Ganin ta fara kuka, Yasa shi tsayar da nashi ya fara lallashinta, Noor ga kukan tausayinshi, Ga kukan rashin sanin inda mahaifiyarta take, a raye take ko a mace Allah kad'ai ya sani, halayyar mahaifinta ma na damunta, Da k'yar ya lallasheta tayi shiru, nan ya fara wasanni da ita.
Cikin Noor ya shiga wata takwas da yan kwanaki, Imran kullum siyan kayan babies yake unisex (wanda maza zasu iya sawa haka matama), Mummy ta kira Imran tace "Tana son ganinshi"
Da ya tashi daga office gidan ya zarce, tana zaune a falo tare dasu Anwar, Bayan sun gaisa tace
"Wata alfarma nake nema wajenka Imran idan ba damuwa"
"Ba abunda bazan iya miki ba mummy indai baifi k'arfina ba"
"Noor nake so Dan Allah ka kawota nan ta haihu, idan tayi arba'in sai ta koma, kaga haihuwar fari ce dole tana buk'atar kula"
Imran gabanshi ne ya fad'i kwata-kwata baya son yayi nisa da Noor, bazan iya cewa mummy a'ah ba, dan haka Yace
"Shikenan mummy mun gode da zumunci, Allah ya biya"
"Ameen Imran, ba komai Noor ya'ta ce ai, zaka kawota ne ko in aiko driver yazo ya d'auketa?"
"Zan kawota"
"Ok sai ka kawota, nagode"
"Mune da godiya"
Ya tashi ya tafi jiki a sanyaye, yana tunanin yadda zai iya rayuwa ba Noor a kusa dashi har na tsawon wata biyu, ya saba idan ya koma gida beautiful face d'inta yake fara gani ko yaji dadd'an k'amshinta, yana ta tunani har ya isa gida.
Noor da far'arta, tana tafiya da k'yar da k'aton cikinta ta tarbeshi, Yanayin fuskarshi yasa jikinta yin sanyi
"Me ya faru my dear?"
Ya k'arasa falon, Ya zauna kan kujera, Yayi ajiyar zuciya ya fad'a mata yadda sukayi da mummy
To his surprise sai yaga tana murna maimaikon yaga ta nuna damuwa
Tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki da b'acin rai,
Tana murna tace
"Yaushe zaka kaini?"
Harara ya watsa mata Yace
"Ban sani ba" Ya tashi yabar falon
Noor murmushi tayi, ta gane baya son ta tafi, ita kuwa tana son zama tare da mummy dan tana k'aunarta, kuma dama Imran ya takura mata kullum sai ya hau network😜 baya ko raga mata saboda cikinta, gwara ta d'an huta da hawa network😜 na kwana biyu.
D'akin ta bishi, ta sameshi zaune yana ta danna system d'inshi, tsayawa tayi gabanshi, ta rufe system d'in, Murtuke fuska yayi Yace
"Me ye haka?"
Zama tayi kan cinyarshi, tasa harshenta ta d'an lashi wuyanshi, ajiyar numfashi yayi
A kunnenshi cikin muryar shagwab'a tace
"Fushi kake dani my hubby?"
"Kece naga baki damu Dani ba, baza kiyi missing d'ina ba ko?, u're even eager to live me"
"I will surely miss you my dear, yadda baka son nayi nisa dakai haka nima bana so kayi nisa dani"
"Then why are u happy?"
"Ina son zama tare da mummy, tana d'ebar kewar mahaifiyata, inji kamar ina tare da mamana" Ta k'arasa da maganar da hawaye
Tausayinta ya Kama shi Yace
"Kar kiyi kuka my angel, ki shirya jibi zan kai ki"
Kanta tayi nodding, tare da yin murmushi zuciyarta fal da farin ciki.
A kwana biyun soyayya sosai Noor da Imran suka kwasa, Imran ya had'a mata kayanta tsaf a babban trolley, sai yar' k'aramar jaka ta kayan shafa,
Bayan sallar isha'i suka kama hanyar Gidan mummy, Imran gashi nan dai baya walwala, sun isa gidan, Ta bud'e k'ofa zata fita ya jawo hannunta, ya maida k'ofar ya rufe, Kissing d'inta ya fara yi kamar tsohon maye, tin daga fuskarta har wuyanta, ya saketa yana cewa
"Zanyi missing d'inki my angel, take care of yourself and our unborn child, I love you soo much"
"I love you more my hubby"
"Kice ina gaida mummy"
"Bazaka Shiga bane?"
"Ina saurin ina da appointment da wasu mutane"
"Ok"
Ta bud'e k'ofa ta fita, jikinta a sanyaye.
Masu aiki suka kwaso mata kayanta, Mummy ta musu umarni sukai d'akinta, Da murna ta tarbe Noor, Su Noor k'arama ma nata murnar ganinta, Nan mummy ta dabaibaiye Noor da kayan k'walama, Ta saki jiki tana ci, suna hira da mummy, Mummy a d'akinta tace Noor zata sauka, ranar a tare suka kwana kan gado d'aya dan Alhaji yayi tafiya GERMANY, Da ta d'an motsa, Mummy zatace "lafiya? Wani wuri ke miki ciwo?"
Imran ranar baiyi bacci ba, sai juyi yake kan gado ya saba Noor na kusa dashi, Tashi yayi yai ta Sallar dare.
Noor na samu kula sosai daga wajen mummy, haka su Noor kullum suna mak'ale da ita suna mata hira, Alhaji Labaran ma na nuna mata kula sosai, Sosai take jin dad'in zama dasu, Imran kuwa a rana idan bai kirata da yawa ba toh sau 10 ne, duk bayan mintuna kad'an ya kira, suyi ta shan love d'insu a waya, yana mata blowing kisses tana mayar mishi, Kunyar zuwa gidan yake akai-akai, sai bayan sati d'aya yake zuwa.
Ranar da Noor ta cika sati hud'u a gidan, ta tashi da matsanancin ciwon mara da baya bata tab'a jin iron ciwon ba, tunda tazo duniya, Kuka take tana kiran sunan Mummy da Imran
"Mummy!, Imran! Kuzo ku ceceni zan mutu"
Da gudu mummy ta shigo d'akin hankalinta ya tashi sosai ganin Noor, nan ta kamata, sai mota driver yaja su zuwa asibitin STANDARD na DR.Galadanci.
Labour room aka Shiga da ita, mummy ta kira Imran ta sanar dashi, Hankalin a tashe yazo asibitin , sao zirga-zirga suke a passage d'in asibitin suna addu'ar Allah ya sauketa lafiya, Mummy hadda kuka tayi na tausayin Noor,Noor sai kiran waya suke suna tambaya Ya jikin Anty Noor, Anwar ya karb'i wayar yana kuka yace "Mummy please kar Anty Noor ta mutu, we love her so much, Tell Dr to save her life"
Mummy k'ok'arin kwantar musu da hankali tayi tace
"Noor is fine, Baby zata haifa muku"
Sannan suka kashe wayar suna ta murna.
Some hours later, Nurse ta fito take sanar dasu Noor ta haihu Bouncing baby boy, Imran anan yai sujjada yana godewa Allah, Farin ciki sosai mummy tayi, Nurse tace
"Zasu iya shiga su ganta"
Tana rungume da babyn, k'ato dashi fari tas, Imran ya k'arbeshi Yace
"You re welcome to the world my baby"
"My angel sannu ya jiki?"
"Alhamdulillah" ta fad'a tana murmushi
Mummy ta rik'e hannunta tace
"Sannu my daughter bari in kira a kawo miki kayan tea"
Nan ta Kira Fiddausi ta sanar da ita, murna sosai tayi.
Imran Nata kallon jaririn dake Kama dashi, son shi na ratsa jinin jikinshi, Ya mishi hud'uba Yace
"Babyn nan dani yake kama, har hancinshi irin nawa ne"
Noor murmushi tayi bata ma son magana, she is feeling weak
Mumy tace
"Kyan d'a ya gaji ubanshi ai, ni kak'i bani shi ma na d'auka"
Ya mik'a mummy shi, Mummy ta rungume yaron tana kallonshi tana jin k'aunarshi a ranta, Imran ke kallon Noor ta k'asan ido, baya so mummy ta ganshi, Noor tayi kamar bata san yana yi ba.
Kan ace haka asibiti ya cika da iyalan Alhaji Labaran, da yan gidansu Fiddausi, Kowa sai d'aukar Baby yake, yana yaba kyanshi, da fad'ar kamarsu da Imran, Mummy ta had'a tea mai kauri taba Noor tasha, Ba'a dad'e ba aka sallamesu, Noor da d'anta na cikin k'oshin lafiya, Gidan Alhaji Labaran suka d'unguma baki d'aya, A babban falon gidan suka zauna ana ta hira cikin nishad'i da jin dad'i hadda Mai jego.
Bayan kowa ya watse, Fiddausi kad'ai ta tsaya, Tace zata zauna har sai anyi suna, Imran ji yayi kamar kar ya tafi ko ya tafi da Babynshi, Mummy ta kira wata tsohuwa wacce me mata wanakan jego idan ta haihu, Ta rik'a ma Noor da Babynta,
Mummy da kanta ta Shiga kitchen tama Noor Pepper soup na naman kaza, Inna ta mata wanka, ta shirya cikin doguwar Riga tana ta k'amshi kamar ba mai jego ba,
Babyn shima an mishi wanka, an shirya shi, Fiddausi ta goya shi, Mummy ta zauna da kanta tana ba Noor pepper soup d'in a baki, Har sai da tace ta k'oshi, Mummy ta cika mata Kofi da kunun masu jego tace ta shanye tas, Tas ta shanye, Suna hira da mummy da Fiddausi, Nabeel ya mik'o mata wayarta "gashi ana kiranki"
Ta duba taga Imran ne, tashi tayi ta hau sama, suka sha wayarsu.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
[11/16, 20:25] Umar Dalha: *ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣9⃣
Noor na Samun kula sosai daga wajen mummy da Fiddausi, Fiddausi ta d'au son duniya ta d'aura ma jaririn, Tana son yara kuma gashi yana kama da Imran, dan har yanzu ta kasa cire Imran daga ranta, kullum son shi k'aruwa ma yake a zuciyarta, idan sonshi ya motso mata sai dai ta Shiga d'aki tasha kukanta, Mummy sosai take shiryen-shiryen suna, tace Imran kar yayi komai, ta d'auki nauyi, Tela har gida yazo yayi measuring Noor.
