Sai da Yace
"Ya k'oshi"
ta daina bashi
"Mik'e k'afa in miki tausa"
"No ka barshi na hutar dakai, kai dai zaka mik'e k'afa in maka"
"Naji Zaki mun amma sai na miki"
Mik'e k'afa tayi dan bata so su cigaba da musu, Tausa ya fara mata a hankali har kan cinyarta, Noor har lumshe ido take saboda dad'in tausar, Ba tausa kad'ai ya tsaya ba, Romancing d'inta ya fara, sai da su duka suka fita hayyacinsu, Ya d'auketa sai kan katifa,
Noor tasha kuka tana rok'on Imran amma ina bai saurara mata ba, Rungume yake da ita tana mishi kukan shagwab'a, Sonta yake ji na ratsa dukkan sassan jikinshi, matsayinta ya k'aru a zuciyarshi, Yana ma Allah godiya da ya bashi Noor a matsayin mata, Farin cikin da ya tsinci kanshi a yau ba zai misaltu ba.
Ruwan zafi ya had'a ya mata wanka, bayan yasa ta zauna cikin ruwan zafi, Ya shafa mata mai yasa mata Kaya, Ta Saki jiki dashi a cewarta zance kunya ya k'are tunda ba daren da jemage bai gani ba,
Ranar ko bakin k'ofa Imran bai fita ba, Yana manne da Noor yana tarairayarta, ita kuwa sai langab'ewa take tana zabga mishi shagwab'a, Kwance take kan cinyarshi yana shafa kanshi ganta
"My angel yau dai shagwab'a kike ji"
Ta tab'e baki tace
"Toh ba kai bane uhmm"
Ya shafi fuskarta
"Am sorry darling hak'k'ina na karb'a, anjima ma zaki bari na karb'a koh?" ya wani langab'ar da kai kamar k'aramin Yaro,
"Tabb hu'um lallai ma"
"Haba babyna"
"Ni ka daina mun maganar bana so"
Ta k'arsa maganar kamar zata yi kuka
"An daina gimbiya"
Wata hirar ya d'auko, suna ta hirarsu ta masoya
Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin so, k'auna da kulawar juna, Kowannensu bashi da buri da ya wuce ya faranta ma d'aya, Imran kullum cikin yin abunda zai faranta ma Noor raina yake, itama haka duk abunda zai faranta mai rai shi takeyi.
Sun Saba sosaii da Ameerah, itace k'awar shawarta, duk wasu maganin mata da na gyaran jiki Ameerah ce ke bata, shiyasa duk lokacin da Imran ya kusanci Noor sai yaji kamar yau ya fara saninta, Noor ta tsare tsarki da Magarya( Magarya nada matuk'ar amfani tana wanke duk wani datti na gaban mace, tana hana warin gaba) kuma bata tsarki da ruwan sanyi dan yana lalata mace.
Yau da gobe, kudi'n da Naseer yaba Imran sun k'are, Cinikin da yayi a shago da kud'in suke cefane, Nama ba kullum suke sawa a miya ba, Noor bata tab'a nuna ta damu ba, kullum k'arfafa ma Imran gwiwa take kan Neman halal d'inshi, da kwantar mai da hankali watarana sai labari.
A radio Imran yaji ana sanarwa, Makarantar CENT LOUIS za'a yi jarabawa duk Wanda yaci za'a bashi scholarship hatta books bazai siya ba duk school d'in ce zata bashi, Yana shigowa gida ya sanar da Noor, Tayi murmushi tace
"Banda abunka ina ni ina cin wannan jarabawa"
"Jarabawa Sa'a ce sai kiga kinci"
"Ni dai abar zancen nan dan nasan ba ci zanyi ba"
"Me yasa kike saurin given-up, never give up in life, Duk yadda kike son yin Karatu, baki da buri da ya wuce kiyi Karatu but you can't fight for yourself, Noor try, I will support you 100% wajen ganin kin cimma burinki , kar kiyi turning d'ina down"
Shiru tayi na seconds tana nazarin maganganun Imran tabbas gaskiya ya fad'a, bata da wani buri da ya wuce tayi Karatu ta zama Lawyer Mai kare hak'k'in al'umma,
"Na yarda, Allah ubangiji yai mana jagora"
"Ameen my angel haka nake son ji"
Yai mata peck a kumatu, itama ta mayar masa.
Da k'yar ya samu ya had'a dubu biyun da ya siyan mata form na scholarship d'in makarantar, Ya cika yayi submitting, Jarabawar Maths, English da government ne zatayi, Yan science kuma suyi Maths English da chemistry, Mutum uku da suka fi kowa marks su za'a ba scholarship, Imran ya dage kullum yana ma Noor lesson, Da ya koya mata nan da nan ta d'auka, Idan yana shago tai ta practising.
Ana washegari jarabawar daga Noor har Imran basuyi bacci ba, Sallar dare suka kwana yi suna rok'on Allah,
Washegari tunda safe Imran ya kaita har makarantar, Gabanta nata fad'uwa ta shiga exam hall.
Jarabawar ta mata sauk'i sosai, Ta fito tana ta far'a, Imran na waje na jiranta, ya tambayeta
"Ya Jarabawar?"
"Tayi sauk'i, Alhamdulillah"
"Allah ya Bada Sa'a, yasa result yayi kyau"
"Ameen"
Kwana biyu da yin jarabawar, Result ya fito, Noor tafi kowa marks, Farin ciki wajen Imran da Noor ba'a gama hadda kukan dad'i Noor tayi.
An bata uniform da books, hadda sock da sandal duk su suka bata, SS3 aka kaita maimaikon ss2, Ranar da zata Fara zuwa Imran ya mata nasiha sosai, Yace ba ruwanta da kowa, abunda ya kaita shi kad'ai zatayi ta dawo, Shi ke kaita a keke napep yana d'aukota, Sai ta tuna lokacin da yake kaita a had'add'iyar motarshi, motoci gasu nan sai wacce ya zab'a, hadda k'walla tayi na tausayin Imran, Rayuwa kenan.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
[11/8, 08:31] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣1⃣
Noor na maida hankali sosai a makaranta tunda ta Shiga ita ke musu na d'aya, bama a na d'aya ta tsaya ba ita ke overall best, Duk k'arshen term sai an bata kyauta, Imran na alfahari da ita kuma yana k'ara k'arfafa mata gwiwa, Abunda bata gane ba a makaranta idan ta dawo shi ke koya mata.
Imran naba Noor duk wata kulawa da ta dace, A kwana a tashi kayan shagon Imran sun k'are, provisions d'in da suka rage kad'an ne, gashi bashi da kud'in siyan wasu, duk kud'in da ya samu kashe su yake a lalurar gida, Ya shiga damuwa sosai, ita kad'ai ce hanyar samunshi, ba abun kuma ya karb'i bashi ba, bai san ranar biya ba.
Imran ya shigo gida d'auke da damuwa a fuskarshi, Noor bayan ta mishi sannu da zuwa, Ta rik'o hannunshi tasa cikin nata, Tace
"Me ke damunka?"
Ta fad'a murya a marairaice
Ajiyar zuciya yayi Yace
"My angel kayan shago sun k'are bani da kud'in siyan wasu, kuma wannan ita kad'ai ce hanyar da muke samu"
Hannunshi ta murza a hankali
"Ka kwantar da hankalinka, bakin da Allah ya tsaga baya hana mishi abinci, Ina so ka zama Mai tawakkali, Allah na sane damu, Dan haka ka saki ranka ka daina damuwa"
Ya d'aga kanshi sama alamar gamsuwa da maganarta
"A gaskiya Noor ke mace ta gari ce, ina alfahari da samunki a matsayin matata, I Luv yhu so much"
"I Luv yhu too"
Abinci ta tashi ta d'auko, tayi serving d'insu suka ci, Bayan sun gama ta zauna tana mishi hira mai dad'i da zata kawar mai da damuwar da yake ciki, Imran sai dariya yake hadda rik'e ciki, Noor sai da tabbatar ta kawar mai da duk wata damuwa, ta sa shi cikin nishad'i.
Imran yau ya tashi bashi da ko naira biyar, kayan abincinsu sun k'are, Shi ba kanshi yake tunani ba Noor, zai iya jure yunwa, amma bazai iya jure ganin Noor najin yunwa ba (yasan tana da ulcer baya son abunda zai cutar da ita),
Ya kalli gefenshi tana ta sharar bacci abunta Ya sumbaci goshinta a ranshi yace,
"I will not allow any harm to come to you my angel I promise",
Mik'ewa yayi ya Shiga toilet, Yayi brush yai wanka, Ya shirya, Saitin Noor ya tsaya Yace
"Zan tafi nema miki abunda zaki ci my angel, zan jure duk wata wahala a kanki"
Kasancewar weekend ne ranar Noor bata farka ba sai wajen k'arfe goma, ta duba gefenta bata ga Imran ba, Falo da kitchen ta lek'a nan bata ganshi ba, A ranta tace "toh ina Imran ya tafi da sassafen nan"
Cikinta yayi k'ara k'olulu alamar yunwa, Shafar cikin tayi, Tayi murmushi tace
" Allah kasa yunwar nan da nake ji, Imran baya jin irinta, Ina tausayin Imran, bai saba wahala ba, bai saba da yunwa ba, gwara ni na Saba, Allah ka azurta Imran ta hanyar halal Allah ka tsare mai imaninshi" Ta fashe da kuka, nan ta duk'a tana ta kuka.
