*31*
Hanifa sam bata yi wani Karin kummalo me dad'i ba duk wani Abu da take yi tana yi a tsorace! Ganin yanda Nasir ya tsira mata idonsa yana tuhumatar dasu yasa gabanta ya tsananta fad'uwa simi-simi ta mi'ke ta futa, duk babu Wanda ya damu da futar ta sai da Ammi taji motsi kamar ana wanki yasa tayi magana kamar haka.
"Hanifa wanki me kike yi da safiyarn nan madadin kizo kiyi shirin makaranta sai ki kama wanki." Muryarta na rawa tace"Ammi hijab dina nake wankewa duk ya 'baci da fallatsin kwata." Ammi tace"Yau babu zuwa makaranta kenan."!? Shiru tayi tana cigaba da durzar hijab din. Abbu yace." Dole yanzu idan na futa in tsaya shagon malam Saleh na yanko mata yadin hijabai naga duk sunyi 'karanci." Nasir yace." Abbu ka bari zan siyo mata a kasuwa sunfi sauki." Abbu yace." To masha Allah Nasir Allah yayi maka albarka." Duk suke fad'i "Ameeen." Suka cigaba da hirarasu Hanifa na jinsu, sai da ta tabbatar da ta wanke hijab din sosai sannan ta hak'ura ta koma cikin dakin ta sanja kaya ta futo ta zauna a rumfar ji takeyi duk a takure, Nasir ne ya mike ya futa Hafiz ya bi bayanshi mintuna goma tsakani Ammi ta mike taje ta hadawa Abbu ruwan wanka kafin ya mike ya futa daga rumfar Hanifa suka bari ita kadai tana ta tunanin abunda ya faru ita da Khalid jiya ji tayi tsigar jikinta duk ta mike wani irin sanyi ya soma shigar ta tunda uwarta ta haifeta bata ta'bajin sha'awar d'a namiji ba sai akan Khalid sunkuyar da kanta tayi tana jin ruwan hawaye na kokarin zubo mata. Kamar daga sama taji muryar Nasir tsaye a kanta. Da sauri ta d'ago kanta tana kallonsa ganin idonta yayi yai ja yasa ya sassauta muryar shi yace." Zo muje ina son magana dake." Hanifa ta mike ta shiga daki domin dauko hijab shi kuma ya futa ya koma d'akin su. Cikin hijab ta futo suka ci karo da Abbu zai shiga band'aki ganinta cikin hijab yasa ya tambaye ta ina zataje muryar na rawa tace"Ya Nasir ne yake kirana." Abbu ya saki wani murmushi na jin dad'i yace." Kije gurin shi kinji ko Allah yayi muku albarka." A hankali tace"Ameen sannan ta wuce. Abbu kuwa cikin zuciyar shi yake tunanin yaran sun soma kulawa da junansu dama abunda yake so kenan. Hamdala yayi cikin zuciyar ya shiga bandakin bakinsa dauke da addu'ar da Annabi Muhammad Slw ya koyar.
Nasir na zaune shi kadai a dakin Hanifa ta shiga da sallama, ya nuna mata gurin zama yana kallonta cikin nazari yace. " Hanifa jiya ina kike je cikin dare k'arfe goma sha d'aya na dare."!? Sunkuyar da kanta tayi ba tare da tace komai ba. Muryarsa ya kwantar sosai yace." Kinyi shiru bayan kuma kece kikace idan na rufa miki asiri zaki fad'a min inda kikaje ki yarda dani babu Wanda zan fad'awa."
A hankali ta d'ago kanta ta kalleshi na minti biyu tayi 'kasa da kanta tace"Gidansu Asalamiyya naje."! Murmushi me ciwo Yayi kafin yace." Gaskiya ban yarda da wannan maganar taki ba, jiya fa naji jikin ki yana 'kamshin turare irin na maza ki fad'a mun Gaskiya kawai." Ranta ya d'an 'baci da maganar sa tace" Ya Nasir me kake nufi ne."!? Sassauta muryarsa yayi yace." Bana nufin komai dake sai alkairi." Tace" to ka yarda da maganar da na fad'a maka cewar daga gidansu Hanifa nake. " kai tsaye yace."To waye ya fesa miki wannan turaran na jikin ki me mugun 'kamshi."! Hanifa taji gabanta ya fad'i! shiru tayi domin bata da abuncewa Nasir ya cigaba da cewa"Idan baki fada min gaskiya ba to babu shakka Yanzu nan zan Sanar da Abbu abunda yake faruwa." Kuka ta fara yi masa ta kalleshi tana jin kamar ta gaggura masa mari tace"To ni na fad'a maka Gaskiya ta duk ka takura min me kake so nace maka ne."!! Murmushi yayi Wanda kana ganinsa kasan na takaici ne yace." Gaskiyar ki Sam bata samu muhalli a gurina ba shiyasa nake so ki fada min." Shiru tayi masa tana zumb'ura baki, mik'ewa yayi da sauri! Yana fadin"To tunda kin'ki bari kawai in je in fad'aw....... Kafin ya karasa ta mike da sauri! Ta tari gabansa tana share hawayen fuskarta tace" Wai Ya Nasir kana so ka had'ani da iyayena ne kome."! Girgiza kansa tayi yana jin tsananin 'kaunarta cikin zuciyarsa tace" To shine zaka fadawa Abbu." Yace." Ai kin ki fada min Gaskiya ne." Cikin ina ina tace"Ka koma ka zauna zan fad'a maka." Komawa yayi ya zauna itama ta zauna minti uku tsakani tace"Nifa ba gurin Wanda naje kamar yanda kake tunani kawai Ya Abbakar ne ya aiko kanwarahi Asalamiyya jiya wai inzo inji Mas........ Shiru tayi ta kasa karasawa Nasir yace."Kinyi shuru kuma." ?
"Wai inzo inji wannan Mawa'kin nan MASHAHURI wai yana sona."! Nasir yaji wani irin fad'uwar gaba ta rikito masa jin abunda Hanifar take fad'a a take ya nemi nutuwarsa ya rasa gumi ya fara zubo masa kamar ba Safiya kallonta yayi idonsa duk sun sauya saboda tashin hankali yace." Da kike je me yayi miki ? Abunda nake so kawai ki fada min kenan."
Gabanta na fad'uwa tace"Ni babu abunda yayi min." Bata ji zata iya fad'ar abunda Khalid din yayi mata.
Cikin b'acin rai Nasir yace." Amma kike yi k'amshin turaransa ni zaki rai nawa hankali Hanifaa."! Jin yanda yake d'aga murya sama yasa ta d'ago kanta da sauri tana kallonsa domin kwata_kwata bata so su Abbu suji komai ta lura Nasir din kamar baya Cikin nutsuwar shi._Ni ko nace dole ne ya hau ka ce saboda yana kishin ki.
