AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
0⃣1⃣to0⃣2⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Bugun kofar da akaine yakauda tinaninta ta'tashi ta'isa kofa tare da budewa
Kallonsa kawai tayi batare da tace dashi komaiba hakan yatabbatar masa da cewar tana tare da damuwa
Tajuya tayi tafiyarta yabita da kallo tare dajan numfashi yarufe kofar yajuya kaitsaye dakin Ambeeshar yanufa
Yasameta tanata sharar barci abinta yazauna daga gefenta yana aikin kallonta
Ha!!! Yanisa tare dajan numfashi yana maisauke ajiyar zuciya
Ambeeshar Allah yabaki lafiya Ubangiji Allah yanunamin lokacin da zaki sami lafiya
Allah yadauke maki wannan lalurar yakawo maki sauki inasanki 'yata yakawo maki dauki Amin ya Allah yasunbaceta aka tare da yimata addu'a sannan yajuya yatafi
Yafito yanufi dakin Umma yasameta zaune bakin gado yazo kusa da ita yazauna tare da kai kallonsa gareta cikin kasa-kasa da murya yake magana da ita
Hajiya kallonsa kawai tayi batare da tace dashi komaiba Hajiya dan Allah kiyi hakuri kigafarceni tabbas nasan cewa bana kyautawa amma duk da haka ina mai'naiman afuwarki
Wallahi ni'kaina ba'asan raina nake aikata maki hakaba wallahi dole ce tasa nake aikata maki nakaba amma duk da haka ina mai'naiman afuwarki dan Allah kigafarceni
Cikin lallausar murya murya take magana haba Alhaji kaima kasan dole nasamu yakake san nayi
Da wanne kakesan naji da rashin lafiyar Ambeeshar zanji ko da rashinka kiyi hakuri Hajiya wallahi kema kinsan dalilin da yasa nake aikata haka
Hajiya wallahi tallahi sam banasan ganin Ambeeshar acikin wannan yanayin hakama wallahi duk lokacin dana ga Ambeeshar acikin wannan yanayin wallahi raina baci yake hankalina tashi yake matuka wannan yasa sam banasan zama agidan
Haba Alhaji maiyasa kake fadar haka maiyasa ba zakayi hakuri da wannan jarrabarwa da Allah yasaukar manaba maiyasa kake tinanin Ambeeshar ce kawai take bukatarka agidan nan baka tinanin cewa ni da sauran mutanan gida muna da bukatarka
Koba kasan cewa rashinka yana cutar damuba Alhaji jiyafa ba yauba Ambeeshar fa balallai ta'iya warwarewa ba da sauri yadakatar da ita a'a Hajiya dan Allah kidena fadar haka
Insha Allah Ambeeshar zata sami lafiya duk da cewar samun hakan yana da matukar wahala amma kisani wallahi tallahi ba'abinda yafi karfin Allah
lokaci daya Umma tasaki kuka Alhaji wallahi rashin lafiyar Ambeeshar yana matukar tada hankalina hardai idan natina cewar jigon samun lafiyarta baya raye hakan sai yakara daga hankalina
A'a Hajiya dan Allah kidena insha Allah Ambeeshar zata samu lafiya koda kuwa Ammar baya acikin wannan duniyar kisani Allah yananan kuma shizaibata lafiya da yadar Allah kiyarda dani to Allah ya'yarda Amin yarabbi
To amma zakadena gudewa ko eh zandena ke nama dena tayi murmushi nagode sosai bakomai
Washe gari bayan takarasa shirinta tana ko'karin tashi tafuta Abba ya'anbaci sunanta
Hajiya ta'amsa tare da kai kallonta garesa na'am zuwa yanzu yakamata kiduba Ambeeshar
Tayi murmushi Alhaji kenan tashinnan danayi gunta zabi ok yakamata to bara natafi ok tafita tanufi dakin Ambeeshar tasameta kwance sai dai ba barci takeba ta'isa inda take ta zauna tare da anbatar sunanta
Ambeeshar kallonta kawai ta'iyayi batare da ta'amsaba Umma tayi murmushi Ambeeshar kenan bara nahada maki ruwan wanka
Harzuwa wannan lokacin kallonta kawai take batare da ta'iya cewa da ita komaiba ta'tashi tanufi bandaki bayan mintuna biyu tafuto am Ambeeshar kitafi ruwan yahadu Ambeeshar tashi mana gar'ruwan yahuce shiru sai kallonta kawai take
Ha!!! Tanisa tare dajan numfashi tarika hannunta tare da tada ita zaune Ambeeshar kiyi hakuri mutafi kiyi wanka kinji Umma ta'tashi tare da tada ita tarakata har toilet sannan tafuto
Bayan wani lokaci tafuto Umma tashiryata cikin wata doguwar riga ta'atamfa takalleta tayi mirmushi kinyikyau Ambeeshar tashi mutafi Abbanki da yayanki suna falo suna jiran fitowarmu ta'tashi tare da tada'ita sunfita
Tinda suka fito Abba yake kallonsu har suka karaso inda suke ha!!! Yanisa tare da sauke ajiyar zuciya yana mai anbatar sunan Ambeeshar sai bata'iya amsawaba Ambeeshar ina fatan Allah yakaimu lokacin da zaki samu lafiya kisan komai atare dake wannan yanzu bakisan komaiba agame dake Allah ya'yaye maki Amin Abba
Sannu kanwata Allah yadauke maki lalura Amin Aliyu bayan wani lokaci suka tashi suka nufi gurin cin'abinci bayan sunkarasa Abba da Aliyu suna ko'karin futa saigasu Al-ameen sunshigo bayan sungaisa
Ahmad yanufi gurin Ambeeshar yazauna tare da dafata kanwata maiyasa har yanzu baki'iya tina komaiba na'rayuwarki
Ambeeshar zuwa yanzu yaka mata ace kobaki tina komaiba ni kitinani Ambeeshar Ahmad fane yayanki har yanzu baki'iya tinani ba
Kallonsa kawai take batare da ta'iya cewa dashi komaiba ha!!! Yanumfasa tare da sauke ajiyar zuciya yasalam Ambeeshar ina fatan Allah yakaini lokacin da zakiyi magana kisami ingantacciyar lafiya Amin yaya Ahmad
Bayan wani lokaci dukansu suka tashi suka nufi office
Bayan kwana biyu da yamma dukansu suna falo suna fira Ahmed yashigo dauke da Amir Aisha takallesa Abban Amir kashigo eh ashe kinanan eh ina gidan Aunty Asma'u dagacan ne mukazonan ok
Aunty Asma'u ina yaya Al-ameen yafuta tare da Habib tinyaushe dajimawa ok to inasu Afra suna islamiya to Allah yadawo dasu lafiya Amin
Ambeeshar sannunki dafatan kina kina samun sauki shiru bata magana ba Allah sarki Ambeeshar Allah yabaki lafiya yakaimu lokacin da zaki fara magana da bakinki Amin ya Allah
By Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
0⃣3⃣to0⃣4⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Abban Amir dare'fa yayi sosai yakamata kazo ka'kwanta amma kafinnan dan Allah kayi hakuri kaci abinci koda kadan ne
Dan Allah garka kwanta da yunwa kaji
Ha!!! Yaja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya
Aisha kenan wallahi ni kaina inasan nayi barci amma kuma sam naji bazan'iyaba
Iya kacina kawai nakwanta amma sam bazan'iya rufe idanuwana ba
Aisha wallahi da zarar narufe idanuwana to ba'abinda nake gani face kanwata wata Ambeeshar