Imran fita yayi yana ta yawo cikin gari, Yana tambaya a ina zai samu aiki kowane iri ne zai iya, a biyashi, Wani mutumi yazo siyan abu a shagon, yaga Imran na tambayar Mai shagon ko akwai wani aiki da zai mai ya biyashi, Mai shagon Yace "Babu".
Mutumin ya kirashi
"Zo d'an samari"
Imran ya k'arasa wajen mutumin
"Zaka iya mun wanki in biyaka, na dad'e ina Neman Mai wanki ban samu ba, Ni bak'o ne a garin nan bamu dad'e da dawowa nan ba, ni da iyalina"
Imran jiki na rawa Yace "Eh zan iya"
"Toh muje gidana kusa ne nan ba nisa"
Kayan wanki ne masu bala'in yawa, Imran na ganinsu sai da gabanshi ya fad'i,
Haka ya zage ya dinga wanki yana ta zufa, Yana yi yana hutawa, Bawan Allah abun tausayi, Tunanin Noor kawai yake ko wane hali take ciki yasan tana can tana jin yunwa, k'walla ne ya zubo mishi.
Sai azahar ya gama wankin, Ya masifar gaji, jikinshi ko'ina ciwo yake mai, Ga bayanshi ya masifar rik'e yana mai ciwo, Mutumin dubu biyu ya bashi, Imran ya mishi godiya ya tafi a ranshi yana cewa neman kud'i da wuya but I will do anything for you Noor.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
[11/8, 08:31] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣2⃣
Restaurant ya zarje, Ya siyo takeaway na jollof rice da nama, sai lemon roba(sprite) mai sanyi da ruwa, Ya nufi gida da chanji dasu zai siyana mata abincin dare.
Noor hankalinta ya tashi jin Imran shiru ,
"Toh ina ya shiga?"
Tambayar da take ma kanta kenan, Sai faman kuka take, Ameerah na lallashinta tana fad'a mata kalamai masu kwantar da hankali
"Imran zai dawo ba abunda ya sameshi In shaa Allah"
Sallama yayi ya shigo falon, Da gudu Noor ta tashi ta rungumeshi, Ajiye ledar dake hannunshi yayi Ya rungumeta shima, Tana hawaye tace
"Ina ka shiga?"
"Naje nema mana abunda zamu ci"
"Hankalina ya tashi da naga ban ganka ba"
"Cry cry baby"
Yasa hannu yana goge mata hawayen fuskarta, hannu yasa ya shafi cikinta
"Am sorry babyna na tafi na barki da yunwa muje kici abinci"
"Uhmm kaima nasan kana jin yunwa"
"No ni bana jin yunwa"
Ameerah kam tun shigowar Imran ta fice.
Plate ta d'auko da spoon da cup, Ya juye abincin a plate, Ya d'auki spoon ya fara feeding d'inta,
"Bani spoon d'in nima in baka"
"No my angel am okay"
"Idan ba zaka ci ba toh nima bazan ci ba"
Ta juyar da kanta gefe, Juyo da kanta yayi suna kallon juna ido cikin ido
"My angel rigima na gaya miki am okay, idan kina so nayi amai toh"
Da sauri ta girgiza kai alamar a'ah
"Toh idan bakya so nayi amai kar kice dole sai naci"
Abincin ya cigaba da bata, cikinshi yayi k'olulo alamar yunwa(muguwar yunwa yake ji), Kallon tuhuma Noor ke mishi
D'an murmushi yayi Yace
"Cikina ya lalace tun d'azu nake ziyartar toilet"
"Ayyah me kaci toh?"
"Nima shine ban sani ba"
"Sannu my dear kasha magani"
Nodding kanshi ya bata
Mik'ewa yayi, Jiri ya fara d'ibarshi, gaba d'aya jikinshi is weak ga yunwa ga wahalar aikin da yasha, Ya tafi zuu zai fad'i, Noor ta rik'o shi tana
"Sannu, ko zan kira Dr ne"
"A'ah had'a mun ruwan wanka masu zafi"
"Tohm"
A daddafe yakai d'aki yana shiga, Ya fad'a kan katifa, Yana maida numfashi kamar yayi ihu haka yake ji saboda yadda jikinshi ke ciwo, abunka da wanda bai saba ba.
Ta had'a mai ruwan, Tazo saitinshi tace
"Na had'a maka ruwan, muje in kama maka kayi wankan ko kaji k'arfin jikinka"
Kai kawai ya iya d'aga mata,
Durk'usawa tayi gabanshi kamar zatayi kuka, ta rik'o hannunshi tace
"Cikin ne?"
"A'ah my angel jikina ke ciwo"
"Ya salam, wane aiki kayi da yasa maka ciwon jiki?"
"Wanki"
Da k'arfi tace
"wanki, me yasa kake son wahalar da kanka Imran? Why zakayi wanki, kasan baka saba wahala ba"
"Its my duty Noor, to take care of you, to do everything for you"
"Idan a kaina ne daga yau na hanaka, bana so Imran"
Ta fashe da kuka, Zai yi magana ta dakatar dashi da hannunta, tare da mik'ewa ta fita daga d'akin.
Ruwan zafi ta zuba a roba, ta d'auko towel da Rub,
Rigar jikinshi ta kama mai ya cire a hankali, Ya kwanta rub da jiki
Towel d'in tasa cikin ruwan zafi, Ta matse tana danna mai bayan tana hawaye, Hawayenta ne ya d'iga a bayanshi, Da sauri ya juya ganin tana hawaye, Ya rungumota jikinshi
"Haba my angel, me yasa kike son azabtar da zuciyata? Kinsan yadda nake jin kukanki a raina?"
D'ago fuskarta yayi, Yasa harshe yana lashe mata hawayen, har sai da ta daina zubar da hawayen, Yace
"Please kar ki k'ara zubar mun da hawayenki"
"Bazan iya jure ganinka cikin wahala bane"
"Sai kinyi hak'uri my angel, jarabawace Allah kuma ya baku ikon cinyeta"
"Ameen, juyo in k'arasa ma"
Kwanciya yayi ta cigaba ta danna mai bayan har k'afafunshi, Sannan ta shafa mai rub, sosai yaji dad'in jikinshi ciwon ya rage.
Sallar la'asar da magriba duk a gida yayi, Tare sukayi sallar, Da suka idar nan suka zauna suna karatun Qur'ani har aka kira isha'i,
Imran ya mik'e Yace
"zai tafi masallaci a can zai yi"
"Zaka iya zuwa masallacin?" Ta fad'a da alamar kulawa
"Eh jikin ya daina ciwo ai, my darling wife tasa ya daina" (fad'a kawai yayi amma har lokacin bayanshi na ciwo but ya rage ba kamar d'azu ba, Yace zashi masallaci ne dan ya samu ya siyo mata a binchin dare)
Murmushi tayi tace
"Tohm a dawo lafiya my dear, ka kula da kanka please"
"In shaa Allah i will"
A masallaci yayi sallar isha'i, Bayan ya idar ya tafi siyo mata abinchi, Tuwo da miyar egusi tasha kifi yayi mata takeaway, Sauran naira d'ari ya rage kud'in ya siyo garin hamsin, gyad'ar hamsin, dan wata irin masifar yunwa yake ji.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
[11/8, 08:31] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣3⃣
Noor fuskarta d'auke da damuwa tace
"My dear ka dad'e, a ina ka tsaya?"
"Restaurant naje na siyo miki abinchi"
D'an dafa goshinta tayi tace
"Me yasa kake son wahalar da kanka, baka gama warkewa ba ka fita"
Hannunshi biyu ya had'a wuri d'aya
"Am so sorry my angel, forgive me"
"Ok ya wuce my dear, but plz ka daina anything da zai tab'a lafiyarka bana son abunda zai tab'a ka"
A ranshi sosai yaji dad'i yadda Noor ke Nuna damuwarta a kanshi
"Zan kiyaye In shaa Allah my angel, muje kici abinchi"
Tare sukaci abinchin, dan k'in ci tayi, ba yadda baiyi da ita ba, sai dai sukaci tare.
Bayan sun gama ci suka kwanta, tana kwance kan k'irjinshi, da k'yar bacci ya d'auke Imran dan tunani yake abunda Noor zataci gobe, gashi tana zuwa school, ko kud'in motar da zata makaranta babu.
Da yaje sallar asuba, Limamin masallacin ya fad'a ma matsalarshi Yace
"Dan Allah ya tayashi addu'a"
Limamin yace "akwai aikin d'aukar blocks idan zai yi"
Imran Yace "eh zai iya Neman halal d'inshi yake"
Liman yace
"Anjima kamar k'arfe tara na safe haka yazo ya sameshi" Ya zaro d'ari biyar ya bashi, Godiya yama limamin sosai,
Gida ya nufa cike da farin cikin ya samu aiki, duk da aiki ne mai wuyar gaske
Noor da ta ganshi ya dawo gida cike da farin ciki ta tambayeshi
"My dear ya akayi naga kana ta farin ciki?"
