*1*
Nutsastiyar yarinya ce take tafiya gefan titi tana sanye da kayan makaranta Wanda kana ganin su kasan na isilamiya ne yadin toyobo blue black Riga doguwa da dogon hijab har 'kasa kafarta cikin safa fara da takalmi plate baka ganin komai a jikinta sai 'kwayar idonta cikin nutsuwa take bin gefan titi domin isa gidan su dake cikin unguwar Shagari Qutears tafiya take a tsarge! Domin tasan kallon da jama'ar gari suke wa masu irin shigar su mussaman matasan unguwar su in suka zo shigewa har ihu! Suke musu suna fad'in"Allah a baki fir'auna a zuci! Sam basa tanka musu sanin da suka yi cewar yin hakan zubewar mutumci ne, to shiyasa take tafiya tana hard'ewa kasancewar a bokiyar tafiyar ta bata zo ba, anyi musu mutuwa a cikin gari sun tafi gaisuwa ita da 'yan gidan su. Aikuwa tana shigowa cikin layin su matansa da suke zaman kashe wando suka fara yi mata d'an kira! "Hi ke 'yar gidan Arrama Sarkin 'kauli Allah yace Annabi yace hahahahaha."! Suka 'karashe maganar tasu suna dariya cike da sha'kiyan ci.
Hanifa taji zuciyar ta na yi mata wani irin suya ta rasa me mahaifinta yayi wa jama'ar unguwar su suka d'auki karan tsana suka d'ora masa yaran su da manyan su, ko Dan ya kasance mutum mai tsoron Allah mai hana aikata 'barna kullum yana tunasar dasu abunda Allah da Annabi suka umarci bawa yayi, shine dalilin da yasa suka tsane shi, ita kad'ai take wannan zancan cikin zuciyar ta har ta isa gida.
Tun daga soron gidan nasu take jin saurin muryar mahaifin nata yana karatun al'kurani mai girma cikin 'kira'a mai da d'in saurare.
Cikin nutsuwa ta tu'be takalman ta a gefe guda ta zare safunan 'kafarta a hankali ta shige shi, cikin rumfar su ta shiga inda ta tadda mahaifiyar ta wacce suke kira da Ammi tana zaune kan kafet din dake shimfede a rumfar da farantin wake a cinyar ta tana gyarawa, cikin nutsuwa tace" Ammi sannu da gida."
A nutse mahaifiyar ta ta tace"Yawwa Hanifa kin dawo." Tana 'kokarin cire ni'kaf din fuskarta tace"Eh Ammi yau ni kad'ai naje makaranta na dawo gida ni kad'ai.! Cikin shagwab'a ta fad'i maganar.
A hankali Ammi tace"Mu bari Abbu ya kammala karatun alk'urani sai muyi maganar." Hanifa ta d'an zumb'ura 'karamin bakinta cikin shagwa'ba ta mi'ke d'akin dake cikin rumfar ta shige domin cire uniporm d'in jikin ta.
*MASHAHURI!!*
[12/13, 6:15 PM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*FREE PEGE*
*2*
Abbu sai da ya had'a izifi biyar sannan ya rufe al'kurani kana yayi addu'a kamar yanda ya saba ya mik'e a nutse yaje ya d'auki buta dake cike da ruwa a tsaya jikin window yana duba a suwakin sa. Alwala yake so ya d'aura ganin lokacin sallahr magriba ya gabato saura bai fi minti goma ba a yi kiran sallah.
Jin motsinsa jikin window d'in yasa Ammi mi'kewa da sauri ta futo tsagar gidan hannunta ri'ke da da a suwakin nasa tasan shi yake lalube jikin window din tace" Abbu ga asuwakin naka na d'auke maka d'azu Dana ga 'kwarika suna yawo a gurin."
"Masha Allah Halimatu Allah yayi miki albarka ina mutukar alfahari da kasancewar ki mata a gare ni ha'kika kina d'aya daga cikin matayen da manzon Allah (Slw) ya fad'a saboda duk suffofin ki sun nuna ke d'in mace ta gari ce."
Abbu ya fad'i maganar bayan ta 'karbi a suwakin hannunta fuskar sa cike da annuri.
A ko da yaushe kalmomin yabo da godiya ne suke futowa daga bakin mijinta zuwa gare ta. Baka ta ta'ba zama da Abbu na minti biyar bai fad'a maka Allah da annbi sunyi hani da aikata fajirci ba, tunda suka yi aure dashi basu ta'ba samun sa'bani ba a tsakanin su a ko da yaushe suna zaman lafiya da juna har Allah yasa suka haifi yara biyu kacal namiji d'aya mace d'aya Nasir shine babba sai Hanifa tsakaninsu akwai tazara sosai shekaru goma sha biyu ne a tsakinsu A halin yanzu Hafiz yana da shekaru ashirin da bakwai a duniya ita Hanifa Yanzu shekarun ta goma sha bakwai a duniya kuma har yanzu Ammi bata 'kara haihuwa ba ko b'atan wata bata 'kara yi ba tun bayan haihuwar Hanifa haka suke yin rayuwar su cikin ilimin addini da sanin ya kamata.
Kamar yanda ya saba bayan idar da sallahr isha'i yana zama 'kofar gidan shi yaja carbi kuma yana kallon yanayin yanda matasan unguwar suke yin rayuwar su, mutukar yaga abunda bai yi masa ba ko yaga ana 'kokarin a sa'bi Allah to babu shakka sai yayi magana akai, ta inda su kuma zasu fara yi masa dariya kamar yanda suka saba suna nuna shi da hannu cikin sha'kiyan ci. To yauma hakace ta kasance yana zaune kam daddumar shi wasu matasa uku suka 'karaso gurin da yake ko wanne da littafi na addini a hannunsa, kamar gaske suka mik'a masa hannu shima ya mi'ka masa nashi suka yi musabaha kamar yanda addini ya tada na, Abbu ya nuna musu gurin zama da hannunshi yana fadin "Masha Allah bisimillah Ku zauna mana." Zama suka yi kamar yanda ya umarce su, suna sinne kai domin sun San da sha'kiyan cin da suka zo gurin sa. Shi kuwa Abbu tufafin jikinsu yake kallo gami da yanda suka tara uban gashi a tsakiyar Kansu yayi wani irin tozo biyu daga cikin su ma har da d'an kunne a kunne su abun ya bashi mamaki sosai
Cikin nazarin su Abbu yace." Alhamdullahi ala kulli halin! Samari me yake tafe daku? Da alama kun zo d'aukar darasi ne."? D'aya daga cikin su yace." 'Kwarai kuwa Arrama munzo mu samu ilimin jima'i a gurun ka Wanda a hausance kuke kira da saduwa turawa kuma suke kiran abun da sexcual."
Abbu yaji wani irin nauyi da kunyar maganar ta rufe shi ko da wasa bai tsammaci wannan maganar ba daga gare su. Sunkuyar da kansa yayi yana nazari.
Wanda yayi maganar yace." Arrama! Munzo a shirye gamu da littafan mu muna 'bukatar d'aukar darussa kan harkar."
Abbu ya d'ago kansa a nutse Yana so yaga fuskar yaron da yake masa wannan maganar me tsauri. Kasancewar gurin babu wadattacan haske yasa bai ga fuskarsa sosai ba, sai ya d'auki wayar shi dake aje gefe ya kunna torchlight d'in Yana haska su. Take ya gane yaron.... Bazai tab'a mance abunda ya faru tsakanin sa da yaron ba shekaru hud'u da suka wuce fuskar yaron baza ta ta'ba 'bace masa ba.
Gyaran murya yayi yace." Masha Allah na ainihin wato idan na fahimci abunda kuke nufi kuna so ki samu ilimi da zaku zauna da iyalan Ku lafiya shine abunda kuke nufi ko."?
Shi d'in ne dai ya 'kara magana a karo na uku yace." 'Kwarai kuwa Arrama muna so ka fed'e mana biri har bindinsa domin mun samu labari a gurin jama'ar gari cewa kana bada darasi iri-iri."
Abbu maganar tayi masa tsauri! Mutu'ka wato sharrin mutanan gari har ta kai sun fara yawo dashi a gari yana koyar da ilimin jima'i babu shi a tunanin sa suna so su 'bata masa suna ne tunda har ta kai tsagerun yara sun fara zuwa gabanshi suna yi masa maganar banza. Daurewa zuciyar sa yayi yace." Cikin ku waye zaiyi aure da har kuke so Ku San ilimin jima'i."
Shi d'in ne dai ya 'kara magana kamar d'azu a tsaye yace." Sanin waye zai yi aure a cikin mu bai dame ka ba Arrama mu dai kawai munzo nan domin ka warware mana komai akan harkar mu biya kud'in ka Ya shaik."! Ya k'arashe maganar sa cike da sha'kiyan ci
Abbu ya d'ago kansa a nutse yana kallonsa, shi d'in ma kallonsa yake da tsayyayun idanunsa na mashahuran 'yan duniya tsayayyun 'yayan gata Wanda suka samu d'aurin gindi a gurin iyayen su.