Wanda wannan yasa sam bana'iyayin barci
Aisha ke'kanki shaida ce akan shakuwar dake tsakanina da Ambeeshar
Kinsani mu'hudu muke agurin iyayenmu Yaya Al-ameen saini sai kuma Aliyu da Ambeeshar su'kuma sunkasance tagwayene
Amma duk da kasancewarsu tagwaye sunfiye samun sabani wanda kuma abu dayane yake sakasu fada
Aliyu yana da san'girma yanasan Ambeeshar tarika kiransa da yaya wanda ita kuma batayi ganin tare aka aifesu to
Wannan dalilin ne yasa tafi shakuwa dani fiye da kowa da yake agidannan amma yanzu abin takaici shine
Aisha duk irin kauna da shakuwar da take atsakanina da Ambeeshar ace wai Ambeeshar tagagara gane ni wallahi wannan abu yana matukar tayar da hankalina matuka
Aisha wallahi duk lokacin danaga Amir sai damuwa tadada shigata domin kuwa ba'abinda yakezomin arai face Ambeeshar wanda natabbata da ace qlau take to da itama tananan tare da yaronta
Aisha kinsani aranar Auranmu gurin Dinar Auranmu wannan lalurar tasami Ambeeshar ranar da yakamata ace ta'tare agidan mujinta sai takare da kwanciya asibiti
Wanda sanadin hakan yaja tarasa tinaninta Aisha wallahi ranar Auranmu itace tazamemin qalubale arayuwata wannan yasa duk ranar tazagayo damuwata takan'karu fiye da ko yaushe
Aisha karin tashin hankalina shine jigon samun lafitar Ambeeshar baya raye yajima akasa kuma abin takaicin shine tagarara tina komai
Amma insha Allah zanjaraba nagani ko Allah zai'azani asa'a to Allah yasa kade ce Amin yarabbi
Aisha wallahi inasan Ambeeshar sosai hakama ina fatan ganin tasami lafiya to Allah yabata lafiya Amin ya Allah
Bayan kwana Ahmed yadauki Ambeeshar suka fara futa yana dan zagawa da ita dan ganin ko zata'iya tina wani abin komai kan'kantarsa amma ina ba wani sauyi atare da ita
Ambeeshar kinsan wannan yanuna mata photo Ammar kallon photo kawai take amma bata'iya furta komaiba
Ambeeshar wannanfa Ammar ne ko kinmantasa kallon photo kawai take kamar zatayi kuka
Ho!!! Subhanalillah Abba wallahi da akwai matsala sosai yafa kamata amayarda Ambeeshar asibiti domin kuwa har yanzu ba wani sauki atare da ita har yanzu tananan yanda take
Ba'abinda yacanjata Al-ameen kenan aikuntafi asibiti ba'abinda zasuyi mana domin kuwa sam bazasu'iya dawomata da tinanin taba hakama bamusan abinda zaidawo mata da tinanin taba tinda munrasa Ammar
To Abba yanzu shikenan haka zamu saka mata idanuwa tarayu ahaka to Aliyu yazamuyi
Ni wallahi tinda naga Ambeeshar tagagara gane Ahmad nayanke kauna da samun lafiyarta da sauri Asma'u tace a'a
Umma dan Allah kidena yimata wannan fatan kisa kwarin guiwarki akan cewar Ambeeshar zata samu lafiya to Asma'u Allah yayarda Amin ya Allah
Ahmad dai shiru yake yayinda yagagara furta komai
Bayan wani tsayin lokaci wata rana yana office wayarsa tadau ruri yakai hannunsa yadaga tare sallama
Sadiq dafatan kana lafiya ya'aiki Alhamdulillah yasu Umma ina Ambeeshar da jiki su Umma suna lafiya
Ambeeshar kuma saidai katayamu da addu'a domin kuwa har yanzu bawani sauyi atare da ita subhanalillah to Allah ya'yaye mata Amin ya Allah
Am Ahmad dama nakiraka ne domin nasanar dakai wani zance mai firgitarwa subhanalillah Sadiq maikake san kasanar dani
Ahmad wallahi nahadu da Ammar cikin rawar murya haryana sarkewa yace Sadiq kaji maikafada kuwa aiya kana cikin haiyacinka kuwa kodai kazare
Ahmad kenan wallahi cikin haiyacina nake ba'abinda yake kaina Sadiq Ammar fa kace eh Ahmad wallahi nahadu da Ammar kai Sadiq gaskiya abin da kamar wuya kaza acikin ramen kura
Sadiq Ammar fa yajima da mutuwa shekaru uku da suka shige kuma kai'kanka dakai akayi jana'izarsa balantana kuma ka'karyata haka
Sadiq mutuwa daya ake ba' biyu hakama duk wanda yamutu baiya dawowa to taya kuma zakazomin da zancan cewa kahadu da Ammar gaskiya ina tanbaba wallahi ina tantama akan haka
Ahmad kenan ai'dama nasani balallai ka'iya yar daba amma garka damu anjima kadan zantabbatarma da abinda nake fada to inajira ok sunyi sallama
Ha!!! Yanisa tare da sauke ajiyar zuciya yana mai magana da zuciyarsa tayama za'ace har yanzu Ammar yana raye gaskiya sam bana gaskata haka mutumen da aka sakasa rame agaban idanuwana
Shine kuma yanzu za'azomin da zancan cewa wai yana raye kai'ina wallahi abin da kamar wuya wai sata alahira amma kuma daga yanayin yanda Sadiq yake yimin magana sam ba wasa acikin maganar sa
To idan tatabbata Ammar yana raye kamar yanda Sadiq yafada da kuwa wallahi nahukuntasa abisa zunubinsa amma hakan zaifarune bayan
Ambeeshar tasamu lafiya ina fatan Allah yasa Ammar yana araye kamar yanda Sadiq yafada domin inakyauta'ta zaton da yardar Allah kanwata zata sami lafiya Allah kayarda da hakan Amin ya Allah
Da yamma Sadiq yakirasa vidio call kuma alokacin yana tare da Ammar Ahmad yawani zaro ido yana kallonsa kafin yafurta komai Sadiq yatashi gurin
Cikin sarkakiyar murya haryana sarkewa hade da rudani yake magana Sadiq tabbas abinda kafada gaskiya ne to amma taya akai hakan tafaru
Sadiq dan Allah kahadani dashi Ahmed kenan aiko nadaka dashi bazai'amsama da cewar yasan kaba domin kuwa yanzu haka nima baiyarda yasanni ba yakuma tsayu akan haka
Ahmad gaskiya abin da akwai rudani da sarkakiya idan zaiyuwu kasami lokaci kashigo domin kahadu dashi fuska da fuska
Sadiq aiwannan yazamemin dole insha Allah gobe zanshigo da yardar Allah domin haduwa dashi to Allah yakaimu Amin sunyi sallama
Da dare ana cikin fira Ahmed yace am Abba gobe zanyi tafiya zuwa ina gombe insha Allah amma lafiya eh wani muhimmin abune zaikaini to Allah yakaimu yasa kayi farar tafiya Amin ya
Bayan wani lokaci sukayiwa juna sallama tare da saida safe
Suna kwance Aisha tace Abban Amir dan Allah kasanar dani dalilin tafiyarka domin kuwa jikina duk yamace saiji nake tamkar na hanaka wannan tafiyar saidai kuma banida wannan kwarin guiwar
Wannan ne yasa dole zanbarka katafi amma wallahi badan inasoba
Abban Amir wallahi ni'sai nake ganin tamkar baka taba sona ba ko Amir Allah ne kawai yakaddara masa zuwa wannan duniyar amma intakaine dabama aifesaba
