Horn driver yayi a gate din gidan gabanta na tsananta faduwa budewa mai gadi yayi suka shiga kallon uwani tayi tace anty uwani kinzo da key's ne eh naxo dasu gashi ta bata karba tayi hanyar part dinta tayi domin tayi missing dinsa budewa tayi tashiga ta lumshe ido haka kawai taji wani farin ciki
Uwani kuwa part din habiba tayi tasameta kwance a parlor sallama tayi ta bude ido ahnkl ta amsa sallaman gaisheta uwani tayi sannan ta mata sannu da jiki kitchen tayi domin dauka plate ta zuba mata abincin
Hidaya kuwa jin uwani bata shigo bane yasata fitowa tana zuwa parking space tacewa driver INA Anty uwani hanyar part din habiba ya nuna mata yace tayi nan cikin fushi tayi hanyar tana tambyar kanta mai tajeyi awajan
Tana zuwa ta tura kofan tajita abude mamaki ne yakamata shiga tayi a lkcn kuwa har uwani ta zubawa habiba dambun shinkafan nan tana gani taji yawunta yatsinke tadaga spoon zatakai bakin kenn hidaya tasaki ihuu gamida cewa keeeeeeeeeeeee ba habiba ba harta uwani ta tsorata saida habiba tasaki spoon din akasa jikinta ya dauki barin domin ta tsorata matuka
A harzuke tace wai dama make nayiwa dambu eh lallai kam Ashe rainani da akayi yayi yawa to baki isa nayi miki girki ba ashe kundawo. Ne keda Mijin naki ayyo shiyasa aka sani nayi miki dambu to karyanki bazakici ba tunda hidaya tafara balbalin bala,i, uwani takeson yimata mgn amma bakinta baiyi shuru ba habiba kuwa kai ta sunkuyar kasa duk abinda hidaya zatace baidameta ba indai zata barta taci dambun
Kan habiba tayi afusace uwani tasa hannu zata riqota amma inaa ta fizge
dambun tasa hannu zata kwace ahannun habiba tanaja hidaya naja tazo matsar da hannunta kawai yabuge habiba awuya jitayi kamar awuta tasa hannunta da sauri tasaki plate a tsorace
Uwani tace haba hidaya me kikeyi ahakane kam batada lpy ne fa sai alkcn taji tausayin habiba yakamata amma afarko kishine yarufe mata ido kallonta tayi ckn tausayi tace kiyi hkr sannu ya jikin kunya ne yakama habiba tace. Da sauki hidaya da kanta tadaukowa habiba wani spoon kafin tafice zata koma part dinta karo sukayi shima yazo shigowa tana ganinshi taji gabanta yafadi wani irin dadi taji gamida farinciki zata miqe tayi hugging dinsa saita tuno da mgnr ruky nanda nan ta hade rai atakaice tace sannu taraba ta gefensa ta wuce suman tsaye yayi SBD mamaki anya kuwa hidaya ce? Ya tmbyi kansa yakai kusan 15mnts awajan yana tsaye har uwani tafito suka gaisa da kyar ya iya jan kafarsa daya masa nauyi yashiga wajan habiba
Tana zaune sai sambadan dambu take zama yayi kusa da ita ckn murna yace hibbata kece kike cin abinci haka gsky naji ddi murmushi tayi tace kaci kaji wlh yayi mugun dadi ba musu kuwa ya hauci yana santi gsky momma na dole ne abata lamban yabo wajan kwarewa agirki habiba tace ko abawa matarka hidaya ba ruwa yazo sha amma saida ya fuzardashi yace me kikace tace abinda kajinnan dai shinace tana fada tana aikawa da dambunta
Hidaya kuwa tana shiga tasaki nauyayyan ajiyar zcy takira ruky tabata lbrn yadda sukayi da habiba da yadda suka kwashe da Yaya Abbas dry sosae ruky tayi tace yww wlh kin burgeni
Dan Allah babu ruwanki ita amma shikam kigasa masa kwakwa ahannu tace angama kawata
Gyara part dinta sukayi ita da uwani share2 da goge2 sai turaren wuta nanda nan wajan ya dauki kamshi
Suna gamawa tashiga tayi wanka ta shirya tace Anty uwani tashi mutafi uwani tace muje ina kuma hidaya
