Noor d'aki ta shiga tayi jigum tana tunani ta rasa me ke mata dad'i duniya
Imran yace kar ta wanke motoci tasan kuma idan bata wanke ba,wata matsalar ce
Nasan yanxu ya fita,bari naje na cigaba da wankewa shine rufin asirina ta fad'a a ranta"
"Hango Imran da tayi yana ta faman wanke mota shi ya matuk'ar bata mamaki she couldn't believe it,at the same time ya bata tausayi ganin yadda ya had'a zufa daga gani bai saba ba,Da sauri ta k'arasa inda yake
Kanta a sunkuye k'asa murya sanyaye tace Me yasa kake wahalar da kanka Imran?me yasa zaka hana ni kai kuma kayi? Baka saba da wahala ba,ka bari ni da na saba nayi
Da sauri ya juyo yana kallonta yaga yadda ta marairaice idonta sun kawo k'walla yace kar in kuskura inga hawayen nan maza mayar dasu,me ma ya fito dake,ba cewa nayi ki tafi ba
Dan Allah ka bari na cigaba da wankewa, ta fad'a a shagwab'e
Ya d'an yi ajiyar zuciya yace kina tsoro ne kar Hajiya ta gane bake kika wanke ba,toh be rest assure bazata sani ba,mai gadi da masu aiki duk nayi warning dinsu not to tell her,dan haka kije ki kwanta nasan bacci bai isheki ba
Ta girgiza kanta tace A'ah ni bashi ba,kai nake tausayi baka saba ba
Ya tuntsire da dariya yace Noor kenan wato ni kike jin tausayi
Ta gyad'a kanta
Yace come on kar kiji tausayina,am a strong Man zan iya jure duk wata wahala saboda ke,don't forget alk'awari nayi xan kula dake,na kare ki,wanke motoci ai ba wani wahala bane a wajen maza,so kar ki damu kanki ,just go and rest
Tsayawa tayi bata motsa daga inda take ba,kanta sunkuye k'asa,bata sake furta ko A ba,Tayi shiru tana jin wani abu na yawo a jinin jikinta game da Imran wanda bata san me ye ba?
Imran wannan karon idonshi k'yam a kanta,duk da baya son kallonta,ya kasa d'auke idonshi a kanta,yana mamaki yadda duk ta damu dan yana wanke mota
Yana jin wani abu na mai yawo a jinin jiki wanda shima bai san me ye ba?
A hankali ya kira sunanta Noor!
Ba tare da ta d'ago ba, ta amsa Na'am
Kar ki damu kanki,ki tafi kawai
Ba musu ta juya,jiki a sanyaye ta tafi,
Ya bita da kallo,yana jin wannan abun nabin duk ilahirin jikinshi"
"D'aki ta zauna tayi shiru,tana tunanin wane irin tausayi ne Imran ke mata haka?,duk yadda baba mai gadi da Lami ke tausayinta basu kai Imran ba,irin yadda take jin Imran a ranta daban da yadda take jinsu,SHI tana so a ko da yaushe ta rik'a ganinshi,tana jin muryarshi komai nashi burgeta yake,yana da wani matsayi babba a zuciyarta wanda duk duniya babu mai shi,ta rasa dalili ko kuma tsabar tausayinta da yake yi yasa haka
Zuciyarta tace tabbas shine,dama zuciya nason mai kyautata mata,ko shakka babu kyautatawar da Imran ke miki, yasa kike jin haka game dashi
Tayi wata sanyayyar ajiyar zuciya tace Allah ya saka maka da alkhairi Imran,(Ameen)"
"Imran ko da ya gama,ya masifar gaji ya galabaita,yace ashe haka Noor ke ji(ni da nake namiji naji haka,ina ga Noor da take mace yarinya,yaji wani tausayinta ya kama shi)
Sharp sharp ya sake having shower,ya shirya ya nufi office
Yayi late sosai ko da ya isa office d'insu goma saura
Kowa yayi mamakin lattin da yayi,an san shi da xuwa da wuri,sun sama ransu duk abunda yasa shi xuwa late ba k'aramin abu bane,shi kuwa ko a jikinshi,ko da zai rasa aikinshi idan akan Noor ne bazai damu ba
A office ya kasa komai tunanin Noor kawai yake,wane hali take yanxu ko suna can suna azabtar da ita"
"Cornflakes ta had'a kakkaura tasha,tayi wanka ta saka d'aya daga cikin rigunan da Imran ya siyo mata,Rigar ta mata kyau sosai charas charas da ita,ta kalli kanta a madubi,taga kamar ba ita ba sbd kyan da tayi(a ranta tace lallai komai nasan gyara, bata tab'a kyau irin na yau ba)
"Kiran mun tsinanniyar can,wato ta gama wankin motoci ba zata xo ta gyara sashen nn ba,naga kwana biyu iskanci take ji xanci ubanta ne hajiya ke cewa Abu mai'aiki
Abu ta tab'e baki tace hmm hajiya ai da bakya nan ko fitowa bata yi,sai dai a girka mata abinchi akai mata har d'aki,ta nad'e k'afa taci,Imran ya d'aure mata gindi
Hajiya ta rik'e baki tace iyyeh samun wuri,kira mun ita da sauri"
"Sai da ta k'are mata kallo sama da k'asa tace iyye anyi kilin samun wuri, hadda su kaza acin dank'o mutum bazai tsaya inda Allah ya ajiyeshi ba
Noor ranta taji ya masifar b'aci a fusace tace kee Abu ki kiyayeni,kar ki manta matsayin matar Alhaji nake a gidan nan,banda k'addara ke baki isa kina gayamun magana son ranki ba,ki cigaba da zama gidan nan,kar hak'urina ya baki damar da zaki cimun fuska,zan d'auki cin mutuncin hajiya da ya'yanta dan ni na kawo kaina gidansu amma bazan d'auki na masu aiki ba
Abu da mamaki take kallon Noor anya ita ce ke fad'ar magana haka
Tasha jinin jikinta,ni dai hajiya na kiranki ta juya ta fita
Ita kanta Noor mamakin kanta ta tsaya tana yi, yadda ta iya yin masifa (duk da a sanyaye ta fad'i maganar,daga ji bata saba fad'a ba)"
"D'an kwalin rigar ta yafa a kanta ta fita
Gaba d'ayansu suna zaune falo Imran ne kawai baya nan
Yazeed ido ya zuba mata yana so ya tantance itace ko ba itace ba
Tazo gaban hajiya ta durk'usa tace Gani hajiya
Tashi! tashi tsaye in ganki
Jiki a sanyaye ta mik'e
Hajiya ta kalleta sama da k'asa tace wa ya baki rigar nn?
Murya na rawa tace Im..im..ran
Hajiya tace madallah! Ya kyauta da ya baki, dan ni kaina na gaji da ganinki cikin tsumman kayanki, ba mutunchi da k'imar gidan nan bane ace ana shigowa ana ganin mutane da yagaggun kaya,
Ihsan tace gaskiya kam,dan bamu gaji tsiya ba
Iman da khairat suka tab'e baki sukace wallahi dan abun kunya ne mutane suzo,su ganta a haka sai a raina mu
Yazeed hankalinshi na kan Noor ya saki baki da hanci yana kallonta yana lasar baki,a ranshi yace lallai Allah yayi halitta anan
Noor tana d'aga kai suka had'a ido
Ya sakar mata wani murmushi,wanda ta kasa gane na me ye? Tasan tunda suke dashi bai tab'a mata murmushi ba,duk suka had'a ido murtuke fuska yake ,ya bita da matsayacin kallo buh yau shine da mata murmushi(me hakan ke nufi)
Kawai tai saurin kawar da kanta gefe
Hajiya tace ba tsaya mun zaki yi kai ba kamar yan sanda, wucewa zaki yi ki shiga ki fara gyara d'akuna
Yazeed yai saurin cewa Ummm....mum pls ina so tamun wani aiki a sashenmu
Toh taje ta maka,kina gamawa kizo ki gyara sashen nan
Ta gyad'a kanta sama
Yazeed ya tashi,tabi bayanshi,Gabanta na dukan uku uku _ohh shiyasa ya mun murmushi yasan muguntar da ya k'ulla zai mun Allah ya mun tsari da kai(ta fad'a a ranta)_...........
*OHW*
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
?
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.W.F*
6⃣2⃣
*This page goes to yhu Mss Aysher,tnx for everything❤❤i soo much love & cherish yhu dear💋💋💋 Allah ya barmu tare💞*
""Noor na biye da Yazeed hr sashensu gabanta nata dukan uku-uku
Suna shiga falo,yaja k'ofa ya rufe,Ya juya yana kallonta,kallo tun daga sama har k'asa yana murmushi tare da lumshe ido da lasar baki
Noor kasa yarda tayi da irin kallon da yazeed ke mata,me yazeed ke nufi da irin kallo nan,tabbas haka Alhaji ya rik'a mata irin kallon nn daren da aka kawota,ba dai hkn na nufin abnda Alhaji yaso yi da ita shi yazeed ke son yi,Tai saurin cewa a ranta Noo it can't be
Muryar Yazeed ce ta katse mata tunani Noor! Ya kira sunanta da wata irin siga wacce bai saba kiranta ba,
Bata amsa shi ba,Ya cigaba da cewa kayan nn sun miki kyau sosai,ashe haka kike da kyawon halitta,so sexy
Tayi kamar bata ji me yace ba, tace fad'a mn aikin da zan maka hajiya na jirana,
Ya d'an yi shiru kamar bai jita ba, idonshi k'yam a kanta,ya nisa yace ki shiga ki gyara d'akina,zan fita ki tabbatar kin gyara kafin na dawo
Jin fita zai yi,yasa ta jin natsuwa ta amsa da toh,ta nufi hanyar d'akinshi
Ya bita da kallo tare da yin wani matsiyacin murmushi"
"D'akin Imran ya shiga yayi having shower,ya fito daga shi sai gajeren wando,Ya nufi d'akinsa
Noor nata faman gyaran gado
Kawai taji an rik'ota ta baya,A tsorace ta juyo,charaf idonsu ya had'u da na Yazeed,idonsa duk sun chnza yana wani lumshe su kmr d'an giya,Da sauri ta fisge kanta ta tunkud'a shi gefe tayi hanyar fita da gudu,Ya fisgota da k'arfi ta fad'o kan gado
Noor plss ki taimaka mn,i am in desperate need of you,zan iya shiga wani hali idan baki bani had'in kai ba
Noor innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta furta wannan wacce irin bak'ar rana ce take gani,Cike da tashin hankali,hawaye na bin kuncinta tace Yazeed kasan me kake shirin aikatawa kuwa,ni fah matar babanka ce,ko ni ba matar babanka bace babban zunubi kake shirin aikatawa ballatana ina matsayin matar babanka, kaji tsoron Allah Yazeed ta sake fashewa da matsanancin kuka
A hankali ya shafa fuskarta tai saurin bige hannunshi ta mik'e tsaye
Haba Noor ki tausaya mun mana,ni ba ruwana da natsayinki na matar babana,kawai ni dai ki biya mn buk'atata ni kuma na miki alk'awari zan baki duk wata kulawa,bazan k'ara bari su mum su cutar dake ba
Da k'arfi tace Noo Yazeed bazan iya ba tana girgiza kanta,kasan bala'i da masifar dake cikin zina kuwa balle zina da matar babanka
Gwiyoyinshi ya kai k'asa,kamar zai yi kuka yace Dan Allah Dan Annabi Noor ki taimaka mn ki tausaya mun,Wallahi zan shiga wani hali idan baki bani had'in kai ba
A fusace tace ko mutuwa zakayi sai dai ka mutu Yazeed
Tayi hanyar fita,ya fisgota da k'arfi ya jefata kan gado Dan kinga ina rok'onki toh zan miki ta k'arfin tsiya
Dan Allah Yazeed kayi hak'uri kar kamun komai ni fah matar babanka ce
Idan baki daina cewa ke matar babana bace zan fasa bakin ki wlh
Tana kuka,tana k'okarin k'wace kanta,shikuma yana k'okarin had'a bakinshi da nata,Aka turo k'ofar d'akin
Imran tsaye yayi yana kallonsu(bai gane noor bace dan bai ga fuskarta ba,ya d'auka matan banza da ya saba kawowa ne)jikinshi yayi sanyi a ranshi yace Yazeed bazai bar halin nn nashi na kawo mata ba koh
Yayi tsaki ya juya zai fita
Yaji muryar Noor nacewa plxxx yazeed ka k'yaleni kaji tsoron Allah
Muryar wa nake ji kamar ta Noor,ya d'an tsaya,ya sake ji tace plxx Yazeed ka k'yaleni kaji tsoron Allah
Ko shakka babu wannan muryar Noor ce
A fusace da zafin nama
Ya fisgo Yazeed ya jefar dashi k'asa,bai k'ara shiga tashin hankali ba sai da yaga Noor kwance kan gado,tana ta kuka
A fusace,fuskarshi ta kad'a tayi jawur saboda b'acin rai ,ya jawo Yazeed tsaye ya fara falla mai mari, ya mishi mari yafi goma ya fara naushin shi👊🏻👊🏻,yana ball dashi
Yazeed na cewa Dan Allah Yaya kayi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne
Imran ko kad'an bai saurareshi ba ya cigaba da dukanshi ko ta ina,Yana cewa yanzu iskancinka har ya kai ga Noor matar babanka
Yaya Dan Allah......kafin ya k'arasa ya kai mai wani wawan naushi a baki,bakinshi sai jini,Noor duk ta gama tsorata da irin dukan da Imran ke mishi,
Noor na kuka tace Dan Allah Imran ka k'yaleshi
Yau sai na kashe shi,sai na illata shi,iskanshi har ya kai ga KE,idan zai lalata ya'yan wasu toh banda KE
Noor ta mik'e ta fita a guje sai sashen hajiya
Hajiya! Hajiya! Kizo Imran na dukan Yaxeed zai kashe shi
A firgice hajiya ta mik'e ,tabi bayan Noor da gudu,suma su ihsan suka bita"
"Ko da suka je, Yazeed na kwance cikin jini baya numfashi,Imran na zaune kan kujerar falon yana huci,yana maida numfashi da k'yar,
Gaba d'ayansu hankalinsu yayi mummunan tashi,Noor kad'ai ce ke furta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Su ihsan ihu kawai suke da kuka
Hajiya tayi kan Imran,tana marinshi tana dukanshi ta ko'ina,ka kashe dan'uwanka ka huta,me ya maka ka kashe shi,Imran anya kai d'a na ne kuwa? taya zaka kashe k'aninka jininka uwa d'aya uba d'aya,kana cikin hankalinka kuwa,ka kalli abunda ka mishi har ka kashe shi,Imran kai ba d'ana bane wallahi,d'an da na haifa bazai kashe d'an uwansa ba
Imran janye hajiya yayi daga jikinsa ya fita ya bar d'akin,
Hajiya ta bishi da kallo tace ko shakka babu,kai ba jinina bane Imran,biri yayi kama da mutum"
"Ko kad'an Imran baya nadamar abnda yama Yazeed,ko da Yazeed zai mutu shima a kashe shi bazai yi nadama ba,Dan gwara yazeed ya mutu akn ya aikata mummunan aikin da yayi niyya akan Noor,bazai tab'a iya bari wani ya cutar da Noor ba ko ya kusanceta,a yadda yake ji yanzu ko Alhaji da yake da hak'k'i a kanta yaga zai kwanta da ita,sai yayi yunk'urin hana shi(Nikm Zee nace Dank'ari mak'ari babbar magana wai d'an sanda yaga gawar soja)
.....................................
