TSOHON ALKAWARI 1
.
Nazir Adam Salih (Nas)
.
A ranar ashirin da takwas ga
watan Afrilu na shekarar
Milladiyya ta dubu biyu da guda
hudu wacce ta yi daidai da ranar
Laraba na tashi a rude,
kwakwalwata a cunkushe domin
sama ko kasa na nemi sabuwar
basirar da zan yi rubutu na rasa.
Tun misalin karfe goma nake
zaune na sa littafin a gaba ina
kallo har zuwa karfe goma sha
biyu na rana kwakwalwata ba ta
zo min da komai ba sai tunane-
tunane marasa amfani. Ina nan
dai zaune cikin akurkin dakina ni
kadai da biro a hannu sai
jujjuyashi nake yi kamar sigari
daga karshe dai na tabbata ta
kare min dan haka sai na ajiye
biron na mike tsaye gami da
mika kuma cikin damuwa.
"Me ke damuna ne?" Na tambayi
kaina ko da idanuna suka kai ga
shafin littafi na ga ko alif ban
rubuta ba sai na yiwa kaina
murmushi, maganar
makaranta littattafaina ta fado min sa'ar
da suke cewa wai ta qare min,
lokacin da na kasa fito musu da
cigaban
ALJANI YA TAKA WUTA
da kuma
BINDIGAR KWALI NA BIYU
lallai ga dukkan alamu suma da
gaskiyarsu tabbas ta kare min
tunda dai gashi na sa littafi a
gaba na kasa rubuta komai
tsawon sa'o'i biyu.
.
Na gama hakura, na fito kofar
gida kenan sai na hango wata
yarinya dauke da fanteka da
kwanuka a samanta abin
tsautsayi ta zo tsallaka kwata
kenan sai kafarta ta zame,
fantekar a cike take da danwake,
wannan shi ne ya yi sanadiyyar
barkowar wani zazzafan gumi a
kan goshina, zuciyata ta fara
harbawa, sakamakon abin da na
tuna, tabbas na san inda zan je
na samo labari. Na sake duban
dunkule-dunkulen dan wake
burjuk a kasa sai ta tuno min da TUBANI
ina tuno da tubani sai na tuno da dattijo
SIDI MAI JAKA A
cikin sauri na nufi gidan wata
kakata, na yi sa'a kuwa na
sameta a gida. Bayan mun gaisa
sai na ce da ita.
"Tubani nake son ki yi min." Ta
dubeni cikin dariya ta ce "Ka ci
gidanku ja'iri dan nema, kai a
zamaninku ana yin tubani ne? Sai
dai jefi-jefi." Na dubeta gami da
sa alamun nutsuwa a fuskata na
ce. "Dan Allah ki yi min wallahi da
gaske na ke yi, fada min duk
abubuwan da za a saya sai na
baki kudin..."
.
Bata sami damar suturta tubanin
nan ba sai bayan karfe biyu.
Bayan na gama sallar Azuhur sai
na ga ta bade tubanin da yaji
sosai, domin na riga na san Sidi
Mai Jaka zai yi matukar farin ciki
da hakan, na sa ta dada kwarara
masa mai, sannan aka zuba min
shi a cikin kwano.
Karfe biyu da kwata na isa gidan
Sidi Mai Jaka dake bakin kasuwa.
Abin da ya fi damuna shi ne tun
sa'ar da muka rabu da shi
shekara biyu da suka wuce ban
kara zuwa wurinsa ba.
.
Ina isa kofar gidan sai na leka
zauren cikin doki, gabana na ta
faduwa domin kada na yi zuwan
banza ko baya nan. Ga mamakina
Sidi Mai Jaka na nan zaune akan
kujerar katakonsa, carbi a
hannunsa, haka nan akwai lofe a
gefensa a ajiye bisa wani farin
buzu. Sidi Mai Jaka ya dago kai
muka yi ido biyu, ko dakika biyu
ba a yi ba ya shaida ni.
.
"A'aha, yaushe a gari inji ma ki
bako Nas, ashe daman kuna
duniya?" Na dubeshi da dariya.
"Baba Sidi kuma tsofaffi ba ku
bar duniya ba ballantana mu."
Sidi Mai jaka ya fashe da wata
shakakkiyar dariya.
Na dubi Sidi Mai jaka kallon tsaf,
kana idanuna suka yo nazarin
zauren. Ko kusa ko alama babu
wani canji a kamannin Sidi Mai
jaka ko kuma zauren gidan. Wani
abin dadin mamaki kuma shi ne,
tsohuwar rigar nan dake jikinsa
mai kamar rariya, ita ce dai har
yanzu bai sake wata ba, na yi
mamakin karfin hali irin na
wannan rigar, domin sa'ar da na
fara ganinta shekaru biyu da
suka wuce ban taba tsammanin
zata sake wata guda a duniya ba
ta fatattake ba. Har yanzu katon
farin tabaron nan nasa na nan
daraf akan hancinsa.
.
Jikinsa kuwa sa'ar da na dubeshi sai na
fara tunanin me yiwuwa tun
bayan rabuwata dashi a shekara
biyu wankansa bai fi sau uku ba,
me yiwuwa ma sai dai ko alwala.
Amma fa duk da wannan
al'amari na Sidi Mai jaka ina
matukar girmamashi. Shekaru
biyu da suka wuce, wannan
tsoho Sidi mai jaka dogo fari
yankwanannen tsoho, kansa fari
fat, da furfura, farin gemu da
fuska ma'abociyar fadin goshi ya
taba bani labarin wata malamar
asibiti TANI da wasu yan fashi.
.
Sidi mai jaka ya dubi kwanon
dake hannuna cikin farin ciki yace.
"Ko shakka ba na yi wannan
alkawarina ne na TUBANI ko?" Na
ajiye kwanon a gabansa lokaci
guda kuma na matsar da lofen
dake kan farin buzun na zauna
na dubeshi cikin murmushi.
"Tabbas ka canka tubaninka ne."
.
Fuskar Sidi Mai jaka ta washe,
cikin nutsuwa ya mika hannu ya
dauko wata butar roba, ya guntsi
ruwa a bakinsa ya kuskure
bakinsa ya fesar a jikin bango.