Inda muka fito mn tayi hanyar kofa ganinsa kawai tayi yana tsaya awajan kofa ko kallon sa batayiba tace zan wuce fuska ya hada kamar Wanda baitaba dry ba hidaya ta tsorata matuka amma ta danne yace idan kika sake kika fita agidan nan zakiga true colour dina tabe baki tayi tace to saime gidanmu zantafi fizgo hannunta yayi ya kaita dakinta ya kulleta yaje yacewa driver yatafi abunsa
Ya koma dakinsa ya kwanta yana tunanin yaushe hidaya ta falle haka harta fara raina shi ko dai taga wani abu atare dashi ne waima miye kwana biyun nan yakejin wani abu akanta wata zuciyarsa tace sonta kake da sauri ya miqe zaune INA karya ne ba sonki nake ba idan kuma kika sakemin wani rashin kunyan saina hukunta ki yadda baki tsammani
Ko da yafita uwani ce ta bude hidaya tace mata kibi umarnin mijinki tunda yace karki fita
To Anty uwani momma da mamu fa basusan nadawo nan ba
Sun sani mn tunda dama hutu kika ce musu kinzo sbd bayanan yanzu kuma gashi yadawo haka dai uwani tadinga bawa hidaya Baki harta hkr ta zaune
Da daddare taje wajan habiba domin tmbyarta ko zataci wani abun SBD uwani ta fada mata habiba ciki gareta batayi mata bakin ciki ba SBD duk qaruwa zasu samu Dan haka zatadinga kula da ita indai wajan abinci ne amma babu abinda zai canza wajan yanayin zamansu
Shiga tayi har dakin karonta na farko kenn da ta taba shiga dakin habiba photo tagani na ya Abbas da habiba saida ta hadiye wani qululun bakin kishi da kyar tayi sallama habiba ta amsa tace zakici wani abu ne nayi miki shuru habiba tayi kafin tace zanci danwake batare da hidaya tayiwata mgn ba tafice kitchen din habiba tashiga domin tayi mata
Tana cikin yi wayarta ya hau ringing tana dubawa taga sweet ya boo da murmushi afuskanta ta dauki wayar gamida sallama amsawa yayi sannan suka gaisa cikin tsokana tace INA amarya domin nasan duk inda akaga zara za,agan wata
Dry yayi yace wlh kamar kinsani gata nan akusa bata mu gaisa miqewa manal wayan yayi takarba tace sisina dry hidaya tayi tace babu wani kin hanasa dawowa ai gwanda kibarsa yadawo asamu ayi mgnr biki musha shagali muryan Maleek taji yana cewa jibi zan dawo ai ayita taqare hidaya tace yakamata kam
Hira sosae suke sha awaya tanayi tana aikin danwake tazo tashi ne ashe yaji motsin mutum a kitchen habiba kuma batada lpy balle yace itane shiyasa yashigo ya duba karo sukayi duk ta mulka masa danyen garin danwaken data kwaba cikin bacin rai ya duba jikinsa yaga duk ta batasa shako gashin kanta yayi da iya karfinsa tayi2 tayi ihun neman ceto amma takasa
Baya2 yayi da ita wajan gas gashi akunne yake da ruwan zafin da ta daura da kyar tace Yaya Abbas wuta wayyoo momma kizo ki ceceni mamu zai kasheni baya sona ya tsaneni duk wnn abun bata kashe wayar da takeyi dasu Maleek ba wayar ta fadi kasa
Sakin gashinta yayi ya fizgo ahannunta yamatsar da ita wajan gas din kuka takeyi Wanda da kyar yake fitowa
Y,,ya,,,y,,ya,,ab,,,abb,,bs,,,,han,n,n,,nu,,,na ,,hannu,,,na,,, kana,, ji,min,,,,cii,wo,,, bai San tana fadi bama
Yace wato ke gaki marar kunya ko kin rainani yanzu kisani ni Abbas bana daukan raini saitaki zanyi duk mgnr dayakeyi bataji sosae SBD tsintsiyar hannunta daya damka iya karfinsa saidaya gama gayamata maganganu son ransa tukunna yasaketa yafice a kitchen din babu Wanda yasan abunda ke faruwa uwani tana can part din hidaya habiba kuwa tana kwance adaki tana jiran danwake
Maleek kuwa dayakejin abinda ke faruwa ran shi yayi matukar baci yace gobe zaibi jirgin safe ya koma bauchi.