*MASHAHURI!*
[12/14, 9:40 PM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*FREE PEGE*
*3*
A nutse Abbu yace." Duk wanda yace muku ina koyar da ilimin jima'i to babu shakka yayi min 'karya alal ha'kika shi jima'i wani abu ne da Allah ya halasta shi a tsakanin mace da namiji anan gurin ina so in fahimtar dake cewar ina nufin miji da mata wanda aka d'aura musu aure da juna a gaban shaidu sannan shi namijin ya biya sadaki kamar yanda addini ya tana da, to babu shakka wannan mata ta zama mallakin sa ta bar hannun iyayen ta ta dawo nasa shike da iko da ita kuma a ko ina ne zai biyawa kansa 'bukata ta aure kamar yanda musulunci ya nuna mana, bayan wannan 'kofa da aka halasta mana ba a yadda mu bi wata kafar dake jikin matayen mu mu biya kan mu bu'kata ba, mutukar muka sa'bi Allah muka bi son zuciyar mu to babu shakka zamu shiga fushin ubangijin mu damu da zuri'ar mu, Wannan shine kawai abunda zan fad'a muku game da maganar da kuka zo min da ita."
Abbu ya 'karashe maganar tashi cikin nutsuwa da kamala.
Khalid ya zakud'a kafad'ar sa yana Sosa kansa cikin sha'kiyan ci yace." Ya sheik wannan tambihin naka bai samu guri ba domin kayi mana k'wange a cikinsa ka'ki ga fayyace mana karatu yanda ya kamata ta'be bakinsa yayi cikin izgili ya zura hannu cikin wandon jins din da yake jikin shi ya zaro kud'i dami ya zube gaban Abbu ya mi'ke tare da fad'in "Guys ku tashi muje ko."
Abbu ya bisu da kallo cikin mamaki! Ya mai da ganinsa kan kud'in da suke gaban shi, kamar Wanda Khalid din yayi masa d'aurin baki sam ya kasa yi musu magana suzo su d'auki kud'in su, babu abunda zaiyi da kud'in da suke bashi domin kwata-kwata bai yarda da tarbiyar yaran ba mussaman shi mai maganar cikin su. Ya san shi farin sani yaron da yayi masa abunda bazai ta'ba mantawa dashi ba.
Yana zaune a gurin yana tunanin yanda rayuwa ta duniya ta lalace da yanda 'yayan da aka haife su cikin musulunci gaba da baya amma suna kokarin mai da Kansu kafurai shi a ganinsa duk mutumin da ya bujerewa fad'ar Allah da manzon sa ta ya kafurta Kuma yazo duniya a banza zai koma a hofi shiyasa yake tsaye akan iyalinsa da su bi sinnar Annabi Muhammad (slw) yasan dai shiriya ta Allah ce duk tsantsenin sa da takatsantsan d'insa shima bai wuce Allah ya jarrabe shi ba, ala kullu halin dai yana addu'ar Allah ya tsallakar dashi da iyalinsa ga fad'awa ga halaka
Sai bayan ya gama sauraran tambihi daga malam Umar Sani fagge a tashar express redio sannan ya nad'e daddumar shi ya shiga gida, a lokacin suka matasan layin suka saki kid'a na wa'kokin Hausa iri-iri sai ihu! Suke yi kamar ba dare ba.
Abbu ya gyada kansa yana musu addu'a shiriya cikin zuciyar sa 'kofar gidan ya kulle yayi addu'a kana ya shiga cikin gidan yana haska torchlight din hannun sa.
Shiru Ammi da Hanifa sun yi bacci ya bude dakin shi ya shiga cikin nutsuwa yake yin komai Abbu kenan kamilin mutum mai ri'ko da addini da bin sinnar Annabi muhammadu (Slw)
*****
'Karfe bakwai na Safiya Hanifa ta gama shirin ta tana makaranta boko dake tana ajin 'karshe na kammala secondary school a nutse ta zauna kusa da mahaifiyar ta tana turo baki kamar yanda ta saba cikin shagwaba tace"Ammi ina kwana."
Ammi dake had'a mata abun karyawa tace"Lafiya lau Hanifa kin tashi lafiya."? Tace"Lafiya lau na tashi Ammi sai dai ke wayar Yayana." Ammi tayi murmushi tace"Yau zaki ganshi ya dawo ai yau juma'a." Cike da farin ciki Hanifa tace" Aikuwa wallahi na manta Allah ya dawo dashi lafiya." Ammi tace"Amin.
Bayan ta gama karyawa ta mi'ke da niyyar tafiya tana gyara ni'kaf din fuskarta tace"Ammi Abbu kuwa ya kammala azakar din da yake bamu gaisa ba kuma idan na tsaya zan makara." Ammi tace"Ai kuwa sai dai ki shige ki tafi domin Abbu bazai futo ba sai kusan sha biyu na rana lokacin zai shirya domin zuwa masallaci."
Hanifa tayi wa Ammi sallama ta futa tana gyara jakarta da take rataye a kafad'ar ta.
Gidan su Asalamiyya na gaba dasu kad'an Hanifa bata ta'ba tafiya ita kad'ai ba tare da ta biya mata ba Asalamiyya 'kawar Hanifa ce tun ta 'kuruciya halinsu yazo d'aya haka ma d'abiun su yazo d'aya bayan nan kuma Abbu ya yarda da tarbiyyar ta sannan mahaifin Asalamiyyar Abokin sa ne d'abi'un su sun zo d'aya shine yasa har ya aminta da 'kanwancen su Abbu yana sanya ido kan irin 'kawayen Hanifa sosai shiyasa itama take taka tsan_tsan bata fiye sakewa da jama'a ba
Tun daga nesa ta hango cincirin don matasan samarin da suke ji da kansu a unguwar sun ke waye shi kamar ko da yaushe shi kuma yana tsakiyar su hannunsa ri'ke da 'katuwar some times tana ganin shi a unguwar amma bata san sunan shi ba ita dai haka kurrum yake burgeta duk ganin da zata yi masa da ni'kaf a fuskarta hakan baya hanata ta 'kare masa kallo sosai guy yake burgeta da irin dressing d'inshi kuma ta lura duk masu yi masa fadanci suna kwaikwayar sa ne da irin dressing din shi, gabanta ya cigaba da fad'uwa har ta iso kusa dasu, kanta a 'kasa tazo shiga cikin gidan su Asalamiyya taji Muryar d'aya daga cikinsu yana fad'in"Wannan munafukar yarinyar watarana sai mun yage ta Wallahi kullum jiki a rufe shegiya ko don tasan tana da kyau ne yasa take rufe jikinta oho."! Dariya suka saka d'ayan yace." Kai 'yar gidan Shaik ce fa."! A slow ya d'ago kanshi yana kallonta lokacin da ke 'kokarin shiga cikin gidan suka ci karo da Ya Abbakar yayan Asalamiyya ne ya futo yana wata irin tafiya irin ta manyan 'kwari yana ganinta ya gane ta ita kuma ta ja da baya da sauri cikin ladabi ta tsuguna har 'kasa ta gaishe shi." Abbakar ya shafa fuskarsa cike da jin dad'i ya amsa mata shi kam ladabin yarinyar yana burge shi babban abunda yake bashi haushi da ita yanda take rufe jikinta sai kace matar Liman. Yace." Hanifa yau ma sai dai ki tafi ke kad'ai don basu dawo ba amma dai mybe yau su dawo."
Jiki a sanyaye Hanifa ta juya tana fad'in to Ya Abbakar." Juyawar da zata yi suka had'a ido dashi, tayi saurin yin 'kasa da kanta a salu'be ta bar gurun. Shi kuma Abbakar ya 'karasa dabar tasu kamar yanda suka saba gaisuwar su yau ma haka suka yi suna dariyar sha'kiyan ci Salis yace." Kai d'an iska naga waccan me ni'kaf din ta gaishe ka har da tsuguna maka kai kuma sai was he baki kake hahahahaha." Ya k'arashe maganar yana dariyar shakiyanci.
Abbakar ya sosa kansa yana kallon hanyar da Hanifa ta wuce yace." Hanny kenan kasan nifa kamar 'kanwata take a gurina tunda 'kawar Asalamiyya ce shiyasa take bani girma."
A hankali ya d'ago kanshi yana kallon Abbakar din cikin yanayin maganar shi kamar ta mata yace." Kome baka girman da take sai mun tu'be ta mun ga abunda yake rufe kusan sau biyar kenan ina ganinta cikin wannan bakin abun sai na yaye ta Wallahi tun da yanzu na gano 'yar babban ma'kiyina ne."
_BintuUm@rAbb@le_
*MASHAHURI!*
[12/15, 10:04 AM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*4*
Abbakar ya kalleshi da jin abunda yake fad'a yasan halin Khalid bashi da kyau a ko wane fanni kuma baya yafiya komai girman mutum idan yayi masa abu sai ya rama gashi yaro ne duk a cikin su amma mugun tsoron sa suke ji Saboda yana da wani irin nasibi da kwarjini na jama'a duk inda ya ratsa sai ya tara mutane ko a makaranta ne haka zasu kewaye shi tun waya na waya ba kowa ne yake da ita ba shi ya mallaketa zai tara su suyi ta kalle kallen wa'kokin Hausa da turanci gami da kallan pictures din turawa masu bayyana tsaraici kai har da ma pictures din hausawa 'yayan musulci duk Khalid na dasu cikin wayar shi na irin 'yan matan da suke sonshi suke turo masa 'bangare-'bangare na jikinsu, shi kuma ya Tara abokan shi yayi ta nuna musu suna dariya in suka ga mai 'kananun nonowa su shek'e da dariya haka ma idan suka ga mai manya manyan nonowa da hifs nan ma kaji su suna dariya had'e da sakin ajiyar zuciya masu rauni kuwa a cikinsu sai kaji suna cewa"Wallahi saura kad'an na kawo haka dai zasu yi ta iskancin su na samarin masu tashan balaga.
