Aliyu na'am Abba jeka ka'duba Ammar kagani lafiya yake kuwa duk yau baifitoba to Abba
Yatashi yanufi dakin da yake yasamesa akwance sai faman juyi yake ga'alama kuma yana tare da tarin damuwa atare dashi
Ya'isa inda yake tare da zauna'wa kusa dashi yana maifadar sunansa Ammar lafiya kake kuwa maiyake damunkane
Ha!!! Yanisa tare da sauke ajiyar zuciya am Aliyu wallahi ina tare da dinbin damuwa nida zuciya"ta subhanalillah maiyasa mekane Aliyu wallahi inasan yar Uwarka wato AMBEESHAR wanda koni kaina bansan yaushe ne nafara Santana
Aliyu damuwata a yanzu shine naga AMBEESHAR tasami lafiya bayan nan kuma saina fara binkice akan kaina wayeni suwaye iyayena a'ina nake da zama maiyasa namanta komai a game dani maiyasa nagagara tina asalin wayeni
Maiyafaru dani wanda yahaifarmin da wannan jarrabawar ha!!! Yaja numfashi tare da girgiza ka tabbas ina acikin tsaka maiwuya tare da kunci atare dani Aliyu ni tsorona daya ne gar
AMBEESHAR tasami lafiya ta'kuma fahimci cewar bani bane asalin Ammar dinta ba domin kuwa na'tabbata da zarar tasan da haka to wallahi zata barni wanda ni'kuma Sam bazanso hakan ba wannan tinanin shiyafi damuna ayanzu fiye da komai
Aliyu dan Allah kataimaken kafadamin taya zansami AMBEESHAR garka damu Ammar insha Allah zaka sami AMBEESHAR kayarda dani to Allah ya'yarda Amin to kaga yanzu tashi mufita Abba yana naimanka
Amma lafiya kuwa garka wani daga hankalinka bakomai ok suntashi sunfita yafara gaisawa dasu Umma sannan yace Abba gani dafatan lafiya bakomai
Ammar dama ganin bangankaba yasa nace akiramin kai da fatan kana lafiya ina qlau Abba saidai ina tare da tarin damu subhanalillah maiyasa mekane Abba
AMBEESHAR ce damuwata yaushe zata sami lafiya domin nafara binkice akan kaina ni'waye amma inaji ajikina insha Allah AMBEESHAR daf take da tasami lafiya da yardar Allah
Domin kuwa ayau nakesan nafara fita da ita domin natina mata wani abu naga ko zata'iya tinawa da wani abu yayinda nafita da ita zankasance tamkar
Ammar dinta zanhau matsayin Ammar tayanda zatayi saurin tinawa nasami duk wani bayani akan Ammar kuma ni ba'abinda bazanyiba domin AMBEESHAR tasami lafiya saboda kuwa ina matukar Santa sosai kuma ina fatan samunta
Saidai kuma da kawai abinda nakejiwa tsoro miyeshi Abba inajin tsoran gar AMBEESHAR tasami lafiya tafahimci cewar niba Ammar dinta bane tabarni domin kuwa idan har AMBEESHAR tabarni to wallahi zan'iya samun matsala watakilma na'iya mutuwa ta'har abada domin kuwa ni kaina bansan wane irin so nakeyiwa
AMBEESHAR ba kamar yanda bansan yaushe nafara Santana amma naji ina bukatar narayu da ita na'duk iya rayuwata Abba dan Allah da girman Allah kutaimaken ku'rufaman asiri garku taba barin AMBEESHAR tasan da cewar bani bane asalin Ammar dinta ba domin kuceci rayuwata dan Allah
Garka damu Ammar insha Allah AMBEESHAR bazata taba sanin wannan sirrin ba wannan yasa muka yanke hikuncin yima Aure da AMBEESHAR domin kasami damar da zaka baiyana duk wata soyayya taka agareta amma idan kayarda da hakan haba
Abba tayama zaka fadi haka ni kana tinani inada wani farin cikine fiye da Auran AMBEESHAR domin kuwa akullum shine mafarkina kuma tinani'na gaskiya Abba zanyi farin ciki sosai idan har abinda kafada ya'tabbata
Amma Abba zanso Aurena da AMBEESHAR yakasance acikin gajeran lokaci garka damu Ammar nima hakan nake fata yauwa Abbana nagode sosai Allah yasakama da mafificin alkhairi Amin
Yakai kallonsa ba Ahmad tare da tashi yanufi inda yake yazauna yace yaya Ahmed wallahi kai mutumen kirkine adalilinka nasami ahali yanzu ina da Umma Abba yayye da kuma mata gaskiya ina farin ciki sosai ina godiya
Allah yabaka duk abinda kake bukata adalilin kane nasami AMBEESHAR amatsayin mata wannan abu bakaramin dadi yaminba inagodiya abisa wannan Alla yasakama da alkhairi Amin Ammar hakama Sam garka damu da wannan domin kuwa ni dakai taima me'keniya mukayiwa junanmu
Kasani wallahi adalilin kanwata ba'abinda bazanyiba dan haka kadena godemin murmushin kawai yake yayinda yagagara furta masa komai sai zuwa wannan lokacin Al-ameen yayi magana am
Ammar na'am zanso kabari sai anyi Auranka da AMBEESHAR sannan kufara futa dan Allah yayi murmushi tare da furta to yaya Al-ameen Allah yakaimu lokacin da alkhairi sun'amsa da Amin
Bayan sati daya aka daura Auran AMBEESHAR da Ammar farin ciki agurin Ammar abin sai wanda yagani ba'a magana su Umma sun'shiga mamakinsa matuka ganin irin farin cikin da yake ciki su'kansu sun'kasa fahimtar wane irin So yake yiwa AMBEESHAR ne haka
Wannan yasa dukan'ninsu zuciyarsu ta'tafi da tinanin cewar shine Ammar dinda sukasani tin'da jimawa to amma miye hujjarsu tafadar haka babu
Wannan dalilin'ne yasa basa furtawa saidai kawai subar abin azuciyarsu
Zaune take tana wasa da Teady Ammar yaturo kofa yashigo tare da sallama takai kallonta garesa lokaci daya yasakar mata wani kyakkyawan murmushi ta'kuma kallonsa kawai take sannu ahankali yake takunsa cikin kasaita harya isa gunda take yazauna tare da kai kallonsa gareta cikin wata lallausar murya cikin harshen turanci yake magana
Sannunki da wasa kyakkyawan mata'ta AMBEESHAR wallahi ina farin ciki da samunki to amma taya zansanar dake kona fahimtar dake cewar ina kaunarki saukinta daya da kikejin duk abinda nake fada inaji ajikina wata rana zakiyi magana kifurtamin cewar kina farin ciki da samuna
