*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
*Shafin yau na ku ne Maman Hannep Novels Group, Rai Biyu Fan's Group Khadeeja Candy Novels Group*❤🖤
4⃣1⃣
Tana daf da kai masa cake din a baki sai ya yi saurin rike hannunta.
“No thanks”
“Haba Bilal sai ka ce wani abu yau ne birthday ka fa”
Sake kai masa a baki da karfi har tana shafa masa ragowar da yake hannunta a fuska tana dariya ita da mutane da suke cikin office din. Sannan ta juyo ta kalleni
“Karo mana Nawwara let's have fun”
“No ina da aiki a ciki, Happy birthday Bilal”
Na fada idanuwa cike da kwalla, sannan na juya na fito hawaye na bin fuskata.
Ban yi nisa a tafiyarba na ji muryarsa yana kirana ni kuma na kara sauri kamin ya karo inda nake har na shige lifted, ina sauka hawa na biyar na shige Office ina kuka, ko mintuna ban yi da zama ba sai gashi yazo gurin kofar, ina kallonsa ta computer na ki budewa sai kuka na ke har ga Allah na ji zafin wannan abun, da ya gaji da tsayuwa ya kirani, ban daga ba har ta yi ringing ta gaji ta katse, haka ya jera min kira har guda goma sha uku ban dauka ba, be bar gurinba sai da Jibril ya karaso sannan ya yi hanzarin barin gurin, ni kuma na yi saurin tashi na share hawayena, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka na yi ba.
“Good morning”
Na fada ina a tsaye idanuwa a kasa muryata na bayyana kukana, a maimakon ya amsa min sai kawai ya karaso gaban table dina yana kallon fuskata.
“Me kike yi ma kuka?”
“Ba komai”
Na fada idanuwa na kara cika da kwalla.
“Fada min mana waya taba ki?”
“Babu”
“Aikin ne baki so?”
Na kasa amsawa sai hawaye nake.
“Mi Bilal ya zo yi nan? Miyasa kika ki bude masa?”
“Ba komai”
Ya daki table dina.
“Dole ne ki fada min abunda yasa Gimbiyata zubar wannan hawayen mai daraja da tsada”
Ya fada kamar ba shi ya yi maganar fuskarsa babu alamun wasa sai ma kara hade rai da ya yi
“He's just come to apologise”
“Apologise for what?”
“Yau ya yi birthday, shine ya yi celebration tare da Zinatu”
Kallona ya tsaya yi sosai kamar mai karantar abu a fuskata, sai kuma ya kyalkyale da dariya har sai da office din ya dauka gaba yana amsa amonsa.
“Wow wow so that's means Zinatu ya ke so ba ke ba? Daman can ba saurayinki ba ne ko? Ko kuma...”
Ganin yadda na ke hawaye yasa shi saurin rufe baki yana gintse dariyar da ke cinsa.
“Okay calm down Naj-Babe i will talk to both of them”
Yana fadar hakan ya nufi office dinsa sai cigaba ya ke da dariyar, kamar cikinsa zai fashe. Ni kuma na zauna a gurin hawaye na ta min zuba zuciyata kuma na mugun zafi.
JIBRIL POV.
Be shigo office din da dadin rai ba, amman wannan labarin na ya faranta masa rai.
“Excellent”
Ya furta yana kokarin zama, abun ya fi tsaya masa a rai Zinatu da gaske tana son shi ko kuma ta yi ne kawai as a friend ita kuma Nawwara kishi ya rufeta.
“Wow”
Ya furta yana dora kafarsa daya saman daya yana lilo da kujerar.
“Allah ya kara raba kanku”
Bayan kamar thirty minutes Nawwara ta shigo Office din idonta a kasa.
“Kana bukatar wani abun ne?”
Kallonta yake, ya ji dadin abunda ya faru amman wannan halin da take ciki baya son shi ga hawayen da ta kasa dainawa har yanzu, yasan tana jin kwatankwacin irin zafin da yake ji a duk lokacin da ta kula wani ba shi ba. Mika hannu ya yi zai riko hannunta sai ta yanje ta yi cikinsa da masifa.
“Miyasa kake son taba hannuna ne? Miyasa kuka dauki rumgumar mace da taba hannunta a matsayin wayewa? Baka san zunubin da ke akwai a taba hannun mace da ba muharramarka ba? Baka da rayuwa mai kyau Jibril”
Uffan be ce mata ba har ta juya ta fita, sai dai maganganunta suna masa zafi, baya jindadin yadda duk maganar da ta zo mata a baki take fada masa, ciwon da ke damunsa ne ya taso masa har yana neman numfashinsa sai da ya dinga sauke ajiyar zuciya yana dafe zuciyar sannan ya samu sassauci har ya nufi freezer ya sha ruwa, sai kuma ya bude durowarsa ya dauko cocaine ya zo ya zauna gaban teburinsa ya soma shaka. Sai ga Nawwara ta shigo da wasu takardu a hannunta tsayawa ya yi kallonta kamar yadda ita ma take kallonsa.
“Kana da meeting da pearls global company misalin sha biyu da rabi, wannan kuma daga Dr Ishak Hacker ne zaka saka hannune a maida masa”
Ta fada tana dora masa takardun saman table dinsa, kamar be damu da ganin da tayi masa yana shan cocaine ba ya dauki pen ya saka hannu, ita kuma ta juya ta fice ba tare da ce masa komai ba. Wayarsa ya dauka ya kira Siraj.
“Ka bincika?”
“Eh amman ance bata da wani da kuma binciken ya nuna bata ma taba yin ciki ba”
Ya busar da iskar bakinsa dan ba abunda yake son ji kenan ba.
“Ka tabbata?”
“Yes, walimar da kasa a shirya yau za'ayi”
“Thank you Siraj ayi abunda ya dace”
Ya katse kiran yana ta tunani, sam zuciyarsa bata yarda babu da tsakaninsa da Nawwara ba, ji yake kamar dai Siraj be yi binciken daidai ba, ko kuma Nawwara tasa a boye masa ne. Rabi ya kira dan jin yadda aka yi daman tun da ta kai kayan ta kirashi be dauka ba sai ta aiko masa da sako amman be bude ba.
“Good morning Sir”
“Ina jinki!”
“Na kira wayarka baka daga ba kuma na aiko maka da sako, anyi komai yadda ya dace Sir sai dai ita kadai na yi ma siyayyar”
Ta fada da zimmar ta ji abunda zai ce tace ba tayi ma yaronta ba dan ita a zatonta Jibril ya san da shi.
“Eh daman ita kadai zaki yi ma”
Yana fadar hakan ya kashe wayar yana jin kansa kamar marar lafiya. Sha biyu saura kwata Nawwara ta sake dawowa office din.
“Akwai wani abun da ya kamata muje da shi gurin meeting din ne?”
“Ee takardun kamfanin nan, suna cikin can”
Ya nuna mata wani katon box dake lake da ginin gurin, karasawa ta yi tana kokarin budewa amman ta kasa.
“Sai kin sa password”
“Miye password din?”
“N¹¹A²³W²¹W³¹A³³R¹³A”
Sunanta ne zere sai mixing da aka yi da numbers, tana saka. Password din sai ya bude, farkon box din cocaine ce mai yawa, na biyu kuma zinari ne irin wanda aka ciro cikin kasa ba a sarrafashi ba, sai dollars dake binsu daga karshe ne takardun suke.
“Duka zan dauko?”
“Ki duba files din wanda aka rubutawa 001 zaki dauko”
Daki-daki ta bisu har ta wanda yake magana akai ta dauko, sannan ya maida marfin box din ta rufe ta taso ta nufo table dinsa.
“Miyasa kake son shan cocaine ne?”
Yaja ragowar dake hancinsa sannan ya dauke idonsa daga barin kallonta.
“Saboda na rage damuwa da bacin rai”
“Waya fada maka tana cire damuwa?”
Ya mike tsaye ya nufi gurin window ya tsaya tare da sanya hannayensa aljihu.
“A lokacin da na haukace akan tunaninki na rabu da kowa, na watsar da dukan abokaina sai Allah ya hadani da Siraj, shi ne kadai mutumen da ya taimaki rayuwata na fara dawowa mutum da wannan cocaine din, a duk lokacin na shakata ina samun sassauci akan tunaninki, musamman a lokacin da take buguna ba kamar yanzu da bata min aiki ba”
“Amman miyasa kake sha?”
“Saboda ta zame min jiki”
“Idan har kana son ka kore damuwa ka rika daukar kur'ane kana karatu, ina tunanin ka san illar wannan cocaine din”
Ya juyo ya kalleta.
“Ba ni da wani zabi ne saboda tunaninki na fara shanta”
NAWWARA POV.
Ban sake ce masa komai ba na juyo ya baro office din, zuciya cike da rashin jindadin halin rayuwar da jibril yake yi. Yanzu akaf a familynsa a rasa wanda zai tsaya ya fada masa gaskiya akan rayuwa? Babu mai iya bata lokacinsa ya zauna da Jibril ko dana dan lokaci ne? Abun bakiciki ne namiji kamarsa ace be san abunda ya dace ba, shikenan saboda be da mahaifiya a raye mahaifinsa ba zai iya zauna da shi ya fahimci rayuwar dansa ba?
Ni kadai ce zan iya canja rayuwar Jibril a yanzu, saboda ni kawai yake saurare ni ce kadai zan matsa tsawa be maida min ba, dole na taimaki rayuwarsa ko dan dana ba ni da wani zabi a yanzu da ya wuce wannan ko na ki ko na so uban Noor ne kuma dole wata rana Noor zai yi rayuwa da Ubansa, idan bashi a tafarki mai kyau taya Noor zai kalleshi?
Tunani kenan sai kuma wata zuciyar ta jefo min tambaya.
‘Yanzu mutumen da ya wulakanta ya nuna baki da muhimmanci a rayuwarsa mutumen da ya kiraki da annoba? Yasa aka kiraki karuwa? Ya ce dan da kike takama da shi ba nasa ba ne? Ya wulakanta mahaifanki ya tozarta ki a idon duniya ya ce ganin bakin maciji ya fi masa ganinki, shi zaki taimaka? Irin wannan mutumen zaki tausayawa? Wanda ya kasa baki taimako daga lokacin da kike bukatarsa ya fifita karuwa akanki?’
“No no ba zan iya ba”
Na furta a fili idanuwana cike da tsanarsa.
“Yaje ya yi ta yin rayuwar da yake ganin zata fidda shi ni babu ruwana a ciki”
Ina rufe bakina yana fitowa daga office, ni kuma na mike tsaye na dauki takardun.
“Naj ina ɗa na?”
Wani wawan kallo na watsa masa.
“Da kuma? Ko cocaine din ta fara bugunka?”
“Ina cikin hayyacina na san abunda na ke ina dana ko yata?”
“Mtssss kana hauka Jibril baka ma san abunda kake fada ba”
Ina yin gaba na ji an fisgoni na fado kirjinsa sai ya rumgume kamkam ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa numfashinsa kuma na fita da sauri. Iya karfin da Allah ya bani da kuma dabara ya saka wajen ganin na kwace kaina amman na kasa ko kwakkwaran motsi, saboda karfinsa ya ninka nawa sau saba'in.
“Ka sake ni ko na maka ihu”
“Ko kin yi ihu babu wanda zai zo”
Ya fada idonsa a lumshe yana kara kwamtar da kaina a kirjinsa.
“Kina jin yadda zuciyata take bugawa ko Naj saboda ke”
“Idan baka sake ni ba zan sake zuwa aikin nan ba, daman saboda ka rika min haka ka tirsasani yin aiki a tare da kai ko?”
Ya dora kansa saman kaina.
“Ina ma zamu dawwama a haka”
“Ba zan sake zuwa aikin nan ba”
Ya yi saurin saki na.
“Ina son ki sosai Naj ina miki irin son da wani da namiji be taba miki ba”
“Ni kuma bana son..”
Na kasa karasa saboda hannunsa da yasa ya rufe min baki, sai kuma ya duka kasan guiwoyinsa ya hade hannayensa.
“Dan Allah dan Annabi Naj ki yafe min abunda na yi miki, dan Allah ki manta da komai”
“Na manta da komai saboda ka san ka zalince ni ko? Mugu bakin azzalumi”
“Ki kirani da ko wane irin suna zan karba miki, ki ayyanani a duk kalar mutumen da kike gani zan dauka, ki ci mutunci a gaban kowa zan jure matukar hakan zaisa ki yafe min”
“Ba zai taba sa na yafe maka ba”
“Fada min abunda zan yi ki yafe min Naj, ni kadai na san irin abunda na ke ji a zuciyana, na kan tsani kaina idan a duk lokacin da na tuna abunda na aikata miki, tunaninki ya haddasa min ciwo da damuwa, rashin kulawar nan taki ina jin kamar yana kokarin rabani da rayuwata ne, i will die soon Naj mai yuyuwa a wannan lokacin zaki tausaya min ki zo gaban gawata ki yafe min”
Hawaye yake irin hawayen nan dake nuna tsantsar abunda ke zuciyarsa, ga nadama da damuwa nan ƙarara a fuskarsa.
“Lokaci meeting yana wuce”
Na fada tare da daukar takardun na nufi kofar fita. A ranar meeting hudu muka yi uku a cikin kamfanin daya kuma a wani kamfanin da muka je tare, sai dai sam babu walwala da sakewa a fuskar Jibril da ma yadda yake maganarsa da mu'alama da mutane, dukan abunda zan yi hankalinsa yana kaina, da muka dawo na yi sallah shi kuma ya dora alwala ya fita zuwa sallah a masallacin da ke kamfanin ni kaina ban taba sanin akwai masallaci a kamfanin ba sai yau, bayan na dawo ya cilasta min zuwa cin abincin rana kamar jiya, da muka shigo office ya dauko wasu takardu ya aje min wai na yi typing dinsu a computer shi kuma ya nemi wata kujera ya aje gaban teburina yana kallona har na yi aikin na gama.
Tare da shi muka shiga mota, ya kawoni a inda ya aje jiya sannan ya mika min wata sabuwar laptop, wai da ita zan dinga zuwa office kuma na je gida ta aiki ce sai kuma na bukaci na kwashe duk abunda ke cikin wacan computer ta office na saka a laptop din, ni dai ban ce masa na gode ba balle sai anjima na fito na yi tafiyata.
Ko da na isa gida yamma ta yi lis saboda yau na dade sosai a gurin aikin, na darar da gidanmu cike da mutane suna ta mana murna wai Sakina ta ci gasa an bata gida kuma wanda yasa gasar ya dauki nauyin karatunta sannan ya yi mata kyautar dubu dari biyu da hansin, ita kanta kamar zata hade kanta dan murya.
Jibril kawai zuciyata ke raya min ya saka gasar nan, sai kuma daga baya na soma tunanin Mustapha domin shine a unguwar ya fi kowa sanin inda Sakina take karatu, har dare mutane nata shigo mana, Inna ta siye minti ta yi sadaka, bayan sallah isha'i Bilal ya kirani a waya na ki na daga sai ya aiko min da sako wai yana kofar gida, nan ma ban mayar masa da amsa ba jim kadan sai ga yaro ya shigo wai ana sallama da Nawwara, sai na yi karaf na ce
“Je ka ce ba zata zo ba”
Inna ta saki baki.
“Ba zaki zo ba? Ba kyau wulakanta dan adam fa, Wallahi ki kama kanki, ni bana son yawan zuwan da ake ama miki sallama, wallahi ko aikin nan da kike zuwa hankalina be kwance yake ba, bani da kwanciyar hankali idan ba aure kika yi ba”
“Inna Bilal ne fa”
“To dan me ba zaki je ba?”
“Wai birthday yayi yau shi da Zinatu suka yanka cake din kuma a gurin aikinmu wai har da kirana dan na gani”
“Kishi kike kenan, ashe ana kishin abunda ba a so?”
“Ni ina son shi”
“Kina son shi kike nuna baki son shi? Kina son shi miya hana ki aure shi? Yanzu ke kina ganin zaki samu namijin da zai so ki kamar yadda Bilal yake son ki? Babu abunda ba a fada masa ba a kanki amman ya toshe kunne ya ce yaji ya gani shi dai son ki yake, kuma kina da ɗa shi yana saurayi kuma a haka yake son ki, babu irin kulawar ta cusa kai da be nuna miki ba amman kiki bashi dama, sai yanzu dan ya kula wata zaki ji haushi har ki zo kina kishi? Wane iriin zama kike son ku yi da shi? Shi dai aure yake son ki idan baki bashi dama ba ai dole yaje inda wacce zata bashi dama,
Idan har son Bilal kike da gaske tau ki bashi dama ya ga magabatanki, sai ki yi kishi mai dalili, amman yanzu ai cin amanarsa zaki yi ki hana shi aurenki kuma ki ce ba zai kula wata ba?”
“Amman Inna ai kin san yan gidansu basa so na, ni bana son na yi aure inda zan wahala ni da Noor”
Na fada ina kuka, sai ta ce
“Zaki wahala dai ke, Noor kan ai ba zai zauna tare da ku ba, duk son da Bilal yake nunuwa Noor ana daura miki aure dole a gida zaki barsa sai dai ya rika zuwa yana ganinki, saboda Bilal Saurayi ba mai mata ba, da ma ace yana da mata da zakiniya zuwa da danki ya rika shi, amman wannan kan ai sai ya kara kiyayyar ki ga yan uwansa kuma jama'a ma sai su zageni ace na bari aka je da yaro ya takura masa, ina tunanin ba a gidansu zai aje ki ba ko da ya aureki, dan haka yan uwansa su daina damunki ba akansu zaki zauna ba, indai mijinki na son ki babu wanda ya isa ya taka ki, sai dai ki shiryar fuskantar kalubale daga garesu”
Na kara fashewa da kuka, ni dai har ga Allah ina son Bilal dina, kuma bana jin zan iya auren wani namiji bayan shi.
*** *** ***
Washe kamar marar lafiya haka na tashi jiki babu dadi zuciya ma babu dadi, bayan mun gama karyawa suka tafi makaranta ni kuma na gyara gida sannan na shiga na yi wanka ina fitowa na shirya cikin wata bakar abaya, da mayafinta, sannan na dauki laptop din da jakata na nufi dakin Inna ina mata sallama.
“Amman dai ina tsoron ki rika wannan abun a hannu, kin san garin ne ko maza ya suka kare balle mata”
“Ai kin ga a ciki jaka take ba wanda zai san abunda ke ciki, kuma ina addu'a inshallah babu abunda zai sameni”
“Tau Allah ya tsare ya kai lafiya, ni jiya ma duk a tsoro na kwana saboda gidan nan da yan kudi da aka bamu, yau zanje na kai gidan Ya Umma na fada mata komai duk shawarar da aka yanke idan kin dawo sai kiji”
Ta karasa tana miko min dari biyar na hau Napep.
“Tau Na gode sai na dawo”
“A dawo lafiya Allah ya tsare, ga wayarki da kika bari jiya”
Nasa hannu na karba, miss call talatin da bakwai Siraj ya yi min, sai kuma kiran Jibril guda daya, da kuma wata bakuwar number ni dai ban wani maida hankali kan wayar ba nasa kai na fice ina ta tuno abunda ya faru jiya sai na ji raina ya sosu.
Yau na ji da wuri sai dai duk da hakan ya rigani zuwa, a gabansa na gyara office din na jera komai yadda ya dace sannan na hada masa tea, files din da aka kawo dake kofar office din farko na dauka ina duba wanda zai saka hannu na kai masa wanda kuma ni zan yi aikin na maida hankalina ina ta yi, misalin sha biyu na shiga na fada nasa meeting din da muke da su da kuma mutane da yake da appointment da su, be samu kansa ba sai biyu daidai saboda ganawa da yake da mutane, abun mamaki sai gashi ya fito da alwalarsa ya sauka saka ya yi sallah, ni dai already na yi sallah duk da kasancewar ina jin marata tana murda min tun Shekaran jiya alamar menstruation dina na daf da zuwa, sai dai na san kamin ta zo na kan yi kurajen fuska ko da kwara daya ne ko biyu, rashin ganin kurajen yasa ban maida hankali akan tararta ba.
Bayan ya dawo ya shiga meeting, yana fitowa yasa na hada masa tea, na shiga office din ya fi a kirga ina kai masa files da documents, sannan na koma na cigaba da saka kwashe abubuwan da suke cikin computer ina sakawa a laptop, muma haka danjar nan tayi kara alamar da mutun a bakin kofar office din, a computer na ga Rabi sai na bude mata ta shigo fuskarta da murmurshi kamar kullum, wata bakar leda ta aje min saman table ta ce
“Oga ya ce a baki wannan”
Tana ajewa ya juya ya fita, ni kuma naja ledar na soma budewa, abaya ce mai dankwali green color sai dozing din pant da pad da kuma turare. Gabana ya fadi mi yake nufi ne, sauri mikewa na yi tsaye na duba baya ashe rigata ta bace, gashi abaya ce ba Hijab balle ya kare min, arzikina ma bakar abaya ce, amman ya aka yi ya zubo min ban ji ba? Wata irin kunya ce ta rufe ni tunanin daya fado min a rai shine.
A haka naje meeting din ko dai bayan mun dawo cikin office haka ya faru? Kaddara dai ta riga fata, bathroom na shiga na tsabtace kaina sannan na wanke rigar da karamin saket dina da ya bace da pant dina, na saka abunda ya bani, sannan na kulle wadancan kayan a ledar na fito na saka a jakata.
Ina zaune da kunyata sai gashi ya fito daga office dinsa yana fadin
“Ba zamu samu damar cin abinci a kamfanin nan ba, saboda akwai wanda zan mu magana da shi a waje, saboda haka tare zamu fita sai na shiga meeting din ke kuma ki ci abinci”
Ni dai ban ce komai ba kuma na ki na kalleshi, sai dai kijina na bani so yake na kalleshi din, na dauki jakata na rayata sannan na rika jakar dake hannunsa a dayan hannuna kuma laptop ce.