Abbakar yace." Kar muyi haka dakai *Mashahuri* sau tari sunan da suke kiran sa dashi kenan ya cigaba da cewa "Jiya na samu labarin abunda kuka je kuka yiwa Shaik don Allah ku k'yale mutumin nan haka kuma babu ruwan Ku da 'yar sa don Allah."
Wani kallo ya watsawa Abbakar d'in cikin yanayin maganar sa a hankali yace." Kana wani tunani daban ina nawa tunanin, ni babu abunda zan yi mata tunda ba ita tayi min ba amma dai duk sanda na kara ganinta da jiki a rufe sai na tu'be naga abunda take 'boye wa ai bata fi sauran 'yan matan unguwa ba."
Su Salis suka sa dariya suna fad'in"Wallahi da kayi mana dai-dai Allah yasa ranar da zaka tu'be ta munanan mu sha kallo shegiya tasan tana da kayan aiki ne shiyasa take yawo cikin hijab, hahahahaha shima Shaik d'in abunda yake dubawa kenan shiyasa ya sa mata ido ai bai isa yayi wa Allah wayo ba." Suka 'karashe maganar tasu suna dariya had'e da tafawa Abbakar dai shiru yayi musu domin yasan sun fi 'karfinsa shima zai so yaga ranar da za'a tu'be Yarinyar yasan a ranar zai sha kallo.
Tunda taje makaranta ta kasa sakewa a aji da ta tuno kamanninsa sai gabanta ya yanke ya fad'i! Ya ilahi kanta ta sunkuyar kan daks tana addu'a cikin zuciyar ta ta rasa me yake damun zuciyar ta da guy, da batasan shi batasan daga inda yake zuwa gurin su Abbakar ba ta tabbata dai abokinsu ne kuma daga ni duk yafi su wadata ko ga yanayin sutturan da yake sawa da irin manya-manyan wayoyin da suke hannunsa tasan yaron d'an masu kudi ne, haka dai tayi ta addu'a kan Allah ya cire mata tunanin shi cikin zuciyarta har lokacin tashi yayi Hanifa bata fahimci komai ba ga kad'acin Asalamiyya ya dame ta suku-suku ta futo daga aji ta d'auki hanyar gidansu tana tafiya a tsarge kamar yanda ta saba.
Jama'a nata futowa daga gidajan su cikin shirin zuwa massalaci domin su sallahr juma'a ya wancin su da sabbin kaya da dadduma wasu da yaran su wasu na tafiya a 'kasa wasu kuwa kan abun hawan su, masu shaguna na rufewa suna tafiya massalaci duk domin samun lada gurin Allah.
A dai-dai wannan Lokacin ne su kuma suka saki kid'a ko cikin shagon Mabson kid'an da ya karad'e unguwar gabaki d'aya tun daga bakin titi mutan yakan iya jin 'kidan Muryar shi ce take tashi cikin sabuwar wa'kar shi mai taken *'Kwalelen ki!* sosai wa'kar tayi Dan banzan dad'i fiye da wa'kar shi ta farko da ya fara, ita wannan jiya ya shiga studio ya sake ta shine fa ya Tara abokan shi suna ji, kafin kace kwabo yaran da suke kokarin tafiya massalaci sun fara taruwa a 'kofar shagon suna le'kawa manyan ma daga cikinsu sun shagala da jin wa'kar azakar d'in da suke yi ma suka daina kawai suna tafiya suna sauraran wak'ar mai taken *Kwalelen ki!* Muryar Khalid akwai dad'i sosai wa'kar taja hankalin 'yan matan da suke cikin gidansu suna le'kowa waje wasu ma babu mayafai a jikinsu.... A dai-dai wannan lokaci ne Abbu ya futo daga gida yana sanye da fararan kaya kar dasu wandon shi ya d'angale sosai kana ya taje gemun shi hannunsa guda rike da dadduma d'aya hannun kuma yana rike da asuwakinsa. Cikin nutsuwa ya fara dube-dube daga inda yake jin tashin kid'an, can kan hanya ne a nutse ya fara tafiya yana tur da dab'iar matasan wato ko wane musulmi ya niyyata ga zuwa massalaci domin ya samu rabo a duniya da lahira amma su sun kunna kida sun cika unguwa babu maganar suje massalaci su bi jam'i babban abunda ya 'bata masa rai kuwa shine ganin da yayi yara mata da iyayen su duk sun le'ko waje suna kallo don rashin hankali wasu ma babu mayafai a jikinsu.
Sai da tazo daf da shagon Mubson ya fahimci a ciki kid'an yake tashi ji yayi kamar ya to she kunnen sa saboda yanda kid'an yake masa k'irjinsa har amsawa yake yi, kallon kofar shagon yayi yaga yara 'kananu masu shirin zuwa massalaci da Wanda ma basu shirya ba sunyi cincurindo a kofar shagon. Takaici ya kamashi ya rasa wane shaid'anin yaro ne a cikinsu ya tsiro da wannan shirme Dole yayi wani Abu akan al'amarin wucewa yayi da sauri domin tsayuwar shi a gurin yanzu bata da amfani dole idan an sakko ya tsaya ya tsawatar musu ko da zasu jefe shi ne.
Yana 'kokarin tsallaka titi ita ma tana 'kokarim tsallakowa a take ta shiga hankalinta ta dai-dai ta nutsuwar ta, ta tsallaka a nutse tace"Abbu na dawo." Fuskarshi babu alamun wasa yace." Masha Allah kiyi maza ki wuce gida kinji ko kada ki kuskura ki tsaya gurin kid'an can idan kika tsaya sai na 'bata miki rai."
Kanta a 'kasa tace"To Abbu sai ka dawo." Gaba tayi tana waiwayen shi har ya tsallaka titi taga yana 'kokarin shigewa massalaci sannan ta wuce zuciyarta cike da so da kaunar mahaifin nata.
Sai da ta shigo layin nasu sosai ta fara jin sautin kid'an na shiga jikinta muryar shi na 'kara tashi cikin *Wa'kar shi ta Kwalelen Ku* Hanifa ta dinga jin wani iri a jikinta tsigar jikinta ta fara mi'kewa sosai take jin dad'i wak'ar da yanayin muryar mawa'kin mai dadin sauraro.
Inda tafa wasu mata sun tsatstsaya suna hirar mawa'kin itama nan taje ta tsaya tana sauraran su gefe guda kuma tana jin shigar wak'ar jikinta Ita nan wai so take ta 'kare sai ta tafi gida, amma da ta kare sai taji wata ta 'kara shigowa Sam takasa barin gurin ta ma manta da maganar da Abbu yayi mata.
*MASHAHURI!*
_BintuUm@rAbb@le_
*15/12/2019*
[12/16, 9:51 AM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*5*
*DEDICATED TO:*
*Husaini 80k*
Hanifa ta shagala a gurin sam ta manta da gargad'in da Abbu yayi mata hankalinta da nutsuwar ta duk basa tare da ita suna can sauraron muryar Khalid cikin wa'kar shi mai taken *'Kwalelen Ku* tanan tsaye har aka sauko daga massalaci jama'a suka fara dawowa gidajan su masu shaguna suna bude wa domin cigaba da Sana'oin su, Abbu ta hango daga can nesa gabanta ya yanke ya fad'i! da sauri! Ta shige soron gidan da take tsaye tana zare ido addu'a take yi cikin zuciyarta Allah yasa Abbu bai ganta ba,
Abbu kuwa tun daga nesa ya gane Hanifa da Lokacin da ta shiga cikin gidan da sauri duk a kan idonsa, sosai abun ya bashi mamaki! Tunda yake da Hanifa bai ta'ba yi mata magana ta sa'ba ba sai yau saboda irin tarbiyar da ya bata sosai 'yayan shi suke ganin girman shi da bin umarnin sa, yana wanannan tunanin ya 'karaso gurin.... Abbakar ne ya futo daga shagon yana 'kokarin shiga gidan su Abbu ya dakatar dashi.
Abbakar ya sunkuyar da kansa domin yasan yanzu Abbu din zai cika shi da 'kauli da ba'adi Allah yace." Annabi yace tsaki kawai yake ja cikin zuciyarsa yana fad'in"Mutumin nan d'an sa'ido ne wallahi.
Abbu ya kalli Abbakar a nutse yace." Malam Abubakar yanzu ya dace wannan abunda kuka yi ? Lokacin sallah kowa ya niyyata domin zuwa gaishe da mahallicin sa Ku kuma a lokacin kuka kunna kad'e-kad'e domin kuja ra'ayin al'umma zuwa gare Ku, Wa'iya zubbulah ha'kika shad'ain ya ribace Ku gami da 'kawata muku duniyar ta inda har kuka shagala cikin duniya kuka mance cewa kud'in bayi ne ma'kaskanta gurin ubangiji ku, subahanallahi wa'iya zubullahi! Abbakar yana da kyau Ku gane mecece duniya Ku daina biyewa son zuciyar ku sannan Ku daina biye wa lalatattun abokan da zasu kai Ku su baro ku su hanaku samun rahamar ubangi........."Sai dai idan kaine zaka hana mu mu samu rahama daga ubangijin mu."! Abbu da Abbakar da jamar gurin suka juyo da sauri suna kallon inda suka ji maganar ta futo.
Wani 'karamin romot dake ri'ke a hannunsa ya danna gurin yayi tsit! Sautin 'kidan ya daina tashi.
