DEDICATION TO.
(Ummy Aysha)
_*Part (1)*_
1...wallahi !tallahi!"na Rantse da Wanda Rayuwata take a hnnunsa!
Ko'da an Daura wannan auren sai An warwaresa.wlhi da inyi zaman aure da *Khaleepha maska*!qa'ra inshiga dunia idan baa warware wannan auren ba .sai naja zamaku bala'i da masifa !" Wannan auren ne zan qa'fa tarihin da ba'taba qa'fawa ba .acikin zuri'ar *MASKA*!
"Saukar mari taji hagu da da'ma Wanda yasa ta nemi jinta da ganinta ta ra'sa na ku'san sa'qon talatin qa'fin ta farfado ya Rufeta da du'ka .khaleepha Maska ne ya ra'tso tsakiyyar fa'lon sanye ya'ke da fararen ka'ya dinki captani da babbar Riga ,
Qa'llo day'a zakayi masa ka'san baya cikin natsuwar sa ,saurin shiga tsakanin lailah da Baba Aminu yyi ya Rungume lailah sosae acikin fa'deden kirjinsa .tareda fa'din gara ka kashemu du'ka ka huta Abban maska.khaleepha yyi maganar gamida qa'ra Rungume Lailah Ajikinsa.muryarsa na qaryewa a hnkali haka idonsa ya ka'da yyi Ja jijiyoyin qansa suka fito sarari!alamar Ransa yyi balain ba'ci .Yanajin dukan da Abban maska keyiwa lailah har cikin Ransa.Aransa ya'ke fa'din Nine ya kamata ka da'ka ba itaba Abba Soyayyarta ,soyayyar LAILAH MASKA Ita ta ka'womu a wannan stage din.''Am so sorry Abba.Khaleepha maska kawae ya'ke fa'da Aransa.
Jinta ajikin Khaleepha maska tamkqar an watsa mata Ruwan da'lma ajikine ,ta tsanesa batason ganinsa ,Runtse idonta tayi tana tu'no ka'lamansa a hnkali na ma'ta ihu acikin ku'nne!
*Mujaheed maska*!
" yayah Khaleepha ko ka yarda ko karka yarda zuciyar ka nason Lailah! Ba tsanarta kakeyi ba!"muJaheed maska yyi maganar yana bin yayan na'sa da ido.'wani irin mugun qa'llo Khaleepha yake Jifan mujaheed dashi.''
"Ya isheka mujaheed!
Khaleepha yyi maganar acikin wani irin tone Wanda mujaheed din ya ka'sa fassarasa.
Ko mata sun qa're a dunia banga abunda zanyi da yarinyar nan ba.
Saboda meye yah khaleepha?''
ga soyayyar lailah maska nan ina hangowa acikin idanunka.
Na tsaneta! Na tsani halinta yarinyar dake kwana a hotel -hotel yarinyar da mazaaaa!
qa'sa qarasawa yyi plss leave me a lone.'' mujaheed ka'fin na ba'ta maka rai.baya -baya mujaheed yyi ya juya yabar da'kin yana Dan murmushi .
*Khaleepha maska*!
Haka kawae kinje kingama zubar da mutunci ki !kingama yawonki na bariki !" Ace wai wani fyade akayi maki shi saurayin na'ki ya gujeki yaqi aurenki sabida abun kunyar da kk yi. ni anzo a ya'baman ke!
Ko yatsar hnnunki banajin zan iya riqawa sabida kazantar sa na tsaneki ! Na tsaneki *LAILAH MASKA*!! Maganganunsa take Juyawa a ranta kirjinta ke mata wani irin ciwo amma qa'rfin hali irin na Lailah kwa'ce Jikinta takeso tayi cikin na'sa.wani irin qarfi taji yazo ma'ta ta fincike Jikinta cikin na'sa hawayen ba'kin ciki na sauqa a fuskarta A hnkali !''
Wani gefe magangan *ALIYU MASKA*! ta'ke tunawa.Na Rantse da Allah baxan saurarawa duk Wanda keda sa hnnu acikin lalata Rayuwarki ba lailah.''zanyi amfani da ilimina ku'dina da qa'rfina WaJen gano Wanda ya aikata ma'ki hakan .koda ace hakan shine Abu na qa'rshe da zan aikata acikin Rayuwata."share hawayenki Kinji princess Aysha Lailah maska!.hnnu yasa yana tare hawayen idanunta dake sauka sosae akan kyakkyawar fuskarta.cikin Rawar murya take fa'din toshi Allurar mecece yakeyi min haka yah Aliyu?''cemasu fa yakeyi banada hnkali ,shiyasa nake wannan haukar Yah Aliyu yah khaleepha ddi yakeji !''farin ciki yakeyi anyimin fyade !
Ya isa haka lailah!zan warware ko'mae dafe kanta tayi da hannayenta du'ka biyu tana qa'ra Rushewa da wani irin kuka .to kafada masa banason ya dubani koda bbu likita a duniar nan gaba day'a bana son nazama qa'rqashin kulawar *Khaleepha maska*.
