Kallonta momma tayi
Hidaya lpyr ki kuwa? Ina tambayarki kin tsaya kinamin kame2 menene ?
Samun kanta tayi da kasa fadawa momma
Kawai saitace momma nazo Hutu ne
Hutu kuma hidaya?wani irin hutu?
Ehh ahh !uhum..eh dama su Yaya Abbas ne sukayi tafiya ..shine..shine...shine...
Katseta momma tayi kin isheni da shine2 shine me?
Ido ta kwalalo waja shine nazo gida na huta inajin tsoron zama nika dai agidan nida Anty uwani
Momma CE ta juya ta kalli uwani
Uwani hakane?da gske ne?
Eh momma gsky ne to shikenn dazu sunzo nan ai kafin suwuce tace kina ina wai kina gida meyasa bakije skll ba
Shagwabe fuska tayi momma bacci nayi fa makara nayi momma tace kai doter ki rage wannan baccin ahakanne kuma mukeso muzama kwararrun lkt dry tayi tafice tana cewa dad yatafi office ko da abbana da Yaya kabeer da ya boo nayi missing dinsa wlh momma tace to ke yau Monday banda abunki wazaki gani agida hartasu daddy suntafi skll kema din bacci ne yahanaki zuwa
Murmushi tayi tace bari naje na gaishe da mamuna da Anty ramla(matar Kabeer)
Awajan tabar jakan momma ta kalla tayi murmushi ta girgiza kai Allah ya shiryeki hidaya daukan jakan tayi ta kai daki
Sallama taketa zabgawa tun kafin tashigo parlour din mamu amma shuru kiranta ta hau yi da iya karfinta mamuna!mamu na!
Fitowa mamu tayi daga dakin Abba da gudu taqarasa ta rungumi mamu tana tsalle dry mamu tayi tace kai doter waike bazaki girma bane dry take tana sunkuyar da kai tace mamuna murnan ganinki nefa amma naga kamar baki murna da ganina bari na koma to riqota mamu tayi tace haba dai ainafi kowa murna rabonki da gida ai an kwana 2 tun randa Abbas yazo daukanki fa murmushi tayi tace lahh eh wlh ashe hakane
Mamuna bari naje part din Anty ramla ai nazo kenn INA nan bata jira amsar mamu ba tafice abunta
Side din ramla tashiga a kitchen tasameta rungume ta tayi saida ramla da tsorata ta juyo da sauri dan ita bataji shigowar mutum ba kuma dady bayanan balle tace ko shine affan ma da kannansa duk suntafi skll
Haba hidaya ai saikisa nayi fitsari atsaye dry ta hau yima ramla ganin yadda duk ta tsorata cikin dry tace haba momyn dadyna saikace baki taba ihun labour ba wannan tsoro haka hararanta ramla tayi tace ke hidaya da bambanci in gama miki labour davan aidama kasan tunda ka dauka saika ajiyesa amma wannan fa akirasa da me?
Kallonta hidaya tayi
Mommyn dadyna haihuwa da zafi dry ramla tayi waya gaya miki ana bada lbr duk Wanda yashiga zaigani domin kinsan ance gani ya kori ji tabe baki hidaya tayi batace komai ba ramla tace kodai2
Kodai me Anty ramla?
