*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO and AUTAR HAJIYA
0⃣1⃣
*BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHEEM*
*Dukkan yabo da godiya, suntabbata ga ubangijin talikai, ubangijin rana da wata, mai tsiro da tsirra akan 'kasa, mai rayawa da kashewa adukkun sanda yaso*
*Allah kai dad'in tsira da aminci ab shugabanmu annabi Muhammad (S.A.W) da ahalinsa gidansa da sahabansa, da manzanninmu,*
*Ya Allah kabamu ikon rubuta labarin nan, ka kuma bamu ikon kammalawa lafiya kuskuren dake ciki Allah kayafe mana, abinda yake dai-dai Allah kasa ya amfani al'umma amin*
*Wannan novel 'ka gaggen labarine, bamuyi shi dan wata kowaniba, idan abinda muka rubuta yayi dai-dai ga rayuwar ki/ka kuyi ha'kuri daga idea ne balaifin writers ciki*
>>>>>>>><<<<<<<<<<<<
Tafe muke nida Qurratul-ayn, tunaninmu yau kuma ina zamuje samo muku 'kaya taccen labari.
Wani layine da muka, shiga yaja hankalinmu, domin tsarukan gidajen layin abin kallone, wucewar da zamuyi ta jikin wani gida da 'kofar gate d'in ke bud'e, Qurratul-ayn ce tata'boni tana fad'in "Zee Yabour kalla kigani, da alamu akwai labari agidannan" najuyo da sauri ina kallon 'kofar gate d'in, danni da nasaki baki da hanci da ido ina kallon wani gida, daya tafi da dukkan tunanina.
Wata matashiyar yarinya ce nagani, kyakkyawa fara sol, da ba zata wuce shekaru goma sha shida da haihuwa ba, ri'ke da tiyo a hannunta, tana bawa flowers dake garden ruwa, Kayan jikinta duk sun yayyage sun tsufa daga gani sun ji jiki,
Wa'ke-wa'kenta kawai take, kai kace babu abinda ke damunta arayuwarta.
Zulum! Zulum!! Faqeer!!! Faqeer! taji muryar mahaifinta na kira.
"Na'am Daddy" ta amsa cikin sanyin murya.
"Kina ina? zo nan" mahaifin nata yafad'a.
Tayi saurin yar da tiyon, dake hannunta jiki na rawa taje ta dur'kusa gabanshi, kanta sunkuye 'kasa, tana kallon 'kasa, bata ta'ba bari su hada ido, tun wata rana da by mistake suka hada ido ya Wanketa da mari yace shi sa'anta ne, da zata hada ido da shi, tun lokacin take tsoron had'a ido dashi.
Dadyn nata Yace "kalleta sumi-sumi kamar ta Allah, ba kiran ki nayi kizo ki du'ka mun, kamar wata mai neman gafara ba, na kira ki ne na gaya miki ki had'a yan tsumukaranki yau, zaki bar gidan nan domin na d'aura miki aure da Alhaji Mamman!"
Damm!!! gabanta yayi mummunar fad'uwa, yayin dataji Kanta yayi wani masifar sarawa, bata san lokacin da ta d'ago kai ba, charaf idonsu ya had'u,
Kakkauran mari taji ya wanke fuskarta dashi, har sai da ta fad'i 'kasa cikin kakkausar murya, yace "sau nawa zan gaya miki kada ki ri'ka hada ido dani, 'yar jakar uba mai kashin tsiya" Yayi tsaki.
Zafafan Hawaye ne ke kwaranya daga idanunta, cikin sanyin muryarta tayi 'karfin halin fad'in
"Dan Allah Daddy kayi ha'kuri, kar ka aura mun Alhaji Mamman tsoho ne, wallahi bana son shi Daddy, kayimin rai karufamin asiri, kabarni incigaba da zama anan" tafashe da wani matsanancin kuka, tare da kifa kanta akan 'kafarsa.
Daddy yajanye 'kafarsa da 'karfi, kanta yabugu da 'kasa, zafin buguwar ya'kara sanyata kuka, cikin 'bacin rai Daddy yacigaba da fad'in "Yi mun shiru! nan ko in tattaka ki, na gaji da ganinki cikin gidan nan, nafi son naga ba'kin kare akan ganinki a yanzu, Allah ya kawo mun hanyar rabuwa dake, cikin sau'ki dan haka ki tattara kayanki anjima nan da daddare za'a zo daukar ki".
"Lafiya dai nakeni jin kuka?" Mummy ce ta fito tana tambaya "ya aka yi ne Alhaji ina ta jin hayaniya".
Dady yakau da kai gefe, yana cewa "Wannan abar" ya nuna ta da yatsa "na aurarwa Alhaji Mamman, shine zatamin rashin kunya ta nunamin ita 'yar zamani ce, zata nunamin tayi gadon ba'kin halin uwarta, waini zata kalla, tacemin batason za'bin danayi mata" yayi kwafa, tare da haurinta da 'kafa.
Momy tazaro ido tare da dafe 'kirji, cikin kid'ima ta furta, "Aure fa kace Alhaji? wato yanzu ka fara son yarinyar nan, da har zaka aurar da ita ga mai kud'i, kuma yanxu idan ta tafi wa zai dinga yin aikace-aikacen gidan nan, bama wannan ba shi yace yana sonta ne?"
Daddy yace "kinsan yanzu kud'i na sun 'kare a caca, to bazan iya ha'kura da caca ba, da ita na dogara, ta hanyarta na zama abinda na zama yau, shiyasa na sata a caca da cewar duk wanda yaci cacar shi zai aureta, sai Allah yasa Alhaji Mamman yaci, anan take aka d'aura auren akan sadaki naira d'ari biyar(500) ".
Mummy ta kyalkyale da dariya tace "hakan shine dai-dai shi yafi dacewa da ita, amma kayan d'aki fa, waye zaiyi?".
Daddy yace "kema Hajiya da maganar ban haushi kike, Wannan faqeer din zan wa kayan d'aki, wallahi ko sule na ba zai yi ciwon kai ba, yadda take matsiyaciyar ta haka za'a kai ta a tsiyar ta".
Mummy tayi dariya tace "yauwa Alhajiji na, zomuje daga ciki, nashirya maka dukkan abinda kakeso, manta da wannan kucakar".
suka shige ciki, suka barta nan, tana kuka kamar ranta zai fita, a fili tahau fad'in
"Anya Daddy shi ya haife ni kuwa? ban ta'ba tunanin tsanar da yake mun har ta kai ya sani a caca ba, a daura aurena akan sadaki 500, wannan wacce irin tsana ce Uba kema yar'sa na rasa me na yiwa Daddy ya tsane ni haka, Wayyo Allah na! Mahaifiyata kina ina? Nasan ko'ina kike ina ranki, kuma ke baki tsane ni ba, kome zan aikata arayuwata.....!"
Kukane yaci 'karfinta sosai, amma babu mai lallashinta Zuciyarta nata tafarfasa kamar zata fito waje
Sageer(kaninta) yazo wucewa ta ri'ko shi tana cewa "Dan Allah Sageer ka ro'kan mun, Daddy, kar ya aurar dani ga d'an caca tsoho".
Sageer Ya bige hannunta ya hankad'ata tafad'i 'kasa Yana tad'in "Dallah ni sakeni, kin ta'bani da wannan kazamin hannunki naki, kar ki shafa mun tsiya, hakan ai shi yafi dacewa dake" ya tofa mata miyau ya wuce.
Wani kukan ta sake fashewa dashi, ita ba miyau da ya tofa mata ya dameta ba, dan in wannan ne kad'an ne daka wulakancin da take fuskanta a gidan, rashin wanda zata kai kukanta gareshi shi ke mata ciwo.
Ta tashi da 'kyar ta nufi gate inda baba mai gadi ke zaune, domin shine kad'ai takejin dad'i agunsa, duk cikar gidan.
Tana isa yaganta duk tafita hayyacinta, cikin rud'ewa Yace "lafiya Noor me ya sameki, me kuma aka miki yau?".
Fuskart fal hawaye ta dubi Baba mai gadi, murya adashe sabida tsabar kuka Tace "Baba dan Allah Daddy shine mahaifina na ainihi kuwa ?"
Baba mai gadi yayi shiru, can yace"Eh shine mahaifinki *Noor* shi ya haifeki"
"To in shi ya haifeni meyasa ya tsane ni haka, kuma ina mahaifiyata take, ba wanda ya ta'ba gaya mun inda mahaifiyata take, ko meyasa ta tafi ta barni, nasan ba zaka rasa sani ba, tunda ka dad'e a gidan nan"
Baban mai gadi yayi ajiyar zuciya yace "Tabbas ina da amsoshin duka tambayoyin nan naki, dole ne infasa bara gurbin kwan daya dad'e ina lailayashi a hannuna, dole zanfad'a miki dukkan abunda ya faru................................!"
*Ku biyo mu next chapter dan jin me yasa mahaifinta ya tsane ta kuma ina mahaifiyarta take, meye silar tafiya tabarta*?????
© *OHW*
🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!*
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
DOWNLOAD MORE NOVELS FROM. www.Hausabooks.com
0⃣2⃣
Baba mai gadi yagyara zama, batare data kalli Noor yasoma bata labarin asalinta.
*ASALIN NOOR*
"Alhaji Ibrahim Had'eja, asalin sa d'an garin had'eja ne dake jahar jigawa,
Iyayensa sun rasu, tun yana 'karami kuma shi kad'ai suka haifa, dan haka ri'konsa ya koma hannun kakarsa, bayan wasu shekaru kakarsa tasa ta rasu, hakan ne yasaka ya tashi sakaka a gidan ba mai kwa'barsa akan komai nasa, baisan dai-dai ba, bai kumasan ba dai-dai ba baya tan-tance fari da ba'ki a duk kan al'amuransa.
Sabida bai yi ilimin addini da na boko ba, kwata-kwata, dan idan an turo shi makaranta yawonsa yake tafiya baya xuwa,
A haka ya fad'a d'a sana'ar caca, ta hanyar wani abokinsa
Anan cikin unguwar da suke yi idan kakansa ya bashi kud'in break, sai yaje ya sasu a caca.
Tunda ya fara caca, ba'a ta'ba cin sa ba, ko da yaushe shi ke ci, dan haka ya fara samun kud'i sosai, kakansa yarasa ta inda yake samun kud'i, domin duk tambayar duniya bazaifad'i gaskiyaba, sabida hanashin da kakan yakeyi".
"Yana shekaru Ashirin da biyar, ya zama hamsha'kin mai kud'i millionaire, dan a lokacin cacar shi ta shahara, har 'kasashen waje yake fita ya buga caca yasamo ma'kudan kud'i.
Kakanshi yayi yayi ya hana shi, ya'ki bari,
Da yaga kakan nashi, na neman takura masa ya had'a kayanshi ya bar garin,
Ya koma Abuja inda ya kama hayar wani gida"
"Bayan wani lokaci kuma, ya siyi wani 'katon fili a Abuja cikin unguwar Garki II, yasa aka mai gina mai kyau, a lokacin kwata-kwata ba aure a tsarin shi a lokacin, amma yana da burin samun d'a namiji wanda zai gaje shi, ya tsani mace, a cewar shi mace bata da wani amfani, banda kai ta wahala da ita, ko aure tayi baka huta ba, shikuwa namiji zai girma ya nemi na kanshi, har kaima ka samu.