*Zee Yabour*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵?
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗?
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.W.F*
6⃣3⃣
"Khairat tai k'arfin halin cewa ba kuka ya kamata mu cigaba da yi ba,we should find a way out,a kira likita yazo ya dubashi maybe Suma ce yayi
Hajiya tace wane suma,kina ganinshi cikin jini,ya riga ya kashe mun shi,Imran baka kyauta mun ba,laifin me ya maka ka kashe shi? ta sake fashewa da matsanancin kuka"
"Batare da khairat ta sake cewa komai ba,ta fita taje sashen hajiya ta d'auki waya ta kira family doctor
In few minutes time yazo,khairat taja shi xuwa sashen su Imran,Dr.Moha(DANGIN MAHAIFINA) shi kanshi ya tsorata da ganin halin da Yazeed yake ciki
Ya d'an dafe kanshi yace Ya salam! Wa ya mishi wannan aikin ko yan fashi ne suka shigo gidan naku?
Hajiya na sharar hawaye tace Imran
Subhanallahi! Garin yaya Imran ya mishi haka,yana cikin hankalinshi kuwa ko ya fara shaye-shaye anyway ba lokacin tambaya bane,yanzu muyi k'ok'arin ceto ranshi,bari na kira a kawo ambulance a tafi dashi asibiti dan bazan iya treating d'inshi nan ba"
"Ba b'ata lokaci,Ambulance tazo tare da wasu nurses,aka d'aukeshi,Hajiya,khairat,ihsan da iman suka shiga wata mota direba yaja su,Noor taso xuwa Hajiya tace bazata ba,waya sani ma ko itace silar dukan da Imran yama Yazeed,kuma ta sani idan ta gano itace sila toh wlh ta kuka da kanta,Furucin Hajiya ba k'aramin tada hankalin Noor yayi ba amma sai tayi tunanin Yazeed ko ya farfad'o bazai fad'a ba dan yasan bashi da gaskiya,Imran ma tasan bazai fad'a ba dan abun kunya ne"
"Jiki a sanyaye,tana sharar k'walla,Fuskarta tayi jajir tsabar kuka abunka da farin mutum
Ta koma sashen su Imran
Ta murd'a k'ofar d'akinshi taji a rufe
Tayi knocking taji shiru,Murya sanyaye can k'asan mak'oshi tace Imran dan Allah ka bud'e
Noor ki tafi kawai bana son magana da kowa
Dan Allah Imran ka bud'e ta fad'a cikin muryar kuka
Jin muryarta kamar ta mai kuka yasa ya taso ya bud'e,ya koma ya zauna
Ta shigo d'akin,ta zauna nesa dashi kanta sunkuye k'asa tace Imran me yasa zaka yi haka?
Yai saurin dakatar da ita da hannu Tsaya idan maganar da kika zo yimun kenan tashi ki fita
Ta marairaice murya tace Haba! Imran kai da na sanka da hak'uri,tausayi da sanyin hali but kana so kayi proving d'ina wrong
Yai shiru bai ce mata komai ba
Ta cigaba da cewa Imran,nasan abunda Yazeed yayi bai kyauta ba,he deserve to be punish but ka d'auki hukunci mai tsanani a kanshi,yanzu bamu da tabbacin ko zai rayu ko bazai rayu ba,idan ya rasa ranshi kai za'a ce ka kashe d'an uwanka,wanda hakan zai sa kai ta nadama har k'arshen rayuwarka
A fusace yace ko kad'an bazan yi nadama ba,nafi so ya mutu akan inga abunda yayi niyyar aikata miki
Kar kace haka Imran ,ka sassauta zuciyarka Dan Allah,Allah na son masu had'iye fushin su,kuma kar ka manta hadisin Manzo SAW da yake cewa La tagdab ma'ana kada kuyi fushi,Yazeed d'an uwanka ne jininka,hannunka baya rub'ewa ka cire ka yar,nasiha ya kamata ka mishi ka lurar dashi,ba ka mai mummunan rauni ba har ka kusa kashe shi,dukanshi da kayi bashi zaisa ya shiryu ba,watak'ila da ka zaunar dashi ka mishi nasiha yafi saurare,Duk kafircin fir'auna,Allah cewa Annabi Musa(AS) yayi: Yayi amfani da harshe mai sanyi wajen yi masa wa'azi,kaga kenan duka ko zagi bashi zai sa mutum ya shiryu ba,tattausan lafazi nasa zuciyar mutum ta karaya yayi nadamar abunda yayi
Gaba d'aya jikin Imran yayi sanyi,duk wata zuciya da yake ji ta tafi,yaji ya k'ara son Noor matsayinta ya k'aru a zuciyarshi,Yayi nadamar dukan da yama Yazeed ba don komai ba,sai dan nasihar da Noor ta mishi,Amma bai daina jin haushin Yazeed ba( _idan ya tuna yadda ya ganshi akan noor_)
A hankali ya furta nagode da shawararki Noor,Allah ya saka miki da alkhairi
Tayi murmushi tace Ameen,ba komai yanxu sai ka shirya kaje asibiti
Ya girgiza kai yace No i can't do that
Dan Allah Imran kaje
Naji zanje
And please one last favour
Am listening
Dan Allah kar ka gayawa su Hajiya abunda Yazeed yayi
Da mamaki yake kallonta yace Why? Dole su sani,Hajiya ta daina ganin laifina akan hukuncin dana d'auka a kanshi,idan kuma suka sani zai ji kunya,yayi nadamar abunda ya aikata
Noor tayi murmushin tak'aici tace ba'a san musulmi da tona ma d'an uwanshi musulmi asiri ba da yad'a laifinsa,ballatana Yazeed jininka ne idan ka rufa mai asiri kamar ka rufa ma kanka asiri ne,sannan idan ka rufa ma wani asiri kai ma Allah zai rufa ma,bai kamata ka fad'a musu ba,Ka mishi nasiha ka lurar dashi a matsayinka na babba
Imran shiru kawai yayi yana kallon Noor gaba d'aya ta tafi da imaninshi ya kasa furta ko A,a ranshi yace ban tab'a sanin Noor na da kaifin tunani,ilimi da hankali sai yau,a gaskiya duk mijin da ya sameki a matsayin matar aure ya godewa Allah,Daddy bai dace dake ba,had'aki da Daddy da akayi an cuceki,banda aure ya haramta tsakanina dake da na aureki,na dad'e ina neman mace mai irin halayyarki gashi Allah ya had'ani dake sai dai Kash aure ya haramta tsakaninmu
Ya kawar da kanshi gefe cike da takaici
Noor tace baka ce komai ba,kamun alk'awari baza ka fad'a ba,zaka barshi sirri tsakananin ni kai Yazeed da Allah
Kai kawai ya gyad'a mata ba tare da ya juyo ya kalleta ba
Cike da murna tace nagode nagode
Ta juya ta fita"
...................................
*Zee Yabour*😘
?
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.W.F*
6⃣4⃣
A asibiti likitoci sun ba Yazeed taimakon gaggawa,nan da aka shiga dashi emergency
Hajiya dasu Ihsan sai faman zirga-zirga suke a passage d'in asibitin suna kuka
Alhaji na can wajen buga caca, Iman ta kira shi ta gaya mai halin da ake ciki,ba shiri ya taso yazo asibitin,bai samu ganin Yazeed ba,amma sai jinjina al'amarin yake,me yama Imran ya mishi dukan da ya kusa kashe shi duk irin shak'uwar su da son juna
Yayi ta kiran Imran yak'i picking,kashe wayar ma yayi gaba d'aya,Alhaji ya tsaya kawai yana cizon yatsa
Dr.Moha ne ya fito yana zufa,Dukansu sukayi kanshi Hajiya tace"Ya dai doctor "
Dr.Moha ya goge zufan da ya k'eto masa yace "mun samu nasarar ceto rayuwarshi,amma har yanzu bai farfad'o ba sai nan da wasu awanni,sannan yana buk'atar jini da za'a mishi k'ari dan ya zubar da jini da yawa"
Hajiya tai saurin cewa"muje a gwada nawa"
"Abunda yafi kyau kuzo muje ku dukanku a gwada,wanda yayi dai-dai da nashi sai a d'iba"
Dukkansu an gwada jininsu bai yi ba, Hajiya cike da damuwa tace "to yanzu ya za'ayi?"
Kafin Dr ya bada amsa,Ihsan tace "Mum kin manta blood group d'insu d'aya da Ya Imran"
Alhaji ne yace"tabbas hakane dan haka yi maza kuje ke da driver azo dashi"
Tayi nodding kanta,ta juya tayi hanyar fita
Tun fitar Noor,Imran na nan inda yake bai motsa ba,tunaninta kawai yake da maganganunta,yana jin wasu feelings game da ita wanda ya kasa gane na meye?
A rud'e Ihsan ta shigo d'akin babu ko sallama
"Yaya Dan Allah ka taso muje asibiti,a d'ibi jininka a sawa Ya yazeed,jinin kowa ba zaiyi ba sai naka"
Banza yayi da ita kamar bai ji ta ba
Ta sake maimaitawa ya mata banza,sau uku tana fad'a yana mata banza
Ta fashe da kuka "haba! Yaya kana ji na fah kayi shiru,kowane laifi Ya yazeed ya maka,ya kamata kaji tausayinshi yana can asibiti unconcious"
A fusace yace"ba kowane laifi ba,laifin da yamun yafi k'arfin in yafe masa,zan iya yafe kowane laifi a duniya banda wannan,dan haka kije kice bazan bayar ba"
Zata sake magana ya daka mata tsawa "I said get out" _Yana jin tausayin Yazeed,amma zafin abunda yayi niyyar yima Noor bazai barshi ya gane tausayinsa da yake ba_
Jiki na rawa ta fita tana hawaye,Taci karo da Noor ( _zata duba ta gani ya tafi asibitin ko yana nan_)
Cike da damuwa tace "Ihsan me aka miki? Ya jikin Yazeed?"
Ihsan ta galla mata harara tace "ban sani ba"
"Please ki gaya mun Ihsan"
"Idan baki kauce mun a hanya ba,zanyi k'asa k'asa dake wlh"
Ta d'an matsa,ta wuce ta bar Noor sake da baki
Falo taga mai wanki ya kawo kayansu Imran
"Idi Dan Allah ko kasan me Ihsan ke ma kuka"
"Imran ne yace bazai bada jininshi a sawa Yazee....."
