukanta, sai da ya daina hangota sannan ya bude motar ya fita ya zagayo gefen da ta fito yasa hannunsa ya kwashi kasar da ta taka wacce ta fitar da sawon kafarta ya danke a hannunsa sannan ya koma cikin motar.
“Gida”
Kai tsaye direban ya nufi Sama road da shi, a hanyar ta tafiya ce ya fiddo wayarsa ya jira Rabi.
“Zan aiko miki da kudi duk abunda ya kamata ki siye, sai ki ka a addiren da zan turo miki yanzu amman sai kin tambaya saboda ban ga ainahin gidan ba”
Daga haka ya kashe wayar, har suka isa kasar na jinke a hannunsa ji yake kamar Nawwara ce ya rike, suna isa ya fita motar direban na tara masa lemar ya daga masa hannu alamar ya bari.
Falonsa ya shiga da hannu daya ya cire kayan jikinsa faffadan kirjinsa ya bayyana muscle din jikinsa duk suka fito real namiji, sai ga karensa ya zo da gudu yana kada masa bindi, shi kuma be kula shi ba ya nufi wata kofar ya bude ya shiga harabar gidan dake can ciki, kwantawa ya yi saman tile din ya shafa kasar a kirjinsa ya ware hannayensa ya lumshe ido ruwan saman na dukansa.
NAWWARA POV.
Sai da na tabbatar ba zasu hango ni sannan na hada da gudu ina ta tunanin subul da bakan da na yi, da yanzu ya gane ya zanyi kenan? Gaskiya ina da yauta sosai ni mi ya kaini wannan maganar ma. Kamin na isa gida komai nawa ya jike saboda ruwan da ake sosai. Inna ma ta yi mamaki ganina cikin ruwa, a bakin kofa na tsaya na cire tufafina sannan na saka wasu su kuma na rabasu gefen kofa har ruwan ya dauke. Wayana ma ruwa ya shiga ciki ya taba shi sai dai na yi sa'a be yi komai ba.
Saman kujera na zauna sai Noor yanzo kusa da ni ya zauna ya jingina kansa da jikina.
“Momy ki ara min wayarki na yi game”
“A'a kai baka da aiki sai game”
“Momy dan Allah”
Ya fada kamar zai yi kuka, ni kuma na hana shi domin wayar babu carji sosai a ciki, sosai na maida hankalina kan Sakina da ke ta rihazar din sira da zasu yi gasa a kai, Inna kuma ta dauko kur'ane tana karatu.
“Inna ki min addu'ah Allah ya sa na yi ta daya”
Cewar Sakina ganin Inna tana addu'a bayan ta gama karatun kur'anen.
“Yaushe ne ma?”
“Gobe kuma?”
“Eh daman kwana biyu aka bamu ai”
“Allah ya bada sa'a”
Na fada tare da tashi na fita waje dan yi alwalar la'asar. Bayan na gama sallah ne Inna take tambaya ya aikin na amsa mata da Al-hamdilillah, sannan na dauki wayata na kira Bilal sai ta saka min user busy, haka na yi ta har biyar na yamma ta yi amman bata shiga ba, hakan yasa na fahimce cewar na saka numberta a blacklist ne, amman mi na masa har haka ne? Ko dai yana fushi da ni ne?
Sallama muka ji da bakuwar murya, duk kokarin da na yi na rike Noor sai ya ci tura domin tuni ya kai bakin kofa shi da Jamila daman rigangan suke gurin amsa sallama ko leke aga wanene.
“Nawwara na nan?”
Na ji kamar muryar da na sani, hakan yasa na yi wuf na fita waje, Rabi ce tsanye da gown ta dora rigar sanyi sama fuskantar dauke da murmushi kamar kullum, sai dai ba ni take kallo ba Noor take kallo cike da burgewa, hakan yasa na maida shi bayana sai ta kalleni tana cigaba da fadada murmushinta, kamin ya matsa jikin kofar gidanmu ta ce
“Bismillah”
Sai ga wasu maza su biyu suna ta shigowa da kayan abinci da kuma manyan akwatuna guda uku suka dora saman barandar dakin Inna. Ni dai kallo na bisu da su har suka gama ganin ta juya zata fita yasa na ce
“Waya ce a akawo?”
“Ke ma ai kin sani”
“Dan Allah ki koma da kayan nan”
“Ni ba zan iya ba, amman zaki maidawa da kanki”
Inna da ke tsaye bayana ta ce
“Malama jeki abinki mun gode kinji”
“Nima na gode Mama, Handsome boy sai anjima ko”
Noor ya daga mata hannu yana murmushi da ya fitar da dimples dinsa.
“Okay Anti mun gode”
Ji na yi kamar na buge masa baki. Bayan ta fice Inna ta kalleni ta ce.
“Ba a maka alheri ka maida ko ya yake Nawwara, idan ma har kina jin ba zaki iya amfani da abunda ya baki ba, zaki iya kyautarwa, kuma idan har kika cigaba da nuna baki son abun hannunsa ba zaki karba hakan yana nufi har yanzu kina sonsa, amman idan har kika karba kika manta da komai kika nuna masa ba komai hakan zai kidimar da shi, domin zai gane cewa yanzu kina mu'ala ne da shi kawai ba ta so ba”
“Amman ai kamar ina son sa ne idan na karba”
“Ba daga nan take ba”
Sakina taje ta bude akwatin tana duba babu komai a ciki sai tufafi da abaya da kuma gowns, sai atamfa da lace wadanda ba a dinka ba,
“Amman gaskiya ba za a maida wannan kayan ba, ai ba mu muka ce ya kawo ba, mun ci banza”
Cewar Sakina tana gwada wasu tufafin a jikinta.
“Wallahi Anty ko ba zaki aureshi ba ki tatsi banza ko zafi ki rage”
Ni dai ban kulata ba balle banzan zancenta, haka na zauna cikin rashin dadin rai har dare saboda Bilal be kira ni kuma na tura masa sako be maido min da amsa ba.
Bayan sallah isha'i dpo ya zo gidanmu, ya yi wasu tambayoyi ni da Inna sannan na fada mana ya shigar da kara kotu kuma karshen watan nan ne za a fara zaman kotu, hakan ya faranta min rai sai na dan sake zuciyata ta washe.