Sati ya zagayo, Yaro yaci suna Muhammad sunan Alhaji Labaran, Gagarumin suna mummy ta had'a, Beejay Mai makeup har gida tazo tama Noor, Tasha dank'ak'reren lace red anad black, Ranar ba k'aramin kyau tayi ba kamar ka sace ta ka gudu, Babyn shima Kaya red and black aka sa mishi, idan kaga ganshi dole zai Shiga ranka,Mummy dasu Fiddausi duk sunci kwalliya, Gidan ya cika da yan uwa da abokan arzik'i,
BALANCY mai hoto, sai hotona yake musu, Noor an d'auketa tana rungume da babynta tayi dariya, ba k'aramin kyau hoton yayi ba, sannan aka musu ita da mummy, wani ita da mummy da baby, aka musu da ita da mummy, dasu anwar, sannan aka musu da babyn da mummy dasu Anwar, Haka dai akai ta pics,
Suna yayi kyau ba kad'an, anci ansha an k'oci, an raba soverniers da hoton Babyn a jiki.
Da daddare bayan an watse Imran yazo, yasha shaddarshi sabuwa dal da hula yayi kyau sosai, Aka musu pics shi Noor da babynsu, sannan sukayi shi da Noor, aka musu gaba d'aya dasu mummy, haka dai sukai ta hotona, Bayan an gama, Fiddausi ta karb'i Muhammad wanda za'a rik'a kira da (Daddy), suka fita tare dasu mummy, Aka bar Imran da Noor,
Tasowa yayi ya dawo kujeran da Noor take yana kallonta Yace
"Kinga kyan da kika yi kuwa my angel kamar wata yar' india"
Tayi murmushi tace
"Kaima ai kayi kyau, kamar wani Balarabe"
"I miss yhu so much angel, kizo mu koma gida ki k'ara wankan ki acan"
Mak'e kafad'a tayi tace
"Uhmm a'ah gaskiya sai nayi arba'in"
A fusace ya mik'e
"Idan kin dama ma ki tabbata anan"
Ya fice, girgiza kai tayi murmushi, tabi bayanshi ko da ta fita, har ya tada motarshi mai gadi ya bud'e mishi gate.
Ciki ta koma abunta, ta d'auki wayarta ta mishi sending text masu dad'ad'an kalamai, ta ajiye wayar, ta nufi d'akin mummy, Su Fiddausi na zaune suna hira, Kusa da mummy ta zauna itama ana hirar da ita.
Imran fushi yake da Noor, ko yazo gidan baya tambayar Noor Daddy kawai yake cewa akai mishi, Idan ta kirashi baya d'auka, ita kam cewa tayi "kayi dai ka gama komawa ne bazanyi sai nayi arba'in, yadda baka da hak'uri nan zan koma banyi arba'in ba"
Mummy kullum sai tama Noor pepper soup na kaza, kuma da kanta take zama ta bata.
Imran yayi missing Noor sosai daurewa kawai yake, Yana kwance man gado sai juye-juye yake tunanin Noor ya hanashi sakat, Wayarshi ya jawo ya kirata, Har ta fara bacci taji wayarta na ringing, Murmushi tayi farin ciki ya ziyarci zuciyarta, ta danna receive
"Hello"
Wata sanyayyar ajiyar zuciya Imran yayi da yaji muryar Noor, sannan Yace
"Kira nayi naji Ya Daddy?, mafarkinshi nayi"
"Daddy lafiya lau yake, gashi yayi bacci"
Tana fad'ar haka ya katse wayarshi,
Noor bin wayar tayi da kallo, tayi murmushi
Ta koma ta kwanta, mintuna kad'an bacci ya d'auketa.
*kuyi hakuri da kadan din nn bnjin dadi wlh*
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣0⃣0⃣
Noor tun kafin tayi arba'in jinin haihuwa ya tsaya mata, sai shan gyara take, kullum sai an tafasa mata ya'yan bagaruwa ta zauna a ciki, bayan wasu had'e-had'e da Mummy tasa a mata, Fiddausi ta koma gida but tana zuwa akai-akai, Noor ta k'ara k'iba da fari, fatarta kamar ka tab'a jini ya fito, Boobs d'inta sun cicciko, dan hadda magunganun gyaran nono mummy ke bata tasha, wani ta shafa.
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, Yau Noor ta cika kwana arba'in da haihuwa, Mummy tasa ayi su waina, sinasir da sauransu, Noor hakanan take jin jikinta ba dad'i dan bata son rabuwa da mummy duk da tana son kasancewa tare da Imran, Zaune take bakin gado tana feeding Daddy, Mummy ta shigo ta zauna gefenta
"Kin gama shirya komai naki? anjima da daddare Imran zai zo ya d'auke ki"
Murya a sanyaye tace
"Eh na gama mummy"
"Ya na ganki wani iri yau ko baki da lafiya ne?"
"A'ah Mummy bana son rabuwa daku ne"
Murmushi mummy tayi tace
"Haka muma bama son rabuwa dake, amma kinsan darajar mace d'akin mijinta koh, sannan ai bamu rabu ba tunda muna gari d'aya zaki rik'a kawo mana zariya muna kai miki, dan haka ki daina damuwa"
Gyad'a kanta sama tayi
"Noor kullum ina so na tambayeki labarinki gashi har zaki tafi, baki tab'a fad'a mun inda iyayenki suke ba, naga har kin haihu amma ba d'an uwanki ko d'aya da yazo, ko basu san garin da kike bane?"
Hawaye ta fara tace
"Basu san inda nake ba, kuma ko sun san inda nake ba zuwa zasu yi"
Cike da mamaki Momy tace
"Saboda me?"
Tana hawaye ta fara ba momy labarinta tun daga rayuwar gidansu da labarin da Baba mai gadi ya bata, bata k'arasa labarin da Baba mai gadi ya bata ba, Mummy ta fashe da kuka ta rungumeta
"Noor ashe ke ya'ta ce shiyasa nake jin k'aunarki a raina dama kina raye Alhaji bai kasheki ba kamar yadda yace mun"
"Mummy kina nufin kece mahaifiyata?"
"Nice Noor, ni na haife ki"
Wani dad'i Noor taji ya lullub'eta wanda tunda tazo duniya bata tab'a jin irinshi ba, ta k'ank'ame Momy tace
"Ya akayi kika zo nan bayan Daddy ya koreki?"
"Cigaba da bani labarin yadda rayuwarki ta kasance kafin na gaya miki nawa"
Tana kukan farin ta k'arasa labarinta,
"Kinga rayuwa ya'ta, An cutar dake da yawa, Allah ya isar miki, Imran kuma da duk wa'inda suka taimake ki Allah ya saka musu da Gidan aljanna"
"Ameen mummy, ashe zan had'u dake mummy inji d'umin jikinki"
Mummy ta shafi fuskar Noor tace
"All this years da kikayi ba tare dani ba, I will try to make it up, I will shower you with my love and care for the rest of your love"
"I love you mummy, Thank you"
"I love you more my daughter, don't thank me its my duty"
Sannan ta fara bata labari
"Bayan Alhaji ya koreni, haka na dinga bin kungo-kungo(uncompleted buildings) ko Allah yasa na had'u da yan'uwa, but ban had'u dasu ba, Sai dai na had'u da wata yar' garinmu wato Agadaz, anan nake zama wajensu tare da wasu buzaye, Kitso nake yi ana biyana, har gidan manyan masu kud'i ina zuwa na musu kitso"
"A gidan wani attajirin mai kud'i da nake musu kitso, anan na had'u da Alhaji Labaran wanda gidan k'anin babanshi ne, ya nuna yana sona, a lokacin tsoron aure nake amma yadda na fuskanci Alhaji Labaran halinshi ya banbanta da na mahaifinki, bamu d'auki lokaci muna soyayya ba, akayi aurenmu yace kano zai tafi Dani can zamu zauna(garinsu kuma can yake aiki), Na fad'a mishi ina so na d'auko ki, Ya amince kuma Yace zai rik'e ki tamkar yar' da ya haifa"
"Da naje d'auko ki, Alhaji Yace ai kin mutu sannan yamun korar kare, Nasha kuka da bak'in cikin rasa ki, haka na dangana na barwa Allah, Muka wuce da Alhaji Labaran, Yana nuna mun so sosai da kula, Da muka haihu aka sa mata Fatima, nace ina so a rik'a kiranta da Noor saboda ke, Fatima na tuna mun dake shiyasa nafi k'aunarta duk cikin ya'yanmu, Bansan kina raye ba Noor da tuni na dad'e da nemoki"
Noor tace "Haka Allah ya k'addara mummy ba zan taso tare dake ba ITACE K'ADDARATA"
Mummy tace
"Nima ITACE K'ADDARATA rabani dake da akayi kina yar k'arama, ba abunda yafi ma uwa ciwo kamar a rabata da d'anta tana ji tana gani amma haka Allah ya tsara, yanzu sai mu yiwa Allah godiya da ya had'amu bayan shekaru masu yawa"
Mummy duk ta kira kowa tace "zata sanar dasu abu mai muhimmanci"
Bayan kowa ya hallara a babban falon gidan hadda Imran take sanar dasu Noor yar'ta ce, Kowa yayi murna ba kad'an, Imran kamar ya zuba ruwa a k'asa yasha dan murnar Noor ta gane mahaifiyarta, duk haushinta da yake ji ya tafi, yanzu ya gane tana ji a jikinta mummy mahaifiyarta ce shiyasa take son zama da ita, Su Fatima suma murna sosai sukayi da jin cewa Noor ya'yarsu ce, Noor godiya tama Fiddausi sosai tace "itace sanadin had'uwarta da mahaifiyarta", Tana mai jin k'aunar Fiddausi a ranta.