Yana wata irin tafiya ya 'karaso gurin dasu Abbu suke tsaye ya soka hannunshi guda cikin aljihun wandon dake jikinsa Wanda ya zamana shi ba gajere ba shi ba dogo ba 3Quarter a turance ido cikin ido yake kallon Abbu Wanda shima ya zuba masa nasa idon cike da d'umbun mamakin sa!
Khalid d'in yace." Ina ruwan ka? Me ya dame ka damu da rayuwar mu kai kenan kullum cikin wa'azi da fad'ar Allah yayi hani da abu kaza da abu kaza, kuma irin ku kun fi aikata sa'bon Allah amma sai ku fakaice da Allah don ha'inci."
Guri yayi tsit! Jama'ar da suke gurin suka zubawa Abbu ido Wanda yake jin ina ma 'kasa ta tsage ya shiga ciki ya huta da wannan ba'kin ciki, gefe guda kuma jama'ar gurin mamaki suke yi da ganin ba'kuwar fuskar matashin yaron da yayi tsaye 'kerere a gaban Abbu kamar zai mare shi.
Hanifa dake cikin soro a 'boye ta futo da sauri jin irin 'kus-kus din da jama'ar gurin suke yi ta'ki ta 'kare.
Khalid ya cigaba da cewa''Ya shaik yana da kyau ka kama mutumcin ka tun kafin ya gudu ya barka babu yadda za'ayi ka zuba mana ido ko kuma kace dole ga irin rayuwar da zamu yi, baka ciyar damu sa'anan baka suturtamu don haka baka da hurumin da ka isa kayi wata magana akan mu da rayuwar mu, naji kana wata magana cewar Abbakar ya daina biyewa lalatattun yara kar su lalata shi, ina fatan cewa ba ka manta da abunda ya faru tsakanina da kai a shekarun baya ba,wannan karon na kyaleka amma ka kuskura ka sake min shishshigi cikin al'amura na nayi al'kawarin sai na lalata maka dukanin wani farin ciki da jin dad'i dake dashi a duniyar nan."!
Guri yayi tsit! Kowa yana mamakin rashin kunyar yaron gashi ba d'an unguwa ba d'ai-d'ai kune daga cikin jama'ar gurin suka gane ko d'an gidan wanene suma da sauri suka bar gurin saboda suna jin tsoron kada sunan su ya futo.
Cikin tsananin ba'kin ciki da takaici Hanifa ta 'karaso gurin ta rike hannun Abbu tana kuka tace"Muje gida Abbu."
Abbu da jikinsa yayi sanyi a gurin Saboda ganin yanda jama'a suke nuna shi suna zind'an sa ya 'kara kashe masa jiki domin ya lura sam jama'ar da suke gurin basa ganin laifin yaron sai nashi Saboda kawai yayi hani da aikata 'barna shine suke zind'an sa kamar Wanda ya aikata zina.
Hannun Hanifa ya rike sosai ya kalli Khalid din dake tsaye a Kansu mhar Yanzu hannunsa guda na cikin aljuhu yana yiwa Hanifa wani irin banza kallo, yanzu ya 'kara tabbatar da cewa yarinyar 'yar shi yayi al'kwarin duk sanda mutumin ya 'kara shiga sabgar shi sai ya huce fushinsa akan 'yar tashi domin ya 'kunsa masa ba'kin ciki.
Abbu yace." Yaro kayi a hankali da duniya wallahi zakace na fad'a maka duk abunda kayi sai anyi maka irin shi Allah ya gani ni na futa." Abbu na gama fad'ar maganar shi yaja hannun Hanifa suka bar gurin zucuyoyinsu cike da bakin ciki.
Khalid kuwa bayansu ya bi da 'kaskantacan kallo yaja tsaki kana ya koma ciki shagon Mobson babu abunda ya dame shi
Abbu da Hanifa tafiya kurrum suke yi zuciyoyin su babu dad'i ko kad'an ga wani irin kallo da mutanan unguwar suke musu kamar wasu 'barayi Hanifa ta kar'bi daddumar hannun Abbu ta rike suka shiga cikin gidan.
Ammi na zaune a tsakar gida tana yanka alayyahu taga sun shigo gidan dukanin su fuskar su babu walwala cikin zuciyarta tace babu shakka akwai abunda ya faru.
Mi'kewa tayi a nutse ta bi bayan Abbu da ya shiga d'akin sa, Hanifa kuma ta zauna gurin da Ammi din ta tashi ta cigaba da yanka alayyahun Zuciyar ta na tariyo mata wala'kanci da 'kaskancin da Khalid yayi wa Abbu, zafafan hawaye ne suka fara kwaranyowa daga idanunta, wula'kancin da Abbu yake fuskanta a cikin unguwar nan yayi yawa idan da Abbu zai yarda da shawarar ta da ya amunce sun bar unguwar domin watarana zuciyar ta tana iya bugawa Sam basu da sakewa a unguwa kullum cikin fargaba da rashin sukuni 'bako ma yafi su daraja cikin unguwa yafi so sakewa wai wane irin Abu suka yi wa matane ne?
Tana yankan Alayyahu tana kuka haka Ya Nasir da Hafiz suka yi sallama suka shigo cikin gidan. Ganinta tana kuka ya d'aga hankalin Nasir da sauri ya 'karaso gurin yana fad'in"Autar Ammi menene uhumm? Daina zubar da hawayen nan yana sani fargaba da tashin hankali. "
Ammi ce ta futo daga d'akin Abbu babu yabo babu fallasa tace"Sannu Ku da zuwa yau kun shigo da wuri." Hafiz yace." Wallahi kuwa Ammi da wuri muka taso don a babban masalacin juma'a na gidan sarki muka yi sallahar juma'a."
Ammi tace"Shiyasa mana to Ku shiga ciki Ku huta a kawo muku abunci." Nasiru ya mi'ke tsaye yanayin fuskarsa duk ta sauya ya kalli Ammi d'in a tsanake yace." Ammi me aka yiwa autar ki ne take kuka. "?
Cikin danne ba'kin cikin da take taso mata a zuciya tace" Yanayin rayuwa ne Nasiru yanzu suma suka shigo ita da Abbu cikin b'acin rai abunda da dai kasani yana faruwa a unguwar shine ya 'kara faruwa, Ammi ta kwashe duk abunda ya faru ta fad'a musu.
Nasiru Uban 'yan zuciya yace." Ammi idan ina numfashi a duniyar nan wallahi babu Wanda ya isa ya ci mutumcin Abbu in kyaleshi ba tare da na d'auki mataki a kansa ba, wannan din da ake magana a kanshi komai kud'in ubansa da mukamin sa bai dame ni ba sai na 'bata masa rai a gaban mutane kamar yanda yake kokarin tozarta Abbu a bainar Jama'a shima sai mun had'ashi da hukuma domin duk gagaran sa bai fi 'k'arfin hukuma ba."
Yana gama maganganun ya nufi kofar futa a fusace!
Gyaran muryar Abbu yaji daga cikin d'akin da yake cikin nutsuwa da kamala Abbu yace." Nasiru zo nan..............
*Shin Wanene Khalid kuma wanene mahaifin sa?*
*Wanene Abbu Kuma menene Ala'karshi da Nasiru?*
*Wane Abu ne ya faru tsakanin Abbu da Khalid?*
*MASHAHURI!*
Yanzu aka fara larabarin
*16/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/17, 12:00 AM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*DEDICATED TO:*
*HAUWA S ZARI'A*
_Mmn Uswan_
*RAHAMA UMMU FARISA*
_Ladingo 'yar Ilu_
*BILKISU ABDULRAHAMAN*
_Mrs Habib_
*6*
Asalin Abbu d'an jahar gombe ne bafulatani ne usul gaba da baya suna da yawa sosai cikin dangi amma kuma ba a guri daya suke ba duk sun rabo garuruwa wasu aiki ya kaisu wasu naiman kudi ya kaisu amma dai duk da haka suna zumunci a junan su.
Abbu da Dan uwanshi Amadu su biyu mahaifiyar su ta Haifa a gurin Baban su kuwa su Tara ne maza hudu mata biyar matan duk sunyi aure suna gidan mazajan su suna rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali Saboda irin tarbiyar da suka samu.
Abbu tunda ya taso yake da tsantsane gami da kula kan addini komai cikin nutsuwa yake yin sa yana ganin ba dai-dai ba zaiyi magana ko da kuwa Wanda ya girme shi ne, aikuwa wannan d'abiar tasa yasa mutanan garin nasu suka sanya masa suna da d'an izala Abbu tun bayason sunan haka ya hak'ura ya rabu dasu suna kiran shi da sunan Dan Izalah sunan Abbu kwata-kwata sai ya 'boya a gari Idan ba kace Munzali d'an Izalah ba to ba a gane wa, Asalin sunan Abbu na Gaskiya shine Munzali a, Yana da shekara ashirin da biyar mahaifin sa ya rasu wata bakwai tsakani mahaifiyar sa ta rasu itama to bayan komai ya lafa ne yayi sallama da sauran 'yan uwanshi ya nufo kano makaranta, ko da ya iso kano babu inda ya dira sai unguwar d'orayi nan ya siyi gida maidaidaci ya zauna shi kadai ya cigaba da rayuwar sa kullum da daddare idan ya dawo daga gurin sa'anar shi zai shiga makaranta Malam Jafar Mahmud Adam ya dauki karatu, bayan an tashi ya koma gida Lokacin akwai waya a gari ya siyi karama Nokia kusan kullum sai ya kira 'yan uwa sun gaisa.
