Dafa kafad'ar Nasreen INDO tayi cikin tausayin halin da take ciki tace.
" Ki daina kukan Nan haka Nasreen, zaki cutar da kanki, Babu makawa wannan Auren sai anyi shi, to meye Amfanin kukan naki, dan Allah ki daina.
Ai kuwa kamar wacce Indo ta k'ara tunzura Nasreen, ta k'ara sautin kukan nata, cikin kukan ne tace.
" Kuka ya Zama Dole a gareni Indo, ko banyi kuka dan takaicin Auren Jungud'o ba, zanyi kuka domin Bak'in cikin da aka k'ulla min na kaini gidan miji da kayan d'akin mahaifiya ta, meyafi wannan bak'in ciki Indo? Ki fad'a min idan banyi kuka ba, me zanyi banda gata a duniya banda mai bin kaduma, ki duba fah kiga Indo, duk cikin dangin mu, aka rasa mai hana Baba kaini gidan miji da kayan d'akin Ammi na, cikin matsanacin kuka ta k'arasa maganar.
Tashi Indo tayi itama cikin hawaye, tace bari naje wajen *NAYI NA* na manta tace naxo na karb'a Miki sako.
Nasreen bata tanka Indo ba har indon ta fice daga d'akin.
Inna Asabe ce yar AMMI take ta faman Rarrashin Nasreen, amma ita Nasreen kamar k'ara zugata suke.
MAMA kuwa yau Zuciyar ta fari tas take jin sa, ko banxa tasan Nasreen gidan wahala zataje koda masifar mahaifiyar jungud'o aka barta ya isheta, bare kuma shi jungud'o tantirin d'an Iska kuma mashayin giya.
Itama yar gwal ba'a barta a baya ba, wajen, jin dad'in abunda ya samu Nasreen, sosai take yiwa Nasreen habaici da isgilanci, ita dai Nasreen saidai ta d'aga ido ta kalle ta, ta sunkuyar.
*JUNGUD'O* kuwa baki yak'i rufuwa, yau Ansha wankan manyan kaya harda, gare, an kifa Hula Zanna bukar, biyu kawai yake jira ta cika su nufi masallaci wajen d'aurin Auren shida abokansa.
Karfe d'aya saura Khabeer da Sadiq suka iso cikin k'auyen, darect k'ofar gidan su Nasreen Khabeer suka nufa, yara Khabeer ya hango suna wasa k'ofar gidan yayin da mutane ke shige da fice cikin gidan, kallon Sadiq Khabeer Yayi yace.
" Ya za'ayi muga yarinyar nan ne kam, naga ma kamar ma biki suke Cikin gidan.
Kallon Khabeer d'in shima Khabeer yayi yace.
" Ka aika yaran nan mana suyi ma kiran ta, kawai tunda ita ba baya gare ta ba bare a kirata.
Juyawa Khabeer yayi da niyan kiran yarinya d'aya a wajen ta musu kiran Nasreen, sai kawai suka had'a Ido da INDO tana k'ok'arin shiga cikin gidan.
Dariya INDO tayi tare da nufo Khabeer cikin jin dad'in ganin sa, sanda taxo daf da motar nasu ta tsaya tare da cewa.
" Kwad'o Kaine a garin namu yau, Lale marhaban.
"Murmushi Khabeer Yayi yace.
" Nice Indo, yau ba kiwo kenan, nagan ki ke d'aya ba tare da shanun ba.
" Eh wlh kwad'o ana bikin k'awata ce, Yau.
" Ayya kice yau Amare kuke, daman kuwa Kinga ina neman wanda zai min sallama da Nasreen d'in gidan nan sai kuma gaki Allah ya kawo ki, ko zaki min kiran ta.
Cikin mamaki Indo tace
" Wacce Nasreen d'in, ai itace ake Auren ta yau.
What Khabeer ya ambata da k'arfi, " kina so kice an d'aura Auren Nasreen yau.
" A'a ba'a d'aura ba sai k'arfe biyu za'a d'aura, kuma Abun haushin ma, bata son Auren, Auren dole zasu Mata.
" Auren Dole kuma cewar SADIQ, Akan me za'a mata Auren dole?
" Akan son Ra'ayin Iyayen ta, ita bama Auren Dolen bane, damuwar ta, wanda za'a Aura matan ne, d'an giya.
Tsawa Khabeer ya dakawa Indo sai da ta tsorata yace
" Kinsan me kike Fad'i kuwa, su iyayen nata mahaukata ne da zasu Aura mata d'an giya, haba ki dinga fad'in Abunda hankali zai d'auka Mana.
Kallon Khabeer tayi cikin jin haushin tsawar da Khabeer ya Mata tace.
" To kwad'o k'arya zan maka, tana fad'in haka ta juya da niyar barin wajen cikin fushi.
Da sauri Khabeer ya dakatar da ita domin kuwa shi ya fahimci Gaskiya Indo ke fad'i,
" Yi hkr y'an mata dan Allah ki tsaya.
Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba.
Kallon Khabeer SADIQ yayi tare da banka masa harara yace.
" Sai ka samu damar fitowa ai Uban y'an zafin Zuciya wanda baka cin ribar Zance.
Fitowa sukayi tare suka bar junior a cikin motar yana shan baccin sa.
Fiskantar indo SADIQ yayi tare da cewa.
" Baiwar Allah dan Allah gaya mana meke faruwa da yarinyar nan ne, wani irin Hali ne da ita marar kyau da za'a dauke ta a bawa d'an giya Auren ta.
" Bata da wani mungun Hali ko kad'an sai ma makircin kishiyar mahaifiyar ta wacce itace sanadiyar wannan Auren da Kakar ta, Saboda tsabagen Rashin k'aunar da suke Mata, sunyi wannan abunne dan ganin sun lalata Rayuwar Nasreen, na Rasa me Nasreen ta tsare musu ita da mahaifiyar ta, tsanar da suke Mata Yayi yawa, cikin kuka Indo ta k'arasa zance.
K'wafa Khabeer Yayi yace tabbas biri yayi Kama da mutum, Nasan wannan mafarkin da nayi dama dole akwai abunda ke faruwa.
Ko kafin SADIQ yayi magana Khabeer ya rigasa ta hanyar cewa,
" A ina zan Samu shi MIJIN da za'a AURA matan.
Shuru Indo tayi, sannan tace
"baxai wuce yana gidan su ba.
" Ko zaki iya kaimu gidan nasu Khabeer ya tambaya Indo.
" Me zaku masa idan na kaiku d'an mai gari ne fah.
Murmushi Khabeer Yayi yace.
" Babu abunda zamu masa kedai ki Mana rakiya.
" Shikenan muje Amma da k'afa zamuje mu.
"Ba damuwa muje da k'afar cewar SADIQ.
Security Khabeer yasa a motar yabar junior a ciki suka d'auki hanyar gidan mai gari.
Isar su k'ofar gidan sun
Tarar da k'ofar gidan mai garin cike da mutane sai kad'e kad'e da raye raye ake, tsayawa sukayi a gefe yayin da ita Kuma INDO ta kutsa kanta zuwa cikin gidan, da k'yar da taimakon Buba k'anin jungud'o Indo ta sami ganin jungud'o, bayanin yana da baki a waje ta masa, duk da yad'an yi mamakin su waye suka zo neman sa, bayan shi yasan baida wasu bak'i da zasu zo neman sa, binta yayi suka fito k'ofar gidan da Indo.
Har inda su khabeer suke tsaye Indo takai jungud'o sannan ne tace.
" To kwad'o ga jungud'o ni zan koma gida kar a neme ni.
