*51*
Ita kadai ya tadda a parlor tayi tsumu da ita, yace." Ina mamy ta barki ke kadai a zaune."!? Shiru tayi masa kawai tana kallonsa tana kokarin b'oye hawayen ta, yana kokarin hawa sama sai ga dady din zai sauko yace." Yawwa dad dama kai nake jira ka dawo Alhaji Tijjani yace." Dama tunda naga wayarka hankalina yayo gida." Kujera guda suka zauna Khalid ya kalli inda take zaune "My wife zo Ku gaisa da dady kinji ko." Alhaji Tijjani yayi saurin kallon inda Hanifa ke zaune yace"Myson ko itace labarin da zaka bani." Khalid yace." Shine Dady yarinyar Shaik na sona K'warai ta biyo ni inda nake dad ina so gobe idan Allah ya kaimu a d'aura mana aure da ita." Alhaji Tijjani ya fata murmushi yana kallon Hanifa dake sunkuyar da kanta kasa yace." Hak'ika so ba karya bane yarinya kin cika yar halak yau na tabbatar da cewa mahaifin ki shine bashi da ra'ayin aura wa yarona ke shine ya fakaice da cewa yayi miki miji Dan uwanki, kada kiji komai don kin rabu dashi kin dawo gare mu ni zan tsaya miki a kome na rayuwa tunda har kika iya SADAUKAR da farin cikin mahaifin ki akan Khalid nayi alk'awari kula dake har karshen rayuwar ki." Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ta goge da gefen hijab dinta.....Alhji Tijjani yace." Insha Allah gobe zamu shiga kotin musulunci domin su shaida da abunda yake faruwa na auran Dole da iyayen ki zasu yi miki kuma gaban Alkali zamu baki sadakin ki kamar yanda addini ya tanada al'kali da shaidu zasu shaida d'aurin auranku insha Allah."
Muryarta na rawa tace"Dady kayi hakuri don Allah ba sai mun shiga koto ba kwai a d'aura mana aure a gida." Alhaji Tijjani yace." Dole mu shiga koto dake domin ki samu wakilai bayan haka kuma alkali zai iya Neman mahaifin ki domin yaji ta bakin shi Idan kuma bai neme shi ba to dama haka muke so mu." Shiru tayi tana tunanin yanzu ko wane irin halin jama'ar gidansu suke ciki tasan dai yanzu sun fahimci bata gidan tana ji Khalid da mahaifin NASA suna hirar su tayi shiru gwanin tausayi....
****
Hannunsa rike da k'atuwar bak'ar Leda ya shigo Ammi na zaune ita kadai a rumfa yayi sallama ya shigo zama yayi suna kara gaisawa yace"Ammi INA Hanifa ne ga dinkunan nata yaya rabi ta kawo.' Ammi tace"Watak'ila tana sashen su Wasila ka duba ta can." Nasiru ya mike ya futo yaro yasa ya shiga ya duba masa ita minti biyu yaron ya dawo yace batanan." Gurin Inno ya nufa tana kashingide da redio a gabanta yayi sallama amsa tayi yace "Inno Hanifa bata shigo gurin ki ba." Girgiza kanta tayi yana fadin",Wace Hanifa kuwa yarinyar da sai taga dama take Magana duba ta sashen su Wasila" yace duk na dubata banganta ba wallahi."
Inno ta mike zaune tana fadin "Ka kara dai dubawa Tana cikin gidanan tunda ba wani gurin ta sani ba balle nace ko taje can." Nasir da jikinsa ya soma sanyi ya futa daga dakin inno yana duba ko INA na cikin gidan sako da loko
Hankalin sa ya soma tashi ya koma sashen su Hanifa lokacin itama Ammi ta fito tsakar gida sai sukayi kici'bus yace." Ammi yarinyar nan fa bata cikin gidanan don duk na duba ko ina banganta ba." Ammi bats dauki abun da tsanani ba tace"To ko an aikesu tare da Wasila ne."? Yace." Eto ban sani ba amma bari inshiga in duba da kaina." Sashensu su Waslar ya nufa tun kafin ya karasa shiga ya hango ta tana wanke-wanke karasawa yayi yana tambayarta Hanifa sai da ta gaishe shi sannan tace"Ya Nasiru tun safe rabona da ita dama yanzu nake cewa bari in gama abunda nakeyi na shiga gurins." Bai tsaya ya bata amsa ba ya juya da sauri ya bar gurin...... Ammi na tsaye a inda take ya fada mata komai to itama sai jikinta yayi sanyi tana mamakin ina hanifa zataje garin da batasan mutane ba a ciki.....babban tsakar gidan suka futo suna maganar hankalin kowa ya dawo Kansu Inno ta futo tana salati tare da fadin"kadda yarinyar nan guduwa tayi innalillahi wa'ina ilahi raji'un."! Ammi ma sai ta kama mai-mai ta Kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un cikin zuciyarta gabanta sai fad'uwa yake.....Maman su Wasila ta baza manya da yara su shiga makota ko ta shiga... Suna tsaye suna mamakin abun yaran suka dawo duk babu wani labari....... Halifa ne ya shigo gidan yana fadin"Nifa dazu misalin goma na safe na ganta ta nufi hanyar titi." Salati suka kama Inno Tace"Ashe tun safe bata cikin gidanan." ? Ammi kuwa tunani takeyi wato tun lokacin da tace mata zata je gurinsu Wasila jin rai dangin goro tun lokacin ta gudu Innalillahi wa'ina ilahi raji'un kawai take maimatawa cikin zuciyarta Inno tace"Maza aje a nemo Haruna duk inda yake." Nasiru yace?" Inno ko baki fada ba kuwa zan nemo shi domin ni shi nafi zarga." Kofar futa ya nufa sukayi kicibus da Harunan ya shigo.. Duk sai jikinsu yayi sanyi Haruna ya maze sosai kamar babu komai yace." Yana kunyi jugum jugum Me ya faru."!? Inno tace"Tun safe ake Neman kafurarar yarinyar nan me siffar Aljani ba a ganta ba don ni har na dauka ko Kaine ka dauke ta jin irin furucin da kayi kwanaki akan lamarin auranta da Nasiru."
Haruna yace." Nifa inno bana son irin wannan abunda kike min kawai sai in dauki Hanifa to in kaita ina.? Duk abunda ya faru da ita ai kune kuka jawo tunda dai kun ki Ku hak'ura Ku aura mata Wanda take so waya gayamu Ku ana auran dole a wannan zamanin gashinan kun jawo ta gudu." Inno ta hayayya'ko masa cikin masifa tace"Eh baza mu bari ta auri maro'ki ba domin roko ba gadon mu bane duk inda ta shiga ma zata dawo." Haruna wucewarsa yayi cikin gidan yana mita,.... Inno sai zagin Hanifa takeyi gami da surutai a kanta hankalin kowa na gidan ya tashi mussaman Ammi daurewa kawai takeyi tabbas tasan Hanifa zata iya aikata wannan danyan aikin.... Shiyasa ms bata Musa ba, sunan tsaye suna al'ajabin abun Abbu da Kawu Amadu Hafiz suka shigo dama tun a waje sun samo labarin abunda yake faruwa, Inno na ganinsu ta fashe da kuka tans fadin"Kunga abun kunyar da yarinyar ta jawo mana a gari ko? Ace ana ya gobe d'aurin auranta ta gudu yanzu wane irin kallo jama'ar gari zasuyi mana." Abbu ya jingina jikinsa da bango tabbas abunda Allah ya nuna masa a mafarkin sa ya tabbata shiyasa bai shiga rud'u sosai ba saboda sai da ya jera kwana uku yana mafarkin Hanifa ta gudu ya kalli Inno dake ta faman share hawaye tana surutai yace." inno ki kwantar da hankali don Allah ki bar wannan koke koken duk abunda kika ga ya faru to dama daga Allah ne ni dai fatana duk inda yarinyar nan zata shiga to Allah yasa ta fada a hannu nagari kuma Allah yasa ta gane abunda muke taso mu nusashe da ita Hak'ika Hanifa tayi kuskure kuma ta aikata aikin k'uruciya ina so dani da Ku duka muyi hakuri mu barwa Allah lamarin sa domin yafi mu sanin abunda yake lullub'e insha Allah zai warware mana wannan komai." Inno tace"Munzali duk naji maganarka kuma na gamsu ni babban abunda yake damuna shine maganar d'aurin aure yaya za'ayi jama'a sun sani suna jiran lokaci mun raba goro wannan Abu da akwai kunya Wallahi. " Abbu yace." Baza'a FASA d'aura aure ba insha Allah Shi Nasiru ya duba wata cikin yan matan dake cikin gidanan sai a d'aura masa auran da ita." Inno tace"Insha Allah haka za'ayi." Abbu yana gama maganar sa ya shiga ciki ya barsu suna jajanta al'amarin. To ko da Nasiru yaji maganar da Abbu yayi kan ya zab'i waya cikin dangin yasa yayi shawarar zaben Wasila domin yaga suna yanayi da Hanifa a halin yanzu yana jin ko Hanifar ce ta dawo bazai iya auranta ba saboda zarginta da shiga zuciyarsa, daddare ya Sanar Abbu cewar ya amunce a d'aura masa auran da Wasila Abbu ya dunga sanya masa albarka ita kuwa Ammi daki ta shige taci Ku kanta ta koshi tana jin duk duniyar tayi mata zafi Ashe zata haifi yarinyar da zata iya bujerewa bukatar su ta gudu kan da namiji kuka take sosai Abbu na rarrashinta da fadin addu'a ya kamata tayi wa Hanifar ba kuka ba Ammi tana ji a zuciyarta baza ta taba yafewa Hanifar abunda tayi musu ba.
****
'B'angaran su Khalid kuwa shi da dad dinshi sun gama yanke hukuncin komai Mamy na jinsu duk irin maganganun da take uffan batace ba balle dady din yayi mata cin mutumci abunda tasani shine kawai yarinyar ta jefa kanta cikin matsala ta San halin Khalid irin na mahaifinsa ne zata fuskanci takaicin da namiji tunda ta amunce da bukatar su ita dai yar kallo ce kuma kome zasuyi babu saka hannunta tunda sam-sam tarbiyar yarinyar batayi mata ba ballanta ta tagaza wani Abu kan lamarin ta dai zuba musu ido kawai..... Da tagaji ma da zantukansu sai ta mike ta haye sama abunta... Minti goma tsakani dady shima ya mike ya bar Khalid din da Hanifa gurin da take ya koma nanikar ta yake yana fada mata kalamai masu dad'i ita dai jinsa kawai takeyi jikinta duk yayi sanyi idan ta tuno gida sai wasu hawayen su zubo mata haka ya dunga rikita ta da salon soyayyarsa tas yake lashe hawayen da harshen shi ya rungume ta kam yana lallab'ata dole tasa tayi shuru ganin lamarin NASA yana nema ya wuce gona da iri..... Wani bedroom dake cikin parlor ya shiga da ita zauna da ita yayi kan bed din yana shishshiga jikinta sai wani lumshe ido yake. A hankali tace"Don Allah ka bari kaje ka kwanta nima bacci zanyi." A kasalance yace." Um-um! Ni anan gurin ki zan kwana ina son jin dumin jikin ki." Girgiza kanta tayi gwanin tausayi cikin shagwaba tace"Nifa abunda yake hadani da Kai kenan,, yanzu meye yayi saura gani gaka Insha Allah Idan ka kwantar da hankali nu mallakinka CE, jikina yayi sanyi da irin kallon da Mamy ke min shiyasa banaso kake shige min." Dago kanshi yayi taga ya hade fuska kasa tayi da kanta, yace." Kawai dan rabi jikin ki shine wani Abu wai me yasa kike da duhun kai ne auran ki fa zanyi idan da nayi nufin cutar dake da bazan tsaya kai da fata nace dole sai na aure ki ba zaki dinga fada min maganar banza." Idonta ya kawo ruwa jin maganar da yake mata daga ni a hasale yake. Tace" nifa ban fadi maganar don ta bata maka rai ba kawai nace ka daina ta bamin jiki bana so irin kallon da momy ke min." Tsaki yaja ya mike ya futa daga dakin a fusace! Kallo ta bishi dashi cike da mamaki meye abun daukar zafi a wannan maganar kawai daga ta fada masa abunda ya dace. Lallai akwai aiki a gabanta, kwanciya tayi kamar wata marainiya wata irin yunwa na cinta ga tunanin halin da gida yake ciki haka ta dunga share hawaye har bacci ya dauke ta.
***
Misalin 'karfe goma sha biyu na dare yaje ya dauro alwala ya dawo cikin dakin lokacin karfafan bacci ya dauke Ammi da taimakon addu'a da yayi mata dadduma ya shimfid'a ya tada sallah raka biyu yayi yayi sallama kana ya koma sujjada ya Dade yana kwararo addu'a wacce duk rabinta ta hanifa ce da nema mata sauki a duk kanin al'amuranta sannan yana rokon Allah yasa ta fada hannu na K'warai ya kuma juyo da hankalinta gida.... Sosai yake rokon Allah bukata kafin ya dago kansa nan ma ya k'ara daga hannun sama ya dunga kwarara addu'a tsawon mintuna ashirin ya shafa, mik'ewa yayi ya nufi gurin kwanciya zuciyarsa tayi sauki sosai daga damuwar da take, cikin ikon Allah yana kwanciya bacci ya dauke shi.
Asubah ta gari Abbu....
****
Wani irin bacci tayi Mara dad'i Wanda yasa ta tashi tsakiyar dare tana kuka Mara sauti cikin wani irin yanayi na damuwa taga Ammin ta abun ya daga mata hankali sosai ga damuwar da ta kwanta da ita na b'acin ran khalid din tana zaune har asubah tayi ta mike taje ta dauro alwala tazo ta tada sallah, addu'a take sosai tana kuka ita kam Yanzu duk kanta ya daure ta rasa meye mafuta a rayuwarta..... Kwanciya tayi kan daddumar bacci ya dauke ta Mai nauyin gaske...... K'arfe goma da rabi ya na safe ya bude dakin ya shiga, ganin ta kwance a kasa tana bacci yasa ya karasa gurin, tsuganawa yayi kusa da ita yans jawo kafarta dake lullub'e da hijab firgigit ta mike zaune ganinshi kusa dai ta yasa ta saki a jiyar zuciya kallonta yake babu walwala yace." Kinyi sallah."!? Daga kanta tayi bata son kallonsa saboda yanayin kayan da suke jikinsa singilet ce fara tas sai boxer duk suffar jikinsa a waje gargasa duk ta rufe masa fata..... Ido ya zuba mata yana kallo, ita kuma sai motsi take da bakinta da kyar tace"Ina kwana."? Ajiyar zuciya ya sauke yace." Lafiya lau kefa." Shiru tayi yace." Kwayar idonki ta nuna min da cewar jiya kin kwana kina kuka hakane ko?". Shiru tayi girgiza kanshi yayi yana sakin murmushi yace." Ki futo Ku gaisa da Mamy sai ki shirya zamu wuce koti yanzu domin ina so ayi komai a gama cikin satinan zamu wuce america tare." Jiki a sanyaye tace." Nifa nace baza ni wani koti ba kawai a d'aura auran a haka." Shan kunu yayi yace." Kina da wakili ne anan."? Shiru tayi yaja tsaki tare da fadin"Na lura kina da taurin kai ni kuma bana so in fad'i magana ana musa wa kawai kiyi abunda nace." Yafad'a yana mik'ewa tsaye..... Hanyar futa ya nufa ta bishi da kallo tana kokarin boye hawayen idonta. Juyo wa yayi yace." Ok baki me nace ba nace kizo Ku gaisa da Mamy kiyi break fast, sai ki shirya ko." Mik'ewa tayi jikinta duk babu kuzari ta biyo bayansa.