Cikin wani sabuwar tsawar!Nasir yace." Zaki fada min abunda kukayi dashi ko sai na Zane ki a gurin nan."!? Kuka tasa zata futa daga d'akin yayi saurin tare hanya yana zare mata jajeyen idonsa cikin kuka tace." Ni ka matsa ka bani hanya na wuce kawai ka nayi min kallon 'yar iska da kake tuhumata kan wani abu daban." Marairaice fuskarsa Yayi kamar zaiyi kuka yace."Hanifa ki rufa mun asiri don girman Allah ki rike mun amanar kanki wallahi Hanifa tun kina zanin goyo Allah ya jarrabe ni da tsananin so da kaunar ki don Allah kar ki kware min baya Hanifa kar wani banza a waje ya yaudare ki, Hanifa kiji tausayin Abbu da Ammi da suke tsaye a kanki suka baki tarbiya don Allah kar ki zubar musu da mutumcin kar ki kunya ta su a idon duniya." Wani irin kallo ta watsa masa tana jin wani irin haushin sa da yace yana sonta danne 'b'acin ran dake taso mata tayi tace." Ya Nasir daga kawai ka ganni a waje cikin dare shine har ka fara zargina."!? Girgiza kansa yayi yana rike hannunta guda tayi saurin fuzge wa ta futa daga d'akin a fusace. "! Karo suka ci da Abbu ya futo daga wanka yaga fuskarta a murtuke kamar ma tayi kuka jikinsa ne yayi sanyi ya kira sunanta tsayuwa tayi tana sunkuyar da kanta. Abbu yace." Ke da d'an uwan naki kun fahimci juna ko."? Hanifa gabanta ya cigaba da fad'uwa shiru tayi Abbu yace." Kije idan na dawo anjima da yamma zamuyi magana dake." Da sauri ta shige daki lokacin Ammi na kicin fad'awa tayi kan gado ta fashe da wani irin kuka me cin rai itafa duk yanda za'ayi sai dai ayi amma baza ta yarda ta auri Nasir ba Sam baiyi mata ba wani 'k'ato dashi gashi gajere baki da ha'kora a bakinsa, kuka tayi tayi kafin taji motsin Ammi a dakin tayi lif! Ammi ta ji tana cewa"Hanifa futo ki tayani tsintar shinkafar nan ta yau ma bata da tsinta sosai Allah dai ya shiyasa yaron nan albarka."! Hanifa tasan kowa Ammi take nufi Nasir domin shine yake musu awo a gida shi kuma Hafiz tayi cefa ne watarana kuma Abbu yayi. Shuru tayiwa Ammi dake magana ita kuma sai tayi tunanin ko tayi bacci ne sai kawai ta k'yaleta ta cigaba da aikin ta.
*****
Nasir kuwa sai da yayi d'an karamin hauka a d'akinshi Kafin ya samu ya dawo normal wannan karon ma duk ya fashe glass din wayarsa gurin kallon pictures din hanifa da yanda yake matse wayar a jikinsa, wanka yayi yana jin wani irin daci a cikin zuciyarsa babu shakka yarinyar shaik ta shammace shi bai ta'ba tunanin zai tsinci kansa a cikin wannan yanayin ba, dole ya sanja shawara baya tunanin aure ko kadan a rayuwar sa amma tsananin sha'awar yin sex da yarinyar shaik ta hadda sa masa yake jin zai ita yin aure domin bukatar sa idan ta taso amma Sam bai yarda da haihuwa ba. Yana d'acin rai ya shirya jikinsa tsaf cikin wasu had'addun k'ananun kaya da suka futo masa da sufar sa ta namiji ya dauki wayarsa me bala'in tsada wacce tayi ratsa-ratsa sim card din ya cire ya jefar da wayar a gurun domin shi kam wayar ta tashi daga aiki a gurin shi dole yanzu idan ya futa ya siyi wata.
Kai tsaye part din Mamy ya nufa shiru parlor babu hayaniyar komai sama ya nufa Kafin ya shiga dakin Mamy din yaji hayaniya na tashi tsakanin iyayen nasa biyu
Tsayawa yayi bakin 'kofar yana sauraron tashin maganar su Mamynshi yaji tana kuka tana fad'in"Har kullum ina 'kara fad'a maka cewa Wannan rayuwar da kake d'ora yaron nan akai ba mai kyau bace ka kasa ganewa abunda nake so in fahimtar da kai anan shine duk irin tarbiyar da ka bashi to ita zai bawa yaranshi, ni na zama 'yar kallo a cikin gidanan kome na fad'a ba'ayi kullum abunda kasa shi kakeyi Yanzu gashi ka bashi lasisin da zai futa yayi zina har fad'a kake yi cewar yaje ya aikata tunda kana da KUDI duk wannan abun ba yanzu nake jiye muku ba sai nan gaba."! Mamy ta k'arashe maganar ta tana kuka gami da cigaba da had'a kayanta Alhaji Tijjani dake tsaye kanta yana sakin murmushi cikin isa da 'k'asaita gami da izza da giyar kudi yace." Duk wani Abu da kike fadarshi a banza yake a gurina abunda NASA kaina shi zanyi ke baki isa ki hanani inji dadina ba kuma yarona baki isa ki hanashi yayi abunda yake so ba don haka kiyi abunda zakiyi."! Mamy ta cigaba da kuka tana hada kanta tace" Zanyi kuwa abunda nayi niyya domin bazan iya cigaba da zama wani ciwo ya kamani ba saboda wannan bakin cikin da kake kunsa min." Alhji Tijjani ya buge babbar rigarsa ya mike da niyar tafiya yana fadin "Kifi ruwa gudu da kafarki zaki dawo domin kin San aurana dake babu saki." Yana gama fadin maganar shi ya bude dakin karo suka ci da Khalid dake tsaye hannunsa duk biyun cikin aljuhu kanshi a 'kasa yana tunani tunda ya taso bai taba jin iyayen NASA sunyi fada da tashin hankali ba sai Yau babu shakka yasan ba tun yau ba Mamynshi Tana mutukar hakuri da halin dad dinshi domin shi mutum ne me mugun son kanshi da yawa gashi da baud'addan ra'ayi.
Nasir ya d'aga kanshi ya kalli dad din nashi babu yabo babu fallasa ya bashi hannu suka gaisa yace."Dad me yasa Mamy ke kuka. "? Alhji Tijjani ns murmushi yace." Wai dole sai anyi maka Dole kayi aure kan nace a kyaleka shine take kuka har tana 'kokarin hada kaya zatayi yaji." Ya mutsa fuskarsa yayi yace." Dad muje dakin muyi magana kaji." Dad din ya kalli agogon hannunsa yace." Muje a gurguje banaso na makara domin zanyi wasu baki."Dakin suka koma Lokacin Mamy har ta gama had'a kayanta ta ta yafa mayafi suka shiga Khalid Yayi saurin rungume ta yana rarrashin ta tare da fad'in "Mamy plaesa stop crying ! Ki zauna zamuyi magana don Allah nima yanzu na janye 'kudirina na baya auran nake so." Mamy taji zuciyarta tayi sanyi don haka sai ta koma ta zauna gefan gado tana sauke ajiyar zuciya!....
*29/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:44 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI!_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, ke kuma da kika futar da book d'in kinci Amana!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124.... Binta Umar gt bank*
*32*
Alhaji Tijjani ya kalli Mamy dake sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi ya kauda kansa daga kanta yace." Tsofai-tsofai dake zakiyi yaji abunda bakiyi shi da 'k'uruciya ba yanzu zaki aikata shi kece baki sani ba aurana dake mutuwa ce zata raba." Idan da sabo Mamy ta saba jin ire-iren wad'annan kalaman daga bakinsa shiyasa Sam! Basuyi wani tasiri a zuciyarta ba. Khalid ya kalleshi tare da fadin"Dad kayi shuru ka bar maganar don Allah." Alhaji Tijjani yace."magana an barta my son Yanzu kai muke saurara a INA ka samo matar aure kuma 'yar wacece."!? Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in"Dad ubanta ba wani bane a garin nan kawai ni ita tayi min." Alhaji Tijjani yace." Za'bin ka shine nawa insha Allah zan sanya ayi mun bunkice sosai kan yarinyar da iyayenta Kafin muje Neman maka auran ta." Ya mutsa fuska Yayi yace." Dad nifa bana so aja lokaci me tsayi ." Alhaji Tijjani yace." Daga nan zuwa gobe insha Allah zan gama duk wani bunkice na ka kwantar da hankalin ka." Khalid yace."Nagode Dad." Alhji Tijjani ya futa daga dakin da sauri domin har ya wuce lokacin futar sa.
