""Pharmacy d'in asibitin yaje ya siyo drugs da likita ya rubuta,ya koma wajensu ""
""Noor na zaune kan kujera duk ta galabaita,tana maida numfashi da k'yar,Kallo d'aya Imran ya mata yaji ta masifar bashi tausayi,Ya kawar da kansa gefe
Yace Abu kamata mu tafi gida
Abu ta amsa da toh""
""Dukkansu bayan mota suka shiga,ko kad'an Imran bai damu ba,dan sun zauna bayan mota,ba kamar yadda samari ke yi ba suce an maida su driver,Tuk'inshi kawai yake,da tunani kala-kala a ranshi da kuma tausayin Noor""
""Noor tayi shiru tana tunani,garin yaya haka ta faru ? Ita dai tasan ta raka lami,ta dawo cikin gida,daga nan bata k'ara sanin me ya faru ba
Ta juya ta kalli Abu, murya can k'asan mak'oshi tace Dan Allah Abu me ya faru dani ?
Duk da a hankali tayi maganar amma hakan bai hana Imran ji ba,Ya rasa gane me yasa duk lokacin da yaji muryarta sai gabanshi ya fad'i kamar yadda in ya kalli fuskarta
Kafin Abu ta bata amsa, yace ki bari idan kun sauka kya tambayeta,bana son sake jin muryarki a motar nan
Tsit Noor tayi bata k'ara cewa komai ba,a ranta tace Ikon Allah,to meye da muryarta da ba'a son ji""
""Har suka kawo gida ba wanda ya sake magana
Da suka fito daga motar ya ba Abu magangunan
Yace gashi ki rik'a bata,ki tabbatar da tana sha akan lokaci
Ta amsa da toh
Noor suna fitowa dama gaba tayi abunta,kafin yace baya son ganinta""
""A d'aki ta sami Noor,ta jefa mata maganin
Tace gashi nan ba dani ba,ba zaki ja a koreni aikina ba,ni yanzu ko hanya ma bana son mu had'a dake,tasa kai ta fice
Noor tayi murmushin tak'aici tace ni dai Noor ,na zama mujiya a cikin mutane kuwa baya sona,gashi ni ba mummuna ba balle ace muni na ya jawo aka tsaneta,ina ga bak'in jini ne dai dani
Ya Allah! Ina rok'on ka ka yaye mun bak'in jinin nan nawa,kasa soyayyata a zuciyar bayinka(Ameen)""
""Ta jawo ledar magungunan tana dubawa
Tacewa kanta tabbas ko shakka babu,bayan na raka lami fad'uwa nayi,shine Imran ya kaini asibiti,a gaskiya Imran nada zuciyar imani,duk da cewa baya sona, ko ganina baya son yi amma yana tausayina,Allah ya saka mai da mafificin Alkhairi
Ta tashi tayo alwala,ta kabbara sallah""
""Imran d'akinshi ya wuce straight,ya kwanta kan gado,tunanin d'azu akan Noor ya sake dawo mai
Ina dangin yarinyar nan ? Me yasa Daddy zai aurota yasan bazai kula da ita ba ? Ko mummy ce ta hana shi kula ta ? Wata zuciyar tace mai itace ma,Daddy me yasa kake haka ka bari mummy na mulka ka,dole in maka magana akan Noor,ka gyara, ka bata cikakkiyar kulawa,in kuma baza ka iya ba,ka sallameta ta koma gidan iyayenta bazan zuba ido inga yarinyar mutane ta mutu ba""
""Ya mik'e da zafin nama,ya nufi sashen Alhaji
Alhaji na zaune shi kad'ai a falon shi yana kallon news
Bayan yayi sallama,sun gaisa
Cikin girmamawa Imran yace Daddy ina so muyi magana da kai
Alhaji ya d'an yi murumshi yace ina saurarenka d'a na""
""Amma Daddy Dan Allah ka tsaya ka saurareni,ka fahimce abunda zance""
""Imran kenan,ina saurarenka""
""Daddy akan maganar Noor ne
Wacce Noor
Matarka
Alhaji da mamaki yake kallon Imran yace Matata kuma ina da wata mata ne bayan hajiya
Imran ya d'an yi yar dariya yace Amaryarka toh
""Take Alhaji ya murtuke fuska yace dama maganar yarinyar nan zaka mun,toh ahir d'inka""
""Daddy matarka ce fah,kuma tana da hak'k'ina a kan ka""
""Nafi ka sanin matata ce,amma yanzu bani da iko da ita,sai abunda hajiya tace
Imran wani bak'in ciki yaji ya turnuk'eshi,shi bai tab'a ganin miji irin babansu ba,mai tsoron matarshi yace Daddy kai fah ne mai gidan nan,kai da iko ka fad'i abu,ayi ko kar ayi
A fusace Alhaji ya mik'e yace baka tab'a ganin b'acin raina ba koh,toh wallahi idan ka k'ara mun maganar nan zaka ga mummunan b'acin raina
""A hasale Imran,ya tashi ya bar falon
Zuciyarshi na mai masifar k'ona,wani irin uba ne dasu
Yanzu shi ya zai yi ya ceto Noor daga wannan hali
Tunda Daddy baya sonta,why not bazai sake ta ba
Bari yaje ya samu Noor d'in yaji ina danginta suke? Duk inda suke zai je ya nemo su,a raba auren nan kowa ya huta
""Noor kwata-kwata ta manta da zancen wanke jeans d'in Yazeed
Kamar an tsunkile shi(Yazeed) yace bari in tashi inje in gani,yar iskar yarinyar nan ta wanke su,ko kuwa""
""Jibge ya gansu,ita kuma bata wurin
A fusace yace what!! Diz girl is trying me,wato i should do my worst,i swear to God i won't spare her today,sai na mata abunda har ta manta bazata tab'a mantawa dani a rayuwarta ba,ni zata ma iskanci,ta nuna mun ita mai taurin kai ce
Noor ! Noor ! Ya k'wala mata kira kai kace tashin duniya ne yadda yake k'wala kiranta
A gigice ta fito ,jiki na rawa tace Gani
Bai tsaya wata-wata ba,ya d'aga hannu zai falla mata mari ,Yaji an rik'e hannunshi ta baya,an murd'e hannun
Noor har ta damtse ido tana jiran saukar mari
Shikuwa da mamaki ya juya yaga waye ya rik'e mai hannu,to his suprise yaga Imran
Noor kuwa jin bata ji saukar mari ba,yasa ta bud'e ido,ta tsaya tana kallonsu
Da mamaki yace Yaya,Noor ce fah zan mara,ba Ihsan ko Iman ba
""Imran ya d'an yi murmushi irin na manya,Yace kana tunanin bansan wacece ba,ina sane da ita ce"'
""Yaya kasan itace ka hana ni,
Ofcourse Yes,bari kaji daga yau kada ka k'ara d'aga hannunka,kace zaka mareta ko daketa,infact duk wani aiki kar k'ara sata,ka fita harkar ka,Matarka ubanka ce ,ba Baiwa ba ,kamar yadda kuka dauketa""
""Baki sake yake kallon Imran,Yace Yaya kasan me kake fad'a,yarinyar da ka tsani ganinta itace kake protecting yau,anya kasan me kake kuwa,ya fara tattab'a shi yana dudduba shi,yaji lafiyarshi kuwa""
""Imran ya fashe da dariya,Yace kana tunanin bansan me nake fad'a ba,lafiyata lau,
""Yazeed yace idan kuwa kace zaka goyi bayan yarinyar nan,zaka fuskanci mummunan b'aci rai daga wajen mummy
Imran yace na dai gaya maka,ka kiyaye yarinyar nan,b'ace mun da gani
Ya wuce ya gunguni,yana huci,a ranshi yana sak'a irin muguntar da zai mata idan Imran baya nan""
""Cike da mamaki Noor ke kallon Imran,tana mamaki ya aka yi yau yayi protecting d'inta,tana jin d'ad'i a ranta,yanzu ta samu mai kareta
Yana kallon gefe yace kada ki d'auki kare ki da nayi a matsayin wani abu,ko tausayinki yasa haka,bana tausayin masu irin halinki(ya fad'a ne kawai but yana masifar tausayinta) nayi hakane saboda abunda likita yace "zaki iya rasa ranki,idan kika cigaba da shiga halin k'unci, ni kuma bana so ki mutu ,a zarge iyayena
so yanzu nazo ki gaya mun ina iyayenki suke ? Kuma taya akai kika auri Daddy ?
