*41*
Ganin irin kukan da take ne yasa Nasir shiga cikin dadin yana kokarin d'ago ta Hanifa ganin yana kokarin ta'bata ne ta fuzge jikinta ta koma gefe guda tana kuka had'e da sharbe majina! Ammi ta cigaba da fad'a tana cewa"Wallahi duk wata futana taki zakiyi ta ki gama Hanifa baki da miji sai Nasiru shi wancan din da kika kwallafa rai akanshi dole ki hak'ura domin zuciya ta batayi na'am da ki aure shi ba idan da ma mutuwa yayi to da mun huta da wannan bakin ciki da kike so kin kunsa mana."
Shuru dakin yayi sai sautin kukanta ne kurrum yake tashi Abbu yayi gyaran murya tare da fad'in "Halima duk Wannan maganar bata taso ba idan zakiyi magana ki dunga taunawa kafin ki fade ta, Nasan k'uruciya CE take damun ita Hanifar kuma ni magana a tsakani na da ita ta kare dole babu gudu babu ja da baya aure tsakanin ta da Nasiru indai ina raye a duniya sai anyi shi tunda na bata hakkinta a matsayin ta tace ta bani wuka da nama magana kuma ta wuce a gurina." Jin abunda Abbu din yake cewa ne yasa Hanifa ta kara fashewa da kuka tana burgima a kasa Hafiz ne ya shigo dakin a zuciya ya dagota tare da daga hannu zai mare ta Abbu ya rike hannun nasa yana girgiza masa kai, yana numfarfashi yace." Abbu baka ganin iskanci. Da take yi kamar hanifa ana gaya mata magana tana wani Abu kawai ka rabu dani na Zane mata jikinta tunda kokari take ta tona mana asiri a gari."
Abbu yace." Hafiz k'yaleta duk wannan abunda take yi me wucewa ne watarana sai labari yawan dukan bashi da amfani. " Hafiz ya futa daga dakin ransa a b'ace, Nasiru kuwa duk jikinsa yayi sanyi sai yake jin kamar yace da abbu din shi ya hak'ura kawai saboda baya son tashin hankali da abunda zai taba zumuncin iyayansa.
Haka suka yi ta Abu daya har asubah Hanifa bata daina iface-iface ba dayawa daga cikin makotansu sunji abunda yake faruwa gidan shaik din sai suke tunani. Ko wani abune ya faru to da yake babu wani zaman lafiya sosai a tsakaninsu yasa babu Wanda ya tambayi ba'asi.......sai k'arfe shida da rabi sannan Hanifa tayi sallah idanunta duk sun kumbura sunyi jazur ita burunta kawai taje gidansu Abbakar ta tambayeshi lafiyar Khalid gashi Abbu yace kar a kara barinta ta futa makaranta ma ya soke ta daga yau ta zauna a gida har lokacin d'aurin auran su da Nasiru Ammi taji dadin wannan hukunci da ya yanke.
****
Garau ya tashi Dr na tsaye a kanshi yana duba jikinsa tare da tambayar yaya yake jin yanayin jikin nasa, Khalid yace. "Baya jin wani Abu sai dai rashin k'arfin jiki." Dr ya cigaba da bashi shawarwari da yanda zai inganta lafiyar sa kana yace." Duk wani Abu da ranshi da gangar jikinsa yake so to yayi kokarin biya wa kanshi bukata wannan shine zai sa ya samu ingantacciya lafiya kuma ya rage saka damuwa cikin zuciyarsa. Khalid duk ya dauki shawarar Dr domin ya Riga ya gama yankewa kansa hukunci mutukar Shaik bai bashi auran Hanifa ba sai ya haddasa masa b'acin rai kamar yanda ya haddasa masa zaiyi amfani da irin son da Hanifar take masa ya rama abunda yayi masa, tunda dai shi baya jin rarrashi da ban baki.
Wannan shine abunda ya kudurta cikin zuciyarsa,ko da Dady nashi ya shigo yaga jikin NASA yayi sauki sai ya kwantar da hankalinsa ya zauna kusa dashi yana rarrashin sa da "Ya kamata ka rabu da yarinyar nan tunda ubanta baya do duk ga 'yan mata nan yayan manyan masu kudi da yayan sarauta duk wacce ka nuna kana so da gudu ubanta zai amunce Myson kana wahalar da kanka gurin yar gidan mutsiyacin mutumin da bai gaji arziki ba inda ya gaji arziki bazai yi wannan jahilcin ba arziki na binshi yana gudu saboda bashi da rabo." Ya karasa maganar cikin tsananin jin haushin Abbu.
Khalid ya sauke ajiyar zuciya cikin yanayin maganar sa yace." Dad ka Bari kawai magana ta wuce a gurina tunda dai mutumin bayajin Allah da Annabi ni na San abunda zanyi akan al'amarin amma maganar cewa in rabu da yarinyar shi Sam bata taso ba Dad kamar yanda suka bani wahala nima sai na basu ita tunda dai ya'ki yarda ayi abun cikin dad'i da kwamciyar hankali to zai fuskanci b'acin rai."!
Alhaji Tijjani ya daga kafad'a sama alamun maganganun da Khalid din yayi basu dame shi ba yace." Duk abunda kake ganin shine mafuta a gareka ka aiwatar dashi ina goyon banyanka."
Khalid sakin jiki yayi sukayi hira da dad din NASA kafin dr ya shigo ya sallemsu, suka nufi gida.
Ammi kuwa futa tayi daga sabgar Hanifa ta cigaba da aikace-aikacen ta babu abunda ya dameta da Hanifar da take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta huta gashi har yanzu gabanta bai daina fad'uwa ba, k'arfe goma shabiyu Abbu ya futo tsaf dashi ya tsaya kusa da Ammi dake zaune kan k'aramar kujera tana gyara alaiyahu yace."Halima zanje dorayi gurin Malam labaran domin ina so cikin satin nan mu tafi gombe jikina Yayi sanyi da wannan al'amari ina ganin gwara kawai muje yan uwa su shaida a d'aura auran yaran nan duk tsiya nasan idan taga ta zama matar wani zata hak'ura da Wannan yaron."
Ammi tace"Abbu haka yayi nima hankalina yafi kwanciya da hakan muyi nesa da garin gaba daya idan ankwana biyu sai mu dawo."
Gyada kai Abbu yayi yace." Halima mawuyacin abune zai dawo damu garin kano idan muka koma mahaifarmu shikkenan kuma."
Ammi tayi hamdala cikin zuciyarta dama Kwata-kwata bata kaunar zaman garin kano saboda yanda aka takura musu ko ina babu sakewa.
Abbu yayi mata sallama ya futa ta rakashi da addi'ar dawowa lafiya
Duk Wannan maganar da suke yi a kunnen Hanifa gwiwar ta tayo sanyi k'alau Jin abunda Abbu ya fada, ta fara share hawaye tana tunanin mafuta ta koma daki ta rakube jikin gado Motsin Ammi taji tana jawo ruwa a rijiya da sauri ta mike tana le'kawa taga ta shiga band'aki hijab dinta ta jawo dake jikin kyaure a rataye ta fuce daga gidan da sauri!
Kai tsaye gidansu Asalamiyya ta nufa gabanta na cigaba da fad'uwa addu'a take Allah yasa ta tadda Abbakar a gidan aikuwa a kofar gida ta ganshi a zaune shin kadai yana latsa waya.
Mik'ewa yayi suka shiga soron gidan yana mamakin ganinta a hargitse yace." Hany meye naga duk kin hargitse idanunki sunyi jawur." Cikin kuka ta fada masa irin mafarkin da tayi sannan ta fada masa maganar da taji Abbu na fadawa Ammi yanzu. Da sauri ya Ciro wayarsa ya fara kiran Khalid din bugu daya tayi ya dauka Hanifa taji muryarsa radau ajiyar zuciya ta sauke ! Abbakar yace." Guy gani ga hany fa tana kuka wai tayi mafarki ka mutu."
Mik'ewa yayi zaune sosai da wayar a hannunsa yace." Pls bani ita." Abbakar ya mik'a mata wayar batasan sanda ta karba ba da sauri ta kara a kunnen ta cikin kyarmar baki tace." Ashe baka mutu ba."!?
Wani killer smile yayi ya shafa sumar kansa cikin wani irin murya yace." Na kusa mutuwa baby sonki ya sanya ni a gaba wai ya za'ayi ne uhum."!!!!
Muryarsa tayi bala'in kashe mata jiki taji k'afafunta sun kasa daukarta jingina tayi jikin bango tana lumshe ido tace"Wallahi nima bansan ya za'ayi ba gashi Abbu ya matsa min sosai yace ma zamu koma gombe ne gaba daya kuma ma yace aurena da Ya Nasiru dole sai anyi."
Wayar ya rike sosai a hannunsa ya gyara zama yana mamakin Ya Shaik wato guduwa zaiyi daga garin ma saboda shi lallai shima ashirye yake."
Ma'ke muryarsa yayi dama gata da sanyi kamar ta mata yace." Ok idan Abbu ya gudu dake ni kuma zaki gudu da zuciya ta nasan lokacina yazo karshen rayuwata yazo baby zuciyata had'e take da taki kar ki bari a rabamu nasan kema kina sona kinji." Cikin shagwaba ya karasa maganar.
Wannan salon da yayi amfani dashi yayi mutukar tasiri a zuciyarta ta inda ta manta ma ita da wanene a gurin ta lumshe idonta tana k'ara kankame wayar a hannunta ido a rufe tace"to me kake so inyi nima nasan Kai nake so amma Abbu ya hana ni kai wai dole sai na auri zabin sa."!
Fuska ya bata kamar tana kallonshi ya canja murya tayi kalar tausayi yace." Abunda zakiyi kawai kije kije masa ni kike so hakan zakiyi na gane kina sona da gaske."
Girgiza kanta tayi a hankali tace"Bazan iya ba ni dai.'"! Khalid ya sha kunu tare da mik'ewa tsaye ya Dan daga muryarsa da b'acin rai yace." To tunda baza kiyi min yanda nake so ba ki bawa Abbakar wayar ki gwamace sonki ya kashe ni ko gwara ma na mutu akan in zauna in ganki tare da wani."!!!! Shiru tayi gabanta na fad'uwa.! A Dan fusace yace." Ki bawa Abbakar wayar zamu yi magana."! Mik'awa Abbakar wayar tayi jikinta duk yayi sanyi.
Abbakar ya futa waje suna magana dashi kusan minti biyar ya dawo yana kallonta a hankali yace." Khalid yace wai kizo muje gurinshi yana so ya ganki ." girgiza kanta tayi yace." Saboda me."? A hankali tace"Abbakar ina jin tsoro ne wallahi." Tsaki Abbakar yaja yace." Kiyi ta tsoro ki cuci kanki guy nan yana bala'in sonki ke kin samu kina wasa shin kin San iya adadin yan matan da suke sonshi kuwa? Kin San kud'in da mahaifinsa yake dashi a garin nan? Wallahi Hany kiyi wa kanki fada kar ki bari Abbu ya cuce ki kisan yanda zakiyi ki kubutar da kanki." Wad'annan hudubobin na Abbakar sunyi bala'in tasiri a zuciyar Hanifa take tayi na'am dasu taji zuciyarta ta kekashe kallonsa tayi Tare da fad'in"Abbakar muje in ganshi ko naji dad'i cikin zuciyata." Abbakar ya nufi kofar futa tabi bayansa.
Titi suka futa suna tsaye suna jiran abun hawa Abbu ya sauka daga a dai-dai ta can ya hango Hanifa suna kokarin shiga a dai-dai ta sahu ita da Abbakar sosai Abu ya bashi mamaki ganinta babu ni'kab hijab din jikinta ma babu girma sosai yake tunanin ya akayi ta futo daga gida kuma INA zasu je ita da Abbakar din.!?
Bashi da Wanda zai bashi amsa haka yana ji yana gani a dai-dai tahu ta wuce dasu da gudu ko da wasa Hanifa bata ganshi ba saboda yana can daya tsallaken dama kuma duk hankalinta da nutsuwarta ba a jikinta suke ba.
Hanifa taga sun tsaya a kofar wani tankamamen gida Abbakar ya futo da kudi ya bawa me Babur din yayi tafiyarsa ita kuwa Hanifa unguwar take bi da kallo gidajen manya manya amma duk girman gadajan basu kai Wanda taga Abbakar ya nufa ba, jiki a sanyaye take bin bayansa Hankalinta bai kara tashi ba sai suka shiga ciki taga yanda securities suke binsu da kallo sai ta tsorace! Sosai ta kankame hannunta cikin hijab dinta kamar munafuka haka tayi kasa da kanta, Abbakar ya gaisa dasu sama-sama suka wuce ciki....... Kai tsaye part din Khalid suka nufa Yana tsaye bakin window din dakinshi ya hango zuwansu kallonta yake yi kamar tsowon maye yayin da sha'awarta take kara ninkuwa cikin zuciyarsa, baya so ya aikata wani Abu na batanci a kanta kuma baya so ya aikata abunda Allah ya haramanta amma Yana ganin kome yayi mata a halin yanzu ubanta me ya jawo tunda dai ya'ki yarda ya bashi auranta....... Dake akwai 'yar tazara daga gurin da ya hango su sai ya bude kofa ya futo ya tsaya hade da soka hannunsa cikin aljuhu yana jiran 'karasowar su, Har yanzu idonsa ns tsaye a kanta, jikinta ya bata ana kallonta a tsarge ta dago kanta aikuwa suka hada ido dashi yana wani marairaice fuska, Hanifa cigaba da tafiya tayi kuma bata dauke idonta daga kansa ba tana jin wani irin fleengs a tartare da ita gaskiya Allah ya sanya mata son guy kamar ta mutu haka take ji tsigar jikinta har ta fara mik'ewa, suna karasawa Abbakar ya bashi hannu suka tafa kamar yanda suka saba ya kalli Hanifa da ta jingina da bango kanta a 'kasa yace."beb kinzo."? A langwabe ta daga masa kai! Yace."Good yanzu na kara tabbatar da cewar kina so ki shigo mu tsara yanda zamu yi ko."!? A kasalance yake maganar, Hanifa ta Dan kalleshi tana so tayi magana amma yanayin da ta ganshi ya sanya taji tana Neman ta rasa nutsuwarta yana sanye ne da karimin wando short nickar da wata d'amammiyar vest abunda da Wanda yake da jiki a murd'e ko ina na jikinsa a cike yake babu wata rama lafiyayyar fatarshi sai shek'i takeyi alamun ana gyara ta sa sabulai gami da mayamayai masu tsada,, k'irjinsa ta Dan kalla taji wani irin Abu a jikinta da sauri tayi kasa da kanta, shi kuma ya matso jikinta sosai masifaffan k'amshin sa yayi mata sallama, hannunta ya rike cikinsa yana Dan murzawa kadan ya kalli Abbakar yana Dan ya mutsa fuska domin har ya fara kwancewa domin dumin hannunta ya soma gigita shi yace."Guy kaje kawai ni zan maido da Queen gida Ok."! Abbakar ya bude bakinsa cike da mamaki yake son yin magana Khalidn ya harare shi kadan yaja hannunta suka shige ciki Abbakar ya bishi da kallo yana sakin dariya ya San halin Guy tunda yaga ya rikice yasan bazai bari yarinyar ba sai yadan 'Dana gyda kansa yayi kawai ya bar gurin.
Suna shiga cikin parlor sosai Hanifa taji wani kamshi da sanyi dad'i sun ziyarci hancin ta wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin ta kwace hannunta daga nashi ya rike tamau! Kokarin juyo fuskarta yake su kalli juna tana kauda kanta, a hankali yace." Beb ki juyo ki kalli maraya ki kalleni da wad'annan kyawawan idon naki ko na samu zuciyata ta daina zafin da take yi kinji ko."! A kasalance ta kalleshi tana marmar da gashin idonta hakan da tayi ya burge shi sosai ya sanya hannunsa a saman idonta yana wasa da gurin, lumshe idonta tayi tana jin wani irin shauki gami da kaunar sa na kara nunkuwa a zuciyarta jikinta ya hau bi da kallo duk da cikin hijan take bai hana bayyanuwar manya-manyan Brest dinta ba Wanda suke mutukar razana shi da bashi tsoro yau dai yayi alk'awarin sai ya gansu a fili.... Hanifa na can da ido a rufe taji ya kamo 'kungunya ya Dora hannunsa kan bom-bom dinta ya dDan dukesa kad'an, tayi saurin bude idonta tana kallonsa, girarsa guda ya daga mata yana Dan sakin murmushi Wanda ya tafi da imaninta...... Ta bishi da kallo har suka isa doguwar kujera 3sitar ya zaunar da ita cinyarsa bayan ya bude kafafunsa ta zauna sosai a jikinsa kallon juna suke yi kamar babu gobe Hanifa duk ta wani susuce sai faman motsa idonda take tana tutturo baki gaba tasan abunda sukeyi bai dace ba amma sonshi da take da kuma yanda gangar jikinta take amsar sakonshi yasa ta kasa hanashi Abunda yake mata....... Cikin wani salo ya dora hannunsa kan le'bunanta da yake mutukar so ya Dan lumshe idonsa a hankali yace." beb ina son wannan ya za'ayi uhum."!! Hannunta me dumi tasa tana kokarin cire hannunsa gefe guda tana jin wani irin Abu na zungurinta yana kuma motsi tsil-tsil!!!! Ganin tana son sauka ne yasa cikin dabara ya zura hannunsa cikin hijab din yana kokarin zare shi hannunsa ta rike tana girgiza masa kanta, shima kansa yake girgizawa cikin langwabe Kai yace." beb pls ki bari in gani ko yaya ne kinji ko."!