Da daddare 9pm Imran yazo d'aukarta, Tasha kwalliya cikin atamfa light blue, tayi kyau sosai sai k'amshi take kamar amarya, Mummy nasiha ta mata sosai, ta bata wasu had'e-had'e, Ta sumbaceta a goshi tace
"Allah ya miki albarka, Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki ya raya muku d'anku ya k'aru muku wasu ya'yan masu albarka"
"Ameen mummyna"
Masu aiki suka sauka da kayanta dana Daddy suka kai mota, Mummy ta samo mata wata tsohuwa wacce zata rik'a kular mata da Daddy saboda zuwa makaranta, K'annenta dukansu sai da sukayi hugging d'inta tare da kissing dinta a cheeks, suna cewa "we will miss you Anty Noor", Da hawayenta suka rabu, ta shiga mota suna ta waving juna.
Gidan fes-fes, Imran yasa masu aiki sun share sun goge ko'ina, Ta nunawa Inna d'akin da zata zauna, ta haye sama, Imran har ya hau sama, ya shimfid'e Daddy dake ta shak'ar bacci abunshi, Tana shiga d'akin ya taso ya rungumeta,
"Welcome back my angel"
"Thank you my love"
"Yau amarya kike, ina fatan kin shirya hak'uri dani dan yau.."
Murmushi kawai tayi dan tasan yau ta shiga hannun Imran hmm, but itama tayi missing abun, bata gama tunani ba, taji ya cire veil d'in da ke jikinta bakinshi ya kai wuyanta, yana kissing yana lasa, hannunshi ya kai cikin rigarta, Ganin tsaye ba zai d'auke su ba, Yasa ta cire hannunshi daga cikin rigarta, Ya d'ago yana kallonta da idonshi da sukayi jajir, hannunshi ta rik'e ta jashi zuwa gado,
Kwanciya yayi kan gadon tare da bud'e hannayenshi alamar tazo, Kayan jikinta ta cire ya rage daga ita sai pant da bra, ta fad'a kanshi tare da had'a bakinshi da nata tana kissing kamar zata cire mai harshe, shima tuni ya fita hayyacinshi ya fara sarrafata yadda yake so, (nikam nace kubi a hankali kar ku taushe Daddy😝)
Sun farantawa juna rai ba kad'an ba, har kusan asuba suka kai, Imran har da kukan dad'i dan ji yayi kamar an sashi aljanna kamar yau ya fara kusantar ta, Bayan sunyi wanka bacci mai dad'i ya d'auke Noor, tana kwance a jikinshi, Shi kuwa ya rungumeta kamar wani zai k'wace mishi ita, wani irin bala'in k'aunarta yake ji a ranshi, yana jin kamar ya bud'e zuciyarshi ya sata, a ranshi sai godewa Allah yake da ya bashi Noor.
Kiran sallar asuba aka fara, baya son katse mata baccinta amma ya zama dole ta tashi tayi sallah, Iskan bakinshi ya rik'a hura mata a hankali a kunne, "uhmm uhmm" kawai take cewa tak'i bud'e idonta, harshen shi yasa cikin kunne yana karkad'awa a hankali, ido ta bud'e ta sauke su kan kyakkyawar fuskar Imran, Smiling ya mata Yace
"Wake up my angel is time for prayer"
Mik'ewa tayi zaune, shi kuma ya tashi ya shiga toilet yayi brush yai alwala ya fito yasa jallabiya, ya nufi masallaci,
Jikinta gaba d'aya is weak dan Imran ya dirjeta ba kad'an ba lol, tana idar da Sallah Daddy ya farka yana kuka, kan gadon ta hau tayi feeding d'inshi ya koma bacci, itama baccin ya d'auketa.
Ta cigaba da zuwa makaranta, Imran ya koya mata driving da kanta take tuk'a dalleliyar motar ta, Daddy a gida take barinshi wajen Inna, Kullum sai tayi waya da mummy, Su Fatima ma na kiranta, Ranar da bata da lecture tana zuwa ta wuni, Fatima ma na zuwan mata weekend, Su Anwar kuma basa kwana sai dai su wuni da daddare su tafi, suyi ta d'aukar Daddy suna mishi wasa har basa son tafiya saboda shi.
Birthday had'add'en aka mishi da ya cika shekara d'aya, Cake 10 aka mishi, tsayawa fad'a muku had'uwar birthday k'auyenci ne, Daddy ya girma yayi wayo, idan ka ganshi kamar d'an turawa kamar shi d'aya da Imran, Yana shekara d'aya da wata biyu, Noor ta sake samun wani cikin dan haka ta yaye shi, wajen mummy ta kaishi, Tayi murnar samun cikin haka Imran yayi farin ciki sosai, Dan akwai su da son yara, Basu k'i su cika gidansu da ya'ya ba.
Wannan karan bata sha wata wahalar laulayi ba, sai dai kwad'ayin bala'i bata son abinchi sai kwad'ayi, Mummy tai ta aiko mata da kayan cinye-cinye kamar su dambun nama, aya,kwakwimeti, tabar Malam, yar' gullisowa da sauransu, Imran yai ta tsokanarta yana ce mata
"Mai cikin kwad'ayi"
Ita kuwa sai ta murgud'a baki ba kunya tace
"Ai kai kamun"
Bata da wata matsala a makaranta, sosai take maida hankali, She is very intelligent GP d'inta na level 1 4.5point, Result d'inta daga A sai B, ba C ko d'aya, Yanzu tana level 2, Burinta kawai ta zama lawyer, Ta rik'a kare hak'k'in al'umma.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣0⃣1⃣
Satin Daddy uku da yaye, Imran Yace "su shirya suje d'aukoshi"
Daddy na zaune tsakiyar falo yana ta wasa da kayan wasa, Yana ganinsu da gudu ya rungume Noor,
Ya koma ya rungume Imran, Ya d'aga shi sama yana mishi wasa, shi kuwa sai dariya yake.
Bayan sun gama gaisawa da mummy tace
"Kar dai kuce mun Daddy kuka zo d'auka"
Noor tace
"Eh Momy"
"Satinshi uku fah, bazaku bari ya cika wata d'aya ba"
Noor da Imran sukayi dariya dan su kad'ai suka san yadda sukayi missing d'ansu.
Sun dad'e suna hira, Mummy tasa d'aya daga cikin masu aikin ta had'o kayan Daddy, ta had'o kayanshi tsaf,
Sai da aka zo tafiya, Daddy ya fara kuka
"Shi mummy da Anwar"
Mamaki yaba kowa yadda yake tsandala ihu, Mummy tace
"A barshi tunda baya so"
Haka suka tafi suka barshi ba don ransu yaso ba.
Imran kullum yana sintirin zuwa gidan mummy, yaga lafiyar Daddy, Daddy na samun kula sosai, Momy dasu Fatima duk sun shagwab'a shi, Noor ma watarana idan ta taso daga makaranta tana biyawa ta ganshi, yai ta murna idan ya ganta amma biyota ne bazai yi ba.
Noor na zaune tsakiyar falo tana cin wainar fulawa da yaji, Imran na kwance kan doguwar kujera, yana kallonta suna hira, lips d'inta taji sun fara zugin yajin dan yajin nada fad'a sosai, cije lips d'in tayi kamar zata yi kuka tace
"Wayyo yaji, lips d'ina zasu cire"
Da sauri Imran ya sauko daga kujerar
Ya d'ago fuskarta, bakinshi yasa ya fara tsotsar lips d'inta, Noor sosai take jin dad'in tsotsar da yake dan ji tayi zugin yajin na ragewa a hankali, ya dad'e yana tsotsa sannan ya saki lips d'in Yace
"Har yanzu kina jin yajin?"
Kanta ta girgiza tace
"A'ah"
"Yawwa, kece baki ji my angel nace ki bar shan yaji amma kin k'i"
"Daga yau na daina In shaa Allah"
"Yawwa angel ki daina plz bana so ya cutar mun dake"
"Tohm my dear"
Kwanaki nata wucewa, watanni na wucewa, Cikin Noor ya shiga watan haihuwa, ta daina zuwa school dan tayi nauyi sosai haihuwa yau ko gobe, Imran yana office hankalinshi na gida duk bayan mintuna sai ya kirata yaji lafiyarta, Ranar wata alhamis Noor ta tashi da nak'uda, Kafin Inna ta kira driver yazo a kaita asibiti, ta haifu santalelen yaronta farin k'al,
Inna ta kamata ta gyara wurin, ta d'auki jaririn ta mishi wanka, Noor ma ta kama mata tayi wanka ta shirya, sannan ta aiki driver ya sanar dasu mummy da Imran dan ba waya ta iya ba, Cikin mintuna kad'an sai gasu mummy, basu fito daga mota ba Imran ya shigo, Noor na zaune a d'aki kamar ba ita ta haihu ba, su mummy suka shigo, Imran ya karb'i jaririn daga hannun Inna, Dashi yaron kema
"Wannan babyn ma dani yake kama"
Mummy tace
"Bani shi in gani"
Ya mik'a mata
"Ah tabbas da kai yake kama kuwa dan kamarsu d'aya da Daddy"
Yana dariya ya kalli Noor Yace
"Jini na yafi naki k'arfi"
Ta murgud'a baki tace
"Naji dai zan haifi baby girl mai kama dani, gwara boys d'in suyi kama da kai"
Kowa yayi dariya
Daddy ne ya matso kusa da mummy
"Mummy zan zauna anan tare da baby bazan bi ku ba" Ya fad'i maganar da tsamin baki
"Butulci zaka mana Daddy"
"Ina son shi ne mu rik'a wasa"
Kowa yayi dariya, ana ta hira cikin nishad'i, sai dare su mummy suka tafi da safe zasu dawo, Anan suka bar Fatima, Daddy ma k'in binsu yayi shi wajen Baby zai zauna.