Amatsayin mijin Auranki inama ace yanzune zaki furtamin haka tabbas da zanyi farin ciki maigirman gaske AMBEESHAR dan Allah zaki'iya yimim wani abu nasan zakiso kiji abinda zanfada to kidanyi murmushi mana
Domin nasami kwarin guuwar sanar dake bukata'ta agareki dan Allah please kinji yafada da indiyanci lokaci daya tawani zaro ido tana kallonsa take taji wani abu yana yimata yawo aka tayi saurin dafe kanta tare da rufe idanuwanta ga'alama tinani take
Yafahimci komai atare da ita saidai baiyi saurin nuna mata ba yashiga fadar sunanta AMBEESHAR saidai bata amsaba yasa hanunsa yariko fuskarta yakai bakinsa dai-dai kunnanta yahura mata iskan bakinta tare da dan ciza kunnanta cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yace inasanki
Ya'sunbaceta aka tare day in hugging dinta AMBEESHAR dan Allah kifadamin cewar kina sona ko ki'sunbaceni aduk inda yabigeki ajikina amma'ni kuma zanfisan ki'sunbaceni abaki domin kuwa zanfi farin ciki fiye da ko ina
Sunjima rungume da juna sannan yasaketa yashiga fadar sunanta AMBEESHAR kasancewar har zuwa wannan lokacin idanuwanta arufe suke sannu ahankali take bude idanuwanta har suka bude tayi tozali da kyakkyawar fuskarsa maidauke da annuri yayinda yake yimata wani kyakkyawan murmushi
Maibirgewa kallonsa kawai take saidai tagagara cewar dashi komai AMBEESHAR bazaki amsamin cewar kina Sonaba ba kuma zaki sunbatanba fadamin maiyasa bakya Sone fadamin mana domin naji kallonsa dai take yayinda idanuwanta suke zubar da kwalla a'a AMBEESHAR yafada tare da girgiza ka yajanyota jikinsa yana rarrashinta
Bayan kwana biyu yashirya tsab cikin kyakkyawar shiga haka AMBEESHAR yadauketa sunfita tare suke da Aliyu saidai ba motarsu dayaba shiyana agaba su'kuma suna biye dashi kasancewar Ammar baiya da sani akan garin kantin Asmeen super market suka fara isa domin kuwa a wannan gurin ne tafara haduwa da Ammar yace
AMBEESHAR shin'kingane wannan gurin kuwa zaki'iya tina wani abu kuwa AMBEESHAR ko'kinsan cewar a wannan kantin a'kima irin wannan ranar ki'ka fara haduwa da Ammar shin'kintina da wannan ko haryanzu baki tina komaiba
AMBEESHAR dan Allah kitina wani abu komai kan-kantarsa kinji shiru batayi magana ba sai nazari da tinani take amma Sam tagagara iya tina komai Aliyu dai yana daga gefe yana kallonsu
Ganin tagagara tina komai yasata zubar da wasu irin zafafan hawaye masu zafin gaske AMBEESHAR maiya samekine haka maiyayi sanadin zubar da hawayenki dan Allah kisanar dani tayanda zangane kinji AMBEESHAR na please bata iyafurta masa komaiba saidai tagirgiza masa ka
Tabbas kina matukar san'kiyi magana nafahimci hakan daga yanayinki amma kisani wallahi zanfiki farin ciki da hakan mutafi kidauki duk wani abu da kike da bukata dashi yarika hanunta suncigaba da tafiya yayi mata siyayya duk abinda yadauka saiya nuna mata cewar yana da matukar anfani agareta
Bayan sunkammala sun'nufi gidan Farida suna shiga Farida tazo da gudu tarungumeta tana maifadar sunanta AMBEESHAR sannunki da zuwa tarikota sunzauna bayan sungaisa
Ammar yace am AMBEESHAR Kinga ne Farida kuwa kawarki tahanin dama ko har yanzu bani wayeta ba kallonsa kawai take tayi wani dan gajeran murmushi take farin ciki yashigesa yace Wow kinganki kuwa wallahi kinyikyau sosai mata'ta AMBEESHAR ke dababance inasanki da yawa
Ammar kenan aibaaai kafada ba domin kuwa mushaidane akan hakan wannan yasa har yanzu kuke tare da juna muna maku fatan alkhairi muna godiya sundan jima anan daga bisani kuma sukayi sallama da Farida suka tafito
To masu karatu kuti hakuri da wannan domin kuwa yau jikin Nasa Sam bakuzari ina baran addu'arku agareni Allah yabani lafiya tare da sauran al'ummar musulmi Allahumma Amin
By. Fauziyya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
3⃣3⃣ to 3⃣5⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Zuwa yanzu Ammar yafara daukan AMBEESHAR suna futa yauma dai kamar kullum yadauketa sunfita
Zaune suke wani kyakkyawan guri zaune kawai suke yayinda suka saka junansu agaba suna kallo
Ha!!! Yanisa tare da fadar sunanta AMBEESHAR wane irin kallo ne ki'ke yimun haka ko zuwa yanzu kinfahimci wayeni agareki
Shin'har yanzu baki tina da Ammar ba AMBEESHAR ni'kuwa maizaiyi wanda zaisa kiyi saurin tina'ni domin kuwa zuwa yanzu yaci ace kinganeni amma saidai kash samun hakan ne da matukar wahala
Jinsa kawai take amma sam tagagara iya furta masa komai
Saima tashi da tayi tanufi wani guri daban shima mikewa ya'yi tare da fadar sunanta
AMBEESHAR saidai ba tako juyoba balantana yayi tinanin zata amsa masa
Yayi tsaye yana kallonta ganin batada lokacin tsaya wa yasa'sa bin'bayanta bataji motsinsa ba saiji taji yayi hugging dinta tabaya tare da sunbatarta awuya
Yasa hannayansa yarungumo hannayenta yakawo bakinsa dai-dai kunnanta cikin wata yar murya yake tada mata kalmar inazuwa
Fadamin ina zaki tafi yajuyota sun'fuskanci juna wani irin kallo suke yiwa junansu mai tare da shauki irin na'So tagagara jure irin kallon da yake mata tasunkuyar da fuskarta
Yasa hannunsa yadago fuskarta AMBEESHAR maiyasa bakya jure kallon cikin idanuwana ni'kuma inasan ki'kalli cikin idanuwana natsayin wadansu muntuna domin watakil ki'iya tina wani abu atare dani