Washe gari ba mu karya da abunda muka saba karyawa ba, saboda Indomie da aka kawo mana ita Sakina ta dafa suka ci ita da Jamila da Noor shi kan har tsalle yake yana direwa kasa yana jindadi sun ci indomie.
Inna kan kunu ta sha as usual nima shi na sha dan bana son ko warin indomie na ji balle kuma na kalleta har ya kai ni ga ci.
Bayan sun wuce makaranta, ni kuma na soma gyara gidan, sai da na gama sannan naje na samo mai ruwa ya zuba mana jalka shida Inna ta bashi dari da hansi, sai na zuba na shiga wanka.
Ina cikin bandaki na ji sallamar Baba Sulaiman da Baba Dahiru, wato kanen mahaifina da kuma yayansa, sai dai ga dukam alamu ba su kadai suke ba, domin Hayaniya ta yi yawa, ko da na fito Inna ta shimfida musu tabarma suna zaune ciki har da abokin Baba wanda ya sama masa aiki a Abuja da kuma Alhaji Bashir Makama wato mahaifin Jibril da wani dattijo tare da su.
Na ji dadin da Allah yasa na shiga wankan da Hijabi da fitowa ta yi min wuya, karasa na yi na durkusa har kasa na gaishesu, sannan na wuce dakinmu zuciyata cike da maganganu kala kala. Ina cikin saka tufafi Inna ta kira hakan yasa na yi hanzarin saka kayan na saka wani Hijabin na fito na zauna kusa da ita.
“Nawwara kin gane ni”
Na dago na kalli Alhaji Bashir da ya yi maganar sannan na daga masa kai.
“Zuwa na yi na baki hakuri akan abunda muka miki, hakika bamu kyauta ba, na sani amman dan Allah dan darajar iyayenki ki yafe mana, Wallahi har ga Allah Jibril ya canja kuma ya yi nadama, be san na zo nan ba ba shi ya turo ni ba, kuma bana son ya san na zo, na yi niyar yin haka tuntuni amman kunya da nauyinki yasa na kasa yi, yanzu ma sai da na biyo ta bangare Babanninki suka karfafa min guiwa sannan na samu na karaso ki dubi girman Allah ke da mahaifiyarki ku yi hakuri da abunda muka muku”
“Ba fa kai ka yi ba”
Cewar Baba Dahiru, sai ya amsa da
“Ai da na ya yi kamar ni na yi kenan”
Ni dai bance komai ba banda hawaye babu abunda na ke, Inna ce kawai take amsa masa, shi ma sai da su Baba Sulaiman suka saka baki, daga karshe ya yi magana agaisuwar rashin Baba, sai kuma ya tambaya yi Noor.
“Sun tafi makaranta”
“Amman Jibril be san yana da ba ko?”
Kai na daga masa, sai ya soma labarta mana yadda Jibril yake son da da kuma irin halin rayuwar da ya shiga bayan rabuwarmu.
Ya dauki kudi mai yawa ya bawa Baba Sulaiman da Baba Dahiru, sannan ya miko mana bandir din yan dubu daya.
Sannan ya yi mana sallama yana cewa yau ya zo kuma yanzu zai koma daman saboda ni ya zo.
Bayan sun tafi Inna ta zaunar da ni tana ta fada min maganganu akan rayuwa da kuma hakuri, ganin irin kuka da na ke.
“Na hakura Inna amman ni fa ba zan taba komawa ba”
“Babu wanda zai cilas miki komawa, amman ko dan ɗan dake tsakaminku ya kamata ace kun yafi juna”
Tashi na yi na fita na koma dakinmu na zauna na yi kuka sai da na koshi sannan na shirya na fito na yi ma Inna sallama. Gidansu Jidda na nufa da Mamanta muka fara gaisawa sannan na shiga dakinta sai ta juya min baya tana dannar wayar da ke hannunta. Ban damu ba na zauna gefen katifarta na soma mata magana.
“Jiya na yi mafarkinki Jidda, na yi mafarkin Mustapha zai cutar da ke”
Tayi banza da ni kamar bata ji ni ba, ganin hakan yasa na tashi zan fita sai ta kira sunana.
“Nawwara”
Hawaye na gani a idonta.
“Yi hakuri”
Dawowa na yi na zauna sai na dafata na fashe da kuka sosai, kwantar da ni tayi kafadarta sai da na yi kuka na gaji sannan na labarta mata abunda ya faru tsakani da Jibril da kuma iyayesa da suka zo gidanmu.
“Ki kara hakuri Nawwara ba gashi kin fara ganin sakamako ba, ni dai abunda na ke so ki yafewa Mustapha”
“Zan yafe masa”
“Amman..... Zaki iya”
Sai kuma ta yi shiru.
“Tashi kije karki makara”
Ta fada, ni kuma na tashi sai ta rakoni har kofar gida sannan na fice ita kuma ta koma. A hanya na hadu da Mustapha ina tunanin ita ta fada masa gani nan na fito, sai ya sha gabana da motarsa sannan ya bude ya fito, sai kuma ya kasa ce min komai sai kallona yake.
“Na yafe maka Mustapha ka dauka kamar komai be faru ba, amman zan gargadeka karka sake shiga hanyata, dan Allah dan Annabi ka fita hanyata”
Ina fadar hakan na kama gabana na cigaba da tafiyata na barshi nan tsaye yana ta kallona.
Har na yi kamar na bi ta gurin gidansu Bilal duk da na san by this time yana gurin aiki, sai kuma na bi hanyar da na saba bi.
Na isa gurin aikin da misalin sha biyu saura kwata, yau ma atamfar roba ce a jikina da gyale. Kai tsaye na wuce gurin aikina zuciyata cike da son ganin Bilal, sai dai ban san takamaiman inda yake aiki ba.
Ina isa kofar ta bude min, office dina na fara gyarawa sannan na shiga na shi Office din baya cikin hakan na nufin be shigo ba kenan, sai na na gyara komai sannan na fito, ko da na dawo nawa Office din wato office din farko wayata na ringing alamar kira ko da na duba sai na ga Number Zinatu da fari na yi mamakin da sunanta ya yi appearing a wayata sai dai tuna Rabi data karbi wayata tace za a saka min numbers mutane kuma nima a basu tawa yasa danna picking na kara a kunne.
“Nawwara dan Allah ki sauko hawa na biyu yanzu”
“Me zanyi?”