Tare muka shiga motar ina jin kamar na natse saboda kunya, har muka isa ban kalli inda yake ba, shi kuma yana ta motsi yana son na kalleshi din.
Kamfanin da muka je kamfanin Chinese ne yan nigerian da suke aiki ciki basa da yawa, komai a tsare gwanin sha'awa. Wani bahaushe ne mai far'a da son mutane ya tare mu kuma ya yi mana iso har inda za'ayi meeting din.
Da zai shiga ya juyo yan karbi jakarsa da laptop din dake hannuna ya kalleni ya ce
“Duk kika sake kika yi fira da wani sai na yanka miki baki”
Be tsaya jiran amsar da zan bashi ba ya shigewarsa tare da mutumen, ni kuma na zauna a gurin ina kallon mutunen dake ta kai da kawo, bayan kamar minti biyar sai ga mutumen ya kawo min abinci na karba ina masa godiya ba dan ina iya ci ba, saboda mutane kowa kallona yake ba zan iya bude baki a irin wannan gurin na ci abinci ba wannan ba mutunci ba ne.
Fira ya soma yi da ni sama sama yana danna laptop dinsa, ana nan yake labarta min cewar shi dan Zaria ne, muna haka wayata ta soma ringing, bakuwar number ce har na yi kamar karna dauka sai kuma na daga, muryar Sakina na ji tana kuka.
“Anty ki yi sauri ki zo Noor ya samu accident gashi nan za a kai shi asibiti”
“Wace asibiti?”
Na tambaya hankalina a tashe.
“Specialist Hospital”
“Gani nan zuwa”
Na kashe wayar a lokacin har na fara kuka,
“Lafiya?”
“Ɗa na ya yi haɗari”
“Bari a fada masa mana”
“A a”
Ina fadin haka na fita da gudu hankalina a tashe har bana iya gani da kyau.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣2⃣
Sun samu kusan mintuna arba'in suna meeting din sannan daga karshe suka cimma matsaya daya akan kwangilar da kamfanin zai bawa kamfaninsu Jibril. Hannu ya mikawa Jibril suka gaisa sannan ya fito, daman hankalinta yana can gurin Nawwara zuciyarsa na raya masa tana can tana fira da wannan mutumen na dazu.
Da ya fito sai ya samu Mutumen shi kadai yana ta aikinsa sai wasu mutun biyu da suka zauna a kujerar da ya bar Nawwara dazu, kamar ba zai tambaya a zatonsa tana can wani gurin ne ko kuma ta koma cikin mota.
“Mai gida matar da kuke tare ta fita wai dan ta ya yi hatsari”
Sai Jibril ya tsaya cak kana ya juyo ya kalleshi.
“Dan ta?”
Ya fada.
“Ee tun dazu ta tafi na ce bari a fada maka sai ta ce a a”
“Kasan matar da muke tare kuwa?”
“Ee wacce kuka shigo tare, ai ni na tarboku na santa wata fara doguwa ba sosai ba mai dan fadin fuska tana sanye da abaya green”
“Amman dan ta ka ji ta ce ko kanenta?”
“Dan ta dai ta ce indai ba rudewa ta yi ba, saboda waya aka kira aka fada mata”
“Kaji wani abu bayan wannan?”
“A a gaskiya hankalinta a tashe yake bata ce komai ba”
Da sauri Jibril ya fita daga harabar gurin direbansa na hangosa ya san a uzurce yake kuma ya san babu abunda ya tsana irin jira, tun kamin ya karaso ya janyo mota kuma ya bude masa. Har Jibril zai shiga sai kuma ya mika masa jakarsa da laptop dake hannunsa.
“Nawwara ta tafi”
“Ee naga ta fice da gudu tana kuka har wani na tambayarta a abunda ya faru bata dai kula shi ba”
Ya amsa masa yana saka Laptop din a mota, juyawa Jibril ya yi ya koma ciki gurin mutumen dazu.
“Please ko kaji inda zata je? Ko kuma inda hadarin ya faru?”
Mutumen da dan yi shiru sannan ya daga masa kai.
“Ee na ji ta ambaci Specialist Hospital gaskiya ina jin ko can aka kai yaron ko kuma can hadarin ya faru”
“Thank you”
Ya juyo da sauri ya nufi gurin motarsa, driver seat ya nufa ya ce direban ya fita ya hau achaba shi akwai inda zai je, @360 ya fisgi motar kamar zai tashi sama, wani irin vibration jininsa yake yana jin kamar ya runtse ido ya gansa a cikin asibitin.
“Dan ta...”
Yana ta maimaita hakan ya iso Abuja road sai ya dauke hanyar da zata sada shi da Specialist, gudu yake sosai kamar dan shi aka yi titi ko kuma ance masa babu ababen hawa sai nasa kadai.
Lokacin da zai kunna kai a gate din Specialist din sai da ya yi kamar zai buge wani magidanci da ke kokarin fitowa.
Ko fakin din kirki be yi ba ya fito yana ta waiwagen inda zai shiga, tsabar rude daman can sau daya ya taba shigo asibitin loacin da yake farkofarkon zuwa sokoto sika yi wata mata tiyata.
Da sauri ya nufi emergency wajen yan hatsari, har ciki ya karasa ya karasa inda Nurses suke ya muna masu id cart dinsa sannan ya soma tambayarsu ko an kawo wani.
“Eh an kawo mutun daya yanzu”
“Zai kai minti nawa?”
“Ten haka yanzu yanzu”
“Babba ne ko yaro?”
“Gaskiya dattijo ne”
“No wanda na ke nema karamin yaro ne yana tare da mamansa ina jin za ayi awa daya yanzu da kawo shi”
“Eh an kawo wani yaro dazu, yana ciki bayan shi ma an kawo wani”
Dayar Matar ta fada.
“Bari na duba”
Ya nufi ciki da sauri ya soma bin dakuna, sai gashi ya hadu da wani likita abokinsa. Shi ya rike Jibril dan hankalinsa gaba daya sama yake baya ganin kowa.
“Jibril”
“Dan Allah wani yaro na kr nema wanda aka kawo ya yi hatsari dazu”
“Yaro ne sosai?”
Ya dan yi shuru yana tunanin ta yadda zai amsa tunda ba sanin yaron ya yi ba.
“Yeah yeah yaro ne”
“Akwai wanda aka shiga tiyata da shi yanzu akwai kuma wanda ya rasu dazu, amman ba a fita da gawarsa ba saboda basu biya hospital bill ba”
“Wait...”
Ya fada sai ya fiddo wayarsa ya kira Nawwara duk da yasan ba zata bari ya karaso ba, ringing biyu aka daga da muryar Sakina tana masa sallama.
“Ina Nawwara?”
“Bata da lafiya”
“Wacece ke?”
“Ni kanwarta ce”
“Kuna ina ne Nawwara tana ina”
“Muna nan asibiti?”
“Wani waje?”
“Dakin Balaraba”
Ya katse wayar yana kallon likitan.
“Ina ne sashen balaraba?”
“Ta can ne, ko shine yaron da ake neman jininsa aka zo diban na uwar ta suma?”
Jibril ya rike.
“Please zan iya ganin yaron”
“Yes this way, amman an shiga tiyata da shi gaskiya ba zaka iya ganinsa yanzu ba sai dai a jira ya fito”
Tare suka karasa sashen da ake yan tiyata, jikin Jibril sai rawa yake sosai ya so ya shiga amman likitan ya hanashi saboda tiyata ake masa kuma yasan irin matsalar da zai janyo matukar ya ce zai shiga yanzu.
“Ka yi hakuri da sun fito zaka ganshi”
Safa da marwa kawai jibril ya ke yana matsar hannunsa.
“Jini ma ake nema garin bada jinin ne Mahaifiyar yaron ta yi ta amai daman da kuka ta zo, sai gashi ta sume mana dole muka kaita sashem Balaraba, kakarsa taje ta siyo”
“Please Doc Ismail muje ka gwada nawa idan zai yi”
“Okay yaron ya ji ciwo sosai gaskiya ya zubar da jini, amman yaron ka ne ko naga kuna da kaman sosai kuma yadda ka tashi hankalinka haka...”
Be gama maganar ba Jibril ya rike shi
“Da gaske muna da kama? Da gaske?”
Ya gyada masa kai cike da mamaki, ko da suka karasa lab Jibril be sani ba saboda hankalinsa yana can gurin tunani. Sai da aka dibi jininsa kadan aka gwada ya bada result iri daya da na Noor sannan Doc Ismail ya kawo masa, Jibril na ganin takardar hawaye suka fara masa zuba jikinsa ya yi mugun sanye, sai da ya karantar result din ya fi a kirga sannan ya yarda da duniya yake, fashewa ya yi da kuka sai kuma ya yi saurin guntse bakinsa tunawa da inda yake, saman table ya aje takardar ya nufi wani bangare na lab din hannayensa a baya yana jin wani irin abu marar misaltuwa.
“Doc Jibril ko ka fasa bada jinin ne?”
Sai ya juyo da sauri ya dawo yana share hawaye abunda ya bawa kowa mamaki, sai dai su abunda suke dauka saboda yaron ya ji rauni sosai ne yake hawayen, har wasu na cewa wai kamar ba namiji ba namijin ma kuma likita wanda be kamata aga yana kuka saboda sun saba ganin tashin hankali.
Dakin da ake dibar jiki ya shiga ya kwanta a saman kujerar nan mai kamar gado, aka saka masa abun diban jinin aka tasti leda biyu sannan ya tashi yana fadin.
“Doc Ismail muje yanzu ko sun fito”
“No Doc kai kansa kasan dole ka dan zauna yanzu na ga kamar a hankalinka a tashe yake”
Tashi tsaye Jibril ya yi da zimmar tafiya, ganin hakan yasa Doc Ismail ya bishi suka koma gurin tare sai suka tarar ba a fito da shi ba har yanzu. Sai kawai suka zarce inda Nawwara take domin itama yana da bukatar ganinta, basu sha wahala wajen nemanta ba saboda farko farko take. Irin dakinnan ne da ake jera masara lafiya dama da hadu, tana kwance saman gadon asibiti idanuwanta a rufe kamar tana bachi ga drip an daura mata a hannu, Sakina na zaune a kujerar da ke kusa da ita tana ta hawaye.
Kallonta yake sosai cike da tausayinta a nan Sakina ita ta samu damar kallonsa a take ta raya a zuciyarta cewar tabbas wannan baban Noor ne domin kamar har ta ba ce.
Zaunawa ya yi gefen gado yana ta kallon fuskar Nawwara kamar yau ya fara ganinta, can kuma ya dago ya kalli Doc Ismail dake ta faman kallonsa da mamaki ya ce
“A sama mata daki inda zata zauna ita kadai ta samu kulawa, if babu zan so ka mata transfer zuwa asibitina”
“No nan din ma akwai”
Gurin Nurses din ya nufa ya yi magana da su sai suka zo suka canja mata daki zuwa wanda take ita kadai sai dai shi kudinsa da daban ne. A nan ma ya dade yana kallonta sannan ya cire rigarsa yar sama kasancewar suit ne a jikinsa ya lulluba mata saman jiki.
“Ki kula da ita please”
Ya ce da Sakina sai kace ita Nawwara wata karamar yarinya ce. Tare suka fito da Doc Ismail har suka hadu da wani likitan Jibril dai be bi ta kansa ba dan hankalinsa yana can gurin dan da aka ce na Nawwara ne.
Sun yi sa'a suna isa ana fitowa da shi dakin tiyata, Sai Doc Ismail ya tsayar da su saboda abokinsa ya samu ganin yaron, mutuwar tsaye Jibril ya yi a gurin idanuwansa suka cika da kwalla kamar ba namiji ba, be ankaro da nauyin da kafafunsa suka yi ba har sai da ya daga kafarsa daya ya taka zuwa gurin gadon da Noor yake kwance.
Sama yake kasa yake duniya yake lahira yake? Sai ya kasa ganewa iyakar abunda idanuwansa suke kallo kamaninsa dake zuba a fuskar Noor, yasan ba mafarki yake ba kuma idanuwan ba gizo kuke masa ba, abunda yake gani zahiri dake shiga har cikin kwakwalwarsa, faduwa ya yi a gurin yana kuka muryarsa na karkarwa.
“This is my Son, ba ko tantama wannan da na ne, he's my Son jinina da na na cikina”
Hannu ya kai zai shafa fuskarsa da ke manne da bandeji sai yaji ya rike masa hannun cak....
____________________________
GOOD NIGHT HABIBATIES 😘😍
Duk Inda Masoyan RAI BIYU Suke Ina Gaishesu Ina Muku SON SO FISABILILLAH ❤ Na yi Wannan guntun Page din ne saboda ku 😍😘
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣3⃣
Dago kai ya yi da sauri domin ganin wanda ya hana hamnunsa zuwa ga gudan jininsa, ganin Nawwara cikin bachin rai da daure fuska yasa shi mikewa tsaye sai ya kama duka hannayensa biyu yana kuka kamar zai narke a gurin.
“Naw.....”
Fisge hannayenta ta yi ta ture da dukan karfinta.
“Karka kuskura ka taba min ɗa, hauka ta daina dibanka kana taba jikina ni ba halalinka ba ce”
Ta fada cikin wani irin zafin rai. Doc Ismail ya karasa ya rika Jibril yana kallon Nawwara tare da fadin
“Amman ke baki da mutunci ta ya zaki wulakanta babban mutum kamar Jibril a gaban mutane”
“Babu ruwanka karka saka min baki a nan”
Jibril ya share hawayen da suka ki tsaya masa ya nufi gurin Noor sai ta tsaya masa tsawa hawaye na zuba a idanuwanta.
“Karka taba min yaro”
Rike shi Doc Ismail ya yi ya ce da Nurses din su wuce da Noor, a gurin Nawwara ta zube kasa saboda jirin da ya dibeta, Doc Ismail ne ya kira wasu Nurse suka kamata suka mayar da kin da ta baro. Hakan ya bawa Jibril damar shiga dakin da aka kai Noor. Ko da ya shiga ya samu Nurses din suna daurashi saman gadon sannan suka saka masa robar jini daya. Fita suka yi daga dakin baya sun gama komai sai Jibril ya karasa inda yake ya durkusa kasan guiwowinsa gurin gadon wasu sabbin hawaye suna zubo masa.
Ko da bachi yake ya farka ya kalli Noor yasan dan sa ne, fuskarsa ce shinfide a fuskar Noor babu inda Noor ya rage shi da komai, hannu ya kai ya rika hannun Noor sai yaji wani irinsa ya shiga hannunsa jini ya hadu da jini Noor din ma da be san inda hankalinsa yake ba sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Kuka Sosai jibril ke yi irin kukan da aka san mata da yinsa, sai kuma yaja hannun Noor ya kai a fuskarsa ya lumshe ido, yana ta goga hannun a fuskarsa, sannan ya yi masa kiss sai kuma ya soma shinshinar hannun kamar zai cinyeshi.
“Am sorry Son, ka yafe min na wulakanta akan haukana, mahaifinka ya tuba ya gane kuskurensa na yi nadama, ban san miya shiga kaina ba ban san miyasa na aikata ba, am really sorry for what i did, please forgive me”
Ya kara fashewa da kuka har numfashinsa na son tsayawa, shigowar Doc Ismail ne yasa shi tsagaita kukan ya dago ya kalleshi.
“Wai miyake faruwa ne? Miye alakar ka da wacan matar ne? Na san dai wannan ba dan ka ba ne ko?”
Tambayar da Doc Ismail ya yi masa kenan.
“Dana ne, ita kuma mata ce”
Daga haka Doc Ismail be kara cewa komai ba, yasan Jibril baya cikin yanayin da zai iya yi masa bayanin komai a yanzu, after that be kama ya saka kanshi akan matsalar iyali ba. Juyawa ya yi ya fice zuciyarsa cike da mamaki bakinsa kuma gumde da tambayoyi.
NAWWARA POV.
Ban san iya awanin da na dauka a sume ma ba, ina farkowa na ji goshina ya cika da nauyi har bana iya gani sosai.
“Sannu”
Muryar Inna ce take gaisheni sai na gyada mata kai dan bana iya magana a wannan lokacin, na dade ina kallon silin sannan idanuwana suka dawo daidai har ya kalleta.
“Ina Noor?”
“Yana can an kaishi wani dakin”
Sai a yanzu na tuno da abunda ya faru, ashe fa wannan suma ta biyu ce na yi.
“Inna miyasa kike bari Jibril ya zo har ya ga Noor”
“Ba zan iya ce miki ga dalilin zuwansa ba, ban kuma san ta ina ya ji ba, nima na tafi neman jini ko da na dawo na tarar ya bada jininsa kuma ya sa an canja miki daki an dawo da ke a nan, shi kuma yasa aka kai shi dakunen nan masu tsada”
Na yi sauri sauka saman gado duk da ina jin jikina kamar babu gwari sosai. na fita daga dakin na mike hanya har na isa manyan dakunan, na bude na farko ba shi bane na biyu ma haka na uku hudu biyar haka na bi dakunan sai da na kai daki na bakwai ina turawa sai na hango Noor kwance Jibril kuma zaune saman kujera ya dora kansa gurin jikin Noor hannun Noor kuma a saman kansa dayan hannunsa kuma na sanye cikin na Jibril.
Ban damu da na rufe kofar ba na karasa kusa da gadon cike da tausayin halin da Noor yake ciki, ina tsayawa dai dai kan Jibril sai ya bude idanuwansa da suka kumbura suka ja a hankali ya kalleni, sai kuma ya lumshe.
“Jibril tashi ka fita”
Na fada a tsawace, sai ya bude ido ya yi ma hannun Noor kiss sai ya sake shi, na yi zaton tsaye zai tashi sai kawai na ga ya zube kasan gwuiwowinsa ya fashe da kuka yana hade hannayensa.
“Ki dubi girman Allah Nawwara, ki sassautawa zuciyarki dan Allah ki yafe min, Wallahi na canja dabi'u da halayya duka na canja ki ceci raina kuma ki ceci ran yarona ki taimakeni ki yafe min ba ni da wani buri da ya wuce na ki da na wannan dan nawa, please Nawwara for the sake of our Son ki hakura mu sake sabuwar rayuwa, zuciyata na cike da kuna ina bakincikin abunda na yi muku, kaina a kasa yake ki taimaka min ki bani damar da zan gyara laifina, ba ni buri sai na ki, ki min masauki a gefen zuciyarki dan Allah Nawwara”
Hawaye na zuba a idanuwansa yake min wannan rokon da ya soma karyar da zuciyata, nima na fara hawaye.
“Bata lokacinka kawai kake Jibril, ka fitar da ni a ranka ka manta da ni a duniyarka, kai ba tsarata ba ne, na rumtse ido daga kallo duk wani abu da ya shafi rayuwata”
“Ji ceci rai Nawwara, idan yanzu na fadi na mutu ke ce sila, ki taimaka ko dan dan mu”
“Dan mu? Ko da na? Dan da ka ce ba naka ba ne? Ka wulakanta ni saboda cikinsa? Dan da tun da ka turo ni gidanmu ba ka taba saka kafarka ka zo duba shi ba? Dan da baka san cin sa ba baka san shansa ba? Dan da baka san ya rayuwarsa ta ke ciki ba? Dan da ka kasa yankawa ragon suna kasa a ka kirashi da shege? Mahaifina shi ya yanka masa rago ya saka masa suna, yanzu har kana da bakin da zaka kira shi da danka? Kana da idon da zaka zo rana tsaka ka kalleshi kuma ka fada masa kai ne mahaifinsa? Ta wace fuskar zai kalleka? Taya zai kiraka Uba?”
Tun da na soma magana ya rumtse ido ya matse hannayensa da ke hade guri daya yana cizo baki, da alama maganar tawa bata masa dadi, sai kuma ya dago fuskarsa da ta yi ja ya kalleni.
“Fada min abunda zan yi wanda zai sa ki yafe min, fada min tafarkin da zan bi Noor ya karbe ni a matsayin ubansa? Taimakeni Nawwara, ki tausayawa rayuwata zan yi komai kike so am ready to die for you”
“Ka wuce sanina Jibril, kaje ka nemi matar da zata so ka ta aureka ta haifa maka yaya, shawara daya zan baka kaje ka yi abunda zai taimaki rayuwarka ina maka fatar samun irin matar da kake so Allah baka sa'a”
Mikewa ya yi tsaye ya fice cike da nauyin kafafu, ba tare da ya share hawayen da ke fuskarsa ba. Ni kuma na zauna kusa da dana ina kukan da ban san na minene ba, tausayin da na ko kuma rayuwar da na cinci kaina a ciki.?
Bayan sallah isha'i Jidda da mahaifiyarta suka zo duba Noor, daman tun da magariba wasu daga cikin mutanen babban gida suka zo duba shi. Bayan fitarsu sai ga Bilal ya shigo hannayensa da ledoji har gudu hudu har kuma lokacin Noor be farka ba gaba daya hankakina ya tashi duk da likitan ya fada min zai dauki tsawon lokaci yana bachin. Kallo daya na yi ma Bilal na kawar da fuskata, bana ganin komai sai wacan abun da ya faru shekaranjiya wani irin kishi da bakinciki sai suka taro min har na ji kamar na dauki wukar da aka aje ta yanka lemu na daba masa a kirji.
Da Inna ya fara gaisawa sannan ya gaishe da wata abokiyar Inna suka gaisa da Sakina, sai duk suka tashi suka ba mu guri, daya ya zama daga ni sai shi sai kuma Noor da baya cikin hayyacinsa.
“Nawancy... Wallahi ba abunda kike tunani ba... ”
Hannu na daga masa
“Kai ko Zinatu ko wani abu da ya shafi rayuwarku a yanzu be dame ni ba”
“I know i shouldn't, ya jikin Noor?”
