🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣4⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*****************
*ABUJA NIGERIA*
........ Ya juya da sauri ya kalli Anjelina Yana magana kasa kasa..... Jeki ce su bude kofa ta fita da sauri...
Ta rike kugu tana ta faman masifar su bude kofa zata wuce.
Ya juya a hankali, yana kallonta ta wutsiyar ido. Matsattsar doguwar Riga light pink ta saka da Dan karamin gyale fari iya wuya, kafarta cikin dogayen takalmi....
Anjelina na fada musu sukayi saurin bude Mata..... Ta bude baki iyyehhh ikon Allah yau Allah ya kawo mu ShopRite shiga da izini fita haka..... mtseww ta buga tsoki ta wuce..... Ya tuntsure da dariya....yarinyar can wata Rana sai ta janyo mun rigimar da za a daureta.
Ya fito a hankali Yana leke duk aka bishi da ido..... yallabai lafiya?
Yayi murmushi Ina zuwa ya fita da sauri.
Tana faman zuba kayan bayan mota.
Ya fiddo waya da sauri ya kirata, ya lafe bayan wata mota.
Ta zumburo Baki kafin ta dauka alamar tayi fushi ya kyalkyace da dariya Yana hangenta.
Sai yau ka tuna dani?
Allah ya Baki hakuri ayyukan ne sunyi yawa Kuma kinsan kauye service din waya sai a hankali... always excuses mtseew.
Yayi murmushi kiyi hakuri ai Yanzu na dawo gari Daman wasu Kaya ne muka siyo......
Naji dan kasuwa, Ina wuni......ta fada tana kokarin shiga mota ya musu nuni da hannu, alamar motar can zasu bi.
Ya manta ma da abinda ya kawo Shi,ya Abuja kina Jin dadin ki fa.
Hmmm kawai tace.
A hankali Yana janta da labari suna bin su a baya har suka je gwarunfa a road *111* gidan yake flat 4 Nan ne gidan su Bilkisu..... Next week fa za a koma school nasanka da Kara kwanaki wannan semester din ka Kara Alalh sai munyi fada...... Amma dai ba ranar da aka koman Zan dawo ba ko? Na Kara ko sati biyu.....daya dai wallahi Nima ranar Zan dawo......
Ya kyalkyace da dariya Hajiya kice kawai kina neman lift Kuma matsalar ba tare da Sadeeq nake dawowa ba Mai rabo ni har na gayyaci wasu.....mtsew a a ka manta... shikenan kayi zamanka....ta ajiye wayar daidai lokacin da motar ke kutsa Kai cikin gate din gidan.
Ikon Allah har taji haushi?...... Kamar yaje gidan yakeji Amma baya so yayi hakan Yanzu.
Komin dare yake son komawa kano, haka suka juya Yana waigen gidan.
Bai kirata ba, ya Bari sai zuwa anjima........
Suka kura ma jaridar ido, daddy yayi murmushi ai yaron nan ne wallahi. Na fada Miki kinki yarda Amma Bari Bilkisun ta dawo muji cikakken sunan sa a bakinta Amma tabbas prof. Hamza yace mun lokacin da na saka ayi binkice Kan dabi'un sa da irin rayuwar da yakeyi makarantar......
Da gudu ta shigo, mommy na samo cheese din kuwa....... Ba sallama?
Assalamu alaikum...ta fada tana dariya.
Gardama mukeyi da dadyn ku akan Anwar meye cikakken sunan sa?
*Hamza Yusuf Hamza*...... Duk suka kalli juna shida ita da sauri,..... Ta zaro ido lafiya? Yanzu Ina fitowa ShopRite ya kirani kuwa.....yace me? Duk suka hada Baki.
Ta tabe baki gaisawa kawai mukayi da yake kwana biyu bamuyi magana ba ya ce sunje kauye siyo ma ubangidan su wasu Kaya..... Nace damuwata ya koma school da wuri kada ya barni da tararrabi inyi ta zare ido saboda idan Yana kusa da anyi ban ganeba ya mun bayani shikenan.....
Aikin meye yake?
Daddy ya Kara bukata...... Daddy hoooo nace maka wani yake mawa fa tsaron shago sukeyi a sabon gari market...this is what he told me na.....
Tohhhhh, ai Yanzu muka fahimta. Jeki ciki abinki.
Kin yarda Yanzu da maganata?
Ta zaro ido shine da gaske wallahi.....baya son fada Mata Shi wanene Kuma makarantar ma badda sawu yayi.
Ba tace first class din ma boyewa yayi ba?.... Tabbas.
Yayi murmushi, shikenan mu Sanya su addu'a Kar ki saki Koda wasa ki sanar da ita, wata kila Yana da dalilinsa nayin hakan....
Hmmm. Tace duk jikinta yayi sanyi tana Kara maimaitawa a zuciya *Hamza Yusuf Hamza bushara* Shi ne *Anwar* ikon Allah.
Karfe biyun dare ya sauka Kano.
Bai Sami kwanciya ba sai uku saura, Shi yasa ya makara washe gari wurin tashi.
Sha biyu saura ya farka tun bayan da yayi sallar asubah ya koma.
Ko juyin farko batayi ba ya mirgina ya janyo wayarsa....... Cikin magagi ta dauka hello.......shine Kika ajiye mun waya jiya ko?.
Hmmm, ina kwana..... Duba agogo ki gani Sha biyu ta wuce kike faman ina kwana.
Ina labarin Suleiman,
Lafiya Lau.
Shi Dan wane gari ne....Ina ruwanka ta fada tana tashi zaune.
Yayi murmushi lallai dai Kam, babu ruwa na.
Next week result zai fito waye zai Miki registration?????... Suleiman nake turawa kudi Yana mun.....kenan yasan password din portal dinki....why not?
Shine ni ban sani ba?
Tayi dariya kawai.
Kinji?.
Nawa ka samo kasuwar? Nawa ne share na Kuma?
Ya kyalkyace da dariya....sai nazo zamuyi lissafi.
Ehee, hakan ya kamata.....tana so tace mishi suyi video call tana Jin nauyi.
Sun kusa awa kafin suyi sallama.
Tunda ya dawo Kano ayyuka sukayi mishi sauki a Rana sai suyi waya sau hudu, chatting kuwa Koda yaushe suna online.
Ya rasa inda zai Sanya kansa da tayin Yan mata.
Sati daya da komawa Bilkisu ta koma, Shi Kuma yace Mata sai satin sama, Amma duk Rana daya suka dawo Yana son Bata surprise ne banbancin shigar dare sukayo sosai don lokacin da suka zo dutsinma daya saura na dare.
.......ya kalli sadeeq an dawo fagen fama.
Suka kyalkyace da dariya.
Sadeeq ya Kara langabe Kai ka dubi girman Allah ko roba roban ne ka sai Mana muma wannan semester din...... Allah ban saye ka Bari kawai muyi ta aro muna 3 in1 hakan Yana matukar birgeni da saka ni nishadi......mtsew..kada Allah yasa ka siya mugu, ya wuce.
Ya bishi Yana dariya, inba kaiba Bilkisu duk duniya Yanzu kunfi sanyani ciwon Kai.
***************
*Federal University dutsinma*
Hutun ya amshe ta, tayi kiba ta Kara yin jawur, Bata son zuwa lecture din Dr Richard munafuki saboda ta tsane Shi. Kuma Yana iya bada test idan yaga ajin ba mutane.
Milk lace ne ta saka Yana da ratsin flowers orange dinkin Riga da skirt, sannan tabi da doguwar hijab.
Agogo kawai ta daura sai zoben azurfar da ke hannun hagu.
Tafiya take kanta a kasa, wani haushi take ji har cikin zuciyar ta idan ta tuna class din yau ba Anwar.
Ga mamakin ta ajin cike fiye da rabi duk an dawo.
Daga nesa Helen ke ihu oyoyo Bilki beauty....
Tana Yar dariya tana Kara sauri tare da ware hannu suka rungume juna.
Kinje America ne irin wannan fresh haka?....
Ta tun tsure da dariya suka fada aji........ Karaf sukayi tozali, ta zaro ido Anwar??????
Ya sakar Mata murmushi kawai, wani dadi ya ziyarce ta kamar ta ruga ta rungume Shi takeji, ya Kara kyau shima yayi haske, tayi kasa da Kai kawai tana murmushi.
Tana Shirin Zama ya taso... Helen move, ya janyota da hannu ya fiddo ta sit din, Shi kuma ya zauna.
Wani mugun kishi ya turnuketa ta kalleshi a hasale ji yanda ka wani kamata ba ka iya cewa ta wuce ko ta gafara dole sai ka cacukumota? Ta Kara sa maganar tana maka mishi harara......
An Kuma dawo fa, yau din nan har na Fara tabka laifi?.
Au hakan da kayi daidai ne??? To ka je Kama kadaddabeta Anwar mtseww ta doka uban tsoki.
Ya dafe Kai, ohhh my God, naji ban kyauta ba kiyi hakuri bazan Kara ba shikenan ko?
Kinji?
Naji, ta fada.
Ina tsarabata?
Ya Mika Mata hannu....... Tana daki na yi tunanin baka dawo ba.
Jeki daukon Ina jiranki.
Kana jirana a Ina? Lecture din Kai zaka mun?
Ai ba zai zo ba Yanzu ya Aiko kafin ya karaso...... Mtsew mutumen nan baiyi ba wallahi.
Tashi muje in baka......ta mike.
Ya shafa Kai da hannu, kije ki dauko mun Ina nan ki dawo.
Inje in kuma dawowa?
Eh, Mana.
Idan na biki muka je kina bani zaki gudu......ta yi Yar dariya in gudu kamar wata marar gaskiya?
Eh, nidai jeki dawo Ina Nan..... Me zakayi anan din?
Jiranki zanyi kawai har ki dawo, a a idan na tafi ka gama sai ka biya ka karba kawai.....wallahi bazan karba ba kuwa, ki je ki dawo akwai labarin da Zan baki.
Ta koma ta zauna, mu gama labarin tukun sai mu tafi tare ka karba.
Ya kalleta better.....
Ina Suleiman Shi bai dawo ba?
Wallahi ban sani ba.
Yasu mommy?
Lafiya Lau.
Meye Kika siyo mun tsaraba?
Tayi Yar dariya kana sauri ne? Ka jira zaka gani Mana..... Ina salalar business dina?
Ba kince zamuje na siya Miki abinda kikeso ba?
Tabbas, Amma dole inji dumus Kuma.....ya kyalkyace da dariya har Yana dukan table....Yan aji duk suka maido hankalin su sai dai ba Wanda kejin me suke cewa.