Kauda kanta tayi gabanta na fad'uwa, Khalid ya saki murmushi cikin zuciyarsa ya lura yarinyar ta kamu sosai hijab din ya zare ya jefar dashi kasa ido ya tsurawa k'irjina yana lumshe ido jikinsa har ya soma rawa duk da cikin rigar atamfa suke bai hanashi ganin yanda shatin niples dinta futo ba abunda ya k'ara gigita shi shi kenan! Ya rike kunguta da kyau! Yana me Dora kansa kan k'irjinta cikin dabura ya zura hannunsa yana kokarin zuge zif din rigarta kuma bai fasa gogo mata fuskarsa ba a gurin...... Idonta a lumshe take kokarin cire kansa tana kokarin sauka ya rike ta tamau! Har sai da yayi nasarar zuge mata zif din da sauri ya cire rigar yayi jifa da ita, Hanifa ta sanya hannu biyu ta rufe k'irjinta Wanda ko rabinsu bata rufe ba saboda girimansa hakan da tayi ya tayar masa da hankali yaji kamar hannuwansa ne a kai jiki na kyarma ya fuzge hannunta ya Dora nasa a kai, kan nono ya kama duka hannun NASA yana murzasu yana sakin nishi duk ya rikitata da salonsa, kuka take tana kokarin cire kansa da manna a gurin yana lashewa!! Ganin ya'ki ya daina ne yasa ta fara du kansa tana kuka take fadin"Ka Bari nace nifa banzo gurin ka don mu sa'bi Allah ba, babu kyau abunda kake min haramun ne." Sam bai san tana yi ba domin burkicewa yayo sosai ya kwantar da ita kan doguwar kujerar ya haye kanta sai lasar jikinta yake sai kace maye!
*10/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*34*
Yace." Myson ka kwantar da hankalinka yarinya ko yar waye ni zan shige maka gaba ka aureta raina ya 'baci da jin abunda ka fada min yanzu cewar yarinyar ma d'iyar talaka ce har za'a zauna ana wasu surutai a kanta yanzu don dare yayi amma insha Allah gobe da kaina zanje har gidansu yarinyar kai zauna cikin shiri zamuje tare da kai har gidan ka kwantar da hankalin ka."
Khalid yace." Allah ya kaimu dad nifa a matse nake sosai Wallahi banaso abun ya dauki dogon lokaci." Mamy ta kalleshi cikin nutsuwa tace"Myson idan mutuminan ya'ki amin cewa ka hak'ura kawai kazo gurin Nasrin yarinyar tana da hankali da nutsuwa nasan kuma duk zata dauke maka laluran ka." Khalid shiru yayi mata saboda yasan zai iya fada mata abunda ranta zai b'aci shine yasa yayi mata shuru kawai shi kuwa Alhaji Tijjani sai fada yake yi ranar Khalid Hanifa Abbu Ammi babu Wanda yayi bacci me dad'i Khalid kasa tafiya yayi part d'insa nan parlor yayi kwanciyar sa har garin Allah ya waye ya tashi ya koma part d'insa domin shiryawa kwana yayi yana mafarkin Hanifa sai da yayi wankan tsarki saboda bai yadda da kanshi ba ya futo ya kimtsa jikinsa cikin wata lafiyayyar shadda geznar irin ta maza anyi masa dinki irin na zamani dama shi ba ma'abocin sanya hula bane sumar shi ya gyara sosai ya gyara sajanshi ya kara kwanciya lif a kyakyawar fuskarshi turaran shi ya dauka ya fesa a jikinsa a take dakin ya dumame da masifaffan kamshi mai dad'i takalmi me gidan yatsa ya sanya a nutse ya futa namiji tsayyaye ingarma jarumi ta ko wane fanni so yana nema ya sanya ya zama malalaci yanzu yanayin tafiyar shi ma ta sauya komai na duniya yayi masa zafi Kwata-kwata baya son damuwa yanzu tunanin yanda zai samu ya mallaki Hanifa kawai yakeyi. Cikin rashin k'warin jiki ya isa part din iyayen sa Alhaji Tijjani da Mamy suna zaune gurin cin abunci ya shiga da sallama a bakinsa kai tsaye daining din ya nufa yaja kujera ya zauna yana ya mutsa fuska Hannu ya mik'awa dad din NASA sukayi musabaha sannan ya shagwabe fuska yana kallon Mamyn sa yace." Mamy jiya da kyar nayi bacci duk kuka barni a parlor ni kad'ai. " mamy ta bude bakinta cike da mamaki tace"Myson kana nufin a parlor ka kwana."!? Gyda kansa yayi kamar wani maraya yace." E Mamy bana so inje part dina ni kadai abun zai 'kara tsanani." Mamy tace"Wannan yarinya ko wacece bata kyauta min ba duk tana nema ta mayar min da yaro lusari myson nifa kwata-kwata jikina na baki kamar babu alkairi a tarayyar ku da ita shiyasa nakeyi maka maganar Nasrin itace dai-dai da kai."
'Bata fuskarsa yayi yace."Mamy jiya ma fa haka kikayi min nayi miki shiru Mamy kika 'karayi min maganar 'yar lukutar yarinyar nan kuka zanyi miki yasin." Cikin shagwaba yake maganar mamy da Alhji Tijjani suka saka dariya yace." Allah dad ita Mamy ta kasa ganewa har yanzu." Mamy na dariya tace." Ta ina zan gane yarinya na nema ta mai dakai sususu zanso ingata da idona." Murmushi yayi yace." Zan kawo miki ita gida insha Allah.
Ta'be bakinta tayi tace"To Allah ya kaimu lokacin ina fatan kar a samu wata matsala idan kunje gidan nasu. " Mamy babu matsalar da za'a samu insha Allah zan amunce mamy nifa yarinyar tana sona mahaifinta ne matsala kuma dama mun ta'ba samun sa'bani dashi shekaru biyar da suka wuce." Mamy tace"Ai kaji ko lokacin kana kan k'uruciya duk da ban San abunda ya hadaku ba nasan Kaine baka da gaskiya Yanzu tunda kana son abun shi sai ka durkusa masa." Dad ya kalleta a yatsune yace." Yarona ne zaije gurin talaka yana durkusa masa lallai baki da hankali indai ina raye yarona sai ya auri yarinyar komai kika ga anyi shi da kai to kana da kudi." Girgiza kai Mamy tayi tace"Allah ya bada nasara ai babu abunda nace me zafi anan ina fatan alkairi." Dad din ya tashi daga gurin yana mita hade da fadin "Indai kudi suna magani a duniya to zamu siyi komai su yanke kud'in sa dakin yar tasu zan biya ko nawane."! Mamy ta bishi da kallo yana kokarin hawa sama sai masifa take yi, Sam bata kaunar d'abi'ar mijinta na girman kai gami da homa mutum ne shi mai nuna shi wanine a duniya gashi bashi da kyauta ko kadan duk uban dukiyarsa baya sadaka baya bada zakka baya hubusi duk abunda Allah yace da me dukiya yayi Sam Alhji Tijjani bayayi Cikin ikon Allah kullum dukiyar tasa kara habaka takeyi Allah kenan.
_Ni kuma cewa nayi akwai ranar da Allah zai futar da zakkar shi a cikin dukiyar tasa, ubangji ya zuba masa idone kawai yana kallonsa_
Cikin wata lafiyayyar shadda wagambari Riga da malin-malin anyi masa wani irin aiki gaban babbar rigar da bayanta kana ganin shi kasan Alhji ne kudi kuma sun zauna ko ta ina ya murza hula damga 'yar asali ya futo yana baza 'kamshin turaransa Khalid ya mike tare da bin bayansa Mamy kan iya kacinta kofar parlor sai da taga sun shiga mota, sannan ta koma ciki tana addu'ar Allah yasa akwai alkairi a cikin wannan al'amarin
*GIDAN ABBU*
Bayan sunyi Karin kumallo kamar yanda suka saba Hanifa ta mi'ke zata shige daki dama babu makaranta tunda Alhamis ce Abbu yace." Hanifa dawo ki zauna ina so nayi magana dake." Ji tayi gabanta ya fad'i ta juyo a hankali ta dawo ta zauna inda ta tashi. Abbu yayi gyaran murya a nutse yace." Hanifa tunda Allah yasa na haife ki nake da buri a kanki Ku biyu kacal Allah ya mallaka min ina alfahari da haka kuma kullum cikin godewa ubangji nake bisa baiwar da yayi min Hanifa INA so ki rike mutumcin ki Wanda Allah yayi miki a matsayin ki na ya mace mai daraja ki kama kanki daga nan har zuwa lokacin da zan auran dake ina fatan kin fahimci kudurina a kanki da Yayanki Nasiru ki? Ina so in hadaku aure dashi idan Allah ya nufa, jiya da daddare wani yaro yazo min da magana a kanki yana cewar yana sonki da aure to tun wuri na sallameshi na fada masa cewar nayi miki miji yayi hakuri, nasan yaron sosai yana da rawar kai ko da wasa ban amunce ki shiga huruminsa ba dole watarana zaku had'u a hanya babu ke babu shi idan yayi miki wata magana kice babanki yayi miki miji kinji ko."
Hanifa da tunda Abbu yake maganar take jin wani irin a jikinta tace."To Abbu insha Allah zanyi maka biyyaya kamar yanda kake so." Muryarta na rawa ta 'karashe maganar Ammi dai kallonta takeyi tana tausaya mata tunda ba tun yau ba tasan bata son Nasiru tunda tana fada da bakinta..... Yace." jeki dauko a'kurani muyi karatu." Mik'ewa tayi tana jin wani irin jiri na kwasarta dakin Ammi ta shiga ta dauko alk'urani ta futo kenan suka ji sallama ana sauke kaya a cikin gidan, Abbu ya mike a nutse yana amsa sallamar ya futa kawai sai yaga ana shigowa da buhuhunan abunci da k'aton k'aton din taliya da macaroni gami da sauran kayan masarufi.! Cike da mamaki! Abbu yace." Wannan kayan fa daga ina ? Ku daina saukewa ba gidan nan bane." Wani matashi yace." Ya shaik kayi shiru kawai kwananan zaka daina sanya yadikan toyobo domin 'yar ka ta jawo maka arziki har gida hahahahaha dama wannan yarinyar taka dakake 'boyewa Ashe kasan kadara ce shiyasa kake kaf-kaf da ita. "! Suna shakiyanci suna sauke kaya har sai da tsakar gidan ya kusa ciki sannan daya daga cikinsu yace." Ya shaik *Alhji Tijjani Canji* yana jiran ka a waje."! Yana gama maganar shi ya futa daga gidan da sauri!
Kafin Abbu yace wani Abu Nasir da Hafiz sun shigo cikin gidan suka dinga bin kayan abincin dake jibge da kallo Nasir jikinsa yayi sanyi domin ya Riga ya fahimci komai tunda yaga Alhaji Tijjani da yaron sa a tsaye a waje, Hafiz yace." Abbu wannan kayan fa? Kuma me ya kawo wancan mutumin kofar gidanan."? Daga masa hannu Yayi kawai ba tare da yace komai ba ya futa daga gidan, shi kuwa Nasir jikinsa a sanyaye ya bude dakinsu ya shiga zubewa yayi cikin kujera yana jin wani irin zafi a zuciyarsa addu'a yakeyi Allah yasa kada kudi su rinjayi zuciyar Abbu.
Alhaji Tijjani sai bin unguwar da wani irin kallo yake yana ya mutsa fuskarsa idan banda dalili babu abunda zaisa ya shigo cikin unguwar domin duk mutanan cikinta ba tsaransa bane don dai babu yadda za'ayi ya hana danshi abunda yake so shiyasa kawai yake biye masa amma shi a ra'ayinsa yafi so Khalid ya auri 'yar gidan shuwagabanin kasa amma ta 'bige da 'yar talaka.
Abbu ya futo cikin kamala ya mik'a masa hannu sukayi musabaha da Juna ya mik'awa Khalid ma suka gaisa, Alhaji Tijjani na ya mutsa fuska yace." Ina fatan Arrama yaga sa'kona."? Abbu yace." Wane irin sa'ko Alhaji."? Gyaran murya Alhaji Tijjani yayi yace."Wannan iyayen kayan abunci da masarufi da na jibge maka a cikin gidan ka sun isa ka gane komai." Abbu yayi murmushi tare da gyara tsayuwarsa yace." Maddalah nagode Alhji Allah y kara suttura da rufin asiri ni bazan ce maka ba mubakaci bane Hak'ika ina bukata to amma kullum Allah ne da ita Ubangiji baya hanani abunda zan kawo gida mu sanya a bakin mu, wannan kayan abunci da kasa aka jibge min sunyi min yawa Abunda yafi kamata kayi shine ka kaisu gidajan marayu sannan ka nemi mabukata sosai sai ka sadakar musu ni Allah yayi mun rufin asiri nafi k'arfin cikina."
Wani irin murmushi Alhji Tijjani yayi yace." Arrama wannan kauli da ba'adin duk kai kasan su ni dai kayan abunci kai nabawa saboda ina Neman biyan bukata a gurinka kana iya zuwa kaje ka SADAUKAR dasu babu damuwa, babban abunda ya kawo ni gurina shine yarona." Yafad'a yana nuna Khalid dake tsaye kanshi a kasa ya zura hannunsa cikin aljuhu Dad ya cigaba da cewa"Yarona yaga yarinyar ka yana sonta da aure jiya ya fadamin yazo gurin ka kan maganar kace wai kayi wa 'yarka miji Hak'ika banji dadin wannan maganar ba Arrama kai abun alfarinka ne yarka ta auri yarona kuma ta bangaranka abun alfahari ka ne ka hada zuria dani, to shine nace ni Bari in taso 'kafa da 'kafa in same ka kan maganar ina so idan da hali maganar da ka fada kan yarka ka warware ta inaso ka mallakawa yarona 'yarka ko nawa kake bukata ni zan baka kafadi nawane sadakin yarka tunda daga kan million daya zuwa millions goma zamu biya."!!
Maganganun Alhaji Tijjani sunyi mutukar yiwa Abbu zafi a zuciyarsa shi mutum ne mai kawaici da danne b'acin rai akan Dade anayi masa Abu a rayuwa yana kauda kansa amma yau yanda yake jin ciwo game da maganar banza da Alhaji Tijjani yazo masa da ita yasa ya bude bakinsa ya fara magana a kausashe!
"Alhaji duk naji maganar ka, kamar yanda na
masa cewar nayiwa Hanifa miji hakane babu fashi kudi ko mulki ko sarauta basu isa su kani na kwance alk'awarin da na dauka ba, bana bukatar kudi nafi bukatar kwamciyar hankali yarinya ta Hanifa ba siyar da ita zanyi ba idan ma zan siyar da ita kai baka da kud'in da zaka iya siyan ta, naira dubu biyar kacal nake bu'kata a matsayin sadakin ta kuma bada b'angaran ku ba, saboda haka bana bukatar komai naka Alhaji wannan kayan abunci dake zube min bana bukatar su ni Riga nayiwa Hanifa miji Yayi hakuri ya nemi wata yarinyar."
A hasale! Alhji yace." Karya kake kace baka bukatar wani Abu a gurina dube ka fa? Dubi gidan ka dubi sutturar dake jikinka."? Yafad'a yana ta'ba yadin toyobo din da yake jikin Abbu cikin izgili ya cigaba da cewa "Dama Ku 'yan Izalah baku da mutumci bakwa kaunar duk wani mai arziki a cikin duniyar nan daga zarar anyi magana sai ku fara fadin" Allah da Annabi har ni zaka fadawa magana idan banda yarona ya nace kan yarka mai gadin gidana baka isa na dauke k....."Dad."! Khalid ya katse mahaifin nasa daga hayaniyar da yake. Abbu kuwa shuru yayi yana mamakin k'arfin hali irin na mutumin yazo kofar gidan shi ya dinga kokarin wulakanta shi gashi har an fara taruwa a gurin....... Muryarsa na d'an rawa yace." Dad nayi nufin raya sunna da 'yarshi yace bai yarda ba a rayuwata ban ta'ba tunanin zan zo gurin wannan mutumin Neman alfarma amma saboda yanda Allah ya jarrabe ni da tsananin kaunar yarshi Nazo na kaskantar da kaina gurin shi duk da haka ya'ki ya karb'i maganar da muhimanci yarinyar ka ita ta koya min yanda zan sota.' Yafad'a yana kallon abbu ya cigaba da cewa"Ya shaik Yarka Hanifa ni take so duk wani Wanda zaka aurata mata a yanzu zata zauna dashi ne kawai domin tayi maka biyayya ina me baka sha'awa ka aura min ita domin samun nutsuwar ka da kwamciyar hankalin yarka. "! Alhaji Tijjani ya buge babbar rigarsa ya bi bayan Khalid da tunda ya kare maganar shi ya bar gurin cikin tsananin b'acin rai da damuwa.!
Jama'ar da suka taru a gurin suka yi wa Abbu caaaaaa! Aka masu zagin sa nayi masu fadin yw cuci kansa nayi wasu tsantsar wautarsa suke gani cewar arziki yazo masa yana guduwa dayawa daga cikinsu suna fadin inama yarsu ce da tuni sun bada kai bori ya hau, hayaniyar da tayi yawa yace yasa Nasir da Hafiz suka futo daga cikin gida suka shigar da Abbu suna tambayar sa abunda ya faru."
*1/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*43*
Sai da ta tabbatar sun futa daga cikin gidan sannan ta mike zaune tana gyara hijab dinta suka hada ido dashi ya mirror girarsa guda ya daga mata da murmushi a fuskarsa yace." Matsoraciya kawai." Turo baki tayi tana dan hararasa yana kallonta ta mirror din yace." Me nayi miki kike hararata."!? Shiru tayi masa tana kauda kanta, ya saki yar dariya tare da fadin"Idan baki fadamin ba zan tsayar da motar ne in hukunta ki yanzu." A hankali tace" me kake so nace maka to."Ajiyar zuciya ya sauke yana. Lumshe idonsa yana bala'in son muryarta kamar yanda take son tashi...... Wani k'aton supar market ya shiga da motar ta kalleshi a tsorace tace"Me zamu yi anan gurin kum."!? A hankali yace." Ki futo mu shiga ki duba abunda kike so." Kafadarta ta make tana fadin" babu wani Abu da nake so ni dai don Allah mu wuce gida." Bude motar yayi yana fadin"Baki isa ba tunda muka shigo to sai kinfuto Wallahi " kallonsa take yans rufe mota ya runkufo da kansa tare da fadin"Ki futo Yanzu ko in ciccibe ki." Jikinta babu kwari ta futo a hankali tana kalle- kalle a gurin, yayi gaba tana binshi a baya hadaddun yan mata da samari ne gurin suna duba kaya yana shigowa kallo ya koma kansa 'yan mata sukayi caaaa a kansa Wai don Allah ya bari suyi hoto babu yanda ya iya haka ya tsaya suna ta salpie tare Hanifa na gefe guda tana kallonsu zuciyarta sai zafi take mata ganin wani irin yahudanci da yake sai rungume yan matan yake da sunan hoto su kuma sai gantsaro k'irji suke suna gogo masa a jiki sai taga babu wani damuwa da yayi murmushi yake yana biye musu kishi kamar ya kashe ta haka sukayi tayi samarin ma suka dunga dakaur shi a hoto da wayoyinsu gajiya tayi ta kama hanya zata futa, yayi saurin futowa daga tsakiyar su hannunta ya kamo suka koma ciki, duka suka bisu da kallo domin Sam basu tsammanin tare yake da yarinyar ba tunda shi kadai ya shigo gurin sai dai yana shigowa itama ta shigo mamaki suke shi kuma me ya hadashi da Wannan mai hijab din yana wayayyen mutum kuma sananne a duniya.