Sati ya zagayo anyi gagarumin suna Yaro yaci suna Ibrahim sunan mahaifin Noor za'a rik'a kiranshi da Aslam, ita ta rok'i Imran yasa, Mummy da Imran sunyi mamaki duk irin tsanar da ya mata amma take son sama d'anta sunanshi, ita kuwa tace kome ye dai mahaifinta ne, Daddy yak'i komawa wajensu mummy, dan haka aka tattaro mai kayanshi ya dawo gida, An sashi makaranta Yandutse college, Driver ke kaishi yana d'auko shi, Suna zaune lafiya da ya'yansu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
*A gurguje please*
*6years later*
Noor na gani sanye da kayan lawyers tayi masifar kyau kamar ba ita ba, Ta fito daga cikin court tana ta murmushi, Wani mutumi babba haka shima sanye yake da kayan lawyers Yace
"Congratulations Barrister Noor finally you have win the case"
Murmushi tayi har hak'orinta na fitowa tace
"Thank you Barr.Nura sai dai mu godewa Allah, dama Allah na bayan mai gaskiya"
"Hakane Allah yasa mu dace"
"Ameen Barr." (Duk case d'in da Noor zatayi ita ke winning dan ta k'ware akan aikinta, har rububinta ake, ita kuwa tana bayan mai gaskiya, duk yadda zatayi ta k'wato Mai hak'k'inshi sai tayi, kuma bata amsar bribery, Manyan mutane sun sha kawo mata bribery tak'i karb'a, Bata da tsoro ko kad'an aikinta kawai tasa a gaba)
Tana fad'ar haka ta shiga motarta, Sahad store ta biya ice-cream da chocolates ta siyo da yawa sannan ta kama hanyar gida, Imran bai dawo ba tana shiga yar' yarinya da bazata wuce 3years ba tazo ta rungumeta, (kamarsu d'aya da yarinyar, ita ke bima Aslam, sunan mummy aka sa mata Zainab Ana kiranta Amal ) Ta d'auketa tace "my baby ina su Aslam?"
"Suna study room suna homework"
"Ke kinyi naki ne"
"Eh mami Ya Daddy ya koya mun"
"Very good..." bata gama rufe baki ba sai gasu da gudu, sunyi hugging d'inta, Ta shafi kansu tana tambayarsu
"Ya school ?"
Duk suka amsa mata
"School lafiya lau"
Ice-cream da chocolates ta fiddo ta basu suna ta murna, ta hau sama tayi freshening-up, Ta fito wanka d'aure da towel, Imran ta gani gabanta Yace
"Koma mu sake wankan tare"
Ta tsaya kallonshi, Gira ya d'aga mata sama alamar Yes
Ta juya ta koma, yabi bayanta, Tare sukayi wankan, sunayi suna wasanninsu, Suka gama ya d'aukota kamar baby, Ya ajiyeta kanastool na dressing mirror, Ya shafa mata mai, itama ta shafa mishi, suka sa kaya.
K'asa suka sauka cin abinchi, gaba d'aya suka zauna kan dinning, Amal na cinyar Imran yana bata a baki, Aslam Yace
"Abi(haka suke kiran Imran) please muje park gobe"
"Ok my boy zamuje"
"Yeey Thank you Abi"
Daddy Yace
"Abi ina son please ka siya mun new bicycle"
"Tohm zan siyan maka"
"Thank you my beloved Abi"
Amal d bata gama iya magana ba tace
"Abi ni ka siya mun teddy"
"Zan siyan miki babyna"
"Thank you"
Noor nata kallonsu tana murmushi
Imran ya kalleta Yace
"Kefah Mamin mu me kike so?"
Kallonshi tayi so romantic tace
"Kai nake so"
Shima wani irin kallon love ya mata Yace
"Am all yours"
"Daddy kuje kuyi wasa" Imran Yace musu
"Okay Abi" suka fad'a, suka mik'e suka bar falon, Sign ya mata da hannu tazo, ta taso ta zauna kan cinyarshi ya shiga sarrafata yadda yake so.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣0⃣2⃣
Firgigit Imran ya tashi daga baccin da yake yana salati, yana ta zufa duk da sanyin Ac dake d'akin, Mafarki yayi Daddyn shi na cikin wani d'aki mai duhu yana ta kuka yana kiran sunan shi yazo ya cece shi, Alwala yayi yai zallah, har asuba bai kwanta ba yana ta nafilfili, Ya tashi Noor sallah, Bayan tayi sallar asuba shi kuma ya dawo daga masallaci, Yake fad'a mata mafarkin da yayi.
Noor tace "Mafarkin nan na nuna maka cewa lokaci yayi da ya kamata kaje gida, bai kamata ace ka d'auki tsawon lokaci har yanzu baka nemi iyayen ka ba, ko ba komai iyayen ka ne, Aljannar ka na k'ark'ashin k'afarsu sannan yanzu kana da abun rik'e kanka baka buk'atar dukiyar Alhaji"
"Hakane my angel, ki shirya yau mu tafi Abuja, Su Daddy ma ki shiryasu tare zamu dasu"
Noor kamar tayi ihu dan murna, nan da nan ta hau had'a kayanta da na Imran a akwati, Nasu Daddy kuma tace mai kula dasu ta shirya musu, K'arfe 7 sun gama shiryawa sunyi breakfast, Imran yasha shaddarshi sabuwa dal mai tsadar gaske, Noor wani dank'araren lace tasa, Su Daddy kuma sun sha English wears masu kyau da tsada, Dukkansu gwanin ban sha'awa.
Had'ad'd'iyar motar Imran da duk garin kano ba irinta(kunsan fa su Imran su ke k'era Mota), Suka shiga, Imran ke driving, Sun biya sun ma su mummy sallama, Imran tunda yayi mafarkin yake jin jikinshi a sanyaye, Suna ta tafiya suna wuce garuruwa, Su Daddy duk sunyi bacci, Imran da Noor kuma na hira.
K'arfe 2 na rana a cikin garin Abuja ta musu, Gidansu Naseer suka fara zuwa, Ummi (mahaifiyar Naseer) da Meenal suka tarar zaune a falo, ga yan' yara guda biyu mata, Wanda da gani ya'yan Meenal ne, Ummi cike da mamaki tace
"Imran kai ne nake gani ko idona ke man gizo"
Yayi dariya
"Ni ne Ummi"
"Allah mai iko, kar dai kace mun Noor ce wannan"
" itace"
"Noor kece kika zama haka Allah mai iko"
Meenal baki sake take kallon Noor da ta zama kamar yar' India tsabar kyau, fatar ta kamar ka tab'a jini ya fito,
Noor na dariya tace
"Wannan kallo haka Meenal kar ki cinyeni"
"Ai naga kin canza ne Noor"
"Ba dole kiga na chanza ba shekaru da yawa ba'a had'u ba"
Ummi ta kira Naseer tace "Yazo yanzun nan yayi bak'o", Tana ta yaba kyan su Daddy, ta d'auki Amal ta d'aura kan cinyarta,
An kawo musu ruwa da abun motsa baki hadda abinchi, Imran bai ci abinchi ba ruwa kad'ai yasha dan hankalinshi yak'i kwanciya.
Kamar a mafarki haka Naseer yaga Imran, ya rungumeshi, ya sake shi yana cewa
"Friend ashe dama zaka dawo garemu"
"Zan dawo Mana"
"I missed you soo much Friend, ka tafi ka manta damu ko waya, na shiga damuwa sosai"
"Ban manta ku ba Friend, all the time kuna cikin tunani na da raina"
"Toh ya bayan rabuwa?"
Imran ya basu labarin komai tun daga ranar da ya bar garin Abuja, sun jinjina ma Imran irin wahalar da yasha, sun taya Noor murnar gane mahaifiyarta.
Naseer cikin tsokana Yace
"Imran mai shagon provisions, wankau, d'aukar blocks da d'an adaidaita, Naso na ganka a d'an a daidaita"
"Kai fa d'an iska ne tuzurun banza kawai ka k'i aure"
Ya fashe da dariya Yace
"Har yanzu ban samu wacce tamun bane"
"Ka tsaya nan dai kana ruwan ido, idan baka yi wasa ba sai ka k'are a auren bazawara"
"Allah ya kiyaye, Budurwa sabuwa dal a leda zan samu ni zan fara b'areta"
"Ka tsaya nan dai"
Bayan sun huta, sunyi sallar la'asar, Suka nufi gidansu Imran hadda Naseer(tunda Imran ya tafi bai k'ara zuwa gidan ba), Gidan na nan yadda yake amma tun daga bakin gate paint d'in duk ya tsufa, Suna ta horn shiru ba'a bud'e ba, sai can aka bud'e, wanda ya bud'e gate d'in tsayawa yayi yana kallon motar da ta shigo, harabar gidan ba mota ko d'aya duk yawan motocin gidan,
Da ya rufe gate ya k'araso wajen su, Yazeed ne duk yayi bak'i ya rame ga kayan jikinshi duk sun kod'e sunji jiki, Kallon-kallo suka tsaya suna ma juna shi da Imran, Yana kallon yadda Imran ya k'ara kyau da k'iba ya zama hamshak'in mai kud'i, Imran kuma na kallon yadda Yazeed ya lalace, K'arasawa Imran yayi ya rungumeshi dukkansu suka fashe da kuka, Suka Saki juna
"Ina su mum?" Imran ya tambaya
"Suna ciki"
Alhaji na kwance rai hannun Allah ko magana baya iya yi sosai, kullum maganarshi itace a kira mishi Imran, Hajiya kuwa zaune take kan wheelchair bata iya tafiya k'afafunta sun rub'e, Ihsan da Iman ba wacce tayi aure duk Wanda yazo aurensu za'a ce babansu d'an caca ne, sai ya fasa, Khairat ta koma zaria wajen mamanta.