Watau kiji dumus...... Ta kalleshi tana murmushi eh Mana....... Ashe da gaske ka dawo.... Sukaji magana daga sama kwatsam, duk suka dago *Mufeeda ce* tsaye tana murmushi Tasha wanka..... Ya Dan Sha mur kamar bashine ya Gama dariya Yanzu ba.... Eh na dawo ya kike?
Qalau, ya hutu?
Lafiya.
Dan Allah kazo minti biyu Ina son magana...... Kodai ki Bari sai anjima ko Kuma ki fada anan.
Anjima yaushe.
Evening may be.......
To anjiman zamu hadu, ta juya ta wuce....
Mikewa tayi,
Ina zakije? Ya bita da idanu.
Ta tsuke fuska, daki.
Saboda mufeeda tazo?
Ta dalla mishi harara ta Isa ta koreni ne?
Idan Bata Isa ba ki zauna to, ko don kinji nace Mata anjima? Wallahi don ta kyaleni Ina zata ganni anjima din?.....
Na sani? Ai zata maka waya ko baka zo ba ko?
Wallahi na Miki alkawari bazan dauki wayar ta ba ko da ta kirani.
Kiyi hakuri zauna.......
Ta koma ta zauna. Ya kalleta Yana Yar dariya, saurayin ki ya shiga uku don kina da kishi sosai da sosai.
Tasha mur batayi magana ba.
Wayarsa tayi Kara, Yana dubawa yaga Alh. Murtala. Ya mishi text cewar zai Kira anjima.
Ya kalleta, haka shima Suleiman kike saka mishi doka da horashi Akan kula Mata?
Murmushi kawai tayi tace humm.
Ina ruwana da su? Kawai bana son raini ne?
Kiyi hakuri Zan Mata fada sai ta ringa Baki girma........
Ta kalleshi, ya gyara fuska alamar ba wasa.
Cikin semester din nan Zaki fiddamun gwana cikin su, Aure nakeso gaskiya.....
Saura kadan ta dora hannu a ka.
Ta ce hmm.
Ko bazaki fidda mun ba?
Ta daure ta cije ba tare da ta kalleshi ba tace cikin su wacece tafi birgeka?
Yayi jimmm, ai ruwan ido bazai barni na tantance ba, wace kike ga tafi?
Ta harareshi ban sani ba ta Mike Ina da aiki daki...... Ya gumtse dariya shima ya Mike.
Suka jera kamar ta kwasa a guje tabarshi agun takeji....... Kin San rayuwata Ina son mace wacce Bata da tsoro, .....,..ai shikenan bani ciki kawai, ta fada cikin Rai saboda nikam kamar farar Kura nake don tsoro.........Mai kyau, Mai ilimin addini, wayayya, fara Mai dogon hanci, Mai tsawon gashi, Yar gayu.......shin Wai ni Yanzu Ina ruwana kake ta faman lissafo mun kaje can ka Nemo Mana....
Yayi Yar dariya ke nake fadawa irin wacce zaki nemo mun..... Mufeeda kaje na zabar maka mufeeda ita ce keda duk qualities din da ka zayyano...... Ya Kara gintse dariya mufeeda ba Fara bace Kuma Bata da gashi dogo attach........ Har ma ka sani? Ta zaro ido.......
Eh, Mana kowa ma yasan haka tana boye gashin ta ne?
Mtsew....sai kaje sadeeq ya Nemo maka...... Ke Zaki Nemo.
Tayi murmushi ikon Allah dole ne?
To ai kece babbar kawar tawa ko?
Kema sai in taya ki zabe......Ni an mun miji..... Ya bazga uban tuntube saboda tashin hankali saura kadan ya Fadi tayi saurin tarewa kamar zata taba Shi tace subhanallahi sannu....
Ya Mike idanuwan say duk sun Fara chanzawa daga farare zuwa jajaye.....
Da gaske an Miki miji?
Ya fada Yana gyara takalmin sa, ta kakaro murmushi ta ce aikuwa dai Ina da Wanda Zan aura......
Bai Kara magana ba har suka je kofar gidan.
Ya tsaya kansa juyawa kawai yakeyi, ta fito da Yar karamar leda ta Mika mishi ga tsarabar.....ya kasa Sanya hannu ya karba.
Ta kura mishi ido ya sunkuyar da Kai kasa kawai.
Lafiya dai ko?,
Yayi shiru.
Gabanta ya Fadi...... Anwar lafiya?
Ta Kara fada a hankali .
Ya dago Kai, kirjinta ya buga duk ya wani gigice yayi kicin kicin da rai, ya sunan Wanda Zaki aura?
Ta kalleshi........ Wai shine abinda ya sanyaka damuwa......
Ya Mata wani kallo dole ta kawar da Kai saboda ta tsani kallon banza da rainin wayau.......
Akan meye zai dameni?
Tayi murmushi to naga ka chanza lokaci guda.......
Kaina ne yake mun ciwo.
Ga tsarabar.....ta Mika mishi ledar.
Ya juya ajiye wurin ki Zan karba......
Wallahi bai yiwuwa. Ina ce shine dalilin biyo ni.
Ya kalleta nace ki ajiye Kuma bana bukata.......
Ta tari gaban sa da sauri Wai me ya faru?
Bani wuri in wuce please.
Wallahi baka tafiya sai ka fada mun me ya Bata maka Rai....... ( Cikin zuciya kuwa sai dadi takeji watau Anwar ita yake so yake ta gewaye gewaye. )
Ya kalleta sai ya koma jikin bango ya harde hannuwa ya sokar da Kai .
Kai nake sauraro ta rike kugu.....ya yi shiru.
Ta Fara magana cikin fada fada.
Kace in nemo maka matar Aure na zabar maka ni Kuma bani da ikon da Zan ce Ina da Wanda nake so......... Ke ! Ya daka Mata tsawa.... Na ce kada kiso wani?
Tayi baya da sauri, cikin razana. Ya matso kusa da ita, da kiso wani da ki tsaya haka bai Dame ni ba, I have nothing to do with that, and it doesn't make any difference to me....... ikon Allah ta fada.
Kamar Yana jiranta?
Cikin bacin Rai ta kalleshi, Ni ya dameni ne? Ko mufeeda Shi yasa da ta tare ni tamun rashin wayau na Bari sai a gabanka na Mata warning... saboda bana tsoron ka baka gaba na..... Damko kafadunta yayi da hannu biyu ya buga bayanta da bango....... Wallahi tallahi idan Kika Kara........kwallah suka zubo Mata sharrrr ta fashe ta runtse ido.
Allah yaso duk ba a dawo sosai ba, kofar gidan ba kowa.
Ya runtse ido da karfi ya saketa a hankali......
Ta yunkura zata ruga gida ya tare ta da hannu idan Baki so in Kara taba ki kada ki motsa...... Ta fashe da kuka.... Hankalin sa yayi kololuwar tashi...... Bai San ya Fadi *Na shiga uku ba*
Bilkisu...... Tasa hannu ta toshe kunnuwanta....
Kiyi hakuri Dan Allah na gwadaki ne kawai.
Ganin yadan matsa baya ta yunkura zata Kara guduwa ya kuwa kamota da karfi ....... Yaya Zan ta Miki magana Baki ganewa? Nace idan Baki so na Kara taba ki kada kice Zaki gudu ko daman kina son hakan ne?
Ya fada cikin tsawa.
Ta Kara rushewa da karfi....na tsane ka wallahi bana son ganin ka , ka kyaleni.
Har cikin kasan zuciya yaji maganar. Ya daure yace ....naji kin tsaneni, kiyi hakuri nayi kuskure bazan Kara ba.....wasa nakeyi.
Nima ai da wasa nakeyi ka Fara .......wasa kikeyi ba a Miki miji ba?
Ta mishi banza...... Saura kadan ya Kara kamota don ya rungume ya saki wani murmushi: nasan wasa kikeyi Nima. Kawai Ina son ganin fushin ki ne don Shi kadai nayi missing cikin hutu.......kiyi hakuri I'm sorry ya rike kunnuwa.
Kinji?
Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan Kara ba....
Ta goge hawayen da kasan hijab dinta. Kawai tayi shiru kanta a kasa.
Baki da wahalar yin kuka meye na kuka anan Bilkisu....kina da shagwaba ko?.
Um? Baki magana?
Yau ni Kuma tawa ta sameni an Kara yin fushi Dani...... Dan Allah kiyi hakuri kinji.
Bani tsarabar ya Mika hannu........ Ta maida duka hannuwanta baya ta boye ledar har lokacin Bata dago Kai ba .
Ba zaki bayar ba?, Zan Kara taba ki wallahi don Zan karba da karfi kibani da arziki kawai....
Zan ajiye sai lokacin da ka nema....
Yanzu na nema saboda haka bani....ya Kara Mika Mata hannu.
Yasa hannu zai janyo hannayenta tayi saurin fiddowa ta Mika mishi. Ta kalleshi Rai bace idan ka Kara gigin taba ni wallahi zakayi Dana sani....... Ya karba Yana murmushi naji bazan Kara ba.
Mun shirya ko?
Ya fada Yana kallonta.
Kinji?
Mun shirya?
Ba zakiyi magana ba?I prefer kiyi mun masifa da wannan shirun fa.
Bani da wannan lokacin......
Me yasa kike da wuyar lallashi haka?
Kai Kuma ka fiye naci ko?
Ya yi Yar dariya. Wallahi naci gareni tabbas ko zamu kwana anan sai kince mun shirya sannan kinyi dariya.
Matukar babu wadannan wallahi kinji na rantse a nan zamu kwana.
Idan Kuma kikayi kokarin guduwa Zan rikeki a hannu na bazan sakeki ba har sai na tashi tafiya, idan Kuma kika Sami damar shiga gida da gudun nan naki binki zanyi har ciki in kamo ki........ Na shiga uku ni Bilkisu akan meye Wai wannan dokokin????
Ya Kara Yar dariya, akan Ina so mu shirya kada mu Bata.... Na ce mun Bata ne? Ko kaji nace nayi fushi?
Au haba? Wai babu ko daya ciki?.... Ta harareshi kawai.
Ya Kara Yar dariya, shikenan.
Maganar lecture, wannan semester din idan na saki na ganki da Suleiman na rantse da Allah zan dauki mataki akansa........ A wane dalili?
Very good question ya gyara tsayuwa....
Na farko ni nake koya Miki karuwa ba Shi ba, na biyu ko Kun zauna a jarabawa ke kike bashi amsa bashi ne ke Baki ba, na uku.....idan ba zaman class din ba ka taba zuwa ka ganshi anan?