Mamy ta kalli d'anta tace"Myson da ni kuma nake cewa ko zaka auri 'yar gidan Momyn ka Mariya gobe insga Allah zata zo ma sai ku fahimci juna."
"Mamy pls don Allah kiyi hakuri ki bar maganar yarinyar nan domin ni Sam bata yi mun ba wannan da zuciya take so din ita nake son aura."
Mamy tace"Shikkenan Allah ya sanya alkairi yaushe zaka kawo mun ita mu gaisa."? Ji yayi gabansa ya fad'i da jin maganar Mamy din sai ya fara tunanin yaushe ma har sukayi sabo da yarinyar da har zai kawo ta gurin Mamy, take ya fara tunanin yanda zai bullowa al'amarin zuciyarsa tace" kana da kudi kawai abunda zakayi kaje gidan ka fara yi musu yayyafin KUDI komai ustazancin sa idan yaga naira sai ya watsar kudi sune 'kare magana.!
******
Kamar ko da yaushe ta futo cikin shirin zuwa makaranta Ammi tayi mata fatan dawowa lafiya, a nutse take tafiya Cikin sababbin uniporm dinta wanda Nasir ya kawo mata hatta da ni'kaf dinta sabo ne gidansu Asalamiyya ta shiga a gurguje suka gaisa da babarsu ko zama batayi ba Asalamiyya ta futo suka tafi. A hanyar su ne ta tafiya Asalamiyya tace"Wai Hanifa ya kukayi da MASHAHURI kuwa nagano yana tsananin sonki a 'kwayar idonsa." Hanifa ta ta'be bakinta tare da fad'in"Asalamiyya ki rabu dani da zancan wannan d'an iskan don Allah ni Yanzu addu'a nakeyi Allah ya cire min sonshi jiya da wani abun ya faru dani dake da Ya Abbakar kune sila domin da kyar na kwaci kaina daga hannunsa Ashe Dan iska ne." Asalamiyya tace"Kiyi hakuri don Allah wallahi ban San abunda za faru ba kenan nima Ya Abbakar ne ya takura min Dole sai naje na kiraki." Hanifa tace"Asalamiyya ke kawata ce tun ta 'kuruciya babu abunda zan 'boye miki wallahi inayi masa so Wanda bansan iya adadinsa ba amma yanzu bana jin zan iya auransa tunda hannunsa ya ta'bani naji na tsaneshi yanzu ina gani idan ya kama wata macan ma haka zaiyi mata." Asalamiyya tace"Dama tuntuni nake so ki fahimci cewar shi d'in ba tsararan ki bane Kiyi addu'a Allah ya za'ba miki miji mafi alkairi." Ajiyar zuciya ta sauke tare da fad'in"Insha Allah 'kawata ki tayani da addu'a.'' Suna wannan hirar suka isa makarantar.
Tsaf! Ya shirya da niyyar shiga studio kasala da sha'awa suka hanashi kwanciya yayi parlor yana tunani har Mamy ta sauko daga sama ta ganshi cikin wani yanayi tace"Myson ya ka kwanta ne ka shirya tsaf kuma ka kwanta. "? " Mamy kasala nake ji wallahi ko na shiga studio din babu abunda zan iya yi ni bacci ma nake ji." Mamy tace"To Allah ya sawake myson amma kar kayi bacci da yamma." Gyada kansa kurrum yayi yana lumshe ido Mamy ta wuce kicin taso ta fahimci abunda yake damun Dan nata.
K'arfe shida dai-dai suka futo daga makarantar a nutse suke tafiya ba kamar Hanifa da take tafiya kamar wata sarauniya ko me nata a nutse. Dai-dai inda yake parking din motar sa nan suka ga wata had'addaiyar mota sabuwa dal! Hanifa ta kauda kanta da sauri ta wuce tana d'agawa Asalamiyya hannu da ta shige gida, Khalid kuwa yana cikin motar duk yaga wuce warsu shima bai Dade da zuwa unguwar ba yana jiran futowar Abbakar........ Ta mirror din motar ya dinga kallon Hanifa yana sauke zazzafar ajiyar zuciya har ya daina ganinta a lokacin ne kuma ya koma ya kwanta kamar Mara lafiya Abbakar ya 'kwankwasa glass din motar ya bude masa tare da koma wa ya kwanta kallonsa Abbakar din yayi tare da fadin"Guy zamu je studio nan kuwa naga kamar kayi laushi wallahi.
Idonsa a lumshe yace." Abbakar yarinyar shaik ta Shammace ni ta rusa min duk wani tsarina ada Sam bana ra'ayin aure amma a halin yanzu saboda yanda sha'awar ta take so ta kashe ni nake ji zan iya aure yanzu ita kad'ai nake muradi Abbakar kaina duk ya 'kulle bansan ya za'ayi na 'bullowa al'amarin ba."
Abbakar ya kalleshi a nutse yace." Guy kana gani wannan abu zai yi kuwa? Nasan tuntuni akwai dabi! A tsakaninka da Ya shaik ina ganin ka tarowa kanka wata rigimar ne kawai." Lumsassun idonsa ya bude yana kallon Abbakar d'in yace." Na sani wallahi ni duk wannan baya damuna tunda ina da abunda zan toshe masa baki dasu so kawai ita yarinyar itace abunji ni kuma kasan zina ba halina bane da tuni an wuce gurin." Dariya Abbakar yayi yace." Baka da matsa da Hany domin ina da tabbacin cewar baza ta bujerewa soyayyar ka ba kawai dama shaik din ne abun dubawa amma kuma tunda kayi maganar kudi nasan kome zai zo da sauk'i.
Key din motar ya mi'ka masa ya karba yana 'yar dariya yace." Gaskiya nima nayi mamakin Hanya tun ba"aje koina ba taci galaba akan ka." Khalid ya Dan ya mutsa fuskar sa yana sakin siririn tsaki yace." Nifa ba wai sonta nakeyi ba kawai dai inaso in kawar da sha'awarta da ta dameni shikkenan abunda yasa kaga na matsu in aureta ita kuma bata isa ta sani na aikata zina ba." Gyda kai abbakar yayi yana kokarin kunna motar yace." Gaskiya ne guy ai Hany ta tsinci dami akala Allah yasa kar tayi wasa da damarta." Motar ya ja suka bar unguwar.
****
Hanifa kuwa sakewa tayi a cikin gida tana taya Ammi aikace-aikace har lokacin sallahr magariba a lokacin Abbu ya shigo gidan da sauri ta mike taje ta karb'i ledar da take hannunsa tana masa sannu da zuwa dafa kanta yayi yana murmushi yace." Hanifa Allah yayi miki albarka." Ammi ta futo daga kicin tana yi masa barka da zuwa buta ta mik'a masa domin tasan alwala zai d'aura Kafin yayi komai tunda lokacin sallah ne.