Nan take komae ya riqa dawo mata tamqar yanzu abun ya faru.
Ràyuwarsu na baya yasoma dawo mata a hnkali !''
Voice of the innocent team#
LAILAH KHALEEPHA.#
[02/08 8:53 AM] YAYA HAYAT: Lailah Khaleepha ~by Asmy b Aliyu.
Haske Writer's Association.
DEDICATION TO.
(Ummy Aysha)
*_ZARIA_*
********
2....Ruwan sa'ma akeyi sosae ,haka ta daure tana driving akai -akai sai taja tsaki ta tsani Ana Ruwa tana driving .ga wata irin Yunwa da takeji tamqar bbu komae acikin cikinta."
"Horn take dannawa maigadi amma ko ka'dan baijita ba.da alamr Ruwan saman da akeyi ya hanasa yaji Horn din tamqar zatayi kuka .tunanin fita daga motar takeyi , Ameera yazo ya bu'demata ?"
Bazata iya Jure zama acikin mota ba."komawa tayi baya tayi pkn.
Sa'annan ta cire key din Jikin motar ,Rau Rau tayi da ido.
da gudu ya hangota tana nufo compound din shiga gidan.
Yana tsaye cikin baranda Yana sanye da Jibgegiyar Rigar sanyi.''
Hannayensa du'ka zube cikin Aljihun wandonsa,
Qa'sa dauke idonsa yyi akanta.
Ba'kin wandon Jean's ne ajikinta wanda ya qa'mata sosae da farar T.shirt sai boy friend jacket "wadda ta Daura a sama amma hakan bai hana A hngo dukiar fulaninta ba,Dan Ruwan sun fara ta'ba Jikinta sai kuma Dan qaramin veil black da tayi Rolling kanta dashi.sai cover shoe na mata dake a qafanta.
Tana qarasowa cikin compound din gidan ,tayi saurin cire boy friend jacket din ,tana Dan tsaki haka ta Warware veil din qa'nta kananun kalabane ke Reto a tsakiyyar bayanta." Idan baka qarasa gafda LAILAH MASKA ba.
Zakayi tunanin tayi qa'rin gashi .gashinta ne ,
Wanda baa samasa Relaxer saidai a wankesa da mayukka .yana day'a daga cikin Abunda kejan hnkalin maza akan Lailah maska!''
Kamar ance ta da'go kanta sukayi ido biyu dashi.
wani Abu ta'ke hangowa acikin idonun Khaleepha maska .Wanda duk lokacin da ta ka'lli idanunsa tana Hango hkan.duk da bawae qa'llon sa take ido da ido ba.
Batace komae ba.tayi saurin dauke kanta a qa'nsa ,
door Bell tashiga dannawa .kusan na minti biyu sai gashi an bu'de ware ido tayi akanta ganin wadda ke tsaye akanta.
Cikin dariar farin ciki take fa'din my Amra?''fa'dawa kanta Amra tayi tana ihun murna ,Sannu da zuwa Yaya lailah!
Ke nake ta famar Jira hajja tace maybe a skull zaki kwana.
Waye ya ka'woku ko baban Kaduna ne?"naga motarsa lailah ta fa'da tana nuna ba'kar Prado da hannunta ."Yah Khaleepha ne !
daga haka lailah ta Juya ta shige ciki batareda tace komae ba.
Hajja ta sama a kitchen tana famar ha'da miya ,shaye da to'ka take qa'llon Hajja wadda ta juyo da far'arta tana sauke idanunta cikin na Lailah.
Mekikeyi haka Hajja?" Tambayr da lailah ta Jefowa Hajja kenan ka'fin ta cigaba da fa'din ,akwae fa ya'n Aiki a gidan nan.?
Khaleepha nake ha'dawa tuwon shinka'fa da miyar.......kafin hajja ta Idar da maganr lailah tayi gaba kai tsaye part dinta ta wuce da sassarfa.
Hajja da Amra sun ba'ta mata rai daga dawowar ta ,ko zama batayi ba.suna tarar ta da maganr mutunen da tafi tsanar sa fiye da komae A dunia.
Tsoki ta Bu'ga ! A qa'ro na farko .
Kafin ta shiga cire kayan Jikinta anan cikin ha'dadden master bedroom dinta .Wanda komae na cikinsa purple and white ne."
Dan qaramin towel ta Daura a kugunta ta shige toilet mintu go'ma kacal tayi a toilet ta fito .Gaban mirror dressing ta tsiya tana qa'llon kanta .lotions nata ta dauka ta shiga shafawa ko wace ga'ba ta Jikinta ta dauki tsayin mintuna takwas agaban mirror dressing simple make up kawai tayi.
Closet nata ta nu'fa anan ta fiddo wasu kananun kaya.wandon pencil ne kalar Red haka na Robane ."sae Rigar T.shirt white wadda katuwa CE har ta sauqa akan gwiwowinta.
Agaban Rigar ka'ton Lion ne aka zana.
Bbu hula akanta haka ta nufi ko'fa.