Bata jira ya k'arasa magana ba,ta shiga d'akin Imran
"Haba! Imran banyi tunanin haka daga gareka ba,ina tausayinka da imaninka suke? ko kasan idan ka ceci rai d'aya kamar ka ceci duka al'umma ne,haka idan ka kashe rai d'aya kamar ka kashe duka al'umma ne,D'an uwanka nacan kwance asibiti amma ba zaka iya taimakonshi ba,
Cike da mamaki kawai yake kallon Noor a fusace yace "wacce irin zuciya ce dake Noor? Ke kika fi kowa tausayine a duniya? Duk abun nan da Yazeed ya miki but still kike tausayinsa,tun azabtar dake da yake har xuwa abunda ya miki yau"
"Imran kenan Allah muke masa laifi ya yafe mana ballatana d'an adam,Ni wallahi na yafe ma Yazeed duniya da lahira"
Imran a fusace yace "lallai Noor baki san ciwon kanki ba,bakya kishin kanki,ayi k'okarin miki fyad'e kuma ki yafe"
Murmushin takaici tayi tace mutum yayi zina,yasha giya Allah ya yafe masa ballatana ni da k'okarin yimun yayi baimun ba mezai hana na yafe masa,dan haka Dan Allah Dan Annabi kaje ka bayar"
"No i can't Noor idan ke kin yafe masa,i can't forgive him"
Cike da mamaki take kallonsa tace "akan me bazaka yafe masa ba,ni yama laifin nan kuma na yafe masa,why not kaima bazaka hak'ura ba"
Bai ce mata komai ba,a ranshi yace "ba zaki gane bane Noor,bakisan ya nake ji game dake ba,ni kaina na kasa ganewa,zuciyata zafi take tana tafarfasa idan na tuna yadda naga Yazeed kan ki"( _Ni Zee nace Imran ko dai kishi ne,taya zaka fara kishinta bayan ba so tsakaninku,Anya Imran baka fara sonta ba🤔,idan kuwa ka kuskura ka fara sonta zaka jefa kanka a rud'ani_)
Kneeling tayi gabanshi,ta fashe da kuka "Dan Allah Imran kaje ka bayar"
Har cikin ranshi yake jin kukanta,idan yana son mutuwarshi yana son kukanta
Da sauri yace "tashi tashi Noor ki daina kuka,zanje"
"kayi alk'awari"
"Eh na miki alk'awari"
"Nagode"
"Ki daina mun godiya ba abunda bazan iya yi akan ki ba"
_Ita kanta Noor tana mamakin yadda yake jin maganarta kuma baya son kukanta ko kad'an_
Ihsan ta koma asibiti sharb'e sharb'e da hawayenm,Hajiya ke tambayarta "Ina Imran d'in?"
"Yace bazai zo ba,ba zai bayar da jininshi ba"
Alhaji yace "haka Imran d'in yace?"
"Eh"
Hajiya tace "lallai Imran,anya yana cikin hankalinshi kuwa,gaskiya shima ya kamata a kawo shi asibitin nan a duba shi"
Alhaji yace "ko shakka babu"
"Dr yanxu me ye abun yi?" Hajiya ta tambaya
Yayi ajiyar zuciya ya d'an yi shiru na yan mintuna,zai yi magana kenan
Iman tace "Ga Ya Imran"
Duk suka juya suna kallonshi,yana tahowa har ya k'araso
Ba wanda ya tanka cikinsu sai Dr
"Dr muje a d'ibi jinin nawa"
Hajiya tace "ai da baka zo ba, mara kunya,mara tausayi,da ka bari ya mutu"
Alhaji yace "Imran me ke damunka? me ya shiga kankam me Yazeed ya maka ka mishi wannan mummunan rauni?"
Ko uffan bai ce musu ba,sai likita da yace ma "Dr plss muje a d'iba ina da abun yi"
Hajiya a fusace tace "Ai da baka zo ba,ka tsaya ka cigaba da abunda kake,mara tausayi kawai,baka damu ma ka tambayi ya jikin d'an uwan naka ba, zaka...."
Dr.Moha ya katse ta"Hajiya kiyi hak'uri yanzu ba lokacin fad'a bane"
Ana d'ibar jininshi,ko wajensu Hajiya bai koma ba,ya tafiyarshi
Su hajiya tunani kawai suke wane laifi ne Yazeed ya mishi haka🤔
Su hajiya na zaune reception,Suna jiran lokacin da akace zasu iya ganin Yazeed yayi,dan ance bazasu iya ganinshi ba sai ya farfad'o
Ana saura 30mins,Hajiya tace su Iman suje gida su had'o kayan tea
Suna dawowa ana cewa su shiga
Hajiya tayi kanshi tana kuka,duk idan Imran yaji mishi ciwo,ansa bandage an rufe,duk ya chanza kamanni,Daga gani yana jin jiki
Dukansu suka had'a baki suka ce "Sannu Ya jiki?"
Kai kad'ai ya gyad'a musu
Alhaji bai yi tunanin raunin har ya kai haka ba,ganin irin raunukan ba k'aramin mamaki ya sake kamashi ba
Hajiya ta had'a mai kakkauran tea,da k'yar yasha
..........................................................
*Zee Yabour*😘
?
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.W.F*
6⃣5⃣
Imran daga asibiti gida ya koma,ya shiga d'aki ya rufe kanshi,yana ta tunani duk akan Noor,Tambayar da yake ma kanshi "me yasa nake jin haushin Yazeed sosai haka akn abunda yama Noor,me yasa zuciyata ke zafi idan na tuna yadda na ganshi a kanta why? why?"🤔
Ko tausayinta da nake yi ne? "NO wannan ba tausayi bane da tausayi ne da ba haka zanji ba,Toh menene?" _Readers ko zaku gayawa Imran me nene?_
Ta b'angaren Noor,Addu' take Allah yasa Yazeed ya samu sauk'i,haka Imran na fad'o mata a rai akai-akai,duk sanda ta tuna shi sai tayi murmushi,sai ta rik'a ji tana son ganinshi
Tambayar da take ma kanta itace "me yasa Imran ya damu kanshi sosai haka,ya d'auki zafi da yawa akn abnda Yazeed ya mata"🤔
Da daddare aka sallami Yazeed,Dr yace "zasu iya tafiya gida,ba wani matsala,ciwonkan da yaji ne kawai kuma sannu a hankli zasu warke"
Su Hajiya sun ma Dr godiya sosai
Yazeed hankalinshi duk ya kasa kwanciya,fargaba kawai yake kar Imran ko Noor su fad'i abunda yayi
Hajiya ta lura da yanayinshi dan haka ta tambayeshi "Me ke damunka ne Yazeed"
Ya d'an k'ak'alo murmishi yace "ba komai mum me kika gani?"
"Like something is bothering you"
"Nothing mum ba abunda ke damuna"
"Ok Allah yasa kuma Allah ya baka lafiya"
"Ameen Mum"
"Iman kira mun Imran da Noor"
"Gaban yazeed ya fad'i da sauri yace "me zasu miki?"
"Ka bari a kira su idan sunzo zaka gani"
Zai sake magana Hajiya ta dakatar dashi da hannu "Iman yi sauri ki kira su"
Zuciyar Yazeed kamar zata fito waje saboda tsoro da fargaba
Dukkansu ana cewa Hajiya na kiransu,sun san tambaya zata yi laifin da Yazeed yama Imran?
Noor ta fara shiga falon,Yazeed ya bita da kallo ji yake kamar ya tashi ya rungumeta ba abnda ya chnza game da yadda yake ji a kanta( _Ni Zee nace baka dandara ba kenan,kana so Imran ya kakkarya ka_😂),gabanshi nata fad'uwa
Da durk'usa tace "mishi ya jiki?"
Ba k'aramin mamaki yayi ba,da tmbayeshi jiki
Yayi murmushi yace "Da sauk'i"
"Allah ya k'ara sauk'i"
"Ameen"
Sai da aka d'au mintuna Imran ya shigo,Fuskar nan tashi babu annuri,Take bugun zuciyar Yazeed ya k'aru da sauri fat fat fat
Ko saitin inda Yazeed yake bai kalla ba,ya samu wuri ya zauna
Kowa ya bishi da kallo,Hajiya ta gyara murya tace "Imran ko zaka iya gaya mana dalilin dukan daka ma Yazeed"
Yazeed yai saurin interrupting yace "No mum tsakaninmu ne laifi na mai,ya hukuntani so no need ai ta tashe tashe ya wuce"
Hajiya ta galla mai wata harara tace " na tambaye,kama mun bakin ka"
Yazeed yaja bakinshi yayi shiru tare da had'iye miyau k'uttt
Ta juya kan Imran "kai nake saurare"
Imran ya d'an yi shiru na seconds sannan yace "Marin Noor yayi"
Hajiya da Alhaji suka had'a baki sukace "WHAT"
Alhaji yace "Dan ya mareta shine zaka mai dukan nan"
Imran yai shiru bai ce komai ba
Yazeed mamaki ne ya cika shi yadda Imran ya rufa mishi asiri
Noor kuwa hakan dad'i ya mata da ya rufa mai asiri( _yaji maganarta kenan_)
Hajiya ta nuna Noor da yatsa tace "Saboda wannan shegiyar ka ji mishi raunuka,har kake cewa ba zaka bashi jini ba"
Ta juya kan Alhaji tace "duk kai ka kawo mana annoba jaraba cikin gida,tunda tazo gidan nan bamu huta ba,gashi ta fara had'a ya'yanka fad'a" Alhaji yayi shiru yana muzurai ji yake kamar yace ya saki Noor,amma ba dama
"Kai koma Imran in dai akan Noor ne ka mishi haka,daga yau ba kai ba Noor,ka zab'a ko ni ko Noor"
Furucin Hajiya ba k'aramin girgiza Imran yayi ba,A kid'ime ya kalli Hajiya
Ya juya kan Noor yace "kiyi hak'uri Noor ki barni na fad'a"
Tai saurin girgiza kai tace "No Imran pls kar kace komai"
"I have to,ki barni kawai na fad'a"
Su Hajiya binsu da kallo kawai suke da mamaki
Yazeed kuwa duk ya tara gumi,ya gama tsorata
"No Imran pls don't say a word" ta fashe da kuka
Ganin kukan da take ya sa shi yin shiru
Yana jinjina ta yadda za'a raba shi da Noor _bayan ya riga ya saba da ita,ko kad'an baya son nisa da ita_
"Ka fad'a mana" cewar Hajiya
"No mum lets forget"
"Karyar iskanci kuke kai da ita,daga yau zaki fara yabawa aya zak'inta,dukan da kika sa aka mishi,wlh sai na rama shi a kanki"
Hajiya ta mik'e tayi kanta
Da sauri Yazeed ya taso ya tare hajiya yace "Please mum kiyi hak'uri kar ki mata komai"
Hajiya sake da baki ta juyo tana kallon Yazeed tana mamaki Yau yazeed ne da tarewa kar a duki Noor kuma itace silar abnda aka mishi,ba hajiya kad'ai ba dukan falon kowa yayi mamaki( _hatta Imran da Noor sunyi mamaki,dan a tunaninsu dole ya rama abnda aka mishi a kanta tunda ya tsaneta_)
"Yazeed kaine ke kare Noor"
"Mum ni dai pls kiyi hak'uri ki k'yaleta,ai ba laifinta bane tunda ba ita ta dukeni ba"
Hajiya komawa kawai tayi ta zauna kan kujera,dan ta zama speechless,jikinta duk yayi sanyi Yau Yazeed ne da kare Noor
Imran a ranshi yace "lallai Yazeed nasan kayi hakane dan ka cimma mummunar manufarka akan Noor,toh wlh ba zaka tab'a samun nasara ba, idan ina numfashi a doran k'asa"
Tsaki yayi ya mik'e ya bar falon
Noor na durk'ushe a kasa ko k'wakk'waran motsi,gaba d'aya she is confused
Yazeed kuwa ko kallonta baya son yi,dan duk sanda ya kalleta sai ya tsinci kansa a wani irin yanayi
Alhaji ko uffan bai ce ba,ya tashi sumi-sumi ya bar falon,dan yaga abun yafi k'arfinshi
.......................................