Dan Allah kidago fuskarki ki'kallen koda kuwa na mintuna biyar ne batare da kinrufe idanuwanki ba ko kinkau da kaiba
AMBEESHAR nasan cewar kinajin duk kannin abinda nake fada magana ce kawai bakyayi da wannan nake naiman dan Allah kiyarda da bukata'ta tadaga masa ka alamar eh yayi wani
Kyakkyawan murmushi tare da furta nagode sunci gaba da kallon junansu kafin lokacin daya dibarmata yayi taji sam bazata iya jurewa ba tayi saurin kauda kanta gefe sai wani irin abu takeji atare da ita
Yasa hannu yajuyo da fuskarta yayi matukar shiga firgici na ganin kwalla akan fuskarta cikin rawar murya yake tambayarta AMBEESHAR maiyafaru dake ne haka maiyasaki zubar da kwalla dan Allah kifadamin tayanda zanfahimta
Kallonsa kawai take tana aikin zubar da kwalla yagirgiza mata ka tare da furta a'a AMBEESHAR dan Allah kidena wallahi banaso
Haka sam bazanjuraba ko kadan bazanjuri ganin zubar hawayenki ba da wannan nake naiman alfarmar dan Allah kidena zubar da kwalla kinji
Yajanyota jikinsa yana aikin rarrashinta yajata suntafi yasata mota sun'tafi
Bayan kwana biyu wani yammaci ranar Umma tafuta Ammar yasami AMBEESHAR adaki zaune yayi tsaye jikin kofa yana kallonsa itama kallonsa take yaciro wayarsa ya'kunna wakar India ya'ajiye wayar gefe
Yakama rawa ita kuwa sai kallonsa take rawa yake sosai irin yanda yake rawa lokaci daya taji wani abu yazo yayi mata tsaye azuciya sai wani kallonsa take tanasan ta'tina wani abu
Amma abin takaici sam tagagara tina komai tamike tsaye da sauri tanufi inda yake tawani rikosa tana tambayarsa kai waye fadamin kai waye maiyasa nagagara tina komai
Dan Allah kasanar dani kai waye tabbas nasanka to amma maiyasa nagagara tinaka maihakan yake nufi dan Allah kasanar dani kafadamin waye kai fadamin mana tafada da karfi
Tare da sakin wani irin kuka kallonta kawai yake domin yagagara fahimtar wane irin kallone take yimasa ganin tana kuka yasashi tambayarta
AMBEESHAR maiyasa mekine haka maiyasaki kuka maiyake faruwa da ke haka dan Allah kisanar dani kinji jin'yasata gaba da tambaya yatabbatar mata da cewar baimaji abinda duk tafada ba
Kenan hakan na'nufin maganar zuci take duk abinda nafada baimasan inayiba tasakesa daga rungumar data masa tajuya tafuta da sauri tamkar wadda tatsorata
Yajuya yabita abaya yana kiranta amma tayi banza dashi ganin tafito afirgice yasa Ahmad yayi saurin taronta yana tambayarta kanwata lafiya maiyafaru dake ne haka lokacin yayi dai-dai da isowar Ammar a'gunda suke
Tashiga nuna masa Ammar tare da tambayarsa wayeshi saidai sam baifahimci tambayar taba kasan cewar ba magana takeba Ammar kawai yagani tana nunamasa
Yakai kallonsa ga Ammar tare da tambayarsa maiyake faruwa yasanar dashi yadawo da kallonsa ga AMBEESHAR kanwata wai maiyake yafaru da kene ganin yagagara fahimtar abinda take fada masa yasa tanufi gun
Al-ameen da Aliyu saidai suma sam sungagara fahimtar maitake nufi wannan yasata sakin wani irin kuka maitada hankalin natare da ita
Sun'shiga rarrashinta dukansu tayi shiru amma hawaye sungagara tsayawa tayi zugum sai magana take da zuciyarta nashiga ukuna waye zai'amsamin amsar tambayata
Maiyasa dukansu ba wanda yakejin abinda nake fada shin'anya ni mutun ce kuwa idan nakasance mutun ce maiyasa dukansu ba wanda yake fahimtar abinda nake fada waye wannan
Tabbas nasan fuskarsa na'kuma san sunansa to amma maiyasa nagagara tinasa mai'hakan yake nufi dani innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un Allahumma ajirni fi'musibati wa'ahlifli khairan minha
Tafada tare da sakin wani saban kuka ta'tashi tanufi dakinta sunbita da kallo yayinda tausayinta yayi yawa atare dasu da sauri
Ahmad yatashi zaibita yana anbatar sunanta kanwata Ammar yayi saurin dakatar dashi a'a yaya Ahmad kabari kawai ni zantafi nasameta
Amma Ammar a'a yaya Ahmad garka damu ba'abinda zaifaru kayarda dani dan Allah bayanda zaiyi dole hakura ya'koma yazauna Ammar yayi murmushi nagode yaya Ahmad
Yajuya yanufi dakin AMBEESHAR yasameta kwance kan'gado sai aikin kuka take sannu ahankali yake tafiya tamkar yana tausayin kasa har ya'isa gunda take bataji shigowarsa ba kasan cewar tabasa baya ya'isa inda take yasami tsayin mintuna biyu atsaye yana kallonta
Rarrashinta yakesanyi to amma tinani yake ta'inama zaifara yadan rufe idanuwansa kadan yabude sam bataji shigowarsaba saiji taji anrungumota tabaya
Azahirin gaskiya tatsorata dajin mutun abayanta wannan yasata juyowa da sauri dan ganin waye lokaci daya tayi ido biyu da Ammar
Wani irin kallo yake mata wanda tagagara fahimtar maiyake nufi dash Ammar maiyasa bazaka fadamin waye kai ba dan Allah kafitar dani acikin wannan duhun danake kasanar dani kai waye
Maiyasa kake zuwa guna maiyasa kake jana ajikina shin'wane matsayi nake dashi agurinka wane irin maysayine kabani haka dan Allah kasanar dani komai agame dakai
Maikike san kisani agame dani domin kuwa nafahimci hakan atare dake
AMBEESHAR niba kowa bane agurinki fame masoyinki kuma mijinki shinkinfahinci mainake fada maki
Idan da gaske kai mijina ne tomaiyasa bansan ka ba tayama hakan zata kasan ce dani gaskiya abin da kamar wuya kasanar dani taya hakan yafaru dani
AMBEESHAR yaushe zaki fara yimin magana domin kuwa ina da tambayoyin da yawa wadanda nakesan ki'amsamin inasanki matata