“Da sauki”
“Allah ya kara sauki”
“Amin”
Bayan wannan bata maganar bata sake shiga tsakanin mu, da ya gaji da zama ne ya mike tsaye ya karasa kusa a Noor cike da nuna kulawa ya duba shi sannan ya kalleni ya ce
“An kama wadanda ya kade sa?”
“Ya gudu, amman mutane sun ce da gangan mutumen ya yi cikinsa da mota ya kadesa, kuma likitan ya ce min Noor ya karye a hannu”
Na fada ina fashewa da kuka.
“Sorry a wani waje ne?”
“Sun taso makaranta ne, mutunen ya gudu”
“Amman Mahaifinaa ya sani?”
Wani kallo na watsa masa na sakar masa idanuwana ina ta kallon fuskarsa cike da tsanar furucinsa.
“I mean Jibril”
“Kaima kana cikin mutanen da je ganin laifina akan Jibril ko?”
Yayi saurin komawa ya zauna.
“No ba hakan na ke nufi ba, Jibril ya wulakanta ki Nawancy kuma ya cancanci ko wane irin sakamako daga gareki, Wallahi ko ke ce baki da gaskiya i will support you ballantama kina da gaskiya, kawai bana son abubuwa su miki yawa ne, tunani a yanzu ba na ki ba ne, ki sassautawa zuciyarki, kuma ki rika neman shawara akan abunda ya shige miki duhu”
Na share hawayena na maida idanuwana gurin da na, sai na cinkayo muryarsa yana fadin.
“Ni kaina ban san ranar birthday dina yayi ba, sai a Facebook, su suka turo Zinatu kuma friend dita ce a fb few weeks ago ta turo min friend request na yi accepting ba tare da tunanin komai ba, ta yi min happy birthday tun ana saura kwana daya na yi birthday na, ina tunanin ta nan ta gane xan yi birthday a ranar har ta siyo wannan cake din, ina zaune ta shigo da shi ta kira abokan aikina ban ma san ta kira ki ba sai da na ganki office din”
“Mi zai sa ta yi haka? Daman can tana son ka?”
“Gaisuwa bata taba shiga tsakanin da Zinatu ba, idan har kiga na mun hadu sai idan aiki zamu yi, ina tunanin ta yi hakan ne saboda ta shiga tsakaninmu ko kuma...”
Sai ya yi shiru be karasa ba.
“Ko kuma me? Jibril ne ya sata ko? Zai iya saboda mugu ne”
“Ni dai iya abunda na ke son ki sani, ba zan taba cin amanarki ba”
“Amman miyasa ka yi blocking din number ta? Kuma ina ta tura maka sako baka min reply”
“Saboda na baki damar yin tunani da zuciyarki, ina ganin kamar ina kan hanyar da ba zata bulle ba ne, zuwan Jibril a karo na biyu cikin rayuwarki ya karyamin kuzari, bana son na shiga tsakanin farincikinki da kuma tunaninki, bana son na yi abunda zai raba hankalinki gida biyu, na yi hakan ne saboda na daga miki kafa kuma na samawa rayuwata mafita saboda bana so na rasa a take, zuciyata na raya min kamar ba zan aureki ba Nawancy, kin ki bani damar da zan ga magabatanki kuma gashi Jibril zai yi duk abunda zai yi wajen ganin ya mallakeki”
Tausayinsa ya kamani, duk da kasancewar ni ma ina tausayin kaina.
“Kokarin mallakata yake Bilal kai kuma tuni ka malleke zuciyata, idan har Nawwara bata auri Bilal ba to ban cancanci auren ko wane irin namiji ba a duniyar nan, na fara rayuwa sau daya sai kuma na mutu, kai ne ka dawo da ni duniyar da mutane suke rayuwa, ka yi nasarar canjani daga mutum mutume zuwa mutum wacce ta san mi ake nufi da rayuwa, na rayu a lokacin da rayuwa take da muhimmanci a gareni, sai Jibril ya kashe min ruhi kuma ya kona shi ya maidashi toka ya shekarda da shi ya bi iska, kai ne mutumen da ka hada tokar ruhina ka tattarata ta sake zama cikakken ruhi na maida shi a cikina, har zuciya ta bude ta kamu da son ka.
Kai ne kadai mutumen da nake so Bilal kai ne mafarkina, burina idan har ka ga ban aureka ba ka tabbatar gawata ce ta ke magana ba ni ba”
Lumshe ido ya yi ya hade yawu sannan ya bude kamar dai be yarda da ni ba, sai ya mike tsaye yana fadin.
“Idan kina bukatar wani abun ki fada min, ko ki kirani, ina son ki san da wannan Nawancy ina sonki sosai ina kaunarki kauna ta hakika”
Da kallo na bishi har ya fice, sannan na juyo ina share hawayena na kalli Noor da ke motsi.
_______________________________
I dedicate this chapter to my wattpad people 😘😘😘
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣4⃣
Bayan fitar Bilal su Inna suka shigo tare da Mama Turai wato Yayar Inna wacce suke uwa daya uba daya. Inna ta zauna saman tabarma ita kuma ta zauna saman kujerar da ke gefen gadon ta Kalli Noor sannan ta kalleni ta ce.
“Innarki ta labarta min komai, kuma abunda kike ba ki kyautawa, tun da har ya tuba ya dawo ya nemi ganin dansa ai sai ki bashi dama, ke yanzu in ban da Allah ya nufa ko hanya kin isa ki hada da babban mutun kamar wannan balle har ya zo yana rokonki? In wani ne karbe dansa zai yi da karfi ya barki nan, kin samu ya dawo yana neman yafiyarki kina ta masa wasa da kwakwalwa kamar karamin yaro”
Na tada kai na kalleta.
“Ke ma laifina kike gani ko Mama Turai?”
“Ai dole na ga laifinki, mutumen arziki irin wannan mai kudi haka, ai sai ki bashi dama ko arzikin nasa ku tatsa ni Wallahi da yana son yata da na aura masa mu ga karshen iskanci”
“Amman yanzu har kun manta irin cin mutuncin da cin zarafi da ya yi min?”
“Yanzu ba ya dawo ya tuba ba? Ai Allah ma mukan masa laifi ya yafe mana balle ke da wani be san da zamanki a duniya ba, ke kikan irin laifin da kike yi ma Allah ne?”
Idanuwa sun cika da kwalla saboda na san babu wanda zai fahimce balle ya goya min baya, ni kadai na ke jin abunda na ke ji wata kila saboda ni Jibril ya yi ma abun ba kowa ba. Wannan karon Inna ce ta dora da
“Idan har sakamakon Ubangiji kike so tau ko ya kamata ki mika lamurranki gurinsa, ba yin kanki ba ne Allah ne ya jarrabeshi da sonki kuma ya saka masa nadamar abunda ya yi saboda ya jarrabeshi, ki yanzu ba jindadinki ba ne mutumen da ya ce Noor ba dan sa ba ne yanzu har yake risina miki kasa yana neman ki hada shi da dansa? Allah yana son masu yafiya, kuma ba a rama cuta da cuta sai dai a maye cuta da alheri, ina ji miki tsoron kar wannan abun ya dawo kanki, kuma da Noor ya girma ya nemi ubansa ai kara ya girma da Ubansa”
Ganin yadda na ke sharar kwalla yasa Inna ta taso ta dafa.
“Na san ya cutar da ke yata amman karki mata shi ma Allah ba zai barshi ba, kuma ba kisan halin da ya shiga ba kamin ya gane cewar ke alheri ce a gareshi, ba dan Jibril yana da arkizi na ke son ki yafe masa ba, sai dan hakan zai wanke ki daga zargin da duniya take miki, kuma Noor zai samu rayuwa mai kyau, ke kuma zaki samu damar gina taki rayuwar a gidan aurenki idan kika auri wanda kike so”
Bani da wani zabin na yafiya ga Jibril saboda yadda Inna take son na yafe masa din, na kan yi kokarin yin abunda duk mahaifiyata take so ko kuwa abun nan baya min dadi, ba dan komai ba sai dan na san ba zata cutar da ni ba, kuma yarda Allah tana tare da yarda iyaye, na yi ma uwar wasu biyayya ma balle tawa uwar wacce ta dauki ciki ta yi nakuda ta haifeni ta raineni na girma, hakika bana da wani farinciki sai na mahaifiyata.
“Zan yafe masa Inna matukar yafe masa din zai faranta ranki, zan yafe masa”
“Na jidadi Allah ya miki albarka kema ya baki yayan da zasu yi miki biyayya”
Ajiyar zuciya na sauke na share hawayen da ke min zuba ina kallon Mama Turai da ke wasar baki.
“Haba ko ke fa, amman ace zuciya kamar ta kafiran farko, Allah ya shiga ya tsakaninku ai mun fi son a shirya”
“Dan na yafe masa ba yana nufin zan aureshi ba ne, dan Allah karku tirsasamin yin wani abun daban kuma”
“Babu wanda zai tirsasa miki, wata rana ke da kanki zaki karanta mana sirrin zuciyarki”
Cewar Inna, ni kuma na kalleta na ce
“Zuciyata bata da wani sirrin bayan wanda ke zahiri ke kanki kin san babu wanda na ke so bayan Bilal, be kamata ki zargeni da son wani bayan shi ba”
Sai Mama Turai ta taso ta karaso kusa da ni tasa hannunta ta tallafo fuskata yadda zan fuskanceta.
“Tausayin Bilal kike Nawwara amman asalin son yana gurin Baban Noor, ke kanki ba ki san abunda ke damunki ba a yanzu, kina tausayin Bilal amman ba za ki iya aurensa ba, kaddarar da ta hada ku ba zata iya bari ku yi aure ba, saboda ke makwafin RAI BIYU ce a gurin Baban Noor idan babu ke koda ya samu Noor rayuwarsa bata kammaluba, haka ma Noor kina matsayin RAI BIYU a gunsa matsayin uwa kuma uba, babu rabon Bilal a jikinki shiyasa kika kasa bashi dama, Baban Noor kuma be da rabo a jikin kowa ce mace sai ke shiyasa kaddara ta sake hada ku kuma zuciyarsa ta kasa barinsa zama lafiya har sai ya nemo mata yar'uwata, ke ma kuma baren zuciyarki yana gurin Noor da Babansa wannan yasa har gobe ba zaki iya amsa kanki a matsayin cikakiyar mace mai jin kanta a mace ba, kika kasa bawa kowa damar sake aurenki gashi Baban Noor ya dawo.
Wani baya auren matar wani Nawwara, da kika auri Faruk baki haihu da shi ba ya mutu ya barki saboda Baban Noor ya samu damar sake aurenki, ko da kin haihu da Faruk sai kin fito saboda kaddara ta yi niyar hadaki da tsohon mijinki Nawwara, kurciya ce take cin ki ke kanki yanzu baki san abunda kike so ba, da yanzu za a daura miki aure da Bilal da ba zaki iya zaman aure da shi ba saboda ba shi zuciyarki ke so ba, kuma kaddara ba zata barku ku yi zaman aure ba, ya kamata ki yi tunani karki aikata abunda zai cutar da ke”
Tana gama fada min haka ta kalli Inna ta ce.
“Ni na tafi Allah ya ba Noor lafiya”
Binta Inna ta yi suka fita tare suka barni a dakin ina faman hawaye, ba zan iya bari kalaman Mama Turai su yaudari zuciyata ba, tabbas ni dai na san Bilal na ke so kuma shi zan aura, ba zan zargi Inna ma domin nasan bata cikin irin mutanen nan da ke son yayanta su auri mai kudi, amman wani lokacin ina ganin kamar saboda Jibril yana da kudi ne yasa take son shi, duk da kasancewar Bilal ba talaka ne talak ba, yana da aikinsa kuma ya yi karatu familynsa ma suna da rufin asiri, amman zuciyar Inna ta fi karkarta gurin Jibril.
Motsi Noor ya sake yi a karo na biyu har yana kokarin bude idonsa yana motsi da hannu.
“Momy... ”
Na yi saurin share hawayena na kama hannunsa.
“Na'am Noor sannu ka ji”
“Momy da zafi sun jimun ciwo sosai”
“Kyalesu Allah ya isar maka ya baka lafiya”
Ya kalleni da idanuwansa da suka yi fari sosai, sai kuma ya kalli gefena.
“Momy na yi mafarkin Babana ya zo nan”
Gabana ya fadi.
“Wane Baba kuma?”
“Wanda ya rasu”
Ajiyar zuciya na sauke.
“Wanda ya rasu ai baya dawowa Noor, mafarki kawai ka yi”
Na shafa kansa sannan na mike na fita dan kiran likita.
JIBRIL POV.
Da taimakon Allah ya isa gida, zuciyarsa ta yi masa mugun nauyi, ko parking din kirki be yi ba ya fito ya nufi main house jiri na dibansa, yana shiga falo na fadi a bakin kofa yana tari a wahalce gubar da ya taba ci ta taso masa ta hadu da dattin cocaine dake cikin huhunsa (lung) sai aman jini, har idanuwansa suka canja kala kamar ba zai rayu ba, gashi falon babu kowa sai shi kadai. Tun yana iya gani har ya koma yana gani dishi-dishi sai kuma numfashinsa ya soma nisa hankalinsa ya ba ce 6at.
Ko da ya farka an dora masa kyalle mai sanyi saman kai, yana kwance saman doguwar kujera, Siraj na zaune kusa da shi Zinatu kuma na fuskantarsa fuskarta dauke da tausayinsa. Unkurawa ya yi ya tashi zaune sai ta yi hanzarin miko masa ruwan gora mai sanyi ya karba ya sha.
“Yaushe kuka shigo?”
“Tun dazu, gashi har an yi magariba kana sume, Zinatu ce ta gyara gurin kuma da taimakonta muka doraka saman kujerar nan”
Cewar Siraj, sai Jibril ya tada kai ya kalleta ya ce
“Thank you”
“Never Mention Allah ya sauwake ni zanje gida”
“Ba zaki bari na sauke ki ba?”
Ta kalli Siraj da ya yi maganar ta ce
“No zan je da kaina ya kamata ace ina gida by this time, ka kula da abokinka please”
Daga haka ta dauki jakarta ta rayata ta fice, sai Jibril ya unkura zai tashi kirjinsa ya yi masa wani mugun tsuka hakan yasa shi saurin komawa ya zauna yana yar kara.
Siraj ya dafa shi.
“Ka bari ka kara hutawa mana, Jibril kana matsawa kanka da yawa akan yarinyar nan, direban ka ya fada min ka bi bayanta sai kuma na zo nan na sameka cikin jini, ka rika sassautawa kanka dan girman Allah ina tausayin halin da kake ciki”
Jibril ya kalleshi irin kallon nan da shi kadai ya san fassarasa.
“Miyasa ka ce min ba ni da Nawwara? Bayan kuma ina da shi”
Siraj ya hade yawu da karfi.
“Wane irin kana da shi? Ban fahimce ka ba”
“Na ga dana da idanuwa Siraj dan da na haifa da Nawwara dan me zaka boye min?”
“Wace riba zan ci idan na boye maka? Mi zaisa na boye maka? Amman ka tabbatar dan ka ne?”
“Da na ne, jinina da nasa iri daya ne, kamata da tasa iri daya ce, da ace ba a kade shi ba da ba zan samu ganinsa da wuri ba”
“Amman abun nan ya bani mamaki, sai gaskiya akwai wani a abu a kasa, domin wanda nasa na bincika mana ba zai yi karya ba, shi ya fada mana Nawwara bata da da ko daya, sai idan mutumen dan uwanta ita kuma ta nemi ya boye mana din”
“Taya xaka yi bincike kuma ka nemi dan uwanta? Dan ina ne mutumen?”
“Dan unguwarsu ne, amman abun nan ya bani mamaki amman ka bincike Nawwara ta tabbatar maka da danta ne? Shin yana ma raye?”
“Yana raye wani ya kade shi da mota, and nayi duk wanda ya taba min yaro ko da Nawwara ce ba zan kyale ba”
Siraj ya karkato ya kalleshi
“Amman idan kaddara ce fa?”
“Ban san kaddara akan da na ba, da ce ni ta mai motar ya kade zan dauka ko amman da na? No never da yanzu na rasashi fa? Kasan halin da Nawwara zata shiga ko kasan halin da ni zan shiga? Who's ever that person is i will never forgive him”
Wani gumi ne ya soma saukowa Siraj, Jibril kuma ya mike tsaye yana jin zafin da kirjinsa ke yi ya nufi bedroom dinsa, saurin mikewa tsaye Siraj ya yi ya rufa masa bayan.
“Yanzu ya zaka karbi danka hannun Nawwara?”
“Shine abunda na ke tunani, zan yi duk yadda take so wajen ganin ta bani da na”
“Ni abunda na ke tunani mai zai hana ka fara fake love da Zinatu, so that ka samu kan Nawwara kuma ka gane idan har yanzu akwai soyayyarta cikin ranka”
Jibril ya kalleshi
“Wani lokacin kana yin abu kamar baka san waye ni ba Siraj, am straight forward, if yes yes if no that's means no for sure”
“Baka fahimta ba ne Jibril ai fake love na ce, kuma da sani Zinatu zaka yi”
“Ba zan yi ba, ka tafi kawai zan samawa kaina mafita”
Cikin sanyin jiki Siraj ya juya har zai fita sai kuma ya juyo ya kalli Jibril ya ce.
“Cocaine...”
“No please bar ni na ji da abunda ke damuna”
Ya fada yana daga masa hannu, sai Siraj ya juya kunya kunya da shi ya fice. Bathroom Jibril ya shiga ya sakarwa kansa ruwa sosai sannan ya yi wanka gaba daya tare da alwala ya fito, ya saka jallabiya ya rama sallah la'asar ya yi magariba, yana saman carpet din har aka kira isha'i, bayan ya yi ya taso ya dawo parlor ya shiga kitchen ya hadawa kansa ruwan tea. Sai kuma ya dawo falo ya zauna hoton Noor kawai idanuwansa ke nuna masa, sai ga wayarsa na ringing sai a lokacin ya kula da inda wayar take gefen kofa inda ya fadi dazu. Zuwa ya yi ya dauka sai yaga number Abbah. Gaiswa suka fara yi da Abbah kamin ya rufe shi da fada.
“An fada min baka da aiki sai shan cocaine, ka maida kanka wani kalar mutun, idan ba zaka iya ba zan karbe ragamar kamfanin nan na mika a hannun Siraj tun da ya fika kula”
“Waya fada maka ina shan cocaine Abbah”
“Kai ka fada min, kai kullum abun ka gaba yake ba baya ba”
“Ka yi hakuri Abbah zan canja”
“Da ya fi maka”
Daga haka Abbah ya kashe wayar. A ranar Jibril be gi bachi ba sai ya tashi ciki dare yana ta sallah nafila abunda be taba yi ba a tsawon rayuwarsa, kuka ya yi sosai ya kaima Allah bukatarsa, shiriyace a cikin abubuwan da ya fi roko sai kuma Nawwara, da asuba ma bayan ya yi sallah asuba ya dora da istigifari yana kankantar da kansa yana neman Allah ya yafe masa.
Washe gari ya kira wani abokinsa ya hada shi da mai tattoo ya zo har gida ya wanke masa tattoos dake wuyansa da kuma na sunan Nawwara da ke hannunsa.
Bayan mutanen ya fita ya shiga kitchen ya soma kansa kwai duk da yana da kuku be nemi ya yi masa ba sai ya hada tea da kansa, a dinning room din kitchen ya zauna yana ci sai ga Siraj ya shigo, bayan sun gaisa ya zauna shima ya zuba ma kansa yana ci, bayan sun gama ya budewa Jibril cocaine. Sai da Jibril ya yi kamar ba zai sha ba sai kuma shaeidan ya zugashi ya dauka ya shaka sosai, sannan ya mike tsaye yana fadin.
“Ba zanje office ba, ka yi duk abunda ya dace, Nawwara ma ba zata je ba, saboda dan mu ba lafiya”
Be jira abunda Siraj zai ce ya fito daga kitchen din na nufi bedroom dinsa. Saman gado ya kwanta ya rika bachi kamar wanda ya mutu, be farka ba sai da aka yi sallah azahar. A daren ranar ma sai da Jibril ya raya shi da nafila yana ta rokon Allah ya karkarto masa da hankalin Nawwara kuma ya shiga tsakaninta da duk wani mai son ta bayan shi, abu daya yake ce masa tuwo a kwarya a yanzu ba komai bane face rashin iya karatun kur'anen, haka zai dauko kur'anen ya rike but he can't read it ko baki be iya hadawa balle har ya tada ya karanta aya, and now he need to know his religion more than everything, yana son yasan abunda Allah ya ce da kuma wanda ya hana, zuciyarsa na raya masa idan har ya shiryu ya zama na kwarai Nawwara zata so shi, a duk lokacin da ya tuna da dansa yana asibiti sai ya ji kamar zai mutu saboda yana son naje ganinsa sai dai yasan Nawwara ba zata bari ba. Haka ya jera kwana uku be sake saka Noor a ido ba a duk lokacin da tunaninsa ya taso masa sai ya dauki cocaine din ya sha sannan ya samu sassauci.
Misalin karfe biyu dare yana zaune saman carpet yana istigifari sai ga Abbah ya kirashi, da fari ya ji tsoro dan yasan Abbah be saba kiranshi a irin wannan lokacin ba, sai kuma daga baya wani tunanin ya zo masa na cewar wata kila Abbah zai masa fada ne akan rashin zuwa aiki da ya yi kwana biyu.
“Hello”
“Jibril kana lafiya?”
“Lafiya kalau Abbah”
“Ka tabbata?”