Gabanta ne ya fad'i ba zata iya gaya mai tarihinta,saboda mummunan halin Babanta ,ba zata so yasan waye ubanta ba
Haka bazata iya gaya mai ya akayi ta auri Babansu ba,saboda tasan basu san sana'ar ubansu caca ba,kuma ba zata so su sani ba,ta dalilinta
Ba zata so familyn su shiga wani hali ba ta dalilinta
Duk wanda yaji sana'ar ubanshi caca dole ya girgiza
*Toh masu karatu,ku ba Noor shawara,me zata cewa Imran,ta fada mai gaskiya ko tayi shiru*
*Idan ta fada mai gaskiya tabbas zai daina ganin laifinta ,kuma zai taimaki rayuwarta*
*Amma kuma idan ta fada zata sa shi cikin tashin hankali,shi da k'annenshi zata ruguza musu farin ciki,Zasu daina ganin girman Ubansu,Toh yanzu ya zata yi*
*Muna jira comments dinku*
*OHW*
🏵🏵 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
2⃣6⃣➖3⃣0⃣
""Tambayarki nake kinyi shiru,Imran ya katse mata tunani
Tayi sauri ta zabura kanta a sunkuye k'asa,tace Na'am
Yace Eh ai kin jini
Ta sake yin shiru
Ya dakata mata tsawa,zaki bani amsa ko kuwa
Murya na rawa tace ni..ni..ma bansan ya akayi auren ba,kawai Babana ne yace ya d'aura mun aure,bayan haka bansan komai ba
K'arya kike yi,ki gaya mun gaskiya ya fad'a yana mata kallon tuhuma
Gaskiyar kenan Allah
Imran yayi shiru yana nazari yace a ranshi hakan na nufin auren dole aka mata kenan,to me yasa Babanta zai aura mata tsoho? i have to find out,Ya d'an sauke numfashi sannan yace Yanzu ina iyayenki ?
Murya a sanyaye tace Gidanmu na Garki II,
Garki II ya nanata a zuciyarshi,ba dai hakan na nufin iyayenta masu kud'i bane,maybe dai irin masu gadin nan ne,dan bata yi kalar ya'yen masu kud'i ba,but bari na tambayi sunan babanta,
Ya sunan mahaifinki ?
Alhaji Ibrahim Had'eja
Ya girgiza kanshi yace Gud,ya wuce ba tare da ya sake ce mata komai ba
Ta bishi da kallo tana mamakin me yasa yake mata tambayoyin nan,dama ya hak'ura da binciken nan,kar yaje ya bincikowa kansa abunda yafi k'arfinsa,dama hausawa sunce kaza wajen tone tonen ta take tonu wuk'ar da za'a yankata,ta kawar da tunanin,ta mik'e
Ta cigaba da wanke jeans d'in da k'yar, _duk da cewa taji mai Imran yace na ya fita harkarta,buh tasan halin Yazeed sarai,idan bata wankesu ba sai ta fuskanci mummunan b'acin rai_kwata-kwata bata jin dad'in jikinta,tana yi tana hutawa""
""Imran sashen su ya koma,ya watsa ruwa,ya sake shiga cikin manyan kaya,ya feshi jikinsa da turaruka designers masu bala'in k'amshi,Imran ba daga baya ba ta fannin gayu,Yayi kyau sosai,kai kace biki zashi,ko zance,Har yanzu bashi da budurwa,tunda yake bai tab'a soyayya ba,Mata masu ji da aji,sun sha kawo kansu gare shi yayi turus dasu,
Yazeed ne mai bala'in son mata kamar bunsuru,kawai shi dai ayi chilling da Yan'mata,Da har Yan'mata yake kawowa gidan,Sai da Imran ya taka mai burki,Yanzu sai dai ya kaisu hotel ko can wani wurin shak'atawa""
""Noor ta gama wanke jeans da k'yar,ta d'aukosu a bucket,zata je laundary ta shanya,ta hango Imran,ya fito sashensu,Taja ta tsaya,tana kallonshi,shi bai ganta ba
Ba k'aramin kyau ya mata ba,a zuciyarta tace Mashaa Allah,Tubarkallah,wannan irin kyau na Imran,Gashi da gayu,tausayi da kyan hali,a gaskiya matar shi ta more,ina ma ace shi Daddyna ya aura mun,da nafi kowa sa'a a duniya,amma inaaa nasan irinsu Imran, ba tsara na bane
Tana ta kallonshi har ya wuce parking space,ya shiga mota,ya tada
Sannan ta wuce laundary""
""Yazeed kuwa da ya wuce,sashen Hajiya yaje,Yana huci kamar wani bajimin zaki
Hajiya dasu Ihsan na zaune falo,
Lafiya Yazeed ya aka yi ?
Hajiya ta tambayeshi
Yana huci yace Mum can you imagine,nazo marin Noor,Ya Imran ya hana ni har yana murd'e mun hannu,yana cewa in fita harkarta,ita ba Baiwa bace kamar yadda muka d'auketa,
What! Imran da kanshi ta fad'a unbelievable
Wlh Mum nima nayi mamaki
Ta kad'a kai tace barni dashi zai zo ya sameni,sai ya gaya mun dalilinshi nayin haka,sannan Noor na nan a matsayin Baiwa,ba wanda ya isa ya kareta gidan nan wlh,kaje ka mata duk abunda kaga dama,idan ta maka laifi ka hukuntata son ranka,Baiwarku ce,Baiwar gidan ubanku ce
Ihsan ta tsomu bakinta tace to akan me ma,Ya Imran zai kareta,shi da ko son ganinta ba yayi
Iman tace nima shi na gani
Hajiya tace kaiii kuma kira mun yar'iska in k'ara tabbatar mata da matsayinta a gidan nan
Iman ta mik'e ta fita kiranta""
""Noor ta dawo d'aki kenan,Iman ta shigo rik'e da k'ugu tace fito munafukar Allah,jibe ta sumi-sumi
Noor bata ce komai ba,tsaye kawai tayi tana kallon Iman
Dallah! Kin wani tsare ni da kallo kamar tsohuwar mayya,wuce muje Mum ke kiran ki
Tayi gaba,Noor tabi bayanta""
""Sai da Hajiya ta k'are mata kallo sama da k'asa,Sannan ta juya kan Yazeed tace yi mata marin da kayi niyyar yi,Imran ya hana ka
Noor gabanta yace Rass,ta tsani a mareta,dan a ganinta, ba cin mutuncin da yawuce a mareka,but ita kullum cikin marinta ake,ba mai ganin mutuncinta ko darajarta
Yazeed yayi dariyar mugunta,ya taso da zafin nama,Ya d'aga hannu ya falla mata lafiyayyan mari
Sai da taga Stars,kanta ya fara juyawa,tana ganin jiri,mari ne ya mata na mugunta da k'arfi
Hajiya tace yawwa da kyau,gata nan ka mata horon duk da kaga dama,Baiwarku ce,ki daina tunanin cewar da Imran yayi ke ba baiwa bace,kin tashi daga Baiwa,kina nan a matsayinki ,duk da cewa ba a yak'i aka ciyo ki ba,amma kinsan inda aka ciyo ki,har gara a ciyoka a yak'i,akan inda aka ciyoki
Da mamaki suke kallon Hajiya,Yazeed yace bamu gane ba Mum,kamar ya?
Hajiya tayi saurin shan kwana tace ina nufin an aurota a banza,hausar tawa ce baku gane ba
Ohh woo suka had'a baki gaba d'aya
Noor hawayen bak'in ciki kawai take,ta rik'e kunci,a zuciyarta tace banda Allah yasa ina da zuciyar imani,yadda kuke azabtar dani d'in nan,da na tona yadda ubanku ya auroni""
""Yazeed yace kin wanke jeans d'in da na baki ko kuwa ?
Na wanke
Ya d'an yi murmushi yace haa....God save you,but duk da haka,ban gama dake ba,i have to punish you for delaying,and making Ya Imran to shout at me
Addu'ar neman tsari daga azzalumai ta fara karantowa
Ji kawai tayi wayarshi na ringing
Hello baby! Wata Babe ta fad'a
Ohh Suzy,hw re u
Fine,ina ta jiranka a Ibro hotel tun d'azu
Ohh sorry baby,on my way
Yayi hanging-up
Ya nuna Noor,da yatsa yace ki jira dawowata
Yana ta sauri,ya d'au car key d'inshi yace bye mum en sisters
Suka ce masa byee
Hajiya tace ke tambayar Su Ihsan,ba wani aiki da zaku sata ?
Ihsan tace ni dai babu
Iman tace nima babu
Hajiya tace ok! Oya tashi kije ki ba flowers ruwa
Wani sanyi taji a zuciyarta, ta furta Alhamdulillah! a ranta, da Allah ya mata tsari da Yazeed,ba flowers ruwa duk mai sauk'i ne""
""Imran Garki II ya nufa,bai sha wahalar gane gidansu ba,tambaya d'aya yayi aka nuna mai gidan,kasancewar mahaifinta sananne ne a unguwar
Yayi horn,Baba mai gadi ya taso ya bud'e mai gate,Bayan sun gaisa yake tambayarsa mai gidan na nan
Baba mai gadi yace eh! yana nan ciki
Shiru Imran yayi yana k'arewa gidan Kallo,har yanzu ya kasa yarda nan ne gidan mahaifin Noor saboda had'uwar gidan
Ya nisa yace Baba Dan Allah waye Ibrahim had'eja a gidan nan ?