Allah yabaki lafiya yakara sakata jikinsa nashiga ukuna yanzu ni kenan ba wanda yakejin abinda nake fada yazanyi kenan ya Allah ka'aikomin da mafutar wannan lamarin nawa Allahumma Amin
Bayan wani lokaci har zuwa wannan lokacin AMBEESHAR tana tare da kuncin akan ba wanda ya'iya amsa mata waye Ammar yanayinta namatukar tada hankalin su Abba
Amma bayanda zasuyi dole sai hakuri tinda dukasu sungagara ffahimtar abinda take nufi wannan yasa dukansu gidan ba wanda yake cikin farin ciki balantana Ahmad da Ammar duk sun'wani susuce sun'fita haiyacinsu
Abban Amir dan Allah da girman Allah kayi hakuri kaci abincin'nan tindazu kasaka abinci agaba har yayi sanyi shiru baiyi magana ba
Amir yazo gurinsa yarika hannunsa tare da fadar sunansa Dady ya'amsa batare da yakallesa ba yaci gaba da fadar sunansa Dady
Ahmad yakallesa Amir wai lafiya yamasa nuni da wani guri yakai kallonsa gunda yake nuna masa da sauri yamike tsaye yana fadin kanwata sannunki da zuwa
ya'isa inda take sun'zauna Aisha tafisa da kallo tare da sauke ajiyar zuciya kanwata yajikinki da fatan kina samun Sauki
Ta'tara masa hannu yayi dan gajeran murmushi kanwata maizanbaki fadamin ni'kuma zanbaki koma miye da yardar Allah tayima alama yagane yaciro wayarsa aljihu yabata takarba
Tayi rubutu tabasa yaduba yakarba abinda tarubuta shine dan Allah kafadamin waye Ammar domin kuwa najima ina tinani takansa amma sam nagagara iya tina komai dan Allah kasanar dani waye
Ammar domin kuwa najima ina tambayarku amma sam kungagara sanar dani komai bansan maiyasa ba bayan yakarasa karanta wa yakai kallonsa gareta yana murmushi
Allah sarki kanwata dama wannan ce damuwarki to kuwa yanzu zankawar maki da ita nanyashiga sanar da ita ko waye
Ammar amma ita sam tagagara tinawa wannan yasa tashiga damuwa sosai
Am kinga kanwata dan Allah garki daga hankalinki zakifahimci komai kinji ina zuwa yatashi yashiga dakinsa bajima wa sosai yafuto hannunta dauke da wani fai'fan sidi
Yakunna yadawo yazauna kusa da ita garki damu kanwata wannan zainuna maki komai kaset din bikinsu ne ya'kunna mata takalli komai har zuwa inda Ammar Yafadi tabbas nasan Ammar na'kuma yarda sshi'mijina ne to amma taya zantina haka
Tashiga nazari da tinani har saida kanta yadau zafi kasan cewar tafara tina wani abu tawani tashi da sauri kamar wadda tafirgita
Ahmed yashiga tambayarta ina zuwa haka tarubuta masa inasan zanhadu da Ammar ne batare da tajira taji maizaifada ba tayi tafiyarta bayan yaduba yatashi yabita abaya
Kwance yake banda juyi ba abinda yake yayinda tinanin AMBEESHAR yayi yawan gaske atare dashi Wannan tinanin yayi sanadin saukar masa da mutuwar jki da kasala saijin jikinsa yake tamkar banasa ba
Ha!!! AMBEESHAR yaushe zaki warware Nafara binkice akan kaina domin kuwa wallahi ina bukatar nasan wani abu agame dani
Ha!!! AMBEESHAR bara natashi natafi nadubaki yatashi yanufi dakin AMBEESHAR fitowarsa tayi dai-dai da shigowarta sai daishi sam baigantaba
Ahmed yakirasa Ammar yajuyo take lokaci daya yayi ido biyu da AMBEESHAR yanufi gunta yana cikin tafiya dama jikin nasa bakuzari take yaji jiri yafara dibarsa
Yayi saurin dafe kansa tare da furta wash lokaci daya AMBEESHAR taji gabanta yawani fadi zuciyarya tashiga buga mata da karfi tanufi inda yake
Bata karasa isa gunda yajeba ya'yanke jiki yafadi lokaci daya yaji kanta yana wani juya mata da sauri tashiga tina abinda yagani acikin film din bikinsu
Da sauri ta'isa tana jijjigasa amma baitashiba da sauri su Abba suka karasu gurin ganin Ammar baitashiba yadaga hankalin AMBEESHAR sai kuka take bada wata tazaraba itama tasheme hankalinsu
Umma yadada tashi dimin hawayentane sukayi sanadin tashinsa daga suman da yayi yatashi yasamisu Ahmad zagaye da AMBEESHAR bai tsaya wata-wata ba yasungumeta yafuta su Abba sunsa abaya yasata mota sun'nufi asibiti
Yan Uwa dan Allah ina baran addu'arku jikina yayi nauyi wannan yasa yanzu bako yaushe nake typing ba
Dan haka dole sai kunyi hakuri dani da kuma yanayina inagodiya sosai agareku fatan alkhairi
By. Fauziya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
3⃣6⃣ to 3⃣8⃣
Na
Fauziyya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Sun'isa asibiti cikin wani irin tashin hankali
Nurse sun'shiga da ita ciki su Umma sunyi zugum suna jiran tsammani yayinda Ahmad da Ammar suke aikin aikawo
Subhanalillah nashiga Ukuna ni Aisha har sai zuwa wane lokaci ne zandauka ina dakon wannan kuncin da yake atare dani
Maiyasa ne har yanzu Ahmad yagagara fahimtar halinda nake ciki adalilinsa
Sam yagagara fahimtar damuwata sai sha'aninsa kawai yake ba damar nayi magana sai yace dani
Kanwarsa AMBEESHAR shi'akullum zancansa baiya wuce AMBEESHAR
Tabbas nayarda yayi matukar sabo da AMBEESHAR to amma kuma maiyasa Sam baiya tina cewar ni ina da haki dashi
Amatsayinsa na mujina idanshi baiya da bukata dani to'ni ina da bukata dashi kuma yakamata yabani hakina amasayinsa na mujina
Ha!!! Tanisa tare dajan numfashi tanamai ajiyar zuciya kukan yaronta ne yayi sanadin dawowarta daga duniyar tinaninta dakai kallonta garesa tare da fadar sunansa
Amir har katashi to mutafi kayi fitsayi kaci abinci kanajin yunwa ko yadaga mata ka alamar eh yauwa Abban Dady mutafi
Ta'taah tare da rika hanunsa sun'shiga bandaki bajimawa suka fito tanufi gurin tebur tana basa abinci