Ta rike kugu akan wane dalili zaka Sanya mishi doka akaina?
Na taba hanaka tsayuwa ko magana da ajabon Yan matanka?.
Ya kyalkyace da dariya Yan matan nawa ne ajebo?
Tayi shiru,
To ki ci gaba da kulashi kiga idan bai bace ba bat!
Ta danyi dariya ........ Ya kura Mata ido, lallai mun shirya. Ya daga hannu sama Alhamdulillah!........ Wayarsa ta yi Kara akayi ta Kira yaki dauka....
Kina ganin wasa ko?
Allah sanyawa zanyi ayi kuku dashi....... Matsayinka naa???
Ta tsareshi da ido, matsayin abokin Bilkisu Wanda bai son kowa ya rabe ta....... Maganar ta makale da alama ya kusa yin *subul da baka*.
Shima abokina nane kamar ka nafi sakewa dashi fiye dakai saboda bashi da fada ko kadan ni Kuma na tsani fada rayuwata wannan abotar da kyar zatayi lasting.....
Ya zaro ido da gaske kikeyi ko wasa?
Tayi shiru tana murmushi,
Ke!, Dago Kai ki kalleni ki Kuma maimaita abinda Kika ce Ni da Suleiman duk matsayin mu daya?.......
Ta Dora hannu bisa Kai *wallahi idan akwai abinda ya fi shiga uku a yau to cikin sa nake*.... Dan Allah Anwar kabar ni haka nan na gaji yunwa nakeji har an kusa Kiran sallah.......
Zan dawo anjima.....
Basai ka dawo ba zamuyi magana ko ta waya ne....... Zan dawo da karfe 8 idan Baki fito ba Zan shiga har ciki in fiddo ki.....
Ta bude Baki, sannan ta tsuke fuska, nifa bana fitowa da dare na Kuma fada maka tun last semester.
Na fi kowa sanin haka sai nidin Anwar ne dole ki fito saboda....... Maganar ta makale. Ita Kuma ta tattara hankalinta kaf akansa......
Yayi murmushi, kije ciki sai na dawo anjima.......
***************
*KADUNA RIGASA*
Tayi turus, duk sukayi tsuru tsuru ba kamar Shi guiltiness ya kamashi........ Ta kakaro murmushi Wanda yafi kuka ciwo kafin tace .... Ohhh sorry ta juya yayi Kiran duniya amma Bata dawo ba,
Ya saki Amira da sauri yabi bayanta Nan da Nan kishi ya turnuke ta itama.....hawaye suka shatato Mata sharrrr.…...✍🏼✍🏼😄
*Zainab Dahiru wowo* ce💖
Ayi hakuri da kadan
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣5⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*****************
*Federal University dutsinma*
Anwar din nan ya mayar dani sakarai. Shi girman Kai ya hana ya fito yace Yana Sona shine yake ta gewaye gewaye, bai San halina ba, a dole yanda banzayen Yan matansa ke zubda class suna crushing din sa nima haka yakeso nayi..... Ba dai Bilkisu ba, ko Zan mutu bazan ce Ina son sa ba.
Zan daure na cije na nuna mishi ban San inda ya dosa ba inaga idan yaji uwar Bari *Zai furta*.
Ya fada bisa gado...... Ya kalli sama .
Sadeeq ya kalleshi an dawo fa!
Baka ga missed calls Dina ba?
Ina so ince ka amso Mana abinci *M&M*...... Abdul din fa ya daina dafa indomie ne?
Kai ubanka da indomie din Nan, Wai me yasa kake son gana Mana azaba?......
Ya kyalkyace da dariya azabace cin indomie?
Nifa bazanje wani *M&M* ba kawai muyi normal life na student kada mu banbanta...... Ubanwa yace to baka sai Mana gida ba ka kawo mu hostel?
Ya Kara murmushi....ba za ka gane ba..
Ban ganewa wallahi....
Ranar da aka ganoka tabbas ka shiga uku.....in shaa Allah har na gama babu wanda zai sani,
Ya bude ledar da Bilkisu ta bashi kamshi ya doki hancin sa, rantsattsen agogo ne Mai tsada cikin cover....... Kai ya tashi zaune.
Menene?
Bilkisu ta siya mun agogo wallahi.
Ya fada Yana daga Shi sama.......
Hmmm, wannan babbar kyauta ce, ka daina cinyewa Yar mutane kudi fa.
Yayi murmushi ya cire na hannunsa ya mayar da nata.......
Anwar a fidda maganar wasa ka dubi girman Allah ka sai Mana gida ko ka Kama Mana haya mubar wannan kwamachalar......
So kakeyi nayi ma wata ciki..... Ya zaro ido.
Yes! Bari na fito maka a mutum sak!
Dan ubanka yanda Yan matan nan ke kawo man hari kana tunanin idan na ware baxasu bini daki ba? Ko ni katako ne da Zan ga mace daga ni sai ita na....... Shikenan, ai shikenan next year by now mun Fara bankwana ma.
Wayarsa tayi Kara ya dauka....... Ya Dan kalli sadeeq buga mun sixteen million times 42 please..........
Bayan ya ajiye sadeeq ya hado musu oat suka Sha sannan suka tafi masallaci.
Akan hanyar su ta dawowa yace sadeeq Ina son ka Sami Suleiman kace kada na Kara ganin sa da Bilkisu....... Dalili?
Ya katseshi.
Haka Nan.....
Zancen banza kenan, haka kawai sai ka raba su babu dalili?
Yaron banza ne bana son sa.....kada ka tsani Dan mutane. Kowa yasan Shi mutumen arziki ne idan kana da wata hujja ka fiddo kafin ka yanke zumunci.
Kana ganin wasa nake ko?
Wallahi semester din nan takunkumi Zan sakawa Bilkisu akan Shi saboda Shi kadai take kulawa yaron Yana da mugun shisshigi.
Anwar! Anwar!! ..... Idan son yarinyar nan kakeyi........ Wai Kai me yasa baka ganewa? Dole sai Ina son ta Zan Sanya doka akanta????
Ni Sona takeyi da take Sanya mun doka inabi?
Ko kasan yarinyar nan juyani takeyi kamar waina?( Masa ).
Kuna dai juya juna.
Kuma duk laifinka ne, ka zauna wurin kallon ruwa kwado yayi ma.....
Sadeeq Banda wani personal business da yarinyar nan da ya wuce friend, kawai bana son tana kula Suleiman period.
Mtseew to ka jaraba ai Bilkisun ba bakuwar ka bace na tabbatar akan Suleiman tana iya kyaleka kwata kwata...... Da gaske? Ya zaro ido.
Lallai dole naci uban yaron nan.
Sadeeq ya tuntsure da dariya, Allah gamu fareka.... Sai ka maida hankali toh.
Kai da Bilkisun duk munafukai ne kowa Yana fama da ciwo ya gwammace ya mutu da ya fitar da cutar......
Kamar ya?
Kai ba bahaushe bane?
Ya doka tsoki....... inyamiri ne ni.
Yaushe Anas yace zai dawo?
Sunday.
Ai Kaine ka kwaso mu badon na shirya ba wlhi.
To ya zanyi?
Ya kalleshi ya zakayi? Wani ya tilasta maka?
Ya kada kafada tare da watsa hannu yace ko daya.
Zaku kaisu idan Kaya ne.
Ina tausaya maka ranar da wani zai maka shigar kutse......
Ku bakwa ganewa, yarinyar nan tana Sona fiye da duk wata yarinya da ke hauka a school din nan, na rasa girman Kan da ya ke hanata *FURTAWA*....... Kai ba sai ka *FURTA* ba?
Mtsew....your are not well.
Ya kwanta bisa gado, ka dafa Mana shinkafa muci da miyar can Mana.yayi murmushi ka canza maganar Kuma? Toh
Yanzu kuwa ya Fara Shirin aiki.
Ya janyo waya ya Kira Bilkisu,
Tana kokarin fere doya Aisha na warming Miya daga gefe Kiran ya shigo,
Ta ce hmm sannan ta daga .....
Hello, Ina wuni......
Ya lumshe ido Yana son gaisuwar ta yarinyar nan nada da'a sosai.
Lafiya, ya kike?
Qalau.
Keda waye nake Jin motsi?
Aisha,
Kuna meye?
Girki.
Me ye ne ?
Kai ai da gangan akai tamabayo......
Doya da Miya.
Zanci.....
Aikuwa baka cinsa sarkin roko....... Ya tuntsure da dariya har Yana sarkewa da miyau.... Aisha ta kura Mata ido tana kallonta. Keda waye?
Ta bude Baki ta Mata alamar Anwar ne ba tare da sautin ya fito ba.
Rowa Zaki mun?
An maka........
Shikenan. Ki shirya anjima zamu je na siya Miki wani Abu cikin kudin Dana tara ko kuwa?
Ka dai ka siyo ka kawon ba sai munje tare ba.
Saboda me?
Haka Nan.
Karya kikeyi ba Kya son samarinki su ganki Dani........ Sadeeq ya kalleshi Kai da wa??????
Harar sa kawai yayi.
Kinji?
Ni nakeyin karya?
Eh, ko gaskiya Kika fada?
Kai Ni ban iya abinda ka iya ba..... Meye na iya Wanda Baki iya ba?
Neman magana...... Ina mamakin yanda ake cewa baka magana kana da jiji da Kai amma Ni wallahi nace surutu gareka ga roko....... Ya Kara yin dariya.... Ke Kuma rowa gareki ko?
Rowar me?
Meye ka ce na baka na Hana?
Abinci.
Mtsew...tayi murmushi badai zance kazo kaci ba .
Muma ga sadeeq na dafa Mana shinkafa Mai dadi Ni na kawo Miki?..... Na koshi aci lafiya.
Allah kuwa..... Bana ci na gode malam .
Kai lazy baka dahuwa sai an dafa an baka ko?
Inji waye? Nafi sadeeq iya girki ko kina musu?
Eh.
In dafo in kawo Miki Zaki ci?
Noooo, ta fada da sauri. Yayi murmushi yarinyar da kinji akul.
Ta ce hmm.
Zan zo anjima kinji ko?
Okay.
Ki gaishe mun da Aishar Bari na dauki wata waya...... Ya katse Kiran.
Ta kalli Aisha Anwar case ne.
......... Gaskiya ai Yana bala'in yinki. Anwar Dan gadara Shi yake Kiran mace kinji yanda ake surutun miskilancin sa kuwa?