A wajen filin dayake ginin gidan sa, akwai wasu buzaye dasuke zaune a wajen, irin buzayan nan masu zama, wato (uncompleted building) dake xuwa daga nijer,
Anan yaga mahaifiyarki mai suna Zainab,
Ya nuna yana sonta, ba musu ta amince dashi ,Da yan'uwanta take zaune iyayenta sun rasu ,Yan'uwanta suka amince da auren, ba ad'au lokaciba aka d'auransu, amarya ta tare a Sabon gidan daya gina.
Bayan aure ya tare da amaryarsa Zainaba a had'ad'd'en Sabon gidanshi, yan'uwanta kuma ya basu ma'kudan kud'i, yace suje su nemi sana'a, daga lkcin suka tafi bata qara jin labarinsu ba.
Ya nuna ma mahaifiyarki so,'kauna da kulawa sosai, ita bata san yana caca ba, kawai yace mata shi d'an kasuwa ne.
A lokacin da ta samu ciki,
Yace mata shi namiji yake so ta haifa, baya son mace kuma idan ta haifi d'a namiji zai mata babbar kyauta, zai bata jari mai yawa, ta ri'ka yin sana'a, amma idan mace ta haifa kuwa, sakinta zai yi kuma sai ya kashe 'yar data haifa.
Zainaba taji tsoron wannan furuci nashi, kuma tayi mamaki sosai meye da 'ya mace da zai ce baya so, taga Allah ke bada haihuwa shi ke bada mace ko namiji, ba kai ke bawa kanka ba to dan me zaice baya son mace.
Haka ta cigaba da addu'a Allah ya bata d'a namiji.
Wataranar jumu'ah ce ta tashi da na'kuda Alhaji ya kaita asibiti yana ta murna yau za'a haifa masa d'a namiji.
Nurses din da suka kar'bi haihuwar, suka fito daga d'akin haihuwar, cike da murna ,
Suke ce masa ta haihuwa lafiya,
Yace mai aka samu?
Suka ce ya' mace
Take ya murtuke fuska, ya zabga wata uwar ashar yace, "Durowan uwa, wato duk abunda na gayawa Zainaba bata ji ba, shine ta haifa mun mace wallahi sai ta gane kurenta, sai ta gwammace mutuwarta da u'kubar da zan gana mata, zata san ba'a karya mun doka, inyi me da 'ya mace meye da 'ya mace banda tsiya(abunku da jahili amfanin ilimin addini kenan dan da yana da ilimin addini ba zai fadi haka ba).
Nurse d:in tace "ban gane ba Alhaji me kake fad'a haka? kar ka manta bafa ita taba kanta ba Allah ne ya bata"
"Kinga likita kama mun bakinki, ko inyi k'asa-k'asa dake wallahi"
Nurse ta ta'be baki tace "Allah ya huci zuciyarka" ta wuce abunta, tabarshi anan yana kumfar baki.
Zainaba na rungume da yar'ta, kyakkyawa fara sol, ga gashi yala-yala tana kallonta tana kuka,
Tana magana a fili
"Yanzu Alhaji kashe ki zai yi, ni kuma ya sakeni,
Ina sonki ya'ta, ina jinki a cikin jinin jikina, bana son rabuwa dake Ya Allah! Ka tsare mun ya'ta, kar kaba Alhaji ikon kashe mun ita,
Ni yanzu idan ya sakeni ina zani bansan inda yan'uwana suka tafi ba,
"Ya Allah dakai na dogara ka kawo mun agaji.......!"
Garammm taji an turo 'kofa' da karfi Alhaji ne ya shigo fuska a murtuke, kamar wani bajimin zaki,
'Yan hanjinta sai da suka kad'a, bata ta'ba ganinshi a irin wannan yanayin ba,
Kanta yayo da Sauri, da 'karfi, ya jawo dogon gashinta,
Tana kuka tace "Dan Allah Alhaji kayi ha'kuri kayi mani rai, wallahi ba laifina bane Allah ya bani.........!"
Gummm ya kai mata naushi a baki ,sai jini baki ya bud'e Yace "yi mun shuri yar'iska, ni zaki ma iskanci, ki karya mun doka, nace miki kar ki haifa mun ya' mace, shine zaki haifa mun, toh wallahi sai kin gane kuranki, sai na d'and'ana miki azabar da sai kin gwammace mutuwarki da ita, wannan shegiyar yar' kuma" ya nuna ta da yatsa "kasheta zanyi".
Zainaba na kuka tace "Dan Allah kar ka kasheta, duk azabar da zaka mun kamun, amma kar ka kashe mun 'ya....!" wani wawan mari ya wanke fuskarta dashi, tare da jan hannunta da 'karfi, duk abinda take mata, tana rungumeta da yar'ta.
Yace "wuce mu tafi gida"(bai ko jira an sallamesu ba), tana kuka yana jan'ta har suka kai mota,
Ya hankad'ata, da ita da jaririyar cikin mota
Ya figi mota sai gida......!
Baba mai gadi yayi shiru, a lokacin daya kawo nan a labarin, saboda hawayen da suka cika idonshi,
Noor kuka take sosaii tace "Baba cigaba da gaya mun, ya aka yi na rayu bai kasheni ba, mai yayimlwa Mahaifiyata kuma ina take yanxu???....................!
*kuyi haquri ku biyo mu next chapter dan jin wacce irin azabar mahaifin Noor ya gana ma mahaifiyar Noor kuma ya akai Noor ta rayu??*
© *OHW*
?
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗?
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣3⃣
Babah mai gadi yacigaba da fad'in "ina zaune bakin aiki, mahaifin yadawo tare da mahaifiyarki, yayi hon, natashi da sauri na bud'e mai gate, ko 'karasa bud'ewa banyiba, yadanno kan motarsa cikin gidan, da sauri namatsa dan kad'an yarage yabugeni, natsorata sosai da ganinsa, yawuce parking space, Yana parking motar cikin harabar gidan,
Ya fito tare da fizgota, ya jata zuwa cikin gida
tana ta kuka, ya fizge jaririyar a hannunta, ya jefar da jaririyar kan gado.
Ta tsandala ihu
Zainaba a rud'e tayi kan jaririyar, cikin zafin nama ya fizgota, yahau dukanta da belt, yana cewa "ni zaki ma iskanci, na d'auko ki cikin rugga na rufa miki asiri, dan ki haifa mun d'a namiji, shine zaki haifa mun mace".
Ya cigaba da zabga mata belt, Jaririyar nata kuka, sai ta tashi zata je wurinta ya jawota ya cigaba da dukanta.
Har jaririyar tai shiru ta daina numfashi
Wata gigitacciyar 'kara Zainaba ta saki, dashi kanshi sai da yaji tsoro,
Tayi wajen jaririyar tana fad'in "shikenan ka kashemin ita....." kafin ta 'karasa ya fizgota, ya ajiye belt d'in, ya cigaba da marinta kota ina yana haurinta da 'kafa.
Ana cikin haka, Wayarshi tayi ringing,
Ya d'auka ya kara a kunnansa.
Akace ana nemanshi yazo yanzu zasu buga caca, mai mahimmanci wacce za'a cankaci ma'kudan kud'i, nan da nan yakashe wayar, ya juyo kanta,
. Yayi k'wallo da ita, yace "bari inje in dawo, zaki ci ubanki kad'an na miki yanzu, kuma zan turo Baba mai gadi ya fitar mun da gawar tsiyar nan" ya nuna jaririyar, yaciga da fad'in " abu na 'karshe kuma kar kiga na fita, kice zaki gudu, wallahi kika gudu sai na nemo ki, duk inda kika shiga na kashe ki" yana kaiwa nan ya fice yana haki.
Kan jaririyar tayi tana kuka, jikinta duk ya mutu, ga haihuwa ga duka, tata'ba jaririyar taji kwata-kwata bata numfashi, ta rungume jaririyar tana kuka, kamar ranta zai fita.
A lokacin ni kuma na shiga, saboda Alhaji da yace nazo na fitar da gawar jaririyar.
Halin da naga mahaifiyarki ta bani tausayi sosai na kar'bi jaririyar a hannunta,na kalleta sosai nace "Hajiya ki kwantar da hankalin, jaririyar nan kamar bata mutu ba,Kawo ruwan Zam-zam da dabino mu gani"
Jiki na rawa, da 'kyar take tafiya, taje ta d'auko ta kawomin.
Na kar'ba na bude ruwan zam-zam d'in, nayi addu'o'i na yayyafa miki a fuska, na bud'e bakinki na zuba tare da dabino nan, cikin Ikon Allah kawai muka ga kina motsi.
Zainaba ta kar'beki tana murna tana wa Allah godiya,
Ganin jikinta rud'u-rud'u yayi jawur shatin duka yasa na tambayeta, mai yasameta, bata tsaya wani tunaniba,
Tana kuka ta gaya mun komai, duk abunda ke faruwa, na tausaya mata sosai, kuma na lallasheta tare bata addu'o'in da zata ri'ka yi, tai mun godiya sosai na koma bakin gate, cike da tausayinta, dana rayuwarta dake.
Alhaji na can wajan buga caca, cikin rashin sa'a aka cinye shi,
Yana ganin haka hankalinshi ya tashi, zuciyarshi ta 'kara harzu'ka yace "tunda yake ba'a ta'ba cin shi caca ba, amma sanadiyyar macen da aka haifa mai gashi an cinye shi caca, ya fara asarar dukiya tun ba'a je ko'ina".
A fusace yaja motarshi ya nufi gida, akan hanyarsane,
A radio'n mota yake jin hukuncin kisan kai, duk wanda yai kisa a kashe shi, hakan ya tada mai hankali, dan shi bai ta'ba sanin hukuncin kisa ba,Yace "yanzu idan Zainaba ta fad'a ni na kashe jaririyar nan, kenan nima kasheni za'a yi, na shiga uku, dole inyi wani abu in hanata fad'a".
Ko da ya dawo gida, Zainaba har tayi wanka, ta gasa jikinta, tama yar'ta wanka itama, tana rungume da ita a d'aki, tana aikin kuka abun duniya duk ya isheta.
Alhaji ya bangazo kofar d'akin ya shigo,
Zainaba ta zabura jiki na rawa,
Ganin jaririyar da yayi a hannunta tana motsi, yasa shi yin ajiyar zuciya, a ranshi yace "ashe bata mutu ba, nima yanzu ba za'a kasheni ba,
Yanzu da uwar da yar' zan had'a, na gana musu azaba, amma haka zan cigaba da zama da tsiya a gidana, gashi daga haihuwarta anci ni a caca", yaja tsaki.
Yayi saurin kawar da tunanin
Yace "keee, tashi yanzu bake ba hutu, kin zama yar aiki a gidan nan, daga yanxu d'akinki ya koma can kusa da na mai gadi, d'akin da ake ajiye kare da(before)".
Zainaba jiki na rawa tace "toh" ta mike(a ranta tana murna jin bai yi maganar yar'ta ba tana ro'kon Allah yasa ya fasa kasheta).
