Washe gari yanar takasance ba school gata kuma tayi Ammar alkawarin cewar zasu hadu zuwa yanzu kira biyar yayimata amma bawanda ta'iya dagawa tasami
Ahmed adakinsa kasan cewar ranar ba ranar aiki bace kallo daya yayi mata yafahimci cewar da magana abakinta yayi murmushi kanwata yadai naganki wani iri maiyake faruwa ne fadamun
Am yayana fita nakesanyi kuma tare nakesan mutafi zuwa ina nima bansani ba kamar yafa am jiyane nayiwa Ammar alkawarin cewar yau zamu hadu gashi kuma yanzu sai kirana yake nagagara dagawa
Maiyasa saboda bansan abinda zanfada masaba idan ya'tambiyan akan haduwarmu wayeshi wannan Ammar din wanda cikin sauki yayi nasarar samun zuciyar kanwata
Tayi murmushi maitare da yar dariya yayana kenan eh mana sanar dani wayeshi nima bansani ba sunansa kawai nafi rikewa nantasanar dashi komai akansa yayana wallahi inasan nahadu dashi garki damu kanwata aikina dani dama da akwai inda zamu tafi tare da Sadiq
Saimu fita atare idan na'ajiyeki sai natafi bayan munkammala komai saina tafi nadaukeki hakan yaimaki tadaga masa ka tana murmushi to jirani na mintuna biyar ok
Bayan mintuna biyar sunfuto Abba yashiga tambayarsu ina zasu am Abba zata rakani gurin yayi shiru tare da kai kallonsa ga Asma'u yana murmushi am
Abba banasan Aunty Asma'u taji haushina tomaiyasa zataji haushinka idan taji inda zamu kasanta da kishi Aliyu yayi dariya yaya Ahmad hakan yana nufin gurin Aunry Aisha zaku tafi eh amma gareka taji tomiye katafi mana aini inanan to shikenan ka'kula da ita yanda yadade insha Allah su
Umma kuwa sai dariyarsu suke da kuma haka suka fita tasanar dashi gunda zasu hadu dakyar ya'iya gane gurin kasan cewar sa bako bayan yagaisa Ahmad yatafi domin haduwa da Sadiq yakalleta yana murmushi kinyikyau sosai
Kanta na'asunkuye ta'amsa da nagode am Ambee zuwa yanzu yakamata nagabatar da kaina agareki sunana Ammar Dadyna Abey Mummyna kuma Nandani Dadyna dan asalin wannan kasarne kuma awannan garin
Mummyna kuma ita yar kasar India ce garin Mumbai kinji mamaki'ko Dadyna yatafi kasar India karatu bayan daya kammala saiya samu aiki acan sai ya'Auri Mummyna inda daga bisani kuma aka aifeni acan nayi wayo na girma nayi komai nawa watanni biyu da suka shige Dad yazo mana da zancan wai zamu dawonan da zama domin kuwa shi"anan yakesan nayi Aure kinsan maiyafaru daya fadi haka
Afusace nace ina Dad wallahi bazaiyuba tayama zan'iya rayuwa awannan kasar balantana har takaini nayi Aure acan tir Allah yakiyaye alokacin ran Dad yabaci sosai abisajin kalamaina
Amma kinsanme bainunaminba kasan cewar yana matukar sona dakyar yasamu nida Mum muka biyosa zuwanan akancewar bayan watanni Uku
Zamu koga India nida Mum kinsan wani abu wallahi tinda mukazonan kullum cikin fatan ganin nabar kasarnan nake nakoma India amma nafada maki wani abu
Ha!!! Yanisa tare dajan numfashi Ambee wallahi haduwata dake saita sauya ni dama komai nawa Ambeeshar wallahi kallo daya nayimaki amma sainaji ina bukatar narayu dake naduk iya rayuwata inasanki wallahi inasanki sosai
To amma taya zansa kiyarda da hakan Ambee nafadamaki wani abu ni yarone mai sa'a Dad da Mum suna sona sosai wannan yasa duk kanninsu kowa yanasan na'Auri yan kabilarsa Dad yanasan na'Auri yarnan Mum kuma tanasan nayi Aure a India
Amma kumani duk bandamu da ra'ayinsu ba nawa ra'ayi shinafi karkata akansa nikawai ke nakeso dan Allah kiyarda da soyayyata kinji domin kuwa ni nariga dana baiwa zuciyarki damake ke'kanki duk kannin soyayyata
Ambeeshar gaskiya yakamata nayi wani abu domin kuwa nasa kiyarda da cewar inasanki ha!!! Tanisa tare da jan numfashi tana maisauke ajiyar zuciya cikin wata lallausar murya take magana cike da shagwaba tamkar zatayi kuka a'a
Ammar basai kayi komaiba ni nayarda da soyayyar da kakemin kuma nima inasanka da gaske kina sona tadaga masa ka tare da furta eh take yaji wani farin ciki yana shigar sa yamike tsaye yayi wani tsalle yana rawa ita kuwa sai dariyarsa take
Yariko hanunta yatada ita muyi rawa ko a'a maiyasa saboda ban'iyaba da gaske eh to'kuwa zankoya maki zamu fara ayau a'a maiyasa tayi shiru tana kallansa shima kallanta yake cike da shauki
Sai wani santa yakeji yana yimasa yawo ajiki ta'ko ina sassan jikinsa yalumshe ido kadan tare dajan numfashi bajima wa yabude yanamai sauke ajiyar zuciya ita kuwa kallonsa kawai take yayinda taji duk yabirgeta
Yajanyota tafada jikinsa yarungumeta tare da sunbatarta Ambee nafada maki kommai agame dani amma bakice dani komaiba balantana kuma ke'ki'iya fadamin wani abu agame dake maiyasa shiru batayi magana ba
Ambee anya kina sona kuwa ki'amsamin kafin tace dashi wani abu wayarta tadau ruri takai kallonta ga'inda jakarta take sannu ahankali take cire hannayesa daga jikinta tafita daga jikinsa tanufi inda jakarta yayi sauri riko hanunta tatsaya tsak batare da tajuya takallesaba
Yafito tagabanta maiyasa zaki tafi kayi hakuri yayana ne yake kiran layina inasan naji maiyake san yafadamin ne ok ta'tafi tadauki wayar daga ciki yake kanwata nazo yanzu domin nakarasa abinda nake eh to ya Ammar din yana lafiya ok sainazo sunyi sallama
Fadamin maiya fada maki domin kuwa naji ya'anbaci sunana tafada masa haba Ambee maiyasa zakice yazo yanzu ni'sam banasan rabuwa dake kayi hakuri wani lokaci zamu koma haduwa
Yamata wani kallo Ambee wani lokaci fa kikace eh gaskiya bazaiyuba domin kuwa ni inasan kullum nahadu dake ok zanduba yuwuwar hakan amma kafinnan sunana Ambeeshar ba Ambee ba kakiyaye ok
Bajima wa sosai saiga Ahmad tare yake da Sadiq tayi sallama dashi sun'tafi suna cikin tafiya Ahmad yashiga tambayarta kanwata yadai murmushi kawai take batare da ta'iya furta masa komaiba Ambeeshar kenan ina yimaku fatan alkhairi nagode yayana yaya Sadiq ina Aunty Salma tana lafiya yaushene bikin
Garka jira yaya Ahmad domin kuwa shi sam ba'Aure yanzu agabansa wasa yake ai'kuwa naga alama to kawai kifito mu'rakarkashi biki to shikenan zanyi ko'kari yauwa yaya Sadiq Allah yakaimu lokacin da alkhairi Amin
Wasa-wasa soyayya tsakanin Ammar da Ambeeshar saidada gaba take akullum ako yaushe suna tare da juna zuwa wannan lokacin sunshaku da juna sosai
Wata rana suna tare kamar kullum takai kallonta ga agogon da yake hanunta taga lokaci yatafi tamaida kallonsa garesa Ammar zantafi gar Aliyu yagaji da jirana maiyasa bazaki yarda ni nakaikiba ko har zuwa yanzu baki bani yardarkiba tayi murmushi Ammar kenan ainajima da baka yardarta na'kumasan kayarda da hakan
To idan kuwa hakane yakamata kitabbatarmin da hakan tahanyar yarda na'kaiki gida tayi shiru kadan tana nazari yatsinketa da cewar dan Allah kinji ha!!! Tanisa toshikenan nayarda gud Ambeeshar yafada tare da sunbatarta tayi murmushi yaciro wayarta takira layin Aliyu yadaga hellow Ambeeshar waikina ina am dan Allah kayi hakuri katafi kawai nizanzo tare da Ammar