Saukowa takeyi akan down stairs Ranta a ha'de qa'llo day'a tamasu ta dauke kai.kai tsaye hanyar kitchen ta Nufa Hajja CE ta dakatar daita ta hanyar fa'din kizo ga Tuwon kici.
da wani hargitsatten qa'llo ta juyo tana yiwa Hajja!"kinsan duk cimar Khaleepha maska ,Lailah maska ta tsanesata.da hka Lailah ta danna kanta cikin kitchen din.qa'llo Hajja ta maida kan Khaleepha maska Wanda kecin tuwon shinqafan sa A hnkali ."tamqar baya wurin suke magana sabida shegen miskilanci irin na'sa amma qarquso ku Tona zuciarsa A lokacin maganganun lailah maska keyi masa Ihu acikin dodon qu'nne.yana Jin kowace Kalma ta maganarta na zauna masa daram acikin zuciarsa.
*****
Quaker oat.kurum ta iya ha'dawa da madarar Ruwa ,
Juyasa take A hnkali cikin bowl Dan a tsarin Rayuwar lailah maska .batacin Abinci da zafinsa haka batashan duk wani abunsha da zafi sae ya sandare ,yyi sanyi.lokaci day'a taji anfisge bowl din hnnunta ,anyi watsi dashi akan Mable's din da'ke malale acikin kitchen din.
Lokaci day'a tabi bowl din da qa'llo da kuma Quaker oat dinta da take marmarin sha."cike da ba'cin rai ta da'go kanta taga wane isasshene yyi mata wannan danyen aiki....
[02/08 8:53 AM] YAYA HAYAT: Lailah khaleepha~by Asmy b Aliyu.
Haske Writer's Association.
DEDICATION TO.
(Ummy Aysha)
3...qa'llonsa ta tsaya tanayi da mamaki a fuskarta haka tana yimasa wani irin qa'llon tsana ,magana takeso tayi ta qa'sa .lokaci day'a taji ya fisgota ya wani ha'de rai .baiyi magana ba.
Sai taga ya ha'de bakinta da na'sa sauqar wani Abu takeji acikin ba'kinta Wanda ta qasa tantance minene .
qazantar bakinsa takeji kokarin fisgar kanta takeyi ta qa'sa haka amai takeji sosae bbu musu ta ha'diye narkakken tuwon shinkafan da khaleepha ya zuba mata acikin ba'ki saida ya tabbatar ya wuce a mako'shita yyi saurin turata da qa'rfi. qaro na farko a Rayuwarsa da ya ha'da bakinsa da na wata ya'h macce.
Amai taji yazo mata bbu musu ta durku'she anan ta shiga yin Aman tamkar Ranta zai fita.
Idan zaki iya ki fiddo da cikin duka Lailah maska!"
Kowane fanni bazaki iya Jadani ba.nafi karfinki !
Ya qa'rasa maganar cike da gadara gamida ficewa daga kitchen din ,
Kusan cin qa'ro sukayi da Hajja ganin lailah zube a qa'sa tana Amai tamqar ranta zai fita idonta na akan khaleepha tana binsa da qa'llon tuhuma .
Ta gefenta ya Ra'ba zai wuce ,tayi saurin dakatar dashi."
dawo nan khaleepha mekayi mata?"
Hajja ta tambayesa gamida tsaresa da ido .batareda khaleepha ya amsawa Hajja ba ya cigaba da tafia .
"Auh tafia xakayi Dan uwarka ina magana?'
Hajja tayi maganar a Dan tsawace!"
Shaye da to'ka khaleepha ya Juyo yana qa'llonta .kinga abunda ke ha'dani dake Hajja kidaina zagarmin uwa!"
"Baki wangalau hajja ke qa'llonsa na zageka ko zaka Rama.?"
Ka'rama nace Abubakar!
baice komai ba ya Juya yafice daga kitchen din Ransa a ba'ce...
Yarasa mai xaiyi Wanda zuri'ar maska zasu tsani lailah gaba day'a kamar Yarda ya tsaneta.
Hajja zata riqa ta tayi saurin ture hnnun Hajja .haka lokaci day'a ta sa'ki kuka ,Lallashinta Hajja keyi ganin haka lailah ta qara lafewa ajikin hajja ."
Meyayi maki?"
Kanta ke ciwo haka tana Jin bakinta ba dai dai ba.
Tana Jin kazantar bakin khaleepha maska ."
Wai yau ita Lailah Maska ke ha'da baki da khaleepha Maska!"tayi Alkawarin Ramawa .
Ta kowace irin hnya ce.
Hajja ta riqata zuwa parlor Amra kawae CE a falon .tana zaune tana qa'llon tashar zee word.''
Murya mujaheed maska ta tsinkaya a tsakiyar falon yana kwa'la mata kira .kwance take akan soofa idonsa a lumshe har yanzu batajin ta dai -dai ."
Kan hannun kujerar da lailah ke kwance Anan ya zauna ."matsahin saurayine Wanda baxai wuce shekara Ashirin da Biyar ba A dunia."
qa'llo day'a zakayi masa zakasan sun ha'da Jini da khaleepha maska.''sae dai shi Mujaheed fari ne tas." Haka baikai Jikin khaleepha maska ba .
