kubra cin karo tayi da digo digon jini gabanta ne yyi mummunar faduwa jitai ana tari da sauri taqarasa shiga dakin dubawa tashiga yi taji sautin tarin baba a toilet kofar tahau bugawa da iya karfinta tana kuka tanacewa baba meya sameka Dan Allah ka fito ka fadamin jin muryan kubra baba mlm yyi hnklnsa ne yatashi da sauri yayi qoqarin saita kanshi
fitowa yyi yasameta fusknta yyi chaba2 da hawaye rungumesa tayi tana kuka yace kubra menene kuma tace baba jini nagani yace jini kuma kubra a ina tace gashi can tafada tana nuna masa kofar dakin yace laahh dazu nefa na Dan yanke akafata amma bb komai tace to baba tarin danaji kanayi fa yace ayyo wnn shan ruwa nakeyi saina kware ya fada yana nuna mata bottle water akasan carpet tace ay wlh har hnkl na yatashi yyi murmushi yace ya akayi
Tace dama fa anty fadila ce aka kaita asibity xata haihu shine big Yaya ya kirani ya gayamin INA skull nace bari nadawo gd na dauka kayan baby saina gaya maka yace ahh masha Allah Allah ya sauketa lpy tace ameen baba mlm yace bari naxo mutafi tace aa baba kadan xauna na kira ya mustapha zaixo ynx saimuje dashi dama baba daurewa kawai yake yace to amma dai zanxo anjima kadan tace to
Dakin fadila ta wuce dama ranan tare suka shirya kayan baby awani akwaty dibowa tayi tasa awani qaramin jaka ta dauko dai duk wani abun dataga yakamata Wanda za abukata tafito kenn saiga mustapha tace yww ya musty muje rai ya hada ya harareta yace banso fa dry tayi tace to yi hkr yayana bazan sakeba murmushi yyi yace yawwa yarinyan kirki itama fuska tayi tace nice yarinyan yace ehma dama mecece ke idan ba yarinya ba tace tab lallai ma kam nida saura wata2 ayi.....Sai kuma ta toshe baki tana dry duka xai kai mata tasa gudu tayi waje murmushi yyi yace Allah ya shiryeki wlh
RIMI HOSPITAL suka nufa suna zuwa suka shiga ciki daga can reception suka hango abubakar yanata sintiri da sauri suka qarasa wajansa sukace big Yaya bata haihun bane basu gama rufe baki ba saiga likita ya nufosu yana murmushi suka taresa suna tmbyansa ta haihu miqawa abubakar hannu yyi yace cngrtltns kazama baban baby boy rungumesa abubakar yyi yana masa gdy yace kana da kyauta
Kubra ihu tasaki ta juya tayi tsalle ta rungumi mustapha cikin farin ciki Marar misaltuwa sannan ta juya wajan abubakar tace big Yaya INA tayamu murna da qaruwan da muka samu wayyoni kubra nazama momyn baby mustapha yace nazama daddyn baby dai keda nanda wata2 xamu kaiki garin lagos gabanta ne ya fadi ta hada rai ta juya ta kalli Yaya abubakar dake ta musu dariya SBD dramansu daria yake bashi kamar xatayi kuka tace big Yaya kanajinsa ko yace yi hkr autarmu gsky ya fadi ai
Kuka tasa Yy abbkr yace haba autarmu kefa kincika shagwaba wlh miye abin kuka tace nafasa auran ido waje yazaro yace so kika ki mayar dani qaramin mutum bake da bakinki kikace bazaki xauna agdn ba
Tace to ai dane ynx kuma ga baby wata nurse CE tafito kubra tace wai INA yaronmu ne kam ko Sai mun mutu da dauki kafin kubamu shi
Nurse tace yi hkr sis ana gyarashi ne ynx zamu kawo muku abunku tace to yakamata dai ayi hanzari mustapha yace sannu amarya tace big Yaya kayi masa mgn banso yace to kai qanina kabari yace to shikenn nabari a ynx tace a anjima fa yace mata bangama tunani ba tukunna hararan wasa tayi masa.
Saiga shi anfito da da' masha Allah da sauri kubra ta karbesa tana oyoyoo Dan albarka haihuwar sa,a oyoyoo Dan baiwa haihuwar nasara Allah yabar mn kai
Mustapha yace yarinya bamu danmu muji dumin jikinsa duk kinwani makuresa tace naqi baxan baka ba abubakar na ya karbesa ya zuba masa ido yana kallonsa yanajin son dan'sa har kwakwalwarsa adduah yyi masa sosae kafin yabawa mustapha domin yadda kubra ke daukin babyn nn idan ba da gsk sukayi ba baxata basuba
Kubra kuwa kiran raliya tayi tana daukawa tace Anty raliya albishirinki tace goro fari qal2 tace munsamu baby boy anty fadila ta haihu murna sosae raliya take tace Allah ya raya mana shi tace ameen raliya tace INA yar uwartawa tace ankaita dakin Hutu tana bacci tace kigaishemin da ita INA nn xuwa gobe tace to xataji insha Allah
Kiran ummi tayi tana daukawa tace antyna albishirinki tce goro kafin kubra tayi mgn ummi tace alhamdulillah mai muka samu cikin jin ddi kubra tace kaii lallai Anty ummi ya akayi kk sani kodai big Yaya ya fada miki ne tace aa kawai nasan murnan da zai samemu kenn tace munsamu baby boy
Allah ya raya mn shi akan sunna da ameen kubra ta amsa tace gobe xanxo OK Allah kaimu Anty ummi tace ameen
Abubakar kuma fita yyi mota yaje yashiga kuka yakeyi da iya karfinsa
Yana cewa yau gani INA farinciki amma kuma ba uwa ba umma nasan da sai sunfini SBD sun samu jika sun samu miji
Adduah sosae yamusu kafin ya kama hanyar gd koda yaje gdn ma wanka yayi yaje yasamu baba yana xaune yake cemasa ta haifi namiji baba yace masha Allah Allah yamasa albarka yasa yadinga maka biyayya kamar yadda kk min ameen abubakar ya amsa xaiyi mgn yaji wayarsa tana ringing yana dubawa yaga autarmu ya dauka yace ya dai tace big Yaya sunyi sallama kaxo ka daukemu yace to