Kana ya janyo kwanon tubanin
nan ya bude ya fara kallonsa
cikin nutsuwa.
"Nas, ina me yi maka albishir da
cewa wannan kyauta ta tubani
da ka kawo mini tamkar wani
dan mukullin labari ne da na
dade ina son na baka to sai dai
kuma shekaru biyu kenan yau
rabonka da nan sai yau Allah a
kawoka."
"Haka ne." Na ce dashi, sannan
na dada gyara zama domin na
san sabon labari ya riga ya zo...Shekaru biyu kenan yau rabonka
da nan sai yau Allah a kawoka."
"Haka ne." Na ce dashi, sannan
na dada gyara zama domin na
san sabon labari ya riga ya zo....
Sidi Mai jaka ya birkita manya-
manyan tubanin, sannan ya
dauki tsinke, ya tsiraki wani kato
ya tura a baki, nan da nan
idanunsa suka fara zubar da
hawaye saboda yaji.Ko wace ce
ta yi ma tubanin nan, ba karamin
kwarewa ta yi ba Nas." Sidi mai
jaka ya ce dani. Na gyada kai. Sidi
mai jaka ya cire farin tabaron
dake idanunsa ya sa hannun
rigarsa ya goge idanunsa sannan
ya dubeni ya ce."Nas kune samari
yanzu idan aka ce ka yi auren jari
za ka yi?" Na dubeshi cikin
mamaki na girgiza kai na ce."Ya
danganta da irin macen...koda
yake dai ni a gaskiya baya bani
sha'awa, ni na fi son auren da
muke kaunar juna don Allah." Sidi
mai jaka ya dubeni ya kyalkyale
da dariya ya ce.Abin da Anas
mijin Mabaruka gurguwa kenan
ya kasa fahimta." Na dubeshi a
karo na biyu "Wa yekuma Anas
mijin Mabaruka gurguwa?" Sidi
mai jaka ya tsikari katon tubani
ya jefa a bakinsa."Shi ne labarin
da nake son na baka Nas ban
saniba ko kana da sha'awar irin
wadannan labarai na irin
wadannan mata masu matukar
son kansu a duniya fiye da
kowa?" Na yi shiru na dan lokaci
ina juya, abin da ya ce cikin
zuciyata. A gaskiya ni a son
zuciyata na fi son a bani labarin
yan ta'adda irin wanda ya bani
shekaru biyu da suka wuce, to
amma da yake ni yanzu ta riga ta
kare min dole ne na saurari
komai domin bani da zabi. Wa ya
sani ma ko wannan ma ya fi
wancan labarin dadi."Zan so
kuwa na ji labarin wannan
gurguwa, wace ce ita'" Na
tambayeshi, Sidi mai jaka ya yi
dariya ce."Bi ni a hankali Nas
dadina da kai gaggawa sannu a
hankali zan fara saka ma
zararrukan labarin ina kulla maka
su kamar yanda gizo-gizo ke
sakar gidansa" Sidi mai jaka ya
dan yi shiru sannan ya ci
gaba."Ita wannan gurguwa mai
suna Mabaruka ba a taba samun
wata mace a zamanin ta mai
arzikinta ba, miloniya ce a fagen
kudi, to sai dai kuma wani ragin
jin dadi da ta samu shi ne
gurguwa aka haife ta" Sidi mai
jaka ya juyo ya dubeni."Nas,
domin ka fahimci zaren labarin
nan da kyau, dole ne na ajiyar
zaren labarin gurguwa
mabaruka, na koma na dauko ma
hoton Anas" Na dago kai a
kagauce na kalle shi."Ka ce kuma
da labarin gurguwa za ka ba ni."
Sidi Mai jaka ya gyara tabaronsa
kana ya tsikari tubani guda ya
jefa a bakin salatinsa."Dole ne
mu fara da zaren labarin Anas, in
kuwaba haka ba Nas, ba za ka
taba fahimtar labarin nan ba" Na
gyada kai cikin fahimta."Yauwa
Nas, ina son ka dauki zuciyarka
ka mayarda ita cikin wata
mashahuriyar otal." Na dubi Sidi
mai jaka cikin kaguwa na ce
dashi "Na mayar""Yauwa" Ya ce
dani sannan ya fara.****
"To Nas ga Anas nan a cikin
dakin karbar
baki na otal din yana zagayawa
cikin farin ciki da annashuwa
domin aljihunsa a cike yake da
albashinsa na wannan
watan"Sidi mai jaka ya yi yar
atishawa sannan ya ce."Kafin na
ci gaba bari na baka hoton Anas.
Ka ga Nas Anas dogo ne wankan
tarwada mai kyawun fuska na
ban mamaki. Domin an ce ba
mata kawai ba hatta maza idan
Anas ya zo wucewa sai sun
kalleshi sun yaba da halittar
Ubangiji. Wani karin abin
burgewa kuma gareshi shi ne
duk irinsuturar da ya sa sai ta
karbeshi cif-cif kamar daman da
ita aka haifeshi. Wannan da
kuma iya zancensa da tarairaya
shi ya sa dimbin mata suke
kaunar Anas kamar su hadiyeshi.
Wani abu da zai baka mamaki
Nas, shi ne Anan ba wai yan mata
bane kawai ke son sa, hatta
dattijan mata ma suna kaunarsa
sau da yawa masu budurwar
zuciya daga cikinsu kan yi
kokarin su kaiwa Anas cafka
musamman ma dattijan
zawarawa attajirai. Wani sa'in
Anas ya kan kula su ba don
komai ba kuwa sai don dan abin
hasafin da sukan bashi.Daya
daga cikin abin da Anas ya fi
kauna a rayuwarsa shi ne hira da
kyawawan mata, sau dayawa
Anas ya kan tsinewa talauci sau
daruruwa cikin zuciyarsa, domin
a cewarsa shi ne ya shiga
tsakaninsa da kyawawan mata
masu aji. Duk da yake dai
kyawunsa kan janyo ra'ayin
kyawawan mata, to amma Anas
bai taba gamsuwa ba domin shi
ya riga ya sani, akwai irin
kyawawan matan da kyawunsa
bai isa ya janyo su ba. Wannan
ita ta sa Anas ya yi kurda-kurda
ya sami aiki a Lagwada Hotel. Duk
da yake dai shi ba kowan kowa
bane a otal din domin aikinsa ya
fi karfi a rabon abinci, wani sa'in
kuma ya kan nunawa baki
dakunansu su ta hanyar daukar
dakon yan jakunkunansu, to
amma wannan bata dami Anas
ba domin shi burinsa ya cika. Dan
wannan ita ce hanya daya jal da
zai yi ta ganin kyawawan mata
iri-iri, yanda yake so duk kuwa
da cewa bashi da ko kwabo.