Bai kuma kai tsayinsa ba."
Yyinda khaleepha maska black beauty haka yana da tsawo haka yana da Jiki.mujaheed maska Ku'llum fuskarsa farin ciki ne da Annashuwa acikinta mai haba-haba da mutane ,mai son qa'nnensa sabanin khaleepha maska.''yarda yake ba'ki haka fuskarsa take bbu fara'a akanta.miskilanci da shegen girman kai."Amma a hka bbu Wanda uwarsa keso fiye shi..
"Hajja meya samu Swt sis ne?''
Yawancin lokutta haka Jaheed maska ke kiran lailah.
Yyi maganr cikin fuskar damuwa."yooh itada wannan mugun ne Wanda bbu Allah azuciyarsa.
''Da mamaki mujaheed ke fa'din Yaushe yah khaleepha yazo zaria?''
Dazun nan mana .bu'de idonta tayi tana qa'llon mujaheed ,Wanda shima idonsa na qanta.
Kuka yasaki ko?
" mujaheed yyi maganar murya a qarye ,Laylah batace komae ba.
Ta tashi zaune sosae ,wasu lokutta tana Dan kyale khaleepha ne sabida mujaheed .Dan duk cikin zuriar maska mujaheed ne Wanda tafi kusanci dashi.
"Wannan qa'ron kuma meya ha'daku?mujaheed yyi maganar Ransa a Dan ha'de .yanajin yarda wani sashe na zuciarsa kejin haushin yayan na'sa ." da wanine keyiwa laylah haka ,da yanzu yakai qarshensa.
Ya tsine fuska Lailah tayi ,Yah mufita zan sha ice cream."tayi maganar gamida tu'ro masa ba'ki.Hajja ta qaraso falon riqe tea cup ta miqawa lailah.ya tsine fuska tayi ,
Ta qa'lli hajja a tausashe tace na qo'shi Hajja fita zamuyi da Yah mujaheed .A masifance Hajja ta dire cup tea.din tana ban bamin fa'da kada Allah yasa kisha cikin ki banawa ba.
Anan Hajja ta wucesu tana banbamin fa'da .mujaheed ya qa'lli Laylah wadda tabi ta ha'de rai .Dan ware idonsa yyi akanta."
Hey babe!"
Kin fasa fitar ne?
Yyi maganar cikin wani irin yanayi .shikawae yasan meyakeji idan yana tareda Laylah maska.
doguwar Abaya ba'ka kawae ta aza asaman kayanta mai maba'llai Ajikinta .
Sai black veil na abayar wadda tayi Rolling kanta dashi ,tun daga kan stairs mujaheed qa'llonta .
Baya gajia da qa'llon Laylah maska komae nata mai kyau ne.
"Jerawa sukayi sukafice daga cikin falon gidan .Amra CE ta fito kitchen da gudu tana fa'din Yah Laylah kizomin da nawa.
Juyowa mujaheed yyi yana wurgawa Amra din mugun qa'llo ,kafin yace wandda kuka fito tare yakai ki shan ice cream mana.
dan turo baki Amra tayi ,tana fadin Yayah mujaheed ni bakai naceba.
Yah Laylah nace !"
girgiza kai Laylah tayi taja hnnun Mujaheed tana fadawa Amra zata siyomata.
Yaya bani najamu mana.bbu musu ya cilla mata car key ta cafke ,
Idon khaleepha maska na Kansu wanda ke zaune Acikin fararen kujeron dake cikin balcony din.
Wya yakeyi amma hnkalinshi na qan'su.
Haka kawae yaji Ransa ya ba'ci ganin yarda Laylah ke wasa da mujaheed hardasu kya'lkyalar daria Sai yaga a yau tafi ko yaushe kyau.
Samun kansa yyi da saita camera yashiga daukarta pics."Wanda zuciarsa ke basa umurnin yin haka.akan idonsa suka fice daga cikin get din gidan.
B~Aliyu.💝
[02/08 8:53 AM] YAYA HAYAT: Lailah khaleepha ~by Asmy b Aliyu.
Haske Writer's Association.
DEDICATION TO.
(Ummy Aysha)
4...Yayah Ice cream din nan da ddi kamar yarda yanayin nan yake da ddi ,
Yayah mujaheed inason yanayin damina yafi kowane irin yanayi ddi.
Lokaci day'a lailah ta ha'de rai ganin yarda mujaheed din hnkalinsa baya ma kanta.
"Yaya mana."
Tayi maganr a shagwabe gamida cinno masa dan qaramin bakinta mai daukeda kyawawan pink Lip's. "Da ware idonsa yyi akanta yana fa'din Lailah mana.
Yyi kwaikwayon muryarta murya can ciki.
" shin wai minene damuwar ?.gaba day'a kabi ka canja fa'damin minene?
Kaga wannan karon bazan kyaleka ba.bazan saurareka ba.
Akwae abunda kake bo'yemin ta qarasa maganr shaye da to'ka.