,,,,,,,,,,,agurguje
Yan kano sunxo anyi hidima yaro yaci suna (KABEER) da aka kaiwa baba mlm shi yasa masa albarka yce kaikam da rabon kakan ka xai daukeka yyi murmushi tare da hawaye bayan suna da kwana3 yan kano suna shirin komawa ummi ma tana ta fama da amai ciwon kai ciwon ciki
Tosu ummi Allah ya raba lpy kema
Sun shirya kenn sunxo yiwa baba mlm sallama a xaune suka samesa akan sallaya sukace baba xamu tafi ya bude baki xai mgn kenn sai yyi wani tari mai karfi gudan jini ya fado tashin hnkl rudewa sukayi
Kafin kace mai baba ya sume sai asibity suna hanya abubakar yana tuka motar mustapha yana riqe dashi Dan usman ya koma shida mansur jiyayi baba mlm yana kalman shahada. Kuka yasa yace big Yaya tsaya kafin Yya abubakar ya tsaya rai yyi halinsa
Kasa motsi abubakar yyi balle ya ja motar su koma gd wayarsa ya dauka ya kira wani abokinsa yace baba. Ya rasu yace kamarya banganeba yace Dan Allah kawo ka mayar damu gd kuna inane yace hanyar specialist hospital yace gani nn baifi Minti goma biyar ba saigashi ga baba kwance akafar mustapha ya rungumesa yana kuka da kyar abokin abubakar yafita dashi yamayar dashi gefe yaja motar sai gd abokin abubakar ne ya fadawa jamaa Allah yyiwa mlm hamza rasuwa kamar tambari jamaa kamar me guri ba matsaka tsinki
Su ummi kawai gawa aka dawo musu dashi da harsunfito xasuje asibityn duka asume aka mayar dasu ckn gd har abubakar ne ya kira usman yace kaxo gd yaudin nn kataso ynx usman yace Yaya lpy maiya faru k.....kit abubakar ya kashe wayan
Haka aka shirya mlm hamza akayi masa Rakiya ixuwa gdnsa na gsky kowa sai fadin alkhairinsa yake almajiransa nada Wanda sukayi sauka awajansa sai kuka suke suna musu adduah
Usman yaxo har andawo daga maqabarta kasa ma kukan usman yyi saidai kukan zcy
Sai gaisuwa ake musu suna amsawa
,,,,,,,,,,,bayan adduar 7
Abubakar yatarasu tunowa yyi lkcn da umma ta rasu dayake musu .nasiha yace lallai baba yayi gsky dayace muzama uwa da uban kanmu na yarda Allah baya barin wani Dan wani haqiqa acikin shekara daya da rabi munga jarrbawa agun ubangiji kuma mu musulmaine mun yarda da kaddara kuma munyarda dukkanmu sai mun mutu amma kawai Zcy batada kashine mu qara hada kanmu muqara son junan mudinga yiwa iyayenmu adduah
Sannan ke kubra idan harna isa aurenki baxa adagaba jia munyi mgn dashi salim din nake cemasa baxa adaga biki ba
Kuka kubra take tace big Yaya daga yau ka koma (Abba) sannan tabbas ka isa kawai kace nayi kagani ko baxanyiba ddi sosae abubakar yaji Dan Kansu ahada yake yace Allah ya miki albarka
Kwana atashi ba wuya wajan Allah shirye2n biki ya kankama yau saura sati 2
,,,,,,,,,
Muhadu a next page fans
Taku har kullum
Zahra abdul
(Momyn ahlan)
Comments
And
Share
[10/25, 2:55 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*NA*
*ZAHRA ABDUL*
_(Momyn ahlan)_
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Dedicated to (fiddausy usman )
Duk da bansanki ma kema hka but son book dina da kk yi yasa naji nima ina sonki wannan page dinki ne kiyi yadda kk so dashi
Bismillahi rahmanirrahim
Page 1⃣9⃣_2⃣0⃣
Yana fita office dinsa yyi direct yaje ya iske anas yana jiransa anas yana ganinsa yasaki murmushi kafin yace ahh gaka na habiba angon hidaya Allah yabar kauna
Tsaki Abbas yyi kafin yace kaga malam meya kawoka office dina dry sosae anas yakeyi Dan yasan halin abokin nasa bayaso kwata2 adinga kiran sunansa dana hidaya amma idan kace habiba harwani cika yake yana batsewa yace Mlm kainake sauraro anas ya nisa yace wani case ne aka kawo kuma nasan kai xaka taimaka mutanan talakawa ne wlh kuma ana so adanne musu hakkinsu ne tunda anas yafara mgn Abbas ya natsu yana sauraronsa kafin yace akan me akeso adanne musu hakkin nasu file's ya miqa masa yace duk na hada komai aciki duk wani tmbyarka akwai amsa aciki ka duba yace OK
Dubawa yashiga yi yana gyada kai yace to ai sharian ba abauchi xa ayiba kuma bansan kwana nawa bane xa adiba anayiba numfashi anas yaja kafin yace a yadda nasan aminina akwana biyu xai iya cin galaban sharian nn saidai baisa kansa ba shuru Abbas yyi kafin yace to kenan kano xanje anas yace ehmn taimakawa xakayi
Kallonsa Abbas yyi yace nasan duk wnn binkicen kane anas ka raba kanka wlh ina gaya maka murmushi anas yyi yace to yallabai xandai kiyaye amma baxan guji aikina ba humm kawai Abbas yace hira suka Dan taba kafin yace shikam yau xai koma kano rakosa yyi har wajan packing space yashiga mota yace nanda kwana3 ne ko eh nanda kwana 2 ne Dan Allah Abbas kaxo akan lkc karka damu xanxo wlh dama hibbata tadameni tanaso taje gd naqi yarda amma ynx kam xamuxo tare da ita inyaso saina kaita gdn