Imran na ganinsu sai hawaye, Noor ma hawaye ta fara, Hannun Alhaji ya kama ya rik'e yana kuka
"Mun cuce kanmu Imran ga abunda kwad'ayin duniya yaja mana, ba tsinanniyar sana'a kamar caca mai sa mutum ya tsiyace lokaci d'aya, bala'in dake tattare cikin caca nada yawa, cin haram baiyi ba Imran, dukiyata kab a caca ta k'are komai na sai da nasa a caca, gidan nan kad'ai na tsira dashi, talaucin da muke gudu, muna ganin kamar idan na bar caca ba zai same mu, gashi ina cikinta na tsiyace ko abincin da zamuci gagararmu yake, Yan uwa kowa ya gujemu sakamakon haka na kamu da ciwon zuciya, nasan kwana na ya k'are Imran, na cuci kaina, Caca ba sana'ar mutanen kirki bace" Alhaji ya k'arasa maganar yana aman jini,
"Sannu Daddy, Yazeed Naseer ku Kama mu kaishi asibiti"
Suna k'ok'arin kamashi rai yayi halinsa bayan yayi Kalmar shahada, Imran dafe zuciyarshi yayi yana kuka, kowa a gurin sai kuka, Su Daddy ma kuka suke ganin iyayensu na kuka,
Imran yaji mutuwar mahaifinshi ba kad'an ba, Allah yayi zasu gana kafin ya rasu, an mishi sutura an kaishi makwancinshi wato kabari inda kowa sai yaje, Kwana uku ana zaman makoki, Hajiya na kuka ta nemi gafarar Noor, Noor tace "bata tab'a rik'eta a zuciyarta ba, ta yafe mata duniya da lahira", Hajiya taga yan jikokinta taji tana k'aunarsu, Daddy ya rik'a tuna mata sanda Imran na k'arami, Tayi farin cikin ganin Imran yadda ya zama, tana ta nadamar duk abubuwan da ta aikata,
"Grandma me ya samu k'afarki?" Daddy ya tambayeta da damuwa
"Ciwo naji"
"Bari na kira Abi ya kai ki hospital, ina so ki warke ki rik'a tafiya"
Wata k'aunar yaron taji ya sake shigarta ta rungumo shi jikinta, tana hawaye, A ranta tana cewa "yanzu wannan d'an Imran ne da Noor yarinyar da na tsana"
Imran nata shiryen-shiryen fitar da Hajiya k'asar waje ai mata aikin k'afarta, Wani had'add'en gida ya siyan musu a gwarinpa, Wanda suke ciki ya siyar, yayi sadaka da kud'in saboda ta hanyar caca aka samu gidan, Ya siyo kayan abinchi da komai da zasu buk'ata a gidan ya ajiye, Hajiya nata sa mishi albarka, Yazeed yanzu ya shiryu ya zama Ustaz tunda sukayi accident sun taso daga club, ya karye a k'afa da hannu, shekara biyu yana jinya, Imran yace zai tafi dashi Kano, ya samar mishi aiki a company Alhaji Labaran.
Noor tacewa Imran tana so taje gidansu taga mahaifinta, Yace ta shirya su tafi, Da ita dashi dasu Aslam suka tafi, Gidan na nan yadda yake ba abunda ya chanza, Baba Mai gadi suka tarar bai gane Noor ba,Tambayarsu yayi "Wa kuke nema?"
Noor tace
"Baba Noor ce"
"Noor ta gidan nan?"
"Eh ita Baba"
"Kece kika zama haka, Allah Mai iko, Gaskiya ne duk tsanani yana tare da sauk'i"
Noor tayi murmushi tace
"Daddy na nan?"
Shiru yayi na seconds, da damuwa d'auke a fuskarshi Yace
"Ba kowa gidan nan sai mamansu sameer(k'anin Noor)"
"Toh shi Daddy dasu sameer suna ina?"
"Suna can a d'aure"
Noor hankali a tashe tace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un me sukayi?"
"Ai bayan kin bar gidan nan, Alhaji ya k'ara lalata su Sameer yana sakar musu kud'i sosai abunda suka ga dama shi sukeyi, Ga shaye-shaye da bin mata, har fyad'e sukewa yara, idan an kawo k'ararsu, Alhaji ya murje ido yace sharri ake musu, Ana haka har komai da Alhaji ya mallaka ya k'are a caca, lokacin fa ya fara dana sanin lalata Su Sameer da yayi, idan suka tambayeshi kud'i yace musu bashi dashi, haka zasu zageshi tas kamar zasu dukeshi, Fashi da makami suka fara sun riga sun saba da kashe kud'i, suka addabi gari da sata kuma an kasa kamasu"
" Ranar sun shiga gidan Alhaji Musa wanda abokin Alhaji ne a harkar caca, shi har yanzu da kud'inshi dan kusan duk abunda ya mallaka na Alhaji ne da yasa a caca, shi kuma ya cinye, Suka kashe shi suka saci kud'i masu d'umbin yawa, kafin su fita gidan Yan' sanda suka kamasu, aka wuce dasu station, Suke sanar da yan' sanda ai Alhaji ne yasa su kashe shi suka kwashe duk abinda ya mallaka, Kuma sukace shi ke sasu suna duk wata sata da suke hadda weapons d'in da suke amfani dashi shi ke basu"
"Nan fah Yan'sanda suka shiga binkice inda suka ga makamai iri-iri a d'akin Alhaji da mak'udan kud'i, kuma an gano cewa akwai gaba tsakanin Alhaji Musa da Alhaji tunda ya cinyeshi a caca basa jituwa, da wa'innan hujjoji aka kai k'arar Alhaji kotu tare dasu Sameer, amma Alhajik'aryata ya cewa bashi yasa su ba, bai masan suna fashi da makami ba, kuma bai san yadda akayi weapons d'in nan suka je d'akinshi ba, yanzu haka Alhaji ya kamu da ciwon zuciya saboda bak'in cikin su Sameer, ance ya nemo lawyer da zai kareshi, shine yasa gidan nan a kasuwa dan ya samu kud'in da zai d'auki lawyer da zai kareshi"
Noor da Imran sun girgiza da jin zancen nan, Noor tace
"Baba ina so a janyen zancen siyar da gidan nan, ni zan tsayawa Daddy a matsayin lawyer, kuma ko da wasa bana so ka fad'awa kowa nice"
"Nayi miki alk'awari ba wanda zai ji"
Ta zaro bindir d'in d'ari biyar ta bashi, Ya karb'a yana ta godiya, ta sake zaro wata bindir d'in tace "wannan kaba mamansu sameer sai na dawo"
Suka wuce, suka bar Baba Mai gadi da mamakin yadda Noor ta chanza Allah ya d'aukaka ta, dama haka Allah ke abunshi.
Ranar Noor batayi bacci ba, tunani kawai take yadda zata b'ullowa case d'in, Alla-alla take safiya ta waye taje ta tattauna da Daddy dan tasan yadda zata taimakeshi, dan jikinta na bata sharri su Sameer ke mishi.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣0⃣3⃣
Washegari wajen k'arfe goma na safe, Noor ta shirya ta nufi station inda Daddyn ta ke d'aure, Ba b'ata lokaci aka fiddo dashi daga cell dan su tattauna da ita, Ya bata tausayi sosai kamar tayi kuka ganin yadda ya lalace ya fita hayyacinsa, ko alama bai gane Noor ba.
"Baiwar Allah ban ganeki ba?"
Ta d'an yi murmushi tace
"Baka sanni ba amma ni Barrister ce, labarinka naji kuma ka bani tausayi shine zan tsaya maka matsayin lawyer in taimake ka"
"Baiwar Allah ai bani da kud'in da zan biyaki"
"Kar ka damu Baba, bana buk'atar ko sisi daga gareka"
"Nagode nagode sosai Baiwar Allah, Allah ya saka miki da alkhairi"
"Ameen Baba, ka daina mun godiya, abunda nake so kawai duk tambayar da zan maka kaji tsoron Allah ka gaya mun gaskiya"
Yadda Baba Mai gadi ya bata Labari haka shima mahaifinta ya gaya mata, ya kuma rantse mata da Allah cewa bashi yasa su ba,
Noor tace
"Baba kuma ya'yenka ne kai ka haife su da cikin ka?"
"Ya'ya ne Barr. Ni na haife su, Allah ne yake nuna mun ishara, alhakin Zainaba da yar'ta ne ke bibiyata, na wulak'antata na koreta dan ta haifa mun ya' mace, gashi ya'yen mazan da nake so, sune suka jefani a halin nan da nake ciki, ina bak'in cikin kasancewarsu ya'yana"
Ya fashe da kuka, Noor ta shiga bashi hak'uri,
"Ka daina kuka Baba In shaa Allah zan wanke ka daga zargin nan da ake maka da yardar Allah"
"Allah ya yarda Barr., Allah ya baki iko"
"Ameen Baba, sai na dawo"
Yana ta mata godiya, ta mik'e ta tafi, Ya bita da kallo a ranshi yana cewa "Tabbas ya' mace nada muhimmanci ga rayuwar al'umma, Iyayenta su gode ma Allah, dan ko wane uba zai yi alfahari da samun ya' kamarta, nayi jahilci da na d'auka ya'ya maza kad'ai ke da amfani"
Noor ko da ta koma hotel d'in da suka sauka ta tarar da Imran zaune kan gado, su Daddy na gidansu Hajiya can suke kwana,
"Sannu my angel"
"Yawwa my love"
Ta k'arasa kan gadon ta zauna kusa dashi tare da d'aura kanta kan kafad'arshi
"Kinyi magana da Daddyn?"