*Sanyi nakeji Laylah maska."
Yyi maganr can cikin maqoshinsa ,ware idonta tayi tana murmushi tana fa'din bbu sanyi Yaya .
Yanayin nan yana da ddi kaji yarda iskan Allah ke kadamu kaji wani irin kamshi na damina.
Ta fa'da tana lumshe idonta kafin ta bu'desu a hnkali ,gamida saukesu akan Mujaheed maska."Wanda ya zuba mata narkakkun idanunsa masu wani irin yanayi.
"Baka da lfy Yaya .
Ga idonka nan ya nuna tashi mutafi Asibiti laylah tayi maganar tana qoqarin miqewa tsaye ,
Kamota yyi ya zaunar daita.
Lfia ta qlau fa.
To minene?"
"Gobe zan ko'ma Cyprus.
Har yaushe ka dawo Yaya sabida Allah ko sati hu'du bakayi ba.ta qarasa maganr tamkar zata fashe masa da kuka.
Na fa'da maki hutun baida yawa .Am so sorry!"
Ya fa'da yana qoqarin kai hnnunsa akan ka'fadarta tayi saurin buge hnnun na'sa ,bakada kirki yah mujaheed ka Rabu dani ."
Zaka ko'ma skull shine sai yanzu zaka sanar dani.?
Tayi maganar tana fashe masa da kuka .da gaske laylah maska hawaye takeyi kuka takeyi dan zai ko'ma skull.
duk wannan tashin hnakalin na minene? "Dan kawae Mujaheed maska zai ko'ma makaranta laylah ke zubar hawaye.
To oya shafe hawayenki kiji." Bbu musu ta fara share hawayen yana qa'llon fuskanta Wanda har ya fara canjawa.
"Bazan ko'maba.
Zanje na fa'dawa Baban Kaduna.bana iya karatu a Cyprus adawo dani Nigeria .Nigeria ma a garin Zari'a shikenan?"
Yyi maganr yana qa'llon ta bata rai tayi haka kawae saika datse karatun da kayi Rabi cikinsa sabida ni yah mujaheed! "
da yanzu Ina karatu a Cyprus da ku'llum muna tare amma wannan mugun ya soke tafiar ya zuga Abban maska.an hanani tafia!"tayi maganar rai abace!
"dan murmushi mujaheed yayi yayah khaleepha fane ko?''
Batareda ta amsa saba take fa'din gobene birthday party din Meela ,ya zanyi yayah?"
Ko'wa da boy friend dinsa zai shiga wurin .ni kuma bani da *Saurayi Yayah mujaheed*!"
Nazata tare zamu tafi Yaya.
Yarda tayi maganar sai tabasa daria.da gaske laylah maska bata da Saurayi duk wannan kyawon nata?"yayi tambayr cikin wani irin yanayi da bazai fassaru ba!"
"Kaima ka sani Yaya !
Ya zanyi .
Saiki fasa zuwa.
Ware masa manyyan idonta tayi.
Abun kunya ne yayah mujaheed kasan kuwa ya matsayin Meela yake a wurina?"
"She is my Best Friend in the whole world. Bazataji ddi ba.yayah!
Wannan zuwa partyn ba addini bane Laylah ki hkura dashi.plss muje gida Kaina ke ciwo.
Yyi maganr gamida dafe kan na'sa.
da gaske sanyi yakeji suna shiga mota ,jacket dinsa ya ya Daura a saman farar shaddarsa.haka ya takure kansa wuri day'a Ac.n ma da suke sha kashesa duka tayi.
Bbu yarda lailah batayi ba akan sutafi Asibiti.amma yaqi dole suka dau hnyar komawa gida.
Haka zakaja mo'ta har Kaduna ?" Bakada lfy kabari sai gobe nan gidan Hajjan maskane ko ka manta.?
Lailah tayi magana cikin fuskar damuwa.
Baya iya magana zuciarsa ke dokawa."sanyi yakeji sosae amma bazai iya kwana Zari'a ba.
da kyar yake fa'din inada abubuawan da zanyi a yau shiyasa .gobe Jirgin qarfe 12:@m zanbi .batareda lailah ta qara magana ba.ta bu'de back side ta saka Ice cream din Amra.
Ga ice cream din Amra nan nasan zaiyi melting kafin ka kai."idan ka kai mata sai ta qara sawa a fridge ka gaisheda su Mami da Hajia.
da haka ta Rufe ko'far gamida matsawa gefe ,tana maganar ne batareda ta qa'llesa ba.
Haka yana nufin fushi tayi ,fitowa yyi daga motar.
Ya qaraso gabanta hnnunta na dama ya riqa yana fa'din haka zan tafi kina fushi dani."?
Yyi maganar a qarye."
Batareda tayi magana ba.ta danyi hugging dinsa,
Tana fa'din I love you.Allah ya kiyaye hnya bata jira mai zaice ba.
Ta zare Jikinta cikin na'sa tabar wurin da gudu.
*****
Kaduna.