Ahmad yafa kamata karika tinawa da cewar nimmafa inada haki dakai bakaine kawai kake da yaki daniba
Duk da cewar nasan damuwarka amma kasani wallahi sam wannan baikai dalilin da zaisa ka'ka sa bamu kyakkyawar kulawarka ba yakamata kasani wallahi nida Amir muna bukatar kulawarka
Wannan kai sam kagagara iya fahimtar haka ha!!! Abban Amir wallahi inasanka kuma wallahi wannan dalilin ne yasani yarda da Auran ka amma bakomai ina fatan Allah yakawo lokacin da
Wannan duhu zaiyaye agaremu dama anfada komai da lokacinsa Allah yakaimu lokacin da alkhairi Amin ya Allah
Am daga karshe dan Allah abinda nafada idan yabata ranka dan Allah kayafemin ina mainaiman afuwarka dan Allah kagafarceni
Kallon yake cike da tausayinta cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yake magana kigafarceni Aisha tabbas har yanzu bakisan kowacece Ambeeshar ba agareni idan kuma kinsani to kinmanta
Wannan yasa kike fadar haka Aisha Ambeeshar bakwai kawai kanwata bace ita rayuwata ce duk yanda zankwatanta maki irin soyayya da kauna da take atsakanina da
Ambeeshar to wallahi sam bazaki taba fahimtaba hakama balallai ki'iya yimin uzuriba wannan yasa kawai saidai na'iya baki hakuri dan Allah kiyi hakuri kigafarceni hakama ina mainaiman afuwarki gafararki da kuma yafi yarki dan Allah
Magana yake cike da kunci bakin ciki bacin rai da kuma tarin damuwa atare dashi itakanta tafahimci hakan daga yanayin da tagansa
Bakomai Abban Amir Allah ya'yafe mana gaba daya da kuma wannan nake fatan Allah yakawo mana qarshen wannan jarrabawar ya'amsa da Amin yarabbi Allah yakarba Amin ya Allah
Washe gari bayan sunyi break fast sunnufi part din Umma shigowarsu tayi dai-dai da shigowarsu Al-ameen duk sungaisa gaba daya Umma ina Ambeeshar tana ciki yanzu nake san natafi nafito da ita
Aliyu yatafi amma sam taki yarda tafito tare dashi Allah sarki toni bara nagwada nagani kozata yarda tafito to shikenan yauwa yatashi yanufi dakinta
Yasameta zaune tsakiyar gado tana wasa da teady hakama yafahimci tana cikin nishadi yagane daga yanda yaga fuskarta tana dauke da annuri sai wani murmushi take fitarwa maikayatar dana tare da'ita
Yayi tsaye jikin kofa yana kallonta sai wani farin ciki yakeji yana shigar sa sannu ahankali yake tafiya harya isa inda take yazauna tare da rika hannunta kanwata wasa kike kinasan natayaki kallonsa kawai take batare datace dashi komaiba
Ambeeshar zantafi gombe kuma insha Allah bazandawoba saitare da Ammar natabbata da yardar Allah daf kike da samun lafiya Allah yayarda Amin
Kanwata dan Allah kiyimin addu'a Allah yasa nasami abinda natafi naiman Allah ya'azani asa'a Allahumma Amin yacire hannunsa cikin nata yashafi fuskarta tare da sunbatarta inasanki kanwata wallahi inasanki sosai Ambeeshar Allah yabaki lafiya yasa karshen wannan jarrabawar taki tazo
Yanzu tashi mufita falo gunsu Abba koba zaki ba kallonsa kawai take amma bata'iya cewa dashi komaiba yatashi tare da rika hannunta mutafi ko dan Allah
Bagardama ta'tashi sunfito Aliyu yace lallaima wannan yarinyar duk da cewar bakida lafiya saikinyi ko'karin raina ni ko zaki sani
Haba Aliyu Dadina dakai mitar tsiya idan kafara mita sam bakajin kagaji haba yarinyar da taje haka zakayi fada da ita banda wauta irintaka dan Allah kabarta tahuta
Amma yaya Al-ameen a'a Aliyu kayi shiru haka kabar zancan to shienan nadena yauwa kokaifa su Umma sunnufi gurin cin'abinci Ahmad kuwa shine yake bawa Ambeeshar harka koshi bayan wani lokaci
Ahmad yatashi tare dayin sallama dasu Abba yakama hanyar gombe
By Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
0⃣5⃣to0⃣6⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Yayi nasarar isa garin gombe lafiya yana kira layin Sadiq yasauke sa masauki
Bayan yahuta yashiga tambayar Sadiq ya'labarin Ammar yaushe zanhadu dashi yayi murmushi Ahmad kenan dadina dakai gaggawa
Sadiq kenan wallahi sam bazaka ganeba wannan yasa kake fadar haka
Wallahi adalilin Ambeeshar ba'abinsa bazanyiba abinda bakasani ba ayanzu shine kullum mafarkina tunanina
Yaza'ayi Ambeeshar tasami lafiya wannan kullum shine araina dan haka kasanar dani yaushe zaka hadani da Ammar
Ha!!! Yaja numfashi garka damu Ahmad nafahinci damuwarka yanzu dare yayi sosai wannan yasa sam bazaka hadu da Ammar ba amma insha Allah gobe zanhadaka da Ammar
To Allah yakaimu Amin bayan wani lokaci suka tafi suka kwanta
Washe fari bayan sunkarasa duk abinda suke Ahmed yakai kallonsa ga Sadiq kafin yafurta wani abu yayi masa rigagi tashi mutafi ashe kasan maizanfada
Ahmad bafa yau nafara ganin kaba shekaru da yawa mukayi atare wannan yasa nasan abubuwa da yawa atare dakai to kaga ka dakata da wannan tarihin naka katashi mutafi ok sunfito sunkama hanyar zuwa gurin Ammar
Sunkawo wani guri Sadiq yayi parking Ahmad yakallesa yadai ka tsaya anan garka damu duba tacan kaga yakai kallonsa ga inda yayi masa nuni dashi kaga inda mutanancan eh to anan zaka sami Ammar
Amma nake ganin baiyanan to mujira fitowarsa ok sunyi zamansu amota bayan wani tsayin lokaci dasukayi anan sukahangesa yana zuwa
Cike da rudani Ahmad yake fadar sunan sa Ammar yadawo da kallonsa ga Sadiq yana maicewa amma Sadiq katabbata kowa yana ganin sa bamu kawai muke ganinsaba
Ahmed kenan kanasan kafadamin cewa kashiga firgici da ganin sa komiye Sadiq wallahi ina cike da rudani matuka taya za'ace mutumen daya yake da shekaru uku akasa sannan ace yana awani guri daban yana rayuwa
Gaskiya abin da akwai rikitarwa Sadiq kadai tabbata shimutunne kamar kowa ba fatalwa bane sannan kuma kowa yana ganinsa bamu kawai muke ganinsaba
Ahmed kenan to mu'kuwa wane zunubi muka aikatawa Ammar da zaihukuntamu da kurwarsa shi'mutunne kamar mudinnan to shikenan bara natafi nasamesa ok saika dawo
Yafito yanufi gunda Ammar yake ya'isa gurin tare da sallama bayan yagaisa da mutanan dake gurin yakai kallonsa ga Ammar tare da kiransa am bismillah ok yatashi sunkoma daga gefe
Ammar ko eh kaiwaye kuma maikake naima guna Ammar kenan kanasan kafadamin cewar bakaganeniba ne komiye ganewa kuma aibawai banganekaba nigaba daya bantaba sanin kaba arayuwata