Inaji amma nake ga kamar hada Sheri..... Wallahi da gaske ne.
Yan matan ne basu da zuciya. Kinga wulakancin da ya ringa yi ma khausar har kuka take mishi.... Jakka kuwa ki Sami fareeda yarinyar nan Bata da zuciya wallahi..... Ke Aisha namiji munafuki ne kedai baki sani ba ko Yana gewaye wa.
Last semester gab da za ayi hutu da yazo cewa yayi zance ya fito ya biyo wurina Kuma kema kinsan kilan bai wuce mufeeda ko wannan dayar banzar Yar aji hudu.
Hmmm, kawai Aisha tace.
Salim bai dawo ba Ina Zan Sami aron mashin?
Sadeeq ya Fara maka mishi uwar harara ai taurin Kai da wulakanci ya Hana ka siya Mana sai kaje ka hau kabu kabu......... Wohohoho..... Wai nawa mashin din yake in siya a huta?
150-200k wannan range din.
Mtsew...... Ka shirya gobe ka shiga katsina ka siyo Mana...... Ya buga ihu.
Ya shako wuyansa..... Koda wasa ka nuna inada alaka da hakan ubanka zanci..... Bazan fada ba cika ni mugu...... Ya wuce har ya Kai bakin kofa ya waigo wane police station ne DPO ke Zama a garin Nan??....... Ya zaro ido DPO? Lafiya meye zakayo wurin DPO?
Zan sa ya ma Dr Dan Musa warning da Suleiman akan Bilkisu.......... Wata muguwar dariya ya saki munafuki karshen tuka tika tik... Yanzu ka *FURTA* mun abinda nake son...... Dawowa yayi zai Kara shako Shi yayi bisa gado.... Allah ya baka hakuri.
Amma Ina baka shawara zaka tona asirinka a banza saboda zasu so sanin wanene....inji waye?
Ba zai fada ba. *This is legal warning* ...... Ya fice da sauri Yana duba agogo.
Ya daga murya inzo in raka ka??....... Da ga can waje yajiyo Yana surfa mishi zagi.
Yana sauka achaba Aisha na zuwa zata tsallaka titi..... Aisha. Ya Kira sunan ta.
Laaa Anwar Barka da dare an dawo lafiya?
Qalau, je Kira mun Bilkisu..... Tayi jimmm sannan ta ce toh ta juya Shi Kuma yayi tsaye maimakon yabi bayanta.
Tana tafe tana masifa, je Kira mun Bilkisu kamar wata barar sa..mtsew. Haushi na da Shi Sam bai da manner of speaking Yana magana a gadarance da Isa na tsani wannan wulakancin wallahi.
Tana wankin toilet ta shigo.... Kizo inji Anwar.
Ta dafe kirji...kin ban tsoro wallahi.
Ta harareta kawai zata juya..... Aisha Wai ya akayi?
....... Pad Zan jarbo Ina sauri ya ganni kawai ba wata magana Wai *je Kiran Bilkisu* irin yarinyar nan wacce ya ajiye....
Kiyi hakuri kin dai San Hali...... Eh amma ki ringa kwatanta mishi wata rana Zan yankwana Shi..... Kiyi hakuri dai, jira mu fita tare Dan Allah. Idan mun Gama Zan rakaki..... Wai injira ki wurin sa?
Baki da hankali wallahi idan yamun wani dizgin inyi Yaya dashi?,
Bazaiyi ba, idan ya ganmu tare bazai...... Wallahi bazan je ba. Kina tare da Anwar seems like you don't know him ko? Mtsew taja guntun tsoki ta fice abinta.
Ikon Allah. Kai Anwar nikam tawa ta sameni........ A yanda yayi rantsuwa tabbas idan ban fita ba shigowa zaiyi.
Ta dauraye hannun ta, Daman Riga da wando ne jikin ta, ta zumbula hijab har kasa ta Dan fesa turare kadan ta fito.....
Bashi babu alamar sa, ta juya ta waiga ba kowa, tana niyyar komawa ciki har ta saka kafa daya ciki kiransa ya shigo...... Ta dauka hello....... Kin fito Kuma kin koma.
Ni Banga kowa ba kana Ina?
Bakin titi..... Bakin titi Kuma?
Eh. Ki karaso.... Meye zanyi a bakin titi?
Kina da gardama ne Wai? Just come here simple and short why are you arguing?? Ya kashe wayar.
Wai ni zai mulka? Irin yanda yake juya Yan matansa Nima haka zai juyani? Ta doka tsoki ta wuce ciki.....
Kofar taki buduwa daman tanayin haka some times, da kyar ta bude tana saka kafa Yana saka tashi...... Ta firgita, ta tsorata sannan ta razana ainun. Gabanta yayi mummunan faduwa ta zaro ido tare da bude baki zatayi magana .....ya riga ta, kina daukar maganata wasa ne?
An fada Miki akwai Wanda nake tsoro ko shakka duk dutsinma?..... Babu, Dan girman Allah kayi hakuri muje tayo hanyar fita yasa hannu ya maidata... Ban gama ba....... Sai kawai tayi kneel down na tuba Dan girman Allah muje waje idanunta sun Fara kwal kwal alamar zata Fara kuka...... Ya buga tsoki ya juya.
Ta Mike da sauri ta janyo dakin ta datse ta bishi da gudu.
Tafiya yakeyi yaki tsayawa.....
Ta Kara sauri ta tari gabansa Wai Ina zame je ne saboda Allah?
Me yasa kika zabi bani wahala da bin yarda nake so?.
Kayi hakuri wallahi daddy ya ce baya son fitar dare Anwar kada a sanar dashi zanji Babu dadi....... Da Yan iska yake nufi ni Kuma ba Dan iska bane...... Ikon Allah ba haka nake nufi ba.
Okay to wuce muje..... Zan siya miki sweet ne da kudin aikina...... Wallahi da wasa nakeyi maka kawai na fada ne..... Ni Kuma da gaske na dauka saboda haka wallahi sai munje.
Shikenan, suka jera.
Tayi murmushi ko ke fa? Amma ke komai sai anyi tsiya tukun.
Me kike so?
Duk abinda ya maka.......
Kinga agogon ya mun kyau? Ya nuna Mata .
Um, kawai tace .
Na gode fa, Allah ya Kara dalili.
Amin.
Zaki ci nama suya?
A'a na gode.
Kaza fa?
Bana ci.
Shawarma...... Nifa bana bukatar komai.
Lallai yau zamu kwana a titi...... Ta kalleshi da sauri. Ya bita da ido Daman so kawai yakeyi su hada ido..... Allah matukar Baki ce ga abinda Zan siya Miki ba haka zamu kwana...... Biscuits. Tayi saurin cewa. Muje ka siya mun biscuits.
Ya yi Yar dariya ko kefa?.
Napep! Ya daga murya. Shi Kuma ya tsaya. Ta kalleshi da sauri...... *Abis supper market* zamu je Nan kadai Zaki Sami biscuits din da kike so..... Anwar, biscuits ko anan akwai Dan Allah...... Mtsew Allah ya raba ki da gardama. Muje ko in daukeki...... Kafin ya rufe Baki har ta tsallaka titi.
Ya dunga mata dariya. Ta turbune fuska..... Gaskiya bana Jin dadin abubuwan nan Anwar bana son abinda kakeyi mun..... Kiyi hakuri.
....Ina zakuje ne?
*Abis supper market* Anwar din ya fada Yana kallonta .
Ta harareshi kallon Kuma na menene?
Wallahi na tsani kallo rayuwata...... Na sani. Yace Yana dariya.
Ka sani Kuma bazaka daina ba?
Ya kyalkyace da dariya Nima na tsani kallo fa ta Yaya Kika San Ina kallon ki?.
Yanzu Ina amfani wani ya ganmu a Sanya Ni a bakin fudma ace har mun Fara fitar dare sai ma a ba abun wata fassara wallahi. Mtsewww.
Fassarar me?
Ta mishi banza.....
Kinji?
Ta harareshi, ya kamata ka daina zuwa mun da dare gaskiya bana iya masifar Yan matanka kullum sai an mun zobe kamar za a dakeni...... Basu iyawa. An fada mun tsoronki sukeyi tun lokacin da Kika Mari kawar mufeeda...... Au ka sani ma ashe.
Yap. Yace Yana murmushi.
Dai dai sun kawo ya Mika mishi kudin suka shiga.
Ranka ya dade..... Ma'aikatan suka taso .
Ta kalleshi da alama regular costumer ne Kai.
Murmushi kawai yayi.
Kije ki zabo biscuits din da kike so.
*Short bread* daya is okay..... Ke bana son gidadanji kije ki kwashi Kaya kinji ko idan kina Jin kunya Kuma muje na Taya ki ya zungureta da hannu.... Kamar ta bude kasa ta shiga don kunya yanda aka Mata ratai da ido.
Sam ta kasa nuna ko daya...... Ya Kira yaron ya ce duk layin Nan sauko shi, tayi Yar dariya tunanin ta zolaya ce yakeyi.
Da sun Kara gaba yaga wani kalar biscuits din sai yace wadannan ma duk safko dasu.......
Wasa wasa ta ga abu da gasken gaske bata San lokacin data janyo Shi baya ba *Kana qalau* kuwa?.
Ya Kai fuskarsa daidai saitin tata kamar zai yi kissing dinta...tayi baya da sauri yayi kasa kasa da murya *Yi kokari ki dizga ni*..... Kamar zatayi kuka ta kalleshi ka dubi girman Allah..... Me yasa kike son yi mun irin wannan magiyar Mai tsada?
Ya katseta hannuwan sa duka a kirji.
Ka ce su mayar da biscuits din can..... Wallahi duk wadanda suka sauko bazasu koma ba, idan Baki sa hannu kin dauki Kaya ba Zan siye duk biscuits din dake super market din Nan...... Ta zaro ido....
Kamar me Zan Dauka?
Na bani ni Bilkisu kawai take nanatawa a zuciya...... Duk abinda kike so perfumes, cosmetics, drinks... everything.
...... Dabara ta fado Mata, okay na amince amma kaga Yanzu duk Ina dasu ka Bari semester tayi nisa Zan biyoka...... Yau fa sai kin dauka Kuma zamu Kara dawowa hakan ma ba laifi bane.
Kamar ta daura hannu a ka ta yi ta ihu.... Ta kalli yaron kaga zo daukon *women million din can please*, Kuna da Apple juice? Eh hajia Mai sanyi ko marar sanyi..... Kamar ta zageshi don takaici, ta daure tace bani marar sanyi.