To idan kaxo da habiba ita kuma hidaya fa ?kallon 9 saura kwata yyiwa anas kafin yyi tsaki mtsww oho maka kuma bansani ba ya juya xai koma office dinsa anas yace wlh Abbas da ka yarda da ko karka yarda gsky dai baxan fasa fada maka ba wlh kaji tsoron Allah idan kacuci yarinya Allah baxai barka ba wlh yatada motarsa yafice SBD Abbas yana bata masa rai wlh Abbas kuwa daga kafada yyi alamun ko ajikina ya koma office ya cigaba da aikinsa bai tashi ba sai karfe 5 gidansu yafara xuwa ya gaishe da iyayensa momma ta hararesa tace ya hidaya da habiba suna nan lpy abinda yace kenan momma tace kullum dai ina qara gaya maka kaji tsoron Allah to momma xan koma gd ta kallesa tace agaishesu to xasuji. part din mamu yashiga suka gaisa yace gdn shuru mamu tace ai sun kusan dawowa suna islamiyya ne yace ayya to mamu xan wuce gd to agaida habiba da hidaya xasuji
Yana komawa gd part din habiba yawuce yaje daki batanan kitchen yasameta tana hada juice din carrot and pawpaw hugging dinta yyi tabaya lumshe ido tayi cikin sanyin murya yace hibbata nagaji su mamu sunce agaida Ku juyowa tayi ta kallesa tace muna amsawa sannu da dawowa kwara kwanciya yyi kan kafadarta yace yww muje kirakani nayi wanka kallonshi tayi kafin tace ni kuma yau ai kwanan hidaya ne kaje ta rakaka shuru yyi yana kallonta idonunsa duk ya kankance yace to inajin yunwa nanma tace nasan hidaya tayi maka kaje part din ta ya jikin nata daxu ka duba mata goshinta daiko kafin kafita uhumm kawai yace ta lura da yanayinsa sarai amma tayi fuska haushine yakamasa yace hibbata meyasa kikemin haka ne kam kallonsa tayi tace menayi my sweet baki sona mn korata kikeyi tace ni na isa na kori mijina ne kawai inasonka ne kuma banaso ka shiga cikin fushin Allah shiyasa humma kawai yace yasakai zai fice a kitchen din ya juyo yace ki shirya nanda kwana3 xamuje kano ihu tayi gamida tsalle taxo tayi hugging dinsa kota ina tadinga basa hot kiss SBD farin ciki jin kalar numfashinsa yafara canxawa ne tayi saurin sakinsa ta fita a kitchen din
Bedroom dinsa ya shige domin ya watsa ruwa
Bangaran hidaya kuwa bayan yafita kuka takumayi kamar ranta koda uwani taga goshinta a kumbure da ta tmbyeta cewa tayi bugewa tayi da kofa tace idonki kuma fa da yyi ja tace kwaro ne yashiga min uwani dai kawai tabar mgnanne SBD batason binciko abinda bai shafeta ba
Yana fitowa wanka ana kiran sallar magriba Dan hka yyi alwala yatafi masallaci baidawo ba saida akayi sallar isha, i,
Yana dawowa ya wuce dakin habiba yana turawa yaji dakin gam ta kulle bugawa yashigayi tana jinsa tayi masa shuru harya gaji ya juya ya koma dakinsa cikeda haushin hababi SBD yana cikin yanayi ina takeso yaje wajan wancan yarinyan mtsww yaja tsaki
Hidaya tana xaune ta rafka tagumi abin dunia ya isheta ga abincin data girka datace baxatayi ba uwani tayi mata mgn koda sukayi waya da ruky cewa tayimata tadinga yimasa girkin koda baxai dinga ci ba
Sallama uwani tayi taga hidaya xaune tace waike baxaki kaiwa mijinki abinci bn kam tundaxu fa yadawo shuru hidaya tayi kafin tace Anty uwani bansan yadawo ba
Dashike uwani ta girme hidaya shiyasa take cemata Anty
Uwani tace to yadawo tashi maza2 ki kaimasa abinci ba kyau barin miji da yunwa kinji ko ? Ta gyada kai alamun eh ta miqe jikinta Sam ba kwari SBD haryanzu kanta yana mata ciwo
Kallon tausayi uwani tabi hidaya dashi gata yarinya karama amma tananeman bata rayuwarta da tunani
Xuwa tayi ta hada abincin ta dafa masa tea tayi komai kafin ta koma daki ta dauko babbar hijab dinta har kasa tasa
Tafito ta kalle uwani tace bari na kai nadawo uwani ta kalleta tace kidawo ina ai saida safe xakice shuru hidaya tayi tana tunanin wani irin kalar rashin kirki xai mata idan taje uwani ce ta katse mata tunani da cewa dauki kije mn kinja kin tsaya dauka tayi tafice
Shi kuma yana kwance adaki sai juyi yake yakasa bacci ya buga kofar habiba harya gaji ya kirata awaya taqi tadaga text ya tura mata kamar haka
(Ina ni kikeyiwa haka ko ba damuwa ngd wlh idan kika bari na kwana ahaka nima xan rufe ido da son danake miki nayi miki abinda baxakiji dadi ba)
Koda ta duba ta krnt tabe baki tayi afili kuma tace wlh baxaka jamin sharri ba nikam
Jiyayi anturo kofar gabanta ne ke dukan9_9
Tayi sallama a hnkl
Shi kuma a tunaninsa habiba ce ajiye abincin tayi ta tsaya tana kallonsa jin anyi shuru kuma anshigo masa dakine yasashi tashi ya juyo gabansa ne yafadi daya ganta tashi yyi ya fizgota yahadata da bango cikin tsawa da masifa yafara mgn
Ubanwa!! yace miki kixomin daki bance miki karki qara xuwa ba fitsari ne kawai hidaya bata sakiba ga tsoron daya gama kamata ganin yanayinsa wani iri idonsa jajur tsikan jikinsa da jijiyoyin wuyarsa duk sun tashi cikin rawar murya tafara mgn
Dan Allah ya Abbas kayi hkr abinci nakawo maka kuma ......kasa karasa mgnr tayi SBD qara matsetan da yayi numfashinta ne taji kamar xai dauke kuka ta kuma saki
Cikin dashenshan murya yace aina jima inamiki gargadi bakiji ko wato ke gaki kin girma to bari ki gani fizge hijab din jikinta yayi wulli dashi ya fizgota da karfin gske ihu hidaya tashigayi tana buga kafa akasa tana basa hkr amma ko jinta baiyiba hannu yasa yana shirin yagemata riga cizo ta lafta masa ahannun hkan ne yasa yasaketa yana yarfe hannu waje tayi da mugun gudu tana kuka
Kwantawa yyi rufda ciki yasa kansa cikin pillow