Haka ita Sam bat'ta da labar cewar su Umma suna asibiti kasancewar tana apart dinta
Bayan wani lokaci Doctor yafito yanufi gunsu Abba domin yasanar dasu halinda AMBEESHAR take lokaci daya yahangi
Ammar yana ta'aikin kai komo yayinda damuwa tayi yawan gaake atare dashi wadda har tabaiyana akan fuskarsa
Take yaji jikinsa yadauki bari lokaci daya gumi yafa saukar masa firgici da tsoro suka shigesa wanda yagagara iya boyewa
Yayi shiru yagagara fadar komai Abba yashiga tambayarsa yajikin AMBEESHAR shiru baiyi magana ba sai aikin kallon Ammar kawai yake
Abba yadafasa yawani juyo firgigit yatsorata Abba yace wai maiyake faruwa da kaine tindazu sai magana nake kayi shiru kafito bakace damu komaiba yajikin
AMBEESHAR am!am!!am!!! wancan ba Ammar ba'ne eh Ammar ne lafiya yayi shiru yana nazari Doctor wai'maiyake faruwa ne
Yagirgiza ka tare da furta bakomai to AMBEESHAR fa tana samun sauki saidai kuma har yanzu bata farkaba am zamu'iya shiga gunta eh yauwa muna godiya bakomai su Ahmad sun'shiga gunta
Doctor yabi Ammar da kallo cike da mamaki yayinda rudani yayi yawa atare dashi jiki asanyaye yajuya yanufi office dinsa yayinda yake magana da zuciyarsa
Tayama za'ace Ammar har yanzu yana araye gaskiya abin da kamar wuya mutumen da aka bin'ne to tayama za'ace zairayu wallahi wannan Sam bazaiyuba
To amma ya'akai hakan tafaru inabukatar nasan tayanda akai har yanzu Ammar yake araye taya akai yarayu bayan ya'mutu yazama dole nasan wani abu
Sun'shiga dakin da AMBEESHAR take sun'sameta akwance ko wani dogon motsi batayi balantana susaran tashinta a wannan lokacin dakin yayi shiru bamai magana turo kofar da akai ne yakauda shirun dakin
Nurse ce tace am wai Doctor yace yana bukatar ganin Ammar ayanzu ok Ammar Yatashi suntafi su Abba sunbisa da kallo to maiyasa yabukaci gani
Ammar to kona miye idan yadawo maji sun'shiga office dinsa tare da sallama yace Nurse din ta'tafi ok tajuya tafuta
Gani Doctor sannu Ammar yauwa inajinka kafadamin abinda yake faruwa da AMBEESHAR yayi murmushi Ammar kenan kaga ni'kuwa bankiraka domin nayi zancan AMBEESHAR dakai ba
To maika'kira kasanar dani am Ammar inasan zaka amsamun wadansu tambayoyi kamar yafa Ammar tabbas nasancewar baka mutuba amma kuma banida wata hujjar da zantabbatar da hakan
Wannan yasa dole na furta cewar kamutu domin kuwa banida wata mafuta bayan wannan amma ni duk ba wannan ba abinda nakesan nasani shine ya"akai kabar asibitin nan da taimakonwa kabarnan
Wannan ne abinda nakesan naji dan Allah kasanar dani cike da rudabi Ammar yace Doctor wai maikake fadane haka domin kuwa ni'sam nagagara fahimtar abinda kake nufi
Ban'mutuba wayataimaken nabarnan Sam nagagara fahimtar abinda kake fada am kaga Ammar a'a dan Allah kabarni garka wani dabultamin lissafi kabarni kawai dama nazonan da
Tinanin zakayimin zancan AMBEESHAR amma sai wani zancan banza wofi kakemun to kaaabi ni'sam banida lokacin sauraren wannan ahirmen naka kaga tafiyata Yatashi yayi tafiyar sa
Doctor nakiransa amma yayi banza dashi yayi tafiyar sa abinsa yadawo dakin da AMBEESHAR take Abba yashiga tambayarsa mai Doctor yafada masa wani shirmensa ne yake fadamin tamkar da wanda yasha kwaya maiya fadama ne nan yasanar dasu komai lokaci daya suka shiga rudani dukanasu ba'abinda yazauna azuciyarsu face dama baka mutuba
Eh haka yafamin to banda shirmensa koma bace hauka to waya fada masa cewar na'mutu idan na'mutu zantsayane agabansa
Ahmad Yatashi yace Ammar mutafi karakani gunsa ok sunfito su Abba sunbiyi bayansu
Ha!!! Yanisa tare dajan numfashi yana maisauke ajiyar lallai Ammar bakaramin zaucewa kayiba tin'da kuwa har yanzu kagagara tina waye kai har zuwa wannan lokacin bakasan komai akan'kaba
Wannan yasa Sam kagagara fahimtar abinda nake fada ni wannan ma gaba tayi dani domin kuwa ba'abinda zaifaru dani
Turo kofar da akaine yakauda tinaninsa ganinsu Al-ameen matukar tada hankalinsa take yaji zuciyarsa nabuga masa da karfi tamkar da zata dashe ba'abinda yake fada face Kalmar innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un
Wani irin kallo Ahmad yake yimasa mai kama da harara cike da kunci, bakin ciki, bacin rai tare da dinbin damuwa yake magana kasanar damu gaskiya a game da mutuwar Ammar
Kasanar damu tinkafin rayuka sufi haka baci cikin wata sarkakiyar murya yake magana to'ni kuwa maizanfada bayan kunriga da kunji komai
Natabbata Ammar yasanar daku dukkan abinda bafa dan haka Sam bakwa bukatar jin'komai daga gareni
Wannan kuma tinaninka ne ba namuba domin kuwa kasani wallahi tallahi yazama dole kasanar damu gaskiya damu bamusan da ita'ba
Maiyasa kafada mana cewar Ammar ya'mutu bayan kuma karya ne bai'mutuba kasani wannan watan tonan asirinka ne yakama dan haka yazama dole kasanar damu abinda na'tambayeka
Tabbas abinda kafada gaskiya ne hakama Sam banida wani zabi domin kuwa yazamemun dole nasanar daku yanda hakan tafaru tabbas Ammar bai'mutuba kamar yanda nafada abinda yafaru shine
Bayan anshiga da Ammar Amisha tashiga gun Doctor am yadai mayakawoki nan yakamata koma miye kibari har nafito saki sanar dani
Ba'bukatar hakan shiyasa nasameka anan am Doctor wata bukata nake naima agurinka kuma kasani idan har na furta to wallahi yazama dole ka'aikata kamarya fa miye bukatarki am da fari karbi wannan