Daga lokacin azaba da u'kuba ba irin wacce mahaifinki baya gana muku, tun kina jaririya
Mahaifiyarki ta sa miki suna *Noor*(haske), ta kalleki tace In shaa Allahu sai kin zamo haske a rayuwar mahaifinki, sai ya dawo yana nadama, kuma sai yasan muhimmancin 'ya mace a cikin al'umma,
Mahaifinki da yaji sunan da take kiran ki *Noor* yaji kuma ma'anar Noor d'in, hakan yasa
Yace "in ita haske ce a gurinta, to shi duhu ce a wurin shi, kuma tsiya ce, dan haka yake kiranki *Zulum* wato duhu ko *Faqeer* (tsiya),
Kina wata tara a duniya ya sake aure, ya auro Hajiya Zulai(mummy)
A lokacin mahaifiyarki taga tijara da wulakanci iri-iri
ba irin cin mutunci da hajiya Zulai bata mata, Kina shekara d'aya tayi kucin-kucin tasaka Alhaji ya saki Zainaba, Yace "ta tafi ta bar mai gida, kuma ta tafi da yar'ta, ta manta ta ta'ba aurenshi balle tayi tunanin ta haihu dashi".
Mummy tace "a'ah kar ta tafi da yar'ta ta barta nan, shine hukuncinta, dan idan aka rabata da yar'ta sai tafi jin rad'ad'i akan abar ta da ita".
Alhaji ya amince da wannan shawara, duk da baya son ganinki a gidan.
Mahaifiyarki ba irin ro'kon da bata mishi ba akan ya barta ta tafi dake, amma Ya'ki, dan mahaifiyarki najin tsoron halin dazaki shiga, daya gaji da magiyarta, jan ta ma yayi ya fitar da ita daga gidan, tana kuka tana ro'konshi, baiko saurare taba.
Baba maigadi ya d'an yi shiru, yana share 'kwalla, "yace kinji yadda aka yi, Alhaji bai kashe ki ba, kuma mahaifiyarki ta tafi ta barki".
Sannan ya cigaba "daga lokacin kika taso cikin rayuwar kunci, wahala da tsangawama
Hajiya zulai kuma ta haifi ya'ya biyu maza, Sageer da Sameer
Alhaji ya d'au son duniya ya d'aura musu su da uwarsu, ke kuma ya tsaneki,
Har kannenki suka taso, suka ga irin tsanar da mahaifinki da mahaifiyarsu suke miki, suma suka d'au tsanar duniya suka d'aura miki, shine kike gani har girmanki.
*BACK TO LABARI*
Noor kuka take sosaii, kamar ranta zai fita, ta kasa cewa komai ,ji take kamar ta mutu ta huta da wannan tsanar da kowa yake mata, a gidansu, musamman tsanar da mahaifinta yake mata itace tajawo mata komai, kuma ya zata iya rayuwa da tsoho, wanda ya girmi mahaifinta, d'an caca a matsayin mijinta, ita meye laifinta, tunda ba ita tayo kanta ba da za'a ce ba'a sonta an tsane ta.......................!?
® *OHW*
🏵 🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* ? 🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣4⃣
Noor tami'ke, jiki babu kwari tana sharar hawaye, tana duban Baba mai gadi amma takasa cemai komai.
D'akinta na kusa da baba mai gadi,ta tashi ta koma ,ba komai a d'akin sai tabarma da ledarta, ta kaya kala uku su kadai ta mallaka a duniya.
Tana shiga tazauna, kan tsohuwar tabarmarta takifa kai da ciny tana aikin kuka.
Kuka take tayi tana tunanin sabuwar rayuwar da zata fara yanzu .
Muryar mummy ta jiyo tana kiranta Zulum! Faqeer!
Noor ta amsa Muryata a dashe, saboda tsabar kuka tace "Na'am momy",
Ta tashi tafito da sauri .
Mummy ri'ke da k'ugu tace "ga kayana da nasu Sageer can, kije ki wanke, idan kin gama ki share tsakar gidan nan, ki wanke duka toilets na gidan nan, dole kiyi na bankwana",
Tayi tsaki tawuce Fuuu.....
Noor tace "oo har yau ma da zan tafi ba za'a kyaleni ba?".
Alhaji Mamman kuwa da murnarsa ya koma gida, Yana murnar ya samu yarinya budurwa, shal a ledarta,
Bai fad'awa kowa ya 'kara aure ba,Ya bari sai an kawo masa Amarya, sannan ya fad'a wa matarsa, dan yasan halinta tsab zata iya lalata auren, kafin a kawota, shiyasa ya bari sai an kawota sannan ya fad'a.
Noor sai ana kiran sallar magriba ta gama ayyukan da aka sata, tayi masifar gajiya sosai.
Alwala tayi tai sallah, tana ro'kon Za'bin Allah, da abunda yafi zama alkhairi a rayuwarta.
Tayi wanka ta chanza kaya dan duk tayi daud'a saboda aikin da tasha.
Wasu kaya tasaka, suma dai sunji jiki sosai, wani gurin ya yage, ta d'inke da zare da allura.
Wajen Baba mai gadi taje, tana hawaye tace "Baba Nagode nagode da ka sanar da *Asalina*(littafin Zee Yabour), ka fidda ni a duhu, ka bani amsoshin tambayoyin da suka dad'e suna mum yawo a kai, Sannan ina ro'konka ka yafe mun Baba, idan na ta'ba maka wani laifi".
Baba mai gadi yayi ajiyar zuciya yace "baki tab'a mun komai ba Noor, kuma ki daina mun godiya haka"Dole in maka godiya Baba, tunda na taso ba mai sona sai kai, ba wanda nake jin dad'i a gurinsa sai kai, kai ka ilimantar dani , a wurinka na sauk'e Al Qur'ani mai girma, nasan hadisai da littafai da dama, ta dalilinki na iya boko duk da ban tab'a zuwa makaranta ba,(D'an shi yasa yana zuwa yana koya mata karatun boko, har ta iya turanci,da rubutu da karatu, Shi kuma shi ke koya mata na addini).
"Baba nagode nagode bani da abunda zan saka maka dashi sai addu'a, domin kamin abinda kowanne uba zaiyiwa 'yarsa, kamin abinda mahaifina yakasamin arayuwa, gashi yau za'a rabamu", ta fashe da matsanancin kuka,
Baba mai gadi ya tausaya mata sosai yace "Yi shiru Noor ki daina kuka ,In sha Allahu hakan shine mafi alkhairi a rayuwarki ,kiyi imani da 'kaddara ta sharri ce ko ta alkhairi kowanne dan'adam da kaddararsa"
Noor cikin shesshekar kuka tace "ni wannan *Itace k'addarata*"
Baba mai gadi yace "tabbas itace 'kaddararki Noor amma haquri zaki yi, ki cigaba da addu'a, ki mi'ka dukkan al'amuranki zuwa ga Allah shi zai miki magani"
Haka Baba mai gadi ya cigaba da lallashinta yana fad'a mata maganganu masu kwantar da hankali.
Har taji natsuwa da dangana tare da mi'ka dukkan al'amuranta zuwa ga Allah.
Da daddare aka aiko direba shi k'adai, daga gidan Alhaji Mamman yazo ya d'auki Noor,
Ta d'auko yan k'ullin kayanta ta sami Mummy da Daddy a falo .
Ta dur'kusa gabansu tace zata wuce, tana neman gafararsu su yafe mata,
Ko kallo bata ishesu ba, haka kuma ba wanda ya tanka ta cikinsu,
tafi minti goma a zaune agurin, tamkar gunki, ba wanda ya tanka.
Da taga basu da niyyar tanka mata , tatashi ta d'au k'ullin kayanta ta fita tana kuka, mai cin rai da bawa dukkan mai sauraro tausayi.
Baba mai gadi ya mata rakiya har bakin motar, Suna ta d'agawa juna a hannu, harsuka fita daga layin gidan.
tunani ta hauyi da maganganu a ranta.
"Ita dai bata tab'a jin, inda aka ce an kai amarya ita kad'ai ba, daga ita sai direba , kuma ba kayan d'aki, ba lefe infact nothing nothing, Wani al'amari sai Allah".
Suna parking mota a farfajiyar gidan
Alhaji ya tarbesu yana ta washe baki,
Noor gabanta ne ya fad'i ganinshi Tsoho tukuf, har yazama mai 'kafa uku, kai duk furfura, amma ahakan aka d'aura mata aure dashi, matsayin miji a gareta.
"Subhanallah"! Ta furta a cikin zuciyarta "yanzu wannan shine mijina ?"
Alhaji yace ma driver'n zaka iya tafiya, ita kuma ya ri'ko hannunta yana cewa "muje ciki koh?".
Hannunta ta fizge, tana hawaye tace "ni ka sakeni".
Alhaji ya kyalkyace da dariya yace "Yarinya kenan ni fah yanzu mijinki ne, in ban tab'a ki ba waye zai tab'a ki".
Ya sake cafko hannunta, tana 'ko'karin k'wace hannunta, ya damtse shi gamm.
Yaja ta cikin gida, Muk'ulli ya fiddo dashi daga aljihunsa, ya bud'e kofar, wani had'ad'd'en falo, suka shiga, sannan ya jata suka wuce k'uryar d'aki,,ya jefar da ita kan gado.
Yana kallonta yana lasar baki,
Yace "kaiii amma caca tayi wlh, banda caca a ina zan samu wannan santaleliyar budurwa, ga komai Mashaa Allah ba tare da aljihuna yayi kuka ba, amma gashi a banza na sameta".
yafad'a Yana kokarin cire rigarsa.
Noor ta jawo bargo ta 'kudundune kanta tana cewa "Dan Allah kayi ha'kuri kar ka min komai,
Wayyo Allahna!"
Ya fashe da dariyar mugunta yace "Haba! Yarinya waye zai samu yarinya kamar ki, ya kyale ke fah matata ce",
Ya cire riga yayo kanta kenan,........!
Suka ji an bangazu 'kofa da karfi.
Hajiya ce ta shigo hannu ri'ke da k'ugu tace "Toh munafuki! Maci amana!, An gaya maka bansan me kake ba ,kaje an baka yarinya a caca kazo kaji dad'i, toh wallahi baka isa ba".
Zufa ce ta fara k'etowa Alhaji, duk da cewa akwai sanyin Ac a d'akin murya na rawa yace "yi hak'uri ki saurareni Hajiya"
Hajiya tasa hannu ta dakatar dashi tace "Dakata! Ba abunda zan saurara, na riga nasan komai dan haka wuce mu tafi, baka isa ka kwana da yarinyar nan ba wlh".
Jiki na rawa ya d'au rigarshi ya nufi hanyar fita.
Ta juyo ta'karewa Noor kallo, tayi tsaki tare da nunata da yatsa, tace "ke kuma zanyi lokacinki, kijirani zuwa safiya, zakisan waceceni, zakisan babu macen data isa ta auri mijina tazauna lafiya", ta juya taga Alhaji natsaye yana dubanta, Hajiya ta daka mai tsawa "mai kake jira? wuce mana"
Yai saurin zabura jiki na rawa ya wuce.
Noor kukan da take ya tsananta, amma ta godewa Allah da ya kawo Hajiya, Alhaji bai mata komai.
Tace "Allah ka yafe mun duk da nasan Alhaji mijina ne, Kuma yana da hak'k'insa a kaina amma bazan iya bashi kaina ba".
Kuka ta cigaba da yi har kanta ya fara ciwo
Anan barci b'arawo ya sace ta.........................!