Uwani tana shirin kulle part din hidaya SBD tagama kallon film din da takeyi bata kai ga kullewa ba saiga hidaya kamar an wullota da gudu hartana buge uwani
_____________________
Wayyo Allah na 😪kuyi manage da wannan
_____________________
Muhadu
A next page
Taku har kullum
Zahra Abdul
Momyn ahlan
Comments
And
Share
[10/25, 2:55 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*NA*
*ZAHRA ABDUL*
_(Momyn ahlan)_
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Bismillahi rahmanirrahim
Page2⃣3⃣_2⃣4⃣
Hanyar Gidan Anty salma yayi yana tuki yana tunanin meyayi ga gabansa na faduwa horn yyi a gate din gdn mai gadi ya bude masa yashiga yayi parking hango rafee,a yayi itada hayrat suna wasa suna ganinsa sukazo da gudu
Oyoyoo uncle Abbas rungumesu yayi yace yana ganku agd ba islamiyya ne akwai cewan rafee,a amma sai anjima zamuje to yayi kyau INA momynku tana ciki cewan hayrat
Gidan ya shiga da sallama daga kitchen Anty salma tafito ta amsa sallaman zama yayi itama zaunawan tayi kallonta yayi yace INA wuni Anty salma
Lpy! Kawai tace
Anty salma lpy kuwa?
Naga gabaki daya yanayinki ya sauya bantaba ganinki haka ba plss Anty babba fadamin meya faru cikin fuskan tausayi
Sassautawa Anty salma tayi tace hidaya nake nema tun jiya nake kiran wayarta bata shiga
Yace au mtsww wlh Anty salma na dauka wani laifin nayi miki yadda naji muryanki awaya kuma kikace nazo yanzu2 shiyasa naji gabana sai faduwa yakeyi Ashe wai hidaya kike nema aida kince nataho da ita
Kallon Dan rainin hnkli Anty salma tayiwa Abbas kafin tace ai ynx ma bai baci ba jeka kawo min ita ynx SBD inason ganinta ne
Lpy dai ko Anty salma !
Lpy lau mana meka gani ko bazaka iya kaje ka kawomin itan bane ido yaware nidin banza na isa nace bazanje ba
Ynx zanje na kawo miki ita miqewa yayi yace anty salma yunwa nakeji Dan Allah me kika dafa harara ta galla masa tace badaga gdnka kake ba sannan mata nawane agidan?
Shuru yayi batare da yayi mgn ba yasakai yafice aransa yace ikon Allah Ashe itama Anty salma tanada zafi tsaki yayi daya tuno sanda take cemasa mata nawane agidan bayan yashiga mota yatayar afili yace ita wannan yarinyance xa awani kirata da mata inatakai matsayin mata yar'shila da ita wlh zata gamu danine SBD ynx akanta zanyi sintiri sau 2 mtsww
Bayan fitar Abbas Anty salma tashiga dakinsu rafee,a inda hidaya take kwance uwani tana zaune agefe tashi tayi ta zauna ta kalli Anty salma ta sunkuyar da kanta tana kallon kasa zama kusa da ita Anty salma tayi kafin tace hidaya kiyi hkr Abbas Dan uwanki ne ko ba aure atsakaninku yakamata yasoki amatsayinki na kanwansa kuma yar'uwansa bansan maike damunsa ba amma kidinga hkr kinji to tace
Sannan tace Anty salma aida baki kara turasa gida ba dakince masa inanan kallonta Anty salma tayi tace wlh saiya koma ya nemeki uwani tace wlh kibarsa yadan wahala nemanki shuru tayi batare da ta kuma yin mgn ba Anty salma ma fita tayi ta koma kitchen tacigaba da aikinta
Yana isa gd ko packing bai tsayayiba yafice a motan part dinta yawuce yashiga yagansa abude tsaki yayi yace baga irin yarintar ba takama tabar kofa abude cike da masifa yayi hanyar bedroom dinta bankada kofar yayi yabude baki zai mgn baiga kowaba tsaki yayi ya koma parlor ya zauna jiranta duk atunaninsa tana toilet ne jin shuru babu alaman motsi yasa yatashi mtsww ke banson raini fa ubanme kikeyi a toilet din tundazu kinbarni inata zaman jiranki over 15mnts kofar toilet din yake bubbugawa yana mita yasa kafa ya nausa kofar kawai saita bude baki Sake yatsaya yana kallon toilet din wayam ba kowa au bata nanne to inataje mtsww wayarsa yadauka yana duba numb ta yagama Ashe banyi save ba tunani yashigayi to INA hidaya zataje yau kuma ba Monday ba balle yace taje skll ne to ko tana part hibbata CE hanyar part din habiba yayi lkcn tana zaune a parlour dinta SBD taji fitarsa kallonta yayi yace INA hidaya itama kallon rashin fahimta tayi masa tace vangane ba hidaya ta taba shigowa nanne yace to nidai bangantaba Anty salma CE kuma kenemanta tashi tsaye habiba tayi tace muje mukara duddubata da kyau ba musu yabi bayan habiba amma tabbas idan yaganta zata gane kuranta saiwani basa wahala take kamar yana neman kudi mtsww
Babu inda basu duba ba agidan babu hidaya babu mai kama da ita hnklinsa ne yatashi cirko2 suka tsaya habiba tace ynx miye abunyi wannan tsayuwarfa bazata yuba akufule yace to me kikeso nayi
habiba itama tafara tunzura SBD alamu sunnuna zai iya jamata tsana awajan danginsa kamar yadda hidaya ta tsaneta barinma abinda yafaru jiya tasan da wuya ace hidaya tamanta gashi ita har kunyan hada ido takeyi da ita duk da ba laifinta bane amma hidaya bazata fahimceta ba guntun tsaki tayi gamida zama
Wayarsa yaji tayi ringing yana dubawa yaga Anty salma tsaki yayi kafin ya dauka tace masa naji shuru kuna inane gamu nan zuwa abinda ya iya cewa kenan Anty salma ta katse kiran gamida cewa zakayi bayanine ai
Shima zaman yayi ya kalli habiba yace kin wani zauna shuru bazakice ga yadda za ayiba kallonsa tayi nace ga yadda za ayi dana tmbyeka yanzun nan miye abinyi mai kace min ?