*20/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*46*
Abbu ya zauna kusa da matar tashi yana tambayar abunda yake faruwa ganin ko da ya shigo din Hanifar bata bar kukan da take ba, Ammi tace"Babu komai Abbu Inno ce ta shigo tana fad'a shine nake 'k'ara ja mata kunne ta kiyaye domin bana son abunda zai jawo min abun magana ko kuma ya shiga tsakanina da mutanan gida nace ta kwantar da hankalinta." Abbu ya sauke ajiyar zuciya tare da fad'in"Halima komai yayi tsanani maganinsa Allah amma ni kam lamarin nan yana damuna Wallahi kullum cikin istahara nake ina jin hankalina na kara kwanciya da auranta da Nasir jiya kuma kafin mu tawo nan din nayi wani irin mafarki akan lamarin hakika mafarkin ya bani tsoro to amma nasan shi mafarki ba gaskiya bane Duk da haka na barwa Allah lamarin ya zama mana abunda yafi alkairi." Ammi tace"Ameen suma ameen bari a kawo abinci Yanzu inno ta ta kawo." Abbu yace." Wannan tsohuwa Allah ya kara mata lafiya ubangji Allah ya ja mana da ranta Hak'ika Tana zumunci Allah ne kawai zai biya ta. " Wasila ce tayi sallama ta shigo yarinya 'yar fara bafulatana kyakyawar gaske kana ganinta zaka gane kamaninsu da Hanifa sai dai Hanifa tafita cika da wayewa da fara'a ta shigo jikinta sanye da uniporm tana fadin"Abbu sannu Ku da zuwa ina makaranta sai Addu'a nake a tashi na dawo gida." Ammi ta saki fuska Tana fadin "Wasila kece kika zama haka."? Hannu tasa ta rufe fuskarta cike da kunya, Abbu na murmushi Yace." Ke ko Halima ai ba yau aka haifeta ba tsakaninsu da Hanifa babu yawa." 'Kwarai kuwa Hakane Hanifa na da wata hudu aka haifeta yanzu shekarunsu goma sha bakwai kenan ." abbu yace." Wasila ya makaranta ina babanki."!? Tace." Abbu yana gurin aiki amma nasan dai yana kan hanya." Abbu yace." Munyi waya dashi muna kan hanya yace yana gurin aiki dama.Wasila ta kalli Hanifa dake takure a gefe guda taki kallonta bare sugaisa 'kawarta ce ita idan sukazo garin ma a sashensu take kwana shashen Baba Amadu kenan Wanda ya kasance kanin Abbu uwa daya uba daya...... Wasila ta mike tana fadin"Hanifa zo muje sashenmu muci abinci." Kamar baza ta mike ba kuma sai ta tashi tana gyara hijab din jikinta suka futa daga dakin.
Suna shiga b'angaran su Wasila mamansu ta fara yiwa Hanifa wani irin kallo ita kanta Hanifar ta lura da kallon tsarguwa tayi ta nemi guri ta zauna tana sadda kanta 'kasa tana gaisheta sakin fuska tayi tana amsawa take fadin "Ai d'azu Ashe bamu gaisa ba ko."!? Hanifa ta daga kanta Wasila ta futo daga dakinsu ta sanja kaya tana fadin" mama abinci na kicin ko."! Tace"Ki bude Fula's ki debo muku wainar shinkaface." Futa tayi da sauri, Ita kuma mamansu wasila ta cigaba da kallon Hanifa k'asa-k'asa har sai da ta dago idonta suka hada ido sai kuma ta wayance tana mik'a mata wata roba me fad'i gyada ce a ciki marau tace"Hanifa ci gyada kinji ko." Girgiza kai tayi Alamu bata fi ta fara tsarguwa da irin kallon da take mata, Wasila ta shigo dakin da kwanoni biyu a hannunta ta aje gaban Hanifar ruwa taje ta debo cikin jug ta dawo ita kuma Ummansu futa tayi tsakar gida ta cigaba da hidimar yaranta..... Hanifa cin abincin kawai take badan ranta na so ba Ita kuwa Wasila sai hira take mata wani ta amsa wani ta share sai da suka gama cin abinci ne Wasila tace"Nifa na kagu lokacin bukin Ku da Yaya Nasiru yazo domin nayi tanadi me kyau wallahi shagali zamu sha." Wani irin kallo ta watsa mata kasa daurewa tace"Wasila karki kara yimin wannan maganar kinji ko."! Wasila tace"Saboda me."? Kawai bana so."! Tafad'a ranta a Dan bace! Gyada kai Wasila tayi tace"Yar uwa Wai da gaske ne don Allah abunda nake ji kinfi son bare kan Dan uwanki haba Hanifa meye laifin Nasiru. "
Tana d'an hararata tace"Wasila idan ke kina sonshi don Allah ki aure shi ni kam bana sonshi akwai Wanda nake so." Wasila tayi shiru tana mamakin maganar Hanifa tace"Dan uwanki ne fa."! A hasale tace"To Dan Dan uwanane kawai sai in cuci kaina wallahi ko an aura minshi sai na bashi wahala sai ya sake ni lokacin da bai shirya ba.... Karaf a kunnen mamansu Wasila sai tayi kamar bata ji ba ta shige daki ta dauko abunda zata dauko ta futo.... Wasila kam mamakin maganar Hanifar take ita a ganinta kamar Nasiru had'addan saurayi wace mace zatace bata sonsa..... Cigaba tayi da cin abinci tana tunanin al'amarin Hanifa tace''idan kina so mu shirya dake to Kar ki kara yimin irin wannan maganar ni yanzu mafuta kawai nake nema." Wasila tace "na daina Insha Allah amma zan tayaki da addu'a Allah yq zama miki abunda yafi alkairi." Ameen tace tana jin zuciyarta tayi Dan yi sanyi suka cigaba da hirarar yan uwansu.
****
Da kyar ya Kai kanshi gida cikin wani irin hali ya shiga parlor Mamy na zaune tare da Momy Nasrin da ita kanta Nasrin din suna hira Mamy ta mike da sauri ganin yanda ya shigo mata kamar zai fad'i ga bakinsa duk ya bushe idonsa ya kada yayi jazur. Hannunsa ta rike cikin damuwa take fadin"Myson yanzunan nagama kiran wayarka bata shiga ba wai ina kajene nifa bana son abunda zai tayar min da hankali myson wannan wace irin rayuwa ce ka jefa kanka ciki umm!? Yarinyar nan wai ita kadai CE mace a duniya."!? Mamy ta karasa maganar cikin damuwa...... Da kyar ya iya furta maganar "Mamy ba ita kadai bace hasali ma akwai wad'anda suka fita komai na rayuwa narasa abunda yasa zuciyata ta nace mata Mamy wai ko mayya ce ne."!!!! Ya fadin maganar Cikin sarewa da kuma gajiyawa da al'amarin kana ganinshi zaka fuskanci yana cikin damuwa me tsanani." Mamy tace"To waye ya sani myson muje ka zauna." Ta kama hannunsa suka nufi kujera tana fadin "Mutane ne kawai an gansu a unguwa ba'asan daga ina suke ba ni kam Allah yasa yarinyar bata lashe maka kurwa ba."! Ta fada cikin damuwa. Zama yayi yana kallon su Dishi-dishi Nasrin yake kallo da mamanta yace." Mamy wacece wannan."!? Momy Nasrin ta dafe k'irjinta cike da mamaki tace"Ni din ka manta Khalid."!? Nasrin ya kalla wacce ta zuba masa ido tana kallonsa cike da so da kauna yace." Mamy wannan yarinyar ma ban Santa ba."! Hajiya Zainab tayi salati tana Sanar da ubangji tace"Anya kuwa yaron nan na cikin hayyacin sa kuwa."!? Mamy kam hawaye ta fara sharewa tana fadin"To waye ya sani ko yarinyar nan ta kashe masa kurwa innalillahi wa'ina ilahi raji'un.! " Mamy ta fada da wasu hawaye na zubo mata domin abunda Khalid din yake yi kamar wani Mara hankali....... Lokacin da yaga Mamy na kuka ne ya dawo hankalinsa ya tsani yaga Tana kuka tamvayarta yake meye take kuka."!? Hakan ma sai ya kara daga mata hankali jiki na kyarma ta dauki wayarta ta fara Neman numbar mijin nata tana ganin gwara yazo suje a duba kwakwalar Khalid kwr abu yayi nisa bugu guda tayi ya dauka bakinta na rawa ta fada abunda yake faruwa cikin rashin hakuri irin nasa ya rufe ta da masifa kamar yanda ya saba kashe wayar tayi ta zauna tana kallon Khalid din da yake kallonta fuskarsa a Dan hade yace." Mamy wai meye naga kina ta wata magana Don nace bangane Momy Zainab shine kika tayar da hankali, nifa ina cikin hankali itama Nasrin din na ganeta yanzu."!
Mamy shiru tayi masa kawai suka cigaba da hira da Kawarta mik'ewa yayi ya futa daga parlor yana jin damuwa cikin ransa shi har ga Allah bai San sanda yayi maganar cewa bai gane su ba amma yaga mamy ta dauki maganar da muhimamci Why!! Soyayyar da yakewa yarinyar Shaik tana nema ta mai dashi zautace yanzu ya fara tunanin wannan abunda yakeyi sone ko kuma sha'awa."? Allah ne ya barwa kansa sani.......... Yana kokarin shiga toilet ne Nasirin ta shigo dakin nasa kayan da suke jikinta suk futo mata da suffarta domin ita tana da wadatar nono amma basu kai girman na Hanifa ba kuma tana da garun jiki irin na hanifa sai dai tsarin jiki me kyau Hanifa tafi ta..... Tsura mata ido yayi tun kafin ta karaso gurinsa kasa tantace wacece yayi domin idanunsa sai suke masa gizo yana ganin kamar Hanifa ce ta dawo wata zuciyar tace itace watak'ila ta gudarwa iyayenta ne, murmushi yake saki har Nasrin ta karasa kusa dashi kafin ta Ankara ya kai mata wawuyar runguma ya matseta tsam! A jikinsa yana sauke ajiyar zuciya lasar fatar wuyanta yake yana kokarin zuge mata zif! Din rigarta.... Nasrin ta gigice tana ture shi daga jikinta a gigice ya kwantar da ita kan bed din ya haye kanta bakinta yake kokarin kamawa yasa ana shi Nasir kuwa yanda tayi laushin fatar jikinsa da yanzu gashin k'irjinsa yake tsikarar jikinta dake yana daure da towol ne iya cinya sai ta fara lanjarewa tana sakar masa jiki da kanta ta kamo bakinsa ta ta fara kiss dinsa Lokacin da ya fara tsotsar bakin nata ne yaji ba irin test din su daya da Wanda ya saba tsotsa ba wancan yayi laushi yafi sugar da Zuma idonsa ya bude Wanda suka kada suka juye suka zama kamar na mashayi ya zubasu kanta, Nasrin ya gani tana ta kokarin mai da bakinsa nata, yayi saurin mik'ewa yana gyara towol dinshi Dan bata fuska yayi yana kallonta ita kuma tana kallon faffadan k'irjinsa me sanya mata haukacewa mik'ewa tayi zaune yace." Ke dama bake bace. "!? NASIRIN ta bata fuska tana fadin" Bangane ba." ? Sosa kansa yayi yace." Owk na dauka fa ita sorry bari inyi wanka in futo kinji ko."! Hanifa taji kamar ta kurma ihu! Lallai ma guy nan wato da bai ganeta ba shiyasa ya rungume ya dauka budurwarsa ce take taji wani irin masifar kishin Hanifa ya dura a zuciyarta.
Wanka Yayi ya futo a gurguje tsaye Yayi gaban dressing mirror dinshi yw gama shafe-shafensa NASIRIN na zaune tana kallonsa ko kunya babu sai kallonta yake ta mudibin yana mamakinta bayan ya dauko kayan shi ne ya nufi wani kebantaccan guri ya shirya tsaf ya futo har ya karaso tana kallonsa kusa da ita ya zauna yana lakuce mata hanci yace." 'Yar lukuta taga had'addan guy ta gigice wai yane."!? Bata fuska tayi domin yanzu ba Lokacin wasa bane tace." Khalid naji kanayi min wata magana wai har ka manta da alk'awarin da kayi min ne."!? Dan kallonta yayi ya dauke kansa yana d'aura a gogo a hannunsa Yace. " wane al'akawari nayi miki 'yar lukuta."!? Hummm! Naga kamar kana nema ka manta ne idan kai ka manta ni ban manta ba karfa ka manta Kaine ka koya min yanda zan soka tun ina yarinya kankanuwa zuciya ta makance akan sonka na tafi karatu da soyayyar ka bayan kayi min alk'awarin aure na amma sai na samu labarin gurin Momyna wai ka ma manta dani."!! Ido ya Dan zaro yana kallonta da mamaki yace." Ni ne nayi miki alk'awari kuma yaushe bana son tsari."!! Kuka tasa tace"watarana da kazo gidanmu idan parlor mu na magana zai fada maka wallahi kayi min alk'awari zaka aure ni." Dariya yasa yana nuna ta da hannu yace." Mybe Lokacin kin dame ni da rigima ne kin San fa a lokacin ni kamar tom and jerry nake kallon ki in kina wani shirmen inyi dariya in more gaji yar lukuta ni kam ban miki alk'awarin aure ba ko nayi ma to wasa nake miki." Cikin kuka tace"Kar muyi haka da kai Khalid Wallahi INA sonka kar ka yarda wata ta shiga tsakaninmu." 'Bata fuska Yayi da damuwa yace." Ai maganar wata ma ki aje gefe ta shiga tsakanina da kowace mace ciki kuwa harda ke ni ko ina jin mayya na had'u da ita ban sani ba."! Da damuwa ya fadi maganar." Nasirin tace"Don Allah ka rabu da wannan yar talakwan Wallahi ba ajinka bace." Kafin ya bata amsa wayar shi tayi k'ara yana dubawa yaga no dad dinshi dauka yayi da sallama a bakinsa, Ya mike da sauri yana fadin"Dady ganinan futowa." Nasirin ta mike tabi bayanshi suka futa tare..............
*15/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*45*
Tunda ya tashi yake jin rashin k'arfin jiki haka dai ya daure ya karya Mamy nayi ta masa labarin Nasirin duk a kokarin ta na ta janye hankalinsa kanta shi kuwa yana can tunanin Hanifa ya kwana shida kenan Rabonsa da ita, take yaji yana sha'awar ganinta wayarsa ya dauka dake aje kusa dashi sai a lokacin ma ya tuna bai kunnata ba kunnawa Yayi ya fara neman no Abbakar bugu daya tayi ya dauka Yana fad'in "Guy gamu nan nida Mobson mun shigo unguwar taku." Khalid yace." Meye ne naji muryarka a sama."!? Abbakar yace." Tun d'azu nake kiran wayarka amma aka she babu lafiya Ya shaik ya tattara iyalinsa sun bar gari."! Khalid ya mike tsaye da sauri! Saura kad'an ya fad'i"Hannunsa na kyarma yake fad'in"Da gaske kake Abbakar."!? Abbakar yace." Wallahi a gaban idona suka nufi tasha ni ban San abunda yake faruwa ba kawai sai gani nayi yara da manya sun cika a waje suna kallonsu irin surutun da suke yi ne ma na fahimci abunda yake faruwa." Jiki ka kyarma yake kokarin futa. Mamy tace." Ina zakaje ne Myson wai me akace maka ne naga duk ka gigice. "! Waiwayo wa yayi muryarsa na rawa yace." Mamy wai Shaik ne ya gudu daga gari saboda ni, bai sai duk inda zai shiga a fadin duniyar nan sai na binkito su Wallahi bai isa ba." Mamy ta mi'ke da sauri tana kokarin kamo shi ganin yanda jikinsa yake tsuma sai abun ya bata tsoro ta wani gefen kuma taji dadin hakan amma kuma yanda taga ya tada hankalinsa yasa take jin tsoron kar ya fad'i irin ranan..... Kokarin rike hannunsa take ya fuzge da k'arfi ya futa bayansa ta bi taga ya nufi ma'adanar motocinsu ya shiga da sauri yake kokarin futa tsaye tayi a bakin kofa tana yi masa addu'a tsari.
Yana futa mashing dinsu Abbakar na shigowa layin kawai sai ya tsayar da motar sukayi parking din mashing din a gefe guda dake unguwar GRA ne akwai tsaro sosai shiyasa Mobson bai damu ba suka shifa motar Khalid din da gudu yaja suka bar gurin. Sai da suka hau kwalta sosai Khalid din ya kalli Abbakar murya a sanyaye yace." Wane gari ne ma."? Abbakar yace." Gombe ne.'''''' Muryarsa na rawa yace." Muje tasha ko zamu same su." Mobson yace." Guy ka nutsu mana naga sai wani rawar jiki kake yi yanzu idan mukaje tasha kuma muka Tarar basu tashi muce musu me? Bamu fa da hurumin da zamu hanasu tafiya."!