"Eh nayi, same story ya gaya mun da na Baba Mai gadi, kuma gaskiya bashi yasa su ba"
Imran yace
"Idan bashi ya sasu ba waye ya kai weapons da mak'udan kud'i d'akinshi?"
Tayi ajiyar zuciya tace
"Shine abunda na kasa ganewa, but I will investigate In shaa Allah, Allah zai bayyana gaskiya"
"Allah ya yarda yayi jagora my angel"
"Ameen my love, na gaji sosai"
"Sannu my love, mik'e k'afa in miki tausa"
K'afarta ta mik'e ya dinga mata tausa a hankali tana lumshe ido,
Phone d'inshi tayi ringing, Yayi picking, bayan sun gama yake cewa Noor
"Visa mu ce ta tafiya da Hajiya India an gama" (Imran, Ihsan da Hajiya zasu tafi, da tare da Noor zasu, case d'in Daddyn ta yasa ta fasa)
Fuskarta d'auke da damuwa tace
"I will miss you my love"
"I will miss you more angel, ko inyi postponding tafiyar sai kin gama case d'in Daddy sai mu tafi tare"
"A'ah my love lafiyar Hajiya zaka duba, tana buk'atar treatment da wuri"
Rungumeta yayi
"I will really miss you my angel, Ina sonki kamar raina, bana son nisa dake"
"U're my happiness Imran, I so much luv u, all the time ina so naji ka kusa dani"
"Ko da gangar jikinmu bata tare ruhinmu na tare my angel"
Haka sukai ta fad'a ma junansu kalaman soyayya,
Bayan kwana biyu su Imran suka tafi, Noor har airport ta rakasu da kuka suka rabu da Imran, Jiki a sanyaye ta koma hotel,
Suna isa Imran ya kirata, suka sha wayarsu, suna bayyanawa juna irin yadda sukayi missing junansu, Amal ta d'auko ta rik'a taya ta kwana, kullum sai sunyi waya da mummy, ta fad'awa mummy komai, ta girgiza da jin al'amarin, ta mata addu'ar samun nasara a case d'in.
Kullum sai taje wajen Daddy ta kai mishi abinchi, yai tama mata godiya, Yau ma ta kai mishi bayan ya gama ci Yace
"Nagode sosai Barr, Allah ya biyaki "
"Ameen Baba, amma da godiyar nan da albarka ka samun zan fi jin dad'i"
Yayi murmushi Yace "Barr. Kina da hankali iyayenki sun baki tarbiya Mai kyau, kinga tunda nake dasu Sameer basu tab'a neman albarka ta ba, gashi ke da ban haifeki ba kina nema, Allah ya miki albarka Allah yayiwa rayuwarki albarka"
Cike da farin ciki tace
"Ameen Baba"
Sosai taji dad'i haka take ji kamar an gafarta mata zunubanta for the same time Daddyn ta yasa mata albarka, Ta koma hotel cike da farin ciki.
Noor ta duk'ufa tana ta investigation kan wanda ya kai weapons d'akin Daddy, ta hanyar kad'ai zata wanke shi daga zargin da ake mishi, Ko isasshen bacci batayi saboda yawan tunani.
*Kuyi hak'uri na yau zaku ganshi kad'an wallahi mura nake fama da ita da ciwon kai*
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣0⃣4⃣
Ana saura kwana biyu a shiga kotu, hankalin Noor duk ya tashi ganin har yanzu bata samu shaida ba, amma tayi bincike sosai har club d'in dasu Sameer ke zuwa, Shiryawa tayi ta nufi gidansu ko zata samu wani k'arin bayani wajen Baba mai gadi.
"Baba Su Sameer basu da abokai ne?"
"Suna dasu sosai Noor"
"Abokan basa zuwa gidan nan?"
"Suna zuwa sosai, duk wani iya shegensu nan suke taruwa suna yi, wani lokacin ma anan suke kwana"
"Sai kayi hak'uri da tambayoyina Baba abun ka da lawyer"
"Ba komai Noor cigaba da tambayata"
"Abokan nasu basu san suna robbery bane kuma ba tare suke yi ba?"
"Gaskiya wannan ne ban sani ba"
"Tohm Baba tambaya ta k'arshe bayan abun ya faru cikin abokan nasu babu wanda yazo gidan nan?"
"Gaskiya ba wanda yazo" sai kuma Yace
"Wai Allah na tuba Lawal abokin Sameer washegarin da abun ya faru yazo, banga shigar shi ba amma naga fitowarshi, dana tambayeshi yace mun yazo ya yama Mamansu Sameer jaje ne"
Noor ta d'an yi shiru tana nazari, ta nisa tace
"Baba ko kasan gidansu?"
"Bansan gidansu ba amma mahaifinshi Alhaji sunusi modi sananne ne da an fad'i sunanshi kowa ya san shi"
"Toh Baba nagode, idan akwai buk'atar ka bada shaida a kotu zaka iya?"
"Tabbas zan iya ko dan ke Noor"
"Nagode Baba"
Ta d'auko kud'i masu yawa ta bashi ta tafi.
Zuciyarta na zargin Lawal yakai weapons d'in but tasan yadda zata b'ullowa al'amarin, Yazeed ta kira ta tambayeshi "Yasan gidan Alhaji Sunusi modi?"
Yace "Eh gidan shi na nan a Asokoro da taje ta tambaya za'a nuna mata"
Ta mishi godiya ta kashe wayar, Kwata-kwata bata sha wahalar gane gidan ba, Security da ta tarar bakin gate tace
"Ya mata sallama da Lawal"
Mintuna kad'an sai gashi ya fito yana ta washe baki, K'ofar motar ta bud'e tace "ya shigo" yana ta rawar jiki ya shiga shi a dole yaga mace.
Bayan sun gaisa, Yake cewa
"Ban ganeki ba?"
Tayi murmushi tace
"Baka sanni ba amma ni na sanka, ba kaine Lawal ba friend d'in Sameer?"
"Yes ni ne, ina kika sanni?"
"Sanin irinku ba abu mai wuya bane, na tab'a ganin ka a club"
Yayi dariya Yace
"Kice ke ta hannun dama ce"
Ta gyad'a kanta sama
"Amma kwana biyu naga kun daina zuwa ko me yasa?"
"Wallahi an kama su sameer ne"
"Subhanallahi, me sukayi?"
"Robbery a gidan wani attajirin mai kud'i har suka kashe shi"
"Su kuwa taya suka yarda aka kamasu, kamar jarumai bane, da sun gudu"
"Ai ni ina fara jin shooting bullet na gudu"
"Kana nufin da kai aka je robbery d'in kenan"
"Sosai ma amma da yake kinsan ni jarumi ne ban yarda an kamani ba" (Ya shagala yana fad'in maganar irin with full confidence dan ya burge)
"Toh yanzu su ba wata hanya da za'a bi a fitar dasu, coz ina masifar son Sameer tun ranar da na ganku tare a club hankalina ya kasa kwanciya"
"Ai ubansu sukace yana sasu, kinga k'ila a sake su a yanke ma uban hukunci tunda shi ya sasu, ko kuma ko da za'a yanke musu hukunci ba wani mai tsanani ba"
"Kotu zata yadda kuwa ba tare da wata k'wak'waran shaida ba tunda ba tare aka kamasu ba"
Dariya ya fashe da ita, Yace
"Yarda ta nawa kuwa, shaida kuma ta nawa, ni nan da kaina naje har gidan nasa weapons da mak'udan kud'i d'akinshi, Da nane ganin Su sameer sukace idan har nayi haka zasu rufa mun asiri, ba zasu fad'a tare muke robbery ba"
Noor tayi dariya tace
"Kai amma naji dad'in jin wannan zance, nasan Sameer zai fito"
"Ai In shaa Allahu ya fito ya gama"
"Allah yasa dan ina k'aunar Sameer"
"Kar ki damu, idan ya fito ni zan miki jagora wajenshi"
"Toh nagode sosai"
Ta kashe recorder da ta kunna tun shigowar Lawal motar, ya fita motar, Taja motar ta cike da farin ciki, ta samu shaidar da zata wanke mahaifinta jibi a kotu, Ta kira Imran ta sanar dashi, Yayi murna sosai kuma ya yaba da k'wazonta ta yadda ta bugi ruwan cikin Lawal.
*After 2days*
A kotu, Noor ta gabatar da shaidu, shaidar ta farko ita ce Baba mai gadi, sai kuma voice recorder da ta kunna, Kowa yayi mamaki, Lawal kuwa hadda fitsari a wando tsabar tsoro yazo yaga yadda case zai k'are sai gashi ya juye kanshi, Kotu ta saki Daddyn Noor bayan ta wanke shi daga zargin da ake mishi, Su Sameer kuwa da Lawal an yanke musu life imprisonment
An fito kotu, Daddy cike da farin ciki yazo wajen Noor zai mata godiya tayi saurin hana shi
Yace
"Allah ya miki albarka, kin ceci rayuwata, Allah ya biya miki dukkkan buk'atunki na alkhairi"
"Ameen"
A motar ta suka tafi gida, Sai yau Noor ta shiga cikin gidan, ba komai cikin gidan ko kujeru babu a falon, Mamansu sameer na zaune ta rafsa tagumi, gashinta kanta gaba d'aya ya kakkabe kamar na namiji, nonuwanta guda biyu kuma an yanke Cancer, Tana ganin Daddy, ta mik'e tace
"Alhaji Kaine, Alhamdulillah Allah na gode ma an saku ka, ina su Sameer?"