Ah nasani ne ko zamu samu qaruwa tunda naji kinfara tmbya haihuwa da zafi
Ido ta zare gamida dafa qirjinta tace rufamin asiri momyn dadyna karwani yaji dry sosae ramla ke mata ganin yadda tawani firgice
Hira sosae hidaya sukasha da matar ya. Kabeer SBD ramla akwai son hira
Ko ba komai taji saukin abinda yake damunta
Duk da kasan zcyrta yana mata zogi saida akayi sallan azhar wajan karfe 2 saura tukunna suka fito a kitchen din bedroom din ramla sukayi alwala domin gabatar da farillah
KANO
Fitowa daga hotel din sukayi habiba saiwani hada fuska takeyi ko kallonta baiyi ba gidan ammi sukaje shap2 suka gaisa take tmbyarsa INA hidaya yace tana gida habiba ma gidansu zai kaita ammi tace gsky kam ka kyauta habiba ki gaishesu ko cikin ladabi tace zasuji ammi
Har gate ammi tarakosu suka Shiga mota ammi tace amma habiba zaki kawo mn ziyara ai kafin Ku koma eh ammi zanxo insha Allah
Yww to Allah yasa kigaida yan gidan duka zasuji
Ta kalli Abbas kai kuma fa sai INA naga saiwani sauri kakeyi kamar Wanda yadauko garwashi
Eh wlh ammina munyi da anas akan zamu hadu 2 gashi yanzu saura 30mnts 2 din tayi shiyasa nake sauri SBD yau akwai shariah da karfe3 ammi tace ayya to Allah ya taimaka yabada asaa da Ameen ya amsa yatada motar yafice ammi tana daga musu hannu
Saida ya kaita gida ya gaisa da mama SBD Abba yatafi aiki tukunna yafita ya kira anas
Anas yace mishi kasameni a office dina
Ko da ya isa saida ya tsaya a masallaci yayi sallah tukunna yashiga yasameshi
Tattaunawa sukayi yadda sharian zata kasance
Domin yace bayaso yakai sati akano
Anas ne yace Abbas hidaya kabarota agidan ammi ne
Mtsww oho bansani ba ai kana iya Kaje ka duba nifa kadameni da zancan yarinyan nan kodai sonta kakeyi ne kam ?saina sake maka ita ka aure
Girgiza kai anas yayi cikeda takaici domin kalaman abokinsa sunyi matukar bata masa rai cikin da shanshiyar murya yace wlh wlh Abbas INA jiye maka ranar da zaka fada son hidaya ranar da zakayi kuka da idonka akan hidaya domin dan hakkin da kai raina wataran saiya tsole maka ido
Abbas nayi maka alkwari rana irin ta yau zata zagayo kazo office dina kana Neman shawarata akan yazakayi da son hidaya alkcn kuwa insha allahu hidaya tayi maka nisa
Zansake yimaka wata alkawarin
Abbas alkcn ne zakaga tsagwaran rashin mutuncina Dan wlh zan mata da abokata kam mune nayi maka rashin kirki Abbas karka manta na fada maka KARUBUTA KA AJIYE
Tunda anas yafara mgn Abbas yake murmushi amma yanaji yafara cewa saiyayi kukan akan wannan yar'shilan fusknsa ya sauya
Tofar da yawu yayi gamida cewa god forbid!!
Ni Abbas alh mustapha hamza nafi karfin haka
Wlh anas dabadin yanda nakeji akanka ba to wlh babu abinda zai hanani banyi shariah da kai ba
Murmushin takaici anas yayi yace why not Abbas bazakayi shariah dani ba gafili ga mai doki
Tsaki Abbas yayi yace gaka malam mubar wannan mgnr rai ne kawai zaidinga baci muyi abinda yakawoni garinnan danna fada maka banaso nafi 2days
Dage kafada anas yayi yace well Aiki yanzu yana gareka cigaba da tattaunawa sukayi amma maganganun anas sun tsaya masa a makogoro har ruwa roba daya ya shanye ko mgnr zata wuce amma ta tsaya qyam🤣
BAUCHI
Karfe 4 da rabi na yamma tsaye take a gate tana kwankwasawa mai gadi ya bude mata yana ganinta yaganeta kawar hajia hidaya CE RUKAYYA gaisawa sukayi tace hidaya fa
Ai bata nan dazu tafita da jaka da hannunta itada uwani
Ina sukaje? ta tmbyesa
Wlh bansani saidai ki kirata OK kawai tace tashiga dealing din number hidaya ta kirata wajan 7 miss calls amma batayi picking ba tsaki ruky tayi gashi tagaji tunda daga mkrnt take ko gida bataje ba balle ta watsa ruwa ta wanke gajiya
Tunani tashiga yi to INA hidaya taje gidan Anty salma ne ko gidan Anty safina ko kuma gidansu taje tsaki ta kuma yi mai gadi yace yadai ruky tace bata dauka ba kuma ni wlh agajiye nake idan tabari naje gida bazan fito ba kuma tace tanason ganina
Gashi bansan taqamaiman gidan dataje ba kuma wlh bazan iya sintiri ba yace bari na kira baba sadau kotana Babban gida ne
Yauwa nagode kuwa kira
Bugu 2 baba sadau ya dauka sallama yayi suka gaisa kafin yace baba hajiya Umma tazo gida ?