“Lafiya ta kalau”
“Allah ya tsare ka, kawai na yi wani mafarki ne marar kyau ina fatar babu komai ko? ”
“Babu komai Abbah sai damuwa, Nawwara ta ki fahimta ta Abbah kuma akwai da a tsakaninmu”
“Ni ma na samu wannan labarin lokacin da na je zan bawa iyalanta da kuma ita kanta hakuri akan abunda ka yi musu, sai dai ba samu ganin yaron ba”
“Abbah da gaske? Yaushe ka zo?”
“An kwana biyu, kawai dan ban fada maka ba ne”
Abbah ya labarta masa komai daga zuwansa da kuma abubuwan da suka faru, Jibril ya ji dadi hakan ya tabbatar masa da mahaifinsa yana sonsa kuma yana tare da shi.
“Abbah ka taimaka ka min izinin zuwa gidansu Nawwara Dan Allah”
“Ka yi alkawarin ba zaka yi wani abu marar kyau ba?”
“Taya mai neman hanyar gyara zai yi wani abu marar kyau? Wallahi Abbah ina son Nawwara sosai kamar zan hauka ce”
“Amman da muka zaba maka ita ai cewa ka yi baka son ta”
Ya yi shiru be ce komai ba, sai Abbah ya kara da
“Kuma kasan sai dai ka yi hauka dan babu aure a tsakaninku ko? Kasan saki uku ka yi mata fa”
Idanuwansa sun cika da kwalla.
“Yanzu Abbah babu wani gyara da za a iya yi? Ba wata mafita?”
“Babu zan kwanta sai da safe”
Abbah ya kashe wayarsa, sai Jibril ya fara surutai
“Dole akwai mafita Wallahi, dole a samu mafita No no no”
Wannan tunanin ne ya hana shi bachi har garin Allah ya waye, tun da asuba ya shirya ya fita, kai tsaye asibitin ya nufa. Ya taki sa'a yau Nawwara ce kwana asibitin, ko da ya tura kofar dakin ya shiga zuciyarsa na bugawa dan ya yi tunanin zai samu Inna a ciki ne ko kuma ya tararda Nawwara a farke, sai ya tarar tana kwance bayan Noor saman gadon asibitin suna ta bachinsu a tare, karasawa ya yi kusa da su fuskarsa dauke da murmushi yana kallon iyalinsa. Wayarsa yasa ya dauke su hoto sannan ya cire jacket dinsa ya lulluba musu ya zauna saman kujerar da ke facing dinsu yana ta kallonsu cike da shauki.
“Na bata komai, da yanzu muna nan a iyali daya”
Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana Noor farkawa daga guntun bachinsa ba, sosai da sosai yake kallon Jibril ganin wani babban mutum mai kama da shi, sai kuma ya unkura ya tashi zaune zai yi magana Jibril ya dora hannunsa saman bakinsa ya yi masa alama da ya yi shiru.
“Shiiiiiiiiiiii”
Sai ya mika masa hannu alamar ya zo, ba musu Noor ya mika masa nashi hannayen sai ya dauke shi ya zaunar saman jikinsa ya rumgume ya lumshe ido. Hawayen farinciki da bakinciki suka cika masa ido lokaci daya.
“Waye kai kai likita ne?”
Noor ya tambaya da muryarsa yar karama.
Sai Jibril ya girgiza masa kai alamar a a ba tare da ya bude idon ba. Shi kuma sai ya sake tambaya cike da mamaki yana ta kallon fuskarsa.
“Kai ne wanda Inna ta ce min zaka zo ka ganki? Kai ne Uncle din?”
Ya gyada masa kai still be bude idon ba dan baya son Noor ya ga hawayensa, Nawwara kam bachi kawai take abinta bama san ana yi ba.
NAWWARA POV.
karar bude kofar da aka yi ne ya tasheni daga dogon bachin da na ke, sai turaren da na fi tsana a duniya ya yi marhaban sannan na kula da jacket din da aka lulluba min saman jiki. Inna na gani zaune tana jan karbi ba Noor a kusa da ni kamar yadda muka kwanta, saurin zabura na yi.
“Ina Noor?”
“Yana gurin Babansa”
“Dauke sa ya yi? Miyasa kika bari ya shigo?”
“Ke ya kamata na tambaya dan nan na shigo na sameshi”
Na sauka saman gadon hankalina a tashe sai Inna ta rike hannuna.
“Ba gudu zai yi da shi ba, sun fita waje ne su sha iska, ina tunanin ya canja Nawwara a nan ya durkusa yana ta ba ni hakuri, wannan abincin karyawar da kika gani daga kamfani yasa aka kawo”
“Wallahi zai iya gudun min da da mugu ne”
Na fita daga dakin hankalina a tashe, ina fitowa harabar asibitin sai na hango Noor saman motarsa zaune shi kuma na jikina jikin motar ya rumgume Noor. Karasa na yi ina masa fada.
“Waya baka izinin fitar min da da?”
Sai ya dago ya kalleni sai ya sauko da Noor da ko riga babu a jikinsa.
“Ki yi hakuri na fita da shi ne ya sha iska”
Daukar Noor na yi na koma da shi ciki, shi ko sai zuba min tambaya yake akan wannan Uncle din nasa da Inna take fada masa zai zo ya duba shi.
A ranar duk wanda ya kawo mana ziyarar dubiya ya tararda Jibril a asibitin saboda nan ya wuni, duk wani tafiyar numfashin Noor yana kula shi hannun kuma maikaraya yana kula da shi sosai, na yi mamakin da Zinatu ta zo ganin Noor ko da yake ba abun mamaki ba ne duba da Jibril yana cikin asibitin, yau kan Bilal dake zuwa kullum duba Noor ya tarar da Jibril wanda hakan yasa shi kin sakewa sosai daman kwana biyu nan na rasa gane kansa, hakan be min dadi ba dan ban jidadin ganin da Bilal ya yi ma Jibril a asibitin ba, ni kuma na raka shi har gurin gate din asibitin sannan na dawo.
A lokacin Jibril ne kawai cikin dakin Jibril ne kawai sai Noor suna rike da hannun juna, daman Inna waje ta koma da zama bata iya zama a cikin dakin matukar Jibril na ciki.
Kamar jira yake na shigo sai ya mike tsaye ya nuna ni da yatsa fuskarasa a kumbure saboda bacin rai ya ce.
“Kar Bilal ya sake zuwa duba min yaro wannan ya zama na farko kuma na karshe...”
Kallonsa na ke sai ma na rasa abunda zan ce masa, daman na san za a rina saboda ya tsargu da yadda na nunawa Bilal kulawa kuma ina ta masa kalamai masu dadi a gaban idonsa, sai dai mai? Ai be isa ya hana Bilal zuwa ganin Noor ba ko dan na bashi dama ya wuni da shi ya bashi damar samun guri har ya fada min wannan maganar? Bana son na yi wata magana a gaban Noor saboda kar ya fahimci wani abu, wannan yasa na kumde maganar da ke bakina har sai ya fita na bishi na fada masa.
Turo kofar da aka yi aka shigo ne yasa dukanmu muka kalli kofar Mustapha ne ya shigo cikin manyan tufafi tare da manyan ledoji Jidda na gafensa.
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣5⃣
MUSTAPHA POV.
Mustapha ya yi farincikin tararda Jibril da ya yi a dakin ko ba komai yasan Jibril ba zai jidadi ba, a farkon shigowarsa ya shigo da fargaba da kuma tunanin irin kallo da wulakancin da Nawwara zata masa, amman ganin Jibril ya sashi sakewa kamar daman can sun saba da Nawwara.
Murmushin fuskarsa ya fadada ya kunno kai cikin dakin tare da Jidda yana kallon Nawwara.
“Pretty ashe Babynmu babu lafiya, Wallahi ban sani ba sai jiya ya jikinsa”
Sai da Nawwara ta hadiye yawu sannan ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa.
“Da sauki”
Kana ta watsa ma Jidda harara. Kamar be san an hallici mutum a gurin ba haka ya bi ta kusa da Jibril ya karasa kusa da Noor ya dire ledodin da ke hannunsa.
“Cute Boy waya kade min kai”
Noor ya dade yana kallonsa kamin ya amsa masa bakinsa da nauyi.
“Nima ban san shi ba”
“Am sorry dear”
Ya fada yana zama kusa da shi tare da duba hannun sai kuma ya juyo ya kalli Nawwara.
“Pretty amman da sauki sosai ko?”
Nawwara kamar ba zata amsa shi sai dai ganin Jibril yasa ta karaso gurin tana fadin.
“Eh a hannu kawai ya kare”
“Wallahi ban sani ba sai dazun nan Jidda ke fada min”
Nawwara ta kalli Jidda sai Jidda ta dan zaro idon tana daga kafadarta.
“Ya matsa ne sai ya ganki kin san yadda yake damuwa”
“Sorry na zo ban fada miki ba”
“Ba komai”
Cewar Nawwara. Jibril ya rumtse ido ya sauke ajiyar zuciyar da ta mamaye masa kirji, sai ya juyo cikin facin rai ya ce.
“Ya kamata ku tafi yanzu, amman kai yaron nan i warning you karka sake shiga sabgar Nawwara ko ban fada maka ba”
Daga Nawwara har Mustapha da Jidda kallonsa suke.
“Waye wannan daman ka san shi ne?”
Jidda ta tambaya tana kallon Mustapha, sai Jibril ya yi cikinta kamar zai dake ta.
“Babu ruwanki a ciki”
Matsawa baya Jidda ta yi ganin yadda temper dinsa take, sai Mustapha ya taso daga inda yake zaune kusa da Noor yana murmushi ya karaso daf da Jibril ya soma gyara masa kwalar rigarsa.
“Ka kwantar da hankalinka Man, macece fa ba namiji ba kasan namijin da ya amsa sunansa namiji baya taba dukan mace, ko da yake kai ragon namiji ne, shiyasa kake duka kuma kake cin zarafin yarinyar nan marainiyar Allah, anya babu kai a cikin kashe mata mahaifi kuwa? Saboda na ga ka tsawwalla rayuwarsu ne da yawa ka siye gidansu... oops sorry na manta she's your ex...- ”
Ya karashe maganar yana murmushi. Jibril ya daga hannu cike da hasala zai naushi bakinsa sai Mustapha ya rike hannunsa cikin zafin nama ya kai masa na shi naushin a baki har sai da Jibril ya yi baya baya ya rike bakin.
“1-1”
Mustapha ya fada yana murmushin keta. Sai Nawwara ta katsa musu tsawa.
“Miye haka? Ya zaku rika yin abu kamar kananan yara?”
Murmushi Jibril ya yi ya kallon Noor da duk tsoro ya gama mamayeshi ya ce
“Wasa ne fa kawai karki daga hankalinki, amman ki fada masa karya sake zuwa kusa da yaro na”
“Ba dan ka na zo nan ba dan Nawwara ne, duk kuma abunda ya shafi Nawwara dole ne ya shafe ni”
Jibril be kara ce masa komai ba, domin yasan wani furuci na fitowa a bakinsa ba mai dadi ba ne, kuma baya son ya yi abunda be kamata ba a gaban dansa, sai kawai ya karasa kusa da Noor ya zauna yana shafashi tare da fiddo wayarsa ya kunna masa game.
“Mu zamu koma, daman na zo ne kawai ganin Noor Allah ya tsare gaba”
“Amin”
Cewar Nawwara, sai Jidda ta daga mata hannu.
“Zamu yi waya”
“Ok thanks”
Suna fita Mustapha ya fara tambayar Jidda labarin Jibril, sai dai bata fada masa komai ba saboda tana tunanin sirrinsu ne ita da Nawwara, but itama tana mamakin yadda aka yi Nawwara ta hakuru har haka ta bari ya zo ganin Noor.
“Amman shi Nawwara take so ko?”
Mustapha ya tambaya yana driving, sai Jidda ta kalleshi.
“Bata son shi, ni dai iya sanina Nawwara Bilal take so”
Kamar zai sake cewa wani abu sai kuma ya yi shiru, sai dai ransa yau yana cike da farinciki saboda abunda ya yi ma Jibril. A bakin kofar gidansu Jidda ya sauketa sannan ya juyo ya dawo gida.
Tun a yanayin shigowarsa ya tabbatarwa da Momynsa yana cikin farinciki, Daddy sa ma ya lura da hakan kasancewar dukansu suna zaune falo ne har su Ikram da Zarah suna kallo harin da aka kai Iraq a channel din Al Jazeera.
“Dad Mom barka da dare”
Sai da suka amsa masa sannan ya zauna saman cushion yana kallon tv kamar yadda suma suke kallo, sai dai ko kadan hakalinsa baya gurin yana can gurin Jibril tunanin halin da Jibril zai kasance kawai yake yana murmushin da be san ya fito masa ba.
“Son lafiya kake wannan far'ar?”
Ya kalleta kamar be san ya yi ba.
“Ba komai, but Mom Dad ya kamata ce kunje ganin yaron Nawwara ya samu accident”
“What...?”
Dadynsa ya fada.
“Mu zaka fadawa muje mu duba yaron Nawwara? Hajiya baki fada masa ya fita harkar yarinyar nan ba? Daman yana nan akan bakansa?”
Momy ta yi saurin dagawa Dadyn hannu.
“Komai da sannu ake binsa kasan halin Mustapha”
“Babu ruwana da wani halinsa, ka var ganin kai kadai na haifa zan iya shafe labarinka a doron kasa matukar ka ce zaka auri yarinyar, ka dauki kanka a matsayin matacce matukar ka tsaya kai da fata akan yarinyar nan”
Mustapha da zuciyarsa ke boiling gumi ya zubo masa ya bude bakinsa da ke rawa ya ce
“Daddy ina son yarinyar nan...”
“Baka san so ba Mustapha, taya zaka so mace da ta auri namiji biyu kuma ta haihu? Kuma in banda haukarka macen da kayi ma kanwarta fyade zaka ce kana sonta kuma da aure? Kana tunanin zata aureka ne? Kana batawa kanka lokacin ne kawai, kuma na fada maka karna sake jin maganar yarinyar nan a cikin gidan nan, ka nemo yar kowa zan aura maka amman ban da ita”
Yana gama fadar hakan ya mike tsaye ya kabe babbar rigarsa cikin bachin rai ya fice, sai Momy ta matso kusa da Mustapha tana kokarin yi masa bayani
“Look son.. ”
“No Mom ke kika ce min Dady ya yarda da maganar yarinyar nan, ashe ba da gaske ba ne? Miyasa ba zaku so abunda na ke so ba? Miyasa kuka gagara ganewa?”
Magana yake kamar ba shiba har numfashinshi na hawa wani kan wani, kamin ta kara cewa wani abu ya tashi rai a bace ya bar mata falon.
NAWWARA POV.
Ba jidadin zuwan Mustapha ba domin ban fiye son yana shige min ba, bana son wata alaka tana shiga tsakanin ni da shi, dan ban yarda mutum ya cuceni kuma ya dawo ya ce zai rabe ni ba Jibrrma dan babu yadda zan yi ne.
Bayan fitar Mustapha da mintuna talatin na kalli Jibril fuska a daure na ce.
“Ina son na kwanta dare na yi fa? Kuma ka san Inna tana waje kai take jiran ka fita”
“Ba zan je ko ina ba, a nan zan kwana tare da da na”
Ban yi mamakin furucinsa saboda cocaine yake sha mahaukacin mutum komai zai iya ai, musamman idan ya samu guri in ban da rainin hankali daga kawai na bashi damar ganin Noor sai kuma ya soma yi min katsalandan a lamurrana.
Tashi ya yi ya fita hakan yasa na bishi baya saboda na samu damar fada masa maganganun da ke bakina, ina fita na samshi bakin kofa a ashe ni yake jira.
“Daga Bilal har wannan dan iskan yaron bana son su sake zuwa gurin da na”
“Baka da damar da zaka shardanta min wanda zai so gurin da na da wanda ba zai zo ba, kai yanzu ko kunya baka ji ka kira Noor da danka? Har kana ikirarin kar wani ya zo dubashi?”
“Yes da na ne, alakar da ke tsakaninku daban babu ruwana a ciki”
“Ni na haifi yarona a hannuna ya girma baka da wannan hujjar Jibril, kuma ko zaka wulakanta kowa ban da Bilal saboda ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta ni da dana, shi Noor ya sani a matsayin Uncle dinsa ba kai ba, da kuma ba naka ba ne nawa ne”
“Ko tau zamu gani”
Na watsa masa harara, ina kokarin juyawa na koma cikin dakin sai ya fisgoni da karfi ya dawo da ni
“Ban yarda ki kwana da shi ba, Inna zata kwana da shi i don't trust you”
Dariya na farayi saboda abun ya bani dariya sosai.
“I'm laughing it's funny very funny”
“Ba wasa nake miki ba Inna zata kwana da shi ba ke ba, idan ba haka ba, ni zan kwana da shi”
“Ban ga dalilin kwana tare da dan da ka kira da shege ba? Kai baka ma jin kunyar yanzu ka kira shi da danka?”
Hannu ya daga kamar zai dakeni sai kuma ya juya baya ya dafe kansa da hannu daya.
“Na dake ni mana, ai ka saba cin zarafina ko? Ka saba yi min wulakanci a gaban kowa, na yi min cin mutumcin da ya fi ko wanne ai ba ka hada hoto da na wani ba? Ka fadawa iyayena cewar ni karuwa ce..”
“Enough...!”
Ya fada a tsawa ce har sai da hankalin wanda duk wajen dakin ya dawo kanmu, wadanda suke cikin daki kuma suka fito waje, sai dai hakan be sashi fasa fadan abunda zai fada ba.
“Ya isa haka Nawwara ya isa haka, wace irin zuciya ce dake haka? Ke kan wace irin mace ce me ke damunki miya ke cikin kanka? Miyasa kika zabi nanata maganganun nan a ko yaushe ne? Kin san abunda yake raina? Kinsan bakinciki da yake raina? Ban isa na wuce wannan kaddarar ba shiyasa na aikata but abunda kike yi babu tausayi a ciki Nawwara, am lemme tell you abunda kike ba burgewa kike ba kokarin kashe rai kike, kokarin rusa wata rayuwar kike kuma babu abunda zai sa na canja daga manufata”
Yana gama fadar hakan yaja hannun Noor ta da fito waje suka koma cikin dakin, Inna hango Inna take na rufa masa baya rai na a bace. Noor na ganina ya yi saurin sakin Jibril ya dawo guna cike da tsoro, dan Noor ya tsani ganin ana fada.
“Da na ni ya sani ba kai ba, karka sake shiga rayuwarsa”
“Dole na shiga rayuwaraa saboda ni ne asalin ubansa”
“Yes ubansa ne kai na gaji da boyewa”
Na juyar da Noor ina nuna masa Jibril.
“Ka ga wacan? Ba Uncle din ka ba ne shine asalin ubanka Baba Faruk ba babanka ba ne rika ka kawai ya yi, wacan azzalumin ne mahaifinka, shine wanda ya ce kai ba dansa ba ne, da aka haifeka be yanka maka rago ba, kuma be san zafinka ba...”
Ban karasa na naji an dago ni an sauke min kyakyawan mari har biyu a fuska, wanda ya haddasa min daukewar wutar cikin kaina tare da ganin wadansu kanana taurari..
___________________________________
Ku yi hakuri da wannan guntun page din 🙏
Mutane da suke cewa kar Nawwara ta yafewa Jibril sai ta musguna masa kuma su ke cewa Nawwara ta cika tsauri da yawa wai zuciya kamar ta kafiran farko 😂
Ni dai nawa ido 👁👁
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣7⃣
Na yi murmushin mamaki ganin irin karfin halin Jibril, lallai maza basa da kunya yanxu har yana da bakin da zai ce min wai sai idan zan rabo da dansa? Ni zai kalli tsabar idanuwana ya ce min haka?
“Ba zaki iya rabuwa da Noor ba, ni kuma ba zan iya rabuwa da ke ba, ba kuma zan daina neman ki yafe min ba”
“Zan iya shiga?”
Na tambaya ina kallon security da ya tare kofar, sai ya kalli security ya ce
“Bata hanya ta wuce matata ce”
Da sauri ya janye min ya bude min kofa, ni kuma na shiga ina murmushin jin ya kira ni da matarsa lallai iska na wahalar da mai kayan kara. Ina gaba yana bina ba dan na san inda dakunan suke ba daman can Inna ce ta kwatantamin, har na wuce dakin sai ya kira da sunan da be taba kirana ba har na dauka cewar ba da ni yake ba
“Mrs Makama”
Ganin ban waigo ba yasa ya kara da cewar
“A nan dakin yake”
Juyowa na yi na dawo na shiga kofar da ya bude min, a yanayin yadda dakin Noor yake sai ka rantse da Allah ba cikin asibiti ba ne, ya kawata masa dakin da teddys ga wani madaidaicin plasma dake lake gurin freezer din dakin. Noor na ganina ya yi saurin saukowa saman gado ya doso inda na ke sai muka rumgume juna.
“Momy miyasa baki zo ba jiya da wata jiya kamin jiya?”
Dariya na yi na shafa kansa.
“Tan ba ga Daddynka yana kula da kai ba?”
Ta da kai ya yi ya kalli Jibril.
“Momy da gaske shine Babana?”
“Ee mana ba ga kamaninka nan kana ganin a fuskarsa ba?”
“Amman Babana Faruk fa?”
Daukarsa na yi na dora saman hospital bed din sai nima na zauna, Jibril kuma ya zauna a kujerar da ke fuskantarmu, sai na kama hannayen Noor na ce
“Baba Faruk ya rike ka kamar dansa, saboda a lokacin Babanka baya nan ya yi tafiya zuwa gurin karatu wata kasar, kuma baya son ace maka baya nan shiyasa ya fadawa Baba Faruk cewar ya ce shine mahaifinka kamin ya dawo”
“Miyasa Inna ta mareki saboda shi?”