Kai haba hibbata kincika rigima wlh kainane yadauki zafi shiyasa sorry kinji kallonsa tayi tace ynx ka kira mamu kaji kotaje gida ne
Anya hidaya zataje gida kuwa kallonsa tayi tace ai ba tabbas ka kirata mn
Mtsw da inada numb ta aidana jima da kira bantsaya wnn wahalan ba kallon mamaki habiba take masa gamida riqe baki kace bakada numb matarka Abbas wlh kaji tsoron Allah harara ya aika mata yace ki kiyayeni wlh shuru tayi bata kuma cewa komai ba
Can anjima tace ka kira momma ka tmbyeta idan bazaka kira mamun ba
What!! Momma dai eh lallai kam sannu matarnan tace yawwa sannu mijin nan yace inkira momma kinaso na kirawa kaina ruwan da bazan iya tarewa ba kam
Shuru sukayi yace yawwa bari na kira matar Yaya Kabeer tace yawwa kirata muji
Dealing din numb matar ya Kabeer yyi ringing 2 ta dauka sallama yayi ta amsa suka gaisa kafin yace matar big bro Dan Allah hidaya tazo gida
Hidaya kuma Abbas ai rabon hidaya da gidan nan tun ranar da kazo ka dauketa yace baki ganta a part din mamu ba ko part din momma tace gsky banganta ba infact ynx nadawo daga part din mamu da momma harnaji momma tana cewa kwana2 tayi missing din hidaya zata kiraka ta tmbye ka idan basuda wani krt sosae skll kabarta tazo suje lagos tareda maleek SBD mom kubra tace bakusan zuwa wajanta shuru Abbas yayi kafin nan kuma yafara zufa yace OK bari na dubata maybe tana toilet ne Dan ynzu na shigo gdn banganta ba
To shikenan ka gaishemin da ita cewar matar ya Kabeer to zasuji matar big bro agaishemin dasu daddy da muhsin da lvly Mamie to zasuji sunje islamiyya ma to shikenn nan sukayi sallama kuka ne ya kwacewa habiba Wanda batasan lkcn daya fito ba kallonta yayi yace miye haka Dan Allah kiyi shuru wlh ni karan kaina yadauki zafi cikin kuka habiba tace ai wlh har gobara saiyayi tunda kai bakajin shawara kuma wlh na tabbata akan abinda yafaru jiya ne hidaya tabar gd wayyo nashiga uku
Malama karki taramin jama,a a cikin gida ayi zaton ko mutuwa akayi cikin kuka tace to miye maraban dambe da fada
To rufamin baki bari na kira Anty safina naji tace wannan kiraye kirayen naka babu wani amfanin da zatayi kawai bari na dauko hijab dina muje nemanta bata jira amsarshi ba tayi daki tadauko hijab tasa amota tasame shi gidan Anty safina sukaje awaje suka hadu da basma tace tayi hugging dinsa oyoyo uncle Abbas INA Anty hidaya yace bakiga Anty habiba bane kallon habiba tayi tace sannu da zuwa Anty habiba murmushi habiba tayi mata tace ni kuma SBD bakisona bakimin oyoyo dinba Dan yatsine fuska basma tayi tace sorry Anty Abbas ne yace my baby kikace hidaya batanan eh bata nan Anty safina CE tafito tana cewa ke basma baki tafiba maza kiwuce danladi ya kaiki inba haka ba nazaneki kinsan halina mota tashiga da sauri sai alkcn Anty safina ta kallesu Abbas tace ah Ku kuma fa daga INA habiba zatayi mgn Abbas yayi saurin cewa sunfito abubakar tafa balewa plaza ne me kukaje yi? Kallonsa habiba tayi Abbas yace kantane ke ciwo shine mukaje pharmacy siyan magani ayya sannu kinji habiba allah yaqara sauki cikeda tausayi ta fada sunkuyar da kai kasa habiba tayi kafin tace ameen kushigo mn cewan Anty safina
Aa Anty safina bari muwuce gd kawai dama biyowa mukayi tunda akan hanya ne to shikenn INA umma gabansa ne yaji yabuga dammmmm!!amma saiyayi ta maza yace tana gida to Ku gaisheta habiba allah yakara lpy ameen Anty safina ngd mota suka shiga yatayar suka fice agidan kallonsa habiba tayi tace sannu yallabai
Yace to sokike da kifada mata eh mana ai gwanda tasan abindake faruwa yace tab Anty safina ai gwara na koma gidan Anty salma akan Anty safina domin halinsu daya da momma
Tace to yanzu gidan Anty salma zamuje eh kawai yace
Suna isa gidan Anty salma ya kalli habiba yace hibbata ynx idan munshiga mai zancewa Anty salma kallonsa tayi tace gsky mn zaka fada mata asan abunyi tunda kaga lkc yana tafia
Hummm wannan yarinya tajawomin mgn habiba tace to laifin waye?