*Kuyi hak'uri naso muku typing da yawa yau,Wlh am very busy ne*
*ZEE YABOUR*😘
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.M.L*
```This page is in honour of yhu my friend Sumeeluv😘😘😘,Thanks for everything *ILYSM*😍```
6⃣6⃣
Noor jiki a sanyaye ta mik'e,ba wanda yace mata uffan ta tashi ta bar falon,Yazeed ya bita da kallon sha'awa
Hajiya har lokacin bata ce komai ba,Yazeed shima ya tashi ya bar falon,haka su Ihsan kowa ya tashi
Hajiya kad'ai ce zaune tana al'ajabi
Imran da ya bar falo,d'aki ya nufa,ya kwanta kan gado yana kallon ceiling duniya ya rasa me ke masa dad'i,Yana maganar zuci "taya za'ace a rabani da Noor,bayan bazan iya jure rashin ganinta ba,bazan iya bari ta cigaba da shiga halin k'unci,i must find a way out,but ita a yadda na lura bata damu ba,duk da taji furucin Hajiya still take goyon bayan Yazeed,Bayan duk gidan nan a wurina kad'ai take jin sanyi, but still ta gwammace a rabamu da na fad'i laifin yazeed,Noor why are yhu like diz? Bazan iya jure rashinki ba, wlh da na fita harkarki a yau d'in nan, tunda ke kika zab'i haka,amma tausayinki yama zuciyata yawa,gashi yanxu wasu feelings nake ji game dake, bansan na me ye ba,da na k'yaleki dasu Hajiya da yazeed" Ya k'arasa maganar kamar zai yi k'walla
Ta b'angaren Noor itama kwance take,hawaye na kwaranya daga idonta,Tana maganar Zuci "Ya zanyi da rayuwata an rabani da Imran,shi kad'ai nake jin sanyi a gurinshi,bani da wani masoyi da ya wuce shi,rayuwata na cikin had'ari muddin babu Imran a kusa dani,gashi ina son ganinshi a ko da yaushe,ina jin muryarsa,Hanya d'aya ce in fad'i abunda Yazeed yamun kuma bazan iya fad'a ba,Ya Allah ka kawo mun fita" Ta fashe da matsanancin kuka
Khairat,Ihsan da Iman ne zaune a d'aki suna hira
Ihsan tace "ni har yanxu i couldn't believe it Ya yazeed ya hana Mum dukan shegiyar can"
Iman tace "Nima wlhy har yanxu abun yawo yake mun a brain, yadda ya tsani yarinyar nan but shine yau da kareta"
Khairat tace "ni duk ba wannan ba mamakin dukan da Ya Imran yama Ya Yazeed nake,akan kawai ya mare ta,ki duba so da shak'uwar dake tsakaninsu amma a kanta ya mishi haka,ni na rasa gane me ya d'auki Noor d'in nan"
Ihsan tace "shegiya wlh ni ban yarda da ita ba,yanzu haka Aljana ce ko mayya,Daddy ya jajubo Mana"
Khairat tace "koma wacece zata ci ubanta dan wlh na tsaneta tunda naga Ya Imran na rawar k'afa a kanta"
Iman tace "ke fah kishin tsiya ne dake sis,ba fah aure tsakaninsu amma kin kasa kwantar da hankalinki"
"Ba zaki gane bane Sis ina masifar son Yayana at d same ina kishin shi,ko kad'an bana so naga mace ta rab'e shi"
"Son maso wani kenan,shi kinga bai san kina yi ba"
"Very soon zai sani"
Ihsan tace " yanxu ba wannan ba,ya kamata muyi planning yadda zamu ci uban yarinyar can yadda da k'afarta sai ta bar gidan nan ko Daddy bai saketa ba,dan wlhy i hate seeing her"
Nan suka yi k'asa k'asa da murya suna planning yadda zasu yi(duk yadda na kai ga kasa kunnena banji me suka ce ba😉)
Yazeed sad'af sad'af ya shige d'akinshi tsoron had'uwa yake da Imran,Mamaki kawai yake yadda Noor ta rufa mishi asiri,coz idan ba don ita ba da Imran ya tona shi,Toh me yasa zata rufa mishi asiri shine bai sani ba
Tunaninta ya hau yi,Suffar jikinta na mishi yawo a k'wak'walawa,wata irin masifar sha'awarta yake,dan masifa ga raunukan dake jikinshi amma ji yake kamar yaje ya tarar da ita a d'aki
Har aka kwana biyu ba abun da ya faru,Hajiya kwata kwata bata bi ta kan Noor,harkokinta kawai take amma ba wai hakan na nufin ta k'yaleta bane,Su ihsan ma hka dey re busy planning abunda zasu mata,
Imran kuwa duk ya sukurkuce ba damar xuwa wajen Noor ko abinchi baya iya ci sosai,bacci da k'yar yake yinshi,Noor kawai yake san sawa a ido ba dama,hajiya na nan tasa a ido, har k'ara ce mishi tayi idan yasa Noor a ido Allah yasa bata yafe mishi ba hkn ya k'ara d'aga mishi hankali,har mamakin kanshi ya rik'a yi,Me yasa zai damu kanshi sosai haka,just dan 2days bai ga Noor ba🤔,Tunaninshi yanxu bai wuce yadda zai shawo kan Hajiya
Noor ma hka take bala'in son ganin Imran ba dama, sai dai tai ta kuka,bata da aiki sai tunaninshi sauk'inta Su Hajiya basu bi ta kanta ba,But duk da haka ta rasa duniya me ke mata dad'i
Duk tsofaffin kayanta ta kwashe ta zubar,kayan da Imran ya siyan mata da wa'inda yasa aka d'inka mata su take sawa,Ba k'aramin kyau suke mata ba
Yazeed yaji sauk'i sosai,har yanzu bai bari sun had'u da Imran ba,Imran kullum idan ya dawo daga office yana d'aki ya daina magana da kowa baya walwala kullum fuskarsa a tamke,ita kanta Hajiya wannan halin nashi ya fara damunta,
Yazeed yai shirin shi tsaf zashi lectures zai biya ta sashen Hajiya ya gaisheta,Noor ta fito sanye da riga da skirt,da suka kama jikinta dai dai ita,suka mata masifar kyau
Kawai suka yi kacib'us,Gabanshi ne yayi wani irin fad'uwa,yai saurin had'iye miyau tare da cewa "Ina kwana Beauty?"
Noor tai saurin juyowar da kanta,ta rab'a ta gefenshi zata wuce,Ya jawo hannunta baya
Juyowa tayi fuska a murtuke ta mishi wani matsayacin kallo,Wani yarr yaji a jikinshi,wata masifar sha'awarta ya sake kamashi ji yake kamar ya had'a jikinshi da nata
A fusace tace "Mallam dallah sakar mun hannu" tana k'ok'arin k'wace hannunta,ya rik'e hannun gam
"Haba! Beauty listen to me Now"
Ta murgud'a baki tace "ka sakar mun hannu toh,kuma ni ba sunana beauty ba"
Tsayawa kawai yayi yana kallon yadda take murgud'a baki,duk ya bashi sha'awa kamar yayi kissing d'inta
"Zan sake ki amma sai kin mun alk'awari ba zaki tafi ba,zaki tsaya kiji me zance miki"
"Nayi"
Ya sakar mata hannu yana wani irin numfashi,yayi ajiyar Zuciya "Noor please Dan Allah Dan Annabi ki tausaya mun,wallahi baki san ya nake ji ba,wlhy ko nawa kike so zan baki,ke da bauta gidan nan har abada,zan baki duk wata kulawa i promise"
Murmushin takaici tayi tace "lallai Yazeed kana da k'arancin ilimi,matar baban naka kake son LALATA(Sadnaf) da ita,kaji tsoron Allah,Wlh ko wahalar duniya zata kasheni bazan baka had'in kai ba,na gwammace mutuwata da wannan abun da kake nema a gurina",bata jira mai zai ce ba,ta wuce abunta
Yazeed tsaye yayi kasak'e yana mamaki wai yau shine yake neman abu wajen Noor take wulak'anta shi,"toh wlh bazan hak'ura ba,i will continue trying my luck,in ma ta kama ko fyad'e ne sai na mata"
A makaranta ciwon mara ya tasowa Yazeed haik'an sai murmud'e-murmud'e yake,yasan ba abunda ya haddasa mai sai masifar sha'awar Noor,dole ya bar lecture hall,Ya nufi Grand Ibro hotel inda ya saba sharholiyarsa da yan'mata,ya kira d'aya daga cikin yan'matansa
Imran ya dawo daga office da wani azababben ciwon kai,kanshi yayi zafi rau,zazzab'i na neman rufe shi
Khairat ce me kawo mishi abinchi kullum
Ta tsara kwalliyarta cikin material mai kyau,Khairat kyakkyawace son kowa k'in wanda ya rasa,Da sallamarta rik'e da tray a hannu ta shigo d'akin,ta ajiye tray,Ta zauna kan bedside drawer, "Yayana" ta kira sunanshi, "Na'am k'anwata" "Ga abinchi na kawo ma" "Toh sannu,je ki wajen Mum ki k'arbo mun panadol"
"Subhanallah baka jin dad'i ne"
"Ehh"
Murya cike da damuwa tace "Sannu Yayana Allah ya baka lafiya"
"Ameen k'anwata"
"Bari naje na k'arbo ma maganin"
Cikin mintuna kad'an sai gata ta dawo tare da Hajiya
"Imran me ke damunka?" Hajiya ta fad'a tare da k'arasawa inda yake tana tab'a kanshi "Subhanallah ai asibiti ya kamata mu tafi" "No Mum ba sai munje asibiti ba"
Cike da damuwa tace "Saboda me Imran"
"Saboda magani na na hannunki,yanzu Mum bakya tsoron hawan jini ya kamani"
Hajiya jikinta yayi sanyi tana masifar k'aunar Imran duk abunda zai tab'a shi bata so,duk cikin ya'yanta tafi son shi "Bana fata Imran, kai d'a na ne jinina,bazan so abunda zai cutar dakai ba,Bana hana ka alak'a da Noor bane don wani abu,sai dan kar zumuncin dake tsakaninka da yan'uwanka dani kaina ya samu tangard'a,tun zuwanta gidan nan muke samun matsala da kai wanda da ba haka bane,amma tunda abun ya zama haka na yarda ka cigaba da mu'amalarka da Noor but plx don't cross ur limit,or try to stop us frm doing anytin to her"
Da saurin Imran ya mik'e yace "naji na yarda Mum,tanque soo much"
Hajiya mamaki take yadda ya d'au son duniya ya d'aura akan Noor(dole ta barshi ya cigaba da alak'a da Noor ko dan a zauna lafiya)
Khairat ta cika,haushi duk ya gama dabaibayeta " yanxu akan Noor ne Yayana ya kwanta ciwo,ji yadda yake murna dan ance ya cigaba da alak'a da ita wlh sai naci uban yarinyar nan dole ta fita sabgar Yayana" Taji hawaye na k'ok'arin gangaro mata
Hajiya ta lura da ita,dan haka tai saurin jan ta suka fita d'akin
Bata mata magana ba har sai da sukaje sashenta,har d'akin Hajiya sannan tace "Haba Khairat me ye na tada Hankali Imran naki ne ke kad'ai,ba fah aure tsakaninsu da Noor dan haka tada hankali na me,Ke Matar Imran ce,nan ba da dadewa ba zan mishi magana,In shaa Allahu wata shekara kamar yanxu kina gidan Imran,k'ila ma kin kusa haifo mun jika",Khairat tai saurin sa hannu ta rufe fuska ta fita d'akin cike da murna,Hajiya ta bita da kallo tana murmushi
Duk da haka Khairat ta riga ta d'aukarwa kanta alk'awari ba zata kyale Noor ba,hakanan hankalinta yak'i kwanciya game da Noor,masifar kishinta take.....................
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵 🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.M.L*
6⃣7⃣
Imran mik'ewa yayi cike da murna,gaba d'aya ya nemi ciwon kai ya rasa( _dama na missing d'in Noor ne_) Toilet ya shiga ya watsa ruwa,Ya sake shiga cikin kaya yan kanti marasa nauyi,Ya taje gashin shi tare da shafa ma mai(mai k'amshi da sa kai santsi)Ya feshe jikin shi da turaruka designers masu masifar k'amshi _Gaskiya ba k'arya Imran ya had'u yana cikin jerin maza ajin farko_ (Ni Zee a raina sai cewa nake wannan gayun, Imran ina zashi?).
Garden ya nufa,Ga flowers da itachen wurin nata kad'a iska mai dad'i da sanyi,kasancewar yanayi ne na damina(Ruwa)
Mai kula da garden ya kira Yace "ya kira mishi Noor".
Noor na zaune d'akinta kan dadduma,ta idar da Sallah tana lazimi,
Taji sallama,mik'ewa tayi ta lek'a,
"Wai kizo inji Imran yana garden"
Ta d'an zaro ido waje "ni kuma?"
"Eh"
A ranta tace "me zai sa Imran yace nazo?,baya tsoron Allah ya isa Hajiya ta kama shi but nasan Imran nada ilimi hknn ba zai ce nazo ba,ba tare da izinin Hajiya ba"
Tayi sanyayyar ajiyar zuciya "kaje kace mishi ina zuwa".
Cikin d'aki ta koma,ta nannad'e daddumar,hijabin jikinta ta bari bata chanza ba,Zuciyarta cike da farin ciki zata ga Imran
Yana zaune kan d'aya daga cikin kujerun iska mai dad'i na ratsa shi,yana kallon sararin samaniya
Noor cikin siririyar muryarta tace "Assalamu Alaikum"
Da saurin ya waigo yana kallonta wani kyau yaga ta k'ara mai sai dai ta rame,Ya mata murmushi tare da amsa sallamarta,
Kujerar kusa dashi ta zauna,tana kallon k'asa hknn ta tsinci kanta da jin kunyarshi
Tsawon seconds ba wanda yace Uffan
Imran yayi breaking silence d'in da cewa "Noor ya kike?"
"Lafiya lau" ta fad'a murya a sanyaye
"Ya naga kamar bakya farin cikin ganina?,ko da yake nasan ni kad'ai nayi missing d'inki,ko zamuyi shekara bamu ga juna ba,ba zaki damu ba"
Tai saurin d'agowa ta kalleshi (a ranta tace lallai ma baka san yadda na rik'a ji ba)
Suna had'a ido tai saurin sunkuyar da kai
"Kin kalleni ko k'arya nayi"
"Baka yi k'arya ba amma ka fad'i ba dai dai ba"
Ya d'an yi murmushi yace "Noor ni fah hadda rashin lafiya akan rashin ganinki na rasa dalili ko dan shak'uwar da muka yi ne🤔"
Shiru tayi "ashe bani kad'ai ke jin haka game da kai ba,ko shakka babu shak'uwar da mukayi ne"ta fad'a a ranta
"Kinyi shiru" ya fad'a tare da tsare ta da idanu
"Eh shak'uwar da mukayi ne ta jawo haka"
"In shaa Allahu ba abunda zai k'ara rabamu muna nan tare abadan da'iman"
Tayi murmushin takaici tace "dama hakan zai kasance but kash watarana dole zamu rabu daga ranar da Alhaji ya sakeni shikenan rabuwar tazo" ta k'arasa maganar kamar zata yi kuka
"Ki kwantar da hankalinki Noor,ko Alhaji ya sake ki ina tare dake,ke ko aure kika yi bazan gujeki ba,sai dai in kece kika zab'i na barki"
"Har abada bazan tab'a zab'ar haka ba,kamun abunda har in mutu bazan tab'a mantawa dashi ba"
Sosai yaji dad'in furucinta
Haka suka cigaba da hira mai dad'i da natsuwa,Yake gaya mata In shaa Allahu sai yayi iyakar k'ok'arinshi yaga ta shiga makaranta( _bata damu ta tambayeshi ya akayi Hajiya ta yarda ba,dan tasan ko shakka babu ta hak'ura_)
Sai gab da magriba suka tashi,Suna ji kamar kar su tashi,suyi ta zama da juna har k'arshen rayuwarsu( _Kowanensu naji ina ma Aure ya halatta a tsakaninsu da sun more aure_.