Murmushi Khabeer yayiwa Indo tare da ciro kud'i a aljihun sa, dubu biyar ya bawa Indo.
K'in karb'a Indo tayi, acewar ta bata buk'atar su, Khabeer yayi yayi da indo ta karb'i kud'in Amma tak'i, haka sai hakura Khabeer yayi ya kyale ta tare da Mata godiya.
Har ta fara tafiya Khabeer ya tsayar da ita ta hanyar ce mata,
" kar tacewa Nasreen sunxo k'auyen nan.
Amsawa tayi da to sannan ta shige.
Kallon Sama da k'asa Khabeer ya k'arewa jungud'o tare dayin tir da Allah wadaran wad'anda suka had'a wannan Auren idan ba Rashin hankali da kuma cuta ba, ina Nasreen ina Auren wannan d'an iskan k'auyen.
Hanu jungud'o ya mik'o musu suyi musabaha, SADIQ ne ya mik'a masa hanun, Amma shikam Khabeer, nad'e Hanun sa yayi cikin Aljihun sa yak'i basa, yana Ganin hararar da Sadiq ke aika masa ya kawar da kansa gefe, kansa na kallon gefen ne ya fara magana cikin nutsuwa, tare da gadara.
" Kaine jungud'o Koh? Ya jefa masa tambaya.
" Eh nine cewar jungud'o cikin tunanin waye wad'annan d'in.
" Kasan da cewa Wacce zaka Aura bata sonka, Koh?
Cikin k'osawa da maganar sa, jungud'o yace.
" Na sani sai Akayi Yaya, iyayen tane suka gaji da ita, suka kawo min tallen ta da kansu kaga kuwa, bani ne nasa aka mata Auren dole ba, wannan iyayen ta ya kamata ka koma ka tuhuma.
Murmushi Khabeer Yayi har saida fararen hak'oran sa suka bayyana, cikin yabawa izza irin ta jungud'o.
SADIQ ne zaiyi magana Khabeer ya d'aga masa Hanu, yace.
" So nake ka fasa Auren ta, ka maida Auren kan yar uwar ta, mema take da suna 🤔 yawwa yar gwal take ko yar zinare, koma menene sunan ta ban damu ba, nidai kawai buk'ata ta ka fasa Auren Nasreen ka Aure ta, idan har ka min haka zan baka millions 5 idan kuma kak'i Amsa buk'ata ta, zakayi *biyu babu* zaka rasa Nasreen tare kuma da rayuwar ka, tare da ciro bindiga ta gefe yanda mutane baxasu gani ba ya nuna Masa *Dan haka zab'i ya rage Naka*, Ka zab'i *Rayuwa ko mutuwa*.
Jungud'o da tun Sanda Khabeer ya nuna masa bindiga ya fara rawar d'ari tare da k'ara ja da baya, cikin in iyna na yace.
Nafi k'aunar rayuwa ta fiye da Nasreen, na yadda na zab'i Rayuwa ta, sai dai buk'atar ka na na Auri yar gwal baxai yiwu ba har sai ka Bani kud'in Hanu da Hanu, Niko na maka Alk'awarin Auren yar gwal a yau d'in nan.
Dariya SADIQ yayi cikin Jin dad'in yanda basu wani sha wahalan samo kan jungud'o ba, tare da d'agawa Abokin nasa yatsa alamun jin jina👍🏻.
Murmushi Khabeer Yayi tare da cewa muje mu baka da matsalar kud'i, sai dai ina k'ara tabbatar maka cewa, sab'awa umarni na, dai dai yake da Rasa Rayuwar ka.
" Na yadda muje cewar jungud'o.
Jerawa sukayi da jungud'o har k'ofar gidan su Nasreen inda sukayi parking d'in motar tasu, wata k'aramar jaka Khabeer ya bud'e motar ya ciro, tare da kallon junior da har yanxu baccin sa yake bai farka ba, bud'e jakar yayi sai ga rafas rafas na dubu dubu, mik'awa jungud'o yayi yace, 4 millions a nan, zan cikata maka sauran kud'in daga baya, ko kuma mu juya dakai, cikin gari na cire kud'i a Bank na baka, kaga yanxu bamu da times muje Koh saura 1 hours ne, a shiga sallah ya kamata kaje kasan yanda zaka wargaza wannan Auren.
Juyawa jungud'o yayi tare da cewa yanxu ma kuwa.
Bayan tafiyan jungud'o ne Khabeer ya jin gina kansa jikin motar sa tare da sauk'e ajiyar zuciya, a fili yace.
" Alhamdulillah na taimaki Rayuwar y'ar ki mamy, domin kuwa bana son ki dawo k'auyen nan cikin bak'in Ciki, har Uku, na rashin Nuruddeen da Kuma b'atar y'arki.
Muryar SADIQ yaji yana cewa,
"baka gama taimakon ta ba Khabeer muddun ka tafi ka barta a haka, to tabbas ka kara jefa cikin wani tashin hankali da masifar ne.
Kallon SADIQ Khabeer Yayi yace
" ban gane me kake nufi ba? Kamin magana yanda zan gane.
Ajiyar zuciya shima SADIQ yayi tare da cewa.
" Ka raba Nasreen da Auren Jungud'o, sannan Kuma ka had'a y'ar Uwar ta da Auren shi, baka tunanin Idan har ka tafi ka barta cikin wannan K'auye, bazasu k'ara neman wani wanda ma yafi jungud'o munanan halayya su had'a ta dashi Aure ba.
Shuru Khabeer yayi zuwa can yace.
" Tabbas maganar ka zata iya kasancewa Gaskiya, domin kuwa, a d'an zaman da nayi dasu na kwana biyu na fahimci irin k'iyayyar da wannan Matar take yiwa yarinyar nan, shiyasa ma yanxu na mata *k'aik'ayi koma kan mashek'iya*.
Menene solution yanxu SADIQ?
" Solution d'aya ne kawai Khabeer, shine kafin mubar K'auyen nan, a d'aura maka Aure da yarinyar nan.
Kallon baka da hankali Khabeer Yayi SADIQ, sannan yace.
" Kasan me kake cewa kuwa, ko ka manta da cewa ina da Mata ne, sannan Kuma Babu niyar mata biyu cikin Rayuwata, na tsara Rayuwata ne da mace d'aya kawai.
Kai mai zai hana kayi wannan taimakon tunda kaga kai baka da Mata single kake, sai mu sami ladan tare.
*************************
Tun fitar Khabeer Zuhura ke Hauka ita d'aya cikin gidan, kuka take tana surutu ita d'aya.
" Wlh baxaka tab'a K'ara Aure ba, domin kuwa ni kad'ai ce matar ka danni kad'ai aka Halicce ka, Babu wacce ta isa shigowa cikin gida na, muyi sharing d'in miji da ita ba, wallahi bazai yiwu ba, ina sonka Khabeer bana son ko wacce Mace ta rab'eka koda kuwa Y'AR UWAR KA ce ta jini.
Khabeer Idan har kace zaka *K'ara Aure sai na kashe duk wacce ka Auro*
Zuhura fah yau ta haukace Akan kishi domin kuwa, gabaki d'aya ta hargitsa kayan d'akin ta, harta zanin gadon ta bai tsira ba, shima sai da ta yaye shi ta wurgar gefe.
Sorry sister's wlh yau ina busy ne, shiyasa na muku typing kad'an, kuyi hkr dashi Babu yawa.
*Share*
*And*
*Comment*
*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻
*(Ummu Nasmah)*
[12/29/2019, 1:47 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏
⛏⛏⛏⛏
*SARA DA SASSAKA*
*(Baya Hana Gamji)*
*Toho*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳🌳🌳
*Story And Writing*
*By*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
🤳🏻
*08147537180*
*(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Sadaukarwa*
Na sadaukar da wannan page d'in gare ku.