Hannunta na cikin nashi suke zaga cikin kantin ta kasa daukar komai sai shine yake jidar mata kaya musamman rurarika da kayan kwalliya na mata sosai yake hada mata kaya ta kalleshi a fakaice tana mamakin yanda ya cika kwando da kaya ita ba mahaukaci ya bace da zata shiga da kayan nan cikin gidansu to tace dasu Ammi waye ya siya mata? Ita kadai take Wannan zantukan cikin zuciyarta har suka karasa gurin biyan kudi aka juye kayan cikin manya-manyan ledoji uku Khalid ya biya kud'in suka futa daga gurin.Hanifa kan ganin gari ya soma duhu yasa hankalinta ya tashi ta fara tunanin abunda zata fada a gida suna shiga mota ya lura da yanda take marmar da ido duk damuwa a tare da ita, Abu biyu ne ya hade mata kishi da damuwa domin idan ta tuno da yanda ya dinga rungumar yan mata da sunan hoto sai taji ta tsane shi ko kallon sa bata so tayi, yana driving yace." Beb naga duk kin wani koma shiru meye wai."! A marairaice tace"Gida nake Jin tsoro Wallahi." Tab'e bakinsa yayi yace." Budurwa kamar ki a dinga sanya miki ido ya kamata fa ki kwaci yan cinki domin ni bantaba ganin inda akayi wannan takurar ba sai a gurin Shaik kullum cikin takura da tsanani." Ya k'arashe maganar yana Jan tsaki k'asa-k'asa, taji ciwon tsakin da yayi dannewa tayi tace"Laifin kane duka ai daga yau bazan Kara zuwa inda kake ba." Murmushi yayi yana shafa sumar sa yace." Ranar da zakizo Ba zakiyi shawara da kowa ba 'yan mata." Hararsa tayi ta dauke kanta tana kallo ya karya kwana ya shiga da motar layinsu yara da matasa suka tasu yuuuuuuu! Suna bin motar da gudu kasamcewar sun San mai ita, a lokacin ne kuma gabanta ya tsananta fad'uwa tana fargabar ta futo daga cikin motar a idanun jama'a......Haka dai tayi shahada ta futo tana sinke kanta kamar munafuka ta kasa dago kanta kokarin wuce take ya rik'o hannunta ta baya dago kanta tayi tana kallonsa shima yana kallonta a lokacin ne kuma Abbu da Nasir Hafiz suka doso gurin dukanin su zasu nufi massalaci idanunsu ya sauka akan Hanifa dake daf da Khalid hannunwan su a hade suna gashi tsakaninsu babu wata tazarar kirki su Kansu suna jin bugun numfashin junanansu
Khalid ya saki wani killer smile lokacin da suka hada ido da Abbu ya dauke kansa kamar bai ganshi ba cigaba yayi da yi mata magana kasa kasa ita kuma sai kallonsa take tana marairaice fuska kwata-kwata bata lura dasu Abbu ba domin baya ta basu sai da suka wuce ne taga giftawarsu gabanta yayi wata irin mummunar fad'uwa da hannu ta nuna masa su. Daga kafad'a yayi alamun bai damu ba yana wani tabe baki.... Kamar zata kifa kasa haka ta bar gurin gabanta na wani irin bugawa kallo ya bita dashi hakanan jama'ar da suke gurin suka dunga kallonta suna mamakin meye alakarta da Mashahuri da har ta kaita shiga motsarsa. Khalid kuwa motar ya shiga yana jin wani irin farin ciki a zuciyarsa Yanzu duk wata damuwa da take damunsa ya samu saukinta saboda yasan ya dasawa yarinyar tambarin da bazata taba mañcewa dashi ba kuma ya lura sonsa yayi mugun k'arfi a cikin zuciyarta bayan Wannan kuma yaji dad'i da yaga Ya Shaik kuma shima ya ganshi ko babu komai shima ya dasa masa damuwa da b'acin rai kamar yanda ya dasa masa a zuciyarsa.
Wayarsa ya dauka ya kira Abbakar..... Sai murmushi yake saki yana shafa kanshi idan ya tuno abunda ya faru dashi da ita sai ya kara jin wata sha'awarta na kara nunkuwa a cikin zuciyarsa,,, Abbakar na zuwa ya ganshi Cikin walwala da farin ciki ya bashi hannu suka tafa yana fadin"Guy da'alama dai ta waru naga sai nishadi kake. " da murmushi a fuskarsa yace." Abbakar yau na kara tabbatar da cewar yarinyar nan tana sona wallahi kawai don karan kaina na k'yaleta babban abunda yayi min dad'i a zuciyata shine yanda Shaik ya gammu tare da ita nasan dole zan saka zuciyarsa a damuwa." Abbakar ya kyalkyale da dariya yana bashi hannu manya-manyan ledojin dake gabansa ya mik'awa Abbakar din yace." Gashi a samu yaro ya kai mata yanzu_yanzu."Abbakar yace." Insha Allah Yanzu zan sanya Asalamiyya ta kaimata." Sallama sukayi da juna Khalid yaja motar ya bar unguwar........ Abbakar kuwa Asalamiyya yaje ya azalzala dole ta bar abunda takeyi ta tafi gidansu Hanifa babarsu sai kallon Abbakar din take tana so ta tambayeahi komeye domin sai take zargin ko shine yayi mata siyayya su sunanan dede da man shafawa baya sai musu ganin Abbakar din ya futa yasa tayi shiru amma taci alwashin sai ta tambaye shi idan ya kara shigowa.
Tsayuwa tayi a soron gidan gabanta na fad'uwa takasa shiga ciki tans tuno tun lokacin da ta futa daga gidan k'arfe daya saura na rana Yanzu gashi ana kokarin kiran sallahar magariba motsin ammi take ji a kicin tana aiki kawai tayo shahada ta shiga gidan suka hada ido da Ammi da ta futo daga kicin fuskarta kawai ta kalla ta gane tana cikin damuwa kasa tayi da idonta Ammi ta shige ba tare da tace mata komai ba, tsaye tayi a gurin cikin damuwa ita kuma Ammi na sabgar gabanta 'kala bata mata ba har ta Dora alwala tana kokarin shiga ciki Asalamiyya tayi sallama . Ammi ta dakata tana amsa sallamar Asalamiyya ta karaso hannunta niki-niki da ledoji Hanifa tunda taga ledojin taji tsayuwa na Neman gagarata sai ta tsuguna a gurin tana jin wata irin fargaba da damuwa tana jin suka gaisa Asalamiyya tace"Gashi inji ya Abbakar wai na Hanifa ne." Ammi tayi shiru tana kallon ledojin daga bisani tace"To maddalah Asalamiyya a jesu anan gurin kinji ko." Asalamiyya tayi yanda akace mata tayi mata sallama Ammi tace "ki gashe min Ummanki." Tace "Zataji Ammi." Sai da tazo futa ne ta tsaya kan Hanifa tana yi mata magana taga taki dago kai tw kalleta kawai sai ta wuce abunta tana mamakin meye dalili.
Ammi ta shige ciki dadduma ta shimfid'a ta tada sallah kana ganinta kasan tans cikin damuwa .
Jikinta babu kwari ta mike a hankali taje ta dauki buta band'aki ta shiga ta kama ruwa ta futo ta d'aura alwala a hankali ta shiga can kuryan dakin ta shige kamar yanda ta saba, kayan jikinta ta cire da sauri ta zura doguwar Riga da babban hijabi ta tada sallah.
Abbu Nasir Hafiz dukaninsu Cikin damuwa da takaici suka shigo gida sai sukayi karo da abun mamaki ledojin da suka gani ya basu mamaki sosai cikin rumfar suka shiga Hanifa naji muryar Abbu gabanta ya hau fad'uwa amma duk da haka dai tayi alk'awarin fada masa abunda yake Cikin zuciyarta domin tana ji tana gani bazata yarda da auran Nasiru ba alhalin ga Wanda take so, Ammi ya kalla dake share hawaye tana addu'a sai bayan ta shafa addu'ar ne yace." Ta shigo ko." Ammi tace"Tana cikin daki Yanzu." Gyada kansa yayi ya cigaba da cewa"Ba sai an tamnayeta komai ba mun gani Yanzu daga gurin Wanda take Halima bantaba tsammanin yarinyar zata yi min haka ba kiri-kiri tana nema ta zubar min da mutumuci ta maida ni k'aramin mutum a gurin jama'a." Yanda ya fad'i maganar zaka San yana cikin damuwa da b'acin rai.Nasir da Hafiz suna tsaye duk ransu babu dad'i Nasir ji yake kamar yaje gurin Khalid din ayi wacce za'ayi domin wata irin tsana yake masa Mara misali...... A zuciyacr Hafiz yace." Abbu mutukar wannan yarinya ta sanya hawayen ka suka zuba to Wallahi sai na karyata sai nayi mata dukan mutuwa a gidanan domin ba kai kadai take kokarin zubarwa da mutumci ba har damu kanku yaron da duniya ta shaida bashi da d'a'a da d'abiu masu kyau saboda tsabar ita din jakace cikin jakuna take binsa suna yawo a mota Abbu ka k'yaleni na karya ta na zubar da shegiya kowa ma ya huta....... Rai abace Abbu yace." Hafiz aiki da lura mana."! Shiru Hafiz yayi yana sauke ajiyar zuciya Ya cigaba da cewa"Kar in kara ji ka kirata da wannana kalmar ta jaka kaji ko."!? Hafiz yayi kasa da kansa cikin damuwa da b'acin tai...... Ammi tace"Abbu nifa wannan yarinya na soma ma zarginta domin ba yau na fara jin k'amshin turare a jikinta na tabbata suk Dade suna tare da yaronan wallahi zuciyata ta shiga rud'u a kanta." Abbu yayi shiru na minti biyu kafin ya bude murya ya kira Hanifa da duk abunda akeyi tana ji tayi shiru... Amsawa tayi da sanyin murya ta futo duk suka bita da kallo abbu ya nuna mata kusa dashi ta zauna Hafiz kuwa ji yake kamar yaje yayi ta dukanta ko ya samu sassauci ita kuwa Ammi Sam taki kallon inda take.
Abbu ya kalleta cikin nutsuwa yace." Hanifa wannan abunda kikayi shine dai-dai."!? Shiru tayi tana zumb'ura baki yace." Kiyiwa Allah da manzon sa ki dawo cikin nutuwar ki ni Mahaifin ki ne bazan taba yi miki abunda zai cuce ki ba kiyi min biyayya kamar yanda na umarce ki kika amunce min zakiyi idan kikayi min biyayya zaki samu riba a duniya da lahira Hanifa tarayyarki da wannan yaron bana sonta domin ni banyarda da d'abi'unsa b..... Kuka ta fashe musu dashi tana fadin"Abbu ka daina fadin haka wallahi yana da d'abi masu kyau don dai kai dashi bakwai jituwa ne amma Khalid yana da hankali kuma yana mutukar sona da gaskiya."! Duk suka yi shiru suna mamakin maganganun ta, Nasir yaji kamar ya cakawa kansa wuka ya huta da wannan bakin ciki..... Abbu ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin"Duk abunda kika fada bakiyi karya ba Hak'ika ko wane Dan Adam yana da nasa baiwar da Allah yayi masa amma kuma ko a gurin Allah wani yafi wani hakanan kuma cikin jinsin mutane dole a samu Wanda yafi nagarta har kullum ni burina a duniya in samar miki farin ciki Wanda ko bayan raina ne zakiyi farin ciki da abunda nayi miki."! Cikin kuka tace"A'a Abbu babban farin cikina a yanzu shine kawai ka yarda na auri Khalid alk'awarin da kayiwa Ya Nasir ka rusa shi ni dama fa bana sonsa kawai dai nayi kokarin nayi maka biyayya ne kuma zuciyata ta kasa yin juriyar hak....... Bata karasa ba Ammi ta mike tsaye a kanta ta dinga dukanta da hannunwan ta cikin b'acin rai murya na rawa take fadin"Hanifa idan kikayi mana haka Kin cuce mu kuma kin zama yarinya mara tarbiyya Allah sai ya saka man.......abbu ya rike hannunta yana kokarin zaunar da ita ransa duk a bace yake fadin"Halima mutukar na kara ganin hannun ki ya taba jikin yarinyar nan da sunan duka ranki sai ya b'aci. "!! Cike da b'acin rai yayi maganar Ammi ta shige kuryan daki tare da zama gefen gado tana share hawayen bakin ciki. Shi kuwa Abbu Hanifa yake kallo dake ta faman gursheken kuka.!
*12/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI!_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*37*
Jikinsa daure da towol me Dan girma ya futo hada ido suka yi da Mamy din sai yayi sauri kauda kansa yana nufi dressing mirror dinshi Mamy tace"Myson kai da kake zazzab'i ina kai ina Wanka zazzab'in sai ya kara k'arfi naga kuma sai wani kauda kanka kake kamar wani Mara Gaskiya."
A hankali yake mutsika mai a jikinsa yace." Mamy nace miki fa ba wani sosai nake jin zazzab'in ba kawai dai don kince dole muje hospital ne." Mik'ewa tayi tana kokarin futa tace"ni dai ka sanya kayanka ka futo ina jiran ka." Shikkenan Mamyna yanzu zan futo. " abunda ya fada kenan ya cigaba da abunda yake yi, Mamy ta futa tana wasiwasi cikin zuciyarta yanzu ta soma fahimtar abunda yake damun Dan nata, Khalid na sanya kayansa yana tunanin abunda zasuji daga gurin Abbu tunda yace a saurare shi daga yau zuwa gobe,turaranshi me masifar kamshi ya fesa ya dauki wayarshi ya futa daga d'akin.
Mamy na zaune a parlor ta shirya tsaf! Don har ta sanya hijab ya shigo Cikin sanyi jiki kallo ta bishi dashi cike da kulawa tace"Myson idan na kira wannan yarinyar shaid'aniya har sanja fuska kake yi nifa na gane duk itace sanadiyar fad'awar ka cikin wannan halin tun ranar da naga kana kallon pictures dinta Shikkenan ka susuce kazama komai naka salau-salau Wannan Yarinyar ko shad'ain ma dole yaji tsoront..... Ka tsaye ta Yayi ta hanyar fadin "Mamy stop."! Cikin yanayin damuwa ya fad'i maganar yana kokarin zama kujerar cin abinci. Ya mutsa fuskarsa ya fara yi yace." Mamy wannan yarinyar da kike magana a kanta ba itace zata sanya ni shiga damuwa ba kawai dai daga Allah ne kuma Mamy kamar kinayi mata daukar Mara tarbiya Mamy itace f.... Kafin ya karasa itama ta katse shi ta hanyar fadin"Itace yarinyar da kake so ko."!? 'Daga kansa yayi kamar wani yaro Karami, jinjina kai tayi tace"lallai biri yayi kama da mutum wato myson ka rasa wa zaka so sai wannan Mara kunyar yarinyar me nuna tsaraicinta a waje shin kasan iya adadin maza nawa ne suka ga jikinta shine zakaje ka kwaso min kara da kiyashi myson ga yarinyar kirki nace maka ka aura kaki daukowa kanka masifa."!
Cikin damuwa takw maganar.
Khalid yaji wani irin daci-daci a bakinsa jikinsa ya fara daukar zafi zazzab'i na so ya sake hawansa Mamy tayiwa Hanifa mummunar fahimta ya za'ayi ya ganar da ita cewar ba mara tarbiyya bace. Yace." Mamy mu bar maganar don Allah kin San bana son damuwa ko? Kaina zai fara ciwo Yanzu. "! A hasale tace"Kanka ya Dade baiyi ciwo ba Myson ai me daure maka gindin ya futa dole inyi magana nace maka idan kasan wannan yarinyar ce wacce ake ta d'auki babu dad'i akanta to tun wuri ka janye maganar auranta kazo ka nemi Nasrin yarinyar arziki kuma cikkakiyar macace."!
Shiru yayi yana kurbar ruwan tea d'insa yasan da Dad dinshi na gurin Mamy baza tayi masa wannan Shouting din ba tuni zai hana shi kuma Allahn da ya hallice Sam baya kaunar hayaniya don dai babu yanda zaiyi da ita ne.
Hafiza ce ta shigo parlor da sallama a bakinta, da gudu yaron ta Mus'ab ya nufi gurin su Mamy yana fadin " ancle Oyoyo."! Khalid ya d'ago kanshi da sauri yake kokarin dakatar da yaron ganin Chocolate a hannunsa duk ya 'b'aci yasa ya fara ya mutse fuska Mus'ab kuwa kokarin tab'a jikinsa yake yana murna wata irin tsawa ya buga masa wacce tasa yaron ya Ruga gurin Mamy da gudu ya fara kuka
Hafiza ta 'bata fuskarta tana Harar sa tace"Wallahi kai mugun d'an wulakanci ne yaron nan tun a mota yake fad'in ancle Khalid Oyoyo shine saboda tsabar wulakanci zaka buga masa tsawa saboda baka San zafin haihuwa ba."! Hararata yayi kawai bai ce komai ya cigaba da kurbar tea d'in sa yana jin haushin zagin da Mamy tayi wa Yarinyar Shaik.