Gefen titi ya tsaki da motar ya d'ora hannunsa akansa kusan minti biyar babu Wanda yace komai ya d'ago kansa idanunsa har sun sauya kala yace." Mobson kaina duk ya kulle Wallahi meye mafuta ne."!? Mobson yace." Baka da wata mafuta guy dama da dai mun riskisu ne to zamu iya rusa tafiyar idan muka ja hankalin yarinyar yanzu kuwa ko munje gombe bamu San wace unguwa suke ba kawai zamu wahalar da kanmu ne." Khalid ya daki! Kan mota da 'karfi! Muryarsa a sama! Yace." Mobson bafa Zan k'yale yarinyar nan ba sai na biyawa kaina bukata Wallahi. " Mobson ya d'anyi dariya tare da dukan kafad'unsa yace." Guy Kaine ka tsaya wasa Wallahi wai dole ne sai ka aure ta sannan zaka biya bukatar ka wace irin damace baka samu a kanta ba kawai ka zuba ido kana kallonta ni Wallahi ma haushi ka bani gashinan Yanzu sunyi ciki dai sun Barka da cizon yatsa."! Mobson ya k'arashe maganar cikin jikn ciwon abunda Khalid din yayi......Abbakar yace." Guyz ina ganin abunda yafi kamata muyi kawai mu koma gida mu shirya shawarar me za'ayi zan shiga gida in d'an bubbigi cikin babarmu insha Allah zata 'karamin haske Kansu domin ita mahaifiyar Hanifar suna mutumci watak'ila ma tasan ko a wace unguwa take a garin gombe."! Jin abunda Abbakar din yace." Yasa Khalid din ya sauke ajiyar zuciya babu yanda ya iya ya juya kan motar suka nufi gida sai yanzu yake takaicin rashin bawa Hanifa waya yasan yanda take sonshi zata fad'a masa komai shi kuma ya dauki mataki.
Shagon mobson suka yada zango Khalid ya kwanta kan katifa kamar wani maraya lumshe idonsa yayi yana jin wani irin zafi cikin zuciyarsa babu shakka Shaik ya shammace shi, juyi yayi hade da lumshe ido yana tunano suffofin jikin Hanifa da ya tuno lafiyayyar fatar jikinta da k'irjinta ya saki nishi tare da kankame pillo yana cije bakinsa, shi kadai yake wannan budurin a shagon lokacin Mobson ya tafi yi musu take awaye shi kuma Abbakar ya shiga gida gurin babarsu yana bugun cikinta kamar yanda ya fad'a. "Wai kai me yasa ka damu da sanin ko a wace unguwa suke ne."? Babar tasu ta fad'a tana kallonsa cikin tuhuma."! Shafa kansa yayi yana 'yar dariya yace." Umma ai ko babu komai anyi zaman mutumci kuma kinga watarana zamu iya kai musu ziyara." Asalamiyya tace"E wallahi Ya Abbakar in zakaje kaje dani. Yace." Ki bari tukkuna mu San unguwar sai muje Insha Allah. " Babar tasu ta kalleshi a nutse tace"Ni kam ban San unguwar da suke ba a gombe nasan dai 'yan garin ne amma duk zaman da mukayi da Halima ban taba tambayar ta wace unguwa suke ba." Abbakar yaji kamar ya kurma ihu! Shifa ganin tayi shiru tana tunani sai yake ganin kamar zata fad'a masa ne. Futa yayi daga gidan yana Jan tsaki! Shagon mobson ya nufa ya tadda Khalid din yana mur'kususu a kan Katifa, jajaen idanunsa ya dago dasu yana kallonsa Abbakar sai yaji shakkar fad'a masa abunda yake faruwa ya mike zaune da kyar muryarsa a har had'e yace." Meye labari Abbakar ina fatan ta fad'a maka wace unguwa ne yau din nan zamu dauki hanya. " Abbakar yace." Wallahi tace bata sani ba."! Khalid ya sunkuyar da kansa yana jin wani irin takaici duk ya shiga damuwa cikin wannan halin Mobson ya shigo ya same su, zama yayi yana bude abinci yake fadin"Ku bari in gama cin abinci akwai shawarar dana yanke insha Allah. " Shuru sukayi Mobson ya fara cin abincin sa hankali kwance sai gyada kansa yake da'alama yana jin dad'i wa'kar da yake ji ya Cikin eirpiz dinsa Khalid duk haushin sa ya kamashi ganin yanda yake walwala yasa ya buga matsa tsawa "Wai meye Hakane ? Mutane na Cikin bakin ciki kai kana wani gyada kai babu abunda ya dame ka, ka San halin da nake ciki kuwa."!? Mobson yace." To ya kake so nayi? Aini babu Wanda nake jin haushi irinka da ka samu dama kaki ka dama Ya shaik din banza wallahi kana da damar da zaka biyawa kanka bukata da yarinyar ba tare da kowa ya tuhumeka ba tunda ita ke kawo kanta gurinka amma ka tsaya kabawa Gayu kunya mtssssss."!
Khalid ya rintse idonsa cikin damuwa Yace. " Guy nima sai yanzu na gane na tafka kuskure da ban nunawa Shaik din ni waye ba har sai da ya samu galaba a kaina amma babu komai zamu sake haduwa ne, kawai kayi ka fad'amin me zanyi Yanzu kaina duk ya kulle wallahi."
Abbakar ya dauki leda guda ya futo da take away din ya bude ya fara ci yana kurbar Lemo Khalid ya dunga binsu da kallo Cikin mamaki wato su abinci ma suke ci babu abunda ya dame su Kansa ya dafe yana sauke ajiyar zuciya.
Mobson ya goge bakinsa da tissue ya kalli Khalid da kansa yake a sunkuye yace." Guy abunda za'ayi kawai kazo mu shiga studio yanzu ka ragargaji Shaik ka shirya masa wa'ka ta tozarci kan rabaka da yarinyar sa da yayi nasan wa'kar ka babu inda bazata shiga ba INA ganin idan kayi haka jama'ar gari zasuyi tur dashi kuma ko a garin nasu nasan kowa zaiga laifin sa ita kuma Hanifar hankalinta zai tashi nasan a lokacin zata kara rikice musu da koke koke to ina mai tabbatar maka ta dalilin wannan wa'kar da kayi zaka samu mutane masu kiranka a waya dayi maka jaje insha Allah zaka samu Wanda zai ce maka ya sansu yasan a unguwar da suke, ina fatan ka fahimce Ni. " Khalid yayi shiru yana nazarin maganar Abbakar yace."Gaskiya Mobson kwakwalwarka tana ja sosai wannan shawara tayi kyau nasan daga zuwa gobe da jibi wa'kar nan ta futa to zata watsu a gari har taje garin da suke Khalid yana da masoya sosai dole za'a samu wannan zaice yasan asalin Shaik din kaga sai mubi ta kanshi kawai......Ajiyar zuciya ya sauke ya Dan samu sassauci a zuciyarsa yana ganin wannan ma damace yace." Ku tashi muje." Mobson yace." Ka zauna kaci abinci tukkuna." Wani irin kallo ya watsa masa Mobson ya mike da sauri yana dariya suka fuce daga shagon.
*****
Kuka 'k'asa-k'asa takeyi cikin motar tabi ta takure kanta gefe guda saboda tsabar kukan da takeyi kanta sai wani irin ciwo yake mata, tana jin yanda suka sake suke ta hira abunsu babu Wanda ya damu da ita Ammi ma Sam bata so su hada ido, sai take ganin kamar rayuwarta tazo karshe tunda kowa ya juya mata baya sun kasa fahimtar halin damuwar da take ciki kuka takeyi zuciyarta nayi mata wani irin zafi lokacin addu'a takeyi kan Allah ya dauki ranta ta huta da wannan masifar da take ji cikin zuciyarta
Haka suka isa garin nasu na gado...'yan uwa da abokanan arziki sun tarbe su kowa sai murna yakeyi haka suka nufi family house d'insu Wanda ya kasance babban gida na b'angare-bangare dama tuni an gyara musu shashensu sai suka dunga shiga da kayansi ciki Hanifa kan rakubewa tayi a gefe tana kallon yanda yan uwa suke ta kai kawo wasu daga cikin su fad'i suke sunji dad'i da Abbu din ya dawo gida tare da iyalinsa k'aton daki ne ciki da rumfa sai tsakar gida mai dai-dai ci da kicin da band'aki wadatattu ko ina an shafe shi da sabon fainti cikin dakunan kuma Leda ce sabuwa dal da sabuwar katifa da labulaye sai agogon bango dake mak'ale a bangon daki.... Dakin sai k'amshin turaran wuta yake Ammi ts shisshigar musu da jakar kayansu ciki ta futo tana duba gidan mamaki take sosai ganin yanda yan uwanta suka siya mata komai na bukata kicin din sabbin tukwane ne da saitin Fula's har guda uku kai duk dai abunda zata bukata gurin girki da akwai shi hawaye ta share tana godewa Allah da ya bata yan uwa masu zumunci Inno ce ta shigo ita da wani yaro a bayanta hannunsa da dauke da k'aton faranti Jere da kayan abinci ta Kalli Hanifa dake rakube a gefe tace"Ke kuwa wannan yarinya anyi me bakin hali kowa yana murna ya shigo cikin yan uwa ke kin zauna kina nukufurci."
Hanifa ta sunkuyar da kanta kasa tana turo baki Inno ta cigaba da cewa"Kafura me wata irin suffa a fili kamar mutuniyar arziki amma a zuciya sharrin ki yafi na wata babbar macan yarinya k'arama dake kike kokarin zubar mana da mutumci." Ammi ta futo daga kicin tana fadin"Inno sannu."! Kallonta tayi tace"Inanan ni dai wannan 'yar taku me kai kamar na goriba ai wallahi naso Munzali ya karya mata k'afafun da take bi gurin saurayi." Cike da mamaki Ammi take kallonta tana tunanin a'ina taji maganar. Domin taji ribar zancan tace"Allah dai ya kyauta Inno shigo daga ciki mana." Tab'e baki tayi tace"A'a ni dama abinci na shigo na kawo muku in juya b'acin ran wannan yarinya yasa ni na tsaya dama kuma yanzu Nasiru ya futa daga gurina duk ya zayyane min abunda ya faru wato itace ma tayi silar sawowarku cikin dangi Ashe."!? Ammi tace"Sai addu'a al'amarin Inno yanzu dai magana ta wuce mu Baro garin da yaron yake kinga Dole ta hak'ura." Inno tayi k'wafa tare da fadin"Karma ta hak'ura auranta da Nasiru tabbatacce ne da yardar Allah."! Kofar futa tana nufa tana mita.... Inno dai matar Kawu Yahya ce Kawun da ya ragewa Su Abbu kenan macace mai masifar fad'a bak'ar magana hakanan surikanta da suke cikin gidan suke hakuri da haleyenta yanzu ma da shekaru suka kara yi mata yawa abun sai ya kara yin tsayi amma kuma tana da kirki da zumunci, kome ya fari tana tsaye kan lamarin mutum, tana jin Munzali wato Abbu cikin ranta sosai saboda yana mata biyayya kuma yana bukata mata ko da suke kano idan yayo aike ita ke rabawa yan uwa shiyasa take ji kamar itace ta haife shi...... Ammi daki ta shige tana mamakin abunda Nasiru yayi yanzu meye amfanin fad'ar maganar a ganinta idan ya sirrinta asirrin matarsa kansa ya rufawa asiri tunda shine zai aureta bai kamata ya futo da maganar ba ta Dade sosai maganar na damunta kuma ranta ya b'aci yasa ta daga murya ta kira Hanifa dake zaune ita kadai a tsakar gida.... Simi-simi ta shigo cikin dakin kanta a kasa ta zauna gefan ta, Ammi ta jima tana kallonta tausayi ta bata ganin yanda Duk ta furgice tace"Hanifa ki nutsu zamuyi magana ta k'arshe dani da ke." Tace. " INA jinki Ammi." Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "Kin San dai nan da inda muka taso na daya bane ko."!? Hanifa tayi shiru tana sauraronta Ammi ta cigaba da cewa " To ki nutsu ki dawo hankalin ki nan kina cikin 'yan uwa ne gaba da baya kar ki manta nan shine tushe na dani da Mahaifin ki haka kazalika kuma ke shine tushen ki Saboda haka INA so ki watsar da Duk wani Abu da kika tawo dashi garinan maganar wannan yaron da kike so an wuce ta har abada babu ke babe shi, Ubanki ya zama miki miji to kiyi biyayya ki aure shi ki zauna dashi lafiya kar inji Kar ingani mutukar kikayi wani abun batanci a garin nan to mu zaki zubarwa da mutumci saboda haka kiyi kokari ki bamu hakkin mu da Allah ya umarce ki dashi."
Tana kuka tace"To Ammi nima ki tayani addu....... Bata karasa ba kuka ya ci karfinta ta kwanta a gurin tana yi zuciyarta kamar ts tsage wato dai ta tabbata an rabata da masoyinta Khalid... Cikin wannan hali Abbu da Hafiz suka shigo suka same ta lokacin shi Nasiru ya tafi gidansu.
*****
Wani irin sauti ne yake tashi kad'an-kad'an kana jinsa zaka ji wani irin imani da tausayi ya ziyarce ka sautin yana tafiya ne a slow irin me ratsa zuciyar nan....... A hankali sautin sanyayar muryarsa da ya 'kara sanyayata gurin wa'kar ta fara tashi cikin wa'kar sa me take *Mahaifinta ne.!*
*"MAHAIFINTA NE."!*
*"Hanifa sanyi na zuciya."!*💔
*"Hanifa Haske na zuciya."!*💔
*"Hanifa Sanyin idaniya."!*
*"Wayyo! Hanifa kin*
*kama zuciya......💔 Mahaifinki ya shiga rayuwa ta."!*
A slow sautin wa'kar ya cigaba da tashi sautin sanyayar muryarsa na 'kara sanyi har wani rawa takeyi saboda tsananin halin damuwa da yake ciki wa'kar ta cigaba da tafiya kamar haka..........
*"Ina sonta."!❤*
*"Tana sona."!❤*
*"Babanta ya shiga rayuwa."!*
*" Ya bar gari saboda Soyayyar gudan jini❤.!"*
*"Garin Kano yayi min zafi babu gudan jini."!❤*
*"Hanifa tayi 'kaura daga kano........ Ni gombe zani koma gurin gudan jini."!❤*
*"Soyayyar babu 'karya tana sona!❤ ina sonta!❤amma babanta ya raba tsaka ni........ Wai ya zanyi ne? Ni garin gombe zana kwana."!!!!!!!!!!!!!"*
*"So Mukkuli na zuciya."!💔*
*"Hanifa ta kulle zuciya."!💔*
*"Ina sonta."!💔*
*"Tana so na."!💔*
*"Baban ta ya shiga rayuwa!!!!!!!!!🕺🏼🕺🏼🕺🏼*
Sai da ya goge wasu gunti hawaye sannan ya cire abunda yake mak'ale a kunnen shi ya jefar kan kujera yaje ya zauna ya dafe kansa yana kukan zuci!
Abbakar Mobson zuciyoyinsu duk sunyi sanyi sosai wa'kar ta kashe musu jiki duk Wanda yake cikin halin soyayya yaji wannan wa'kar zaiji kamar dashi ake to ballanta ga Wanda akayi don ita.... A take suka shiga tace wa'kar gami sai da suka tabbatar komai yayi ne sannan suka futo daga studio lokacin Khalid yaji wani irin jiri na d'ibarsa yasan damuwa ce kawai mota suka shiga gabadayan su.