Ko da Abbu ya shiga kasuwa Jama'a sai Ku fara yi masa wani kallo na daban ganin sai ana hira dashi k'arfe sha biyu da rabi nayi ko k'arfe daya zai mike da sauri yaje ya dauro alwala kadan daga cikin mutanan ne masu bin shi jam'i a hankali Abbu ya dinga Jan ra'ayin wasu zuwa gare shi, wasu na ganin mutumcin sa wasu kuwa kullum cikin zaginsa suke suna fadin"D'an Izalah mugun bawa."! Abbu bai ta'ba tanka musu ba idan ya shigo kasuwar dukanin su sai ya bi kowa bakin shagon sa ya gaisa dashi. Sana'ar Abbu itace sai da takalam soso a cikin kasuwar wambai dake jahar kano Alhmdullahi Allah ya sanya masa Albarka sosai yana siyarwa Kuma ya bada sari, take Abbu ya suyi fili maidaidaci a unguwar shagari Quartes cikin hikima da sanin meye rayuwa ya fara ginin shi mai sauki duk da ya fuskanci cewar unguwar akwai masu hannu da shuni wannan bai dame shi ba.
'Kokarin shi yaya za'ayi a sirin shi ya rufo kullum cikin yiwa 'yan uwanshi aike yake alkairi iri-iri babu Wanda baya yi musu katsam! Ya samu labarin rasuwar babbar yarsu da suka mayar a matsayin uwa. Cikin tashin hankali Abbu ya nufi garin nasu na Gombe cike da alhinin rasuwar Addah Halima sosai suke girmama ta saboda karamcin ta a gurinsu
Bayan sadakar bakwai ne Abbu yayi nufin komawa gida wani Kawun su da yayi musu shaura ya tsayar dashi da maganar aure dole abbu yabi umarnin Kawun shi, shi kuma ya fada masa cewar yayi masa mata 'yar gidan Iiman ce Yarinyar sunan ta Halimatu.
Jin cewa yar gidan Liman ce yarinyar kuma sunan su d'aya da Addah Halima sai ya amunce kawai..... Nan Kawu yace." Amma dole zaka yi hakuri domin ba budurwa bace tayi aure wata uku kenan da futowar ta mijinta yayi mata sakin wulakanci shine nake so ka aure ta."
Abbu yace." Na amince Kawu idan tani ne gobe a d'aura aure idan na auri bazawara nayi juhadi kuma na aikata sinna domin manzo Allah (Slw) shima da bazawara ya fara Kawu ina so gobe a d'aura mun aure da ita.
Aikuwa kamar yanda Abbu din ya fad'a haka akayi dake juma'a ce ana saukowa daga massalaci aka d'aura auran Abbu da Halima cikin aminci da yarda juna.
Abbu yace." Baya bukatar komai domin duk abun buk'ata ya zuba a cikin gidan shi kawai zai tafi da matar sa ne kano, haka akayi da zasu tafi Abbu ya umarci Nasiru Dan Addah Halima mai rasuwa cewa ya shirya ya bishi domin ya fara nuna masa harkoki Kuma yana so ya sanya shi makaranta.
Ko da Nasiru ya Sanar da mahaifin sa take ya amunce yayi Abbu fatan alkairi tare da addu'ar Allah ya taya shi rikon Nasiru. Haka suka nufo garin kano cike da kewar 'yan uwansu, mussaman Halima da take tunani irin zaman da zata yi a garin da bana su ba, ita kanta tasan zata sha kadaici
****
Abbu da matar shi Halima suna zama na gaskiya gami da bin dokokin aure kamar yanda Ubangiji ya umarci ma'aurata da suyi sosai Halima take jin dadin zama da Nasiru yaron yana yi mata biyayya sosai a lokacin yana da shekaru tara a duniya Halima ta haifi d'a namiji Abbu ya sanya masa suna da Hafizu komai Abbu yayi ya tsaya tsayin daka akan iyalinsa cikin ikon Allah ya kammala gingin shi, da kanshi ya shiga Sabon gidan nasu yayi saukar al'kurani mai girma kana suka tare a gidan daran juma'a babbar rana.
Farko zaman lafiya ne ya wanzu tsakanin Abbu da ma'kotan sa tsawon shekaru goma kenan Lokacin an haifi Hanifa tana shekaru tara Al'amarin Abbu ya 'kara tsananta akan su babu sakewa a cikin unguwa ita kanta Halima idan wani Abu ya faru cikin ugunwar sai dai taje cikin dare kullum tana cikin k'aton hijab da safa hakama Hanifa kullum ciki hijab kuma duk makarantun da suke zuwa na Ahalil sunnah ne kullum Abbu ya dawo daga kasuwa zai zauna da yamma kofar gidan shi yayi ta karatun LITTAFIN addini Lokacin ne kuma yaran unguwa zasuyi ta nuna shi suna dariya ko Kuma kaji suna tsokanar sa da 'Dan izaha wawa ne jakin banza la'ananne."! Abbu yana jin su bazai ce musu komai ba.
A hankali wasu daga cikin matasan layi suka fara zuwa daukar karatu gurin shi shi kuma yana sake wa dasu ya koyar dasu yanda zasu inganta rayuwar su da addinin su.
Haka Abbu yayi ta hakuri da jama'ar unguwa Lokacin su Nasir da Hafiz suna can Sudan karatu can Abbu ya tura su domin samun ingantaccan ilimin addini don haka basu San abunda yake faruwa ba, sai Hanifa a lokacin babu wayo daga baya kuma da ta fara wayo sosai ta fara jin ciwon abunda akewa mahaifinta to da yake yarinya ce Mara kwarafniya da son hayaniya sai dai kurrum tayi kuka ko kuma ta zauna kusa da mahaifin NATA tana bashi hakuri sai dai yayi murmushi kawai yayi ta nusashe da ita yanayin rayuwa ne.
Wata ranar juma'a da Abbu bazai ta'ba mancewa da ita ba a shafin rayuwar sa shine ya shirya tsaf domin zuwa massalaci juma'a na cikin gari domin yau yana son ya zauna sosai yayi azkar kafin fad'uwar rana shiyasa yake so ya tafi da wuri, Yana sanye da sabon yadinsa toyobo fari tas! Dashi hannusa rike da dadduma ya futo yana gyara hular sa mai raga-raga kamar ta larabawan k'asar saudia hular fara ce kamar yadin jikinsa.
Ammi ta futo daga d'akinta hannunta rike da kwalabar turare mai saukin kudi tazo ta fesa masa a jikinsa da daddumar hannunsa kana tayi masa fatan dawowa lafiya. Abbu yayi mata sallama ya futa daga gidan yanajin 'kaunarta cikin ransa, a nutse yake tafiya har ya 'karasa bakin titi yana jiran abun hawa, Allah bai kawo ba gashi yana gudun lokaci ya kure kar ya rasa sallah sai ya fara tafiya da k'afarsa yana tafiya yana tasbihi cikin zuciyarsa.... Wata motar fara tas! Ta fafaro da gudu daga wani layi dake gaba dasu sosai motar tayo kan Abbu da yake kokarin kauce wa motar gashi gefe da gefan shi ruwa ne a kwance a gurin kasancewar lokacin ne na damuna bai an karaba motar ta tawo da gudu tabi ta cikin kwantaccan ruwan dake gaban shi duk ya 'bata masa jikinsa gabaki d'aya!! Abu yabi jikinsa da Kallo cike da takaici da kyama domin ga warin kwata nan tabbatae cewar ba ruwan sama bane hade yake da ruwan sama, Motar yabi da kallo yana jinjina rashin rad'a da rashin tarbiyar Wanda yake cikin motar! Gani yayi motar ta dawo da baya har zuwa inda yake tsaye, Mintuna biyu tsakani Wanda yake cikin motar ya futo Abbu yabi yaron da kallo cikin mamaki! Ganin da yayi wa yaron take ya 'kiyasta a ransa cewar bai fi sa'an Hafiz ba, A hankali yake tafiya har ya 'karaso kusa da Abbu ya fara watsa masa wani irin kallo na rainin hankali...................
*17/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/17, 10:31 AM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*DEDICATED TO:*
*MY MOMYS*
*Momy FATIMA MUSU*
_Nijar_
*Momy INDO AMADU*
_Katsina_
*Ha'kika kun cika iyayen 'kwarai kuna da mutukar girma a gurina wallahi ina alfahari da sanin da nayi muku a rayuwa ta Ubangiji Allah ya saka muku da alkairin sa Allah ya 'kara lafiya da nisan kwana kwanciyar hankali da zaman lafiya, Allah ya albarkaci zuri'arku baki d'aya👏🏻 d'iyar ku tana alfahari daku.*
_______________________
*7*
Abbu ya kalleshi cikin kyakyawan lafazi yace." Haba samari irin wannan tu'kin akwai had'ari a cikinsa, mussaman idan akan titi ne don Allah ka kiyaye ko don gab....."Kaga dakata malam."! Khalid ya katse shi cikin izgili da nuna waye Kai.
Abbu ya bishi da kallo cike da mamaki! Khalid ya cigaba da cewa"Babu babban shashasha irin ka! Ya za'ayi kana ganin mota tundaga nesa baza ka kauce ba sai ka tsaya kalle-kalle don tsabar kidahumanci da 'kauyanci irin naku kawai ka tsaya kan hanya sai kace hanyar ka kai kad'ai."!