Yakarba inasan kayi masa wannan allurar tukun'na akanme ke mahaukaciya ce ko bakya da hankali da zakice nayi masa wannan allurar da zata'iya daukansa tsayin kwanaki goma zuwa shabiyar baifarkaba
Bayan wannan kuma zata'iya sawa yarasa tinaninsa gaba daya gaak bazan'iya ba karbi kayanki kifita tayi dariya to wallahi baka'isaba aina fadama idan har nafadama to sai ka'aikata
Zanbaka kudi maiyawan gaske kimamin dubu dari uku idan kuma baka yarda da tayina ba to zanjuye abin akan'ka zanfita nasanar da jama'ar dake jiranka awaje cewar zaka kashesa
Kasani wallahi idan har na furta haka to taka takare domin kuwa dukansu dani zasu yarda bayan nafadi haka kana tinanin za'abarka haka to wallahi ni zansaka shari'a nacewar kaiba likita bane makashi ne kafin Ammar ka'kashe jama'a masu tarin yawa
Wadanda ko'kai kan'ka balallai ka'iya ganewaba yayinda nafadi haka kasan maizaifaru tabbas zakarasa aikin'ka gabaki daya kuma kasani bawata asibiti da zasu koma daukanka aiki
Kaida aiki saidai kuma kaga anayi amma badai kaiba to kainakeji maikayanke domin kuwa bamu da wani ishashshan lokaci balantana nabaka
Damar da zakayi tinani kallonta kawai yake cike da mamakinta bashida wata mafuta wannan yasa dole yayarda da bukatarta tayi murmushi mai tare da yar dariya nagode ina tayaka murna da bakayi ko'karin rasa aikin ka ba
Bayan nafuta zaka fito kafada masu cewar Ammar ya'mutu yayinda suka bukaci gawarsa saika musanya masu da wata gawar saikaci gaba da kulaman da
Ammar har zuwa lokacin da zanbukaci yakoma hanuna nasancewar ba lallai ka'iya samun daukar gawa asaukakeba wannan yasa zanbaka kudi domin kasami damar daukan gawar tahanyar siyan
Masu tsaron gawarwaki zan'kuma baka kudin da zaka kulaman da Ammar garki damu zanyi komai kamar yanda ki'ka tsara domin kuwa ni ba'abinda ba nayi akan kudi
To shikenan garka damu kawai ka'aikata abinda nasaka angama ranki shidade ya'aikata komai yanda tatsara masa saidai kuma yanaimi Ammar yarasa daga dare zuwa wayewar gari ganin baiya da wata mafuta yasa yafadawa
Amisha cewar koda akazo daukan gawar bayanan wannan yasa aka'dauki Ammar akatafi dashi Amisha tashiga tashin hankali maigirman gaske kuma koda taji labarin har anbin'ne Ammar balantana tadakatar dasu wannan yasa dole taja bakinta tayi shiru tabar abin azuciyarta
To kinji abinda yafaru dan Allah kugafarceni duk kan'ninsu wani irin kallo suke yimasa mai'cike da mamakinsa
Tabbas kayi babban kuskure arayuwarka domin kuwa abisan wannan san'dukiyar taka kasa kanwata takasance cikin mawuyacin hali kanisantamu da farin ciki
Akullum tinaninmu yaza'ayi kanwata tasami lafiya kasa kanwata kadawo tamkar wata karamar mahaukaciya kalullubemu da hijabin bakin ciki da kunci to wallahi da sauri Al-ameen yarufe masa baki a'a
Ahmad garkayi saurin yanke hukunci dan Allah kabari ayi tinani mana kafasan komai tanasan nazari
Haba yaya Al-ameen wane tinani ko nazari zamuyi akan wannan ni'sam bana bukatar nazari ko tinani yayinda zanyankewa wannan hukunci
A'a Ahmad kayi hakuri kayi yanda Al-ameen yafada to Abba gurin yayi shiru na'mintuna biyu Ammar ne ya'kauda shirun office din tahanyar fadar sunan Abba
Yace Abba yanzu shikenan narasa AMBEESHAR tin'da kunfahimci cewar har yanzu Ammar yana araye Abba dan Allah garku rabani da AMBEESHAR
Domin kuwa wallahi Sam banajin zan'iya jure hakuri rashin AMBEESHAR saboda inasanta da yawa haka ina fatan kasancewa atare da ita
Abba AMBEESHAR itace komai nawa idan narasata to nima zaku'iya rasani Abba kutaimaken dan Allah kubarni da AMBEESHAR magana yake tamkar zaiyi kuka yayinda idaniwansa suke zubar da kwalla
Duk kansu kallonsa suke cike da mamakinsa yayinda tausayinsa yayi yawa atare dasu ganin San har yanzu yagagara fahimtar abinda ake fada Sam yagagara tina wayeshi
Garka damu Ammar AMBEESHAR takace har akullum har koyaushe kuma dukanmu muna yimaku fatan alkhairi take yayi wani kyakkyawan murmushi tare da furta nagode Abba bakomai Ammar
Abba yakai kallonsa ga Doctor yace am Doctor yanzu yazamuyi domin musamu Ammar yadawo ahaiyacinsa to wannan kuma saidai ku'naimi Amisha amma'ni Sam bansan makarin wannan allurar ba
Kasancewar ba'bu irinta anan dalili kuwa tana da matukar hatsari sosai wannan yasa Sam ba'azuwa da ita anan dan haka sai kunaimi Amisha
Ahmad yakai kallonsa ga Ammar yace Ammar kasan Amisha yagirgiza ka tare da furta a'a subhanalillah sai zuwa wannan lokacin Aliyu yayi magana to
Abba ayanayin da Ammar yake ciki taya zai'iya sanin Amisha garku damu mubar wannan zancan har zuwa lokacin da kanwata zata farfado sannan sai'mu naimi abinyi amma kusani wallahi kafin haduwarmu da Amisha saina hukunta wannan likitan abisa zinubinsa nima ina bayanka yaya Ahma
Nagode Aliyu yadawo da kallonsa ga Doctor yace idan kaga dama kagudu ko kabar gari bazanhanakaba domin kuwa wallahi aduk inda kake bazaka gujewa hukuncina ba kuma kasaka ido kayi kallo yajuya tafuta bajimawa su Abba suka bi bayansa
Doctor Yanisa tare dajan numfashi yana mai'furta innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un nashiga uku nalalace ni Saminu wace masifa ce take ko'karin hawa kaiba ina mafuta miye abinyi
By. Fauziyya Usman Kogo
Maman Adyan
[3/15, 16:49] Bil Fauzee😘: 💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
AMBEESHAR
💞💞💞
💞💞
💞
💞💞💞
💞💞
💞
3⃣9⃣ to 4⃣0⃣
Na.