*14/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*49*
Kamar yanda ya kwana cikin wasi-wasi da tashin hankali haka itama ta kwana cikin tsananin damuwa da kuma wani irin ciwon kai irin na gefe guda, Safiya nayi ta nufi b'angaran su Wasila duk suna cikin daki basu futo ba taji dadin hakan, dakin Haruna ta tura ta shiga Allah yasa a sakaye yake bacci yake sosai yaji maganar ta a kansa ya Bude idonsa da sauri yana mik'ewa zaune kallonta yake da yanayin bacci a idonsa ya mike tsaye yana fad'in "Hanifa zauna INA zuwa." Zama tayi kan wata k'aramar kujera dake dakin, tana sak'e-sak'e shi kuma Haruna bursh yayi ya dawo dakin ya zauna da mamaki a fuskarsa yake tambayar Lafiya ? Kuka ta sanya masa yace." Kiyi shiru kar wani ya jiki menene? Ko inno CE." Girgiza kanta tayi murya na rawa tace"Ya Haruna har fa Nasiru ya kawo lefe suna b'angaran mu kuma naga sai shirye-shirye suke wai wace irin mafuta ka samo min ne."!? Haruna yace." Yaushe duk akayi wannan bani da labari."! Tace"Ai baza ka sani ba dama tunda baka yini a gida kuma sai dare kake dawowa." Yace." K'warai kuwa hakane."! Shiru sukayi dukan su Haruna ya sauke ajiyar zuciya Yana kallon Hanifar yace." Kin San me."? Girgiza kanta tayi alamun bata sani ba. Yace." Kina da numbar guy ne."!? Shiru tayi tana tunani Sam bata rike numbar sa a kwakwalarta ba kawai dai idan Abbakar ya bata waya bata tsayawa duba numbar girgiza kai tayi tace"ban da ita wallahi." Haruna yace." Yaushe ne sukace d'aurin auran."!? Muryarta na rawa tace"Jibi yau saura kwana uku." Yace."juma'a kenan."? Daga kai tayi ita duk ta 'kagara ya nema mata mafuta sai kallonsa take..... Dakin ne yayi shuru kusan minti biyar sannan yace." Zan kaiki garin kano gobe nasan kin San inda yake da zama in yaso sai mu neme shi ke dashi sai Ku nemawa kanku mafuta duk tsiya dai idan suka ga bakya gari sai su hak'ura da auran ko."! Daga kai tayi cikin jin dadin abunda ya fada tace"Ya Haruna nagode sosai wallahi bazan ta'ba mantawa da kai ba cikin rayuwata." Yace." Haba Hanifa ai duk yiwa Kaine nasan kema watarana kina da ranar da zakiyi min."tace"Yanzu ya za'ayi mu tafi."? Yace." Ke dai kawai ko zauna cikin shiri misalin goma na safe nasan hankalin mutan gidan ya dauke gurin sauraran wannan shirin na rai dangin goro a lokacin zaki San yanda zakiyi ki futo ki same ni bakin layi sai mu tafi tasha Insha Allah. " Tace"Insha Allah zanyi kokarin hakan." Yace." Yanzu kije ki saki jikin ki da kowa kinji ko."? Mik'ewa tayi ta futo daga dakin har yanzu mutanan gidan basu futo ba.
Ko da ta koma sashensu sai ta saki jikinta sosai har tana taya Ammi aiki Ammi ta dunga mamakin yanda ta saki jikinta suna hira sai ta fara addu'a Allah yasa Addu'ar tace ta karbu Abbu da Hafiz ma da suka shigo sunga sauyi sosai suma sunyi murna da hakan Abbu ya zaunar da ita yana tambayar ta ko da abunda take bukata ta fada masa ko menene zai siya mata tace"Babu komai Abbu shi kuma Nasir yace." Yayi mata alk'awarin zai siya mata keken dinki sabo fil godiya tayi masa tana jin tausayinsu cikin zuciyarta, kusan k'arfe takwas da rabi na dare bayan sun gama cin abinci dai ga Nasiru ya shigo gidan fuskarsa a sake take yana sanye da wata shadda sabuwa sai k'amshin turarasa yake me saukin kudi ya shigo da sallama ya zauna kusa da Hanifar ko kunya babu saurin matsawa tayi daga kusa dashi tana jin wani irin haushin sa gaisawa sukayi da Abbu da kuma Ammi ya yace." Ammi zamuje da Hanifa gidan babbar yayarmu Rabi zasu gaisa wai tana so ta duba yanayin jikinta ne akwai wasu atampopi da zata dinka mata." Abbu yace." Ai babu wata matsala sai kun dawo." Ammi ta kalli Hanifa da take ji kamar ta Dora hannu aka tayi ta kurma ihu! Tace"Ki tashi kisa hijab dinki kuje." Mik'ewa tayi jikinta duk a sabule ta dauko hijab din Nasiru ya mike Yana fadi sai mun dawo." Bayansa tabi ranta duk babu dad'i
Tafiya sukeyi kamar ta kurame taki kulashi shine dai da yaga shurun tayi yawa ya fara janta da magana kanzil bata ce masa sai ma tsabar haushin sa da yake kara nunnukuwa cikin zuciyarta haka suka isa gidan yayar tasa, wacce ta dunga ina a saka ina a aje da Hanifa kayan ciye-ciye ta aje mata gabanta tana ta janta da hira Hanifa gaisuwa ce kawai ta hada su da ita takasa sakewa da ita, haka tace ta mike ta gwada ta, ta dauka Nasir din zai futa sai taga ya zauna ya wani tsura mata ido gashi tana jin nauyin matar ita kuma taki gane abunda ya dace haka dai ta mike gami da cire hijab dinta matar ta fara aunata shi kuma Nasiru ya dunga yi mata wani irin kallo na tsantsar sha'awa babu abunda yafi daukar hankalinsa da shi kamar k'irjinta bai taba dauka cika da kasaitar yarinyar ya Kai haka ba, zuciyarsa ta saka masa wani Abu akanta yana ganin tunda dai jibi ne d'aurin auransu yana da damar da zai rungume ta ko ya samu ya rage zafi da radadin sha'awarta. Kallonta yake idonsa duk yayi ja haka aka gama ta dauki hijab dinta ta zura tana jin haushin matar da rashin kan gado da sai tace masa ya futa a ganinta ai bai dace ba, bata fuska tayi tayi har Nasir din ya fuskanci bata son zaman ya mike yana yiwa yayar tasa sallama mik'ewa tayi ta futa ta barsu minti biyu sai gashi ya biyo bayanta taki kallonsa hannunta ya rike suka futa Rabi tana tayi mata godiya da fadin "Amarya sai munzo ganin daki Hanifa kanzil batace mata suka futa dake soran gidan irin me duhunan ne kawai Nasiru ya kai ta loka ya makure ta da bango k'irjinsa ya danne nata zura hannunsa ta bayanta ya rungume ta kam a jikinsa.
Rud'u ta shiga da tashin hankali kamar kunama ce ta harbe ta haka taji lokacin da taji hannunsa a jikinta ta dunga tureshi tana ja masa Allah ya isa kuka take tana ture shi ya'ki sakinta sai kokarin hada bakinsa yake da nata kara ta kurma me k'arfin gaske yayi saurin sakinta yana diri-diri hannunta ya kama ta fuzge da gudu ta futa daga gidan... Jin motsi daga cikin gidan yana jin muryar yayar tasa tana fad'in "Waye nan ne."!? Sai yayi wuf ya futa can ya hango Hanifa ta sauri kamar ta kifa ya dunga bin bayanta da sauri inaaaa ai tayi masa nisa domin har da gudu ma tana hadawa, hawaye kurrum take sharewa tana mamakin halin maza Abbu ya yarda da tarbiyar Nasiru ya zab'a mata shi a matsayin miji Ashe bashi da halin K'warai yabi ya matseta a soro don yana gadara shi zai aureta shine ya fara taba jikinta wata irin tsana da kiyayarsa ta kara nunnukuwa cikin zuciyarta mussaman da ya rungume ta Sam bata ji wani dad'i ba sai zafi da zuciyarta take dole ne ma ta gudu ta bar musu garin gabadaya tunda dai yanzu ta fahimci shima Nasiru din sha'awarta tafi son da yake mata yawa ai ya bari a d'aura aure kome zaiyi sai yayi mata..... Haka ta isa gida tana wannan sake saken Abbu ta tarar dashi da Kawu Amadu suna hira ta gaidashi ta wuce cikin dakin Lokacin Ammi bacci har ya dauke ta, kawai sai ta shige can kuryar dakin ta zube kan katifa har yanzu jikinta rawa yake tunanin abunda Nasir yayi mata take........Ranar bacci rabi da rabi tayi da asubah ta Riga kowa tashi tayi sallah tayi zaune kan dadduma tana gyangyadi sai da ta fara juyo motsin Ammi a tsakar gida ta futo ta fara taya ta aiki suna shira sama-sama har suka kammala abun kari suka zauna suka karya Hanifa dai lokaci kurum take jira ta futa taji dad'i da Abbu da Hafiz sun futa da wuri ita da Ammi ne kurrum sunan zaune Hafiz ya shigo hannunsa dauke da d'aurin goro ya aje k'ara fita yayi ya dauko wani d'aurin guron ya aje ya dinga shigo da dabino da sauran kayan d'aurin aure haka ya tarasu guri guda ya zauna fad'in "Ammi na gaji sosai Wallahi." Ammi ta mike tana fad'in "Bari in kawo maka kayan kari nasan akwai yunwa ma." Hafiz yace." Abbu ma yanzu zai shigo suna tare da Baba Amadu ne." Hanifa jinsu kawai takeyi suna hirarasu gabanta sai fad'uwa yake ta mike gami da zura hijab ta futo kicin din ta tsaya tana fadin"Ammi bari inje gurin su Wasila zanji shirin rai dangin goro. " ammi tace "To sai kin shigo." Hanifa ta bar shashen nasu diri-diri ta fara tana bin babban tsakar gidan da kallo maganganun su Abbu taji a dakin Inno da'alama futowa zasuyi wuf!! Ta futa daga gidan kai tsaye bakin titi ta nufa kamar yanda Haruna yace mata tayi..
Bani da chaji ne kuyi min uziri nagode
*18/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*48*
Abbu yana jin sallamar Inno ya futo daga dakin.
Inno ta kalleshi tana fadin"Sannu bawan Allah kana ciki yara suna tayi maka hayaniya a gida ita kuma Halima tana jinsu saboda rashin hankali." Abbu ya nuna mata gurin zama yana fad'in "Inno zauna sai muyi maganar." Zama tayi tana kara jadaddada magar Abbu ya kara gaishe ta amsa har yanzu muryarta a sama yace."Inno ki kwantar da hankalin ki kan maganar Insha Allah kome zai wuce nasan itama Hanifar k'uruciya ce take damunta." Tsaki taja tana fadin "K'uruciya ko kuma rashin hankali? Wannan kafurarar yarinyar me shegen bakin hali ai aure ne kawai zai kintsa ta don haka na yanke hukunci cewar rana ita yau za'a d'aura auranta Insha Allah ranar juma'a me zuwa kenan." Abbu yace." Allah ya kaimu Inno nima dama na damu da abun kinga akayi auran hankalin mu sai ya kwanta." Tace"Komai na bukata bazaiyi wahala ba insha Allah daga yau za'a fara shirye-shiryen buki." Abbu yace."Allah ya kaimu Lafiya. " duk Wannan maganar da suke Haruna da Hanifa Nasir Hafiz na jinsu.... Haruna yaja tsaki k'asa-kasa yace." Hanifa wuce muje b'angaran mu na lura idan na barki a gurin nan wad'annan sai sun kusa kasheki duba da yanda suke wani huci a kanki kamar sun kama ki da abun wani." Hanifa ta bi bayansa tana jin wata irin tsanar Nasir dashi kanshi Hafiz din. Shi kuwa Haruna yana sane yace su tafi sashensa yana so ya danyi mata tambayoyi kan lamarin.... Akayi sa'a babarsu batanan taje bukin suna, d'akinsa ya bude yace ta shigo Hanifa ta shiga babu wani jin nauyi a lokacin ita kawai Neman wamda zai taimake ta take akan lamarin,Wasila dake kicin ta bisu da kallo cikin mamaki domin akwai tazara tsakanin sashensu Dana su Hanifar shiyasa bata ji abunda ya faru ba, Haruna yace." Hanifa Wai meye tsakaninku da Mashahuri ne."? Shiru tayi sai da ya kara tambayar ta sannan tace"Ya Haruna shine Wanda nake so yake sona amma kuma Abbu da Ammi sun kasa gane hakan wai dole sai na auri Ya Nasiru."! Haruna yace." Kin tabbatar kina sonsa."!? Daga kanta tayi alamun "Eh." Shiru yayi yana nazarin maganar shi kam yana ganin dole ya taimakawa yarinyar domin ba karamin tausayi ta bashi ba so masifa ne kuma yana ganin iyayen su cutar ta kawai zasuyi domin shi a ganinsa duk uban da ya samu yarsa ta samu mai sonta kamar Mashahurin to zaiyi alfahari da hakan shima zaiso Hanifar ta auri Mashahuri domin ya kara samun shiga a gurinsa bayanan kuma cikin abokansa zai zama abun kallo 'kanwarsa na auran Mashahurin mawa'kin da duniya ta San da zaman sa, wato *Khalid*
Yace." Ki kwantar da hankalin ki insha Allah zan shige miki gaba kan lamarin ki zaki cimma bukatarki naji waccan tsohuwar tana fadin"Wai rana ita yau za'a d'aura miki aure ke da nasiru kar wannan ya daga miki hankali insha Allah kafin zuwan ranar na nema miki mafuta." Hanifa ta sauke ajiyar zuciya me sanyi sai yanzu ta Dan samu sassauci cikin zuciyarta tace"Nagode sosai Ya Haruna ubangiji Allah ya kara zumunci. Wallahi ni ba wai ina in Yaya Nasiru bane kawai da bana jin zan iya zaman aure dashi kamar yanda nake son Khalid din ina ganin idan na auri Ya nasiru bazan bashi kulawar da ta kamata ba tunda nasan hankalina yana kan wani daban kaga ni dashi zamu shiga cikin wani hali wannan nake so su Abbu su fahimta amma sun kasa ganewa."
Haruna yace."ai baza su gane ba tunda duk cikinsu babu Wanda ya ta'ba fadawa komar so shiyasa suka kasa ganewa ni na tabbatar guy nan na bala'in sonki tunda har kikaga ya zauna ya tsara miki wa'ka irin wannan akwai tsantsar soyayarki a tare dashi." Hanifa ta sauke ajiyar zuciya tana jin dadin kalaman da Haruna yake fada a tsakanin ta da Khalid din.... Koda ta futo daga dakin sai tayi zamanta nan tsakar gidan suna hira da Wasila dake kicin tana yi musu abinci sunanan zaune har Ummansu ta dawo daga gidan suna Lokacin ne kuma aka fara kiran sallah magariba......... Hanifa kin komawa tayi sashen su tayi kwanciyar ta nan har Safiya nan din ma sai kusan goma na safe ta shiga sashensu abun bakin ciki da takaici Inno ta Tarar ita da Abbu da Ammi din suna ta tsara yanda hidimar auranta zai kasance tana tsuguna wa tayi duk ta gaishe su..... Ammi da abbu suka amsa babu yabo babu fallasa Inno kuwa surutu ta kamayi mata, Takaici yasa Hanifa mik'ewa da sauri ta shige dakin tana tsaki k'asa-k'asa tace"Tsohuwa sai shishshigin tsiya kawai katifa ta kwanta ta rungume pillo tana tunanin Khalid a zuciyarta...... Muryar abbu taji yana fadin"Wai yanzu su Nasiru sun tafi gurin masu printing domin a buga katin d'aurin aure gabanta na fad'uwa ta mike zaune tana fad'in "Mutanan da gaske suke ashe ? Innalillahi wa'ina ilahi raji'un." Hawaye ta fara sharewa futowar ta daga sashen su Wasila Haruna ya futa da ta koma ta fada masa halin da ake ciki ita duk kanta ya kulle kuka take tana addu'ar Allah ya kashe Nasiru tana ganin da ta aure shi gwara ta zauna haka babu aure.
_Hanifa har kiyayar ta kai haka?_
Motsin shigowar Ammi dakin yasa tayi shiru hade da saurin juya bayanta don kar Ammi din ta fahimci kuka take Ammi ta gama abunda take ta futa daga dakin.