“Dan Allah dai ki sauko Bilal yake nemanki”
“Okay”
Cikin hanzari na fita na shiga lifter, a hawa na biyu na sauka komai na gurin glass ne ma'ana wani ma'aikacin yana iya hango dan uwansa, haka na rika duba sunayen da ke gurin har na kai ga wanda aka rubuta Bilal Usman na tura na shiga, sai na samu dakin cike da mutane duka tsaye wani katon cake na gaban Bilal da wuka a jiki,
Ina shigowa sai hankalinsa ya dawo kaina kamar marar gaskiya, sam baya farinciki kamar ba shi suke yi ma wakar happy birthday ba, kasa jurewa na yi sai idanuwa suka cika da kwalla, shi kuma ya gagara karbar cake din da Zinatu take kokarin kai masa a baki.
“Happy birthday my dear”
Shi kuma hankalinsa gaba daya a tashe yake ni kawai yake kallo.
__________________________________________
Masu son ganin Jibril da Mustapha da Bilal da Nawwara ku kwatantasu a idonku, ni dai iya abunda na sani Bilal ya fi su kyau 😜
#COMMENT
#VOTE
#SHARE
#FOLLOW.
kalmomi dubu hudu na yi🙄 dan haka har na jibi ne wannan 👻
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
*Dedicated to My Asmee*
3⃣7⃣
Ina fitowa daga banɗaki na zauna saman tabarma da na tashi sai Noor ya miƙon wayata da ke hannunsa.
“Momy gashi an kira na ɗauka amman ba ayi magana ba”
Ina karɓar wayar na duba sai na ga number Jibril number nan ce da ya saba kirana da ita.
“Ka yi magana?”
“Ee amman ban ce ance komai ba, sai na ce idan kin zo zan faɗa miki sai na kashe”
“Na shiga uku Noor miyasa ka yi magana?”
Hankalina ya tashi sosai zuciyata na ta raya min Jibril zai gane cewar Noor ɗansa ne.
“Momy ban ce komai ba”
Ya faɗa ganin yadda duk na bi na rikice, kai na gyaɗa masa naja shi zuwa saman ƙafafuna na zaunar da shi na rumgumeshi, muna haka wayar ta ƙara ringing ina dubawa na ga Number Jibril sai na kashe wayar gaba ɗaya, gabana sai faɗuwa yake, zuciyata na nuna min Jibril zai uya zuwa gidan nan a yanzu ko anjima saboda ɗansa.
Unƙurawa na yi na tashi sai ga Jidda ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, sai jikina ya ƙara yin sanyi har na ke ganin kamar ita ma tare take da Jibril.
“Noor tashi kaje ɗaki yi sauri”
Sai da ya gaisheta sannan ya tashi ya nufi ɗakin, ita kuma ta zauna kusa da ni tare da dafani.
“Ki kwantar da hankalinki ba zan cuceki ba, ba kuma za a haɗa baki da ni a cuceki ba”
“Idan har ni be cuceni ke zai cuce ki”
“Mustaphan da kika sani a baya ba shi ne a yanzu ba, Wallahi ya canja Nawwara kuma saboda ke ina ganin wannan kaɗai abun farincikine ace ta dalilinka wani ya shiryu”
Na gyara zamana ina kallonta da kyau.
“Bakin san waye Mustapha ba shiyasa kika wannan maganar, baki san iya ta'asar da ya yi ba shiyasa kike ganin kamar ya canja”
“Ya canja Nawwara ko ki yarda ko karki yarda Mustapha ya canja, ganin da kika mana tare yazo gurina ne saboda yana neman yafiyarki, yana son na taimaka masa na nema masa yafiyarki”
“Kin san abunda ya aikata min kuwa?”
“Shine mutumen da ya yi fyaɗe ya bata dubu ashirin ko? Ko ba wannan ba ne?”
Kallon mamaki na yi mata.
“Ya faɗa miki kenan?”
“Ya faɗa min komai saboda kawai yana neman yafiyarki, ki dubi girman Allah Nawwara ki yafe masa ko ya samu sassaucin rayuwa”
“Taya kika san tuban gaskiya ya yi? Maza suna yaudararmu Jidda saboda sun san mu mata muna raunin zuciya, sukan yi amfani da wannan damar su sake cutar da mu”
“Ba zai taɓa cutar da kr ba Nawwara, tun daga lokacin da kika taɓa marinsa ya ƙyaleki zuciyata ta raya min Mustapha son kin yake ko kuma son wani na ki, ya isa shaidar kirki cewar Mustapha tuban kirki ya yi tun da ya biyo ki har ƙofar gidanku ya nemi yafiyarki, idan har yana son cutar da ke ba zai taɓa neman yafiyarki ba, zai iya sakawa a ɗauko masa ke ya yi miki yadda ya ke so, zan iya dafa miki ƙur'ane cewar Mustapha tuban ƙwarai ya yi kuma ya yi nadama”
“Ba zan yafe masa ba da gangan mutun zai aikata abu sai kuma ya dawo neman yafiya, da ace be mata fyaɗe ba da bata samu ciki ba da duk be kaita ga halaka ba, da yanzu ƴar'uwata tana nan raye”
Na faɗa zuciyata na mugun ƙuna. Sai dai abunda ya fito daga bakin Jidda ya kusa ya ruɗar da ni ko kuma ma na ce haukatarda ni gaba ɗaya.
“Ashe jahila ce ke Nawwara, karatun addininki be amfaneki da komai ba, baki da imani ko kaɗan saboda baki yarda da ƙaddara ba, kuma bari na gyara miki kalamanki da ace yar'uwarki bata je ta kai kanta gunsa ba da be samu damar yi mata fyaɗen ba, kuma ko da Mustapha ko babu Mustapha dole Habiba zata mutu kuma dole sai wani ya yi mata fyaɗe kuma dole sai ta yi ciki saboda yana rubuce cikin kundin ƙaddararta, tirr da halinki Nawwara tirr zuciyar da bata yarda da ƙaddara marar kyau ba sai mai kyau, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle ke da Allah zai cewa faɗi ki mutun kuma ki faɗin ki mutu dan dolenki, zuciyarki bata da kyau Nawwara saboda babu imani babu tausayi a cikinta, bawan Allah nan ko shi da hannunsa ya kashe Habiba ya kamata ki yafe masa tun da har yace miki ya tuba, balle fyaɗen da idan aka bincika daga shi har ita suna da laifi-!”