Wata irin sabuwar shak'uwa ce ta shiga tsakanin Imran da Noor,idan baya office toh suna garden suna hira,idan ya dawo lunch tare suke ci a garden,haka abinchin dare( _sai dai kowa a plate d'inshi_) Har d'aukarta yake su fita yawo,yayi mata siyayya
Hajiya ta sani amma bata da damar hana su,gudun kar Imran ya kwanta ciwo _but tsanar Noor na nan a ranta_
Su ihsan abun ba k'aramin haushi yake basu ba,tun ba Khairat ba,tafi kowa jin haushi( _ita da zai aura ita ya kamata suyi wannan shak'uwar ba Noor ba_)
Tasha alwashin raba su.
Da sanyin safiya Noor na kwance k'udundene cikin bargo tana sharar barci,Taji an fisge bargon da k'arfi,Tai saurin bud'e ido tana mutsittsika su
Hajiya ta gani tsaye a kanta
"Hutun ya isa haka,sai ki tashi zuwa share-share da gyaran gida"
Noor bata yi mamaki dan tasan Hajiya ba zata k'yaleta ba
"Toh"
Hajiya ta juya ta fita fuuu
Wanke fuskarta tayi,tayi brush dama tayi sallah tunda asuba ( _wani abun mamaki shine shekarar Noor goma sha shida amma har yanzu bata fara al'ada ba,ita kanta abun na damunta,buh wani lokacin sai tayi tunanin k'ila daga yanayin halittar tane_).
Sharar falo take tayi,Hajiya na zaune gefe tana shan tea da chips,Imran yai sallama ya shigo,office zashi ya shigo ya gaida Hajiya, _Ganin Noor na shara, ranshi ba k'aramin b'aci yayi ba,kawai ya basar dan bashi da yadda zai yi,yana yin magana Hajiya zata taso mishi,yana tsoron abunda zai sa a k'ara rabashi da Noor_
"Mum ina kwana?"
"Lafiya lau Son har ka shirya zuwa office ne?"
"Eh mum"
"Dama magana nake so muyi dakai,dan anjima zan tafi Zaria"
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau "
"Toh Alhamdulillah"
"Ina so ka saurareni da kyau,akan Khairat ne,a bisa dogon tunani da nayi da nazari,Kaga Khairat marainiya ce,tana buk'atar kula da kuma wanda zai rik'eta tsakani da Allah,Dan haka na yanke shawarar had'aku aure"
A kid'ime ya kallo hajiya Yace "Aure"
Noor ma kallon hajiya tayi a kid'ime
"Sosai kuwa aure ko akwai wani abu ne"
Muryarshi na rawa Yace "naga ai Khairat yarinyace bata isa aure ba, kar taga an shiga hak'k'inta"
"Ba wani yarinya sa'aninta nawa aka ma aure,zance shiga hak'k'i kuma babu shi dan Khairat na sonka,kasan mace da kunya shiyasa ta kasa fad'a ma"
Shiri yayi ya rasa abun cewa _bai tab'a jin yana son khairat da aure ba,yana dai mata son yan'uwantaka,Khairat nada qualities d'in da ake nema a wajen Matar aure but shi sonta ne ba yayi_
"Kayi shiru"
"Zanyi tunani akai"
"Ba shawara nake nema a wajenka ba,umarni nake baka,yau zanje Zaria mu tattauna da Maryam(maman khairat) dan bana so a d'au lokaci"
Kai kad'ai ya iya gyad'a mata,ji yake kamar ya kurma ihu
Jiki ba k'wari ya tashi ya bar falon
Hajiya ta k'ara da cewa "Auren ka kai da Khairat kamar anyi an gama,ko kana so ko baka so,yo me ye khairat bata dashi,kai da ya kamata kafi kowa farin ciki an had'a ka da yar'uwarka"
Noor k'irjinta taji yana masifar zafi kamar zai fito waje,hankalinta gaba d'aya ya tashi,hawaye na kwaranya daga idonta tambayar kanta take "me ye sa nake jin haka Dan ance Za'a had'a Imran da khairat Why? Why?" Fans ko zaku bata amsa😉
Da k'yar ta gama shara tayi mopping da goge goge,dan har wani dishi dishi take gani.
Ranar taci kuka kamar ranta zai fita da ta tuna furucin Hajiya,sai taji wasu sababbin hawaye,zuciyarta na zugi _ta rasa dalilin kukanta_
Imran da ya dawo lunch,yai ta knocking k'ofar d'akinta tazo suyi lunch
Tana ji tayi banza dashi _hakanan taji bata son ganinshi,a ranta tace "kaje kaci da Khairat mana ita da zaka aura"_
Da yaji shiru yayi tunanin ko bacci take,tunda yau da wuri ta tashi
Haka ya tafi ranshi bai so ba,Lunch d'in kasa ci yayi sai dai ya koma office yanaji dama bai dawo gidan ba.
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵?🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.M.L*
6⃣8⃣
*Dedicated this page to my dear supporters Husnerh(Hussy),Humairah madaki,Nana fa'ad nd Sis Rabi'ah❤ ,Nagode da kwarin gwiwar da kuke bani,Allah ya bar zumunci,I Love yhu all*
Kiran Sallar azahar da taji yasa ta mik'ewa ta shiga toilet,Kanta taji na masifar sarawa kamar zai cire,Da k'yar tayi sallah,nan ta Zauna kan dadduma tana lazimi,zuciyarta na zafi,Al Qur'ani ta d'auko tana karantawa,wani sanyi taji ya ziyarci zuciyarta
Bata ankara ba taji bacci na son awon gaba da ita,Qur'anin ta rufe tayi addu'a ,anan bacci ya d'auketa kan dadduma.
Imran a office kasa cigaba da aikin komai yayi,tunanin Noor kawai yake, Yacewa kanshi "Da tana da waya da na kirata naji lafiyarta ko nan in rage zafi" Yayi siririn tsaki da ya tuna had'ashi aure da Khairat da ake so yi"Taya zan auri wacce banso? Ina tausayawa Khairat zanso ta samu wanda zai rik'eta amana,kwata kwata ba aure a tsarina yanzu,Am just 23 ina da sauran lokaci bansan rushing d'in me Mum keyi ba,kuma ta rasa da wacce zata had'ani sai Khairat She is 19 ba sa'ar aurena bace,Ya Allah! Help me through" ya fad'a tare da dafe kanshi
Knocking yaji anayi, "Yes! Waye? Come in" "Naseer ashe kai ne?"
"Eh wlh" ya fad'a tare da zama kan kujera,Ya cigaba da cewa ina ta kiran ka baka picking"
"Really? ga wayar a kusa dani fah but banji ringing ba"
"Ina fah zaka ji ringing kana can kana aiki,Wlh ina mamakin yadda baka wasa da aikin ka,Allah kad'ai zai biyaka"
"Friend wannan karon bama aiki nake ba,na dai yi nisa a tunani"
"Tunanin me? Ko dai wata ta sace Zuciyar abokin nawa ne?"
"Baka rabuwa da tsokana,sanin kanka ne bani da lokacin wata,bama aure a tsarina yanzu,i want to further my studies,har PHD sai nayi"
"Ok then,what are you thinking of?"
Imran yai ajiyar zuciya Yace "Ina Cousin d'ita Khairat da nake baka labari wacce Dad d'inta ya rasu kwanakin baya"
"Yeah"
"Wai ita Mum ke son had'ani aure da ita nan bada dad'ewa ba"
Naseer yayi dariya Yace "Kai abokina to me ye a ciki,kai da ya kamata kayi farin ciki an had'aka da yar'uwarka and Khairat bata da wani makusa"
"My friend bazaka gane ba,bana sonta,just ina sonta as my cousin"
"Hak'uri zakayi kabi umurnin Mahaifiyarka,sai kaga bin umurninta ya zama alkhairi"
Shiru yayi,a ranshi yana tunanin yadda za'ayi ya auri Khairat
Naseer ya cigaba da bashi shawarwari da kwantar mai da hankali.
Yazeed yanzu kullum sai ya kwanta da mace,wanda da ba kullum yake yi ba,ba abunda ya haddasa mai sai masifar sha'awar Noor da yake
Yau lectures d'in 12-2pm yayi,Around 3 ya shigo gidan,Sashensu ya nufa yayi having shower,Ya saka wando three-quarter da shirt mara hannu
Yazeed ma kyakkyawan guy ne kuma had'ad'de
Ya fito sashensu yana tako d'ai d'ai bai yadda ba shi gaye,Hanyar d'akin Noor naga yayi,Ya murd'a k'ofar d'akin a rufe
Hannu kawai naga yasa a aljihu ya fiddo spare key(a raina nace lallai Yazeed kai criminal ne ko a ina ya samu spare key d'akin oho)
Noor na kwance nata bacci,Yana ganinta wata masifar sha'awarta ta sake kamashi,baisan lokacin da ya k'arasa inda take ba,a hankali ya cire hijabin jikinta (Noor wani irin nauyin bacci ne dake ?da har za'a cire miki hijabi baki ji ba🤔)
A hankali ya shiga shafata,yana shak'ar dadd'an k'amshin turarenta,Gaba d'aya hankalinshi baya jikinshi
Kamar a mafarki taji ana shafa ta da sauri ta bud'e ido,ganin Yazeed a kanta shi ya masifar firgita ta,ta mik'e tsaye tare da hankad'a shi
Jikinta na rawa ta d'auki hijabinta ta tasa
Kneeling yayi "Dan Allah Dan Allah Noor ki taimka mun wlhy ina cikin wani irin matsananci yanayi"
"Yazeed wlh tlh bazaka samu abunda kake so ba"
"Dan kinga ina rok'on ki ko,toh ta k'arfi da yaji zan miki" Yayi kanta,Da sauri ta rarumu kwalbar turare ta buga mai a goshi sau biyu,kwalbar ta fashe,Ya dafe kai jini na tsiyaya
Ta nuna shi da yatsa "Wlh wlh idan baka fita harkata ba,zan tona asirinka kowa ya sani a gidan nan,kaga daga nan girmanka ya fad'i,daga kan Alhaji,Hajiya k'annenka,masu aiki ba wanda zai sake ganinka da mutunchi a gidan nan,bunsuru kawai" Ta fice d'akin tana tunanin yadda akai ya shigo d'akin,Keyn da ta gani ta waje tace "Lallai Yazeed criminal ne,Allah yamun tsari dashi" (Ni zee nace Ameen Noor).
Gaba d'aya fuskar shi ta wanke da jini,a daddafe ya fita d'akin,Ya nufi chemist d'in kusa dasu,aka mishi dressing,ya dawo gida
Zaune yayi jigum a d'akinshi da tunani birjik a ranshi "Noor Noor Noor wlh bazan hak'ura dake ba kome zaki mun,kasheni kad'ai zakiyi ya hana ni cimma k'udirina a kanki,Yanxu ya zanyi" Can ya tuno wata idea yayi murmushi Yace "Yes i think this will work".
*Kuyi hak'uri typing d'in yau ba yawa*
*ZEE YABOUR*❤?🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.M.L*
6⃣9⃣
*This page is dedicated to my adorable fwendy Jannart💋,Thanks for everything😍,its nice meeting you,May God reward yhu abundantly*
A ranar Hajiya ta tafi Zaria,Sosai Maman khairat taji dad'in zancen da tazo mata dashi,"Amma sai naga kamar Imran yayi yaro da aure gwara khairat" "Ba wani yarinta,Imran na da hankali nasan zai iya rik'e khairat,fatan mu kawai Allah ya basu zaman lafiya" "Ameen Ya Allah" Sun tattauna sosai akai ,kuma sun yanke shawarar sa rana nan bada dad'ewa ba,A ranar ta koma,ba yadda Maman khairat batayi da ita ba ta kwana,Tak'i tace a ranar take son komawa.
Naseer na tafiya,Shima Imran ya tashi ya nufi gida dan ji yayi bazai iya cigaba da zaman office d'in ba.
Noor da ta bar d'aki,Kitchen ta nufa,ta tarar an tara kayan wanke-wanke ta hau wankewa,Bayan ta gama tasa hannu suna aikace-aikacen kitchen,a ranta tana tunanin maita irin ta Yazeed,a ranta tace "ko kafi k'oda naci In shaa Allahu ba zaka samu abunda kake so ba"
Sai da suka gama aikin kitchen tas,ta koma d'akinta,ta share inda kwalba ta fashe,
Ta kwanta kan katifarta,ita kanta yau bata ci lunch ba,ta riga ta saba tare da Imran suke ci,Cewa kanta tayi "Noor ki ma kanki fad'a,kima dawo da cin abinchi ke kad'ai kamar yadda kika saba, dan Imran ya kusa zama mijin wata daga ya aureta kuma shikenan,ganinshi ma wuya zai rik'a miki" Wasu zazzafan hawaye taji sun zubo mata "Ya Allah! Ka cire mun abunda nake ji a raina game da Imran".
Tsakanin Imran da Yazeed yanzu sai sama sama,basa zama suyi hira kamar da,Yazeed shakkar Imran yake,Imran kuma najin haushin shi
Yazeed na zaune falo yana kallo,Imran ya shigo tare da yin sallama,
Yazeed ya juyo ya kalleshi tare da amsawa yace "Yaya sannu da zuwa"
"Yawwa sannu,me ya samu goshinka ko wata kaje dannewa ta bugeka?"
