Ana tashin su Imran yazo d'aukarta, A mota yake tambayarta "Ya makarantar? Ba dai wata matsala koh?"
Ta amsa da "Eh Babu"
Yace "Ok Gud".
Suna isa gida, Ta cire uniform ta watsa ruwa, ta saka doguwar riga mara nauyi, Kuloli ta gani ajiye gefe d'aya, Baki ta saki tana kallonsu, Imran ya shigo tare da sallama(shima ya sake wanka,ya saka kayan shan iska) Yace "Ni nasa a kawo su nan, Lunch d'in mune zauna muci" Ya k'arasa maganar tare da zama
Tayi murmushi tace "Toh bari naje na gaida Hajiya"
"Ok kiyi sauri"
"Toh" ta fice
Ya bita da kallo a ranshi yana mamakin sanyin hali da hak'uri irin na Noor,duk da abunda Hajiya ta mata but zuwa zatayi ta gaisheta.
Hajiya na kishingid'e a falo ita kad'ai, Su ihsan duk basa nan suna school
"Hajiya ina wuni"
"Lafiya lau,Ya jiki?"
Ba k'aramin mamaki ne ya kama Noor ba ta amsa "Jiki da sauki"
"Toh sannu,Allah ya k'ara lafiya"
"Ameen" Ta tashi ta fito tana mamakin Hajiya, a zuciyarta tana cewa "Lallai Hajiya ta chanza"
Hajiya kuwa a zuciyarta ba abunda ke ciki sai tsantsar tsanar Noor, ba yadda zatayi ne kawai saboda Imran.
Ta dawo d'aki tana ta far'a, Imran yaji dad'in yadda ya ganta, Yau ce rana ta farko da Noor taje wajen Hajiya bata sata kuka ba,ko ta gaya mata bak'ar magana,
Imran ya zuba musu abinchi kowa a plate d'inshi,sukaci tare da mango juice
Nan ya zauna suna hira, Yana tambayarta about school, Kiran sallar la'asar yasa shi mik'ewa ya fita
Noor itama ta mik'e, tayi alwala tayi sallah,tasa uniform d'inta ta nufi islamiyya, A islamiyya ma tayi k'awa Saudat,shekararsu d'aya da Saudat sai dai Saudat ta d'an fita girman jiki,Ajin akwai manya da suka girmi Noor ba kamar boko ba.
Rayuwa haka ta cigaba Noor bata fuskantar wata matsala daga wajen Hajiya ko su Ihsan,Yazeed kuma bai fasa bibiyar taba yana rok'onta ta bashi had'in kai, dan har yanxu masifar sha'awarta yake idan ya ganta ma abun k'aruwa yake, ita kuwa tana nan akan zancenta na ba zata bashi had'in kai ba.
K'unarta ta warke har an cire bandage d'in,Tana maida hankali sosai akan karatun ta both boko da islamiyya, Islamiyya kullum sumuni take bayarwa hadda( Malaman har mamaki take basu,kuma ba'a wani cinta gyara sosai,wataran ma ko gyaran ba'a cinta,Malamai da d'alibai duka suna sonta,kowa burgeshi take), Boko sun fara JSCE,karatu take ba wasa, Imran kuma na helping d'inta ya mata explaining wasu abu da bata gane ba.
A school suna zaune tare da k'awayenta Ilham da kausar, Suna karatu kafin a shiga exam, kawai Noor taji mararta ta masifar murd'awa
"Ya salam! " ta furta, Abu kamar wasa taji mararta ta rik'e tana masifar ciwo kamar zata cire, ta dafe mararta tana kuka, tana kiran Sunan Allah, Ilham da Kausar suka yi kanta suna tambayarta "Lafiya?"
Tace musu "mararta".
Nan suka kamata suka kaita clinic d'in makaranta,Nurse tace "su tsaya daga waje zatayi magana da ita"
Noor nata sharar k'walla
"Me ke miki ciwo?"
Ta nuna mararta dan bata iya magana saboda azaba
"Kina period ne?"
Noor tuni ta zube k'asa tana birgima dan azaba
Nurse ta tsorata da ganinta tace "wannan irinsu ne masu wahalar ciwon mara, har kwantar dasu asibiti ake dan haka tafi k'arfina sai asibiti"
Su Ilham ta kira,sukayi kan Noor suka d'agota suna cewa "Sannu" sai dukansu take tana birgima tana karanta duk addu'ar da tazo bakinta
Nurse kuwa tuni ta fita ta sanar da Principal, Nan take Principal ta kira Imran(dan kowanne student akwai numbern guardian d'inshi,ta sanar dashi halin da ake ciki.
Cikin mintuna kad'an Imran yazo makarantar hankali a tashe, Ya tsorata da ganin Noor sai zufa yake duk ya gama rud'ewa, Nurse yasa ta d'auketa ta kaita mota
Ya figi mota a 360 bai tsaya ko'ina na sai asibitin MANAN(Dangin mahaifina)
Nurses suka kama aka shiga da ita, Yau sunzo a sa'a dan Dr.Aysher basma na nan, ita da kanta tace zata duba Noor ( duk taji tausayinta)
Bayan ta gama dubata,ta bata maganganu hadda nasa bacci, anan take barci ya d'auke Noor, Tana kwance kan lallausar cushion d'in dake office d'in Dr.Aysher mai kamar gado
Imran yace "Dr wai me ke damunta?"
Dr Aysher tace "Ciwon mara ne wanda mata keyi idan zasu fara al'adansu, toh gaskiya ciwon ma ba kowa ne keyi ba, masu yin ma, na wani yafi na wani, kaga in her case ita tana layin masu irin azababban ciwon marar nan wanda idan ba'a ci sa'a ba duk zata yi sai ansa mata drip".
Zufa ta fara k'etowa Imran duk da sanyin Ac dake office d'in
Yace "yanzu ba wani magani da za'a iya mata?"
"Magani d'aya ne a mata aure"
A kid'ime ya kallo Basma Yace "Aure?"
"Ofcourse dats d only solution, but xan bata maganin da zai d'an taimaketa but gsky ku mata aure shine kawai"
Wata zufar da k'ara keto mishi a ranshi Yace "Tana da aure but ba damar Alhaji ya kusanceta, sakinta kuma ba rana, ko an saketa waye zai aureta?" Ya dafe kanshi "yanzu haka Noor zatai tashan wahalar nan, i can't bear to see her suffering" k'walla yaji na k'ok'arin zubo mishi yai saurin mayar da ita
Dr. tace "Ya dai? Naga duk ka tada hankalinka , akwai matsala ne?"
Murmushin dole yayi Yace "No ba komai just ina tausayinta ne"
"Ohh ni zan d'an fita na duba wasu patients, nan da like 30mins zata farka"
"Ok Dr mun gode"
"Ba komai ai" ta fice.
Tsurawa Noor ido yayi ko k'iftawa baya yi, wani irin tausayinta yake ji a ranshi, ga wani abu game da ita dake ratsa dukkan sassan jikinshi, ji yake kamar ya rungumeta just to comfort her.
Bayan minti 30, Noor ta bud'e idonta charaf suka had'u dana Imran, a take zuciyar kowannensu ta buga fat, haka suka zubawa juna ido har na tsawon seconds 30.
Imran ya kawar da kanshi tare da cewa "Noor kin farka? Ya kike jin jikin ki yanxu?"
"Da sauki, ya rage mun ciwo"
"Toh Alhamdulillah" Yana rufe baki, Dr.Aysher tayi sallama ta shigo rik'e da d'anta Aseem
Ta k'araso cikin office d'in tace "patient har kin farka, Ya ciwon? Ya rage?"
Noor tace "eh ya rage but ina ji kad'an kad'an"
"Ok, sannu" Ta juya kan Imran "ko zaka iya excusing d'inmu zamuyi magana"
Imran yace "ok" tare da mik'ewa ya karb'i Aseem a hannunta dan yaron ya burgeshi.
Dr.Aysher cike da tausayin Noor, Tace "kin fara period ne ko this your first time?"
Noor ta zaro ido tace "ban tab'a ba, period na fara ne?"
Dariya ma taba Dr yadda ta zaro ido "kar ki damu ba wani abu bane kowacce mace nayi, nasan kinsan da haka"
Noor ta gyad'a kanta sama, a zuciyarta murna kawai take dama ta dad'e tana jiran wannan rana, Fargabarta ciwon mara da take yanzu haka zatai tashan wahala duk zatayi kenan?, sannan Allah yasa Imran bai san period ta fara ba,
Dr.Aysher ta bata shawarwari sosai tare da bata leda pad hud'u da magunguna kyauta, Ta kira Imran tace zasu iya tafiya, Sun mata godiya sosai a ransu suna yaba kirki irin nata, Imran ji yayi kamar kar ya rabu da Aseem coz yana son yara.