Tun da ya fara maganar na ke kallon yadda take dantsar baki tana faɗa min duk maganar da tazo daga bakinta idonta na hawaye kamar yadda nima nawa idanuwan suke hawaye, cikin muryar kuka na ce.
“Faɗa min nawa Mustapha ya biyaki Jidda? Dala dubu nawa ya biyaki da har tasa kika goya masa baya tsaɓanin aminiyarki? Da me ya siye zuciyarki har kika ƙoƙarin ɓata abotarmu?”
“Da imani da tausayi ya siye zuciyata, ni na yarda da ƙaddara a yayinda ke baki yarda da ita ba”
“Saboda baki dan yadda na ke ji ba Jidda, a gaban idona yar'uwata ra rasa ranta saboda wannan azzalumin”
“Na san yadda kike ji, amman na fi jin yadda Mustapha ya ke ji saboda ƙaddara ta faɗa kansa wacce bata wuce faɗawa kowa ba”
Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye ta fice ta barni a gurin ina ta hawaye da mamakin kalamanta. Jin ana kiran sallah isha'i yasa na tashi na wanke fuskata na yi alwala a waje na yi sallah isha'i kamar yadda na yi ta magariba.
Bayan na gama addu'o'ina na tashi na nufi ɗakin Inna, ko da na shiga na tarar tana sha'u da wutiri Noor da Jamila kuma na saman gado suna mugun wasa, ƙasa na zauna kusa da ita ina jiran ta ƙare idona suna kan ɗana da ke ta sukuwa saman gadon.
“Noor bari mana gadon Inna zaka yi sukuwa”
Da sauri ya sauko sai ya nufo inda na ke yana faɗin.
“Momy zaki ara min wayarki na yi game ko?”
Sai a lokacin na tuna da na bar wayar a wajen da na zauna har na yi a zamar tashi na fita na ɗauko wayar cike da fargaba na kunnata ina shigowa ɗaki, zan miƙawa Noor naji ƙarar shigowar saƙo, hakan yasa na tsaya dubawa.
_Matiƙar baki dawo aiki gobe ba, wannan shegen saurayin na ki zamu sallameshi kuma try me_
Ba shiri na zaro ido gabana ya shiga faɗuwa na furta shiga uku da kirama kaina hallaka.
“Na shiga uku na lalace”
Da sauri duk suka kalleni har Inna dake jan carbi.
“Miya faru?”
Kallonta na yi sai kuma na rasa ta yadda zan mata bayanin ga Noor da Jamila har Sakina duka idonsu a kaina, saurin goge saƙon na yi na miƙa masa wayar.
“Ungo je kayi game ɗin”
“Momy miya faru?”
“Ba komai kuje waje da Mama Jamila sai ku yi”
Yana karɓa sai suka yi waje ni kuma na zauna kusa da Inna idona cike da ƙwalla na kama hannunta na riƙe sai na kasa yin magana hawaye suka fara yin aikinsu.
“Nawwara mi yake damunki?”
Hannuna ɗaya na kai na share hawayena yayinda wasu ke ƙara zubo min.
“Inna ko na faɗa miki ba zaki fahimce ni ba, kuma fushi zaki yi da ni”
Nan take hankalinta ya tashi ta damƙe hannayena biyu tana kallon cikin idona.
“Me kika aikata har haka ne Nawwara? Abunda ƴar'uwarki ta aikata shi kika aikata kema?”
“A'a Inna Jibril ne”
Na faɗa ina sosa kaina hawaye na sauka a fuskata.
“Wane Jibril?”
“Baban Noor”
Da sauri Sakina ta tashi zaune daga kwancen da take tana kallona, Inna kuma ta saki baki. Ni kuma na rasa ta inda zan fara mata bayani.
“Kamfanin da na samu aiki ashe na Jibril ne, ni ma ban sani ba sai daga baya....”
Haka na bi na zana mata komai tun daga farko har ƙarshe ban ɓoye mata komai ba, har maganar siye gidan da kuma wannan saƙon da ya aiko min yanzu.
Lunshe ido ta yi ta jingina da gado tana sauke ajiyar zuciya.
“Miyasa kika ɓoye min wannan tun farko? Da ace kin shawarce ni da duk abun be kai haka ba, har yanzu baki san ƙima da matarba uwa ba ko? Wani na waje ya ji sirrinki mahaifiyarki bata sani ba? Akwai wanda ya cancanci ki yi sirrin da shi fiye da ni?”
“Ba haka ba ne Inna, kawai ina tunanin irin halin da zaki shiga ne idan na faɗa miki, wata ƙila ma ba zaki fahimce ni ba, kuma abun zai tsaya miki a rai ki riƙa tunanin wanda ni kuma ba zan so haka, Wallahi ban ɓoye miki da wata manufa ba bayan wannan”
“Ƴaƴan mazani kenan masu yarda da ƙawaye fiye da uwaye, masu yin gaban kansu waɗanda suke ganin kamar tasu zata fisshesu”
“Dan Allah Inna ki yi haƙuri”
Na faɗa ina kuka.
“Amman da gaske Jibril ya baki haƙuri kuma kika mare shi ya ƙyale ki”
Sakina ta tambaya, ni kuma na ɗaga mata kai.
“Idan har yafiyarki yake nema ba zai tsaya jiran ki kawo kanki ya nemi yafiyarki ba, sai dai na nemi inda kike ya zo ya baki haƙuri kuma ya nuna miki ya yi nadama”
Cewar Inna, ni kuma na ce.
“Bana ma son ya zo dan ba zan yafe masa ba”
“Allah ma aka masa laifi aka roƙi ya yafe balle ɗan'adam? Idan baki yafe masa ba ai kya bashi ɗansa idan ya zo karɓar abunsa”
“Haba Inna duk wulaƙancin da ya yi min ya ce ɗan nan ba nasa ba ne sai kuma na bashu Noor gaskiya ba zan iya ba”
“Akwai hujjar da ta zata hana ni ganin ɗansa ne?, idan har ya dawo ya buƙaci ɗansa ki bashi kawai shine masliha a gareki da kuma mu, ku bar shi da Allah Nawwara idan har kika yi haƙuri sai ki ga kyakkyawan sakamako daga gurin Allah amman matuƙar kika ce zaki rama abunda ya yi miki Allah zai iya barinki da dabararki a ƙarshe sai ki cuci kanki, amman idan har kika barshi da Allah sai ya saka miki.