"An yanke musu d'aurin rai da rai"
Ta fashe da kuka tana cewa
"Yaran nan ga abunda suka jawa kansu, mun cuce su mun cuci kanmu da bamu basu tarbiyar arziki ba"
Da k'yar suka samu tayi shiru,
Daddy Yace
"Babban burina bai wuce inga Noor ba idan har tana raye in nemeta gafara duk da nasan da k'yar ta yafe mun, naci amanarta na azabtar da ita, na manta cewa Allah shi ke bada haihuwa mace ko namiji, ba ita tayi kanta ba na d'auki karan tsana na d'aura mata, na sata a caca na aurar da ita ga tsoho, ban sake waiwaiyarta ba, nasan hak'k'in Noor ne ke bina, kina Ina Noor in nemi gafararki? duk da nasan kin tsane ni ba zaki so sake sani a idonki ba"
Noor dake hawaye tace
"Gani Daddy, tuni na dad'e da yafe maka, ban tab'a tsanarka ba ko na rana d'aya kai mahaifina ne ina sonka"
Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki
"Nice yar'ka Noor Daddy"
Kasa magana yayi sai rungumota jikinshi da yayi yana kuka, itama kukan take, sai da sukayi mai isar su ya saketa yana cewa
"Allah ka yafe mun Allah na tuba kuskuren da nayi, Ya' macen da bana son nake k'yama nake kiranta Faqeer(tsiya) itace ta zama wani abu har ta ceceni daga halin bala'in da na tsinci kaina, Ya'yan mazan da nake so su suka jawo mun masifa, Tabbas ya' mace abun so ce kuma da darajawa a cikin al'umma, A yau na kasance ina mai alfahari dake Noor kin fiye mun ya'ya maza dubu, Ya'ya mata rahama ne, Na yarda ke haske ce a rayuwata, Sunanki ya tabbata NOOR( HASKE), ba ZULUM(DUHU)ba kamar yadda nake kiran ki"
*Iyayen maza da mata Ku sani haihuwa Allah ne ke bada ita mace ko namiji, abun bak'in cikin shine yanzu wai kuga wasu iyayen basu son mace sai namiji, har idan bakya haihuwar ya'ya maza gori ake miki, Ku sani mace nada matuk'ar muhimmanci a rayuwar al'umma ko a ciki Al -kur'ani mai girma Allah ya fad'i darajoji na ya' mace, Har Surah guda Allah ya saukar a Al-Qur'ani akan mata Suratul Nisa'i, Ku mazan da bakwa so a haifa muku mace naga macen ce ta haifeku, tayi d'awainiya daku tun kuna cikin ciki, ta haifeku ta raine Ku har kuka girma kuka mallaki hankalin kanku, naga matan kuke aure kuke samun natsuwa daga garesu, Kuyi tunani shin mace bata da amfani ga rayuwar al'umma Allah ya halicceta, ai da sai a halicci maza kad'ai, Sannan ya'mace tafi taimakon iyayenta sau da yawa akan da' namiji, shi namiji komai ya samu na matarshi ne da ya'yenshi sai Allah ya had'ashi da mace ta gari zata rik'a bari yana taimaka ma iyayenshi, mace fah komai ta samu gida tayi, Ya'yan mata akwai tausayi da raunin zuciya, mu d'auki Noor duk irin tsanar da mahaifinta ya mata, bata fasa tausayin shi ba ta taimake shi, Ko a zamanin Annabawa da sahabbai mata sun taka muhimmiyar rawa a musulunci kamr Nana Khadija matar Manzo Allah(SAW), Nusaiba, Asiya matar Fir'auna,Ummu Salma, Rabi'atul badawiyya da dai sauransu, Mace nada matuk'ar muhimmanci ga rayuwa Al'umma Wanda ko da zan kwana bazan gama fad'ar su ba, Allah yasa mu dace mu daina tsanar ya'ya mata da fifita ya'ya maza kansu duk da cewa Arrijalu kauwamuna alal nisa, Amma suma mata suna da nasu hak'ki*
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣0⃣5⃣
*LAST PAGE*
*24th Nov, 2017*
Noor taba Daddynta labarin bayan ya aurar da ita ga Alhaji Mamman duk abunda ya faru, Ya jinjina al'amarin, Yace
"Yanzu kin had'u da Zainaba, Dan Allah ki nema mun gafararta, Ta yafe mun"
"In shaa Allah Daddy"
"Yawwa nagode Ya'ta, yaushe zaki kawo mun yan' jikoki in gansu?"
"Gobe In shaa Allah zan kawo ma su"
"Yawwa Dan Allah ki kawo su, dan na k'osa na gansu"
Noor ta tafi bayan taba Daddynta kud'i masu yawa tace zata aiko musu da kayan abinchi, Yana ta sa mata albarka, Farin da Noor ke ciki bazai misaltu ba, Ta kub'utar da Daddynta kuma yana alfahari da ita.
Washegari ta d'auki su Aslam suka je gidansu, Daddy bakinshi k'in rufowa yayi ganin kyawawan jikokinshi, Yana tambayarsu sunan su, suka fad'a mishi, Ba k'aramin farin ciki yayi ba da yaji sunan Aslam Ibrahim, Wata k'aunar Noor ta sake shigarshi
Yace
"Aslam kaine mai sunana kenan"
Ya gyad'a kanshi sama
"Allah yayi ma rayuwarku Albarka daku da mahaifiyarku"
Suka amsa da Ameen
Daddy Yace
"Kai ka haifi Ummi?"
"Eh na haifeta"
Ya juya kan Noor Yace
"Ummi Fathers d'inki nawa? Ga grandpa na Kano, ga wannan shima kince Daddynki ne?"
Tambayar Mamaki da dariya taba Noor tace
"Yes, they are all my fathers, wannan shine real father na, na kano kuma step-father"
Tsayawa yayi yana kallon Noor da mamaki Yace
"Dama mace na aure maza biyu Ummi?"
Harararshi tayi tace
"Ban sani ba ka cika tambayar tsiya"
"Am sorry Ummi"
Daddy kuwa burgeshi yaron yayi, yana ta kallonshi yana murmushi, Sun dad'e a gidan, Daddy nata wasa da yan' jikokinshi, Da zasu tafi ji yayi kamar a bar mishi su, Mamansu Sameer kuwa tana asibiti an kwantar da ita jikinta yayi tsanani, k'anwarta ke zama da ita.
Ranar dasu Imran zasu dawo, farin ciki wajen Noor ba'a gama, Gidan Hajiya taje ta musu girke-girke Iman ta tayata, Bayan ta gama tayi wanka ta tsantsara kwalliya, kayan da tasa sunyi fitting d'inta tayi masifar kyau, Iman kanta sai da ta yaba da kyan da tayi, Bayan sallar magriba driver yaje ya d'auko su airport, Hajiya taji sauk'i sosai, an yanke k'afafunta ansa mata na roba amma ba zaka tab'a cewa na roba bane idan ba gaya maka akayi ba, Imran sai murna yake zai ga sahibarshi ji yake kamar sunyi shekara basu ga juna ba.
Motar su na parking da gudu Su Aslam suka fito suna "Abi oyoyo Abi oyoyo" suka rungumeshi, Ya d'auki Amal suka shiga ciki, Noor na zaune falo ta tashi tana musu sannu da zuwa, ji take kamar ta rungume Imran but ba dama su Hajiya na wurin, Kallonta kawai yake shima yana ji kamar ya rungumeta, suna had'a ido ya mata blowing kiss tare da k'yafta mata ido, tai saurin juyawa wajen Hajiya tana cewa
"Ya hanya?, Ya jiki?"
"Alhamdulillah, an gode da Allah Noor"
Bayan an gama yan' gaishe-gaishe da ya hanya, Suka zauna dinning table cin abinchi, Noor tayi serving d'insu, kowa ya yaba girkin dan yayi dad'i, Imran yana ci yana kallo Noor so kawai yake su keb'e su biyu, Kowa tas ya cinye wanda akayi serving d'inshi, Yazeed hadda k'ari,
Bayan sallar isha'i, Imran yace ta tashi su tafi, Driver ya kaisu dan cewa yayi bazai iya tuk'i ba, ya dawo ya gaji, Suna shiga d'aki yasa key ya rufe ya jawota jikinshi, Yana shisshinar k'amshin turarenta, Yana fad'in "I miss you angel, I miss you soo much"
Shiru tayi tana amsar sak'onnin da yake isar mata dan tuni ya fita hayyacinsa, Yana sarrafata cikin salo na k'warewa, itama ta shiga mayar masa martani, A daren sun farantawa juna ba kad'an ba, Imran nata sa mata albarka.
Mamansu Sameer kwana ya k'are, Rai yayi halinsa, Daddyn Noor yaji mutuwarta ba kad'an ba, Noor dasu ake zaman makoki hadda su Hajiya da Ihsan, Yan gidansu Naseer ma sun zo gaisuwa, Kwana uku ana zaman makoki kowa ya watse, Ana washegari su Noor zasu koma kano, Tana cikin had'a kayansu a akwati, Imran na kwance saman gado Tace
"Ni kuwa my dear ina da wata shawara sai dai ban sani ba ko zaka amince"
"Fad'i muji ta mecece, nasan duk shawarar da zaki bani bata banza bace"
"Me zai hana mu had'a Hajiya da Daddy aure"
Shiru na mintuna sannan Yace
"Kin kawo shawara mai kyau angel, amma kina ganin zasu amince?"
"Wannan ba matsala bace, zan ma Daddy magana"
"Toh Allah ya tabbatar da alkhairi"
"Ameen my dear"
Noor ta samu Daddynta da zancen ya amshi maganar hannu bibbiyu, dan shi yasan yanzu duk abunda zai zo daga wajen Noor alkhairi, Hajiya ma da Imran ya mata maganar ba musu ta amince dan ce mata yayi "Daddyn Noor ne da kanshi yace yana sonta", Sun d'aga tafiyarsu har sai an d'aura auren iyayensu.