Babban abin farin cikin Anas shi
ne ya ga ana liyafa a otal din,
musamman ma ta bakin aure,
domin tana bashi damar gani
kyawawan mata wani sa'in ma
har yazanta da su. Anas yana
daya daga cikin irin samarin nan
marasa zuciyar nema, wadanda
harkullum kwanan duniya
burinsu su ci BULUS ba tare da
sun sha wahala ba. Dan haka.Wadanda harkullum kwanan
duniya
burinsu su ci bulus ba tare da
sun sha wahala ba.
.
Dan haka Naira dubu takwas din da ake
biyan Anas a wata sun isa su
sashi farin ciki, tun da dai ba zai
iya kokarin samun abin da ya fi
haka ba.Anan, sai Sidi mai jaka ya
yi shiru ya dago kai ya dube
ni."Nas, ina fatan kana fahimtar
hoton Anas da nake ta kokarin
zana ma" Na gyada kai na ce."Ina
fahimta" Sidi mai jaka ya gyara
zama sannansai ya ce."Bari to in
koma da kai can baya kadan inda
nake cewa Anas yana zagaya wa
a otal din cikin farin ciki, lokaci-
lokaci ya kan shafi aljihunsa a
fakaice domin baya son mutane
su fahimci cewar dan albashin
Naira dubu takwas din aljihunsa
yake tabawa. Haka nan shi kuma
bashi da imanin da zai iya jurewa
daidai da minti gudabai taba
aljihunsa ba domin ji yake yi
kamar kudin za su zube.Anas ya
ci gaba da zagaya wa a dakin
karbar bakina otal din ya gaisa
da wancan ya yiwa wannan
wasa har dai ya kawo daidai kan
kanta inda Balaraba mai bada
dan mukullan dakuna ke zaune.
Anas ya matsa kusa da kantar ya
dora hannunsa sannan ya dubi
Balaraba da kyakkyawar fuskarsa
ya hasketa da murmushi fararen
hakoransa suka fito fili."Hajiya
Balaraba ya ya garin
ne?"Balaraba ta dubeshi da
murmushi sannan ta turo biron
dake hannunta cikin kunne ta
fara juya shi, tana kanne
ido."Lafiya lau Anas. Har ka tashi
ne?"Anas ya dubi agogo sannan
ya dube ta."Da saura dai
Balaraba." ya dan yi shiru sannan
sai ya ce."Balaraba ba ki ga
motsin Halima ba ne?" Balaraba
ta girgiza kai."Ban ganta ba,
rabona da ita tun jiya da yamma
kamar ya yanzu da ta zo neman
ka." Balaraba ta ci gaba da susa
da biron cikin kunnenta."Anas,
wai don Allah yaushe za ka daina
yaudarar yayan mutane ne?"
Anas ya dubeta da murmushi ya
ce."Sai kin shirya Balaraba."
Balaraba ta harareshi."Me kake
nufi da sai na shirya?"Anas ya
shafi kyakkyawar fuskarsa."In
har kin yarda za ki aure ni, me zai
sa na ci gaba da yaudara? Daman
ke ce ai ki ka ki da tuntuni kin
amince dani da tuni na yi aure na
huta." Balaraba ta kyalkyale da
dariya."Oh! Anas Allah ya rufa
asiri wallahi wadda bata san ka
ba ka cuce ta." Ta dan yi shiru ta
sunkuyarda kai.Balaraba
bazawara ce, sau uku tana aure
tana fitowa. Da yake tana da
sakamakon diflomarta a hannu
kuma basira ta bace mata
maimakon ta yizamanta a dakin
miji sai ta nemi aiki a otal, a
lokacin watanta takwas kenan da
fara aiki. Tun sa'ar da ta fara
dora idanu akan Anas ta ji duk
duniya babu wanda take kauna
sai shi. Balaraba kyakkyawa ce
daidai misali, to sai dai kuma
bata cikin irin tsarin matan da
Anas ke so, domin a cewar Anas
duk macen da ta fiye gajarta bata
cika kyakkyawa ba ko da kuwa
tana da kyawun fuska. Balaraba
ta so ta cusa kanta a wurin
Anas,to amma irin jeri-jerin
matan da kan zo neman Anas tun
daga cikin gari har otal din, shi
ya gargadi Balaraba ta hadiye
maitarta ta yi shiru. To sai gashi
kuma yanzu Anas da kansa yana
zolayarta da zancen soyayya. Duk
da yake Balaraba ta tabbata
karya yake sai da kalaman nasa
ya faranta mata rai."Balaraba."
Anas ya kira sunanta. Balaraba ta
juyo frgigit."Tunani n me ki ke
yi?" Balaraba ta dago kai ta
dubeshi na dan tsawon lokaci
sannan sai ta ce."Kana da labarin
kayatacciyar liyafar da za a yi yau
a otal din nan?" Anas ya dubeta
cikin mamaki."Tun jiya na sami
labari a wurin Sabi'u amma ni bai
ce dani ta hadu ba." Balaraba ta
dube shi."Ai kuwa tun..."
Kalamanta suka makale a fatar
bakinta ba ta karasa ba. Anas ya
dubeta cikin mamaki sai ya ga
bashi take kallo ba bayansa take
kallo. Can wajen kofar shigowa.