***
Khalid wa'kar shi tq samu masifar kar'buwa fiye da yanda kuke tsammani domin ba Najeria kadai ta tsaya ba harda sauran kasashen waje wayoyin jama'a"a kuwa har gajiya yayi da dauka su Mobson suka cigaba da d'agawa suna amsa masa, shi kam duk wannan bai dame shi ba burinsa kawai wa'kar ita isa inda ake so....... Kiran waya ne ya kara shigowa Khalid yace"Mobson ka kashe wayoyin nan haka nifa ba abunda ya dame ni ba kenan." Mobson yace." Bari in daga wannan nagama kamar ta 'k'asar waje ce in yaso daga ita sai a kashe wayar." Gyda kansa yayi Mobson ya daga wayar da tare da sallama
Cikin wani irin turanci irin na america mutumin yayi sallama yana tambayar yana magana da Khalid ne."!? Mobson ya bashi amsa da nasa turanci irin namu na Nigeria yace." A'a a bokinsa ne." Mutumin yace." Idan babu damuwa hadani da Khalid din zamuyi magana." Mobson ya mik'awa Khalid wayar dake duk yana jin abunda suke cewa yayi magana da turanci, mutum yace." Sunana Sonop ni d'an america a can aka haifeni amma kuma mahaifiyata bak'ar fatace yar asalin k'asar Ghana ni mutum ne mai son jin wake-wake sosai yanayin muryarka yayi min na saurari wa'kokin ka masu ma'ana muna tare da Abudulbasit Yana jin yaran Hausa ya fassara min Gaskiya ina mutukar jinjina maka K'warai da gaske, dani da abokaina muna so mu ganka ido da ido shine muka shirya domin kawo maka ziyara har Nejeria idan kuma zamu samu muna so kaziyarci k'asar mu muna so Kayi mana wa'ka mai dad'i irin ta gayu ina fatan ka gane."! Khalid ya sauke ajiyar zuciya da murmushi a fuskarsa yace." Sonop nagode K'warai kuma nima ina alfahari daku gaskiya naji dad'i da har wakata taje inda kuke kuma insha Allah kamar yanda ka bukata din zamu shiga studio dani daku zamu yi wa'ka irin wacce kuke so sai kuzo da shiri wannan karon zamu futar da vedio ne insha Allah. " Sonop yaji dad'i sosai yace." Zamu zo najeria cikin satinan." Khalid yace." Babu damuwa ina sauraran zuwan Ku." Sunayin sallama Mobson ya fasa wani irin ihu! Yana buga katifar da suke kai fad'i yake." Guy ka tsallake Wallahi kayi kudi ka gama zaka hada ala'ka da baturan mutum gaskiya kai d'an baiwa ne, Guy kayi bai-bai da talauci don ina me tabbatar maka da cewar mutukar wa'kar ta futa to za'a samu manyan masu kudi ko masu mulki dake America su siya Shikkenan zaman nejeria ya kare sai dai kazo da yawo." Mobson duk a gigice yake wannan maganar yana ihu.!!! Khalid yaja tsaki yana Dan girgiza kansa yace." Mobson naji dadin al'amarin nan nima amma kuma damuwar da nake ciki baza ta barni in samu nutsuwa, kuma kana mantawa da Abu d'aya nafad'a na kara fad'a muku nifa wannan wa'kar da nake yi ba don kudi nake ba kawai ra'ayina ne kai kanka kasan kudi ba matsala ta bane so Ku daina wannan maganar." Mobson ya gyara zamansa sosai yake fuskantar Khalid din yace." Wannan karon baza kayi mana bukulu ba wallahi nake fada maka kafarka kafarmu duk inda zaka shiga a fadin duniyar nan muna biye dakai domin mu muna bukatar kudi kai da kaci ka tada kai sai ka barma na." Khalid yace." Duk abunda na samu ta dalilin wa'ka na bar muku kuci kuyi sadaka kuma Ku bawa Wanda kuke so."
Abbakar ne ya shigo ya tsinci maganar da suke ai shi har yafi Mobson din rudewa sai murna suke suna ganin suma lokacin su yazo ta dalilin Khalid Mashahuri Ashe banbadancin da suke masa bazai tashi a banza ba.
*****
Lamari fa ya girma ma tsakanin bangarori biyu sai hidima suke gami da shirye-shiryen buki domin har mahaifin Nasiru ya bashi kudi kusan dubu Dari da Hamsin a cewar sa sun isa yayi siyayar aure suturun sawa da kayan kwalliya tundai duk al'amarin na gida ne baza'a tsawwala ba, gurin zama kuwa bashi da matsala domin har an gyara masa wani b'angare dake jikin gidan nasu har fanti anyi sai jiran zuwan amarya..... Nasir akwati biyu ya hadawa Hanifa komai ansaka dai-dai gwargwado Inno da ta gani sai ta dunga fada tana cewa''Yayi barna kudi ai ba irin su Hanifa y akewa gwanin ta ba da ya sani ma turmi uku ya siyo da abunda ba'a rasa ba.
Shi dai shuru kawai yayi mata aka shiga da akwatinan gurin su Abbu yayi ta sa'albarka yana fadin "Da ya sani bai wahalar da kansa ba shi kawai burinsa ya rike Hanifa amana. " Nasir yayi masa bayanin komai nan Abbu yayi tawa mahaifin nasa addu'a, Hanifa ranar kwanta tayi kuka bini-bini ta duba hanyar shigowa Haruna kawai take so ya dawo to har k'arfe goma na dare bai shigo ba haka ta hak'ura ta kwanta da kayar bacci ya dauke ta bayan taci kukanta ta koshi....
Wani irin mafarki yakeyi mai dad'i ya dunga rungume pillow yana motsa cinyarsa nishi yake saki yana kara matse pillow da hannunsa...... Duk cikin baccin yake ta motsi da hannunsa burinsa kawai ya damk'i abunda yake tsokane masa ido amma ina sai buge-buge yake a jigace ya bude ido firgigit ya mike zaune wata irin zufa na keto masa. Dakin yake bi da kallo yana Neman inda yarinyar take ya juya da sauri bayan shi da gefansa babu kowa sai tarin k'ananun pillows da suke baje kan bed din, Yanzu ya tabbatar mafarki yake. Sunkuyar da kansa yayi cikin tsananin damuwa da tashin hankalin abunda yake damunsa mafarkin da yakeyi kamar gaske wai gashi ga yarinyar Shaik sunyi aure suna soyayya tana kwance a jikinsa tana masa wasa irin Wanda yake so a rayuwarsa ji yayi joystick dinshi na kara harbawa zuciyarsa ta harba da tsananin damuwa da sha'awa kawai sai yayi 'kasa da kansa wasu 'kananun hawaye na takaici suka fara futa daga idonsa, Wa'kar da yayi domin ita ta tafi can wani guri da ba'a bukatar ta yau kwanaki hudu kenan da tafiyar su amma babu wani labari gamsashe dangane da Wanda yasan su da inda suke zaune a garin gombe kullum cikin bunkice yake yana aikin duba sytem ko zai ci karo da sa'kon Wanda zai ce mishi yasan yarinyar shiru daurewa kawai yake ga wata irin masifa da babu damar ya rufe idonsa suffofinta suyi tayi masa gizo idan ya kwanta bacci ma haka zatazo ta dame shi kullum haka yake fama.... Cike da damuwa ya koma ya kwanta yana tunanin ta inda zai 'bullowa lamarin a duniya yana ji bashi da babban makiyi sama da Shaik shine duk ya jefashi cikin wannan masifar..... Shawarar da ya yanke kawai za suje gombe suyi ta bunkice har Allah yasa a dace, yasan duk umarnin da ya bawa yarinyar zata shi kadai yasan abunda ya shirya domin nemawa kansa mafuta.
*17/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*47*
Alhaji Tijjani na tsaye tsakiyar parlor Khalid din ya shigo da sallama a bakinsa suka amsa duka Nasrin ta durkusa har kasa ta gaida shi hankalin sa na kan Khalid din ya amsa mata Khalid ya zauna kan kujera yana fadin"Dady ya kasuwa Mamy ta taso ka ko."? Yace."abunda nake so nace kenan Myson tayi min waya tana kuka wai kana nema ka zauce ka kasa gane mutane duk ta gigita ni na tawo babu shiri kuma gashi nazo na ganka rad'au dama ni na San yaro na jarumi ne." Khalid ya shafa kansa yana Dan murmushi yace." Dady kawai rigimar mamy ce wai kawai don bangane Momy zainab ba shine take cewa na zauce kan soyayyar yarinyar Shaik." Alhaji Tijjani ya zauna kusa dashi da damuwa a fuskarsa yace." Myson yau a kasuwa yini akayi ana sauraron sabuwar wa'kar ka mai taken *Mahaifinta ne!"* wannan mutumin gaskiya bai kyauta mana ba Ko yanzu kafin na futo daga kasuwar sai da nasha tambayoyin mutane kan wa'kar taka in banda Alhaji Lawan babu Wanda yasan abunda yake faruwa,, akwai wani abokin harkata Alhaji Bilyaminu shine ya 'bukaci da kaje ka ga yarinyar sa idan tayi maka sai yayi maka huce haushi da ita."! Nasirin da mahaifiyar ta da ita kan ta Mamyn sukaji wani rugugu a zuciyarsu addu'a suka farayi Allah yasa Khalid din ya bujerewa bukatar mutumin Nasrin har ta soma share hawaye...... Shiru yayi na minti biyu kafin yace." Dad mu bar wannan maganar don Allah inaji a jikina zan auri yarinyar shaik anan kusa kai dai ka cigaba da tayani addu'a."Alhaji Tijjani yayi shiru domin bai so jin haka daga bakin Dan nasa ba yaso ya hada huldar auratayya da Alhaji Bilyaminu domin mutum ne shi shararre a duniya yana da kudi Wanda suka ci Uwar nasa shiyasa yake so ya kara d'aura aminta dashi..... Amma Tunda Khalid din ya nuna baya so ya hak'ura domin samun kwanciyar hankalin sa, mik'ewa yayi ya hau sama yana mita yanda Mamy ta kirashi a waya a cewar sa tasa duk jikinsa babu dad'i domin shi har ga Allah ya dauka wani mummunar Abu ne ya faru da Dan nasa, Mamy dai shiru tayi Saboda sanin halinsa Hajiya Zainab itace me Dan bashi hakuri sai dai ya haye sama sannan tayi shiru.....shima Khalid din daining ya nufa NASIRIN ta mike ts bishi tans so ta zame masa kaska taki ta kama kanta har ya soma jin haushinta domin shi baya son takurawa.
Hira take masa yana wani ya amsa wani ya basar haka har ya kammala cin abincin ya mike ya futa daga gidan kai tsaye gidansu Abbakar ya nufa domin yaji me yake tafiya aikuwa tunda yana hawa titi ya fara ganin manya-manyan pastas dinsa a manne daga sama an rubuta sabuwar wa'kar Mashahuri mai taken *MAHAIFINTA NE!* yara ya gani suna ta kallo wasu kuma mannawa jikin shagunan mutane da gefen kwalta ga wani me shagon Chaji ya saki wa'kar cikin mayan sifi'ku gurin dai duk ya hautsine da samari kowa yana fadin albarkacin bakinsa, sai da yayi da ya sanin futowa domin suna ganin motar shi kin barin sa sukayi caaaaa! Suka baibaye shi suna fadin albarkacin bakinsu kan sabuwar wakarsa wasu daga ciki kuwa fad'i suke Shaik yayi a sara kuma ya cuci yarinyar sa.... Haka dai ya dunga daga musu hannu ya samu ya wuce to yana karya kwana da motarsa domin shiga layin su Abbakar ya fara jin sautin tashin wa'kar Mobson ya ware kida layin ya cika da yara da manya ko wane bango ka kalla pastar d'insa manne ya nan ma ganin motarsa ta shigo yasa gurin ya kara hautsine wa da ihu duk suka yanyame motar ya kasa ma futowa daga ciki sai da Abbakar yazo gurin ya futo dashi sannan ya dunga daga musu hannu yana dariya da kyar dai ya samu suka shige shagon mobson duk da haka basu bar gurin ba hayaniya a gurin kamar me! Khalid yaji masifar dad'i da wa'kar ta samu karbuwa tun kafin aje ko INA gashi Dad dinsa ma yaji cikin kasuwa lallai ya godewa Allah kuma yana sa ran wa'kar zataje har garin da yake so.
****
A shashen su Wasila Hanifa ta kwana bata shiga b'angaran nasu ba sai kusan 'karfe goma na safe taje suka gaisa da Ammi a lokacin Abbu ya futa..... Aiki ta Dan taya ammi ta dawo ta zauna Ammi ta shigo dakin ta ganta zaune tana zabga tagumi tace"Wato kinan kina tunani ko Hanifa wai baza kiyiwa kanki fada ba ko." ? Kasa tayi da idon ta tana kokarin tsane hawayen da yake kokarin zubo mata. Ammi ta shige daki ta futo hannunta rike da wata roba me fad'i da wake a ciki tace"Ki gyara min waken nan yau ina so inyi mana fate Abbu baya jin dadin jikinsa yanzu ma sun je Chamis ne."
Jikinta a sanyaye ta karb'i robar tace"Ammi me ya same shi."!? Zazzab'i ya kwana dashi jiya nasan dai gajiyar hanya CE." Ta fada tana kokarin futa daga dakin Hanifa ts share hawayen tana tausayawa Abbu da rayuwarta..... Waken ta fara gyarawa tana tuno sanyayyar murmushin Khalid da salon soyayyar sa.
Haruna ne ya shigo shashen nasu hannunsa rike da wayarsa madaidaciya yana sauraron wa'kar Mahaifinta ne! Bakin kicin ya tsaya suna gaisawa da Ammi, Haruna dai yayan Wasila ne daga shi sai ita yaro ne da yake gan ganiyarsa domin duka sutturunsa babu manya sai kananu ga wani mutsiyacin aski da yake kullum sumar kanshi a taje take da kum a jiki Bini-bini zai cire ya taje mugun Dan gayu ne da son dabi'un nigogi duk gidan sun hak'ura sun kyaleshi Inno ma tayi masifar ta gaji tunda ya fara sauraron wa'kokin Khalid yake da burin yaje har kano gurinsa yana mutukar son wa'kokin sa a cewar sa shima yana da burin ya zama mawa'ki a duniya shiyasa yake so ya zama yaron Khalid wa'kar yake saurara yana gyada kansa cikin shauki dad'i.
Ammi tayi kasa'ke! Tana sauraron baitocin wa'kar me taken Mahaifinta ne gashi taji ana ambton sunan Hanifa....... Kafin su Ankara suka ga Hanifa tsaye a Kansu kamar anje fota gurin.... Haruna yace." Ke meye haka sai kace wata aljana zaki fad'o guri." Kallonsa take tana marmar da idonta bakinta sai motsi yake. Ammi ta kalleta yanzu ta fahimci daga inda wa'kar ta futo tunda taga Hanifar ta futo wato yaronan bai rabu dasu ba kenan har ya shirya musu wa'ka wacce take ganin kamar tozarwa ce." Haruna ya kama hanyar futa yana dad'in "To tunda baza kiyi magana ba ni kinga tafiy..... Kafin ya karasa ta bishi da gudu ta rike hannunsa sai ga hawaye sharrrrrrrr!!! Sun biyo kuncinta. Haruna ya tsaya yana kallonta da mamaki a fuskarsa yace." Me akayi miki kike kuka ne? Na lura fa Tunda kuka zo garin nan kin kasa sakewa damu wai meye ne."? Haruna ya kara tunzura zuciyarta ta saki hannunsa gami da zubewa a gurin tana rusa kuka na futar hankali..... Wanda yayi dai-dai da shigowar Abbu da Nasir da Hafiz suka riski abunda yake faruwa Ammi ma futowa tayo daga kicin din duk sukayi tsaye a kanta suna mamaki kukan da takeyi..... Abbu ne yake tambayar abunda ya faru. Haruna yace shi bai sani bs kawai ta futo daga daki ta biyoshi Tana kuka." Ammi tace"Haruna k'ara kunna wa'kar nan suji?" Haruna yasa dariya yana fad'in"Ammi ina ruwan wa'kar Mashahuri da kuma damuwar Hanifa. " jin sunan da Haruna ya ambata yasa duk jikinsu yayi sanyi.... Nasir da jikinsa yake tsuma yace" ka kunna mana Malam." Haruna ya kunna wa'kar yana fadin"Yaro me tashe kenan 'yar wani mutum yake so shine mutumin dake albada ne ya gudu da yarsa harda barin gari donshi mtsssss! Ya karasa maganar yana Jan tsaki! Su dai shiru sukayi masa suna sauraron sautin wa'kar da ya fara tashi a hankali a hankali kafin sautin muryarsa ya fara bayyana ta Cikin wa'kar mai taken.