Ko da suka shiga studio an had'a komai Khalid ya tsaya da niyyar fara wa'karshi yaji muryar shi na rawa ya gagara nutsuwa dole tasa ya matsa daga gurin hade da cire abun dake mak'ale a kunnanshi ya jefar a gurin cikin wata katowar kujera ya zauna ya dafe kansa Cikin damuwa yake mamakin kansa wato yanzu yarinyar Shaik baza ta bari yayi komai na rayuwa ba Kenan. "? Why! Abbakar ne yazo ya dafa kad'arshi tare da fad'in" Yans Guy ka fara Abu kuma ka zauna please kasa dauriya cikin zuciyarka mana."! Shiru yayi masa kawai Abbakar din yq zauna kusa dashi yana rarrashin sa tsawon mintina goma kafin ya d'ago kansa a hankali yace." Muje gidansu yarinyar Abbakar ita kawai nake da muradi na gani a halin yanzu." Abbakar ya kalleshi cike da mamaki! Lallai yanzu ya tabbatar Khalid din ya fada komar son Hany dama shi yasan babu da NAMIJIN Da zai ga siffofin yarinyar ya iya daurewa zuciyarsa duk abunda Khalid din a halin yanzu bai ga laifinsa ba
A kasalance ya mi'ke Abbakar din ma ya mike yana d'an satar kallonsa ganin duk yayi wani laushi kamar ba Khalid din da ya sani ba namijin duniya muskili mai jan'aji amma ta farar d'aya soyayya na kokarin ta komar dashi malalaci! Gashi dai kiri-kiri ya shiga studio Amma ya kasa tsinana komai, ko a cikin mota ma ba wata hirar arziki suke ba,Abbakar din ne me jansa sa magana yana amsawa sama-sama, k'arfe Tara da kwata na dare sun shigo unguwar tasu, bayan sun futo daga motar Khalid yace." Kira Mobson yazo muje dashi ." abbakar ya futo da wayarsa ya kira Mobson din Wanda yake shirin tafiya club yana sanya da wasu 'yan iskan kaya, wando ne iya gwiwa sai k'aramar Riga da ta d'ame shi ya d'aura bandana a kansa gaban rigar dake jikinsa kuwa hoton mawa'kin nan ne wato macal jocson yace." Ni gani zan tafi club ne yanzu." Abbakar yace." Ka futo kawai gamu nan karasowa Mobson ya futo daga shagon sa ya kulle can ya hango su suna zuwa gurin shi ko.
Suna karasowa ya basu hannu suka gaisa Abbakar yace." Gidan ya shaik zamu je." Dariya yasa yana nuna Khalid yace." Guy ka shirya wani wulakancin kenan!? Hahahahaha yau kuma akan me zamu je masa."
Abbakar yace."Dallah ka nutsu malama neman aure zamuje." A zabure! Mobson yake kallonsu yace." Ban gane Neman aure ba? Hahahahaha. "! Ya kara sakin wata mahaukaciyar dariya wani kallo Khalid din ya watsa masa yace." Kaifa tsiyata da Kai rashin kamun kai dubi wata dariya da kake yi dallah malam muje mu." Mobson ya kunshe dariyar sa yana fadin "Muje to lallai yau zan sha kallo da dariya." Abbakar ya kalleshi a nutse yace." Na lura har yanzu baka fahimci inda abun yake ba, yau fa da wani sabon salo zamuje gidan ya shaik din don Allah ka nutsu kar kayi mana shirme domin yau bashi ne zai kaimu ba." Mobson yace." Wai don Allah da gaske ne Wannan maganar."!? Khalid yace." Eh ko akwai wani aibu ne."!? Girgiza kai Mobson yayi yace." No! Kawai dai naga abun ne akwai matsala kai ko Abbakar din kunsan ko a mafarki Shaik bazai tsaya yw saurare ku da wannan maganar ba amma dai tunda kunce zakuje muje in raka Ku."!
Tare suka rankaya suka nufi gdan kamar zuwan su na farko lokacin da suka je Abbu ya koya musu ilimin jima'i.
*30/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*36*
Khalid ne ya d'auki Abbakar a motar dady d'insa suka wuce gida shi kuma Alhaji Tijjani da abokinsa sai bayan sunyi sallahar Insha a cikin kasuwar sannan suka nufi gidan Abbu cikin motar Alhaji Lawan din.
Abbu na zaune a 'kofar gida kamar yanda ya saba hannunshi rike da alk'urani mai girma yana haskawa da torchlight 'karama karatu yake yi cikin nutsuwa da dadin sauraro can gefe suka yi parking din motar duk suka futo suna baza babbar Riga tuni k'amshin turaran su ya dume gurin kana ganinsu kasan Alhazawa ne, Abbu kansa a kasa yake sha'ko k'amshin turaran da yaji jikin Alhaji Tijjani d'azu a hankali ya d'ago kansa Wanda yayi dai-dai da karasowar su gurin. Sallama suka yi Abbu ya kai karshen ayar da yake kai ya amsa musu yana me rufe alk'uranin dake hannunsa gurin zama ya nuna musu dake irin k'atuwar daddumar nan ce Alhaji Lawan ya tube takalmin sa a nutse ya zauna shi kuwa Alhji Tijjani kamar ba zai zauna ba domin bai so Abokin nasa ya zauna ba a cewar sa daddumar bata kyau zasu iya daukar Datti da kyar dai ya zauna yana dauke kansa domin har yanzu yana jin zafin Abunda Abbu yayi masa.
Cikin kamala da dattako Alhaji Lawan ya mik'awa Abbu hannu suka yi musabaha yana tambayar sa mutanan gida abbu yace." Kowa lafiya lau Alhmdullahi." Hannu ya mikawa Alhaji Tijjani tare da fad'in"Barka da dare Alhaji. " Alhaji Tijjani ya mik'a masa hannu yana fadin "Barka dai Arrama kaga mai bakin naci ya kara dawowa ko."!? Murmushi Abbu yayi kawai ya maida hankalinsa kan Alhaji Lawan da yake masa magana.
" malam mun sake dawowa a karo na uku gurinka muna kara Neman alfarma a gurin ka ba don halinmu ba Malam idan har ka bamu yarka zamu rike maka ita da amana kamar yanda addini ya tanada Gaskiya banji dad'i Abunda ya faru d'azu ba ka dauke she abusa kuskure Alhaji duk yayi min bayanin komai kuma na fahimta shima na fahimtar dashi, Hak'ika Allah ya jarrabi yaron nan da soyayyar yarinyar ka don girman Allah ka duba al'amarin nan Arrama."! Alhji Lawan ya k'arashe maganar sa cikin kwantar da murya.
Abbu yaji wani irin nauyin mutumin sosai yake jin nauyin ya d'ago kansa ya kalleshi har ya samu damar fadamasa abunda yake bakinsa shiru yayi yana tunani kansa har yanzu a kasa, Alhji Lawan yace."Aramma kar kayi kokwanto akan al'amarin insha Allah akwai alkairi a ciki muna sauraran amincewar ka."
Abbu ya dago kansa a nutse yace."Alhaji wallahi kafi k'arfin kazo Neman Alfarma a gurina na kasa yi maka ita mutukar ina da iko da ita wallahi idan da babu maganar Nasir a kasa to babu shakka zan bawa yaron nan Hanifa ya aura duk da cewa tarbiyarsa bata yi min ba, to amma babu yanda Allah baya shirya bawansa watak'ila ta dalilin auran ma sai ya shiryu ya gyara halayen sa."! Alhaji Tijjani yaji kamar ya shake Abbu wato saboda samun dama a gabansa yake kokarin aibata d'ansa kawai saboda sunzo Neman alfarma a gurin shi babu shakka da badon wanann al'amarin ya ratsa ba da babu abunda zai hanashi ya daure shi saboda yana kokarin shiga hurumin da bana shi ba, a ganinshi kamar Abbu yana so yayi danshi baki.
Abbu ya cika da cewa"Alhaji ka dubi girma irin na al'kawari kayiwa magana ta kyakyawar fahimta akwai yaron yaya ta Dana rik'e ya girma a hannuna ya nuna min yana son Hanifa tun tana k'arama yake dawainiya da ita Nasir babu abunda zai nema a gurina na hanashi nine uwarshi nine ubanshi tunda na fahimci haka nayi masa alk'awarin aura masa Hanifa saboda na yarda da tarbiyar da na bashi, shi yasan da wannan alk'awarin ni nasa ni mahaifiyar sa ta sani hakanan mahaifiyar hanifa ta sani garin mu da duk wasu dangina sun San da wannan alk'awarin ita kanta Hanifar na kira ta na shaida mata kudirina akanta ta sani kaga yana da kyau in cika wannan alk'awarin da na daukar wa yaron nan domin kubuta daga fushin ubangiji ina yi wa wannan yaron fatan alkairi a rayuwar sa Allah ya mu sanya masa da wata wacce tafi Hanifa komai na rayuwa."