Packing ya gyara suka fito suka shiga gdn parlour din ba kowa sallama yashiga Anty salma tafito tace ahh habiba sannu da zuwa gaisheta habiba tayi fuska dauke da damuwa kallon Abbas Anty salma tayi tace naga habiba INA hidayan fuska kamar zai kuka yace Anty salma wlh banganta ba
Hada rai Anty salma tayi tace zancan banza kenan kamaryaya bakaganta ba
Wlh babu inda bamu duba ba nida habiba amma bata nan
Kallonsa Anty salma tasakeyi kafin tace tun yaushe ne batanan din sunkuyar da kai kasa yayi yana Sosa keya wlh bansan ko yaushe tafita ba ai kuwa Anty salma ta hau shi da bala'i inda take shiga banan take fita ba ranta yayi mummunar baci
Wlh kaban mamaki Abbas kuma kabani kunya hidaya bata gida amma bakasani ba hakan ne yaqara tabbatar min da cewa Sam bata samun kulawa awajanka
Da kana kula da ita babu yanda za ayi ka nemeta karasa yanzu ko mutuwa hidaya tayi lallai na yarda bakada asara to wlh ka farayiwa kanka karatun tanatsu tun kafin duniya tafara yimaka shuru yayi baice komai ba Dan yasan baida gsky
Anty salma kuwa ta wankesa tassssss!!
Tukunna ta tashi tashiga ta kira hidaya tana fitowa suka hada ido gabanta yafadi harara ya aika mata masu fassaran gske can gefe ta zauna ta rakube anty salma tace jiya a asibity ta kwana amma duk baka Sani ba ko yamaka kyau
Hakuri yashiga bawa anty salma tace ai hidaya zakabawa hkr bani ba yace eh zanbata itama amma Dan Allah kiyi hkr kihuce kinji Anty babba tace to wlh karka sake kasan kuma hukuncin namijin dayake zalintar matarshi aiba saina cemaka komai ba tunda kasani kuma kasan hukuncin Wanda yakeda Sani yataketa Dan haka kayiwa kanka hisabi tun aduniya jikinsa ne yadanyi sanyi yace insha Allah
Yace kutashi mutafi gida tashi sukayi hidaya tashiga daki ta dauko hijab dinta ta kalli uwani tace Anty uwani muje ko
Aa kutafi abinku xanxo da kaina
Meyasa?
Wlh ba komai kuje zanxo
To amma Dan Allah karki jima to hidaya bazan dade ba fita hidaya tayi tasamesu awajan Anty salma taqara musu nasiha yace anty salma gobe insha Allah zanje kano yinwata case amma nida habiba ne zamuje
Kallonsa tace ita kuma hidayan fa....??
More comments more typing
_________________________
Wlh yau agajiye nake lilisss SBD na wuni a mkrnt banyi tunaninma zan iya wnn ba ngd sosae fan's ana mugun tare
Muhadu a next page
Taku har kullum
Zahra Abdul
Momyn ahlan
______________________
Ku nema sabbin littafinmu na rayuwar barikin sojoji
Hadakan marubuciya
Surayyahh B Abdul
And zahra Abdul
(Momyn ahlan)
Da kuma rayuwarmu a barracks
Na
Neeshar jay
And feedyn bash
Comments
And
Share
[10/25, 2:55 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*NA*
*ZAHRA ABDUL*
_(Momyn ahlan)_
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Wannan page din sadaukarwa ne ga duk mai karanta book din halitta daga Allah ne inajin dadin comments shiyasa sometimes idan nadawo makaranta ko nagaji nakeyin typing..... Much Luv to urs fan's💓💓💓
Bismillahi rahmanirrahim
Page2⃣5⃣_2⃣6⃣
Kallon hidayan yayi kafin ya kalli Anty salma yace tanada skll ai bazaiyu mutafi tare ba harara Anty salma ta aika masa dashi tace au haba hidaya kuna karatu sosae idan bakuyi ki shirya kutafi tare idan yaso saiya wullar dake ahanya ya huta sai hararan hidaya yakeyi cikeda tsoro tace aa Anty salma zamu fara test awannan week din kuma banyi karatu sosae ba suje kawai Allah ya kiyaye hanya
To ke kuma fa zaki iya zama agidan daga ke sai uwani tace eh zan iya ba matsala Anty salma tace kwana nawa zakuyi Abbas yace baifi 2days ba domin gobe da karfi3 akwai zaman kotu
To Allah taimaka habiba kigaishe da yan gidanku duka
To zasuji Anty mungode
Badamuwa sai anjima
Mota hidaya ta bude gidan baya ta zauna yadda taga yana aika mata sakon harara yasa jikinta yayi sanyi ko wani kalar rashin mutunci zai shuka mata insunje gida oho muryan habiba taji tana mata sannu yi tayi kamar bataji habiban ba
Kara juyowa habiba tayi tace sannu hidaya ya jiki bude ido hidaya tayi ta galla mata harara sannan taqara rufe idonta ko kala bai ce musu ba sai haushin da hibba ke basa tawani dage sai sannu takewa yarinya tana raina mata hankali
Suna isa gida bai gama parking ba hidaya tafice abunta habiba tabi bayanta tana shiga parlour habiba tace Dan Allah hidaya kitsaya Mu fahimci juna wlh banajin ddin zaman da mukeyi
Dake juyowa hidaya tayi ta kalli habiba gamida murmushin takaici amma ai kina jin dadin zama da mijinki ko?