Eh tazo tana nan! lpy dai ko? Eh lpy baba kawartace tazo
To shikenn yakashe wayar
Kallon ruky yayi hajiya tana Babban gida gdy sosae ruky tayi masa taciro 500# tabasa tace yasa kati gdy yayi mata
Taje bakin titi ta tsari adaidaita tace yakaita g,r,a kano road
Hidaya kuwa tana can side din Anty ramla wayarta kuma yana handbag dinta data zubardasu a parlor din momma ta kwashe ta kai mata bedroom shiyasa ruky take kiranta batayi picking ba
Harsu Affan sukadawo amakaranta Anty safina CE takawosu kasancewar skll dinsu daya da basma
Da gudu suke mata oyoyo tace babu ruwana daku tunda Baku taba zuwamin weekend ba basma tace Anty hidaya wlh inason zuwa momy nace taqi kawoni muryan Anty safina CE ta katse basma tana cewa ke rabonki da gida na tun yaushe ai jiya yazo shida habiba amma kekam hajiya kina gida
Basma tace lahhh ni kuma uncle Abbas cewa yamin banga Anty hidaya ba nemanta fa momy sukazo yi kum.....bata karasa ba Affan yatoshe mata baki ya hade rai yace ban hanaki yawan surutu ba kinaso mubata ko
Girgiza kai tayi da sauri tace sorry Yaya nadai bazan sake ba dry muhsin yayi mata shagwabe fuska tayi kmar zatayi kuka
Yaya kaga ya muhsin yanamin daria kallon muhsin yayi ya hararesa da sauri yariqe bakinsa yana mayarda dryn momynsu tace kuwuce kucanza kaya kuyi shirin islamiyya kallonsu yayi yace kuwuce da Sauri kuwa suka wuce Anty safina tasa dry tace da kyau Yaya dady aikinka na kyau kunya yaji ya sunkuyar da kai kasa yana murmushi hidaya tace dadyna kukeji
Hira suka hauyi harsu Affan sukatafi islamiyya
Dukda dai shi yayi sauka rafee,a ne zasuyi nasu yanzu
Ko da ruky tazo tsayawa tayi tarasa wani part ne
Zata shiga can ta hango usaina mai aikin momma kiranta tayi ta juyo usaina taganeta Dan haka da sauri tazo suka gaisa tace INA hidaya
Tana bangaren Anty ramla
OK ngd momma tana ciki ne
Eh tana nan Anty ruky
To bari nashiga wajan hidayan zan shigo yanzu
To kawai usaina ta amsa tatafi aiken da akayi mata
Sallama ruky tayi alkcn hidaya ce kadai zaune a parlor amsawa tayi gamida miqewa da sauri tanayiwa ruky oyoyo tureta ruky tayi ta hade rai ke yanzu fisabilillahi Dan tsabaragin wulakanci daga skll fa nake kikece nafara zuwa gidanki kinsan kina nan shine baki fadamin ba naja can gidan kuma inata kiranki SBD rashin kirki bakayi picking
Daura hannu akai hidaya tayi Dan Allah kawallita kiyi hkr wlh nima bansan zanxo nan ba wayar kuma yanacan part din momma a handbag dina kiyi hkr plss kinji
Is ok ya wuce to kawass
Hugging dinta hidaya tayi tace ddina da ke saukin kai ruky tace ba kamar mijinki ba ko mai taurin kai bata rai tayi banson cin fuska kuma mn
Anty ramla CE tashigo tace ah rukayya kina nan abunki wato tunda kawarki tayi aure shikenn muka nemeki muka rasa dry ruky tayi wlh ba haka bane Anty ramla karatun ne yadauki zafi
To Allah ya taimaka tace ameen
Jan hannunta hidaya tayi tace muje kigaishe da mamu saimuje part din momma kugaisa kafin mushiga daga ciki mugana murmushi Anty ramla tayi tace eh lallai kam dry sukasa suka fice
Saida tagaishe da mamu sannan sukaje ta gaishe da momma
Sannan suka shiga daki
Zama sukayi hidaya tafita takawo mata kayan motsa bakin kafin tazauna ta rafka tagumi shuru sukayi nadan wani lkc kafin ruky tace hidee meke faruwa ne kam akwai matsala ko?