Yazeed sai da hanjin cikinshi suka bada k'olulolo ya d'an yi dariyar yak'e,Yace "No wlhy,bugewa nayi da bango"
"Hmmm toh Allah ya sawwak'e"
"Ameen"
Ya wuce d'aki ya barshi nan,Yazeed sai hamdala yake da Imran bai gano shi ba.
Ruwa ya watsa,ya chanza kaya,ya fito ya nufi garden,ya aika a kira masa Noor
Da d'an aike yazo,Noor har tayi niyyar tace aje ace mishi bacci take,sai kuma taji tana son ganinshi
Hijabi ta zura,ta nufi garden
Tun da ta shigo garden d'in yake kallonta har ta samu wuri ta zauna,Idonta ya kumbura yayi jajir tsabar kuka ganin haka ba k'aramin d'aga mishi hankali yayi ba
Yace "Noor me ya sameki? Me aka miki? Wa ya tab'aki?"
"Kaina ke ciwo" ta bashi amsa a tak'aice
"Banda abunki Noor kanki na ciwo,ai sai ki gaya mun baki ta kuka ba,baki san kuka na k'ara sa ciwon kai ba,tashi muje a siyo miki magani,daga nan mu zagaya gari"
"A'ah Imran barshi nasha panadol,yawo kuma ba sai munje ba"
"A'ah ki bari muje dai kiga likita,sai muje kisha ice cream"
"Imran kenan ya kamata tun yanzu mu rage sabawa da juna,mu d'an rik'a nisa da juna"
A kid'ime ya kallo ta yace "Akan me?"
"Ka kusa zama mijin wata,kuma da kayi aure shikenana fah ,dole ka zauna gida tare da matarka"
"OMG! me yasa kika tuna mun da zance nan,ni fah bazan auri khairat ba,kuma ko na aureta ba abunda zai canza daga alak'armu"
Da mamaki take kallonshi "ba zaka aureta ba?"
"Ni dai plxx ki bar zancen nan tashi muje"
"Ni fah ba inda zani"
"Haba Noor me yasa kike haka,yanzu so kike na nisanta kaina dake?"
Ta gyad'a kanta sama "Wlh bazan iya ba Noor,ko nayi aure bazan iya ba,ballatana a yanzu da banyi ba,plxx Noor kar kice haka" Ya fad'i maganar cike da damuwa
Kawai taji ya bata tausayi,itama tana tausayin kanta dan rashin Imran a kusa da ita babban cuta ne,Tace "Muje" tana d'an murmushin dole
Sosai farin ciki ya bayyaa a fuskar Imran Yace "Yawwa ko ke fah"
Ya kaita chemist ya siya mata maganin ciwon kai,sannan suka je wuraren shak'awata da NEXT ya mata siyayya tare da siyan mata kayan k'walama
Sun dawo gida cike da nishad'i,damuwar da Noor ke ciki ta rage sosai.
Khairat ce zaune gaban madubi,tana ta tsara kwalliya,Ihsan tace "Wai ina zaki kike ta kwalliyar nan?"
"Ina zani da ya wuce wajen Yayana"
"Lallai fah masu Yaya,Allah dai ya nuna mana aurenku mu sha biki"
"Ameen yar'uwa" ta mik'e tsaye "Ya kika ganni nayi?" Tana jujjuya wata doguwar riga ce a jikinta material,ta mata kyau charas charas, "Wow kin had'u sis,wannan ai sai kisa Ya Imran ya rikice"
Khairat ta k'yalk'yace da dariya,kanta ya k'ara girma
Turare ta sake fesawa,ta gyara d'aurinta tace "sai na dawo"
"A dawo lafiya".
Bayan sun dawo d'aki yaje ya kwanta yana huce gajiya,Da sallama khairat ta shiga d'akin
Ba tare da ya d'ago ba ko ya kalleta,Ya amsa sallamar,ya gane muryarta
"Yayana sannu da hutawa" ta fad'a tare da zama kan kujerar kusa da gadon
"Yawwa sannu k'anwata" ya fad'a tare da kallo ta,Sosai yaga ta mishi kyau
Ya mik'e zaune yace "k'anwata wannan kwalliyar sai ina?"
Ba kunya tana murmushi tace "kai nama Yayana"
"Ni! Lallai k'anwata toh nagode kuma kinyi kyau" (tausayinta yake ji,yana ganinta marainiya shiyasa yake k'ok'arin yin duk abunda zai faranta mata rai)
Sosai taji dad'in yadda ya yaba mata,tayi murmushi tace "nagode Yayana"
Haka suka cigaba da hira mai dad'i,Khairat nayi na sako kalaman soyayya a ciki,hakanan Imran ke daurewa yana mayar mata kalaman,Dad'i duk ya gama lullub'eta.
Noor tana bubbud'e kayan,taga ledar kayanshi an had'u da ita,Tace "wannan kayan Imran ne bari na kai mishi" ta mik'e.
"Yayana kana sona kuwa kamar yadda nake sonka?"
Noor tasa kai kenan cikin d'akin, taji Imran na cewa "Ina sonki sosai k'anwata fiye da yadda kike sona ma" (ya kawai fad'a ne amma ba har zuci ba)
Da sauri ta juya ta koma,sai hawaye shaaa
Kan katifar ta,ta fad'a tana kuka sosai,tana tuna kalaman Imran kukanta na k'aruwa
sai da tayi mai isarta sannan ta dawo hayyacinta take tambayar kanta
"To ke Noor meye na kuka? Me ye naki a ciki dan Imran na son Khairat? D'an mijinki ne fah" Tai saurin goge hawaye taja siririn tsaki "me zai sa na b'ata lokaci har ina kuka".
Kwana biyu Yazeed bai waiwayi Noor ba duk yana cikin plan d'inshi,
Da yamma lokacin Imran ya dawo daga office
Yazeed ya siyo kaza,da youghurt mai sanyi,ya zuba maganin bacci mai nauyi a ciki
Ya ba Abu yace ta kaiwa Noor tace inji Imran
"Gashi inji Imran" ta ajiye mata,bata jira me zata ce ba,tasa kai ta fita
Ta bud'e ledar,a ranta tace Allah sarki Imran
Dama yunwa take ji,ta hau ci,ta kura da youghurt
Hamma ta fara,wani irin bacci ta fara ji,tashi tayi ta rufe d'akin tasa key,tabar key a jiki bata cire ba
In less than 1min bacci ya d'auketa
Bayan kamar minti sha biyar,Yazeed ya shiryu yana lasar baki "Yana yau zan fad'a kogin dad'i,damo zai kai ga harawa,yau zanyi yadda nake so dake"
Yana ta waige-waige yaga ba kowa,ya murd'a k'ofar a rufe,ya fiddo spare key yasa yak'i shi(kunsan tabar key a jiki)yai ta sawa yak'i shiga,Ya lek'a yar kusurwar,yaga a rufe
Tsaki yaja tare da buga k'afa yace oh shit! Damn it!
Yace "idan yau kin kub'uta next time bazaki kub'uta ba wlhy"
Ya tafi yana cizon yatsa,plan d'inshi yayi ruining.
Khairat na nunawa Imran so har na fitar hankali,ganin irin son da take mishi yasa take bashi tausayi shima yana kulata,Sukan zauna suyi hira,su fita yawo
Tana k'ok'arin ganin ta rabashi da Noor,buh still Imran na nan manne da Noor,sai dai sun rage zama tare,saboda khairat tayi kane-kane,Abun na damun Noor,idan ta gansu tare sai dai tayi ta kuka tana cewa tun yanzu sun fara rage zama toh ina ga idan yayi aure.
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*P.M.L*
7⃣0⃣
*Dedicated this page to my k'awayen arzik'i kuma masoyan littafin nan _Dija waziri,Aunty jamila(Maman bobo),Maryam Kaumi,Aishat A Muhd,Meryam Abdoul(Neighbour),Mufeen,Huwailat nd Biebie_ Allah ya bar mun ku,Love yhu all*❤
``` The day is beautiful, but you make it special. May this wonderful day bring loads of fun and frolic in your journey of life. Happy Birthday```🎂🎂🎂🎈🎈 *BABY NURSE*😍
Yau weekend Imran na gida,Suna zaune garden da Noor suna hira cikin nishad'i da kwanciyar hankali,Yace "In shaa Allahu ranar monday zanje makarantar da nake so na nemar miki,kiyi JSCE,idan yaso sai ki fara daga SS1,Zaki iya yi dai ko?"
Wani dad'i ya lullub'eta ta gyad'a kai sama "Eh zan iya"
"Toh Mashaa Allah,In shaa Allahu zan siyo miki text books da zasu yi helping d'inki,kuma zan rik'a miki lesson"
"Nagode so...."
"Shhhh" ya katseta "Anything for you"
Tayi murmushi tare da jin son Imran na ratsa dukkan sassan jikinta,ba tare da tasan SON SHI bane
Khairat ce ta shigo garden d'in tana yatsina fuska dama tasan a tare zata gansu
Kamar an soketa da kibiya haka taji da taga yadda suke hira cikin nishad'i,tana rangwad'a ta k'arasa wajen su "Yayanah kazo muje ka kaini saloon"
"Haba k'anwata kije driver ya kai ki mana"
Wani k'ulloton bak'in ciki taji yazo ya tokare mata wuya,ta juya ta tafi, a ranta tana cewa "Saboda banzar nan zaka ce naje driver ya kaini"
D'aki ta koma tana hawaye
"Lafiya sis cewa yayi ba zai kai ki ba?"Ihsan ta tambaya
"Ni wlhy Noor na shiga gona ta da yawa,na tsaneta na gaji da ganinta cikin gidan nan,wai Alhaji ba zai saketa ba kowa ya huta"
"Hmm ai da zai iya sakinta da tuni Hajiya tasa ya saketa amma tunda kika ga Hajiya ta sa ido,toh kowa ma ya zuba ido"
"Toh ni kuwa ko Alhaji bai saketa ba da k'afarta zata bar gidan nan,zo kiji" Ta rad'a ma Ihsan magana a kunne suka yi shewa,suka tab'a.
Daddyn Noor,da mummy da k'annenta sun manta da wata wai ita Noor,harkokinsu kawai suke suna cin duniyarsu da tsinke,Sana'ar caca nata habbak'a ,yana ganin ya rabu da tsiya(Noor),Baba mai gadi kuwa kullum cikin kewar Noor yake yana addu'a "Allah yasa can tana samun kula bata wahala".
Hajiya ce ta fito daga d'akinta tana masifa, "Uban wa ya shiga d'akina ya d'aukar mun sarkar gwal da yan kunne"
Ihsan,Khairat da Iman ne suka fito a tare
Ihsan tace "Sark'a kuma mummy kin duba ko'ina?"
"Sosai ma kuwa na duba,ko kira mun masu aikin gidan nan"
Iman ce ta tafi kiransu,
Noor na kwance a d'aki coz Imran ya fita,ya tafi gidansu Naseer
"Ki taso Mum na kiranki"
Jiki na rawa ta mik'e dan tasan kiran Hajiya ba alkhairi bane
Duka masu aikin gidan sun hallara,suna duk'e gaban Hajiya hadda Noor
Hajiya ta nuna su da yatsa "Cikin ku waya shiga d'akina ya daukar mun sark'a da yan kunne"
Nan fa kowacce ta hau rantse-rantse ba ita bace
"Sark'a zata d'auki kanta ne,wacce ta d'auka tun wuri ta kawota,idan ba haka ba,idan nasa aka binciki kayanku aka gani,ko wacece zata fuskanci hukunci mai tsanani"
Dukkansu ba wacce ta motsa,rantsuwa suka cigaba da yi
Noor ita dai jikinta ne yayi sanyi duk da tasan ba ita bace
Hajiya tace "Ihsan kuje ku bincika mun kayansu,ku kuma ku tsaya nan har su dawo"Ta koma kan kujera ta zauna tana karkad'a k'afa.
Suna fita suka tab'a suka kashe,Khairat tace "Yau zata ci ubanta"
Ihsan tace "ke dai bari yar'uwa"
Bayan mintuna kad'an suka dawo da sark'a suna salati
Hajiya ta mik'e tsaye tace "A ina kuka gani?"
Iman tace "hmm mum abun mamaki ko da yake ba abun mamaki bane,a kayan Noor"
Hajiya ta rafsa salati tana tafa hannu"La haila ha ilallahu Noor sata kika koma" tayi kanta ta wanketa da lafiyayyan mari sai da ta fad'i
Ta rik'e kumatunta,tana hawaye ba marin ya mata zafi ba, sharrin satar da aka mata,Ita da ko tsinke bata d'auko ba amma yau ance ta saci sark'ar gwal,Tace "Wallahi tallahi ba ni ba...." kafin ta k'arasa hajiya ta kai mata wani wawan naushi a baki "Yi ma mutane shiru munafukar Allah,Yau Allah ya toni asirinki ,kud'ina ma da ake sacewa nasan ba kowa bane face ke,kin zamar mana annoba cikin gida"
Noor kukan bak'in ciki take,Zuciyarta na k'una kamar zata fito,
Masu aiki kowa na tofah albarkacin bakinsa,Su khairat na zaginta da fad'a mata bak'ak'en maganganu
Hajiya tace "Yau zan hora ki dan ya zama darasi ga yan baya"
Yazeed ne ya shigo yana tambaya "me ya faru?"
Iman ce ta fad'a mishi abunda ya faru
Yayi murmushi a ranshi yace "ga wata dama na samu da zan cimma k'udirina" Ya kawar da tunanin yace "Tunda tace ba ita bace,ku bani 1min na keb'e da ita xanji gaskiyar al'amarin"
Khairat tai saurin cewa "wane gaskiya,abunda k'iri k'iri a kayanta muka gani"
"Me kike ce na baka na zuba,Noor biyoni"
Addu'a su khairat keyi "Allah yasa kar plan d'insu yayi ruining".