Baba mai gadi ya d'an yi murmushi yace Ai shine mai gidan
Toh Baba dan Allah tambaya ta k'arshe in baza ka damun ba,
Ina saurarenka yaro
Imran yace shine mahaifin wata yarinya Noor
Baba mai gadi yace Eh shine,ita ce Babbar yar'sa wani abu ne
A'ah ba komai,kawai kace ana sallama dashi
Baba yace toh toh
Imran yayi shiru yana nazari yace yanzu ace wannan shine gidansu Noor,amma iyayenta suka kaita ba kayan arziki,gaskiya akwai wani abu a k'asa
Baba mai gadi ne ya katse mai tunani,Yace ka shiga ciki
Ok toh nagode
Falon da ya shiga,ba k'aramin tsaruwa yayi ba,Aljannar duniya,babu abunda babu na more rayuwar duniya,shi dai mamaki kawai yake
Masu aiki suka kawo mai abun motsa baki
Jim kad'an Daddyn Noor ya fito,da ka ganshi kaga mai ji da naira
Ya bashi hannu suka gaisa
Sannan ya samu wuri ya zauna,Yace d'an samari sai dai ban gane ka ba
Imran ya d'an yi murmushi tare da sosa k'eya yace D'an gidan Alhaji Mamman ne
Toooo tooo na gane,yana lafiya dai ko Daddy ya fad'a
Eh lafiya lau
Toh madallah,shi ya aiko ka ne
A'ah bashi ya aiko ni ba,nazo akan maganar yar'ka ne Noor
Ya'ta Noor kuma,ai ni yanzu bani da wata ya' Noor,dan yanzu ta tashi daga hannuna ta kuma hannunku
Eh Baba,nasan da haka amma maganar da zamu yi tana da amfani,da ka tsaya ka saurareni
Daddy ya b'ata rai yace kaga d'an samari,indai maganar Noor ce,bana son ji ka tashi,ka fita tun girma da arziki,kaje ka sami Ubanka shi ke da iko akanta bani ba
Yana fad'ar haka,ya tashi ya bar falon
Imran ya bishi da kallo,kallon mamaki,Me Daddy da mutumin nan ke nufi,ko shakka babu akwai wani b'oyayyen al'amari tsakaninsu,Ta ya za'a ce Uba baya son maganar yar'sa,kuma duk kud'insa ace ya bar yar'sa a tsiyace,cikin yagaggun kaya
Kuma me zai sa Daddy ba zai saketa ba,tunda baya sonta,baya kulata
Ya salam! Ina zan samu amsar tambayoyin nan, Ya dafe kanshi
Da k'yar ya iya mik'ewa,jiki ba k'wari
Yai sallama da Baba mai gadi tare da bashi 1k
Ya kama hanyar gida,da tunani barkatai a k'wak'walwarshi""................
*OHW*
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
3⃣1⃣➖3⃣5⃣
""Yana driving yana tunani,Anya yarinyar nan ba laifi tama iyayenta ba,shiyasa suka barta hka,toh ina mahaifiyarta? Ga dukkan alamu akwai abunda ita kanta yarinyar ke b'oyewa,dole in bugi ruwan cikinta inji me ye take b'oyewa,bana son aurensu da Daddy""
""Noor na watering flowers,tana wak'e wak'enta kamar yadda ta saba a gidansu,damuwa fal a cikin ranta
Imran ya fito daga mota ya hangota,Ya Salam! Ya furta sannan Yace ba xasu tab'a bari yarinyar nan ta huta ba,yanzu kuma waya sata watering flowers,ina fatan ba Yazeed bane coz in shine sai ya had'u da mummunan b'acin raina wlh,
Ya k'arasa inda take,
Wa ya saki wannan aiki? Ya tambayeta
Da saurin ta juyo,charaf idonsu ya had'u,gaba d'ayansu sai da suka ji fad'uwar gaba,Tai saurin sunkuyar da kanta,shima ya kawar da kansa gefe
A hnkli tace Hajiya
Ya d'an yi shiru,Yace ajiye,ki biyoni
Ta ajiye tiyon ba musu,tabi bayanshi
Can bayan gidan yaje da ita,akwai wasu kujerun roba masu kyau a wajen,ya mata nuni da d'aya yace ta zauna
Tana d'ari d'ari dashi ta zauna,kunyarshi take ji kuma at d same time tana shakkar shi,kwarjini yake mata,bata so yace tayi wani laifi
Ya murtuke fuska ba tare da ya kalleta ba,ita kuwa tana satar kallonshi,masifar kyaunshi take gani kuma bata gajiya da kallonshi
Yace ki saurareni da kyau,bana son k'arya,na tsani k'arya,duk wanda ya mun k'arya ina tsanarshi,tsana mai tsanani
Dan haka tambayoyin da zan miki yanzu,ina so ki gaya mun gaskiya,idan kika mun k'arya,na gano k'arya kikai mun,zan tsaneki fiye da yadda kike zato,
Gabanta ya fad'i, _ita idan kowa duniya zai tsaneta,ya tsaneta amma banda Imran,hknn taji bata so ya tsaneta,ta bashi wani matsayi mai girma a zuciyarta sbd shi kad'ai ne,bai tab'a mata wani abu ba ,na cin mutunchi tunda tazo gidan,Allah yasa kar ya mata tambayoyin da ba zata iya bashi amsa ba_
Maganarshi ta katse mata tunani,ki saurari tambayoyin da zan miki,ki bani amsa
Me ya had'aki da mahaifinki da baya son ko maganarki?
Ina mahaifiyarki take,da ta bari kike fuskantar rayuwar k'unci haka?
Noor tayi shiru sai hawaye,ya fama mata inda ke mata ciwo,rashin mahaifiyarta da tsanarta da Ubanta yayi
_Har ga Allah bana so asan babana ya tsane nine sbd wani dalili da ya sab'awa addinin musulunci,da yadda ubana ya ma mahaifiyata korar kare sbd ta haifeni,bana so girman Ubana ya fad'i a idon kowa,ko na mai k'aryar dalilin da yasa Daddy baya son maganata,nasan har duniya ta nad'e bazai samu ainihin dalilin ba,sbd ba wanda ya sani daga ni Daddy,mummy sai Baba mai gadi,sai fa mahaifiyata kuma cikinsu bbu wanda zai sanar dashi_
Ya katse mata tunani da cewa kina tunanin k'aryar da zaki gaya mun ne,oya go ahead and lie to me
Ta girgiza kanta tace A'ah ba k'arya zan ma ba,zan gaya ma gaskiya
_Mahaifiyata bata gidanmu,tun tasowa ta ban santa ba,ban san inda take ba, a wajen matar babana na tashi,ita ce bata sona take azabtar dani tasa Daddynah ya tsane ni_ ta k'arasa maganar tana kuka
Sosai ta bashi tausayi,kuma ya girgiza da jin bayaninta
Kina nufin baki tab'a ganin mahaifiyarki ba,tun tasowarki ?
Tayi nodding kanta alamar Eh
Gaba d'aya ta gama kashe mai jiki,duk haushinta da yake ji na auren daddysu,ya nemi ya rasa a zuciyarshi,Amma shi abunda ya kasa ganewa me yasa Daddynsu ya aureta,ita knta tace bata sani ba,babu wanda yasan wannan dalili sai Babanta da Daddynsu,anyway yanzu tunda ya gano ba laifinta bane,zai je ya gayawa su mummy, su daina azabtar da baiwar Allah,
Ita km Noor sai kuka take
Daina kuka kinji,share hawayenki
Kina so ki cigaba da auren Daddy?
Ta girgiza kanta,kina so ki koma gida
Tace Eh _Dan tafi so ta koma gidansu,akan ta cigaba da rayuwa gidan nan a matsayin matar Alhaji_
Shikenan kar ki damu In shaa Allahu zaki koma gidanku,tashi ki tafi d'aki,ki bar watering flowers d'in
Tace toh,Nagode
Ta tashi tafi,shima mik'ewa yayi ya bar wurin""
""Kan y'ar katifar ta ,ta kwanta,zuciyarta cike da farin ciki,finally zata bar gidan nan,zata koma gidansu duk da tasan can ma ba dad'i take ji ba,buh ta gwammace can da nan
Imran hak'ik'a kai mutum ne,kuma kana da hali mai kyau,Allah ya saka maka da alkhairi,
Da ta tuna in tabar gidan ba zata sake ganin Imran ba,sai kuma taji ba dad'i
Allah sarki! I will miss yhu wlh although bn saba dakai ba,bfr ko magana baka mun,ko mgn zaka mun sai da fad'a,but care d'in da ka nuna mun kwana biyu,naji bana son rabuwa da kai""
""Yana shiga falon Hajiya,bata ko tsaya ya gaisheta ba,ta rufe shi da fad'a Akan me zaka hana Yazeed marin Noor,har kana cewa ya fita harkarta,ita ba baiwa bace
Imran ya d'an yi murmushi yace Mum kenan,Dalilina na yin hka ba komai bane,illa na dawo daga office,naci karo da Noor a sume,na d'auketa na kaita asibiti,likita ke cewa damuwa ta mata yawa,idan ta cigaba da shiga damuwa,zuciyarta zata iya bugawa ta rasa ranta
Hajiya tace toh sai me in ta rasa ranta? Akan me ma zaka d'auketa ka kai ta asibiti ta mutu a wurin,ina ruwan wani
Da mamaki yake kallon mum d'inshi bai san rashin imaninta ya kai haka ba,Yace ta mutu fah kika ce Mum
Eh ta mutu
Imran ranshi ya fara b'aci yace gaskiya mum bazan iya bari yar mutane ta mutu ba,afterall itama ba da son ranta aka mata auren nan ba,yarinyar da ko mahaifiyarta bata sani ba,a hannun kishiyar mamanta ta tashi,ya kamata ace an tausaya mata
Wato ta gaya maka labarin k'arya ka yarda,me ye had'inka da ita da har zata baka wannan labarin,
Mum ni dai duk ba wannan ba,pls ku bar yarinyar nan ta huta,taji da abunda ke damunta
Hajiya a fusace tace ba za'a barta ba,Imran ka fita a idona,kuma ka fita hanyar yarinyar nan in baso kake ka fuskanci mummunan b'acin rai ba,
Imran yace naji zan fita harkarta Mum,but please kisa Daddy ya saketa,ta koma gidansu kowa ya huta
Idan da ace zai iya sakinta,da tuni ya saketa ta bar gidan nan,dan ni kaina bason auren nan nake ba
Da mamaki ya kalli Hajiya yace dan me bazai iya sakinta ba?