Abbu yayi shiru yana mamakin halin da d'abiar 'yayan wasu masu kud'in Sam basu da tarbiyya tabbas ba sai an fad'a ga alamu nan sun nuna yaron D'an gata ne ko ga yanayin suttuarar jikinsa da ita kanta motar da yake ciki.
Tsaki! Khalid yaja ya juya zai tafi Abbu yace." Yaro wannan abunda kayi min a yanzu ya nuna min cewar baka San darajar iyayen ka ba kuma tabbas tarbiyya bata isheka ba, ko ban haife ka ina da kamar ka ya cancanci kayi min haka? Duba fa kaga yanda ka 'bata min jiki da gur'bataccan ruwa."
Khalid ya juyo da sauri yana watsa masa kallon raini yace." Ka haife ni ne."!? Abbu yaji maganar wata iri shiru yayi yana binshi da kallo, Khalid din ya cigaba da cewa"Idan kana jin ciwo da takaicin abunda nayi maka kazo ka rama idan kuma baka rama ba ni zan rama."
Abbu bai fahimci inda maganar tashi ta dosa ba shidai kawai yana 'kokarin nusar dashi cewar abunda yayi bai dace ba.
Khalid mota ya shige cikin zafin zuciya yayi ribas ya dawo da baya da gudu ya shiga cikin kwantaccan ruwan nan Yayi wani irin fallatsi a jikin Abbu wannan karon hadda fuskarshi da daddumar dake hannun shi duk sun b'aci da ruwan dauda Wanda ya fara sanja launi, babu inda bai 'baci ba a jikin Abbu.
Khalid ya zuge glass din motar shi cikin isa da ginshera yace." Tunda nace kazo ka rama ka'ki to na kara wani duk sanda kayi niyyar rama abunda nayi maka ina jiran ka, ya kalato miyau a bakinsa ya tofar a 'kasa cikin izgili yaja motar sa ya tafi.
Abbu yayi tsaye da dadduma a hannu yana tu'ajibun wannan al'amari dai-dai da agogon da yake daure a hannunsa ya jike da ruwa ko da zai duba lokaci sai da ya goge sannan ya duba Lokacin da sauri ya juya da niyyar komawa gida yana me cire hular kansa ya goge ruwan fuskar sa, da sauri yake tafiya domin isa gida ganin lokacin sallahr ya kusa domin har an fara kiran farko.
Yaran cikin unguwar suka fara binshi da kallo suna dariya suna nuna shi wani mai kaud'in tsiya a cikinsu ya fara ihu yana buga jarkar dake hannunsa wacce aka aike shi ya siyo kalanzir ihu yake yana fad'in Ya Shaik ya kamo kifi! Ya kamo kifi ni da sid'in kwano!!! Ya Shaik ni da sid'in kwano yeeeee!! Kafin kace kwabo ya sun taru a gurin suna ihu! Had'e da fad'in "Ya Shaik ya kamo kifi ko taro shi ni da sid'in kwano."!! Abbu ya dinga tafiya da sauri shi Sam wannan ihun da yara suke masa bai dame shi ba burun shi kawai ya isa gida yayi wanka ya sauya kaya kar ya rasa sallah.
Yuya guda yara suka yi har kofar gidan sai da suka ga ya shiga gida sannan suka juya da gudu suna dariya cike da nishadi, Babban abunda zai baka mamaki gami da d'aure Kai shine wasu daga cikin manya unguwa da iyayen yaran suna ganin abunda yake faruwa amma babu Wanda yayi yun'kurin hana yaran abunda suke yi wasu ma dariya suke yi domin suna mutukar adawa da zaman Abbu a unguwar a cewar su zaman shi cikin unguwar ne yasa albarka da rahama bata shigowa saboda ya kasance d'an Izalah.
Ko da Ammi taga Abbu cikin wannan yanayi jikinta yayi sanyi sosai sai suka had'u da ita da Hanifa suka fara kuka domin sun san 'yayan unguwa ne suka yi masa wannan shegantakar Ammi tayi saurin shiga kicin ta juyo ruwan zafi da sauri ta hada ta kai masa cikin band'aki ya shiga cikin sauri, sai da ya shirya tsaf kana ya futo daga d'akin sa wannan Karon ma Ammi dadduma wankakkiya ta mik'o masa ta fesa masa turare Abbu yana sa mata albarka ya futa daga gidan a gurguje.
*Wannan shine abunda ya faru tsakanin Abbu da Khalid shekara hudu da suka wuce*
*17/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/17, 10:12 PM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*8*
Hanifa ce ta wanke 'batattun kayan da Abbu ya cire tas ta shanye su kan igiya tanayi tana sharar hawayen tausayin mahaifin ta, tasan yaran unguwa ne suka yi masa wannan abun sosai take jin takaicin abun Dan dai kawai bata da hayaniya ne yasa take yin shiru ko kuma idan ba'kin ciki da damuwa sun ishe ta tasa kuka sai tayi me isarar ta sannan take yin shiru.
Hanifa kyakyawar yarinya son kowa kin Wanda ya rasa fara ce tas duguwa tana da fad'in 'kugu da yalwar gashin kai Hanifa tana macace mai manyan ga'bai inda Allah ya albarkace ta da manya manyan nonowa Wanda sune suka fara futowa ma kafin ta fara jinin al'ada, lokacin hankalin Abbu ya tashi nan ya mike tsaye a kanta ko da wasa baya bari ta futa da mayafi dole sai hijab mai kauri baya ta'ba bari ta sanya hijab mai roba-roba saboda yanda Allah ya tsara mata hallitan jikinta, tana da wasu irin idanu nasu mutukar daukar hankalin mai kallonta idanunta basu fiye girma ba sosai dai-dai misali ni sun yi wani irin sarf ga gashin ido gazar-gazar hade da gashin girarta fuskarta tana da fad'i amma ba sosai ba hakanan hancin ta yana da tsayi dai-dai misali, babban abunda yake kara mata kyau a fuskarta shine 'karamin bakinta mai dauke da sirarar le'buna masu taushi Duk inda ake neman cikkakiyar mace mai kyau Hanifa ta kai domin ita kanta tasan tana da kyau shiyasa itama take kokarin 'boye wa cikin hijab da ni'kabi Hanifa kenan yarinya mai ladabi da hankali Hanifa saukakkiyar al'kurani ce a halin yanzu suna yin hadda ne shiyasa suke zuwa makaranta kullum da k'arfe hudu na yamma. Hanifa yanzu tana cikin shekara ta goma sha bakwai da haihuwa, Abbu jira yake kawai ta kammala karatun ta na secondary school sai yayi mata aure da mijin da ya za'ba mata.
*Wanene Khalid?*
Alhaji Tijjani Adam shine mahaifin Khalid MASHAHURI, Alhaji Tijjani hamshakin mai kudi ne mai fada aji cikin unguwa Alhaji Tijjani yana harkar canji kudi na ko wace 'kasa yana da mata d'aya da yaya uku biyu mata guda namiji shine Khalid Wanda ya dauki son duniya ya d'ora a kanshi
Khalid baya ta'ba yin laifi gurin shi gashi dai shine 'karami cikin yayan shi amma kamar shine babbansu saboda yanda yake basu doka da oda komai suka yi ba su iyaba tun yana yaro yake iko dasu Idan sunyi magana Dadyn nasu yace." Ai shi namiji ne a cikinsu dole ya zama wakilinsu wataran kuma duk 'kankatar namiji a ko'ina ne to sai yayi jagoran ci, haka zasu hak'ura su kyaleshi yayi tai musu masifa da iko ko kudi suke so gurin mahaifinsh to sai sun bi ta kan Khalid sannan zasu samu, da suka gane haka sai suke lalla'bashi tun da sun lura shi mai son girma da son a dinga kwantar masa da kai.
Khalid yana da mutukar izzah da ta'kama idan ba'a fada maka ba sai kace ya had'a dangataka da jinin sarauta ko kad'an basu da ala'ka da sarauta kawai abun a jinin sa yake, duk da wannan halin nasa na jin kai baya da wulakanci kuma bashi da rowa komai nashi na abokai ne haka suke cika d'akin shi sosai suci su sha su tafi dana tafiya, Khalid tunda ya taso yake da ra'ayin ya zama mawa'ki sosai yake da su a rubuce kusan guda bakwai a halin yanzu ya futar da guda biyu Wanda sukayi mugun dad'i da ma'ana gashi sun karbo a gurun jama'ar gari mussaman wak'ar shi ta biyu mai taken *Kwalelen Ku* sosai wa'kar tayi matasa da 'yan mata suna jin dadinta saboda yanda yake zuba kalaman soyayya cikin wa'kar ko wace budurwa sai taji kamar da ita yake.
Duk Abunda Khalid ya nuna yana so iyayan shi da 'yan uwanshi suna so suna Goya masa baya shiyasa yake alfahari dasu a duk inda ya shiga. Mahaifiyar sa dama ba macace mai zafi ba ita dai tsakanin ta dashi nasiha ce kullum da Jan kunne ya kula da duniya
Khalid Diploma kawai yayi ya watsar da karatun hankalinsa ya dauke kan harkar wa'ke-wa'ken sa Lokacin Alhaji Tijjani yaji babu dad'i domin yana da burin yaga Khalid din yayi karatu sosai to gudun ya 'bata masa rai ya 'kyaleshi kawai yake sakar masa kudi don kasuwa ma sai yaga dama yake zuwa idan yaje ma banda kallon 'yan mata babu abunda yake yi cikin wayar shi hotonan yan mata ne kala-kala gasunan Wanda Allah yayi masa baiwar su kwailaye da cikkakun mata zawarawa da matan aure kowa Khalid mussaman da ya fara wa'ke-wa'ke zamana har so ake a ganshi.