Suka Kara zagayawa ta dauki robar chewing gum banana.
Ta kalleshi wadannan sun isah na gode.
Are you sure?
Um. Tace da kyar.
Biscuits din da yasa aka kwaso anata packaging a kwalaye manya...... Assorted biscuits ne na kwalaye da gwangwanaye...
Tayi tsuru duk da diririce.
Watau Anwar gidansu akwai kudi shine yake boyewa yace karkashin sadeeq yake komai sai ya nuna sadeeq ke dashi ko zaiyi.
Hmmm, kawai take cewa.
Yasa hannu ya fiddo ATM wasu dunkulallun dollars suka fado........ Ta bishi da ido jikinta sai karkarwa yakeyi ta Fara tsorata da al'amarain sa.
Ya Dan kalleta Yana Yar dariya, ajiyar sadeeq ne.....mtsew taja guntun tsoki tayi gaba.
Ya biyota da sauri ki jira zasu bayar da mota akai mu kayan sunyi yawa....... Ta rike kugu ta tsare Shi da ido sannan tace *WHO ARE YOU??gg?*
****************
*KADUNA RIGASA*
Ta fada bisa gado ta saki kuka..... Ya karaso Ummi tashi ya dagota.... Kiyi hakuri wallahi ba abinda kike tunani bane I just hugged her..... I don't want hear about it.
Naji but kiyi hakuri ya rungume ta, I was confused these days.
Tsakanin Miji da Mata sai Allah cikin second zancen ya sauya launi ya shawo kanta ....
Kuka sosai Amira keyi tana cewa tabbas na ma kaina wauta me yasa na bayyana Mata abinda yake so da Wanda baya so? Me yasa na sakar Mata ragama...
Tabbas ya shiga rudani ya kasa tantance daya cikin biyu... Ta Kara rushewa da kuka.
Yayi lamooo bisa cikinta, ita Kuma tana shafa kansa.... A hankali take magana.
Kafi son matarka Dani, har Yanzu ka kasa sabawa da ni matsayin matarka, a kullum...
Ya rufe mata baki da hannu, I'm sorry baby, Ina sonki musamman Yanzu da Kika dawo normal wife kina biyayya ga sharudda na sannan kina kula dani....
Me yasa kake saurin kamuwa Koda kuwa wani abun munyi shine saboda makircin mu na Mata?..
Yayi shiruuuu..... Ya kasa magana hakika ya gano inda zancen ta ya nufa, ta yi murmushi hakika Yana da kyau ka Zama jarumi Mai iko da bukatar sa.
Kiyi hakuri please I'll change..... Hmmm Allah yasa zaka iya.
Kuma Ina rokon ka Dan Allah idan kasan har Yanzu kana kokwanto akan son da kakeyi mun.... Ba wannan maganar Ummi ya fada tare da janyo ta jikinsa..... Wallahi Ina sonki fiye da yanda kike tunani sometimes Ina rasa meke damuna amma na gano bakin zaren na Miki alkawarin zakiga canji.
Please am sorry dear.
Ya Kara rungume ta........✍🏼
*Zainab wowo ce*💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣8⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA i love you so much, remember this always*🥰😍😘.
***************
*Federal University dutsinma*
```Ya juya hannun da karfi, wallahi duk ranar da wannan hannun ya yi gigin taba Bilkisu sai na karya shi, nima akanta Zan iya kisa```......... Ya wurgar da hannun. Sannan ya kalli wadanda ke tsaye *What the hell are you doing here?* Ya daka musu tsawa...... Suka Fara darewa, mufeeda ta juya zata tafi ya fizgota..... ``` Bata hakuri```....... Tayi saurin kallon sa, Jin haka yasa kawayenta Suma suka Fara yin baya,
Bakiji abinda na fada ba?
```ki Bata hakuri ko Kuma wallahi....```
Ta fizge hannunta, bazan bayar ba..... Ta wuce da sauri kamar zata tashi sama.....
Aisha ta rike hannun Bilkisu tamau.
Ita kuwa kanta a kasa kawai tayi shiru......
Ya kalli Aisha, me ya hada su ne?
Me kuwa zai hada su inba kaiba??? Ita har Yanzu tana zargin akwai wani abu tsakanin ka da Bilkisu shine fa suka tare mu Yanzu mun dawo sallah..... Mtseww ya doka tsoki.
Ya Mika ma Aisha basket ungo je Mata dashi ciki..... Ta juya kawai zata tafi ya yi saurin fizgota ta fada jikinsa kanta ya daki kirjinshi........ Yaushe Zaki fahimci da gaske bana so ki ringa tafiya idan nazo wurinki ko muna tare?
Ya hakuri sakeni please..... Ya Kara manneta jikinsa..... Aisha jeki tana zuwa.
Ta wuce tana dariya da mamakin wannan rigimammiyar soyayya.
Wai Anwar Kan ka qalau? Na shiga uku ni Bilkisu ka dubi Allah ka sakeni..... Yana rungume da ita ya Fara tafiya a hankali ..... Na shiga uku Anwar..... Ya sunkuyo Yana kokarin hada fuskar sa da tata tayi saurin sunnewa jikinsa tana Kara fadin na shiga uku ni Bilkisu..... Ya manna bayan ta da Bango sannan ya matsa baya kadan ya rabu da jikin ta yasa hannuwa biyu ya tokare bango tare da Dan sunkuyawa fuskar sa daidai tata suna shakar numfashin juna ya kafa Mata idanu.......
Innalillahi Anwar Wai meye haka? Ta fada tana faman yin kasa da Kai.......Haka zamuyi firar tunda ita Kika zaba..... Na zabi meye? Ka gyara Mana dan Allah ka matsa..... Allah ba inda zanje, ba dai taurin Kai gareki ba? Wallahi zanci gaba da binki yanda kike so, ke me yasa baki da tausayi?...... Tausayin me Wai? Ta fada tana kallonsa kamar zatayi kuka.
Gashi yauma saboda mufeeda zaki Kara guduwa kibar ni anan Kuma kin san zuwan naki ne....... Nayi Alkawarin Zan tsaya I'll give you the time you...... Never mind, I'm okay like this.....Anwar am not okay please shift back na tuba kayi hakuri Dan ...... Ke nafiki wuyar lallashi fa ki natsu muyi magana nafi Jin dadin hakan ma..... Tayi kwal kwal, ya kamata..... Na rantse da Allah kina mun kuka Zan mayar dake Nan... Ya nuna kirjin sa.
Ta hadiye kwallan ba shiri , kayi hakuri Anwar bazan Kara ba I promised.
Yayi murmushi naji but next time.
Kina da sauran tuwon nan?
Babu.
Yayi Yar dariya Yana kallon Dan karamin bakin ta da take ta faman turowa.
Duk kin cinye?, Amma fa yayi dadi. Zuwa nayi godiya waccen useless din ta Bata mun plan.... Ba komai nidai jeka sai da safe.
Ya kyalkyace da dariya kina korata ne?.
Ya Mike ya tsaya daidai ta saki wata ajiyar zuciya Mai karfi ya bita da ido Yana murmushi...... Matsoraciya kina motsawa Zan.... Ba inda zanje ta fada tare da makurewa jikin bango.
Kiyi hakuri ya fada a hankali, wallahi Nima fa bana son Ina taba ki Bilkisu ki daina mun gardama kinji?
To, ta fada a kagare.
Sadeeq ma yaji dadin tuwon nan. Ina Kika Sami manshanu?
Ina dashi. Ta fada a hankali. Duk jikinta yayi sanyi....ya Kara tsareta da ido sai ta bashi tausayi.
Bilkisu.....ya kirata a hankali.
Taji wani Yarrrr, tsikar jikinta duk ta tashi, ta kasa amsawa.
Ya Kara cewa Bilkisu......
Na'am ta fada tana murza yatsunta.
Dan Allah kiyi hakuri kinji ko?
Ba komi ta ce a hankali.
Da komai. Gashi naga duk kinyi relax, please I'm sorry.
Ba Kya so Ina taba ki ko?
Ta daga Kai alamar eh, yayi murmushi to duk laifin da nayi Miki idan muna magana ko Ina a wajen don't leave me, kinji ko?
Ta Kara daga Kai .....yayi murmushi Baki magana?
Ta ce hmmm.
Dan Allah ki daina bana so kinji?
To Wai me yasa baka iya kyaleni in tafi?...... Saboda.. sai Kuma yayi shiru Yana murmushi.
Saboda me? Ta tsare shi da ido.
Bazaki gane ba, yace Yana Yar dariya.
Zata Kara magana ya yi saurin cewa na saka Miki turaruka a basket din da na maido Allah yasa kamshin suyi miki.
Biyana kayi kenan?
Ya zaro ido na Isa in biyaki? Allah kadai zai iya biyan ki Bilkisu.
Na zo dasu ne tun daga gida ban dai kawo Miki bane ....... Turaruwanka Zan saka ajikina?
Nope, na Mata ne musamman na siyo Miki.
Hmm, na gode sosai.
Yaushe Zaki Kara mun tuwo?
Sai an kwana biyu kuma .
Gobe me Zaki dafa?
Ina ruwanka, Kai fa abinci ne damuwanka ni kuma ba girki nazo yi ba karatu..... Dariya yakeyi har Yana dukewa...... Wannan tsiwar taki na bir.... Sai yayi saurin canza magana yace tana bani dariya.
Ta ce hmmm, ai gara na fada maka na lura Kai baka san ayi abu Dan marmari ba.
Dan Allah kiyi abinci dani gobe.... Indomie Zan dafa malam..... Zanci indomie din please ki taimaka.
Mtsew taja guntun tsoki.
Amma ki bari Zan Miki waya ten minutes before yanda Ina zuwa kin karasa naci da zafi..... Kaci a Ina? Ka Bari Zan Aiko maka.... Bana cin indomie idan ta shiga wani kwano ba plate ba daga tukunya..... Kiyi hakuri zanzo nan in ci..... Anwar! Ta Kira sunan sa.
Ya kalleta Bilkisu!
Shima ya fadi nata .
Idan na tambayeka zaka bani amsa saboda Allah?
Ya danyi Yar dariya in shaa Allah.
```me yasa yake son takura mun bayan ga wadanda keson attention dinka kaki basu sai ni da ban nema ba?```
Ya fada murmushin fuskar sa ya zuki iska ya hurar..... Saboda kece best friend Dita. I'm More comfortable with you than any other girl in this school.
Tayi shiruuuuu, ya kalleta ko ba wannan amsar kike son ji ba ya karasa maganar Yana dariya.