*Ku biyo mu next chapter dan jin ya rayuwar Noor zata kasance a gidan Alhaji Mamman kuma Alhaji Mamman ba mijin hajiya bane kuwa yadda yake tsoronta nan*????!🤔
Ku dai biyo mu, kusha labari...........!
® *OHW*🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵 🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣5⃣
""Kiran Sallar asuba ya sata farkawa,Ta tashi ta shiga toilet tayi alwala
Tayi sallah ta rok'i Allah abunda yafi zama alkhairi a rayuwarta
""Cikinta taji yayi kuka ""kooooo"" alamun yunwa rabonta da abinchi yau kwana biyu
Tashi tayi taje falon tana dube dube ko zata samu wani abu da zata sama cikinta,Wata k'ofa ta gani ta bude kitchen ne
Tayi ajiyar Zuciya a ranta tace k'ila in samu abunda zan sa a cikina,Shiga tayi tana dube dube, cupboard duk sai da ta dubasu amma wayam ba komai a kitchen din
Dawowa tayi falo ta zauna a fili tace Ya Salaam! Yanxu ya zanyi gashi ba abunda zanci
Bayan wasu mintuna tana zaune tayi jigum, taji an turo k'ofa an shigo
Wata yarinya ce yar budurwa haka ta Shigo rik'e da tray a hannu
Daga gani yar aikin gidan ce ,
Ta ajiye tray din tace Gashi ,Alhaji yace na kawo miki
""Noor ta mata godiya ta juya ta fita
Dankali ne soyayye da k'wai, sai kayan tea tunda aka haifeta bata t'aba cin dankali ko k'wai ba,kai duk wani abu ma mai d'adi bata t'aba ci ba, daga tuwo sai shinkafa
""Ba b'ata lokaci ta fara kai lomomi har kunnenta taji yana motsi tsabar dadin dankali da k'wai da taji,Tace Ashe haka su Mummy ke kwasar d'adi tana ci tana santi ita k'adai
Hajiya ce ta tasa Alhaji a sashen shi(part) sai masifa take mai
""Yanxu Alhaji dan cin mutunci shine zaka je a baka yarinya a caca,ka kawo min ita muyi zaman kishi da ita, yar cikina fah ce yarinyar nan
""Haba! Hajiya ya kike magana haka ai musulunci ya yarda da haka
""Ta daka mai tsawa Dallah rufe ma mutane baki, kai kasan Allah ne,wlhy da kasan Allah da baka rik'a yin wasu abubuwa ba, dan haka ni yanxu ba wani dogon zance ba ka saketa a yau din nan ta koma can gidan ubanta
""Alhaji baki na rawa yace Haba! Hajiya in saketa fah kikace, kar ki manta yarinyar a caca aka bani ita kuma Ubanta abokina ne sosai tare dashi muke harkar cacar nan, kina ganin idan na saketa kwana daya da aure na mai adalchi kenan,sannan sauran abokanmu na caca kallon mai zasu mun maci amana, kuma zasu yi korata daga cikinsu ,kinsan kuwa idan suka koreni shikenan tawa ta qara dan suke had'a ni da manyan mutane mu buga caca ta makudan kudi
""Hajiya ta d'an yi shiru tana nazari sai can tace naji dalilinka, amma ina so kar ka kuskura wani abu ya hada ka da yarinyar,kar ka qara shiga d'akinta, kai ko kallo ma bata isheka ba tana matsayin matarka ce amma kar ka tab'a mata kallon matarka kai kama manta kayi aure a duniya ka d'auka ni kadai ce matarka
""Alhaji yayi shiru yana cewa a ranshi anya zan iya daukar wannan sharudda na hajiya gaskiya sun min tsauri,ina son yarinyar nan kuma ina son mu hada kwanciya da ita dan gaskiya tana da kyakkyawar halitta
""Hajiya ce ta daka mai tsawa kayi shiru kana wasu mazurai
""Murya na rawa yace Umm...ummm na amince
A ranta tace kar ma ka amince. nasan maganinka ai,ba ma yarinyar nan ba,ba macen da zata sake burgeka a duniya wlh,Ni kadai ce matarka, dani kadai zakai ta rayuwa ba wacce ta isa ta rab'eka wlhy
Ita kuma zata gane kurenta sai tasan ba macen da ta isa ta auri Alhaji Mamman ta zauna lafiya, duk da nasan a caca aka sata amma har da k'wadayi yasa ta amince, da sai tace ma Ubanta bata son auren,Wato taga mai kud'i zata zo ta huta
Bata san ta kawo kanta gidan wahala ba
""Ta tashi ta fita tana haki
A bakin kofa tayi kacib'us da Imran zai shiga sashen Abban na shi
Ya dan rissina ya gaida mahaifiyar tashi
""Mum ina kwana ??
Lafiya lau Imran
Ya dan yi fuskar damuwa sannan yace
Mum wai da gaske ne Dad ya qara aure
Hajiya tayi Ajiyar zuciya tace Da gaske ne Imran,abun bak'in cikin ma sa'ar Iman ya auro
""A firgice Imran ya kallo mahaifiyarsa yace Wat,abomination wannan ai child abuse ne,Daddy fah is 62yrs and ace ya auri yarinyar yar' 16yrx,haba Daddy me zai sa yayi haka wannan ai mu zai ja ma zagi a gari,Su iyayen yarinyar basu da hankali ne da zasu bada yar' su ga tsoho,sannan ita yarinyar shashashar ina ce da zata bari a aura mata tsoho
""Hajiya tayi k'wafa tace hmm! Kud'i suka gani shine kawai dalilin( *dan yaran basu san sana'ar Ubansu ba wato Caca,kawai sun dauka kasuwanci kawai yake,tunda sunga yana kasuwanci*)
Imran yaja tsaki yace ""kaii ! Kaiii! Wai mutane ina zasu da son duniya neh
Mtcheeewww!! Ya qara jan wani dogon tsaki kawai ya juya,ya wuce ya fasa shiga sashen mahaifin nashi
""Hajiya tace ai ga irinta nan,haka kurum ka jawowa ya'yenka abun kunya, ka auro yarinyar da ka isa jika da ita
Ni ina ma tausaya musu ranar da zasu gano sana'arka
""Ta kawar da wannan tunanin tace bama wannan ba ,kamata yayi na fara tunanin ta ya zan fara cin uban waccar Barorojin(Noor)....................
*Waye Alhaji Mamman*
Alhaji Mamman asalinsa dan garin Bauchi ne Azare bafullatani ne,Zama ya kawo shi Abuja
Matarsa ta farko ta rasu,auren zumunci aka musu, ya'yensu Uku duk mata Salma,Rahma da Maryam yanxu duk sunyi aure da ya'yansu
Bayan ta rasu da Shekara biyar ya Auri Halima(Wato Hajiya)wacce itace matarsa har yanxu, itama yar bauchi ce amma a Misau,Hajiya ta gama mallake Alhaji gaba daya sai yadda tayi dashi,tana da masifar kishi da ganin k'yashi bata bari kowa ya rab'i Alhaji daga ita sai ya'yanta,ta zama kamar ita ce mai gidan,Ya'yensu Hudu tare , *Imran* ne Babba shekararshi ashirin da Uku da haihuwa,Kyakkyawa ne fari sol ( _kamar Sid din Roshni@king of hearts LoL_) duk gidansu yafi su kyau,Miskillin mutum ne ko dariya bai cika yi ba Sai murmushi,kuma bai cika son mutane ba,Ya gama degree dinshi akan Mechanical Engineering a Turkey, yanxu haka yana so ya kuma yayi masters, IMRAN hadadden guy ne ajin farko ,kuma d'an gayu ,idan nace na tsaya bayyana muku kyau da had'uwar *IMRAN* sai in dau 3 hours bn gama ba,Mata na daye masa
Hajiya ta d'au son duniya ta d'aura masa tana bala'in ji dashi kuma ta d'au dogon buri a kanshi
Yazeed ke bima masa 21yrx yana karatu nan Abuja a *Nile Turkish University* Final year yake , Ihsan 18yrx tana *baze university* Level one sai yar autarsu Iman 16yrs Ss2 a Al-amin international school
Kan yaran duka a had'e yake,kuma familyn suna zaune lafiya sai dai yadda Mahaifiyarsu ke controlling mahaifin nasu, abun na damunsu tun ba IMRAN ba yafi kowa jin haushi, ya rasa yadda zaiyi ya lurar da mahaifin nashi ya zama namiji,yasan cewa shine mai gida,Shine shugaba a gidan ba mummy ba,shi ke da damar bada order a gidan abi ba Mummy ba..........................
® *OHW*
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣6⃣
""Noor da ta gama breakfast,ta tattara kwanukan ta d'au tray ta fito
A tsakar gida taga mai shara ,Ta tambayeshi Dan Allah ina ne kitchen ??