Khalid dogone amma ba sosai ba yana da fad'in k'irji had'e da murdadan jiki gab'obinsa duk a bude suke bashi da haske sosai amma yanayin Hutu da kwanciyar hankalin da yake ciki yasa ya zama fari hade kuma da had'addun Maya Mayan da yake shafawa a jikinshi Khalid yana da kyau da shiga zuciyar mutum yanayin yanda yake magana sanyi-sanyi zai yi mutukar burge ka Ammafa Khalid mugun futinanne ne a 'bangaran mata yana da muguwar sha'awa sosai gashi Mayan nono manya ne a kirjin mace ya tsani yaga mace mai 'kananon nono ko cikin'yan matan shi yafi kula cikkayar mace duk kwailayen nan baya sauraran su sai da yaga pictures dinsu ya wuce su yana dariya tare da fad'in"Kayan takaici."!
Khalid kenan d'a d'aya tamkar da dubu gurin Alhaji Tijjani d'an canji, yanzu Khalid yana da shekaru ashirin da bakwai a duniya ya kai munzakin yayi aure amma Sam bashi ne a gaban shi duk da yanayin hallitar da Allah yayi masa ta tsananin sha'awa, kusan kullum ya kwanta sai yayi mafarkin mace haka yake tashi da gabanshi a mike dai da yan dabaru sannan yake samun sauki, duk da wannan halin da yake ciki bai matsantawa kansa lallai sai yayi aure ba, harkokinsa ne a gabanshi duk randa sha'awar shi ta dame shi kawai dai bude wayar sa Yayi ta kalle-kallen pictures d'in 'yan mata iri_iri.....To tanan yake samun sau'ki sha'awar da ta ta taso masa.
Yanzu Khalid shi kad'ai gaban iyayen sa. Yayunsa mata anyi musu aure Hafiza ta haifi 'yaya biyu Kalisat ce me haihuwa d'aya.
Gidan Alhaji Tijjani d'an canji yana gab da futa Babban titin da zai sadaka da cikin gari 'katon gidane na gaske Wanda yake dauke da masu gadi har guda hud'u saboda yanayin tsaro da kuma yanda Alhaji yake shige da fuce da kudi cikin gidan...... Motocin da suke harabar gidan sun fi biyar duk masu tsada ne Alhaji Tijjani yana da amintaccan dravar sa shine Kuma yake masa bunkice a cikin ugunwar duk wani abu da ya faru shine zai zo ya fada masa. Hamza dravar shine ya kawo wa Alhaji gulmar Abunda ya faru tsakanin Khalid din da Abbu.
Lokacin Alhaji Tijjani fad'a ya dinga yi sosai yake cewa Abbu bai isa yayi wa d'an sa baki ba lalacewa sai da ya gani cikin zuri'ar shi amma badai tashi zuri'ar ba, Hamza dravar yace." Wallahi kuwa Alhaji kasan mutumin mugun d'an Izalah ne irin masu mugun bakin ciki da kyashi game KUDI Kai kanka da zai samu fuska a gurin ka sai yazo ya kawo maka 'kauli da ba'adi Allah yace Annabi yace."
ALHAJI Tijjani yace." Haba shiyasa mana ya sanyawa yaro na ido har yana kokarin yi masa baki to Allah yasa yace zai zo min gida wallahi sai na sanya anyi masa tsirara dama irin su basu da amfani cikin Al'umma.
Hamza dravar ya dinga dariya cike da nishadi yace." Alhaji ai ba sai ka sanya ba mu da kanmu zamuyi masa tsirara mu sa yara su raka shi da dutse."
To tun daga wannan abunda ya faru Alhaji Tijjani ya kara bawa Khalid Lasisi gami da d'aurin gidi cewar duk wanda ya ta'bashi cikin unguwa kar ya saurara masa A wannan lokacin ne kuma su Khalid din suka je gurin Abbu da nufin ya koya musu ilimin jima'a don tsabar tantiranci kuma duk Khalid din ya shirya plan din domin ya 'batawa Abbu rai.
*Wannan shine abunda ya faru, Yanzu za mu koma ainihin labari*
*18/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/18, 9:22 AM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*9*
Rai a'bace Nasir ya shiga dakin da Abbu yake ya same shi a zaune kan dadduma hannunsa rike da wani k'aramin littafi irin na addini.
Abbu ya aje littafin hannunsa ya kalli Nasir din a nutse yace." Haba Nasir kayi aiki da hankali mana ka dinga sassauta wa zuciyarka kan abunda bai kai ya kawo ba, idan kace zaka biye masa to kai ma kazama Mara d'a'a da tarbiyya kenan? Kar ka kuskura ka tanka musu ka kyalesu idan duniya ce duk zata koya musu hankali ni dai duk cikinsu babu Wanda zan yiwa baki a cikinsu amma fad'ar Annabi Muhammad (Slw) gaskiya ne cewar duk abunda ka shuka shi zaka girba idan sharri ne ka girbi sharri idan alkairi ne ka girbi alkairi, ni dai nasan tarbiyya da na baku saboda haka duk wani Abu na cin mutumci da jama'ar ugunwa suke min cikin Ku babu wanda na amunce yace zai dauki fansa."
Nasiru jikinsa yayi sanyi jin nasihar Abbu kullum hakace take kasance wa a tsakaninsu dashi Sam baya bari ayi rigima dasu a cikin unguwa tun suna yara idan suna fada da yara suka cuce su Abbu baya bari su rama, Nasiru yana bala'in tausayin Abbu ta inda yake addu'a gurin Allah da ya huwace masa yayi arzikin da zai dauke Abbu daga cikin unguwar ya huta da ganin wannan 'kaskanci.
******
Hanifa ne da Asalamiyya can tsallaken titi suna so su tsallaka titi su isa gida hadari ya had'o sosai gashi ana wata irin iska mai 'k'arfi mai tada 'kura ledoji sai yawo suke a sama.
Hanifa duk jin ta take a takure dalili iskar da akeyi duk tabi tasa hijab din jikinta ya manne a jikinta shatin jikinta duk sun bayyana shi kanshin ni'kab din sama yake yi yana kwancewa tana sake d'aure wa, titi ta kalla manya motoci da 'kananu mashina da a dai-dai sahu suna ta wuce wa a lokacin kowa ko 'kari yake ya isa gida kar ruwa ya jinbgeshi.
Jin an fara yayyafi ne yasa Hanifa kallon Asalamiyya tace" Kinga ni ko an fara yayyafi dama nace miki mu bari tukkuna ruwan ya dauke sai mu futo wallahi ina jin tsoron dukan ruwa a jikina domin yana sani zazzab'i kawai kizo mu koma cikin makaranta."
Asalamiyya tace"Ai tunda muka futo wallahi sai mun isa gida humm wai mu koma makaranta to kika San sanda ruwan zai dauke idan muka Kom....... Kafin Asalamiyya ta rufe bakinta ruwa ya kece da k'arfin gaske! Hanifa ta waiwaye ko ina babu gurin mafaka sai shagunan mutane Wanda a lokacin duk maza sun shiga sun fake gudun dukan ruwa! Ita kanta Asalamiyya ta tsorata da yanda ruwan yake zuba da k'arfi tuni Hanifa ta fara matsar hawaye ta tsani dukan ruwan sama gashi saboda rashin imani masu ababen hawa sunki su bari su wuce
Wata lafiyayyar mota ce tazo ta gifta su da gudu. Abbakar yayi saurin Kallon Khalid da yake driving yace" ,Khalid please koma da baya don Allah 'kanwata Asalamiyya gasu can tsaye ruwa na dukan su.
Ya mutsa fuskar sa yayi a hankali yace." Kace ruwa na dukan su ita da waye ne ni fa kasan ba kowa ne tarkace na dauka a cikin mota na ba."
Abbakar yace." Ita da 'kawarta ne please Handsome muje don Allah taimako zaka yi kasan tana da Asma Kuma idan ta tashi muna shan wahala wallahi."
Khalid ya fara dawowa da baya-baya har ya isa inda suke tsaye, Abbakar ya zuge glass din motar Wanda ya kasance me duhu sosai, Asalamiyya na ganin yayanta ta saki a ajiyar zuciya hannun Hanifa ta rike tace Ya Abbak bude mana don Allah mu shiga ruwa sanyi nake ji."!! Da sauri ya bude masu gidan baya, Asalamiyya tayi saurin shigewa, Hanifa na kokarin shiga suka ji muryar shi yana fad'in "Wannan yarinyar kar ta sake ta shigar mota da wannan 'bakin abun na fuskarta."
Abbakar yasan halin Abokinshi idan ya fad'i magana baya karya ta, da sauri ya kalli Hanifa dake tsaye ruwa na dukanta sai makyarkyata takeyi yace/"Hanny cire wannan abun ki shigo muje gida dama kuma ya ji'ke da ruwa."
Girgiza kanta tayi tana jin wani irin fad'uwar gaba ganin mutumin da take ba'in so duk duniya wato Khalid ita dai Allah ya d'ora mata sonshi, a hankali tace"Ya Abbakar kuje kawai Abbu ya hanani cerewa." Cike da mamaki! Ya d'ago kansa yana kallonta dama tunda yaji Abbakar ya ambaci sunan Hanny ya fahimci yarinyar ce, wato za'a taimake ta saboda tsabar taurin kai irin nata ta gwammace ruwan yayi ta dukanta a kan ta bude fuskata.