*Amina Abubakar*
*And*
*Mu'az*
Wannan page d'in naku ne kuyi yadda kuke so dashi, domin kuwa Gaskiya ina Jin dad'in yanda kuke min shares na book D'ina, Allah ya bar k'auna na gode sosai.
P••••••••5️⃣4️⃣ to 5️⃣5️⃣
" Ni ina da wacce nake so, Kuma ka ganta yau a cikin gidan mu, duk da ban sanar da ita soyayya ta ba har yanxu, amma ina da tabbacin zata Soni, please Abokina duk da bansan yarinyar nan Nasreen ba, Amma na fahimci Halin k'uncin rayuwa da take ciki, ka taimaki Rayuwar ta Khabeer.
Wani Irin kallo mai wuyar fassarawa Khabeer ke yiwa SADIQ, kafin cikin Halin ko inkula yake cewa.
" Idan shikenan abunda zaka fad'a kana iya shiga mota mu tafi Koh.
SADIQ dai bai daddara ba, yaci gaba da cewa.
" Khabeer kayi tunani kafin mubar Nan, kar kaxo kana danasani daga baya, a lokacin Kuma time's ya k'ure maka.
" Na gaji dajin wad'annan tatsuniyar taka, SADIQ, gani nayi kaima fah a Yanxu kana da Halin da zaka Auri Mata sama da Hud'u ma idan anayi, ka Aure su mana dukan su, dole sai ni zaka tursasa Nayi abunda banyi niyya ba, ko kuma zanyi Aure ba tare da sanin iyaye na bane, please SADIQ na rok'eka ka shiga mota mu tafi.
SADIQ bai k'ara cewa komai ba ya shiga motar Khabeer yaja suka bar k'ofar gidan su Nasreen.
Ita kuwa Mama Y'AR GWAL ta kira gefe tare da bata kud'i dubu Arba'in tace.
" Ki rik'e su da kyau, ki kaiwa Malam kice masa iya Abunda ya samu kenan, ya baki sak'on ki kawo min, saura kuma Idan ya baki, shima ki fasa, kiga yanda zanyi dake a cikin gidan nan.
Karb'a y'ar gwal tayi, tana tura baki tare da k'unk'uni, ta fita.
" Sai yanxu kika dawo ne INDO, naga kin juma.
" Ehh wlh Nasreen, Nayi ce ta aikeni, shiyasa na juma, sak'on naki ma tace sai ta shigo anjuma.
" Ayya Babu damuwa, bari na zaga bayan gida,
Jungud'o kuwa ya tada bori a wajen d'aurin Aure, shifa Baya son Auren sa da Nasreen, saboda suna da Abun kunya cikin zuri'ar su, Uwar ta ta shiga duniya yawon karuwanci, haka ma y'ar Uwarta, dan haka shi da y'ar gwal yake son a d'aura musu Aure.
Mari mai gari ya d'auke jungud'o dashi, tare da cewa.
" Baka isa ba wlh, baxaka mai Dani tsohon banxa ba, wani Irin rashin hankali ne wannan, za'a d'aura maka Aure da yarinya ka dawo kace baka sonta Y'AR UWAR TA kake so, ba zai yiwu ba to.
Baba ne yace Babu damuwa, ranka shi dad'e, nine mahaifin Nasreen da Amina, dan haka na amince a d'aurawa Jungud'o Aure da AMINA.
Har gitsewa gidan yayi da hayaniya, kowa yana mamakin Baba, wannan wani Irin Uba ne, yak'i y'ar ka, kuma ka basa wata Y'ar taka.
Shiko Baba ba komai yasa yayi hakan ba, sai dan ya nunawa Mama kuskuren ta, saboda yana sane tsaf da itace ta had'a Auren Nasreen da jungud'o, ta hanyar tunzura Goggo, baya k'aunar Auren Nasreen da jungud'o, Babu yanda ya iya ne, yasa ya amince, yasan Halin Goggo zata iya daina magana dashi kan wannan Auren, kuma fushin Uwa akan d'anta masifa ce babba.
Mai gari ne yace
" Mlm Musa kasan Abunda kake cewa kuwa.
" Na sani ranka ya dad'e, a d'aura Auren kawai.
" Shikenan tunda Kaine kace haka da kanka.
Sun kusa ficewa daga cikin Rugar wani tunani yaxo zuciyar Khabeer.
" Karfa nabar garin nan, su d'aura Mata Aure da wani Irin jungud'o, ya Mamy zataji a zuciyar ta idan ta dawo ta samu, duka rayuwar yaranta ya lalace, ya kamata koda Nasreen d'in ce ta tsira, ciwon zaizo Mata da sauk'i fiye da ace duka Babu Ingantacciyar Rayuwa.
Reba's yayi tare da juyawa cikin Rugar da bala'in gudu yana cewa SADIQ zanje na taimaki Rayuwar ta, kodan Saboda mutuncin mahaifiyar ta, da kuma k'aunar da take yiwa d'ana junior, sai ina son ka zama shaidata, bawai zan Auri Nasreen da niyar zama da ita na har Abada bane, zan Aure tane domin na inganta mata Rayuwar ta, ta hanyar fitar da ita cikin gari, tare da bata ilimin da zata dogara da Rayuwar ta, ina mata wad'annan abubuwa zan sauwak'e mata, taje ta nemi miji tayi Auren ta.
Murmushi SADIQ yayi, cikin jin dad'in zancen Khabeer yace hakan ma Yayi, Amma muyi sauri mu k'arasa karsu watse daga wajen d'aurin Auren.
Cikin 15 minute suka k'arasa masallacin Juma'a na Rugar, sun Samu har an d'aura Auren Jungud'o da y'ar gwal ana raba goro, k'arasawa sukayi wajen, tare da mik'a musu Hanu, mlm Iro da Mlm Musa sunyi mamakin ganin Khabeer a wannan lokaci, bayan sun gaisa ne, Khabeer ke cewa mlm Musa, yanxu shigowar su garin, sake jin abunda ke faruwa na fasa Auren Nasreen da Jungud'o yayi, Gaskiya Baba banji dad'in Abunda ya faru ba, shine na yanke shawarar cewa Zan Auri Nasreen Idan har ka amince mini.
Kallon kallo aka hau yi a wajen tare da sauraron Amsar da Mlm Musa zai bawa Khabeer.
Yayin da jungud'o kuma ya sake baki yana kallon Khabeer,
"wato so yake ya Aure ta, shine yasa zai had'ani da kud'i da bindiga, yace na fasa Auren Nasreen, Allah ya isa to tsakanina da kai.
Nisawa Baba yayi tare da cewa.
" Khabiru ka tab'a ganin inda aka d'aura Aure ba tare da sanin iyaye ba, kaje ka nemo yardar iyayen ka, ka dawo ni kuma zan baka Auren Nasreen.
SADIQ ne ya nisa tare da cewa.
" Mahaifin Khabeer ya Amince Mana, asali ma bamu xomu nan ba saida muka nemi yardar sa, yace mucewa mlm Iro ya karb'awa Khabeer Auren idan har ka yadda zaka had'a zuri'a dashi.
Saurin kallon SADIQ Khabeer yayi, Jin k'aryar daya tsula take ko tsoro baya ji.
Washe Baki shi kuma mlm Iro yayi jin ance Uban gidan sa yace ya karb'a masa Auren d'ansa.