A mota babu yadda Imran bai yi da ita ba, ta bashi ledar yaga magungunan da aka bata tak'i tace mishi "ai ba sai ya gani ba, Dr ta mata bayanin komai", Ba komai ya sata k'in bashi ba sai dan kar yaga pad d'in dake ciki, Ya gane shiyasa kawai ya k'yaleta, Da suka dawo gida, Imran yai saurin fita ya zagaya ya bud'e mata k'ofa
Tazo fitowa leda ta fad'i pad d'aya ta fad'o, Da sauri ta duk'a ta d'auka tana b'oyewa cikin hijabi, kasa d'agowa tayi dan wani masifar kunyar Imran taji, Shi dariya ma ta bashi,ganin tak'i d'agowa, Ya juya ya wuce abunshi dan yasan in dai yana tsaye ba zata tashi ba.
Sashen Hajiya ya nufa, tana zaune falo kamar kullum ita dasu Yazeed suna hira, "Mum ina wuni?"
"Lafiya lau Son,ina ka shiga ne? ina ta kiran wayarka baka picking"
"Am sorry mum nakai Noor asibiti ne"
"Me ke damunta?"
"Ciwon mara" , "Allah ya bata lafiya", " Ameen"
Yazeed naji an ambaci ciwon mara yai murmushi Yace "very good, shegiyar itama sha'awa ta fara damunta, na kusa cimma burina" yai wata dariya dad'i ya lullub'e shi,
Hajiya ta cigaba da cewa "Zancen aurenka da Khairat, duk da Khairat yar'uwarka ce but a al'adance ana kai kayan an gani ana so, toh dan haka za'a kai daga nan iyaye zasu zauna a tattauna asa ranar aurenku dan hadda sadaki za'a kai, na riga nayi magana da Alhaji shi kuma ya sanar dasu Bawa( k'anin Alhaji), Jibi In shaa Allahu zasu tafi"
Imran kamar ana soka mai kibiya haka yake jin zancen Hajiya, idan yana k'aunar mutuwarshi yana k'aunar aurenshi da Khairat, ya tsani zancen aurensu
Hajiya tace "kayi shiru"
"Eh! Naji Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
"Ameen" Ya mik'e ya bar falon rai a b'ace
Hajiya ta lura da yanayinshi a ranta tace "ko ka k'i ko kaso sai ka auri khairat"
Khairat dake gefe sai washe baki take, murna duk ta cika ta.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣4⃣
D'akinshi ya nufa,ya rufe kanshi gaba d'aya ya rasa inda zai sa kanshi yaji dad'i, da matsalar Noor zai ji, ko da auren da ake so a had'a shi da Khairat, Why mum zata mishi auren dole? He is still young yana da lokaci kwata-kwata ba aure a tsarinshi yanzu,
Fridge ya bud'e ya d'auko bottle na ruwa, ya kwankwad'a ko zai ji sanyi a ranshi still zuciyarshi sai tafarfasa take, Kan gado ya kwanta yana kallon ceiling da tunani birjik a ranshi.
Noor kuwa yana tafiya ta mik'e jiki a sanyaye ta nufi d'aki, Kwanciya tayi kan katifarta coz har yanzu tana jin ciwon kad'an-kad'an, ga jikinta yayi weak, A ranta tana tunanin yadda zata iya k'ara had'a ido da Imran dan yanzu masifar kunyarshi take ji.
Har dare Imran na d'aki bai fito ba, Sallah kad'ai yake tashi yayi ya koma ya kwanta, Yana so yaje yaga Noor yana tunanin ko yaje ba zata bari su had'u ba, dan yasan yanzu kunyarshi take ji.
Noor kuwa rashin shigowar Imran ba k'aramin dad'i ya mata ba, Tea kad'ai tasha tasha magani, Ta kwanta but ta kasa barci.
*9:30pm*
Yazeed ne ya fito daga sashen su, Ya nufi d'akin Noor( ohh ni zainab amma Yazeed da nacin tsiya kake), Yana murd'a k'ofar ta bud'e (ta manta bata rufe ba) Yayi murmushi a ranshi Yace "yau har da barin k'ofa a bud'e, wato jirana take nazo"
Ya k'arasa cikin d'akin, Tana kwance ta d'aura hannu d'aya kan mararta, Ya zauna kan katifar yana lasar baki yana murmushi, Da sauri ta tashi zaune tace "Lafiya? Me kake mun a d'aki? Maza tashi ka fita kafin na maka rashin mutunci"
Ya fashe da dariya Yace "me ye na d'aga murya, dama ance tabarmar kunya da hauka ake nad'eta me ye na pretending, nasan abunda ke damunki ki taimaki kanki kawai kizo mu hole"
A fusace tace "me ke damuna? Ni dallah tashi ka fita bunsuru kawai"
Ya sake fashewa da dariya "me ke damunki kuwa banda sha'awa ,gashi kina ciwon mara"
Da sauri ta toshe kunnuwanta, ta rufe idonta tace da k'arfi "Ka fitar mun a d'aki ko na maka ihun kwarto"
Jin haka yai saurin mik'ewa yace "waitt....abun duk be kai ga haka ba dama zuwa nayi muyi helping juna, ni zan tafi ki zauna kiyi shawara"
Yasa kai ya fice.
Dafe kai tayi tace "Yanzu Imran zuwa yayi yana fad'a ga ciwon dake damuna, Ya Allah! Kasa shima ba tunanin da yake mun ba kenan, Yazeed kuma ina rok'on Allah kai mun tsari dashi"
Ganinta da Imran bai yi yaji duk yayi missing d'inta, Yayi shirin office tsab sanye yake da manyan kaya da suka masifar yi mishi kyau, Sashen Hajiya yaje bayan sun gaisa, ya nufi d'akin Noor
Tana zaune rik'e da hisnul muslim tana azkar
Tana jin sallamarshi gabanta ya fad'i, tai saurin juya mai baya, Murmushi kawai yayi, ya gane har yanzu kunyarshi take ji
"Noor ina kwana?"
Ba tare da ta juya ba ta amsa "Lafiya lau"
"Ya jiki?
"Da sauki" , "Ni zan wuce office" , "Allah ya kai lafiya" (daurewa kawai take tana bashi amsa dan ta matso ya bar d'akin)
"Ameen" (yaso ganin fuskarta kafin ya tafi).
Rayuwa haka ta cigaba, Su Alhaji sun je, Manya sun zauna an tattauna ansa biki nan da wata uku, Ranar Imran ji yayi kamar ya had'iyi zuciya ya mutu dan bak'in ciki, Noor kuwa tasha kuka kamar ranta zai fita, tana cewa yanzu shikenan nan da wata uku zata rabu da Imran, Gashi tunda aka sa rana Khairat ke k'ara shisshigi mai.
Soyayyar da suke ma juna sai dad'a ruruwa take ba tare da sun sani ba, Imran wani irin masifar so yake ma Noor, baya iya komai ba tare da yayi tunaninta ba, kusan kullum sai yayi mafarkinta, kullum so yake yai ta jinta kusa dashi, yana jin muryarta komai nata so yake, idan abu ya sameta gaba d'aya rud'ewa yake ya shiga tashin hankali, Tsayawa bayyana muku irin masifar son Noor da ya kama Imran b'ata lokaci ne, kowacce kawai ta ayyana irin azababben son da zuciyarshi ta kamu dashi na Noor.
Abun ya fara damunshi har ya fara fita hayyacin shi *SO*, Yana zaune office ce kad'ai ba abunda yake sai tunanin Noor, Yana kallon hotonta da ya d'auketa ranar da zata fara zuwa makaranta, Tambayar kanshi yake "Me yasa nake jin haka game da Noor? Me ye wannan nake ji?, Dole in sanar da Naseer,abun har yana so ya tab'a lafiyata"
Mik'ewa yayi ya d'auki mukullin motarshi da waya.
Ya figi mota sai gidansu Naseer,
Naseer na zaune falo yana kallo, "Abokina lafiya? Ya na ganka haka kamar ba'a hayyacinka ba"
"Hmm! Wlh Friend ba lafiya ba, ina cikin wani yanayi"
"Subhanallah! Me ya faru?"
Nan ya fad'a masa komai game da Noor, Amma bai fad'a mishi matsayin Noor a wurinshi ba
Naseer ya fashe da dariya yace "My friend you are in love, Who is the lucky girl da ta rud'a mun aboki"
Imran idonshi tuni ya kad'a yayi jajir bai tab'a jin tashin hankali irin na yau ba, bai san sanda ya furta "How can i fall for my father's wife, Me zai sa na SO matar babana Why? Why?"