*Mahaifinta ne."!*
Abbu yaji jikinsa ya kara rikicewa da zafi jiri ya fara dibarsa bai tsaya ya gama sauraron wa'kar ba ya wuce daki tunda dai ya fuskanci daga inda wa'kar take zuwa yayi ya kwanta kan katifa cikin kuryar daki jikinsa babu dad'i Al'amarin ya soma bashi tsoro addu'a yake cikin zuciyarsa kan duk abunda yafi alkairi Allah ya zab'a.
Can tsakar gida kuwa Hafiz yayi kan Hanifa da duka da hauri da kafa dukanta yake yana fad'in "Wannan kukan da kikeyi na uban meye wai ke wace irin mayyace ne don ubanki me zakiyi da wannan Dan iskan da kullum yake kokarin ya to zarta Mahaifin ki, Ammi shigewa tayi kicin ta cigaba da aikinta ranta duk babu dad'i Hafiz bala'i yake ma Hanifa yana dukanta da k'afarsa kamar bai San daga inda take ba Nasir na tsaye duk ya rasa ma me zaiyi yana ganin dukan shine yafi amfani gareta tunda taki hak'ura shi sai yake ganin kamar ma itace tasa Khalid din ya shirya wannan wa'kar...... Haruna ya karaso gurin yana kokarin janye Hanifa dake kwance kasa Hafiz tsaye a kanta yana duka yace." Wai meye ne ni kun sani a duhu na soma fahimtar inda al'amarin ya dosa amma ina bukatar Karin haske a gurinka." Hafiz na cigaba da dukan Hanifa ya kwashe komai ya fadawa Haruna tsaki yaja da k'arfi ya janye Hanifa daga gurin yana fadin"Wallahi sai Allah ya saka mata wannan ai cin zali ne, Hafiz kasan daci da masifar so kuwa? Ko Dan baka son abunda yake damunta a zuciyarta bane,? Haka kawai dame zata ji? Dole sai an aura mata Wanda bata so kan me? Kawai yarinya Allah ya rufa mata asiri zaku cuce ta wannan tsarin baiyi ba wallahi ni bana cikinsa." Haruna ya karasa maganar sa a zafafe! Cikin hayaniya Nasir yace." Kai! Me kake nufi ne? Kana nufin kace abbu din ne yayi ba dai-dai ba kome ko kuma ni kakewa bakin ciki da hassada akan Hanifar da har kake fadin wannan maganar."!? Haruna ya daga kafadarsa alamun babu abunda ya dame shi yace." Kaine ka sani Wallahi Sam baku dace da hanifa kaje ka nemi dai-dai da kai kabarwa Oga matarshi da yardar Allah sai na tsaya mata kan biyan bukatar ta." Tofa fad'ar wannan magana sai ta dugunzuma zuciyar Nasiru yayi kan Haruna kamar zai Doke shi yake zaginsa duk idonsa ya rufe, Abbu na cikin Uwar daki kwance duk yana jinyo hayaniyar da take faruwa Lokacin ne kuma inno ta bayyana a gurin Jama'ar gidan suka fata turawa a gurin da 'daya bayan d'aya..... Inno tace"Wai me yake faruwa ne tun d'azu nake jiyo hayaniyar Ku menene ? Ina Haliman take ne? Tams jinku kuna d'iban albarka irin haka."! Ta k'arashe maganar cikin fad'a da daga murya.
Ammi ta futo daga kicin tana fad'in"Inno gani a kicin."! Inno tace"Au! Da kina jinsu suna fada gami da zagin junansu kikayi shiru."? Ammi tace"Inno ayi hakuri don Allah wallahi na rasa ma me zance kan al'amarin.'' Inno ta maida hankalinta kan su Haruna dake rike da Hanifa dake kukan wurjajan!! Tace"Haruna me ya faru ne."? Haruna ya kwashe komai ya fada mata."Inno ta kalli Hanifa ranta a mugun bace tace"Au abun kunyar da zaki jawo mana kenan ? Me zamuyi da mawa'ki Wanda bashi da cikkakiyar sana'a to Bari kiji mu lokacin mu duk saurayin da yake wa'ka ba'a bashi aure domin wa'ka dai ba Sana'a bace don ubanki dame zai rike ki? Duk Wanda yake wa'ka ro'ko yake mu kuma duk fadin zuriarmu bama fatan su auri maro'ki saboda haka idan zaki hak'ura to ki hak'ura Wallahi tallahi bazaki auri mawa'ki ba.''
Haruna yaji kamar ya tsinka ma inno mari jin abunda take fada wai me yasa mutane suke hakane? Wai wa'ka itace inno take kira da ro'ko to shi kuma da yake da burin ya zama mawaki Ashe zasu sallame shi daga cikinsu don babu abunda zai hanashi zuwa kano gurin Mashahuri..... Yace." Inno banji dadin wannan maganar ba a matsayin ki na babba nifa sai dai Idan Ku sallama ni cikin dangi don ina da burin in zama mawa'ki kuma babu laifi anan don Ku bada yarku ga mawa'ki baiwace da Allah yayi masa baiwar da ba kowa yakewa irinta ba." Inno tace." Kul! Haruna kar in kara jin wannan Kalmar daga bakin ka indai ina da mutumci a idonka to ban lamunce maka da wannan sana'ar ta roko kuma kar ka kara maganar ka nemi wata sana'ar zaifi maka.... Ita kuma Hanifa daga yau zuwa rana ita yau za'a d'aura auranta da Nasiru sai inga karshen kiyayyar da takewa Dan uwanta kan bare kuma maroki.... Halima ina Munzali yake."!? Ta fada Tana kallon Ammi dake tsaye taji dadin hukunci da ta yanke tace"Yana cikin daki Wallahi jiya ya kwana da zazzab'i ." Inno ta nufi dakin tana gyara d'aurin zaninta take fadin"Saboda rashin hankali yarinya tana nema ta kai kanta ga halaka waye kuma Khakid to indai ina Raye baza'ayi wannan shashancin ba na Riga na gama yanke hukunci. " ta k'arashe maganar lokacin da ta d'aga labulen dakin.............
*16/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*44*
Shiru dakin yayi sai sautin kukan Hanifa ne kawai yake tashi Abbu zuciyarsa zafi kurrum take masa bai taba tsammanin yarinyar zata bujere masa ba sai gashi lokaci guda tana nema ta watsa masa kasa a ido, cikin taaushin harshe yace." Hanifa tun farko sai da na zaunar dake nace ki fadamin gaskiyar game da zabin da nayi miki me zai sanya ki rufe min abunda yake zuciyarki,? Sai bayan kin bari na Sanar da yan uwa da abokanan arziki kuma daga baya ki bullo da wata magana to a gaskiya bazan lamunta ba dole zaki auri Dan uwanki ko kin so ko kinki Nasiru dai shine mijinki kuma zaman Kano kafin nan kafin rana me kama da ta yau mun barshi zamu koma mahaifarmu saboda haka ina me umartarki a karo na biyu cewar ki cire wannan yaro a ranki domin bazan taba yin magana biyu ba da tun farko kin fada min gaskiyar ki zan iya tausar zuciya ta data Nasiru a baki abunda kike so amma yanzu kam lokaci ya kure miki." Yana gama maganar sa ya mike ya futa ransa duk babu dad'i Nasir da Hafiz bayansa suka bi nan suka ci karo da ledojin Shopping Wanda Khalid yayi wa Hanifa Nasir ya dauke su a fusace suka futa da Hafiz din yana fadin"Mu za'ayi wa k'aryar arziki bama so domin mu mutumci yafi komai a gurin bama bukatar kayan mutumin da bai San darajarmu ba."!!! Kuka kurrum takeyi ta hade kanta da gwiwa Ammi ta futo ta bar mata dakin shimfid'a tayi a tsakar gida ta kunna redion ta Sam Yanzu shawarar da ta sanja shine zata daina kula Hanifa har sai ta gane kuranta.
Ranar yanda ta fa dare haka taga rana bacci baiga idonta ba Khalid kuwa baccin sa yake harda munshari yana mafarki gashinan yana soyayya da Hanifa haka ya tashi jikinsa kaca-kaca tsaki ya dunga bugawa domin sosai yaji dadin mafarkin Wanda yake ganin kamar gaske sai da ya farka ne ya gane Ashe gaibu ne.
Cike da walwala da farin ciki ya shiga sashen iyayen nasa Mamy ta tsaya tana kallonsa cike da mamaki!! Yar dariya yake yana Sosa sumarshi yace." Mamy kin tsaya kina ta kallona ne me nayi kuma.'' Yana kokarin zama kujerar daining yake maganar yake tayi tana fadin"Dole in tsaya in kalleka Myson naga sai wani farin ciki kake da alama dai sun amunce maka ko." Ya fuskanci inda maganar ta ta dosa yace." Insha Allah Mamy Nike da nasara da Mahaifinta tunda dai tana sona magana ta kare idan yana son kwamciyar hankalin yarsa to ya aura mata ni." Girgiza kanta kurrum tayi domin bata da tace wa Mai gidan yana nan tana iya magana cibi ya zama kari shiru shine yafi mata a cikin wannan al'amari cikin shagwaba yace."Mamy hada min break fast yau zanyi irin Wanda na Dade banyi irinshi ba." Tab'e baki tayi tare da fadin"Kamar gaske Yanzu kana fara ci zakace ka koshi." Yace." Mamy ke dai hada mi ki gani ai ina cikin farin ciki ne zanci da yawa." Mamy ta fara hada masa tana fadin "Allah yasa dai." Alhji Tijjani ne ya sauko daga sama yana sanye da shadda yar ubansu anyi mata dinkin hannu kana ganin shaddar da dinki kasan irin na manyan mutane ne sai sabe babbar rigar yake yana ta zabga k'amshin tura ransa ya karaso gurin Hannu ya bawa Khalid din suka gaisa yana fadin"ya kama ta fa yau ka futa kasuwa domin jiya da shekaran jiya aiki ne ya hade min sosai akwai lissafin wasu kudi da zamuyi da Alhaji Ayuba bana so ya cuce ni INA so kaje ka tsaya ayi komai a gabanka inyaso sai a shiga dasu banki." Khalid na kurbar ruwan tea yace." Shikkenan dady zan shigo insha Allah. " A gurguje ya zauna Mamy ta hada masa abun kari yana ci suna hira da Dan NASA Khalid na fada masa abunda ya faru amma bai fada masa cewar Hanifar ce tazo gidan ba yace masa dai sun had'u a hanya ne." Alhji Tijjani ya dunga dariya yana yabawa da jarumtar dan nasa yace." Irin wad'annan mutanan masu taurin kai dama irin Ku ne maganinsu Myson ko auran yar tasa kayi kar ka yarda ya raina ka kowa ya zauna a matsayin sa."
Mamy kallonsu kawai takeyi bata da damar da zata tsoma musu baki a maganar su domin idan tayi kuskure ko yayane masifa zata sha gurin mijin nata shiyasa kawai tayi musu shiru amma taki sakar ma dad din fuska dake ta kokarin sakata cikin maganar sai dai kurrum tace "E ko a'a domin ita da zasu bi ta ta ma da sun aje maganar gefe guda don ba k'aramin bata mata rai take ba kwata-kwata bata kaunar yarinyar da Khalid...... Cike da nishadi suka futa daga gidan Khalid na kara samun daurin gindi gurin Dadyn nasa.
****
Yau kwanaki hudu da faruwar al'amarin Hanifa duk ta muzanta ta futa daga hayyacin ta kullum cikin b'oye kanta take cikin dakine ko band'aki ko kicin tana kuka babban abunda ya daga mata hankali yanda Ammi ta futa daga sangarta gaisuwa ce kawai take hada su Shikkenan Ammi sai ta dauke mata wuta Abbu kuwa dasu Nasir basa zama kullum cikin shirye-shiryen suke na tafiya gwambe gidan da suke ciki ma tuni Abbu ya sai dashi hade da k'aramin gidanshi dake D'orayi Wanda ya sanya haya can gombe basu da matsalar gurin zama tunda dama yana da gurin shi na gado, Hanifa hankalinta ya tashi sosai mussaman da taga ana ya gobe tafiyar suna ta hada kaya cikin buhunhuna Ammi na ta shiga makota tana sallame gami da Neman afuwar juna dama tuni wani me kafunta yazo ya dauke gado da sif Ammi ta karb'i kud'in kayanta Yanzu kayansu duk suna cikin gana masgo komai Ammi ta kammala hadawa ranar tafiya a ke jira a lokacin ne kuma Abbu ya futo da wannan shopping din na Khalid ya damkasu a hannun Nasiru yace suje har gida su mai yar masa da kayansa dama jira yake lokacin tafiya yayi aikuwa dama Nasiru jira yakeyi take suka nufi gidansu Khalid Nasir yana ji zaiyi futo na futo da Khalid din indai akan Hanifa ne
Lokacin da suka isa gidansu Khalid k'arfe shida saura na yamma a lokacin ne kuma motarsa ta kunno kai layin suna tsaye a bakin gate masu gadi sun hanasu shiga sai tambayoyi suke musu Nasir fad'i yake gurin Khalid mukazo ganin motar Khalid din ta shigo layin yasa daya daga cikinsu yace." Gashi nan ma ya dawo." Duka suka juya suna kallon bayansu daya daga cikin masu gadin ne ya bude gate din motar ta shiga ciki da gudu ya bi bayansa har inda ake parking ya bude masa motar yau yana sanye ne da k'ananun kaya dogon wandon jins da shart mai dogon hannu a hannunsa daure da agogo kafarshi tana sanye da rufaffan takalmi yayi kyau sosai amma kuma kallo daya zakayi wa fuskarsa ka gane yana cikin damuwa.... Mai gadi yace."Ranka shi Dade Kayi baki gasu can bakin gate tun d'azu sukace gurinka suka zo...A hankali yace." Ok muje in gansu." Mai gadi yayi gaba da sauri! Khalid din yabi bayansa.... Kallonsu yakeyi daya bayan daya yana so ya tuno a inda yasan fuskarsu... Hafiz ya bashi hannu suka gaisa babu yabo babu fallasa shi kuwa Nasir cogewa yayi yana jin wani irin kishinsa cikin zuciyarsa ga k'amshin turaran da yaji a jikin Hanifa kwanaki yaji shi jikin Khalid din shiyasa yake jin kamar ya kai masa duka yana ganin Khalid ya Riga ya gama tatta'be masa jikin Hanifa yana ji zuciyarsa kamar ta buga saboda kishin sa.
A Dan ya mutse yace." Zan shiga gida Yanzu Malam Iliya yake fadamin nayi baki ban gane ku ba."!? Nasir yace."Dama bama so ka gane mu munzo ne kawai mu ja maka kunne kan ka kama kanka kuma ka futa daga sabgar yarinyar nan Hanifa domin dai tuntuni mahaifinta yayi mata miji saboda haka kaje ka nemi wata ga kayan kanan mutumci yafi komai a gurin mu." Khalid ya kalleshi lokacin da yake aje ledojin a gabansa yanzu ya fahimci daga inda suke murmushi yake yana kallon Nasir din da yake sauke nuffashi ya wani murtuke fuskarsa! Cikin yanayin maganar shi yace." Yanzu ni nayi kama da Wanda za'azo har gida ajawa kunne."!?