Imran me yasa kake son shiga hurumin da ba naka ba,
Toh Mum plxx one last favor,Dan Allah Dan Annabi tunda Daddy bazai iya sakinta ba,ku barta ta zauna peacefully har ranar da Allah zai kawo rabuwarsu da Daddy,
Nan kuma ne baka isa ba,aiki ne dole tayi shi
Ya d'unkule hannunshi,ya buga a d'ayan tafin hannu yace OMG ,Zuciyar shi ta kawo wuya,bai sake cewa komai ba sbd yasan mahaifiyarshi ce idanal yace zai k'ara magana zai iya fad'in ba dai dai ba,Imran akwai Zuciya
Buga k'ofar falon yayi ya fice
Hajiya ta bishi da kallo,tace Ikon Allah,ku ganmu da yaro,kayi ka gama ,Noor ce dai sai ta cigaba da bauta a gidan nan ko zata mutu""
""Kamar ya had'iye zuciya ya mutu haka yake ji,tsabar yadda zuciyarshi ke tafasa
D'akinshi ya shiga ya rufe kanshi da key,yana huci,yana magana shi kad'ai, _daga yau nayi alk'awarin zan kare ki Noor,i won't allow any harm to come to yhu,bazan bari kowa ya cutar da ita ba,zan kula da ita sai inda k'arfina ya k'are,ba wanda ya isa ya hana ni,kuma zanyi iya k'ok'arina dan ganin na raba aurensu da Daddy,akan me zai ce bazai iya sakinta ba,bayan baya kula da ita ya barta tana wahala,Wane irin Uba,Uwa da yan'uwa ne dani, da basu da tausayi ko kad'an a zuciyarsu,Allah ina rok'on ka shiryesu,ka ganar dasu hanya madaidaiciya_
Ya mik'e ya bud'e fridge,ya d'auko gorar ruwa,yasha ko ya rage jin zafi a zuciyarshi
Ya kwankwad'a sannan yayi ajiyar zuciya yace
*Zan kare ki Noor*
*Zan kula dake*
*Bazan sake bari wani ya cutar dake ba ko mahaifiyata ce kuwa*"
*OHW* 🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
3⃣6⃣➖4⃣0⃣
""Har dare Imran na d'aki bai fito bh,tunani ne birjik a ranshi,ta yadda zai taimaki Noor
Kwan!kwan!kwan! Yaji ana mai knocking bakin k'ofa,tsaki yayi yace Waye
Yazeed yace Nine bro
Ya aka yi?
Ka dai bud'e hot hot
See Yaxeed idan na bud'e k'ofar nn,naga shirme ne ranka zai b'aci
Eh! Na yadda
Imran ya taso ya bud'e mai k'ofa,ya juya ciki
Yazeed ya biyo bayanshi yana mik'a mishi wayarshi yace kalli wata babe bro,
Bata had'uwa ba Dan Allah
Wani dogon tsaki Imran yaja,yace dama abunda zaka gaya mun kenan,wai kai yaushe zaka yi hnkli,kaji tsoron Allah Yaxeed,baka da aiki sai bin mata,
Yazeed ya fara gunguni yace haba! Yaya baka tsaya kaji me zance bh,wannan fah aurenta xanyi
Na dai gaya maka kaji tsoron Allah
Yaya ni fah ina tsoron Allah
Fitar mun a d'aki
Ya fita yana gunguni yana cewa kai! You re always negative wlh
Imran ya tashi ya k'ara sa key ya rufe d'akinshi""
""Su Hajiya duk ranar basu k'ara waiwayar Noor ba,amma hakan ba wai yana nufin sun bi abunda Imran yace ba,they are just planning me zasu mata,irin azabar da xasu d'and'ana mata,su nuna mata Imran bai isa ya hana su dealing with her ba
Hajiya na tak'amar ita ta haifeshi so she has right over him,su Yazeed na tak'ama Hajiya na bayansu""
""Noor da taga basu bi ta kanta ba,tana ta murna
A tunaninta Imran ya musu magana shiyasa suka k'yaleta,yanzu jira kawai take ace Alhaji ya saketa
Dan burinta yanzu bai wuce na Alhaji ya saketa ba""
*8:00am*
*Ana sanyi sosai har buji ake*
""Engr.Imran ya shirya tsaf zashi office,yana aiki a wani company da ake Generator,Shine Accountant,Sosai yake samun kud'i
Sashen masu aiki ya nufa,bakin k'ofar d'akin Noor ya tsaya,yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga,yana so yaga lafiyarta
kawai wata zuciyar tace toh me ye just ka shiga,ai lafiyarta zaka duba""
""A hankali ya tura k'ofar d'akin,ya shiga
Tana kwance kan sallaya(daga gani Sallah ta gama barci ya d'auketa a nan),ta takure wuri d'aya alamun sanyi take ji,
D'akin ya dudduba yaga ko zai ga bargo,yaga babu ko bedsheet,katifar da take kwana a kanta ma hknn take wayam
A ranshi yace yanzu duk sanyin nan haka take kwana ba bargo infact ko ma bedsheet babu a katifarta,Wacce irin zuciya ce da Mum haka,da bata da tausayi ko kad'an
Ya juya ya fita,d'akinshi ya koma
Ya d'auko d'aya daga cikin bedsheet d'inshi tare da blanket
Ya rufe ta da bargon,sannan ya shimfid'a mata bedsheet
Ya kalleta,yaga yadda taja bargon ta k'udundene,yayi murmushi ya fita,Yana mai masifar jin tausayinta""
""Noor barcinta kawai take sha,ta lume cikin bargo""
""Tunda sassafe aka kira Hajiya k'anin babanta ya rasu,ba shiri suka kama hanyar zaria(garinsu),ita,Alhaji ,Yaxeed dasu ihsan,Imran na office bai sani ba""
*11:20am*
""Noor ta farka taji ta cikin bargo
Tai saurin tashi zaune,tana kallon bargon mamaki take waye ya lullub'eta da bargon nan mai kyau,takai dubanta ga katifarta taga bedsheet shimfid'e
Shiru tayi tana tunani,can zuciyarta tace mata tabbas Maganar da Imran yama su Hajiya ne yasa suka chanza,gashi har rana ta fito ba'a tashe ta ba
Murmushi tayi,wani d'ad'i ya ziyarci zuciyarta
D'akin ya game da wani daddad'an k'amshi turare
Ita dai ji take kmr tasan mai k'amshin turaren nan amma ta kasa gane waye
Mik'ewa tayi ta shiga toilet ta kuskure bakinta dan bata da brush,aswaki kawai take kullum(tun tana gidansu,hak'oranta tas suke farare kamar tana sa musu toothpaste),tayi wanka da sabulun(Giv) na lami ne da ta mnta,amma Noor tun tasowarta bata wanka da Sabulu sai fah sabulun wanki ,idan tayi wanki ya rage ta d'auka""
""Yagaggun kayanta tasa,ta fita kitchen dan tambayar masu aiki,wa ya lullub'eta a cikinsu,ta mata godiya
Suna ta famar aikinsu
Noor tayi sallama ba wanda ya amsata
Ta sake yi, suka mata banza,hkn ya tabbatar mata sun jita suka mata banza
Murya a sanyaye tace Dan Allah wa ya rufeni da bargo cikinku ya shimfid'a mun bedsheet
Tsaki Abu taja,tace kuji wannan wa zai rufe ki kuwa
Suka b'arke da dariya ,suka ce amma ke anyi yar' rainin hnkli wlh,wa kika ajiye da zai miki wannan
Ko kin manta matsayinki ne a gidan nan,Baiwa ce kefah ba kowa ba
Wannan ya fad'a mata bak'ar magana,wannan ya fad'a,haka suka dinga gasa mata bak'ak'en maganganu
Wani bak'in ciki taji yazo ya tokareta,ace gidan mijinka,masu aiki na maka wannan cin mutunchi,ita wannan ba zaman aure tazo yi ba,bauta aka kawota
Wasu zazzafan hawaye taji suna kwaranya daga idanunta
Ta juya ta fita daga kitchen d'in
D'aki ta koma tana ta kukan bak'in ciki da tunanin wa ya shimfid'a mata bedsheet/ya rufe ta da bargo,ta dai san yaran gidan nn ko nasu basa shimfid'awa balle su shimfid'a mata toh ko waye? Ko aljani ne?