Motar yq bude ya futo ruwa ya fara dukan jikinshi bai damu ba ya zagayo inda take tsaye, tun kafin ya 'karaso ya 'kurawa kirjin ta ido kurr! Ruwa ya jika mata jiki sosai hjib din duk ya manne mata a jikinta shatin nonowan ta duk sun futo hattada da nipple dinta sai da suka mike ga Kansu nan yana gani wata irin ajiyar zuciya ya sauke muguwar futinar shi ta motsa lips dinshi yasa a bakinsa ya 'karasa da sauri ya fuzge ni'kab din yana watsa mata kallon dame kika fi sauran mata.
Hanifa ta takure jikinta tana kauda fuskarta tsoro duk ya shigeta kallonta yake daga sama har 'kasa She is beautiful girl!! Zuciyarsa yake ayyana abubuwa da dama a kanta sosai yanayin yarinyar yayi masa babu abunda yafi daukar hankalinsa a jikinta irin Girman nonowan ta gasu masu fad'i da tsini ji yake kamar ya ta'basu Yanzu ya fahimci Abunda yasa Ya Shaik din yake kaffa kaffa da ita Saboda tsarin jikinta. Tsaki yaja ya bar gurin.
Mota ya bude ya zauna mazaunin sa, wayarsa ya dauka ya bude camera sosai ya saita inda take tsaye ya dauke ta a hoto kusan guda uku Abbakar din da Asalamiyya da ita kanta Hanifa basu komai ba, a guje yaja motar sa suka bar gurin kamar walkiya......... Hanifa ta bi motar da kallo wasu irin hawaye masu d'umi suna ziraro mata a fuska.
*8/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/18, 8:57 PM] .: *MASHAHURI!*
*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*
*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*
*FREE PEGE*
*10*
Hawaye ne kawai yake zubo mata saboda tsabar bakin ciki da takaici! Babban abunda ya d'aga mata hankali a yanzu shine ni'kab din ta da yake hannu shi gashi ya tafi dashi, batasan abunda zata ce a gida ba, hawayen fuskarta ta share tana jin shigar wani irin sanyi a jikinta sosai take kyarma ruwa sama na zuba a jikinta. Hijab dinta ta tattare da hannunta guda ta kalli titin taga babu goslow kamar d'azu da sauri ta matsaya kusa wata mota na wuce wa tayi saurin tsallake wa tana hamdala cikin zuciyar ta, kai tsaye layin su ta shiga cikin sauri sauri take tafiya Lokacin ruwan ya fara yin sauki mutane sun fara futowa mussaman masu Sana'a cikin unguwar.
Motar d'azu ta gani a fake a 'kofar gidan su Asalamiyya tayi saurin kauda kanta tana jin matsanancin fad'uwar gaba.
Khalid ya futo daga shagon Mobson da key a hannunsa ya ga gilmawar ta wani irin mayen kallo yabi bom-bom dinta dashi yanda suke wani irin motsi duk shatin su sun futo dalilin ruwan da ya ji'ka mata hijab, ita kanta tana jin yanda suke motsi don na yanda zatayi ne taci sa'a ma babu mutane sosai a unguwar saboda ruwan da akayi da tasan sai sunyi mata ihu!
Mota ya bud'e ya shiga jikinsa duk yayi sanyi masifaffiyar sha'awar yarinyar yake ji a jiki da jininsa.
Wayar sa ya bude hannunsa na kyarma ya fara duba pictures din da ya dauketa d'azu, lafiyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanunsa suka yi masa tozali da had'adadu cikakkau lafiyayyyn Brest dinta. Ya dinga sakin wata irin ajiyar zuciya yana cije lips d'insa gawurtaciyyar sha'awar ta na kara nunkuwa a cikin zuciyar sa.
Gefen fuskar ta ya tsurawa ido inda wani lafiyayayan gashi ya kwanta sai yaji yana sha'awar ganin fuskarta domin d'azu Sam bai tsaya ya kalle ta ba, wannan hoton kuma ta juya fuskar ta can ya d'auke ta.
Gefan Le'bunanta ya tsurawa ido yana makyarkyata! Da sauri ya d'ora fuskar shi kan scerrn din wayar inda saitin nonowan ta suke ya hau goga fuskarsa yana sakin nishi.
Tunda yake kalle-kallen pictures din 'yan mata iri-iri bai ta'ba hauka cewa irin na yau ba Hanifa ta gama rikita shi da tsarin hallitunta a halin yanzu babu wata 'ya mace da yake sha'awa sama da ita, da kam baya sha'awar zina ko kad'an amma yanzu ji yake yi zai iya yin sex da yarinyar mutukar zata bashi had'in kai shi kuma zai sakar mata kudi sosai zai tsaya mata a komai na rayuwa burin shi kawai yaji shi a jikinta hannunsa na lallaya 'kawatattun nonowan ta masu rikita masa lissafi
*Ni kam nace wai Khalid ka mance Yarinyar 'yar babban ma'kiyin ka ce kamar yanda ka fad'a Ya Shaik*
*****
Cikin siriryar muryar ta tayi sallama cikin gidan Ammi ta amsa da sauri hade da le'ko da kanta ta window tana mamakin Hanifa ta tawo cikin ruwa, nan bakin kofa ta tsuguna tana cire safar da take 'kafarta wacce ta jike jagab da ruwa ta cire hijab dinta da yake d'igar da ruwa kan igiya ta rataye.
Ammi tace"Yanzu Hanifa don rashin hankali cikin ruwa kika tawo mai makon ki bari ya tsagaita tukkuna."
Turo baki gaba tayi cikin shawaga'ba tace"Ammi to a ina zan fake ko wane guri cike da maza ai tare muka tawo da Asalamiyya ma."
Ammi tace"Lallai kun cika sakarkaru masu wasa da lafiyar Ku, idan banda rashin dubara irin taku ai sai Ku koma cikin makarantar ku bari ruwan ya tsagaita sai ku tawo gida.
Hanifa shiru tayi tana tutturo bakinta! Ammi tace"Wuce maza ki cire kayan ni nayi mamaki ma da baku had'u da Abbu ba domin yanzu yayi alwala ya futa."
Tace"Ammi kin san hanyar ba d'aya bace tunda massalacin yana bayan layi." Ammi tsakar gida ta futa tana ta faman fad'a kan Abunda su Hanifa suka yi na tawowa cikin ruwa .
Riga da zani ta sanya a jikinta ta futo da ji'kakkun uniporm din ta zuba su a bokitin da suke yin wanki ta dauki buta ta fara d'aura alwala I dan ta gabatar da sallahr sai ta wanke su domin dasu zata je gobe idan Allah ya kaimu.
Cikin Uwar d'aki ta shiga tw shimfid'a dadduma a nutse ta sanya dogon hijab dinta ta tada sallah bayan ta idar tayi azkar kamar yanda ta saba tayi addu'oin da Abbu ya koyar da ita ta shafe fuskarta, abun mamaki sai ta gaza tashi daga gurin ta fad'a tunanin abincin zuciyar ta wato Khalid lumshe idonta tayi tana kara tunano suffarsa da yanayin sa da yanda yake magana sanyi-sanyi wani irin shauki ya kama ta lumshe idonta tayi hade da kifa fuskarta jikin gadon Ammi tana sauke wata irin ajiyar zuciya ta tsantsar kaunar Wanda bai san tana yi ba ikon Allah kenan.
Ammi ce take'kwala mata kira tana daga kicin take fad'in"Hanifa kizo ki dauki abunci ko." Inaaa! Hanifa batasan tana yi ba tana can tunanin Khalid *MASHAHURI*
Ammi ta kira Hanifa ya kai sau biyar shiru Ammi tace"Kadai yarinyar har tayi bacci? Abunci ta fara d'auka tana shiga dashi cikin. Ta d'aga labulan d'akinta tana fad'in"Hanifa ke Hanifa."!
Firgigit! Hanifa tayi tana kallon Ammi dake tsaye bakin 'kofa. Nan Ammi ta fahimci ba bacci take yi ba kuma ga yanayin ta nan duk ya sauya kamar wacce take cikin damuwa.
Ammi tace"Tunanin me kike yi Hanifa uhum? Tun d'azu ina ta kwala miki kira shiru ."?
Hanifa ta fara magana cikin sangarta kamar yanda ta saba tace"Ammi ni babu komai bacci nake so nayi ga wani irin sanyi yana damuna."
Ammi dai ba yarinya bace balle Hanifa ta ninke wa baibai gyada kanta kurrum tayi ta saki labulan ta futa tana tunanin lallai babu shakka akwai abunda yake damun yarinyar dole ta zauna da ita tun kafin Abu yayi nisa."
Jiki a salu'be ta futo daga d'akin ta d'auki wani k'aramin kaskon 'kasa Wanda Ammi take yin turarar wuta dashi kicin ta nufa ta fara d'ibar garwashin wuta a ciki.
Ammi tace"Me zakiyi dashi."?
"Ammi sanyi nake ji wallahi nasan dole yau sai nasha panodol." Ammi tace"Dole ne kuwa so nake Yayunki su dawo su kar'bo a chamis ni kaina ina 'bukatar Robb jikina duk ciwo yake yi.
Abbu ne ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama.
0 comments:
Post a Comment