Yaune ganina dakai nafari dan haka kafadamin kai waye mai'kuma kake naima guna ha!!! Yanisa tare da numfasawa Ammar kenan tinda nibakasanni ba to kasan wannan yaciro wayarsa aljihu tare da nuna masa photo Ambeeshar kasan wannan
Yagirgiza ka tare da furta a'a amma kataba ganinta a'a Ammar wallahi bazaiyuwuba cikin biyu dole daya yafaru kodai yaudarmu kake ko'kuma karasa tinanin ka kamar dai ita
Ammar dan Allah garka yaudari zuciyar da tayarda dakai garkaci Amanar zuciyar da ta'aminta dakai garka han'inci zuciyarda gabanta da bayanta cike take da kaunarka
Ammar mu'kuwa wane irin laifine muka aikata maka arayuwa da kake ta azabtar damu haka Ammar kafa tina da cewar akwai lahira shinwaikai sam bakada tausayine komiye
Maiyasa bakayin tinanin abu kafin aikatashi ko kana tinanin abinda kayi balaifi bane wane daliline dakai wanda yasaka aikatamana haka
Jin'sai zuba yake sam yaki yayi shiru yasashi dakatar dashi malan ya'isa haka garkayi ko'karin fadamin magana dan kawai nabaka damar dazakayi magana dani
Ni bansan kaba bantaba ganin kaba hakama bansan komai game da abinda kake fadaba dan haka katafi kanaimi abokin sa'insarka canku'karata aikin banza kawai kabatamin rai abanza mst yaja tsaki yajuya yayi tafiyarsa
Ahmad yanisa cike da mamakinsa yana haka yaji andafashi yajuyo dan ganin waye lokaci daya yayi ido biyu da Sadiq Ahmad kenan ainafadama sam bazaitaba amsama da cewar shine Ammar dinda kake naima ba
Saidai kawai kaharuka bazaiyuba Sadiq wallahi sam bazan hakuraba toya zakayi tabbas zanyi koma miye dan ganin nasashi ya'amsa cewar shine Ammar
Sadiq ni wallahi abu daya nake jiwa tsoro miyeshi Sadiq inajintsoron gar'ace shima yarasa tinanin sa domin kuwa nafara shakka akansa yaune kawai nafara ganin sa amma nafahimci wani abu atare dashi
Miyeshi Sadiq idan kalura dashi sam ba wadata atare dashi kallo daya nayi masa amma nafahimci cewar yana da bukatar taimako daga yanayinsa kuma nafahinci cewar sam baiyasan asan damuwarsa
Ahmed idan har hasashenka yatabbata cewar wannan ba Ammar bane to shiwaye kuma maiyasa yake amsa sunan Ammar Sadiq ni kaina wadannan tambayoyin ne sukayiman yawa aka abin takaicin kuma nagagara mai amsamansu
Lallai kuwa yazama dole nakara haduwa da wannan domin ya'amsaman wadannan tambayoyin nawa sannan kuma yafitar damu acikin wannan duhun damuke Sadiq ina bukatar nasake haduwa dashi yaushe kenan ko ayanzu
Aiyariga daya tafi sai kuma gobe kananufin bazan hadu dashi ba yau sosaima kuwa dominshi komansa yanayinsane ayanda yatsara bakuma wanda yasan komai atare dashi
Ha!!! Yanisa tare dajan numfashi to shikenan Allah yakaimu goben lafiya Amin ya'Allah sunjuya sun'tafi da dare Ahmad yagagara barci Sadiq yakallesa haba Ahmad miye haka kake garfa kaje garin naiman lafiyar Ambeeshar kaikarasa taka lafiyar
Sadiq wallahi ina cike da rudani wannan yasa tinani yayi yawa atare dani Sadiq waye wannan idan har yatabbata cewar shiba Ammar dinmu bane kuma maiyasa yake amsa sunan Ammar
Gaskiya abin da akwai daurekai matuka amma duk da haka dan Allah kasamawa kan'ka sassauci kaji to shikenan zanyi ko'karin hakan Allah yabaka iko Amin ya Allah
Washe gari sun'koma domin haduwa dashi amma sam basu sami ganinsaba yadaukesu tsayin kwanaki uku suna yawan neman sa amma bashi balabarinsa domin kuwa duk wanda suka tambaya amsa daya ake basu shine ba'asan komai komai game dashiba
Ahmed yadada tsorata dashi yakalli Sadiq tare da kiransa Sadiq anya kuwa wannan mutunne nifa natsinke Sadiq maiyasa bawanda yasan komai game dashi maiyasa yake da wani tsayi daban wanda bakowa yake dashi ba
Ahmad wallahi mutun ne saidai baikasance kamar kowaba wannan yasa komansa dabanne amma kayarda dani cewar shi'mutunne to Allah ya'azamu akanka Amin ya Allah
Wani yammaci zaune kawai suke bamai magana turo kofar da akaine yakauda shirun dakin duk kanninsu sukai kallonsu ga kofar dan ganin waye take lokaci daya sukayi ido hudu da Ammar da sauri cikin rawar murya suke anbatar sunan sa har suna sarkewa
Ammar kaine ya'akai kasannan anya kai mutunne kuwa shiru bai'amsaba sai wani kallonsu yake cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yace ku'suwaye maikuke naima guna maiyasa kukesan kushiga rayuwata
Dajimawa nafada maku cewar kurabu dani amma kinki maiyasa zakushiga cigiyata tako ina lungu da tsako maiyasa kuke bibiyar rayuwata abinda bakusaniba shine koyaushe ina atare daku wannan yasa sam bakwaganina duk inda kukaje naimana
Kusani kamar yanda kuke naimana haka nima nake bibiyarku jinbakuda niyar cutar dani yasani nabarku kufadamin ku'suwaye waya aikoku gareni kuma maikuke naima guna
Kallonsa suke cike damamakinsa Ahmed yagagara fadar komai yayinda mamakinsa yabaiyana atare dashi Sadiq yace to karaso ciki mana aikataho adai-dai lokacin da muke bukatarka Ammar kasan wannan ko har yanzu baka'iya tinasaba
Taya zantina mutumen da bantaba saninsa ba to amma katina Ambeeshar wacece maiwannan sunan yarinyarda na'nuna naka photo ta awancan ranar balallai na'iya tinawaba inazuwa
Ahmed yadauki wayarsa yanuna masa photo ta yagirgiza ka tare da furta a'a bansan taba balantana kuma na'iya ganeta ho! Subhanalillah
Ammar wallahi inajin tsoran gar'ace kaima karasa tinanin ka kamar dai'ita kasani ni qlau nake ba'abinda yake kaina to kuma taya zanrasa tinanina dan haka kawai kusanar dani abinda kuke naima dani to zansanar dakai ko nace zantinama abinda kamanta
Wannan sunansa Sadiq ni'kuma Ahmad ina da yaya mai'suna Al-ameen ina kani mai suna Aliyu hakama ina da kanwa mai'suna Ambeeshar munkasance muhudu agurin iyayenmu Ambeeshar itace kawai mace acikinmu hakama itace Auta duk da cewar ita da Aliyu tagwayene amma dai itace karama wannan yasa tafiye shagwaba kuma tasamu gata sosai agurinmu
Nida Ambeeshar munshaku da junanmu sosai tamkar 'ya da Uwa kanwa ita wutar kyauce zanma iya cewa tamafi kyau kyau 'yan matama kyashinta suke domin kuwa ita fitilace acikinsu
Yayinda samari kuma sukaganta gigicewa suke amma duk da kyanta sam bata baiwa samari fuska sam basa gabanta wata rana