Koda yasaketa kasa tsayuwa tayi ta zube kasa hannunta kamar yanka dabba ne aka zuba jini yayi wani jajur kamar garwashi wani azaba takeji Wanda tunda mahaifiyarta ta haifeta bata taba ji ba da kyar tagada jajayen idanunta tana neman wayarta can ta hangosa glass ma harya fashe da kyar tayi jada ciki ta dauki wayar uwani tadinga kira amma ba ta dauka ba ta kira Anty salma itama bata dauka ba wata wahalalliyar kuka ta kuma saki SBD azaba ya isheta jitake kamar mutuwa zatayi afili ta furta insha Allah na rabu da kai kenn har gaban abada Anty safina ta kira itama yaita ringing batayi picking
Wayyo nashiga uku Dan Allah Ku dauki wayar nan karna mutu bakuzo ba
Momma ta kira ringing biyu ta dauka kuka tasaki momma Dan Allah kizo yanzu karna mutu momma zan mutu kizo yanzu Dan Allah hnkln momma ne yatashi tahau tmbyar hidaya lpy meyasameki kedawa
Hidaya babu baki sai kuka hnkln momma yayi qoluluwa wajan tashi hijabi tasaka da takalmi daban tafice tana kwalawa driver kira
Kaini gidan da kukaje dazu kuma kayi Sauri ganin yanayinta ne yasashi gudu amma ahakan momma tana cewa baya sauri
Ana zuwa bata jira ya tsaya ba tafice amotar part din hidaya tashiga uwani na zaune a parlor tana ganin momma taji gabanta yafadi momma tace uwani INA daughter
Tace tana can wajan habiba juyawa momma tayi uwani tana biye da ita sallama momma keyi amma parlourn shuru uwani ce tayi hanyar kitchen SBD hidaya taga yamata zataje mata girki ne ganin haka momma tabi bayan uwani
Turus uwani ta tsaya gamida sakin ihu tace hidaya harta suma momma ne taganta kwance kamar gawa hannunta suka gani jajur cikin tashin hnkli suka dauketa sai AMINIYA HOSPITAL
Tofa more comments more typing.....✍🏻✍🏻✍🏻
Sai mun hadu a next Page
Comments
And
Share
[10/25, 2:55 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*NA*
*ZAHRA ABDUL*
_(Momyn ahlan)_
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Bismillahi rahmanirrahim
Page3⃣3⃣_3⃣4⃣
Momma da uwani sai sintiri sukeyi a reception sunkasa zama saida likita yafito yace musu su kwantar da hnklinsu tasamu rauni ne ahannu sannan hannun ya karye amma sun daura ta zuwa anjima zata tashi insha Allah kuka momma tasaki uwani kuma tana sharan kwalla domin tasan dayan biyun ne bazai wuce Abbas bane
Har wajan karfe 10pm hidaya bata farka ba dad kuma sai kiran momma yake SBD bata fadawa kowa ba tafita inama taga natsuwan tsayawa tafadi yanda taji muryan hidaya awaya
Uwani ta kalla tace Bari naje gida na gaya musu halin da ake ciki ki tsaya akanta SBD karta farka ba kowa akusa da ita dad dinsu yanata kira yanzu kuma naga hardasu mamu da ramla dasu salma
To momma saikin dawo
Yawwa
Bayan Abbas yafita a kitchen din
gidan ma gabaki daya yabari yayi tafiya mai nisa kafin yayi parking agefen titi kanshi ya kifa kan sitiyarin mota
Ohhh Abbas me na aikata haka nan da nan yaji zcyr shi takaraya motar ya tada yayi hanyar komawa gida
Habiba tana kwance adaki har wajan karfe 9 da rabi taji hidaya shuru tashi tayi da kyar sbd wani jirin da taji yana shirin zubar da ita da sauri tariqe bango tanabi ahankali harta fito parlour hanyar kitchen tayi tana shiga ta tsaya tana kallon ikon Allah gashi wasu kayan akasa ga danwake an kwaba ga ruwa akan gas kitchen din ne kace2 mamaki sosae takamayi tace to meya faru kuma Allah dai yasa hidaya lpy take sbd wani faduwan gaban dataji ya ziyarci zcyrta lkc daya hanyar fita tayi domin taje ta duba hidaya saiga shi yashigo kamar an wullo shi tsayawa habiba tayi tace mishi daga INA kake INA hidaya kallonta yayi yace bata nan ne domin kafin yashigo saida yabiya part dinta yaga akulle
bangane ba da tana nan har zatamin danwake tundazu najita shuru nazo na dubata ko lpy sainaga bata nan kuma gashi can ta kwaba danwaken shuru yayi yana sauraronta
Gani tayi yana zufa tace wai menene kam Abbas INA hidaya? Meka mata?wlh ban yarda da kai ba INA hidaya ?