Mamy tace"Ke kuma daga ina da sassafe haka."!? Zama tayi daya daga cikin kujerun gurin tace"Mamy naje hospital ne na kai Mus'ab jiya ya ha namu bacci wai Ashe kunnen sa ne yake ciwo." Mamy ta jawo Mus'ab din tana dubawa tace"babu shakka kuwa gashinan har ya soma ruwa." Hafiza tace"Wallahi jiya yasha kuka har ya bani tausayi. " Mamy tace"Ciwon kunne ai masifa ne wallahi sai ki kiyaye bashi magani kan 'ka'ida kuma ki dinga sanya masa hula idan iska ta kad'a." Tace"Insha Allah Mamy Dady ya futa ne." ? Ya futa tun sassafe yau yana da ba'ki ne." Cikin shagwaba tace"wallahi wasu kudi nake so masu kauri a gurinsa."
Wani irin kallo Khalid ya watsa mata yana ta'be bakinsa, 'bata fuska tayi tace"Dan rainin hankali kawai baka gaishe ni ba ina matsayin yayar ka kana tab'e min baki." Bata fuskarsa yayi kicin-kicin da ita ya tsani suce sun girme shi a ganinsa tunda shine namiji a cikinsu dole su bashi girma yace." Wannan kud'in masu kauri da kike magana akansu to ba samu zakiyi ba indai nine zan futar dasu zaki daskare anan gurin." Mamy ta kalleshi tare da fadin"Kudinka ne da zaka fad'i haka? Kuma ai ba Kai ta tambaya ba ko." ? Shiru yayi kawai yana latsa wayarsa
Haushi ya turnuke Hafiza Tace " Wallahi komai dare ina gidanan idan ta kama ma in kwana sai na kwana dady ya dawo ya bani kudi domin ba kai kadai ya Haifa da zaka dinga gwadawa mutane iko."!
Ganin yanda take masifa ne ya bashi dariya ya gimtse fuskarsa tare da fadin"Ki Bini a hankali kawai ki samu idan kuma ki kece hayaniya zakayi Wallahi baza a bayar ba." Shiru tayi masa tana hada tea domin haka ta futo daga gidanta bata karya ba.
Mik'ewa yake kokarin yi Mamy tace"Ina zakaje ne."!? Tsayuwa yayi ba tare da yace." Komai ba Mik'ewa tayi tana kallon Hafiza dake bawa yaronta soyayyan kwai tace." Zamuje asibiti mu dawo yanzu."
"Mamy waye babu lafiya kuma."!? Mamy tace" Gashinan a gabanki." Yar dariya tayi tace"Mamy godai-godai dashi zaki kaishi asibiti bayan yanzu ya gama rashin mutunci Wallahi ki kyaleshi yayi tafiyar sa shi kadai kar bawa kanki wahala."
Mamy tace "Gwara dai na kaishi da kaina a duba shi jiya kwana yayi da zazzab'i wata shegiyar yarinya ce ta sanyo shi a gaba kullum cikin damuwa da tunani haka ta koma."
Hafiza tasa ihu ! Tana nuna Khalid da hannunta Wanda yayi wani irin shan kunu shifa Mamy ta takura masa wallahi kamar shi zata ta kai asibiti kawai dai yanayi mata ladabi ne." Hafiza ta cigaba da dariya tana fad'in"Wannan yarinyar yar albarka ce wallahi gwara da ta sanya ka a gaba oh! Ni Hafiza amma Wannan yarinyar ta burge ni wallahi da ta samo lagonka hahahahaha."! Ta k'arashe maganar tana dariya.
Kamar ya gaura mata mari haka yake ji ba tare da yace komai ba ya fuce daga parlor yana hira hanci shifa yanzu abunda ya dame shi anan shine yaji daga gurin Abbu gashi dady ya futa Wanda a gurinsa yake sa ran jin maganar , wayarsa ya dauko yana Neman wayar dady nasa akace ma sa line is busy wai ana amfani da ita hak'ura yayi ya bude mota ya zauna dravar dake Jan Mamy yaga ta futo da sauri yaje ya bude mata motar ta shiga sannan ya shiga motar suka futa daga gidan.
Wani pravite hospital suka nufa Mamy sai lallabashi takeyi a cikin mota tana bashi shawarar cewar ya rabu da Hanifa domin ba yarinyar arziki bace kuma ita sam yarinyar bata kwanta mata ba ya kwantar da hankalinsa ya duba wata Yarinyar idan ma baya son Nasrin din to ya rabu da Hanifar shine yafi alkairi a gareshi.
Lokaci da Mamy take masa wannan maganar ji yayi zuciyarsa tana masa wani irin zafi shifa yanzu duk Wanda zai ce masa ya rabu da yarinyar shaik yana ganin kamar makiyin sa ne idan banda Mamy sa ce da babu abunda zai hana bai fada mata wacce zatayi mata zafi ba, Sam baya kaunar b'acin ranta shiyasa ma da take masa maganar yayi shiru da bakinsa a lokacin kuma zazzab'in ya kara rufe shi ya dinga jin wani irin sanyi tsigar jikinsa na Mik'ewa cikin wannan halin suka isa asibitin. Dake jarumin namiji ne ko alama Mamy ta ba gani ba na cewar yana jin jiki shi dai shi yasan abunda yake ji a jikinsa.
Koda Dr ya ga yanayin sa nan ya fahimci zazzab'i me zafi ne yake damunshi Wanda dole ma sai ya kwanta anyi masa Karin ruwa saboda yanayin k'warin jikinsa nan Mamy da taji maganar Karin ruwa ta kara tayar da hankalinta Dr tace "ki kwantar da hankalin ki ba wata matsala bace kawai zan kara masa ruwa ne domin ya samu k'arfi a jikinsa."
Mamy futa tayi tana kiran wayar mijinta a hankalinta a tashe Kwata-kwata basa kaunar Abunda zai taba lafiya Khalid din idan bashi da lafiya sun shiga damuwa kenan tasan Yanzu Mijin NATA idan yaji duk abunda yakeyi zai aje ne ya dawo gida. Ko da ta kira wayar itama akace mata line is busy dama kuma ya fada mata yau yana da baki sosai kuma akwai aiki a kasuwa haka ta hak'ura ta dawo jikin dakin da Khalid din yake kwance.lokacin har Dr ya futa bayan ya d'aura masa ruwa, Khalid ya kurawa fuskar wayarsa ido Mamy ta shigo saurin wayance wa yayi ya kashe wayar ya aje yana lumshe idonsa lokacin pictures din Hanifa yake kallo.
Zama tayi kusa dashi tana kallon fuskarsa a nutse tace"Myson don Allah ka kwantar da hankalin ka kaji ko."! Bude idonsa yayi a hankali yace." Mamy ki daina tayar da hankali nida bani da wata damuwa a halin yanzu sai guda daya kuma ina so kema ki fuskance idan na samu biyan bukata ta Shikkenan amma nutsuwa da kwamciyar hankali na duk ya tattara ne a gurin yarinyar Shaik ita kadai ce muradi na a halin yanzu."
Girman da maganar tayi mata ne yasa kawai tayi shiru da bakinta tana mamakin wannan a'lamari." A hankali yace." Mamy kije gida ki huta please zan kira Abbakar yanzu ya zauna dani zuwa yamma tun d'azu na kira wayar dady ban samu ba."
Tace"Nima Yanzu na kira in fada masa baka da lafiya." Kallonta yayi ta kalleshi itama yayi saurin yin kasa da idonsa domin baya son ta fuskanci wani abun yace." Mamy please kar ki fada masa don Allah kin San dai halinsa ko."? Shiru tayi masa kawai Mintuna biyar tsakani Dr ya dawo da magani a hannunshi duk ya mik'awa Khalid ya mike zaune sosai ya karba da ruwan da yake miko masa ya shanye tas Dr yace ." insha Allah zaka samu sauki zuwa anjima ciki harda na bacci domin idanunka sun nuna alamun rashin bacci ka kwanta ka huta zaka tashi da k'arfin jiki."
Khalid yace." Tank u dr koma yayi ya kwanta shi kuma Dr ya futa da sauri. Ya kalli Mamyn yace." Kinji abunda Dr yace ko cikin maganin da nasha yanzu akwai na bacci kije gida Da yamma sai ki dawo."
Tace"Myson bana son na tafi na barka kai kadai ne." A hankali yace. " mamy yanzu zan kira Abbakar yazo kar ki damu kinga Hafiza na can tana jiran ki." Shiru tayi masa Khalid ya cigaba da lallab'ata da kyar ta tashi ta tafi, ajiyar zuciya ya sauke bayan ta futa wayarsa ya dauka ya fara Neman layin Abbakar bugu daya tayi ya dauka a kasalance yace." Abbakar bana jin dad'i wallahi ina Asibiti yanzu yaya alk'awarin mu. "? Abbakar yace." Guy wane asibiti ne ganin zuwa Yanzu. " a hankali yace." Dr Habib hospital gashinan a wajan ringirod." Abbakar yace. " Nagane hospital din ganin zuw...... Katseshi yayi ta hanyar fadin Abbakar ina alk'awarin mu da kai na jiya. "
Yace." Alk'awari yana nan kasan sai k'arfe uku na rana suke shiga makaranta kuma kai yanzu kana kwance a asibiti ya za'ayi kenan. "? Ajiyar zuciya ya sauke yace." Ka bari sai k'arfe uku tayi sai kazo amma ka tabbatar kazo min da ita yanzu bacci zanyi zuwa lokacin." Abbakar yace." Kar kadamu guy zan maka kokari insha Allah Yanzu ya jikin naka."!?
A ya mutse yace." Da sauki dai mybe idan na ganta in samu nutsuwa domun ni kaina a halin yanzu na rasa meke damuna wallahi." Yar dariya Abbakar yayi yace."Guy Allah ya Kai damo ga harawa dai." Yana sauke ajiyar zuciya yace." Ameen my friend ina sauraron zuwan Ku." Abbakar yace." Insha Allah." Kashe wayar yayi yana lumshe idonsa da tunanin yarinyar Shaik bacci ya dauke shi mai cike da mafarkinta........
*Yanzu a ka fara labarin*
*4/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI!_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*35*
Nasir ne ya zauna da Abbu gefan tabarma ranshi duk babu dad'i sosai yake jin tsananin takaicin zagin da jama'ar unguwa suke masa yanzu idan da zaiyi nufin daukar mataki babu yadda za'ayi Abbu ya barshi shi kam ya rasa wace irin zuciya ce dashi.
Cikin wata irin murya Abbu yace." Halimatu kawo mun ruwan sha." Ammi ta bude randa ta ciko Kofi da ruwa ta mik'a masa. Kafa kai Yayi a bakinsa sai da ya shanye tas sannan ya aje kofin yana sauke wata irin ajiyar zuciya shuru Yayi yana kallon guri guda duk sukayi cirko-cirko a kansa mintuna goma ya dawo nutsuwar sa Nasir ya kalla a nutse yace." Kira min Hanifa. " kafin nasir ya yunk'ura Hanifa ta futo daga daki tana matsar hawaye.Abbu ya nuna mata kusa dashi.
Zama tayi jikinta duk a sanyaye. Ido ya tsira mata yana kallo Hanifa taji wani sabon hawayen yana zubo mata wani irin tausayin mahaifin NATA ya lullub'e ta. Hannunta ya rike cikin nasa a tausashe yace." Hanifa ki fada min gaskiya kan abunda zan tambaye ki." Kai ta d'aga sama, ya cigaba da cewa"Nasan ke din yarinya ce mai gaskiya bakya karya duk rintsi ni nayi miki wannan shaidar Hanifa ina so ki fadamin shin gaskiya ne kece kika fara fadin cewar kina son wannan yaron da suka zo gidanan Yanzu ." hannu tasa ta toshe bakinta dashi wasu irin zafafan hawaye na kwaranyo mata.
Murmushi Abbu yayi yace." Ba kuka nace kiyi min ba gaskiya nace ki fadamin Hanifa." Ammi ta bude baki zatayi magana ya daga mata hannu shiru tayi tana addu'ar Allah yasa hanifa ta fad'i gaskiyar al'amari.
Kukan da Hanifa takeyi ya soma bawa Abbu haushi cikin tsawa yace." Idan baki fada min Gaskiya ba yanzu zan sanya yayunki su Zane miki jiki don kinga ina rarrashin ko."!?
Hannunta duk biyun tasa ta rufe bakinta dashi muryar ta bata futa sosai tace"Abbu nima ban San lokacin da nace ina sonsa na Wallahi haka kurrum nake jin gabana na fad'uwa Idan na tuna dashi Abbu kayi min addu'a indaina sonshi. "
Gurin tsit!! Yayi kowa na mamakin Abunda Hanifa ta fad'a Ammi kuwa mamakinta kadan ne dama tuntuni tasan da maganar Abbu wani irin gumi ne ya tsinke masa a jiki kallon Hanifa kurrum yake cike da mamaki har ta iya budar baki tace tana son namiji.
Hafiz ya zaburo! Cikin tsawa yace." Hanifa don baki da mutumci ki rasa wa zakice kina so sai Wannan Dan iskan yaron da ya gagari kowa a gari mawa'kin da bai taba wake ma'aiki ba kullum bashi da aiki sai raye-raye kina so ki zubar mana da mutumci a gari kina nufin ko kin rasa mijin aure a duniya zaki auri wannan Mara tarbiyya to ki rubuta ki aje ko da ran Abbu ko babu ransa bazaki taba auran mawa'ki ba."! Cikin zafi Hafiz ya kare maganar dama shu mutum ne me sanyin hali amma kuma Idan ya dau zafi bai iya fushi ba.
Kuka ta saki sosai tana matsawa jikin Abbu domin Hafiz kokarin kai mata duka yake. Abbu yace." Hafiz sassautawa zuciyarka ka saurare ni." Hafiz ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya Abbu ya cigaba da cewa "Hanifa batayi laifi ba mune muke ganin kamar ta aikata laifi abunda tayi shi ya samo asali ne daga gurin sayyada Nana khadija matar Annabi Muhammad (slw) babu laifi anan don mace taga namiji ta nuna tana sonta sai dai ita Hanifa zuciyarta batayi mata adalci ba da dauko mata son Wanda ya fi karfinta Idan da wani ne takewa wannan son bazan damu ba wallahi amma jin cewar wai ita da kanta ta furtawa yaron Kalmar so yasa duk jikina yayi sanyi yanzu ma kuma na kara tabbatar da hakan tunda gashi ta fada da bakinta gashi kuma tana koke-koke tabbas Gaskiya ne, Abunda dai bana son yi shi zanyi dole cikin biyu za'ayi d'aya ko mu koma gombe da zama ko kuma in saka gidan nan a kasuwa mu sanja gurin zama duk Dan wannan yaron domin ina ganin idan tayi nesa dashi hankalinta zai kwanta." Duk sukayi na'am da maganar Abbu Nasir yace." Abbu ni narasa wane irin shad'ainin yaro ne Wallahi na tabbata shine ya rinjayi Hanifa har ta furta masa Kalmar so ni a shawarata kawai mu koma gombe shi zafi domin ina jin tsoron sharrin Mahaifin yaron wallahi."
Abbu yace." Dole cikin biyu za'ayi d'aya dama." Ammi dai na zaune tana sauraran su dama kuma irin wannan ranar take jin tsoro addu'a takeyi Allah yasa karshen al'amarin ne yazo domin itama bata kaunar Hanifa da Khalid din ko kadan domin tasan Khalid ba sa'an auran yarta bane.
Hanifa kuwa jin zagin da Nasir yakewa Khalid yasa taji kamar ta zageshi itama don dai kawai su Abbu na gurin ne hararasa kurrum take yi ta kasan ido tana share hawayen ta, daga k'arshe ma tashi tayi ta shige daki gado ta kwanta ta dura Sabon kuka wai zasu tashi daga unguwar nan akan Khalid ko kuma su koma gombe wato su Abbu har yanzu basu fahimci yanda take ji ba a jikin zuciyar ta, idonta na zubar da hawaye ta zato pastar dinshi da ta soma yagewa ta tsirawa fuskarshi ido lumshe idonta tayi tana kallon k'aramin bakinsa Wanda wani irin kayattacan gashi ya kewaye kasan ha"barshi Wanda ya d'an lotsa kad'an fuskarta ta matsar daf da tashi ta d'ora bakinta kan nasa take ta tuno ranar da yayi kiss dinta hannuta tasa ta ta'bo lebanta tana lumshe ido hawaye suka zubo jikin pastar a hankali tace"I lov my chocolate Khalid Allah ya d'ora min sonka Abbuna baya sonka Zuciya kamar zata stage saboda kaunar kaaaaaa! A carke ta k'arashe maganar tayi ruf da ciki kan pastar tana wani irin kuka me tsuma zuciya.
Muryar Ammi taji a kanta tayi saurin goge hawayen ta tana kokarin mik'ewa zaune Ammi tace"Kuka kike yi ko."? Girgiza kanta tayi taki yarda su hada ido da Ammi.
Gyada kanta tayi cike da damuwa tace"Na fada miki ba tun yau ba wannan yaron ba tsaran ki bane kika nuna min cewa kin hak'ura dashi Ashe kinyi min lumbu-lumbu ne ko wai Hanifa kamar ke da nasani mace me kunya da kawaici kije ki fadawa namiji cewar kina sonshi Gaskiya nayi mamakin Wannan ab......... Bubbuga k'afafu take yi kan gadon tana kuka take fadin"Ammi wai yaya kuke so inyi ne? Uhumm nace nima bana so nake sonshi a jikina nake ji kuma ai Abbu Yanzu ya gama fada cewa abunda na aikata ba laifi bane Ammi ni dai don Allah ki k'yaleni naji da radadin da zuciya take min kome nake a cikin gidanan daurewa nake yi."!!! Ammi ta sassauta muryar ta saboda bata so Abbu yaji komai cikin sigar rarrashi tace"Shikkenan ai dama ba laifi kikayi ba kawai tarbiyar yaron da kika dauko ce bata yi mana ba shiyasa muke nuna miki illahr hakan." Shiru tayi tana kokari. Kwanciya nan hankalin Ammi ya Kai kan pastar Khalid hannu tasa zata jawo da sauri Hanifa ta rike Ammi naja Hanifa na ja.