Ya mata nuni da hannu
""Kitchen ta shiga ,taga masu aiki nata aiki,bayan ta gaisa dasu ta ajiye kayan a sink,ta juya zata fita kenan, taci kaci karo da hajiya
""Ina kwana ?? Ta gaishe da Hajiyar tare da d'an rissinawa
""Da ban kwana ba da zan kika ganni munafuka,to bari kiji ba hutu kika zo yi ba,matsayinki d'aya da wa'innan masu aikin,ta nuna su da yatsa,ke sunma fiki daraja a gidan,sannan ni ba kishiya aka kawo mun ba yar'aiki aka kawo mun, dan haka ki gaggautawa jyyawa ki wanke wadanda can kwanukan da kika ci abinchi,dama sauran da ke wurin idan kin gama ,ki sameni falo na gaya miki sauran ayyukanki
""Hawaye Noor ta fara,a ranta tace anan d'in ma ban huta ba,ni dai haka Allah yayi rayuwata cikin k'unci da wahala,wannan *itace kaddarata*
""Ta juya kan masu aikin
Wacce shegiyar ce a cikin ku ta kai mata breakfast
""Lami muryar na rawa duk ta gama tsorata tace Al...Alhaaaa.....ji ne yace na a kai mata
""Ina so wannan ya zama na farko kuma na k'arshe,matsayinku d'aya da ita a gidan nan ,kai har ma kun fita matsayi a gidan nan
Kun jini ku
""Suka amsa da ""toh Hajiya
Ta fice
""Noor wanke-wanken take tana kuka
""Masu aiki da gulma,d'aya daga cikinsu tace ba kece amaryar da Alhaji yayi ba
""Noor ta g'yada kai sama ""Lami tace ke kuwa me ya kai ki auren tsohon
""Noor cikin muryar kuka tace Mahaifina ne ya aura mun shi
""Sauran masu aikin guda biyu suka tab'e baki,suka ce tabd'i wlh ke kika yarda
""Lami ce tace "'Allah sarki! Sai kinyi hakuri gidan nan,dan ba Hajiya ba ya'yanta ba,duka basu da kirki wlhy,baka shiga hancinsu ba ma sun ma,toh ina ga ka shiga gonarsu dan haka sai kinyi haquri da juriya
""Sauran biyun suka ce wlh kuwa, dan har kin fara bamu tausayi
""Noor ko uffan bata ce ba, wanke-wanke kawai take a ranta tace ni ba wata wahala da zata razana ni, dan ba irin wacce ban sha ba a gidanmu,bak'in cikina tsohon da aka aura mun,rabani da Baba maigadi,da kuma rashin mahaifiyata
Masu aiki nata hira abun su,ita dai Noor bata sa musu baki ba
Da ta gama wanke wanke, ta tambayi Lami ina ne sashen hajiya
Lami ta jata, ta nuna mata
""Hajiya na zaune da ya'yenta mata(Ihsan da Iman) a k'yatattacen falonta suna hira
""Noor tayi sallama ta shiga,
Ta duk'a tace Na gama hajiya
""Ihsan tace wacece wannan Mum, ko sabuwar mai'aiki ce aka kawo
""Hajiya ta yatsina fuska tace wai itace yarinyar da babanku ya aura
""Iman da Ihsan a tare suka ce Wat!! Wannan d'in suka nuna ta da yatsa
""Hajiya tace ita fah
""Ihsan tace watz wrong wif Dad da zai auri yarinya kamar wannan,gaskiya Daddy bai kyauta mana ba
""Iman tace Jibe ta fah kazama ma da ita,daga gani yar matsiyata ce,ji kayanta duk sun yage,kyau kawai daddy ya gani ya auri wannan yarinyar
""Ihsan tace ni wlhy duk ma ta cika mun hanci da wari,sai d'oyi take, ta tashi ta d'auko air freshner tana feffesawa a falon
""Noor wasu hawayen bak'in ciki ne yazo mata,wannan cin mutunchi haka,duk da tasan bata sa turare(dan bata da shi,kuma bata da kud'in siya) amma bata wari
""Ihsan tace Gaskiya mum kisan yadda zaki yi da wannan yarinyar ,ba zai yiyu ba ace wannan kazamar,k'aramar yarinyarce kishiyarki ba
""Hajiya tayi dariyar mugunta tace ""ku kwantar da hankalinku,kunsan halin mahaifiyarku bazan tab'a zuba ido ina kallon yarinyar nan,a cikin gidan nan tana hutawa ba,ba ita son kud'i ya sata ta auri tsoho ba,tazo ta huta,toh wlhy sai ta gwammace kid'a da karatu
""Iman tace yawwa mummy gwara a koya mata hankali,Wlhy sai kinyi regretting auren mahaifinmu,Shegiya kamar aljana
""Keee!! Hajiya ta kira Noor a tsawace
""Noor ta d'an zabura tace Na'am
Ina so ki saurareni da kyau kiji abunda zan gaya miki
Na farko ki tattaro kayanki ki dawo d'akin masu aiki,Sannan daga yau kin koma baiwa a gidan nan ,ba mai aiki ba *Baiwa*, ba wasu ayyukan da zan cire miki nace su zaki rik'a yi, duk aiki da ya kama yin shi zaki yi,
Iman ! Ihsan! Ga *baiwa* nan sai yadda kuka yi da ita
""Yes! Mummy shiyasa muke sonki
*Imran* da *Yazeed* ne suka shigo a tare
Ina kwana mum? Suka fad'a a tare
Lafiya lau my two luvly sons
Suka samu wuri suka zauna
Kujerar da *Imran* ya zaune, ita ke facing Noor
Idonshi caraf suka kai kanta ,kanta a sunkuye tana hawaye,
Yace ""kee lafiyarki ?? Me ya sameki kike kuka ??
_Bai ma san wacece ba ,hakanan ya tsinci kanshi da tambayarta_
Har a lokacin bata d'ago kanta ba,kuma bata tanka shi ba
""Hajiya tace au kuka take ,tun yanxu har kin fara kuka, ashe nan gaba sai hawayenki sun k'are
""Imran yace Who is she ??
""Hajiya tace Matar babanku
""Imran yaja tsaki yace Toh me take anan, i guess da part dinta
""Kiranta nayi na gaya mata matsayinta a gidan nan,dan daga yau ta koma *Baiwa* ,nafi k'arfin nayi kishi da k'azamar nan ,yar cikina
""Imran ya tab'e baki,irin ko ohon nan(i dnt care) dama yasan za'ayi haka, yasan halin mum din tashi
Ya mik'e yace Dad na nan ko ya fita ??
Yana nan ka duba part dinshi,wani abu ne ?
""Ok , i need to talk to him about my job( ina so na mai maganar aiki na)
""Hajiya tace toh Allah yasa a dace
Yace Ameen ya fice
""Yazeed yace dama ita ce wannan,wlh sai na huce takaicin jiya a kanki,dama ina ta rok'on Allah yasa na had'u dake
""Hajiya tace me ya faru ne ??
""Yazeed yace Allah mum kar kiso kiga yadda friends d'ina ke teasing d'ina jiya,wai Babana ya auri yarinya wacce ya isa jika da ita
""Hajiya tace ai ga irin abunda ake gudu kenan,yanxu gaka gata,ka mata duk abunda kaga dama
""Yazeed yayi murmushi irin na mugunta, yace haaaa!! Ba dai tana gidan nan ba, kuma ta tashi daga matsayin matar daddy ta koma Baiwa, hmmm zanyi lokacinta, yanxu ina da lectures
Byee mum and sisters
""Iman da ihsan suka ce bye Bro sai ka dawo
""Hajiya tace Allah ya bada sa'a
""Ya amsa da Ameen
""Ihsan ta mik'e tace kee!! Biyoni baya,akwai aikin da zaki mun
""Iman tace in kin gama nata nima akwai nawa
""Muryar a dashe Noor tace Toh
""Jiki a sanyaye ta tashi tabi bayanta.....................
® *OHW*
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵 🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣7⃣
""Noor na biye da ita har suka kawo dakin Ihsan
""Ihsan ta juyo ta kalleta tace ina so ki gyara dakin nan tas,ki wanke toilet ,akwai inners(bra,pant,vest,underskirt) dina nan a basket ki wanke su tas
""Noor tace Toh,
Ta fice tare da buga k'ofar d'akin
""Noor ko a jikinta,dan ta riga ta saba da wahala tun gidansu,ta hau gyaran d'aki,ta gama ta wanke toilet,ta d'auki kayan ta fito
""Laundary taje,tana wankewa tana karatun Qur'ani,Wasu pants din ma duk tayi staining dinsu,dan haka Noor ta ajiyesu gefe dan bazata iya wankewa ba coz tana da bala'in kyankyami
Imran bayan ya fito sashen Alhaji, Sashensu ya nufa
Yayi wanka ,yana ta sauri zai fita,coz akwai wanda Daddynshi ya turashi wurin shi akan maganar aikinshi
Rigar da zai sa yake ta nema bai gani ba,
Yace nasan tana laundary bari naje na duba
""Noor nata wanki abunta
""Taji kamar mutum ne tsaye a kanta,d'agowar da zata yi suka had'a ido,tai saurin sunkuyar da kanta k'asa,saboda kwarjinin da ya mata
Shi kuwa gabanshi ne ya fadi
""Ya dake yace Kee! Waya gaya miki anan ake wanke wa'innan abubuwan anan
""Kunya ta kama ta, ta kasa furta ko A,(ga pants din da suka yi staining ta cire su gefe ,kuma tasan definitely ya gani)
""Tsaki yaja yace in zaki wanke wa'innan abubuwan naki ,ki rik'a wanke su toilet ba nan ba
""Kai kawai ta iya d'agawa sama
""Ya duba rigarshi,ya d'auko ya fita(kwata-kwata bai d'auka itace matar Daddynsu ba,ya d'auka yar'aiki ce,dan dama ba duka yan'aikin ya sani ba)
""Noor kuwa wata irin kunya ta cigaba daji ,tace yanxu fah shikenan ya gani,kuma zai d'auka nawa ne,anyway da gani ba ruwanshi,ba kamar sauran yan'uwanshi ba,
Ta gama wankewa,ta kwashi masu staining d'in
A d'akinta(ihsan) ta sameta
""Murya a sanyaye tace ga wa'innan sun b'aci
""Ihsan dake kwance,ta tashi zaune cikin zafin nama tace me kike nufi ? Ai nasan yadda suke na baki su
""Noor tace Staining ne fah,kuma ba kyau,ka wanke ma mutum
""Ihsan ta daka mata tsawa tace kafin in k'irga uku ki fitar mun a d'aki,kije ki wankesu
""Noor ji tayi har ga Allah ba zata iya wanke wannan kayan k'azantar ba,Dan haka tace Dan Allah kiyi hak'uri bazan iya ba
""Ihsan tace me kika ce? Ba zaki iya ba
""Noor ta d'aga kanta sama
""Dirkowa tayi daga kan gado,Sai gata gaban Noor,Tasss Tasss kake ji saukar mari,mari biyu ta mata lafiyayyu,ta hankad'ata ta fad'i,Noor sai hawaye abun tausayi
""Ihsan tace kad'an na miki,Gobe na k'ara saki aiki kice ba zaki yi ba,
Maza tashi ki fitar mun a d'aki kuma ki tabbatar kin wankesu,in ba haka hmmmm.......,ba sai na gaya miki me zan miki ba
""Noor ta kwashe kayan ta fita tana kuka,tsakar gida taje ta zauna,tana ta kukan bak'in ciki,duk wani mai imani ya ganta dole ta bashi tausayi
""Lami ce tazo ta dafa ta,tace lafiya ,me suka miki
""Cikin dasasshiyar muryata ta labarta ma Lami duk abunda ya faru
""Lami tace Allah sarki,yi shiru daina kuka,kema me ya kai ki cewa ba zaki yi,da kin sani kin wanke
""Noor tace Allah Lami ina da k'yank'yami bazan iya wankewa ba
""Lami tace muje laundary ki wanke a washing machine
""Noor tace ai Yayansu ya hana
""Wanne daga ciki Imran ko Yazeed
""Wani dai kyakkyawa haka da baya dariya
""Lami tace Imran kenan,wannan miskilin ko magana ma shi wahala take mai,muje ki wanke ,ai ba yanan ya fita
""Lami ta rik'e hannun Noor suka je
""Noor ta godewa Allah da ya had'ata da Lami,dan yau ba don Lami ba,bata san me zai faru akanta ba,dan bazata iya wankewa ba ko kasheta za'a yi
""Tana gamawa,taje wajen Iman,itama ta bata nata aikin
""Tun safe Noor ke aiki da ta gama wannan ,za'a ce yi wannan,tana yi ana zaginta,ana hantara
Sai dare wajen k'arfe sha d'aya suka sallameta,ta masifar gaji
Kayanta ta tattaro daga part d'in da Alhaji ya kai ta,ta maidasu d'akin da Lami take,dama ita kad'ai ce a d'akin,Sauran masu aikin biyu d'akinsu d'aya, kansu had'e yake
""Tayi wanka taji k'arfin jikinta,sannan Lami ta zubo mata abinchi taci,suka kwanta barci
""Alhaji nata tunanin ko wane hali Noor take ciki,yana so yaje ya dubata amma yana tsoron Hajiya
""Hajiya kuwa nata shige shigen(boka da mallam)yadda zata sa Alhaji ya tsani Noor,ya manta da ita
""Kiran sallar farko na Asuba,Noor taji saukar ruwan k'ank'ara a jikinta
""Firgigit ta tashi tana mutsittsika ido,
""Hajiya ta gani tsaye a kanta
""Hajiya tace Tashi Yar'iska an gaya miki hutu kike zo,da zaki kwanta kina ma mutane barci,Maza tashi kije ki wanke mototocin dake gidan nan,ki share tsakar gida
""Noor ta amsa da toh jiki na rawar sanyi
Hajiya ta juya ta fice, tana masifa
Lami itama ta tashi, hayaniyar hajiya ta tada ta,Noor tama kasa yin kuka,tashi tayi ta cire kayan jikinta,tasa wasu
""Har zata fita taji muryar Lami nace mata kiyi hakuri Noor,komai yai farko yana da k'arshe,watarana sai labari
""Noor tayi murmushin takaici tace ba komai Lami wannan *itace k'addarata*
""Lami tace hakane itace k'addaraki
""Bari na tafi kar tace na d'ade
""Lami tace toh,tana mai jin tausayin Noor...........