Maiyasa bakomai amma Ambeeshar a'a Aliyu garka fadi komai toshikenan sunyi sallama takai kallonta ga Ammar to mutafi ok yabude mata mota tashiga yazaga shima yashiga suntafi yakaita har gida sannan kuma yabukaci yashiga ciki saidai sam bata bashi wannan damar ba bai nuna damuwarsa ba sunyi sallama yatafi tashigo ciki Al-ameen yashiga tambayarta daga ina take dajimawa Aliyu yadawo natambiyesa yafadamin kinfita tare da kawayenki ina kika tafi shiru batayi magana ba ki'amsamin daga ina kike suna haka saiga
Ahmad yashigo wanda yariga dayaji komai yana shigowa yace Kanwata har kindawo da sauri haka tinba'akarasaba gaskiya baki kyautaba domin kuwa bai kamata kidawo yanzu ba kallonsa kawai take tana murmushi yayana kenan aiganin banfada agidaba wannan nadawo yanzu eh kumafa hakane kinyi tinani hakan yayikyau Al-ameen yace kasan daga inda takene eh aini nakaita hidimar kawarta ake na birthday ok am kinga Ambeeshar daga yau garki koma tafiya wani guri batare da kinfada ba insha Allah
Tanufi dakinta tana shiga takira layin Ahmad tana yimasa godiya nagode yayana bakomai kanwata yanzu ki'kira layin Ammar kiji koya'isa gida to shikenan sun'aje wayar tanufi bandaki tawatsa ruwa tafito tashirya washe gari ranar takasance ba school da yamma suna falo suna fira sukaji anturo kofa anshigo sunkai kallonsu ga kofar dan ganin waye
Cikin rawar murya ta'anbaci sunansa Ammar yayi murmushi yakaso ciki su Umma sai kallonsa suke cike da mamakinsa Ambeeshar taji wani gumi yana saukar mata tare da kai kallonta ga Ahmad yagirgiza mata ka a'a kanwata garki damu kinji ok yauwa bara kiga yakaraso gurinsu Abba yasunkuya tare da shafa kafafun sa haka Umma yashafi kafafunta yadago tare da hade hannayesa yayi masu gaisuwa irinta indiyawa ya'kuma gabatar da kansa garesu cike da mamaki sunkai kallonsu ga Ambeeshar da sauri tasunkuyar da kanta kasa Dad inasan Ambeeshar sosai hakama inasan kabani Auranta dan Allah domin kuwa idan kahana ni Auran Ambeeshar zan'iya mutuwa domin kuwa soyayyarta tazamemin abokiyar rayuwa sam bazan'iya rabuwa da soyayyarta ba dan Allah kataimaken kabani Auranta yafadi tare da kama kafafun sa yashiga rarrashinsa tamkar da zaimasa kuka
Jin Abba baiyi magana ba yasa yakoma gun Umma itama yana aikin rarrashinta lokaci daya sukaji tausayinsa duk yashigesu Abba yadago sa yazaunar da ita kaga garka damu zanbaka Auran Ambeeshar amma da sharadin idan ita tanasan ka nagode Dad
Abba yakai kallonsa ga Ambeeshar tare da fadar sunanta Ambeeshar kifadamin gaskiya garki boyemin komai kinasan sa kifadamin gaskiya kinasan sa tadaga masa ka alamar eh yadawo da kallonsa ga
Ammar to kaga Ammar yanzu sam bakada wata damuwa Ambeeshar tazama taka inamaka fatan alkhairi nagode Dad yafada yana dariya ita kuwa murmushi take Abba yanuna masa Al-ameen da Ahmad da Aliyu tare da gabatar dasu agaresa yagaiahesu cike da girmamawa
Farin ciki gurin Ambeeshar abin ba'a magana to balantana kuma Ammar yajima anan inda daga bisani kuma yatafi zuciyar fara kal yayinda farin ciki yayi yawa atare dashi haka Ambeeshar zamu'iya cewa duk kanninsu suna tare da farin ciki maigirman gaske
Wasa-wasa Ammar yazama dan gida akoyaushe yakantafi domin haduwa da Ambeeshar yayinda shakuwa tadada shiga atsakaninsu inda suka kasance tamkar tagwayen juna ko yaushe suna tare da junansu
By Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
2⃣3⃣ to 2⃣4⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Ambeeshar zuwa yanzu yakamata ace nahadaki da iyayena domin kuwa akullum cikin zancanki suke
Ammar kanasan kafadamin cewa Mum tasauya ra'ayinta tayarda da ka'Auran Ambeeshar kisani yardana itace yarda ra'ayina shine abinda nafi yarda dashi fiye da komai
Inasanki ba'kuma abinda zaicanja ni ina fatan nakasance dake na'duk iya rayuwata ke ruhina ce soyayyarki kuma numfashi nace bazan'rayuba idan har baki kece ginshikina jagoran rayuwata
Soyayyarki kawai nasani kuma itace abar danafi yarda da ita fiye da komai tayi murmushi tare da mikewa tsaye Ammar shin wane irin Sone kake yimin har haka taya Auranmu zaikasance bada yardar Mum ba gaskiya abin da kamar wuya wai sata alahira gaskiya inajin tsoro mutuka zanfisan muyi Aure da amincewar Mum domin kuwa zamifi farin ciki
Tana cikin magana bata sararba saiji tayi anyi hugging dinta tare da sunbatarta yajuyota sunfuskanci juna wani irin kallo yake yimata maitare da So yashiga sunbatarta yana ko'karin kaibakinsa ga nata tayi saurin dakatar dashi tahanyar fita jikinsa tare da furta a'a
A'a Ammar kadena dan Allah magana take tana tafiya da baya shi'kuwa sai wani kallo yake yimata tare dajin mamakinta sai wani irin abu yakeji aransa yawani yanyo hannunta haba
Ambeeshar wai miye haka maiyasa duk lokacin da nake ko'karin baiyana soyayyata agareki kike hanani maiyasa kikeyimin haka shin kina sona kuwa anya zan'iya yarda da soyayyarki kuwa maiyasa kike guduna shin'kina da wani saurayin me bayanni fadamin naji
Ambeeshar kiyi magana mana maiyasa kike guduna dan Allah kisanar dani shiru batayi magana ba yasa hannu yadago fuskarta Ambeeshar maiyasa kike hanani kaiwa gareki shinbaki yarda dani bane ko miye
Ko kina tinanin zanbarki ko bazan Aurekiba fadamin Ambeeshar dan Allah kiyimin magana kinji magana yake kamar zaiyi kuka cikin wata sarkakiyar murya take magana a'a
Ammar ni'sam bana tinanin duk abinda kafada domin kuwa wallahi bantaba tinanin cewar zaka yaudareni ba akullum cikin kyauta'tama niya nake
Ammar wallahi inasanka yakamata kasani ka'kuma san cewar nanba India bane nan Nigeria ce kana ajahar Adamawa agarin Yola kuma kana tare da Fulani
Dan haka yanakyau kaima kazama kamar yanda muke kayi kwaikwayonmu wannan shine yagirgiza ka bazan'iyaba Ambeeshar wallahi sam bazan'iya irin wannan rayuwar takuma domin kuwa da takura acikinta wannan wace irin al'adace daku haka
Wai ace mutun sam bazaibaiyana soyayyarsa ga abar kaunarsaba wato budurwarsa wai sai anyi Aure gaskiya wannan sam baiyi ba domin kuwa yana dakyau musamu farin ciki kafin Aure amma nafahimci cewar ke'sam baki yarda da hakanba maiyasa
Ammar ha!!! Ta'kumayi shiru fadamin miye tagirgiza ka bakomai am Ambeeshar dan Allah zan'iya naiman wata alfarma agareki inajinka dan Allah kidena hanani kaiwa gareki dan Allah kinji kitaimaken please tana sansa da yawa wannan yasa ta'amincewa da bukatarsa yayi matukar farin ciki sosai abisa hakan
To fadamin yaushe zaki tafi gida kigaisa dasu Dad tayi shiru fadamin mana tayi murmushi jibi a'a mubarsa gobe kinji ok yauwa Ambeeshar na yafada yana murmushi itama murmushin take bayan wani lokaci suka tafi ganin yamma tayi sosai yasauketa agida yatafi
Da dare tasami Ahmad adakinsa yakalleta yana murmushi kanwata ya'akaine am yayana wallahi da akwai matsala subhanalillah maiyafaru ne yayana wallahi Aure nakeso kuma nankusa wani irin kallo yake mata maicike da mamakinta yayinda yagagara cewa da ita komai ha!!!