An d'aura aure, Daddyn Noor ya dawo gidan da Imran ya siyan ma Hajiya, Sun fara sabuwar rayuwarsu, Baba mai gadi Noor ta siyan mishi d'an madaidacin gida , ta bashi jari ya fara Sana'a, Ihsan ta had'u da wani mai kud'i a airport ranar da suka dawo daga India, Iman kuma Naseer yace yana sonta kuma ta amince, Dukkansu ansa bikinsu nan da wata uku.
Ranar da zasu koma kano, haka suka rik'a ji kamar kar su tafi sun saba dasu Hajiya, but Noor na missing Mummynta, Aslam cewa yayi a barshi wurin Daddy saboda irin yadda Daddy ke shi ji dashi, shi kuma Daddy cewa yayi a barshi wajen Hajiya dan ita kuma shine d'an gidanta, Amal kuwa yar' gidan Ihsan da Iman suna sonta kullum tana wajensu, tare da Yazeed suka tafi, A mota suna ta hira, Tunda suka kira mummy suka ce mata suna hanya, ta Shiga kitchen da kanta tana had'a musu delicious girki, Fiddausi ta tayata tazo gidan.
Suna isa gidansu mummy suka zarce, Noor ta k'ank'ame mummynta kamar zata koma cikinta,
"Nayi missing d'inki mummyna"
"Nima nayi naki sosai daughter"
"Kunsha hanya Imran mutan Abuja"
"Wallahi mummy"
"Ina wuni?" Yazeed ya gaisheta tare da d'sn rissinawa
"Lafiya lau, wannan ai kai ne photocopy d'in Imran"
"A'ah mummy ni ba'a Kama da wannan mummuna" (ni zee nace Imran kai kunyar surukan nan bakayi)
"Tafi can yama fika kyau"
Akayi dariya
A falo duk suka baje, suna ta kwasar girkin mummy suna zuba santi, Fiddausi sai kallon Yazeed take tana mamakin kamar su da Imran a ranta tana cewa ina ma ace bashi da aure ya aureta taji duk sin da take ma Imran ya dawo kanshi, Shima Yazeed tunda ya ganta yaji ta mishi a ranshi addu'a yake Allah yasa bata da aure.
Sai da dare suka tafi, tun a Mota Yazeed ya fara tambayar Imran
"Bro yarinyar da na gani gidan nan Dan Allah wacece?"
Wani irin kallo Imran ya watsa mishi Yace
"Wato baka bar halinka ba kenan"
"Haba Bro, wallahi na daina, wannan son aure nake mata"
"Toh ka makaro dan tana da aure"
Yazeed numfashin shi kusan d'aukewa yayi, wani k'ololo yazo ya tsaya mishi a zuciya dan yadda ya kamu da sonta farat d'aya shi kanshi abun mamaki ya bashi,
Ganin yadda yanayinshi ya sauya lokaci d'aya yasa Imran cewa
"Am kidding bro bata da aure"
Wata sanyayyar ajiyar zuciya yayi Yace
"Har kasa temperature na yayi raising"
Dariya Imran yayi
"My lil-bro is in love"
"Deeply in love ma, can't wait for tomorrow na mata express feelings d'ina"
"Allah yasa kar tayi turning d'inka down"
"In shaa Allah she will not"
Ya juya bayan mota yace
"Auntynmu Noor zaki tayani kamun k'afa ko?"
Tayi dariya tace
"Sosai ma"
Imran Yace
"Gamu gani dai"
"Zaka sha mamaki, dan nasan da gudu zatayi accepting d'ina"
Har suka isa gida suna maganar, Yazeed ya yaba da kyau da tsaruwar gidan, Guest room dake k'asa aka bashi, Washegari Imran yaje dashi company, aka nad'a shi a matsayin accountant, Ya samu Fiddausi ya fad'a mata yana sonta, ta amince kuma tayi farin ciki sosai, Soyayya sosai suke sha, Manya sun sa baki, ansa bikinsu lokaci d'aya da nasu Ihsan tare za'ayi, Rayuwa haka ta cigaba musu cikin jin dad'i, kusan kullum sai sunyi waya da mutanen Kano.
Tun ana saura wata d'aya biki, Kowane family suke ta faman shirye-shirye, A Abuja za'ayi komai, Fiddausi ma iyayenta sun amince ayi har a nata acan, Ana saura sati d'aya biki gab'a d'ayansu suka tafi Abuja, Hadda su Mummy, Wasu suka sauka gidansu Hajiya, wasu kuma a gidan Imran (Ya siya tantsamemen gida a Maitama babu abunda babu ciki na more rayuwa), Daddyn Noor da yaga Mummy ya rok'eta gafara, Ta yafe mishi, A zuciyar shi yana ta dana sanin rabuwa da ita da yayi, Idan ka ganta bazaka ce ita ta haifi Noor ba, gashi ya k'are a auren Mai k'afar roba.
Kwana hud'u suna shan biki, Bikin ya had'u ba kad'an ba naira tayi kuka, ko'ina a garin abuja maganar bikin ake, Dinner su ma ta tsaru wacce akayi a SHERATON HOTEL, Amaren Ihsan da Iman anan Abuja aka kaisu, Fiddausi kuwa kano aka wuce da ita.
Sati d'aya da bikinsu, Noor da Imran suka cika 8years anniversary na aurensu, Had'add'en Dinner party Imran ya had'a musu a BRISTOL HOTEL, Ya gayyaci friends d'inshi masu hannu da Shuni, Noor ta gayyaci friends d'inta, Imran yayi long speech ya yabi Noor sosai kuma ya fad'i irin sonta da yake, Noor ma ta fad'i irin muhimmiyar rawar da ya taka a rayuwarta tun kafin aurensu da irin son shi da take, Kowa a gurin sun burgesu ana ta cewa Best couple ever, Ya yanka had'add'en cake d'in da aka musu, Ya bata a baki, Itama ta yanka zata bashi Yace
"No tasa a bakinta sannan ta bashi"
Haka tayi kuwa, Wuri aka d'auki tafi da ihu, Anci ansha an k'oshi kowa ya watse.
Imran harka ta cigaba arzik'i ya k'aru dan company BENZ dake Germany sun d'auke shi aiki, Sunyi sallama da yan'uwa har kano suka je suka musu sallama, Ya d'aura Yazeed a matsayinshi wato MD a company Alhaji Labaran, Shi kuwa shi da sahibarshi Noor, da ya'yansu sun koma Germany.
Imran ya zama DON, company biyu ya bud'e na motoci d'aya a kano, d'aya a Abuja da sunan *NOORUL IMRAN MOTORS*, Yazeed ke kular mai da companies d'in, Kud'i ko'ina ta ina shigo mai suke, Ya k'ara kyau da fari, Noor itama tayi fresh abunta, Dasu da ya'yansu kamar turawa, (Dama ance bayan wuya sai d'adi)
Imran, Noor dasu Daddy ne a garden d'in gidansu, Dukkansu sanye da english wears, Suna ta wasa , Noor ta rufe ido tana binsu zata kamasu su kuma suna guduwa, Imran ta kama, Su Aslam suka fara ihu suna cewa "Ta Kama Abi, its ur turn Abi"
Rungumeta yayi ya cire mata scarf d'in da d'aure fuskarta, ido suka had'a Yace
"I love you my angel, u're my world, my happiness infact my everything, look into my eyes its full of ur love"
Zatayi magana kenan, Su Aslam suka zo da gudu suka rungumesu suna dariya, Imran duk'awa yayi, Noor itama ta duk'a, Ya rungumosu gaba d'aya jikinshi Yace
"My Family my everything I love you all"
"We love you too" suka fad'a a tare
"Allah ya barmu tare"
"Ameen"
_Nima Zee nace Ameen, dan sun matuk'ar burgeni_
*TAMMAT BI HAMDILLLAHI*
Anan na kawo k'arshen littafin nan, Kurakuren da nayi a ciki Allah ka yafe mun, kunsan ance duk d'an Adam ajizi, Allah yasa littafin nan ya amfanemu gaba d'aya Ameen
*Habeebtyna Aminiyata Sadiya Abdallah Shehu(Stylish Bch) Ina mik'o gaisuwata gareki, Hak'ik'a ke ta dabance a rayuwata, ke aminiya ce da kowa zai iya alfahari da samu a matsayin abokiyar shawara, u're just more dan a best frnd but a sister, u have always been there for me, U always show ur love n care towards me, I want you to know dat I Luv u more dan words could say, and I'll always love u till my last breath😍, I promise to always be by ur side, Allah ya barmu tare har abada*
_REAL PURE MOMENTS OF LIFE WRITERS K'UNGIYA MAI ALBARKA ALLAH YA K'ARA D'AUKAKA, YA KAREMU DAGA SHARRIN MAHASSADA YA KARA HADA KANMU I LOVE Y'LL MEMBERS OF PML_
My co-writer I luv u guys
Amnoor(Nagode da so da kulawarki)
Zeezee(Noscol)
Ya Hajja
Memxy Fulla
ZeeZee(Abler)
My Abeeda
Xoxocism
Aishat A Muhd
Nana Fa'ad
Meelat AHK
Ummu Yahya
Faty Azland
Maryam Abdoul(neighbor)
Biebie Dee
Pherty
Anty Jamila(Maman bobo)
Xuhura(my ride or die)
Suhana
Mizz Purple
Jedda Aliyu
Hawwer Sarki
Dija waziri
Wash na gajiya kuna da yawa wlh those dat I don't mention bn manta daku ba I love you all❤
Ina alfahari daku
Amina(Besty)
Elbeelah, Ray, Amal
Maryam kaumi, Muhmeelat,Rabi'a Haruna, Reeder Malaysia, Memuh dandutse, Mum twins, Aunty Barakah Jamsy mg and all members of ITACE KADDARATA FANS GROUP
*SAI KUN JINI A SABON NOVEL DINA MAI ZUWA IN SHAA ALLAH*
*ZEE YABOUR*
*ZEELISH*
Compiled by Princess Aysha Muhammad
Copied by Umar Dalha
0 comments:
Post a Comment