Abin mamaki sai hawaye kawai tagani a idonsa
Itama zufan taji yafara kamata ckn tashin hnkl ta kuma tmbyarsa INA hidaya bai boye mata komai ba yabata lbrn abinda yafaru
Habiba kasa kuka tayi ta zube kasa ta zauna tana kallo abbas hannu ta daura akai tasaki wahalalliyar kuka nashiga uku Abbas ka kasheni zaka jamin sharri to yanzu INA taje ai wlh zaman gidan nan bai ganka ba fita zakayi kanemo ta Ku kulata baiyi ba yafice
Asibity
Sai karfe 11 hidaya ta farka da kuka uwani ta riqota tana tmbyarta meya sameta kuka kawai takeyi uwani tafara lallashinta amma duk batasan tanayi ba wani azaba takeji yana ratsa cikin hannunta har kwakwalwar kanta ga hannun yamata nauyi ckn kuka tace anty uwani bani wayata ba musu tabata
Batayi la,akari da dare bane tayi dealing No din surayyah
Surayya tana bacci ta farka afirgice mijinta dake kusa da ita yariqota yana tmbyarta meya faru
Tace nayi mafarkin kanwata ce hid....bata karasa ba wayarta yahau ringing da sauri ta duba taga hidaya gabanta taji ya tsananta bugawa daukawa tayi da sauri cinkaro da kuka tayi ckn tashin hnkli surayya ke tmbyar knwr ta ta meya sameta ckn kuka ta hau bawa Anty surayya lbrn abinda yahada su bacin ran da surayya tashiga baya misaltuwa
Ckn murya kamar tasa kuka tace. ki hada kayanki ki taho India gobe2n nan tace to kafin ta katse kiran duk wnn mgnr da tayi agaban uwani
Abinda bata sani ba shine lkcn da tafara bada lbrn alkcn su dad momma mamu ya kabeer Anty ramla Anty safina duk sunshigo
Tana daga kai ta gansu momma da dad suman tsaye sukayi Anty safina ta juya zata fita da sauri mamu tariqota sannu sarauniyar masu zcy INA zakije
Mamu dan Allah kisake ni wlh duk yanda akayi wnn matar tasa akwai hannunta aciki
Hidaya tace wlh Anty safina ba ruwanta kallonsu dad da momma mamu tayi Wanda suntsaya kamar basu motsi
Dan Allah Ku kwantar da hnkln Ku gobe Idan allah ya kaimu sai akira family meeting asan ta inda za afara gyara abun
Ficewa dad yayi momma tabi bayansa batare da sunce komai ba
Hidaya tace uwani kije ki karasawa habiba danwaken dana fara mata kinga batada lpy wani kallo Anty safina ta zabgawa hidaya saida ta tsorata ya kabeer ne yamata yajiki tareda saida safe idan an sallameta zaixo ramla ma fita tayi
Hidaya tace Anty safina anan zaki kwana
Eh nan zan kwana
To basma fa ?
Tana gida wajan momma
Nan dai gurin yadauki shuru kowa da abinda yake tunani amma tunanin hidaya yafi yawa
Haka yagama yawansa baiganta ba kuma yasan yayi aika2 bai isa yace zaije gidan Anty salma ko Anty safina ba balle yace zaije gidansu shiyasa ma yakashe wayoyinsa gaba daya
Domin fitan dad daga asibity yata kiran Abbas din amma sai ace masa switch up shiyasa dad ranshi yaqara baci ranan ko rintsawa yakasa hakama momma itama takasa baccin
Shima kuma Abbas din baidawo gida ba kuma yasan dole habiba ta kirashi shiyasa na kashe wayoyinsa domin yaji da abu daya
Washe gari
Likitan da zai sallamesu baizo da wuri ba Dan haka sai wajan karfe goma tukunna aka sallamesu kafin lkcn Anty safina ta kira Anty salma tace tazo ba lpy za ayi meeting
Karfe nawa ne meeting din?