Taja numfashi dama nasani yayinda nasanar dakai abinda yake azuciyata balallai ka'iya yarda da bukata'taba zakace nayi yarinya da nayi Aure
Zaka fadamin cewa shekaruna iya sha'takwas ne ina aji biyu amakaranta dan haka bazantaba samin abinda nake kwadayiba amma yayinda na'aikata wani babban zunubi kuma zakurufeni da fada
Yayana shin'mace irita bazata iya rayuwar Aure bane ko miye ko kuna tinanin idan akayimin Aure ayanzu bazan'aihuba ha!!! Tanisa tare dajan numfashi
Yayana kasan dalilin da yasa nazoma da wannan zancan shiru baiyi magana ba yayana Ammar wata irin soyayya yake yimin akullum akoyaushe da wani saban salo yake zomin
Yayana zuwa yanzu ni'kaina wallahi bansan wane irin So nake yiwa Ammar ba domin kuwa takai takawo sam bazan'iya hana Ammar yakai ga jikina ba yakanyimin abubuwa da dama wadanda bazan'iya sanar dakai ba
Yayana wallahi inajin tsoro sosai wannan dalilin yasa bakasan nayi Aure ayanzu wannan yasa nazo gareka sai kasan yanda zakayi domin ka'isar da sakona zuwa ga Abba
Ni zantafi na kwanta saida safe ta'tashi zata tafi yayi saurin riko hanunta tajuyo takallesa yayi murmushi zauna mana takoma tazauna am garki damu kanwata domin kuwa nafahimceki dan haka yazamemin dole na'naima maki mafuta
Tayi murmushi sosai maidauke da yar dariya nagode yayana bakomai kanwata to bara natafi dare yayi ok Allah yabamu al'khairi Amin yayana ta'tashi tafice abinta yabita da kallo yana murmushi
Zaune suke afalo sukaji anturo kofa anshigo dukansu sunkai kallonsu ga kofar dan ganin waye Ammar ne tare da Ambeeshar lokaci daya Mum tadaure fuska tahadiye rai tamkar wadda aka aikowa da sakon mutuwa Dad kuwa sai murmushi yake sunkaraso ciki yanufi gin Dad yasunkuya yashafi kafafun sa yakuma shafi na Mum yajuyo da kallonsa ga
Ambeeshar zomana ta'tafi jikinta asanyaye yace sunkuya kiyi kamar yanda nayi kinaimi albarka agurin iyayena tayi murmushi ok tasunkuya tashafi kafafun Abba shi'kuma yashafi kanta tare da furta Allah yaimaki albarka takoma gun Mum takai hanunta zata shafi kafafunta da sauri tajanye kafafunta tare da mikewa tsaye
Tawani firgota tamike tsaye kebara kiji wallahi duk wannan sunkuye-sunkuyen naki bazaisa nabarki ki'Auri yarona ba wato kinga yaro kyakkyawa dan India dan masu kudi ko to wallahi karyarki yarona yafi karfinki bazaki taba samunsa ba domin kuwa yahuce da saninki
Kuma bara kiji najima da zabawa yarona matar da zai'Aura yar Uwarsa yar India bakeba dan haka saiki kama gabanki kisan inda dare yayi maki jeki kuma kisani daga yau garki koma kuskuran rabarmin yaro tafi bama bukatarki a'a Mum
Ya'isa haka kisani wannan bakwai kawai budurwata bace ita rayuwata ce idan kika rabani da ita to kisani nima bazan'rayuba dan haka kidena hantararta
Ammar tadakatar dashi cikin tsawa tadawo da kallonta ga Ambeeshar ke kigaggauta fita kibar gidan'nan kuma garna kara ganinki tare da yarona tashi kitafi tadaka mata tsawa tajuya firgice jikinta sai bari yake yana karkarwa da sauri Ammar yasha gabanta a'a Ambeeshar dan Allah garki tafi Dad dan Allah kace garta'tafi
Ambeeshar kidakata mana kisaurari abinda zanfada dan Allah cikin firgici da tsoro take magana kagafarceni Dad amma wallahi sam bazan'iya kara mintuna biyu agidannan ba tajuya tayi tafiyarta
Ammar yabita abaya Mum tadakatar dashi garka yarda kafuta kadawo yajuyo yawani dafe ka idanuwansa suncanja launi sunyi jajir sai wata kwalla yake zubarwa maitsananin zafi da kuna
Mum kinyi nasarar raba tsakanina da Ambeeshar to amma kisani wallahi bazaki iya hanani hukunta kaina ba kamar yanda bazaki dakatar dani ga abinda nayi niyar aiwatarwa ba
Yajuya yahaura sama yakai hawa na karshe kasan cewar gidan hawa hudu ne sunbisa suna kiransa amma yasharesu yana isa bai tsaya wata-wata ba yayi tsalle yadira yafada kasa ta'anbaci sunansa da karfi Ammar
Tawani tashi afirgice yayinda take anbatar sunan Ammar Dad yashiga tambayarta lafiya Ammar ta'tashi da sauri tanufi dakin Ammar Dad yabiyota abaya sunsamesa yanata sharar barci abinsa takarasa inda yake yaxauna daga gefensa tana kallonsa tadan shafi fuskarsa tare da sunbatarsa inasanka yarona
Dad kuwa sai kallonta kawai yake bajima wa sosai suka fito suka nufi dakinsu Dad yashiga tambayarta maiyake faruwa tasanar dashi abinda tagani acikin mafarkinta am
Abey dan Allah mubar kasarnan wallahi bana santa dan Allah kamaidamu India domin kuwa sam bazan'iya cigaba da rayuwa ananba bakuma zanbar yarona yayi Aure ananba dan haka yazama dole mukoma India
Saboda afara shirin Auran Ammar da Amisha kinga Nandani banasan irin haka bara kiji ni'duk abinda Ammar yakaso toshi zanyi koda kuwa banyi dai-dai da ra'ayinkiba dan haka saiki kiyaye yajuya yayi kwanciyarsa tabisa da kallo cike da takaicinsa yayi yawa atare da ita
Washe gari bayan yakarasa shirinsa yafito tagaisa da iyayensa Mum tace Ammar yafa kamata mushirya komawa gida wane gidan India mana ho!!! Mum gaskiya ahalin yanzu ni'sam ba zantafi India ba
Akanme saboda ina bukatar Ambeeshar zanci gaba da zama anan harzuwa lokacin da zansameta Ammar to Amisha fa Mum maiyasa ki'kadamu da Amisha ne nafa fada maki cewar ba soyayya atsakanina da Amisha to maiyasa bazakibar zancan ba saboda ni inasan ka'Auri Amisha
Mum Aure fa kika ce eh haba Mum to tayama zan'Auri Amisha bayan bana tare da soyayyarta Mum ni Ambeeshar nakeso kuma ita zan'Aura kisaka wannan aranki tayanda zaki fitar da zancan Amisha azuciyarki
Am Dad yau zankawo Ambeeshar tagaisheka domin kuwa nariga dana gama fahimtar cewa Mum sam bata da ra'ayi da ita
Mum dan Allah garkiyi yunkurin cutar da Ambeeshar yayinda tazo gaisheku hakama sam banasan kiyi wani abinda zaisa Ambeeshar tafahimci cewar bakya da ra'ayi da ita domin kuwa sam banasan ganin bacin ranta ko damuwarta
Kisani ita bawai kawai budurwata bace ita rayuwata ce inasanta sosai dan haka saiki kiyaye dan Allah My swt Mum ok my Son yauwa Mum yafada yana dariya bayan sunyi break fast yafuta abinsa