Naseer da ya kasa fahimtar abunda abokin nashi ke cewa Yace "what? What are you saying Imran"
Ya kamu hannun Naseer gam ya rik'e yana hawaye Yace forgive me friend, i have been hidden something from you ba dan komai ba sai dan na kare mutuchin mahaifina"
Naseer cikin rashin fahimta yace "me kake cewa ne frnd, ni fah ban gane ba"
Nan ya fad'awa Naseer tun farkon aure daddy da Noor har zuwa yanxu
Naseer ya masifar girgiza da jin zancen at d same time ya tausayawa abokinshi
Yace "friend diz is a very serious issue, ka fad'a tarkon Son matar babanka, we have to find a way out"
Imran na hawaye yace "ya zanyi friend, am madly in love with her, yadda nake ji yanzu bazan iya rayuwa babu ita ba"
Naseer ya dafe kanshi yace "Ya salam! SO bai maka adalchi ba abokina,son matar babanka is a big crime".
Imran nata hawaye, Zuciyarshi na tafarfasa kamar zata fito waje
Naseer nata lallashin shi "Kayi hak'uri abokina, we will find a way out"
Imran ya mik'e Yace "i have to go home now"
"Ok abokina plx ka kwantar da hankalinka, zamu samu mafita In shaa Allah"
Kai kad'ai ya iya d'aga mishi, Ya mishi rakiya har bakin mota yana k'ara bashi baki, Naseer ya dawo cikin gida cike da tausayin abokinshi
Imran driving yake kwata-kwata hankalinshi baya jikinshi, Allah ne ya tsare ya kawo shi gida lafiya.
Rufe kanshi yayi a d'aki, Yana kuka yana magana shi kad'ai " Why? Why? Zan fad'a tarkon son matar babana, I deeply love her me zai sa na fara son matar da ba aure tsakaninmu? In rasa wacce zan fara so sai matar Daddy", Kanshi ya fara bugawa a bango yana "ya zanyi da raina?, how can i survive without her? Taya zan cire sonta a raina, Zuciyata ta kamu da masifar sonta, Why? Zan fara sonki Noor kina matar babana, tabbas wannan ITACE K'ADDARATA son matar mahaifina, Nan ya fara jefar da kayan d'aki yana fashe-fashe yana buga kanshi a bango, Kwalbar da ya fasa ya d'auko, Yana tsaga hannunshi ko zai rage zafin rad'ad'in dake zuciyarshi, hannunshi nata jini ko kad'an baya jin zafin yankar, Zuciyarshi kawai ke tafasa, Kan gado ya fad'a duk ya fita hayyacinshi a yan' awanni
*ME YE FITA YANZU?*
Wata zuciya tace mishi "Dole ka nisanta kanka da Noor na tsawon lokaci i think thats d only way da zaka cire sonta coz idan kana ganinta sonta k'aruwa zai cigaba dayi"
Wayarshi ya d'auka ya kira Naseer yace "Yazo gidansu yanzu zasu yi wata important magana".
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣5⃣
*This page is for you Ridallah, Nagode da kulawarki😍, Allah ya biyaki, I cherish yhu dear❤*
Mintuna kad'an Naseer ya iso gidan
Ya tsorata da ganin yadda Imran ya haukata d'akinshi ga hannunshi nata jini, Ya k'arasa inda yake, Ya rik'o shi "Friend me yasa kama kanka haka? Haba! Frnd tashi muje chemist a maka dressing hannun",
Imran ya girgiza kai Yace "No! ba dan shi na kira ka ba,rad'ad'i da nake ji a zuciyata ya ninka zafin ciwon nan sau dubu"
"Nasan da haka but ka bari muje a maka dressing,ji yadda hannunka ke bleeding" ya k'arasa maganar cike da damuwa
"Don't worry, bari na fad'a maka dalilin da yasa na kira ka"
"Ok ina jinka"
"Na yanke shawarar barin k'asar nan".
A kid'ime Naseer ya kallo shi Yace "Why?", "Dan in nisanta kaina da Noor, nasan idan nayi nisa da ita na tsawon lokaci zan cire sonta a raina,but idan ina ganinta kusa dani sonta k'aruwa zai cigaba da yi wanda hakan ba k'aramin cuta bane a gareni kuma zan sab'awa Allah".
Naseer yayi ajiyar zuciya Yace "tabbas hakane kawai mafita, but me zaka cewa su Hajiya? ,and ita Noor kayi yaya da ita tunda bata da kowa sai kai?", Imran ya nisa Yace "zan tafi Turkey ne yin masters d'ina dama tuntuni ya kamata na tafi, so ko nace musu zan tafi ba zasu zargi komai ba, Noor kuma tana tare da Allah, i will make her understand ba barinta nayi ba, sannan zan bar amanarta a hannunka, please Naseer ka kula da Noor ka dauk'eta tamkar Meenal(k'anwarshi)"
"In shaa Allahu na maka alk'awari zan rik'eta amana, Yaushe zaka tafi?"
"Gobe In shaa Allah"
"Haba! Friend gobe fah, ba zaka bari sai jibi ba"
"No am leaving tomorrow, the earlier the better, muje ka rakani office na sanar dasu"
"Ok muje daga nan a maka dressing hannun".
Chemist suka fara tsayawa aka ma Imran dressing hannunshi, Sannan suka nufin office, MD ya samu ya mishi bayani zai koma ya cigaba da karatu, Md yace "ba wata matsala( dama abokin Alhaji ne) Allah ya taimaka ya bada sa'a yasa a k'aru ilimi mai amfani"
"Ameen nagode sir"
Ya bashi cheque d'in dubu d'ari Yace "yasha ruwa a hanya"
Sosai ya mishi godiya sannan ya tafi.
"Imran yana ganka haka duk ba a hayyacinka ba, kamar wani mai ciwo,me ya samu hannunka?"
Yayi murmushin yak'e yace "bacci nayi, hannuna kuma ina yanka lemo na yanke"
"Ayyah, Sannu Son"
"Yawwa mum"
"Dama ina so na koma turkey nayi masters d'ina"
"Kaii amma naji dad'in wannan zance tuntuni nake so ka tafi kayi masters d'in nan, Yanzu yaushe zaka tafi?"
"Gobe In shaa Allah"
"Gobe Goben nan?"
"Eh" , "Toh Allah ya kaimu, yasa a k'aru ilimi mai amfani"
"Ameen" , "Zancen aurenku da Khairat fah, kasan nan da wata uku ne"
"Zan dawo idan lokacin yayi", "Toh Allah ya tabbatar mana, ya kuma nuna mana lokacin amma zamuyi kewar ka"
"Ameen" kad'ai yace, Ya mik'e ni zanje na cigaba da shirye-shirye ( baya son doguwar magana,coz shi kad'ai yasan pain d'in da yake ji a zuciyarshi,he want to be alone).
Kwance yake d'aki yana tunanin yadda zai tunkari Noor da zancen tafiyarshi gobe, bai san a halin da zata tsinci kanta ba idan taji zancen nan, tabbas idan ya gaya mata zata shiga tashin hankali, tashin hankalin da zata shiga zai iya chanza mishi ra'ayi ya fasa tafiya dan bazai iya jure ganinta haka ba,
Mik'ewa yayi ya d'auko paper da biro ya fara rubutu kmr haka:
_Assalamu Alaikum, Dafatan kina lafiya, Bansan taya zan fara fad'a miki ba,kiyi hak'uri da abunda zan gaya miki,Zan tafi masters d'ina yau,bazan iya fad'a miki baki da baki ba sbd bana son ganin damuwarki shiyasa na rubuta miki a letter, ki sani Noor ba da son raina zan tafi na barki ba sai dan tafiyar ta zama dole, But zan dawo idan komai ya daidaita,ki kula da kanki Noor Allah na tare dake, kuma ga Naseer nan Aminina zai maye miki gurbina, Ina miki fatan Alkhairi da samun farin ciki a rayuwarki, kimun alk'awari idan kin gama karanta letter nan ba zakiyi kuka ba ko ki tada hankalinki, idan kinyi zanji a jikina dan haka nake rokonki kar kiyi, Allah na tare dake_
_IMRAN_.
Yana hawaye ya nannad'e letter, ya jawo bedside drawer yasa, Ya mik'e ya nufi sashen Alhaji,
Alhaji yayi farin ciki sosai da jin Imran zai koma karatu, yasa mishi Albarka tare da mishi fatan Alkhairi.
Noor kwance take ta rasa me ke mata dad'i, kwata-kwata bata jin dad'in jikinta, Gabanta nata fad'uwa, Ga rashin shigowar Imran tun safe da ya shigo bai k'ara shigowa ba, duk ta damu shi kawai take son gani,
Shiru har dare bata ganshi ba, ta fara tambayar kanta "Lafiya Imran bai shigo ba?, ko dan yaga ina jin kunyarshi? " Tasa ma ranta tabbas dan yaga tana jin kunyarshi ne, but gobe da safe idan bai lek'o ba zata cire kunyarshi taje da kanta sashen, dan ba zata iya jure rashin ganinshi ba( Wayyo Noor har kin fara bani tausayi😰)
Haka tayi bacci da tunanin Imran a ranta.