" An gama ai mlm Musa tabbas y'arka ta Samu miji na gari da kuma surukai na gari muddun ka bawa khabiru Auren y'arka.
Mai gari ne yace.
" Kunsa wad'annan d'in ne da suke maganar a basu Aure.
" Mun sansu Ranka shi dad'e, nuna Khabeer yayi yace, a gidan mahaifin sa nake Aiki, shi kuma mlm Musa, shi yake kiwon shanun mahaifiyar sa.
" Alhamdulillah cewar mai gari, Mlm Musa shawarin da zan baka itace ka d'auki yarinyar nan ka basa, kaga dai cikin garin nan zaiyi wuya ta samu mai Auren ta, kasancewar Abun kunya da Uwarta da y'ar Uwarta suka bar Mata.
" Babu damuwa mlm Musa yace, na yadda a d'aura Auren Allah yasa hakan shine Alkairin ta.
SADIQ ne ya ciro kud'i dubu d'ari ya dank'awa mlm Iro sadakin Nasreen, amsa mlm Iro Yayi shima ya dank'awa mlm Musa, k'in karb'a mlm Musa yayi yace, a rage kud'in sunyi yawa.
SADIQ ne yace,
" A'a Baba karka damu, sadaki baya yawa, mudai buk'atar mu, Allah ya sanyawa Auren Albarka.
Babu yanda mlm Musa ya iya haka ya k'arbi sadakin inda aka d'aura *AUREN MUHAMMAD KHABEER ISAH BABA DA NASREEN MUSA TUKUR AKAN SADAKI NAIRA DUBU D'ARI*.
Inda mutanen gari suka watse suna gulmar cewa mlm Musa ya sayar da y'arsa domin kuwa babu wacce aka tab'a bada sadakin ta sama da dubu 15 a K'auyen sai Nasreen mai dubu dari.
Da gudu shehu mak'ocin su MAMA ya shiga cikin gidan yana k'walawa MAMA kira.
Da sauri MAMA ta fito daga cikin d'akin ta, tana cewa.
" Lafiya Shehu har an d'aura Auren Nasreen d'in ne.
Tab'e bakin sa Shehu yayi cikin gulma da tsegumi yake cewa Mama.
" Cewa zakiyi har an d'aura Auren nasu ne, ai Aure biyu aka d'aura, k'asa yayi da muryar sa yace, Mama Salame, ashe daman Auren nan cutar ki za'ayi to bari kiji, Nasreen ba jungud'o ta Aura ba, wani Attajiri d'an Binni, kinma sanshi wanda yaxo kwanakin nan.
" Ehhh na ganesa k'arasa min zancen da sauri.
" To shi Nasreen ta AURA ba jungud'o ba, sadakin ta ma dubu d'ari ne, sai kuma aka Aurawa y'ar gwal jungud'o.
" Kasan me kake cewa kuwa, kaga bana Irin wannan wasan da kai meye had'in y'ar gwal kuma da Dan giya, ai sai dai Nasreen d'in marar Gata.
" Wallahi da gaske nake Mama Salame, wlh y'ar gwal ce ta Auri jungud'o Nasreen ce ta Auri wannan d'an Binnin.
*DAM !! DAM !! DAM DAM !! DAM* kike jin k'irjin Mama ya bugae, dafe k'irjin tayi tare da yanke jiki ta fad'i.
*************************
MOMY SARAH da Hajiya Hindatu, suna zaune waje d'aya cikin cell d'in, duk wanda yasan Momy Sarah da, ya ganta Yanxu baxai gane ta ba tayi bak'i ta rame, duk ta fata hayyacin ta, a Yanxu Momy Sarah ta fara Nadamar abunda ta Aikata tun kafin ma a yanke mata hukunci, tana kuma shirye da ta fad'awa Khabeer gaskiyar inda John yake, ko a Mafarki bata tab'a tsammanin cewa Asirin ta zai tonu ba, duk da ta kawana biyu bata ga Khabeer ba, Amma tana shirye a duk lokacin da yaxo ta bashi good information Akan k'ungiyar su.
A yau daddy ya kawo mata ziyara cell d'in, inda aka fiddota domin su gana.
Sunkuyar da kanta k'asa Momy Sarah tayi domin kuwa tana kunyar hada Ido da Daddy, bata da Idon da zata kalle sa dashi, kanta a sunkuye ta gaishe da Daddy.
Amsawa Daddy yayi tare da ce Mata.
" Saratu dubi yanda kika maida Rayuwar ki Abun tausayi, da gatan ki da mutuncin ki, duk kika manta dasu kika ta Aikata b'arna, a yau an wayi gari Saratu kin zubar da mutuncin ki dana yaran ki, gashi Sanadin wannan Abun kunya da kikayi, Kinsa Khalid yabar garin nan, ya wurgar da matar sa da ciki ya tafi yabar ta, duk ta dalilin ki, yaran ki mata kullum suna cikin k'unci, ina zaki kai wannan zunubin Saratu.
Shuru Momy Sarah tayi ba tare da tacewa Daddy komai ba, har time d'in da aka basu ya cika, Momy Sarah taki tankawa Daddy bayan gaisuwar da ta shiga tsakanin su.
Sai da daddy ya tafi ne Momy Sarah ta fashe da wani Irin kuka mai cin rai, a Yanxu ta tsani kanta, ta tsani HAJIYA BARA'ATU domin kuwa duk itace tasa ta cikin wannan mummunan Halin da take ci, sai yanxu ta yarda da sharrin k'awa da kuma Zuciya duk sune suka sata wannan Halin da take ciki a Yanxu. " Kaicona ni Saratu na cuci rayuwata, gashi yanxu inda son Abun duniya da son zuciya ya kaini.
Momma da Mamy kuwa zama suke na lafiya da Amana, komai tare sukeyi hatta ga girki.
Suna zaune a falo ne momma take cewa Mamy ya kamata ta bata labarin Rayuwar ta, tunda an zama daya ai yanxu.
Murmushi Mamy tayi tare da cewa yanxu kuwa.
Daddy dake shigawa ne yace.
" Kuce nayi sa'ar shigowa da wuri da ansha labari banda ni.
Dariya sukayi dukan su, sannan Mamy ta fara cewa.
Nan zan dakata sai kuma gobe, saboda ina busy, kuyi hkr idan kun sami, kuskure cikin Rubutun yau Saboda banyi editing ba Gaskiya.
*Share*
*And*
*Comment*
*Alk'alamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah)*
[1/1, 12:39 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏
⛏⛏⛏⛏
*SARA DA SASSAKA*
*(Baya Hana Gamji)*
*Toho*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳🌳🌳
*Story And Writing*
*By*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
🤳🏻
*08147537180*
*(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Deducated to
All fan's of SARA DA SASSAKA baya hana gamji toho.
Ina sonku kamar yanda kuke Sona.
Sannan ina neman Addu'ar ku, zan fara Exam Ranar Alhamis.
P•••••••5️⃣6️⃣ to 5️⃣7️⃣
" Suna na Maimuna, ni y'ar Asalin cikin garin Dukku ne, a wata K'aramar Rugar fulani, wacce ake kira da Rugar Buba, mahaifina Mlm Nura yana da matar sa d'aya mai suna Aishatu, Mutanen gari na kiran ta da Sogiji amma mu muna ce Mata Innah, yaranta Uku ne kacal a duniya, Sani shine babba muna kiran sa da suna Bandirawo, sai Zainabu Wacce muke kira da Yaya Asabe, tayi Aure harda yaran ta Hud'u, sannan ni Auta cuna cemin, Bod'd'o, na taso cikin gata da kulawar iyayena da y'an Uwana, tsabar soyayyar da suke min yasa mahaifina da Bandirawo, sanda na cika shekara 12 a duniya, suke tafiya dani wajen kiwon shanun su acewar su basa son suyi nisa dani, kasancewar mahaifina makiyayi ne, niko nakan jin dad'in tafiya dasu kiwon, domin suna kula dani fiye da yanda ya dace, sab'anin mahaifiya ta, da bata min Abunda suke min acewar ta zan sangarce, shiyasa bana yadda na zauna kusa da Innah indai Baffa na yana nan.