Cikinta taji yayi k'uuu,alamun yunwa rabon da taci abinchi tun tafiyar Lami,Tace wa kanta yanzu ina zan samu abinchi,nasan masu aikin nan bazasu bani abinchi ba,Allah sarki lami Allah ya jik'anta ba don ta mutu ba
Kamar wasa taji cikinta ya murd'e,k'irjinta na zafi,
Nan ta rik'e cikinta tana kuka,tana kiran sunan Allah
Bargo ta jawo ta k'udundune,tana ta murd'e murd'en ciwon ciki""
""Tana nan kwance har azahar,tayi kuka har ta gaji,idonta duk sun kumbura,fuskarta tayi jajir kunsan farin mutum
Su Hajiya har lkcin basu dawo ba
Imran ya dawo gida lunch,dama gida yake lunch
Yana parking motar shi straight d'akin Noor ya nufa(ya gani tana nn k an sata wani aikin)""
""Shesshek'ar kuka yaji,a rud'e ya yaye bargon,yana tambayarta lafiya? Wani abu aka miki?
Kamar daga sama haka taji muryarshi,ba tare da ta tashi zaune ba
Tace cikina ke ciwo,
A hnkli ya furta Ya Salam! Tashi muje asibiti,xaki iya tashi ko na kira Abu ta kama miki
Murya a sanyaye tace zan iya
Ok tashi muje,Sannu
Da k'yar ta mik'e,tana tafiya da k'yar har suka kai mota,ya bud'e mata k'ofar baya,ta shiga ta kwanta,ya mayar ya rufe
Ya koma driver's seat yaja mota""
""A asibitin sai makyarkyatar sanyi take,Sweater(rigar sanyi)dake jikinshi ya cire ya mik'a mata Yace gashi kisa
Da mamaki take kallonshi snn ta girgiza kanta tace A'ah
Yace karb'a mana
Da k'yar take magana sbd zafin ciwo tace ya za'a yi nasa sweater'nka,
Ya d'an murtuke fuska yace ki karb'a,bana son kilibibi
Jiki a sanyaye ta karb'a,ta rik'e
Da d'an tsawa yace sa mana
Sannan jiki na rawa tasa coz taga ranshi ya fara b'aci ita kuma abunda bata so kenan""
""Likita bayan ya dubata ya d'an yi gwaje gwaje,Yace Ulcer ne da ita
Imran bai yi mamakin jin tana da Ulcer ba,yasan za'a rina,tsab mum zata iya hana mata abinci
Likita ya rubuta magungunan ulcer,tare da cewa ta rik'a cin abinchi,da shan irinsu madara da maltina haka""
""Imran da ya siya magungunan,shopping mall ya biya
Ya siyo katon d'in Maltina biyu,Family size madara d'aya,madarar ruwa katon d'aya,milo,sugar,biscuit,Yoghurt,katon na swan water(ruwan gora)
Ya kuma biya restaurant ya siyo take away na jollof rice with chicken,
Ko da suka isa gida,shi ya kwashi kayan da kanshi,ko tsinki bai bari ta d'auka ba,har d'aki ya kai mata,
Kawai gani tayi yana shigo da kaya,ita mamaki ma ya hanata yin magana,sai da ya gama shigo da kayan,ya samu wuri ya zauna,ya jawo leda take away,ya bud'e ya tura gabanta,Yace oya ci
Ba tare da tace uffan ba,ta fara ci,duk da tana jin kunyarshi,hakan bai hanata ci ba, sbd yunwar da take ji,Sai da ta cinye tas
Ya jawo kofin dake gefen katifarta,ya bud'e maltina ya zuba a ciki tare da juye gungun madara d'aya(na ruwa)
Ya mik'a mata,ta k'arba ta kafa kai ta shanye,
Snn ya b'allo magani da ruwan gora,ya bata tasha
Ita dai binshi da ido kawai take tana mamaki""
""Ya mik'e yace kayan nn naki ne,ki rik'a ci,kina shan magani akan lkci,nasan ba lallai ki rik'a samun abinci kullum ba,but zan ma masu aiki magana su rik'a kawo miki
Har yasa k'afa d'aya waje
A hnkli murya can k'asa tace nago........
Yai saurin katse da cewa No need""
""Noor tana magana a fili lallai Imran mutum ne,tunda nake ba wanda ya tab'a mun irin abunda Imran yamun sai fah Baba maigadi da ya ilamantar dani,Allah yayi shi mai tausayi, ina ma ace haka sauran yan'uwanshi suke,ko shakka babu d'azu ma shi ya rufeni da bargo,k'amshin turarenshi ne naji d'azu
Zuciyarta taji tayi fari k'al,kamar an zuba mata k'ank'ara a zuciya
Allah ya saka maka da Alkhairi Imran,Matarka ta more wlh
Ya Allah! Ka raba aurena da Alhaji ka bani miji mai irin halin Imran,inma da hali mai kama dashi,dan Imran nada kyau,ina son namiji mai irin kyaunshi
Wata zuciyar tace mata baki da hankali,kina a hakan zaki samu miji kamar Imran,ai sai dai mummuna ko tsoho,
Kawai sai taji hawaye ita dai bata da madafa,Allah kad'ai ne gatan ta,sai fa Imran yanzu dake neman taimakon rayuwarta.................
*OHW*
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!*
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*Wannan page sadaukarwa ne gareki Ummu Yahya(Goyon kaka🍒) Mun gode da k'auna da bibiyar littafin nan da kike Allah ya bar k'auna da zumunci tsakaninmu*❣❣❣
4⃣6⃣➖5⃣0⃣
""Noor da ta tashi daga barci,taga kula ajiye gefenta
Murmushi tayi,dan da wata masifar yunwa ta tashi
Bakinta ta kuskure,coz tayi Sallah da asuba
Ta zauna taci breakfast d'in(Chips,plantain and fried egg)
Ta had'a kakkauran tea'nta
A ranta sai addu'a take yiwa Imran(coz shine sillar take samun abinchi haka)
Tana gamawa wanka tayi,kamar kullum yagaggun kayanta tasa
Ta d'auki kula ta tafi kaiwa kitchen
Kular kawai ta ajiye bata tanka su ba
Har ta juya zata fita
D'aya daga cikin masu aikin wadda ake cewa Lubah tace wai me kike nufi Kwana nan da bakya fitowa kiyi aiki,ko dan kinga hajiya bata nan
Noor tace dama Hajiya bata nan
Lubah ta yatsina fuska tace ban sani ba
Abu ta tsoma baki in ma dan kinga bata nan ne,kike iskancin nan, zata dawo ta same ki ne
Noor murmushin takaici tayi tace kuyi hak'uri ba haka bane,bana jin dad'i ne
Yatsina fuska suka yi,suka ce Umm....kar ma kiyi ,Zaki amsa kira wajenta idan ta dawo
Noor bata sake cewa uffan ba,tasa kai ta fita""
""Dama Hajiya bata nan,toh ina taje? Tambayar da take wa kanta kenan
Ni bama wannan ba,Yaushe zan bar gidan nan,in huta da wannan wulak'anci da cin fuska,duk da nasan can ma ba dad'i nake ji ba,amma gwara gidanmu da nan,Imran ne kawai bana son bari,in na tuna shi sai inji kamar nai ta zama a gidan nan amma cin fuskar yayi yawa
Mik'ewa tayi tana kallon kanta a madubin d'akin,taga ta masifar rame,Amma bata yi bak'i ba(farinta na nan,jawur da ita)
Hawaye ta fara, tacewa kanta wallahi idan ba'a d'au mataki ba,na cigaba da zama gidan nan mutuwa zanyi😭,Allah yasa su Hajiya su chanza behaviour d'insu towards me,idan kuma baza su chanza ba Allah ya kawo mun mafitar alkhairi,ni dai tun da na taso bansan dad'in rayuwa ba,sai wahalar rayuwa
Allah gani gare ka,ni baiwarka ce na kawo kukana gareka kaji k'aina""
*4:30pm* dai-dai
Su Imran suka shigo garin Abuja,Jikin Imran duk ya gama sanyi,mutuwar Uncle Suleiman ba k'aramin girgizashi tayi ba,hakan ya k'ara tabbatar mishi da duniya ba bakin komai bace,kuma a koda yaushe kana iya mutuwa,
Wunin ranar da bai ga Noor ba( _coz lkcin da ya lek'a d'akinta tana barci,kuma ta k'udundune a bargo ko fuskarta ba'a gani_)
Duk sai yaji yayi missing d'inta,so kawai yake ya koma gida ya ganta,
Tambayar kanshi ya tsaya yana yi,to akan me zanyi missing d'inta?,dan wuni d'aya ban ganta ba,ba kwana ba,ba sati ba
Wata zuciyar tace mishi tausayinta ne da ya maka yawa,ya yarda cewa eh! tausayinta ne""
""Noor itama duk tayi missing d'inshi,kwanakin nn ta saba yana lek'owa ya tambayi lafiyarta,ko ya tambayeta tasha magani,inma bai lek'o d'akinta ba,Suna had'uwa a filin gidan
Dan haka duk ta kasa sukuni,sai sintiri take a tsakar gidan(tasan by this time yana dawowa lunch)
Ji take kamar taje sashen su(Imran da Yazeed) har tayi hanyar sashen,Zuciyarta tace mata baki da hankaline zaki je, toh kije kice mishi me,kuma idan kika je baya nan fah,kika ga Yazeed u knw Yazeed won't allow you to go free, sai yayi hurting d'inki,
Ta juyo ta dawo,d'aki ta koma, ta zauna tayi jigum,tana cewa Allah yasa ba k'yaleni zai yi ba,ni in kowa zai fita harkarta bazan damu ba,amma Imran bazan iya jurewa ba,i dnt knw why Imran ina jin shi har k'asan zuciyata( _kuma hankalinta bai bata ta duba motocin gidan ba_)""
""Imran suna parking motar su yayi hanyar d'akin Noor( _dan ba wanda yake so yasa a ido kamar Noor_)
Yazeed yace ina kuma zaka nan?