Imran ya had'a komai da komai nashi, dama ba wasu kaya mai yawa ya d'iba ba, idan yaje can zai siya
Daren ranar kasa bacci yayi, yana ta mirgine-mirgine a kan gado, da ya rufe ido Noor yake gani, Ya rungume pillow tsam, Yana kukan So,k'auna da zafin Rabuwa da Noor.
Ana kiran assalatu ya tashi yayi alwala, ya fara gabatar da raka'atanil fijr, sannan yayi Sallah, A sujada yana rok'on Allah ya cire mai son Noor, Yasa tafiyar nan da zai yi shine mafi alkhairi a gareshi, Wanka ya shiga yayi, Ya shirya cikin english wears, sun mishi kyau but daka kalleshi zaka san yana cikin tsantar damuwa,
Naseer yai sallama ya shigo,.
Bayan sun gaisa Yace "ka dai shirya ko kasan flight d'inku k'arfe 7 ne"
"Eh na shirya"
"Kayi sallama da Noor kuwa?"
"Wallahi banyi ba, dan bazan iya fad'a mata but ga letter na rubuta mata" Ya jawo drawer ya fiddo letter yasa a aljihu.
"kana ganin hakan yafi"
"Yes friend"
"Ok muje".
Naseer ya nufi wajen motarshi, Imran kuma yayi d'akin Noor, gabanshi na fad'uwa, Cikin sanyin murya jiki a sanyaye, Yayi sallama ya shiga d'akin
Noor dake kwance ta tashi zaune, tare da amsa sallamar.
Yana daga tsaye Yace "ina kwana? Ya jiki?"
Ganin yanayinshi tasan ba lafiya ba( a ranta tace ko dai Imran bashi da lafiya ne?) A fili ta amsa "Lafiya lau"
Ba tare da ya k'ara ce mata komai ba ya zaro letter ya mik'a mata, itama bata ce mishi komai ba, ta k'arba
Ya juya ya fita yana hawaye.
Su Hajiya duk sun fito za'a tafi rakiya hadda Alhaji, Imran kam jiki a sanyaye, Hajiya sai da ta tambayeshi "me ke damunshi?"
Yace "ba komai"
Khairat ma jikinta duk yayi sanyi, bata son tafiyarshi hadda yan' matan hawayenta.
Noor yana fita tai sauri bud'e letter tana karantawa, Hankalinta ne yayi mummunan tashi sai hawaye, ta jefar da takardar, a guje ta fito, ko da ta fito har sun tada mota mai gadi ya bud'e musu gate
Da k'arfi ta kira sunanshi IMRAN, but its too late motar su ta riga ta fita,
Nan ta fad'i tana kuka kamar ranta zai fita.
*Nima Zee sai da nayi k'walla dan Noor ta bani tausayi, na koma gefe na d'auko wayata na kunna wak'a:*
_Kuji bana so bana son kalmar RABUWA kuji bana so bana son kalmar RABUWAAA, Bana so so bana sooo bana so bana so so bana soo bana son kalmar nan da ankace RABUWA tunda soyayyata dake akwai dad'i_🎤🎧🎼🎹
Ina saurare ina taya so kukan RABUWA😭
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*
😘🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣6⃣
*This page is for yhu beloved Sis Ya hajja😘, Ina tayaki murnar kammala littafinki BABBAN SIRRI it was such an amazing,marvelous,exceptional novel, Allah ya k'ara basira,Ya kare mana ke, Allah ya raya mana Ihsan😍, I so much love yhu❤❤❤*
Har suka isa airport Imran bai ma kowa magana ba, Ba abunda Zuciyarshi ke yi sai tafasa, Yana ji a jikinshi Noor na can cikin tashin hankali but bashi da yadda zai yi dole ya tafi ya barta.
Ko da suka isa har an fara kiransu, jirginsu zai tashi,
Ya kalli Hajiya yace "Mum please ki mun alk'awari idan na tafi, ba zaki cigaba da sa Noor aiki ba" kamar zai yi kuka duk ya zama abun tausayi
Gaba d'aya tausayinshi ya kama ta tace "Na maka alk'awari Son"
"Nagode sosai Mum"
Ya juya kan Naseer "Friend Dan Allah ka rik'e amanar da na baka"
"In shaa Allah Frnd, na maka alk'awari"
Khairat ta marairaice tace "Yayana plx kana isa ka kirani naga numberka ta can"
Kai kawai ya d'aga mata,
Nan yayi sallama dasu, Yazeed duk yaji ba dad'i zai yi missing Yayanshi
Suna ta waving d'inshi har ya b'ace musu, Suka juyo suka dawo jiki a sanyaye.
Noor kuwa tunda suka tafi take nan durk'ushe tana kuka, Zuciyarta na mata masifar zafi, mai gadi yazo yayi ta lallashinta ta tashi, tayi banza dashi har ya gaji ya tafiyarshi ya barta nan.
Anan su hajiya suka dawo suka tarar da ita, bata ishi kowa kallo ba, Yi sukayi kamar basu san da ita ba, Khairat kad'ai ce tace "ko ke kika haife shi sai haka,munafucin banza" tai tsaki ta wuce ciki abunta.
Naseer ne ya k'araso inda take, Ya durk'usa gabanta duk ta bashi tausayi "Noor" Ya kira sunanta
A hankali ta d'ago ta kalleshi
Take yaji gabanshi ya fad'i tunda yake bai tab'a ganin kyakkyawa kamar Noor ba, a ranshi Yace "Dole Imran ya fad'a tarkon sonta, bai ga laifinshi ba"
Yayi saurin kawar da tunanin Yace "Please ki kwantar da hankalinki Noor, Allah na tare dake kuma zan maye miki gurbin Imran In shaa Allah".
Cikin muryarta da ta dashe tsabar kuka tace "Me zai sa Imran ya tafi ya barni? Bayan yasan bani da kowa sai shi, Yasan tafiya zai yi ya barni me yasa ya bari muka shak'u?" Ta sake fashewa da matsanancin kuka.
Tausayinta ya sake kama Naseer "Please Noor kar kiga laifin Imran, wlh ba da son ranshi ya tafi ba, ina mai tabbata miki yafi ki jin zafin rabuwarku, yana da babban dalili da yasa ya tafi"
"Wane dalili ne dashi? Dama duk cewa da yake zai kula dani ba zai tab'a barina ba, ashe duk karya ce"
"No! Noor kar kice haka, kar kiga laifin Imran, nan gaba zaki san dalilin shi nayin haka"
"Hmm" tace ta fara share hawayenta ta cigaba da cewa "Bai kamata na cigaba da zubar da hawayena a banza ba akan wanda bai damuna dani ba, ko da yake yama ce kar nayi kuka ko na tada hankalina which means yin hakan bashi da amfani, Imran baka mun adalchi ba"
"Kar kice haka Noor, ba wanda ya tsani ganinki cikin damuwa kamar Imran, tun jiya yake kukan rabuwa dake, har ya tafi kuka yake".
Tayi murmushin takaici tace "kai dai kawai kana kare abokin ka ne, da ace Imran da gaske yake baya son rabuwa dani bazai tafi ya barni ba, no matter the situation bayan yasan yadda nake a gidan nan"
Naseer yayi ajiyar zuciya Yace "Hmm! Noor kenan ki sani babu mai sonki da tausayinki kamar Imran, duk abunda zance miki ba zaki gane ba but ina fatan nan gaba ki gane"
Murmushin takaici tayi tace "Hmm! Ni zan koma cikin gida"
"Ok plx ki daina damun kanki, ki kwantar da hanklinki, am here for you"
"Ok nagode da kulawarka"
"Ba komai sai na dawo anjima".
Kan kafita ta fad'a ta cigaba da kuka mai tsuma rai, duk yadda taso ta tsayar da kukan ta kasa, Zuciyarta na mata zafi da rad'ad'i, Tana tambayar kanta "wane dalili ne zai sa Imran ya tafi ya barta?, Yanzu ya zatayi rayuwa a gidan nan ba Imran? Tabbas Imran ya zama wani sashe na rayuwata wanda rashin shi kusa da ni babbar matsala ce a gareni, Imran me yasa zaka tafi ka barni a lokacin da nafi buk'atar ka?, baka mun adalchi ba, da kasan barina zakayi da baka bari mun shak'u ba".
Mik'ewa tayi, tayi alwala, ta kabbara sallah tana rok'on Allah ya cire mata duk wani abu da take ji a ranta game da Imran, Allah yasa tafiyarshi shine mafi alkhairi a gareta".
Imran a cikin jirgi zaune yake jigum, Ya rufe ido kamar mai bacci, ba abunda yake sai tunanin Noor, Wane hali take ciki yanzu? Ya rayuwarta zata kasance idan bashi? Shi kanshi bai san ya rayuwarshi zata kasance babu ita ba?, but ya zama dole ya nisanta kanshi da ita, Wasu zazzafan hawaye suka fara zubo mishi.