“Saboda na boye maka gaskiya tun farko ban fada maka ba sai yanzu, tana ganin kamar ba zaka fahimta ba”
“Miyasa kika ce Uncle dina ne sai kuma yanzu kika ce shine Babana kuma?”
Yanzu kan ban san mi zan kara ce masa ba kuma, jin na yi shiru ban amsa masa ba yasa ya kara aiko min da wata tambayar.
“Ko dai da Baba Faruk ya rasu sai wannan ya dawo?”
“Aa kamin na auri Faruk na fara auren Babanka sai kaddarar aure ta raba mu, ya tafi karatu wata kasar sai Faruk ya aureni kai kuma ya rika ka kamar dansa saboda yana so na kuma ya san kimata, amman ba shine asalin mahaifinka ba, wannan shine mahaifinka na gaskiya shiyasa ake kiranka da Muhammad Jibril ba Muhammad Faruk ba”
Ya yi shiru kamar mai tunani sai kuma ya yi murmushin da ya bayyana hakoransa.
“Momy na gane, yanzu Babana be rasu ba kenan?”
“Gashi a gabanka kana gani, kuma yana son ka sosai kai har ma ya fi ni son ka”
Na fada ina nuna masa Jibril
Murmushi Noor ya yi sosai ga dukan alamun yaji dadin haka, sai na rika shi ya sauka saman gadon ya nufi inda Jibril yake yana ta kallonsa.
“Kuma fuskarmu guda ko Momy?”
“To ai shine mahaifinka shiyasa kuka yi kama, kaga ai baku yi kama da Baba Faruk ba ko kun yi kama?”
“A'a”
Sai Jibril ya daukeshi ya dora saman cinyoyinsa ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya.
“Thank you so much Dear”
Ya fada yana kallona fuskarsa na nuna jindadin da ke cikin ransa. Tun daga ranar na ke ta kokari wajen kawarda duk wani abu da zuciyata take nuna min, hakan ba karamin faranta ran Jibril da Inna ya yi, ni ko farincikina farincikin mahaifita da kuma da na, sati daya da muka a asibiti ya isa ya samarda wani kudi na littafin soyayyar uba da da tsakanin Jibril da Noor, saosai da sosai Noor yake son babansa yana shiga jikinsa wani lokacin haka zai kyaleni ya yi ta sha'aninsa shi da mahaifinsa, Jibril kuma kamar ya cinye shi yake ji cikin kwana biyu ya yayatawa duniya cewar yana da, abun mamaki har Abbah sai da ya zo ganinsa yan uwansa ma wadanda suke uba daya sai da suka zo, abokaninsa na nesa da na kusa suna ta zuwa ganin Noor saboda ya fada musu dansa ya kare a gabana wasu ke cewa daman wai kana da? Mun samu alheri sosai domin duk abunda ka bawa Noor Jibril baya dauka ni yake barwa, sai dai wani abun da yake bani mamaki duk cikin masu nan ban taba ganin Siraj ba duk kuwa da kasancewar ba ko yaushe na ke tare da Noor ba, amman a yadda nake ganin abotarsu ya kamata ace Siraj gana zuwa ko da be zo kullum ba ya zo ko da sau hudu ne a sati. Ranar da Noor ya kwana takwas a asibitin na bukaci a sallamemu amman sai ya ki, ni kuma ba dan komai na ke son komawa gida ba sai dan Bilal saboda kwana biyu nan na rasa gane kansa ya kasa fahimtata yawan zuwa da nake asibiti jinyar Noor yana ganin kamar wata sabuwar soyayyace ke kulluwa tsakanin da Jibril.
A ranar da muka fara zuwa kotu zama na farko na sha kuka a ranar saboda ya tuna min da mahaifina da kuma Habiba, na yabawa Dpo sosai domin ya nuna kulawa akan case din ga kuma police din da alkali ya bada ikon tsarewa har zama na gaba, wani abun da ya bani mamakin matar da ta ce Mahaifinmu ya yi mata sata tana da yanayi da Siraj sosai kuma ita ba ce a tsareta ba saboda tana da kudi ko kuma tana da daurin gindi ko kuma dan tana da kokarin kare kanta cewar ba ita ta saka su ba oho. Ni dai har muka fito daga cikin kotun ban daina harararta ba ita kuma bata daina kallona ba.
Tare muka fito da Inna da Sakina, sai Jidda da Bilal da kuma yan uwan Baba da na Inna, kowa da abunda yake fada ni dai ban ce komai ba, har muka shiga Napep muka dawo gida. Muna shigowa gida Jidda take labarta min cewar Mustapha ba shi da lafiya jiya aka kai shi asibitinsu Jibril.
“Miya ke damunsa?”
“Ke kika damunsa Nawwara”
“Kamar ya? Ai na ce na yafe masa”
Ta yi shiru bata sake cewa komai ba.
“Kinje kin duba shi?”
“Ina tsoron mahaifansa”
“Mai tsoro baya zama gwanin Jidda matukar kika saka tsoro a zuciyarki Mustapha ba zai taba fahimtar cewar kina son shi ba”
Ta kalleni da sauri.
“Waya ce ina son sa? Mustapha da yake son ki sai kuma ace ni ina son sa?”
“Ba fada min aka yi ba, a idanuwanki na karanta”
“Baki min adalci ba Nawwara baki san komai a kaina ba”
Ya mike tsaye a fusace ta fice, ni kuma na bita da kallon mamaki domin ban ga abun daga hankali a cikin wannan maganar ba.
Tashi na yi soma dora girki muna ta firar yadda zaman kotun ya wakana ni da Inna, da dare sai ga Bilal ya kirani a waya wai na fito yana kofar gida.
Na yi mamakin jin hakan saboda kwana biyu ya dauke min kafa daga zuwa fira ko da kuwa ni na bukaci hakan sai dai mu gaisa a waya, na dauri aniyar sakashi farinciki a yau ko da kuwa ba da niyar hakan ya taho ba, dan haka na dauki kayan kwaliyata na dandasa kwaliya mai kyau na feshe jikina da turaren da Jibril ya aiko min cikin kayan da ya siyo min kwanaki, na dauki gown din atamfa da take cikin kayan da Jibril ya aiko min na saka, ni kaina na san na yi kyau a wannan dare, Inna ma kallona kawai ta yi tayi murmushi, nima na fice ina murmushi.
A yanayin yadda na tararda shi yasa ni jin babu dadi, domin kuwa fuskarsa babu annuri jikinsa kamar a sanyaye, bayan na masa sallama sai ya amsa min idonsa akaina kamar zai cinyeni.
“Nawancy kin yi kyau”
“Dan kai kadai na yi ta na gode da ka yaba”
Sai dan yi murmushi.
“Aiko ya kamata na bada tukuici ko?”
“Ka adana tukuicinka da daddadan kalamanka har sai na fada maka dalilin wannan kwaliyar tawa”
“Akwai wani daliline bayan wanda na gani?”
“Sosai ma, a wancan gani ka yi, wannan kuma ji zaka yi”
Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi.
“Nawancy kina yaudarar zuciyata da yawa, da fushi na zo nan gurin, amman kin shiga kin yi nikaya kin tarwatsa duk wani damuwa da fada da na zo da su”
“Ai daman haka ya kamata ko wace amarya ta kasance gurin angonta, mai wanke danuwarsa ta shimfida farinciki a zuciyarsa”
“Ina ma da gaske Nawancy amaryar Bilal ce da yafi kowa farinciki a duniyar nan”
“Akwai wanda ya isa ya hana abunda Allah ya zo kasanewarsa tun farkon hallitar Nawwara?”
“Babu”
“Ashe ko Nawwara sai ta fi Bilal kasancewa a cikin farinciki daga ranar da aka daura aurenta da angon da ya fi ko wane ango tsada a duniyar nan”
Ya yi murmushi yana kallona tare da lumshe ido.
“Ina son ki sosai Nawancy”
“Kai so na kawai ka ke ni ko kaunar ka na ke”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Kamin ki kaini duniyar da ba zan iya dawowa ba, fadan min dalilinki na yi wannan kwaliyar”
“Kamin na maka albishir mai tsada ya kamata ace ka fada min abunda ya kawo ka nan”
“Yo tun yaushe kika duniyar kwakwalwa kika mantar da ni wanene ni ma, balle abunda ya kawo ni nan kuma”
“Yanzu dai rumtse idonka sai na fada maka albishir din”
“Ai kunnene yake ji ba idanuwa ba”
“Ina gudun kyawawan idanuwan nan naka su ba ni kunya ne”
Sai ya yi dariya ya lumshe idanuwasa.
“Inna ta ce na fada maka, idan ka shirya ka turo magabatanka suje can Baban gida su gana da nawa magabatan”
Da sauri ya bude idanuwansa ya kallini
“Da gaske Nawancy?”
“Na saba maka irin wannan wasan ne?”
Wani ihu ya yi ya daka tsalle ya dire, ni kuma na yo cikin gida da gudu ina dariya. Da na shigo sai na ce da Inna Bilal ya ce zai turo magabatansa amman be saka rana ba.
“Mashallah Allah ina fatar kina sonshi dan karki yi wa kanki zabi irin na baya, kuma ina son ki bawa Allah zabi a cikin lamurranki nima zan taya ki da addua idan aurenki da Bilal alheri Allah yasa ayi, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya kawo maslaha”
“Amin Inna, inshallah Alheri ne”
Daga wannan sai fira ta biyo baya Inna na ta nanata min burinta na ganin na yi aure domin shine kwanciyar hankalinta, a daren Bilal ya yi min kira ya fi a kirga ni kuma na ki dagawa, misalin uku da rabi na dare na tashi na yi nafila na Mikawa Allah zabina akan ya zaba min dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata. Washe gari bayan na gama komai na shirya na nufi asibiti zuciyata cike da tunanin yanayin Jidda gabana kuma nata faduwar da ban san daliliba.
Jirbil kawai na tarar a dakin Noor baya nan, na gaisheshi cikin ladabi kamar yadda na saba masa a yanzu. Be amsa min ba sai ya matso kusa da ni yana ta kallona kamin ya risina kasa wanda hakan yasa ni ja da baya.
“Nawwara dan Allah ki yafe min abunda na yi miki na san na yi kuskure amman ki dubi girman Allah ki yafe min”
“A kwanakin nan da muka dauka be isa yasa ka fahimci cewar na yafe maka ba?”
Ya mike tsaye yana kallona.
“Ki kalli cikin kwayar idanuwana ki ce kin yafe min”
Ya fadi hakan ne saboda ya tabbatar da yafiyar tawa, domin yasan babu abunda zan gani a cikin idanuwansa sai tsanarsa da kiyayyarsa, ras na sauke idanuwa cikina nasa zuciya a natse bakina ya furta cewar.
“Na yafe maka Jibril Allah ma ya shaida na yafe maka”
Lumshe ido ya yi sai ga hawaye sun sauko masa, yaja wani dogon numfashi ya sauke, sannan ya bude idanuwansa ya kalleni
“Yanzu za ki iya aure na kenan?”
“Dan na yafe maka ba shi yake nufin zan iya sake zaman aure da kai ba, ni ina da wanda zuciyata take so”
“Wa kike so Nawwara? Wanene wannan wanda ya fini sa'a da dacewa a rayuwa? Wanene wanda be shirya zaman duniya a yanzu ba?”
Na shiru ina kallonsa.
“Mustapha ne ko?”
Kamin na ce wani abu sai wata nurse ta turo kofar dakin ta shigo hannunta rike da na Noor.
“Sir an gama”
“Thank you”
Ya fada yana share hawayensa, sai da ta fice sannan ya nufi Noor ya dauke shi ya rumgume.
“Come here my happiness”
“Momy yanzu kika zo?”
Na daga masa kai sai na karasa gurin gadon na zauna, Jibril kuma ya zauna a kujerar da ke fuskantata yana rumgume da Noor, idanuwansa na ta xika da hawaye tana kallona.
Muna haka aka turo kofar dakin a aka shigo Zinatu ce tare da Rabi sai kuma wani bakon mutun da ban waye fuskarsa ba. Da dan farka ta karaso kusa da mu ta aje ledodin da ke hannunta sannan ya zauna kusa da ni tana kallon Jibril.
“Ashe kana nan”
“Akwai wani gurin da ya kamata na kasancene bayan nan?”
Ya fada yana mikawa mutumen hannunsa su gaisa. Rabi kuma ya zo tana mikawa Noor hannu
“Zo nan dan Daddynsa”
Dariya kawai ya yi mata amman be yarda ya bar jikin Jibril ba, ya labe sosai kamar wani karamin yaro mai shan mama.
“Sir Akwai maganar da ya kamata mu yi”
“Tana da muhimmanci ne sosai?”
“Eh akan abunda kasa ayi ne, kuma Siraj yana waje yana jiranka ya ce a gaishe da Noor”
Zinatu ta mike tsaye ta karbi Noor shi kuma ya tashi ya fice dare da mutumen da kuma Rabi.
“My Son ya jikinka?”
“Na ji sauki Daddy ya ce nan da kwana biyu za a warware hannu”
“Mashallah Allah ya tsare gaba ya kara lafiya”
“Amin”
Ya amsa bakin nan chakoi, sai ta kalleni.
“Kin kusa komawa aiki kenan ko?”
“Inshallah”
Daga haka ban sake cewa wani abu ba, itama bata sake cewa ba, sai ma dauko ledar da ta zo da ita da tayi ta bude ta fiddo chocolate mai shegen tsada ta mikawa Noor. Bayan kamar mintuna talatin sai Rabi ta sake shigowa tana fadin.
“Zinatu Siraj na kiranki wai ki zo zai wuce”
Zinatu ta sauke Noor saman jikinta ta aje shi kasa tare da yi masa kiss.
“Allah ya kara sauki da na”
“Amin na gode”
“Nawwara na wuce”
“Mun gode Zinatu Allah ya bar zumunci”
“Amin”
Bayan ta fice, Rabi ta maida kofar dakin ta rufe ta nufo ni tana fadin.
“Nawwara ina son muyi magana da ke mai muhimmanci”
“Akan me?”
“Akan ke da Noor da Jibril da kuma Siraj abunda ya shafi rayuwarku ne ku duka”
Gabana ya fadi
“Ban gane ba”
“Asirrance na ke son mu yi maganar, amman kamin nan ko kin san cewar Jibril ya kori Bilal a kamfani tun last week? And there's something behind Noor accident...”
Na mike tsaye da sauri.
“When how i don't understand?”
Kamin ta kara cewa wani abu sai ta ga Jibril ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin juyawa tana dariya.
“Kin jiki Nawwara da wata magana, masu kudi ai suna can inda suke, ni dai na tafi Allah kara lafiya”
Kamar na ce wani abu sai kuma na amsa da.
“Amin na gode”
Tana ficewa, Jibril ya kalleni ya ce.
“Kin san an kawo Mustapha a asibitinmu kuma ba shi da lafiya sosai, yana icu room 14”
“Na sani”
“Mi kike son a masa?”
Na masa wani kallo kamar ban fahimci abunda yake cewa ba. Sai yasa hannunsa aljihu ya ciro karamin hoton Habiba ya mika min. Na karba hannuna na rawa sam na manta da inda na jefarda hoton ma. Ina karba sai ya juya ya fice ya bar nan tsaye da mamaki, ya aka yi yasan abunda Mustapha ya aikata? Ina ya samu hoton Habiba? Me yake nufi da abunda nake son a yi masa, ga kuma maganganun Rabi da suka tsaya min a rai.
Saurin juyawa na yi na fita harabar asibitin ina tambayar inda icu yake, aka fada min sai na doshi gurin da sauri ina duba number din room din har na kai ga mai 14, ina dosar dakin sai Jibril ya fito tare da wasu Nurses, kallona kawai ya yi ya dauke kai ya fice, ni kuma na saki baki jikina a sanyaye ina kallon dakin, Mustapha nake hangowa da ke kwance kamar gawa, Mutanen da ke cikin dakin suna ta rusar kuka, ban san lokacin da nawa hawayen suka fara zuba ba, na juyo da sauri na biyo bayan Jibril hangosa na yi tsaye yana magana da wani likita na doshi inda yake ina hawayena bakina na rawa kafafuwana kuma kamar zan fadi.
Yana hangoni ya yi saurin sallamar mutumen ya shige dakin, ni kuma ina isa na baki kofar office din na fada.
“Me ka masa Jibril? Me ka masa?”
Ya zauna saman kujera yana kallona
“Duk mutumen da ya kashe rai shima kisa ne ya cancanta da shi, daukar fansar yar uwarki na yi miki”
“Be kashe rai ba, fyade kawai ya yi mata miyasa zaka kasheshi mi ya kama?”
“Ba shi kadai zan kashe ba?”
“Mutum nawa zaka kashe?”
“Adadin mutanen da zasu furta ko kuma su nuna soyayyarsu a gareki, kamar Bilal”
Ya fada yana tabe baki, ni kuma na zaro ido naja baya baya har ina kokarin faduwa, sai kuma na juya a firgice na fice daga office din kamar mahaukaciya.
____________________________
Da gaske Jibril ya kashe Mustapha? Ko dai mafarki ne Nawwara take?
Mai Rabi zata fadawa Nawwara mai muhimmaci har haka ne? Mi ta sani akan Siraj da Noor da kuma Nawwara?
I can't wait for the next chapter 😍
KhadeejaCandy ce ✍️
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣8⃣
Har na kawo bakin gate din asibitin kuka na ke ina ta tunanin abun yi, wane irin mutum ne da zai kashe rai saboda cin ma wata bukata tasa ta kanshin kansa? Ko ni da na tsani Mustapha ba zan iya kasheshi ba ko na saka a kasheshi ba, bayan shi kuma ya ce Bilal ne next, dole ne na sanar da police wannan maganar ba zan iya kyalewa ba, wayata na dauko na kira Bilal bugu daya ya dauka muryarsa da walwala da alama yana cikin farinciki.
“Nawancy”
“Kana ina”
“Ina kofar gidanmu”
“Dan Allah ka sameni guiwa station yanzu”
“Lafiya? Kuka kike yi”
“Ka zo yanzu ka ji”
“Okay tau”
Daga haka na kashe wayar na tari achaba na hau domin shi ya fi kusa da station, ko da na isa har ya isa bakin station din yana ta yi min waya, yana ganina ya doso inda na ke yana tambaya dalilin kiransa da na yi.
“Bilal Jibril ya kashe Mustapha kuma ya ce kai ne na biyu”
“What? Nawancy kin san abunda kike fada kuwa”
“Na sani na gani da idona ya kasheshi”
Na fada ina kuka, sai ya matso kusa da ni yana kwantar da hannayensa.
“No listen Jibril is very smart ba zai kashe Mustapha, maybe dai yana miki wasa ne, ko kuma yana son ya yi amfani da wannan damar ne ya cinma wani buri nasa”
“Wallahi da gaske ne, na ga gawar Jibril da kaina”
Na fada ina cigaba da kuka, sai ga wani dan sanda ya zo kusa da mu yana tambayar dalilin zuwanmu gurin.
“Dpo na ke son gani shi yace na same shi nan akan case din mahaifinmu”
“Amman baki da number shi?”
“Ba ni da amman shi yana da tawa number, dan Allah ka fada masa da gaggauwa”
“Okay”
Ya juya ya koma ciki, na yi wannan karyar ne saboda na samu gamin dpo cikin sauki, domin nasan duka wadannan kananan yan sandan ba zasu iya handling case din Jibril ba. Bayan kamar minti biyar sai ga police din ya dawo ya ce mu shiga ciki, sai dai basu bamu damar hakan ba sai da suka binka komai na mu.
Cikin office dinsa muka sameshi yana sanye uniform dinsa na yansanda yana ta rubuce rubuce a takardun da ke gabansa, da hannu ya nuna mana kujerar zama.
“Bismillah”
Na zauna hawaye na ta bin fuskata, sai ya aje rubutun da yake ya fuskance mu.
“Lafiya dai Nawwara?”
“Ba.. Ba.. Ba akan case din Baba na zo ba, na ce haka ne saboda na samu ganinka”
Na fada ina kuka, sai mika hannunsa ya dauko tissue ya bani na share hawayena da majinar da ta zubo min, sai kuma ya mike tsaye ya nufi freezer sa ya bude ya dauko gorar ruwa da kofi ya bulbula min.
Ba musu na dauka na shanye, ya sake zuba min na shanye sai ya karbe kofin ya maida gefe ya zauna yana kallona.
“Relax ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki a nan”
Na gyada masa kai sannan na sauke ajiyar zuciya wanda hakan ya bani damar soma masa bayani.
“Wani ne yake barazana ga rayuwar Bilal ya ce sai ya kasheshi”
Ya kalli Bilal a kaikaice.
“Miye tsakaninki da Bilal din?”
“Shine wanda zan aura”
“Wacan wanda yake barazana ga rayuwarki fa?”
“Tsohon mijina ne”
Jinginawa ya yi da kujerar yana kallonmu.
“Fada suka yi da har maganar kisa ta shiga ciki”
“Aa kawai dai baya son shi ne, yanzu ya kashe wani kuma ya ce Bilal ne na biyu”
“Dan taadda ne mijin na ki?”
“Aa likita ne, amman yanzu yayi ma wani allura ya mutu”
Ya kalli Bilal
“Kai namiji ne maybe zaka fi yin bayani mai gamsarwa, ko fada ya taba hada ka da mutumen? Ko kuma wani abu ya shiga tsakaminku”
“Gaskiya babu abunda ya taba shigo tsakaninmu”
“Haka kawai yayi maka barazanar kisa?”
“Aa shi besan an yi ba, ni ya fadawa kawai ina son a shiga tsakaninmu da shine domin duk abunda ya samu Bilal shine”
“Okay amman dole ne zamu yi magana da shi, yanzu zan sa a dauki statement dinku, kin san inda zamu samu wacan din?”