"Noor nasan bake kika yi satar nan ba,sharri aka miki dan haka ki bani had'in kai,idan har kika bani had'in kai na miki alk'awarin wanke ki daga sharrin da aka miki,idan kuma kika k'i zance tabbas ke kika yi satar nan har in bada gudunmuwa a hukuntaki"
Murmushin takaici tayi tace "kayi asara Yazeed,to bari kaji ko za'a yanka naman jikina gunduwa-gunduwa wlh tlh bazan baka had'in kai,Allah na nan shi zai wanke ni,bana neman kariyar kowa sai ta Allah"
"Haka kika ce zaki ci k'wal ubanki kuwa"
Ya zare belt zai zuba mata,tai saurin rik'ewa ta nuna shi da d'an yatsa "Ahir! d'inka da akayi wannan lokacin da nake ganin mutuncinka amma yanzu bana ganin mutuncinka ko na sisin kobo,mutunci madara ne idan ya zube bai kwasowa,kana dukana zaka ga abunda zan aikata ma"
Gaba d'aya jikinshi yayi sanyi,ya tsaya yana kallonta da mamaki,ya fisge belt d'in a hannunta ya koma cikin falo,ta biyo bayanshi
"Mum ita tayi satar nan,wlh ki hukuntata yadda gobe ko sweet ta gani ba zata d'auka ba" Yazeed ya fad'a
Noor a ranta tace "Allah na nan shi zai mun sakayya"
Hajiya ta fisgo Noor,ta jata xuwa kitchen,Duk suka biyo bayan Hajiya,Serving spoon ta d'auko irin flat one d'in nan,ta kunna electric cooker
Ta d'aura a kai sai da ya d'au zafi rau,yayi jajir
Ta jawo hannu Noor,ta manna mata a tafin hannunta,Tana ihu tana kuka,tana k'ok'arin k'wace hannunta,ba tausayi Hajiya ta cigaba da manna mata
Ba mai ba Hajiya hak'uri sai ma k'ara zugata da suke
Tana sawa a wuta,tana manna mata a hannu,sai da hannu Noor ya sale duk ya k'one,yana ta jini sannan Hajiya ta sake ta Tace "wannan shine hukuncinki yan baya sai ku koyi darasi"
Noor ta duk'e nan k'asa rik'e da hannunta tana kukan azaba,ba wanda ya kulata,Kowa ya fice sai Yazeed
Yace "kinfi son haka akan ki bani had'in kai?"
Tai banza dashi ,Ya juya ya fice.
Ta mik'e ta koma d'akinta,tana kallon hannun yadda yayi,sai rad'ad'i yake mata tana kuka
Ta hau magana ita kad'ai "bazan iya da azabar nan ba da cin mutunchi,tafiya zanyi na bar gidan nan,nafi son nabi duniya da na cigaba da zama gidan nan" Duk wani mai imani yaga Noor a yanayin nan dole ta bashi tausayi".
Imran suna zaune,suna hira da Naseer,kawai yaji gabanshi na fad'uwa
"Naseer gabana ke fad'i,ina ji kamar ba lafiya ba"
"Kar ka damu ba wani abu bane abokina"
"No naseer,bari na tafi gida,ina ji a jikina ba lafiya ba"
"In shaa Allahu lafiya zaka tarar da kowa,ba wata matsala"
"Allah yasa friend"
"Ameen sai munyi waya"
Su khairat,a d'aki sai dariya suke suna murna,Plan d'insu yayi,Khairat tace "kunga Yayana na dawo aka ce mishi sata tayi,mutunchinta zai zube a idonshi k'ila har tsanarta sai yayi,shikenan ba zance wata alak'a tsakaninsu,mu kuma kinga sai mu samu damar azabtar da ita da kyau tunda ba mai tareta ,har sai ta bar gidan nan dan kanta"
Ihsan tace "Very gud idea,kanki na kawo wuta fah"
Sukayi shewa.
Imran hankalinshi duk ba'a kwance ba ya shigo gida
Sashen Hajiya ya nufa,Ya sameta a falo zaune tana shan kayan marmari,tana kallo hankali kwance,Ajiyar zuciya yayi(hakan da ya gani ya tabbatar mishi lafiya)
"Mum sannu da hutawa"
"Son Ya kake? Ina ka shiga ne tun d'azu ban ganka ba"
"Lafiya lau,ina gidansu Naseer"
"Kai mai kare Noor baka had'ata da kowa ba,toh ka sani b'arauniya ce,har d'akina ta shiga ta saci sark'ar gold"
Kamar an watsa mai ruwan zafi haka yaji zancen Hajiya
"Wallahi mum Noor ba b'arauniya bace sharri aka mata" ya k'arasa maganar kamar yayi kuka
"Dama haka zaka ce"
Da sauri ya mik'e Yace "ina zuwa"
D'akin Noor ya nufa da saurinshi har yana tuntub'e
Noor har a lokacin kuka take tana kallon hannunta, inda take ya durk'usa idon shi ya sauka kan hannunta,a firgice ya kamo hannunta yana cewa "Wa ya miki wannan Noor? Waye ya k'ona miki hannu? Wane azzalumin ne?"
Kukanta ne ya tsananta ta kasa cewa komai
Shima tuni ya fara hawaye,yana kallon hannunta zuciyarshi na k'una da tafarfasa,ga mugun tausayinta da ya kama shi
Yana kuka,a fusace yace "ki gaya mun Wa ya miki wannan abun? I swear i won't spare that person" Ya k'arasa maganar yana huci,hawaye na zaba daga idonshi.
........
*Please ina baran addu'arku bana jin dad'i,typing d'in yau daurewa kawai nayi na muku wallahi*
*I love yhu all*❤
*ZEE YABOUR*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣1⃣
```NOTE``` *Masu biyoni private kuna cewa na turo muku novel daga farko,tsakani da Allah tura novel prvt akwai wuya,ku daina ganin laifina idan ban tura muku ba,gaskiya ina jin wahalar tura novel prvt shiyasa na bude group duk mai so yayi joining ko yamun magana nayi adding dinshi,but plxx Dan Allah a daina biyoni pc ana cewa na tura,wasu a gadarance zasu maka magana kamar ajiyeka sukayi,idan baka tura ba kuma a gaya ma maganar banza,Duk wacce ta biyoni pc idan ban tura ba kar taga laifina*
Bata bashi amsa ba, hawaye ne kawai ke kwaranya daga idonta
"Please ki gaya mun wane ne?"
"Hajiya" ta fad'a da shesshek'ar kuka
Ya saki hannun ta da k'arfi ya mik'e, ya nufi hanyar fita
"Ina zaka Imran? Don't do something stupid mahaifiyarka ce" bai tanka ta ba, ya fice
Ta durk'ushe nan tana kuka tana fad'in "Oh Allah! Gani gareka ka samar mun mafita".
Da k'arfin tsiya ya turo k'ofar falon Hajiya,sai da taji tsoro
Gaba d'aya fuskarshi ta chanza tayi jajir,sai huci yake, yana maida numfashi da k'yar, jikinshi na rawa Yace
"Mum why are you so heartless?, mum ina tausayinki da imaninki suke? Wlhy mum ban tab'a tunanin rashin tausayinki ya kai haka ba, ban tab'a jin na tsani kasancewa ta d'anki ba sai yau, Mum why? Why? Mum me yasa kike haka? Ba zaki ji tausayin marainiyar Allah ba, wuta fah kika sa kika k'onata, zaki yi iyawa Iman ko Ihsan haka? na tabbata idan sune sukayi satar nan wlhy bazaki k'ona su ba, ballatana ita da ba ita tayi ba, sharri aka mata, ko ita tayi wannan hukunci ya mata tsauri, wlh tlh idan na gane wanda ya mata sharrin nan dat person must pay for it" ya k'arasa maganar yana dafe zuciyarshi da yaji tana mishi zafi, jiri na neman d'ibarshi
Hajiya tunda ya fara magana jikinta yayi sanyi (bata tab'a ganin Imran yanayi irin na yau ba, gaba d'aya ta tsorata da ganinshi, tana masifar son Imran bata son abunda zai tab'a shi)
Da sauri ta k'arasa inda yake ta rik'o shi tana cewa "Kayi a hankali imran"
Ya cire hannunta a jikinshi yace "its okay, Am fine"
Ya juya ya fita
Hajiya tabi bayanshi da kallo,Yau ce rana ta farko da ta fara nadama akan abunda tama Noor ba don komai ba, sai yanda taga Imran, Addu'a take Allah yasa kar wani abu ya sameshi, tana kuma mamakin yadda yake masifar son Noor
Duk abunda ake su Khairat naji daga d'aki coz da k'arfi yake magana, Haushi duk yabi ya cikasu, kuma sun tsorata da jin yadda Imran ke magana, abunda yafi tsorata su shine da yace idan ya gano wanda ya mata sharri............
D'akin Noor ya koma, Ya k'arasa inda take "Sannu Noor tashi muje asibiti"
Da hannu d'aya tasa hijabi
Ya bud'e mata k'ofa ta shiga, ya mayar ya rufe ya koma driver's seat
Yana ta lallashinta, yana bata hak'uri
*Manan Specialist hostipal* Asibitin Dr.Aysher Basma(DANGIN MAHAIFINA) suka nufa
Basu samu ganinta ba lokacin ta tafi kaduna(d'ayan asibitinta)
D'aya daga cikin k'wararrun likitan asibitin d'an india Dr.Aditya yayi treating d'inta, shi kanshi ta masifar bashi tausayi, yana cewa waya mata haka? Da a k'asar sune takai k'ara, Sai an d'aure mutum
Ya gama treating d'inta, wurin aka sa bandage aka rufe, ya rubuta mata drugs
Imran da Noor suka mishi godiya sosai, suka tafi
A mota Imran ke k'ara bata hak'uri
"Noor ki k'ara hak'uri komai kika gani muk'addari ne daga Allah, duk wahalar nan da kike shiga watarana sai labari, nasan baki yi sata ba sharri aka miki, wlh idan na gano wanda ya miki sharrin nan ba zai ji da dad'i ba"
Noor murmushi kawai tayi, matsayin Imran na k'aruwa a zuciyarta, tabbas babu mai sonta a duniya kamar Imran, wa'inda aka k'onata a gabansu basu ji tausayinta ba, shi da ba'a gabanshi akayi ba hadda kuka, ji yadda ya tada hankalinshi, Duniya bani da masoyi kamar Imran, ta sake yin wani murmushi, Zuciyarta ta wani harbu akan Imran(SO)
Imran a ranshi masifar tausayin Noor yake ji, da sonta da ya dabaibayeshi, tunaninshi hanyar da zai bi ya taimaketa ta fita daga wahalar nan yake.
Da suka koma gida, zama yayi a d'akinta, yana ta jan ta hira, yana bata labarai masu sanyaya zuciya da kwantar da hankali, Kiran sallar magrib da yaji yasa shi tashi ya fita
Sashen su ya nufa, Ya rage rad'ad'in da yake ji sosai sbd Noor ta daina kuka har tana dariya, Ya fad'a kan gado tare da yin ajiyar zuciya,
"WAYE YAMA NOOR SHARRIN NAN? WHO COULD DAT PERSON BE? WHO? WHO?"
Ya kasa kawo kowa a ranshi
Ya kawar da tunanin yace "yanzu ya zanyi, na taimaki Noor, ta fita halin k'uncin nan da azabtarwa?, its pain me alots naga ana azabtar da ita, Wlhy ko shara na tsani naga tana yi, Zuciyata zafi take"
Ya d'an yi shiru yana nazari tare da buga kanshi,sai can Yace
"Yes i have an idea"
Yayi murmushi
Alwala ya tashi yayi, ya gabatar da sallar magrib tare da yin nafila, ya zauna yana karatun Qur'ani har aka kira isha'i, Yana idar da sallar Isha'i
Ya d'auko wayarshi ya kira Dr.Moha (suka gama magana ya ajiye wayar tare da mishi godiya)
Gado ya hau,yaja bargo ya rufe kanshi.
Bayan mintuna kad'an, sai ga Khairat ta shigo rik'e da tray na abincin shi, ta ajiye kan centre table
"Yayana tashi ga abincinka"
Wani irin numfashi ya rik'a yi,
Da sauri ta k'arasa inda yake tace
"Yayana me ya sameka?
Wani irin numfashi yaja, sai kuma d'ib ya d'auke
Ihu khairat ta fasa da taga baya numfashi, da gudu ta fita sashen taje ta gayawa Hajiya
Hajiya a rud'e da gudunta, ta nufi sashen su
Jijjiga Imran ta hau yi tana fad'in "Dan Allah Imran ka tashi,nasan ni na saka halin nan wallahi na tuba,Dan Allah ka tashi, kayi hak'uri" ta fad'a kanshi tana kuka
Khairat ce ta kira Dr. Moha, Cikin minti uku sai gashi
Khairat tace "Dr har kazo"
"Eh dama ina nan area nazo duba wani patient"
"Ok"
Dr.Moha yayi gwaje-gwajen da zanyi sannan ya juyo kansu Yace "A gaskiya damuwa tama Imran, yanzu haka ya kamu da ciwon zuciya"
Hajiya a firgice tace "Ciwon Zuciya Dr" ta fashe da kuka
Khairat ma ta tsorata da jin furucin Dr
"Eh ciwon zuciya,dan haka sai a rik'a kiyaye duk abunda zai sa shi damuwa ko ya b'ata mishi rai, idan ba haka ba Zuciyarshi zata iya bugawa ya rasa ranshi"
Hajiya na sharar k'walla tace "ba kowa ya haddasa masa ciwon zuciyar nan sai ni, In shaa Allah Dr za'a kiyaye"
"Yawwa Dan Allah Hajiya a kiyaye ni zan koma,Nan da 1hour zai farfad'o In shaa Allah"
"Toh Dr. Mun gode"
"Ba damuwa"
Hajiya zaune tayi gaban Imran, tana kallonshi tana kuka, cike da nadamar abunda ta rik'a ma Noor dan shi ya jawo halin nan da yake ciki
Khairat ma sai hawaye take, Su Ihsan suma duk sun hallara a d'akin, Yazeed baya nan yana can wajen sharholiyarshi
Noor na d'akinta bata san abunda ke faruwa ba.