Ai kuwa kaman jira take tasaki kuka ckn kuka tace
Kawata ya Abbas zai kasheni kasheni yakesonyin wlh ckn tashin hnkli ruky ta ajiye cup. Dindake hannunta ta janyo hidaya
Dan Allah kibar kuka kawata kifadamin abunda yafaru
Tace dole na fada miki ruky ke kawatace tunna yarinta kinsan komai akaina nima kuma haka babu damuwar da bazata dameni ba tareda kinsani va
SBD rashin adalci irin na Yaya Abbas zasuyi tafia shida matarsa amma bansani va kwashe lbrn abinda yafaru lkcn da takai mishi abinci da ganinsu datayi shida habiba da ciwon datayi harta kwana asibiti da fadan da Anty salma tayimishi tace sai ranar yake fadawa Anty salma zasuje kano ance yatafi dani sai kallon banza yakemin shiyasa nace bazanje ba Allah kiyaye hanya
Da safe namakara zasutafi ko sallama baizo munyi ba inata kiran wayarsa baidaga ba sai akarshe daya dauka SBD Cin mutunci kawai banda saukar nishinsu babu abinda nakeji Dan Allah ruky kibani shawara yazanyi shiyasa na dauki kayana kala 4 nazo gida ko zcyta zatayi sanyi
Ajiyar zcy ruky ta sauke kafin tace tin farko hidaya na fada miki amma kikace kinji kuma kingani zaki iya
To tunda kuwa hakane ko kimiqe tsaya acikin gidanki domin kwatan yancinki ko kuma kicigaba da zama sakarya kamar yadda kike ayanzu
Tace to kamarya miye abunyi murmushi ruky tayi tace kai haba karki bani kunya mn saikace va mace ba
Hidaya dole kizama yar'bariki agidanki kinunawa Abbas kema kece kidingasa damanmun kaya kuma kananu zare ido hidaya tayi tace ayanzun ma yana kare balle nayi abunda kikace kullum saiyace banda kunyafa
Murmushi ruky tayi tace ai tunda aka shafa fatiha to kunya yaqare Idan kuma kika biye mata zaki mutu ba ido
Shawarwari ruky tabawa hidaya sannan tace kidaina nunawa kuma kinajin tsoronsa sannan kidinga suturta sonda kike masa SBD tsaro
Ajiyar zcy hidaya ta sauke tace ngd sosae kawata
Ba komi kinwuce haka
Sallan magriba sukayi
Ruky tace zata tafi kar Umma tayi mata fada hidaya tace kibari muyi sallan isha saimukaiki nida ya boo
Babban parlor sukaje momma na tsokanar ruky wai itama tafiddo miji asha biki tace momma ba yanzu va mamu CE tace to rukayya sai yaushe ?
SAina gama karatuna
Haba rukayya ai aure baya hana karatu tunda ga kawarki ma tanayi
Eh hakane momma amma nikam nafison hnkli ya natsu waje daya bayan nazama ana kirana da DOCTOR RUKAYYA zainayi auren dry suka hau mata sukace to allah kaimu ta amsa da ameeen
Abba ne da dad suka shigo da sallama da alamu daga mallaci suke sannu da dawowa sukayi musu Abba ya kalli hidaya
Ummanmu yaushe akazo
Abbana tundazu Nazo dad yace Umma Fatan komai lpy ko eh dadna komi lpy sallama ya kabeer yayi shida yaransa Affan da muhsin nan parlourn yakidime da hiran family tace waini INA ya boo ne kam Anty ramla tace yaje zance muryanshi sukaji yanacewa zance ana INA kuma ana zaune kalau ihu ta saki ta miqe da gudu tayi hugging dinsa
I really miss u wlh ya boo
Dry yayi yace ni wlh kinma bani kunya shagwabe fuska tayi kunyar me kuma hannunta Yakama yakaraso parlor yagaishe da iyayensa sannan yace INA Mamie ? Tayi bacci cewan momynta
Kai bacci da wuri haka amma ina fata lpyrta kalau
Eh lpyrta lau gajiyace kawai kasan mamie da gagara
Hidaya tace ah wlh mamana batada gagara hira sosae suka hauyi hidaya tace ya boo zamukai ruky gida idan mukayi sallan isha to kawai yace yamiqe yafice
Bedroom suka koma domun yin sallar isha
Hidaya ta idar wayar ruky y hau ringing daukawa tayi dataga umma CE fada umma ta fara dataji muryan hidaya tayi shuru
Umma kiyi hkr sallah take gamunan zuwa yanzu tana idarwa tace tashi Ku kaini tace wlh saimunci abinci hakan kuwa akayi bayan suncine ruky tayimusu sallama maleek da hidaya suka kaita hargida
Ahanya ne yake gayamata zaije lagos jibi tace xanbika yace aa kibari ayi Hutu zamuje duka amma nikam zanfara zuwa SBD mom kubra tace bamusan ziyartan ta tace to Allah kaimu hira sukaci gaba dayi harsukazo gida
Anty ramla tace gsky munkusan mudaina yin girki muba mawani gwauro agidan nan dry maleek yayi domin yasan dashi take Abba yace kyalesa ramla saina bada sadakarsa ai momma tace wlh dayafi