Cire kayan Jikinsa yyi gamida dannna su acikin washing machine. "Har lokacin Jikinsa qamshin Turaren Laylah maska yakeyi.
Baita ba ha'da Jikinsa daita ba." Amma yaushine da ha'da ba'ki da Yarinyar da yakeyiwa tsanar da baisan adadin taba.
Fa'dawa yyi akan bed gamida lumshe idonsa ,haka yakejin bakinsa tamkar Wanda yasha swt.baisan mai yakaisa ha'da bakinsa danata?
Baisan waya aikesa ba!"
Barci yakeso yyi da gaske barci yakeji .....Amma kowane Juyi da zaiyi Laylah.
Maska ke manne aransa.
Tsoki ya buga a qaro na farko tamkar Wanda aka tsakura ya miqe tsaye gamida daukar brown jallabiyar sa ya saka.haka ya xura Bed shoes nasa yyi part din mamin sa.
[02/08 8:54 AM] YAYA HAYAT: Lailah khaleepha~By Asmy b Aliyu.
Haske Writer's Association.
DEDICATION TO.
(Ummy Aysha)
*( unguwar Zari'a city)*
***
5...gidane qa'ton gaske wandda get din gidan ba'kine haka a saman gidan Anyi Rubutu da farin Fenti .ABUBAKAR MASKA PLACE......
Cikin gidan kuwa Estate ba zasu wuce kwara biyar zuwa shidda ba .
Sai kuma gefen da'ke qa'llon gabas yafi kowane gida girma acikin su.
Shine mamallakin Hajia Maryam maska !wato tsohuwa Hajja wadda bazata wuce shekaru Sabain ba.A dunia.
Zuri'ar Abubakar maska ,zuri'ace da tayi fice da suna daga cikin tsatson su.Asalin su Katsinawa ne cikin wani kauye da ake kira MASKA.*
Sa'annan kuma Fulani ne gaban su da bayansu .
Tun a wancan zamanin Alh.Abubakar maska yake da tarin dukia.
azamanin da Yyi kasuwancinsa da Turawa.
Lokacin da ya cika shekara 25 adunia iyayensa suka so suyi masa aure ganin ya kamalla makaranta .Wanda a wancan zamanin makarantar secondary skull itace karshen karatu.
Tunda ya kammala karatunsa haka yana kasuwancin sa.
Lokacin ne aka daurawa Abubakar Maska da ya'r wajen baffan sa ,mai suna maryama .
Itama bafullatana CE.
Bayan bikin su na Fulani da akai mai tarin Al'adu Wanda hakan ya qara burge iyayen gidan sa Turawa way'andda yake aeki a karkashin su.
Dan sunason Al'adun gargajia.
Bayan biki da sati day'a suka da'ga kasar burtaniyya abunsu.
Sai da suka kwashe fiye da shekara bakwae basu le'ko gida Nigeria ba.
Acikin shekara ta takwas ne sukazo Nigeria da Albarka yaransu har biyu.Muhammad Habeeb maska shine babba Sai Muhammad Amin maska.
Alh.Abubakar Ya dawo da arziki mai tarin yawa.arzikin da yazama kace -kuce acikin kauyensu na maska.
Anaganin kamar Abubakar din ba dukiar halal CE garesa ba."
da hka garin maska ya fara gagarar su duk inda zasu fice Sai a riqa nuna su ana fa'din yankan kai sukeyi.
"Alokacin mahaifin Abubakar din ya kwanta ciwo ,hnkalin Abubakar maska ya tashi sosae.
Hka ya daukesa ya kaisa
Babbar Asibitin Zari'a Ta shika."
dan alokacin bai Rayu da mahaifiyarsa ba.da mahaifinsa ya Rayu.
Baiyi kwana biyu ba A Asibiti Allah ya dauki abunsa.mutuwar ba qaramin girgiza Abubakar maska tayi ba."dama mahaifinsa kawae ya yarda da dukiarsa ,
Ko ya'n uwansa yan uba kowa hantarar sa yakeyi.
Wani tunani yazo masa na bu'de company saida Auduga yariqa turawa iyayen Gidansa turawa acan basai sunzo ba.acikin garin zar'i'a haka kawae yaji garin ya masa.wannan shine dalilin dawowar Abubakar maska cikin garin Zari'a.agurguje Cikin shekara 10 da Rasuwar mahaifinsa yyi ku'din da baisan iyakar suba.
Ya'yansu Ukku da Hajja Muhammad Habeeb Sai Muhammad Amin Sai Auta macce Hadiza.daganan kuma haihuwar ya tsiya cak!
Haka ya'yan Abbakar maska suka taso cikin gata da kulawa .
Abubakar maska yana da shekara hamsin Yabar dunia.
Agurguje su Hajja ba karamin Rashinsa sukayi ba.
Ya'n uwan Hajja sun so sutafi daita can kauyen maska fafur takiya !"
Tace subarta anan yazatayi da karatun ya'yanta ?"
Idan suka ganta kusa sunfi maida hnkali.