Fauziya Usman Kogo
{ Bil Fauzee }
Marubuciyar ZABINA❤
Bayan kwana biyu har zuwa wannan lokacin
AMBEESHAR bata farka ba duk da cewar tana numfashi amma hankalinsu sam yagagara kwanciya
Wani yammaci duk suna tare da gurin AMBEESHAR lokaci daya AMBEESHAR tafara alamun tashi sai wani motsi take
Tana wani juyi take da sauri Ahmad yanufi gunta yana kiran sunanta
Kanwata shiru yakai kallonsa ga Aliyu yace yatafi da sauri yakira Doctor ya'amsa da to yatashi yafuta da sauri
Alokacin Ammar yafuta baiya kusa bajimawa Aliyu yadawo tare da Doctor Ahmad yabashi guri yadubata
Am garku damu wannan sam bakomai bane insha Allah yanzu zata'iya farfadowa kuyarda dani to Allah yasa Amin
Lokaci daya abu'buwan da suka faru da ita suka fara dawo mata daya bayan daya sannu ahankali tinaninta yafara dawowa
Tawani dafe ka hanu biyu tana wani juyasa saijin kanta take tamkar zaitsage dan zafi wannan yasa yake sarrafasa
Tahanyar juyasa dama da hagu su Umma sai kallonta suke cike da tausayinta
Ahmed yagagara jurewa yafara zubar da kwalla yana fadin Abba kanwata duba kaga halin da take ciki tana bukatar taimakonmu
Dan Allah mutaimaketa kafin wani abu yafaru da ita ha!!! Yanisa tare dajan numfashi garka damu Ahmad insha Allah kanwar ka zata sami lafiya da yardar Allah to Abba Allah yayarda Amin
Lokaci daya tinaninta yadawo duka ba'abinda take gani a'idanuwanta face fuskar Ammar yayinda kunnuwanta suke jiyo mata furucin
Ammar ya'mutu tashiga girgiza ka tare da furta a'a tawani tashi firgigit wani afirgice tare da fadar sunan Ammar su Al-ameen sai kallonsa suke
Da sauri Umma tarikata tana fadar sunanta AMBEESHAR Umma wai da gaske Ammar ya'mutu yayana dan Allah kusanar dani gaskiya akan zancan mutuwar Ammar a'a kanwata sam ba gaskiya ba
Ammar har yanzu yana araye kuma yana atare dake tamike tsaye tanufi gun Doctor cikin muryar kuka take magana kai wane irin mutun'ne da zaka dubi tabar idanuwana kafada mana cewar wai
Ammar dina ya'mutu ko'kana tinanin cewar zanrayu ne bayan ba Ammar dina acikin wannan duniyar to kasani idan har da wannan tinanin aranka tokayi kuskure
Maigirman gaske kafadamin ina Ammar dina maiyafaru dashi yana ina dan Allah kasanar dani kafadamin ina Ammar yake tafada da karfi cikin tsawa tare da sakin wani irin kuka
A'a kanwata dan Allah kidena wannan kukan nafada maki cewar har yanzu Ammar yana araye kuma cikin koshin lafiya yayana idan abinda kake fada gaskiya ne to yana ina maiyasa baku kasan ce atare dashi ba mutumen daya'yanke jiki yafadi sannan kuma kafadamin cewar wai yana cikin koshin lafiya
Taya hakan zata kasance dashi am kinga AMBEESHAR dan Allah ki'kwantar da hankalinki kiyarda da abinda Ahmad yake fada maki a'a
Yaya Al-ameen ni'sam bazantaba yarda da abinda kuke fadaba kawai kusanar dani ina Ammar kuma awane hali yake dan Allah kusanar dani halinda Ammar yake ciki garku boyemin komai dan Allah tafada yayinda take wani irin kuka
Lolacin yayi dai-dai da shigowar Ammar daga gida yake tare yake Asma'u yayinda yake rike da hanun Asharaf cikin rawar murya ya'anbaci sunanta
AMBEESHAR maiyasameki ne kike irin wannan kuka haka maiyake faruwa da kene haka dan Allah kisanar dani tayanda zangane
Domin na'iya fahimtar abinda kike nufi take tasaki wani kyakkyawan murmushi tare da isa gunda yake tare da fadawa jikinsa Ammar tafada tare da sabanta kukanta a'a AMBEESHAR kidena mana ai'ina tare dake ba'abinda zaifaru dake kiyarda dani
Abba Yaushe AMBEESHAR tafara magana yanzu man kai'amma gaskiya Abba yau ina cikin farin ciki maigirman gaske
Ammar kenan ai'bakai kawaiba na tabbata dukanmu muna cikin farin ciki maigirman gaske saidai kawai mutaru muyiwa Allah godiya abisa wannan ijabar da Allah yasaukar mana to Abba Alhamdulillah
AMBEESHAR yafita daga jikin Ammar tanufi gun Doctor tana zuwa tawanke masa fuska da tafi cikin fishi dabacin rai take magana kai wane irin mutun'ne banza wawa wanda baisan abinda yakeba
Wama yadauke ka aikin likita bayan bakasan yanda zaka kare rayukan Al'umma ba wane daliline dakai wanda zaisa kafada mana cewar Ammar maiyasa fadamin naji miye dalilinka kafadamin tafada cikin tsawa
Ka'kuwasan maifadar hakan zai'iya haifarmin da babbar illa tahanyar cutar dani to wallahi kagode wa Allah da ba'abinda yafaru da Ammar dina da wallahi nasa ka'kasance cikin nadama tahar abasa kuma wallahi ni'sam bazan'iya gafartama wannan zunubinba domin kuwa kazalintan da yawa bazan'iya yafema ba tamaida kallonta ga
Ahmad yayana yana da kyau kahutunta wannan Doctor abisa zunubinsa garki damu kanwata domin kuwa nima sam bazanbarsa ba yazama dole muhukuntasa abisa zunubinta
To saika fita domin kuwa sam bama bukatarka anan cikin mutuwar jiki yajuya yafuta dakin yayi shiru na mintuna biyu
Al-ameen ne yakauda shirun dakin to Abba sai mugodewa Allah da yanuna mana wannan ranar taganin AMBEESHAR tasamu lafiya Alhamdulillah saimuyiwa juna murna Allah yakara mata lafiya Amin yarabbi
Abba yakai kallonsa ga AMBEESHAR tare da fadar sunansa AMBEESHAR na'am Abba yanzu yaki'kejin jikin naki Alhamdulillah to Allah yakara maki lafiya Amin Abbana
Yayana waye wannan domin kuwa sam nagagara ganesa abinda bansani ba shine shin'mantasa nayi ko can'dama bansansaba yayi murmushi kanwata kenan wannan fa