Hidaya tace. Ya boo kona nemo maka ne
Banso ainima ba makaho bane nandai sukaci gabada hiransu har kowa watse hidaya ta dauko Mamie ta tayata kwana wayarta taduba amma ba Miss din Abbas aikinda tasaba shi tayi kafintayi bacci
Washe gari taje skll tadawo taje gidan anty safina ta wuni itada maleek kasancewar maleek da Anty safina akwai shakuwa mai karfi sallama yamata akan cewa gobe zaije Lagos Allah yakiyaye hanya tayi masa saidare sukaje gidan Anty salma tace Dan Allah yagaishe da mom sosae yace zataji
Da washe gari yadaga da safe yabi jirgin Lagos
Hidaya saida ta rakashi har airport
Abbas yana nan yana aikin abunda yakaisa habiba kuma tana gidansu amma takaiwa su matan ya mukhtar da ya sabeer ziyara harda ammi
Ya Isa Lagos lpy driver din mom CE yadaukosa
A airport
A Babban gate din gidan sukayi horn mai gadi yabude musu suka shiga
Har cikin gidan driver yamasa jagora da karamun trollynsa
Sallama yaketayi a parlor din amma yaji shuru zama yayi akan daya daga ckn kujerun parlorn masu numfashi
Ya lumshe ido wani sanyayyan kamshi ne yadoki hancinsa ba shiri yabude idon yasauketa akan wata kyakkaywan budurwa Wanda bazata wuce 20years ba murmushi mai karya zuciya tayi masa Wanda yaqara sakashi mutuwan zaune
Kodai gamo yayi ne kam danshi baitaba ganinta bata
______________________
To masu karatu wacece😜kodai agske yayi gamo dinne
Ku biyoni domin muji
More comments more typing........
(Zahra Abdul momyn ahlan)
Comments
And
Share
[10/25, 2:55 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*NA*
*ZAHRA ABDUL*
_(Momyn ahlan)_
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Bismillahi rahmanirrahim
PAGE2⃣9⃣_3⃣0⃣
Karasowa gabansa tayi tace sannu da zuwa bro maleek kasa amsawa yayi au ashema tasan shi ne murmushin karfin hali kawai yayi tashi tayi taje takawo masa ruwa dasu drinks tace bro gashi bari na kira mom
To my sis abinda ya iya cewa kenan
Bata jima ba saiga mom tafito tana ganinsa ta hade rai dry yafarayi domin yasan hada ran namenene tashi yayi ya rungumeta oyoyoo gwaggo kubra bata San lkcn da tasaki dry ba tace kaci uwariyonka nice gwaggon din
Ehmn zama sukayi har kasa maleek ya duqa ya gaishe da mom kafin yatashi ya koma kujera kusa da ita ya zauna
Tace ai wlh Abdulmaleek kun kyauta kwata2 bakuson zuwa inda nake waima kuma ahakan gwarakai akan Abbas
Hakuri yashiga bata kafin tace ba komai yawuce kai kam ka wanke laifinka saura
Su
Yace yww mom dina
Waini mom Dan Allah wannan budurwan fa dana gani takawomin drinks wacece
Daura hannu akai mom tayi tace yanzu Abdulmaleek bakasan yar'uwarka ba manal ce fa kanwar ameera
Yace nidai mom wlh bansanta ba ni duk atunani na Anty ameera ce kawai yar'ki kuma ko da mukazo bikin sis bangantaba
Tace ok lkcn taxo amma kuma sai aka kirata sunada exam ba shiri tana kuka ta hada kayanta ta koma
Ina take da zama dama?
Tana sch ne a ibadan shiyasa
Yace mom gsky nima yar'gida za ayi ina son kanwata kuma aurenta zanyi dryn farin ciki mom tayi tace ahh ni ina ruwana indai kuna son juna mgn yakare
Tashi mom tayi tana kiran manal tazo ta rakasa part dinsa na musamman da aka tanadar masa
Har bedroom tarakasa tace kayi wanka saika fito kaci abinci
Kashe mata ido daya yayi yace INA fatan kece kika girka min ko kunya taji ta rufe idonta da tafin hannunta tafice da gudu tana dry tare da jin wani farin ciki na daban wani sabon yanayi takeji akan Dan uwan nata
Bayan yafito wanka Anty safina ya kira suka gaishe take cemishi ya isa lpy yace mata qlu
Antyna albishirinki tace goro fari qal yace wlh ina zuwa nasamu matar aure ckn murna tace da gske yace wlh
To wace haka mai sa,a
Yace ya'gidan mom ce manal tace haba
Wlh kuma my Anty kinsan wani abun kunyan bansantaba sai yau Allah ni duk atunani na sis meera ce kawai yar'mom
Dry sosae Anty safina tayi kafin tace gsky kam anji kunya tunda Yaya baisan kanwarsa ba yanzu kuma yafada soyayyar ta
Zaka dawo jibin ne ?