Ta galla mishi harara.
Kin San fa a tarihi abincin ki daya na taba ci duk school din Nan apart from sadeeq da ke Mana girki sometimes da Abdul Mai indomie...
Yanzu kuwa I don't think ko na sadeeq zan Kara ci....... Ta zaro ido sai nawa?
Naki zanci. Gaskiya gara na fada Miki Zaki ringa Mana girki once in a day ko twice idan kina da lokaci...... Amma ka debo dala ba gammo ..... Ya kwashe da dariya.
You are my personal person am sure you'll do it.... Bazan yi ba.
Naji bazakiyi ba shikenan Amma gobe zanci indomie ko?
Eh, amma daga ita karka Kuma cewa don bazaka samu ba....
Yayi murmushi is alright!
Zan koma ciki, na gaji da tsayuwa....... To muje ga bench a can mu zauna akwai sakon da Zan fada Miki...... Tana son mishi gardama tana tsoron ya Kara damkar ta, ta yi Dan jimmm ya tsareta da ido...... Muje ta fada a hankali.
Kaiiii, amma fa kin bani mamaki na ji dadi sosai ko kefa? Ai gardama bata da amfani..... Suna tafiya Yana surutai kamar ta shako wuyansa takeji.
Suna niyyar Zama wayarsa tayi Kara.
Ya dauka hello.....
Ya zauna tare da Mata nuni da hannu alamar ita ta zauna. Ta Dan raba can karshe a dosane.
Ina jinka ya fada Kai tsaye.
Ta Dan saci kallon sa sai taga hankalin sa na ga babbar wayar sa Yana latsawa lokacin ne ta lura da iPhone 11x+ yake rikewa ta Dan zaro ido tana satar kallonsa.
Wai ita yau wannan tsadadden yaron ke bi.... Ikon Allah, Ina ma zai *FURTA* Yana sonta? Wallahi zata bashi amsa da gaggawa.... Har Yanzu tana wasi wasi shin da gaske friends din ya tsaya ko kuwa ita ya mayar friends???
Ko in jaraba cewa Ina sonsa?...... Tabb idan Kuma yace baya Sona hakan ya kawo karshen friendship din mu?
Ko Yanzu a tafi a Haka nasan wasu zasuyi ta misunderstanding irin su useless mufeeda.... Ko banza dai a FUDMA nabar record............ Ke kici kanki tubbb ya tofa Mata miyau... Tayi firgigi innalillahi...ta sa hijab tana gogewa... Wannan wane danyen wulakanci ne haka zaka tofan yawu?.... An tofa sai tsareni da ido kina kallo?
Ya harareta..... Bata San lokacin da tayi dariya ba, lallai wanzami baya son jarfa, Kai duk kallon da kakeyi mun nace me?
Eh, aini bana munafurci nake ba ke kuwa sai kin lura bana kallonki sai kina dan sacewa kina..... Mtseww ta doka tsoki.
Ya kyalkyace da dariya.
Ke bakya gajiya da hijab kamar matar liman?
Kai Kuma baka iya gani ka kyale???
Ya langabar da Kai don Allah gobe kisa gyale ki fito idan na zo cin indomie....... Bani da gyale.
Anan ko?
Abuja kina sa.... Maganar ta makale ta bishi da kallo.
Abuja ma bana sawa ni hijab nake sakawa ko gida..... Dan Allah Bilkisu... Ta kalleshi Kai bana sa gyale fa.
Saboda me?
Saboda Ina kishin mijina!!!
Waye mijinki???
Mai rabo.... Ta fada tare da Dan kallon sa....
Yayi murmushi, lallai ya more ko wanene.
Ta ce hmmmm.
Amma fa mijinki zai Sha rigima.
Ko? Ta ce tana murmushi.
Eh, Mana.
Hmmm.
Kaima matarka zata rigima..... Ni Ina da rigima???
Kwarai kuwa.
Wace iri?
Na ci, magiya, damuwa....Kai komai ma.
Amma Kuma I'm sweet ko?
Ta harareshi a'a chewing gum.... Ya kyalkyace da dariya.....
Tashi muje ki shiga gida idan Kika biye mun zan iya kwana haka dake ban gaji ba..... Tayi zumbur kamar tana jira.
Ya Mata kallon kasa kasa har taji Yar kunya.... Ta Dan juya tana murmushi.
Kin gaji dani already ko?
Um um.
Eh Mana .
Hmmm. Tace.
Zan tura miki assignment din nan ta WhatsApp kinji ko?
Har kayi?
Yayi murmushi kawai.
Har bakin kofa ya raka ta sannan yace okay have a pleasant sleep....
Same. Ta fada tare da shigewa......
Ta biya dakin su Aisha ta dauki key ta wuce.
Kagare take taga turarukan da yace.
Ai kuwa ta gansu don tsadaddu ne designers Kai Anwar babba ne ta fada tana juya daya Wanda yafi daukar hankalinta.
Mashin ya hau bai Kira sadeeq ba.
Kai Yanzu ka gane firar dare ko?
Kai Kuma ka gane sa ido nonsense ya Kai mishi duka.
Allah Anwar Kai munafuki ne....... Ya kyalkyace da dariya Kai Allah ne ya fiddani da wuri ina zuwa na tarar da mufeeda ta janyo gardawa zasu daki Bilkisu..... Ya dauki waya ya Fara nemanta.
Da gaske??? Sadeeq ya fada Yana mamaki.
Wallahi, yarinyar Bata da tarbiyya....kaga Ina Kira taki dauka gobe Zan buge Mata warning na karshe idan Kuma bata ji ba nasa a koreta ko waye ubanta.....
Anwar kabi sannu, fitina kwance take....
Sannan yarinyar nan kada ka takura Mata fa.
Naji. Ya fada Yana kokarin tube Kaya.
Washe gari ta tashi da wani ciwon ciki Mai tsanani ta kasa zuwa class.
Suleiman na ganin an Gama lecture ya kirata saboda yasan ta dawo.... Anwar na bayansa Koda yaga yasa waya a kunne sai ya kura mishi ido yasan tabbas Bilkisu yake nema.
Hello....
Lafiya dai ko? Naji muryar kamar Mai bacci kamar Kuma wacce bata lafiya....
Ciki?, Subhanallahi..... Anwar najin haka yayi zumbur ya mike ya ce zo muje sadeeq... Sauri yakeyi sosai, sadeeq ya fito da gudu, Ina zamu je?
Bilkisu ce Bata lafiya.... Me ya sameta?
Kamar naji Yana ambaton ciki it might be ciwon ciki... Suna zuwa bakin titi yace tare Mai napep ka taho dashi.... Ya tsallaka da sauri.
Allah ya rufa Mata asiri akwai doguwar Riga a jikinta , Aisha na ta faman dama Mata oat ya shigo dakin..... Kanta ba kallabi gashi ya bazo a gadon bayanta ta kifa Kai a filo tana ta murkususu Aisha kuwa daga ita sai shimi.... Ya fado dakin.... Duk suka firgita.
Aisha tayi saurin janyo bargo .
Ko kallonta baiyi ba ya zauna bakin katifar.... Ciwon ciki ke damunki? Ya fada Yana kallon Bilkisu cikin damuwa....
Firgigi ta dago tare da janyo towel dake kusa da filon ta rufe kanta.... Anwar meye haka? Ta fada da kyar .
Ya doka tsoki. Tashi muje hospital.
Ba sai naje ba na Sha magani..... Tashi muje hospital ya fada cikin daga murya..... Ta kalli Aisha ita Daman su kawai take kallo.
Cikin ya Kara katsawa ta runtse ido tare da dukewa.... Ya dagota da karfi ya kalli Aisha Ina hijab dinta?????.... Wayarsa tayi Kara... Ya dauka sadeeq ya?
Kana inane? Gani a bakin gidan ban ganka ba.... Okay Ina zuwa...ya kashe.
Tana son magana amma ta kasa saboda murdawar da cikin keyi ... Ya taimaka ma Aisha suka saka Mata hijab kawai sai ya sungumeta.......
Yi sauri ki fito...ya fada Yana kokarin fita da ita.
Sadeeq ya zaro ido Wai ciki ka shiga???? Seriously tayi penting ne????
Aisha ta fito da gudu rike da kofin oat.
Sadeeq ka same mu Sima hospital ya fada, ya kalli Mai napep muje sima.
Suna Zama ta janye jikinta daga nashi ta dora kanta bisa kafadar Aisha.
Bai bi ta kanta ba yace Aisha meye taci ne?
Bata ci komai ba Daman haka take fama dashi..... Ciwon cikin?
Eh, tana da wani magani da take Sha ne?
Eh, Amma dai baya lafawa da wuri.
Wane irin ciwon ciki ne Haka?
Tayi shiru kawai.
Kinji?
Ta ce hmmm, Daman duk wata sai tayi?
Bai gane ba ya kalleta duk wata Kuma?
Eh.
Mtseww...... Ya kalli Bilkisu kin taba zuwa asibiti an Miki test?
Tayi shiru kawai tana murkususu.
Ya Kara doka tsoki.
Ya dauki waya....hello yah good morning doctor please I have emergency patient are you.... Good. On my way...
Ya ajiye.
Ya kalleta sorry.
Aisha dai tayi zugum.
Bakin gate suka tarar da kijerar daukar marar lafiya.
Aisha ta Fara sumke dariya.
Suna saukowa yace hau Bilkisu...... Tayi karfin halin maka mishi harara sannan ta dafa Aisha suka wuce..... Ya biyota Baki lafiya amma Baki daina gardama ba ko?
Dashi aka shiga wurin doctor.
Ka ce ya fita , ta fada tana kallon doctor din cikin fushi..,.. yadanyi dariya to kaji yallabai an koreka.
Wallahi ba inda zanje ka Mata test kayi scanning..... Ya Fara Mata tambayoyi.
Ta yi shiru.. akayi Justin duniya tayi magana taki.
Dole Anwar ya fita. Yana fita sadeeq na isowa....Aisha na zaune tayi zugummm tana kallon ikon Allah.
Doctor menstrual pain ke damuna Amma bana son ya sani. Ina Shan wannan maganin amma baya mun idan akwai Wanda ya fishi pls help me...... Ya danyi murmushi I expect it.
Ya karbi maganin ta runtse ido tare da dafe cikin lokacin da ya katsa.....
Sorry ya fada tare da mikewa..... Ya dauko wata allura yace Amma fa zata Sanya ki barci sosai, sannan ya rubuta wani magani ya ce gaskiya babu Shi anan sai Kano ko katsina Yana da tsada kwarai.... Ba komai rubuta... Burummm ya banko kofa daidai ya Gama allurar tana murzawa. Ta dalla mishi harara.....