........................
*Masu complaining page yayi kad'an ,muna baku hak'uri ,kuyi hak'uri da kad'an din da kuke samu ,abubuwan ne sai a slow*
*OHW*
🏵🏵🏵
🏵 🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* ?🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣8⃣
""Tsintsiya ta d'auka ta fara share tsakar gida,
Mai sharar tsakar gida,da wanke mota duk Hajiya ta sallamesu, tace Noor ce zata rik'a yi
Tana yi tana hutawa,kasancewar gidan k'ato ne,ba ita ta gama ba Sai k'arfe 8am
Ta nufi parking space inda Cars din gidan suke,mototoci 20 ne a gidan
""A ranta tace ni kadai zan wanke duka motocin nan,gashi ta masifar gajiya
Ruwa ta debo,ta Zuba car wash,ta d'auko soson k'arfe,duk aikin da ake sata gidansu ba'a taba sata wankin mota ba,dan haka ta d'auka da soson k'arfe ake wankewa,
Wata hadaddiyar mota k'irar Bugatti ,ta fara wankewa,Tana gurza soson,Paint din ya goge,wurin ya k'oje(gashi sosai ta gurza,wurin ya k'oje da yawa),Tana ganin haka hankalinta ya tashi
""Innalillahi wa inna ilai hir raji'un ta furta,tace Yau na shiga uku,k'ila yau hajiya sai ta yanka ni
""Nan ta kifa kai tana kuka,tama rasa me zata yi,ko taje ta gayawa Hajiya b'arnar da tayi,ta gaya mata a bisa rashin sani ne,sai kuma taji tsoro kar ta gaya mata ta kasheta,ita yanzu ya zata yi,addu'o'i kawai take karantowa
Can taga kukan bazai fissheta ba,dan haka ta tashi,ta cigaba da wanke motocin ba da soson k'arfe ba,Zuciyarta cike da tsoron kar a gano b'arnar da tayi
Tana yi tana hutawa,har ta gama
""Ko Lami bata gayawa b'arnar da tayi ba,Addu'a kawai take Allah yasa kar a gane
""Tare da Lami suka yi breakfast(kunu da k'osai)
""Hajiya tace Noor taje sashenta,ta gyara ko'ina lungu da sak'o a sashen daga kan dakuna,toilets,falo
""Noor na jin haka sai hawaye(saboda ta masifar gaji,bayanta har ciwo yake,ta ya zata iya gyaran Sashen,ita dai ta rasa gata,ba mai sonta,ba mai tausayinta)
""Kukan da take ko a kwallar rigar Hajiya,kwata kwata bata ji tausayinta
""Babban falon take gyarawa,da kyar take shara,Duk wanda ya kalleta yasan a gajiye take,Haka take ji kamar zata fad'i,A zaune ta koma yin sharar
""Hajiya ta daka mata tsawa tace Maza tashi,wane aiki kika da har zaki gaji,kin manta ke Baiwa ce a gidan nan,baki ba komai ba tukunna
""Noor ta mik'e jiki ba k'wari,Tana shara da k'yar
""Yazeed ya shirya zai fita,yana da lectures
""Duk zai fita sai ya dudduba Motarshi,yaga bata da wata matsala,ko kadan baya so yaga datti jikin motarshi ko wani k'warzane shiyasa kullum cikin painting car dinshi yake,ko kad'an yaga datti jikin motarshi,to Mai wankin motar ya boni
""Dubawar da zai yi,yaga k'aton k'warzane jikin motar,
A fusace yace What d hell is diz ??
Ya cije lab'e,ya buga motar da k'arfi yace Damn it!,tare da harbin tayar motar,
""Iro You must pay for doing this ya fad'a
A fusace yake kiran Iro! Iro ! Iro!
""Mai gadi ne ya rugu da gudu,ya durk'usa gabanshi yace Ranka ya dad'e,Iro baya nan
""A fusace yace Gidan uwar wa yaje ??
""Mai gadi yace Ai hajiya ta sallame shi
""Toh Uban wa ya wanke motocin gidan nan yau
""Wata yarinya ce
""Yana huci yace ko yar gidan uban waye,Yau sai ta gane kurenta infact yau sai ta bar gidan nan
""Yana huci ya nufi sashen Hajiya
""Da k'arfi ya tura k'ofar falon,
Yana huci ,ya had'e girar sama da ta k'asa ya shiga
""Hajiya kanta ta tsorata da ganinshi,tasan duk abunda aka mishi ba k'arami bane,kafin ta tambayeshi me ke faruwa
""Yace Wa ya wanke cars din gidan nan Yau ??
""Noor hanjin cikinta ne ya kad'a,tsintsiyar dake hannunta ta fad'i,kunnenta taji ya d'au ruwa tsabar tsoro
""Hajiya tace wani abu ne ??
""Yace mum,imagine motata fah aka k'urje,kuma wallahi daga gani da gangan aka yi
""Hajiya Salati ta rafsa tace Noor ashe ke muguwar yarinya ce ban sani ba,yar hassada,wato tunda na saki wankin mota bari ki k'warzane motar
""Noor murya na rawa tace wlh.....ba...da
Yazeed ya katse ta tare da daka mata tsawa da k'arfi yace Enough!! ,dama kina cikin case d'ina,kafin in hukunta ki akan wance,kin k'ara wani, ki rasa motar da zaki ma haka sai tawa,Duk yawan motocin gidan nan
""Iman tace da gangan tayi ,dama daga ganinta sai tayi k'eta
""Yazeed yace yau kuwa zan koya mata hankali
Belt ya zare
""Ya fara zabga mata ,yana k'wallo da ita
""Su hajiya na zuga shi,suna cewa yawwa k'ara ma shegiya
""Shikuwa ya zage sai dukanta yake,Tana kuka tana bashi hak'uri amma kamar rok'onshi take ya k'ara
Imran ne ya shigo,idonshi straight suka kai inda Yazeed ke dukan Noor(bai ma lura wacece ake duka ba),
Yai saurin k'arasawa wajen,ya rik'o shi yana cewa lafiyar ka,sai kashe yar'mutane
""Yazeed yace k'yaleni kawai Bro,in kasheta in kashe banza
""Imran yaja shi ya zaunar dashi,Yana ta huci
Yace Haba Yazeed! Ka rage zuciyar nan taka
""Barni kawai da shegiya,motata fah ta k'uje mun
""Imran yai dariya yace to me ye a ciki,ni na d'auka ma wani babban laifin ta ma,
""But kasan bana son,ko kadan mota ta ta b'aci
""Toh ba sai an chanja paint din ba,me ye na b'ata ranka a banza
""Yai shiru yana haki
Noor bakinta da hanci ya fashe sai jini yake ,tana kuka
""Imran ya kai dubanshi gareta,ta bashi tausayi,Yace ke kuma tashi kije ki wanke bakin ki
Me ma ya kai ki wajen motarshi
""Hajiya tace daga na sata wankin mota,shine tayi wannan muguntar
""Imran yace Mum ban da abunki, ina mace ina wankin mota
""Hajiya tace to akanta za'a fara kuwa,ba ita ta auri mai kud'i tazo ta huta,zata ga hutu
""Imran cike da mamaki yake kallon Hajiya a ranshi yace dama ita ce matar Daddy,yarinya kyakkyawa da ita,ta auri tsoho dan kud'i,dama ya sani bai rik'e Yazeed ba,ya barshi ya cigaba da dukanta,Hakan shine dai dai da ita,Da ace duk yan'matan nan masu auren tsofaffi dan kud'i ,zasu rika samun haka gidan mazajen su,da an rage auren kud'i,mata yanxu sun lalace da sun kud'i,sai su jefa kansu wani hali saboda kud'i
Yaja tsaki,ba tare da ya sake kallon saitin ta ba, a fusace yace Oya Get out,dan baya son ma sake sata a ido _A rayuwarshi ya tsani mace na banzarta da rayuwarta a banza a wofi,Yana so yaga mace tana daraja kanta,kuma shima yana matuk'ar daraja mace_
*OHW*
[4/14, 14:08] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
0⃣9⃣
""Noor jiki a sanyaye da k'yar ta mik'e dan duk ta galabaita, tana mamakin why the sudden change daga Imran,taga shi ba ruwanshi da ita amma lokaci daya ya hayayyak'o mata
""D'akinsu ta shiga,a tsorace Lami tace Lafiya Noor,me suka miki
""Noor tai saurin mayar da hawayen dake k'ok'arin xubo mata tace manta ba komai
""Haba! Noor ya zaki ce ba komai,bayan ga jini duk jikinki
""Noor tace bari ina zuwa lami
""Toilet ta shiga,ta wanke jinin dake zuba bakinta,da hancinta
Ta fito,har yanzu jinin bai bar zuba ba
""Lami tace tashi muje chemist Noor,jinin nan yak'i tsayawa
""Noor tayi murmushi takaici tace ko munje chemist bani da kud'in da zan biya
""Tashi muje ni ina da kud'i
Noor tace a'ah Lami,barshi kar na d'aura miki wahala
""Ba wata wahala wallahi,me ye amfanin zaman tare,tashi mu tafi
""Noor ta tashi,tana mai jin k'aunar Lami a ranta
""Chemist d'in kusa dasu suka je,aka mata dressing tare da bata maganguna,Suka dawo gida
""Tana ta ma Lami Godiya
""Lami tace ba komai,tun farkon da taga Noor taji tana k'aunarta
""Ranar Hajiya,Gaba d'ayansu suka fita,dan haka Noor ta samu sarari
Ta kwanta,tana ta barci,tana huce gajiya
Sai ana kiran Sallar magriba ta tashi,Tayi wanka da ruwa masu d'umi,Sosai taji dad'in jikinta,dan ta huce gajiya sosai
Tana jin dama ace haka kullum take samun hutu,amma ina ba zata samu ba
Alhaji kwata-kwata ya fidda Noor a ranshi,yaji baya ma son sake sata a ido(aikin asiri)sai sun had'u da mahaifinta wurin caca ma yake tunawa da ita, kuma ba wai mahaifin nata ,na tambayarshi bane ina take, a'ah,Mahaifinta shi harkokinshi ma yake,ji yake kamar an cire mai k'aya
Noor kuwa rashin kula ta da Alhaji ba yayi,ba k'aramin dad'i ya mata ba,amma sai dai kuma ta rasa gane me ya kawo sudden change d'in,Sai kuma can zuciyarta ta bata hajiya ta hana shi,saboda a yadda ta lura mijin hajiya ne
""Tana aiki a kitchen,Iman ta lek'o
Tace kee!! Kije Ya Yazeed na kira
""Murya a sanyaye tace toh
Ta ajiye yanke alayyahun da take,tace Lami Dan Allah ki k'arasa mun ina zuwa
""Gabanta nata fad'uwa ta nufi sashensu Yazeed,wannan ce rana ta farko data fara zuwa,a ranta tana cewa ko me zai mun
""A hadadden falonsu ta same shi zaune shi da Imran,Suna kallon k'wallo(Ball)
""Ta duk'a nesa dasu,tace Sannunku gani
""Imran ya gane muryata dan haka bai juya ba,Dan baya son sake sata a ido,Dan a duk sanda ya kalleta sai gabanshi ya fad'i ,kuma yanzu ga haushin auren daddynsu da tayi saboda kud'i
""A fusace yace me kike yi anan?