Dan lokacin Muhammad Habeeb yana level 3 a nan jami'ar Ado bayero dake kano.fannin business yake karanta ,yyinda Muhammad Amin ke anan cikin A.b.u Zaria yana qarantar Economic computer yyinda Autar Hajja Hadiza ke aji biyar na secondary skull.
Agurguje plss.
Muhammad Habeeb yanada matan Aure biyu a dunia matarsa ta farko Hajia zulai wadda suke cewa Hajia tun can Asali Sai zainabu wadda suke kira Mami.Aliyu Habeeb maska shine Jikan maska na farko haka Dane a wajen Hajia zulai.ya'yanta biyu a dunia Aliyu shine na farko Sai Nafeesa.
Hajia Zainab kuma Mami."
Khaleepha ne na farko Sai mujaheed Sai Amra.
Abubakar Habeeb(Khaleepha) maska shine da nabiyu a wajen mahaifinsa.haka shine yazama takwaran margayi Abubakar maska.
Sai Alh.Muhammad Amin maska Wanda yakeda matar aure day'a Hajia Asiya. Ya'rsu Ta farko Sunan mahaifiyar Hajja gareta Ayshatu .kuma a alokacin an haifi laylah A Daren lailatul qadri aka haifeta shine dalilin kiranta Laylah.tun a wancan zamanin Hajja ke fa'din sun samu Aysha Laylah.
Daga laylah sai Hafiz sae Autansu Habeeb Wanda suke kira (Junior). Dan sunan Baban Kaduna yaci a alokacin.
Sai Hajia Hadiza maska.wadda tana nan cikin garin Kaduna tana aure tsohon minister a unguwar Rimi.shaddad ne danta na farko sai Maryam wadda suke kira (Meema.)
Alh.Habeeb maska Wanda yara ke kira Baban Kaduna.yana zaune acikin garin Kaduna yana nan da ka'ton gida acikin unguwar Rimi.
Sai Alh.Amin maska Wanda shikuma yana zaune acikin garin Zari'a .
A unguwar samaru shiyake kula da companyn mahaifinsu na Auduga dake Nan.
Yyinda Habeeb maska ke kula da sauran kaddarorinsa dake cikin garin Kaduna.irin su gidajen man da aka bu'da da sunan Maska.schools islamiyya da bo'ka sai kuma Hospital.
Aliyu maska fannin computer engineering ya qaranta.shine C.E.O .
Company maska dake cikin garin Kaduna.
Yyinda Khaleepha maska kwararren doctor ne ,haka babban Likitan Ne Wanda ya kware A fanninsa Aikinsa.
Yanayin tiyata.haka yana qarbar Haihuwa.shine babban Likata Maska hospital duk wani tiyata da zaayi saida sa hnnunsa.
Zakayi mamaki idan kaji ance duk makeken gidan nan nacikina garin zari'a Hajia maryama dai ke Rayuwa acikinsa,sai dai idan Yaya'nata sunzo yimata Hutu ko jikokinta .bayan Rasuwar Abubakar maska yaya'n Hajjan basuyi wani maraici mai yawa ba.don Hajjan itace tazama bangonsu abun Jinginarwarsu.wannan bayana nufin tayi saka -saka da tarbiyarsu bane A'a ,akwae tarbiya akwae kuma girmamawa da duk wani da ko Jikan dake cikin zu'ria'r maska.bbu Wanda zata azawa magana ya tsallaka haka baa musu da Hajja da tazartar da hukunci shikenan .macce CE mai kyakkyawan tunani ,ta yadda duk wani motsi da ya'yanta ko Jikokinta keyi tasan sa.
Jikokinta suna kaunarta sosae fiye da iyayen da suka haifesu.
Acikin gidan Hajja na Zaria akwae bangaren maza boy's quartets .Wanda acikin samarin zuri'ar maska masu tasowa suna zuwa Hutu gidan ,suna kaunar gidan Aliyu da lailah ne kawae suka tashi a hnnun Hajja.
Yayinda Aliyun Hajja CE ,
Ta yayesa agidanta ya girma .
tasowarsa bai wani shaku da iyayensa kamar yarda ya shaku da Hajjan ba.
Girmansa da Aikinsa ne ya Rabasa da Hajja qarfi da Yaji.
Sai dai yana yin week End dinsa.Agarin Zari'a.
Sai Lalaih maska.Wanda mahaifiyarta da zata tafi Hajji ta kawota wurin Hajja shikenan koda ta dawo kin ko'mawa tayi ta riga ta saba da Hajja kaunar da takeyiwa Hajjan ta daban CE.dan haka Hajja ta saka aka amso mata form .din Islamiyya da na boko duka.
Mutane da yawa suna fa'din zuri'ar maska suna kama da Junansu Ta fannin fuskokinsu da yanayin Jikinsu .haka suna ganin Girman kai garesu amma azahirin gaskiyya nutsuwace kawae da Allah ya halicce su daita da sanin ciwon Kansu ,domin dukkansu Ilimin muhammadiyya da na zamani ya Ratsasu .har kullum Arzikin Maska qa'ruwa yakeyi domin basa wasa da hakkin Allah cikin dukiyoyinsu.(Zakka)har zuwa inda yau ke motsi tun bayan Rasuwar margayi Abubakar maska.