Shuru gurin yayi bayan Abbu ya gama maganar shi tabbas maganar da yayi abun dubawa ce, Alhaji Lawan yake maganar cikin zuciyarsa kafin ya d'ago kansa ya kalli abbu zuciyar sa duk babu dad'i yace." Arrama abunda nake so ka fahimta anan shine ita rayuwar nan da kake gani tana tafiya ne da ZAMANI tabbas Annabi Muhammad (Slw) ya hore mu da zabawa yayan mu miji suna 'yan mata wato idan zamuyi musu auran fari, a shekarun baya iyayanmu da kakaninmu duk irin wannan auran akayi musu har muka zo wannan duniyar, mai cike da rud'u Abunda nake so ka fahimta anan shine baza ka hada wancan lokacin da wannan ba domin Zamani ya sauya irin wannan auran da kake kokarin hadawa yana iya lalata zumunci tunda abunda na fahimta a maganar cewar ita yarinyar taka baka bata za'bi ba baka tambayeta shin tana son zabin da kayi mata ko kuwa bata so domin samun nutsuwar ta, yaran yanzu da nada ba daya bane idan shi yana so ita kuma bata so kaga akwai matsala babba kofa anyi auran za'ayi ta samun matsala kamar yanda kasani nima na sani cewar babu abunda yake damun Al'umma a halin yanzu irin yanda zamantakewa ta aure ta lalace kuma al'amarin duk ya samo Asali ne daga faruwar irin wannan Abu damu iyaye muke yi, arrama yana da kyau ka zauna da Yarinyar nan ka tambaye ta ra'ayin ta kan zabin da kayi mata saboda gudun afkuwar wata matsalar wacce ba'a fata.
Abbu yayi shuru yana tunanin maganar Alhaji Lawan baya shakka da irin tarbiyar da yayi wa Hanifa kuma yasan baza ta bashi kunya ba kamar yanda ta fada masa zata yi masa biyayya shi yasan nan gaba zata fi kowa murna da jin dad'i bayan ta mallakin hankalin kanta zata San baza zaben tumun dare yayi mata ba.
Yace."Alhaji duk naji maganar insha Allah zan zauna da yarinyar muyi maganar da ita idan ta nuna bata son Nasir zan bukaci ta kawo min zabin ta idan ya kasance shi wannan yaron naku ne to insha Allah zaku ji daga gare ni."
"Alhamdullahi."! Alhaji Lawan ya fada da murmushi ya fuskar sa yace." Mungode K'warai arrama kuma muna sauraran ka daga nan zuwa wane lokaci."!? Abbu yace." Daga nan zuwa gobe insha Allah."
Alhaji Tijjani ya sauke ajiyar zuciya tunda suke maganar sai yanzu ya samu sassaucin a zuciyar sa ya kalli Abbu a nutse yace." Muna saurare domin yaro yace baya bukatar aja lokaci in yaso sai ka yanke sadakin yarinyar ka." Takaici bai bari Abbu ya bashi amsa ba kawai hannu ya mik'awa Alhaji Lawan suka na sallama cike da mutumuta juna."
[1/3, 10:30 AM] .: Bayan tafiyar su Abbu ya jima a gurin yana tunanin maganganun alhaji Lawan sosai suka shiga jikinsa kamar yanda ya dauki alk'awarin zai zauna da Hanifa to babu shakka zai zauna da ita gobe da safe domin yaji meye ra'ayin ta a game da auran Nasiru. Yana kokarin shiga gida lokacin su Nasir din suka dawo tare suka shiga cikin gida Nasir hannunsa rike da daddumar Abbu. Ammi tayi bacci hakama Hanifa tayi bacci bayan ta gama koke-koken ta.
Alhaji Tijjani na Sanar da Khalid abunda abbu yace take yaji wani irin sanyi ya dura a zuciyarsa da yana zaune yana d'acin rai Mamy sai lallabashi takeyi yaci abunci yana kaucewa murna tasa shi ya zage ya cika cikinsa da abinci yana hira da iyayen NASA har da dariya Mamy ta dinga mamakin sa sai dai tayi shuru kawai tana addu'ar Allah yasa yarinyar rabonshi ce don ta lura yaron nata bai iya so ba, Alhaji Tijjani kuwa yaji dad'i sosai da yaga Khalid din ya saki jikinsa har sa dariya, dama shi babban jin dadin sa a duniya walwalar danshi don bai fiye damuwa da damuwar yayan shi mata ba sai da ita Mamy itace me nuna kulawa a kansu.
Anan parlor suka barshi yana kallo Sam ya'ki komawa part dinshi, kallon wa'kokin turawa yake wata mawa'kiya Nicky minaj tana wa'aka sosai yake son yarinyar da muryar ta mik'ewa yayi zaune yana kallon siffar jikinta gaban shi ya fad'i Cikin rawar Hannu ya dauki wayarsa ya fara duba pictures din Hanifa tsarin jiki da yanayin fadin 'kugu gami da cikar nonowa duk irin nata ne sai da Hanifa tafi ta fari gami da girman idano wata lafiyayyar ajiyar zuciya ya sauke a take muguwar sha'awar sa ta motsa masa pictures din yake kallo jikinsa na tsuma jijiyarsa ta mike da 'karfin ta sai motsi take masa, kwanciya yayi kan doguwar kujera yana rintse idonsa tare da hade kafafunsa guri daya nishi yake saki yana kara matse wayar a k'irjinsa, wasu zafafan hawaye ne suka fara zubo masa ta gefen ido, cikin futar hayyaci ya mi'ke zaune hade da jefar da wayar kan kujera kanshi ya dafe duka sa hannunwan sa biyu har yanzu idonsa a rintse yake yafi minti talatin Cikin wannan halin kafin ya fara dawowa dai-dai ya mike da sauri ya futa tsit!!! Harabar gidan sai haske ko ina part dinshi ya bude ya shige kai tsaye toilet ya nufa ruwan sanyi ya dunga kwarawa a jikinsa yana makyarkyata gashi dai lokacin anyi ruwa an dauke gari ya dauki sanyi haka Khalid ya dinga zubawa jikinsa ruwa ya futo daure da towol zubewa yayi kan bed yana numfarfashi blanket ya jawo ya rufe jikinsa gabadaya har fuskarsa Kafin kice kwabo jikinsa ya rikice zazzafan zazzab'i ya rufe shi!
****
Jiki a sanyaye take yi komai tunda ta tashi taki sakewa da kowa gabanta sai fad'uwa yake yi Karin kummalo ma kamar bata so haka tayi kamar yanda ta saba bayan taga ma karyawa ta mike zata shiga daki Abbu ya dakatar da ita, komawa tayi ta zauna tana jin sabuwar fargaba... Mik'ewa yayi yace." Hanifa kizo d'akina yanzu zamuyi magana." A hankali tace."To Abbu." Wucewa yayi Ammi tace"Zaman me kike yi munafuka ki tashi ki bishi kuma kiyi masa biyayya Hanifa ni yanzu lamarin ki ya soma bani tsoro."
Jiki a sanyaye ta mike tabi bayan Abbu tana mamakin Ammi wai yau ita take kira da munafuka."