Asharaf ne baki ganesaba cike da mamakinjin abinda yafada cikin rawar murya tace
Yayana Asharaf fa kace eh shine to amma taya hakan zata kasance Asharaf dinda nasani baifi mako biyuba taya za'ace yagirma haka gaskiya ina tantama akan abinda kafadamin yama za'ayi hakan yafaru kiyarda dani kanwata wallahi iya gaskiya ta nake fadamaki
nayarda dakai yayana saidai kuma ina mamakin yanda hakan yafaru garki damu AMBEESHAR zaki fahimci komai Ammar kenan kallonsa kawai take tana murmushi
Wani irin kallo sukeyiwa junansu mai'tare da So takai kallonta ga Asharaf tana murmushi tare da kiransa Asharaf zo mana zoga mama kasan'ni kuwa yazo yana tayi murmushi yauwa yarona
Tamaida kallonta ga Amar tare da tambayar Ahmad yayana wancan fa wayeshi nimadai kamarke bansan'saba bankuma san komai agame dashiba zan'iya yarda dakai kuwa to maiyasa bazaki yarda daniba murmushi kawai tayi tare da kai kallonta ga
Aliyu am Aliyu dan Allah kasanar dani gaskiyar waye wannan yayi murmuahi sunansa Amir shi'danki ne kinasan kisan waya haifa makishi eh yayanki wane yayan yayanki dai kanasan kafadamin cewar Aunty takoma aihuwa komiye a'a sam bahaka nake nufiba tomai kakesan kafadamin inasan nasanar dake cewar wannan yaron
Yaya Ahmed ne amma sam kingagara fahimta cikin rawar murya take magana Aliyu kaji maikafada kuwa mu'da ake bikinmu ajiya taya kuma zaka fadamin cewar wannan yaron dan yayana ne wannan shine abinda bazaitaba faruwa ba
AMBEESHAR maiyasa zanyi maki karya kona fada maki abinda ba shiba kiyarda dani wallahi iya gaskiyata nake fadamaki
Abba Umma wai abinda Aliyu yake fada gaskene sundaga mata ka alamar eh tadawo da kallonta ga Ahmad cike da mamakin sa tare da kai kallonta ga Amir tana kiransa zonan yarona duk da cewar yasanta amma baitafi gunta ba ta'tashi zuwa gunsa tasunkuya zata daukesa da sauri Ahmad yadakatar da ita a'a kanwata
Wani irin kallo take masa maikama da harara tadauke sa sunzauna sai wani kallonsa take Amir bakasan Mama ba taya za'ace yarona baisan'niba kamar yanda nima bansansaba gaskiya inatakaicin wannan abu matuka tomai yafaru dani haka kona ce maiyake faruwa dani ne haka
Maiyasa niban aihuba amma yayana ba jiya bane ake Indian night din'muba taya to za'ace ka'aifamin wannan kyakkyawan saurayi maiyafaru dani maiyasa nagagara iya tina komai kuma yakamata natina wani abu komai kan'kantarsa
Yayana dan Allah katinasar dani abinda nagagata tinawa garki damu kanwata zansanar dake koma da sauri Ammar yace yaya Ahmad shin'zaka sanar da ita cewar Ammar baimutuba har yanzu yana araye kuma yana tare da soyayyarta
Garka damu Ammar domin kuwa kanwata zata fahimci duk abinda zansanar da ita kaidai kawai ka'kasance acikin farin ciki domin kuwa kanwata takace nagode yaya Ahmad bakomai Ammar ita kuwa sai aikin murmushi take
Nan Ahmad yashiga sanar da ita duk abinda yafaru da ita dama Ammar tashiga tashin hankali maigirman gaske dajin abinda yayanta yake sanar da ita yayinda idanuwanta suke zubar da wasu zafafan hawaye masu tsananin zafi da kuna
Garki damu kanwata komai zaidai'daita Abba Umma yaza'ayi Amma yadawo adai-dai taya tinani sa zaidawo tabbas wannan likitan da Amisha yana dakyau susami hukunci maitsananin gaske abisa zunubinsu garki damu AMBEESHAR kadai kawai kibari kikara samun sauki
Yaya Al-ameen ni yanzu bawani abinda yake damuna face naga Ammar yadai-daita tinaninsa yadawo masa yafahimci komai atare dashi
Ammar shin'bazaka iya tina komai agame dakai ba komai kan'kantarsa AMBEESHAR wallahi ni'sam bazsn'iya tina konaiba game da rayuwata ba ke'kadai nasani sai kuma soyayyarki sai Abba Umma yaya Al-ameen yaya Ahmad da kuma Aliyu bayanku to bansan kowaba
Innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un nashiga Uku nalalace ni AMBEESHAR wannan wace irin musiba ce haka maiyake kunshene acikin rayuwata data Amanar mai'muka aikatawa wadan'nan mutanan da zasu hukuntamu da irin wannan tsat'tsauran hukunci haka
Mai'mukai masu ko muka aikata masu da muka can'canci haka daga garesu maiyasa basu kashenuba akan aikata mana wannan fitanar da tashin hankali wadanda basusan garahensa ba subhanalillah
Kinga AMBEESHAR dan Allah gar wannan yadaga hankalinki kisani ni'sam bandamu da sanin ni'waye ba saninki kawai yawadatar dani AMBEESHAR nikece komai nawa kisani zan'iya rayuwa batare da nasan ni'waye ba
Amma kisani wallahi sam bazan jure rayuwa bakiba bakuma zan'iya koyawa kaina ko zuciyata rashinki ba domin kuwa kece abokiyar rayuwata idan baki tonima bazan rayuba AMBEESHAR wallahi nasaba da soyayyarki matukar sabo
Wannan yasa sam ban'nasan duk abinda zaishiga atsakaninmu koyazamemana kalubale arayuwa garka damu Ammar insha Allah ni dakai zamu rayu atare kuma ba'abinda zairaba tsakaninmu da yardar Allah to Allah ya'amsamana sun'amsa da Amin
Adaran ranar AMBEESHAR takoma gida kasan cewar sam bata bukatar wata kulawar Doctor hankalinta gaba daya Yana gun Ammar akullum zancanta daya yaza'ayi Ammar yasami lafiya wannan dalilin ne yasa suka fara zancan tafiya India suka fara shirin tafiya Abba yayimasu biza dukansu bayan sati Uku jirginsu yatashi zuwa India
0 comments:
Post a Comment