Zan duba Noor
Noor kuma bro
Yes! Anything wrong with that
Bro! Wai me yasa kake damun kanka akan yarinyar nan? Haba! Nasan kana da tausayi sosai buh please ka daina tausayin yarinyar nan,Green snake ce under the green grass,tana wani sumi-sumi kamar ta Allah
Imran tsaki kawai yaja,ya girgiza kai ya wuce _coz bashi dama lokacinshi_
Yazeed yaji wani haushi ya mamaye zuciyarshi,shi yafi so Imran ya fita harkarta,yadda zai ji dad'in yi mata mugunta""
""Sallamar Imran Noor taji,kamar an zuba mata k'ank'ara a zuciyarta haka taji,tai saurin mik'ewa zaune daga kwance da take,
Ta amsa masa sallamar da muryar farin ciki
Yasa kai ya shiga d'akin
Kanta tai saurin sunkuyar tana murmushi,(coz ta tuna jiya,da ta tsura mishi ido yace ya dai)
Kallo d'aya ya mata,ya kawar da kanshi gefe _wani sanyi yaji a zuciyarta da bai san dalili ba_
Shiru ba wanda yace komai
Noor ji take kmr tace mishi ina ka shiga yau,sai kuma ta basar
Cikin sanyin murya Noor tace Ina wuni?
Yace Ina wuni kuma,Kina matsayin matar babana kina gaisheni,ai ni ya kamata na gaishe ki
Dan haka ina wuni?
Ranta taji ya b'aci da ya kirata da matar babanshi(ta tsani ace ita matar Alhaji ce)
Shiru tayi bata amsa ba,
Yasan dama zai yi wuya ta amsa gaisuwar,Yace tunda ba zaki amsa gaisuwar d'anki ba,Toh Ya jikin ki?
Jiki Alhamdulillah!
Hope kinci abinchi kin sha magani?
Eh! Ta bashi amsa
Ok! Good
Murya a sanyaye tace Dan Allah ina su Hajiya?
Ya d'an yi shiru,sannan yace Suna zaria,k'aninta ne ya rasu
Noor bata san sanda tai saurin d'ago kai ba, ta kalli shi( _sai dai shi ba ita yake kallo ba_)
Tace Subhanallah! Allah ya jik'anshi
Ameen ya bata masa
Ba tare da ya sake cewa komai ba yasa kai ya fita
Ya bar Noor nata jimamin mutuwar (duk da bata san shi ba)
*Bayan kwana biyu*
""Yan gaisuwa an fara watsewa,dan jiya aka yi sadakar uku
Hajiya ma na shirin dawowa Abuja,Ta nemi alfarmar yan'uwa akan Dan Allah abata Khairat ta tafi da ita Abuja,tasa ta makaranta acan
Barinta nan shi zai sa ta rik'a tuno da Daddynta,can kuma gasu Ihsan zasu d'ebeta kewa,yanzu gashi daga zuwan Imran,har yasa ta saki jikinta
Ba musu Aunty maryam da Yan'uwa suka amince
Kuma sunji dad'i sosai,dan Hajiya ta nuna zumunci
Khairat d'inma ta amince,dan tafi so tayi nisa da gida,ko zata rage damuwa en she want to be close to Imran(tana son kasancewa kusa da Imran) _but zata yi missing mum d'inta da k'annenta_
Khairat ta had'a kayanta
Washegari zasu dawo Abuja""..................
*OHW*
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗?
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
5⃣1⃣➖5⃣5⃣
*DAN ALLAH FANS INA BARAR ADDU'ARKU👏🏻,INA FAMA DA CIWON KUNNE*
""Masu aiki sai faman gyare-gyare suke yau Hajiya zata dawo,Noor ta fito tasa hannu an gyara sashen hajiya,Anyi girke-girke
Hajiya bata sanar da Alhaji ta d'auko khairat ba,dan a ganinta itace mai gidan, hka su Imran basu sani ba""
""Noor ko kad'an bata farin cikin dawowar Hajiya,kwana biyun nan da bata nn,ta samu hutu duk da tana addu'ar Allah yasa su chanza
Tana zaune d'aki tayi jigum tana karatun Qur'ani,a rayuwarta tana bala'in son ta haddace Qur'ani,a gidansu Baba mai gadi ke k'arbar mata hadda,har ta haddace hizib goma,kuma tana bala'in son mkrnta amma bata da wanda zai kaita,sai hawaye shaa ya wanke fuskarta
Ta hau magana a fili
_Ni bnga amfanin rayuwata ba,bani da kowa ,bana zuwa makaranta Allah balle ta boko,Taya zanyi ilimi,kullum ina zaune gida cikin wahala da k'uncin rayuwa,bani da k'awa,bani da masoyi_
Ya Allah! Ka d'au raina na huta.....ta k'ara tsananta sautin kukanta
Kamar daga sama taji muryar Imran cikin b'acin rai yake magana Noor kina da hnkli kuwa,kinsan me kike fad'a,me yasa baza kiyi imani da k'addara ba,duk tsanani yana tare da sauk'i kuma Allah na tare da masu hak'uri,wasu ma an jarrabesu fiye da yadda kike fuskanta,hak'uri zaki cigaba dayi kina addu'a,
Shesshek'ar kuka kawai take ta kasa cewa komai
Imran har cikin ranshi yake jin kukanta,idan akwai abunda ya tsani ji shine kukan Noor
Hannu yasa a aljihi ya zaro handkerchief ya mik'a mata,tare da cewa karb'a ki goge hawayenki,bana son ganinsu
Jin yace baya son ganin hawayenta yasa ta saurin gogesu
Yana kallonta yadda take ta saurin gogewa,tana k'ok'arin had'iye kukan
Hakan ba k'aramin dad'i ya mishi ba(dashi knshi baisan dalilin jin dad'i dan ta daina kuka ba)
Yayi ajiyar zuciya yace makaranta kike so?
Tai saurin d'aga kanta sama tace Eh
Rashin makaranta ke saki kuka?
Ta sake cewa Eh
Yace kar ki damu,In shaa Allah xn saki makaranta
Kamar an mata albishirin kujeran makka,haka taji dad'in zancen Imran ko a mafarki bata tab'a tunanin xuwa makaranta ba
Murya a sanyaye tace Nagode Allah ya saka da alkhairi
Yai murmushi yace No!ki daina mun godiya,Duk abunda kike buk'ata duniyar nan zan miki shi, indai bai fi k'arfina ba,
I will stand by your side no matter the situation
Farin ciki ne ya mamaye zuciyarta kawai sai tunanin sakinta da Alhaji zai yi ya fad'o mata rai(tasan idan Alhaji ya saketa shknn gidansu zata koma ba zance mkrnta,ko kula da ita da Imran ke fad'in zai yi)dan haka murna ta koma ciki
Idonta suka kawo k'walla bnda Imran da tabar hawaye sun xubo
Ya dai? Imran ya fad'a
Ta had'iye miyau tace tunani nake idan na bar gidan nan shikenan bani ba makaranta
Imran ya d'an yi shiru,sannan ya nisa yace barin ki gidan nan abu mai wuya ne, sai dai Ikon Allah,dan nama Alhaji magana yace bazai iya sakin ki ba,wanda na rasa dalilinshi nacewa haka
Noor tayi shiru taji dad'in zance,at d same time bata ji ba _tana son yin makaranta,haka tana son tashi daga matsayin matar Alhaji_
Ganin Imran na kallonta,yana jiran yaji me zata ce,Tayi murmushi tace Allah yasa haka yafi zama alkhairi
Ya amsa da Ameen,kinci abinchi?