Karfe daya tace to zanxo
Hidaya na zaune a parlour momma takawo mata abinci tana bata abaki amma takasa kallonta balle tayi mata mgn hannunta hidaya takama tace mommana bazaki kalleni ba ki kalle daughter dinki kuka momma tafara ta rungume hidaya kiyi hkr my daughter Allah saiya saka miki wlh zakiga sakayya kiyi hkr murmushi tayi hawayee na zuba tace momma ba komai wlh ni zan iya yafe masa SBD bazanso ace ganawa ya lalace ba momma Dan Allah keda dad yanda naga ranka yabaci Dan Allah ko a kuskure ne karkuyiwa Yaya Abbas baki wani sabon kukan ne ya kufcewa momma tace insha Allah bazamuyi masa baki ba daughter amma ahankali zaiga hukuncin ubangiji Dan wlh Allah bazai barsa ba saiya saka miki marainiyan Allah kuka ne ya kwacewa hidaya nan momma tadinga lallashinta tana hawaye itama
Habiba shuru2 ba Abbas balle tayi tunanin ganin hidaya gashi itama a zaune ta kwana takasa bacci tabarace tafado mata
Tashi tayi tasa hijab dinta harkasa tana tafia da kyar harta fita bakin titi adaidaita ta tsara tace yagaita g,r,a kano road
Tana isa kai tsaye part din momma tashiga a parlor tayi sallama tsayawa tayi tana kallon hidaya ga hannu yasha bandage kuka tasa tazo kusa da ita tace hidaya maiya sameki shuru tayi ta sunkuyar da kai kasa
Habiba zata kumayin mgn kenn taji muryan Anty safina tana cewa INA mijinki tun jiya muke nemansa amma duk phones dinsa akashe
Jikin habiha ne yayi sanyi yanda taga Anty safina ta sauya mata karfin hali tayi tace Anty safina nima wlh bansani ba tunjiya yafita wai yaje nemanta batare da Anty safina tabawa habiba amsa ba tafice a parlorn
Abbas kuwa hotel yaje ya kwanta abun duniya masa yawa kunna wayarsa daya yayi ya kira habiba lkcn tana tare da hidaya adaki Dan momma tace su koma daki da sauri ta duba ta kalli hidaya tace shi yake kira fa saida taji gabanta yafadi daukawa habiba tayi shuru yyi itama kuma batace qala ba tayi shuru yakai kusan 10mnts baiyi mgn ba dayaga itama ba mgn zatayi tukunna yace
Ya ake ciki?
Dame? Tabasa amsa atakaice
Yace anganta ?tmbyar tabatawa habiba rai wlh Dan mijinta ne da tafada masa wani mgn amma saitace kanemota ne?
Duk mgnr da sukeyi hidaya tanaji domin habiba takarawa mata akunne tanaji
Murya saikace na Allah yace Dan Allah hibbata kidaina tayarmin d hnkl d wnn maganganun naki dame zanji kuka tasa
Wlh bakaga tashin hnkl ba kazo yanzu2 tunjiya ake nemanka agida nima inacan kuma umarnin dad ne da momma sunce kazo yanzu tana gama fadi takashe wayar bai Ankara ba saiga kiran dad jikinsa ne yadauki rawa yadauka dad akufule yace kazo yanzun nan yana gama fadi ya katse kiran tashi Abbas yayi zaije koma miye ayita takare amma gsky yanzu yanason hidaya
(Haba abbas kama kara ai daga baya kenn)
Karfe 12 da rabi maleek ya sauka a bauchi taxi yahau yakaishi gida lkcn daya iso yagasu dad da ya Kabeer zasushiga masallaci Dan lkcn sallah yayi gaishesu yayi sama2 sannan shima yayi alwala suga shiga tare bayan an idar ma tare suka fito sukayi ckn gida
Gaishe da iyayensa mata yaje yayi SBD Abba baya kasan yayi tafiya
Fitowa yayi zaije part dinsa ya hango motar Abbas tsayawa yayi yahade giran sama daba kasa kamar baitaba dry ba har abbs yayi parking yafito yana ganin yanda Dan uwan nasa yahade rai Wanda tunyana karamin baitaba gani ba yasan cewa yaudai kam saita Allah yana zuwa kusa dashi yabude maki zai mgn kenn yaji saukan mara!Tass!Tass! Lafiyayyu kuwa har 2 saida ya duqa domin marin yashigesa tashi yayi idonsa harsun canza