Bayan awa d'aya, Imran ya farfad'o, yana ganin Hajiya akanshi yai saurin juyar da kanshi, Yace "me kuke yi anan?" Kunzo nan ne ku k'arasa ni, in mutu ku huta"
Hajiya tai saurin katse shi "A'ah Imran kar kace haka, muna sonka, ba zamu so wani abu ya sameka ba"
Wayarshi da keyn motarshi ya d'auka ya bar d'akin, Hajiya ta bishi da kallo tana hawaye, Su khairat ma mamaki ne ya cika su.
D'akin Noor ya fara zuwa, ya murd'a yaji a rufe, yayi knocking shiru, haka ya tabbatar mishi barci take
Yana shiga motarshi, Yayi dialing numbern Dr.Moha
"Dr. Na kira ne na k'ara maka godiya, nagode sosai fah, Allah ya biyaka"
"Haba! Imran Anything for you, kafi k'arfin haka a wurina"
Yayi dariya yace "ai godiya dole ne"
Dr.Moha yayi dariya
Imran yayi hanging-up
Ya tada motarshi zuwa gidansu Naseer
Zuciyarshi cike da farin ciki, Finally Noor zata huta.
*BAYA*
Imran a lokacin da yana tunani, idea da tazo mishi ita ce "Yasan Hajiya na masifar son shi ba zata so abunda zai cutar dashi ba, shiyasa ya yanke shawarar had'a baki da Dr.Moha ace yana da ciwon zuciya yasan itace kad'ai hanyar da zai kub'utar da Noor,
Dai-dai lokacin da yasan Khairat na kawo mishi abinchi, Dr.Moha yazo ya mishi allurar da zata sa shi unconcious for some hours
Yana mishi allura ya tafi, shiyasa ana kiranshi yazo ba b'ata lokaci.
*ZEE YABOUR*❤
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
*THIS PAGE IS FOR YOU MY ADORABLE,EVERLASTING,AMAZING,SWEETEST FRIEND,SISTER STYLISH BCH(HABEEBTY)*
_I am so lucky to have a friend like you_
_I am so blessed to have you,_
_Friends like you are too rare,_
_Friends like you a really few,_
_You are the real gem that shines_,
_With you things are so good and fine_,
_Thanks my friend for being there,_
_Love you more dan words could say_ *Habeebtynah*❣💋
*ALLAH YA BARMU TARE FOREVER*👩❤💋👩
7⃣2⃣
Naseer na zaune d'akinshi yana operating system, Imran yayi sallama ya shigo.
"Ah! Abokina ya naga ka dawo?"
"Just gidan so bored nace bari nazo nan muyi hira" (Duk yadda suke da Naseer bai tab'a fad'a masa about Noor ba, dan baya so yasan babanshi ya auri yarinya)
"Amma ka kyauta wlhy, nima zaune kawai nake na rasa abun yi shine na d'auko system ina duba wasu abubuwa, " ina fatan lafiya ka tarar da mutanen gida?"
"Lafiya lau suke"
"Toh madallah"
Nan suka dasa hirar duniya, Sai k'arfe goma Imran ya dawo gida
Yaso ganin Noor a daren, but yasan tayi barci kuma ko bata yi barci ba yanzu dare yayi ya shigar mata d'aki.
Haka ya kwana da tunaninta a ranshi, da k'yar barci ya d'aukeshi, Hajiya kuwa tana yi tana lek'a window daga sashen Alhaji, taga ko Imran ya dawo, sai da taga dawowarshi hankalinta ya kwanta.
Su khairat kuwa,da na sanin plan d'insu suka rik'a yi, maimaikon suyi succeeding komai ya lalace.
Yazeed bai dawo gida ba sai 3,(da mai gadi yake had'a baki yace mai gadi yace da wuri ya dawo) Kusan kullum sai yaje Club, yau ma club yaje, Yana dawowa ba sallah ba salati kawai yabi lafiyar gado dan wani irin bacci yake ji.
Washegari da sassafe around 7,Imran ko wanka bai yi ba yana sanye da jallabiya,ya nufi d'akin Noor
Tana zaune kan dadduma(praying mat)tana karatun Qur'ani, tunda tayi sallar asuba bata koma ba
Yai sallama ya shiga, Ta amsa mishi sallamar tana murmushi.
"Kin tashi lafiya? Ya jiki?"
"Lfya,Alhamdulillah"
"Kin sha magani?"
"A'ah sai nayi breakfast"
"Plx kar kiyi wasa da shan magani,ina zuwa" Ya fice
Kitchen yaje, ya samu masu aikin nata k'ok'arin had'a breakfast
Yace ma Abu "Ta had'a breakfast d'inshi, ta kawo mishi d'akin Noor"
Tace "Toh"
A ranta tace "sabon salo,kiran sallah da usur, yau kuma d'akinta zakayi breakfast".
D'akin ya koma, Ya zauna gefenta d'an nesa da ita kad'an Yace "tunda muke dake ban tab'a jin kinyi karatu da k'arfi ba,yau dai ina son jin muryarki kina karatun Qur'ani"
Tayi murmushi tace "ai muryata bata da dad'i,bani da k'ira'a"
"Ni dai ina son ji"
Tace "shikenan"
Tayi gyaran murya ta fara zuba karatu cikin k'ira'arta mai masifar dad'i muryata sak ta Sudais kai kace Sudais ne ke karatu, Gaba d'aya ta gama tafiya da imanin Imran har wani lumshe ido yake dan dad'in karatun
Shafi d'aya ta karanta a cikin Suratul bak'ara, tana kawo k'arshen shafin tayi shiru, Imran ji yayi kamar kar ta tsaya
"Mashaa Allahu Barakallahu, Noor haka kike da dad'in k'ira'a gashi kin iya karatu, kin sauke Qur'ani ne?"
"Eh na sauke"
"Hadda fah?"
"Na dai haddace hizib 15 dama Baba mai gadi ke k'arbar mun hadda"
Wani dad'i yaji ya lullub'e shi da ya rasa na me ye? Yace "Gaskiya ya kamata ki cigaba da hadda,In shaa Allah zan nemar miki islamiyyar nan kusa damu ki rik'a xuwa,nima anan nayi haddata(Imran ya haddace Qur'ani tun yana shekara 17)
Kamar tayi ihu dan murnar za'a sata islamiyya tace "Nago....."
Da saurin ya katseta "shhhh in kina mun godiya zamu samu matsala"
Tayi shiru tana murmushi.
Abu ce tayi sallama,suka amsa mata,ta ajiye breakfast d'in ta juya ta fita
Chips da egg sauce,sai kayan tea
Ya had'a musu kakkauran tea,kowa a kofinshi,ya zuba mata a plate ya ajiye gabanta Yace "gashi nan ki cinye ki sha magani" har zata mai godiya sai ta tuna tace "Sannu"
Ya zuba shima yaci,Shi ya d'auko mata maganin tare da zuba mata ruwa a kofi,ta karb'a tasha
Sannan yace "shi zai koma sashen su, kar ta kuskura ta fita ko'ina ta zauna d'aki ta huta,kwanukan zai aiko Abu ta kwashe"
Noor ta amsa da "Toh"
Tana jinjina irin d'awainiya da ita da Imran keyi, wanda take zaune gidan danshi bai masan da zamanta ba.
Wanka yayi ya shirya cikin k'ananan kaya,Ya zauna falo yana kallon Discovery channel
Hajiya ce tayi sallama ta shigo falon
Ya juya ya kalleta fuska a d'aure ya amsar sallamar, tare da cewa "Ina kwana?" (UWA UWA CE,dole ya bata girmanta komai ta aikata kuwa)
Dad'i taji da taga ya gaisheta amma ta lura fuskar shi a d'aura take, Ta amsa "lafiya lau Son" tare da k'arasawa inda yake, ta zauna kujerar da yake, Ta dafa shi "Ya jiki?"
"Alhamdulillah"
"Haba! Imran yanzu da ni mahaifiyarka kake fushi,idan akan abunda nake ma Noor ne yasaka shiga damuwa hadda ciwo,wallahi na tuba na daina daga yau,xan fitar da hannuna a al'amarin Noor"
Da saurin ya kalleta "Da gaske kike mum?"
"Yes son" Ta gyad'a mishi kai
Rungumeta yayi, Yace "Thank you so much mum, I love you"
Hajiya mamaki ne ya cikata yadda Imran ke murna buh tasan shi da tausayi tun yana yaro tace "i love you too son,Allah ya maka albarka"
Ya saketa tare da cewa "Ameen Mum,me kike so in miki da zai faranta miki rai"
"Ba komai Son,bari naje nayi breakfast"
"Toh Mum"
Ta tafi a ranta tana cewa "ko dan farin cikin ka da lafiyarka Imran nayi alk'awarin bazan sake tab'a Noor ba, dan farin cikin ka shine farin cikina".
Imran dad'i ya cika shi,ya rasa inda zai sa kanshi ,Alhamdulillah kawai yake furtawa,Yanzu Noor zata samu hutu babban burinshi kenan,sai kuma Alhaji ya saketa, dan bata dace da Alhaji ba.
Bayan sallar la'asar,Imran sashen Alhaji yaje, Ya same shi zaune a falo Yace "Daddy Dan Allah ina so nasa Noor a makaranta,ka amince?"
Alhaji a fusace yace "toh ni ina ruwana,idan kaga dama ka sata a mak'abarta ba makaranta ba"
"Daddy gani nayi a matsayinka na mijinta,kana da hak'k'i a kanta ya kamata a sanar dake"
"Kaga Imran kar ka k'ara danganta ni da mijin Noor ko ranka yai mummunan b'aci, fitar mun daga falo ya nuna mai hanyar fita"
Imran tab'e baki yayi ya mik'e ya fita a ranshi yana cewa "kasan baka sonta me yasa ka aureta? Kuma yanzu dan me da baza ka saketa ba?".
Noor na d'aki kwance tana hutawa duk ranar bata fito ba, kuma ba wanda ya nemeta coz Hajiya tayi warning d'insu Ihsan akan kar wanda ta k'ara gani ya shiga harkar Noor(hakan ba k'aramin haushi suka ji ba, tun ba khairat ba da taci alwashin azabtar da Noor)
Imran ne ya shigo d'akin Yace "ta tashi suje islamiyya"
Ta mik'e zaune tana cewa "Da wuri haka"
"To me za'a tsaya jira"
"Ka gayawa Hajiya?"
Yayi murmushi Yace "yanzu Hajiya ai tace ba ruwanta da al'amuranki,ta tuba"
Noor dariya tayi har hak'oranta na fitowa tsabar murna kasa cewa komai tayi, a zuciyarta tace "Alhamdulillah"
Sosai yaji dad'in ganin yadda take dariya.
Sunje islamiyya, an mata interview an d'auketa, Imran ya biya duk wasu kud'i da ake buk'ata har na uniform d'inta, Malamin yace "Gobe ta fara zuwa makaranta" An nuna mata ajinsu, Suka dawo gida.
Grade height Academy nan Imran ya nemar ma Noor, Sun d'auketa bayan an mata interview, Js3 class(aji uku) aka bata saura sati d'aya su fara JSCE,ba k'aramin kud'i ya kashe ba kafin su d'auketa saboda bata da takardun makaranta
Noor farin ciki kamar zai kasheta burin ta ya cika na son zuwa makaranta
Wani farin cikin ma, sai ranar da zata fara zuwa tana sanye da Uniform d'inta da suka amshi jikinta, charas-charas suka mata kyau,tasha farar safa da black cover shoe, sai Side bag da ta rataya.
Ba k'aramin kyau tama Imran ba, har hoto ya d'auketa a wayarshi ita kuwa sai wangale baki take murna duk ta cika ta, Shi ya kaita makaranta, Ya mata nasiha sosai akan tayi karatu banda biyewa k'awaye tasan ita matar aure ce,ta kula sosai da karatun ta(haushi taji da ya kirata matar aure but bata nuna mishi ba),
Tace mishi "Toh"
Ya zaro d'ari biyar ya bata, Yace
"Ga kud'in break d'inki"
"A'ah ka barshi"
Banza ya mata kamar bai ji ta ba Yace "sai na dawo d'aukar ki" Yaja motarshi ya tafi.
Yan'ajin duk girmansu d'aya da ita sai dai zata girmesu a shekaru,Yan'ajin kansu ta burgesu gata kyakkyawa suna ta kallonta,Suna ta mata sannu tare da tambayarta Sunanta,Tace musu "Noor"
"wow nice name" suke ce mata
A ranar tayi k'awaye Ilham da Kausar, Suna ta janta a jiki,Daga ganinsu ya'yen masu hannu da shuni ne kuma wayayyu(Saboda makarantar ta ya'yan masu kud'i ne).
0 comments:
Post a Comment