Eh! Naci
Toh kinsha magani?
Eh!
Good! Pls ki kiyaye shan magani da cin abinchi
Tayi nodding kanta tace In shaa Allah""
""Noor tasan dalilin da yasa Alhaji yace bazai saketa ba,ba zai wuce kan harkarsu ta caca ba,Mik'a al'amuranta kawai tayi ga Allah ya zab'a mata mafi alkhairi""
""Su hajiya sun iso
Imran da Yazeed ba k'aramin farin cikin ganin Khairat suka yi ba
Imran na tausayinta sosai
Gaba d'ayansu sun baje a falon sashen Hajiya,
Imran yace Mum dama tare da Khairat zaku dawo shine baki sanar damu ba,mu shirya tarbonta
Hajiya tace ina son nayi suprising d'inku ne amma yanzu bata b'aci ba,kuna iya tarbon nata
Khairat tace k'yaleshi mum,ko kin fad'a musu,ba wani abu da zai yi
Imran yace au haka kikace,shikenan na fasa abunda nayi niyya
Khairat tace Sorry Yayana,wasa nake
Imran yace a'ah ni dai na fasa
Please!please! Yayana, ta fad'a tana shagwab'a
Imran yace ji yadda ta wani marairaice,ba dan halinki ba,na hak'ura
Khairat tayi murmushi tace Yawwa Yayana
Hajiya kallonsu kawai take tana murmushi tana sak'a abubuwa a ranta""
""Noor ta mik'e daga kwance da take,Tace bari naje nama Hajiya sannu da zuwa
Gabanta nata fad'uwa ta shiga falon
Kowa ya bita da matsiyacin kallo,Imran kad'ai ne ya mata kallon arzik'i,Khairat ma wani irin kallo take mata na k'ask'anci(daga yanayin shigarta ya tabbatar mata yar'aiki ce)
Noor duk ta gama tsarguwa,ta durk'usa gaban Hajiya,kanta sunkuye k'asa
Murya a sanyaye tace Sannu da Zuwa hajiya,Ya hanya? Ya hak'uri? Allah ya jik'anshi
Hajiya hannu tasa ta dakatar da ita✋🏻
Nace miki ina buk'atar gaisuwarki,Munafuka
Imran yace haba! Mum me ye a ciki dan ta miki gaisuwa
Hajiya tace Baza ka daina sa mun baki akan harkar yarinyar nan ba koh
Imran yace Mum ba haka bane,naga ba wani laifi a ciki dan ta miki gaisuwa
A fusace Hajiya tace toh bana buk'ata
Ta juya kan Noor
A tsawace tace tashi ki b'ace mun da gani kafin nayi k'wallo dake makira
Yazeed yace Bro! Wai me yasa kake haka?
A fusace Imran yace keep your mouth shut or else.... _ya riga ya kawo wuya zuciyarshi har zafi take,Yadda yake ji gwara a tsinka mai mari akan a tab'a Noor,ko bak'ar magana baya so yaga an mata_
Ganin yanayinshi yasa Yazeed yaja bakinshi yayi shiru,yasan halin Yayan nashi
Tashi yayi ya bar falon
Hajiya ta bishi da kallo tace sannu Uban yan tausayi
Yazeed yace ni na kasa gane kan Yaya akan yarinyar nan
Hajiya tace wai shi mai tausayi
Ihsan tace but mum ai da baya tausayinta,yanzu ne ya fara
Hajiya tace hmm! Wai ce mishi tayi ba da son ranta aka mata aure ba,hannun kishiyar mamanta ta tashi,bata tab'a ganin mamanta ba
Yazeed dogon tsaki yaja yace and so,shi zai sa yaji tausayinta
Hajiya tace kunsan haka zuciyarshi take kamar ta mata,har gwara ta wasu matan
Iman tace mu dai gaskiya zai takura mana,ya hana mu dealing with her
Yazeed yace wlh sai dai yayi duk abunda zai yi, amma bazai hana ni dealing with her ba
Ya tashi ya fita a fusace""
""Khairat ita dai sun sata a duhu
Wacece ita? Ta tambaya
Matar Daddy Ihsan ta fad'a
Cike da mamaki take kallon Ihsan tace matar Daddy kuma(Hajiya bata gayawa kowa Alhaji yayi aure ba,dan a ganinta abun kunya ne)
Ihsan tace Yes,tashi muje d'aki na baki labari
Iman tace nima bari na tafi d'aki,mun dawo tafiya ko hutawa bamu yi mun had'u da crises d'in shegiyar yarinyar nan""
""Imran tunaninshi taya zai b'ullo da al'amarin sa Noor makaranta,yasan ba k'aramin gwagwarmaya za'ayi ba kafin hajiya ta yarda,but kome zai faru ya dad'e bai faru ba,amma ya riga yayi alwashin sa Noor makaranta,da kud'inshi zai sata bayan buk'atar sulen kowa""
""Khairat an sata makarantarsu Ihsan,level d'insu d'aya
Khairat itama ta d'au tsanar duniya ta d'aurawa Noor,dama tana ganinta taji bata mata ba,da k'arin ganin yadda Imran ke rawar k'afa a kanta(Noor),duk da cewa itama yana bata kula sosai""
""Duk yamma bayan sallar la'asar,Imran sai ya kira Noor garden,sun sha hira sai magrib suke tashi,yana yin hakane dan ya kawar mata da damuwa,sosai hkn ya rage mata damuwa( _duk da ita bata wani magana shine ke bata labari,kuma yakan tambayeta abubuwan da take so,da wanda bata so,ita kuma tana fad'a mishi tun bata sakin jiki dashi har takai ga yanzu ta saba,sosai take jin Imran a ranta,idan suna hirar bata k'i su kwana suna yi ba,gidan ba wanda ya sani_""
""Yau ma zaune suke suna hira,
Itatuwan dake garden nata kad'awa
sanyin iskan na dukansu,Imran har wani lumshe ido yake idan iskan na dukanshi
Meye babban burinki a rayuwarki?
Noor na wasa da yan'yatsunta tace Naga mahaifiyata
Ta bashi tausayi Yace baki san ina ne garinsu ba?
Baba mai gadi yace mun asalinta yar Nijer ce,irin buzayen nan ne dake zama kongo,anan mahaifina ya ganta,ya aureta
Imran yayi shiru na d'an mintuna a ranshi yace No wonder kike da kyau haka ashe ke buzuwa ce,snn ya nisa yace Allah ya had'aki da ita watarana
Ameen ta bashi amsa
Kallonta yayi yaga yadda kayan jikinta suka bala'in tsufa,atamfar duk ta k'od'e,Ya mik'e yace tashi muje wani wuri
Ido ta zaro tace idan hajiya ko wani ya ganmu fah
And so,Sai me,Ya fad'a da irin i don't care d'in nan
Noor kamar ba zata mik'e ba,a tsorace take
Da d'an tsawa yace tashi mu tafi mana,ke matar Babana ce,so meye a ciki dan na fita dake,matsayin mahaifiyata kike
Noor bata ce komai ba,ta mik'e,
Yayi gaba tabi bayanshi""
""Gani tayi yaja ya tsaya,itama ta tsaya
Khairat ya dai?
Ta shagwab'e tace dama kana nan tun d'azu ina ta nemanka
Imran yayi murmushi yace Uhmm....k'anwata rigima,me kike so ne?
Ta turo baki tace Shawarma nake son ci,ka kaini na siya
Your wish is my command k'anwata,je ki d'auka mayafinki,dama yanzu zamu fita da Noor
Sai a lokacin ta lura da Noor,tsaye bayanshi kamar munafuka
Ta yatsina fuska tace zaku fita? Ina zaku?
Imran yace ke dai kije ki d'auko mayafinki muje
Ta b'ata rai tace No! Na fasa,sai kun dawo
Imran yace me ya faru kuma?
Idonta ya ciko da k'walla tace ba komai,ta juya zata wuce
Yai saurin shan gabanta yace haba! K'anwata me ye na fushi kuma?
Noor na ganin haka tasan saboda ita ne tace ta fasa,dan haka tace kuje,ka bari ni sai gobe maje
Yace a'ah Noor ki bari mu tafi tare
Ta girgiza kanta ta wuce
Ya bita da kallo(dukkansu yana tausayinsu,baya son ya b'ata ran d'aya daga cikinsu)
Khairat ta tafa hannunta saitin idonshi,ya juya yace na'am
Tace Yayana wai me yasa kake damun kanka akan yarinyar nan?