Yace bro ka mareni? Ckn daqilalliyar murya yace kozaka rama ne? nace ko zaka rama ne ? yadaga hannu zaikara zuba masa wani yaji muryan Anty salma tana cewa innalillahi yau maizangani haka maleek Abbas tsayawa maleek yayi jikinsa harna bari abinka da mutumin dabayada saurin fushi
Riqesa Anty salma tayi tace wai meke shirin faruwa ne kam agidan nan ckn barin rai maleek yahau bata lbr tungada wayar dasukeyi harzuwa abinda yafaru zufa Anty salma keyi ta ko INA
Ta kalli Abbas tace hakane? Maleek yace Anty saikin tmbayesa hannu tadaga maleek alamum yyi mata shuru tace Abbas da kai nake hakane ? Hawaye ne yafara ambaliya a fuskansa kafin yace eh anty hakane
Tace lallai na yarda Abbas ka rainani ko yakema harda iyayenmu kuwuce mushiga
Babban parlorn abba aka hadu
Dad na fitowa baiyi wata2 ba yarufe Abbas da duka baji bagani da kyar ya Kabeer da maleek suka janye dad momma tace saura nawa da sauri mamu tariqota tace aa Dan Allah bafa duka aka taru ayi anan ba idan kuma ba haka ba bari nakira Abba gyara za ayi ba barna ba tuni hidaya ta hau kuka ganin yanda dad yajibgi ya abbs saikace jaki
Parlorn yadauki shuru can zuwa anjima dad yafara mgn ckn daga murya har parlorn yana amsawa
Wato kai gaka ishashshe ko nizaka tozarta Abbas to wlh karyanka kayi kadan ka tozartani Abbas shin kasan tarihin wnn family kuwa? Kasan tarihin familyn malam hamza kuwa? Shin kasan darajan sunan hidaya kuwa? Hajara sunan uwatace wacce ta tsuguna ta haifeni shin kasan tarihin zaman da iyayenmu sukayi bisa soyayyah da gsky da riqon amana shin kasan kalar soyayyar dake tsakaninmu SBD dashi su uwa da umma suka rainemu
Kafin kace me parlor ya gauraye da kuka sai muryan dad dake mgn harbari yakeyi
Yacigaba da cewa
Da wannan soyayyar muka tashi harba a iya banbace koba ciki daya muke ba
Idan harka mance wacece hidaya anan Abbas ni yanzu ubanka mustapha zan tuna maka
Itace dai yar' gidan! Kuka ne yake Neman Cin karfin dad saida. Yayi ta tukunna kafin yadanji sauki azcyrsa yacigaba da cewa itace yar'gidan wannan mutumin kirkin nan Wanda lkcn da aka haifeka yakeji da kai bayason bacin ranka Wanda shida matarsa ba kalan soyayyar dabasu nuna maka ba hardani ubanka! Ba kowa bane face magaryi Yaya Usman da Anty raliya
Kuka dad keyi kamar yaro nadama ne matuka yakama Abbas Wanda yanzu shi karan kansa yasan bazata masa amfani ba
Kuka hidaya take habiba natayata
Hidaya ckn kuka tace Dan Allah dad momma mamu kuyi hkr Ku gafarceni duk nice najawo haka da tun lkcn dayace baya sona da hkr nayi amma kuma son Yaya Abbas halitta daga Allah ne bayin kaina bane amma yanzu kam SBD hnkln kowa ya kwanta na hkr da Yaya Abbas har gaban abada gobe zantafi India zan koma wajan Anty surayya da zama Dan Allah dad amincewan Ku nake bukata idan kuka hanani zan iya mutuwa
Da sauri dad yace ba komi Umma Allah ya kaimu goben Maleek saiya kaiki airport saikibi jirgin safe
Kowa yatashi cewan dad
Abbas yanaso yayi mgn amma yakasa kowa yatashi yabarsa yana zaune awajan
Habiba bata jirashi ba ta koma gida abunta
Haka shima yatashi jiki babu kwari ya koma gida Dan babu Wanda yasake masa fuska