*kuyi hakuri da kadan din nn plx, wlh abubuwa sun mun yawa*
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣7⃣
Noor nan ta zauna kan dadduma tana karatun Qur'ani, Kanta taji na masifar sarawa kamar zai cire, Ta rufe Qur'anin ta ajiye, Panadol ta d'auka tasha, Ta kwanta but still ji take kanta yayi nauyi, Zuciyarta na d'aci.
Hajiya ta kira yan gidan daga kan masu aiki zuwa su Yazeed tace musu "Daga yau Noor bata cikin mutanen gidan nan, su d'auka cewa babu wata mai suna Noor a gidan nan, bata so taga kowa ya shiga harkarta, ko abinchi kar wanda ya kuskura ya bata, She is on her own "
Duka suka masa da "Toh" Su Ihsan sunso abar su, su cigaba da azabtar da ita, Yazeed hakan dad'i ya mishi, a ranshi yace "idan ta matso ba mai kula da ita, yunwa ta addabeta dole ta bani had'in kai ko dan na taimaka mata"
Naseer da masifar tausayin Noor ya koma gida, Ya cewa kanshi "Tabbas Noor na buk'atar kulawa, nayi alk'awari In shaa zan maye mata gurbin Imran, duk wani kulawa In shaa Allah zan bata, da ba igiyar aure a kanta da nan gidan zai maidota but duk da haka zanyi iyakacin k'ok'arina"
Bacci ya koma, ya d'anyi na 30mins sannan ya tafi office, Office d'insu d'aya da Imran.
*Waye Naseer?*
Naseer d'a ne ga Alhaji Isma'il Borno, Asalinsu yan borno ne, Mahaifinshi hamshak'in mai kud'i ne, dan yafi Baban Imran kud'i,Sana'ar man fetur yake, Yana da gidajen mai wanda duk Naseer ke tafiyar dasu, Ya mallakawa Naseer d'aya daga cikin gidajen, Hajiya Asma'u itace mahaifiyarshi, itama asalin yar'borno ce, Yana da Yaya d'aya mace Sameera tayi aure, Sai shi Naseer d'an gaban goshin Ummi da Abba, Meenal ita ke bi mishi tana Ss2 sai autarsu Salma tana js1 suke nn iyayensu suka haifa, Kyawawa ne, su farare, amma suna da kyau sosai, Iyayensu naji dasu, Sun d'au son duniya sun d'aura akan su, Suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali, ga girmama da mutunta junansu, ba wata matsala da suke fuskanta a familynsu.
Naseer da ya taso daga office, Restaurant ya biya, Ya siyo take-away da lemun kwali guda biyu masu sanyi,
Ya nufi gidansu Imran
A harabar gidan yayi parking, Ya kira mai gadi Yace "ya kira mishi Noor".
Noor bata je school ba, kwance kawai take da tunani birjik a ranta, Tayi tayi ta cire tunanin Imran a ranta ta kasa
Mai gadi yayi sallama yace "Tazo inji Naseer" , ta amsa da "Toh".
Bakin motar ta tsaya, Ya bud'e k'ofa ya fito, tare da jingina jikin motar, Murya a sanyaye tace "Sannu, Ina wuni?"
"Lafiya lau Auntynmu"
Ya tsura mata ido, _Masifar kyanta yake gani_, Yace "Ya school? , har kin dawo?"
"A'ah banje ba"
Ya d'an zaro ido waje Yace "Akan me baki je ba?"
"Imran ke kaini dama"
Ya d'an dafe kanshi yace "Oops! Am sorry na manta, daga yau driver dake kai su Meenal makaranta zai rik'a zuwa yana kai ki, yana d'auko ki"
Tayi murmushi tace "toh nagode"
"Aah kar ki mun godiya, ki d'aukeni tamkar Imran"
Kai kawai ta d'aga mishi, a ranta tace "Ba zaka tab'a maye mun gurbin Imran ba, matsayinshi daban ne a zuciyata"
"Ina fatan kin cire duk wata damuwa a ranki?"
Ta d'aga kanta sama
"Yawwa haka nake son ji".
Ya bud'e mota ya fiddo ledan take-away da lemu, Ya mik'a mata Yace "Gashi nan, nasan ba'a baki abinchi ba tunda Imran baya nan"
Tayi murmushi tace "Ai da ka barshi"
Ya d'an b'ata fuska Yace "da Imran ne haka zaki ce mishi"
Tace "Am sorry"
Yace "Apology accepted, but kar ki k'ara"
Ta gyad'a kanta tare da sakin murmushi
_Murmushinta ba k'aramin burgeshi yayi ba_
Ya mik'a mata ledar, ta karb'a
Yace "Ni zan tafi sai na dawo anjima"
"Toh sai anjima nagode"
Ta juya ta tafi, Ya bita da kallo yana murmushi, Yana sak'a abubuwa a ranshi.
Imran suna isa, Ya siya sim, Ya fara kiran Naseer
"Assalamu Alaikum"
"Wa alaikassalam mutane turkey Ya hanya?"
"Alhamdulillah! Ina Noor? Ina fatan bata damu kanta ba?"
Naseer yayi murmushi yace "Noor na nan lfya lau, bata cikin wata damuwa"
"Are you serious?, kar ka mun karya dan ka kwantar mun da hankali"
"Friend believe me, gaskiya nake gaya ma, ko d'azu naje wurinta"
Yayi wata sanyayyar ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah! Plx abokina ka kula da ita, idan ka kula da ita ka gama mun komai a duniya"
"Kar ka damu frnd"
"Ok tnx, bye sai mun sake magana"
"Ok bye"
Ya kashe wayar yana tunanin yadda Imran ya damu Noor.
Ta b'angaren Imran, taxi ya shiga ta kaishi hotel, kafin gobe ya nemi gidan da zai zauna,
Ruwa ya watsa, yayi sallolin da yayi missing, kasa cin komai yayi, Ruwa kad'ai yasha, Ya kwanta ya rufe ido ko bacci zai zo ya kasa, tunanin Noor kawai yake, ba wanda yake son gani kamarta, Ji yake kamar yai ta buga kanshi a bango ko zai ji sassaucin abunda ke damunshi a zuciya.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣8⃣
Naseer naba Noor duk wata kulawa da ta dace, Duk bayan kwana biyu sai yayo mata siyayya na gani na fad'a, tun bata sakin jiki dashi, Yanzu har sun saba sosai, ( _Tana mamakin kirki irin nashi kmr imran hka yake tausayinta, yake ji da ita_), Kullum yakan zo gidan sau uku sau hud'u, Shi ke kawo mata abinchi, Watarana kuma k'anwarshi meenal ke kawo mata kuma takan zo su sha hira, Sun saba sosai da meenal, Makaranta tana maida hankali sosai, Naseer na k'ara mata k'arfin gwiwa kan tayi karatu, zata ga amfaninshi nan gaba, Sun kusa gama JSCE.
Noor bata fuskantar wata matsala da su Hajiya sun fita harkarta, basu ma san da zamanta gidan ba,Duk da haka ta kasa kwantar da hankalinta, tunanin Imran da kewarshi ya mata yawa, dashi take kwana, ta tashi a ranta, ko na second d'aya ta kasa manta shi, kullum sai tayi kuka, Addu'arta itace Allah ya cire mata Imran a ranta amma kamar addu'a take Allah ya k'ara mata, kullum da irin yadda take ji game dashi.
Imran kullum sai ya kira Naseer yaji lafiyar Noor, a rana ya kira shi sau uku, Safe rana dare
Naseer yace mishi tana nan lafiya lau, bata cikin damuwa ko matsala
Sai yaji dad'i da sanyi a ranshi, kud'in makarantar ta yace zai rik'a aikowa, Naseer yace ya barshi, zai d'auki nauyin duk wata lalura tata,
Imran yaji dad'i sosai yana mishi godiya, Naseer yace mishi ba komai, ba abunda ba zai iyama Noor ba, dan shima yana tausayinta
Imran yai ta godewa Allah, Idan ba Naseer da bai san ya rayuwar Noor zata kasance ba.
Imran yana zuwa makaranta ne amma baya maida hankali, Duk ya rame abinchi da k'yar yake ci, Son Noor k'ara ruruwa kawai yake a ranshi, Ko kad'an ya kasa cireta a ranshi, ko walwala bai cika ba, Murmushi kad'ai yake ma mutane, har wasu na cewa shi wannan baya dariya.
Kwata-kwata duniyar ta mishi zafi, baya jin dad'inta ko kad'an, Har ji yake dama ya mutu ya huta, daya cigaba da son wacce har abada ba zai tab'a aurenta ba.