Doctor meye tace Yana damunta?
Yayi dariya it's normal an Mata allura ga magani nan na rubuta Yana da tsada da kudi sosai....... Ya karbe takardar Yana karanta sunan maganin.
Ya fiddo waya..... Hello musbah ga magani Nan Zan turo maka asiyo mun carton dinsa a Aiko Yanzu Yanzu ko ka tado wani ya kawo sannan kace a fada maka maganin menene da Kuma yanda ake shansa.
Kaje wurin nagari pharmacy kace ni na Aiko kaga hamisu a wurin.......
Ya Mika mishi hannu thank you doctor.
Tashi muje.... Idan kin hada Baki da doctor wannan maganin zaisa na San komai.
Idanunta suka Fara nauyi alamar allurar ya Fara aiki.
Allaurar zata sanyata barci sosai fa.....okay.
Ya ce Yana Shirin Kai hannu ya taba ta, ta mike da sauri tare da maka mishi harara...... Yayi dariya Kai yau Ina Shan harara ni Hamza.
Ta fito ya biyota ga oat din ki zauna Kisha Aisha Bata... Ka barshi Zan Sha a daki.. muje please.
Ya kalli Aisha allura akayi Mata Mai Sanya barci shine ke dibarta ga idanunta nan sun Fara canzawa da kunje kada ki yarda ta kwanta bata ci komai ba...... Ko na ajiyeta.... Ya banka mishi wani kallo. Wancen Mai napep din da na tsayar Kuma fa?
Ta kalleshi ka bi sadeeq ku tafi mu sai muje a napep din na gode.
Kamar zaiyi gardama yayi shiru....sai Kuma ya kada Kai okay.
Idan kin tashi barcin ki mun flashing please.
Ta ce toh.
Ya zaro dubu biyu ya Mika ma driver yace mayar dasu inda ka dauko mu.
Ya Dan leka Allah ya bada lafiya Zan kawo Miki maganin kinji ko?
Ta ce toh, tana ta faman lumshe ido..... Jinsa take har cikin ranta. Bata so ya tafi.....ashe shima hakan yakeji.......Sadeeq ya kalleshi abokin Bilkisu..... Ya Kai mishi duka. Shi Kuma ya tuntsure da dariya.....
Ta kalli Aisha kinji yayi waya maganin da aka rubuta a kawo carton dinsa daga Kano.....ta zaro ido carton?
Wallahi....
Bilkisu Anwar ya Fara bani tsoro...Nima Aisha. Anwar Yana bani tsoro. Da na motsa sai yace mun friend.... Ke ya mayar friend wannan abun nasa ya Fara wuce shari'a...Ni saboda ma duk na rikice can daki na bar wayar.
Aisha tayi dariya nima. Wai Kinga yanda ya wani fado kamar an jefo Shi????
Tayi tagumi tawa ta sameni Aisha......
Ta kyalkyace da dariya ai sai ma ya *FURTA* saboda tabbas Anwar gabbb yake da furta Miki Yana sonki alamomi dai sun gama bayyana..... Gabanta ya Fadi ta dafe kirji..... Na shiga uku.....ta galla Mata harara *Baki sonsa?*..........✍🏼 *Zainab wowo*💖
👉🏼💞mowa
👉🏼💕 Unex
👉🏼😡 Alaweez
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣7⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
***************
*KADUNA RIGASA*
Duk ina son ganin ku falona da karfe takwas...
Ya tura ma kowace sako.
Duk sun you zugum suna mamakin wannan Kira , abinda bai taba ba.
Ya rage karar TV.
Agurguje ba lokaci maganar zata dauka ba, da farko Ina godiya da Jin dadin yanda ko wace ke kokarin faranta mun da Kuma dagewa wurin kyautatawa, hakika naga canji a gidan Nan. Allah ya saka ma ko wace da mafificin alkhairi.
Magana ta karshe doka ce Zan saka na neman shawara ko neman izini ba.
Daga yau na Hana ko wace ziyarar dakina matukar ba ita ce da girki ba. Sannan daga yau kada wacce ta Kara bina ko ta shiga sashen dayar ku matukar Ina ciki.
Wannan shine.
Ummi kina iya tashi ki tafi sai da safe...... Ya Mike yayi ciki.
***************
*Federal University dutsinma*
Gaban Bilkisu ya fadi ita Kam ta tsani fitina a rayuwar ta, tayi kasa da Kai tare da wucewa a hankali..... Ya chafko hannunta ya rike gammm, ba Bilkisu da mufeedar ba duk wadanda ke wurin sai da suka fiddo idanu waje.
Yasha mur ya Kara janyo facing cap dinsa ya rufe idanun sa Yana kallon kowa kasa kasa sannan ya maida kallon sa ga Bilkisu Yana janyota baya a hankali Yana fadin ```yaya Zaki tafi ki barni bayan kin San...``` Amma Anwar ka maida mayar dani Yar iska. Au daman saboda wannan sillan Karan kake Mana yawo da hankali....tabbas yau na gane ma ido na.....
Sake mun hannu Bilkisu ta fada tana doka mishi harara, yayi kamar baiji ta ba.
Ya kalli mufeeda kin gama mu tafi?...... Na gama ai daman ban tsayar da Kai ba ko?
Ta fada tana huci.... Ya ja hannun Bilkisu suka wuce..... Kwallah suka zubo Mata sharrrrrr ta fizge hannun ta da karfi yayi saurin kallonta cikin hula Yana Mai daga kansa sama..... Kuka again?
Ya fada Yana kallonta.
Ni zaka zubda wa mutunci a gaban bainar jama'a? Ana ganina da kima da mutunci.....ke! Wai me nayi?
Hannu na da ka rike ni muharramarka ce? Ta zaro mishi ido. Yayi murmushi Bilkisu rigima, na lura duk duniya ba abinda Kika fi so da kauna irin na taba ki saboda na fada Miki cewar matukar Ina tare dake ban sallameki ba Kika nemi Bari na ki tafi wallahi ko a gaban waye Zan Kama ki, me yasa ke baki ganewa kiyi mun biyayya?......
Bazanyi biyayyar ba, na ce bazanyi biyayyar ba.... Ta nuna Shi da yatsa jira kaji Anwar na lura da take taken ka kana son mayar dani irin su mufeeda da ke binka suna maka biyayya kana musu yanda kaga dama ko?
Saurara da kyau, bana tsoron ka , bana shakkar ka na gaji da wannan dokokina naka marassa Kan gado.
Ka tafi kaje mufeeda is ready for that not me.....ta hada hannuwa alamar tana rokonsa abeg leave me alone.... Ya rungume hannuwa duka a kirji ya tsareta da ido kawai Yana kallo.
Ta mishi kallon up and down ta wuce tabarshi a tsaye.
Yabita da ido har ya daina ganinta...
Yayi shiruuu, me yasa bazan kyale yarinyar can ba?
Anya Bilkisu ta damu dani kamar yanda nake jinta azuciya?
Me yasa ta fita daban cikin matan jami'ar nan take bani wahala ta kasa gane irin qimar da nake da ita.?
Wai ko wannan haukan da Yan Mata keyi a kaina me yasa ita bazata ringa mun yanda nake so ba don su fahimci tafisu?
Mtsewww yaja dogon tsoki, sannan ya fiddo waya ya kira sadeeq, *zo ka daukeni*
Yanayin muryar sa kawai yaji yasan an Kara kwafsawa .
Kicin kicin ya iskeshi bakin gate ya hau mashin din kawai suka tafi.
Yana zuwa daki ya fada bisa gado yayi ruf da ciki....
A bakin kofa ta hadu da Aisha ta bita da kallo kafin ta rufa Mata baya suka nufi dakin Aishar........ Yau ma kuka?
Kuka Zaki ringa mishi lallai kina da aiki...... Aisha bana son abinda Anwar kemun kawai a gaban su mufeeda ya rikon hannu Kuma ya rikeni yaki saki saboda Allah me zasu daukeni?
Ke yau ai na shiga uku Kinga kallon da kawayenta ke mun da ita kanta....... Ai dole. Kut! Wallahi dole su kalleki, Al'amarin Anwar ya Fara ta'azzara gaskiya Kuma Shi yaki fitowa ya Fadi ainahin abinda ke ransa ...... Yana jiran ni na bishi irin su mufeeda haka na lura amma wallahi ki barshi idan yasan wata bai San wata ba.
Ta wuce dakin ta don ta gabatar da alwalar magriba.
Ta kashe wayarta kada ma ya kirata,
Washe gari tara suke da lecture, akayi sa'a malamin ya zo. Ya bayar da first assignment cikin part of outline din da zasuyi semester din, Anwar na baya can karshe idanun sa na Kan Bilkisu dake tsakiya ita da su Joseph, lokacin da ya fita ne ta karbi littafin Joseph din tana rubuta inda aka wuce ta. Tana gamawa ta mike Anwar ya kwada Mata Kira.....
Bilkisu.... Ta waiga da sauri saboda yanayin yanda ya daga murya duk ya janyo hankalin wadanda Basu Kai ga fita ba.
Zo ki zauna anan ya nuna Mata kujerar dake gefensa ..... Kowa ya tsareta da ido Yana jiran response dinta,
Me Zan maka? Ta fada tare da tsuke fuska.
Kawo mun note dinki zanyi using ...... Bai rufe baki ba ta jefa mishi littafin har ya daki fuskar sa, gashi nan idan ka gama gobe Zan karba Ina sauri ta yi hanyar waje.....da gudu ya fito har ya ba wasu tsoro.
Ita kanta sai da gabanta ya Fadi lokacin da ta wurga mishi book din saboda tasan cewa ta debo ma kanta wutar dafa kanta.
Ta yi sauri ta tsaya tare da rike kugu....... Ni Kika jefa?
Ya fada Yana zaro ido.
Ta mishi kallon up and down kafin tace idan kaji haushi ka maido mun littafi na Mana.... Jeki dauka bana so ya fada Rai bace .
Fine , ta fada tare da wuce Shi ta koma class din.
Duk aka kawar da fuska ganin ya biyo bayanta, samm bata lura ba Bata Kuma ji takunsa ba.
Littafin ya fada can karkashin desk ta kutsa can ciki ta Kuma duka tana kokarin dauko Shi, ya shigo sit din ya zauna, ita kuma tana ciki.
Dagowar da zatayi taji ta fada bisa kafar mutum ta mike da sauri innalillahi.... Wai kanka daya Anwar??? Ta daka mishi tsawa.