Mamu ta kira Abba tabasa lbrn abinda yafaru ba karamin bakin ciki yayi ba sannan ba karamin mamaki Abbas yabashi ba da ace wanine yayiwa hidaya haka da ba shakka sai yayi zaman prison
Ranar Abbas baiyi bacci ba SBD tashin hnkln yaje yayita yiwa habiba mgn taqi kulasa
Da washe gari
Da asuba Abbas yaje gidansu Dan yasan ana bude kofa ana tafiya sallah
Bayan anshiga antada sallah ne yashiga gidan kai tsaye dakin hidaya yanufa lkcn tafito daga toilet tayi alwala zatayi sallah ganin mutum kawai tayi juyawa tayi da gudu zata koma toilet din SBD ta tsorata saurin riqota yayi muryan kaman zaiyi kuka
Plss hidaya ki saurareni kiyi hkr nayi Babban kuskure kiyafeni karki tafi Dan Allah wlh na tuba nayi nadama mutsu2 take tanason ta kwace. Ahannunsa amma yariqeta kam karshe ma rungumeta yayi ckn jikinsa kamar takoma ciki da zama tayi2 ta kwace takasa kawai tasaki kuka
Hakanne yasa yasaketa ckn kuka tace abu 1 tak zan fada maka Yaya Abbas ngd !ngd !ngd ! da sakamakon soyayyar dana nuna maka nangaba koda wani yaqini bazanji haushi ba SBD nawa ma yaqini roqon da zanyima na karshe shine kafita adakin nan tunkafin na tsaneka ! Ba karamin sanyi jikinsa yayi ba ba yanda ya iya ganin yanda take kuka yasa yafice SBD bayaso ta tsane shi
Gida ya koma yashiga part dinta ya hau kuka
Karfe 7 tagama shirinta Maleek ma yashirya sallama ta hau yi da yan gidan kowa fuskansa babu walwala Mamie tasa kuka Anty hidaya zanbiki lallashinta hidaya tayi tace da anyi hutu sai ya boo yakawoki kafin ta yarda
Momma rungume hidaya tayi kafin tasaketa tace daughter Allah ya kaiki lpy zai munyi waya
ta juya tashiga daki tana hawaye SBD tashaku da hidaya tun tana karama suke tare
Fitowa sukayi su kaga Anty salma da habiba
Mota suka shiga sai airport
Nan ta kalli Maleek Wanda idonshi jajur murmushi tayi tace sweet ya boo idan baka murmushi kafi kyau dama kata zama haka kallonta yayi ya fahimce abinda take nufi murmushi take amma idonta hawaye ne aciki tam Dan haka yayi hugging dinta yasaketa yashiga mota yana kuka rungume Anty salma tayi tana hawaye ta juya ta kalli habiba Wanda tun zuwansu batayi mgn ba kuma bata dago kanta ba
Kusa da ita hidaya tayi tace Allah ya saukeyi lpy
Dago kanta habiba tayi ta kalli hidaya zatayi mgn sai kuma takasa fashewa da kuka tayi da karfin gske rungumeta hidaya tayi karo na farko kenn
Ckn kuka habiba tace hidaya Dan Allah karki tafi kiyi hkr sakinta hidaya tayi tace anan aka haifeni amma ko amafarki bana fata nadawo saduwar alkhairi
Taja akwatynta tayi hanyar shiga jirgi
Awajan habiba ta durqusa tana kuka Anty salma CE ta dagota tasata amota suka kama hanyar gida
Agurguje
Bayan hidaya ta isa India Anty surayya da mijinta suka daukota kuka tadinga yi Anty surayya tana lallashinta
Bayan sati daya
Fasalta Mu Ku yanda Abbas ya koma bata lkc ne
Hidaya kuwa mijin surayya yanema mata wata mkrnt a delhi tana zuwa kuma kullum tana waya da yan'gidansu
Amma kullum tazo bacci saitayi tunanin Abbas
Maleek agaban momma yana cewa momma
Inason manal yar'gidan mom kubra afirgice momma ta miqe tace wlh Maleek baka isaba bazaka aure yar'gidan mom ba ayyo wato Dan uwanka ya auri dayan ya wulakantata shine kaima kakeso ka auri manal to baka isaba
Tashin hankalin da Maleek yashiga bai misaltuwa domin yakasa mgn
More comments more typing
Comments
And
Share
0 comments:
Post a Comment