Wa? ni wai Anty safina ai yanzu babu mgnr dawowa sainayi sati dry sosae anty safina tayi race lallai kam to kagaishe su saimunyi mgn bye
Anty salma ya kira suka gaisa sannan ya kira iyayensa yace musu ya isa lpy sukace masha Allah ya gaishesu duka zasuji da kiran hidaya zaiyi sai ya tuno warhaka batadawo daga sch ba
Tashi yayi ya koma parlour yaganta tana zaune tana waya tana dry isowarsa ne yasa tace idan baki yardaba gashi kiji miqa masa wayar manal tayi batare daya tmbyeta ko waye bane yakarba yayi sallama ihu ameera tasaki wlh shine Dan uwana barka da zuwa yaushe zakazo gidana
Dry yayi zanzo ai sis INA gari sainayi muku sati ahh to gsky kam
Inasu anty's dina da iyayena da kanne na da ya'ya' na?
Suna lpy duk sunce agaisheku kafinsu zo
Ayya muna amsawa nandai sukayi hira kafin sukayi sallama
Bayan kwana2
kwance yake yana tunanin daya zame masa jiki wato kalaman amininsa anas Wanda kullum yawo yake masa acikin kwakwalwa afili yace ni Abbas ne zan fada soyayyarki hidaya ni Abbas ne zanyi kuka da idona akanki hidaya no karyane bazaiyu ba anas kayi karya wlh wannan ranar bazatazo ba mtsww waima miye na damun kaina da wannan tunanin banzan nan ne kam mtsww tashi yayi yashiga ckn gida ammi tana zaune a parlour tana duba newspaper sallama yayi yashigo ckn kulawa ammi ta amsa zuwa yayi ya kwanta kan cinyarta Abbas yadai naganka haka kwana biyun nan fa nakasa gane maka meke damunka gayamin numfashi yaja ba komi ammi gobe zamu koma bauchi insha Allah dry ammi tayi tace kodai kayi missing din doter hidaya ne gabansa ne ya buga da karfi Wanda baisan dalilin hakan ba hummm kawai yace tace to Allah kaimu ka fadawa matarka ta shirya ne ? Eh ammi na fada mata zan biye gobe na dauketa muwuce to yayi kyau Allah kaimu ya amsa da ameen
Da washe gari da sassafe bayan sallan asuba ya kira habiba
Hibbata ki shirya yanzu gani nan zuwa sonake kafin karfe 11 muna bauchi bata iya ta amsa masa ba Dan tunjiya suke rigima yabarta tayi sati saitadawo amma fir yaki yarda dan haka baisa ran zata amsa ba ya kashe wayarsa yana cewa tunda dai za abi umarnina ai mgn yaqare
Karfe 6 da rabi yagama shirinsa sallama yashiga sukayi da ammi da baba mansur sukayi musu Allah kiyaye awaya ya kira su Yaya mukhtar sukayi sallama Dan yace sauri yakeyi shiyasa bazai biyo suyi ba Allah ya kiyaye hanya akayi musu kafin yawuce gidansu habiba sai hade rai take mamanta tana lallashinta gamida nasiha har gate ta rakota yafito ya duqa ya gaishe ta amsa ckn fara,a saida kunya takamasa yaji kamar yace habiba ta koma idan kuma yayi haka shi zai cutu shiyasa yayi fuska Allah ya kiyaye hanya tayi musu habiba tana shiga mota tasaki kuka da iya karfinta mama ta kalli Abbas tace da'na sai hkr fa kuje Allah yakare yace ba komai ameen
Hanya suka kama haka kawai yau yaji babu abinda yakeson yin TOZALI DASHI BAYAN HEEDAYA kukan habiba ne yadawo dashi hayyacinsa daga duniyar tunanin da yake sunyi tafiya mai nisa yaji kukan nata banakare bane Dan haka yasamu gefen titi yayi parking ko kallonsa batayi ba jawota jikinsa yayi ya rungume ta jikinta haryayi zafi alamun zazzabi cikin sigar lallashi da taushin murya yace haba hibbata yanzu dannace kizo Mu koma gida shine zaki dinga wnnan kukan ai koda nina mutu bazakiyi wannan kukan ba gashi jikinki yayi zafi zazzabi zai kamamin ke kiyi hkr kidaina kuka nayi miki alkawari zanbarki nan gaba kizo kiyi wata daya bama sati daya ba Ko kala bata ce masa amma ta sassauta kukan nata ta koma ajiyar zuciya idanunta sunyi luhu2 sun kumbura