Tana cikin shirinta wayarta tadau kara tayi wani kyakkyawan murmushi kasan cewar tasan maikiranta takai hanunta tadauko tare da dagawa hellow Ammar da fatan kana qlau eh kefa nima haka maikike yine ina shirine zantafi makaranta to inasan muhadu yaushe yanzu kayi hakuri zuwa anjima mana
Gaskiya bazan'iyaba kiyi hakuri muhadu dan Allah to shikenan amma a school zamu hadu ba damuwa ok sunyi sallama takarasa shirinta tafito yasamu ita kawai ake jira suyi break bayan tagaisa dasu Abba takai kallonta ga Aliyu tace am
Aliyu mutafi ko yanzu Anisa tayimin waya wai za'ayi test cike da mamaki yace test kuma eh to amma maiyasa Samar baisanar daniba to watakil mantawa yayi ok to'mutafi ok Umma sai mundawo haka zaku tafi batare da kinyi break ba bakomai
Umma zamuyi acan to shikenan Allah yakiyaye adawo lafiya Allah yasa Amin suntafi suna cikin tafiya tayi murmushi kagafarceni Aliyu abinda nafada sam ba gaskiya bane kamar yafa wallahi bawata test da za'ayi kawai zanin hadu da Ammar ne wannan yasani fadama haka wani kallo yake mata maikama da harara tayi murmushi maitare da yar dariya eh nadaiji
Allah yabaka hakiri shiru baiyi magana ba har suka isa makaranta sunsami Ammar agurin parking yana garinsu yafuto bayan sungaisa Aliyu yanufi class Ambeeshar nazo nadaukeki mutafi gidanmu Ammar yanzu eh mana to miye dan Allah kinji yashiga rarrashinta har yasamu tayarda da zata bisa yauwa Ambee yabude mata mota tashiga shima yashiga suntafi sun'isa gidan ransa fari kal sun'shiga daga ciki sunsami Dad zaifita ganinsu yasashi komawa yazauna tagaishesu Ammar yasa tashafi kafafunsu
Dad sai wani dauki yake yasanar da ita komai agame dasu haka itama tasanar dasu asalin ta da komanta Dad yayi farin ciki sosai haka
Mum bata nuna mata cewar bara da ra'ayi da itaba tajima anan har saida sukaci abinci sannan suka tafi taji dadi sosai da irin yanda suka tarbeta hakan yasata farin ciki sosai
Bayan sunfito yatafi da ita yayi mata siyayya maiyawan gaske sannan yamaida ita makaranta zuwanta yayi dai-dai da tashinsu Aliyu yashiga tambayarta ina ta'tafi tasanar dashi komai to amma kina ganin hakan dai-daine kuwa kibar karatunki jibi wani
. Aliyu wanifa kace Ammar dinne yayikyau nagode ke kinga Allah yahuci zuciyarki mutafi sun'shiga mota suntafi
Bayan kwana biyu Dad yadauko Mum suka tafi gidansu Ambeeshar domin sukai kayan Aure tare da tsaida magana sabida yanda Ammar ya'addabesa da zancan Ambeeshar Mum cikin bataso-bataso haka tahakura dan dole
Suntafi sunyi magana saidai Abba yace Ambeeshar karatun zatayi jin hakan yasa Ahmed yayi magana bai fito yabaiyana cewar Ambeeshar nada bukatar Aure ba saidai yasa hakima acikin maganar sa wanda
Abba yace saiyayi tinani akai sun'kuma ajiye akan hakan sunyi sallama suntafi
.......
By. Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
2⃣5⃣ to 2⃣6⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Da fari Abba baiyarda da yayiwa Ambeeshar Aure ba saidaga bisani da yafahimci cewar tana da ra'ayi da tayi Aure
Wannan yasa yayarda da bukatarta ya'amince akan cewar zaiyi mata Aure da Ammar yace za'ahade Auranta da Ahmad tayi farin ciki sosai haka Ammar
Bayan kwana biyu su Abba suka tafi gidansu Aisha domin haduwa da iyayenta sunyi magana tare da bada kudin Aure bada jimawaba aka saka masu ranar Aure
Asma'u taji wani irin kasan cewar alokacin tana da juna biyu tsohu sai fatan take ta'aihu kafin zuwan bikinsu Ahmad
Ambeeshar tasanar dasu Farida zancan Auranta dukansu sun'mutu da mamakin abinda tafada to balantana kuma su Salman suncika da mamakinta mutuka
Ambeeshar Aurefa ki'kace eh zanyi Aure kana da matsala akan haka ne haba Ambeeshar kedin guda nawace yaushe kika fara karatu da har zaki bijiro da zancan Aure yaka matafa kiyi tinani
Kisani rayuwa yanzu tasauya karatu yana da matukar anfani agareki Ambeeshar dan Allah ki'ajiye zancan Auran nan ki'kula da kanki kikama karatunki domin kuwa ayanzu shiyafi dacewa dake fiye da komai
Salim kenan wannan tinaninkane ba nawaba kasani sam ba'abinda zaicanjani ko yasauya ra'ayi na Aure kuma bazan fasaba kawai kuyimin fatan alkhairi nagode ta'tashi tayi tafiyarta sunbita da kallo cike dajin mamakinta
Mum tasanar da danginta dake India sunshiga mamakinta to tayama za'ace Ammar yasami matar Aure awannan garin gaskiya abin da kamar wuya wai kare da gudun laiya to yazanyi
Ammar yakafe akan cewar shi'wannan yarinyar yakeso ya'Aura kuma Abey yagoyi da bayansa sunhademin kai wannan yasa dole nahakura
To amma Nandani yazakuyi da Amisha domin kuwa akullum cikin mafarkin samun Ammar take wanda kuma wannan dalilinne yasa har yanzu taki tafidda mijin Aure
Yafa kamata kiduba wannan lamarin toni kuwa yazanayi sam banida wata mafuta ko dabara amma zanyi ko'karin fahimtar da Ammar naga kozaifahimta ok saikiyi ko'karin hakan sunyima suna magana daga bisani sukayi sallama
Mum tayi duk iya ko'karinta amma sam yanuna mata cewar shi Ambeeshar kawai dole tahakura tabarsa akaci gaba da hidima
Asma'u tayi nasarar ai'huwa kafin zuwan ranar biki ta'aifi yaronta namuji kyakkyawa wanda akasa wa suna Asharaf
Wasa-wasa biki sai kawo kaiyake hidima sai kara gaba take biki uku suka shirya zasuyi da fari zasuyi Kamu tare da budan kai zasuyi Dinner sai kuma India night
Kwance yake yakai hannunsa yadauki wayansa yashiga kiran layin Amisha bata dagaba sai akaro na biyar sannan tadaga shidinma batare da rayi magana ba yayi murmushi maitare da yar dariya haba
Amisha babbar kawa maiyake faruwa ne sanar dani mana ha!!! Tanisa tare dajan numfashi haba Ammar maiyasa zakayimin haka garka fadamin cewar wai bakasan cewar inatare da soyayyarka ba tabbas kasan cewar inasanka amma ka'aikatamin haka maiyasa kafadamin
Ammar maiyasa itadin damai tafini dazaka dauketa kabarni Ammar shin'ka'kuwa sam irin sanda nakeyima kuwa ko bakasan cewar zan'iya mutuwa ba yayinda na tabbatar da cewar narasaka
Amnat dan Allah kataimaken kadawo gareki dan Allah kiyi hakuri Amisha amma kisani wallahi sam bazan'iya hakura da rashin Ambeeshar ba wannan dalilin ne yasa nake shirin Auranta dan Allah kigafarceni