Anas ya yi mamaki domin duk
kusan lokaci guda jama'ar dake
cikin dakin tarbar bakin suna
surutai suka yi shiru na dan
lokaci. Anas ya juyo sosai domin
ya ga abin da ke faruwa. A daidai
lokacin ne to ya hangesu.Wasu
kyawawan mata ne suka shigo
kowaccen suta ci kwalliya ta gani
ta fada. Anas ya ji yawun bakinsa
ya kafe, sannan sai ya lura daya
daga cikin yan matan tana tura
kujerar guragu ta farinkarfe akan
kujerar a zaune sanye da kayan
alfarma masu tsadar gaske, wata
budurwa ce gurguwa, za ta yi
kimanin shekaru ashirin da
bakwai.Koda Anas ya ci gaba da
kallon gurguwar da yan matan
ke turawa, sai ya yi ajiyar
zuciya."Kai amma fa an yi asarar
kayan kwalliya." Balaraba ta
dubeshi da dan murmushi ta
ce."Me ya sa ka ce haka?" Anas ya
dan yi shiru sannan ya dada
waigawa a karo na biyu ya kalli
gurguwar, sannan ya juya ga
Balaraba."Kin san ni ban cika
shiri da munanan mata ba.Dube
ta fa gurguwa mummuna amma
kayan jikinta sun fi na kowa
tsada, ai dole in ce an yi asarar
kayan kwalliya." Balaraba ta fashe
da dariya."Kai dai Anas wallahi ba
ka da kaico, me ya sa kake son
muzanta munana? Suma fa Allah
ne ya haliccesu kamar yadda ya
halicceka kyakkyawa kuma idan
ya so yana iya sa wa ka aure ta...Me ya sa kake son
muzanta munana? Suma fa Allah
ne ya haliccesu kamar yadda ya
halicceka kyakkyawa, kuma idan
ya so yana iya sa wa
KA AURE TA."
Anasya harare ta."Allah sawwake,
kin ga Balaraba ni fa bana son
mugun fata, tun da abin na ki
haka ne ma ni kin ga tafiya ta."
Anas ya juya cikin sauri ya nufi
cikin otal din a daidai lokacin ne
to ya hango Sabi'u cikin sauri ya
matsa gareshi."Sabi'u ka ga
wata mummuna da alamun
kudi." Sabi'u ya dubi Anas ido da
ido, akwai wani yanayi a irin
kallon da yake yi da ya sa Anas ya
jigwiwarsa ta yi sanyi."Ya ya na
ga kana yi min wani kallon uku
ahu?" Sabi'u dan lukuti, gajere
ma'aboin son sa kayan turawa
duk kuwa da cewa ba wani kyau
suke yi masa ba, ya gyara
tsayuwa sannan ya dubi Anas "Ka
san
inda kake wage bakinka, in kuwa
ba hakaba wata ran za ka kwana
a ciki. Shin ka san waccan
gurguwa ko wace ce kuwa?"
Anas ya girgiza kai ya
ce."Fahimtar dani." Sabi'u ya
gyara wandonsa wanda ke
kokarin sullubewa ya fado."Ni na
san ba ka santa ba shi yasa kake
kokarin muzantata. To bari in
fada ma, ka ga duk munin nan
nata, wallahi ba muni bane a
gurina, kuma ka ga dai gurguwa
ce to ni a gurina kafafunta sunfi
naka sau dubu amfani." Sabi'u ya
dan yi shiru sannan sai ya dago
hannunsa ya dan daki kirjin Anas
ya ce."Wannan gurguwa da kake
gani ita ce Mabaruka S. Faruk,
daya daga cikin matan da suka fi
kowacce arziki a matan Afirka."
Sabi'u ya ya balligoro ya jefa a
bakinsa sannan ya dubi
kyakkyawar fuskar Anas da
murmushi."Na san ka sha jin
labarinta, me yiyuwa a zahiri ma
baka taba ganinta ba, to yau gata
a otal din ka, bikin cika
shekarunta ashirin da takwas a
duniya za a yi. Mu kanmu nan
otal din ba karamar sa'a muka yi
ba, domin da liyafar a Landan za
a yi sai Mabaruka ta ce ba za ta
iya doguwar tafiya a cikin jirgi ba
domin wai juwa kedamunta
wannan shi ya sa su zuwa nan,
ina fatan ka fahimce ni? Dan
haka Anas ina son ka yishiru da
bakinka domin otal din nan ta yi
muguwar cin riba da liyafar nan
da za a yi, idan ka sake manaja ya
ji kalamanka akan Mabaruka, na
rantse ma har da gemun tsohona
ba za ka sake awa guda a gidan
nan ba za a sallame ka daga aiki."
Anas fuska na tsiyayar da gumi
ya dubi Sabi'u a tsorace. Ya mari
bakinsa da hannu"Shegen baki
yau ya kusan ya janyo min tsiya."
Sabi'u ya fashe da dariya ya
ce."Zo mu je mu fara shirye-
shiryen abubuwan da za su
bukata, ka san fa muke da
alhakin kula dasu." Sabi'u ya juya
cikin sauri Anas ya bi shi a baya
da sassarfa kamar doki. A
zuciyarsa yana tunani, Mabaruka!
Cab! Ai kuwa ya sha jin labarinta
ba tun yau ba. Wani abokinsa ya
taba cewa dashi. "Anas duk
matan kasar nan babu mai
arzikin Mabaruka gurguwa, kai
bar ma ta kasar nan duk Afirka
sai an tona. To amma a
tsammanin Anas da ya ji an ce
tafi kowacce mace kudi a Afirka
ya dauka zai ganta wata
kyakkyawa ajin farko, irin matan
nan masu shekia fuska kamar
madubi irin wadanda duk
tsananin duhun dare sai kaga
surar fuskarsu saboda tsabar
kyau. Abin da Anas ya gani ya
sashi kaduwa musamman ma
yanzu da aka ce dashi wannan
yankwananniyar matar mai
tababben hanci kamar begila ita
ce Mabaruka gurguwa uwar
kudi! Allah mai yadda ya so. Anas
ya ce cikin zuciyarsa.Tun karfe
biyar na yamma aka fara liyafar
farfajiyar otal din babu masaka
tsinke duk inda ka duba motoci
ne manya-manya masu bawo. Da
yawa daga cikin bakin basu sami
damar shigowa da motocinsu ba
saboda cunkuso.Anas da sauran
ma'aikatan dake bangaren girke-
girke suka yi ta rabon kayan
lashe-lashe da makulashe. Dakin
da ake liyafar tangamemen gaske
ne, wanda aka gina shi da
zummar ya dauki mutum dari
uku ba tare da wani ya shaki
numafshin dan uwansa ba, Anas
ya fara waige-waige yana
kokarin ya karewa Mabaruka
kallo.Ya ce gaba da zagaya wa
lokaci guda kuma cikin jama,a
yana yin abin da ya kamata sai
dai kuma akwai wani abu da ke
damun Anas sa'ar da ya kawo
kusa da inda su Mabaruka suke
zaune da manyan kawayenta.