Yace kinji hibbata tashi tayi daga jikinsa ta koma ta jinginu da sit din murmushi yayi azuciyarsa yace hibba rigima tuki ya cigaba dayi
Hidaya tana zaune a class itada kawarta ruky
Ruky sai mgn take mata amma hnklnta baya wajan Dan haka bataji mai ruky tace ba ganin sai zuba takeyi kamar ruwa batare da anbata amsa ba yasa ta tabota firgigit tace naam kawata me kika CE mtswww oho dallah malama bansani ba inata miki mgn kina can kina tunanin shaho
Kallonta hidaya tayi nikam ba tunanin shaho nakeyi ba tunanin mijina nakeyi gashi kin hanani na kirasa wlh idan yakara kwana2 hkr na zai kare saina kirasa riqe baki ruky tayi wlh hidi kina kiransa mun raba jaha dake duk abinda kikaga inayi bawai danna cutar dake bane to riban mai zansamu idan nayi hakan inaso yasan darajanki ne ni ba komai ba idan shi yadamu dake kuma yana tunawa dake meyasa ko a wulakance bai taba turo miki da text messages ba koda kuwa na zagi ne ? ckn fushi ruky take mgn tana gamawa ta kwashe su books din ta da bag dinta tafice hidaya tana kiranta ko kallanta batayi ba balle ta amsa hanyar gate ta nufa da gudu gudu hidaya ta riqota tace Dan Allah kawata kiyi hkr karkiga laifina wlh badagani bane daga zuciyata ne son Yaya Abbas halitta daga Allah ne bayin kaine bane kiyi hkr ta karasa mgnr da kwalla tam ckn idonta
harkasan ranta taji tausayin kawarta hannunta ta kama suka fice a makarantan tunda dama sungama lecture dinsu gidansu ruky suka wuce gaishe da mama sukayi Dan dama yanzu kusan kullum idan aka tashi sai sunje can kafn hidaya ta koma gida
Dakin ruky suka shiga ruky tafita taje kawo musu abinci nan sukaci
Bayan sungama ta kwashe kwanukan takai kitchen tadawo ta zauna
Tace hidaya soyayya mugun ciwo ne Dan ana mutuwa akanta nasani ba sauki amma fa ke kam yazama miki dole ki danne naki SBD son maso wani kikeyi kina sonsa yana son wata kwalla ta goge tace wlh kawata duk ranar dunia INA adduah akan wnn jarabawan da Allah yamin kuma INA fatan cinyesa kuma bana bakin ciki akai
Hakane Allah yadafa mn to ameen hidaya tace
Wayarta ta dauko acikin bag dinta ganin Miss calls tayi har 7 tace wayyo ashema ankirani dubawa tayi taga na Anty surayyah 3 Anty ramla 2 Anty ameera 2 murmushi tayi tafara kiran surayya tana dauka ta hau tsokanarta sisina kodai Mu shirya zuwa India suna ne dry surayyah tayi Allah ya shirya minke hiransu sukasha cikeda kewan juna daga bisani sukayi sallama ta kira Anty ramla bata daga ba Anty safina ma haka ajiye wayar tayi tacigaba da hidimarta da ruky
12 suka iso bauchi Dan haka gidansu ya wuce alkcn kuma habiba ba karamin zazzabi bane ya rufeta suna shiga aka hau yimusu sannu da zuwa gaishe da mamu sukafara zuwa sukayi kafin suka Shiga part momma nanma gaisawan sukayi
Momma ta kalli habiba amma bakida lpy ko eh zazzabi ne yakamata. cewan Abbas momma ta hau shi da fada meyasa bai bartaba tunda batada lpy habiba tace momma ciwon ahanya ne inaji gajiyar mota ne
Ayya to sannu kinji ku samu Ku karasa gida ko kuma muje asibity
Aa momma basai anje asibity ba zansha mgni kawai momma dakanta ta hado mata tea tabata magani tacewa Abbas su wuce gida kawai
Suna zuwa gidan yyi horn mai gadi ya bude suka shiga
Dukda habiba batajin dadi amma saidata share gidan ta goge tayi wanka ta kwanta shima dakinsa yashiga yawatsa ruwa