Ma a son mace da irin zuciya da halinki Nawwara, duk da zata iya ɗaga hannunta ta mari namiji ta kuma tsaya ta ci masa mutunci akan abunda zata iya kawar da ido ana mata kallon marar tarbiya kuma marar mutunci da kamun kai, raunin zuciya tausayi kawaici kunya haƙuri abubuwa da aka fi samu sun gurin ƴa mace,
Na san Jibril ya zalinceki Nawwara, amman ki barshi da Allah karki yarda ki ce zaki ɗauki fansa wannan ba halin musulmin kirki ba ne”
Daker na iya tsayar da kuka da na ke har na furta.
“Ni ba zan iya yafe masa ba Inna”
“Ban ce ki yafe masa ba, amman ki bishi a hankali kuma ki yi taka tsantsan”
“Kuma ba zan bashi Noor ba be cancanci zama ubansa ba, ni ba zan iya yafe masa ba”
“Har gobe ina faɗa miki rufin asirinki ne idan har ya dawo ya nemi ɗansa, ni kuma ban ce ki yafe masa ba”
Sakina ta dawo kusa da mu tana faɗin
“Amman gaskiya idan har aka bashi Noor ya ci riba biyu”
“Ba riba ya ci ba, Wallahi ina da tabbacin Allah ba zai barshi hakan nan ba, wata ƙila ya jarrabeshi ko zai jarrabeshi nan gaba, duk ɗa ai ƴaƴan maza ne ba na mata ba, itama wani auren zatayi ta haifi wasu ƴaƴan, ni dai abunda na ke so da ke ki yi min alkawari zaki riƙe mutuncinki kar kuɗi da ƙyaliƙyalin duniya ya yaudari zuciyarki ya kaiki ga faɗawa halaka”
“Na miki alƙawari Inna ba zan sake sakaki hawaye ba”
“Allah ya miki albarka, ki je gurin aikinki ki koma kamar yadda ya buƙata, amman karki taɓa nuna masa saboda Bilal kika dawo, kar ki nunawa Bilal saboda shi kike aikin, ko wannensu ki nuna masa saboda kanki kike yi kuma zaki iya dainawa a ko wane lokaci, idan har kika bar aikin yanzu zai kori Bilal kamar yadda ya faɗa, wanda hakan zai jefaku ciki wani halin, kuma baki san ta wace hanyar zai ƙara ɓullo miki ba”
“Amman Inna ina ganin kamar yana son ya yi amfani da damarsa ne ya sake cutar da ni”
“Ba zai sake cutar da ke ba, waya sani ko saboda ke ya dawo garin nan da aiki? Wanda ma yake likita miya kawo shi aikin kamfanin? Baki taɓa tambayar kanki ba?”
Na yi shiru ina nazari, sai Sakina ta yi karaf ta ce
“Wata ƙila yasan ta samu aiki a kamfanin shiyasa ya zo”
Inna ta amsa mata.
“Nima haka na ke tunani, ƴaƴan manyan masu kuɗi basa ganin irinmu talakawa da mutunci, yana ganin kamar ƙasƙanci ne a gareshi yazo neman yafiyarkin kai tsaye, bana tantama shi ne ya aiko mana da ɓarayin nan kuma ya siye gidan nan saboda ki matsu ki koma aikin a kamfanin kamar yadda yake buƙuta ta yadda zai iya kyautata miki har ya nemi yafiyarki cikin sauƙi, da ace cutar da ke yake son yi da wata hanyar zai ɗauko ba wannan ba, kuma kin ga idan har yana da wata niyar ta daban akanki babu yadda za'ayi ya ki mareshi a bayanar jama'a ya ƙyaleki har ma ya risina ƙasa yana baki haƙuri, wannan saboda yana ganin bashi wata mafita sai ita ne shiyasa ya ɓullo miki ta hanyar Bilal”
“Amman ina tunanin be san da Noor ba ko?”
Sakina ta tambaya. Sai Inna ta amsa ta
“Ya san ya barki da ciki, sai dai be sani ba ɗan yana raye ko baya raye, wata ƙila ma yasa an masa bincike akan haka, amman ki yi tunani Nawwara dukan mutumen da ya yi miki wannan wulaƙanci yana kunyar ya tunkareki kai tsaye ya nemi yafiyarki, kuma ta hanyar aikin nan da zaki yi a ƙarƙashinsa zaki iya fahimtar irin rayuwar da ɗan ki zai yi idan har ya zauna gunsa, ke da shi duka ƙurciya da wauta tana cinku”
Shiru na yi ina ta nazarin maganganun Inna akwai hiƙima da kuma ƙamshin gaskiya a duk abunda ya faɗa, ni kaina na san da Jibril be yi nadama ban iya na masa irin wannan cin kashin a gaban ma'aikatansa ba, kuma babu dalilin da zai ya riƙa bibiyata har yana neman na dawo aiki.
Ajiyar zuciya na sauke nasa hannu ina share hawayena, Inna kuma tana amsa sallamar da almajiri yake yi.
“Assalamu alaikum wai ance ana sallama da Nawwara a waje”
Da fari gabana ya faɗi na fara tunanin mai min sallamar.
“Waye ne?”
Na tambaya a cikin muryata mai amon kuka a cikinta.
“Haka ya ce wai bawon Allah ne”
Zan ƙara tambayarsa sai ga Noor ya shigo da gudu ya miƙa min wayar.
“Momy ga Uncle Bilal ya ce na baki”
Ina karɓa na kara a kunne already Noor ya yi picking.
“Nawancy gani nan akan hanya”
“Ka ce ma ka iso”
Sai kawai ya yi dariya ya kashe wayar, jin haka yasa na ce da almajirin ya ce ina zuwa, wayar na miƙawa Noor ni kuma na tashi na je waje na wanke fuskata na shigo na shafa mai sannan na saka Hijabi na fita.
Mustapha na tarar ƙofar gida sanye da jallabiya yana kallon ƙofar gidan, waigawa na yi gabas na duba yamma ban ga mai kirana ba hakan ya tabbatar min da cewar shi ne yaƙe kirana.