Murmushi yayi Yace
"Aiki Liman ya Samar mun zan rik'a Lura da ginin da ake. Ma uban gidanshi" (Yasan idan ya gaya mata d'aukar blocks ne Bazata barshi ba)
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Noor
"Alhamdulillah Allah mun gode ma, Allah ya daukaka ka my dear, ya azurtaka ta hanyar halal"
"Ameen my angel" Ya fad'a tare da kissing d'inta a goshi
D'ari biyar d'in ya zaro daga aljihu
"Gashi my angel, Yau bazan samu Kai ki makaranta ba, kinga idan nace zan kaiki kud'in ba zasu isa ba, idan kinje makaranta sai ki siya abinchi kici"
Girgiza kanta tayi cike da tausayin Imran tace
"A'ah idan na karb'i kud'in kaci me?na hak'ura da zuwa makarantar har sai ranar da ka samu"
Hannunta ya jawo ya damk'a mata kud'in
"Don't worry my angel, can wurin aiki za'a rik'a bani abinchi"
"Are u sure?"
"Yes sure" ya fad'a tare da d'aga mata kai.
Peck ta mishi, Ji tayi ya had'a bakinshi da nata, yana isar mata da sak'onni masu rikatarwa, itama martani ta Fara mayar Masa, Sun dad'e a haka, Sannan ya saketa yana maida numfashi, Lumshe ido tayi son Imran na ratsa dukkan sassan jikinta.
Jiki ba k'wari ta shirya, Imran ya rakata har waje, ya tarar mata Mai keke napep ta hau,
Cikin gida ya dawo ya fad'a kan gado, Idonshi ya rufe yana tunanin rayuwarsu, Ba abunda yake tunawa yaji farin ciki sai Noor, Yayi missing Hajiya, Alhaji, siblings d'inshi da Naseer but yayi alk'awari bazai koma ba, sai ya nemi halal d'inshi, Ya samu abunda zai rik'e kanshi, yanda idan ya koma ko ruwan gidan bazai sha ba, Kuma koda yaushe yana rok'a ma iyayenshi shiriya.
Tausayin Noor yake ji, He want to give her d best life, tunda ta taso cikin wahala take da k'uncin rayuwa, a ranshi Yace
"I promise to give u d best life my angel, da k'arfina da lafiyata zan nemi halal d'ina"
Mik'ewa yayi ya d'auko garin da ya siyo da gyad'a, Ya had'a da sugar yana sha yana yamutsa fuska, tunda uwarshi ta haifeshi bai tab'a shan gari ba, Da k'yar yake sha, Yunwa kad'ai tasa yasha shi , Ya gama ya wanke kofin, Yayi wanka ya shirya ya nufi Gidan liman.
Imran duk wahalar d'aukar blocks haka ya jure saboda ya riga ya sama ranshi he will endure it, But by mere looking zaka san bai saba wahala ba, sai zufa yake.
Rayuwa kenan Imran ne wai da d'aukar blocks, I pity you Imran😥
Noor ana tashinsu, wata k'awarta yar ajinsu tace "tazo su rik'a tafiya gida tare tunda unguwarsu d'aya, Noor ba musu ta bita tare da mata godiya, Har k'ofar gida suka kaita tace
"Gobe da safe ta shirya da wuri zasu biyo su d'auketa"
Uniform ta cire, tayi wanka, tasa riga da skirt na lace, ta feshe jikinta da turaruka masu bala'in k'amshi, da yake taci abinchi a makaranta so bata jin yunwa, Qur'ani ta dauka tana karantawa.
Gab da la'asar Imran ya shigo gida a gajiye, gaba d'aya joint d'inshi ciwo suke ga yunwa, Noor ta tarbeshi da murnarta, ta had'a Mai ruwan wanka yayi wanka yasa kayan shan iska.
Tausa take Mai, tana tambayarshi
"Ya wajen aiki ba wata matsala dai koh?"
"Eh babu my angel"
"Tohm Allah ya taimaka"
"Ameen"
"Kaci abinchi?"
"Eh naci, ko banci ba ganinki kad'ai ya isa ya k'osar dani"
Dariya tace
"I Luv yhu so much"
"I Luv yhu more n more"
Yai mata peck, itama ta mayar masa.
Ta gaya mishi tare da k'awarta zasu rik'a tafiya suna dawowa, sosai yaji dad'in haka sun samu sauk'in kud'in mota.
*Bayan wata hud'u*
Haka suka cigaba da rayuwarsu yau akwai gobe babu, Imran bai taba barin Noor da yunwa ba duk yadda zai yi ya samu mata abunda zataci sai yayi, Kullum sai yaje aikin blocks, har yanzu Noor bata San aikin da yake ba kenan, Imran duk ya rame yayi bak'i, kmr ba Imran d'in nan handsome classy guy ba, Ramar shi na damun Noor kawai ba yadda zatayi ne, Duk da talaucin da suke fama dashi hakan bai hanasu nuna ma juna tsantsar soyayya ba, kullum kamar zasu had'iye juna, Noor har yanzu ko b'atan wata bata tab'a yi ba.
Imran suna zaune a majalisar k'ofar gidansu, Wani jibril Yace
"Imran ji yadda kayi bak'i ka rame kamar ba kai ba"
Murmushi yayi Yace
"Toh yana iya, halin rayuwa kenan"
"Me zai hana kabar sana'ar nan ta blocks wlh bata dace da kai ba, ji yadda ka lalace"
"Idan na barta toh nayi Yaya? Ita kadai ce hanyata ta samu"
Shiru yayi na seconds sannan yace
"Akwai wani Alhaji da zan had'aka dashi yana Bada keke napep, amma kullum zaka kai Masa #1,500 sai dai matsalarshi d'aya bashi da mutunci ko kad'an tun ba akan kud'i ba, zaka iya in had'a ka dashi"
Imran ajiyar zuciya yayi
"Zan iya dan yafi mun sana'ar block d'in nan"
"Toh madallah, Gobe in Allah ya kaimu da safe kafin na wuce wurin aiki sai na kai ka wurinshi, Ku daidaita"
"Nagode sosai"
"Ba komai ai, Kar ka damu"
Daya koma cikin gida yake sanar da Noor yadda sukayi da Jibril, Murna sosai tayi kuma ta godewa Allah,
Hannunta ya rik'o yasa cikin nashi
"My angel kiyi hak'uri da situation d'in nan da muke ciki, In shaa Allah watarana komai zai wuce"
Murmushi tayi tace
"Ban damu da halin rashin da muke ciki ba, ko da k'wanzo zan rik'a ci kullum, kasancewata tare da kai shine farin ciki na da kwanciyar hankalina, damuwa da kaga inayi is because of you, nasan baka Saba wahala ba"
Rungumeta Imran yayi
"I soo much luv u my angel more than my own life, please ki daina damuwa dani, am okay with this life, akan naci haram"
"I love you Imran, I care for you, all I want is ur happiness, so dole zan damu"
"Bana kina damuwa my angel, I love u unconditionally
Wuyanta ya Fara kissing yana lasa, ya dawo kan fuskarta yana ta kissing ba tsayawa, Noor lamo tayi ta lumshe ido tana jin dad'in abunda yake mata, Romancing d'inta ya fara, itama nan ta fara romancing d'inshi, Imran gaba d'aya ta gama rikita shi ya kawo climax , Ba b'ata lokaci suka tsunduma wata duniya lol😜
Duk Sanda ya kusanci Noor, sai yaji sonta ya k'ara ninkuwa a zuciyarshi saboda natsuwar da yake samu daga gareta, kullum daban yake jinta (taimakon Ameerah lol)
Tare sukayi wankan, Bayan sun shirya tana kwance kan k'irjinshi yana hura mata iska a kunne, sai lumshe ido take, Har bacci mai dad'i ya d'auketa, Shima daga baya Imran baccin ya d'aukeshi.
Basu farka ba sai asuba, Yayi alwala ya tafi masallaci, Ita tayi sallarta a nan, Bayan ta idar tayi karatun Qur'ani, da azkar
Ruwan liptop ta dafa musu tasa a flask, dan shi kad'ai ne dasu a gidan, Wanka tayi tasa uniform tana jiran Imran ya dawo daga masallaci, su sha tea.
D'ari biyun da ta rage mai a aljihu, Ya siyo bread na d'ari,
A k'ofi d'aya suka sha ruwan liptop d'in, Yana sha yana bata, Bread d'in cewa yayi tayi taci ita kad'ai, Tace ba zata ci ba, sai dai suci tare, Tare suka ci, Ba don kowannensu ya k'oshi, sai dai su d'au na Annabawa
D'arin data rage, Ya bata
"My angel kiyi hak'uri da wannan"
Karb'a tayi tai murmushi
"Don't worry my dear, Allah ya baka Sa'a ya kare ka ya Sada ka da alkahirinshi a duk inda zaka Shiga"
"Ameen my angel, ina jin dad'in addu'o'inki a gareni, U're d best wife ever"
"U're also d best husband ever"
Sukayi dariya, Yayi hugging d'inta tare da amta kisses a fuska
"I Luv angel"
"I Luv u too my dear"
Jakarta ta d'auko tayi waje, dan taji horn na motarsu k'awarta Amal, Imran bin bayanta yayi da kallo yana murmushi sonta na ratsa jinin jikina, A fili ya furta
"NOOR KECE HASKE NA, KE KIKE HASKAKA RAYUWATA, IDAN BAKE RAYUWATA ZATA YI DUHU"
(Ni zee nace NOORUL IMRAN kenan hasken Imran).