Dafatan zakishigo biki bayan nakarasa tare zamu koma domin kuwa acan zanzauna da Ambeeshar kayi hakuri domin kuwa sam banida wannan karfin zuciyar da zan'iya halartar Auranka kawai kayi hakuri takashe wayarta
Ha!!! Yanisa tare fa numfasawa yana maifadar sunanta Amisha ya'koma kiran layinta dakyar yasamu ta'iya dagawa yashiga rarrashinta tare da lallanata har saida yasamu ta'amsa masa dacewar zata shigo sannan sukayi sallama
Dama anfada idan aski yakawo gaban goshi yafi zafi dangin Mum sunshigo duk da cewar sam basa farin ciki da Auran domin kuwa sunfi bukatar ya'Auri Amisha ganin irin yanda take mutuwar sansa da ita akashigo
Ammar kuwa sai wani daukin ganinta yake sai wani nan-nan yake da ita tamkar zaisata ciki ya'aife kallonsa kawai take yayinda tagagara furta masa komai Amisha lafiyarki kuwa tagirgiza masa ka tare da furta bakomai to kisaki jikinki mana ok
Ranar Alhamis ita ce ranar da suka fara bikinsu aranar sukayi Kamu da budan kai washe garin ranar sukayi Dinner Aranar Asabar ne da misalin karfe 12:30pm akayi addu'ar dauin Auran Ahmad da Aisha Ammar da Ambeeshar agida sunci gaba da bikinsu misalin karfe 0:700pm aka kawo Amarya Aisha adakinta anan gidansu Abba akaui masu part din'da zasu zauna ita kuwa Ambeeshar daga gurin India night za'akaita gidanta misalin karfe 09:00pm suka nufi gurin India night
Duk kanninsu shigar India sukayi sunyikyau sosai biki yayikyau sosai bayan wani lokaci suka tafi gurin yanka cate sunyanka cate sunjuya zasu koma mazauninsu
Lokaci daya Ammar yaji kansa yasara da karfi da sauri yadafe kansa tare da furta wash dukansu sunkai kallonsu garesa tare da tambayarsa lafiya saidai kuma sam yagagara iya furta komai sunci gaba da tafiya basu karasa kaiwaba yazame jiki yafadi da sauri
Ambeeshar tasunkuya tana anbatar sunansa Ammar amma ko wani motsi baiyi ba kowa yayi takansa ganin irin yanayin sa yasa akadaukesa akanufi asibiti dashi kafin anshiga dashi ciki yafarka yayinda yake fadar sunan
Ambeeshar yakirata da ka da sauri ta'isa gunda yake yarike hannunta cikin wata yar murya yake magana Ambee inasanki amma sainakeji kamar bazan'rayu dakeba irin ciyon da nakeji ajikina wallahi abin bazaifaduba amma kisani zanyi farin ciki idan har. Namutu da soyayyarki kema kikasance cikin farin ciki
Tashiga girgiza masa ka a'a Ammar dan Allah kadena fadar haka zaka sami lafiya nida kai zamu rayu atare insha Allah ba'abinda zaifaru dakai kayarda dani inasanki Ambee wallahi inasanki sosai nima ina kaunarka Ammar
Hakama ina fatan narayu dakai rayuwa tahar abasa suna haka Doctor sukajasa suka shiga dashi ciki Ambeeshar tajuya tanufi gun Ahmad tafada jikinsa tana wani irin kuka maitada hankalin natare da ita yashiga rarrashinta tare da bata magana kinyi hakuri
Kanwata da yardar Allah Ammar zaisami lafiya kiyarda dani kinji Asma'u takira layin Umma tasanar da ita abinda yake faruwa bajima wa saigasu Abba dasu Mum guri yakoma ciki
Bayan wani lokaci Doctor yafito tare da sanar dasu labari nafi muni shine mutuwar Ammar jin'wannan kalmar tagirgiza kowa da yake gurin Ambeeshar kuwa take tayanke jiki tafadi Al-ameen yakira doctor sunshiga da ita ciki Mum da Dad sunshiga wani irin yanayi wanda sam bazan'iya fadansaba saidai kumisalta
Bayan kwana biyu hat zuwa wannan lokacin Ambeeshar bata farfadoba su Abba sunshiga tashin hankali maigirman gaske barinma Ahmad wanda yadawo tamkar wani karamin mahaukaci duk yakidime yazauce
Zaune yake ba kuka yakeba amma idanuwansa kwalla suke zubarwa Sadiq yasamesa ahaka yanisa tare da girgiza ka yada fasa tare da fadar sunansa Ahmad kallonsa kawai yayi batare daya'amsaba Ahmad dan Allah kayi hakuri garwani abu yazo yafaru dakai insha Allah Ambeeshar zatafarka za'kuma tasami lafiya kayarda dani amma dan Allah kanaimawa kanka mafuta da sassauci
Ha!!! Yanisa tare da sauke ajiyar zuciya Sadiq kanwata bansan maizaifaru da itaba garka damu insha Allah ba'abinda zaifaru da ita kayarda dani suna haka sukaga Aliyu yafito daga dakin da Ambeeshar take wani afirgice yawuce tagabansu tamkar baigansuba
Wannan yatabbatar masu da cewar ba lafiya ba suntashi da sauri sunshiga ciki sunsami Ambeeshar azaune Umma da Abba sai magana suke mata amma sam ko kallonsu batayi
Ahmad yakarasa gunda suke yayinda yake fadar sunanta kanwata kinfarka sannu da fatan kina samun sauki ko kallonsa batayi ba balantana ta'iya amsa masa Yamaida kallonsa gasu Umma
Yace Abba wai maiyake faruwa ne maiyasa bata magana to Ahmad taya zamu sani mumadai kamarkai bamusan komaiba subhanalillah suna haka Doctor yashigo
Yabukaci sufita zaidubata sun'amsa da to sunfita
Bayan wani gajeran lokaci yafito yace da fari zanfara da banhakuri kugafarceni abisajin abinda zanfada maku lokaci daya sukaji jikinsu tasoma mutuwa
Abba yace munajinka Doctor kasanar damu halinda Ambeeshar take ciki saikunjure dajin abinda zanfada yarinyarku tarasa tinaninta hakama tamanta komai nagame da rayuwarta amma da akwai mafuta kwaya daya mafutar dayace
Yanadakyau abinda yayi sanadin faduwarta ya'koma faruwa da ita to watakil idan Allah yasa anyi dace to tinaninta zaidawo zan'iya cewa wannan itace kawai mafutarku yajuya yayi tafiyarsa su
Abba sunshiga tashin hankali maigirman gaske barinma Ahmad yawani dora hanu aka yasaki ihu tare da fashewa da kuka yana fadin kanwata Sadiq kanwata kafadamin cewar ba'abinda zaifaru da ita Sadiq Ammar yamutu to taya kuma tinanin Ambeeshar zaidawo innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un su Abba sunshiga rarrashinsa
Bayan kwana biyu suka koma gida su Dad kuma suka tattara suka koma India cike da kuncin rashin Ammar
Ha!!! Yanisa tare dajan numfashi yanamai sauke ajiyar zuciya yayinda idanuwansa suke zubar da wasu irin zafafan hawaye masu tsananin zafi da kuna
Ha!!! Ammar tokaji labarin kanwata ko'kanasan kafadamin cewar har yanzu baka fahimci wacece Ambeeshar ba ha!!! Yanisa tare dajan numfashi yana Maisauke ajiyar zuciya tabbas labarinka yana dauke da rudani maigirman gaske
Tabbas rayuwar kanwar ka tana cike da kunci da kuma tarin duhu atare da ita to saidai kumani bazan'iya taimakonta da komaiba kasan cewar niba Ammar dinta bane niba