Yayi ajiyar zuciya yace tausayinta nake ji k'anwata
Ta tab'e baki tace tausayi,lallai tausayi,gaskiya ka rage damun kanka a kanta
Imran ranshi ya d'an soma b'aci yace kar kice mun kinbi layinsu Mum
Ta girgiza kai tace A'ah,mu tafi
Ok! Ina jiranki a mota,kiyi sauri
Tace toh Yayana,ta wuce tana rausaya""
*OHW*
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
5⃣6⃣➖6⃣0⃣
""Noor d'aki ta koma,ko kad'an bata ji haushin rashin fitar su da Imran ba,dad'i ma taji coz bata son fitar""
""A mota Imran da Khairat nata hira
Har suka kai,(SHOPRITE) anan yan gidansu ke siyan Shawarma
A tare suka shiga
Shawarma biyar ya siyan mata da Rubber ice-cream uku
Khairat tace Yayana ai tamun yawa bazan iya cinyewa ba,
Imran yace A'ah ke dai gashin nn kici kici har sai kin k'oshi,kinga yau ba sai kinci abinchin dare ba
Tayi dariya tace Yayana kenan
Har sun bar wajen shawarma sai kuma ya koma
Guda biyu yace a bashi,da Rubber ice-cream biyu
Khairat tace ai da baka siyo ba,ka bari munci wannan tare
Imran yace no! K'anwata kar ki damu""
""Shagon boutique na mata suka shiga
Khairat da bakinta baya shiru tace me kuma zamu yi anan Yayana?
Imran yayi dariya yace k'anwata kenan sarkin tambaya,ki zab'i abunda kike so
A ranta taji dad'i,nan ta shiga zab'ar riguna da wando
Imran gefen doguyan riguna yaje, yana ta zab'a ya d'auki sun kai kala goma
Khairat kuwa sai dad'i take ji Imran na siyan mata
Sashen inners ya koma
Ya zab'o pants,bras,da underskirts kowanne guda shida
Khairat kunya taji a ranta tace Yayana kenan maimaikon yace nazo na d'auka da kaina,shine yake zab'ar mun da kanshi
Nan suka gama da boutique,ya biya kud'i suka fita
Shagon Cosmetics suka shiga
Khairat ita dai biye take dashi kawai
Nan ma Imran yace ta zab'i abunda take so
Ta shiga zab'a
Shima ya kwashi turaruka,kayan shafa,brush,maclean
In tak'aice muku dai siyayya sosai Imran yayi a Shoprite,hadda atamfofi ya siyo,laces da material
Khairat dad'i kamar zai kasheta,ji take kamar ta had'iye Imran,Son shi na k'ara shigarta _Ni Zee na kalli 👀Qurratu nace dama son shi take_""
""Sun dawo gida,Imran ya kwashi kayan da ya siyo
Khairat a tunaninta kai mata zai yi
Kawai taga yayi hanyar d'akin Noor
Binshi da kallo kawai take,ta kasa furta ko A
Ba dai kayan nan Noor ya siyo ma ba,No! It can't be
Nan ta ajiye kayan hannunta,tabi bayanshi
Bakin k'ofa ta tsaya,ta lab'e""
""Noor sallamar Imran kawai taji,Ya shigo nik'i- nik'i da kaya
Ya ajiyesu gefe,ya samu wuri ya zauna
Batace masa uffan ba
Yace ba magana Noor,ko fushi kike dani,ai ke kikace mu tafi ba zaki ba
Murmushi tayi tace ko kad'an bnji haushi ba,kawai naga ka shigo da kaya ne shine na tsaya ina mamaki
Yai murmushi yace kayank ki duba kiga insun miki,in kuma basu miki,Sai ki shirya muje ki zab'i wanda ranki ke so
Ya mik'e yace bari na baki waje, kiji dad'in dubawa""
""Khairat tai saurin lab'ewa da taji alamun xai fito
Ya fito ya wuce sashensu,ba tare da ya lura da khairat ba
Khairat ta kawo wuya,zuciyarta har wani zafi-zafi take
Sai hawaye
A guje ta nufi sashen Hajiya _ko ta kayanta bata bi ba_
_D'akinsu d'aya da Ihsan_
Ta shiga d'akin tana kuka
Ihsan tace lafiya khairat me aka miki?
Nan ta fad'awa ihsan duk yadda aka yi
Ihsan tace Dnt tell me,kina nufin siyayya ya mata
Khairat na kuka tace sosai ma kuwa sai ma kinga kayan
Ihsan ta rik'e baki tace lallai abun Ya Imran yayi yawa,amma ke yanzu me ye na kuka,kinsan dai kinfi k'arfin kayan da ya bata,zaki iya siyan ma kanki wanda suka ninka su
Khairat tace kinsan irin son da nake wa Ya Imran,duk da shi baisan ina yi ba,bana son kowacce mace kusa dashi in dai ba muharramarshi ba
Ihsan ta tuntsire da dariya tace lallai khairat,toh ai itama Noor muharramarshi ce ko kin manta matar Daddy ce
Khairat tace Ya salam! Wlh mantawa nake,kar kiso kiji yadda zuciyata ke zafi,Tai ajiyar zuciya ta cigaba da cewa Wai! har na samu relief,but duk da hka bana son yarinyar
Ihsan tace kisa ranki a ruwan sanyi,ba fah aure tsakaninsu ko da kuwa Daddy ya saketa,ina mai tabbatar miki Ya Imran baya sonta,tausayinta yake,Taya ma zai fara son Matar Babanshi,kema kiyi tunani abu ne da bazai tab'a yiwuwa ba
Khairat tayi murmushi tare da jin wani sanyi a ranta
Kayan da ta bari waje,sai mai gadi ne ya shigo mata dasu""
""Noor bud'e kayan kawai take,ta saki baki tana kallo
Wacce irin Zuciyar imani ce da Imran,a gsky samun irinshi sai an tona
Wannan kaya kamar lefe
Bata san taya zata fara mishi godiya ba
Ledar shawarma da ice-cream ta bud'e
Tasan ice-cream amma bata san shawarma ba,ta d'auko tana jujjuya tana cewa me ye wannan kuma?
Ta d'an gutsira taji bala'in dad'i
Tas ta cinye shawarma,dan dama bala'in yunwa take ji(tun dawowar Hajiya ta hana a rik'a zuba mata abinchi,sai dai tasha tea ko maltina,idan Imran ya tambayeta taci abinchi? Eh take ce masa)""
""Bayan sallar isha'i,Tayi wanke-wanke ta gyara kitchen
Sannan ta dawo,ta kwanta sai barci
Imran bai k'ara shigowa d'akin ba""
""Tunda asuba Hajiya ta tasheta da ruwan sanyi
Tai saurin mik'ewa,tana rawar sanyi
Hajiya rik'e da k'ugu tace Inyee! Kilewa Uban wa ya baki bargo
Murya na rawa tace Imran
Ina so ki wanke shi ki kawo mun
Noor ta gyad'a kanta tace toh
Hajiya ta cigaba da masifa ""Naga kwana biyu kin manta aikin ki na sharar tsakar gida da wanke motoci,Toh wlh daga yau kar ki bari in k'ara tuna miki
Ta fice tana kumfar baki""
""Noor murmushi kawai tayi,inda sabo ta saba
Toilet ta shiga tayi brush,tayi alwala
Tayi Sallah""
""Sharar tsakar gida ta fara,ko da ta gama ta masifar gaji ta hau wankin motoci
Imran yayi shirin shi tsaf( ya masifar yi kyau😍)zashi office
Daga nesa ya hangota,tana wanke mota duk ta had'a gumi
Kamar an watsa mai ruwan zafi haka yaji zafin ganinta
A fusace ya k'arasa inda take
Tsayawa tayi tana kallonshi sbd kyan da yayi
Wa ya saki wannan aiki?
Murya a sanyaye tace Hajiya
A fusace yace wuce ki tafi d'aki
Da ka bari na......
Ya katseta kar kice komai wuce kawai
Jiki a sanyaye ta wuce""
""Yana huci ya shiga falon Hajiya
Haba! Haba! Hajiya ya za'a sa Noor wankin mota
Hajiya ta ajiye kofin tea dake hannunta tace na sata zo ka dukeni
Imran yace is not proper wlh
Hajiya tace Imran! Imran! Imran! Sau nawa na kira sunanka sau uku koh
Wlh kaji na rantse idan baka daina tuhumata akan aikin da nake sa Noor ba,zaka fuskanci mummunan b'acin rai,aiki yanzu na fara sata,Ko Ubanka da ya aurota bai isa ya hana ni,yi mata abunda naga dama ba balle kai,kuma wlh idan bata wanke motocin nan ba,kasheta ne kawai ba.........
Bai jira ta k'arasa ba,ya fita a fusace,ya buga k'ofar falon kamar zata b'alle
Zuciyarshi sai tafarfasa take kamar zata fashe
Hajiya tace ku ganmu da yara,taja dogon tsaki
Ta cigaba da shan tea'n ta hankali kwance""
""Kayanshi ya cire,daga shi sai three-quarter da singlet
Ya nufi wajen motoci yana wankewa duk ya had'a gumi
( _yafi so ya wanke akan ita ta wanke_)
A ranshi yace gaskiya Mum bata da tausayi,yanzu hk Noor ke shan wahalar wankesu,daga yau nayi alk'awarin in dai ina numfashi a doran k'asa ba zata sake wankewa ba..................
*OHW*
0 comments:
Post a Comment