Shiryawa yayi tsaf, Suka fita da Jibril, Ya kaishi wajen Alhaji Iro Na mata(Ana ce mishi Na mata ne saboda shegen son matanshi da auri sakin bala'i, indai akan mace ne zai iya kashe ko nawa ne, amma fa bashi da mutunci ta fannin kud'i, akan naira biyar sai yasa a d'aureka), Yayi introducing d'inshi wajen Alhaji ya tafi, Alhaji Na mata ya yaba da hankalin Imran, Bayan ya gindaya mai sharud'd'a, Ya bashi sabuwar keke napep dal a Leda, Yace daga yau zai fara aiki, Imran nata murna yana godiya
"Kar ka damu d'an samari, ni dai kawai inji dumus(wato kud'i)"
"In shaa Allah ba za'a samu wata matsala ba Alhaji"
"Yawwa haka nake son ji, sai na jika".
*Rayuwa kenan, Imran handsome guy ya zama D'an Adaidaita, Toh Noor Allah yasa kar mata su k'wace miki shi dan yanzu sana'ar mata zai Fara, Har sai ya gaji da ganinsu lol*
*TEAM NOOROUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
[11/8, 08:31] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣4⃣
*THIS PAGE IS FOR YOU MUHMEELAT LUV AND RABI'A HARUNA, nagode da k'aunar novel d'in nan da kuke*
Noor sosai taji dad'i ganin anba Imran Adaidaita, har cikin napep d'in ta shiga ta mishi addu'ar "Allah ya tsare yayi bud'i na alkhairi"
Imran ya amsa da
"Ameen my angel"
Shiru tayi da alamar damuwa d'auke a fuskarta
Shafar fuskarta yayi
"Ya dai my angel"
"Ina tsoro kar wata ta k'wace mun kai, nasan yanzu zakai ta ganin Yan' mata"
Dariya yayi yace
"Ohh my beautiful angel, Am all yours, ba wacce ta isa ta k'wace miki ni, ni wa ma zanso ina da kamarki, akanki na fara so kuma akanki na rufe, my heart belong to you alone, NOORUL IMRAN"
Bata San sanda tayi hugging d'inshi ba
"I love yhu, I Luv u soo much my love"
Peck ya mata
"I Luv yhu more my cwt angel, mu Shiga gida"
Imran ya fara sana'ar Adaidaita, kullum da safe idan Noor ta wuce makaranta shi kuma ya fita, A wurinshi keke napep d'in ke kwana, Noor sun fara WAEC Karatu take ba wasa, Imran ya siyan mata JAMB FORM ya cika mata, tayi submitting, LAW tasa.
Sosai Imran yake samun passengers tun ba mata ba, sunfi kowa tare shi saboda kyanshi, Shi kuwa ko d'aga kai ba yayi ya kallesu, sannan baya tsaya dogon ciniki dan kar yayi magana, Har ya kaisu inda zai ajiyesu baya magana, Su kuwa suta jan shi da hira, tsakaninshi dasu Eh a'ah, ko kuma yayi banza kamar bai ji ba, Da yawansu sun sha cewa ya basu numbernshi Yace"bashi da waya", Akwai wata da tace "zata siyan mishi waya"
Yace "Ba ya so"
Yan matan BUK da NORTHWEST Masu ji da class sun sha cewa suna sonshi.
Ranar wata asabar ya ajiye wata a bakin gate d'in BUK, sai ga wata kyakkyawar Budurwa yar gayu ta fito, rataye da Jakarta da wayarta IPhone 7, Tsayar dashi tayi cikin siririyar muryata tace
"Nasarawa GRA, Sultan road" Ta zuba mishi ido, gaba d'aya ya tafi da imaninta, bata tab'a ganin kyakkyawa irinshi ba,
Ba tare da ya d'ago kai ya kalleta ba Yace
"Muje"
Shiga tayi, K'amshin turarenshi ne ya daki hancinta, napep d'in tsaf-tsaf, Ji tayi ya sake shiga ranta dan tana son mutum mai tsafta.
Tana so ta mishi magana tana d'an tsoro kar ya disgata dan yadda ta lura dashi miskili ne bai cika son surutu ba,
Bakin katafaren wani gida tace "ya ajiyeta"
Bata fito daga Napep d'in ba tace
"Dan Allah ko zaka iya fad'a mun sunanka?"
Shiru yayi na seconds sannan Yace
"Imran"
"Nice name"
"Imran Dan Allah wani taimako zaka mun idan ba damuwa"
"Am listening"
"Dan Allah ina so ka rik'a zuwa kana kaini makaranta ina biyanka a wata, kaga unguwar nan ina shan wahala kafin na samu napep, wataran har missing lectures d'ina nake, akwai ranar da har exam d'ina nayi missing"
Imran shiru yayi yana nazari sai can Yace
"Ok ba Matsala" shi dai kawai burinshi ya samu kud'in da zai kula da Noor,
Sosai taji dad'i tace
"Nagode sosai Imran, ga phone d'ita ka samun numbernka"
Ba musu ya karb'a ya sa mata
Ta zaro 1k ta bashi, zata wuce Yace
"Tsaya ki karb'i canjinki"
"No ka barshi"
Kafin ya sake wata magana ta shige cikin gida, Yaja napep d'inshi yayi gaba.
Noor kai ya d'au zafi wataran har 6 tana makaranta, idan suna da papern yamma, bata samun wani isasshen bacci, Imran dama idan ya fita tun safe sai k'arfe tara na dare yake dawowa, idan Noor na gida da rana, zai dawo yaci abinchi su d'an tab'a love ya fita sai dare, Yanzu kam basa rasa abun ci, wataran har kaza ko kifi ko gasasshen nama yake siyo musu suci abun su.
Gida ya wuce dan Noor na nan, Yana shiga Gidan wani k'amshin turaren wuta Mai dad'i ya daki hancinshi, Lumshe ido yayi yana godewa da Allah da ya bashi Noor a matsayin mata, Kafin ya k'arasa d'akin, Noor ta fito ta rungumeshi ta mishi kisses a fuskarshi,
Binta kawai yayi da kallo, Yana kallon kwalliyar da ta mishi, Cikin doguwar Riga ta material, d'inkin ya kamata sosai ya mata kyau tana ta k'amshi, Janshi tayi zuwa toilet, ta tayashi ya cire kayanshi, Ta Kama mishi yayi wanka, Kayan ma ita tayashi sawa, ta fesa mishi turare, Ta jashi zuwa falo,
Serving d'insu tayi Jollof spaghetti tasha busasshen kifi, tana ta k'amshi, Ta tsiyaya zob'o a Kofi da yasha kayan had'i, Ita ta rik'a bashi a baki, shima yana bata, sai da suka k'oshi, Suka kora da zob'o.
Kwashe kwanukan tayi ta wanke, ta dawo kan cinyarshi ta kwanta
Ya shafi goshinta yace
"My angel"
"Na'am my love"
Kwashe yadda sukayi da budurwar nan da ya d'auko daga BUK yayi ya gaya mata.
Shiru tayi bata ce komai ba, zuciyarta taji na mata ba dad'i(kishi)
"My sweet angel ko baki yarda na rik'a d'aukarta ba"
"A'ah my dear na yarda, ina tsoron a k'wace mun kai ne, I soon much Luv you"
"My angel nasha gaya miki, ke kad'ai ke sarauta a Birnin zuciyata, ba wacce ta isa ta k'wace miki mulkinki"
"Ina sonka mijina"
Zaunar da ita yayi, Bakinshi taji cikin nata ya fara kissing d'inta, sai da yasa ta manta wacce duniya take, Sannan ya saketa, lips d'inshi ta Kama ta fara tsotsa kamar ta samu lollipop, Tsawon minti biyu tana tsotsa sannan ta sakeshi tana kallonshi ido cikin ido,
Ta shafi lips d'inshi tace
"Promise me, lips d'in nan naka, ni kad'ai zan rik'a kissing d'insu ina tsotsa, har abada ba wacce zata ko tab'asu da hannunta"
"I promise you my angel"
"Ur lips re soo sweet my love, I Luv kissing them" ta fad'a tare da d'an rufe fuskarta
"Urs re sweeter my angel"
Sun dad'e suna farantawa junansu rai, Sannan Noor ta rakashi yaja napep d'inshi ya fita, Cikin gida ta dawo cike da so da k'aunar Imran, littafinta ta d'auko tana karantawa dan saura paper biyu su gama WAEC, upper week kuma zasuyi JAMB.