Wata Rana a can wajen kiwon namu, na gamu da wani matashin saurayi mai suna Musa, d'an gefen Rugar mu, ana Kiran Rugar tasu da Rugar Ard'o B'oyi, da farko da wasa muka Fara dashi yakan yawan zolaya ta, a haka sabo mai tsanani ya shiga tsakanin mu, har soyayya ta fad'a Mana, wata Irin soyyayah muke, mai Tsananin Gaske, wacce muke jin baxamu iya Rayuwa ba, idan Babu d'aya, Amma duk soyyayar da muke bamu tab'a yadda iyayen mu sun Sani, muna soyyayar mune a b'oye, kwatsan Rana tsaka sai Baffah ya gane akwai soyyayah tsakanin mu, Hakan ce ta sashi kiran Musa ya ajiye sa, tare da tambayan sa gaskiyar abunda ke tsakanin mu, Musa bai b'oyewa Baffah komai ba, yayin da Baffah yaji dad'in jin zancen Musa, ya Kuma yi masa na'am akan yaje ya turo mahaifin sa idan da Gaske yana sona.
Sai a Ranar nake jin cewa Musa yana da Mata, Amma baida yara ko d'aya, kasancewar Allah baya bar masa yaran ana Haifan su suke komawa.
Duk da jin da nayi Musa Yana da mata, hakan baisa naji wani Abun a Raina ba, kuma na shiryawa Auren sa, koda kuwa matan sa Uku ni zanje ta Hud'u.
Dangina dana Musa sunyi na'am da Auren mu, sai labarin matar sa, da mukaji tace, badai na shigo gidan ba, sai dai idan mutuwa tayi.
Nida iyayena hakan sam bai d'aga mana hankali ba, acewar mu, haukar kishi ke damun ta, mahaifiya ta kullum cikin fad'a da nasiha take min da kuma yanda zan zauna da kishiya, alhamdulillah kuma ina d'aukar duk abunda ta fad'a min kamar hadda.
Wata Rana ana saura sati bikin mu, Musa yaxo Rugar mu, naga rigar sa, kamar Alamun manja, naso nayi shuru ban tambaye sa, ba, sai na kasa hkr, har saida na tambaye sa.
Bud'ar bakin Musa cemin yayi Uwar gidan kine, ta watsa min manja jikin kayana wai dan kar naxo Hira.
Zaro ido waje Nayi tare da cewa " Daman da gaske ne Abunda ake fad'a Akan Matar ka.
Kallo na Musa Yayi tare da cewa, Kinga Maimuna mubar zancen nan, kinsan fah mutan gari da gulma tare da yad'a k'arya, kawai mubar zancen nan.
Shuru nayi ba tare da na k'ara d'ago masa zancen ba har ya koma.
Bana mantawa A Ranar Alhamis ana gobe za'a d'aura Aure na, a ranar kwana nayi banyi bacci ba, ina mugayen mafarkai, kasancewar Allah Yayi mai yawan ibada, hakan yasa na d'an samu sassauci, Amma fah na kwana cikin wahala, tun daga Ranar na dage da Addu'a, Azkar safiya da maraice baya wuce ni,.
Washe gari Juma'a aka d'aura Aure na, da Musa, iyayena sun min fad'a sosai kafin a kaini d'akin mijina.
Bayan an kaini ne, da yamma lis, goggo Addaji k'anwar mahaifiya ta, da Yaya Asabe suka d'auke ni zuwa d'akin Uwar gida domin kai Amanata, tun daga kallon da Uwar gidan Musa ta Mana, Wacce suke Kira da mama Salame, zaki san Babu mutunci gunta, Amma hakan bai kashewa yan uwana gwiwwa ba, goggo Addaji ne ta fara magana.
" To Uwar gida, ganan k'anwa na kawo miki Amanar ta,. Da fatan zaki Amshe ta, Hanu biyu, idan tayi ba daidai ba, a gyara Mata, ita kuma Maimuna, baxata sab'a miki ba insha Allah.
Tabe bakin ta, Mama Salame tayi cikin isa da iko take magana.
" Ban d'auki wannan Amanar ba, ina son ku tashi ku fice min daga d'aki tunda babu kud'in wani tsoho cikin ginin d'akin nan, kin Aure min Miji sannan kuxo kuce ga Amana an kawo min, ai Babu Amana tsakanina da kishiya.
Tashi Goggo Addaji tayi tana Allah wadarai da Halin Mama Salame, muka bar d'akin ta Zuwa nawa d'akin.
Sanda su Goggo Addaji zasu tafi nasiha suka min sosai tare da cewa na rik'e Azkar domin kuwa wannan Uwar gidan nawa Babu Imani cikin lamarin ta.
Godiya na musa, ina kuka suka fice suka barni.
Da farko zamana a gidan mlm Musa, MAMA Salame bata, shiga lamarina, ganin da tayi ina mata biyayya yanda ya dace, hatta ga girki, nice meyi har Ranar girkin ta, Mlm Musa yana jin dad'in yanda nake wa Salame biyayya, A idona Salame ta haifi yara wajen Uku Babu rai, kasancewar ni ban samu haihuwa da wuri ba, kwatsan rana tsaka sai Allah ya bani Ciki, wohoho kuxo kuga Bak'in Ciki wajen Salame, tun daga Ranar da akace ina da ciki Salame ta fara min mugunta da nemana da masifa, sai dai ban tab'a nuna mata ya dameni ba, kuma bawai bana jin zafin Abunda take min bane, ina ji hakuri ne kawai nake da Salame duk dan a zauna lfy, tsabar wahalan da Salame take bani shine yasa ciki na zubewa, Salame taji dad'in hakan sosai, tun daga yanayin ta zaki gane farin cikin da take ciki baya misaltuwa, Niko Nayi hkr na rungumi k'addara, wata takwas da zubewar ciki na, sai Kuma Allah ya K'ara bani wani cikin, wanda shi Kuma duk muguntar Salame baisa ya zube ba, hakan ne yasa Salame, fara shiga malamai dan Azabar da cikin a cewar ta, ita bata haihu ba nima baxan haihu ba, tasha barbad'a min magani cikin Abinci, zan kuma yi Bismillah tare da Addu'a naci, duk yanda Salame zatayi cikina ya zube tayi amma yaki zubuwa, hakan yasa Salame, fara zagina da gaya min bak'ar magana, bana kulata, watan Ciki na tare da kwana goma na haihu, inda na samu yarinya mace, Salame Ranar Hauka ce kawai batayi tsabar Bak'in ciki, dan ko ruwa ma k'in daura min tayi, sai da Mahaifiyar mlm Musa Goggo taxo ta d'aura min, kasancewar goggo tana sona fiye da Salame, Ranar Suna y'ata taci suna Nasreen, tun Nasreen bata san kanta ba Salame take mata mugunta, har duka tana mata, amma ban tab'a nuna mata ina jin haushin Abunda take yiwa Nasreen ba, shekarar Nasreen d'aya ita ma Salame Allah ya bata Ciki, murna wajen Salame ba'a magana.