Nasir yace."K'warai kuwa domin kana kokarin shiga hurumin da banaka ba."Girgiza yayi yana Dan ya mutsa fuskarsa yace."Ya shaik din ne ya turo Ku kuzo Ku garfade ni na futa daga hanyar yarinyar shi ko kuma Kaine ka kawo kanka domin naga zakewarka tayi yawa ko Kaine mijin ne."!? Nasir yace." Sanin nine mijin ko bani bane duk bai shafeka ba kawai dai ka futa daga harkar yarinya domin ba sa'ar auranka bace kaje ka nemi dai-dai kai ka k'yaleta tayi zaman auranta
Fuskarsa a sake yace." Kake wani wahalar da kanka kana nufin soyayyar da Hanifa take min ta gaibu CE."? Shuru sukayi suna sauransa ya saki dariya yana shafa sajanshi ya cigaba da cewa"So da kaunar da take min bazai taba bari tayi rayuwar aure da kai ba. Domin zuciyarta tana gurina nutsuwa da kwanciyar hankalinta duk ya tattara a hannu abunda kawai nake bukata daku shine kuje ku fadawa Shaik cewa inji ni yayi hakuri ba don halina ba da mugwayen d'abi'una da yake fada cewar ina dasu to yayi hakuri ya aura min yarsa da nake so na raya sunna da ita hakan shine samun kwanciyar hankalin yarsa daku kanku gaba daya." Nasir da Hafiz suka rasa abunda zasuce masa saboda ganin irin maganganu da yake musu na rainin hankali, Khalid kuwa yana gama maganarsa ya wuce cikin gidan Tare da bada umarni a rufe shi aikuwa masu gadi suka bugu gate da k'arfi karar gate dine ya dawo dasu Hayyacin su Nasir ya cizi ya tsa tare da fadin "Gaskiya wannan guy bashi da mutumci." Hafiz yace." Zai aikata abunda yafi haka ma mu dai burinmu ko mun bar gari yasa mu huta wannan shine kawai muje mu mu bar masa tsiyarsa a gurin." Haka suka aje ledojin a gurin suka bar gurin cike da takaici da b'acin rai.
******
Gidansu Asalamiyya ne kurrum Ammi bataje tayi sallama ba ta bari ne sai da daddare tukkuna bayan sun gama cin abinci sai ta tafi gidan, cike da girmamawa suka gaisa da juna Ummansu Asalamiyya na tsokanar ta da fadin"Matar malam sai dare ake ganin Ku.*!? Ammi tace"Wallahi kuwa dama zuwa nayi inyi miki sallama gobe insha Allah zamu tafi gombe kuma Gaskiya babu ranar dawowa watakila ma mun tafi kenan." Ummansu Asalamiyya ta rike baki ciki da mamaki tace"Bangane me kike so kice min ba Halima."!? Ammi tayi mata bayanin abunda yake faruwa Shiru tayi tana nazarin maganar daga bisani tace"Halima ni kam wannan tafiya taku batayi min dad'i ba wallahi Hanifa kuma ta bata wayonta tunda akan bare take nema ta tozarta Dan uwanta gaskiya bata kyauta ba Allah yasa haka shi yafi alkairi. " Asalamiyya ta futo ta tsaya jikinta duk yayi sanyi tace"Ammi don Allah kar Ku tafi kinji." Murya na rawa tayi maganar
Ammi tace"Asalamiyya kawarki na nema ta jawo mans abun magana a gari game da wannan yaron taki ta rabu dashi." Asalamiyya tace"Ammi kuyi hakuri don Allah Wallahi ni banga aibun sa ba mutumin da yake da farin jini kuma yana da kirki kawai dai baku fahimce shi ba." Ummansu tace "rufe min baki shashasha dama ai baza Ku gane abunda ake nuna muku ba sai Abu ya faru kizo kuna da kun sani duk iyaye na K'warai baza su so yarsu ta auri irin wannan yaron ba da ya maida mutane ba a bakin komai ha nutsatstsiyar yarinya kamar Hanifa bata dace dashi ba." Asalamiyya tayi shiru tana mamakin lamarin itafa duk aibata shi da suke da fad'ar munanan halayensa bata taba gani ko taji ance gashi ya zagi wani ba ko tayiwa wata Cikin shege tun dai abunda ya faru tsakanssa da Abbu bata taba jin ance yayi wani Abu na rashin kyauta wa a gari ba amma duka sunyi masa mummunar fahimta.
ta mike tana karayi wa Ummansu Asalamiyya sallama, har soro ta rakata ta dawo gidan jikinta duk a sanyaye sun Riga sun saba sosai gaskiya bataji dadin wannan Abu ba amma tana fatan haka shine alkairi.....Asalamiyya kuwa daki ta shige tana kuka sosai taji rashin dadin al'amarin sun shaku da Hanifa gashi zasu rabu da juna.......
Yanda taga rana haka taga dare asubar fari suka tashi kowa Yayi wanka ya shirya tsaf Ammi ta bar mata ruwan wankanta cikin tukunya jikinta a sanyaye ta futo ta juye ruwan band'aki ta shiga ta dunga kuka na bakin ciki tana tunani an rabata da Khalid Shikkenan ita ba waya ba balle ta fada masa halin da ake ciki haka tayi wanka ta futo Ammi ta kalleta taga idonta yayi fulu-fulu gyada kanta kurrum tayi ta cigaba da hada abun Karin kummalo tana addu'ar Allah ya sa karshen abun akazo..... A gurguje suka karya Nasir da Hafiz suka dunga dibar kaya suna futa dasu bakin titi nan 'yan unguwa suka San abunda yake faruwa yara da manya duk suka tsatsya suna kallon ikon Allah surutu da kananun maganganu har cikin gidajen matan aure cewa ya shaik zai bar gari zai koma garinsu gombe saboda Khalid Mashahuri, lokacin Abbakar da Mobson suna tsaye kofar shago nan Abbakar ya fahimci a abunda yake faruwa hankali a tashe ya shifa gidansu d'akinsa ya shiga da cire wayarsa da ya jona a charge Khalid ya soma kira hannunsa sai rawa yake,,,,,, Sai biyu yana kiran wayar ana masa switch up, da sauri ya futo ya tadda Mobson zai tafi yawonsa kan mashing d'insa yace." Muje maza gidansu Khalid wayarsa a kashe take." Mobson yaja mashing da gudu suka bar gurin......
*13/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:45 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI_
*_Mallakar: Binta Umar_*
*_Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar da book d'in na barki da Allah!_*
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....Binta Umar Gt bank*
*50*
Haruna na tsaye a gefan titi ya hangi tawowar Hanifa da sauri ya fara Tarar me abun hawa tana karasowa ta shiga shima ya shiga suka bar gurin.... Sai da sukayi nisa sosai diraban yace." Ina zan kai Ku."? Kai tsaye Haruna yace."kai mu tasha da sauri." Mai a dai-dai ta ya kara gudu minti goma KACAL ta kaisu tashar garin.... Suka futo Haruna ya futo da kudi ya bashi hakkinsa sannan suka shiga cikin tashar sosai gurin da ake lodin motar kano suka nufa cikin sa'a saura mutum uku ta cika suna zama da minti biyar wani ya shigo mota ta shi.
Sai da sukayi nisa da tafiya ne ta dunga jin gabanta na fad'uwa Abbu da Ammi ta tuno tana tunanin Idan suka gane guduwa tayi ya zasu ji a ransu? Wasu siraran hawaye ta goge tayi kasa da kanta don kar mutanan dake cikin motar su fuskanci wani abun, Haruna na gaban mota kusa da direba shiyasa bai san wainar da take toya ba, haka sukayi ta tafiya kan titi kowa na abunda ya dame shi Hanifa kam gabanta ne yake wata irin fad'uwa haka dai har suka isa kano ta dabo tumbin gwiwa kano ko da me kazo an fika.
Suna sauka a mota Haruna yace.'' Yanzu Kai tsaye inda yake zamu nema ina fatan kin San gidansu ko."!? Daga kai tayi jikinta duk yayi sanyi yace." Naga kinyi sanyi ki kwantar da hankali ki duk abunda kike tsammanin zai faru a gida Dole ya faru amma da anyi kwanaki zai wuce sai ki zo ki basu hakuri kawai amma hakan da kikayi shine mafuta a rayuwar ki suma baza su gane ba sai nan gaba." Ita dai shiru tayi tana addu'a cikin zuciyarta Dan sahu ya tsare ya kalleta tare da fadin"Wace unguwa ce.? A hankali tace"Shagari quetars ne ." Haruna yace." Shiga muje." Shiga tayi ta zauna jikinta a sanyaye.... Suka tafi. Tunda suka doshi layin gidansu Khalid din gabanta yake wata irin fad'uwa aikuwa gate din taga an bude wata 'bakar mota ta futo a guje motar irin tintc din na ce yasa bata gane ko wane a ciki ba, shima Khalid dake hankalinsa ba a jikinsa yake ba yasa bai gane komai ba, motar tabi da kallo nan ta gane tashi ce domin wataran yana zuwa unguwar su da ita, da sauri tace." Ya Haruna gashi can cikin mota da alama futa zaiyi." Haruna ya futo da sauri kamar zai bi motar da gudu ta Riga tayi musu nisa.... Gurin me gadin ya nufa yace"Yallab'ai don Allah bani numbar Mashahuri zamuyi magana dashi." Kallon banza ya watsa masa ya rufe gate din... Haruna ya saki baki cike da mamaki.... Komawa yayi ya sallami mai Dan sahun yana fad'in "Ai tunda munzo munyi mai wuyar insha Allah zamu samu Wanda zai bamu numbar shi, tsayawa sukayi jikin gate din suna raba ido.
Khalid kuwa da shiri ya futa kai tsaye gidansu Abbakar ya nufa lokacin suma sun shirya suna jiran zuwanshi..... Yana parking ne ya shafa jikinshi yaji babu waya takaici ya ishe shi dole tasa ya juyar da mota domin ya koma ya dauko bazai iya tafiya ya bar wayar ba saboda pictures din da yayiwa Hanifa lokacin da taje gidansu tana dashi yake so yayi amfani gurin bunkicen inda suke...... Tun daga nesa yaga kamar idonsa ne yake masa gizo hannunsa da yake draving ya kama rawa da sauri ya figi motar ya ci wani irin burki a gaban su so yake kurrum ya tabbatar IRA dince ko kuma dai ta soma yi masa gizo
Haruna na ganinshi ya futo daga cikin mota ya sauke a jiyar zuciya da har ya fara tunanin mafuta domin so yake ya koma da wuri don kar mutanan gidan su farga kuma suga bayanan zasu zarge shi..... Hanifa ganin ya nufo ta gadan-gadan yasa tayi saurin tsuguwa tana dukunkune jikinta da hijab yana zuwa ya d'aga da duka hannuwansa biyu ya hau tatta'ba fuskarta yana fadin"Beb kece ko kuma idona ne yake min gizo."!? Haruna ya karaso gurin fuskarsa a sake yace."itace ranka shi Dade." Haruna ya kalla da mamaki a fuskarsa yace." Ina ka samo min ita."!? Dariya Haruna yayi yana jin wani irin nishadi yau gashi suna magana da Mashahuri yace." Ni din ai yayan ta tana a matsayin kanwata ne."! Khalid ya saki kafad'un Hanifa ya rungume Haruna yana fad'in "Gaskiya bazan taba mancewa da Kai ba a rayuwata me kake so nayi maka ka fade shi kome nene kar Kayi shakka." Haruna yace." Ranka ya Dade bana bukatar komai a gareka ganin da nayi maka ta sanadiyar Hanifa ya gamshe ni Hak'ika naji dadin Wannan alakar taku kai dai ita shiyasa nayi ruwa nayi tsaki gurin ganin burunku ya cika gobe ne suke shirin d'aura mata aure shine na kawota Ku samawa kanku mafuta. " Khalid yaji wani irin cikin ransa wato da sai da suje suji mummunan labari Shaik ya daura mata aure da wani.... Kansa kawai yake gyadawa yana godewa Allah cikin zuciyarsa hannunta ya rike ana shi yana murzawa ya kalli Haruna tare da fadin "Mu shiga ciki kaci abunci ka huta ko kayi kokari kuma kayi jihadi." Haruna yayi dariya tare da fadin "Ai kar ka damu kawai na hango cancantar ka da ita ne shiyasa nayi Wannan abun." Shiru Khalid din yayi duk hankalinsa na kan Hanifar yana kallon yanda duk idonta ya zurma duk tayi wani firi-firi da ita sosai ta bashi tausayi yana ji kamar ya dauketa haka suka shiga cikin gidan kafadarta na gogar tashi kai tsaye part din Mamy ya nufa dasu kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki yaga muradi na zuciyarsa Hanifa.
Daf da zasu shiga ciki ne Hanifa taja tunga ta tsaya tana matse ido kallonta yayi yana marairaice fuska yace." Menene. "!? A hankali tace" Ina jin tsoron shigane."! Yace." Kar ki damu babu abunda zai faru Insha Allah Mamy zata karb'e ki hannu biyu." D'ago kanta tayi tana kallon Haruna da ya zuba musu ido yana mamakin yanda suke kaunar juna yace." Ki shiga mana babu abunda zai faru kamar yanda oga ya fada." Hannunta dake cikin NASA ta cire ta kudunfune su cikin hijab tana jin tsoron haduwarta da mahaifiyar sa tasan bata kaunarta duk da batayi wannan tunanin ba sai yanzu.... A langabe yace." Beb ki nutsu babu fa wani damuwa insha Allah kin shigo cikin family me kyau." Tana kokarin b'oye hawayen ta tace" muje to." Hannunta dai yake so ya rike ta hana haka suka shiga yana ta faman kallonta kamar zai cinye ta sai magana yake mata k'asa-kasa. Mamy na sama lokacin da suka, zama ma bai bari tayi da kanta na shi ya zaunar da ita kan kujera, ita kam kunyar abunda yake mata take ji ga Haruna yana kallo, batasan Haruna yana daukar darasi bane..... Yace." Mamy na sama bari in kirata ko."? Kai ta daga masa da sauri ya tafi yana waiwayen ta ita kanta sai mamakin rawar jikin da yake mata take.
Mamy na shirin saukowa ya shiga dakin tace"Myson meye na ganka duk a furgice." Muryarsa na Dan rawa yace." Mamy gashi can na kawo miki Hanifa please Mamy don Allah kar ki nuna mata wani Abu Mamy in dai kina son walwata da farin cikina to ki kula min Hanifa kafin in samu mafuta."
Kallonsa tayi da mamaki tace"Myson bangane ba kana nufin gombe din kaje ka dauko ta ko kuwa."? Girgiza kansa yayi yace." Mamy yarinyar ce ta kawo kanta da kanta tare da yayanta wai gobe za'a d'aura mata aure da wani shine tazo gurina muyi aure." Mamy taji kanta ya kulle tana mamakin anya yarinyar nan kuwa na da hankali! Namiji tabi ta gudarwa iyayenta kawai saboda soyayya lallai akwai alamun tambaya kan yayan NATA domin idan uwarsu daya ubansu daya da ita bazai goyi da bayan abunda zatayi ba.... Saboda samun nutsuwar yaron NATA tace"Muje kasa gurin su amma Myson nayi mamakin wannan al'amari" yace." Mamy yarinyar tana na ina sonta ubanta ya shiga tsakani." Takaici bai bar Mamy tace komai ba suka sauka 'kasa.
Hanifa na hango isowar momy gurin ta sunkuyar da kanta kasa gabanta sai fad'uwa yake, Mamy ta zauna kan kujerar da take fuskantar su fuskarta a Dan sake take amsa gaisuwar Haruna tana tambayar sa mutan gida Haruna yace." Kowa lafiya lau.
Sakkowa tayi kasa ta durkusa murya a sanyaye tace"Mamy ina yini."!? Mamy tace"lafiya Lou ya kika bar mutanan gida."!? Murya na rawa tace"Sunan lafiya Lou." Shiru parlor yayi mamy duk ta rasa me zatayi babu abunda take mamaki sai irin gangancin da yarinyar tayi gaskiya ba matar aure bace tunda zata bujere ma iyayaenta saboda son zuciyarta. Khalid kuwa no din dady dinshi yake kira so yake kawai ayi wacce za'ayi tun kafin su Shaik su Ankara da abunda yake faruwa an d'aura masa aure da ita.