*WACECE BUDUWAR DA IMRAN YA D'AUKO*
Nana Fiddausi d'iyar Alhaji Muhammad Yaro, hamshak'in mai kud'i ne yana cikin masu fad'a aji a garin kano, Matarshi d'aya Ya'yanshi biyar, Uku maza sai Fiddausi yar' shekara 20, wacce ake cewa Nana sai k'anwarta Fatima, Iyayensu na matuk'ar sonsu kuma suna basu duk wata kulawa da ta dace, Yana sakar musu kud'i sosai, Duk da haka baiyi wasa ba wajen ganin ya basu tarbiyya mai kyau, suna da ladabi da natsuwa,
Fiddausi BUK take level 2 tana karantar mass com, Ta fito tana jiran driver'nsu tana ganin Imran taji duniya ba Wanda take so kamarshi, shine ta tari napep d'inshi dan ta samu magana dashi, zancen da tace Mai tana wahalar samun napep, k'arya take driver ke kaita yana d'aukota makaranta kullum.
Mahaifinsu ta samu tace mishi bata so driver na akaita makaranta dan kullum sai yaja tayi late, ko kuma yak'i zuwa d'aukarta da wuri, Baban yace "sai a samu mata wani driver, dan bai yadda tayi tuk'i da kanta ba"
Tace "na samu wani mai napep da zai rik'a kai ni"
Yace "kinfi so mai napep ya kaiki"
Tace "Eh Daddy"
"Shikenan Allah ya Bada Sa'a" Shi duk abunda ya'yanshi keso shi yake so
Ta amsa da "Ameen"
Ta fita tana murna.
Ranar kasa bacci tayi tana tunanin Imran, Alla-alla safiya take tayi, Taga Imran, A ranta tana cewa "nasan Imran bazai k'i ni ba, ba abunda bani dashi, ba namijin da zai kalleni bai k'ara kallona ba, maza nawa ma ke sona ina musu wulak'anci, So I will try my best to win his heart"
_Ni zee a raina nace indai a idon Imran ne toh tamkar namiji kike, Dan NOOR Tasha gabanki a komai da ake buk'ata a jikin mace, Noor kad'ai yake ma kullum mace sauran matan duk maza ne a idonshi_
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣5⃣
Fiddausi ce tsaye bakin dressing mirror d'in d'akinta, Tasha kwalliya cikin doguwar Riga ta Levoi le, Tayi kyau sosai, Gyara kwalliyarta tayi a fili ta furta
"Kai nai ma kwalliyar nan Imran"
Wayarta ta fara ringing, Dubawa tayi taga Imran ne, Jakarta ta d'auka tayi waje
Sallama ta mishi, Ya amsa ba tare da ya d'ago ba,
Ta Shiga napep d'in jiki a sanyaye ganin bai kalleta ba, Har suka isa gate d'in makarantar ba Mai cewa kowa komai, Tana sauka ta tsandala ihu tare da rik'e k'afarta, A gigice Imran ya kallota yana tambayarta
"Lafiya me ya sameki?"
"K'aya na taka"
Kauda kanshi gefe yayi Yace "Sannu"
A ranshi yace "wannan anyi yar rainin hankali dan ta taka k'aya, shine zata tsandala wannan uban ihun", Yaja napep d'inshi yayi gaba.
Fiddausi dariya tayi, zuciyarta cike da far in ciki tayi hakane dama dan ya kalleta, bata san ko Lura da kwalliyarta bai yi, dan da za'a tambayeshi wane irin kaya tasa, bazai iya fad'a ba.
Fiddausi yau bata fahimci lecture komai ba, shiru tayi tana tunani, k'awarta Fa'iza ta lura da ita, Da suka fito lecture take tambayarta
"Me ke damunki ne Nana? na ganki yau ba kamar kullum ba"
Sauke numfashi tayi
Ta fad'awa k'awarta had'uwarta da Imran, da yadda ta kamu da son shi,
Fa'iza tuntsire tayi da dariya tace
"Ke kuma a Mai napep kika k'are, wlh Allah ne ya tashi kamakisaboda yadda kike wulak'antawa maza, ya had'aki da Mai napep"
"Ke wlh he is damn handsome, ga class"
"Dallah gafara har wani class ne da mai napep"
"Hmm fa'i kenan wlh baki ganshi bane"
Wata dariyar ta sake fashewa da ita,
Fiddausi ranta ya d'an fara b'aci tace
"Bana son dariya fah, ni kawai ki bani shawara ya zanyi"
"Ki fad'a mishi abunda ke ranki"
"Kina ganin nayi haka banyi rashin kunya ba"
"Ba wata rashin kunya, abunda ke ranki kika fad'a"
"Toh shikenan k'awata"
Haka suka cigaba da hirarsu.
Tana fitowa taga Imran har yazo, Kama hannuna Fa'iza tayi tace
"Muje Ku gaisa da Imran, sai ki gani idan abunda nake gaya maki gaskiya ne ko k'arya"
Fa'iza da taga Imran sakin bacci da hanci tayi tana kallonshi, har suka gama gaisawa bai d'ago kai ya kalleta ba, Jan Fiddausi tayi gefe
"Ke wlh ya had'u, ga class"
Fiddausi tayi murmushi tace
"Bana gaya miki ba"
Nan sukayi sallama, Fiddausi ta shiga napep, suka wuce.
Sai da suka kawo bakin gidansu,
Bata fita daga napep ba, Marairaice murya tayi ta fayyace mai abunda ke zuciyarta, Imran bai yi mamakin jin abunda tace ba, dan matan da suka fita komai ma sunce suna sonshi,
Ba tare da ya juyo ba Yace mata" Shi yana da mata kuma bazai iya mata kishiya ba"
Kamar diran mikiya haka taji zancen dan bata tab'a tunanin Imran nada mata ba, Murmushin k'arfin hali tayi tace
"Toh shikenan Imran, nagode but please can we be friends?"
"No problem"
"Nagode"
Ta fita napep d'in Jiki a sanyaye,
Tana Shiga d'aki ta fad'a kan gado, tana ta kuka, A ranta tana cewa
"Dole in hak'ura da Imran, dan ni bana son mai mata, kuma bazan so na Shiga tsakaninshi da matar shi ba"
Ta cigaba da kukanta tana rok'on Allah ya cire mata son Imran.
Noor ta gama WAEC, sun samu hutun sati biyu kafin su Fara NECO, ranar wuni tayi bacci, Baccin huce gajiya.
Fiddausi na k'ok'arin fitar da Imran daga ranta, Amma yanzu sun saba, suna d'an tab'a hira, duk da bai cika sakewa da ita ba, Itama tana kiyayewa bata cika shige mai ba.
Hutun da Noor ta samu, soyayya sosai suka sha da Imran, taga kalar soyayya iri-iri daga Imran, Son shi ya k'ara ninkuwa a zuciyarta, haka shima sonta kullum k'aruwa yake a zuciyarshi, A cikin hutun tayi Jamb, The next day result d'inta ya fito ta samu 305, Farin wajen Imran da Noor ba'a magana.
Imran ne goye da Noor, Yana zagaye falon su, Sai dariya take, Ajiyeta yayi kan kujera Yace
"Wash na gaji"
Hannunshi ta rik'o
"Uhmm Allah baka isa ba, sai ka k'ara goyani" Tana magnar cikin shagwab'a
"Toh bari sai anjima idan na huta"
"A'ah ni wlh yanzu nake so"
"Toh shikenan hau in goyaki"
Ya duk'a, tana zuwa hawa ya matsa saura kad'an ta fad'i, aikam ta bishi, shi kuma yana gudu tana binshi, suna ta guje-guje, d'aki ya ahiga ya fad'a kan katifa, ta fad'o kanshi
Rungumeta yayi, Ya fara sarrafata yanda yake so.
*Bayan wata biyu*
Noor ta gama NECO, sai zaman jiran result, Imran nata sana'ar shi ta napep, basu da wata matsala, Har yanzu shi ke kai fiddausi makaranta ya d'aukota, Duk wata 20k take bashi,
Noor da wata irin kasala ta tashi, sai faman amai take da zubar da miyau,
Imran hankalinshi duk ya tashi, Ya kira Mijin Ameerah, Bayan yayi yan gwaje-gwajenshi yake sanar dasu tana d'auke da ciki na wata d'aya, Anan Imran yayi sujjada yana godewa Allah, wai shine zai zama Uba, Noor itama farin ciki tayi sosai.
Tun daga ranar kula da tarairayar da Imran keba Noor ta k'aru, Shi ke aikin komai a gidan kasancewar cikin na bata wahala, Girki ne kawai take yi, shima ba kullum ba wataran sai dai ya siyo.
Wajen k'arfe tara Imran ya kamu hanyar gida saura kad'an ya k'arasa, Layin shiru ba kowa, magrib nayi kowa yake shigewa gida,
Wasu k'attin maza ya gani tsaye a gabanshi, kowanensu d'auke da k'atuwar sanda,
"Innalillahi wa inna ilaihr raji'un" Ya Fara furtawa
Zagaye napep d'in sukayi Babban cikinsu Yace
"Oya fito ka bamu key"
Imran fitowa yayi amma yak'i basu key
"Dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ba tawa bace"
"Shut up! Key muka buk'ata ba dogon zancen ba"
Imran duk'awa yayi kamar zai d'auki abu, Gudu ya fara, suka bishi, Nan da nan suka kamoshi, dukan tsiya suka mai suka k'wace key d'in, suka tafi suka barshi nan yana numfashi sama-sama, Bayan wasu mintuna ya mik'e da k'yar, yana tafiya a hankali.