Nasreen nada shekara d'aya da wata tara Salame ta haifi y'arta mace itama, aka rad'a mata Suna Amina inda Salame take kiran ta da y'ar gwal, sosai Salame take nunawa Y'ar Gwal soyayya, ko kusa da y'ar gwal Nasreen taxo Salame sai ta maketa, ta ta hantarar ta, muna cikin wannan Halin ne Allah ya K'ara bani Ciki, kuxo kuga murna wajen mlm musa, a cewar sa Allah ya Azurta shi da zuri'a, a wannan karon Salame, har guba ta samin a cikin Abinci, Allah ya kiyaye banci ba.
Salame fah ta rasa Yaya zatayi dani cikin gidan mlm musa, duk wani muguntar ta, baya tasiri a kaina, haka Kuma asirin ta baya cina, na K'ara haihuwar y'ata Mace, taci suna Nabiya, Nabiya tun tana zama na fara gane tana da fad'a, Sanda Nabiya tayi shekara, Uku a duniya Salame ko hararar ta tayi saita rama, duk fad'an da dukan da Salame zata mata sai tace mata Allah ya isa, Amma duk Salame tafi tsanar Nasreen na rasa me Nasreen taci Mata a duniya ana haka fa na K'ara Samun Ciki, Ranar cikin dare Salame ta kama ni da kokuwa tana k'ok'arin dukan Ciki na, Mlm Musa ne ya kwace ni da k'yar Hanun ta, a Ranar kuwa ya yiwa Salame Saki d'aya, Har na haifi d'ana Nuruddeen mai sunan mahaifina, mlm Musa bai dawo da Salame ba saida Nuruddeen, yayi shekara Uku kafin mlm Musa ya yadda nan ma dakyar ya yadda ya dawo da Salame, tun dawowar Salame nake fama da ciwon kai mai Tsananin Gaske, kullum mlm Musa cikin karb'o min magani yake, wata Rana bana mantawa muna Zaune tsakar gida dukan mu har da yara, bud'ar bakin Salame sai take cewa insha Allah Maimuna kin kusa barin garin nan, yanda kikayi sanadiyar igiyar Aure na d'aya haka kema sai kin bar garin nan, d'ago Kaina Nayi na kalleta ba tare dana tanka ta ba, bayan Salame tayi wannan maganar baifi da sati d'aya ba, na shiga ban d'aki, tunda na shiga naji Kaina ya juya min daga lokacin naji bana k'aunar garin burina kawai naga nabar garin, hakan ne kuma ta kasance, na fice nabar garin mu, Amma duk abunda nake hankali nah yana jikina magana ne kawai baxan iya yiba, har had'uwa ta da Alhaji, zuwa yanxu danake baku labarin nan hankali na bai tab'a barin jiki na ba.
Kallon momma tayi tace wannan shine labari nah.
A nan zan dakata sai gobe zamu dawo cikin labari, masu zuwa gidan mai gari kai Aure Kuyi hakuri sai gobe kuje kuci tuwon dawar ku miyar kuka🤪
*Share*
*And*
*Comment*
*Alk'alamin Rasheedat Usman*✍🏻
*(Ummu Nasmah)*
[1/3, 10:11 AM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏
⛏⛏⛏⛏
*SARA DA SASSAKA*
*(Baya Hana Gamji)*
*Toho*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳🌳🌳
*Story And Writing*
*By*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
🤳🏻
*08147537180*
*(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Deducated to*
Amina Abubakar.
Ina yinki irin overn nan, kamar yadda yanda kike son book ɗina.
5️⃣8️⃣ To 5️⃣9️⃣
Ko kafin mamy ta gama bada Labarin tuni Hawaye na tausayin Baƙar wahalar da mamy tasha wajen Mama, ya wanke fuskar momma, kallon mamy mommo tayi, tace.
" Lallai maimuna kinsha wahala a hanun Salame, wannan matar zaiyi wuya tayi ƙarshe mai, domin kuwa ta Aikata munanan Ayyuka a rayuwarta, kiyi hkr maimuna insha Allah zaki ci ribar hkr.
Daddy ne ya nisa yace,
" Alhamdulillah mun godewa Allah, tunda gashi yanxu kin samu lafiyar jikin ki, saura kuma idan An gama case ɗin Saratu, muje garin naku tare dukan mu harda shi khabirun, Ubangiji ya ƙara miki hkr sai kuma ki dage da Azkar, bari naje na watsa Ruwa.
Tare daddy da momma suka tashi, tayi ɗakin nasa domin haɗa masa Ruwan wankan.
*************************
Jijjiga Mama suke suna ƙiran sunan ta Amma ko gezau Mama bata yi ba, Gabaki ɗaya ƴan Aure sun taru tsakar gida cikin, al'ajabin mai ya samu Mama, mero ce ta kasa hkr ta dubi Shehu tace
" Kai Shehu mai ya sami Salame, gani nayi kuna magana ta yanki jiki ta faɗi, me kace mata?
Cikin tsoro, Shehu yace.
" Nifa wlh Innah mero ba wani Abu nace mata ba, cewa fah kawai nayi bada junguɗo aka ɗaurawa Nasreen Aure ba, da ƴar gwal ne.
Salati kowa ya ɗauka tare da cewa,
" Shehu kasan me kake cewa kuwa bada Nasreen aka ɗaura Aure ba, da ƴar gwal, chap *wannan shi ake kira Dara taci gida* cewar Asabe ƙanwar mamy.
Ita ko Nasreen wani irin sanyi taji a ranta, *Lallai Allah maji Roƙon Bawan sa ne, gashi Allah ya rabani da Auren junguɗo Alhamdulillah* Nasreen ce ke maganar zuci.
Juyawa tayi ita da innah Asabe, suna mai godiya ga Allah, suka shige ɗakin Ammi, ba tare da damuwa da Halin da Mama take ciki ba.
Da ƙyar suka samu Mama ta dawo hayyacinta, Amma dai tun farfaɗowar ta, bata kula kowa ba, sai hawayen dake gudu samar fuskar ta, ita kuwa ƴar gwal har yanxu bata dawo daga gidan boka da Mama ta aike ta ba.
Tare Baba da su khabeer suka jero har ƙofar gidan, khabeer ne yace.
To mufa Baba zamu koma, saboda dare ya fara kawo kai, naga yanzu har 3:30.
Kallon khabeer Baba yayi yace.
" Khabiru ka tsaya na shiga na fito maka da matar ka, ku tafi tare, zaman Nasreen cikin wannan ƙauye da Auren ta, zai zama abun magana, gara ka tafi da ita, babu kuma wanda zai bika Saboda ina tsoron kar wani Abu ya faru kasan mutanen karkarar nan namu sai a hankali, sihiri ba komai bane a wajen su, ka tafi da ita daga baya koni zan Kawo goggo da Halima suxo suga wajen zaman ta, itama goggo baxan sanar da ita ba sai bayan kun tafi.
Shiru khabeer yayi kasancewar baiso haka ba yaso sai yaje ya sami iyayen sa, sun tattauna tukunna, sai dai baxai yiwa Baba musu ba, dole yasa shi amsawa Baba da to.
Iso Baba ya musu zuwa ɗakin dake cikin zauren gidan. Sannan ya shiga ciki.
Ɗakin mamy ya shiga ya sami Innah Asabe da Nasreen suna zaune, sannu da shigowa Innah Asabe ta masa sannan ya sami gefe guda ya zauna, ya mata bayanin yanda ɗaurin Aure ya kasance, tare da ce mata.
" Yaron kirki ne na sansa nasan gidan su, asali ma shanun da nake kiwon su na mahaifiyar sa ne, zasu tafi da mijinta, kuma bana son kowa ya bisu, yanda yayiwa Khabeer bayani haka itama ya mata.