“Ee ina da number wayarsa”
“Tau ki bamu sai mu kira”
Daga haka ya dauki telephone dinsa ya kira wani police yana shigowa ya sare masa shi kuma ya nuna mu.
“Kaje ku dauki statement dinsu, kuma ka karbi number a hannunta ka kira mutumen ka ce ana nemansa”
“Yes Sir”
Tare muka fito da police din suka kawo mu reception suka dauko takardar aka saka sunana da na Bilal sannan na soma yi musus bayanin komai, bayan mun gama na basu number Jibril suka kira shi, ko thirty minutes ba a kara ba sai gashi ya iso gurin fuskara babu annuri. Sai aka sake maida mu gurin dpo tare da statement din da aka dauka. Muna shiga Jibril ya mika masa hannu suka gaisa ya zauna saman kujera ba tare da ya jira an masa izinin zaman ba, Bilal ya zauna a kujerar da ke fuskantar ta Jibril, ni kuma na zauna a kujerar da ke bayan Bilal.
“Dpo kun ce kuna bukatar ganina”
“Yes Nawwara ta kawo kararka akan cewar kana barazana ga rayuwar mijin da zata aura Bilal”
Sai ya juyo ya kalli Bilal kamar daman can be san da shi a gurin ba sai yanzu, sai kuma ya maida dubansa gurin dpo.
“Mi nayi?”
“Ta ce ka ce sai ka kashe Bilal, kuma ka kashe wani kamin shi ka ce shine next”
“Yanzu dpo tsakanin da Allah na maka kama da mai kisa?”
“Ai abun ba daga kama ba ne”
“Idan ina son kashe Bilal ba sai na fadawa Nawwara ba, kuma taya namiji mai iyali kamar ni xai bata lokacinsa gurin wannan wasan kamar wani karamin yaro? Ni ban kawo kararshi ba shi zai kawo karata? Mutumen da kake gani yana barazana ga rayuwata da ta iyalina, my friend has told me Bilal din nan yana da hannu a kokari kashe min yaro, amman ban masa komai ba saboda ban tabbatar da gaskiyar ba na fi son na kama shi red handle, wannan yasa na koreshi daga kamfanina, a kamfanina yake aiki amman babu irin cin fuskar da baya min da matar nan saboda ya san ina sonta”
Ya juyo ya kalli Bilal.
“Saboda na koreka daga aiki shiyasa kake kokarin bata min sunan asibiti ko? Kake kokarin saka Nawwara against me ko? Idan mun gama da wannan case din zan shigar da nawa case din akanka, dan zaka iyayi min komai wajen ganin ka bata min suna ko aikina”
“Kana ganin xaka iya taka kowa saboda kana da kudi ko Jibril? Zuciyarka tana yaudararka akan ka aikata dukan abunda kake so saboda kana da kudi ko? Har yanzu zuciyarka karya take fada maka, ka kasa fahimtar cewar ba komai kudi suke siya ba, kana yaudarar kanka da yawa Jibril”
Cewar Bilal cikin fushi. Sai Jibril yasa dariya ya kalli dpo ya ce
“Kaga abunda na ke fada maka ko? Babu komai a zuciyarsa sai tsanata da neman hanyar da zai lalata min suna”
Ni kuma na mike tsaye ina fadin.
“Ba bata maka suna zai yi ba, gaskiya ya fada, kuma ni ka fadawa cewar sai ka kashe Bilal kuma yanzu haka ka kashe Mustapha”
Dpo ya daga mana hannu.
“Ba fada muka kiraku ku mana a nan ba”
“Kamin nan dan Allah dpo ina son ka bani yaranka suje su duba wanda ta ke cewa na kashe”
Mun dade a office din Bilal da Jibril suna ta musayar yawu, sannan saka rubuta yarjejeniyar cewar duk abunda ya samu Bilal Jibril ya saka hannu akan cewar ya yarda aka kira Siraj ya yi sheida Bilal kuma aka kira mahaifinsa. Daga bisani muka dunguma gaba daya muka nufi asibitin. Abun mamaki muna shiga dakin da Mustapha yake sai muka same shi zaune yana cin abinci kamar ba shi na ga a mace ba dazu. Yana ganina ya rika kokarin saukowa saman gadon sai mahaifiyarsa ta katsa min tsara.
“Ke kan kin shiga uku Nawwara, ba zaki bar dan mu ya huta ba, wannan wace irin rayuwa ce saboda ke dan mu yake kwance nan yanzu kuma sai ki biyoshi har nan asibiti akan wane dalili”
Juyawa kawai yan sanda suka yi suka koma ni kuma na sulale kasa a gurin ba dan na suma ba sai dan kafafuwana da suka min sanyi, ga hawayen da suka soma nin zuba babu kakkautawa.
“Haba Mom miyasa kike min haka ne? Wallahi da ki yi ma Nawwara fada kara ki yi min”
Tasowa ta yi ta karaso inda na ke.
“Ban san kaddara ba Nawwara, duk na rasa dana saboda ke ki fara kirga irin asarar da zata sameki kema”
“Tir da mace dattijowa irin ki ta tsaya tana fadin bata yarda da kaddaraba, ke an fada miki Nawwara son Mustapha take ne?”
Cewar Bilal yana kokarin defending dina, wata muguwar harara Hajiyar Mustapha ta watsa masa. Sai mahaifin Bilal ya katsa masa tsawa.
“Bilal wuce muje”
Sai da ya kalleni kamar ba zai iya bari a gurin ba, sai kuma ya juya ya fice tare da mahaifinsa, ni kuma na unkura na tashi ina nuna na fito daga gurin na nufi sashen da Noor yake.
Ko da na tura kofar na shiga Noor yana bachi hankalinsa kwance, kusa da shi na zauna hawaye na zuba a idanuwana, na kai hannu na shafa shi. Ina haka sai Jibril ya turo kofar dakin ya shigo yana sanye da labcoat, bayan ya maida kofar ya rufe ya zuba hannayensa cikin aljihu ya doso inda nake.
“Na sallami yan sandan”
Ban dago na kalleshi ba balle kuma har na amsa masa.
“I'm sorry Nawwara”
“Na tsane ka Jibril”
“Na sani”
Ya amsa min a takaice.
“Ka sake dawowa saboda ka ruguza sauran farincikin da ya rage min ko?”
“Wallahi ba dan haka na dawo rayuwarki ba, Nawwara ba ki cancanci auren kowa ba sai ni ko dan Noor, yanzu kin fi son ki barwa wata uwar ta yi miki rainon da? Dan kin san ba zan taba bari kije min da shi gidan duk wanda kika aura ba ko?”
“Kowa kallon mahaukaciya yake min, ka kunyata ni a gaban mahaifin Bilal”
“Bani da wani zabin ne Nawwara, Wallahi ina son ki sosai, saboda ke nake ta canja rayuwata Nawwara, dis week wani Malami zai fara zuwa yana karantar da ni saboda kawai na samu xama cikakkane namiji da kike so, amman hankalin ya koma kan Bilal, kin kasa fahimtata Nawwara”
Na daga kai na kalleshi.
“Bana son ka Jibril miyasa ka kasa fahimta? Hakika Noor be yi dacen uba”
“Babu wanda zuciyarki take so sai ni Nawwara, Nawwara idan kika aure wani ba ni ba, rayuwata da ta Noor tana cikin hadari”
“Bari idan na auri Bilal din, ku fadi ku mutu”
Ina fadar hakan na mike tsaye na share hawayena na fice daga dakin zuciyata na mugun kuna.
Ko da na iso gida numfashina har sama yake kamar zan hadiye zuciya na mutu saboda bacin rai, tun daga yanayin sallama ta ya kwantarda Inna irin damuwar da na taho da ita ga wani uban ja da idanuwa suka yi sun kumbura sosai saboda kukan da nayi. Muryata a dakishe na zauna saman tabarmar da Inna take zaune na fara rusa kuka, sai hankalin Inna ya tashi.
“Lafiya miya same ki?”
“Jibril ne”
“Yi hakuri tsagaita kukan sai ki min bayani, amman kamin nan kina da bakuwa”
“Wacece?”
Na tambaya cikin kuka.
“Muma ba mu santa ba, amman tun dazu take jiranki”
Na share hawayena na mike tsaye na nufi dakin Inna domin ganin wacece, abun mamaki sai na samu Aisha zaune tana kallon kofa da alama ta ji shigowata kuma ta ji lokacin da na doso dakin.
_____________________________
Assalamu alaikum fans i will be offline for awhile saboda fever na damuna sosai, jiya ma daker na yi typing yau ma karfin hali kawai na yi Wallahi dan kar na barku kuna ta jira, zan je ganin doctor gobe so yanzu kan sai na samu sauki sosai sannan zan sake yin typing. Thanks All
Best regards ♥️🖤
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣6⃣
Zafin marin ya haddasa min ganin duhu a idanuwana, sai na kyabta idon sau biyar sannan na ga Inna dake tsaye tana hararata, Noor kuma ya fashe da kuka ya rike min kafafu da dayan hannunsa. Hawayene suka soma zuba a idanuwana ina dafe da kuncina, sai na juyo na kalli Jibril da shi ma idanuwansa ke cike da kwalla, juyawa ya yi ya bar dakin ba tare da ya ce komai ba, sai da yaja kofar dakin sannan Inna ta soma fadamin maganganu marar dadi.
“Ina miki kallon mai hankali ashe baki da hankali, abunda kika aikata a yanzu ya fi abunda Jibril ya yi ma Noor shekarun da suka wuce, miye abun burgewa a cikin fadar irin wannan maganar a gaban idon dansa? Wane irin kallo kike son dan sa ya masa? Kina tunanin burgeshi zaki yi? Ki haddasawa danki tsanar ubansa da kanki? Idan ke baki son shi karki shiga tsakanin uba da da, Wallahi da Noor zai girma a cikin talaucin da ya fi wannan kuma daga baya ya hadu da mahaifinsa dole ne sai ya masa biyayya saboda haka Allah ya ce.
Wace irin zuciya ce da ke Nawwara, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne? Wa kika fi? Idan ma ba zaki yafe masa ba ai ba sai kin shiga tsakaninsa da dansa, Wannan ba halinki ba ne Nawwara kuma ba halina ba ne ba kuma halin Babanki ba ne, ban san inda kika dauko wannan bakar zuciyar ba”
Tun da ta soma maganar na lumshe ido hawaye na cigaba da min zuba, sai na ji ta fisge Noor daga rikon da ya yi min ina bude ido ta nuna min hanyar fita.
“Fita ki bar dakin nan”
Na bude baki zan yi magana ta daga min hannu.
“Bana son jin wata magana daga bakinki ki fice kawai kije gida”
Juyawa na yi kafafuna da nauyi zuciyata kuma da rauni na fito daga dakin ina share hawayena. Kowa kallona yake ni kuma na ki na kalli kowa na fito ina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi bakin gate din asibitin.
Miyasa kowa ya kasa fahimtata? Miyasa ni kadai na ke jin abunda na ke ji babu mai ji min zafi? Ni kadai na san irin wulakancin da na fuskanta a gidan Jibril amman yau Inna har ta tana marina saboda shi? Zama da mutane da kalubale shi yake canjawa mutum rayuwa Inna ta kasa fahimtar hakan.
Har na isa gida kuka nake, mai Napep din har tambaya ya yi wai ko an yi min mutuwa ne nidai ban amsa shi ba, da hawayen fuskata na shiga gida Sakina da Jamila suna zaune waje suna shan iskar hadari da ke kadawa, yanayin shogowata yasa Sakina ta taso ta sauri ta tari ne sai ta haska fuskata.
“Lafiya Anti Nawwara? Ko Noor ya mutu ne?”
Na girgiza mata kai alamar a'a, ina kallon yanayinta da ya yi min kama da na Habiba, banbancinsu da Habiba ce rumgumeni zata yi ta fashe da kuka ko da kuwa bata san abunda na ke wa kuka ba.
“Anti Nawwara miya faru?”
Ta tambaya tana jijjigani zuciyarta cike da fargabar abunda ya saka ni kuka.
“Na rasa komai Sakina, na rasa karatuna wanda shine gimshiken rayuwata saboda Jibril, na rasa mahaifina mai fahimtar kukana, na rasa yar'uwar da ke goyon bayana, yanzu kuma zan rasa Noor Inna kuma tana goyon bayan Jibril, ni kan miya ragemin a duniyar nan? Kowa baya fahimtata, babu mai jin yarena, ni kadai na ke kukana, damuwata ni kadai ta dama, ni kadai na ke jin zafina, duniya ta juya min baya ta kona min komai na farinciki, duk abunda na taba zafi yake min, mai amfanin kuma ta mayarda shi toka da na taba sai dai ya bi iska, na kasa gane bayana balle na fuskancin gaba, babu ranar tsayuwar hawayena”
Ta rika hannuna tana kuka kamar yadda Habiba take min.
“Allah yana tare da ke Anti Nawwara shi zai miki maganin komai”
Na gyada kaina alamar gamsu har na saukarda nauyayyen ajiyar zuciya. Sannan na share hawayena na nufi dakinmu.
“Habiba”
Ina shiga na ambaci sunanta kamar tana jina, sai kuma na kwanta saman katifa ina hawaye, wayar da ke hannuna ta yi kara alamar sako, ina dubawa na ga number Jibril.
_I'm so Sorry Nawwara i'm sorry_
Haka ya rubuta a sakon, wai na yi wurgi da wayar na kara fashewa da kuka. A ranar kwana na yi ina kaiwa Allah kukana saboda bachi ya yi kaura daga idona. Na mikawa Allah lamurana, sannan na bar masa zabi akan dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata, a ranar na roka idan ma mutuwa ce ta fi alheri a gareni Allah ya matso min da ita, idan kuma ba iyakar wahalata kenan ba, Allah ya bani zuciyar da zan iya dauka, saboda shi ya tsara min komai.
Washe gari Inna bata dawo ba sai tara da rabi, ban ga annuri a fuskarta ba wanda hakan ke nuna har yanxu bata huce ba kenan, ban kuma ji ta ce na shirya na je ba, daman ni na ke kwana da shi sannan ita kuma da rana taje ni sai na dawo na yi wanka na shirya sannan na koma.
A daki na sameta na durkusa kasa na rike kafafunta ina kukan da ni kadai nasan zafin fitar hawayena
“Inna ki dubi girma Allah ki yafe min, Wallahi duk kika yi fushi da ni Allah ma fushi zai yi da ni, ke kadai kika rage min a duniyar nan, ba ni da wani gata sai na Ubangiji da yayi min ta hanyarki, zan iya jure komai amman ban da fushinki da rashinki babu dan da zaiyi albarka matukar uwarshi tana fushi da shi, mai yawan neman yafiyar mahaifiyarsa da mahaliccinsa kuma dan gata ne har a gurin Allah, kuma ba zai taba tabewa ba, yarda Allah tana tare da yardar iyaye, idan suka yarda da kai to Allah ma ya yarda da kai, ki taimaki rayuwa kada na zama daya daga cikin masu tabewa, kar soyyayyar wami yasa ki yi fushi da yarki”
Zaunawa ta yi bakin gadon tana kallona fuskarta dauke da damuwa.
“Ba zan taba fushi da ke ba, domin na san illar fushin uwa ga yayanta, na mareki ne kuma na daure miki fuska ne saboda ki gane abunda kika aikata babba ne, na san zuciyarki zata zargeni da cewar ina son Jibril fiye da ke, ba saboda kudin Jibril yasa na yi miki haka ba, da kudinsa na ke kwadayi da na cilasta miki komawa gidansa ko kuma kulla wata alaka da shi, ba wannan na ke dubi ba Nawwara, rayuwar dan ki ta nan gaba nake hangowa da kuma taki rayuwar, wata rana zaki gane gaskiya nake fada miki wata kila a lokacin bana raye, amman za ki gasgatani, ba zan taba cilasta miki gurin auren Jibril daman tun farko bamu cilasta miki ba, amman na san ko da mahaifinki yana raye kwatankwacin abunda na aikata shi zai aikata a gareki, ba zan taba fushi da ke ba”
Na kwantar da kaina saman cinyoyinta wata kalar rahama ta uwa tana shiga cikina.
“Na gode Inna, na miki alkawari ba zan sake yin abunda zai sa ki fushi ba, ko da kuwa abun nan baya min dadi”
“Allah ya sauwake miki wannan rayuwa ya baki wanda zuciyarki take muradi wanda zai share miki kukanki kuma wanda za ki more hakurin da kika yi ta hanyarsa”
“Amin”
Sakina ta shigo tana tambayar jikin Noor, sai Inna ta amsa mata da
“Ya ji sauki, yanzu wanka zan yi na koma”
“Bari na shirya na je”
Na fada ina kokarin tashi tsaye, sai Inna ta rike min hannu.
“Aa ba sai kin je ba, ki hutar da kanki daga yau zuwa gobe”
“Saboda mai?”
“Saboda ki samu sukuni a zuciyarki, kuma ki shirya amsa tambayoyin da Noor zai miki, domin yana ta min na ce masa ban sani ba ke kadai kika sani, dan haka yana nan yana jiranki, kuma Jibril yasa an canja mana wata asibitin tun jiya da dare an kaimu wata”
“Tau Inna”
Na amsa ba dan raina ya so ba, tabbas Jibril na daf da rabani da dan na ni kadai na sha zafin daukar cikinsa na raineshi kuma na haifi abuna saboda kawai shi yana da dukiya.
JIBRIL POV.
Shiru ya yi ya rasa abunda zai cewa Abbah, zuwa can ya sauke ajiyar zuciya ya ce
“Abbah sam na manta da ranar ma sai yanzu”
“This is rubbish kasan hasarar kwangila irin wannan tana janyo a fara raina mana kamfani? Kowa ya sa rai mu za a bawa kwangilar nan amman saboda sakacinka komai ya lalace”
“Abbah kasan ba guri daya hankalina yake a yanzu ba”
“Fine ka mikawa Siraj ragamar kamfanin nan, a duk lokacin da ka dawo cikin hayyacinka sai ka kamfanin ya dawo hannunka, amman ba zai yiyu muyi ta hasara hakan nan kawai ba”
“Okay Abbah nima hakan zai fi min an gaskiya bana cikin kwanciyar hankali a yanzu”
“Ai kai ka jawa kanka komai saboda baka jin magana, da gaskiyar Hajiya (step mother dinsa) da take cewa na rika kyaleka duk da gangan kake komai”
Ajiyar zuciya Jibril ya sauke be sake cewa komai ba, yana ta sauraren fadan da Abbah ke masa, kamin daga bisani ya kashe wayar.
“Oh Allahna kai kadaine gatana”
Ya furta yana shafa fuskarsa. Siraj dake gefensa ya dashi
“Ka kwamtar da hankalinka Jibril komai zai wuce, matsalar ka kawai kana sakewa Nawwara ne da yawa, be kamata ace tana maka irin wannan cin mutuncin ba”
“Idan bata min wannan cin mutuncin Siraj ba zan taba gane cewar tana so na ba, kuma a duk lokacin da ta yi fushi ta kan fadi kalmar da zata amfaneni, jiya ma ta fadi kalmar wani Faruk wanda na fada maka maybe tsohon mijinta ne”
“Ba lallai ya zama tsohon mijinta ba Jibril ina ta nanata maka, maybe wani dan uwanta ne ko makocinsu, ni abunda na ke ganin ya fi kawai ka ka fitar da kudi sai a nemo wani wanda zai aureta ana daura auren sai ya saketa kaga shikenan sai kai kuma ka aureta hankali kwance zuciya zaune, sai a nemo wani talaka mai neman na kansa ko da tsoho ne Nawwara ta aura”
“Amman dai kai wawa ne Siraj, taya zan bari Nawwara ta auri wani? Ai itama ba zata taba yarda ta auri wani dan ta fito ta aureni ba, and ba zan iya barin kowa ya kwanta kusa da ita ba saboda har yanzu ita iyalina ce, duk wanda ya kwanta gado daya da matata sai na hora shi, ballantana kaddara ta kaishi ya kusanceta ko waye mutuwa kawai ta dace da shi”
“No Man no ba ina nufin ya aureta ba ya kwana da ita ba, ana daura auren zai saketa shikenan fa, idan kuma kana jinnrashin natsuwar hakan sai ka nemi wanda yake kusa da kai wadda ba zai musa maka ba sai ya aureta”
“Zan yi tunani akai, amman ina son ka bincika min gaskiya magana akan auren nan, and Abbah ya ce na mika maka ragamar kamfanin nan yanzu”
“What...?”
Ya amsa da karfi zuciyarsa kuma cike da farinciki.
“Saboda mai?”
“Ba komai kawai ina ganin kamar akwai wanda yake tsegunta ma Abbah wani abun ne akan kamfanin da kuma rayuwata, saboda kwanaki ma yayi ta min fada akan wai ina shan cocaine yanzu kuma yana fada akan kwangilar gobnatin taraiya da muka rasa ta gina gidaje, wai an fada masa ko takardar kamfaninmu bamu tura ba”
“Gaskiya akwai wanda yake labarta masa wani abu akai, amman gaskiya ni ba zan iya daukar ragamar kamfanin nan ba, taya kai za ace ka aje abu ni kuma sai ace na dauka? Gaskiya ba zai yiyu ba”
“No no he trust you ne, ai kasan Abbah idan be yarda da mutum ba ba zai saka shi a arkar kasuwancinsa ba, ni ma da be yarda da ni ba ai da ba zai kawo nan a wannan kamfanin ba, so karka bashi kunya kawai ka yi aikin nan nima zaka taimakamin domin zan samu na kula da Nawwara”
“Zan yi tunani a kai”
“Ba wani tunani sai ka karba”
Siraj ya tashi tsaye yana nuna kamar be jidadin abun ba, alhalin kasan zuciyarsa farinciki ne kawai da murna.