Noor gabanta taji nata fad'uwa, ta kasa zama sai zirga-zirga take a falo, Imran ne ya shigo bakinshi nata jini, Noor cike da tashin hankali tayi kanshi, ta rik'o shi
"Me ya sameka? Waya maka haka?"
Kan kujera ya fad'a yana nishi, Da gudu ta fita, Mijin Ameerah ta Kira, Ameerah ma ta biyo shi a baya,
Dr hankalinshi ya tashi ganin Imran, tambayarshi yake
"Me ya sameshi?"
Imran kasa magana yayi yana ta nishi, Noor kuwa sai kuka take kamar ranta zai fita,
Ya mishi dressing ciwokan da yaji, Ya bashi drugs da zasu mishi healing ciwonka da wuri, Bayan ya huta na mintuna
Dr ya sake tambayarshi "me ya sameshi?"
Ya fad'a musu duk yadda akayi, Hankalinsu ya tashi
Dr yace
"Ya kwantar da hankalinshi gobe da safe, suje Police station akai report"
Noor kwana tayi kuka tana addu'ar Allah ya saka ma Imran wanda ya mishi haka, shi kam Imran tuni yayi bacci dan maganin da Dr ya bashi hadda nasa bacci, Kallonshi take tausayinshi na sake kamata
"Ya Allah ka kawo ma Imran k'arshen wahalar nan".
Washegari an kai report police station, Imran yaji sauk'i sosai, Tsoronshi d'aya Alhaji Iro na mata, ko zai saurareshi
Imran na kwance kan cinyar Noor, Tana shafa gashin kanshi, tana kwantar mai da hankali
"In shaa Allah my dear, Alhaji zai fahimceka kowa yasan k'addar....."
Bata k'arasa magana ba taji an bankad'u k'ofar falon ana cewa
"Banda ni bansan k'addara ba, yaje ya siyar da napep zai had'a labarinshi na k'arya toh wlh sai an biyani" Alhaji Iro na mata ne ke maganar
"Officer Ku shigo Ku tafi dashi"
Yan Sanda ne suka shigo su uku,
Imran da sauri ya mik'e yana cewa
"Dan Allah ka tsaya ka saurareni wlh ba siyarwa nayi ba"
"Ba abunda zan saurara"
Noor zubewa k'asa tayi tana kuka tana rok'on Alhaji
"Ka dubi girman Allah kar ka rabani da mijina, wallahi shi kad'ai ne gatana bani da kowa sai shi sai Allah, wallahi ba siyarwa yayi ba"
Alhaji ko kallo bata ishe shi ba, yace
"Officer tafi dashi"
Kama Imran sukayi suka sa mai handcuff (ankwa), Yana hawaye Yace
"Alhaji dan girman Allah Kada ka rabani da matata, ko dan junan biyu da take dashi kaji tausayinta"
Haka suka ja Imran zasu tafi dashi, Noor nan ta fad'i tana kuka tana birgima, Imran har cikin zuciyarshi yake jin kukanta amma bashi da yadda zai yi,
Juyowa yayi Yace
"My angel kukan ki yafi mun zafi akan halin nan da nake ciki, Dan Allah ki daina kuka, kiji tausayin zuciyata, ki daina azabatar da ita da kukan ki, Allah na tare damu kuma yana sane damu, I will come back for you, tare zamuyi rainin Cikin mu"
Noor had'iye kukan tayi amma bata fasa hawaye ba, Tana gani aka tafi da Imran
K'asa ta fad'i ta cigaba da birgima tana kuka.
*Allah Sarki Noor da Imran Ku kam kunga rayuwa😰*
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣6⃣
Noor mik'ewa tayi ta nufi gidan Ameerah tana ta kuka, Cike da tashin hankali tayi kanta tana tambayarta
"Lafiya Noor me ya faru?"
Nan take sanar da ita, Ameerah salati tayi, ta rungumo Noor jikinta tana lallashinta, Da fad'a mata kalamai masu kwantar da hankali kuma ta d'auki k'addara.
Noor ranar kwana tayi kuka, tana sallar dare, tana rok'on Allah ya fitar da Imran daga wannan musiba da ta same shi, Ameerah ta kawo mata abinchi ko bud'e kular batayi ba balle tasan me ye a ciki.
Imran kuwa suna zuwa suka jefashi Cell, ba irin rok'on da bai musu ba, amma ina basu saurareshi ba, cewa ma sukayi idan ya cigaba da damunsu dukan tsiya zasu mai, Alhaji Iro kuwa cewa yayi kada a sake shi sai ya kawo napep ko kud'in napep 600k, Imran ba abunda yake sai kuka, ba komai yasa shi kuka ba sai tunanin wane hali Noor take ce, Bazai iya jure kasancewa ba tare da Noor ba, Haka ya kwana kuka.
Washegari Noor tayi wanka bata ci komai ba cikinta har kukan yunwa yake, idonta duk sun kumbura sunyi jajir saboda kuka, Hijab tasa ta jawo drawer da Imran kesa kud'i, 500 ta d'auka, Gidan Jibril ta shiga, Matarshi ta tarar a falo, Matar tama mata jaje cike da tausayinta, Noor tace "ta mata sallama da mijinta".
"Noor Dan Allah kiyi hak'uri da abun nan da ya Faru, bansan haka abun zai zama ba, wallahi da ban had'a Imran dashi ba, da abun ya faru kuma naje naba Alhaji hak'uri ashe yan sanda yazo dasu, Dan Allah kuyi hak'uri In shaa Allah komai zai daidaita" Jibril k'arasa maganar d'auke da damuwa a fuskar sa,
"Ba komai, k'addara ce kuma ba Wanda ya isa ya wuce k'addararasa mu wannan itace tamu k'addarar, munyi imani da k'addara, Allah kad'ai ya isa ya magance muna matsalar" Ta fad'i maganar tana hawaye
"Hakane Noor, daina kuka, addu'a kawai zamuyi tayi"
Ta share hawayenta tace "kwatancen police station d'in da aka kai Imran nake so kamun"
Bai tsaya wata-wata ba ya mata kwatance
Ta mishi godiya, ta fito
Jibril da matarsa suka bi bayanta da kallo cike da tausayinta.
Noor da gudunta ta shiga police station d'in, hankalinta ya tashi tausayin Imran ya kamata da ta ganshi, duk ya fita hayyacinsa, Yana ganinta sai hawaye, hannunshi ya ziro ta k'arafu nan, ta Kama hannun ta rik'e gamm suna ta kuka ba mai lallashin wani, Tsawon mintuna suna kuka, sannan Imran ya tsaya da nashi kukan, Ya fara share mata hawaye
"Daina kuka my angel, bana son kukan ki, kukan ki na sani wani hali, hak'uri zamuyi mu rungumi k'addara, wannan ITACE K'ADDARATA ko ince K'ADDARARMU"
Tsayar da kukan tayi ta zuba mishi ido,
"My dear kalli yadda ka koma, Allah ya saka maka, Allah ya bi maka hak'k'in ka"
"Ameen my angel, promise me ba Zaki k'ara kuka ba"
D'aga mishi kai kawai tayi dan tasan ba zata iya daina zubar da hawaye ba akan halin da Imran yake ciki.
"Yawwa Smile for me"
D'an murmushin k'arfin hali tayi
"Har kinsa zuciyata tayi sanyi da murmushin nan naki"
Hannunshi ta Kama ta mishi peck, shima ya mata a nata, Ya shafi cikinta yace
"Ya lafiyar babynmu?"
"Lafiya lau yake, sai dai yayi missing Daddynshi"
"Daddynshi very soon will be with him"
Jakarta ta bud'e ta fiddo breakfast d'in da Ameerah ta kawo mata, Chips da sauce, A baki ta rik'a bashi shima yana bata har suka cinye. Bata bar police station d'in ba sai dare, shima sai da Yan sandan sukazo, suka korata, Da kuka suka rabu, kowannensu na hawaye.
Data koma gida sabon babin kuka ta bud'e tana ta kuka, tana magana ita kad'ai
"Bazan iya jure ganinka cikin halin nan ba Imran, I have to find a way out"
Kanta har wani nauyi ya mata saboda rashin bacci da kuma kuka.
Washegari jibril tace ya mata kwatancen Gidan Alhaji Iro, Zata je ta rok'e shi, Jibril ba musu ya mata Yace "k'ila yaji tausayinta ya yafewa Imran" (nikam nace da zaiji tausayinta ai da tun sanda suka zo tafiya da Imran zai ji)
Alhaji Iro ne zaune a had'add'en falonshi dake guest house d'inshi, Kayan marmari ne gefenshi yana sha, Noor tayi sallama ta shigo, Kallonta yake tun daga sama har k'asa, sai da ta tsargu da irin kallon da yake mata, Zama tayi k'asa kan carpet har lokacin bai daina kallonta ba, Muryarta na rawa tace
"Alhaji ka dubi girman Allah, kaji tausayinmu kasa a Saki mijina, wallahi ba siyarwa yayi ba, Dan Allah ka yafe mishi" ta fashe da kuka
Alhaji kallonta yake a zuciyarshi yana ayyana abubuwa da yawa, sai can Yace
"Daina kukan yan mata, zansa a sake shi.