Yau takasance Monday Aliyu yagama shirin sa yafuto banga Ambeeshar ba yashiga tambayar Umma ina Ambeeshar tana dakinta gardai bata shirya ba to saika duba kagani ok yanufi dakinta yasameta akwance saijuyi take
Ke maikike nufi da har yanzu baki tashi kinshiryaba koba kiga time ba kai kaga garka wani matsantamin kabarni nayi shirina atsanake
Idan kuma bazaka jiraniba saikayi tafiyarka ta'tashi tashiga toilet domin tawatsa ruwa shikuma yajuya yafuta Abba tagansa wani iri ransa anace Abba yashiga tambayar sa
Aliyu lafiya wallahi Abba bansan maiyasaba yarinyarcan tarainani maitayiba kuma wai Abba sai yanzu take shiga wanka ita kullum sai tasa munmakara
Sam batasan tashirya dauwuri tafiye lalaci da yawa kai'ka'iya bakinka Allah kanwar tawa kake'kira malalaciya wallahi zansa karaina Lanka
Kajiko Abba wallahi dama duk yaya Ahmad ne yake kara sangarta'ta wannan yasa takeyin duk abinda taga dama kuma sam batajin tayi abinda baidaceba
Aliyu Allah ka'kama kanka kadena sawa kanwata ido to yaya Ahmad nadena tinda kai sam bakasan gaskiya yaya Al-ameen yafika fadar gaskiya eh naji su Umma sai kallonsu suke suna murmushi
Bayan mintuna biyar saiga Ambeeshar tafito sannun da fitowa kanwata yauwa yayana barka da hutawa ina kwana Abba ina kwana Umma lafiya qlau kinfuto eh to tashi mutafi
Kana nufin hakan zantafi banyi break ba gaskiya Ambeeshar kina da matsala dan Allah kisaki jiki kinga mun'makara kai'kaga garkayi ko'karin fadamun magana domin ba zanyi shiru ba yayana mutafi muyi break ok
Yatashi sun'tafi sunyi break bayan sun'karasa ta'tafi tasunbaci Abbata da Ummarta sannan suka tafi kanwata saikin dawo to yayana sunfita sunyi tafiyar su yayinda Aliyu yaketa fada da ita haka suka isa makaranta suna fada da rigima
By Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
0⃣7⃣to0⃣8⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Sun'isa school sunsamu ana dukan makara tinkan sukarasa Ambeeshar tafara zubar da kwalla
Aliyu yamata wani banzan kallo to aiga inda taurin kan'naki yakaimu kinsa mun'makara
Yanzu dole sai andakemu mst yaja tsaki aisaiki shige mutafi nibazani ba awane dalilin saboda ina tsoran duka
Allah dan Allah kayi wani abu akai to ni'kuma maizan'iya dan Allah kayi abinda zaihana adakyan bazanba shige mutafi
Kuma wallahi kimun shiru garki karani takaici sun'isa gurin sun'dukursa dukansu malamin yakalli Ambeeshar yayi dariya tofa ke tinkafin adakeki kike kuka dacan bakyasan duka maiyasaki kika makara
Aliyu yabada hannunsa anyi masa nasa yakai kallonsa ga Ambeeshar lokaci daya suka hada ido yadaka mata harara tayi saurin sunkuyarda kanta kasa
Yace am malan wannan kanwata ce hakama batada lafiya idan bazaiyuwu ayafe mataba to ayimun nata yamika adayan hannunsa haka akayi masa nata sannan suka tashi suna nufi class
Duk wannan halaccin da yayi mata amaimakon ta'iya yimasa godiya saima tabijiro masa da wani zance kaga Aliyu kafa dena kirana da kanwar ka domin nibanyarda kai yayana bane tinda tare aka aifemu
Dan haka kaiba yayana bane niba kanwar ka bace kawai dai mutagwaye ne to maiyasa baki kasance Hassna ba saiki kazo amatsayin Hussaina kai ni'wallahi bansan maiyasa Umma tafara aifanka ba gashinan sai ko'karin raina ni kake
Da kuma wannan zancan suka isa class ananma sunsamu anadukan makara Aliyu yayi murmushi yakalleta inasan irin haka wallahi anzo gurin zaki raina kanki ne am kaga dan Allah kayi hakuri
Wallahi duk abinda nake fada kawai abakine baikai zuciba dan Allah kataimakyan kaji ni'kuma zankiraka da yayana kayarda dani sam bana bukuta yashige abinsa tabiyo bayansa jikinta asanyaye
Am malan dama kai adokarka idan mutun biyu sukayi laifi adabi'arka babba kake hukuntawa to'ga yayata ce idan takaraso saika hada dukunka da nawa duka saikayi mata malamin yakallesa
Aliyu da gaske Ambeeshar kanwar ka ce malan kenan ka'tambayeta kaji na tabbata zata fadama gaskiya to shikenan zaka'iya zuwa ka'zauna ke'kuma karaso ciki ganin Aliyu yatafi yazauna malamin tana ko'karin kaimata duka yasata tashi tace a'a
Malan a'a wallahi ni'ba yayarsa bace ni'kanwarsa ce duk da cewar munkasance tagwaye anhaifemu atare amma shi'aka fara haidawa shine Hassan ni'kuma Husaina dan haka shine babba malamin yakai kallonsa ga Aliyu tare da kiransa
Aliyu na'am zonan yatashi yatafi abinda tafada gaskiya ne eh tomaiyasa kafadamin sabanin haka saboda ita sam taki yardar cewar ni yayanta ne yakai kallonsa gareta
Ambeeshar shinkinyarda cewar ni yayanki ne kamar bazata amsaba ganin kuma batada wata mafuta yasata amsawa da eh ok yanzu zaki iya tafiya kizauna kamar dai akofar gate nanma Aliyu yadauki dukansa dana Ambeeshar
Bayan wani lokaci malamin yafuta Ambeeshar takai kallonta ga Aliyu wanda gaba daya tausayinsa yagama kamata yaga yasaka hannayensa agaba yana kallo cikin kwantar da murya take magana dashi
Tare da dora hanninta kan'nasa tana maicewa Kagafarceni dan Uwana dan Allah kayafemin yadago kai yakalleta tare da yimata murmushi bakomai yar Uwata matsayinki agurina yafi da haka
Bayan sundawo gida Aliyu yace am Abba dan Allah inasan araba mana mota nida Ambeeshar domin kuwa sam bazan jure zuwa school atare da itaba maiyasa nan yashiga sanar dasu komai
Abba wallahi ni'sam bazan jure ganin ana dukan Ambeeshar ba wannan yasa duk laifunda tayi ni'ake duka gata kuma da yar banzar tsokana akullum cikin kai'korafinta ake tayiwa wannan tayiwa wancan ita take laifi amma kuma ni ake duka
Wannan yasa sam taki tadena yayin zuwa makaranta kuma tasa mu'makara Abba wallahi nasoma gajiya wannan yasa nakesan araba mana school da
Sauri Ambeeshar tace wallahi bazaiyuba Abba wallahi idan karaba mana school toni kuma saidai nahakura nabar karatu gaba daya
Subhanalillah a'a kunga duk baza'ayi hakaba ainesa tazo kusa watanni biyar suka rageku ku'kammala dan Allah kuyi hakuri da junanku kunji
Abba ai'agida muke wannan rigimar amma amakaranta kanmu ahade yake garkaso kaga yanda Aliyu yake nan-nan dani tamkar yayana ina nufin wannan tanuna Ahmad tana dariya shikuma murmushi yake