Sosai taji ciwon abun har sai da hawaye suka zubo mata saurin gogewa tayi ta shiga dakin Abbu bakinta dauke da sallama. Yana zaune gefan katifa ya amsa tsuguna wa tayi bakin kofa yace." Karaso ciki sosai ai sirri zamuyi." Hanifa ta matsa ciki sosai tana sinne kanta gabanta sai dukan uku-uku yake. Shiru na minti biyu Abbu yayi gyaran murya tare da fad'in"Hanifa ina so ki fad'amin gaskiyar abunda zan tambaye ki kar ki munadurce ni kar ki kuma munafurci kanki ni mahaifin kine me kaunar farin ciki, ina so duk wani abunda yake ranki ki fadamin shi kinji ko."!? Daga kanta tayi tare da fadin"Insha Allah Abbu zan fada maka." Abbu yace." Alhamdullahi haka nake son ji daga gare ki, shin Hanifa meye ra'ayin ki a game da auran ki da Nasir ma'ana kina sonsa ko bakya sonsa bana so daga baya kizo kina kuka dani duk ni nasan bazan zab'a miki abunda zai cuce ki a rayuwa ba duk inda nagartacan namiji yake Nasir ya kai shiyasa nake miki sha'awar auran sa INA so ki fadamin gaskiyar abunda take zuciyar ki." Shuru tayi batace komai ba yace." Ke nake saurare." Tayi shiru nan Abbu yace." Kar kiji nauyin komai ki fada min gaskiya." Muryarta na rawa tace"Abbu ni bani da zab'i kuma bani da ra'ayi sai naka nasan hazak'a zab'a min abunda zai cutar dani ba duk abunda ka yanke a kaina dai-dai ne." Abbu ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Alhmdullahi nagode Allah Hanifa Allah ya shi miki albarka nagode irin biyayar da kike min insha Allah kema yayanki zasu biki kuma insha Allah zakiyi alfahari dani a ko ina kike kuma zakiyi alfahari da zabin da nayi miki, dama maganar kenan ki tashi ki tafi." Hanifa ta mike da jiki a sanyaye ta futa daga d'akin...... Ammi ta kalleta lokacin da take shigowa dakin ganin yanayin fuskarta yasa ta aje tsintsiyar da take hannunta ta nufi dakin Abbu. Hanifa na ganin futar ta ta fashe da kuka tana damk'e bakinta da hannuta domin kar sautin kukan ya futo tunani takeyi yaya ma za'ace tace da Abbu bata son zabinsa mutumin da ya sadaukar da rayuwasa duk a Kansu ta gwammace son Khalid ya kashe ta kan ta fadawa Abbu cewar bata son Nasir su idan sun fahimci haka daga gurina sai su aura mata Wanda take so.
_Hanifa kinyi ganganci_
******
Ganin har k'arfe Tara da rabi Khalid bai futo ba yasa Mamy ta nufi part d'insa hannuta rike da wayarta tana kara gwada kira domin tun d'azu take kiran wayoyinsa duk a kashe dake a bude ya bar kofar dakin yasa tana turawa ta bude kai tsaye bedroom d'insa ta nufa nan ma tana tura kofar ta bud'e can ta hango shi kudundune kan bed da sauri ta karasa gurin tana fadin"Myson yaya ne blanket din take kokarin cirewa ya bude jajayen idonsa yana kallonta ganin yanda jijiyar kansa ta mike tayi rada-rada tasa hankalinta ya kara tashi ta cire blakent din tana ta'ba jikinsa taji zafi kau! "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Myson me yake damun ka."!? Kansa ya nuna mata da hannunsa. Hannu na rawa ta fara laluben numbar family dactor masu wayar is switch up. Cikin damuwa tace" Myson tashi ka sanya kaya mu wuce hospital zafin jikin nan ka tayi yawa." A hankali yace." Mamy ki barshi kawai zazzab'i ne kuma Masha magani zai sauka." Girgiza kanta tayi tace"ban yarda ba kawai ka tashi muje asibiti a duba ka." Mik'ewa yayi yana ya mutsa fuska yace." Mamy Bari inyi wanka tukkuna." Cikin damuwa "Tace ka sanya rigarka kurrum muje idan ka dawo kayi wankan."
"Mamy k..... Ka tseshi tayi ta hanyar daga masa hannu, yasan halin mamyn sa da damuwa shi kuma abunda yasa baya son ya mike a gabanta saboda babu kaya a jikinsa sai k'aramin towol kuma har yanzu joystick d'insa a tsaye take sai dai ba kamar jiya ba shi kanshi yasan wannan zazzab'in da yake yi ba na komai bane sai na tsantsar sha'awar da ta dame shi, Cikin sa'a kuwa ta mike da sauri wardrobe d'insa ta bude tana Ciro masa kaya shi kuma yayi wuf ya dira daga gadon toilet ya bude ya shige da sauri. Mamy ta juyo da sauri tana kallon kofar toilet din girgiza kanta tayi ta rufe wardrobe din bayan ta dauko masa Riga da wando Pakistan irin na maza zama tayi gefen bed din tana jiran futowar sa.
*3/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*40*
Khalid kuwa 'kin sakin jikinsa yayi a motar Hafiza sai jansa take da magana Yayi mata banza haushin abunda Mamy tayi ma yarinyar Shaik yake ji har yanzu don haka Mamy nayi parking ya bude motar ya futa kai tsaye part d'insa ya nufa Mamy da Hafiza suka bishi da kallo girgiza kai Mamy tayi ta bude mota ta futo
Yana shiga dakinshi ya fara neman wayar dady nashi cikin sa'a ya samu wayar ta shiga ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace." Dad ya kasuwar ? Tun d'azu ake Neman ka a waya ba'a samu ba."Yace." Ina tare da baki ne Myson amma yanzu sunyi sau'ki yanzu zan dawo gida Insha Allah. "
"Dady ina fatan jin alkairi daga bakinka game da maganar Hanifa." Alhji Tijjani ya dawo nutsuwar sa sai yanzu ya tuna da maganar wallahi jama'a sun sanya ya manta yace." Myson ka kwantar da hankalin ka insha Allah zamu koma Yanzu ni da Alhaji Lawan insha Allah. " ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata irin fargaba domin zuciyarsa bata bashi cewar za'a samu nasara Yace. " Shikkenan dady ina sauraran Ku." Kashe wayar yayi ya kwanta rigingine ya kurawa calling ido yana tunani abunda ya faru tsakaninsa da ita a d'azu
Alhji Tijjani kuwa bayan sunyi sallahr Isha'i kamar jiya suka nufi gurin Abbu yau yana cikin gida sai da suka aika yaro akayi musu sallama dashi abbu bai bata lokaci ba ya futo dama ya tsammace su suka gaisa cikin mutumci Alhji Lawan yace." Arrama mun dawo domin karb'ar sakamako. "
Shiru abbu yayi na minti biyu yace." Alhji kuyi hakuri don Allah kamar yanda na fada cewar zan zauna da yarinyar jiya to na zauna da ita kuma ta tabbatar min da cewar tayi na' am da zab'i na saboda haka ina yiwa Wannan yaron fatan alkairi."
Alhji Tijjani yaji wani irin gumi na zubo masa yana mamakin Ashe a duniya akwai Abunda zaice yana so ya kasa samunshi. Alhji Lawan yace."To arrama babu komai Allah ya sanya alkairi a ciki mungode." Yanda ya fadi maganar zaka San ransa a bace yake.
Alhji Tijjani kuwa bakinsa mutuwa yayi wani irin kallon tsana yake watsawa Abbu din ya buge babbar rigarsa ya bar gurin Alhji Lawan kuwa ya tsaya suna sallama da Abbu kafin ya biyo bayansa.
Dady jikinsa babu kwari ya shiga gida duk da cewa kasuwa tayu kyau an samu kudi sosai amma yana fargabar tunkarar Khalid din da wannan maganar Mara dadin ji.