Shuru habiba tayi batace komai ba tacigaba da cewa indai kinajin dadin zama da mijinki to babu ruwanki dani agidan kiyi hidimarki kawai da mijinki nima kibarni nayi tawa tana kaiwa nan tashige dakinta juyawa habiba tayi zatafita suka hada ido da Abbas Wanda tun dazu yake tsaye yana jinsu wucesa tayi tafita tayi hanyan part dinta Dan karya sake jamata wani tsana
Dakin hidaya yashiga tana zaune abakin gado kallonta yayi yace sannu wato bakida lpy ban isa ki kirani ki fadamin ba saidai ki kira Anty salma ki gaya mata to anyimin abinda zcyr ki takeso kinji dadi
Ido cikeda kwalla tace kayi hkr wlh bansan komai ba kawai na farka ne naganni a asibityn harara ya galla mata yace kicigaba da gwadani wlh duk ranar dana riqeki zaki San ainihin true color dina mtsww yafici adakin
Dakin habiba yashiga tsayawa kallon ikon Allah yakeyi wani jibgegen akwatin da ta hada kaya aciki
Hibbata wannan akwatyn fa? Shagwabe fuska tayi my luv na tafiya ne mn
Natafiya dai shekara zakiyi
tafiyan kwana biyun ne zaki kama ki dauki wnn katuwar akwaty saikace zakibar gari gabaki daya to wlh ki rage kayan nan idan kuma ba haka ba saidai kiyi zamanki agida
Yasakai yafice adakin
Turo baki tayi gamida cewa mutum tunda yayi aure baije gida ba ynz kuma mutum zaije ance kaya yayi yawa tunowa tayi da kowaye mijinta idan bata rage ba xai iya hanata tunda tun ba yauba take tmbyarsa zataje amma saiyace mata kibari ba yanzu ba hakanne yasata rage kayan amma badin taso ba
Hidaya kwance take agadonta tunani kala2 duk sun addabe zuciyarta gashi kullum wani azababben son Yaya Abbas qaruwa yakeyi acikin zuciyarta shin anya kuwa Yaya Abbas zai sota ?tmbyar datayiwa kanta kenn lkc daya hawaye suka sauko mata kamar anbude famfo tashi tayi taje gaban mirror tana kallon kanta to miye batadashi Wanda bai cancanci namiji yasota ba kukan daya zame mata jiki shitayi kafin ta tashi tayi wanka tayi sallah uwani bata dawo ba sai bayan sallar isha,i,
Koda ta tmbyeta kinyiwa mijinki girki kwanciya tayi tace batajin ddin jikinta bazata iyaba babu lallashin da uwani batayi ba akan ta daure tayi amma fir taqi haka uwani ta kyaleta
Tun bayan fitarsa baisake dawowa ba balle yazo yaga yajikin nata itama batasa arai zaizo ba kuma baizon ba habiba ma baibi takanta ba yasan koyaje bata masa rai kawai zatayi karshe tasani kwana da ciwo Dan haka yayi kwanciyarsa duk da dai ba baccin yayi ba habiba kuwa baccinta tasha amma itama hidaya kam takasa bacci sallah tayi ta kai kukanta wajan mahaliccinta domin tasan shikadaine zai share mata hawaye adduah tayiwa iyayenta da kakanninta da yan uwa musulmai na duniya Wanda suka rigamu gidan gsky sannan ta roqi Allah ya sassauta mata son abinda baya sonta saida tayi asuba tukunna bacci yadauketa
Washe gari bata farka ba sai 11 nanma wayar rukayya CE ta tashe ta
Afirgice ta miqe ta duba agogon dake manne adakin taga 11 goge ido tayi kafin ta dauki wayan
Hlo kawata
Ina kike ne kam yau bakizo skll ba fatan kina lpy
Eh wlh ruky jiya banyi bacci bane saida asuba shiyasa namakara
Hummm kina nan kina aikin banzan tunanin da kikeyi ko to Allah kyauta miki Ameen hidaya tace
Dan Allah ruky idan antashi kizo gidana inason ganinki zamuyi mgn ne
To hidaya zanzo amma saina koma gida na watsa ruwa tukunna
Haba ruky Dan Allah kifara zuwa
To shikenn naji zanzo
Yawwa kawata ngd saikinxo daga nan sukayi sallama
Wanka tashiga shap2
Tafito tashirya parlor tayi tasamu uwani tana zaune gaisheta tayi ta amsa ckin kulawa uwani tace hidaya wnn wani irin bacci kikeyi yau haka babu irin tashinki dabanyi ba amma kinkasa tashi har habiba tashigo miki sallama zasu wuce nace mata kina bacci kallon rashin fahimta tayiwa uwani tace zasu wuce INA kuma Dan itakam tamanta dawani zancan zasuje kano yau
Uwani tace ahh kano mn ko kin mantane sai lkcn ta tuna afirgice ta tashi tace yaya Abbas yatafi shine bai tasheni munyi sallama ba hawaye tafara tayi hanyar dakinta wayanta ta dauko tayi dealing din numb sa wato (my life)
Sunan datayi save din numb Sa kenn kira tayi yakai sau 5 ajere ba adauka ba hnklnta ne yatashi harwani zufa takeyi
Lkcn da hidaya ta kira Abbas yana kallon kiran amma dashike yaga new numb ne shiyasa yayi banza da kiran habiba tace ka dauka mn anata kiranka ajere kasan ko waye ne yi yayi kamar baiji me tace ba tasa hannu zata dauki wayar yabuge hannunta tace to kasata silent idan bazaka daga ba domin tacika min kunne kallonta yayi kafin yace Allah hajiya tacika miki kunne to ba saiki dauki mataki ba shuru tamishi SBD dai2 nan sun shigo garin kano habiba sai murna take kallonta yayi ya girgiza kai wayarsa ya dauka ya kira anas