Ammar dinda kake naima bane nida kake gani anan banda kowa bankumasan kowa ba nikadai nake rayuwata kaga kuwa banida abinda zai'iya taimakonka da komaiba saidai kawai nabaka hakuri
A'a Ammar dan Allah garkayimin haka duk da cewar ba kaibane Ammar dinda nake naimaba amma zaka'iya taimako na ni'kuwa taya zan'iya taimakonka dame zantaimakeka zansanar dakai amma kafinnan zanfisan kayarda dani sannan kuma ka'amsamin da cewar zaka taimaken dan Allah garka damu nizan'taimakeka domin ganin ka cimma burinka nagode yagirgiza masa ka tare da furta a'a bakomai
By. Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
2⃣7⃣ to 2⃣8⃣
Na Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyat ZABINA❤
Ahmed kafadamin dame zan'iya taimakonka domin naji
Ha!!! Tanisa tare dajan numfashi Ammar da fari zanso nasan kai'waye tukunnan am ainafadama cewar ni kaina bansan komai komai agame da rayuwata ba
Niba kowa bane ban'kumasan kowa ba nikadai nake rayuwata bana tare da kowa
Cike da mamakinjin abinda tafada Sadiq yace Ammar idan kuwa hakane to tabbas kaine Ammar din'mu
Haba yaya Sadiq tayama hakan zata kasance dani kai a'duk iya rayuwarka kataba ganin mutumen da yamutu kuma yatashi sam wannan bazaitaba kasan cewa ba
Nidai kawai kusanar dani yanda zanyaimakeku domin mutaimaki rayuwar Ambeeshar bansan taba amma naji inabukatar nataimaketa koda kuwa nizsnsara tawa rayuwar
Kasan cewar rayuwarta tafi tawa muhim'manci ina fatan yarayu cikin aminci da farin ciki ina godiya sosai abisa wannan jajircewar taka ga lafiyar kanwata
Garka damu yaya Ahmad wallahi nizan'iya komai dan ganin Ambeeshar tasami lafiya nidai abinda nakeso shine kasanar dani tayanda zan'iya taimakonka
Am Ammar domin taimako kanwata to yazama dole ka'kasance kamar Ammar dole zaka koma Ammar ka'kuma haimatsayinsa to amma taya zankasance amatsayin Ammar acikin labarinka kafadamin cewar shi wancan
Ammar din asalinsa dan India ne indiyanci yakeyi ni'kuma bansan komaiba game da India to taya zan'zsmashi abin da kamar wuya gaskiya bazsn'iya ba garka damu
Ammar domin kuwa abin ba wahala ne dashi ba abinda zaifaru shine zani daukeka zuwa India nadan wani lokaci wanda hakan zaisa kadawo tamkar Ammar tayanda ko'kai bazaka fahimci cewar ba wancan Ammar dinbane
Kana ganin hakan zaiyuwu sosaima kuwa amincewarka kawai nake naima to shikenan na'amince Allah yabamu sa'a Amin yarabbi
Washe gari yatafi yayi masu biza wadda tadaukesu natsayin kwanaki goma sannan suka tafi saidai kafin sutafi yakoma gida yasanar dasu Abba cewar tafiya takamasa saidai baisanar dasu asalin sanadin tafiyarsa ba
Sunyi nasarar isa kasar India cikin koshin lafiya suna isa Ahmad yafara abinda yakawo sa yakai Ammar makarantar koyon rawa da indiyanci kasan cewar wancan Ammar din ganin rawane
Jama'a da dama sunyi tinanin Ammar ne saida Ahmad yasanar dasu cewar bashibane
Sunjima anan suna abu daya shine ganin anwayar da Ammar yadawo tamkar wancan Ammar din cikin kan'kanan lokaci Ammar yayi saurin sauya wa komansa yacanja yadawo tamkar wancan Ammar din
Hakama indiyanci yashige sa ya'kuma zauna aharshensa tamkar damacan yaransane Ahmad yaji dadin hakan sosai domin kuwa yana maikyauta'ta zaton karshen wahalar Ambeeshar tazo zata sami lafiya da yardar Allah wani yammaci sunfita gurin siyayya kasan cewar suna hanyar komawa gida kwana biyu yarage masu
Sunshiga wani kanti wani yazo yana masa magana Ammar kaine kuwa domin kuwa dajimawa akafada mana cewar kamutu
Ammar dai kallonsa kawai yake yayinda yagagara cewa dashi komai bayan sunkarasa siyayyar suntafi gurin biyan kudi mutumen yakallesa tare da girgiza ka haba dai
Ammar nanfa kantinka ne ya'kuma zakabiya kudi aibazaiyuba sai wannan lokacin yayi magana cikin rawar murya yace kantinafa kace eh kana mamakine amma zaka'iya dubawa awaje
Domin samun tabbacin abinda nafadama Ammar wai maiyafaru da kaine haka domin kuwa nafahimci cewar sam baka acikin haiyacinka saboda sam kagagara iya tina komai tabbas wani abu yafaru dakai amma kahadu da iyayenka kuwa
Shiru baiyi magana ba jinyayi shiru yasa Ahmad yinmagana am kaga malan kayi hakuri wannan da kake gani ba Ammar dinda kake tinani bane sai anjima sunfita kafin sutafi
Ammar yatada kansa sama dan ganin abinda akarubuta cike da mamaki yaga sunansa Ammar Abey batik dan super market
Yayi shiru yana nazari amma sam yagagara tina komai mst yaja tsaki towaima maizaisa yadami kansa tinda yasan cewar shiba wancan Ammar din bane
Wannan yasa yashare abin yakama hidimar dake gabansa bayan kwana biyu jirginsu yatashi saidai baisanarwasu Abba dawowarsa ba Sadiq ne kawai yasan dawowarsu domin kuwa shiya tafi daukar wa tafiyar dare sukayi
Su Umma suna falo dukansu sukaji anturo kofa anshigo tare da sallama jin'muryar Ahmad yasasu juyawa tare dakai kallonsu garesa basu gama mamakin ganinsaba sai suka ga Ammar yashigo tare da Sadiq
Da sauri sunmike tsaye cike da rudani suke fadar sunansa Ammar kallonsu kawai yake batare daya amsaba sunkasaraso ciki am Abba ku'zauna mana
Ahmad taya zamu'iya zama Abba kuzauna zansanar daku komai amma kafinnan kufara sanar dani ina kanwata naga kowa amma bangantaba garka damu Ambeeshar tana daki salla take ok yakai kallonsa ga Sadiq yace am Sadiq kasanar dasu komai ni zantafi gurin kanwata to shikenan yatashi tanufi dakin Ambeeshar su Umma kuwa sindawo da kallosu ga Sadiq
Sadiq na'am Abba dan Allah kayi saurin sanar damu abinda yake faruwa domin kufitar damu acikin wannan duhun da rudani da suka yimana dabaibayi am garka damu Abba domin kuwa yanzunnan zansanar dakai komai nan yashiga sanar dasu duk abinda yafaru
Cike da mamaki Abba yace Sadiq yanzu kanaso kafadamin cewar wannan ba Ammar din damuka sanibane eh Abba Ikon Allah Ikon gaske Allah sarkin baiwa to Abba kadaiga yanda Allah yake labarinsa da buwayarsa hakane
Al-ameen gaskiya inatantama wannan Ammar ne domin kuwa samun irin haka to'ko a film zaiyi matukar wahala amma Umma wanda yamutu aibaiya dawowa dan haka kiyarda wannan ba