Idan baki so na Miki abinda Kika tsana ki zauna silently muyi magana wallahi idan Kika kuskura anan zan Miki abinda...... Bazan zauna ba bani wuri in wuce.
Naki na bayar ko Zaki daukeni da tsiya ki fitar? Me yasa kike da gardama Bilkisu???
Kai Kuma me yasa baka da zuciya?.
Yayi murmushi nima Ina neman amsar nan wallahi..... Ta ja tsoki kanka akeji bani wuri.
Ya kalleta alamar ba wasa yayi baya da hular sa , kin san Allah idan Baki zauna ba Zan daura ki a bisa cinyata ki zauna in kuma rikeki har sai na gama maganar da zanyi ko bazan iya ba?
Tayi shiruuuuu, sai Kuma ta zauna saboda tasan karamin aikin sa ne sai dai idan ya aiwatar daga baya ya bada hakuri.
Ya bita da ido Yana murmushi..... Ta Kara tsuke fuska Ina sauraron ka ba ka tsareni da ido ba......
Me yasa Kika tafi Kika barni jiya?
Saboda ka gane baka gabana bana son wannan shisshigin, Kuma na Kara fahimtar fakai bana son kana taba ni na tsani hakan .
Kin tabbatar bana gabanki?
Ta kalleshi shekeke Zan ma karya ne don Ina tsoronka ko kana nufin...... Ina nufin mufeeda ce ta Kara Bata Miki Rai ko?
Mufeeda? Mtseww a'a ka manta.
Idan ba ita bace me yasa Kika hasala sosai Kika tafi Kika barni?
Saboda ka rike ni na kuma fada maka bana so..... Me yasa ke bazaki daina abinda nima bana so ba?
Ajiyeni kayi? Ko kana iko dani da zaka Sanya mun doka kace kuma dole sai na bi?
Kiyi hakuri, ya fada a hankali.
Tayi sokoko ta kasa ci gaba da masifar.
Ya tsareta da ido, Dan Allah kiyi hakuri naji nayi kuskure bazan Kara ba I'm sorry please.
Tayi shiru,
Bana son fadan nan wallahi, bana son kina wannan tada jijiyoyin kina fushi dani bana so ko kadan please kiyi hakuri shikenan ko?.... Ba shikenan ba, sai ka mun alkawarin bazaka Kuma taba ni ba sannan.
Yayi shiruuuu, gaskiya ban yi alkawari ba amma Zan kiyaye.
Ya wuce ko?
Eh, ta fada a hankali.
Mun shirya?
Ta dan harareshi.
Yayi Yar dariya. Mun shirya ko?
Um, ta ce tana murmushi.
Hmmm, Bilkisu kenan kina yarda Kika ga dama.
Karfe nawa Zaki kawon tuwo?
5, ta ce .
Lokacin na gama mutuwa da yunwa ko?
Ba abinci dare zakaci ba?
Waya fada Miki?
Shi zanci a matsayin lunch..... Tuwon???
Yayi Yar dariya yes!
Hmmm,
Zaki kawon irin two din nan?
I'll try. Ta fada a hankali.
Waye Zaki Aiko ko nine Zan turo?
Zan kiraka idan na gama dai.
Ya Mike tashi muje.
Ga book din ta Mika mishi .
Yayi Yar dariya daman ke nake bukata ba Shi ba...... Ta zaro ido what?
Ya Kara yin dariya ya ce Ina nufin ke nake so kizo inyi magana dake ba littafin ne a gaba na ba.
Tace hmmmm.
Suka jera suna tafiya..... Tana tsallaka titi sadeeq ya karaso suka wuce.
Ta zagaya can baya wurin Mai nama ta siyo tsoka Mai kyau ta Shani kilo daya.
Tana shiga ta cire hijab ta Fara hada Miya...( Duk kudi irin nasu Bilkisu baisa anyi sake da koya Mata girki ba ) har catering school tayi ga karance karance da tambaye tambaye saboda girki na daya daga cikin abinda take so a rayuwarta.
Ta shirya miyar kuka Mai Rai da lafiya, naman yayi ruguf a ciki wurin Aisha ta Samo kukar da daudawa saboda bata dasu Kuma Bata Kai ga ta siya ba, anan daman take siye.
Duk wacce taji kamshin sai ta leko. Tana gamawa ta daura tuwon bai wani dauki lokaci ba, karfe daya da kwata ta kullashi a leda, ta janyo sabbin coolers manya cikin kwali Wanda batayi amfani dasu ba daya kawai take amfani da ita karamar tana zuba Miya.
Ta jera tuwon guda Sha biyar aciki.
Ta zuba Miya ga Mai bi Mata duk naman ta kwashe musu kaf! Ta bi da manshanu saboda bata rabo dashi ita ma'abociyar taliyar hausa ce dahuwar daudawa Tasha manshanu.
Ta kwalala mishi ta rufe.
Ta jera a basket ta Sanya mishi gwangwanin biscuit biyu cikin wadanda ya siya Mata da lemuka kala kala, ta dauki basket din da 200 ta fita.
Napep ta tsaida tare da mishi kwatancen hostel..... Zan kirashi ya fito sai ya karba sunan sa Anwar..... Anwar? Ya zaro ido... Anwar din zai fito ya karba? Ta banka mishi harara ka San sa ne?
Ni kuwa na sanshi an bani abinci na Kai mishi kwanaki nafi awa banga kowa ba na Kira abokin sa da aka bani number sa Koda yaji zancen nawa ya kashe waya bai Kara..... Malam zaka Kai mun sakon Nan ko na nemi wani?
Zan Kai Hajiya Amma idan bai karba ba Ina Zan ganki saboda wadancan kayan har Yanzu suna gidan mu...... Kaga compound gashi can??? Ka ce Bilkisu kake nema ta ajiye mishi basket din ta bashi 200 ta juya kawai.... Ya kalleta a yamutse wahalallu.....
Ta kanga waya a kunne tana Kiran sa..... Barci yakeyi kasa rika Kuma yanajin dadin barcin.
A hankali wakar *Because you love me* ta Fara tashi ta cylindion.
Yayi firgigi saboda Bilkisu kadai keda ring tone din.....
Hello ya fada cikin muryar barci.
Ina hanya Zan kawo maka tuwon na kusa karasowa na sameka bakin gate din ku kada ka barni Ina jira......ta kashe wayar.
Idanun sa suka bude tangaran ya bi fuskar wayar da kallo..... Ya Mike zumbur ya zura jallabiya ya fice da silifas kafarsa.
Dai dai tsayuwar Mai napep din Yana hango napep yanufe ta da sauri Yana lekawa..... Kai ne Anwar?
Sai kawai yayi murmushi watau yarinyar nan dabara tayi mishi don ya fito?
Ya kalleshi eh, tare da Mika hannu ya karbi basket din.
Yasa hannu aljihun jallabiya ya fiddo 500 ya Mika mishi.... Ta biya yallabai.
Yayi Yar dariya to in mayar kenan baxaka Kara ba tunda na fiddo?..... Yayi charaf ya karbe Yana fadin wazai mayar da alheri?.
Na gode yaba napep wuta Shi Kuma ya nufi hostel Yana murmushi.
Ya bishi da kallo Yana jinjina Kai. Yanda suke fama da student wurin neman ragi da amsar chanji amma ga wani na kyautar 500, ita Kuma ta biya 200 zuwa kawai..... Wurin Nan akwai magana ya ce kafin ya chilla keken titi.
Sadeeq nata barci bai motsa ba. Yasa kafa ya Kai mishi harbi.... Tashi Dan ubanka Bilkisu ta Mana girki..... Zumbur ya Mike Yana kallon basket din.... Yayi dariya wallahi tuwon ne ta kawo .
Yunwa sukeji Daman, sadeeq ya Fara kwashe lemukan Yana ajiyewa kasa, sannan ya fiddo coolers din, kamshin manshanu ya buge dakin Anwar ya hadiye wani tsinkakken miyau ya gyara Zama .
Baiwar Allah hada biscuit ta debo da lemuka...... Tana so ta rage su ne sun Mata yasa Anwar ya katse Shi Yana murmushi.
Sun kwashi tuwon sosai musamman Anwar kulli hudu suka Bari.
Amma fa yarinyar ta iya girki in har itace tayi.... Ita tayi nasan bazata ba kowa yamun ba ya janyo waya .
Hello ta fada tana Yar dariya..... Ni Kika mayar gaki nan zuwa ko?
Ta kyalkyace da dariya.... Tuwon nan yayi dadi fa ga Sadeeq nan Yana lasar kwano.... Shi na Bari Yana lashewa karya yakeyi ya fada da karfi.
Ta tuntsure da dariya..... Na gode sai na maido kwanonin Allah ya biya thank you so much Bilkisu Mai gadon zinari...
Ya fada Yana dariya.
Ta ce hmmm.
You and this your hmmm. Bye wanna baf. Ya kashe wayar.
Haka kawai taji ranar ta Mata dadi tana nishadi. Wunin ranar wani nishadi takeji.
Akan hanyarsu ta dawowa daga masallaci isha'i take ba Aisha labarin wayar da sukayi cewar yaci tuwon.
Kamar daga sama suka ga mutane gewaye dasu hada maza..... Gabansu ya Fadi suka tsarata ainun Aisha tayi karfin hali tace lafiya?
Mufeeda suka gani ta fado gabansu tana taunar chingam.
Ta kalli Bilkisu ke karamar Yar iska ce wallahi.... Ni zakiyi ma karuwanci?
Akan Anwar har kisan Kai Ina iyayi na rantse da Allah ta daga hannu zata kwada Mata Mari akayi charaf da hannun aka rike Shi ta baya.... Kowa yabi hannun da kallo zuwa inda aka Kama don suga waye?
Anwar ne yasha boyel fari kansa da hula kube ya murzata irin sa hular kanawa sai kamshi ke tashi, hannunsa dayan rike da basket........✍🏼
*ZAINAB DAHIRU WOWO DUTSINMA*💖
*KAUNAR KI AZIMUN CE Ina yinki over RUKAYYA BAKO DANBATTA* *ZAINAB WOWO NA JIN JINA MIKI ALALH YA SHIRYA ZURI'A AMIN*
A ringa mun uzuri, Ina zuwa aiki, Ina da miji Ina da Yara kafin na Fara rubutun na fada I won't be able to post all the time na Fadi haka saboda Ina da hidindimu.
Alawiyya ciwon ciki🗣🗣🗣🗣🙄🙄
0 comments:
Post a Comment