Jikinsa na bashi cewa kamar
kallonsa ake yi a baya. Wannan
ita ta sa Anas juyawa a wayance
ya dubi bayansa. Gabansa ya fadi
ras! Sa'ar da suka hada idanu da
Mabaruka, ko shakka ba ya yi shi
take kallo, haka nan har da
murmushi a fatar bakinta. Anas
ya ji bugun zuciyarsa ya karu
lokacin da yaga kamar mabaruka
ta daga hannu ta yafato shi. Anas
ya shiga cikin rudani domin yana
fargabar kada ya je wurin kuma
ya kasance ba shi take kira
ba.Anas ya waiga bayansa domin
ya ga koda wani take sannan ya
sake juyowa, sai ya ga ta sake
yafuto shi da hannunta. Cikin
rawar jiki ya nufi inda take zaune
tare da sauran kyawawan
matannan. Anas ya ji duk gwiwarsa ta yi rauni kamar ba za
ta iya daukarsa ba domin
kyawun matan da suka kura
masa idanu ya yi yawa, ko kusa
ko alama basu yi kama da irin
yan matan da yake mu'amala da
su a baya ba.Anas ya ratsa a
hankali ta tsakanin kyawawan
tebura ya karasa gaban
Mabaruka. Yana zuwa saiya
rankwafa a gabanta ya ce."Gani
ranki ya dade ko bani ki ke kira
ba?" Mabaruka ta dubeshi da
mummunar fuskarta ta saki wani
abu da take tsammanin wai
tattausan murmushi ne."Kai nake
kira mana" Ta dan yi shiru,
sannan ta ci gaba."Daman so
nake na fada ma don Allah ku yi
sauri ku gama shirye-shiryen
mana, ka ga kamata ya yi ace tun
da wurwuri kun gama komai
kafin mu zo" Anas bai iya dago
kai ya kallisauran yan matan da
ke bayanta ba, to amma
yatabbata duk kallonsa suke."To
ranki ya dade" Anas ya amsa. Ya
yi kamar yamike tsaye ya koma
kan aikinsa to amma sai ya ga
alamun bata gama bayaninta ba.
Mabaruka tadubeshi ido da ido,
kana sai ta yi kasa-kasa da
muryarta ta ce dashi."Ka bar aikin
haka nan ka tafi ka gyara jikinka
sosai, ka jirani a waje idan an
tashi ina son ganinka.
"Kasa-kasa da murya, Ehemm..
Anas ya dubeta cikin mamaki,
lokaci guda kuma ya godewa
hayaniyar al'ummar dake wurin
liyafar domin ya tabbata hatta
kyawawan matan dake jere a
bayanta ma ba su ji abin da ta ce
dashi ba ballantana sauran
jama'a. Shi kansa yasan ba dan
yana kallon motsin fatar bakinta
ba da ba zai taba fahimtar abin
da ta ce ba. To amma duk da
haka yana shakkar abin da ta ce
dashi. Dan haka sai ya ya dubeta
a rude ya ce. "Ban fahimce ki ba
ranki ya dade?" Mabaruka ta yi
masa murmushi ta maimaita.
"Ka je ka sake kayan dake jikinka
ka kuma jirani a waje, idan an
tashi zan turo a yi min kiranka
ina son magana da kai."
Kusan awa daya da rabi ya shafe
zaune karkashin wata
dukurkusar bishiya mai kama da
ta dabino dake farfajiyar otal din
yana jiran tsammani zuciyarsa
cike da tambayoyi sama da guda
dari.
Amma manya-manyan
tambayoyin da suka fi damun
zuciyarsa sune; shin mene ne
dalilin ganawa dashi? Shin laifi ya
yi mata? To ai kuwa har
murmushi take yi masa sa'ar da
take bayanin. To mene ne dalilin
da zai sa ta ce ya sake kayan
dake jikinsa? Babu mamaki ji ta
yi kamar jikina yana wari. Anas
ya ce da kansa. Duk da yake dai
sa'ar da ya baro wurin liyafar sai
da ya yi ta shinshina jikinsa
domin ya ji ko wari yake yi, to
amma har zuwa wannan lokacin
da yake sake kayan dake jikin
nasa Anas bai gamsu ba, lokaci-
lokaci sai ya sunsuna hannun
rigarsa kana ya duba agogon.
Sa'a daya da rabi kenan yana
zaune a gurin yana jira. Tab!
Anas ya yamutse fuska cikin
damuwa. A karo na farko a
rayuwarsa ta harkar mata sai ya
ji ya fadi babu nauyi domin a
tarihinsa wata mace bata taba
sashi ya yi jiranta daidai da na
mintuna biyar ba, sai dai ita ta
jirashi. Amma sai gashi yau
tarihin ya sauya, wai Anas da
kansa ne yake zaman jiran wata
nannadaddiyar gurguwa
mummuna mai dogon hanci da
fadi kamar nakiya, lallai duniya
juyi-juyi! Wannan tunani shi ya sa
Anas ya saki wani tattausan
murmushi a cikin duhun daren
da ya fara shigowa sannan ya
dada jingina bayansa a jikin
bishiyar da yake zaune, ya share
gumi daga goshinsa a zuciyarsa
ya ce.
"Kada ka damu Anas, a da can
kyawawan mata sun yi jiranka, a
yanzu kuwa kai ne kake jiran
mummuna da kudi, ko ba komai
dai ba talaka kake jira ba. Abin ya
kan baiwa Anas mamaki, wata
sa'ar ma har dariya idan ya tuna
da cewa wai daya daga cikin
matan da ta fi kowace kudi a
Afirka yake jira! Anas na nan a
zaune yana ta sake-sake bai ji
zuwanta ba sai muryarta ya ji a
bayansa ta ce.
"Ka zo wai tana kira". Anas ya
juya firgigit domin ganin mai
zazzakar muryar. Daya daga cikin
kyawawan matan nan ce ke
tsaye a kansa. Da yake ita kadai
ce a wurin sai Anas ya sami
damar kare mata Kallo sosai.