Amkinga Ambeeshar dan Allah kidena domin kuwa nafahimci cewar damuwar daga kene ni'kuma Abba kajiko yaya Ahmad ta'tashi tanufi dakinta tana fishi Ahmad yabita yana rarrashinta su Umma kuma sunbita da kallo suna murmushi Ambeeshar kenan kayan Allah sarkin shagwaba kesam ba"ayimaki dai-dai Allah yakyauta sun'amsa da Amin
Bayan wani lokaci yau takasance ranar Saturday ce idan suka tafi islamiya karfe 08:30am basa dawowa sai 08:00pm yaumadai kamar kullum Aliyu yakarasa shirin sa yayinda Ambeeshar komai bata aikatawa kantaba suna cikin sa'insa saiga Ahmad yafito yashiga tambayar su lafiya
Yaya Ahmad wallahi nagaji da halin wannan yarinyar ita kenan kullum abu daya ni wallahi nagaji saidai araba mana makaranta kowa yatafi lokacin daya shirya narasa dalilin dayasa ita magana daya sam bata zaunawa akunnanta
Tarainani da tawa haka sam bayayimin kallon yayanta wannan yasa takeyimin duk wulakancin da taga dama amma nasan yanda zanyi zan'ajiye tausayinki da soyayyarki agefe daya nasassaba maki domin nafahimci kinfi bukatar nafara dukanki agidannan
Ahmad yadakatar dashi ya'isa haka Aliyu maikuma yakawo zancan duka itadin halama ja kace dazaka daketa yan second din dakabata ne zasujaka harkayi tinanin dukanta to kasani sam bazandaukarma ba kawai kaci gaba da lallabata har zuwa lokacin da zata 'iya fahimtarka amma yaya Ahmad kaimafa kasan cewar sam batakyautawa kaga dan Allah kabar zancan nan yadawo da kallonsa ga
Ambeeshar wadda yaketa aikin fishi tamkar wadda akayiwa sakon mutuwa yagirgiza ka haba kanwata dan Allah kidena wannan fishin kefa sarauniyar gidannan ce ko Umma da Abba umarninki suke jira to balantana kuma Aliyu wanda yakasance kaninki aishine baisa niba amma mu'duk munyarda da cewar kece yayarsa
Yaya Ahmad da gaskene yayi murmushi tare da daga mata ka to yakamata kasanar dashi domin yafara kirana da Aunty damanican tantama nakeyi nakasancewar Hassan saidai yakasance amatsayin Hussaini kajuya kafada masa angama ranki yadade
Yadawo da kallonsa ga Aliyu wanda shi'gaba daya takaicinsu yagama isarsa am Aliyu inasan kasani daga yau kuma awannan lokacin Ambeeshar itace yayarka kuma sam banasan katambayeni akan haka kawai kayi kamar yanda nafadama kajiko kallonsa kawai yake yayinda yagagara iya cewa dashi komai suna haka saiga Al-ameen yafito fitowarsa tayi dai-dai da fitowarsu Abba bayan sungaisa Al-ameen yashiga tambayar su lafiya
Domin yafahimci kamar da damuwa atare dasu shiru basuyi magana ba yadai Ku"kayi shiru kufadamin maiyake faruwa Ahmad yace bakomai yaya Al-ameen ok Aliyu ya'akai har yanzu ba kufita zuwa makarantaba cike da bacin rai yake sanar dashi abinda yake faruwa yakai kallonsa ga Ahmad
Ahmed kai da bakinka kafurta cewar Aliyu yarika kiran Ambeeshar da Aunty acewarka itace yayarsa am yaya Al-ameen dama kaga yadakatar dashi just answer mee kafada ko baka fadaba eh nafada to akanme am yaya dama dai kasanni nakanyi duk abinda kanwata take so wannan dalilinne yasani fadar haka
To gargadi wannan yanda yazama na farko to'inasan yakasance na'qarshe insha Allah ok yawuce yamaida kallonsa ga Ambeeshar yamata wani kallo maikama da harara ke waimaiyasa bakyajin magana maiyasa kika raina Aliyu da yawa dan kawai anhaifeku atare wannan shine dalilinki to kisani kasancewarku tagwaye baiya nufin kirainasa domin kuwa ko'kinaso ko'bakyaso shi'yayankine wanda duniyama tashaida haka
Dan haka kisani yimasa biyayya wajibinkine dole kuma zankafa maki doka daga yau danake fada maki garki yarda najiwa kunnena kinkira sunan Aliyu batare da kinhada da yaya ba wannan kenan sannan kuma duk abinda kike kitabbata kinyi shieinki nazuwa makaranta akan lokaci inma taboko ko islamiya
Idan kuma kika sabawa Umurnina to kisani nima zansaba maki tashi kitafi kidauko hijabinku kutafi makaranta da sauri takalli jikinta tamaida kallonta ga yayan nata haba yaya taya zantafi makaranta ahaka yayi hakuri nashirya mana da'can bakisan da shirin ba da kika kwanta kikayita barci abinki
Maza saki jiki kitashi kidauko hijabinki kutafi Abba Umma kusa baki mana taya zantafi makaranta ahaka kafin sufurta komai tadawo da kallonta ga
Ahmad cikin muryar kuka take masa magana yaya Ahmad kace dashi wani abu mana tayama zan'iya tafiya makaranta ahaka yoko Afra zata fita ahaka balantana kumani yaya dan Allah kayi mata sassauci domin kuwa hukuncinka yamata tsauri da yawa balallai ta iya daukaba yaya Al-ameen Ambeeshar fa har yanzu ita yarintace tana bukatar alallabata tare da rarrashinta kai ya'isa haka damacan ai'rainonkace wannan yasa takasance ahaka
Yamaida kallonsa gareta ke tashi kidauko hijabinku kutafi garki bari nakara mai-maitawa tamike tsaye tare da sakin wani irin kuka tafice Ahmad yatashi zaibi bayanta Al-ameen yadakatar dashi koma kazauna bayanda zaiyi dole Yakoma yazauna sai kuma zuwa wannan lokacin
Abba yayi magana yace haba Al-ameen yakake ko'karin firgitamin 'ya yanzu wannan duk akan Aliyu ne itafa yarinyace bakomai bane yake zauna banta farar dayaba dole tana bukatar rarrashi da lallami amma Abba yanzu kenan abinda nayi na'aikata kuskure a'a sam baka aikata kuskureba amma kasani hakuncin daka daukar mata yayi tsauri da yawa yaka mata kayi mata sassauci
Aikuwa idan hakane Ambeeshar bazata taba kasan cewa adai-daiba kuma kusani wallahi tana cutar da Aliyu nasani dukanmu munasan Ambeeshar sosai saidai kuma sam bai kamata mubar soyayyarta tahanamu sata ahanyaba wannan yasa nake ko'karin sai-saita'ta nida Aliyu saidai kuma Ku sam kungagara fahimtarmu saima kuke ganin kamar muna tsaurara mata
Wanda kuma sam ba haka bane zuwa yanzu yakamata kufahimcemu dajimawa nafahimceku Al-ameen Allah yataimakeku yarayamunku yakuma albarkaci rayuwarku Amin Abba
Bayan wani lokaci Ambeeshar tafuto kallo daya zakayi mata kafahimci cewar cikin fishi da bacin rai take hadi da damuwa tafice tagabansu batare da tace da kowansu komaiba Aliyu yatashi Abba Umma saimundawo adawo lafiya yafita yayi tafiyarsa abinsa