Haka kawai ya tsinci kansa da tashi yaje duba hidaya
Yana zuwa yataba kofar yajita gam akulle mamaki ne yakamasa to inataje wata zucia tace masa taje skll mn to amma kuma uwani fa maybe taje unguwa juyawa yayi ya koma bedroom dinsa ya kwanta anas ya kira
Anas yana daukawa yace abokina muhadu anjima a,,,,bai karasa ba yace masa INA bauchi
Au wai kai dama da gske kake yau zaka koma murmushin dauriya yayi yace ba yau zan koma ba dai zakace yau na koma tunda gani kwance agidana kuma agadona to yayi kyau mutanan nan sunce sungode sosae wlh
Yace ba komai bari na Dan taba bacci zamuyi mgn anjima
Wasa2 har dare baiga hidaya ba kuma yasan idan tadawo taga motarsa ba shakka zatazo amma shuru kakeji
Hidaya kuwa sai bayan magriba ta koma gida babu kuma Wanda ya gaya mata Abbas yadawo
Da washe gari ma haka koda ya shirya zashi office baiji motsinta ba hakan kuma yasa yadamu Wanda shidai yakasa sanin dalilin damuwar dakin habiba yaje yaji jikinta yakara zafi Dan haka yafasa zuwa office din yadauki habiba yakaita asibity nan aka tabbatar masa tana dauke da cikin wata daya da sati biyu murna yashiga yi yana tsalle shima zai zama dady mamu ya kira yafada mata nan tayi masa murna fadawa yan gidan tayi suma murna suka tayasa amma hidaya batasan shagalin da akeyi ba yanzu ta mayar da hnklnta akan karatunta ba laifi
Har yau ta kama sunday weekend ba skll Dan haka tana gida kuma har yau batasan abbas yadawo ba shima yadamu din daya ganta amma ynz jinyar habiba yakeyi Dan ba laifi kam cikin yana bata wahala
Mamaki ne Yakama momma ganin Abbas yadawo kwanansa uku amma baiyi mgn akan hidaya ba ya gwadama kamar baisan tana gidan ba koda kuwa yazo daukan abinci baya mgnr ta momma shuru tayi ta zubawa sarautan Allah ido
Lagos
Soyayyah da shakuwa mai karfin gsk yashiga tsakanin maleek da manal Wanda sukeji kamar sunkai shekaru atare
Hidaya tana daki momma ta kirata tace Dan Allah doter taimaka kiyi dambun shinkafa yanzu za azo akarba to tace ta tashi tayi hanyar kitchen ckn 30mnts tagama ta zuba ta rufe tayi dakin momma taje tace mata tagama momma ta zare ido harkin gama doter tana murmushi tace eh momma nagama
Kai amma gsky Allah yamiki albarka my baby dry tayi tace ameen momma tafice adakin
Bayan hidaya tafita ne ya kira momma yace Dan Allah abama wani abincin yakai zaije asibity karbama habiba mgani momma tace kasan dai mado bayanan kuma sabon driver baisan gidanka ba yace to wlh momma bansan yaza ayiba kuma bataci komai ba tace dambun shinkafan take jira shuru momma tayi kafin tace tunda hidaya yau tana gida bari ta kai mata
Jin momma ta kira sunan hidaya saida gabansa yafadi au dama yarinyan nan gida tatafi eh lallai kam amma afili yace to momma ngd ya katse kiran
Kiran uwani momma tayi tamata jawabi tace ki kira hidaya Ku shirya saikuje to tace kafin tafita taje ta kira hidaya tace mata ta shirya sukai abinci batare da tunanin komai ba ta shirya suka kama hanyar statelocost
Ganin uwani tanayiwa driver kwatancen gidanta ne yasata dago kai tace anty uwani mai kuma zamujeyi agidan ? zaki gani ai hidaya
Shuru tayi amma qirjinta sai dukan tara2 yakeyi
_________________________
Tofa yanzu idan hidaya tasan ma habiba tayiwa dambun shinkafa
Shin zata batane ko bazata bataba ?tunda ba kulata takeyi ba sannan idan suka hadu da Abbas yazata kaya
Duk domin jin wannan Ku biyoni a next page
________________________
Comments
And
Share
0 comments:
Post a Comment