Budurwar dake tsaye a kansa
doguwa ce fara, kyakkyawar
gaske mai hasken fata. Budurwar
za ta yi kimanin shekaru goma
sha takwas, ko sha tara me
yiyuwa ma ashirin, abu ne mai
wuya ka iya fadin shekarunta kai
tsaye, domin kyawun fuskarta
ma'abociyar annuri da kwarjini
sun isa su sa duk wani mai iya
hasashen shekaru cikin rudani.
Budurwar tana da manyan idanu
farare tas! Wadanda duhun dare
bai hana Anas ganin fararen
idanun ba, wani abu da ya so
tsayarwa Anas numfashi shi ne
kundukukinta mai annuri gami
da shafaffiyar mararta wacce ta
bayyana a fili sakamakon
tsukakken dinkin bakar shaddar
dake jikinta. Kafarta fara sol
gwanin sha'awa cikin bakin
takalmi. Anas a zuciyarsa ya ce da
za a barshi ko da daidai da na
dakika guda ne ya sumbaci
kafarta da babu abin da zai hana
shi ya bada albashinsa na wata
guda.
.
"Tana ina?" Anas ya tambaya
cikin karfin hali zuciyarsa na
harbawa, lokaci guda kuma ya
mike tsaye.
"Zo mu je na kai ka inda take."
Budurwar ta ce dashi. Babu
alamun bakin ko farin ciki a
fuskarta. Budurwar ta juya tana
rausaya. Anas ya bi ta a baya
kamar tunkiya. Sannu a hankali
suna tafe har ta kawo shi filin da
ake fakin da motoci na ota din.
Anas ya godewa Allah, domin har
suka isa wurin bai hadu da ko
ma'aikacin otal din kwaya daya
ba, domin sun dade da yi masa
muguwar lambar yawan
mu'amala da mata. To amma duk
da haka sai da Anas ya raya a
zuciyarsa cewa inama su hadu
da Sabi'u, domin abin alfahari ne
ya ganshi da wannan zukekiyar.
Sa'ar da suka kawo farfajiyar sai
Anas ya lura duk kusan tarin
motocin nan sun baje, sauran da
suka rage basu fi guda ashirin ba
kawai. Anas na bin dudurwar a
baya har ta zo dashi jikin wata
mota katuwar (Jeep) Shudiya.
Tun kafin su karasa kofar motar
ta bude sannan sai muryar
Mabaruka ta ratsa kunnensa.
"Sannu da zuwa lallai ka cika
alkawarinan mabaruka ce zaune
a bayan motar ita kadai, sannan
a gidan gaba akwai direba wani
dogo ne, fari bafulatani.
Mabaruka ta dubi kyakkyawar
budurwar ta ce.
"Na gode Ummi, sai goben kenan
idan kin zo. Budurwar ta yi
murmushi a karo na farko ta
dubi Mabaruka ta ce.
"To Mabaruka, Allah maimaita
mana, sai da safen, bari in yi
sauri ga su fati can a mota suna
jirana." Sannan ga mamakin Anas
sai ta juya gare shi ta haske shi
da murmushi ta ce. "Malam sai da
safe." Ta juya cikin sauri ta bar
wurin.
Anas ya bi ta da kallo, a zuciyarsa
yana cewa kai lallai kudi ma dai
wallahi banzaye ne domin basu
san inda ya kamata su je ba.
Koda ya kwatanta kyawun
Mabaruka Miloniya da budurwar,
sai ya ga tamkar ka kwatanta alli
da bakin gawayi ne.
"Ga shi har dare ya fara yi."
Muryar Mabaruka ta katsewa
Anas tunaninsa. Anas ya juya
firgigit sannan ya saki wani
fatalwar murmushi ya ce.
"Ranki ya dade gani." Mubaruka
ta kura masa idanu na tsawon
lokaci, akwai murmushi a
fuskarta. "Da za ka kirani da
sunana Mabaruka ina gani zai fi"
Anas ya dan rankwafa cikin
girmamawa to amma ba ita yake
girmamawa ba, miliyoyin kudin
da ya ji labarin ta mallaka yake
girmamawa.
"To ranki...Mabaruk a."
Mabaruka
ta fashe da yar dariya.
"Ka kuwa iya fadar sunan" Anas
ya ji wani daddadan kamshi sai
hurowa yake daga cikin motar.
A iya tsawon lokacin da ya yi
yana aiki a otal din ya sha jin
kamshi iri-iri daga jikin yan birni
da masu hannu da shuni da yan
kwalisa masu kunan bakin wake
da yan kuru, amma a duk cikin su
bai taba jin kamshin da ya kai
koda rabin wanda ke hurowa
daga motar Mabaruka ba.
"Idan ba za ka damu ba, ba zan
kuma takura maka ba, zan so ka
shigo motar nan mu tafi tare da
kai." Mabaruka ta ce da Anas tana
duban fuskarsa. Anas ya dubeta
cikin tsananin kaduwa ya ce baki
na rawa.
"Mu tafi...ina?" Mabaruka ta
dubeshi da murmushi.
"Gidana nake son mu tafi tare da
kai domin akwai maganganun
da nake son mu tattauna da kai
masu muhimmanci" Anas ya dubi
nannadadun kafafunta kana ya
dago kai ya ce.
"Har yanzu ban fahimce ki ba"
Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce.
"Duk abin da zan fada ma anan
ba zai gamsar da kai ba, shi yasa
nake so na tafi gidana da kai
inda zamu samu damar
tattaunawa sosai" Ta dan yi shiru
tana nazarin fuskarsa ganin
cewa har yanzu a rude yake sai
ta ce.
"In kuma har yanzu ba ka gamsu
ba bari in fito fili in fada ma abin
da zamu tattauna. So nake na
saye ka!" Anas ya ji gabansa ya
fadi ya dubi Mabaruka a rude.
Mabaruka ta dubi Anas ta fashe
da dariya ta ce
"Me ye na ga ka hada fuska kana
jin ba zan iya sayen naka bane?"
Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya
dubeni "Nas wannan shi ne
karshen wannan dogon zaren
labarin" Na dubeshi cikin
kaguwa "Haba Baba ya ya sai da
labarin ya dauko dadi za ka katse
ni anan?" Sidi mai jaka ya tsikari
katon tubani daya ya jefa a baki
kana ya dube ni ya ce.
"Nas kenan, har kullum ba ka
fahimtata in ban da abin ka ai
sauran zararrukan labarin da ke
gaba sun fi wannan ma dadi
nesa ba kusa ba. Ka yi min afuwa
Nas zan koma da kai can baya
shekaru ashirin da takwas da
suka wuce kada ka damu sannu
a hankali zan dawo da kai kan
tsohon zaren labarin da na gama
yanzun nan na hada maka
bakinsu in kulle guri guda"
Na gyara zama sannan na ce
dashi.
"To Baba Sidi, ina sauraronka"
Abin da yake bani mamaki ga
lamarin Sidi mai jaka shi ne irin
yadda yake bada labarin ko
sarkewa ba yayi.
.
SIDI MAI JAKA ya dubi kwanon
tubanin dake gabansa ya dubeni
cikin murmushi, sannan sai ya
tura tsinke ya tsikari wani
dankareren tubani ya tura a baki.
"Nas duk duniya babu abin da na
fi so kamar tubani"
"Haka ne" Na ce dashi. Sidi mai
jaka ya dubeni.
"Me yiwuwa ka yi mamakin irin
yadda nake ta zubo maka labari
bana ko tsayawa" Na gyada kai.
"Kwarai kuwa" Na ce dashi
"Domin a wancan karon da na zo
duk kusan mintuna goma sai ka
tsaya"
Sidi mai jaka ya fashe da dariya.
Sannan ya sunkuyar da kai ya ce.
TSOHON ALKAWARIN da ka cika
min ne ya sa nake ta kwararo
labarin nan ba wakafi balle aya"
Na dubeshi cikin mamaki.
"Wane tsohon alkawari kuma?"
Sidi Mai jaka ya dubi kwanon
dake gabansa ya ce.
"Tubanin da ka yi min alkawari
shekaru biyu da suka wuce shi
nake nufi da tsohon alkawari.
Domin ba duka mutum bane a
wannan zamanin kan iya cika
alkawari" Sidi mai jaka ya dan yi
shiru sannan sai ya dubeni ya ce.
"Nas, ina son ka dauki zuciyarka
cancak ka mayar da ita shekaru
ashirin da takwas da suka wuce
a lokacin ma ba a haifi Mabaruka
ba" Na dago da kai cikin kaduwa.
"Shekaru ashirin da takwas?" Sidi
mai jaka ya gyada kai.
"Kwarai kuwa, domin shi ne
zaren labarin mu na biyu." Ya dan
yi shiru kana ya tsikari tubani ya
jefa baki sannan ya dubeni.
"Nas, shekaru ashirin da takwas
da suka wuce, wasu ma'aurata
guda biyu wadanda ke cikin
tsananin shauki na kaunar
junansu sun kasance zaune a
wani fankadeden falo na alfarma
wanda a takure zai iya cin
mutune sittin ba tare da wani ya
shaki numfashin dan uwansa ba.
A zaune a daya daga cikin
kujerun wani mutum ne dogo,
baki, sanye da farar riga suwaita
da shudin wanda na shadda,
kansa babu hula, hakan shi ya
bayyana matashin sankonsa a fili,
da yawa daga cikin wadanda
suka sanshi a lokacin, sun riga
sun yi imani da cewa mutumin
ba zai dade da gashi a kansa ba,
domin gashi dai a lokacin bai fi
shekara talatin da biyar ba a
duniya, amma dogon sankon ya
gama cinye rabin gashin kansa.
Wannan dogon sanko dake kan
mutumin bai hana matarsa Aliya
mutuwar kaunarsa ba, duk kuwa
da cewa a lokacin ma tana da
cikin dan wata takwas Wannan
mutum mai dogon
sankon sunansa A. Faruk. Ba
karamin mutum bane, domin a
fagen kudi biloniya ne,
mamallakin kamfanoni ashirin da
takwas a nan kasar. Jita-jita
kuma na cewa wai yana da
kamfanunnuka sama da goma a
kasar Amurka, da kuma wani
katon asibiti a kasar Birtaniya.
Lokacin da ya auri matarsa Aliya
tana yar shekaru ashirin daidai.
In ban da yawan maganganu n
yan uwa da babu abin da zai sa
ya yi aure a lokacin. Domin tun
yana dan saurayi kafin ya yi arziki
ya taba neman wata yarinya
Murja, wani direban mota ya
kasa shi, tun daga wannan bai
kara sha'awar ya nemi wata
mace ba a duniya sai da ya hadu
da Aliya.
Da farko sa'ar da aka yi bikinsu
da Aliya bai taba tsammanin
auren zai sami wata kyakkyawar
nasara ba. To amma kwanaki
uku kacal da yin auren sai ya
fuskanci ashe Aliya mace ce ta
gari mai iya kissa da soyayyar
janyo hankalin maza. Wannan ita
ta sa a yanzu A. Faruk yake
mutuwar kaunar matarsa Aliya.
Duk inda zashi koda kasashen
ketare ne tare suke tafiya, to
amma yanzu da yake cikinta ya
tsufa sun fi wata uku a gida
Najeriya suna renon cikin.
Aliya ta muskuta akan kujerar ta
shafa cikinta ta ce.
"Kwanta Mabaruka yar gata." A.
Faruk ya ajiye jaridar dake
hannunsa kana ya shafi dogon
sankonsa ya dubi matarsa Aliya
cikin murmushi.
"Aliya, ke fa wallahi ba kya
rabuwa da rigima in ban da abin
ki wa ya ce dake mace za ki haifa
da har ki ke sanya mata suna
Mabaruka?" Aliya ta harareshi,
sannan ta mike da kyar, ta nufo
inda yake, tana zuwa sai ta
kwanta akan cinyarsa a rigingine
kana ta shafo cikin nata ta
dubeshi ta ce a tausashe.
"Ni na san mace ma zan haifa in
Allah ya yarda." Faruk ya fashe da
dariya ya dubeta.
"To yanzu da har ki ka sa mata
suna Mabaruka idan kika haifi
namiji kuma me za ki sa masa?