Cike da mamaki! Tace''Baza ki Bari in ga ki menene ba."!? Zumb'ura baki tayi tace"Ammi ni......... Ammi taja pastar da k'arfi ta fara kokarin yagewa..... Da k'arfi hanifa tace",Wayyo Ammi kar ki yaga min don Alla....Kafin ta 'karasa Ammi ta fuzge pastar daga hannunta ta rabe gida biyu a take Hanifa ta hade kanta da gwiwa tana shashshekar kuka. Ammi kuwa hade pastar takeyi tana kokarin tantance waye a jiki.
[1/2, 9:42 AM] .: Cike da mamaki Ammi take kallon Pastar tunani takeyi a cikin zuciyarta yaron duk inada namiji yake ya kai ko ba'a fada mata ba tasan shine Khalid din da ake rigima a kansa sai yanzu ta kara tabbatar da cewar soyayyar Yaron tayi nisa a cikin zuciyar yar tata tunda gashi suna tare da ita tana mak'ale da hotonsa kullum su suna can gefe basu sani ba. Ammi ta mike da pastar a hannunta.
Dago kanta tayi tana kallonta har ta futa Ammi kai tsaye kicin ta nufa ta cusa pastar cikin murhu ta kyasta ashana ta kama da wuta, bata koma dakin ba ta cigaba da aikace-aikacenta tana yi Hanifar addu'ar ta Neman zabin Allah tsakar gidan babu komai Wanda ya dangaci kayan masarufin da Alhji Tijjani ya kawo Abbu yasa Duk an futa dasu waje yace duk su Nasir ya rabar dasu kafin kace kwabo kofar gidan ya cika abunka da unguwar yaku bayi dama kowa Cikin bukata yake, bayan sun gama ne suka wuce cikin gari domin fara shirye-shirye. Hanifa kuwa kwanciya tayi ta dinga sharar hawaye Shikkenan Ammi ta kona mata hotonta Wanda shine yake rage mata rad'ad'in soyayyar sa idan ya taso mata.
***
Alhaji Tijjani fada kawai yakeyi cikin mota yana ganin kamarshi yaje Neman auran yar talaka tilis har a tsaya ana fada masa magana da kudinsa da komai babu dad'i ko kadan yace." Myson Wannan yarinyar ko itace autar mata ya kamata ka rabu da ita ubanta mutsiyaci ne me k'ashin tsiya Idan akayi auran ma kai da yarinyar zatazo ta gada mana tsiya ne ni idan da zaka bi nawa ra'ayin kaje ka nemi auran yayan sarakai da masu mulkin k'asar nan nasan da gudu zasu amunce maka amma ka tsaya kan yar mutsiyata."!
Khalid da yake jin zuciyarsa kamar zata tarwatse yace." Dad ni kaina bayin kaina bane laifin zuciyata ne wacce na kasa sarrafata a halin yanzu kasan aure baya tsarina amma ganin yarinyar yasa naji ina bukatar in aureta in raya sunna Dad meye aibuna da mahaifinta yake gani har zai hanani auranta Dad wallahi nayi rantsuwar ya sake ya aura wa yarinsa wani mijin bani ba to sai na hanasu jin dad'i rayuwa kamar yanda suka hanani jin dadin tawa rayuwar. "
Alhaji Tijjani yace." Duk wani kokari da zanyi nayi akai amma zan sanya Alhaji Lawan abokina ya koma da maganar idan ya amunce Shikkenan idan kuma bai amunce ba sai ka hak'ura ko kuma ka dauki ko wane irin mataki akansu."
Shuru Khalid yayi yana tunanin mafuta abunda zuciyarsa take tunzurashi ya aikata yana ganin shine kawai zai fi masa don haka ya bari aka zuwa gurin abbu din a karo na uku idan ya'ki amincewa zai zartar da hukunci da ya yanke. Kasuwa suka wuce Khalid wani bene ya hau Cikin kasuwar nan shagunan Alhji Tijjani suke da ofis dinshi nan ya shige ofis din ya kwanta kan kujera yana sake sake yau abunda bai taba sha yaji yana sha'awar sha Mobson ya Dade yana fada masa sigari na gusar da damuwa yau ta dalilin yarinyar Shaik zai fara sha lallai Ya shaik da yarinyar sa sun shammace shi sun shiga rayuwar sa sunyi Kane Kane Wanda yake ganin tilas ne ma ta dauki mataki akan hakan. Mi'kewa yayi ya le'ka ta window yana kallon yanda mutane suke ta harkokinsu na kasuwanci wani yaronsu ya hango shigowar sa kasuwa kenan cikin ikon Allah suka had'a ido dashi Hannu ya daga masa alamun kira ya koma ciki shi koma yaron da sauri ya hau saman ofis din ya nufa sama-sama suka gaisa Khalid ya zaro dubu guda aljihunsa ya mik'a masa tare da fad'in"siyo min sigari kwali daya." Ba tare da bata lokaci ba yaron ya sauka kasa da sauri shi kuma ya koma ya zauna hade da dafe kansa minti biyar tsakani sai ga saurayin ya dawo karba yayi yana mik'a masa canji ya daga masa hannu godiya saurayin yayi ya sauka kasa, Khalid na bude ledar yaga harda leghtar yayi dad'i sosai don haka ya zaro guda ya kunna ya bata wuta Zuka yake yana lumshe ido tare da addu'ar Allah yasa ya daina jin abunda yake ji a zuciyarsa a game da yarinyar shaik.
Alhji Tijjani da abokina Alhji lawan suna rattuana maganaer komai Alhaji Tijjani ya fada masa Alhaji Lawan yace." Alhaji kayi gajan hakuri Gaskiya banji dad'i abunda kayi ma bawan Allah nan ba domin wani mutumci yafi kudi a gurunshi kaga mutumin ya nuna maka cewar shi kudunka basu ne a gabansa ba mutumci ne a gabansa Kai da kaje nema Kaine dole zaka kaskantar da kanka kaga yanzu abunda kayi masa zai sa ya kara d'aura damara ko yayi niyyar bawa yaron ka yarinyar ya janye saboda zaice kai ma baka da halin K'warai Gaskiya banji dad'i ba kuma wannan halayyar da ka nuna itace take sakawa ake zagin mu a gari Dole dai yanzu idan mun tashi daga kasuwa muje mu kara Neman alfarma a gurin shi kuma dole mu bashi hakuri kan abunda kayi masa."
Alhaji Tijjani sai yanzu ya fahimci kwabar da yayi tayi ruwa domin ya Riga ya gama fahimtar cewar yarinyar itace kwanciyar hankalin danshi Idan Hankalin Khalid din ba akwance yake ba to suma dole zasu kasance cikin tsananin damuwa da b'acin rai. Don haka sai ya amunce da shawarar da abokin nasa ya bashi.
Khalid kuwa sai da ya kusa shanye kwalin sigarin nan sannan ya aje lokaci guda yaji wata irin azababbiyar yunwa ta durar masa wayarsa ya dauka hannu na kyarma ya fara kira numbar Abbakar bugu guda tayi ya dauka a sark'e yace." Abbakar ina Cikin kasuwa a halin yanzu don Allah ka shigo ina son ganinka amma kafin kazo din ka tsaya kayi min take away yunwa nake ji wallahi." Abbakar yace." Insha Allah Yanzu zan shigo." Kashe wayar yayi ya zame ya kwanta kan doguwar kujera lamo yayi gwanin tausayi shi kadai yasan Abunda yake damunsa a lokacin.
30mintus Abbakar ya shigo cikin kasuwar kai tsaye 'b'angaran *Alhaji Tijjani Chanji* ya nufa kamar yanda ya sani idan Khalid din na cikin kasuwar baya zama a ko ina sai ofis dinsu kai tsaye can ya nufa hannunsa rike da wata farar leda mai dauke da tambarin *Nagarta restaurant* knocking yayi Khalid yace." Turo kofar." Abbakar ya bude ya shiga ya mai da kofar ya rufe.
Khalid mik'ewa yayi ya zauna yana kallon Abbakar din har ya karaso ya zauna kusa dashi kafadarsa ya dafa tare da fad'in "Yane guy naga kamar duk kana cikin damuwa Allah yasa ba hanifa bace." Ledar hannunsa ya karba ya bude abincin ya dauko ya bude bai jira komai ba ya fara ci Abbakar na kallonsa yana masa dariya sai da ya kammala tukkuna ya kalli Abbakar din a nutse yace." Dama haka sigari take sanya yunwa."!? Abbakar yace." No wandar mana da na shigo naji warinta yau ka karya alk'awarin ka kenan." Dariya yake yana nuna shi.'' Bata fuska yayi yace." Abbakar ya shaik naso ya Dora min ciwo d'azu munje gidan dani da dady anyi babu dad'i tsakaninsa da dady wallahi narasa wane irin mutum ne shi me taurin kan tsiya Abbakar idan Shaik ya'ki ya amunce min da auran yarsa to zan aikata Abunda banyi niyyaba akanta."
Abbakar ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin"Wallahi idan da nasan abunda zai faru kenan da ban turo maka pictures din nan ba tunda ni a ganina sune sila sau nawa kana ganin yarinya baka taba jin kana sonta ba sai da ka ganta a zahiri ni sai nake ganin kamar sha'awar ta ce take damunka da zaka dauki shawara ta kawai shine kayi kokarin kawar da sha'awar ka a kanta ka k'yale 'yar iska shaid'aniya ni shaidaincin ta ma tsoro yake bani tunda ta rikirkita ka to waye ma bazata rikirkita ba."! Khalid ya sauke zazzafar ajiyar zuciya yace." Ka San ni zina ba halina bane kuma banaso yarinyar taci galaba akaina har ta sanya ni na fara aikata wa akanta mutukar sha'awarta da haddasa min bata bar gangar jikina ba to babu shakka zan dauketa ne mu bar gari idan taki amincewa to dole in kauda sha'awarta da take damuna kaga kenan tayi galaba akaina abunda kwata-kwata bana so na aikata a kanta."
Abbakar yace." Kaine kake damun kanka a Kansu run wuri ma da haka kayi da yafi domin nake fada maka Wallahi ya shaik Yayi nisa d'azu na samu labarin duk abunda ya faru bayan tafiyar ku duk kayan abunci da Dady ya zube masa futo dasu yayi ya rabar wa da mutane gidan mu an kai shin kafa buhu guda kaga baya bukatar ka da abunda ya shafeka mutumin mugun taurin Kaine dashi kawai ka aikata abunda kayi niyya tunda ya'ki fahimta."
Ajiyar zuciya Khalid din ya sauke tace." Dad yace zasu koma tare da Abokinsa mu bari tukkuna muji da abunda zasu zo dashi." Tab'e baki Abbakar yayi yace." To Allah yasa suzo da alkairi amma nifa jikina na bani babu wani cigaba da za'a samu. Shiru sukayi na kusan minti biyar Khalid yace." Yanzu Abbakar ya za'ayi naga yarinyar." Abbakar yayi shiru yana nazari sai kuma yace." Gobe asabar suna da makaranta kuma kullum sai ta shigo gidanmu sun tafi da kanwat..... Khalid yayi saurin katse shi tare da fad'in"ya za'ayi na dauketa a motata." Murmushi Abbakar yayi yace." Duk wannan me sauki ne zanyi maka kokari." Hannu ya bashi suka tafa yace."Abbakar duk cikin abokina nafi alfahari da kai kana damuwa da damuwa ta." abbakar yace"Guy duk an zama daya bazan taba mance alkairin ka a gare ni ba. Hira suka cigaba da yi irin ta abokai har lokacin tashi daga kasuwa yayi..
*2/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*38*
'Karfe uku shaura kwata ta futo cikin shirin zuwa makaranta baka ganin komai a jikinta sai kwayar idonta muryar ta a dashe tayiwa Ammi sallama ta futa zuciyarta duk babu dad'i.
A nutse take tafiya har ta isa gidansu Asalamiyya tana kokarin shiga Abbakar ya dakatar da ita tsayuwa tayi suna gaisawa sannan tayi yunk'urin shiga cikin gidan ya tare hanya cikin wata irin siga yayi magana "Hanifa kin San kuwa Khalid bashi da lafiya."!? Wata irin fad'uwar gaba ce ta rikito mata take taji miyau na bakinta ya tsinke k'afafunta sun soma rawa abbakar din ta tsurawa ido tana kallonsa.
Marairaice fuska yayi yace." Wallahi bashi da lafiya sosai d'azu ya kirani a waya yana kwance ma a asibiti anayi masa 'karin ruwa kuma kin San ko meye dalili."!?
Girgiza kanta tayi tana son taji abunda zai fada
Yace." Wallahi so da kaunar ki ne ya kwantar dashi Hanifa kiyi wani Abu akai mana Abbu yana nema ya tar watsa muku farin cikin Ku ke da Khalid tunda nasan ke din ma shi kike so ya kamata kiyi wani Abu akan al'amarin nan." Da kyar tace" Ya Abbakar me zanyi akan wannan al'amarin? Tabbas bakayi karya ba ina tsananin sonshi da kaunar shi amma bana jin zan iya bujerewa bukatar mahaifina akanshi zan hak'ura dashi kawai watak'ila ma tarayyar mu dashi babu alkairi."
Abbakar yace." Ke kanki kika sani Hany shi kuwa da umm!? Ki duba ki gani soyayyar ki tasa shi har ya kwanta a asibiti ya kamata ki tausaya masa."!
Ajiyar zuciya ta sauke muryarta na rawa tace"Ya Abbakar yanzu me kake so nayi masa."?
Abbakar ya futo da wayarsa Ashe yayi rocouding lokacin da suke waya da Khalid din, muryarsa ta bayyana lokacin da yake cewa "Abbakar jikina da sauki dai amma Ganinta shine samun nutsuwa ta.""""""!! Tsigar jikinta ta dinga Mik'ewa wani irin kauna da sonsa suka bujiro mata hawayen da take kokarin boyewa sune suke kokarin zubowa murya k'asa-k'asa tace " Abbakar ni makaranta zanje gaskiya babu inda zanje."!
Abbakar yayi wani Kalar tausayi dashi yace." Kiyiwa Allah da manzon sa kije gurinsa ya ganki ko ya samu sa'ida wallahi na tabbata da kece a kwance cikin halin da yake ciki da tuni yazo minti goma ma tayi yawa zan dawo dake gida."
Shiru tayi tana tunani wata zuciyar tace"kije kawai idan aka futo sallah sai ki shiga makarantar zuwan ki Si baya yana nufin kun amunce masa da auran sa ba.
A hankali tace"Ya Abbakar muje mu dawo yanzu wane asibiti ne." Ajiyar zuciya ya sauke yana fadin"Asibitin a cikin gari yake muje mu samu a dai-dai ta sahu." Bayansa tabi suka futa daga soran gidan.
Bacci yayi sosai sai kusan uku da kwata Allah ya farkar dashi ya tashi da d'an kuzari a jikinsa zazzab'in ya sauka hakanan ciwon kan da yake damunsa ya ragu Mik'ewa yayi ya shiga toilet din dake cikin dakin sabon brush ya cire a ledar shi ya matsa markilin a jiki bakinsa ya wanke sosai ya dauro alwala ya futo kafin ya tada sallah sai da ya kara kallon agogo dake mak'ale jikin bango sannan ya tada sallah cikin nutsuwa.
Bayan ya idar yayi addu'a yanda ya sawwaka Mik'ewa yayi yaje ya dauki wayarshi numbar Abbakar ya kira lokacin suna daf da shiga asibitin Abbakar yace." gamu nan shigowa." A za'ke! Yace." Tare da ita ne."!? Abbakar yace." Insha Allah." Hanifa najin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya wacce tasa tsigar jikinta ta cigaba da Mik'ewa.
Lumshe idonta tayi tana ji zuciyarta kamar zata tsage saboda fargaba cikin wannan yanayin a dai-dai ta ya sauke su cikin harabar a asibitin Abbakar ya sallame shi suka shiga ciki sosai Hanifa a tsarge take tafiya kanta a kasa har suka shiga abbakar na kokarin kiran wayar Khalid din Dr ya futo daga wani room nan abbakar ya tambaye shi Khalid yace." Muje dakin da yake zan shiga yanzu." Abbakar ya kalli Hanifa da tayo lakwas yace." Muje Hany." Bayansa tabi salau-salau.
Yana zaune gefan gado da waya a hannunsa kana kallon fuskarsa zaka fahimci yana cikin damuwa bude kofar da akayi yasa ya dago kansa da sauri aikuwa idanunsu ya sark'e da juna saurin kauda kanta tayi tana jin wani yammmm! Sakamakon kallon k'wayar idonsa a hankali take bin bayan Abbakar har suka isa kusa da gadonsa suna magana da Dr da yake fadin"Ashe ka cire ruwan ma."
Cikin yanayin maganar sa yace." Sallah zanyi ne yasa na cire dama kuma ya kare." Dr yace." Ya kake jin jikin naka."? Lumshe idonsa yayi ya bude su maimakon ya sauke su kan Dr da yake tambayar sa sai ya sauke su kanta yana yi mata wani irin kallo mai kashe jiki yace." Dr jiki Alhmdullahi Yanzu zai kara warware wa tunda ya samu abunda yake so."
Dr yaso ya fahimci wani Abu shine dalilin da yasa ma ya Dan juyo yana kallon Hanifa ganin ita Khalid din yake kallo Murmushi yayi kawai Dr yaso yaga fuskar yarinyar k'wayar idonta kurrum ya gani ta cikin ni'kab yaji gabansa na fad'uwa babu shakka Yarinyar zata yi kyau dama irinsu ne masu b'oye baiwar da Allah yayi musu.
Yana wannan tunanin ya gama abunda yake ya futa. Abbakar ya matso kusa dashi ya bashi hannu suka tafa, Khalid ya nuna Hanifa da baki yana wani munafukin murmushi."