""Yazeed yace ni na kirata aiki zata mun
""Tsaki kawai Imran yayi,ya tashi ya bar falon,ya koma d'aki,Ya kwanta kan gado yana cewa i want to get rid of this girl,bana son sake kallonta ko jin muryarta,haushi yake ji,ya tsani mace mai irin halinta(wato auren kud'i),
""Yazeed ya kai dubanshi gareta,Yace kar ki d'auka dukan da na miki jiya shi kad'ai ne punishment d'inki,yanzu kika fara,dan haka weeding(noma)zaki yi,na grasses dake bayan d'akunan mu
Duk grasses d'in da suka fito,ina so ki cire su
""Noor gabanta ya fad'i tace na shiga uku ni Noor,weeding abunda ban tab'a yi ba, a gidanmu,me zai sa su rik'a sani aikin da ban saba dashi ba
""Yazeed ya daka mata tsawa yace kinji ko
""Ta d'aga kanta sama,yace fice mun da gani
""Ta tashi sumi-sumi ta fita
Bayan rooms dinsu taje,anan taga hoe
""Ta d'auka ta fara cire grasses d'in wurin
""Da k'yar take cirewa
""Imran yaji kamar motsin mutum ta window'n d'akinshi
""Ya tashi ya lek'a,yaga sai weeding take duk tayi zufa
""Yayi murmushi ya dawo,ya zauna yace Shege Yazeed baka da dama wlhy,Anyway hakan shine daidai da ita,ko wata taji zata yi auren kud'i,zata bata shawara kar tayi
""Yama kawar da tunanin,ya jawo system d'inshi yana operating
""Tunda take,ba aikin da aka tab'a sata ya wahalar da ita,kamar na yau
""Sai nishi take tana sweating
""Ta ciccire grasses d'in,ta ajiye hoe, zata tafi taga Yazeed tsaye gabanta,
A tsawace yace Ina zaki ?
Murya na rawa tace na....ga....ma(dan masifar tsoron shi take tun dukan da ya mata)
""Yace nace idan kin gama ki tafi
""Ta girgiza kai alamar a'ah
Ya wuce,yana dudduba,saura sauran grasses dake can k'asa,Ya nuna yace wannan fa ,wa kika bar wa ya cire
""Maza zo ki cire su kafin na k'irga uku
""Jiki na rawa ta d'auki hoe
""Ya daka mata tsawa yace ajiye shi,da hannu zaki cire
""Ba musu tasa hannu,tana tsige grasses d'in,Yazeed na tsaye kanta
Sai da ta tsige shi tas,kai kace machine ne ya cire shi,ba mutum ba
""Yace oya tashi muje akwai sauran aiki
""Idonta suka yi narai-narai suka cika da hawaye tace Dan Allah kai mun rai,ka barni na huta,ko me kace inyi zanyi
""Kawai yaji ta bashi tausayi yadda yaga ta galabaita tana hawaye
Yace na baki 15mints,ki huta,ki sameni sashenmu
""Nagode nagode
""Bai sake tankawa ba,Ya wuce
Imran na jin su ta window,Yana dariya duk da cewa yana da tausayi sosai amma kwata kwata baya jin tausayinta,dan a ganinshi kome aka mata, ita taja ma kanta
""Da k'yar ta kai d'akinsu,ta fad'a katifa tana maida numfashi ga yunwar cikinta ma ta isheta
""Tsawon minti biyar tana kwance ta kasa yin ko k'wak'waran motsi,Bayanta taji ya rik'e yana ciwo
""Iman ta gani tsaye kanta,rik'e da k'ugu ,tana juya key'n mota da d'an yatsa,tace lallai samun wuri,har kina ma da lokacin hutu, baki gyara mun d'aki ba,shine kika zo nan kika kwanta
""Noor bata tashi daga kwanciyar da tayi ba,tace Dan Allah,ki d'aga mun k'afa yau Iman,wlhy bayana ke ciwo
""Iman tace wannan kuma ke ta shafa,ba matsalata bace,all i know shine ki tabbata kin gyara mun d'aki,kafin naje na dawo,ta kad'a kai ta fice
""Noor kuwa gyara kwanciya tayi,in less than 2min barci ya saceta
.................................
*OHW*
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
1⃣0⃣➖1⃣5⃣
""Har 15mints ya cika,Yazeed bai ga Noor ba,Yace me yarinyar nan take nufi,bari in k'ara mata 5mints in gani
Yana yi yana duba Wall clock d'in falon,har 5mints ya cika
A fusace ya tashi yace lallai yarinyar nan ta raina mun hankali,amma zanyi maganinta
Ya tashi ya fita, yana huci
""Noor sharar barcinta kawai take, tayi nisa a barci
""K'ofar d'akin ya tura da k'arfi,kwance ya ganta tana barci
""Ya cije yatsa yace kutt! Wato ma yarinyar nan barci take,ni zata maida d'an iska
Ya fita d'akin,kitchen ya nufa ,ya bud'e fridge,ya d'auko ice block(k'ank'ara),ya farfasa ta yasa jug,Sannan ya samu ruwa masu bala'in sanyi,ya zuba a k'ank'anrar
""Ya koma d'akin,
Ya shek'a mata ruwan,ice block na dukan jikinta
Firgigit ta tashi,kafin ta k'arasa bud'e ido,ya fara zabga mata belt(ku hango an zuba maka ruwa,an dake ka,k'arshen zafi kenan)
""K'ara ta saki saboda zafin bulalar,Tace Dan Allah kayi hak'uri,kayi mani rai
""Yace hak'uri,hak'uri fah kika ce,ni zaki maida d'an iska ,daga baki 15mints kizo nan kina barci,ko kina d'aukar kanki har yanxu a matsayin matar Daddy,in ma kina tunanin haka,u bttr remove it frm dat ur corrupt head,coz yanzu ke Baiwa ce a gidan nan
""Tana hawaye tace wlh nima ban san lokacin da barcin ya kwasheni ba
""Zama ki sani ne,ya cigaba da zabga mata belt
""Tun tana kuka,tana rok'onshi, har ta gaji da rok'onshi,sai da ya mata lilis
""Ya dakata,yana hak'i
Wayarshi ta hau ringing
Yayi receiving
""Hello Baaba kana ina? Abokinshi ya fad'a
""Ina gida wlhy
""Toh kai sauri kazo yau akwai test
""Ok toh,Gani nan
Yayi hanging-up
Ya juya kanta yace ki jira dawowata,i will mercilessly deal with you today,coz kashe ki ne kawai bazan yi ba
""Yana fad'ar haka ya fice,a harabar gidan,Yaga Imran
""Imran yace daga ina haka,kana ta hak'i
""Ni da waccen yar'iskan,wlh yau sai ta gane kurenta,bata san waye Yazeed ba,ni zata raina ma hankali
""Imran yayi murmushi,ya k'ark'ada kai ,kawai ya wuce
A ranshi yana jin dad'i,gwara da Allah ya hada ta da Yazeed,shi zai koya mata hankali,inda ace da ne kafin ya gano matar Daddy ce,zai iya yiwa Yazeed magana,ya k'yaleta(coz yana da tausayi) but tunda ya gano matar Daddy ce,baya tausayinta ko kad'an,dan shi kawai baya son hayaniya ne but da shima sai ta gane kurenta a hannunshi
""Noor ta kifa kanta tana kuka mai tsuma rai,tana magana a fili
""Wannan wacce irin rayuwa ce,ni bani nace ina son Daddynsu ba,nima ba da son raina na aure shi ba,amma sunzo suna ta huce haushi a kaina,da sun san ta hanyar da Daddynsu ya aureni,da shi zasu tsana bani ba
""Tana ta kuka,tama manta da zancen gyaran d'akin Iman
""Lami ta shigo d'akin rik'e da plate na abinchi
Da saurin ta ajiye plate d'in,ganin Noor na kuka
Tace Subhanallah! Ya kike kuka?me Yazeed d'in ya miki
""Ta fad'a ma Lami komai
""Tace kaii wlh mugu ne,su kwata kwata basa tausayinki,kamar ba matar ubansu ba,ko da yake laifin Alhaji,shi da ya auro ki,ya banzatar dake,kamar baki da hak'k'i a kanshi,ya bari matarshi da ya'yenshi na gallaza miki
""Noor tana sharar k'walla tace haka Allah ya k'addaro mun rayuwata,ba yadda na iya,kar ki d'aura laifin kan Alhaji,
""Lami tace eh da wannan kuma,ga abincinki nan,
""Tace toh,nagode
Tana kai loma d'aya bakinta,Taji muryar Iman
na k'wala mata kira,sai a lokacin ta tuna da aikin da tasa
""Yan hancinta suka kad'a,ta mik'e zumbur tace Lami ina zuwa
""Lami tace ki dawo,ki gama cin abincinki,sannan kije
""A'ah bari kawai inje Lami
""Jiki na rawa ta tafi,a falo ta sameta ita da Ihsan
""Ta d'an tsaya nesa da ita,dan kar taji, ta kai mata masga
""Iman ta fisgota ta shek'e mata wuya tace ina gyaran d'akin da na saki
""Da k'yar take magana saboda yadda ta shek'eta ,tace mantawa nayi
""Iman ta saketa da k'arfi tare da hankad'ata,ta fad'i
Tace kin manta koh,
ta juya kan Ihsan tace Sis,wane punishment xan ba yar'iskan nan
""Ihsan tace ki bata punishment irin na yan boarding,ki sata zama kan takalmi
""Yawwa sis,very gud idea
""Ta d'auko takalmi,ta mik'ar dashi tsaye,tace oya tashi ki zauna a kai
""Noor ta zaro ido,tana mamakin taya za'a ce,ta zauna kan takalmi
""Iman tace ke nake jira,kin tsaya kina b'ata mun lokaci
""Noor ta tashi da k'yar,ta zauna kan takalmin
Sai ta tafi tangal-tangal kamar zata fad'i,Iman ta masgota, dole ta gyara zamanta kan takalmin
""Tsawon minti biyar 20 tana haka,duk ta gama gajiya
""Sai ga Imran ya fito daga d'akin Hajiya
""Wani irin tsaki yaja ganinta yace Why wai nake had'uwa da yarinyar nan,i hate seeing her in my life,Sai kuma yayi murmushi ganin punishment d'in da take(a ranshi yace ko dan ina son ganinta a wahala,shiyasa duk lokacin da take cikin wahala, nake xuwa wurin)
Ya sake yin wani murmushin,ya wuce batare da yace ma su Ihsan komai ba
""Sai da ta k'ara 10mints sannan Iman tace oya foolish tashi kije ki gyara mun d'aki
""Noor jiki ba k'wari ta tashi ta nufi d'akin Iman,ta hau gyarawa..................................................