Tun kafin ya shiga parlor ya fara jiyo hayaniya Maganar ta ya tsinta inda take fadin"Khalid indai nice na haife ka to ban amunce ka auri wannan yarinyar ba Ka auri NASIRIN idan baka sonta to kaje ka nemo wata yarinyar domin wannan yarinyar da kake so bana Allah da Annabi bane ko kunyi aure bazaiyi karko ba saboda kun gama ta'ba junan ku a waje idona yq nuna min na gani dama so nake mu dawo gida ayi wacce za'ayi domin wannan Koron ina ji ina gani baza'a yi Abunda bai dace ba.
Cikin 'bacin rai Alhji Tijjani ya shiga ciki yana kallon yanda Mamy din tayi tsaye kan Khalid tana zuba masa masifa Yace." Wai ke Mamy me yake damun ki ne."!? Duka suka juyo suna kallonsa domin basu yi tsammanin shi ba Khalid ya dago idonsa Wanda ya kada yayi jazur yana kallon Mahaifin nasa, Dad din ya cigaba da cewa"Wannan yarinyar da kike ta magana akanta idan matarshi ce sai ya aurta idan kuma ba matarshi bace bazai aureta ba gwarama ki kwantar da hankalin ki akan lamarin ko da zina ya aikata da ita yana da damar da zai aureta kuma ke baki isa ki hana auransu yayi albarka ba ki tasa yaro a gaba kina zuba masa fad'a kamar me? To ki shiga hankalin ki."!!!!
Mamy ta fashe da kuka tana fadin"Dady Abunda zakace kenan! Duk abunda na fada banyi karya ba kuma ga Hafiza nan shaida mungansu da Idan mu yayi k'aryar bashi da lafiya yarinyar tazo har asibiti sun kule kofa da kyar na samu ya bude kofar shine ya 'boye yarinyar a band'aki ."! Ko ba haka bane."!? Ta fada tana kallon Khalid din da kanshi yake sunkuye a kasa wani irin kyarma jikinsa yakeyi na tsananin b'acin rai ya rasa yaushe Mamynsa ta zama burkitacciya.
Alhji Tijjani ya zauna kusa da Khalid din ya dafa kafadansa tare ra fadin"Abunda mahaifiyar ka ta fada gaskiya ko ba gaskiya bane." ?
Kukan Mamy ya tsananta wato bai yarda ma sai ya tambayeshi Khalid ya dago kanshi sake Sara masa yace." Dad duk abunda mamy ta FAda haka ne." Gyada kai dady yayi yace. " mai ya kai ka hospital. " A hankali yace." Dad Mamy CE wallahi jiya na Dan kwana da zazzab'i amma kafin safiya ya sauka shine mamy ta matsa dole sai munje asibiti na samu Dr ya sa min ruwa naji kwari a jikina yanza." Gyada kai dad din yayi yace." Ya akayi kuka kulle kofa da yarinyar mutane duk dai nasan ka baka sha'awar aikita zina amma shaidan zai iya rijayar ka."
Cikin damuwa Yace. " Dad yarinyar ce tazi duba jikina a lokacin to jin muryar Mamy din yasa na kulle kofa na b'oye ta a toilet saboda sanin halin Mamy din ba ta kaunar t....... Ya katse shi ta hanyar fad'in"Myson da gaske yarinyar na sonka shine mahaifinta yace ya zauna da ita tace ya zab'a mata miji a taikace dai mahaifinta Yace kayi hakuri ka nemi wata domin yayi mata miji Dan uwanta kuma itama yarinyar ta amunce da zabinsa ."
A zabure! Yace. " Wallahi 'karya yake dad yarinyar shi bata da miji sai ni duk abunda ya fad'a muku yayi karya dady yarinyar itace ta fara nuna min so tun bana sonta na zo INA sonta kuma ko d'azu ta kara tabbatar min da haka tana kuka tana komai muka rabu da juna."!
Alhji Tijjani yayi kasake yana tunanin wannan lamari Yace."Yanzu ja fahimci cewar wancan mutsiyacin mutumin me gemun banza shine bayaso ya baka yarshi yarinya na sonka shi kuma yana so ya rusa muku farin ciki saboda mugunta Wallahi da ina da hali sai na daure shi."!
Ya k'arashe maganar a zafafe!
Mamy kuwa komawa tayi ya zauna tana hamdala cikin zuciyata a ganinta tunda uban yarinyar bayaso to suma dole su hak'ura.
Cikin wani irin yanayi na tashin hankali ya mi'ke tsaye kokarin futa yake duk suka bishi da kallo sai da ya kusa zuwa bakin kofa ya fad'i a gurin, cikin tashin hankali Alhji Tijjani yayi kansa yana salati.
Mamy da Hafiza suka karasa gurin cikin tashin hankali Waje ya futa da sauri ya kira daya daga cikin securitys daukar shi sukayi suka futa, dravar ne ya bude motar suka saka shi ciki Alhji Tijjani ya shiga ciki da damuwa suka futa daga gidan Mamy da Hafiza suka shiga mota cikin damuwa suka bi bayansu.
Hafiza hawaye take sharewa tana fadin"Mamy kinga irin abunda nake ka fada miki ko wannan fad'uwar da bro yayi tana nufin abubuwa da dama don Allah ki dinga hakuri Abu komai a sannu a hankali."
Mamy shiru tayi kawai zuciyarta duk babu dad'i motar Dady din take bi wacce take wani irin gudu kan titi.
Kai tsaye pravite hospital suka nufa emagancy aka nufa dashi Alhji Tijjani sai kaiwa yake yana kawowa a gurin yana ganin kamar Matar tashi ce silar faruwan komai wata zuciyar tace masa babu mutumin da ya jefa rayuwar danka cikin bala'i da damuwa sai wancan me gemun banza Wanda ya kasa fahimtar Abunda yake faruwa a take yaji wata irin tsanar Abbu ta kamashi cikin zuciyarsa yake fadin har in dai wani ciwon ya kama danshi ta sanadiyar wannan Abu to babu shakka sai yayi shari'a dashi.
Ko dasu Mamy suka iso asibitin Alhaji Tijjani wuta ya bude mata sosai yake zazzaga mata bala'i yana "Fad'in" Idan kuka kasa zuciyarsa tayi buga dake da wannan mutsiyacin mutumin wallahi sai na daure Ku."!
Mamy dai shiru tayi jikinta duk yayi sanyi yanzu kuma ta fara nadamar abunda ta aikata wa Dan nata hawaye ta share lokacin da ta tuno maganar da ya fada mata a asibiti d'azu da yake cewa"Mamy idan kina bukatar kwamciyar hankalina ki so abunda nake so shine zaki ga walwala ta da farin ciki." Hawaye ta share cikin sarewa da al'amarin, ya kalleta da fuska a turbune yace." Baki fara kuka ba tukkuna Wallahi wani ciwon ya kamashi sai na bata miki rai."! Hafiza da taga dady nasu yana daga murya tayi saurin karasawa kusa dashi tana rarrashin sa da kalamai masu dad'i da kwantar da hankali.
Tana kuka tace" Dady me Dr yace game da Khalid din."
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yar tasa da damuwa a fuskarsa Yace. " an shiga ciki Dr bai futo ba tukkuna amma numfashin sa ya dauke gaba d'aya." Hankalin su ya kara tashi Mamy sai ta fara addu'a Cikin zuciyarta......Hafiza kuwa hawaye ta fara sharewa cike da tausayin Dan uwanta.