Sai zuwa wannan lokacin Umma tayi magana tab tirkashi da sauri Al-ameen yace Umma maiyafaru Ambeeshar mana tadauzafi da yawa bansan har zuwa yaushe wannan fishin zaidauketa ba garki damu Umma zata sauko aijiya ba'yauba girma take hankali nashigarta
Yanzu Umma tayama zaki yarda cewar Ambeeshar da Aliyu tare aka'haifesu gaskiya idan ba'anfadaba sam baza'aganeba hankalinsu ba dayaba ni wallahi wani sa"in idan tanayin wani abun sainayita ganinta tamkar Afra wanda batafi shekaru biyu ba to Allah yakara shirya mana
Bajima wa da tafiyarsu Ambeeshar Ahmad yatashi yayi tafiyarsa su Abba sunbisa da kallo Ahmad kenan yayan Ambeeshar shidai sam bayasan yaga abinda zaibata ran Ambeeshar to Abba muzamu biye masa ne aiyazama dole musata ahanya bawai dan banasan taba ko dan natursasata ba a'a saidan rayuwarta tayikyau nangaba to Allah yakyauta sun'amsa da Amin
By Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
0⃣9⃣to1⃣0⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Tin'daga lokacin da Al-ameen yasakawa Ambeeshar doka akan Aliyu sai komai yasauya idan ba da Ahmad ba bata fira da kowa dayake gidan
Su Abba sai aikin rarrashinta suke dakyar suka samu tasauko saidai tsakaninta da Aliyu ba fada ba sakin fuska gadaisunan
Wata rana tana part din Al-ameen tana fira da Asma'u saiga Afra Aliyu yadaukota daga makaranta da sauri Ambeeshar tazo tana yimata oyoyo tasunkuya domin daukarta kafin tadauketa Aliyu yayi mata rigagi da sauri yadauketa tare da cillata sama yana mata wasa
Ita kuwa sai dariya take azahirin gaskiya ran Ambeeshar yayi matukar baci wanda dukansu sunfahimci haka bata'iya furta komaiba saima juyawa da tayi tanufi hanyar futa Asma'u takirata Ambeeshar ta'amsa tare da juyowa na'am Aunty
Gardai tafiya zakiyi eh harkingaji da firar zandawo anjima to shikenan nagode Aunty tajuya tayi tafiyarta sunbita da kallo Aliyu yayi murmushi tare da anbatar sunanta Ambeeshar kenan Allah yakyauta Asma'u takallesa Aliyu ka zauna mana
Toh yafara ajiye Afra sannan yazauna am Aliyu zan'iya fadar wani abu inajinki Aunty wai maiyasa bazaka dai-daita tsakaninka da Ambeeshar ba wallahi ni'sam banasan kuna wannan halin domin kuwa wannan sam baikamaceku ba
To Aunty yazanayi ni' wallahi bansan dalilin da yasa Ambeeshar take hakaba wai'itasam batasan aceni yayanta ne kawai dan anhaifemu tare wannanfa shine kawai damuwar to Aliyu idan kuwa hakane maiyasa ba zakayi yanda takesoba domin kawai azauna lafiya saika fada mata cewar kayarda kaiba yayanta bane itace yayarka idan zaka'iyama saika rika kiranta da Aunty
Sannan kuma kadena tsokanarka kaga dai yanzu kai'katsokaneta dalilin haka yasa tafusata harta tafi wanda kuma kaine sanadin tafiyarta Aliyu dan Allah kadai-daita tsakaninka da yar uwarka kaji yayi murmushi to
Aunty insha Allah zanyi ko'ganin hakan duk da cewar itace da matsala yauwa Aliyu Allah yabaka iko Amin ya Allah
Ta'isa part din Umma rai abace tamkar wadda dan ginta gaba yada suka kare Umma tace to! to!! to!!! Maikuma yafaru waya tabaki kedawa fadamin waya tsokaneki dan neman rigima fadamun waya tabaki cikin muryar shagwaba tamkar zatayi kuka yayinda idanuwanta suke zubar da kwalla Umma wa kike tinanin zaitsokanan banda Aliyu kai subhanalillah
Maikuma yaimaki kawai kibar zancan garki'karani takaici toshikenan amma dan Allah alfarma daya nake naima agurinki inajinki dan Allah kidena wannan fishin wallahi banaso kinji tadaga mata ka alamar to yauwa Ambeeshar na Autana inasanki da yawa tayi dan gajeran murmushi nagode Ummana
Da dare suna falo suna fira Abba ya'tambayi Ahmad ina Aliyu wallahi Abba bansan ina yashiga ba kanwata ko'kinsan inda yashiga amma garkiji haushina kinji shiru bata amsaba Ambeeshar zan'iya cewa wani abu eh kafin yafurta wani abu Aliyu yaturo kofa yashigo tare yake dasu Afra
Allah sarki yaron kirki yanzu nake cigiyarka yayi murmushi nagode Abbana bakomai Aliyu amma yau ina kashiga ne haka Abba kenan ina part din yaya Al-ameen tofa kace yau Asma'u ka'kaiwa fira eh Umma aikuwa kakyauta sai kuma zuwa wannan lokacinne suka gaisa gaba dayansu
Yakai kallonsa ga Ambeeshar yace yayata maiyasa bazaki yimin magana ba Ahmed yace tofa saban salo yau kuma da haka kake kiran Aunty Asma'u yayi murmushi yaya Ahmad kenan ni'sam bada Aunty Asma'u nakeba da yayata nake wato Ambeeshar zuwa yanzu nayarda da cewar itace yayata ni'kuma zankasance amatsayin kaninta
Domin kuwa ina bukatar ganin farin ciki atare dake dan haka kidena wannan fishin dani wannan yawuce hakama daga yau zanrika kiranki da yayata kiyarda dani dan Allah kinji
Take taji wani farin ciki yana shigarta tayi wani kyakkyawan murmushi maitake da yar dariya yauwa Aliyu ko'kaifa amma kawani kafe akancewar kaine yayana to kaga yanzu komai yawuce insha Allah ba'abinda zaifaru atsakaninmu domin kuwa kawarware matsalar yanzu ba wata damuwa su Abba sai kallonta suke Al-ameen yace Ikon Allah ikon gaske lallai Ambeeshar wallahi san'girmanki yayi yawa
Yadawo da kallonsa ga Aliyu yace haba Aliyu to yanzu maikayi yanzu a'a yaya Al-ameen sam garka damu da wannan hakama dan Allah garkace komai
Toh shikenan Allah yakyauta Amin
Shekara kwana zuwa yanzu su Aliyu sun'kammala karatunsu na secondary kuma sunyi nasarar fita da kyakkyawan result duk da cewar bawasu shekarune da itaba hakama bawani girman jikine da itaba saidai kuma samari sunyi mata ca aka
Wanda ita kanta sam bata da ra'ayi dasu balantana kuma ta'iya basu fuska wannan yasa tama dena fito da kawaye domin kuwa tafahimci cewar duk tafuta sai tasami wani wanda zaitareta da zancan soyayyarsa yayinda ita'kuma hakan yake matukar kona ranta
Bajima wa sosai suka fara zuwa makaranta inda kuma anan'ne Ambeeshar tayita haduwa da kawaye iri daban-daban wadansu ra'ayinsu yazi iri daya wasu kuma sabanin haka
Amma ita duk acikinsu da mace biyu tafi shiri Farida da Anisa zuwa yanzu Ambeeshar da Aliyu sundai-daita tsakaninsu sai yar rigimar dabatakai takawoba yanayin yau da gobe
bayan wani lokaci yan matan makarantarsu suka fara kyashinta ganin yanda samari suke bata kulawarsu hakan tasa suka fara kishinta duk da cewar ita bata basu kulawarta amma hakan baisa sundena kishinta ba