Da sauri ta d'ago kai ta fara zuba mishi godiya
Yar'dariya yayi Yace
"Daina saurin godiya, kinsan rayuwar nan bani in baka ne, dan haka kema Zaki taimaka mun"
Cikin rashin fahimtar maganarsa ta kalleshi tace "Wane irin taimako Alhaji?"
Dariya yayi Yace
"Jikinki nake so ki bani na kwana d'aya"
"A'uzubillahi minash shaid'anir rajeem, kasan me kake fad'a kuwa?"
"Lafiya toh me ye a ciki?"
"Ina matar aure zaka ce in baka jikina, wallahi nafi so Imran ya tabbata a cell da inyi abunda kake nema"
"Aikuwa zai tabbata acan, I assure you idan har bazaki bani had'in kai ba toh wallahi Imran zai ta zama a can cikin uk'uba da azaba"
"Allah yafi ka, Kai baka isa kama mishi abunda Allah bai mishi ba, kuma ka jira kaga k'arshen ka dan bazai yi kyau ba"
Tana fad'ar haka ta fice.
Alhaji cizon yatsa yake yana tunanin muguntar da zai shirya musu, wacce zata sa dole Noor dole ta dawo gareshi, Can yayi dariyar mugunta Yace
"Yarinya da kanki zaki dawo gareni, Baki san waye Alhaji Iro na mata ba"
Daga ranar Alhaji yasa a rik'a azabtar da Imran, Noor kuwa yasa a hanata zuwa gurinshi, wani abun cin ran ma sai taje police station d'in za'a fara jibgarshi, tana jin ihunshi a hanata k'arasa wurinshi, haka zatai ta kuka, ta koma gida.
Fiddausi hankalinta ya tashi jin Imran shiru kwana biyu, tayi ta kiran numbernshi bata samu, bata san gidanshi balle taje, ta damu sosai, kullum cikin kuka take, tana addu'ar Allah yasa ba wani abu ya samu Imran ba, dan har yanzu tana son shi.
Kwana uku Noor bata sa Imran a ido ba, gaba d'aya ta fita hayyacinta, ta rame tayi bak'i, ga laulayin ciki, Imran shima yana cikin matsananciyar damuwa na rashin ganin Noor da sanin halin da take ciki, Ga azabtar dashi da ake kullum, Noor kullum tunanin mafita take, Naseer ya fad'o mata a rai, wayarshi ta d'auko ta kunna ko zata samu numbern Naseer a ciki, ta sanar dashi, dan a tunaninta suna waya da Naseer, Ta duba duka contact d'inshi ba numbern Naseer, Dafe kanta tayi saboda takaici, wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta.
Tsawon mintuna bata motsa daga inda take ba, Wayar ta fara ringing, Dubawa tayi taga mai Kira Fiddausi ta gani, kamar ba zata d'auka ba, sai da ta kusa tsinkewa tayi picking, Bayan sun gaisa take tambayarta "Ina Imran?"
Fashewa da kuka tayi ta sanar mata duk abunda ke faruwa,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Fiddausi ke ta maimaitawa sannan tace
"Yi mun kwatancen gidanku gani nan zuwa yanzu"
Kwatance Noor ta mata.
In few minutes time sai gata, Noor nata kuka, lallashin Noor take
"Ki kwantar da hankalinki, jarabawa ce daga Allah, sai kunyi hak'uri, amma ina miki albishir Imran bazai kwana a cell ba, Yau d'in nan za'a sake shi"
Bata san sanda ta rungume Fiddausi ba,
"Thank you so much Fiddausi, Allah ya saka miki da gidan aljanna"
"Ameen Noor kar ki damu, taso muje"
Hijab Noor tasa, Suka fita, Motar Fiddausi na waje da driver, Suka shiga driver yaja su, basu zarje ko'ina ba sai gidan Alhaji Iro, Magana Fiddausi ta rad'a mata a kunne sannan ta fiddo yar' k'aramar waya ta bata,
Noor ta shiga gidan a falo ta sameshi, Yana ganinta farin ciki ya lullub'e shi, a zahiri amma Yace
"Me kika zo yi gidana?"
Ta marairaice murya tace
"Nazo na gaya ma na amince"
Dariya ya fashe da ita
"Yawwa ko kefa yan mata, irinku ai sai irinmu na d'an kwasar dad'i daga gareku, yanzu abunda za'ayi ki dawo anjima bayan sallar isha'i"
Ta amsa da "Toh" ta fice
Alhaji Iro Yace "waya gaya miki borno gabas take, yau zan dirji dad'i, irin wannan kaya haka ai sai irinmu na latsawa"
Ya fashe da wata dariya.
Daga Gidan Alhaji, banki suka wuce, Fiddausi ta karb'o miliyan d'aya daga account d'inta, Daga nan suka wuce police station, tace "Noor ta zauna a mota tana zuwa", DPO ta samu tayi magana dashi.
K'arfe 8:30 a gidan Alhaji tama Noor, Har cikin d'aki yaja Noor, yana ta washe baki,
Riga ya fara cirewa, Noor na tsaye kanta a sunkuye k'asa,
"Ya kika tsaya, ko inzo in cire miki kayan ne?"
"A'ah na hutar da kai"
Kanta tasa cikin hijab kamar tana k'ok'arin cirewa, Waya ta d'auko numbern Fiddausi ta kira,
Dariya yayi, Ya cire wando daga shi sai boxers ba riga, Yayo kan Noor kenan yaji an bankad'u k'ofa, Yan jarida, da yan Sanda tare da Fiddausi suka shigo, Alhaji Iro zaro ido yayi, yana neman hanyar guduwa, kamar ya nutse k'asa dan kunya, sai d'aukar shi video suke, har recording d'in maganar banza da ya rik'a mata ranar da taje tace mishi ta amince, ta kunna yan jarida sukayi recording,
Kud'i a cikin jaka Noor ta jefa mishi tace
"Ga tsiyarka nan, Allah ya raba kowa da dukiya irin taka, ka dai ji kunyar duniya, idan baka tuba ba haka zaka ji kunyar lahira wacce tafi wannan", Fiddausi taja hannunta suka fita, suka barshi nan da Yan jarida, Fiddausi ta biya su kud'i masu yawa tace su yad'a shi, duniya ta ganshi.
Police station suka wuce, aka saki Imran, Da gudu Noor taje ta rungumeshi, shima ya rungumeta sai kukan farin ciki.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
ZEELISH
[11/16, 20:19] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
9⃣7⃣
*This page is for you Aishat A Muhd😘 Ina tayaki murnar kammala novel d'inki YAYI SAKE🌲Itz such an amazing n exceptional novel, You really try 👍🏻 Allah ya k'ara Basira da d'aukaka*
A motar Fiddausi suka koma gida, har cikin gida ta rakasu, Dukkansu suna zaune falo, Imran da Noor sai godiya suke mata.
Fiddausi tace
"Godiyar ta isa haka, ba komai ai, yiwa kaine, idan ka taimaki wani kaima sai Allah ya taimake ka, kuma baka san ranar da mutum zai ma ba"
Noor tace "Hakane"
Imran baice komai ba danshi ya kasa yarda da Fiddausi, gani yake tayi hakane dan ya aureta.
Fiddausi ta cigaba da cewa
"Me zai Hana Imran muje wurin Babana ya samar maka aiki, ko dan ku huta da wahalar nan da kuke ciki"
Wani mugun kallo ya watsa mata Yace
"Bana buk'ata, Wahala kuma Allah yana sane damu shi zai mana magani"
Fiddausi jikinta yayi sanyi tace
"Toh shikenan, Allah ya muku bud'i na alkhairi, ni zan wuce"
Ta mik'e
Ya amsa da "Ameen" a tak'aice,
Noor kwata-kwata bata ji dad'in yadda Imran yayi ba, Ta tashi ta rakata har bakin mota, Fiddausi ta rik'o hannunta tace
"Wallahi Noor bana nufinku da sharri sai alkhairi, ina tausayin halin da kuke ciki, shiyasa naga ya kamata na taimaka muku, na had'a Imran da Daddy ya samar mishi aiki"
"Na sani Fiddausi, In shaa Allah zanyi k'ok'arin fahimtar dashi, Allah ubangiji ya saka miki da alkhairi"
"Yawwa kiyi k'ok'ari Dan Allah banson ganinku a halin nan, Ameen"
Fiddausi ta wuce Noor ta dawo cikin gida.
Ruwan wanka masu zafi ta had'a, ita ta mishi wankan ta gasa mishi jiki duk tabon duka ne a jikinshi sai auchh! wash! yake cewa, sai da tayi hawaye, ta shirya shi, Lafiyayyen abinchi da Ameerah ta aiko musu, suka ci suka k'oshi, Kwance take kan k'irjinshi yana shafa bayanta,
"My dear" ta Kira shi cikin siririyar muryarta
"Na'am my angel"
"Me yasa ba zaka je wajen Baban Fiddausi ba?"