“Zan tafi xan sa ayi bincike akan Nawwara din”
“Thank you so Friend Allah ya bar mu tare”
“Amin akwai hoda idan...”
“Hodar nan tana daya daga cikin abunda Nawwara ta tsana, ina ta kokarin daina shanta ina son na zama mutumen kirki Siraj, ina da yaro a yanzu kuma ina son Nawwara ta dawo rayuwata dole ne wani halin za a zubar da shi”
Tabe baki Siraj ya yi.
“Nawwara dai Nawwara, ga Zinatu tana son ka amman hankalinka yana gurin wacce bata ganin tausayinka”
“Ka tafi kawai zai fi maka, bana son kana min maganar kowa ban da Nawwara”
Ya fice yana wani sunsun da kai. Yana fita Jibril ya kira Rabi ta waya yana fada mata abunda yake son ta yi.
“Bincike na ke son ki min akan Nawwara saboda na san Siraj ba zai samu dama ba a yanzu saboda shi ne new ceo din ku yanzu”
“New ceo Sir? Why ka bar garin ne?”
“No Abbah ya bukaci a bashi ni akwai abunda na ke, ki bincika sosai please”
“Okay Sir amman miye alakarka da ita saboda na san irin binciken da zan yi”
“She's my wife, my ex-wife mother of my only Son”
“Okay Sir zan yi komai inshallah”
Sai ya kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bathroom, in 40 minutes ya shirya ya fito ya nufi asibitin zuciyarsa cike da zumudin ganin dansa.
Tunda ya shigo cikin aaibitin ake ta gaishe shi har ya isa sashen da Noor yake be riko masa komai ba, saboda yasa a rika kawo masa abincin da abun tabawa daga wani kasaitaccen restaurant sau uku a rana.
Yana tura kofar dakin ya shiga, sai ya nemi farincikin da ke zuciyarsa da fuskarsa ya rasa, saboda ganin Bilal da ya yi zaune saman hospital bed din rumgume da Noor da ya shige jikinsa sosai ya labe kamar mai bachi.
“What are you doing here?”
Ya tambaya kamar be san inda Bilal ya fito ba. Uffan Bilal be ce masa ba ya yi kokarin sauke Noor daga jikinsa sai Noor ya kara lake masa wanda hakan ya bata ran Jibril.
“Uncle Bilal zan bi ka”
“Aa baka ganin baka da lafiya? Kana bukatar kulawa idan ka ji sauki da kaina xan zo na daukeka na kaina gida sai muje yawo ka ji”
Ya gyada masa kai yana kuka.
“Uncle Bilal zaka dawo anjima ko?”
“Eh zan dawo”
“Tau ka zo min da Momy”
“Zata zo, aiki take yi shiyasa bata zo ba”
Sai da Bilal ya shafa kansa sannan ya fita sai Jibril ya bishi a bakin kofar dakin ya jefa masa wata magana.
“Nawwara bata fada maka karka sake zuwa ganin Noor ba”
“Bata fada min ba”
“To ni na fada maka”
Bilal ya kalleshi ta kyau sannan ya ce.
“Look Jibril duk abunda na ke maka a kamfani ina yi maka ne sabida you're my boss a gurin kuma ina aikine dole duk abunda ka ce na bi, a waje ma ina respecting dinka so karka zubar da girmanka”
“Karka soma fada min wata maganar banza a nan, daga Nawwara har Noor mallakina ne”
“Noor ne kawai Mallakinka, amman Nawwara ba mallakinka ba ce, ka bar ganin kana da duka ba komai kudi yake siya ba, rashin arziki kuma ba shi zaisa takala ya wofintar da kanta a raina shi ba, ka taka a hankali”
Sai kawai Jibril ya yi dariya ya juya ya koma ciki. A ranar ya sha fama da Noor kamin Inna ta zo saboda Noor na ganin kamar Nawwara ba zata sake zuwa gurin ba, a ranar ya saka cewar kar securities din su sake bawa kowa damar ganin dansa in ban da Inna sai kuma wanda Inna ta fito da kanta ta zo da shigo da shi.
Da dare ya koma gida jikinsa agajewa ba dan kuma ya yi wani aikin ba sai dan tunanin da ke zuciyarsa ne ya saukar masa da gajiya. A lokacin ne Rabi ta kira shi take labarta masa abunda ta samo kamin fa kara bincike.
“Sir Nawwara ta auri miji biyu bayan baban Noor da auri wani Faruk amman ya rasu, sai dai mutane suna zargin cewa aurenta na fari ba aure ta yi ba saboda an boye abun kuma sai ta dawo gida da ciki”
Ya dan yi Jimm kamar ba zai ce komai ba.
“Ina kika ji wannan”
“A wani gidan makotansu ne na ji, saboda na nuna musu yayana yana son ya aureta ita kuma ta boye masa tace budurwa ce”
“Thank you, akwai wani abun da ya kamata na sani ne bayan wannan”
“Babu amman nace suna fama da talauci sosai, Babanta ya rasu saboda sukan da police suka masa akan sun kamashi ya yi sata wacce matar da yayanta suke cewa wai ba gaskiya bane, wasu kuma ce gaskiya ne, yar uwarta kuma ta rasu wacce ta fi so a cikin kananeta, zan fadada bincike nan har sai idan na kammala sannan zan labarta maka komai”
“Na gode, na san ba aikinki bane amman na gode, ki turo min account number dinki”
“Okay Sir thank you”
Yana sauke wayar sai duk jikinsa ya yi sanyi, wani irin tausayin Nawwara ya rufe shi. Ranar kwana ya yi da tunaninta da kuma tunanin irin wahalar da ta fuskanta gidansa. Washe gari sun da safe ya shirya ya nufi asibitin dan yana son ya yi breakfast tare da Noor, sai ya samu Nawwara bakin kofar harabar da zata sadata da dakin an hanata shiga, tana ganinshi ta sauke kanta kasa har sai da ya karaso kusa da ita.
“Nawwara da yanzu ban dawo rayuwar Noor ba, haka za ki yi ta masa bitar maratun na ko?”
“Akwai sama ko kasa da abunda ya kamata na karanta masa ne bayan abunda ya faru? Kana da sa'a Jibril komai kake so kana samu, na raini da na rana daya ya zo ya zama naka”
Ya cije lebensa na kasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce
“Kina ganin kamar darin duniya ne abunda kawai nake so? Ba shi ne kadai gata ba Nawwara, matukar babu ke babu Noor ina jin kamar rayuwata bata da amfani a duniyar nan, ni taimake ni Nawwara ki bani damar da zan zama silar farincikinki”
Ta tada kai ta kalleshi da idanuwata dake cike da kwalla.
“Idan na yafe maka zaka daina shiga sabgata?”
“Zan daina matukar za ki daina shiga rayuwar da na....!”
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
4⃣9⃣
JIBRIL POV.
Bayan fitar Nawwara ya zauna kusa da gudan jininsa yana ta kallonsa, shi kansa yana jin rashin kyauta a abunda ya yi ma Nawwara sai dai ya yi hakan dan ya bata ta a gurin iyayen Bilal, kuma ya banbance wanda ta fi so tsakamin Bilal da Mustapha.
Hannunsa yasa aljihu ya dauko wayarsa ya kira wata nurse ta kawo masa wani file tare da sai ya cire wata kadarda ya rubuta ma Noor takardar sallama, sannan ya dauki dansa ya saba a kafada hakan yasa Noor farkawa sai ya soma jijjigashi kamar jariri.
“Shiiiiii cigaba da bachinka Daddynka ne”
Hakan yasa Noor tafewa a kafadar Jibril ya fito tare da shi harabar asibitin ya sakashi gaban mota sannan na zagayo ya shiga driver seat ya tashi motar sai kuma ya daga wayarsa ya kira wata number
“Ki shiga dakin da aka sallami Noor ki kwashe komai zan aiko da dareba ya dauka”
Yana fadar haka ya kashe wayar, ya tashi motar ya hau titi dake cikin asibitin kamin ya sadu da babban titi marafa dan baba da ke cikin birnin sokoto.
Duk bayan seconds ya kan kalli gefen da dansa yake sai idanuwansa su cika da kwalla, hamdalla yake yi ma Allah akan yau yana da gudan jinin wannan dalilin kadai ya isa yasa ya cigaba da tirsasa kansa gurin Nawwara, domin ita ce kadai macen da ta kawo masa wannan farinciki a rayuwa, bayan ya yanke tsammanin zuwansa.
‘I promise you Noor i will to my very own best na ga na zama uba na gari a gareka, i will make you and Nawwara proud of me’
A kasan zuciyaraa yake wannan tunanin yana sauke ajiyar zuciya.
“Ba zan iya hakura da kw ba Nawwara, kema kina bukatar farinciki a rayuwarki, ni na bata komai dan haka ni ya kamata ace na gyara komai”
Wannan karon a fili ya yi furucin yana danna horn a bakin gate din gidansa, a hankali ya yi parking sannan ya dauko wayarsa ya yi ma Nawwara text akan cewar an sallami Noor saboda kar taje asibitin bata tarar da kowa ba, sannan ya fita motar ya zagaya ya bude ya dauko Noor da ke kokarin bude idanuwansa.
“Zan iya tafiya”
Ya fada saboda ya samu a sauke shi ya samu kallon gidan da kyau, kamar Jibril ya sani sai ya sauke shi ya rika hannunsa suna tafiya a hankali, rabon ido kawai Noor yake kamar zasu fado sabo kallon yadda kukasan wani tsohon bakauye, yana saka kafarsa cikin falon sai sayin tile din ya ratsashi ga sanyin ac da ya mamaye ko ina a cikin falon, suna shigowa Jibril ya sake shi ya nufi bedroom yana amsa waya, sai Noor ya daga kansa sama yana kallon pop falon da fankar kamin da dawo gurin kujerun falon da suka katsance farare sol kamar fentin falon da kuma center carpet din da ke falon, karasawa ya yi gurin kujeru sai ya zauna kasa ya kai hannu yana shafa manyan cushion din idanuwansa kuma suna kan katuwar plasma TV mai daukar ido gashi an kawata gurin da wallpaper fari mai daukar hankali, ga wasu manyan flowers da aka aje a gurin suma farar kamar labulayen falon.
“Noor Son tashi tashi zauna saman kujera ya zaka dauka kasa”
Jibril ya fada ganin dansa a kasa kamar wani almajiri.
“Momy ta ce idan mun shiga gidan mutane mu daina hawa musu kan kujera, kuma wasu mutane fada suke idan aka hau musu kujera”
Noor ya fada yana kallon Jibril da ya risino da kansa ya dauke ya dora saman kujerar ya rumgume ya lumshe ido, jikinsa ya yi sanyi sosai taya za a ce yana da irin wannan kudin amman ya kasa bawa dansa kulawa ta musamman da har wani abun na duniya zai burgeni ya kasa hawa? Shi ai iyayensa sun bashi kulawa taya ya kasa bawa dansa?
‘Lokaci be kure ba yanzu ma zaka iya he's still a boy’
Wata zuciyar ta amsa masa wanda hakan yasa shi jin sauki, har ya bude ido ya kalli hoton Nawwara da Noor ke nuna masa.
“Laaaa ji Momy can”
“Kai ma za a maka naka ina son ka sosai Noor”
Noor ya dago ya kalleshi ganin ya yi masa abunda ba a saba masa ba, wato kiss shi dai yana ma Momysa amman ita bata masa jara ma Mama Habiba wani lokacin tana masa kiss idan ya yi abun kirki.
“Me kake so ka ci?”
“Bana jin yunwa a yanzu sai anjima, amman akan wacan abun zan ci”
Ya fada yana nuna dinning area da aka kawata da farin dinning table da aka kawata da farin cabinets mai kyau da kuma freezer da ke hade da cabinets din har baka iya banbancewa. Jibril ya shafa kansa yana murmushi.
“Idan ma a saman dakin nan kake son cin abinci Noor zan dora ka ka ci, ka saki jikinka nan gidanku ne”
“Da gaske?”
Ya gyada masa kai.
“Har da Momy nan zata zo mu zauna? Kuma da Inna?”
Ya sake gyada masa kai yana murmushi, sai Noor ya sauka saman kujerar yana kallon falon bakinsa har kunne hakuran nan a watse bakauye ya shigo gari.
“Can ina ne?”
Ya nuna Kitchen.
“Jeka ka gani”
Sai ya mika hannunaa ya riko hannun Daddynsa
“Aa zo muje tare dai”
“Idan na rigaka isa ba zan bari na shiga ciki ba idan kuma kai ka rigani isa ba zaka bari na shiga ciki ba, ka yarda?”
Ya daga kai yana dariya, sai suka fara yar tseren gudu shi da Jibril da yana lakkame da hannunsa mai ciwo, da gangan Jibril ya bari Noor ya riga shi isa sai duk suka rika dariya Noor har da tsalle, abunda ya dauki hankalin babansa sosai yana kallonsa kamar ya hadeyeshi saboda Kauna.
Suna fitowa daga kitchen din suka sake rigangan shiga bedroom haka suka bi suka zagaje gidan Jibril ya nuna masa ko ina har Swimming pool, a Garden sai da Jibril ya hau icen guava ya katso masa sannan aka sauna lafiya.
“Acan za a saka maka lilo”
Jibril ya fada yana nuna wani bangare na Garden din, sai Noor ya zaro ido.
“Da gaske”
“Eh har dakinka za a maka daban, a saka maka komai da komai har da tv ka da games”
Dadi ne yasa Noor ya rumgumeshi yana dariya, sai kuma ya dago kai ya kalleshi
“Sai gobe zamu je mu lallabata sai ta dawo nan mu zauna, mu a nan zamu kauna har gobe ko?”
Ya daga masa kai, sai Jibril yasa hannunsa ya daukosa suka nufo falo, saman kujera ya zaunar da shi ya yi masa hotuna kala kala har da video sannan ya kunna masa tv ya saka masa kids channel sai yazo ya dauke ya rumgume suna kallon tv tare.
NAWWARA POV.
Tsayawa na yi kallonta saboda na tantancewa idanuwa ita din ce ko kuwa wata ce mai kama da ita, idan har ita dince to gaskiya ta canja sosai fuskarta ta yi kala biyu fari da kuma wani farin na daban, ga wata uwar rama da ta yi fuskarta ta matse sosai.
“Na san zaki yi mamakin ganina Nawwara, kin yi kokari da baki manta fuskata ba duk tsawon wannan lokacin”
“Taya zan manta fuskar da ta kwace min yan ce a gidan aurena? Fuskar da mijina ya fifita sama da tawa”
“Ashe har yanzu a akwai soyayyar Jibril a cikin zuciyarki tun da har za ki iya kiransa da sunan mijinki”
“Miya kawo ki gidanmu? Taya kika zo me kike nema a gareni?”
“Wacce daga cikin ukun tambayar ki nan zan fara amsawa?”
“Duka zaki amsa min kuma ki tashi ki bar mana gida”
“Zan tafi Nawwara gidanku ya yi min yawa da zama, amman ina son ki bani lokacin ki ki saurari abunda zan fada miki ko kuma na ce zan rokeki”
Kamar ba zan zauna ba, sai kuma na zauna saman gadon Inna ina kallonta da jiran abunda zai fito bakinta.
“Na san za ki yi mamaki ganina a wannan lokacin kuma a cikin gidanku, abun da ya fi ko wanne mamaki ma taya aka yi yarinyar da ke Abuja ta zo har sokoto kuma ta gane gidanku ko”
“Ba abun mamaki ba ne Jibril zai iya fada miki”
Na fada mata kai tsaye, sai ta yi murmushin da ke nuna cewar maganar ta soketa.
“Mai zai sa Jibril ya fada min inda kike bayan ya gargade da cewar na fita daga rayuwarsa? Rabon da na saka Jibril a ido shekara biyu da rabi kuma saboda ke Nawwara”
“Ni kuma?”
Na tambaya da mamaki sai ta gyada min kai.
“Ke fa, sai bayan ya rabu da ke ya gane yaudarar kansa yake da cewar baya son ki, ni kaina a wacan lokacin na san yana sonki ko da kuwa baya son ki tau ya san kimarki domin baya taba bari wani ya fadi wata magana marar dadi gareki a gaban idanunki ko bayan idonkin ciki kuwa har da ni”
“Ban tambayeki labarin abunda ya wuce ko abunda zai zo gaba ba, dalilin zuwanki kawai nake son ji”
Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleni idanuwanta raurau ta ce.
“Yafiyarki na zo nema Nawwara”
“Ai ni baki min komai ba”
“Na yi komai Nawwara, na tozarta aure na yi amfani da dama ta na ci mutunci auren wata taya Allah ya zai bar ni na gina tawa rayuwar auren a cikin kwanciyar hankali? Bayan ban so yar'uwata abunda na so wa kaina ba?
Kaddarorin rayuwa sun yi ta faruwa da ni Nawwara wanda na ke sa ran saboda na ci mutuncin aurenki ne, a iya sanin da kika min ina budurwa har yau ina nan haka ban yi aure ba, a lokacin da muke soyayya da Jibril muna tsaka da maganar aure sai kawai babansa ya cilasta masa aurenki, a wacan lokacin Jibril sai yake ganin kamar idan ya rabu da ni be aureni ya ci amanata, da wannan damar na yi amfani na dauke masa hankali, ni da kaina na rika jan ra'ayinsa har muka fada kogin aikata alfasha wato zina, a tunani wayewa ce na yaudari kaina sosai da sakewa namiji jiki tun kamin ya aureni, ba ni da tufafin sakawa sai na tsiraici gyale ma irin wanda zai bayyana siffar jikina na ke sakawa saboda na dauki hankalinsa, haka duniya ta yi ta yaudarata har muka tsufa a kogin alfasha ban ankaro ba, bayan Jibril ya rabu da ke sai na bijirowa da Jibril maganar aurenmu abun mamaki sai ya ki amincewa, kin san dalili? Saboda ya riga ya san ni a ya mace tun kamin ya aureni, sai ya zamo baya ganin kimata kuma rashin yarda ta shiga tsakaninmu har ta kai shi da kansa yake cewa ko ya aureni ba zai samu natsuwa ba domin zuciyarsa tana raya masa bayan shi zan iya taraiya da wasu mazan, ina ji ina gani Jibril ya auri wasu matan ya bar a lokacin na ko sunana baya son a kira, ni kuma na gagara samun wani mijin aure na kirki saboda kowa kallon yar iska yake min, saboda na riga na gama zubar da mutunci na tun a yanayin suturata, duk wanda yanzo ba da aure zai neme ni ba sai dai da lalata ko kuma soyayya, wadanda suka zo neman aurena da gaske kuma sai a bi a zuge, a haka zama garin Abuja ya gagareni na koma gurin Yayata Kaduna, na natsu sosai a lokacin na zama ta kwarai fiye da yadda kike tsammani, amman mutuncin da na gagara tsarewa tun a wacan lokacin sai ya kasa bani damar na yi rayuwa yadda na ke so, a haka na fara shafa man nan na mai saka haske wai ko farina zai karu na kara burge maza amman a banza sai ma lalata fatata da na yi, ke ce kadai kika tsaya min a rai ina gani kamar hakkin ki ne yake bibiyata dan Allah dan girman Allah dan darajar Annabinsa ki dubi girman Allah ki yafe min Nawwara”
Kuka take sosai tana kokarin kama kafafuna, wanda hakan ke tabbatar min da cewar lallai Aysha ta yi nadama, sai dai me abunda bata sani ba, ba hakkina ne kawai yake binta ba, tabbas hakkin aure ba zai barta ba saboda ta tozarta da aure a lokacin da ta samu dama, amman an baro kyau tun ranar haihuwa, domin kuwa ta yi abun da yan mata yanzu suka dauka wayewa wato bayarda kai ga Namiji tun kamin ka aureshi da kuma shigar banza wacce Annabi Allah da kansa yake cewa masu wannan shigar tufafin ba zasu shiga aljannaba kuma ba za su ji kamshinta ba, taya namijin da ya sakin tun a gidanku zai yarda ya aureki? Ko da kuwa ya aureki ba zai taba ganin darajar ki ba kuma babu aminci na zaman aure a tsakaninku har a bada ga kuma azabar Allah tana jiranki matukar baki tuba ba, daman shi namiji duk abunda ya aikata ado ne, ko ina a qur'ane idan Allah zai ambata da da namiji yake farawa sannan mace amman da aka kai babin Zina sai Allah ya fara da macen kamin namiji saboda mace tafi shiga tarko kuma idan bata bada dama ba babu yadda za ayi ta namiji ya aikata.
Ajiyar zuciya na sauke zan yi magana sai ga text ya shigo a wayata na Jibril, wai an sallami Noor kuma ya tafi gida da shi sai gobe za su zo nan. Aje wayar na yi na kalleta zan yi magana sai ga Inna ta shigo cikin dakin tana tambayar lafiya jin shisshikar kukan Aysha.
____________________________________
Al-hamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin da ke ba mu lafiya da rashinta, na samu sauki sosai na gode sosai da kukawarku da addu'o'inku Jazakallahu Khairan 😘
Let my advice be here, For those ladies da suke daukar mallaka kai ga saurayi ko da an muku engaged a matsayin wayewa ko soyayya Wallahi babu soyayya babu wayewa a cikin zina, kuma ko da mutun ya aureki baki da wata kima da mutunci a idanuwanshi, wani ma ba zai aureki ba kin ga kin ga kin zubar da mutunci a banza, kar kalaman banxa su yaudari zuciyarki kar karatun wasu littafan yasa ki rika daukar saka suturar banza a matsayin wayewa Wallahi ba duka writers ba ne include me suke rubuta dai dai ko rashinsa ba me some of our readers suna daukar dukan abunda aka rubuta ko abunda duniya take yayi a matsayin wayewa wanda sam ba haka ne kama mutunci da kimarki shi zai nunawa duniya ko wacece ke kuma mijinki da yayanki zasu yi alfahari da wannan, kar ki ga wata ta yi haka at the end ta auri a mijin kwarai a novels ne ko movies irin wannan abun yake faruwa, in reality 75% basa auren mutanen kirki matukar kika maida kanki karuwa babu namijin kwarai da zai so ki a matsayin matarsa, su ma mazajen na banza ai matan kwarai suke nema su aura, be wise, women with attitude na kwarai a lady with class class din kuma na kare mutunci ba na zubarwa, ko da ke ta kwarai a irin shigar da kike wani zai dauka ke yar iskace ko kuma marar tarbiya.