Yazeed yanzu ba sha'awar Noor kad'ai yake ba, Ya kamu da masifar sonta farat d'aya, dashi kanshi bai san lokacin da ya kamu dashi ba ( _nikm Zee nama rasa ta cewa_ 🤐🤐), Duk yan'matanshi bai tab'a jin yana son wata ba sai dai sha'awa, but yanzu ya kamu da ciwon son Noor, yadda yake ji idan ya rasa ta mutuwa zai yi.
Yayi ta k'ok'arin ya gaya mata Son ta yake yanzu ba sha'awa ba tak'i bashi fuska, Da ya fara magana zata bar wurin, ko tace zata mishi ihun kwarto, Ya rasa yadda zai yi da sonta a ranshi, duk ya shiga damuwa, Tunaninshi d'aya yadda zai yi Alhaji ya saketa shi kuma ya aureta( abunku da mara ilimi, Yazeed ba abunda ya sani ta fannin addini, dan ba islamiyya yake zuwa ba), Ya sawa ranshi da Alhaji ya saketa, Shikuma zai aureta ko tana so ko bata so.
Naseer kwance d'akinshi ya rungume pillow tsam, Ya lumshe ido, Ba wacce yake tunani sai Noor, Maganarta yake ji a kunnuwanshi, Yana hango kyakkyawar fuskarta yanayin tafiyarta,murmushinta infact komai nata, Yana jin nishad'i
Tun ranar da ya fara ganinta, Ya kamu da azababben sonta, haka yake jinshi kamar zautaccen akan sonta ( _Toh fah😳 Kai ma Tirk'ashi gaskiya Noor u get white blood_😉).
Sonta yawo yake a jinin jikinshi, yadda yake ji zai iya rasa ranshi a kanta, Tunaninshi yadda zaiyi Alhaji ya saketa, Alhaji na sakinta zai fito ya nuna mata irin tsananin sonta da yake,zai koya mata yadda zata so shi, ya aureta Suyi rayuwa mai dad'i, ya bata duk wani jin dad'i da kulawa, Yacewa kanshi "Tabbas idan na auri Noor na taimaki Imran, sai yafi kowa ji dad'in haka" ( _a tunaninka kenan, amma ni nasan sai yafi kowa bak'in ciki_).
Noor ta dawo daga school ta gaji sosai, Ruwa ta watsa, Ta saka atamfa riga da skirt (wacce Naseer ya d'inka musu ita da Meenal)
Atamfar ta mata kyau sosai,
Ta d'auko wayarta wacce Naseer ya siyan mata tana game, ko da wasa bata tab'a cewa a bata numbern Imran ta kirashi ba, bata ga amfanin kiranshi ba tunda ya zab'i tafiya ya barta, kuma da yana son waya da ita zai kira, ta wayar Naseer su gaisa a cewarta.
Wayar tayi ringing, Naseer ke kira, bata yi picking ba( tasan yazo kenan, idan yazo kiranta yake sai ta fito)
Gyale ta yafa, tayi kyau sosai, tayi fresh yanzu ba wahala, sai dai ta rame saboda kewar Imran.
Tana fitowa, Sukayi kacib'us da Yazeed
Tuni ya rud'e, ta mishi masifar kyau, Murya na rawa Yace "Ina wuni?"
Ta galla mishi harara, ta wuce abunta
Ya bita da kallo, Sonta da sha'awarta nabin duk ilahirin jikinshi, A ranshi yace "wlh Noor sai kin zama matata, sai nayi yadda zanyi Alhaji ya sake ki".
Naseer na jingine jikin mota, Yayi folding hannunshi, Naseer ma ba daga baya ba, Ta fannin kyau da had'uwa, Ya hangota tana tafiyarta mai d'aukar hankali,
Ya kasa d'auke idonshi a kanta, A ranshi cewa yake "Allah ka mallaka mun Noor, ta zama mata a gareni uwar yayana, Allah ya kawo sanadiyyar rabuwarsu da Alhaji"
Tana k'arasowa k'irjinshi ya hau dukan uku-uku, tsabar sonta.
Ita kanta sai da ta tsargu da irin kallon da yake mata, Tai k'arfin halin cewa "Yayanmu Ina wuni?" (Saboda meenal take ce mishi Yayanmu, haka taji tana ce mishi)
Yayi murmushi ba tare da ya d'auke idonshi a kanta( gaba d'aya ya manta irin kallon da yake mata haramun ne tunda akwai igiyar aure wani a kanta).
Yace "Lafiya lau Auntynmu, Ya exam d'in yau? Ina fatan tayi dad'i?"
Tayi murmushin dake tafiya da imaninshi tace "Alhamdulillah", saura biyu mu gama"
"Wow, Mashaa Allah, Allah ya kaimu"
"Ameen"
"Kice zamuyi celebrating kin gama JSCE".
Dariya kawai tayi, har cikin ranshi yake jin dariyarta
"Ina fatan baki da wata matsala?"
"Eh babu"
"Toh madallah, Ehen kar na manta Imran na gaisheki"
B'ata rai tayi tace "ya rik'e gaisuwarshi banso".
Naseer yayi murmushi yace "Auntynmu kenan, nan gaba zaki gane dalilin Imran"
Ta tab'e baki tace "ni zan tafi, nayi shirin islamiyya"
Leda biyu ya fiddo daga mota, Yace "Ga abincinki nan, Yau ban samu komawa gida ba, balle na karb'o miki na Ummi"
Tace "toh shikenan, Nagode amma nafi son na Ummi dan ta iya girki".
Naseer yayi dariya, yana jin dad'in yadda ta yaba girkin mahaifiyarshi
Nan sukayi sallama, Yace sai ya dawo anjima ta koma cikin gida.
Kullum Naseer sai ya siyo ma Noor abun k'walama kamar su kaza, shawarma, pizza, ice-cream da dai sauransu, Yau ma bayan abinchi, Ya had'o mata da Shawarma da robar ice-cream guda uku, Shiyasa take ta fresh abunta tana k'ara kyau.
Naseer ma ta bashi matsayi mai girma a ranta, dan yana daga cikin masoyanta kuma wa'inda bazata tab'a mantawa dasu ba a rayuwarta, but ba kamar Imran( shi daban yake a cikin zuciyarta, Yadda take jinshi a ranta bata jin kowa haka).
*TO FAH READERS GA IMRAN,GA NASEER, GA YAZEED DUK SUN KAMU DA CIWON SON NOOR❤, NI ZEE NACE NOOR DAI TA NASEER CE🤓 , IMRAN DA YAZEED SAI DAI KUYI HAKURI DAN AURE BAI HALATTA TSAKANINKU DA ITA BA😞, KO ME KUKE CE FANS*
*TEAM NOORUL IMRAN KO TEAM NOORUL NASEER NE😜 LOL*
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
7⃣9⃣
*READERS INA BAKU HAKURU AKAN JINA SHIRU DA KUKAYI KWANA BIYU,ABUBUWA SUNYI YAWA,BUT YANZU ZAN CIGABA IN SHAA ALLAH*
_Lots of greetings to My habeebty😍 (Sadeeya Stylish), Allah ya k'ara miki lafiya( Ameen) Wish u a blink of an eye recovery, U're always in my hrt❤,Love yhu beyond expectation_❣❣
Yau Su Noor, Suka kammala jarabawarsu ta Jsce, Noor sai murna take tana washe baki kai kace Ssce ta gama, Sai hotona suke da wayoyinsu,
Friends d'inta Ilham da Kausar sukace ta basu address d'inta zasu gidansu, Ba tare da tayi tunani komai ba ta basu.
Nan suka fito waje, kowa na jiran drivernsu yazo,
Noor hankalinta na can, Suna ta kallon pics a waya
Taji wani dadd'an k'amshi ya daki hancinta, D'agowar da zatayi idonsu ya had'u da Naseer
Take yaji gabanshi na dukan uku-uku, Sonta na ruruwa a ranshi
Tace "Yayanmu yau kai kazo d'aukata?"
Ya sakar mata murmushi Yace "Eh Auntynmu, Yau fah kika gama exam kinga kuwa ni ya kamata nazo na d'auke ki"
Tayi dariya a ranta tana jin dad'in yadda Naseer ke bata kulawa, Nan ya gaisa dasu kausar, Tayi sallama dasu, Suka shiga mota.
"Ya final paper?"
"Alhamdulillah"
"Toh Allah ya bada sa'a, Yasa ki fito da excellent result"
"Ameen".
Wata hanya taga yabi da ba ta gida ba, Bakinta ya kasa shiru tace "Yayanmu ina zamu?"
"Zamuje ki gaida Ummi ne"
"Shine zanje a haka, ba zaka bari naje na shirya ba"
Yayi dariya yace "kamar zaki je ganin wata bak'uwa, Ummi ce fah, ta d'auke ki tamkar yar'ta duk da bata tab'a ganinki ba",
Murmushi kawai tayi but bata so, taso ace taje gida ta cire uniform.