Dariya Abbakr yasa yace." Guy gata nan ka sallame ta da wuri ta wuce makaranta domun da kyar na rarrashe ta tazo."
Kyataccan murmushi ne a kwance a kyakyawar fuskar sa yace." Abbakar kaje waje zamu gaisa da Quin."! Abbakar yace."ko baka fad'a yanzu zan futa." Cikin dariya yake maganar sannan ya kama hanya zai futa,
"Ya Abbakar."! Maganar ta ta dakatar dashi juyo wa yayi yana kallonta, marairaice fuska tayi murya ta na rawa tace" Haka mukayi da kai."? Girgiza kansa yayi yace." Hany Ku gama ina waje ina jiran ki." Futa yayi da sauri har da rufe 'Kofar!
Hanifa taji gabanta na wata irin fad'uwa Kwata-kwata bata son su 'ke'be guri guda dashi saboda abunda yayi mata kwanaki tana tsaka da wannan tunanin taji muryarahi mai mugun kashe mata jiki yace." Ki cire wannan abun na fuskarki kizo mu gaisa kizo ki duba jikina kiga yanda soyayyar ki ta mai dani."!!! Shiru tayi gabanta na fad'uwa. "Hanifa."! Ta k'ara jin sautin muryar shi ido ta lumshe a hankali ta bude su gami da kallon inda yake zaune ya wani zuba mata ido, a hankali tace" Sannu ya jikin naka."!? Shiru yayi mata tace"Allah ya sawake yasa kaffara ne." Nan ma bai ce komai ba, ganin kallon da yake mata yayi yawa yasa ta kauda kanta kawai ta kama hanyar futa.
Mik'ewa yayi da sauri ya tare gabanta rikitattun idanunsa ya zuba mata ya sanya hannusa guda yana kokarin dauke ni'kab din fuskarta. Da sauri ta kwa'be hannunsa tana 'bata fuska tace" Meye hakane."?
Hannunta ya rike cikin nashi ya matse tsam! 'Dumin hannunsa ya sanya taji wani irin yanayi a jikinta kafin ta Ankara taji yana Jan hannunta da sauri ta dawo dai-dai tana kokarin fuzgewa tace"Kana aikata haram fa wai so hauka ne ? Shikkenan don nace INA sonka sai ka dunga kokarin wuce gona da iri."!
Cikin wani irin voice yace." Nine ma na wuce gona da iri ashe."!? Dauke kanta tayi tace"Ni dai Yanzu Abbakar ne ya tilastani kan inzo in duba jikin ka wai baka da lafiya nifa yanzu bana bukatar Abunda zai d'agawa mahaifana hankali nice nace ina sonka kuma Yanzu na janye Shikkenan kawai Allah yq hada kowa da rabonsa."
Maganganun ta sun bata masa rai sosai yace." Abbakar ne ya tilastaki kizo ki dubani wato da bai tilastaki ba baza kizo ba kenan? Ok kar kiyi tunanin kinci bulus kan masifar da kika jaza min kince kina so kin turo min sufar jikin ki kin hanani nutsuwa da kwamciyar hankali in kwana in wuni cikin tsananin begen ki da sha'awar ki saboda ke din Mara imani ne kiyi min wata maganar banza ra wofi anan gurun, kamar yanda kika haddasa min fitina a rayuwata kema sai na haddasa miki duk Wanda zaki aura sai na hanaki jin dadin rayuwa."
Hanifa ta fara kokarin b'oye hawayen ta da yake kokarin zubo mata fuzge ni'kaf din yayi ya jefar dashi a gurin....... Suka kurawa juna ido, Khalid ji yayi tsayuwr tana nema ta gagare shi dama jikinsa babu kwari sosai gashi kuma yaga abincin zuciyarsa sai ya fara kokarin janta nufin sa su isa bakin gado.
Hanifa kuwa kokarin dauko ni'kaf dinta take tq d'aura ya hanata kuka tasa masa tana fuzge hannuta kawai sai ya rungumeta yana sauke zazzafar ajiyar zuciya. Tudun Brest dinta suka sanya shi ya kusa suma sai ya hau gogo k'irjinsa a gurin yana wani irin nishi hannunsa ya sanya ya runk'unkume kugunta dai-dai kunnen ta taji muryarshi yana mata wa'ka wacce tasa ta fashe da kukun da bata shirya ba.
*"Zuciya ta taki ce."!*
*"Ruhina na naki ne."!*
*"Nutsuwa ta taki CE."!*
*"Gangar jikina naki ne.!"*
*"Hanifa ta sace zuciyar Khalid ya shiga yanayi na damuwa."!!!!!"*
Wannan sune baitocin da suka mugun kashe mata jiki duk wani karsashi da 'k'warin gwiwar da take ji sai ta neme su ta rasa ta zube a gurin tana gursheken kuka. Kanta tsakanin k'afafunta.
Gefan gado ya koma ya zauna fuskar dauke da wani irin murmushi Wanda shi kadai yasan meye ma'anarsa, sosai take kuka bai ce mata komai ba sai da tayi shiru don kanta ta dago kanta tana kallonshi da jajen idanunta, yanayin fuskarsa ya sauya! Yana wani marairaice ido da hannu ya nuna mata kusa dashi wai tazo ta zauna.
Da kamar baza taje ba sai kuma ta mike ta kara ta zauna zama tayi kusa dashi shi kuma ya sanya hannu sa ya rungumo kugunta kafad'unsu suka had'a da na juna.
A hankali yace." Ya kika ji wa'kar."! Shiru tayi tana lumshe idonta, gefan fuskarsa yake gogo mata a NATA fuskar cikin wani irin salo da ya kusa sata ta zauce yace." Ya Shaik yace yayi miki miji hakane."!? Gyada kanta tayi, yace."Kuma kina sonsa."? Girgiza kanta tayi shiru yayi na minti biyu kafin yace." Wace shawara kika yanke mana." Kamar yanda take wa Ammi shagwaba idan tana magana haka tayi masa magana "Ni ban sani ba."! K'aramin bakinta ya tsurawa ido take yaji wani irin fleeng shawa'ar ya tsots le'bunanta ya taso masa idanunsa ya 'kankantar cikin sigar Jan hankali ya juyo da fuskar ta yana mata wani irin kallo.
*5/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*42*
Wani irin lasa yake wa fuskanta da kuncinta har ya gangaro saitin bakinta ya sanya hannunsa biyu ya talfo fuskarta yana kallonta da rikitattaun idonsa Wanda suka sanja kala, le'bunanta ya tsurawa ido yana lashe baki. Harshensa ya futo dashi cikin wata iriyar siga ya fara lasar lebenta na lasa yana Dan ciza ahankali,, idonta ta bude tana kallonsa tayi saurin sunkuyar da kanta gashin idonta ya b'oye halin da take ciki gabanta ne yake dukan uku-uku ganin yanda duk kamanin sa suka sauya kafin ta dawo kauda fuska takeyi tana Dan ture shi yana kara sakar mata nauyin sa, sai wani lumshe idonsa yake yana yi abun irin na tausayi muryarsa a sark'e yace." Ki bani na tsotsi wannan sweet moth naki don Allah kar kice a'a."! Cikin shagwaba ya fad'i maganar wannan salon nasa yana mugun kassara mata jikinta shagala tayi da kallon shi yana wani kashe mata ido kafin tayi wani yun'kuri ya zura bakinsa a nata baiyi wata-wata ba ya sarkafo harshenta da nasa tsotsa yake a haukace!
Hanifa ta soma raina kanta ganin yanda Khalid din ya gigice kokarin zare mata siket din atamfar yake jikin na kyarma ya dago ta rungume ta yayi kamar wani mahaukaci ya dauketa cak bedroom d'insa ya nufa da ita aje ta yayi kan bed din Allah ya bata sa'a ta mike tsaye da sauri hannunta jikin zif din siket dinta da ya zuge kokari kawai take taja shi sama amma ya Riga ya burge k'irjinta ta kalla murarar gashinan a waje lokacin tsananin tsoro da fargaba suka shige ta, Khalid ya hau bed din ya jawo kafarta ta fada jikinsa jikinsa na kyarma yace." Beb naga duk kin wani furgice pls babu abunda zanyi miki kawai ina so in ragewa kaina damuwa ne sonki na nema ya kashe ni ki Bari inyi remocing dinki ki taimaka wa me sonki kinji ko."!
Girgiza kanta takeyi domin bakinta yayi mata nauyi a lokacin ta Gaza furta komai sai zare ido take tana Neman hanyar gudu..... Khalid ya kalli yanda take tsaye kan bed din nonowan ta suna tsaye carrr! Sai motsi suke sakamakon yanda take motsa jikinta a kid'ime ya mike tsaye shima ya rufe ta da jikinsa manneta yayi jikin bango ya rungume ta tsam-tsam! A k'irjinsa yana sauke wata irin zazzafar ajiyar zuciya kuka ta farayi tana ture shi take fadin"Ka bude min kofa na tafi sau uku kenan kana min irin wannan dabi'ar nifa ba irin wannan son nake maka ba don Allah kar ka cuci me sonka."!!!! Jikinsa ne yayi sanyi kadan ya sassauta rik'on da yayi mata fuskarsa ya sanya dai-dai wunyata yana sauke mata numfashin sa da yake sanya wa tsigar jikinta na tashi cikin rikitacciyar murya yace." Ni bazan cuce ki ba sai dai idan ke ki cuci ni ke da Mahaifin ki, na rasa me nayi masa ya tsane ni idan kinga na kyaleki a gurin nan to sai na biyawa kaina bukata ta."
Ido ta zaro cike da tsoro take motsa bakinta domin tarasa ma abunda zatace masa, lumshe idonsa yayi yanayin yanda take motsa bakinta yana kara dilmiyar dashi duk ya wani susuce, Hanifa kuwa addu'a ta farayi cikin zuciyarta take taji wata dauriya tazo mata kallonsa tayi tana harhade fuska tace"Yau na tabbatar ba son Allah da Annabi kake min ba jikina kake so Nagode Allah da ban furtawa mahaifina kai nake so ba, dama Abbu yace ya tsani dabi'unka." Jin abunda tace ransa ya b'aci kallonta yake da fuka a hade yace." Wato har wani mugun hali ne dani kenan. " Dauke kanta tayi tana kare jikinta da d'ankwalin kanta."
Tsawa ya buga mata ransa a bace yace." Wane irin mugayen dabi'u ne dani da za'a dunga guduna ne."!? Tsorata tayi ganin yanda idonsa ya karayin jazur! Hawaye take sharewa gabanta na cigaba da fad'uwa!
Gyda kansa yayi yaje ya zare key din dake jikin kofa da karfafan taku ya karaso kusa da ita muryarsa sama-sama yace." Bana da ra'ayin nayi wata mu'amula dake da ta wuce romancing amma ina tunanin yau zan nunawa mahaifin ki waye Khalid idan na keta abunda ya Dade yana boyewa sai ya tabbatar da cewa ni din me mugwayen dabi'u ne."
Hanifa tace"Khalid kar ka zager min mahaifina ina ganin girman sa kuma duk wani Abu dake tsakanin ka dashi na sani kawai ina nunawa ne kamar ban sani ba ina jin ciwon Abunda kuke wa mahaifina."
A tsawace! Yace." Ki rufe min baki a gurin nan ko kuma Yanzu in fasa shi wallahi! Shiru tayi gabanta na fad'uwa ya cigaba da cewa"Ke da mahaifin naki duk baku ishe ni kallo ba idan banda jarabta irin ta so ni me zanyi dake."!? Ya fada yana nuna ta da Hannu.... Cikin jin ciwon abunda yace take kallonsa ya mutsa fuska yayi ya cigaba da cewa"Kece babbar shadainiya wacce ta jefa ni a masifa ina zaman zamana kika turo min da pictures Wanda suka sanya ni na kasa nutsuwa a rayuwata koma menene kece sila ke da Abbu naki da kike karewa babu Wanda ya haifar miki da matsala kamar sa saboda haka dashi zakiyi kuka ba da kowa ba."! Yana gama maganar shi ya fuzgo kafarta ta fad'i kan bed din danne ta yayi gaba daya ya zare siket din jikinta ya jefar ransa a mugun bace yake yana ganin idan bai nunawa Shaik wanene shi ba bazai daina aibatashi ba a duniya.
Kuka take tana rokonshi Da yayi hakuri ya k'yaleta kar ya wulakanta ta a duniya yana jinta ya shareta yana cigaba da wasa da sassan jikinta cikin futar hayyaci yake kokarin zura Dan yatsansa cikin headquarter nata ta matse cinyarta tana dukansa a haukace! Ko ina duka take a jikinsa tana kuka tana turje-turje gami da bashi hakuri da kyar ya dago kansa ya zuba mata ido duk tayi wani wujiga-wujiga da ita a sark'e yace." Ina so in nunawa Shaik Mugwayen d'abi'una ne da kin daina kuka kina wahalar da kanki a banza da wofi!" Yana gama maganar sa ya maida kansa kan k'irjinta ya cigaba da abunda yake yi........ Ihu! Ta kurma! "Wayo Allah na! Amminaaa."!!!!!! Da sauri ya dago kansa yana kallonta da jajayen idonsa, wani bahagon mari ta taska masa a kuncin sa tana ture fuskarsa dake kusantota da tata. Murmushi yayi yana shafa inda ta mare shi din cikin narkakkiyar murya yace." Ni kika mara ko."!? "An mareka din Dan iska kurum daga yau na daina sonka kuma Allah sai ya saka min abunda kayi min Wallahi kaci amanar so.! Tana shashshekar kuka ta karasa maganar...... Tausayi ta bashi ganin yanda take kuka duk tayi wujiga-wujiga d'agata yayi yana shafa fuskarsa mamaki yakeyi yanda ya kasa aiwatar da abunda yayi NIYYA akan yarinyar. Hannunsa na kuncin sa still da murmushi a fuskarsa yake kallonta wai yau yarinyar Shaik itace ta mareshi lailai yana cikin taskun rayuwa ta tabbata kenan Ya Shaik shine yayi galaba a kansa.
Hanifa a jigace ta dirgo daga bed din ta dauki siket dinta ta zura kofar futa ta nufa kamar zararriya rigarta da take yashe a 'kasa ta dauka ta sanya har yanzu kan nonowan ta zugi suke mata saboda yanda suka sha murza a hannunsa tana kuka ta kama hanya zata futa....... Gabanta ya tare yana mata kallon kasa da sama tayi saurin kauda kanta gabanta na fad'uwa muryarsa taji a hankali yace." Wane irin mataki kika dauka Akan maganar da Mahaifin ki yayi? Kin san Wallahi duk inda kika shiga a fadin du niyar nan sai na zame miki kadangaran bakin tulu gwara ma kije ki fada masa ni kike so."! Muryar ta na rawa tace"ka bud'e min kofa na tafi Allah ya saka min abunda kayi min kaci amanar soyayya." Matse ta yayi jikin kofar ya Dora kansa kan kafadar ta cikin wata irin murya ya fara mata wa'ka kamar haka.
*Farin ciki na guda ne."!*
*A kanki zan zamma wane*
*Kinga hallaya Zane ne*
*Shi kuma so rayuwa n!*
*Me ladabi hankali ne."!*
*Kuma d'abi'un ki sune."!*
*Ki zama rurin cida ne....... Kunne yana jinki 'yar uwa.!"*
Ajiyar zuciya ta fara saukewa hawaye masu d'umi suka shiga gangaro mata a fuska rungume shi tayi kam! Jikinta na karkarwa shima matse ta yayi a jikinsa sosai ya lumshe idonsa yana Jin yanda zuciyarta take bugawa da k'arfi.!
Sai ya da tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya sake ta hannunta ya rike suka futa parlor tare suka zauna kujera daya Hanifa sai share hawaye take tana sauke ajiyar zuciya, cikin yanayin maganar shi yace." Akwai shawarar da na yanke akan al'amarin mu kuma ina fatan zaki bani goyon baya."
Shiru tayi batace komai ba ya cigaba da cewa"Idan Shaik ya'ki aminincewa da bukatar mu to cikin biyu za'ayi d'aya ko in gudu dake america muyi auranmu ko kuma muje dake koton musulunci a d'aura mana aure wanne kike ka dauka."!?
Girgiza kanta takeyi tana jin wata irin fargaba da tashin hankali jin kalaman sa bata jin zata amunce da daya daga ciki, yace." Ke nake sauraro."?
"Nifa babu Wanda na yarda zan aikata cikin maganar ka kawai mu barwa Allah al'amarin."
A d'an hasale yace." Ashe karya kike yi kenan son da kike min na karya ne."!?.
Girgiza kanta tayi tana matse fuskarta da hannunta.
Yace."karya ne mana tunda gashi kinki amincewa da bukatata Wannan shine mafuta a garemu baki d'aya."
Ganin yanda ya tsare ta da ido kuma fuskarsa a murtuke tsoro taji kar ya kara kaita d'akinsa ta samu Allah ya kubutar da ita tace"To ka bari zanyi sha'awara.'
Ya mutsa fuskarsa yayi yana mata wani irin kallo na zallar sha'awa yace." Dawa zakiyi shawara bayan nine abokin shawarar taki.''
Hannunsa ta rike cikin sigar rarrashi tace"Ba da kowa zanyi sha'awara ba da zuciyata zanyi kayi hakuri insha Allah ni dai kai mutu karaba." Lumshe idonsa yayi yana jin dumin hannunta na shiga jikinsa ya bude idon a hankali ya sauke su kanta, lebansa ya motsa kadan yana so yayi magana kuma sai yayi shiru....... Tsira mata jajeyen idonsa yayi kawai.
'Kasa tayi da nata idon tana addu'a neman rinjaye ta lura dole sai da addu'a ganin yanda. Yake mata a lokacin babu abunda bazai iya aikata mata ba..... Tace ." kayi shiru bakace komai ba."
Ajiyar zuciya ya sauke yace." Kin tabbata da maganar da kika fad'a."?