Some will say ya zata kawo mana wannan dogon sharhin nan ko? 😂 Wallahi abun yana ci damuna ne sosai kuma wannan ce kadai damar da na ke da ita wanjen yin wannan bayanin. Wanda na batawa rai ya yafe min Allah ya shirya mu gaba daya.
See you next page i can't wait na ji labarin da Rabi zata bawa Nawwara 💃idan Nawwata ta ji za tayi wani abu kuwan? Anya Iayayen Bilal zasu bari ya auri Nawwara kuwa? Duka zai zo a next page Inshallah. 😘
*RAI BIYU...♥🖤*
Wattpad @KhadeejaCandy
_This Chapter is yours Auntie Sis♥_
5⃣0⃣
“Lafiya?”
Inna ta tambaya.
“Lafiya kalau magana ce kawai muke”
“Kin tabbata?”
“Ba komai Inna”
Ba dan ta yarda ta juya ta koma waje, ni kuma na gyara zamana na kalli Aysha na ce
“Ba ni kika cuta ba Aysha kan ki kika yi ma, daman duk mai cutar wani yana jin dadi kansa yake cuta domin alhaki zai dawo akansa wata rana, idan ma hakkina ne yake bibiyarki Wallahi na yafe miki daga yau ba zai sake binki ba”
Dagowa ta tu ta kalleni da idanuwanta da take faman kuka da su bakinta na rawa ta ce
“Wallahi Nawwara ke ta daban ce ban tsammaci zaki yafe min da wuri haka ba, na gode sosai Allah ya saka miki da Alheri”
“Amin, amman dan Allah ina son ki fada min taya aka yi kika gane gidanmu?”
Sai da ta share hawayenta ta koma saman kujerar ta zauna daidai sannan ta kalleni
“Siraj ne ya kwatanta min”
“Siraj kuma? Waye haka”
Na mata kamar ban san waye shi ba.
“Wani abokin Jibril ne, shi kadai ne wanda Jibril ya aminta da shi a yanzu, shine kadai mutumen da yake karfafa min guiwar cewar zai yi duk yadda zai yi wajen ganin Jibril ya aure ni”
“Yanzu kina nan akan bakarki cewar Jibril rai aureki duk bayan yaudarar da ya yi miki?”
“Bana jiransa shi kadai, idan wanda zai aureni da gaske ya zo zan aureshi, na dade da yafe masa abunda ya yi min saboda na san tun farko laifina ne ba nasa ba, kuma har gobe ina son Jibril”
Na sauke numfashi a hankali ina mamakin karfin hali irin nata son wanda baya son ka, ko da yake ya so ta da farko,amman ai ya cuce dan me zata wahalar da kanta gurin son sa. Kamar ta san abunda ke raina sai kawai ta ce
“Na san za ki yi mamakin jin har yanzu ina son Jibril, ke ma da ace kina son shi tun farko ko kuma rabo ya shiga tsakaninku da za ki kula shi, ko da yake Siraj ya fada min yanzu matsalar rashin haihuwa take damunsa shiyasa babu ruwansa da ko wace mace”
“Haka ya ce miki? Yaushe rabon da ki yi magana da shi?”
“Ko jiya mun yi waya da shi”
“Amman har yanzu be fada miki Jibril na da da ba?”
“Haka ya ce min Jibril ba shi da da kuma ya lalata rayuwarsa da shayeshaye hakan yasa mahaifinsa ya koreshi daga kamfanin da yake ya dora Siraj”
“Amman gaskiya Jibril be kyautawa rayuwarsa”
“Ni ma da na ji ban jidadi ba, amman Siraj ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya dawo da shi hanya”
“Allah ya bashi iko”
“Amin”
Sai da ta shafe fuskarta ta gyara Hijabinta sannan ta dauki jakarta ta rayata ta mike tsaye.
“Na gode sosai Nawwara zan wuce”
Har bakin kofa na rakata sai zuciyata na ta tunani akan abokinsa Siraj, miyasa be fada mata cewar yana da da ba? Haka ma yasan lokacin da na fara aiki a kamfanin amman be sanar da Jibril bayan yasan Jibril yana neman ganina, amman kuma miye damuwata da shi ai abokinsa ne babu ruwana a ciki, maganganun Rabi ne suka fado min a rai kan na ankaro Inna ta jefo min wata tambayar.
“Wacece wannan yarinyar? Kamin nan miye shigo da ke kina kuka?”
Sai a lokacin na tuna da cewar na shigo ina kuka, sai wacan bacin rai ya dawo min na soma jin tsanar Jibril sosai a raina. Kusa da ita na zauna.
“Inna wannan Aysha wacce ta yi soyayya da Jibril ce lokacin da ya aureni, ita ce wacce ya ce yana so, shine yanzu take neman gafarata”
Haka na kwashe firarmu gaba daya na fada mata irin halin rayuwar da ta ce ta shiga bayan rabuwarsu da Jibril, sai kuma na dora mata da bayanin abunda Jibril ya yi min kamin ya fada mata cewar ya ansallami Noor daga asibiti.
“Jibril be kyauta ba, be da ce ya yi miki haka ba, ina tunanin ya yi haka ne saboda ya bata ki a gurin iyayen Bilal kuma suma ya saka musu fargabar wani abu zai iya faruwa da dansu matukar ya aureki”
“Ni Inna na tsane Jibril bakin mugu ne Wallahi ni ya dawo min da yarona ba zan barshi ya kwana a can ba”
Na fada ina shirin fashewa da kuka.
“Ai kara ki kyale Noor ya shaku da Ubansa tun wuri domin kin san dai Jibril ba zai ta ba bari ki je masa agolanci da dansa ba, ke ma kuma ba za ki ji dadin zaman auren ba matukar kika je da Noor domin Mahaifinsa zai rika amfani da wannan damar yana cin zarafinki da mijin da zaki aura, idan kuma mijin da kika aura ya nuna baya son zaman Noor ki ce baya son ki”
“Allah ka min mafita”
Na fada a fili a zuci kuma na ce Jibril din nan yabi ya tare min ko ina bana da wani sakewa. Muna nan zaune su Sakina suka dawo daga islamiya sai muka dauko wata firar har take fada mana wai malaminsu ya ce satin saman za a kawo kudin da zasu ba iyayensu domin su cigaba da daukar nauyin karatunsu.
“Wai Inna ba zamu koma sabon gidan nan ba?”
Ta tambaya, ni har na manta da maganar gida domin ban taba zuwa ma ganinsa ba.
“Ba zamu koma ba, ko kudin nan ba zamu karba ba duk Jibril ne yake shirya wannan abun, saboda ya siye mu da dukiyarsa”
“Ya fada miki shine?”
Inna ta tambaya.
“A a amman na san shi kadai zai iya wannan abun, idan ba shi ba ne waye ne”
“Nima na yi wannan tunani”
“Dan Allah Inna karku sake karba komai na sa idan ya baku, Wallahi mutumen ya raina mana hankali sosai ma saboda ya maida mu talakawa, ai da masu kudi ne mu be isa ya taka mu ba”
“Kin dai ce kin yafe masa, bana son wata rigima kuma bamu je muka rokeshi ya bamu ba bana son wata fitanar kuma”
“Ba zan yi komai ba ai, amman kawai abun yana ci na sosai Wallahi ya ci amanata sosai, kuma ya raina min da wayo da har zai ce ya wai yana neman ya sake aureni, Wallahi aurena da be so da Bilal sai an yi sai dai ya mutu azzalumi kawai”
Na fada cikin daga murya hawaye na zuba a ido, ji nake kamar ace Jibril yana kusa da ni yanzu na shakeshi ya mutu. Bayan mun yi sallah magariba na kira Bilal a waya sai ya dauka, na yi tsammanin zan ji shi a cikin wani yanayi marar dadi ko makamancin haka amman sai ya zo a kasin tunanina na jishi cikin farinciki da walwala
“Yar halak kin kirani daidai lokacin da zan kiraki na ce ki fito waje gani nan”
“Bilal kai ne”
“Ni ne mana, wani kika je kira ne kika kirani?”
“Aa kawai na ji na cikin farinciki”
Ya yi dariya
“Cikin bakinciki kike son jina”
“Aa kawai na dauka zaka ji haushi na ne kai da Abbah”
“Akan me zan ji haushinki Nawwara, abunda kika aikata be kara min komai ba sai kaunarki, yanzu dai fito gani nan kofar gida”
Daga haka ya kashe wayar ni kuma na lumshe ido cike da jindadi na sauke ajiyar zuciya, sannan na fadawa Inna na dauki Hijabi na saka na fito kofar gida, jingine da ginin gidan na sameshi kamar kullum yana jiran fitowa.
“Pearl”
Na kalleshi fuskarta da murmushi.
“Wallahi ban tsamaci haka ba ko kadan, na yi tsamanin Abbah zai maka fada ne”
“Nawancy kenan, ya yi min fada sosai amman akan rashin kunyar da na yi ma Hajiyar Mustapha ba wai akan abunda ya faru ba, kuma ko da yayi min fada akan ai ba zan dora laifin akanki ba, shine ma ya bani shawarar karna fadawa Mama cewar kin je station domin ya fahimci muna son junan kuma idan Mama ta ji zata yi fada”
“Na gode Allah da Abbah ya fahimta”
“Kuma ya ce na fada miki cewar Assabar din nan mai zuwa zai zo ya ga su Baba Sulaiman”
Na rufe idona da sauri saboda dadi da kunya da suka rufe ni lokaci daya.
“Da gaske?”
“Aa da karya”
Ya fada da fuskar zolaya, sai na sa dariya.
“Mama fa mi ta ce?”
“Me kike tsammanin zata ce?Addu'a kawai ta yi mana da fatar Allah ya sa alheri a ciki”
Na san yace haka ne kawai dan ya kareta amman ba zata so aurena da danta saboda tana ganin kamar kwaruwace xan yi ma danta bayan na yi aure biyu har da kuma yanzu na ce zan auri danta. Mun sha fira sosai a wannan daren sai da aka fara kiran sallah isha'i sannan muka yi sallama ba dan ran mu ya so ba ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindadinta akan maganar har ma ta yi mana addu'a, daga baya kuma ta tambaya abunda iyayensa suka ce kan abunda ya faru yau, ni kuma na labarta mata kamar yadda ya labarta min.
Bayan mun gama sallah isha'i wayata ta yi ringing ko da na duba sai na ga number Rabi na yi mamakin kiranta a wannan lokacin sai dai hakan be hanani dauka ba.
“Assalamu alaikum”
“Wa'alaikissalam Nawwara kina gida?”
“Ina gida lafiya dai?”
“Lafiya kalau akan maganar nan ne, bana son na yi shigowar rana wani ya gan ne, alhalin kuma ba Oga Jibril ba ne ya aiko ni”
“Yanzu zaki zo kenan”
“Idan zan samu dama ba”
“Allah ya kawo ki lafiya”
Daga haka na kashe wayar sai ga kiran Jibril ya shigo wayata, da gangan na ki dauka saboda ina tunanin wata maganar zai min ta daban, har sai da ya yi min kira fiye da uku sai kuma ya aiko min da sako karta kwana wato sms cewar Noor ne yake son magana da ni, da ya sake kira sai na dauka cikin rashin walwalah saboda tsanarsa da na ke ji cikin raina.
“Hello”
“Babe-Naj ga Noor zai yi magana ina fatar kina lafiya”
“Zan bashi but ki amsa min mana ko sanyi na ji”
“Zan kashe wayar idan baka ba shi ba”
“Allah ya huci zuciyarki, ya dorani akan ki Naj”
Yana fadar haka ya mikawa Noor wayar.
“Hello Momy ina wuni? Momy i miss you”
“I miss you too miyasa ka bi Daddynka ba ka zo nan ba?”
“Daddy ne ya zo da ni, kuma ya ce ke ma za ki zo gobe, Momy ki zo yanzu mu kwana nan dan Allah”
“Ba zan zo ba Noor, gobe ma ba zan zo ba har abada ba zan zo ba, idan kana son zama da ni ka ce ya dawo da kai gidanmu”
“Saboda me ba za ki zo ba?”
“Saboda nan ne gidanmu ni ba zan zauna ko ina ba sai gidanmu”
“Momy gidan yana da kyau fa, har ya fi na su Sadiq kyau dan Allah ki zo”
“Ba zan zo ba Noor, idan kana son zama tare da mu ka ce ya dawo da kai gida gurin mu”
“Momy zan yi kuka”
Ya fada cikin muryarsa mai nuna yana shirin yin kuka da gaske. Sai na ji muryar Jibril yana fadin
“No no don't cry Noor tana maka wasa ne kawai zata zo”
Ni kuma na katse wayar na kalli Inna.
“Inna rabi zata zo yanzu, akwai maganar da zamuyi da ita”
“Wace magana ce?”
“Wallahi nima ban sani ba, amman dai ta ce tana da muhimmanci sosai”
“Da wa kike waya yanzu”
“Noor ne”
“Amman shine kike fada masa wannan maganar kamar wani babba? Kina son ki saka danki a damuwa ko? Ki raba masa hankali gida biyu”
“Amman Inna ai kara na fada masa gaskiya saboda yasan ba zan taba zama da mahaifinsa ba tun yanzu”
“Amman be kamata ki masa magana ta wannan hanyar ba, ki daina sauke masa haushin mahaifinsa akansa”
“Inshallah Inna ba zan kara ba”
“Allah ya kyauta gaba”
Sai da na amsa da Amin sannan na tashi na soma duba dakin inda be kintsu ba kimtsa saboda kar Rabi ta zo ta tarar da dakin ba a natse ba.
Tara saura kwata ta Rabi ta shigo gidanmu da lullubinta na katon gyale kai baka ma ce ita ba ce, duka muka hada baki gurin amsa mata sai na fita na shigo da ita cikin dakin ta gaisa da Inna sannan Inna da su Sakina da Jamila suka fita waje suka bar mu mu kadai.
“Ina tunanin babu wani gurin da ya kamata mu yi maganar nan sama da gidanku shiyasa na zabi na tarar da ke a gida, kuma idan da dare ba kowa zai gan ni ba balle har a tsammaci wani abu”
“Me kike so mu tattauna mai muhimmanci har haka?”
“Na fada miki akan ki da kuma dan ki da kuma Noor”
“Me muka yi?”
“Ba ku yi komai ba sai dai wanda ake shirin yi muku”
“Ban fahimta ba”
Ta sauke ajiyar zuciya.
“Nawwara ke kadai ce mace da zata iya tsamo Jibril daga tarkon Siraj a yanzu, ke kadaice zaki iya raba alakar da ke tsakaninsa da Siraj a yanzu”
“Miye nawa a ciki da har zan shiga na raba alakarsu? Babu komai fa tsanina da Jibril”
“Na san babu komai a tsakaninku a yanzu, amman ai akwai yaro tsakaninku, iya abunda na fahimta Oga Jibril yana son ki sosai, ke ce kadai zaki iya anrar da shi daga ramen da yake kokarin fadawa”
“Ni fa ban gane wannan bayanin na ke ba”
“Nawwara Siraj ba abokin kwarai ba ne, kokarin zamewa Oga jibril kafafu yake ya dilmiyar da shi, kokarin kwace duk wani abu da Jibril ya mallaka yake kokarin ganin ya zama na sa.
Sunana Rabi'at Abdulrazak, ni ba bahaushiya ba ce ni ibira ce asalina ni yar jihar kogi ce, ina zaman gurin Antyna ne a Abuja bayan na gama karatu na, daga baya na samu aiki a kamfanin One on One limitless company da ke Abuja, da sannu na fara aikina kwarewata da kuma jajircewa ta a akan aiki yasa mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir yake yaba min sosai kuma ya dauki yarda ya bani, lokacin da zai turo Jibril aiki a nan sokoto sai ya sa muka zo tare akan na rika kula da duk wani abu da Jibril yake yi saboda yana ganin kamar Jibril ba zai iya kula da kamfanin yadda ya kamata ba, da muka dawo nan sai Jibril yasa aka yi ma Siraj transfer daga Abuja zuwa nan, ban san cewa Siraj abokin Jibril ba ne sai a wannan lokacin, ba zan iya fada miki dalilin alakarsu ba domin ni ma ban sani ba, amman da aka dawo da shi nan sai Jibril ya dauki yarda da amana ya mika masa, idan be samu zuwa meeting ba Siraj yake turawa, komai za ayi sai ya ce a a nemi Siraj”
Ta gyara zamanta kana ta yi dariya.
“Ba ina kishin Siraj ba ne Nawwara, sai dai akwai abubuwan da na lura da su akan Siraj, ina tunanin kamar shi ya koya masa shan cocaine saboda ua haukarta shi ko kuma ya juyar da hankalinsa zuwa wani gurin ba dan damuwar Jibril kawai ba, idan har dan damuwa ce shi Siraj baya da ita? Miyasa baya sha sai Jibril yake bawa? Abu na biyu ni yake sa na kira mahaifinsa na fada masa dukan abunda yake gudana a kamfanin marar kyau, Siraj ne yayi kokarin kashe Noor saboda yana tunanin idan har Jibril ya san yana da da zai sashi ya daina abunda yake kuma ya natsu, wanda ba haka Siraj ke so ba kuma yana ganin kamar idan Noor yana raye dole wata alakar zata sake kulluwa tsakaninki da Jibril wanda baya son haka shi be ki ma Jibril ya mutu ya mamaye dukiyarsa ba, da hadarin ya faru sai ya dorawa Bilal laifin ta hanyar sanar da Jibril cewar wani ya fada masa cewar Bilal ne ya yi kokarin kashe Noor saboda yana bakinciki Jibril, wannan yasa Jibril ya koreshi daga aiki har ma yayi kokarin kai kararsa kotu amman sai Siraj ya hana a cewar su wai basu da hujja su jira har sai an samu wani abun na daban wanda zasu rike su yi hujja da shi, ke kanki rayuwarki tana cikin hadari domin Siraj zai iya sawa a kasheki kuma a kashe Noor saboda Noor ya ga fuskarsa lokacin da ya yi kokarin kadeshi da mota, ya yi nadanar hakan kuma ya ji bakinciki sosai da Noor be mutuba, daga baya kuma sai ya wani tunanin ya zo masa cewar miyasa be sa wani ya aikata ba sai shi ya aikata? Wannan ya tabbatar da cewar nan gaba ba da kansa zai je kashe ki ko Noor ba wani ko wasu zai sa su yi, yana tunanin idan ya yi haka shikenan ya gama da rayuwar Jibril sai kuma ya yi amfani da cocaine ya karasa halaka shi.
Na san zaki yi mamakin jin haka ko kuma ki yi mamakin a ina na san duk wannan ko? Na sani ne saboda Siraj ya fada min, yana amfani da ni ne a matsayin wacce mahaifin Jibril ya yarda da ni, ya ce min zai aureni kuma duk abunda ya samu zai raba rabi ya bani rabi abunda yake kokarin yi yanzu ya mallaki nasa kamfanin ta karshin wannan kamfanin, a yanzu haka mahaifin Jibril ya sauke Jibril ya dorashi akan kamfanin kin ga ya fara samun dama kenan, ni kaina rayuwata tana cikin hadari domin mugun mutum baya yarda da kowa, ni kaina xai iya cutar da ni idan ya samu abunda yake so, saboda yana ganina kamar ba bahaushiya ba yasa yake son ya yi amfani da wannan damar ya cilla burinsa saboda yana ganin kamar muna da son kudi kuma idanuwana a bude suke, na masa na amince ne saboda na san idan har na ki amincewa zai iya kashe ko ya kulla min wani sheri saboda ya san na san sirrinsa, kuma a matsayin na wacce ke aiki karkashin Jibril ba zan iya fada masa wannan ba, bana da wata hanyar sai ta ki, ke kadai ce zaki iya hankaltar da shi domin ceton rayuwarki da ta danki da kuma ta Jibril har ma da tawa gaba daya, ki kuma tsirarta da Bilal daga sherin da yake kokarin laka masa, kin san idan wani abu ya samu Noor dole Jibril ya zargi Bilal kuma ba zai taba kyaleshi ba”
Hannu nasa na rufe bakina sai kuma na sauke ajiyar zuciya, kaina ya yi nauyi sosai kalamanta sun min hawa har na rasa wanne zan fara tunani balle na samu abunda zan ce mata, ji na yi ta dafani.
“Nasan yana da nauyi Nawwara, ki yi tunani akai, ban san abunda ya raba ki da Jibril ba, amman yana da kyau ki shiga rayuwarsa ko dan gaba ko kuma na ce ko dan danki, abu na karshe da zan fada miki shine Jibril yana son ki sosai da sosai, domin lokacin da Siraj ya sanar masa cewar kin mutu ya yi kamar na haukace, ba sai na gargadeki akan karki fadawa kowa wannan sirrin ba saboda ina ganin a mace mai tunani da hangen nesa na barki lafiya”
Da ido kawai na bita har ta fice, sannan na dawo duniyar mamaki da aljabi anya zan iya wannan aikin kuwa? Mi ma zai kai ni taimakon mutumen da ya nemi salwantar da tawa rayuwar? Abu na farko da ya zo min a rai shine Inna dole ne na fada mata komai ko dan neman shawararta, cikin hanzari na tashi na fita waje gurin Inna.
0 comments:
Post a Comment