Hamdala Innah Asabe tayi tace.
" Alhamdulillah tunda ka yadda da Asalin sa ai shikenan, Allah yasa hakan shiyafi Alkairi, tashi Baba yayi yace, Innah Asabe ta haɗawa Nasreen kayan ta zata bi mijinta su tafi, yanzu.
Nasiha sosai Innah Asabe tayiwa Nasreen, sannan ta haɗata da kayan ta, ta rakota har ɗakin zauren.
Shiko Mlm Musa fitowar sa daga ɗakin Ammi, Innah mero ke cemasa Salame bata da lfy.
Allah ya ƙara sauƙi yace, sannan ya shige ba tare da ya leka ɗakin nata ba.
Kusan tare su Nasreen suka shiga ɗakin da Mlm Musa, Nasreen kanta a ƙasa ta gaishe su, yayin da sadiq ya tashi a firgice yana nuna Nasreen da hanu.
" Na Na Nabiya, Kardai ace kene Nasreen yar nabiya.
Saurin ɗago Ido Nasreen tayi tace.
" Ina kaga Nabiya, ina take dan Allah.
Zama sadiq, tare da kallon Baba dake zaune shima, sannan ya gaishe da innah Asabe, shima khabeer cikin mutunci ya gaishe ta.
Mlm Musa ne ya jefowa sadiq tambaya, ina kasan Nabiya.
Amsa masa Sadiq yayi da cewa, mahaifiya tace ta tsince ta, yanxu haka tana gidan mu hanun mahaifiya ta.
"Alhamdulillah cewar Baba, Allah kaine abun godiya daka tsare min ƴata.
Gaskiya naji daɗi sosai, kuma insha Allah zan samu lokaci naxo khabiru ya kaini gidan ku, domin na godewa mahaifiyar ku.
Kamo hanun Nasreen yayi ya haɗa dana khabeer yace.
" Khabiru ganan ƴata Nasreen na baka Amanar ta, khabeer ka riƙe min Nasreen kamar yanda Uba yake riƙe ƴarsa, karka cutar min da ita, idan ta maka laifi ka mata hukunci kamar yanda Addini ya tana da mana.
Itama Nasreen kallon ta yayi yace.
" Nasan ke mai biyayya ce da hkr, ina son ki ƙara akan wanda kike dashi, Nasreen ki Sani zaman Aure ba zaman wasa bane, kibi mijin ki domin aljannar ki tana tafin ƙafar sa, ki sani cewa mijin da kika Aure yana da iyalinsa, bake ƙadai bace, karki Raina matarsa koda wasa, kibi iyayen mijin ki da ƴan uwansa, ki kasance mai kyauta, da sakin fuskar cikin mutane, ki zama mai hkr a duk inda kike Allah ya muku Albarka.
Da ameen suka Amsa Nasreen tana kuka ta shiga mota suka tafi.
Ita kuwa ƴar gwal, da gudu ta shigo gidan, Innah mero ta samu a tsakar gida, cikin haki take cewa Innah mero da gaske waini ce aka Aurawa junguɗo.
" Ehhh dai dai kika ji, kece kika Auri junguɗo.
Wani irin ƙara ƴar gwal tasa tare da sakin kwalbar da boka ya bata ta kawowa Mama, kwalbar na isa ƙasa ta tarwatse, fashewar ta keda wuya Mama ta fito a guje tana dariya tare da tsire ɗankwalin ta tayi jifa dashi gefe, sai kuma ta fara soshe soshe tana tonawa kanta asiri,
" Nice na yiwa maimuna asiri ta shiga duniya, nice nayi asiri goggo ta tsani ƴaƴan maimuna, haka tata tonawa kanta asiri, zurawa tayi da gudu tayi waje, binta Mlm Musa sukayi tare da wasu manzan dake waje amma duk da haka sun kasa kama Mama ta shige jeji.
Dawowa Mlm Musa yayi, ita kuwa ƴar gwal Babu abunda take sai kaku, da daddare Mlm musa yasa aka ɗauki ƴar gwal aka kaita gidan mai gari, ɗaki ɗaya ne aka saka ƴar gwal nanma ko siminti Babu Babu wata tarba da aka bawa ƴan kawo amarya ko arzikin ruwa basu samu ba, bare abinci, haka suka juyo suka dawo suka bar ƴar gwal cikin ɗakin ta.
A bige junguɗo ya shigo cikin gidan yana warin giya, haka ya faɗawa Ƴar gwal ba tare da cika sunnar Manzo ba.
Kuyi khr da wannan ina jarabawa ne.
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah)*
[1/6, 8:13 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: ⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏⛏
⛏⛏⛏⛏
*SARA DA SASSAKA*
*(Baya Hana Gamji)*
*Toho*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳🌳🌳
*Story And Writing*
*By*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
🤳🏻
*08147537180*
*(MAKAMAR KAINUWA)* 👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Deducated to*
Mu'az
Amina Abubakar
Momyn Ajmal
Munaya
Wannan Page ɗin naku ne kuyi yanda kuke so dashi.
*P* 6️⃣0️⃣ to 6️⃣1️⃣
Ƙarfe huɗu da rabi khabeer suka iso cikin Gombe, SADIQ ya fara sauƙewa, tare da Cewa SADIQ gobe ya kawo masa Nabiya misalin ƙarfe goma na safe, inyaso kayiwa Hajiya bayanin komai, idan yaso ko da hajiyar sai kuxo tunda Daddyn ku baya nan.
" Ba damuwa khabeer insha Allah zamu xo kallon Nasreen da kanta ke ƙasa yayi, yace.
Amarya me maganar suger, sai gobe, a ajiye min sauran kaxar amarcin zanzo, na ƙarasa miki Ita.
Murmurshi Nasreen tayi A hankali tace Allah ya kaimu goben, ka gaishe min da Nabiya.
" Zataji insha Allah, khabeer sai ka ganni, junior kam yana bacci ya buɗe Ido ya gansa, kusa da Uwar sa.
Dariya khabeer yayi tare da cewa Allah ya kaimu, ka gaida min da Hajiya.
" Zataji SADIQ yace sannan ya shige cikin gidan nasu.
Jan motar khabeer yayi ba tare daya ɗaga kanka Ido ya kalli Nasreen ba, khabeer yaso bin gidan su, amma gara kawai ya shige gidan sa, idan yaso gobe yaje gidan nasu, da safe, da wannan tunanin khabeer ya nufi hanyar gidan sa.
Daniel Khabeer ya samu zaune bakin get ɗin gidan shida Isma'il, Bayan yayi parking ne, suka zo tare da miƙa masa gaisuwa, kallon rashin sani suke bin Nasreen dashi, lura da hakan da khabeer yayi ne yasa shi ce musu kowa ya koma bakin Aikin sa.
Muje ya cewa Nasreen.
Binsa a baya Nasreen tayi, har cikin falon nasa, da sallama suka ƙarasa falon, Zuhura dake zaune, a cikin falon ne ta ɗago kanta, ta sauke sa kanna khabeer, da junior dake maƙale a kafaɗar mahaifin nasa.
Tashi tayi da sauri ta nufo Khabeer tana ƙoƙarin karɓar junior cikin dariya da murnar ganin ɗan nata data fara cire rai dashi, sai kuma idon sa, ya sauƙa a kan Nasreen dake tsaye bayan khabeer, ta sunkuyar da kanta ƙasa, kallon mamaki da wulaƙanci tayi mata, sannan tace.
" Abban junior waye wannan? Tana nuna Nasreen da hanu.