Kamata ya yi ki zabi sunaye biyu,
na mace da na namiji, ina ganin
zai fi kyau idan namiji ne mu sa
masa suna Mabaruki."
Aliya ta fashe da dariya.
"Kai (darling) don Allah ka daina
sa ni dariya, kar ka sa cikina ya yi
ciwo." Faruk ya dubeta.
"A'a, to ke kin ga laifina? Tun da
dai kin ce idan mace ce za ki sa
mata Mabaruka ni kuwa idan
namiji ne sai in sa masa
Mabaruki." Aliya ta kamo
wuyansa cikin dariya ta matso da
fuskarsa kusa da tata, ta dora
bakinta akan kunnensa ta ce.
"Kai a tunaninka idan na haifi
mace da wa za ta yi kama?"
Faruk ya dan dago kansa sama
ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya,
sannan
Faruk ya dan dago kansa sama
ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya
sannan ya tuna da dogon
sankonsa, gami da tababben
hancinsa wanda sau da yawa, shi
yake hana shi ganin madubi, sai
ya dubeta da murmushi ya ce.
"Ina fatan ko mace, ko namiji za
ki haifa Allah ya sa ya yi kama da
ke Aliya. Aliya ta rungumo shi
cikin farin ciki domin ita kanta ta
san kyakkyawa ce.
Anan, sai Sidi Mai Jaka ya yi shiru,
sannan ya sa hannu ya goge
gumin da ke sartu akan
goshinsa. Me yiwuwa zafi ne,
babu mamaki kuma zazzafan
yajin tubanin ne ya sashi gumi.
Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce.
"Nas, wani sa'in matasan mata
sukan bani mamaki, da zarar sun
sami ciki sai kaga suna ta zaben,
wai sun fi son su haifi mace, ko
namiji ko kuma mai kama da su,
ko kyakkyawa...hak a dai za ka ji
suna ta kawo tsarabobi iri
daban-daban kai ka ce su ke da
ikon halitta. Ni a ganina Nas, gara
a bar wa Allah zabi domin shi ne
gwani akan komai ko kuwa me
ka gani?" Na gyada kai cikin
sauri.
"Haka ne. Ci gaba baba." Sidi mai
jaka ya dubi kwanon tubanin
dake gabansa kana ya girgizaq
kai cikin takaici, domin duk
yawan tubanin nan dake ciki ya
nhadidiyesu kamar zakara
wadanda suka rage basu fi
kwaya goma ba. Sidi Mai jaka ya
canki na goman karshen ya jefa
baki kana ya ci ga.
"Nas, wata guda da yan kwanaki,
da faruwar wannan hira da na
baka labari dazu tsakanin
ma'auratan biyu, sai Aliya ta
haihu. Ta wani bangaren
haihuwar ta zo musu kamar
yadda suka zata tun farko to sai
dai kuma ta wani bangaren
haihuwar ta zo musu a murde,
musamman ma Aliya. Lokacin da
Aliya ta haihu bata san inda
hankalinta yake ba, sai bayan
kusan sa'a guda da haihuwar ne
sannan likita ta zo gabanta da
murmushi ta ce.
"Ina taya ki murna kin haifi
mace." Aliya ta yi matukar farin
ciki da jin cewa mace ta haifa,
amma sa'ar da likitan ta miko
mata jaririyar da ta haifa sai
duniyar jin dadin Aliya ta birkice
lokaci guda. Aliya ta dubi jaririyar
cikin kaduwa, ko kusa ko alama
jaririyar bata yi kama da ita ba,
gashi dai lafiyayyace sosai to
amma irin tabebben hancin
mahaifinta ya mamaye kusan
rabin fuskarta, bugu da karin
bakin ciki ga Aliya kuma jaririyar
ba ta da kafafu domin duk a
shanye suke sili-sili kamar
maburgi.
"Wannan...kafaf un nata ba za
su
gyaru ba?" Aliya ta tambayi likitan
muryata na rawa. Likitan ta
girgiza kai cikin jimami.
"Babu wani likita a duniya da ya
isa ya gyara kafafun nan nata. Ki
godewa Allah da ya kawota
duniya cikin koshin lafiya, ba kya
ganin idan ki ka dauke
shanyayyun kafafun lafiyarta
kalau." A daidai lokacin da likitar
ta yi shiru sai jaririyar ta bude
idanu. Aliya ta dubeta tayi kamar
za ta fashe da kuka
Ga mamakinta sai jaririyar ta
dubeta ta washe baki cikin
murmushi Aliya ta rungume yar
jaririyarta cikin kuka ya ce.
"Ina son ki Mabaruka, ina son ki
haka nan domin haka Allah ya so
ya gan ki."
Shekaru ashirin suka shude
kamar wasa, a cikin shekaru
ashirin din nan babu irin gatan
duniyar da Mabaruka bata gani
ba. Anan Najeriya ta yi
makarantar firamare dinta,
amma duk sauran karatunta a
Burtaniya ta yi.
Duk da kasancewar Mabaruka
gurguwa kuma mummuna,
iyayenta basu ki nuna mata
tsananin soyayya ba. Wani Ikon
Allah kuma tun daga kan
Mabaruka, Aliya ba ta sake
haihuwa ba, wannan shi ya kara
tsananin kaunarsu a gare ta.
Mabaruka ta tashi cikin jin dadi,
da gata marar misaltuwa, ga ta
dai gurguwa amma duk satin
duniya sai ta hada hadaddiyar
liyafa, wani sa'in kuwa sai ta tara
guragu irinta, ta sa su bi layi a
kofar gida, ita ko a yi ta turata
akan keken guragu na
musamman tana raba musu kudi,
tufa, ko abinci. Kudi ba matsalar
Mabaruka bane, domin
mahaifinta Alhaji Faruk biloniya
ne, ya gama tara mata su gashi
kuma ita kadai ce bata da ko kani
guda daya. Wata rana Mahaifinta
ya taba cewa da ita.
"Mabaruka, duk abin da ki ke so
ki yi da kudi ki yi kawai kar ki ji
tsoron komai ki yi ta kashewa
tun da dai naki ne. Ki godewa
Allah da ya yi ki gurguwa da uba
biloniya."
0 comments:
Post a Comment