Ammar din da'kika sani bane wani ne daban Allah yasake hadamu dashi hakane Aliyu tabbas abinda kafada gaskiya ne duk wanda yamutu baiya dawowa to amma kuma samun mutun sak kai shima yana da matukar wahala
Gaskiya nida zuciyata cike muke da rudani a'a Umma kiyarda wallahi iya gaskiyata nake fada maku nayarda dakai Sadiq yauwa Umma
Ahmad yasami Ambeeshar ta'idar da sallama yayi tsaye jikin kofa yana kallonta sannu ahannkali yake tafiya harya karasa isa gunda take yazauna daga gefe yana kallonta kanwata yajikinki da fatan kinasamun sauki kallonsa kawai take batare data furta masa komaiba
Ha!!! Yanisa tare da jan numfashi kanwata taso mutafi kiga wani abin al'ajabi wanda nasan zakiyi mutukar farin ciki tashi mutafi yarika hanunta ta'tashi sunfita tin'daga nesa yake yimata nuni da Ammar kallonsa kawai take har suka isa gunda suke wani irin kallo takeyiwa
Ammar wanda koshi kansa baisan wane irin kallone takeyimasa ba kallo daya yayimata yaji tabirgesa hakama yana yanada bukatar yarayu da ita na'duk iya rayuwarsa
Ahmad ya'anbaci sunansa Ammar kallonsa kawai yayi toga kanwata Ambeeshar aibasai kafa daba domin kuwa najima da sanin fuskarta ba'kuma zantaba manta wannan fuskarba har'abada nagode
Godiya kuma tomaiyasa zaka godemin bayan ni'yakamata nagodema abisa bani kyakkyawar rayuwa da kayi tare da hadani da kyakkyawar kanwar ka ma'abociya san yaya zuciya
Gaskiya ina farin ciki sosai abisa wannan yanufi gurin Ambeeshar yazauna gefe da ita cikin tausasa murya tare da kwantar da ita yake magana
Ambeeshar shin'kinganeni kuwa shin'zaki iya fadar wani abu agame dani maiyasa bazakiyi magana ba
Ambeeshar daga yanayin kallonda kikeyimin nafahimci kinfara fahimtar wani abu atare dani miyeshi kisanar dani mana Ambeeshar garki fadamin cewar kinmanta da masoyinki kuma mujinki Ammar kallonsa kawai take tamkar da taganesa saidai ba baki atare da ita wannan yasa basuyi saurin fahimtar komaiba ammashi yafahimci wani abu atare da ita
Ha!!! Yanisa tare dajan numfashi am kinga Ambee garki damu zakifahimci komai nan da'dan kankanan lokaci kinji yafada yana wani lallausan murmushi ita kuwa har zuwa wannan lokacin kallonsa kawai take bako rintsawa sai kuma zuwa wannan lokacin ne su
Ahmad suka gaisa da su Abba bayan sungaisa Aisha tace sutafi part dinta suci abinci ta'amsa da to bajima wa sosai suka tashi Suka nufi part din Aisha suna isa kaitsaye gurincin abinci suka nufa Aisha tahada masu kayan abinci sannan tazuba masu
Suna cikin cin'abinci Ammar yace am yaya Ahmad zanso nahadu da wanda yakasance yana yawan futa tare da Ambeeshar domin kuwa da akwai abinda nakesan na'tambiyesu
To kabari sai zuwa gobe saina hadaka da Aliyu domin kuwa shine abokin tafiyarta ko'ina yasan komai akanta to shikenan Allah yakaimu goben Amin bayan sunkarasa sunkoma part dinsu Umma sunsamu Ambeeshar batanan Ahmad yatambayeta Umma tafada masa cewar takwanta ok sai kuma zuwa wannan lokacin ne
Ahmad yagabatar dasu Abba gurin Ammar am Abba Ammar zaicigaba da zama anan har zuwa lokacin da zaibukaci yatafi yaya Ahmad ni'kuwa maizaisa natafi aibazan komayin kus'kuran kara barin Ambeeshar ba zankasance da ita har karshen rayuwata yaya Ahmad wallahi inasan Ambeeshar sosai saiji nake ajikina tamkar najima da saninta
Domin kuwa kallo daya nayimata amma nikadai ne nasan irin yanda naji kuma har yanzu inaji banajin kuma zandenajin abinda nakeji agame da Ambeeshar bansan komai agame da ita ba face soyayyarta
Tabbas zankasance daku na har abada domin kawai narayu da Ambeeshar duk kanninsu kallonsa kawai suke cike dajin mamakinsa yayinda farin ciki duk yashigesu Abba yayi murmushi sosai nagode Ammar a'a Abba dan Allah kadena yimin godiya domin kuwa har yanzu banyi abinda zaka godemin ba
Idan da akwai wani maigodiya to ni'ne inagodiya sosai abisa yunkurinku nakoma hadani da Ambeeshar nagode sosai Allah yabar zumunci sun'amsa da Amin
By. Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
2⃣9⃣ to 3⃣0⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Aliyu inasan kafadamin guraren da Ammar yake zuwa da Ambeeshar domin kuwa nasamu makama
To gaskiya niba zance ga wani takamammen gurin da Ambeeshar take zuwa tare da Ammar ba domin kuwa duk lokacin da zasu fita to a school yake daukanta sufita ko'agida
Wannan yasa sam banida wani sani da guraren da suke zuwa saidai inada wata shawara
Inajinka am da akwai kawayenta Anisa da Farida su'zasu iya sanin wani abu agame da hakan yauwa Alhamdulillah to yanzu yaza'ayi nahadu da daya daga cikinsu
Nima kaina shine abinda nake tinani kamarya saboda banida da number su taya hakan takasance abaya inada number su tinda sukayi Aure saina sara layinsu kasan cewar sunyi canjin number to bakasan gidansu ba nasani to mutafi can
Saboda zamu sami number acan ok sunfito sun'nufi gidansu Anisa sun'isa gidan Aliyu ne kawai yashiga gidan bayan wani lokaci yafuto
Ammar yashiga tambayarsa toya kasami number eh ansamu gud to kira layin kayi magana da ita ok yashiga kiran layin Farida bajima wa tadaga tare dayin sallama ya'amsa
Am Farida kina da magana da Aliyu na Ambeeshar Allah sarki Aliyu yakake kwana biyu haduwa tayi wuya wallahi kuwa to gida ya Ambeeshar da fatan tana samun sauki
Eh Alhamdulillah to Allah yakara afuwa Amin am Farida dan Allah zaiyuwu muhadu inasan zamuyi wata magana akan Ambeeshar haba Aliyu maikake fadane haka
Aibana tinanin da akwai abinda zaitaba zumuncinmu kai'kakasance tamkar yayana dan haka bawani abinda zaihanaka ganina kawai duk lokacin da kakeda bukatar ganina kazo
Toshikenan godiya nake zanshigo yanzu ba damuwa saikazo am to kiyomin text na full addres dinki ok sunyi sallama Ammar kuwa sai aikin kallonsa yake yace to yadai garka damu yanzu zamu tafi baifi da muntuna biyu ba wayarsa tayi kawa alamar shigowar sako yaduba sun'nufi gidan Farida suna isa yakirata awaya yasanar da ita
Haba Aliyu kashigo mana Farida tarefa nake da bako aibakonka ne ko eh to kashigo dashi ok yauwa sunyi sallama sun'karasa daga ciki tana zaune afalo suka turo kofa suka shigo lokaci daya firgici yashigi Farida yayinda tsoro da fargabar abinda tagani yabaiyana akan fuskarta cikin rawar murya