Mai aiki ce ta shigo parlor ganin baki yasa ta koma kicin din ta hado musu abinci da abun sha , ta jera kam centar table din dake gabansu Mamy ta mike ta haye sama zuciyarta na zafi ganin yanda Khalid din yake ta rawar jiki akan yarinyar.... Haruna ya had'a abinci Yana ci a gurguje ya kammala ya goge bakinsa yana kallon Khalid din dake jikin Hanifa a ma'ke duk ya dagula mata lissafi sai matsawa take yana kara nanikar ta yace." Oga ni zan tafi bana so iyayen mu su farga da al'amari suga bananan nasan zasu zargi wani Abu." Khalid ya gyara zaman sa sosai yace." Ka bari dad ya dawo mana Yana kan hanya Insha Allah. " Haruna yace." Ka mik'a min gaisuwa ta gurinsa insha Allah zan kawo muku ziyara kuma ina muku fatan samun albarka cikin auran Ku." Khalid ya mike daga inda yake yana fadin"muje in kai ka shiga mota insha Allah zan neme ka idan kura ta lafa ka bani numbar wayark." Nan sukayi musayen numbar Hanifa na kallonsu hawaye na zuba a idonta murya na rawa tace"Ya Haruna idan kaje ka bawa Abbu da Ammi hakuri don Allah kace kar su kullace ni." Haruna yace." Na fada miki ki daina wannan koke koken da kikeyi komai yayi farko yana da k'arshe Insha Allah kome zaizo da sauk'i." Haka dai ya lallab'ata suka kama hanyar futa da sauri ta mike ta biyo bayansu... Khalid ya juyo yana mata wani irin kallo yace." Ki koma ki zauna Zan dawo yanzu." Tace"Muje in raka ko." Tunani yayi cikin ransa kar ta bujire idan sun je gurin shiga mota tace sai ta koma yasa ya jawo ta jikinsa da sauri ya rungume ta tsam-tsam a jikinsa yana rarrashinta Haruna yayi saurin futa ganin abunda yafi k'arfin idonsa, Mamy na kokarin saukowa ta hango abunda yake faruwa da sauri ta koma cikin d'akinta tana mamakin halin Khalid din bashi da kunya ko kadan da kuma ita yarinyar da bata da kamun kai a gidansu saurayi take bari yana taba mata jikinta ita kam da tana da yanda zatayi da ta hana auran nan jira zuwan Dady take taji wane irin hukunci zai yanks tasan dai zai bi son zuciyarsa ne da kuma ra'ayin dansa.
[1/19, 10:02 AM] .: Da kyar ya samu ta hak'ura ya zaunar da ita kan kujera ya futa da sauri. Part dinsa ya nufa minti biyar ya futo Haruna na tsaye na jiransa yace." Haruna muje kasan motar ma a waje na barta saboda farin ciki." Tare suka jera Haruna sai murmushi yake.
Kudin mota guda Khalid ya biya domin baya son a tsaya Lodi ya futo da kudi ta bawa diraba Wanda suka fi kudinsa, Haruna ya mik'awa wata fararar ta karda kana ganinta kasan kudi ne a ciki tunda ga alamarsu nan Haruna ya karba yana godiya Khalid bai bar gurin ba sai da yaga motar ta tashi sannan ya nufi inda yayi parking din tashi ya nufi gidan..... Daf da zai shiga gidane wayar shi ta fara kara yana dubawa yaga Mobson dariya yayi ya daga wayar. Mobson yace." Guy ka barmu muna jira tun dazu Allah yasa lafiya dai." Khalid ya sauke ajiyar zuciya yana shafa sumar kansa yace." Mobson Allah ya gajarta mana wahala Yanzu haka yarinyar nan na hannuna ta kawo kanta." Mobson ya kalli Abbakar dake zaune kusa da cikin mamaki.!
****
Tsumu tayi a parlor sai kalle kale take tana kallon yanda me aiki take shige da fuce tana aikace aikacen ta bata ce mata komai ba ita ma haka, motsin taji daga sama taga mamy na kokarin saukowa gabanta ya fadi da sauri tayi kasa da kanta.... Mamy ta karaso tsakiyar parlor tana kwala wa mai aiki kira ta futo da sauri tana fadin"Hajiya gani." Mamy tace"Ki kwashe Wannan kayan abinci ki gyara gurin dady na kan hanya."! Dayyiba me aiki tace"Hajiya naga bakuwar bataci abinci bane."! Momy ta nemi guri ta zauna tana fad'in "Kiyi abunda nace miki kawai." Dayyiba ta fara dibar kayan abincin tana shiga kicin dasu, Mamy ko kallon inda Hanifa take zaune bata yi ba ta kunna TV tana kalle-kallenta...... Minti goma tsakani Alhaji Tijjani ya shigo parlor k'amshin turarasa ya cika gurin Hanifa kanta a kasa take masa sannu da zuwa ya tsaya yana amsawa gami da nazarinta wucewa yayi ciki sosai mamy ta karb'i jakar hannunsa tana masa barka da zuwa ya amsa sama-sama yana tambayar ta Hanifa. ? A cunkushe tace"Myson ne ya kawota ya aje ni baiyi min bayanin komai ba amma dai yanzu zai shigo gidan." Kallon gefen da Hanifa take zaune yayi na minti biyu kafin ya dauke kansa ya nufi sama Mamy ta bishi a baya..... Suka bar Hanifa ita daya a parlor jikinta duk yayi sanyi amma har yanzu batayi na damar abunda tayi ba kamar yanda Haruna ya fada cewa komai zai wuce Insha Allah tana fatan komai din ya wuce tasan dama dole zata fuskanci matsala daga gurin mahaifiyar sa ita a ganinta Wannan ba damuwa bace tunda Khalid din yana sonta..
*19/1/2020*
_BintuUm@rAbb@le_
[1/21, 9:46 PM] BintaUmarAbbale: _MASHAHURI!!_
_*Ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, ke kuma da kika futar min da book na barki da Allah!.*_
*08089965176*
*07084653262*
*0542382124....... Binta Umar Gt bank*
*52*
Sama-sama Mamy ta amsa gaisuwarta ta cigaba da abunda takeyi Alhji Tijjani ya sakko cikin shiri yaci wata Uwar shadda me mugun tsada dinki babbar Riga da yar ciki sai kamshi ne yake tashi a gurin. Kana kallonsa kasan alhaji ne Wanda yaci ya tada Kai da kudi, bakin daining din ya tsaya yana gyara agogonsa har kasa ta durkusa tana gaishe shi ya saki fuskarsa sosai yana amsawa Mamy ya kalla da tayi kicin_kicin da fuska yace." Ki kawo min abinci parlor." Wucewa yayi Mamy ta hada masa break fast din ta dauka duk zuciyarta babu dad'i jiya kwana sukayi ita dashi suna rigima kan auran tace ita bata so shi kuma yace tunda yaro yana so sai anyi shine zai shige masa gaba kan komai kuma idan tayi wani abun da ya tada hankalin Khalid din to ranta sai ya 'baci..... Tun safe ta kira aminyarta Hajiya Zainab mahaifiyar Nasrin kenan tana so tazo suyi shawarar meye mafuta.... Hanifa cin abincin take sama-sama ta tsame hannunta tana kokarin tashi daga gurin ne ya shigo parlor saurin sunkuyar da kanta tayi gabanta na fad'uwa ganin wani irin kyau da yayi ya futo ango sak yana sanye da irin shaddar dake jikin dady nashi babbar Riga da yar ciki har dinki ma iri daya ne sai zuba kamshi yake ya Dora hula saman lafiyayyar sumar sa sai shek'i take. Ka tsaye inda take ya nufa... Cikin yanayin muryarsa yace." Ga naki kayan kije kiyi wanka ke kadai muke jira." Dago kanta tayi ta fara kwal-kwal hawaye na so ya zubo yayi sauri kauda kansa daga gareta a hankali tace"Nifa nace bazani koto ba." Cikin wani irin yanayi yake kallonta yace." OK ya kike so ayi Yanzu nifa yau din nan nake so a d'aura mana aure na shirya tafiya ta Monday komai nayi miki na tafiyar baza ki rusa min tsari ba." Tana share hawaye tace." Kawai a d'aura a gida.. Kallonta yayi na minti biyu kafin ya bar gurin. Can parlor ya nufa ya zauna kusa da dady nashi yana dafe kansa. Alhji Tijjani yace." Ya akayi ne ango. " bata fuska yayi yace"Dady yarinyar naso ta bamu matsala wai bata so aje koto." Murmushi Alhaji Tijjani yayi yana kurbar tea a hankali yace." Son yarinyar nan na lura tana kaunar mahaifinta gashi shi kuma baya kaunar ta don da yana kaunarta zai so abunda take so kamar yanda nake son abunda kake so, kasan abunda yasa bata so aje koto."!? Girgiza kai yayi cikin damuwa. Yace." Tana jin tsoro ne alkali ya bukaci ganin mahaifinta ni na gane." Khalid ya sauke ajiyar zuciya da damuwa a fuskarsa yace." Dady meye abunyi yanzu."? Kar ka damu insha Allah da an sako daga sallahr jama'a za'a d'aura auran Ku a massalaci tunda bata so aje koto Alhaji Lawan zai zama waliyinta insha Allah, duk dai bai San abunda yake faruwa ba zan masa bayanin. Komai insha Alla."
Ajiyar zuciya ya sauke hade da kwanciya kan kujerar so kawai yake yaga an d'aura auran yasan dai ko menene zai biyo baya mai sauki ne idonsa ya bude a hankali yake bin Mamynshi da kallo wacce take kokarin barin gurin ya lura tunda ya kawo hanifa gidan take sha masa kamshi to koma dai menene zai lallab'ata har ta huce fushinta.
***
B'angaran su Abbu komai ya tafi dai-dai an d'aura auran Nasiru da Wasila cikin amunce kome Abbu yake yanayin sa ne cikin tawakalli da mik'awa Allah lamuransa haka ya dunga hidima da jama'a har taro ya watse mutane yan Gaza gani suyi shiru suka dunga yi kasa jaje da abunda ya faru tunda gari ya dauka cewar yarinyar shi ta gudu haka dai yake kokarin danne damuwar sa har taro ya watse Nasiru kam sabgar gabansa yake don sai ka rantse da Allah bai taba cewa yana son Hanifa yaji zugar jama'ar gari da suke fadin "Kawai ya watsar da yarinyar tunda bata da tarbiyya watak'ila ma za'a iya yin auran ta kasheshi tunda bata sonsa wannan kallma ta bashi tsoro sosai don haka sai ya watsar da lamarin hanifa ya shiga hada hada da jama'a wato dai Wanda Abu ya shafa shi ya shafa, haka cikin gidan ma ko ina ka zauna zancan kenan mata da cancana magana masu zagin Hanifa nayi da fadin" Taje duniya ce zata koya mata hankali masu hankalin cikinsu kuwa fadi suke rayuwace ita haka kaddararta take amma gaskiya masu zaginta sun fi yawa, da gayya suka dunga shiga shashen Ammi suna yi mata jaje sai su fake da cewar Allah sanya alkairi suka shigo yi mata, ita dai haka ta daure tana Amsar baki tare da 'yan uwanta amma fa da zaka tona zuciyarta a lokacin ganin b'acin ran da take ciki sai ka tausaya mata.
****
Alhji Tijjani yayi jiran zuwan Abokinsa Alhji Lawan Wanda yake so ya karb'i waliccin Hanifa to har aka idar da sallahr juma'a bai samu isowa ba,,, haka ya hak'ura Alhji Bilya ya karb'i wallicin Khalid maimartaba da bai San abunda yake faruwa ba ya karb'i wallicin Hanifa aka d'aura aure kan sadaki dubu Dari biyu nan sarki yayi addu'a kowa ya shaida d'aurin aure aka shiga raba goro da alawa, Maimartaba ya damk'a kudin sadaki hannun Khalid tare da umartarsa ya baiwa matarsa hannu da hannu Khalid na karba suka bar gurin shi da abokansa da suka zame masa garkuwa.... Mota suka shiga cikin farin ciki suka nufi studio yau wa'kar da zai saki ta mussamance.
_Khalid kenan kanwa takar tsami kwarnafi ya kwana_
***
Alhaji Tijjani shi da Alhji bilya a gefe guda suna tattaunawa game da yanda Al'amarin ya kasance Alh bilya yace." Abunda Kayi shine dai-dai tunda dai yarinyar ita ta kawo kanta in banda abun Khalid ma nace yaje gurina ya duba mata ya'ki babu laifi hakan ko yau yayi niyyar kara ta biyu zai iya zuwa ya duba cikin yarana insha Allah. " Alhji Tijjani yayi godiya da jin abunda yace to suna kokarin rabuwa ne Alhaji Lawan ya iso gurin gaisawa sukayi cikin mutumci Alhji Lawan yace." Tum kafin in iso nan ake tayi min murna Khalid ya daura aure hakane."
Alhji Tijjani yace." K'warai kuwa tun safe nake Neman wayarka a kashe nace ko madam ce ta hana daukar wayane."? Dariya Alhji Lawan yayi yace. " ko daya yau ns yini ina bacci ne a gida gashi ban samu sallah ba." Alhji Tijjani ya shiga warware masa duk abunda ya faru.... Ransa a Dan bace yace." Alhji wannan abunda da kukayi gaskiya bai dace ba, kuma ni banji dadin sa ba tun farko idan nasan abunda yake faruwa bazan bari a d'aura auran nan bata da sanin mahaifin yarinyar nan ba, dole zan dauketa in kaita har gabansa in nuna masa illahar abunda ya aikata itama in nuna mata kuskuranta na aikata haka nasan zaiji kunya kuma zai amunce da bukatar mu saboda abunda yarinyar tayi amma a d'aura aure kai tsaye ba tare da ya sani ba akwai ciwo a ciki."
Alhji Tijjani yace." Kasan fa taurin kan mutumin nan Alhaji wallahi zamu iya zuwa har garin ya nuna bai yarda ba ni a ganina d'aura musu auran shi yafi cancanta gudun haihuwar d'a Mara ido saboda haka ka rabu dashi kawai ina ganin duk abunda ya faru shine jawa kanshi. "
Alhji Lawan yace." Dole gobe mu shirya zuwa garin tare da yarinyar domin ta nemi gafarar iyayenta abunda tayi aure dai an Riga an d'aura shi Allah ya basu zaman lafiya amma banji dadin yanda ya kasance ba." Alhji Tijjani yace." Wannan karon sai dai Kai kaje domin ni!! Bazanje gurin talaka kamar wannan mutumin ba ina rokonsa Abu yana nuna min iko aure da yarshi an d'aura sai ya barwa Allah kawai."
Alhji bilya Wanda tunda suka fara maganar baice komai ba yace." K'warai kuwa wannan magana itace dai-dai Alhji su talakawan nan ka sake ka basu fuska sai su raina ka, kawai ka kyaleshi da an kwana biyu magana zata wuce." Kallonsu yayi yana mamakin maganar su kullum maganar su kan talaka take sun ki su gane cewar mai kudi da talaka duka Allah ne ya hallice su ba da wata manufa ba, duk sun da yaso zai iya kwace kudin ya mai dakai talaka ya damka kudin hannun talaka da kake rainawa su har yanzu sun kasa gane haka sai suke ganin kamar iyawarsu ce.... Ranshi a bace yayi musu sallama ya barsu gurin
***
Hanifa zaune a cikin bedroom din da ta kwanta jiya taci kukanta ta koshi tunda taga k'arfe biyu ha wuce ta sannan an Riga an gama d'aurin aure kafin ya futa ya fada mata cewar bayan sallahr juma'a za'a d'aura auran kuka take yi tana sharbe majina zuciyarta Sam ta kasa nutsuwa guri daya sai wasi wasi take mata tana tunanin anya abunda tayiwa iyayenta ya dace shin ko yanzu wane irin hali suke ciki tasan dai duka zuciyoyin su babu dad'i tana nan zaune tana sake-sake taji hayani daga parlor shiru tayi gabanta ns fad'uwa jin kamar ana kokarin bude kofar dakin da take ne yasa tayi saurin rufe jikinta da hijab har fuskarta tana ji aka bude dakin aka shigo tare da sallama....
0 comments:
Post a Comment