Yace Mu hadu karfe2 gani na iso yanzu amma kafin nan akwai inda zamuje da hibbata idan mundawo zankaita su gaisa da ammi saina kaita gida OK kawai anas yace sukayi sallama tare da alkawarin zasu hadu karfe2
Cike da mamaki habiba ta kalle Sa INA kuma zamuje banza yayi da ita gamida hade giran sama dana kasa saikace bai taba fara,a ba hkan ne yasatayin shurun dole ta zubawa sarautan Allah ido
Hidaya zaune abakin gado ta zabga tagumi sai hawaye takeyi duk wulakancin da Abbas zai mata idan tagansa tanajin ddi shiyasa kullum ko da sau dari zataje wajansa to ba shakka da kuka zata dawo idan kuma bataje ba hnklnta yakasa kwanciya kiran numb Sa tasakeyi bai dauka ba zama tayi tana kallon wayan
Parking yayi awani Babban hotel kallon mamaki habiba tayi masa fuska kamar zatayi kuka tace me zamuyi a hotel kuma my luv Dan Allah ka kaini gida plss
Juyowa yayi ya kalleta fuska ba rahama kafin yace hibbata me kike nufi me kike mayar dani
Itace ko miye? dama ai dole zan kaiki gdn amma wlh saikin biyemun bukatata kuka tasaka
Dan Allah ka kaini naga abbana da mamana
Banza yayi da ita yafita amotan hotel din yashiga yayi burking yadawo wajanta bude mata kofar motan yayi ya kalleta yace fito batafiton ba illa ma kifa kanta datayi akan kafarta tana kuka ranshine yafara baci
Kifito nace ki gizau batayi ba juyawa yayi yace wlh wlh wlh kinjina rantse miki harsau 3 ko idan harkika bari nashiga mota bakifito ba wlh yanzun nan zaki koma bauchi ya juya da sauri habiba tafito ganin yanda yayi mgnr babu alamun sauki ko sassauci gaba yayi tabi bayansa
Ciki suka shiga har bedroom yamaida kofar yasaka mata key janyota jikinsa yayi atare da wayarsa suka saki kuka. Tsaki yayi yaga number dazu ne cike da masifa yayi picking shuru yayi sai kukan habiba dake tashi
Hidaya zatayi mgn taji kukan habiba hkanne yasata yin shuru muryanshi taji yana cewa ki rufamin baki mgn zanyi maganin kukan nan yanzu daganan hidaya bata karajin kowani sauti ba saina nishi
Numfashinta ne taji yana mata barazanar daukewa dafe qirjinta tayi tana karanto innalillahi wainna ilayhirrajiun
Ahankali ta sulale ta zauna akasan agado hawayen ma sun tsaya cak lumshe ido tayi wani bala,in,kishi taji ya tirniqe zuciyarta kasa motsi tayi ta kai kusan 30mnts ahaka kafin ta tashi da kyar bata gani sosae jaka ta dauka karami ta zuba kayanta kala4 tadauki duk wani abun da zata bukata tafito parlor tana layi Dan haryanzu bata dawo dai2 ba
Anty uwani!Anty uwani!Anty uwani!
Uwani tana kitchen taji hidaya tana kiranta da sauri ta karaso wajanta ganin tana shirin faduwa riqeta tayi tana tmbyarta lpyr ta kalau kuwa eh kawai tace kira mana mado yazo ya kaimu gida
Wani gidan ?uwani ta tmbyeta kuka tasa tace Dan Allah Anty uwani kikaini gida wajan masu sona kikaini awajan abbana da dad dina
Kikaini wajan mommana da mamuna da Yaya boo(Maleek) ta kuma sakin wata kuka mai taba zuciya hawaye uwani tafara kiyi hkr hidaya karki tafi gida duk wahala duk kunci komai wulakanci kishanye sa zakiiga ribarsa
Wlh yau bazan kwana agidan nan ba bakin ciki zai kasheni
Kiyi hkr mn hidaya karki mantafa innallaha ma'assabeeriin
Allah yana tare da masu hkr kinji ganin uwani zatasa jikinta yayi sanyi ne ta yunkura da kyar taja karamin jakarta tayi hanyar waje
Da sauri uwani tashiga daki dauko hijab da kulle kofa amma kafin tagama hidaya ta isa bakin titi kiranta uwani keyi amma harta tare napep tashiga tace masa kaini G,R,A kano road bamusu kuwa yaja kekensa Dan haka uwani ta hau mashin
Atare aka ajiyesu a gate riqo hannunta uwani tayi tace haba hidaya yanzu Dan Allah bakiji nasihan danamiki ba murmushin karfin hali tayi Anty uwani naji kuma nadauka amma kawai gidan nakeso naje
Amma hidaya aibaki tmbyesa ba shuru tayi kafin tace bazai CE komai ba ai tunda gida nazo
Eh ai koda bazaice komai ba yakamata ki tmbyesa yanzu dai kizo Mu koma gida tsayawa tayi galala tana kallon uwani na koma gida fa kikace wani gidan zan koma?
Gidanki mana hidaya
Tab wlh Anty uwani saidai ke kikoma amma nikam bazan koma prison ba gate din ta kwankwasa mai gadi yabude yana ganinta yahau dry ahhh umma sannu da zuwa murmushi tayi tace sannu baba sadau INA wuni ya aiki y rana
Lpy lau Umma INA yallabai Abbas da yar'uwarki atakaice tace yayi tafiya tashige ciki
Part din momma tashige
Momma kuma tafito dakin dad da alama kuma gyaran dakin takeyi
Ganin hidaya tayi kawai kamar Wanda ta diro daga sama ga jaka ahannunta
Tmbyarta momma tayi ke. Kuma daga INA haka da jaka ahannu rarraba ido tafara tarasa mai zatace uhum...ummm...uhummmnnn...momma....
Muhadu a next page
Taku har kullum
Zahra Abdul momyn ahlan
Comments
And
Share
0 comments:
Post a Comment