Gidansu Naseer had'adden mansion ne, Yana yin horn security yazo ya bud'e
Wayarshi ya d'auko ya kira meenal Yace "ta fito"
Cikin minti d'aya ta fito
Yace "taja Noor su shiga ciki, ta dai san abunda ya kamata ba sai ya maimaita mata ba"
Tace "Eh".
Ta rik'o hannun Noor, suna shiga ciki sai kalle-kalle take, gidan ba k'aramin kyau ya mata ba, daga gani an zuba dukiya, D'akin meenal suka nufa
Meenal ta nuna mata toilet tace "shiga kiyi wanka"
Noor ta d'an zaro ido tace "wanka kuma?, ni da gaida Ummi kawai nazo yi, na tafi"
Meenal tayi murmushi tace "toh haka kike so Ummi ta ganki da uniform, kin dawo daga school duk kin gaji"
Noor tace "a'ah, bari na shiga nayi".
Minti ashirin ya d'auketa yin wanka,
Bayan ta shafa mai, Meenal tace ta tsaya ta mata kwalliya, ba musu Noor ta tsaya dama Noor akwai sun kwalliya, Meenal ta iya kwalliya sosai, har na kud'i tana yi a biyata,
Ta tsantara mata kwalliya, Sannan ta d'auko wata had'add'iyar dress, ta bata tace "tasa".
Noor ta kalleta tace "wannan dress kamar wata mai xuwa wajen biki"
"Ni dai karb'a kisa"
Ta karb'a tasa, Meenal ta mata d'auri.
Meenal ta kalleta tace "Wow! Kin ganki kuwa, wlh Noor ke kyakkyawace kin had'u, ga figure 8, kinga kyan da kika yi kuwa"
Noor tayi dariya tace "kaii meenal kin cika exaggerating"
"Wlh sis ba exaggerating nake ba, kalli kanki a madubi"
Ita kanta da taga kanta a madubi tasan tayi kyau, ba k'aramin kyau Noor tayi ba, Meenal ta d'auko wayarta Galaxy S7 tace "tsaya in miki hoto"
Ta gyara tsayuwarta Meenal nata d'aukarta.
Kiran Naseer ne ya shigo wayar
"Hello kun gama shiryawa?"
"Eh Yayanmu"
"Toh ki kaita ta gaida Ummi, ku fito mu tafi"
"Toh",
Taja hannun Meenal "muje ki gaida Ummi, Sun gaisa da Ummi", ta yaba da hankalin Noor, Harda turare designer ta bata, Noor a ranta cewa take "Dama haka halin Hajiya yake".
Naseer tun daga nesa da ya hango Noor, Ya saki baki yana kallonta, Tunda yake a duniya bai tab'a ganin mace mai kyau da k'irar Noor ba, Sonta kawai ke k'ara shigarshi, Yana ratsa jinin jikinshi, K'afarshi har rawa take, Sanye yake da black suit, Yayi kyau sosai.
Noor da Meenal sun lura da irin kallon da Naseer ke mata ko k'iftawa baya yi, Meenal ta tab'ata tace "Kinga irin kallon da Yayanmu ke miki, nasan zai ce kece ko bake bace, dan kin masifar had'u wlh", Tayi murmushi, hakanan sai taji ina ma Imran ne ya ganta yadda tayi kyau d'in nan.
Da suka k'araso Naseer k'ara rikicewa yayi baisan sanda Yace "U look extremely beautiful, So charming"
Kunya ta kama ta, ta duk'ar da kanta k'asa, Ya bud'e mata gaban mota, Ta shiga ya mayar ya rufe
Meenal ta shiga baya.
Yaja mota, basu tsaya ko'ina ba sai NICON HOTEL
Naseer ne gaba, Noor da Meenal na binshi a baya, Wani had'adden hall suka shiga, Anyi decorating d'inshi, acan sama jikin bango ga hoton Noor ansa CONGRATULATIONS ON YOUR JSCE GRADUATION NOOR,
Noor gaba d'aya speechless ta zama a ranta tace "whats a suprise", Kan wata kujera da aka tanadar domin ita, Meenal ta jata ta zaunar da ita, Friends dinta Kausar da ilham da wasu classmates d'inta duk sunzo, Bazan iya bayyana muku farin cikin da Noor ta tsinci kanta ba.
Anyi rawa,anci an k'oshi, anata pics
Noor da Naseer an musu pic tare, sun masifar yin kyau, kowa sai cewa yake sun dace da juna, ba'a watse ba sai 6, an raba soverniers su jaka, littafi, memo, biro da sauransu.
Noor tama rasa da wane baki zata ma Naseer godiya, Da ya kaita gida, ya d'auko wata leda ya bata,
Tace "Nago....."
Da sauri ya katseta Yace "Shhhh.....banson haka"
Murmushi kawai tayi ta wuce ciki.
Had'adden laptop Apple ce ya siyan mata, Noor tama rasa ta cewa, Sai kallon laptop d'in take tana jujjuyawa, "Tabbas ko shakka babu Naseer masoyinta ne".
Matsayinshi ya k'aru sosai a ranta, Nan ta zauna tana tunanin Imran da Naseer cikinsu ta rasa wanda yafi wani sonta, Zuciyarta tace mata "Naseer", tai saurin cewa "a'ah Imran", ta sake cewa "No Naseer tunda Imran ya tafi ya barni"
"Kai bani da tabbas wanda yafi wani tunda Naseer ban gama saninshi ba", Haka dai ta cigaba da sak'e-sak'e a ranta.
Yazeed sai da yasan yadda yayi, Yasa Abu ta sato mai numbern Noor,
Ya tsara mata love message had'e da na congratulating d'inta ta gama Jsce ya tura mata, a k'arshe yasa Yazeed, Yana gamawa turawa, Ya d'auki mukullin mota ya fita, Siyo mata gift.
Tana karantar text d'in, a ranta tana cewa "Toh waye wannan?", Sai da ta kawo k'arshe taga Yazeed
Wani dogon tsaki taja tace "waya bashi numberta?, bunsuru kawai", Tayi deleting text d'in tare da jillar da wayar.
Had'adden Wristwatch( agogon hannu) ya siyo mata designer na (Calvin klein), da takalmi da jaka suma designer(Chann£l), Ya kashe dubu d'ari biyu wajen siyansu, Abu ya kira Yace "ta kai mata tace inji Naseer" (Yasan idan yace inji shi ba zata karb'a ba), Noor da taga kayan rasa tacewa tayi, Yazeed kuwa sosai yaji dad'i kayan sun isa wurinta.
Naseer yau da yaga Noor wani sabon sonta ne ya shige shi, Kwance yake d'akinshi yana kallon pics d'inta, Yana kawowa wanda aka musu tare Yace "Ya Allah! Ka nuna mun, mun zama mata da miji" , kawai ya shiga Instagram yayi uploading d'inshi", Ya kuma kan hotonta ya d'aura shi kan k'irjinshi, Ya lumshe ido bacci mai dad'i ya d'auke shi.
Imran ya dawo daga shopping, a gajiye lemo kad'ai yasha kamar kullum, Ya kwanta ya jawo wayarshi ya shiga instagram, Yana duba post d'in mutane
Yazo kan na Naseer, bai san sanda ya mik'e zaune ba, Ganin yadda Noor tayi masifar kyau kamar ba ita ba, Tayi fresh, take zuciyarshi ta hau halbawa.
Yana duba comments d'in mutane yaga yadda ake cewa Naseer da Noor sun dace, Ya sake kallon hoton yaga yadda sukayi hoton kamar mata da miji, Wani kishi ya turnik'eshi, ya jefar da wayar, Ya dafe zuciyarshi dake mishi zafi, Ya fad'a kan gado yana maida numfashi da k'yar, Maganinshi ya jawo nasa bacci yasha( dan yanzu baya iya bacci sai yasha maganin bacci), Anan take bacci ya d'auke shi _Allah sarki Imran_😢
*Bayan kwana biyu*
Kwata-kwata Imran bai kira Naseer ba, tunda ya tafi bai tab'a kiranshi ko sau d'aya a rana ba, sai dai sau uku ko hud'u, Naseer ya damu sosai, idan ya kirashi kuma baya samu, har text ya mishi bai yi reply ba, Imran daga Naseer har Noor duk haushin su yake ji,shiyasa ya kashe wayarshi kar Naseer ya nemeshi, Zuciyarshi har yau bata bar zafi ba idan ya tuna hoton, Ya k'ara sukurkucewa, ga sonta dake addabar zuciyarshi.
Naseer da ya gayama Noor yana ta kiran Imran baya samu, tab'e baki kawai tayi, ta nuna ko in kula, Amma ba hakane a ranta ba gaba d'aya ji tayi hankalinta ya tashi
Kasa cigaba da hirar da suke tayi, tace mishi "kanta na ciwo, zata koma ciki".
Ya mata sallama ya tafi, Ranar kasa bacci tayi tana addu'a Allah yasa ba wani abu ya samu Imran ba.