“Miya kawo ka nan kuma? Kamin nan dai bari na fara taya ka murna ka yi nasarar haɗa ni da ƙawata ta faɗa min har abunda ban zaci zata iya faɗa min ba, burinka ya cika”
“Ba burina kenan ba, burina ki yarda na tuba kuma ki yafe min”
“Akwai aiki a gabanka babba Mustapha, yafiyar Ubangiji ta fi cancanta ka nema ba tawa ba”
Sai ya kirana sunana a hankali.
“Nawwara idan na kai kaina kotu aka min hukunci zaki tafe min?”
“Allah ya rufa maka asiri karka tonawa kanka”
“Ina ma ace zan iya raba zuciyata biyu ki karanta ki ga abunda yake raina”
“Kasan zaka nemi yafiya ka aikata?”
“Ƙaddarata ce ta zo a haka, an rubutoni a cikin ƙaddarar Habiba kamar yadda aka rubutoki a cikin ƙaddararta, Wallahi da nasan Allah zai jarrabe ni da sonki da ban yarda ba kalli Habiba balle har wani abu ya shiga tsakanina da ita”
Ya faɗa yana ƙwalla, har na buɗe baki na sake masa wata maganar sai na hango Bilal tafe, sai na tattarahankalina na maida gurinsa gudun kar ya zargi wani abu, hakan yasa Mustapha waigaya ya kalleshi.
Tsayawa Bilal ya yi cak sai kawai ya ɗago min hannu daga can inda yake ya juya ya koma.
“Ka gani ko? Ka hana masoyi ya ƙaraso kusa da ni”
Na faɗa a tsawace.
“Yi haƙuri”
Sai ya yi saurin juyawa ya bar gurin cikin sauri, na daɗe tsaye bakin ƙofar wai ko zan hango Bilal ya dawo amman har na gaji ban dawo ba hakan yasa na juya na koma cikin gida raina a jagule.
Assalamu alaikum habibaties. Ina nan lfy kalau sai dai phone dina ce ta ci screen amman yanzu an gyara, Alhamdulillah.
A cigaba da gashi...
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
*Dedicated to My Asmee*
3⃣9⃣
Ba ni da wani zaɓi face na bashi damar shiga, domin nasan komai dare daɗewa dole zai sani. Kamar yadda Rabi ta nuna a wacan karo haka na danna sai ƙofar ta buɗe masa, a ta biyu mai gilashi muka riƙa kallon kallo ni da shi. Ƴar ƙaramar danjar sai tsuwa take tana nuna min agogon hannunsa da pose ɗin kuɗinsa sai kuma takardun da ke hannunsa.
Ban damu da ce masa ya aje ba na sake dannawa ta buɗe ya shigo yana ta kallona kamar wanda be sanni ba. Hanzarin miƙewa na yi tsaye Cikin yanayin damuwa na zan masa magana sai ya rigani
“Takardun nan zaki kai wa oga ya saka hannu”
“Na yi ta kiran wayarka ban samu ba, miyasa ka kashe wayar”
“Zamu yi maganar anjima let's do this now”
Yawun bakina na haɗe kana na ɗaga masa kai sannan na karɓi takardun kai tsaye na nufi office ɗin Jibril duk kuwa da kasancewar ya yi min gargaɗi ɗazu akan na daina shigowa ba noticing, waya na tarar yana yi fuskarsa shimfiɗe da farinciki tea da na haɗa masa yana hannunsa sai kurɓa yake, yana ganina sai ya yayi hanzarin yanke wayar ya kalleni, sai dai be ce min komai ba jira yake ni na fara masa magana.
“Hannu zaka saka a waɗannan takardun Bilal ne ya kawo”
Na faɗa kamar mai shirin yin kuka, domin har ga Allah ban jidaɗin yadda na ga fuskar Bilal kamar baya cikin farinciki. Saman tebur na aje masa takardu sai ya duba ya saka hannu sannan ya miƙa min. Ni kuma na karɓa na juyo jiki ba gwari na miƙawa Bilal takardun sai ya karɓa yana faɗin
“Congratulations”
Ni dai ban ce masa komai ba har ya juya ya isa gurin ƙofar sai ta buɗe masa da kanta ya fice. Faɗuwa na yi saman kujera da ke kusa da ƙofar ta zaman baƙi ina sauke ajiyar zuciya, har ga Allah na san dole ne sai Bilal ya zargeni amman ta yarda zan fahimtar da shi ne aiki tasowa na yi na dawo saman saman kujera ko kuma na ce kujerar office ɗin na zauna zuciyata a jagule, ina ta tunani mafita sai bachi ɓarawo ya yi gaba da ni.
Babu komai a mafarkina sai Jidda da Mustapha, wai ya mata fyaɗe kuma ya kasheta ga ƴan sanda da mutane cike a gidansu, ni kuma sai aikin kuka na ke ina kiran Mustapha, abunda ban sani ba ashe har a fili na ke kiran sunansa.
“Mustapha...”
Abunda na furta kenan daga farkowatawa, sai na ga Jibril tsaye a kaina yana kallona, hakan yasa ni saurin zabura na tashi.
“Me zaka min?”
“Me kike tunanin zan miki? Mayaudariya kina spn Mustapha kina yaudarar Bilal ko?”
“Ina ruwanka babu ruwanka da rayuwata”
Sai ya mire baki tare da ɗaga kafaɗunsa sama alamar abun be dame shi ba.
“Tashi muje meeting, baki da aiki sai bachi abunda ya kamata ace ke zaki faɗa min lokacin meeting ɗin ya yi amman wani ne daga can waje yake sanar da ni”
Na tashi tsaye idona kan agogon office ɗin da ke nuna ƙarfe goma sha ɗaya na safe, shi ya fara fita ni kuma ina binsa a baya har muka shiga Lifter, a nan ya miƙa min ƙaramar jakar da ke hannunsa.
“Kin duba akan me zamu yi meeting ɗin?”
Na girgiza kai alamar ban sani ba, sai kawai ta cigaba da kallona ko kunya baya ji, ni kuma na yi kamar ban ganshi ina ta kallon numbobin lifter, sai dai haka be sa ya ɗauke idonsa daga kallon da yake min ba har lifter ta tsaya a hawa na uku ta buɗe da kanta, sai na yi saurin fita duk da ban san inda zamu shiga ba, sannan shi ma ya fito sai ga Rabi ta tare mu ta karɓi layin wayata wai zaa saka min numbobin ƴan ƙamfanin ta yadda zan gane duk wanda ya kirani.