Kanta ta d'aga masa.... Hannunsa ya zare daga nata ya fara cire zobon azirfar dake 'karamin yatsan sa, d'an ya tsanta na tsakiya ya kamo ya zura mata zoban ya sumbaci gurin kana ya kalleta tare da I'm promise you ina tare dake har abada Ina so inji haka daga bakin ki."
Hanifa tayi shiru tana kallon zobon dake hannunta jikinta duk ya shika ta ma rasa wane tunani zatayi kallon zoben kawai take tana mamakin yanda yayi mata bala'in kyau a hannu.
Khalid ya rike Dan ya tsan da zoben yake jiki yana kokarin kaishi baki ya tsotsa tayo saurin fuzge wa tana dan hararasa mik'ewa tayi tsaye shima ya mike da sauri ya rungume ta ta baya, Cikin zuciyarta take fadin"Yau naga jaraba gurin mutumin nan dai-dai kunnenta ya sanya bakinsa a hankali yace." beb kiyi min alk'awarin kinji ko." Kokarin gocewa tayi tace"Nayi maka alk'awari insha Allah. " Sakinta yayi yace." Bari inyi wanka in futo sai in kai ki gida ko." Kafin tace wani Abu ya shige bedroom d'insa da sauri.
[1/11, 9:21 AM Zama tayi kan kujera tana sauke ajiyar zuciya wannan al'amari ta rasa ta inda zata fasaltashi a yanzu dai babu wani da namiji da take so kamar ta mutu kamar Khalid din ita kanta tasan idan Abbu yayi ganganci aura mata Nasiru to za'a samu k'atuwar matsala watakila ma zumunci ya lalace domin Sam bata yiwa Nasiru kwatankwacin son da take wa Khalid ko kadan tasan dai tana sonshi irin na 'yan uwanta ka kanta duk ya kulle ta rasa wane tunani zatayi a kan al'amarin amma ta yanke shawarar tunkarar Abbu da maganar dake cikin zuciyarta in yaso ko wace-wace dole shi Ya Nasiru ya janye idan yace ya janye shi Abbu din zai hak'ura shima ya janye da Wannan tunanin ya futo ya same ta, kasa dauke idonta tayi daga kanshi yana sanye da lafiyayyar shaddar geznar milk color anyi masa dinki hannu da bakin zare rigar iya Kacin ta gwiwarsa sai dogon hannu inda yayi amfani da links masu shek'i da daukar ido Hannunsa daure da agogo baki na sallahr fata kana ganinshi kasan zai ja kudi lafiyayyar sumar kamshi tasha gyara sai shek'i take, k'amshin turarashi kuwa tuni ya game parlor har ya karaso kusa da ita ya zauna bata dauke idonta ba, sai da yayi kamar zai tsokane mata idone sannan ta dauke idonta tana Dan ya mutsa fuskarta, Kafadar ta ya rungumo dai-dai saitin kunnen ta yace." Nayi kyau ko."!? Gyada kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya! Munafukin murmushi ya saki ya Dan sumbace ta a gefan fuskarta kana yace." Nima kiyi min abunda nayi miki zan kara tabbatar da cewar kwaliyata ta burge ki." Mik'ewa tayi ba tare da tace masa komai ba ta kama hanyar futa, cikin shu'umin kallo yabi bayanta dashi yana shafa sajenshi mik'ewa yayi yaje ya bude mata kofa ta futa ya bi bayanta bai yarda sun jera ba gaba yayi da sauri ya nufi inda motocinsu suke Hanifa ta dinga binsa a baya kamar munafuka sai sinkewa take cikin hijab kafin ta karaso ya bude mata motar ta shiga ciki da sauri, Wanda yayi dai-dai da futowar Mamy tare da Hafiza Cikin shirin zuwa unguwa.
Khalid ya sauke ajiyar zuciya yana hamdala ga Allah hijab dinta da ya Dan futo ta kasa yayi sauri ya gyara ya rufe motar da sauri lokacin suka karaso gurin 'bata fuska yake yana 'kara cin kuno domin yasan halin Mamy d'insa da takura wa aikuwa suna karasowa tace"Yawwa Myson Muje ka kaimu gidansu NASIRIN mamanta ce babu lafiya wallahi kaga kaima sai ka duba ta ko."?
"A'a Mamy kuje kawai ni Yanzu akwai inda zanje ." yafad'a babu wasa a tare dashi...... Hanifa kuwa kwanciya tayi doguwar kujera gabanta na lugudan duka jin muryar matar da ta zage ta a asibiti tasan mahaifinyar sa ce Muryar Hafiza ta jiyo tana fadin"Au! Don zakaje zance shine zaka ki daukar mu a mota naga sai wani ya mutsa fuska kake kamar zaka dauki kashi.""" Ta k'arashe maganar tana tab'e bakinta.
Hararata Yayi baice komai ba yace." Mamy pls kuyi amfani da. wata motar don Allah ni ba hanyar Ku zanyi ba." So yake su matsa daga gurin ya bude motar ya shiga don ma Allah yasa motar me duhun gilashi ce.
Mamy tace"To aishikenn da ina cewa ko Kai ma zaka je sai ka gashe ta."
"A'a Mamy kuje kawai ni idan na samu lokaci zanje." Ya fada yana shafa siririn sajen sa, Mamy tayi gaba Hafiza tabi bayanta suka bar gurin. Ajiyar zuciya ya sauke ya bude motar da sauri ya shiga ya zauna gurin zaman shi ta mirror ya hangota a kwance sosai ta bashi tausayi da dariya kawai ya girgiza kai hade da kunna motar ya futa daga gidan.
*Yanzu aka fara!*
*11/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*39*
Kallon da yake mata ya rikita ta sosai jikinta ya soma karkarwa tsoro duk ya shige sai ta fara kokarin k'watar fuskarta da ya rike da hannunsa duk biyun..... Cikin zafin nama ya 'kara juyo da ita da sauri ya had'e bakinsa da nata ya hau tsotsar le'bunanta masu mutukar taushi tsotsar su yake yana lumshe idonsa ita kuma ta rinmtse hakoranta taki bude bakin nata hakan ma da tayi shi yayi masa dai-dai dole idan taji wuya ta bude bakin hannunta ya rike Wanda take faman dukan shi dashi shi ya rike tsam! Ya sanya daya hannun nasa cikin hijab dinta.
Gantsarewa tayi tana sakin ihu jin yanda ya dam'kar mata Brest da 'k'arfi yana murzawa... Idanunsa ya bud'e yana kallonta tana zubar sa hawaye har yanzu bakinsa na Cikin nata yayi nasarar kamo harshenta a lokacin ya shiga cikin wani irin yanayi mai mutukar wahala lokacin ne kuma bugun da akeyi wa 'kofar dakin ta tsananta...... Kamar a mafarki ya juyo muryar Mamy d'insa da Hafiza suna kiransa, a kasalance ya zare bakinsa daga nata Hanifa ta samu ta mi'ke a guje cikin gigita take kokarin bude kofa ta futa. Ya tari gabanta ita dashi duk sun wani hargitse kowa sai nuffashi yake saukewa.
Kuka takeyi sosai tana fad'in"Allah ya isa ban YAfe ba banza Dan iska wallahi Allah sai ya saka min ."! Kokarin rufe bakinta yakeyi domin yana jin tsoron kar su Mamy suji ita kuma tana ture hannunsa tana kokarin futa duk ta d'imauce.
'Daukar ta yayi cak! Ya nufi toilet da ita ajeta yayi kafin tayi wani yun'kuri ya rufo kofar ya futa. Har Yanzu yana jin muryar Mamy tana kiran sunan sa.
Muryarsa a sark'e yace."Mamy ganin fa ina toilet ne." Bude kofar yayi Mamy tace"Myson wai me kake ne tum d'azu a ciki ga abokinka yace ya Dade yana jiran ka." Abbakar ya kalla yayi masa alama da idonsa Abbakar ya bar gurun da sauri.
Mamy ta kalleshi sosai cikin nazari tace"Meye naga idanunka duk sun sauya ko dai baka samu kayi bacci ba."!?
Sumar kansa ya shafa yana kokarin juya ciki yace."Daga bacci ma na tashi shine na shiga toilet a lokacin ne kuma naji maganar ki."!
Dakin suke kokarin shigowa tana fad'in"Ai ga alamanan na gan..... Kafin ta 'karasa suka ji wani irin mahaukacin bugu daga kofar toilet Hanifa nayi tana kuka take fadin"Ka bude min kofa munafuki azzalimi Allah sai ya sakamin Abunda kayi min."!!! 'Kasa yayi da kansa yana jin wani irin takaici Hanifa ta tona musu asiri Shikkenan kuma.
Mamy tace"Myson muryar wa nake ji tana kuka a band'aki bude ta ka fada min me tayiwa yarinyar mutane."? Jikinsa babu kwari yaje ya bude kofar Hanifa ta futo kamar zararrariya ta nufi kofar futa.
Mamy tace" ke yar nan tsaya kar ki futa zo nan ki fad'a min abunda yayi miki kike masa wannan mugun alkaba'in." Hanifa na juyowa Mamy ta mike tsaye da sauri tana nuna ta da hannu ta tace"Myson me ya kawo wannan yarinyar dakin nan."
A hankaliYace." Mamy nine na kawo ta ta duba ni.Tsawa ta buga masa tana fad'in"wato kallon pictures dinta da kakeyi bai isheka ba sai da ka gayyato ta nan don shaid'anci shine take kuka don taji muryar mu zata sauya maganar ina ce d'azu a cikin mota sai da na gargade ka ka rabu da ita ko."
Hanifa taji zuciyarta ta kara tsinkewa jin irin maganar da take futowa daga bakin matar da take tunanin mahaifiyarsa ce kunya da taikaci suka sa jikinta yayi sanyin da ta kasa bude kofar ta futa.
Mamy ta cigaba da fad'a sosai take fad'in"Idan aure kakeso na fad'a maka kaje ka duba wata yarinyar a gari duk ga sunan masu hankali da kyau masu tarbiya na kawo maka yarinya kintsatsiya kace baka so yanzu Myson me zakayi da yarinyar da take bibbiyar ka babu kamun Kai babu komai." Hafiza tace"Mamy ki bar maganar don Allah, bawai Allah zo ki dauki abunki ki tafi."! Hafiza ta fad'a tana kallon inda Hanifa take tsaye tana kukan takaici Yanzu ta bar kukan abunda Yayi mata tana kukan maganganun da mahaifiyar sa ta fada akanta ne kuma yana ji bai ce komai ba.
Jikinta a sanyaye taje ta dauki ni'kaf dinta ta juya Mamy tace"Dakata nan."! Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba. Mamy tace"Ki kama kanki kuma ki sani duk inda ya mace take indai ta cika mace tana tattala mutumcin ta ya kamata ki nutsu ki gane rayuwa ko kya samu Wanda zai aure ki da daraja ina so ki k'yale min yaro hakanan ya huta don Allah kar ki kara shiga ray........" Mamy."!!!! Ya katse ta da muryarsa a sha'ke! Shiru tayi tana kallonsa baice komai ba ya mi'ke yana had'a hanya ya 'karasa inda take tsaye ni'kaf din dake hannunta ya 'kar'ba a hankali ya soma d'aura mata, halin bak'in cikin da take ciki ya hanata hanashi abunda yake mata tsaf ya d'aura mata kamar yanda takeyi ta d'ago idanunta masu cike da gashin ido gazar-gazar ta kalleshi k'walla na shatata shima ita yake kallo yana marairaice mata fuska a hankali yace." Kiyi hakuri kinji ko."! Ba tace masa komai ba tayi gaba da sauri ta bud'e kofar dakin ta futa. Bayanta ya bi da kallo har sai da ta fuce ya juya yana fuskantar su Mamy din fuskarsa a had'e yace." Mamy meye kike yi hakane!? Zaki zubar da 'kimar ki a gurinta tuntuni na fad'a miki cewar yanda kika dauketa ba haka take ba Mamy ban sanki da wannan halin ba don Allah ki daina min haka indai kina son kwamciyar hankalina ki so Abunda nake so."
Cikin fusata tace"Myson bafa zanso wannan yarinyar ba da jiki kamar na karuwai Wallahi nasan abunda yake rud'ar ka da Ita kenan Kuma nasan sha'awarta kakeyi ni kuma bazan bari ka aure ta ba domin baza ka za'bawa 'yayan ka uwa Mara tarbiyya ba, wallahi tunda naga pictures dinta na tsane ta."
Zama yayi gefen gado ya dafe kansa mamy na nema ta d'ora masa hawan jini Hafiza Tace"Mamy don Allah karki tsawalla akan al'amarin nan daga baya Kuma kizo kiji kunya duk da banga yanayin pictures din da turi masa ba amma ni na tsaya nayi wa yarinyar kallon nutsuwa ina ganin kamar da akwai alamun nutsuwa da kunya a tare da ita maganar pictures kuma ki ajeta gefe indai 'yan matan Yanzu mafi akasarin su haka suke turawa samarinsu pictures dinsu don haka karki damu."
Mamy tace"Wannan karon fa bazan yarda ba sai dai duk abunda zakuyi kuyi naga Abu da idona ba nuna min akayi ba kuma kice in Bari ya aure ta."!
Khalid cikin jin haushi yace." Wai Mamy zina nayi da ita ne? Kofa zina na aikata da ita shari'a ta yarda na aureta ballanta pictures dinta kawai na kalla idan da Wanda a ga laifi ni ni ne ba ita ba."!!!
Mamy ta fara share hawaye tana fad'in"Yanzu ni kake fad'awa wannan maganar har da buga min tsawa kamad wata sa'arka."!?
Hankalinsa ne ya tashi yasa ya taso daga inda yake da sauri yaje ya rike k'afafunta yana bata hakuri "Mamy please stop crying, wannan kukan da kikayi zan iya jawo min wata masifar don Allah kiyi shuru muyi magana ta fahimta."! Duk a gigice yake maganar domin kwata-kwata baya kaunar 'b'acin mahaifiyar tasa.
Mamy matsar hawaye takeyi taki cewa komai Hafiza tace" Mamy wallahi ni banga abun tada hankali ba a nan ki daina wannan kukan don Allah kar wani ya shigo ya zaci wani abun ne."
Tace"Hafiza kina jin abunda yake fadamin kan ina nuna masa abunda ya dace dashi har yana min tsawa kinga kenan ko auranta yayi abunda zai dinga yi min kenan. "
Girgiza kansa yayi gami da fad'in"Mamy babu wata mace da zan aura tasa tana wulakanta ki wallahi duk son da nake mata sai na rabu da ita mutukar tace baza ta zauna lafiya dake ba, shiyasa nakeso ki kwantar da hankalin ki akan wannan yarinyar ki cigaba da tayani addu'a idan alkairi ce a tare dani Allah ya mallaka min ita idan kuma babu alkairi Allah ya musanya min da mafi alkairi. "
"Dole in kasance cikin yi maka addu'a myson amma ni kam wannan yarinya bata kwanta min ba." Hannunta ya rike yana rarrashinta da kalamai masu sanyi har Dr ya shigo ya salleme shi bayan ya hada masa maganin da zai cigaba da amfani dasu.
***
Kanta a 'kasa take tafiya har ta futa daga cikin asibitin taji muryar abbakar yana kiranta kin juyawa tayi ta cigaba da tafiya shima Yanzu wani irin haushin sa take ji tana ganin da be tilasta ta zuwa ba da bata fuskanci Wannan b'acin ran ba.
Da sauri ya 'karaso gurin da take tsaye yana yi mata magana taki tanka masa yace."Kiyi hakuri na Dan futo waje ne naga mamanshi tazo da ya yarshi DA fatan dai kunyi gaisuwar arziki."
Shiru tayi masa wani mai adao-dai ya tsaya gabansu nan Abbakar ya fada masa inda zai kaisu suka shiga, Abbakar ya nace da tambayar ta abunda ya faru take kuka taki fada masa, Khalid ya kira a waya yana tambayar sa "Wai me akai mata ne gatanan tana ta faman kuka." Khalid yaji wani irin a jikinsa Mamy ya kalla da take draving yace." Abbakar bani ita." Hanifar ya mik'awa wayar taki kar'ba Khalid na juyo shashskar kukanta ya 'kara rikice wa Yace." Abbakar ka bata wayar mana bana son wannan kukan ." Abbakar yace." Taki karba Wallahi." Kamar ya kurma ihu haka yaji muryarsa a shake yace."Kara mata wayar a kunnen ta. " Hafiza ta kalleshi cike da mamaki tace." Wannan wane irin takura ne dole ne sai tayi maka magana.Mamy na driving na girgiza kanta duk abunda yake faruwa tana ji a hankali tace"Rabu dashi Hafiza Yayi yanda yake so a cikin motar nan Na lura iyayen yarinyar nan sun gama dashi domin wannan abunda yake ba na me hankali bane."
Dariya Hafiza takeyi k'asa-k'asa shi kuma Khalid na aikin tafka mata harara gefe guda kuma yana ta faman rarrashin Hanifa ta cikin wayar Abbakar din sai kalamai yake zubo mata abun Har mamaki yake bashi. Tunda yake soyayya babu wata 'ya mace da ta taba cin sa'a ya furta mata Kalmar so da bakinsa amma Hanifa ta kwance masa kai Wannan aikin na so ne ko kuma na sha'awa?
Shiru tayi tana sauraran wa'kar da yake mata wacce ya 'kirkireta a d'azu sosai kalamsa suka kashe mata jiki sai sauke ajiyar zuciya take yi tana sauraran sanya yar muryarshi da take bala'in so
Sai da ya tabbatar da ta daina kukan sannan ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya gaskiya yaji ciwon irin kalaman da Mamynshi ya ya'ba mata duk Wanda aka muzanta irin wannan dole yaji takaici a zuciyarsa lumshe idonsa yayi yana tunano moment dinsu da ita na d'azu.
Mamy da Hafiza kuwa abun ya girmama a gurinsu Hafiza har ta fara jin tausayin Dan uwanta ganin yanda soyayya take nema ta zautar dashi gashi ga dukanin alamu zasu sha fama da Mahaifiyar su tunda ta nuna bata son al'amarin.
Hanifa kuwa sai kusan biyar shaura ta shiga makaranta aikuwa malam yakub ya tsada ita yana tambayar ta ." a raunane tace"Malam kayi hakuri don Allah wani Dan uwana ne bashi da lafiya naje na duba shi."