Aysha laylah maska.tashiga Ran Hajja ,sabida laylah maska yarinyace mai shiga Rai .kuma mai nuna mata kulawa fiye da kowa a zuri'ar .komae laylah ta samu na Hajja ne tun tana ya'r kankanuwarta.
Tun tana ya'r kankanuwarta Aliyu maska shine komae na'ta .haka tun tana ya'r kankanuwarta Allah ya dasa mata wani irin kyau Wanda duk cikin zuri'ar maska bbu Wanda yyi kyawonta ,kyawonta da tsayin gashinta shine ya Jamata farin jini acikin zuri'ar maska.wayo da surutu kuma baa magana.haka duk Wanda zaizo gaisheda Hajja da tsarabar Laylah maska a hnnunsa iyayen ne ko kuma ya'yan.
"Lokacin da Aliyu na secondary skull ,idan ya dawo baiganta ba.haka zai tada hnkalinsa ya Shiga nemanta makwafta.nan kuma zai Rufeta da fa'da yace idan tana yawo bazai qara siyamata swt ba.
Haka zata fada masa ta daina amma gobe sai ta qara fita.
Tun lokacin da Lailah ta fara girma kyawonta ya qa'ra fitowa sosae .
Akwae lokacin da tana primary 6.
Ta dawo daga makaranta.
Bbu ko'wa a falon Hajja .yinwa takeji sosae zuwa tayi ta fa'dawa mai aikinsu yinwa takeji .
Anan ta fito daukeda plate dinta na Abinci shinkafa da miya da naman kaji a sama.
Zaune tayi a falon Hajja tanaci tana qa'llo cartoon.
Uniform ne ajikinta bbu dan kwali akanta haka ta fisge katon Ribbom dinda aka tufke sumar kan nata.dakyar.gashin na'ta har a duwawunta lokacin ba'ki sidik!
Shigowarsa kenan ,matashin Saurayi Wanda bazai wuce shekara 17 ba a dunia idonsa na akanta .tsoron wannan yarinyar yakeyi bayason gashin nan .#
da sauri ya ko'ma mo'ta sai gashi dauke da Almakashi ,tanacin abinci taji kamar ana ta'bamata gashi a tsorace ta Juyo tana qa'llonsa wazata gani Yayah khaleepha mutunenda take tsoro mutunen da take gudun ha'da hanya dashi mutunen da ,ya tsaneta sabida wani dalili na'sa na banza.gashinta taga yana sauka akan Rug din da take zaune akai."
Lokaci day'a tayi ihu gamida fatali da abinci da takeci .ihunta bai girgiza khaleepha maska ba.dan yaji abakin mai aikinta Hajja na anan makwaftansu gidan suna.
Haka Aliyun mai tare mata .yana makaranta lokacin.
Rashin imani irin na Khaleepha maska baisa ya qyale laylah ba duk ihunn kukan da takeyi da roqon da takeyi masa saida yamaida kanta bo'la sa'annan ya qyaleta.salati yaji abayansa lokacin laylah harta suma a hnnunsa.
Hajja tayi gurinta tana mai fashewa da kuka.yyinda Abban maska.wato mahaifin laylah ke fa'din Assha!Assha!
Babana duk mai yyi zafi haka?''
ga mamakin su sai suga yasa kuka lokaci day'a.
Cikin ihu da masifa yake fa'din ni banason ta Abba !"
Wani irin bugawa kirjin Abban maska yyi alokacin mahaifin laylah ne.amma yaji Kalmar sosae ,
Cikin qarfin hali irin na'sa yake fa'din to ta'su mutafi ka fa'damin meyasa baka son kanwarka.?"
Zonan Aminu daukarta mutafi Asibiti ko so kake ta mutu !"Hajja tayi maganar cikin kuka.
Tana tsinewa khaleepha!
Tana fyace majina.
Shin meyasa khaleepha maska yake tsanar laylah maska har haka?"
Shima bai sani ba!"kawae yasan ita kyakkyawa CE tafisa kyau .A lokacin yasan shi Abubakar khaleepha maska.yafi duka zuri'ar Maska kyau da farin Jini haihuwar laylah komae ya canja ,zuri'ar maska maza da mata ko'wa laylah?
Kan wane dalili xaisa bazai tsaneta ba.
Ga Aliyu maska nan idan kanason kaga ba'cin Ransa ka ta'ba laylah maska.
Hakama Mujaheed kaninsa ,Rigima yake azawa akan sai anzo dashi Zari'a yaga laylah.duk da akwae shekaru biyu a tsakaninsa.duk wani da'h nacikin zuri'ar maska kowa *AYSHA LAYLAH MASKA*#
Haka ba qaramin tafasa zuciyar khaleepha maska.yakeyi ba ya tsani wannan kyawon nata mai kashewa ko'wa ido maisata farin Jini ga zuri'ar Maska..
0 comments:
Post a Comment