Ko da muka shiga ɗakin taron mun tarar da mutum biyar wannna abokin nasa Siraj sai kuma Zinatu da wasu ɓakin fuska uku, yana shigowa duk suka miƙe tsaye ya miƙa ma baƙin fuskar hannunsa suka gaisa sannan ya gabatar musu da ni.
Ɗaya daga cikinsu ne wanda na ke zaton ba musulmi ba ne ya miƙo min hannu dan mu gaisa yana faɗin sunansa.
“Divid Sam”
Sai Jibril ya yi saurin miƙa masa na sa hannun a ƙaro na biyu, ya kuma amsa masa kamar ni ɗin.
“Nawwara”
Ni kuma na zauna a kujerar da ya nuna min, ban maida hankalina kan abunda suke tattaunawa ba, sai dai hakan be hanani fahimtar cewa wani kamfanine yake son siye, har aka yi meeting ɗin aka gama Siraj da Zinatu idonsu na kaina duk wani motsi da nake suna kallona har na soma jin babu daɗi.
Tare muka fito daga ɗakin taron sai ya koma daga bayana yana kallon tafiyata, hakan yasa ni ƙara sauri na shiga tifter, sai da tana daf da rufewa sannan ya ƙaraso ya shigo, still yanzu ma idonsa na kai, da alama dai kallona daɗi yake masa, ko kuma yana min ne dan kawai na tsargu, sau ɗaya na ɗago na kalleshi sai yayi min kwarjini sosai na yi saurin sadda kaina ƙasa ban sake kallonsa ba har Lifter ta sauke mu a hawa na biyar, har na miƙa jiki na fita sai ya riga fita.
“Baki iya competition da ni”
Ya furta daidai lokacin da zai fice, a nan na kalli bayan kansa sannan na fito muka doshi office ɗin, da fari na tsaya tunanin wa zai buɗe mana tun da ba mu bar kowa a ciki ba, muna isa sai kawai naga wata ƙaramar na'ura tana ɗaukar fuskarsa, sai ƙofar ta buɗe masa ya shiga, ina zuwa na shiga sai wani jan layi ya shata yana ta ƙara.
“Ki tsaya a nan karki raunata kanki, ba zaki iya shiga yanzu ba saboda bata tantance fuskarki ba”
Bayan ya shiga ciki da kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe min. Ina shiga ya jawo ni gaban computer ta ɗauki hotona ya saka sunana sannan ya juya ya shige Office ɗinsa.
Ina zaunawa idanuwa suka kai kan agogon Office ɗin na ga ɗaya da kwata, lokacin Sallah azahar ya yi, wata ƙofar da ke cikin Office ɗin na nufa ina taɓawa sai ta soma ƙara tana nuna min na saka password, ta biyu kuma ina turawa na ga toilet, daman shi na ke nema, alwala na yi na fito na d8ba ko'ina na gurin babu carpet ɗin Sallah sai na shimfiɗa ɗankwalina na yi dashi bayan na gama, na nufi Office ɗinsa dan tunatar da shi lokacin Sallah ya yi.
Zaune na sameshi yana ta aiki a system ɗinsa, kamar jira yake na shigo mayun idanuwansa suka dawo kaina har na ƙaraso kusa da teburinsa.
“Lokacin Sallah ya yi”
Iskarka bakinsa ya busar sannan ya kalli tsadadden agogon hannunsa.
“Idan na gama aikin nan zan yi”
“Har sai ka gama aikin? Jibril mi ka ɗauki sallah ne? Sallah ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan addinin musulunci, kuma ita ce gimshiken addinin musulunci. Barinta kafirci ne da yake fitar da mutun daga cikin addini, babu addini babu musulunci ga wanda ya bar sallah namiji ko mace!”
“Ba fa kafiri ba ne ni, ina sallah”
“Na san ai kana sallah, amman ba akan lokacinta ba, ina mamakin avunda zai ɗaukewa mutun hankali har ya watsar da bautar Ubangijinsa, kasan irin azabar da Allah ya tanadarwa masu wulaƙanta sallah kuwa? Jinkira sallah lokacin ya fita ba tare da wani uzuri na shari'a ba, wannan tozarta sallah ne kamar yadda Allah ya faɗa a suratul Maryam aya ta hansi da tara zuwa sitti : Sai mutanen banza suka maye bayansu, suka tozarta sallah, suka bi sha'awace-sha'awace na saɓo; to ba da daɗewa ba zasu haɗu da gayyu wato wani gwalolon azaba a cikin wutar jahannama, sai fa wanda ya tuba.
Farkon abunda za a maka hisabi da shi a cikin ƙabarinka sallah ce, kuma ita ce zata tayaka zaman ƙabari (Allah ka bamu ikon tsaida Allah akan lokaci 🙏😭)”
Tun da na soma maganar yake kallona fuska a sake, da alama na burgeshi ne ko kuma mamakina yake oho, but to my surprise sai na ji ya ce
“Thank you, da kika tunatar da ni, babu wanda ya taɓa faɗa min wannan, inshallah zan gyara ko dan na samu damar rayuwa da ke a aljanna”
“Aljanna kowa gidansa daban, na Jibril daban haka ma na Nawwara daban”
Dariya ya yi kamar ba shiba ya miƙe tsaye ya nufi wata ƙofar da nake zaton banɗakine a ciki. Ni kuma na juyo na fito, sai na samu computer tana nuna min Rabi da ke waje, sai da na zauna sannan na buɗe mata sai ta shigo fuskarta a sake kamar ko yaushe.
“Ga sim ɗinki anyi miki dukan abunda ya dace”
“Thank you, amman yanzu idan ina son na kira general meeting a madadin Jibril ya zanyi?”