Ajiyar zuciya yayi Yace
"Masu kud'in nan ba yarda nayi dasu yanzu ba, baka san taya suka tara dukiyarsu ba, wajen Neman gira a rasa ido, gwara na tsaya inda Allah ya ajiyeni ina neman halal d'ina"
Mik'ewa zaune tayi tace
"Ka yarda da Allah, kuma Allah yaga zuciyarka halal d'inka kake nema, ka sani ko alkhairi ke kiranka kana k'in zuwa, kaje ka gani idan kaga aikin da zai baka akwai matsala sai ka barshi, wahalar nan da kake tana damuna, bazan iya jure ganinka haka ba, yanzu haka kake so d'an da zamu haifa ya taso cikin wahala" Ta k'arasa maganar da hawaye,
Rungomuta yayi jikinshi
"Its okay my angel, Gobe In shaa Allah zanje na samu Fiddausi, stop crying"
"Promise me zaka je"
"I promise my cute angel"
Dariya tayi tace
"I love yhu darling"
"I love you more, kinsan me?"
Ta girgiza kanta alamar a'ah
"Am eager naga cikin nan naki yayi girma, naga ya angel d'ina zata rik'a tafiya" Ya fashe da dariya
Ta turo baki zatayi magana, bakinshi kawai taji cikin nata, sai da ya tsotsi bakinta son ranshi, Ya cire bakinshi, idonshi sunyi ja kamar d'an maye yana maida numfashi da k'yar Yace
"I miss everything about you darling, I miss you like hell" Ya jawota jikinshi ya fara romancing d'inta, itama tana mayar masa martani, kamar zasu had'iye juna, Sun farantawa juna rai ba kad'an ba.
Washegari tunda safe yaje gidansu Fiddausi a bakin gate ya tsaya ya kirata ta fito, Da ta ganshi tayi farin ciki sosai. Sashen Babansu ta kaishi, ta ma Daddynta bayanin komai, ta fita ta barsu su biyu,
Daddynta ya yaba da hankalinshi ya tambayeshi "me ya karanta a school?"
Yace "Mechanical engineering"
"Very good course, zan had'aka da brother na yana da company da yake motoci, yanzu tashi muje wurinshi"
Daddyn Fiddausi ya had'a Imran da k'anin shi Alhaji Muhammad Labaran wanda ke da Babban company na k'ere motoci duk fad'in Nigeria da k'asar waje ansan company *LABARAN MOTORS*, Alhaji labaran ya yaba da hankalin Imran kuma ya karb'e shi hannu biyu, Yace daga Yau zai fara aiki, yana so yaga yadda ya iya aiki sai yasan matsayin da ya dace ya bashi, Imran sosai yayi murna dan da ga
ni Alhaji Labaran mutumin kirki ne.
Alhaji Labaran hamshak'in Mai kud'i ne ya taka Daddyn Fiddausi a kud'i, uwarsu d'aya ubansu d'aya, Suna son junansu kuma kan iyalansu a had'e yake, Alhaji Labaran nada mata d'aya da Ya'ya hud'u, d'aya mace uku maza, Yana ji da iyalanshi abunda suke so shi yake musu, kuma yana masifar son matarsa saboda kyawawan halinta.
*Bayan wata uku*
Imran sun shak'u sosai da Alhaji Labaran, har gidanshi yana zuwa ya saba da matarshi da Ya'yanshi, duk cikin employees d'inshi yafi son Imran, ya sakar mishi komai na company ko meeting za'ayi shi yake turawa yayi representing d'inshi, Ya nad'a shi MD na company, Ya bashi kuma had'add'en gida a Hotoro, Imran kud'i sun fara shigowa yayi fari da kyau, Ya dawo Imran d'inshi nada d'an gayu d'in nan, Noor ma tayi fresh tayi kyau, cikinta ya d'an fara fitowa, bata da k'awa kamar Fiddausi sun shak'u sosai.
Imran ya d'an duk'a, Noor ta sa mishi hula tace
"Kayi kyau my dear"
"Dole inyi kyau tunda cute angel d'ina ta shiryani"
Dariya tayi
"Yawwa kar in manta anjima zamuje ki gaida Hajiya(matar Alhaji Labaran)"
"Tohm, dama ina so naje na gaisheta"
Ta mishi rakiya har bakin mota tare da mishi addu'ar "Allah ya tsare"
Da daddare bayan Imran ya dawo daga office, Suka shirya zuwa Gidan Alhaji Labaran, Gidanshi mansion house ne, ya had'u iya had'uwa, Suna shiga gidan gaban Noor ya fara fad'uwa,
A falo suka tarar da yaran, da gudu d'an k'araminsu da bazai wuce shekara biyar ba yazo ya rungume Imran, D'aukarshi yayi ya d'aga shi sama
"Anwar yane ina Momy?"
"Tana sama"
D'aya daga cikin yaran ne da bazai wuce shekara goma ba
Yace
"Let me call her"
Ya hau sama da gudu
K'arasawa sukayi cikin falon suka zauna, Yaran Noor taji sun burgeta, tana jin son su cikin ranta,
Hajiya ce ta sauko, daga ganinta naira ta zauna mata, kyakkyawa ce sosai kuma fara tas yaran duk da ita suke Kama, Yar' budurwace biye da ita a baya wacce ba zata wuce shekara sha hud'u ba, Da far'arta ta sauko,
"Ah Imran ne a Gidan namu, sai yau kaga damar kawon mun yar' tawa"
Noor da kanta ke sunkuye ta d'ago kanta suna had'a ido taji wani iri a jikinta, haka itama Hajiya taji.
Gaisheta tayi, ta amsa da far'a tana jin son Noor a ranta tace
"Ya sunanki?"
"Noor"
"Ashe Takwarar ya'ta ce"
Yar' buduwar tace "mummy sunanmu d'aya"
"Eh sunanku d'aya har Kama ma naga kuna yi"
Akayi dariya, sun d'ade suna hira, Imran yace "ta tashi su tafi dare yayi",
Hakanan taji bata son rabuwa da Mummy, Turare designer mai k'amshi Momy ta bata
Tacewa Imran "Dan Allah ka rik'a kawo min Noor, ina sonta na yaba da hankalinta"
"In shaa Allah mummy" Yaji dad'in tarban da suka samu daga wajen Momy da yadda ta yaba da Noor.
Da suka dawo gida Noor ke cewa Imran "ita dai taji tana son mummy da ya'yenta",
Imran yace "ai suna da kirki duk wanda ya gansu dole zasu shiga ranshi"
Haka rayuwa ta cigaban musu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, Noor na zuwa wajen mummy akai-akai ta saba da ita da ya'yenta(Noor ce babba 14yrs, Nabeel 12yrs, Ayman 10yrs, Anwar 5yrs), Ta samu admission a BUK LAW department har ta fara zuwa driver na kaita ya d'aukota a dalleliyar motar da Imran ya siyan mata, Yace "sai ta haihu zata fara driving da kanta"
Tana maida hankali sosai a makaranta, bata manta da Ameerah ba tana kai mata ziyara itama haka Ameerah tana zuwa wajenta.
Noor na zaune a had'add'en falonsu, ga cikinta da yayi tsini, Soyayyen nama kaza take ci, tana kallon ZEEWORLD, Imran yai sallama ya shigo
"Ana nan ana kwad'ayi my angel"
Turo baki tayi cikin shagwab'a tace
"Ni ba kwad'ayi nake ba, Babynka keso"
Ajiye briefcase d'inshi yayi , Ya k'araso inda take, kanshi ya d'aura kan cikin Yace
"My baby ka rage kwad'ayi ka bari sai kazo duniya zaka ci kayan dad'i har ka k'oshi"
Dariya tayi ,
Da alamar damuwa d'auke a fuskarata ta Kira sunan Imran, Ya amsa
"My dear me zai hana idan na haihu, muje Abuja muga su Hajiya mu dawo"
Murtuke fuska yayi Yace
"Ba yanzu ba, kuma bana so ki k'ara mun maganar zuwa Abuja"
Yana fad'ar haka ya mik'e ya haye sama, Noor ta tashi tabi bayanshi,
D'aki ta same shi yana kallon Saman ceiling, hawaye nabin gefen fuskar shi, Ta fama mishi inda ke mishi ciwo, Hankalinta a tashe ta k'arasa kan gadon, Harshenta tasa tana lashe mai hawayen
"Am sorry my dear, I hurt ur feelings, I never mean to do that"
Rungumeta yayi Yace
"Bake kika sani kuka ba my angel, idan na tuna su waye iyayena ina bak'in cikin kasancewata d'ansu saboda halayyarsu, Duk da halinsu ina missing d'insu My angel, I miss being with them, idan naga gidan Alhaji Labaran ina tuna yadda muke zama mu duka muna hira da nishad'i, da yadda muke so da k'aunar junanmu, I miss mum, Dad, Yazeed,Ihsan, Iman but I can't go back to them"
Ya fashe da kuka, tausayinshi sosai ya Kama Noor itama kukan ta fara.
0 comments:
Post a Comment