Yazeed gaba d'aya ya gama haukacewa akan son Noor, So kawai yake yaga ta zama matarshi ko ta halin yaya, so yake ya aureta kafin Imran ya dawo, yasan shi kad'ai zai mai cikas ya hana mishi aurenta, Ya gama had'a plan d'in da yasan Alhaji zai saketa.
Da daddare wajen k'arfe tara na dare, Noor na bacci kamar a mafarki taji ana hayaniya ana salati, Bud'e idonta tayi taga Su Alhaji duka yan gidan nan akanta, Ta duba gefenta taga k'ato kan kafitar ta ba riga yana mazurai, Da sauri ta rufe idonta ta fasa ihu.
Hajiya ta daka mata tsawa "dallah munafukar banza, rufe ma mutane baki yau Allah ya toni asirinki, da aurenki kina zina kinyi asarar duniya, fasik'a, Allah wadai da hali irin naki", Kalaman Hajiya haka take jinsu kamar tafassasun ruwan zafi a jikinta, Alhaji yace "Amma Noor tir da halinki, matar aure mazinaciya".
Noor toshe kunnuwanta kawai tayi dan bata son jin mummunan kalamansu a ranta tana "Allah ya isa ga duk wanda ya mata sharrin nan, ba zata tab'a yafe mai ba"
Yazeed yace "Daddy ai sai ka saketa dan banga amfanin zama da mazinaciya ba",
Nan fa Alhaji ya fara zufa an fad'i abunda ba zai iya ba, Ya dubi Yazeed yace "da zanyi iya sakinta yazeed da tuni ta dad'e da barin gidan nan"
"Me yasa ba zaka iya sakinta ba?"
Hajiya tace "wannan bai shafeka ba Yazeed"
Yazeed hankalinshi ya fara tashi Allah yasa plan d'inshi ba ruining zai yi ba.
Noor ta tuna akwai wuk'a gefenta da ta fasa madara da ita d'azu, Ta rarumu wuk'ar, Ta saita ta cikin K'aton nan tace "ko ka fad'i gaskiya ko wallahi na soka ma ita"
Da sauri Yazeed yayi kanta yace "me kike yi haka?"
"Kana k'arasowa nan zan soka maka wuk'ar nan and i mean it, dama kasan na tsaneka".
Ganin da gaske take yasa yaja baya, Zufa na keto mai, Su Hajiya tsayawa kawai sukayi suna kallon ikon Allah,
Ta juya kan k'aton "Zaka fad'i gaskiya ko sai na soka ma ita", Jiki na rawa dama matsoraci ne Yace "Wlh zan fad'i, Yazeed ne yasa ni", Kowa was shocked, ba wanda ya iya cewa komai, K'ato kam na fad'ar haka ya mik'e ya fice da sauri, Alhaji yabi bayanshi, Su Hajiya duk suka bi bayanshi saboda borin kunya.
Yazeed ya kai gwiwoyinshi k'asa yace "Dan Allah ki yafe mun Noor, banyi haka dan cin mutunc...."
Ta daka mai tsawa enough Yazeed, me nai maka ka tsaneni haka, ka jefani da sharrin zina?, dan nak'i baka had'in kai?, Na tsaneka Yazeed sai yau na k'ara jin tsanarka a zuciyata, bazan tab'a yafe maka ba"
Tuni Yazeed ya fara hawaye muryarshi na rawa yace "Please try to un...."
Ta sake daka mai tsawa "Get out of my room, i hate you, out ko in kashe ka"
Jiki na rawa, Yana hawaye ya fita, Bakin k'ofar d'akinta ya zauna yana kuka, Yana dana sanin abunda yayi bai tab'a jin ya tsani kanshi ba sai yau, Yayi haka dan ya sameta but hakan ya nisanta shi da ita, Ba abunda ke mishi ciwo irin cewa da tayi ta tsane shi, Shi yanzu ya zaiyi da ranshi.
Wayarshi ya fiddo ya mata text, Ya fad'a mata dalilinshi nayin haka, Noor jin ranta take fari tass, tunda asiri ya tonu gaban kowa, Allah ya wanketa, Yazeed kuma wani haushin shi da tsanarshi take ji a ranta, k'irrr taji k'arar shigowar text tana dubawa taga numbern Yazeed, taja dogon tsaki tayi deleting text d'in.
*TEAM NOORUL IMRAN/ TEAM NOORUL NASEER/ TEAM NOORUL YAZEED*🤣
Kowa ya fad'i d'an wane TEAM ne
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
8⃣0⃣
Yazeed tunda daga ranar ya zama sukuku,Soyayya ta rikita shi, Ya zama salihin k'arfin hali da yaji, ko club ya bar zuwa ba abunda ke mishi dad'i, Sallah kuwa yanzu bata wuce shi, Yana rok'on Allah ya kawo sanadin da zai auri Noor, Su Hajiya da sauran abokanshi duk suna mamakin sauyin halin shi, Ba ruwanshi da kowa, _lallai Soyayya tayi rana tunda ta maida Yazeed salihi🤣_, Hajiya bata tambayeshi dalilin da yasa yama Noor haka ba, dan a tunaninta duk cikin tsanar da ya mata ne.
Noor suna ta shan hutun Jsce, Naseer na mata duk wani abu da take so, ba irin kular da baya bata, Ta saba sosai da yan gidansu, Ummi na sonta sosai tana tausayinta, Ta daina cin abinchin restaurant sai na Ummi, idan taje gidan Ummi na koya mata wasu girke girke, Meenal kuma na koya mata kwalliya, Noor ta kile ta waye sosai, Islamiyya yanxu ta haddace hizib 30, Tunanin Imran na nan a ranta, Son shi na nan a zuciyarta but ita har yanzu ta kasa fahimtar son shi take.
Imran sai da aka yi sati sannan ya kunna wayarshi, Kiran Naseer ya fara shigowa
Da Naseer ya tambayeshi cewa yayi "School suna test shiyasa ya kashe wayar ya samu yayi karatu".
*Bayan wata biyu*
Hajiya nata shirye-shiryen bikin Imran da Khairat, Da kanta taje Dubai tayo lefe na gani na fad'a, aka kai Bauchi, Imran ya daina jin haushin auren Khairat a cewar shi "maybe idan ya aureta ya daina son Noor, tunda har k'asar ya bari amma still ya kasa daina sonta ko ragewa ya kasa", ita kuma Khairat ba d'igon sonta ko kad'an a zuciyarshi, Kullum ita ke kiranshi, bai tab'a kiranta ba, Tayi complain har ta gaji, ta daina.
Yazeed ya buga ya buga ko'ina ya rasa hanyar da zai bi, yasa Alhaji ya saki Noor ya aureta kafin Imran ya dawo, Ya hak'ura ya barwa Allah komai, kullum da k'atuwar Tasbaha a hannunshi, Noor chanza sim tayi saboda shi kullum sai ya mata text.
Naseer ma kullum tunanin shi hanyar da zai bi Alhaji yasaki Noor, kafin Imran ya dawo, Yana so a had'a bikinshi da nasu Imran.
Yasan idan Imran yaji Alhaji ya saki Noor sai yafi kowa farin ciki a duniya dan yasan farin cikin Noor shine nashi
*Bayan sati biyu*
Hajiya ta kira Imran tace "Ya dawo Nigeria cikin satin nan saboda bikinsu"
Hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba yace "Mum ba za'a iya d'aura aure ko bana nan ba"
"Baka isa ba dole ka dawo"
"Please mum ba sai na dawo ba"
"Wallahi Imran idan baka dawo ba sai na d'aga ma nono"
Hankalinshi ya k'ara tashi yace "Shikenan mum zan dawo"
"Yawwa yaushe zaka dawo?"
"Cikin satin nan In shaa Allah"
"Kada ka kuskura ka wuce satin nan"
"Toh" kawai ya iya cewa.
Ya kashe wayar cike da tashin hankali, Kwata-kwata baya son komawa 9ja dan baya son had'uwa da Noor, Yasan tabbas idan ya ganta, wani sabon sonta ne zai kamashi, Ya dafe kanshi da yake ganin jiri, Tsawon minti biyu ya kasa ko k'wakk'waran motsi, Da k'yar ya mik'e yayi alwala, Ya fara nafilfili yana rok'on zab'in Allah.
Imran ya kira Naseer ya sanar dashi abunda Hajiya tace, Naseer yai ta kwantar mai da hankali Yace mishi "ya dawo tunda har Hajiya tace ya dawo", Imran bashi da wani option da ya wuce ya dawo, Har yaje School ya sanar dasu zai tafi Nigeria bikinshi, Sun bashi izini ya tafi yayi wata d'aya.
Naseer bai sanar da Noor dawowar Imran ba, but ya gama yanke shawarar yadda zai raba auren Noor da Alhaji.
0 comments:
Post a Comment