“Sir Jibril zaki ce ko kuma mai gida”
Ta faɗa sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi dake gefen teburin ta soma nuna min
“Wannan number zaki kira, idan an ɗaga ba sai kin tsaya gaisuwa ba, kawai ki ce Sir Jibril ya ce haɗa masa general meeting, idan emergency ne sai ki faɗa, idan kuma meeting ɗin yana da date da time sai ki faɗa, zasu haɗu a hawa na biyu room 24 domin shi ne kawai ɗakin da yake iya ɗaukar yawan ma'aikatan da ke kamfanin nan, idan har ya yarda ki yi magana a madadinsa zaki iya zuwa kiyi idan kuma shi zaiyi da kansa sai ki raka shi”
“Thank you so much”
“Your welcome”
Sannan ta juya ta fita, ni kuma na saka number da ta nuna min a telephone zuciyata na ta raya min kar na yi, idan har na yi haka na yi karanbani, wata zuciyar kuma na nuna min idan har na yi haka na taimaiki Jibril da rayuwarsa har da da sauran ma'aikatan.
Sai kawai na dannan kiran na ce ina buƙatar a haɗa min meeting ɗin gagawa, ni kuma na tashi na fita riƙe da wayata na nufi lifter, ina sauka hawa na biyu na soma ƙirga ɗaki, har na hango ɗakin da mutane suke shiga. Tsayawa na yi sai na kasa ƙarasawa ina ta tunanin ma yadda zan ce musu abunka da wanda be saba ba, sai kawai na juya na koma lifter, na yi mamakin yadda ina isowa bakin ƙofar office ɗin sai kawai ta buɗe min.
Ina shigowa na samu Jibril tsaye yana jiran shigowata.
“Akan mi kika kira general meeting kuma emergency?”
“Am sorry”
“Ba hakuri na ce ki ba ni ba, dalili zaki faɗa min”
“Da na yi ƙoƙarin na faɗa musu idan lokacin sallah ya yi kowa yaje ya yi sallah, sai kuma na ga kamar na maka karanbani”
“Karabanni ne mana, ba yau yau kika kama aikin ba?”
“Am sorry”
Na faɗa cike da nadama sai ya matso kusa da ni.
“Is okay, zan faɗa musu da kaina indai har haka kike so, follow me”
Yana faɗar hakan ya nufi ƙofar fita na bishi, tare muka isa da kansa ya faɗa musu cewar a yanzu da lokacin sallah ya yi kowa ya aje aikin da yake yaje ya yi sallah, daman akwai masallaci a cikin kamfanin. A yanayin yadda fuskokin musulmin ma'aikatan suka nuna sun yi farinciki sosai kuma sun nuna jindaɗinsu har ma da yin godiya.
Ina tsaye gefen Jibril Bilal na kallona kamar zai cinye ni, irin kallon nan da mutum zai kasa gane manufarsa sai hakan yasa duk na bi na tsargu, mu muka fara fita sannan sauran suka fito. A bayan na tsaya ina amsa waya shi kan gogan na ku tuni ya yi nisa tare da Siraj.
Dpo ne ya kirani wai an bashi number ta daga gida, saboda ya zo be sameni ba kuma yana son magana da ni, a ina nake ya zo ya tafi da ni.
“Na kusa dawowa aiki, idan na dawo zan kira ka”
“Okay”
Daga haka na kashe wayar, na cigaba da tafiyata. Ko da na shiga office ɗin ƙpfar Office ɗin Jibril tana buɗe ina hango abokinsa sai dai ban san mi suke tattaunawa a akai ba har sai da na zauna sannan na soma jiyo muryar abokin nasa.
“Be kamata ka sake mata har haka ba, so ai ba hauka ba ne....”
Sai kawai na ji an ba ƙofar gam an rufe, bayan wani ɗan lokaci sai abokin nasa wato Siraj ya fito kamar cikin ɓacin rai ya fice ba tare da ya kalli inda na ke ba.
Takardar da ke gabana na ɗauka na duba sai na ga lokacin meeting ɗinsa da wani Hon Usman Dahiru ya yi, a maimakon na kira sai kawai na tura ƙofar na shiga.
Saurin saka bayan hannunsa ya yi ya kare hancinsa, sai dai abunda be sani ba abunda ke gabansa a farar takarda mai kamar hoda ya taɓa masa hannu, juyawa na yi zan fita sai ya kira ni.
“Naj”
Ina juyowa ya ce
“Madarace na ke sha ina fama da ulcer”
Ni dai ban ce masa komai ba na juya na fita, ina shirin zama sai gashi na fito daga office ɗinsa ya biyoni.
“Madara ce Naj”
Nan ma kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya ɗaga hannayenasa sama domin shi ma yasan ban yarda da shi ba.
“Fine cocaine ce shikenan?”
“Allah ya wadaranka Jibril, kullum abunka gaba yake ba baya ba, har yanzu akwai tattoo a jikinka, yanzu kuma cocaine kake sha bayan neman matan da kake? A haka iyeyenka za su nuna ka a matsayin ɗansu ɗan ka kuma ya nuna ka a matsayin uba? Iya yau kawai na zauna da kai, amman na ga halaye masu marar kyau a tare da kai, wasu baka canja ba wasu kuma sabbi ne, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata Jibril...”
Na faɗa cikin hawaye da kuka na ɓakinciki da jin zafi, yanzu irin wannan mutunen ne na haihu da shi? Ina baƙincikin da ya kasance uban Noor sam, ɗa na be yi dacen uba ba, dan haka ban zan nuna masa ko kuma faɗa masa cewar Jibril ne ubansa na gaskiya ba.
“Bana neman mata Naj, Aisha ce kawai na ke taraiya da ita ma kuma na daina na tuba, cocaine ɗin ma akwai dalili shanta da na ke, amman na ji kamar kin yi wata magana, na ji kin ce ɗa me kike nufi akwai abunda ya kamata na sani ne?”
Ganin yadda yake matsowa yasa na yi hanzarin miƙewa tsaye har ina ɗauke numfashi, shi kuma yana ta kallona kamar mai karantar abu a fuskata, sai takowa yake har sai da ya kowa daf da ni...!
“Ina da ɗa ko Nawwara...?”
____________________________________
Zaku ga wasu kalmomin kamar ba a ƙarasa ba wasu kuma ana mistakes da yawa ana dai akwai errors or omissions a ciki, hakan yana faruwa ne saboda rashin editing, idan har na ce zan tsaya editing zai ɗauke ni tsawon lokaci ban yi updated ba domin editing ya fi bani wahala fiye da typing.
Fatar zaku fahimta kuma zaku min uzuri 🙏
FOLLOW ME
VOTE
COMMENT
SHARE
0 comments:
Post a Comment