Malam Yakub yace." Hanifa da kam kin fi kaunar makaranta amma a 'yan kwanakin nan duk kin shiririce duka wancan satin da ya wuce sau biyu kika shigo makaranta ko meye dalili."
Cikin rawar murya tace"Malam wancan satin ni'kab dina ne ya bata Wallahi sai da aka dinka wani don Allah kayi hakuri." Malam yakub yace." Ki shige ciki Yanzu kam sai dai ki tadda saura zan shigo yanzu in karb'i haddar jiya."
Gabanta ne ya fad'i jin abunda ya fada simi-simi ta wuce cikin aji Asalamiyya na hangota ta window tazo ta zauna kusa da ita jikinta duk a sanyaye."
Asalamiyya tace"Hanifa jikin ki kamshi yake me dad'i wallahi wai ina kika je."!?
Shiru tayi mata Asalamiyya tace"Ina fatan kinyi haddar ki ko."!? Wallahi Asalamiyya in banda Yanzu malam yayi min magana na manta." Ta fada tana bude al'kuranin dake hannunta, a lokacin ta bude inda akace su haddace ta fara,cikin ikon Allah ayoyin suka zauna akanta, Malam yakub ya shigo ya karba kamar yanda ya fada lokacin tashi yayi aka tashi
Tambayar duniya Asalamiyya tayiwa Hanifa kan a ina ta samo turare me kamshi Hanifa taki fada mata dole tasa Asalamiyya ta hak'ura ta k'yaleta amma itama ta fara zargin wani Abu domin k'amshin turaran kamar ta taba jinshi a jikin mutum d'aya, haka dai suka rabu ko wanne zuciyarsa babu dad'i.
Ammi ta ganta ta shigo sukuku kallo ta bita dashi har ta shige daki, ammi ta gyada kanta gami da cigaba da aikinta Hanifa kam uniporm din ta hau cirewa jikinta duk babu kwari har yanzu idan ta tuno abunda ya faru ita da Khalid sai taji fad'uwar gaba idan ta tuno da yanda ya damkar mata Brest sai tsigar jikinta ta kara mik'ewa abunda yake kara rikita idan ta tuno yanda ya dinga tsotsar bakinta sai taji wata irin sha'awar namiji ta kama ta, duguwar Riga ta zura tayi kwance a kan gado Cikin damuwa da jin wani irin azababban fleengs lumshe idonta take tana jin yanda kan nonowan ta suke kumborowa bata taba shiga irin wannan yanayin ba sai wannan karon. Cikin wannan yanayi Ammi ta shigo ta same ta.
Ammi na shigowa dakin taji k'amshin turaran itama dake a jikin kyauran kofar shigowa Hanifa ta rataye kayan sai ta jawo hijab din tana sansanawa cike da mamaki take kallon Hanifa da gabanta take wata irin fad'uwa tace"Hanifa wannan turaran a ina kika same shi me k'arfin tsiya."!?
A Dan furgice tace"Ammi wane turare ne."!? Ammi tace "Gashinan jikin hijab dinki." Cikin ina_ina tace"Ammi na Asalamiyya ne na fesa nima sai da na fesa nazo ina da nasa ni." Ammi ta zuba mata ido tana kallo tace"Wannan turaran na maza ne Hanifa ki fada min gaskiya."
Kuka ta fashe dashi tace"Ammi a ina kike tunanin zan samu turaran maza in shafa a jikina ki yarda da magana ta Ammi."
Amma tace"Hanifa bana zargin ki da komai kawai da cikin maganar ki da yanda kike inda inda yasa na fahimci alamun rashin gaskiya a tare dake."
Hanifa na kuka tana rantse-rantse na cewar turaran Asalamiyya ne sai da Ammi taga tana Neman futa daga hayyacin ta saboda kuka yasa tace to ta yarda amma daga yau kar ta kara fesa wa domin babu kyau.
Daga kanta tayi tana fadin"Insha Allah Ammi bazan karaba Ammi ta futa daga d'akin. Goge fuskarta tayi tana hamdala cikin zuciyarta minti goma da futar Ammi din ta mike tabi bayan ta, aiki ta kama mata suna hira kad'an-kad'an haka Abbu ya shigo gidan ya same su sosai yaji dadin yanda yaga Hanifa ta saki jikinta ba kamar yanda ya futa ya barta ba, ledar hannunsa ta karba shi kuma ya dauki buta ya futa waje domin d'aura alwalar sallahr magariba.
*6/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*33*
Abbu na zaune kan dadduma a 'kofar gidansa kamar yanda ya saba zama duk daran duniya idan bai yi zaman karatu ba to akwai wani abu da ya hanashi yanzu ma hannunshi na rike da al'kurani mai girma yana karanta a nutse, Khalid tun kafin su karasa yaji gabansa na fad'uwa daurewa kawai yayi har suka 'karasa kusa dashi sunayi masa sallama. Abbu ya d'ago kansa yana kallonsu dake babu haske sosai a gurin yasa fai fahimci ko su waye ba ya nuna masu kusa dashi alamun su zauna, duk suka cire takalman su suka zauna suna saurarar karatun al'kur'an me girma take suka ji wani irin mutuwar jiki sunkuyar da Kansu sukayi domin yau Ya shaik din yayi musu kwarjini sosai.
_Ni kuma cewa nayi ai alk'urani ba abun wasa bane duk taurin kan mutum idan yaji wata ayar sai zuciyarsa ta raunanana! Allah kasa muna daga cikin wa'yanda alk'urani mai girma zai ceta._
Abbu sai da ya kammala surarar da yake kai sannan ya rufe alk'urani ya aje kusa dashi ya juyo da hankalinsa Kansu yana mik'a musu hannu alamun suyi musabaha.
Abbakar ne ya fara mik'a nashi sai Mobson Khalid ne a 'karshe. Gyaran murya yayi yace." Samari kunzo d'aukar darasi n.'? Abbakar yace." Eh hakane Ya shaik munzo daukar darasi da kuma wata buk'ata ta a gurin ka."
Abba sai yanzu ya fahimci ko su wanene a gabanshi ya gane Abbakar sosai tunda akwai ala'kar arziki tsakaninsa da mahaifinsa fuskokin su Khalid yake kallo take ya gane yaran ikon Allah ya fada cikin zuciyarsa babu abunda ya nuna musu a zahiri yace." To Alhmdullahi Masha Allah kace kunzo daukar darasi banga ku da littatafai ba."
Shiru sukayi Kansu a sunkuye, shima Abbu kallonsu yake yi cikin nazari, minti biyar tsakani Khalid ya d'ago kansa suka had'a ido da Abbu yace." Ya shaik kamar yanda ka sanni na sanka tsawon shekaru biyar mukayi wa junanmu farin sani a ido yau ina so in sanar maka da cikkaken sunana shine Khalid Tijjani d'an canji a yanzu nake da shekaru ashirin da takwas a duniya naga yarinyar ka Hanifa naji ina sha'awar auranta wannan shine bukatar da muka zo da ita."
Abbu ya jima yana mamakin maganar data futo daga bakin Khalid din tsawon mintuna goma babu Wanda yace komai a cikinsu, Abbu ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Khalid din cikin nutsuwa yace." Masha Allah Khalid ko da bakayi min bayanin kai wanene ba dama tuntuni nasan kai d'an waye a cikin unguwar nan sai dai abunda zan fada maka anan shine Hanifa tuntuni nayi mata miji kayi hakuri kaji ko Allah ya baka mace mai daraja irinta ko wacce ta fita."!
Khalid yaji kamar ya watsa masa ruwan zafi a jikinsa jin abunda ya fad'a yayi wa yarinyar shi miji waye wannan maiganganci lallai abunda bazai ta'ba amunce wa dashi ba kenan yana gani Hanifa tashi ce shi kad'ai. Abbu ya kalla muryar shi babu sauki yace."Shaik daga dubu daya zuwa miliyan zan iya baka kud'in auran yarinyar ka saboda haka ka maida alk'awarin auran Hanifa kaina domin ni nafi cancanta da in aure ta."
Wannan magana tayi mugun 'batawa Abbu rai wato yana nufin kudi zai sa ya siyar masa da Hanifa lallai yau ya 'kara tabbatar da cewar yaron bashi da nutsuwa . kamar yanda Khalid din yayi magana babu wasa a maganar shi, yace." Magana ta farko da k'arshe a tsakanina daku itace kar Ku kara zuwar min da wannan maganar kai!." Ya fada yana nuna Khalid ya cigaba da cewa na Riga nayiwa Hanifa Miji tun tana zanin goyo saboda haka babu Wanda ya isa na janye wannan 'kudirin nawa sai ubangijin da ya hallice ni kudi ko mulki ko sarauta basu isa su saka na janye wannan maganar ba, saboda haka ku tashi Ku bani guri na gama magana."!
Mobson ya zaburo! Har ya d'aga hannu zai nuna Shaik domin yayi masa rashin mutumci Khalid din ya buge hannunsa Mobson sai gyda kansa yake yana wani irin huci!
Khalid yaji maganganun Abbu kamar ana tsiyaya masa dalma a jikinsa sai zufa yake yi murya a Har hade yace." Yanzu ina son ganin yarinyar taka yaya za'ayi."!?
Abbu ya bishi da kallo na rashin fahimta yace." Malam Khaludu bakaji abunda nace maka bane." ? Gyada kai yayi yace." Naji."! Abbu ya mi'ke a nutse ya dauki alk'uranisa yace." Ni zan shiga gida Ku tashi lafiya." Babu Wanda yace. Masa komai Abbu ya shiga gida yana mugun mamakin abun.
Khalid Abbakar Mobson shuru sukayi suna sun rasa ta cewa,Mobson ya mike yana zura takalminsa yake fad'in "Wallahi da ka barni da wannan mutumin sai na FASA masa baki har sai yayi jini mu zai fadawa Wannan maganar dama ai tun farko sai da na fada muku mugun d'an akuya ne shi ba yarda zaiyi ba arziki na bishi yana gudu aikin banza kawai! Kai kuma Khalid duk ga mata nan a duniya karasa wa zaka mak'ale wa sai yarshi dole ya wulakanta ka."!
Khalid ya mike ransa a dagule ya doki kafadar Mobson din yace." Ka rabu dashi Guy nasan dole sai na fuskanci haka daga gurin shi tuntuni mutumin baya kaunata ni kuma yanzu Allah ya jarrabeni da kaunar yarinyar shi, zan cigaba da binshi a sannu a hankali idan ya'ki amincewa tq dad'i to babu shakka zan nuna masa ruwa ba sa'an kwando bane babban kwanciyar hankalinsa shine ya bani auran sa yarshi data dame ni idan ba haka ba dashi da yarshi sai na 'kunsa musu bakin ciki Wallahi."!
Abbakar yace." Guy ka rabu da Hanifa don Allah bafa ita kad'ai ce macace mai kyau ba duk ga mata nan burjik zaka zo nan ana maka wulakanci da kud'in ka da komai." Mobson yace." Nima abunda na gani kenan
Khalid jinsu kawai yake yi idan suna cewa ya rabu da Hanifa ji yake ranshi na b'aci shifa baiga dalilin da zai sa ya rabu da ita ba, idan bai aure ta ya kawar da sha'awar ta da take damunsa ba yana jin a rayuwar duniya komai nashi zai tsaya. Haka suka karasa inda yayi parking ya bude ya shiga Mobson ya haye maching d'insa sai mita yakeyi yana zagin Abbu! Shi kuwa Abbakar nacan na tausar zuciyar Khalid kan kawai ya hukura da Hanifa Cikin jin haushi da takaici Khalid din yace." Abbakar ka daina min wannan maganar Shaik da yarinyar sa basu isa su sani cikin masiba ba kuma kace in rabu dasu ban dauki fansa ba, nifa yanzu babu Wanda nake jin haushi irinka domin Kaine duk ka zama silar faruwar komai in da baka turo min pictures din yarinyar ba kaga hankalina a kwance amma saboda da kai da ita duk shaid'anune kuka turo min abunda ya tayar min da hankali ya hanani sukuni a rayuwa Abbakar ka kara cewa na rabu da ita sai ranka ya b'aci."!!! Abbakar yace." Itace shaid'aniya dai tunda ina zamana tazo tace tana sonka dole in taimaka mata akanka ni kuma naga Wannan hanyar itace dai-dai." Wani irin tsaki yaja ya kunna motar shi ba tare da yace wa Abbakar din komai ba ya bar gurin cike da bakin ciki da damuwa!
***
Abbu da 'bacin rai ya shiga gida kai tsaye dakinshi ya nufa Ammi tayi bacci tun k'arfe Tara ji yayi bazai iya hak'ura da maganar ba yasa ya tashe ta Ammi ta mike ta futa band'aki ta shiga sannan ta dawo dakin. Motsin Ammi shine ya farkar da Hanifa ta fara jiyo maganar sama-sama.
Abbu duk ya fad'awa Ammi abunda yake faruwa, Ammi tace"Gaskiya nima ban bada goyon bayan wannan al'amarin ba, Dole idan Allah ya kaimu a kara Jan kunne Hanifa da ta kiyaye babu ita babu Wannan yaro domin ba tsarin auran ta bane ni Sam ban ma yarda cewar tsakani da Allah yake sonta ba kawai dai akwai munufar sa insha Allah kuma Allah ya fishi." Abbu yace." Idan ba makaranta ba kar ki kara bari ta futa ko ina narasa a ina ya ganta har zai zo mun da wannan maganar." Ammi dai shiru tayi domin tana jin tsoron ta fada masa cewar a gidansu Abbakar ne tasan dole zai tambaye ta cewar dama tasan da maganar kenan shiyasa tayi shiru da bakinta.
Hanifa kuwa tunda taji maganar da Abbu yake yi ta mike ta zauna dungurgur gabanta na fad'uwa tana mamakin jin cewar wai MASHAHURI yazo gurin Abbu Neman auranta jin abunda Abbu din yace masa ne yasa taji wasu irin hawaye na kokarin zubo mata kwanciya tayi rigingine tana kuka sosai ita kam dama Abbu yayi hakuri ya aura mata shi domin ita bata son Ya Nasir jin zuciyarta na zafi yasa tq zura hannunta inda ta 'boye pastar shi ta dauko touch light ta kunna ta kurawa fuskarshi ido tana jin sonshi na 'kara yin k'arfi a cikin zuciyarta rungume pastar tayi tana sakin ajiyar zuciya haka bacci ya dauketa
****
Khalid kuwa duk ransa a 'bace ya koma gida kai tsaye part din iyayen sa ya nufa komai na duniya yana ji yayi masa daci bai ta'ba tunanin zai shiga irin wannan yanayin ba sai gashi lokaci guda rayuwar shi tana zo ta zama abun kallo kwana da yini babu abunda take tunani sai yarinyar wannan wace irin masifa ce take so ta rufto masa.
Alhaji Tijjani na zaune a katafaran parlor nashi yana kallon tashoshin Larabawa Mamy na gefen shi taci Uwar kwalliya kamar ba d'azu suka gama fada ba, shi kanshi Khalid din yayi mamaki shiyasa wani lokacin baya shiga sabgarsu sai su shirya su barshi a ciki. Ya shigo bakinsa dauke da sallama yanayin yanda yake tafiya cikin rashin kuzari yasa iyayen NASA mai da hankalinsu kansa har ya 'karaso ya zube kujerar da take kallon dad din nasa,
Alhaji Tijjani yace."Myson yanzu nake zancan ka a zuciyata domin d'azu mukayi waya da senotor yace kunyi magana dashi zakayi wa mai girma shugaban 'kasa wa'ka shine nace Wane irin tanadi yayi maka kafin ka shiga studion kasan dole sai ya zube maka ma'kudan kudi ko."?
Dad din nasa ya kalla yana jin sabon b'acin rai kullum yana fad'a masa cewar shi fa ba don kudi yake wa'ka ba kawai ra'ayinsa ce ya rasa ina dad din nasa zai kai kudi bashi da magana sai ta kudi idan da kudi suna magana a jikinsa to tabbas zasuyi a jikinsa domin yana da wasu irin mahaukatan kudi Wanda shi kanshi bai San iya adadinsu ba.
A ya mutse yace." Dad nifa duk ba Wannan ne yanzu a gabana ba, a halin yanzu babu wata wa'ka da zan iyayi idan ba burina ne ya cika ba kuma kullum ina fada maka bana yin wa'ka domin a bani kudi dad wa'ka ra'ayina ce kawai."
Alhaji Tijjani yace." To ni bazan Bari kud'in nan su wuce ni ba mutukar kayi musu wa'ka kamar yanda suke so zasu turo min kud'in ni ina so." Mamy ta kalleshi da mamaki! Tace" sai ka bari mai wa'kar yayi tukkuna ko." Dariya yayi yana kallon Khalid din da yake ya mutsa fuska cikin damuwa yace." Dad yanzu daga gidansu Hanifa nake naje domin in ganta mahaifinta ya hanani ganinta yana kawo min kauli da ba'adi dad kayi wani Abu akai don Allah."!
Alhaji Tijjani ya 'bata fuskarsa tare da fad'in"Wannan wane irin Mara rabo ne kamar ka kazo Neman auran 'yarsa ya tsaya yana shirme myson da alama dai Dan 'k'auye ne ko domin sune basu da hankali. " tab'e baki yayi yace." To waye ya sani dad ni dai abunda na sani kawai cewar shi din d'an Izalah ne gudanshi na gaba da gidan su Abbakar Abokin nan nawa."
Alhaji Tijjani ranshi ya 'baci in wai yarinyar da Dan nashi yake so d'iyar d'an Izalah ce kuma 'yar talaka ce saboda duk Wanda yake zaune cikin layin talaka ne sai mutum ya futo sosai zai fara karo da manya manya gidaje, amma baiji dad'i ba da Dan nashi yaje Neman auran 'yar talaka kawai Dan dai baya son b'acin ransa yasa zai kyaleshi ya aurta amma da badon haka ba bai ga ta yanda za'ayi ya had'a hanya da talaka ba.
0 comments:
Post a Comment