Take magana Aliyu wanake gani kamar Ammar kodai idanuwana ne suke yaudarata yagirgiza ka a'a Farida sam idanuwanki basa yaudararki Ammar ne agabanki Aliyu Ammar fa kace eh Ammar
Aliyu Ammar dai Ammar wanda nasani eh to miye gaskiya akan labarin mutuwar sa nima kaina banida sani akan haka Farida tirkashi to muzauna ko ok mungode bakomai
Bayan sun'zauna sunsami shiru namintuna biyu Ammar ne yakauda shirun dakin tahanyar anbatar sunan Farida am Farida ko eh am dan Allah inasan kisanar dani guraren da kikasan Ammar yana zuwa da Ambeeshar
Maiyasa kake tambaya na abinda kake da sani akansa ko kanasan kafadamin cewar ba kaibane Ammar din danasani ba
Tayama zanfurta hakan tinda kona fada balallai ki'iya yarda ba kawai dai nasami hatsirine wanda wannan dalilin ne yasa na'manta komai agame dani nayi nasarar sake haduwa da
Ambeeshar wannan yasa nakesan natina irin soyayyar da nayi da Ambeeshar domin kuwa tahakanne kawai zamu'iya taimakon Ambeeshar tadawo haiyacinta wannan yasa nazo gareki dan Allah kitaimakeni kisanar dani wani abu agame da soyayyata da Ambeeshar kinji
Dan Allah tabbas ina tan'tama akanka fuskarka muryarka yanayin ka dama komanka sak Ammar to amma abinda yatsayamin arai shine taya za'ace wanda ya'mutu tsayin shekaru uku da rabi yanzu kuma yabaiyana agaba na gaskiya abin da kamar wuya wai sata akiyama
Am kinga Farida ki'ajiye wannan zancan agefe kisanar dani abinda na'tambiyeki dan Allah to shikenan da fari dai Ambeeshar ce take daukanka kuna fita kasan cewar kai bakone baka da sani danan
Ammar kanayiwa Ambeeshar wata irin soyayya ce wadda harkasa tafara zaucewa wanda kuma wannan dalilin ne yasa Ambeeshar tabijiro da zancan kuyi Aure domin kuwa sam tagagara jure soyayyarka kasan cewar sam bazata iya hanaka kaiwa gareta ba nan tashiga sanar dashi komai
Da irin guraren da suke zuwa yanisa tare dajan numfashi nagode Farida bakomai Ammar wannan ai'taimakon kai da kaine fatana anan shine Allah ya'azamu asa'a ya'kuma sa mudace Amin yarabbi bajima wa sosai sukayi mata sallama suka tafi
Sundawo gida Ammar jikinsa tamkar banasaba zancan Farida yayi zaune azuciyarsa suna shigowa kaitsaye dakin Ambeeshar yanufa kasan cewar baisameta afaloba su Umma sunbisa da kallo
Abba yakai kallonsa ga Aliyu yana maitambayarsa Aliyu daga ina kuke maiyafaru da Ammar ne haka nan yashiga fada masu komai Abba nima fa nafara tsorata da Ammar domin kuwa komansa irin na wancan Ammar din ne to Aliyu jiya dana fada aisam bakuyardaba gashi kuma yanzu kazo kana fada zuwa gobe ko jibi bankuma San wanda zaizo da wani zancan irin namuba
Abba yakai kallonsa ga Ahmad yace am Ahmad kasanar damu waye wannan Ammar din suwaye ahalinsa Abba nimadai kamarku sam bansan komai agame dashi ba domin kuwa koshi karan kansa baisan komai agame dashiba
Balantana wani yasane masa nima tin'aranar farko dana fara hakuwa dashi nayi tinanin koshima yarasa tinaninsa kamar kanwata amma saiya fadamin cewar sam shiba
Ammar din da nake naima bane amma ina da wani kudiri araina na cewar idan Allah ya'azamu asa'a kanwata tasami lafiya to zamu koma da Ammar gurin Doctor daya fada mana cewar ya'mutu
Domin kuwa da akwai tambayoyin da suke yimin yawo aka wadanda kuma shikadaine zai'iya amsaminsu to Allah yataimakemu Amin ya Allah
Sai zuwa wannan lokacin Al-ameen yayi magana am Abba ni'kuma da akwai abinda nakesan nafada bismilla am Abba maizaihaka ayi Auran wannan Ammar din da Ambeeshar tinda zuwa yanzu duk muna da yakinin cewar Ammar ne yadawo garesu
Duk da cewar bama da wata kwakkwarar shaida akan hakan ni abu daya nafi yarda dashi shine Ammar yanasan Ambeeshar kuma itama tana sansa dan haka kawai yadaura Auransu wannan shine abinda yadace bantari hanzarinka ba Al-ameen amma kai kana tinanin Ammar zaiyarda ya'Auri Ambeeshar ahaka magana zamuyi dashi sai muji to shikenan Allah yasa mudace Amin Abba
Ammar ya'isa dakin Ambeeshar yasameta zaune tana kallon hutuna yakarasa gunda take yazauna kusa da ita kusa sosai yakai kallonsa ga hutunan da take kallo yafada azuciyarsa tabbas wadannan hotunan Auranta ne ya anbaci sunanta
Ambeeshar waye wannan yanuna Ammar kallonsa kawai take batare da tace dashi kanzilba Ambeeshar dan Allah kifadamin waye ni maiyasa namantaki nakasa tina komai agame dani Ambeeshar idan har da gaske nine Ammar dinki to bai kamata ace namantaki ba domin kuwa yanda Farida tafadamin irin soyayyar da nake maki dama wadda mukeyiwa junanmu to sam bai kamata ace mun'manta junanmuba
Ambeeshar tabbas inaji ajikina nine acikin hotonnan ina nufin ni'ne Ammar dinki mujinki Ambeeshar nayarda da soyayyar da nake yimaki wannan yasani fadar haka domin kuwa idan da ace bansankiba toda sam bazantaba jin'soyayyarki har'haka ba wanda daga jiya zuwa yauwa wallahi sam bazan'iya sanar dake irin tsantsar san da nake yimaki
Ambeeshar wallahi inasanki da yawa inasanki sosai wallahi har inajin kamar zanyi hauka adalilin soyayyarki Ambeeshar ni kaina bansan wane irin so nake yimaki ba balantana kuma na'iya furta makishi saidai kawai nabar abin azuciyata
Amma kisani wallahi soyayyarki tana azabtar dani da yawa iinafatan ganin zuwan ranar da zaki sami lafiya ni'kuma daganan saina fara binkice akan waye ni itadai kallonsa kawai take tamkar da zata yimasa magana amma badamar hakan wani irin kallo suke yiwa junansu wanda su'kansu basusan maisuke nufi dashi ba yagagara hakura ya'rungumota jikinsa yayinda idanuwansa suka canja launi daga fari zuwa ja
Sai wata kwalla yake zubarwa maitsananin zafi da kuna yana maifurta mata kalmar I LUV U I LUV U SO MUCH ina kaunarki sosai lokaci daya taji wani irin abu atare da iita yanayimata kai'kawo ajikinta take tafara zubar da kwalla
Dimin hawayenta ne sukasashi dagota yagirgiza mata ka tare da furta a'a Ambeeshar dan Allah kidena wallahi ba naso ba'kuma zanjureba zokiga yajanyota jikinsa yana rarrashinta sun'kasance ahaka har natsayin wani lokaci
0 comments:
Post a Comment