Dr ya futo ya kira Alhji Tijjani wani ofis suka shifa Dr ya cire glass din dake idonsa Cikin damuwa ya kalle shi yace." Alhaji gaskiya an auna arziki sosai domin Yaron ka jininsa yayi sama irin Wanda ba'a so tsananin damuwa da fargaba gami da rud'u sune suka haddasa masa shiga wannan halin gashi dama babu cikakkyar lafiya a tare dashi shiyasa ya da ya mike jiri ya yar dashi yana da kyau a kiyaye duk wani Abu da zai bata masa rai ko kuma ya sanya shi damuwa don gaskiya banyi tunanin zai farfad'o ba tare da wani shashen na jikinsa ya samu matsala ba amma cikin ikon Allah ya farfad'o komai nashi yana aiki sai dai matsanancin ciwon kan da yake damunsa insha Allah shima zai daina in har za'abi kaidojin komai."
Alhji Tijjani yace." Insha Allah Dr Yanzu ya jikin nasa."!? Dr yace." Alhmdullahi ya samu bacci yanzu ka kwantar da hankalin ka." Ajiyar zuciya Ya sauke yayi wa Dr godiya ya futa.... Kan Mamy din ya tsaya muryarsa babu sauki a cikinta yace." Maza Ku koma gida domin zaman Ku a gurin nan bashi da amfani. "
Mamy ta d'ago jajayen idonta tana kallonsa cikin rawar baki tace." Ya jikin My..... Kafin ta karasa ya daka mata wata irin tsawa a harzuke Yace." Ba'a sani ba! Duk bake ce kika zama silar faruwar komai ba, zaki tambayi jikinsa yanzu da kin damu dashi ai baza kiyi masa abunda zai jawo masa hawan jini ba."!
Hankali a tashe take kallon mijin nata yanzu yaron nata ne yake da hawan jini ko su da suke manya Allah bai Dora musu ba sai shi tasan hawan jini mugun ciwo ne dole tayi taka tsan-tsan..... Bala'i yake zuba mata sosai hade da cin mutumci Mamy tayi da ta sanin abunda tayi ita kuwa Hafiza Mamy ta kama suka futa da gurin tana share hawaye da tasan wannan tashin hankali zata zo ta tarar da bata zo gidan ba, Abunda take fada kenan cikin ranta, haka suka koma gida zuciyonsu duk babu dad'i lokacin Mus'ab ya Dade da yin bacci gurin me aikin Mamy Habiba.
A furgice ta tashi tana zare ido cikin dakin! Duhu d'umdum kasancewar basa kwana da hasken wutar lantarki duk sun kashe kwaya kwayan gidan... Hannunta na kyarma ta lalubo k'aramar torchlight din da suke haskawa ta kuna tana kallon dakin jikinta sai rawa yake yi ga wata irin fad'uwar gaba da take ji, takure wa tayi guri guda wasu irin hawaye suka fara biyo kuncinta
Munmunan mafarki tayi Wanda yayi mutukar gigita ta da bata tsoro wai Khalid ya mutu gashi kwance a makara mutane sun dauke shi zasu kaishi makabarta lokacin ne ita kuma ta futo daga gida tana kuka tana rirrike makarar tana fadin"Kar ku rabani dashi bamuyi aure ba bai mutu ba!! Don Allah Ku sauke shi Wallahi be mutu baaa."!!! Kuka take sosai tana rirrike makarar kawai sai taga Abbu ya ratso cikin jama'a yazo yana Jan hannunta ita kuma tana turjewa tare da rike makarar Abbu ya'ki cewa komai sai janta yake a lokacin ne tace"Abbu ka sake ni kar ka rabani da mijina."!!!!!! Muryar Abbu din taji yana fadin"Hanifa kinga mijin ki nan."! Tana juyowa taga Nasir yana yi mata murmushi Abbu ya kama hannunta ya hada da na Nasiru din yana fadin"Hanifa wannan ne mijin ki!!!! Lokacin ta farka a furgice!!
Kanta ta sanya tsakanin k'afafunta gabanta na wani irin bugawa Yanzu idan Khalid ya mutu da gaske ya zata yi da rayuwar ta, zuciyarta tace sai ki hak'ura kiyi masa addu'a kawai girigaza kanta tayi kamar wata mahaukaya ta diro daga kan gadon waje ta futa ta tsaya tsakar gida tana zare ido k'arfe 3 na dare gari yayi tsitt! Hanyar futa ta nufa, tana tangadi! Nasir yaji motsi a soro da sauri ya kunna torchlight d'insa ya mike zaune yana fadin "Waye anan."!? Hanifa ta dawo hayyacin ta soron take bi da kallo tana tunanin ya a kayi tazo cikin gidan tayi nufin komawa da sauri.lokacin ne shi kuma Nasir ya futo yana hasketa da torchlight dinsa.
Kallon juna sukayi gabansa ya fad'i ganin yanda idonta sukayi jazur duk sun wani juye bakinsa na rawa yace." Hanifa ina zakiji ne ? Me ya futo dake yanzu? Kafin tayi magana suka ji muryar Abbu yana fad'in "Nasiru menene ya faru." ? Hanifa ya gani tsaye a jikin kofar futa. Cike da mamaki yake kallonta. Nasir yace." Abbu babu komai kawai ina kwance naji motsi ina futowa naga tana kokarin bude kofa ta futa." Abbu ya kalle ta cikin nutsuwa baice komai ba yaja hannunta suka nufi cikin gidan ya juyo yana kallon Nasir da yayi kasake a tsaye yace"Kaje ka kwanta Nasiru da safe zamuyi magana." Nasiru ya shiga dakinsu yana mamaki abun.
Ammi na tsaye a tsakar gida Abbu ya shigo da Hanifa kai tsaye dakin sa ya nufa da ita ita kuma sai zazzare ido takeyi kamar ma bata cikin hayyacinta.
Abbu ya zauna da ita gefen kati Ammi ta zauna jikinta duk a sanyaye Kallonsa tayi tace"Abbu wai menene? Naji maganganu sama-sama."! Abbu ya kalli Hanifa ba tare da ya bawa Ammi amsarta ba yace. " Hanifa ina kike kokarin zuwa da daran nan."!?
Kallonsa tayi wasu irin hawaye masu zafi suka zubo mata a fuska.Ammi ta daka mata wata irin tsawa tana fadin"Ba tambayar ki akayi ba ne."!? Abbu da jikinsa ya gama yin sanyi yace." Halima yi mata a hankali kar ki manta kuma dare ne Yanzu. " Shiru Ammi tayi gabanta na fad'uwa wato Hanifa futa zata yi to ina zata je? Dukan su basu da amsar sai a gurin ita Hanifa r Abbu yace."Hanifa ina zakije da dare."! Wannan karon muryarsa a kaurare take. Kuka ta fashe dashi tana fadin",Abbu mafarki nayi ya mutu!!!! Ammi da Abbu suka kalli juna cike da mamaki suka ce waye ya mutu? Kuka ta fashe dashi ta fad'a jikin Ammi tana wani irin kuka take fadin"Ammi nayi mafarki ya mutu za'aje a bunne shi!!! Ammi jikinta ya soma rawa ganin yarinyar ta tana wani Abu kamar zauntacciya tace"Wai wa kika gani ya mutu an fada miki mafarki gaskiya ne."!? Tana kuka tace"Ammi wannan da gaske ne wallahi ance min ya mutu.!" Abbu yace." Wanene ya mutu."? Cikin futar hayyaci tace"Abbu Khalid ne na ganshi cikin makara mutane sun dauke shi zasu kaishi su bin......... Bata 'karasa ba Ammi ta yarfa mata wani irin mari!! Wanda yasa ta kwallara 'kara! Da tasa gidan ya amsa su Nasiru suka futo a gigice! Bakin kofar dakin suka tsaya cikin tashin hankali.!
0 comments:
Post a Comment