*Note: masu cewa wahalar da ake ba Noor tayi yawa,Hak'uri zaku yi,haka tsarin labarin yake,kuma ba haka zata yi ta zama cikin wahala ba,kunsan dukkan tsanani yana tare da sauk'i, So ku cigaba da biyo mu dai,Sannu a hankali komai zai warware,Wahalar da take ciki zai k'are Hausawa sunce komai nisan jifa k'asa zai dawo*
*OHW*
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
1⃣6⃣➖2⃣0⃣
""Tana gamawa,ta koma d'akin ta k'arasa cin abincinta
Ta fito zata kai plate kitchen,taga Yazeed ya dawo kenan za shi sashen Hajiya
Tai saurin komawa d'aki,Yace fito yar'iska,na ganki
""Ta fito jiki na b'ari,
""Yace wato wasan hide-and-seek zamu fara dake shaa,tunda ni sa'anki ne
""Ta girgiza kanta tace a'ah
""Useless ki ma fara,Oya wuce kije sashenmu ki jira ni,dama na gaya miki yau haaaaa.......ba sai na k'arasa ba
""Tace toh
Kitchen ta fara xuwa ta ajiye plate d'in
Ta wuce sashen su,a ranta tana cewa ko wacce muguntar zai mun kuma,ni dai Allah kai mun tsari dashi,Monster kawai
""Ta murd'a k'ofar falon a hankali ta shiga,
Imran dake falon,ya d'auka Yazeed ne ya shigo,dan haka ya juya yace Yazeed ya test d'in ?
""Kawai ya ganta,tsaki yaja ,ya kawar da kanshi a ranshi yace why ??why?? Oh shit,wallahi na tsani ganin yarinyar nan,tana sa naji b'acin rai ,buh sai ganinta nake all time,how can i get rid of her,ya kawai wuce d'akinshi
""Noor da mamaki ta tsaya tana kallonshi,ita dai yana burgeta,dan ba ruwanshi bai tab'a mata wani abu,amma ta rasa gane,me yasa duk lokacin da ya ganta,sai ya b'ata rai ya bar wurin,
Tana cikin tunanin,Yazeed ya shigo,
Kallon uku saura kwata ya mata,ya wuce d'akinshi
Jeans trousers ta gani ya kwaso da yawa, sun kai guda ashirin
Ya jibge su gabanta
""Yace ina so ki wanke su tas,sannan kar ki kuskura,ki sa su a washing machine ko ki wankesu da brush,da hannunki nake so ki wankesu
""Tuni idonta ya kawo k'walla,ita dai taga ta kanta,taya zata iya wanke jeans din nan
""Ya daka mata tsawa kinji ni ko baki ji ba
""Ta d'aga kanta sama alamun taji
""Oya dismiss
""Ta mik'e,da k'yar ta iya kwashe su,saboda nauyinsu
""Ta fita tana hawaye
Can wajen d'akinsu,akwai famfo nan taje,ta ajiye
Ta fara wankewa,tana kuka
Da k'yar take wankewa,gashi yau ta wahala da yawa,duk ta galabaita,
Wasu ma duk a wanke ne,tsabar mugunta ce kawai,ya had'a mata dasu
""Bayan wasu mintuna
Imran na kwance a d'akinshi,yana latsa waya
""Can kuma yace wa kanshi i have to warn Yazeed,idan zai sa yarinyar nan aiki,ya daina kawota sashenmu,yaje can ya gaya mata aikin da zata mishi,kuma daga yau bazan sake zuwa sashen Mum ba,sai na tabbata yarinyar nan bata nan,Daddy baka kyauta mana ba wlhy,
Mtcheewww yaja tsaki ya mik'e,ya fito
""Yazeed ya kira sunan shi fuska babu annuri
""Na'am Bro,
""Ina so daga yau kar ka k'ara kawo yarinyar nan sashen nan,idan zaka sa ta aiki,kaje can ka gaya mata
""But me yasa ?
""Saboda bana son ganinta,tana sani b'acin rai,idan na tuna matar Daddy ce,da kuma yadda ta banzatar da rayuwarta akan kud'i
""Yazeed yace ok bro,am sorry bazan k'ara kawota ba
""Bai sake cewa komai ba,ya juya ya koma d'akinshi
Lami rik'e da baki tace Noor waya saki wannan aikin ?
""Noor ta d'an yi murmushi tace wa kuwa banda wancan mugun
""Ohh ni Lami,na rasa me yasa yafi kuwa tsanarki a gidan nan
""Noor tace tun k'uje masa mota da nayi,sai kuma ya bani 15mints nazo ina bacci,da kuma haushin na auri Babansu
""Ai wannan duk ba k'akk'aura hujja ce da zai sa ya tsaneki haka ba,gwara na auren Babansu but duk da haka tsanar tayi yawa,ya dai bi a hankali wlh,dan idan k'iyayya tayi yawa tana iya komawa so,duk da kina matar babanshi kuwa,bari na taya ki,
""Kamar daga sama suka ji ana tafi
""Lokaci d'aya suka kai dubansu ga mai tafin
""Yazeed ne
""Gaba d'ayansu sai da gabansu ya fad'i,Noor duk tafi tsorata
""Yace weldone👍🏻,Allah ya tona asirinki dama kece mai zuga ta ko
""Jiki na rawa,Lami ta girgiza kai tace a'ah
""Lafiyayyan mari ya mata,Yace a'ahn Ubanki,naji komai ai,Yau zaki bar gidan nan,kije ki fara had'a kayanki
""Ba Lami kad'ai ba,har Noor ta girgiza da jin furucin shi
""Lami tai saurin kai gwiwoyinta k'asa tace kayi wa Allah da Annabi ,ka rufe min asiri kayi hak'uri,iyayena da wannan aikin nawa suka dogara
""I don't care,b'ace mun da gani ko in tattaka ki
""Jiki na rawa ta wuce tana kuka
""Ya juya kan Noor,yace da take ce miki k'iyayya zata iya komawa So,let me make it clear to you,nan ba film bane ko littafin hausa,da saurayi zai gama gasa yarinya,ya dawo yana sonta,nan ana maganar reality ne,so listen to me carefully,na tsaneki na tsaneki,bazan tab'a sonki ba,ko da ace ba igiyar auren Babana a kanki ballatana akwai,I hate you more dan u could ever imagine,sannan kika ce ni mugu ne koh
""Baki yi k'arya ba ni mugu ne,amma har yanzu baki shaida mugunta ta ba,but daga yau zaki tabbata cewa lallai Yazeed mugu ne,.........
""Sashen Hajiya,ya nufa
Tana zaune falo
Yace mum,wacce yar'iskan Lami ta bar gidan nan yau,munafuka ce ita ke zuga Noor
""Hajiya tace yau d'in nan kuwa,dan ina adawa da duk wanda zai nuna soyayya ko tausayi ga yarinyar nan,a cikin gidan nan,toh wlh sai ya bar gidan nan,dan haka barinta gidan nan ya zama dole,
""Noor d'aki tabi Lami,tana bata hak'uri
""Kiyi hak'uri Lami,In shaa Allahu bazai kore ki
""Muryar Hajiya suka ji tace kamar kin bar gidan nan kin gama,ko awa biyu,bana so ki k'ara a cikin gidan nan,hakan ya zama gargad'i ga yan baya,duk wanda ya nuna so ko tausayi ga Noor kora ce
""Na baki minti talatin ki had'a kayanki kibar gidan nan,ko ki fuskanci mummunan wulak'anci,ta watsa mata kud'inta,ga kud'inki nan
Ta fice fuuuu
""Kukan Lami ya tsananta,Noor ma kuka take sun k'ank'ame juna
A ranta tana cewa me yasa ake son raba ta da masoyanta,haka zata yi ta zama da wa'inda basa sonta,ita dai wannan *itace kaddarata*
""Lami ta raba jikinta,dana Noor,tace bari in tashi in tafi Noor,kar ta dawo ta wulaknta ni
""Noor na kuka tace yanzu tafiya zaki yi,ki barni ,ke kad'ai ke sona gidan nan Lami,gashi kema zaki tafi
""Kiyi hak'uri Noor,ki ta hak'uri watarana sai labari
""Har bakin gate tama Lami rakiya ,Suna ta kuka
Ta dawo cikin gida,rai a jagule,ji take kamar Allah ya d'au ranta ta huta
Har wani dishi-dishi take gani,Zuciyarta na mata zafi
Jiri ta fara gani,anan tsakar gidan ta fad'i sumammiyya
""Imran ya fito ,xai fita yana cikin mota,kawai yaga mota kwance gabanshi
""A tsorace ya fito daga motar
""Noor ya gani kwance bata numfashi,a rud'e yayi kanta har zai tab'ata,sai ya tuna matar babanshi ce, kuma ko ba matar babanshi bace ita ba muharramarshi bace
""Yayi cikin gida a rud'e yana kiran Lami! Lami! Lami! Shiru
""Abu(dayar mai'aikin) ta fito tace Lami bata nan
""Toh ke zo,tabi bayanshi
""D'auketa da sauri ki sata mota,mu kaita asibiti
""Da yake Abu k'atowa ce,kuma Noor bata da nauyi
Nan da nan ta d'auketa,ta sata mota
""Imran yaja motar sai asibiti
""Ta samu taimako na gaggawa,Imran duk ya rud'e saboda yana da masifar tausayi
Sai zirga zirga yake a passage d'in asibitin
""Bayan wasu mintuna,Likita yace yana son magana dashi
""A bisa binciken da muka yi,mun gano yarinyar nan damuwa ta mata yawa da tashin hankali,bai kamata ace at her age,tana da wannan damuwar ba
Dan haka tana buk'atar kula sosai,idan ba haka ba,komai zai iya faruwa,Zuciyarta zata iya bugawa ta mutu
""Imran a kid'ime yake kallon likita
""Likita yace Yes,so dan haka a kiyaye,yanzu zan rubuta muku,magunguna,ta rik'a sha In shaa Allahu zata samu sauk'i,amma fa sai ta rage damuwa,da shiga tashin hankali
""Ok Doctor,In shaa Allahu za'a kiyaye
""Ya rubuta mai drugs,ya fito kanshi na masifar sarawa,Yanzu ya zai yi,yasa ta samu kyakkyawar kulawa,yasan Hajiya ba zata tab'a barinta ta huta ba,ko su Yazeed,Shima kanshi bai so haka ta faru ba,Yaso ta cigaba da gasuwa tunda ita ta jefa kanta a halin,but yana da tausayi,Ba zai iya bari ta cigaba da shiga halin k'uncin nan ba,daga k'arshe ta mutu,iyayenta da danginta wane irin mutane ne,da zasu aurar da yarinya ba zasu rik'a zuwa suna duba lafiyarta ba,ko mahaifiyarta ce ya kamata ace tazo,tunda aka kawota ko mage bai tab'a ganin tazo dubata ba,gashi ko kayan arzik'i bata dashi kullum cikin yagaggun kaya,Daddy bai mata lefe bane da zai aureta,duk talaucin iyayenta ba'a ce an kawo ta gidan miji,da yagaggun kaya ba???
Me yasa ???? Shi ya kasan gane wannan al'amari ????
*OHW*
0 comments:
Post a Comment