Kallon Nasreen yayi, cikin halin ko inkula yace.
" Nasreen ce wacce take Mazaunin matata a halin yanzu, yau ɗinnan aka ɗaura mana Aure da Ita.
" Na shiga Uku, Aure khabeer, sai Kuma tayi dariya tace, kaga ka daina min irin wannan wasan, banso yana tsinka min Zuciyata.
" Babu wasa tsakanina dake a halin yanzu maganar gaskiya nake gaya miki, kinga karɓi junior ki kwantar dashi.
" Dallah dakata min malam✋ kasan me kake faɗi kuwa Aure da wannan kazamar bafulatanar, hmm Idan ma mafarki kake to ka farka, domin kuwa Babu kai Babu ƙara Aure a rayuwar ka, har Abada, dani kaɗai zaka ƙarasa rayuwar ka.
Kallon Nasreen tayi, cikin tsawa tace, ke kuma malama fice min daga gida kafin na miki mungun dukan da baxaki Amfanu ba.
Cikin tsoro da rawar jiki Nasreen take ƙoƙarin juyawa tabar cikin gidan.
A Zuciyar ta kuwa cewa take na shiga Uku, nabar wahala na dawo cikin wahala.
Kamo hanun Nasreen khabeer yayi tare da kwantar da junior kan kujera, bai Kuma tankawa Zuhura ba, yaja hanun Nasreen yana ƙoƙarin shiga da ita ɗakin sa.
Tare gaban sa Zuhura tayi,tace.
" Wlh yarinyar nan bazata zauna cikin gidan nan ba idan ba so kake yau ayi kisan kai cikin gidan nan ba.
Murmurshi khabeer yayi mai sauti, kafin yace.
" Idan kin tashi kisan kai ɗin, akwai bindiga cikin dressing merro na, zaki iya Amfani da ita, kinga daga nan zaki ƙarasa rayuwar ki a gidan kaso.
" Sai dai kuwa na ƙarasa rayuwar tawa a gidan kason amma muddun kabar yarinyar nan cikin gidan nan tabbas sai na kashe ta.
" Mahaukaciya sai kuma kitayi, yana faɗi mata haka yayi cikin ɗakin sa da Nasreen, tare da ture Zuhura gefe, ya sawa ƙofar key.
Hauka Zuhura take tsakanin ta da Allah tana zagin khabeer, tare da masa fashe fashe cikin falon, khabeer yana jin haukar da Zuhura take, yayi banxa da ita.
Kallon Nasreen yayi, tare da miƙo mata take away ɗin da suka saya a hanya tare da abun sha, yace.
" Gashi, ganan banɗaki ki tashi mu shiga na nuna miki yanda ake amfani da kayan ciki, sannan ki tabbatar kinyi brush, ma'ana kin wanke bakin ki kafin kixo kici abinci ni zanje office sai Anjuma zan dawo, cikin tsoron kar khabeer ya fice ya barta da Zuhura ta tashi suka shiga tollet ɗin, ya nuna mata komai kafin ya fito ya barta, Bayan ya fito ne yasawa kofar key yanda duk haukar Zuhura baxata iya buɗewa ba.
Tana zaune tayi kaca kaca da falon yayin da duk ta fasa hanun ta da kwalaben turaren wuta, jini ne kawai ke zuba a hanun nata, sunkuyawa khabeer yayi tare da ƙoƙarin kamo hanun nata dake zubar da jinin, saurin kwace hanun ta Zuhura tayi tana cewa,.
" Na tsaneka khabeer bana son ganin ka, ka matsa daga kusa dani, mungu azzalumi, macuci ka cuceni, ka faɗa min dame na rageka dashi da zaka ƙara Aure meye bana maka, Allah ya isa tsakanina dakai baxan taɓa yafe maka ba ka cuceni.
Tashi khabeer yayi tare da ficewa daga gidan ma gabaki ɗaya, dan ya lura Zuhura neman masifa take dashi.
Ganin ficewar khabeer yasa Zuhura tashi tayi kitchen ɗinta wuƙa ta ɗauko tare da nufo ɗakin khabeer, sai dai Kash ɗakin rufe yake gam da key Babu halin ta buɗe, duk iya dabarar ta, ta kasa buɗewa, zagin Nasreen take daga bakin ƙofar tana cewa, ki buɗe ƙofar nan, idan kika bari na buɗe, wlh sai nayi ajalin ki, cikin gidan nan, zaki san kin Auri mijina, nice ajalin ki.
Ganin da Zuhura tayi Nasreen bazata buɗe bane, yasata komawa saman kujera, tare da sakin wani marayan kuka, mai ban tausayi.
Nasreen dake cikin ɗakin tama kasa cin abincin tsabar masifar tsoron Zuhura daya tsarga mata, gani take kamar Zuhura zata ɓalla ƙofar ta shigo, addu'a ta shiga yi cikin Zuciyar ta, tare da neman tsarin Ubangiji daga sharrin Zuhura.
Oh ni kuma tawa ƙaddarar kenan ta shan wahala, ya Allah ka duba wahalar dana sha a baya ka, kareni daga sharrin wannan matar, ka rabani da ƙara shan wani wahalar.
Shi kuma khabeer darect office ɗin su ya shige, office ɗin Kamal ya shiga tare da zama, bayan sun gaisa ne khabeer, ya fara yiwa kamal tambaya game da yanda case ɗin su Momy Sarah ke tafiya.
" Ranka ya daɗe yau kwana biyu kenan Momy Sarah take cewa tana son ganin ka.
" Momy Sarah Kuma? Okey bari naje naji abunda ke faruwa.
Tana zaune ta haɗa kanta da gwiwwa, Gaba ɗaya ta rame ta fice hayyacinta idan ka ganta baza kace Momy sarah da ka sani bace.
" Momy Sarah khabeer ya kira sunan ta
Ɗago kanta tayi, tare da kama hanun khabeer, tace
" Khabeer nayi dana sanin abunda na aikata cikin rayuwata, gashi yanxu ba'aje ko ina ba, na fara girban Abunda na shuka kaicona khabeer gashi mungun Aikin da nayi yasa, ɗana ya shige duniya yabar matar sa, na cuci rayuwar ƙananan yara da basu san komai ba, a duniya, nayi sanadiyyar lalacewar yaran mutane da yawa, kaicona khabeer, daga kai har mahaifiyar ka, kun riƙeni da zuciya ɗaya ni kuma na cuce ku, maganar take tana kuka sosai har tana ajiyar zuciya.
Oga John da kake nema, yana India, cikin birnin mumbai, a unguwar kwalkwata, ka kawo wayana zan tura masa text ɗin cewa ina zuwa jibi cikin India ya faɗa min inda zamu haɗu, zai kira ni a waya domin ya tabbatar da cewa nice na turo text ɗin, kai kuma kayi ƙoƙari zuwa jibi ku haɗu, idan kuma ka sake baku haɗu ba, to tabbas ka rasa John kenan.
Khabeer yaji tsusayin Momy sarah sosai, har takai ga idon sa ya ciko da kwalla.
" Na gode Momy da bani wannan information da kikayi, sannan kici gaba da tubawa Ubangijin ki, shine kikayiwa laifi, zai kuma yafe Miki.
Sawa khabeer yayi aka kawo wa Momy sarah wayar, ta turawa John text, ba'a juma da tura text ɗin ba, john ya kira, inda Momy sarah tace masa zasu haɗu, duk abunda suke khabeer ya danna recording.
Bayan sun gama ne khabeer ya fice daga office ɗin cikin tsusayin Momy sarah.
*Share*
*And*
*Comments*
0 comments:
Post a Comment