wata rana zaune suke tare da manyan kawayenta Farida da Anisa Safiya tasamesu ranta abace kallo daya zakayi mata kafahimci sam bata cikin dadin rai cike da bacin rai take magana ke Ambeeshar wallahi kishiga hankalinki kirabu da Salman idan kuma bahaka ba to wallahi zansa kiraina kanki domin kuwa nafahimci abin naki sam ba mutunci to kisani wallahi Salman yafi karfinki domin shiba sa'arki bane kitafi kinaimi sa'arki banza
Ambeeshar kallonta kawai take yayinda takaicinta yayi yawa atare da ita wanda wannan dalilin'ne yahanata furta komai ganin sai zuba take yasa
Farida dakatar da ita ke dan Allah ya'isa haka banza ke Salman yake gabanki kuma ke'kike jintsoran garki rasa Salman tinanin balallai ki'iya samun wani nankusaba to kisani Ambeeshar Salman sam baiya gabanta saiki tafi kitambayi Salman yanda sukai da ita
Ke'kinga sarkin fada badake nakeyiba kibari Uwar dakinki tayi magana domin da ita nakeyi kuma itace abaryina bakeba yar asha'miya kinga Farida dan Allah kidena wahalar da kanki tare da bata yawunki abanza wofi saboda wannan kawai kibarta idan ta'isa tayi sa'insa da Ambeeshar domin tasan maizaifaru
Kunga kudaje niba daku nakeba da Uwar dakinku nake kubarta tayi magana Ambeeshar dai kallonta kawai take yayinda tayi mata ko oho tamkar ma bata gurin suna haka wayarta tadau ruri tadaga hellow Ambeeshar kina ta'ina ina kusa da Department dinsu Salman Sani ok to kizo mutafi ok kajirani kadan ok saikin zo yauwa ta'ajiye wayarta tare da kai kallonta gasu Farida Anisa kutashi mutafi ok sun'tashi zasu tafi
Da sauri Safiya tawani janyota da karfi ke malama da ke nake magana kike ko'karin wulakantani to kisani wallahi nafi karfin wulakancinki Ambeeshar tajuyo afusace cike da bacin rai da takaicinta tawanketa da tafi wallahi inamaiyi maki gargadi daga yau garki koma kuskuran dora hanninki akan jikina bana ballagaza kitafi kinaimawa kanki yanci tajuya sunyi tafiyarsu tabisu da kallo cike da manakin
Ambeeshar tare da takaicinta nikika mara tabbas sainasa kinraina kanki dani kikeyi zamu hadune sun'isa gun Aliyu sunyi sallama da Ambeeshar suntafi
Ahanyarsu ta'tafiyane Aliyu yake tambayar ta maiyake faruwa da ita ne ganin bara cikin dadin rai ha!!! Tanisa tare dajan numfashi Aliyu wata yarinyace nakesan tashiga konata nantashiga sanar dashi abinda yake faruwa yayata kenan gaskiya ke kyakkyawace wannan yasa dole yan mata suyi kishinki
Hum tayi dan gajeran murmushi Aliyu kenan aikuwa zanyi maganinsu domin kuwa daya bayan daya saina haddasa masu ciyon zuciya da damuwa saboda kuwa wallahi nafidasan dukansu suhadu zuciya zumace dani suke zancan yayi yar dariya
Ambeeshar kenan to maikike shirin kullamasu garka kayi gajin hakuri kawai kazama dan kallo to shikenan da kuma wannan zancan suka isa gida
Washe gari bayan sunfito daga Ambeeshar takalli su Farida tace Anisa yaza'ayi nahadu da Salman cike da mamakinta sunce Salman fa kikace eh Salman inasan nahadu dashi amma Ambeeshar maiyasa kike san kihadu da Salman bayan kinyi masa kashedi akanki eh nasani inasan Safiya taraina kantane wannan yasa nake bukatar
Salman ayanzu domin tahakanne zanyiwa Safiya yawo da hankali wallahi tinda tashigo gonata yazama dole nasa taraina kanta eh to hakanma dai-daine yanzu domin haduwa dashi yazama dole mutafi Department dinsu ok kutashi mutafi ok suntashi sunfice
Suna cikin tafiya basu karasa kaiwa ba suka hadu dashi yakaraso gunsu yana murmushi gimbiya sarautar mata sannunki da zagawa maiyasa baki naimi naraka'kiba koda yake nasan cewar sam bakyada ra'ayi dani saidai kuma'ni haryanzu nakasa sabawa zuciyata da rashinki
Ambeeshar dan Allah kiyarda nakasance amatsayin abokinki please kice dani wani abu kamar ba zatayi magana ba ganin Safiya nazuwa yasata sakin wani lallausar murmushi tana maicewa haba Salman mai'kuma nakesan nafada bayan katuro Safiya taci mutiincina ta'Uwa ta'Uba ni'sam ba'abinda zan'iya fadama har saikanunawa Safiya cewar ina da daraja agurinka idan yaso daga bisani saina yarda ka'kasance abokina
Ambeeshar wai maikike fadane haka taya zantura Safiya tayi batanci gareki kuma harda zagi wallahi sam bazantaba aikata maki hakanba dan Allah kiyarda dani domin kuwa sam banida wata masaniya akan haka dan Allah kiyarda dani please suna haka saiga
Safiya tawani zo afusace tare da nuna Ambeeshar ke wai bana yimaki tsakani da Salman ba maiyasa ke'sam bakya da zuciya ne da sauri Salman yadakatar da ita ke'kinga ya'isa haka garkiyi wa mutane rashin kunya da futsara sa'arkice maiyasa kike abune tamkar wata mara hankali maiyasa ke'sam bakya aiki da hankali da kuma tinaninki ganin yadukufa yasasu
Ambeeshar sukayi tafiyarsu suna dariyar Safiya ganin yanda Salman yarufeta da fada yayinda ita kuma tagagara furta masa komai Farida ammafa Safiya tasoma bani tausayi Anisa kenan ai wallahi saita raina kanta domin kuwa guguwa tajanyowa kanta dani takeyi wallahi zata gani
Salman kuwa yashiga fada da Safiya ta'inda take shiga batanan yake futa ba ita kuwa sai wani kallonsa take cike da mamakinsa jinsai masifa yake mata yasata dakatar dashi ya'isa haka
Salman ya'isa maiyasa kake ko'karin wulakantani akan Ambeeshar santa kake kome to wallahi baka'isa ba ba'kuma zanbarka ba kuma kasani yazamemaka dole karabu da Ambeeshar koda kuwa hakan zaitukar dakai domin kuwa wallahi bazantaba barin ku'kasance atare ba nafadama tajuya rai bace tayi tafiyarta shikuwa yabita da kallo cike da mamakinta yayinda yake magana da zuciyarsa lallaima wannan yarinyar tomai take nufi dani ko anfada mata niyatonta ne da zatayi ko'karin juyani kamar wani yaronta wallahi kiyi kigama dole kihakura dani domin kuwa nida zuciyata Ambeeshar mukeso kuma ita muke da burin samu da fari zanfara kasan cewa abokinta daga bisani kuma saina baiyana soyayyata agareta ha! Yanisa tare da anbatar sunanta cikin wani shauki Ambeeshar wallahi inasanki sosai hakama ina fatan damunki yalumshe idanuwanta yayinda yake ganin kyakkyawar fuskarta acikin duhun idanuwansa
0 comments:
Post a Comment